Mahmud mai abaya babu abin da zai iya yiwa jahar nan ubansa ma me yayi balle d'ansa don haka kar a kuskura a za'beshi. maganganu dai iri-iri irin dai na hamayya da neman za'be da kuma neman farin jini, haka mutanan Alhaji Tafida ke zuwa suna kushe jam'iyyar su Ahmad da nuna kar mutane su kuskura su za'besa, wannan abu da ake yana dawowa kunnan Ahmad yana ji kuma yana gani wani lokacin abin ma dariya yake basa wannan ne yasa masa son yin siyasar gadan-gadan,shi kuwa sai ya nuna musu siyasar ma iyawa ce domin sosai yake fita tarurruka kala-kala da shiga unguyoyin talakawa k'auyayyaku duk yana yad'a musu manufarsa,sosai jama'a ke k'aunarsa domin akace idan ka iya allonka sai ka wanke siyasa iyawa ce.
Tabbas a wannan lokacin Alhaji Tafida ya fara shiga rud'u ganin yadda yaro k'arami ke juya masa k'wanya amma idan yasan wata bai san wata ba,shi ta k'ark'ashin k'asa zai biyo masa.
Yarda Alhaji Tafida ya rud'e zai baku mamaki musamman da yaga za'ben nan k'ara kusantowa yake. 'Bangaren k'arshe ya nufa jikinsa har rawa yake ya bud'e ya shiga,kamar kullum yauma Hajiya Falmata tana parloun cikin shigarta ta alfarma duk irin kuncin da take ciki hakan baisa ta zauna da datti,kallonta ya shiga yi idanuwanta cike da ruwan hawaye ta ce"siyasa ko ina rok'on Allah ya k'ara maka k'aunarta da sonta ita siyasar sannan ina rok'on kar Allah ya d'auraka a kai Allah ya saka maka sonta kar ya baka daman wanda yake so bashi ya cencenta yayi ba,wanda baya so mutane ke sonsa shi ya dace da mulki." Saboda rud'ewar da yake ciki bai iya tanka mata ba d'akin duhunsa ya nufa har yana tuntu'be ta bisa da wani mugun kallo na tsantsar tsana da nadamar saninsa da tayi.
Komai nasa ya kusan tsayawa chek,cikin muryarsa kamar kullum dodon ya ce"Tafida kana cikin matsala fa muna buk'atar jini koma na waye idan ba haka ba komai zai tsaya sannan kai da mulki kuma har abada!!!" Dodon ya ƙare magana cikin sauti cikin rud'u ya ce"ayi hak'uri za'a kawo." Fita yayi a rud'e ya wuce Hajiya Falmata nan,bayan fitarsa Alhaji Mudi ya kira cewa ya bada kwangilar satar yara kamar guda goma ko biyar dodo na buk'atar jini,ya ce"to,bayan ya rufe gidan ya koma gidansa Hajiya Umma ta bisa da kallo ganin yanayin da ya shugo ya ce"bana son takura hutu nake so na awa biyu sannan ya wuce sama" Ta'be bakinta tayi aranta ta ce"Tafi nono fari." Taci gaba da danna wayarta.
..............................
"Haba Ahmad tun da ka fara siyasar nan yanzu naga ko ishasshen lokacina baka dashi." Ta fad'a tana sake narkewa jikinsa,hannu yasa ya d'ago fuskarta ya ce"sai kin min uzuri fa kin san yadda siyasa take." Ta ce"ada ina murna da d'okin mijina zai zama gwamna amma zuwa yanzu na fara sarewa ganin a yanzu ma baka da lokacina mai yawa, ina kuma da ka zamo gwamnan?" ta idasa cikin raunin murya,shafa gefen fuskarta yayi zaiyi magana wayarsa tayi k'ara d'agawa yayi sai gani tayi ya tashi"ok to ina zuwa" Ko kallonta baiyi ba ya fice,hawaye ne suka gangaro mata tare da d'aukar fillow ta rungume da k'arfi sosai take kewar mijinta yanzu bashi da lokacinta sai siyasarsa yasa gaba,kwantawa tayi hawaye na bin kuncinta aranta ta ce"Hafsat dole fa ki nemi mafita idan ba haka ba kuwa zaki shiga uku shi babu abinda ya shafesa,ta sake cewa"to taya ya zakiyi yanzu,ganin ta kasa gano mafita ta saki kuka tana sake rungume fillow cike da son kasancewa da mijinta....
[10/11, 3:22 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._
_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._
*UMMU AFFAN.*🤏
🅿️ 1️⃣5️⃣ & 1️⃣6️⃣
Alhamdulillahi jikin Zahra yayi sauk'i ta sami lafiya sosai, sai lokacin hankalin Feesu ya kwanta wacce ta share kwana biyu tana jinyar Zahran ko fita ba ta yi tana kwana tare da 'yar uwarta haka ma Habu yana k'ok'ari sosai ganin ya sama musu duk abin da ya dace suci.
Musa ma kullum yana shugowa gaisheta ita ma Hanne haka don tare suke wuni da Feesu a d'aka duk abin da Habu ya kawo tare suke ci don ta ce"Ita ma jinyar take ba za a ci ba tare da ita ba.
Zarah sosai taji dad'in jikinta sannan kwana biyun nan tana samin ishasshen bacci ba kamar baya ba, sannan ta dai na ganin Hisham ko don saboda allurar baccin da ake mata ne oho!domin Malam Shehu idan yazo yana mata yace"harda rashin samun barci mai yawa yasata halin da taje ciki,suna zaune da Feesu wacce ta k'wad'a mata k'wad'in rama wanda yaji k'wuli da maggi harda suger kad'an domin ya k'ara almashi sosai kuma taji dad'in kwad'on tana ci a hankali,Feesu ta dubeta tace"Zarah mai yasa baki samun barci?,kallonta tayi kafin tace"mai kika gani?,"Ina tambayarki kina tambayata,to Malam Shehu yace ciwonki harda rashin barci Zarah me ke damunki da kika kasa sanar mini ko Hanne?,shuru tayi kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru Feesu tace"wa kike dasu da zaki fad'awa matsalarki bayan mu?,Zarah tace"nifa babu abinda ke damuna inayin barcina,da banyi zaki ga inayi yanzu?,tace"amma yanzu harda rashin lafiya ke saki barci da allurorin da ake miki",Zarah tace"to ni babu komai kawai dai shawarar da zan baki ki dinga kwana gida" Harara Feesu ta wurga mata tace"da kin fad'a min matsalarki to da sai na duba inda ya dace na temaka amma tunda kin ki sanar dani to ke baki isa kisani kwana gida ba saboda idan ban fita ba ke zaki ciyar dani?,tace"Feesu ba lallai sai kin ba gardawa kanki bane zaki sami kud'i ki nemi aikinyi mana ko aikatau kikayi zaki ciyar da kanki ni da nakeyi dame kika fini?" tace"nafi ki kuwa domin ni kullum zan sami kud'i ke kuwa sai wata sannan ni bazan iya aikin wahala irin naki ba,bazan iya zuwa ina baitawa mutane ba sannan a biyani,tsaki Zarah taja tace"idan baki baitawa mutane ba ai kin sakarwa k'attan banza jikinki suna murza wallahi kece babbar mai aikin wahala Feesu ina jiye miki abinda zaije yazo please ki dena wannan halkar ba hanya bace da zata 'bille miki ba."
Feesu tashi tayi tace"tunda har kinji sauk'i wa'azin naki ya dawo to yau fita zanyi bazan zauna kina gayamin magana ba kamar wata sa'arki." Mik'ewa tayi tare da d'aukar bokin wanka ta fita,girgiza kai Zarah tayi tace"ke kika sani" taci gaba da cin ramarta.
..............................
Saif Alhamdulillah ya kammala karatunsa cike da jin dad'i cikakken d'an jarida kenan wanda ya amsa sunansa,k'asar taso d'aukarsa aiki amma sai yace"zai je gida ya dawo sai ya fara. Domin shi kansa baya son aiki a Nigeria don a ganinsa babu wahalar da zata sashi aiki a Nigeria bashi da wannan tunanin ko kad'an yanzu ma zai koma gida ne saboda dai iyayensa su gansa tunda ya fara karatu yake England ko hutu suka samu bai cika zuwa sai lokaci zuwa lokaci,Rihah ta fisa zuwa sosai hakan yasa wannan lokacin yace zai je daga nan ya sanar musu zai fara aiki a cen,lokacinne su Rihah za su shiga SS2 to ganin cikin hutu suke sai suka taho tare bayan d'umbin alk'awarin da ya d'aukarwa abokansa da 'yan matansa da k'awayensa zai dawo very soon,sannan suka taho,tun a air port suka fara ganin dandazon mutanan da sukazo tarbarsu don motoci uku ne duk mutanan Alhaji Tafita ne,doguwar k'afarsa ya zure daga cikin jirgin zuwa matattakalar benen jirgin,iskar NIGERIA ya shak'a a hankali ya fesar da numfashi tare da bud'e idanuwansa tas,d'an murmushi yayi Rihah na biye dashi a baya har suka sakko,da murna mutanan suka taro su,fuskar nan tasa a d'aure yake takowa cike da izza har zuwa bakin motocin da yaga alamar su ake jira domin yana sakko suke kallonsa da binsa da murmushi yana zuwa aka bud'e masa baya ya shiga haka Rihah ma, sai sannu suke musu bai amsa ba Rihah ce cikin fara'a take amsa musu har suka isa gida,daga ahalin gidan suna tsaye a harabar gidan,tsoho mai ran k'arfe magajin gari haka Alhaji Tafida Alhaji Kamalu Alhaji Auwalu,matayensu da yaransu dukansu suna gurin domin nuna murna da farin cikinsu da kammaluwar katatun d'a kuma babban jika na farko a gidan.
Suna parking duka aka d'unguma bakin motar,cikin takusansa na isa ya sakko ganinsu yasa shi sakin wata fara'a tare da k'arasawa gabansu,gurin Kaka ya fara nufa tare da rungumesa yana jin farin ciki,Duka aka bisa da kallo ana dariya da yawa ciki suna mamakin yarda Saif d'in ya koma girmansa jikinsa da tsayi sannan shigarsa taba kowa mamaki sai-dai da suka tuna yanayin tarbiyyarsa sai suka sallama domin kowa baida bakin magana har kuwa da Kaka domin abin nasu kamar d'aurin baki uwar sumar da ya tara gefe da gefe aske tsakiya mai uban yawa da gani bayan maya-mayan gara har da mai yake mata sabida yanayin laushi da sentsinta ta koma sak irin na k'asar da ya baro,yana shigarsa sun d'auka zasuga yasha wata shadda ko yadi sai dai wasu 'yan manzan kaya wando k'ari wanda ya matsesa sosai daga k'asa daga saman harda wasu igiyoyi ga t-shirt d'insa matsattsiya sosai ta kamasa sai ta kalminsa shima na gayu da agwogwonsa a hannu,tabbas shigar batayi kama da ta d'an musulmi ba sai-dai dukansu sunji ba dad'i aransu don naka naka ne sai dai fa ba wanda yayi magana domin Alhaji Tafida shine kawai ya isa ya zartar da hukunci a zuriarsu hatta mahaifinsu baida ta cewa.(Nasan zaku so kuji su waye wad'an nan zuriar ko?).😂
Haka yayi ta rungumarsu d'aya bayan d'aya,yaje zai rungumi iyayensa mata da sauri sukayi baya,suna amsa gaisuwarsa suna kallon junansu k'asa-k'asa,Hajiya Balaraba taja tsaki mtsuww tare da k'arasawa gaban d'anta rta rungumesa tare da manna masa kiss tace"you are welcome my son" yace"Thank you Mum" ta kama hannunsa sukayi ciki Alhaji Tafida yabi bayansu yana jinsa cikin farin ciki mara musaltuwa ganin yarda yaron nasa ya kammala karatunsa cikin nasara.
Su kuwa saura kallon-kallo sukewa juna duk da haka ba wanda ko wacce tace"k'ala Rihah ta kallesu jiki a sanyaye tace"kuyi hakuri don Allah" SAnnan tabi bayansu,suma kowa wucewa yayi ciki jikinsu a sanyaye.
Saif kallon iyayen nasa yake cikin farin ciki bayan ya zauna yace"sai naga komai ya cenza min ba kamar da ba,ina Abbu da Ammi da su......bai k'ara ba Dad ya d'aga masa hannu da cewa"kowa lafiya bana son ka sake tambayarsu." Zuba masa ido Saif yayi cike da mamaki zai sake magana Dad ya katse shi da cewa"nace kar inji komai" Shuru yayi ita kuwa Rihah k'asa tayi da kai hawaye na zuba.
Bayan yayi wanka sannan suka ci abinci cikin farin ciki daga annashuwa sannan yaje ya gaida Kaka sun dad'e suna hira ya dawo,d'akinsa ya shiga ya duba wayarsa da ake kira,d'agawa yayi zaiyi magana Lubna ta rigasa wata budurwarsa ce 'yar k'asar Gabon ce amma tare suke karatu sosai suke shek'e ayarsu da Lubna wacce take sonsa kamar ranta cikin harshen turanci taje magana"my Saif nayi kewarka wuni guda kawai amma ji nake kamar mun kusan wata bama tare ina cikin kewarka da begenka masoyina,murmushi yayi tare da cusa hannunsa cikin sumar kansa yace"Lubna ko kwana fa banyi ba,nima ina kewarki sosai,kukan shagwa'ba tasa masa dacewa"zata biyosa Nigeria gobe"yace"no Lubna kiyi hakuri tunda nace miki zan dawo to zan dawo ne,da haka ya samu ya lalla'bata,kwanciya yayi don ya huta sai yaji mararsa na masa ciwo,tashi yayi zaune shi yasan matsalarsa domin idan har bai kusanci mace ba akwai matsala shi mutum ne mai muguwar sha'awa sosai,tashi yayi ya cenja shiri sannan ya fito,Umma na Parlour kallonsa tayi"ina kuma zaka Saif?sosa k'eya yayi yace"uhmm Umma zanje ganin gari kwana da yawa rabona da 9j" Murmushi tayi"haka ne amma tunda ka dawo ai saita isheka yau ka huta,girgiza kai yayi cikin shagwa'ba yace"ni dai ki barni Umma nifa ba k'aramin yaro bane,tace"shi kenan my son Allah ya tsare" yace"yauwa Ummana amin" ya fice da sauri binsa tayi da murmushi,Rihah da ta fito yanzu tace"Umma ina kuma Yah Saif zashi?harara ta banka mata tace"ina ruwanki ko shi k'aninki ne?,da sauri ta bi bayansa amma sai fitar motarsa ta gani,yarfe hannu tayi da jan tsaki aranta tace"Allah ya shiryaka Yaya Saifudden.
...........................
"Ahmad in sha Allahu kana tare da nasara addu'a kullum cikin yi maka nake" Ya ce"Mum na gode sosai daman Addu'arku ita muke buk'ata ga nasara nan ina ta gani duk daga cikin addu'arki ne." Murmushi tayi ta ce"Ahmad kai yaro ne mai ladabi a gare ni addu'a dole ce na maka fatana dai idan ka sami mulkin nan kaji tsoran Allah kayi aiyukan da ya dace." ya ce"In sha Allahu zaki sha mamaki sai kinyi alfahari dani sai Daddy yaji dad'i sai yasan bai bar baya da k'ura ba sai yayi alfahari da samuna kamar yarda yake fad'a." Mummy ta share hawayen dake zubo mata ta ce"Allah ya maka albarka kai ma ya baka 'ya'yan da zasu maka." ya amsa da amin. Kud'i ya ajiye mata sannan ya mata sallama sai albarka take sa masa.
"Hafsat ya kamata zuwa wannan lokacin ace mun sami baby boy ko girl ina son naga kin haifa min yara." Zaro ido tayi sai kuma ta rungumesa ta baya ta ce"haba my honey saurin na me haka?ya ce"ba maganar sauri ko dai zamuje asibiti ne a duba mu, jiya bakiji abin da su Alhaji Tafida suka fad'a a gidan radio ba wai taya zan iya kula da mata da k'ananun yara don ban san zafinsu ba, ban haifa ba kar talakawa su dangwala mini." Cikin kissa ta ce"to meye abin damuwa anan maganarsa cen yake idan Allah yayi fa zakayi nima haihuwar nan ina sonta." Hannu yasa yana shafa cikinta ya ce"anya a yau bazan sama mana baby ba,da sauri ta haye cinyarsa tana ta'ba sandar girmansa ta ce"gara dai hakan nan suka fara aikin romantic junansu cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa har akazo ga oganniyar, cikin wani irin salo da k'warewa yake tafiya da ita,itamma sosai ta sakar masa jiki tana aika masa da tana sak'on lokaci k'ank'ani suka fita daga haiyacinsu.
..............................
Da wuri yau Zarah ta wuce gurin aiki kasancewar kwana uku bata zuwa Allah-Allah take ta tafi ga tsoran da takeji a zuciyarta,sai-dai tana zuwa taji, sai ya jiki ake mata abin ya bata mamaki taji ogarsu nacewa"Yayanki da ya nemar miki aiki ne yazo ya sanar mana baki lafiya." Baki bud'e take kallonsu sai-dai ta kasa magana, suna cikin aiki taje wani tebur sai ganinsa tayi zaune, da sauri ta k'ara Hisham ta kira sunansa, Saif wanda yazo gurin tun d'azu ya bita da kallo cike da mamaki,ta ce"Hisham wai me yasa kake bibiyar rayuwata nace maka waye kai kak'i sanar mini al'amuranka suna da mamaki." Kallon abin Saif yake kamar wata durama aransa ya ce"bari dai na biyewa wannan yarinyar k'ilan na samu na rage zafi don a mugun matse nake. Gyara zama ya yi ya ce......
[10/11, 3:26 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._
_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._
*UMMU AFFAN.*🤏
🅿️ 1️⃣7️⃣ & 1️⃣8️⃣
...Ya ce"Saboda ina sonki ne!" Wata harara ta ban ka mashi da cewa" To ni ba na sonka ko ana so dole ne?" Kallonta ya yi sama da k'asa gani ya yi kamar yasan fuskar amma sam ya mance inda yasanta, sai lokacin ya lura da kalar shigarta ya ce"Wai ni da mace ma nake magana ko namiji?" Wani irin mugun kallo ta masa ba ta san lokacin da ta k'arasa gabanshi ba, har suna shak'ar numfashin juna cikin muryar maza ta ce"Dawa ka ga nafi kama?" Kusancin da tayi dashi yasa lokaci kad'an ya diriri ce abin ya tashi waigawa yayi ganin ba mai kallonsa ya zawota da k'arfi sai gata jikinsa sosai ya matse ta yana saukar da numfashi,da sauri ta turesa tana cewa"Wannan iskancin har ina bayan cikin bacci da kake zo min yanxu har a zahiri kenan?" Jin abin da ta ce ya saki wani murmushi a ran sa ya ce"Tabbas wannan za a je da ita dole na sami biyan buk'atata,"Ina ne gidanku?" Ya tambayeta juyawa tayi ta ce"Da da kake zuwa waye ya sanar maka gidan.
Wata irin muguwar sha'awarta yaji ta bijiro masa murmushi ya saki yana kallonta har ta gama aikinta takama hanyar gida yabi bayanta, har sai da ya ga gidansu, tsaki yaja ya ce"Nan ne gidan naku matsiyata aiko dole ma na sami abin da na ke so tun da har naji ina sha'awarki domin babu abin da nake nema na kasa samu.
Sakkowa ya yi ya tambayi wani mutum takaitaccen tarihin mutanan gidan ya sanar masa,ya basa dubu d'aya mutumin sai murna yake,komawa mota yayi yana sakin murmushi da cewa"Zarah kamar na sameki gashi sunanki ya min dad'i sunan yarinyar da nake k'auna ada sannan sunan kakata Fatima Zarah amma hakan ba zai sa nak'i cimma burina akan ki ba 'yan mata" Yaja motarsa ya wuce Club domin ya rage zafi,cen ya had'u da zafafan mata sukayi sharholiyarsu amma duk motsinsa Zarah yake hange,bai ta'ba jin irin abin da yaji ba lokacin da ya rungumeta alamu sun nuna zazzafa ce yarinyar tabbas yana son tarayya da ita. Ranar saboda giya da yasha ta masa yawa a club d'in ya kwana.
...........................
Hajiya Falmata ce ke gyaran parlournta bayan ta gama ta jawo plate d'in abincin da ta ajiye a center table amma ta kasa ci sai hawaye ne ke bin gefen fuskarta idanuwanta d'aure akan k'ofar d'akin duhun su Alhaji Tafida, hawaye kawai ke zubo mata ko hannu ta kasa sawa bare ta taresu domin ko ta tare bazasu dena zuba ba ba,hannu tasa tayi tagumi hankalinta a matuk'ar tashe wannan wacce irin rayuwa ce mai cike da tarin jarabobi tabbas duniya ta lalace abubuwan dake cikinta tuni suka fita cikin ran Falmata sosai take kuka da tuno rayuwarsu ta baya mai cike da jin dadi da farin ciki lokaci guda komai ya tsaya.
Alhaji Tafida shi da Mudi suka shugo,ko d'agowa batayi ba bare ta kallesu,su d'umma basu kulata ba suka shige ciki,girgiza kai tayi tana matsar hawaye Yanayin da suka ga abin tsafinsu abin ya basu tsoro,kallon juna su ka yi. Alhaji Mudi ya rikice ya ce"Me ke faruwa ne?,Da sauri Alhaji Tafida ya fara zufa sai keto masa take wata k'warya ya bud'e sai-dai ya ga abin ciki
Showing 15001 words to 18000 words out of 22503 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6 Chapter 7Chapter 8