ra'ba da Ac suna hutunsu sai dai su tura 'ya'yan talakawa suna wahala dasu idan sun ci kuma su mance dasu. Shi kuwa Ahmad Mahmud mai Abaya da kansa da amininsa Usman Ishak da mutanansa suke komai tare, su kan su mutane mamakinsu suke domin sam Ahmad bashi da girman kai irin na sauran 'yan siyasar k'asar nan.

Kai da fata ya ke abin sa domin ganin jaharshi taci gaba, kullum kuma cikin addu'ar mahaifiyarsa ya ke ya zamo k'adangaren bakin turo kainuwa dashen Allah d'aya tamkar ya dubu Alhaji Ahmad Mahmud mai abaya, kwarjini kamala da dattako ya tarasu matashin d'an siyasa mai kimanin shekaru 40y a duniya kyakkyawa mai kwarjini mutane na k'aunarsa hak'k'un, yanzu haka za'be bai wuce kwana biyu ba za'a gabatar sosai suke yak'in neman za'be k'auyuka da burane, ga Alhaji Sani gwamna me ruk'on k'warya sosai yake ba da gudunmawarsa akan za'ben babu hassada bare k'yashi.

'Bangaren su Alhaji Tafida ma batun haka yake domin sosai suka mayar da hankali na ganin sun ci za'ben nan babu abin da yake fata da buri ganin ya mallaki jaharsa a matsayin gwamna mai ci. Duk wani fata da buri sun d'aurasa a wannan za'ben domin kallo suke ma kamar sun ci sun gama sun kayar da wannan gwamnati ta yanzu.

A ranar da za'ayi za'be sosai abin zai k'ayatar da kai saboda an samu tsaro sosai duk wani abu da zai tayar da hankalin jama'a an toshe, sai hada-hada ake burin kowa ya amshi wannan farar doguwar takarda da jam'iyyoyi ke kai domin samu ya dan gwalawa wanda ransa ke so, anja layi dogo rerass na maza daban na mata daban yarda abin ke tafiya zai k'ayatar da kai sosai. Haka suma masu gudanar da al'amuran za'ben duk suna zaune kowa yana abin da ya kamata da haka ake ta za'ben. Ɓangare guda kuwa wasu mutane a 'boye suna bawa mutane kud'i da niyyar su dangwalawa jam'iyyar hamayya ta PRP kun san mutane da kud'i duk wanda aka bawa amsa yake. (Abin da ke zuciyarsu ne kawai dai ban sani ba🤪suna dangwalawa PRP ko ANPC ko kuwa wata jam'iyyar daban ni dai an hanani gani, duk wanda zai dangwala shi kad'ai yake zuwa bare na samo rahonton wanda suke dangwala mawa lolx🤪).
Habu ne yake ta shiri zai fita. Zarah tazo gabansa ta zauna tana kallon abubuwan da yake ta shiryawa, sosai take kallonsa ta ce"Habu wai shirin me ye kakeyi haka?" Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"Zarah anjima kad'an zamu fita ne domin sace akwatinan za'be na jam'iyyar ANPC da zarar an kammala guri-guri mabanbanta aka tura ko wanne daga cikinmu, ni ne zan sace na wannan unguwar." Zuba masa ido tayi kafin ta gyara zama ta ce"Haba Habu wai mene ne amfanin hakan? Me yasa 'yan siyasar nan suke amfani da ku sannan ku kuma kuna biye musu saboda wasu 'yan k'alilan kud'in da suke baku yanzu? Da zarar kuma anyi za'be shi kenan sun manta daku me yasa bazaku yiwa kanku karatun ta natsu ba. Suna amfani da ku suna jefa rayuwarku cikin had'ari nadama da danasani" Shuru yayi sannan ya d'ago a hankali ya ce"Kusan haka ne maganarki amma ya muka iya tun da mun riga mun amshi kud'insu kawai ki basar abar maganar" ta ce"Habu ba zai fa yuwu ba" Sosai yake kallonta da kalar tata k'arfin halin ta ce"Ina so duk wad'anda za su yi aikin nan kai to ka kirasu akwai wata magana da zan muku."

Ba musu ya d'auki wayarsa ya kira duk wad'anda za su yi aikin tare, kusan awa guda sannan dukansu suka taru. Wani Tsalha ya ce"Wai Baabaa me ke faruwa ne? Kasan fa muna ta shirye-shirye ne akan hark'allar nan" ya ce"karka damu Baabaa ku zauna kuji" Bayan kowa ya zauna Zarah ta fito bin ta sukayi da kallo cikin mamaki Isuhulle ya ce"Baabaa wannan mata mazar kuma fa?" ta ce"Kai dalla kama bakinka" Da sauri ya ciro addarsa ya ce"Ki mini iskanci yanzu in sassaraki." Habu ya ce"Haba baabaa yarinya ce macece fa rabu da ita" Zarah ta ce"Wai kasan ni wacece ma?" Duka suka bita da kallo gyara tsayuwarta tayi ta ce"Ni d'in nan da kuke gani babban mutum ne zai aure ni, nayi alk'awarin idan nayi aure zan baku kulawa zan samarwa ko wanne daga cikinku aikinyi in har zaku hakura da satar k'uruk'un mutane akwatin za'be" Nan fa ihuw ya tashi sai zage-zage suke Isuhu ya ce "Wannan rainin wayan har ina mu tsaranki ne ko an fad'a miki ba mu da abinyi ne?" Kasa cewa komai tayi ganin sai masifa suke, fita waje tayi duka suka biyo bayanta daidai tsayuwar motarsu Ahmad shi da Usman duka suka fito da sauri ganin 'yan sara sukar da suka biyota, tana ganin Ahmad ta saki murmushi da sauri ta k'arasa gabansa ta tsaya tana murmushi suma duka suka tsaya chek suna kallonta, cikin gadara da iko ta ce"Me na fad'a muku?" nuna Ahmad tayi ta ce"Kun ga wannan babban mutum ne yana da kud'i sosai idan kuka fasa k'udurinku to shi zai baku aikin yi da kud'ad'e domin ku gyara rayuwarku nayi muku alk'awari bayan aurena da shi zaku sha mamaki sai kun zamo abin alfahari" Daga Ahmad har Usman sakin baki sukayi suna kallonta cike da mamakin jin furucinta su kuwa abokan Habu murmushi suka fara da sarawa Zarah. Kallon Ahmad tayi sai kuma ta kau da kai da sauri idanuwanta a k'asa ta ce"Ai haka ne ko?" Ta fad'a k'irjinta na bugawa saboda kar ya gwalasheta, zai yi magana Usman ya rigashi daccewa"Naganarta haka ne kuma ni na baku tabbaci." Wani sanyi Zarah taji yayin dasu suka fara ihuw da cewa sun fasa suka shige gidansu Zarah domin su jira zuwanta ta musu k'arin bayani. Ahmad cikin fushi da takaici ya ce"Baki da hankali? Kin san koni waye kike wannan maganar?" ta ce"kayi hakuri don Allah ni ban fad'a da wata manufa ba ina so su yarda dani ne domin subar k'udirunsu." Cikin d'aure fuska da masifa ya ce"Ƙudirinsu na banza da wofi wallahi zan d'au mummunan mataki a kan ki!" ta ce"Am...!" Katseta ya yi"Yi min shuru sakarya daƙiƙiya kawai!" Ya wuce mota. Hawaye taji na bin kuncinta Usman ya ce"Ki yi hakuri Zarah komai zai wuce amma me yasa kika ce musu haka?" ta ce"Wai an sasu satar k'uriyar za'be ne wai ba'aso ko mai abaya yaci kowa shine akace suje su sace ni kuma nace idan basu sace ba zan ba su aikin yi saboda mai arziki da mulki zan aura basu yarda ba suka biyoni shine na had'u daku nace haka."

Sosai yake kallonta kamar idanuwansa zai fito ya ce"kKin san waye mai abaya?" Girgiza kanta tayi alamar a'a ta ce"Ni ban san shi ba na dai san yana takarar gwamnan jahar nan." Ajiyar zuciya ya saki ya ce"Haka ne, abin da kika yi kin kyauta sosai kuma tukwicinki mai tsoka ne." Ta ce"Wanne irin tukwici kuma?" Zai yi magana Ahmad ya banko k'ofar motar a fusace ya fito "Ka ga Malam idan bazaka shugo ba zan wuce" Usman ya ce"Zarah ki koma gida" Hannu yasa aljihu ya d'auko wasu kud'i masu yawa ya ce"Wannan kud'in ki rabawa matasan can sannan ki ba su tabbacin zasu sami aikin yi kar ki ji komai idan na sami lokaci zan dawo" Har zai shiga mota ta ce"uhmm tare zaku dawo dashi" Murmushi ya yi ya ce"Shi wa?" Ƙasa tayi da kai tana murmushi shima cikin dariya ya ce"Karki damu tare zamu dawo" Cike da murna ta shiga gida" Direba ya jasu suka bar unguwar saboda takaici Ahmad ko magana ya kasa yi idan ya tuno abin da Zarah tayi ya ja tsaki ya furta jahila kawai Usman na jinsa bai tanka masa ba.

Ganin kud'in da Zarah ta raba musu suka k'ara yarda tabbas shid'in Zarah zata aura. Wani daga cikinsu ya ce"Nifa mutumin nan gani nake kamai Ahmad mai abaya ne" suka ce"Kai Baabaa sai kace baka da ido mai zai kawo mai abaya wannan unguwar karka mance da matsayinsa mana" Da haka suka banzatar da maganar domin ba sosai suka kallesa ba kuma sun yi shaye-shayensu ba lallai su gane ba, da haka wannan taro ya watse. Zarah ta shige d'aki tana jin farin ciki sosai take jin Ahmad cikin zuciyarta sai murmushi take da ta tuno fuskarsa da haka ta tashi ta d'auro alwala tayi sallah Feesu ta fice ita kuma bayan tasha kankana da lemun da ta siyo ta gyara kwanciya don bacci take ji sosai. _Zarah"Zarah"Zarahta me yasa kika bari wannan mutumin ya shiga zuciyarki kinsan ko shi waye kuwa?Zarahta me yasa kwana biyun nan ki ka mance dani saboda tafiyar da nayi to gani na dawo gare ki Zarahta kuma babu wani da ya isa ya shiga tsakanina da ke._

Muryar Hisham taji cijin masarrafar sautinta. Yana faɗa cikin sautinsa mai amsa kuwwa! Da sauri ta fara waige-waige........✍️


*Last free pages ya ƙare a 20 ƴar uwa hanzarta saya kar ayi babu ke, gawurtattu biyar tafiyar ta musammance. 08104335144*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.


Shaidar biya tanan ??
0810 433 5144

Showing 21001 words to 22503 words out of 22503 words