hoto ?”
”muma bamu san wanda ya daukeku hoton ba amman dai Kinsan dole idan kana yin abu mara kyau wata rana sai allah ya tona maka asiri gaban maryama ya sake bada rasss yan office din sun kasa yarda cewar kece ni kuma na tabba tarwa yan office din nan kice dan wadan nan hotunan basuyi kama da had’awa akayi ba Sul .”sultana“ sai kuma tai shiru ta kasa cewa komai kema kin mamakin yarda asirinki ya tono ko ?”sul..” sultana !ai kafin ta cigaba da magana sultana ta juya ta bar office din da sauri “ya rab garin yaya hakan ta kasance ta fad’a tare da dafe goshinta cikin tsananin tashin hankali cike da zafin zuciya ta dunkule hannunta tana son tono wani abu .”bata san sanda wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata ba .”


Sultana na fita ta kira aunty abida “aunty baki ga yadda hankalinta ya tashi ba ai kad’an ta gani tabbas kuwa dan wannna hoton na maryama da adam duk sai na yad’asa a social media kinsan har aunty’s dinsa na turawa uhm ai wallahi sai na bashi mamaki nasan sai yayi haukan neman wanda yayi masa wannna sharrin sai dai bazai sani ba tana magana tana juya bayanta wannna haka ne amman kafin ki yadashi ki barshi iya tsakanin ma’akata da yanuwansa ko yanzu zata fuskanci tsana mai tsanani daga garesu sauran aikin ki bar min ni zan qarasa nasan adam dole zai tsaneta kuma idan akwai wani abu acikin zuciyarsa akanta dole zai hakura wallahi aunty sai kinga kallon tsanar da ma’akatan office dinmu suke wa professional maryama yau ta qarasa maganar tana murmushin farinciki “ai tunda taso shiga rayuwamu tofa ta saka kanta cikin tsaka mai wuya kafin mutuwarta dan ba iya ma’akatan zamu tsaya ba har duniya sai sun san halin da tantiriya irinta take ciki a wajen aiki sultana ta sake washe baki kina jina sultana ?ina jinki aunty” Kiyi taka tsantsna kada a gano shirinmu ne baki da matsala aunty Kinsan irin farinciki da nake ciki kuwa ni nama fi son hotunan su isa gidansu kamar anyi an gama dan Allah aunty kiyi duk yadda zakiyi ya aureni nan kusa kafin ya auri wata dan jikina yana bani zai auri wata ne bani ba “babu wacce zai sake aure dan ko wacan shegiyar yarinyar daya aura rashin baki kusa ne yasa ya auresa ,ki kwantar da hankalinki ko da tsiya koda arziki sai kin auresa muddin ina raye ke ko zanyi yawo tsirara sai adam ya zamo mallakinki yanzu haka akwia wani malami daakayi min maganrsa matsa larsa shi sai ya kwanta da mace kafin yayi aiki ,naga bazan iya bari wani katon banza ya kusanceki ba dan haka nace a samo min mai dama dama .”
“ gaky aunty a nemo wani dan bazan iya yarda wani malamin can ya ta’ba min jiki ba bare har ta kai ga sex ta qarasa maganar tana jan tsaki.”



bangaren maryama kuwa cikin tsannin tashin hankali tace “na shiga uku ta soma kuka tana zariya tabbas tasan itace da mr ata to waye wanda yayi mana hoton ?tayiwa kanta tambayar da bata da mai bata amsa to yanzu menene riban wanda ya daukesu wadan nan hotuna ?cikin tsananin tashin hankali ta koma gefe ta rike kugunta tana mai jin bakinciki tana magana hawaye na zubo mata ta qarasa ta d’auki pencil ta tura cikin bakinta ta cigaba da zariya kafin ahankali ta koma ta jingina jikinta da bango bata an kara ba sai gani tayi an miko mata cup din pencil din gbdy wanda ke d’auke da tarin pencil mai yawa take ta dago idanunta dake cike da ruwan hawaye tana dubansa “tunda kina ra’ayin cin pencil ga qari na kawo miki ki cigaba da ci har ki koshi “ta tsura masa ido tana goge hawayenta tare da cewa “no sir bana bukata !”ta qarasa maganar tare karbar cup din pencil ta ajiye da qarfi akan table wanda yasa abokan aikinta sake maida hankullansu garesu “da alamun fa shi wannan mutumin bai san halin da’ake ciki ba ?maryama ta fad’a akasan ranta tana duban abokan aikinta da suka zuba masu ido “ban san dadin me kike ji acikin cin pencil ba da kullum yana cikin bakinki “tai shiru bata ce masa komai ba sai ma sunkuyar da kanta tayi “am talking to you !”ta d’ago kanta da sauri tana cewa “me kace sir ?matsota yayi yana cewa “meke damunki mryam!?kullum kuka kuka bakya gajiya da kuka?shiru tayi ta kasa cewa komai sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin tashin hankali ,ganin taki yin magana ya sauke numfashi tare lumshe idanunshi ya juya ya fita adaidai lokacin da take qoqarin yi masa bayani ya kiran sunan some !tace yes sir ta bishi zuwa office “maryama tai shiru tana dubansa tare da madam some tana zance zuci “ya kamata kije kiyi masa bayani abinda ke faruwa dan da alamun bai san abinda Ke faruwa ba cike da tsananin tashin hankali ta fito .”



Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 40


Mr ATA yana tsaye tare da madam some inda take masa bayani tare da nuna masa wani file da zai saka hannunsa maryama ta shiga office din a firgice hannunta rike da waya.”cikin tsananin tashin hankali ta qaraso inda yake ta nuna masa hotunansu da’aka tura mata.”Cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata ba’a ta’ba ganinsa ciki ba yake kallon hotunansu tare da maryama ,”ba iya ni kad’ai aka turawa hotunan ba.”gabad’aya duk wani dake aiki a wannan bangaren an tura masa.” ta qarasa maganar tamkar mai shirin zarewa .” a sukwane ya maida kallonsa ga madam some yana cewa is that true ?! yayi maganar tamkar mai koyan magana .”a d’an gigice tace “ye ..yes sir!” “amman mai yasa tunda na shigo baki sanar dani ba ?tayi shiru zuciyarta cike da tsananin tsoro da fargaba “why !”ya fad’a a hassale yana mata wani irin duba mai hargitsa kayan ciki .”amm umm no I mean ..”
“You mean what ?”what’s the meaning of all this ?ya fad’a yana mai watsa mata kallon banza yayinda maryama ta sake shiga tashin hankali “ni yanzu ya za’ayi a goge hotunan nan a wayar kowa dan wannan hotunan zai iya zama barazana ga rayuwata sannan zai iya zama ‘batad’anci ne gareni .”ta fad’a tana goge hawayenta “karki damu mutane please .”!“kina magana akan ‘batad’anci ni bakya tunanin nawa mutun ci? yayi maganar yana zare mata ido kafin ahankali ya d’auke kwayar idanunshi akanta ya soma taku cikin Isa da kasaita yana hura hanci “ni kaina nasani saboda ni mace ce mutane zasuyi tayi dani sannan mutuncina zai zube a idanun mutane mutane zasu dinga min kallon kaskanci “ inna lillahi ni maryama naga ta kaina wace irin maseefa ce na tsinci kaina ciki yau ?”dogon tsaki yaja tare da tsayawa cak yana fuskatarta .”



tsumammun idanunshi ya zuba mata yana cewa “amman waye ya d’auke mu wad’an nan hotunan ?.”
Muryar maryama da jikinta suna rawa tace “ni..”nima bansani ba dan allah ka taimakeni ka taimaki rayuwata kayi wani abu akai kar sunana ya ‘baci a idanun duniya “wani tsaki ya sake ja yana mata kallon ta shiga hankalinta “ some ! yes sir “
“waye ya turo miki hotunan “. Madam some tayi shiru tana kallonsa tare da nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sauya cikin kankanin lokacin tamkar bada son ranshi komai ya faru ba .”“waye wanda ya turo maku hotunan?”ya sake tambayarta a karo na biyu “lallai ina son nasani.”muryarta na rawa tace“ I don’t know the person sir an dai yi amfani da wata number ce .”“okay zan san abun yi amman irin abu haka ya faru kiyi shiru kina kallona ki kasa ce min komai ,abinda ya faru ba wai ya dameni bane amman lallai ina son nasan wanda yake min shishigi acikin rayuwata.”haka ne sir kuma na fahimceka amman maryama ..“kinga ni karki kira sunana ni dai nasan Kinsan komai kawai kiyi duk yadda zakiyi a goge hotunan akan wayar kowa ..”
“Nasan komai fa kika ce ?”maryama tayi shiru ta rasa me zata ce dan sai yanzu ta fahimci ba abinda ya kamata ta fad’a mata kenan ba .”



Mr ata yayi taku biyu ya isa inda maryama take tsaye cikin tsananin damuwa da tashin hankali “kina jina maryama ki natsu zan san abinda zanyi akai kisani ba iya mutuncinki kad’ai ake qoqarin zubarwa ba har da mutuncina ake son zubarwa “.“exactly sir exactly sir”. inji cewar madam some “ni dai babu ruwana da wani mutuncinka ni dai nawa mutuncin nasani kuma ina matukar son shi dan shine silar da mutane dayawa suke sona da ganin mutuncina idan hotunan nan suka fita mai zance ?”me zan cewa mahaifi yata?” me zan cewa umma da habib?” ki yiwa mutane shiru ana .”yayi maganar a matuqar tsawace yana dubanta “saboda mai zanyi shiru ?”ina da ‘yancin da zanyi magana tunda an cuceni an cuci rayuwata”kai nmj ne nifa? duk wanda yaga wad’an nan hotunan bazai sake ganina da kima ba a qarshe ma bazan sake auruwa ba” so what idan kin kasa auruwa dole ne sai wani ya aureki? yayi mata tambayar yana kallonta a d’age “ko ba dole bane mutuncina fa ?itama tayi masa tamabayar tana dubansa da shayayyun idanunta wad’an da suka canza kala tsabar zubar hawaye .”



wasu hawaye yaga suna turereniyar zubawa daga kwarnin idanunta daga inda yake tsaye ya tsura mata ido yana jin yada sautin kukanta ke ratsa kunnuwansa “.“dan Allah sir kayi hakuri ka daina biyewa yarinyar nan “.“sorry may I coming aka fad’a daga bakin kofar shigowa“yes coming! d’aya daga cikin ma’aikatan ne” ma ga wata akan layi tana son magana dake “okay kaje kace gani nan zuwa “okay ma ya fad’a tare da juya wa ,numfashi madam some ta sauke tana dubansa kafin ahankali tace “dan allah gaba d’ayanku kuyi hakuri na wani lokaci yanzu zanje na amsa kira zan dawo muyi magana akan wannan matsalar kuma in sha allahu zamu nemi mafuta akan matsalar “tana gama fad’ar haka ta juya ta fice daga office din cikin sauri .tana fita maryama
ta sake fashewa da wani rikitaccen kuka tana dafe goshinta .”gabad’aya ta rasa abinda zatai, ta rasa meke mata dadi tana jin idan ba kukan tayi ba bata san me zatai ba dan cuta tasan an mata an cuceta an cuci rayuwarta ana son ‘bata mata suna ta qarfi da yaji. sosai take kuka har da shesheka .”ta rasa waye yake son ‘bata mata suna da rayuwarta a iya saninta bata gaba da kowa abinda yake gabanta shi take yi ,bata da matsala da kowa tana qoqarin zama da kowa lafiya “to mai yasa za’ayi mata haka ?” kuka maryama take sosai .”



wani irin tausayinta ne ya dinga ratsa sansar jikinsa har tsigar jikinsa na mikewa,bai san me yasa take d’aukar abu da zafi haka ba,shi a ganinsa wannan ba wata matsala bace ahankali zai gano wanda ke da hannu ciki .”taku biyu ya qara zuwa inda take tsaye tana risgar kuka ya kai hannu zai dafa kafad’arta tayi saurin zamewa tana masa wani irin mugun kallo mai d’auke da gargadi.”cak ya tsaida hannunsa tamkar wanda aka dasa yana kallon cikin kwayar idanunta dake tsiyayar da ruwan hawaye .”cike da sanyin jiki ta samu waje ta zauna ta kwantar da kanta Akan table din dake gabanta tana cigaba da rera kuka mai tsuma zuciya yayinda mr ata yake tsaye yana kallonta jikinsa yayi matukar yin sanyi.”




Ahankali madam some tace “hello good morning !”daga can bangaren aka amsa mata madam some tace “ko zan iya sani dawa nake magana ?”okay okay!! ta fad’a tana gyara tsayuwarta babu matsala akwai su a qasa nuna da desing’s masu matukar kyau da d’aukar hankali karki damu sai dai kuma idan kina da desing dinki da kike so wannan ma babu wata damuwa zan tura miki sako nan da awa d’aya .”“okay thank you “ta fad’a tare da ajiye kan wayar ta juya ko cikakken taku uku batayi ba wayar ta sake d’aukar qara ta dawo da sauri a tunaninta ko abokiyar kasuwancinta ce amman sai taga number landline din mami ne dan haka da sauri ta d’aga cike da girma mawa ta gaisheta “good mrning ma!sannan ta qara da cewa “momy kina son magana da mr ata ne ?”no no! dake nake son yin magana “ni kuma mumy?”madam some tai tambayar cike da tashin hankali “eh !”.“okay ma ina jinki !”ina son nayi magana dake ne amman ba anan ba idan bakya wani aiki yanzu kizo gida kar kuma ki bari adamcy yasan nace kizo don’t tell him anything tai shiru tana sauraronta har ta dasa aya madam some tace”okay ma zan zo yanzu daga office din bata koma office din mr ata ba ta fito zuwa haraban ma’aikata kai tsaye inda tai parking din motarta ta nufa ta shiga ta d’auki hanya zuwa gidan mami .”




Sannu ahankali madam some take murza kan stearing tana adduar allah yasa ba hotunansu maryama da mr ata aka tura ma mami ba yasa take son ganinta cikin kankanin lokacin ta isa gidan a natse ta tsaya a bakin kofar shiga bayan an kira an sheidawa mami zuwanta ta bata umarnin shigowa cike dari dari ta shigo makeken had’ad’den parlour’n inda ta iske mami tsaye sanye cikin shiga ta alfarma cike da girmamawa madam some ta gaisheta ,inda mami ta amsa mata cikin sakin fuska tana nuna mata wajen zauna “ki zauna !”ta fad’a tare da shigewa parlour’nta na biyu .”madam some tayi matukar mamaki ganin yanayi mami wanda yake nuna alamun babu wata matsala ,cike da sanyin jiki ta zauna tana zance zuci to ko mai yasa mahaifiyar mr ata ta tace zo ?gabadaya kwakwalu warta ta toshe tare da jin wata irin mummunar fad’uwar gaba mami ta fito kunneta manne da waya “a’a babu wani abu kawai dai ‘yan tambayoyi zan mata kafin mu san irin macen da zata shigo family dinmu .” macen da zata shigo family kuma?madam some ta yiwa kanta tambaya tana cigaba da duban mami daga can bangaren aunty khadija tace “yanzu ke mami qoqrin kike yayi wani auren bayan ga maryam har yanzu bamu san matsayinta a wajen sa ba bare matsayin cikin jikinta?”ai kuma bazai yuwu khadija ace ya zauna haka babu mata ba, addua kawai zamuyi Allah yasa wannan auren ya zama silar samun kwanciyar hankalinsa da namu gabadaya.“Ameen !”amman mami shi yace miki yana sonta ne ?”



“Khadija ko bai ce min yana sonta ba ,nasan abinda adamcy yake so ni naga hakan acikin kwayar idanunshi wanda ke nuna min tabbas yana son yarinyar .”mami karkiyi haka tukun kinfa san halinsa tunda har bai ce miki yana sónta ba ki barshi kawai har sanda zai bud’e baki yayi miki maganarta karki sake yanke masa hukun cin a karo na biyu ki bar magna yarinya nan kawai “naji duk maganarki, yanzu ma gaskiyar da yake boyewa nake son nasani “.mami ta gama wayar tare da zama opposite din madam some alokacin da masu aiki suka cika gabanta da abinci kala kala “kici wani abu tukun kafin muyi maganar da tasa na kiraki .”madam some ta girgiza mata kai tana cewa “momy kiyi maganarki kawai dan right now akoshe nake “okay daman akan yarinyar nan ce maryama “.nan take gaban madam some ya bada ras tayi saurin gyara zamanta “nasan kusan kece mai kula da duk wani bangaren adamcy ,nasan zaki fi kowa sanin meke tfy abangarensa.”



“haka ne mumy “! yauwa some ina son ki fad’a min meke tsakaninsa da wannan yarinyar?“madam some tai shiru tana dubanta cike da matsanancin mamaki kenan abida suke zargi tsakaninsu itama mahaifi yarsa tana tunanin haka atsakaninsu “some karki boye min komai ki fad’a min abinda kika sani nayi miki alqawarin bazan bari ya sani ba ,shiyasa ma kikaji nace karki bari yasan zakizo madam some ta tsura mata ido tana kallonta da nazarinta kafin ahankali ta numfasa kana ta soma magana “a zahirin gaskiya mumy bansan akwai wani abu a tsakaninsu ba yadda kika min tambayar nan haka na tsare maryama nayi mata sai dai maganganun da suka fito daga bakinta ba masu dadi bane ,domin maganganu ne masu zafi sannan da nuna alamun babu wani abu a tsakaninsu wanda ya wuce aiki sai dai ko ta bangaren sir ko shi yana son yarinyar bamu sani ba ko da yake shi din ma gaskiya bazamu iya tabbatar da hakan ba ,dan wani lokaci kinsan halinsa birkice mata yake yayita wasu abubuwa ta yadda mutun bai isa ya fahimci komai akanshi ba .”



tunda madam some ta fara magana mami ta zuba mata ido tana kallonta tana jin fad’uwar gaba har sanda madam some ta dasa aya kana ta numfasa tace “yanzu dai kina nufi babu komai tsakaninsu?” gaskiya mumy ni dai a iya sanina babu komai atsakaninsu sai muamula ta aiki “numfashi mami ta sauke tace” to shikenan na gode sosai”! babu komai mumy ta mike tsaye tana cewa” ni zan koma office saboda sir yana jirana,” okay sai anjima “.
madam some ta d’an rusuna tanawa mami sallama inda mami tabi bayanta da kallo dan taso taji kyakkwan labari daga bakinta “kenan dai gaskiya adamcy ya fad’a mata babu komai a tsakaninsu da yarinyar ta d’auki lokaci zaune tana zurfafa tunaninta dan ta rasa dalilin da yasa zuciyarta
Showing 135001 words to 138000 words out of 176292 words