farouq tashiga azaune ta sameshi yana aiki a system ya d'ago ya kalleta yana murmushi, "breakfast is ready Habibi" tafad'a yayinda ta fara bud'e warmars Dan tayi sarving nashi, Murmushi yayi batareda yace komaiba kasancewarshi bamai surutu bane sosai, harta gama zuba mishi yana kallonta tad'auko masa rua da lemo a fridge, "bismillah" tace masa yayinda itama ta daidaita idonta akan kyakkyawar fuskarsa, "amma dai tare zamuchi ko?"
Ya tambayeta, far tayi da idonta tace "nawa na office d'ina, bye zandawo ingani inbakaci dayawaba"
ta cije lip d'inta na kasa Ta girgiza kanta gamida zare masa ido shikuwa tagumi ya zafga ya zuba mata ido harta fice batareda ya iya cemata komaiba


_5:40 pm_
Fahima CE Zaune a garden itada farouq sunata hira gefensu kayan fruits ne dayawa sunad'an CI da drinks masu sanyi gamida ruwan c'est born, zaune suke akan darduma suna fiskantar junansu, wayace ahannun farouq yanata d'aukarta photo bayan sungama hira suka mik'e domin tafiya farouq ya matso daf da ita sannan yad'aukesu pictures (selfie) masu kyau tana murmushi, cikin natsuwa suka fito suka Nufi wajen car pack domin ya tafi, kana ganinsu kasan soyayyah ta ginu anan sosai harwani haske na musanman sukeyi, but d'in motarsa yadauko wata katuwar Leda ya mik'a mata, sosai tayimasa godiya ta nuna jin dad'inta dukda tafishi kud'i yana k'ok'arin kyautata mata ita kuma tana yabawa komai k'ank'antar abinda farouq zaivata tanajin dad'insa gani take yafi Wanda abbanta zai siya mata, ahaka sukayi sallama ya tafi suna masu son junansu, toh i kon Allah kenan!


Salahuddeen kyakkyawan matashin saurayine maijida kud'i, ilimi, wayewa uwa uba kyakkyawane ga gata, yataso cikin kulawar iyayensa duk abinda yace yanaso iyayenshi sunaso kuma suna bashi Komai yawanshi ko tsadarshi, Dan haka ya shagala da duniya yake shan cocaine da whiskey da wasu abubuwan na kayan maye .

Yau takama talata sukazo Dutse shida Daad d'insa da k'annen Dad d'insa ( uncles) sunkawo sadakin auren Fahima dubu 500 wanda akasa rana watanni 2 masu zuwa, Abban Fahima ya yi haka da shawarar Y'an uwansa batareda Ammi ko Fahima sunsaniba


A b'angaren ango Salahuddeen sai dad'i yakeji yanata shirye2 Amma tunsanda aka karb'i sadakin Fahima baisake kirantaba itakam ganima tayi ta huta da jarabarsa, Ana sauran wata 1 biki Abbanta ya sanarda Ammi akan taje tayiwa Fahima siyayyah a Saudi Arab, Abin yabata mamaki matuk'a kuma ya b'ata ranta "yaza ayi Alhaji ka yanke kalan wannan hukunchi?" Gaskiya nikam bada hannuna awannan lamarinba, Auren dole zakayima Fahima kenan?" "Dakata Hajiya waya gayamiki Auren dole zan mata? Salahuddeen yafad'amin cewa sun dai data," Ammi ta dakatar dashi dacewa "k'arya yake Alhaji Fahima Farouq takeso bashiba,"
" Farouq? Waye Farouq? Meye aikinsa? Waye ubansa A Nigeria ko jigawa?" Alhaji sageer ya tambaya yayinda ya nad'e hannunsa abayansa ya kafe Ammi da ido yana jiran Amsar tamvayoyin dayaimata.


_Toh fa_馃

鉁嶐煆� 漏 _*cwtjiddah*_馃挒
[3:00PM, 4/4/2017] 鈥�+234 706 774 5996鈥�: . 馃専
馃崄馃崄馃崄
馃暩馃暩馃暩馃暩馃暩
鈽傗槀鈽傗様鈽傗槀鈽�
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�
_*BABBAN RABO*_
_( An Untouchable Desire)_
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�

*In dedication to UMMEE GARKUWA*

_*55 to 60*_

Cikin k'arfin hali Ammi ta bashi amsa cewa "Farouq ne, yaro mai hankali da tarbiyyah ga sanin girman manya..."
".. dakata"
Abbah ya katseta tareda d'aga mata hannu, "mekike nufi? Dake aka had'a baki ake munafintana wato Fahima hartana soyayyah da wani kuma har gidan nan yake zuwa batareda izini naba?" Ammi tace
"meye laifinsa? Gaisheni yake zuwa yi" murmushin takaici Abbah yayi tareda cewa

"Ba shakka aike zaki d'aura mata auren naga alama, toh kisani Yau saura 1 month auren Fahima inkinga dama ki shirya inkinga dama kizauna haka", yak'ara da cewa

"aure da salahuddeen Ba fashi wallahi itama fahiman zatazo ta sameni" ihun da Fahima tasa ne ya dawo da ganin Abbah gareta hakan yana nufin taji duk abinda sukayi da Ammi, da gudu tazo ta rungume Abbanta tana kuka mai sauti har cikin ranshi yakejin kukanta duk hankalinshi ya tashi ta fara magana, "Abbanah inason Farouq Dan Allah karka rabani dashi ! shima yana sona!! wallahi Abbah karabani dashi karabani da farin cikin a rayuwata"

ta d'ago kanta tace Ammi ki fad'a masa yafasa min auren dole Farouq yanada rufin asirin dazai rikeni shine P.A a company na, dasauri Abbah ya tureta yace "ke mahaukaciyar ina CE Fahima? Wanda kike biyanshi albashi shine zai aureki? Dame? to wallahi ahir d'inki shashasha kawai, kuma Yau saura 1 month aurenki wallahi babu fashi"

wani murmushi Fahima tayi tareda share hawayen idonta tace "tunda nataso akemin abinda nakeso koda zai bak'anta ran dubban jama'a, duk abinda banaso haramtattcene akan kowa, sai yanzu danasan Human right shine za amin auren dole?"
Saukan mari Fahima taji wadda ya gigitata "bakida hankaline Fahima ni zaki fad'awa maganar banza? Shekarata 32 ina harkar siyasa ni zaki fad'awa human right? To wallahi kinji na fad'a miki saikin auri salahuddeen ko kinaso ko bakyaso" dariya Fahima tayi sannan tace "ka rantse na rantse zamuga wazaiyyi wining waye kuma zaiyi kaffara!!!!"

fuuu ta wuceshi ta haura sama tabarshi yanata ban bami shikad'ai, Ammi wanda tunda suka fara tayi mutuwar tsaye baki bud'e, k'arar buga k'ofar yayi bayan yaficene yadawo da ita haiyyacinta.


Zama Ammi tayi dabas akujera tana maimaita innalillahi wa inna elaihirraj'un idonta na fitarda hawaye, Alhaji ka cuci rayuwarmu wajen tarbiyar da kayiwa Fahima na gata abinda nake tsoro kenan gashi ya fara faruwa, ( wannan matsalar tana yawan faruwa iyaye mu rink'a kulawa Akan hakan bawa yayanmu gata Ba laifi bane Amma gatan Ba kowanne kalaba dole zaka so naka Amma tarbiyyah yanada kyau wasu basu tsawatarwa yayansu idan sunyi Ba Dai daiba zakuga yara kanana sunacin zarafin manya wasuma sunyi jika dasu just bcse they 'r poor sukuma Allah ya azurtasu basa fahimtar duk Allah ne ya haliccemu, wasu kuma daga cikin iyayen awurinsu yaran suke gani suma suyi daga k'arshe asamu matsala kaga yaran sunfi k'arfin iyayensu hartakai anfad'a wani hali Allah ya Sa mudace)

Bayan Fahima tashiga d'aki ta fad'a gado tasa kuka, saida tayi mai isarta sannan ta tashi tahau fasa glasses d'in d'akin tana ihu, da gudu Ammi ta hauro sama ta sameta tanata rik'eta itakuma tana kwacewa tana cewa "Ammi kibarni Abbah ya tsaneni baya sona I hate him Ammi I hate him more than my enemy"
taci gaba da aikin rushe2 mari Ammi ta zabga mata hakan yayi sanadin samowa Fahima natsuwar dole, a fusace Ammi tace "kinyi zaton wannan haukar shizai Sa mahaifinki ya janye kudirinshi na aurar dake ga salahuddeen? Wannan shine abinda nake hango wa nakemiki fad'a Abban ki yak'i ganin laifina, kinga gata kenan" tafad'a yayinda ta k'urawa yartata ido, a hankali fahima ta sulale kasa tana kuka sosai, hawayene ya zubo daga idon Ammi maid'aukeda takaici na ganin yarta cikin damuwa dakuma takaicin zata aurar da yarta 1 tilo cikin b'acin rai da takaichi.

Washe gari fahima ko lek'owa batayiba haka ta rufe kanta a d'aki tana kukan rashin mafita gashi Abbah yayi seasen duk simcards nata so take taji muryar farouq amma Ba hali pics d'insu kawai taketa gani awayarta tana hawaye, maganarda farouq ya mata take tunawa "Fahima banida uwa Ba uba Ba yaya Ba k'ani banida kowa cikin maraici na tashi babu mai taimakona sai Allah shikad'aine gatana, Dan Allah karki gujeni komai rintsi kizama matata yayata k'anwata uwana da ubana kizama dangina Fahima karki barni,"

hawayene yasauko mata mai tsananin zafi tace "am with yhu Farouq habibi bazan barbakaba inasonka farouq I luv yhu ko Abbah zai kasheni bazan masa biyayyah Ba bazan yadda ya rabamuba farooouq" tafad'a yayinda ta sake fashewa da kuka.





鉁嶐煆� _*cwtjiddah*_馃挒
[3:00PM, 4/4/2017] 鈥�+234 706 774 5996鈥�: . 馃専
馃崄馃崄馃崄
馃暩馃暩馃暩馃暩馃暩
鈽傗槀鈽傗様鈽傗槀鈽�
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�
_*BABBAN RABO*_
_( An Untouchable Desire)_
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�

*In dedication to UMMEE GARKUWA*

_*60 to 65*_



Wunin ranarma Fahima cikin kuka tayishi ga tunanin Farouq ya dameta Had'eda tausayinshi Tasan duk inda yake hankalinsa a tashe yake, a daddafe ta tashi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala dayake yunwa ya addabeta nanda nan zazzabi ya rufeta had'eda jiri, dakyar tayi sallah Tana idarwa Amai yazo ta fara kamar y'ay'an cikinta zasu fito sosai ta galabaita, Ammi harta gaji da bugawa Fahima k'ofa ta koma ta d'auko key tasa ta bud'e halin da taga Fahima shiya d'aga hankalinta, da gudu ta k'arasa wurinta tana kiran sunanta tana jijjigata Amma ko motsi batayiba, da gudu ta fito tana kwala kiran drivern ta agigice hakan yajawo hankalin masu aikin gidan suka firfito da gudu suna tambayan Ammi Amma bata kulasuba da gudu ta nufi k'ofar fita sukayi karo da Abbah yana k'ok'arin shigowa ya rike Ammi yana tambayanta Amma ta gagara magana sai haki take tana nuna hanyar d'akin Fahima, "menene acan d'in?" yake tambayanta dakyar tafurta" Fa.. hi..ma..!" tana k'ara nuna hanyar d'akin Fahima,

"meya sameta? Meya samu 'yata"
" ta mutu Alhaji wallahi Fahima ta mutu!" da gudu Abbah ya ruga d'akin Fahima suka rufa masa baya Fahima tana sanye da hijabi pink colour wadda tayi sallah akan sallayar da take zube jikinta duk Amai, da slow ya k'arasa wurinta yana jijjigata yana kiran sunanta a hankali Kamar Wanda aka tsikara ya rarumeta yayi waje da ita Ammi ta rufa masa baya tana kuka, dasauri driver ya d'ebesu sukabar gida suka nufi asbiti mai suna Rasheed shekoni specialist hospital, kasancewar Asibitine mai tsada dawuri kuwa suka samu likitoci suka karb'eta aka hau bata taimakon gaggawa oxygen aka samata da drip kafin likitan Abbanta ya k'araso shine Babban Dr a asibitin, tunda sukazo Ammi take kuka Abbah yana rarrashinta Amma duk haushinsa takeji tunda duk shiya jefa yartasu cikin wannan Halin........Hmmmmm Alhaji Sageer kenan.


Tafe yake cikin farin shet mai gajeren hannu da blue jeans ya d'aura agogon Gucci a hanunsa takalminsa toms ne bak'i gashin kansa yasha gyara a kwance luf2 da sauri yake tafiya ma aikata nata gaisheshi yana d'aga musu hannu kawai Amma yaddah na fahimta basu damuba Dan Ba haka yasaba amsamusu Ba, duba da yadda yake sauri sunsan Abu muhimmi yakawoshi tunda Ba time d'in aiki bane, yana zuwa yawuce d'akina musanman a emergency inda aka kwantar da Fahima yafara dubata, tsawon minti 30 ya fito fuskarsa d'aukeda murmushi "masha Allah" shine abinda na furta yayinda nayi karo da fuskarsa, kyakkyawan saurayi Wanda bai cika fariba, yanada manyan idanuwa farare tas2 da dogon hancinsa mai kyau gamida lips d'insa D'an dadai wanda yasamu kyakkyawan mazauni ak'asan hancinsa, da Sauri Ammi ta mik'e Abbah ma haka, suka nufo inda yake dasuri Abbah ya tambayeshi "Dr yajikin nata?" Smile yak'arayi Wanda yasa na sulale nazauna k'asa batareda na saniba,

"Ba Matsala Alhaji muje kuganta" suka shige d'akin, "baiwar Allah" yafad'a tareda D'an tafa hannunsa firgigit na mik'e littafin hannuna da Biro na suka zube
"'r u OK?" Shine abinda yafad'amin yayinda ya bud'e idonsa sosai, "E eeee am OK" nafad'a cikin in ina sunkuya na kwashe littatafina da sauri gudu2 nashige d'akinda Fahima take yayinda yabini da kallon mamaki daga bisani ya tab'e bakinsa yawuce yana cire hand glove ahanunsa, yakasance mai tausayin mutane musanman marasa lafiya yana taimakonsu da k'arfinsa da dukiyarsa sannan yanajan Mara lafiya ajiki harya bashi taimakon da zai Iya, DR SANI AHMAD kenan Wanda kowa ke kiransa da (Dr sahmed) kwararren likitane a fannoni da dama, educated, rich and young handsome!

Kwance nasamu Fahima tanata sharar baccinta kamar bazata tashiba dukda Dr yace zata iya Farkawa a kowanni lokachi

10 mins letter, Fahima ta tashi dasauri Ammi ta k'arasa wajenta ta taimaketa ta tashi zaune, "Ammi Ina Farouq" abinda ta fara tambaya kenan hakan ya tunzura Abbanta ya daka mata tsawa Amma ko kallo bai ishetaba tadubi Amminta tace "Ammi zanyi wanka, "toh Sweethrt Amma tsaya inhada miki tea kisha zai taimaka miki inkiyi wankan saikici Abinci kinji?"

Muryar Abbah CE ta katsesu yamacewa "dama na fahimchi munafircine ya kwantar dake, toh kisani wannan kwanakin acikin kwanakin da suka rage na aurenkine wallahi babu fashi" murmushi Fahima tayi batareda tace komai Ba ta fara kurb'an tea d'in da Ammi ta bata.




鉁嶐煆� _*cwtjiddah*_馃挒
[3:00PM, 4/4/2017] 鈥�+234 706 774 5996鈥�: . 馃専
馃崄馃崄馃崄
馃暩馃暩馃暩馃暩馃暩
鈽傗槀鈽傗様鈽傗槀鈽�
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�
_*BABBAN RABO*_
_( An Untouchable Desire)_
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�

*In dedication to UMMEE GARKUWA*


_*65 to 70*_

A hankali ta shanye tea d'in hannunta ta mik'e tsaye ta rage kayan jikinta batareda taji kunyar Abbah kota kalleshiba, saida takai bakin k'ofar toilet d'in ta juyo tace "naji Abbah kaima kasani wad'annan kwanakin suna daga cikin kwanakin daya rage kayi kaffara" baki sake yake kallonta ta shige band'akin yarufe Ammi da masifa da zagi kamar wani zararre, ko kallonshi Ammi ma batayiba illah tuk'uk'in da zuciyarta take mata idonta yaciko taf da kwallah yagama masifarsa ya fice a d'akin dai2 lokachin Fahima ta bud'e k'ofa tafito a wanka tana zuwa kusada Ammi taga hawaye nata kwararowa Amminta, cije lip d'inta tayi sannan ta dafa kafad'ar Ammi ta fara bata hak'uri tana share mata hawaye, ajiyan zuciya Ammi tayi sannan tace "ina tsoron Abubuwan dasuke faruwa Fahima, bahaka nasoba banida mafita ga shi dangin mahaifinki haushina sukeji akan maganar Abbanki ma zagina yakeyi, Fahima kiyi hakuri kisawa zuciyarki ruwan sanyi kiyiwa Abbanki biyayyah" da sauri Fahima ta d'auke hannunta daga jikin Ammi tana smile Wanda nidai bansan meyake nufiva, a bakin gadon ta zauna ta Sa kaya sannan ta CE "Ammi" dasauri Ammi ta amsa tana jiran taji Fahima tace wani Abu akan maganar Amma saitaji tace "kizubamin abinchi yunwa nakeji kuma nayi alwala zanyi sallah"
" toh" Ammi tace cikin sanyin jiki ta zuba mata abinchin ta bata har tsawon lokaci babu Wanda yayi magana acikinsu, Fahima tana gamawa ta mik'e tayi sallah dai2 lokachin da k'awarta baby afreen ta shigo d'akin a firgice, ganin kawartata na sallah yasa tayi ajiyar zuciya tukunna tayi sallama Ammi ta Amsa, bayan sun gaisa tace "Ammi wallahi bansaniba sai yanzu inata kiran wayarta yak'i shiga shine na kira wayarki wata mai aikinki tad'aga tacemin kuna asibiti Fahimata Ba lafiya" tafad'a yayinda idonta yaciko da hawaye, sautin kukan Fahima yajawo hankalinsu da sauri baby Afreen ta k'arasa wajenta itama ta fashe da kuka tana magana "meya jefamin ke a wannan halin my Fahima? Meyasa zaki wahalar da ni dake da Ammi? Kinaso dukkanmu mukwanta a asbitine habibti? Meya sameki?"

Fahima ta fad'a mata komai da komai kukanta ya tsananta Ammi ta zuba musu ido tana hawaye itama, wayar Afreen ne ya fara ruri ta d'aga tace tana asbiti gani tareda ita toh saika zo, ta ajje wayar

A hankali aka bud'e k'ofar ya shigo da sallama Fahima wadda take kwance jikin k'awarta afreen Ammi na zaune agefe tayi tagumi, "Farouq" tafad'a yayinda ta tashi zaune idonta na fidda hawaye Saida ya fara gaida Ammi sannan yamaida kallonsa ga Fahima Wanda yakasa furta mata komai tsawon minti 5, sannan yace "Fahima wani laifi na aiktawa Abbah daya yankemin kalan wannan hukunchin?" Ya juya wurin Ammi yace "Ki taimakeni Ammi banida kowa said Allah sai Fahima dake mahaifiyarmu Ammi, wallah idan kud'ine inada rufin asiri zan iya rik'e Fahima Ammi kitaimakamin Fahima karki barni Dan Allah !" yafad'a yayinda hawaye yafarabin kunchinsa ya durk'usa agaban Ammi Wanda hakan yasata tashi tabar d'akin Dan dolenta, Afreen CE tayi k'arfin hali tace "farouq karka damu Fahima matarkace insha Allah kaga yanzu magariba tayi kaje katafi gida: girgizamata kai yayi yace "bazan Iya tafiyaba Afreen Fahima batace komaiba hankalina bazai kwantaba" a hankali Fahima tace "share hawayenka Handsome ni takace Alkawarina yananan bazan karyaba I luv yhu now and 4rever Farouq bazan barkaba" smile yayi ya share hawsyensa kafin yace "nagode Beauty I luv u more" ya mik'e kamar bai so ya kalli afreen k'aramin murmushi yai mata ya fita Fahima tace "Afreen Abbah zai kasheni ki taimakamin karya rabani da farin cikina" a hankali Afreen ta mik'e tsaye tace "akwai mafita k'awata, da hanzari Fahima ta mik'e ta fuskanci Afreen ta nason K'arin bayani.



鉁嶐煆� _*cwtjiddah*_馃挒
[3:01PM, 4/4/2017] 鈥�+234 706 774 5996鈥�: . 馃専
馃崄馃崄馃崄
馃暩馃暩馃暩馃暩馃暩
鈽傗槀鈽傗様鈽傗槀鈽�
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�
_*BABBAN RABO*_
_( An Untouchable Desire)_
鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽斺様鈽�

*In dedication to UMMEE GARKUWA*


_*70 to 75*_

Cikin k'aguwa fahima take tambayar k'awar tata menene mafita? A hankali afreen tace Hak'uri, shine kad'ai mafita k'awata cikin tsantsar mamaki Fahima take kallonta takasa furta komai sabida bakinta yayi nauyi dayawa, cikin sanyin jiki Afreen ta jasu zuwa bakin gado suka zauna, taci gaba cewa "rashin amincewarki matsala ne k2awata anan ina nufin rashin biyayyah ga Abbah zai Iya jefaki halaka duk da nagari baya sab'awa iyayensa komai 'kunci dazab'insu zai sakashi amma sanadin biyayyah zakiga mahaifa sunji dad'i sunmiki addua hakan zaisa kiga zab'in yazame miki alkhayri ta kowanne b'angare, zakiga kina tunanin an musguna miki amma sanadin biyayyah saikiga kinsamu farinciki da cigaba arayuwarki, k'awata inaso ki kasance mai hak'uri kidubi rayuwarki ta baya Kituna babu
Showing 6001 words to 9000 words out of 20240 words