guda biyu sai lemun kwalba biyu da kankana da ta saya aka yanka mata.

A jiyewa tayi tana kallonsu,"Hanne me ya faru ne?" ta ce"Daga farkawa ya fara zage-zage kinsan dai halinsa wai sai yaje ya rama" ta ce"Ai da kin barshi, kai yanzu bayan wannan bugun mutuwar da suka maka kake son komawa tabb, ni dai ga abin da na kawo muku nan kuci muje ka biya likitoci kud'insu kafin ka tafi'' Da sauri ya zaro ido"Daman baku biya su ba?" Hanne ta ce"Da me zamu biya su?" Bai ce komai ba suna cin abincin Zarah ta ce"Bari na koma ni idan kun gama sai kuje ku biyasu kun ga lokacin tashina baiyi ba daman nazo na kawo muku na koma ne." Duka suka amsa da"To ta fita tana bonsewa, Suna gamawa Musa ya kalli Hanne ya ce"to Hanne idan kin shirya ki tashi don wallahi guduwa zanyi ko sisi bana magani." Hanne ta sake tura dubu hudun nan a ha'bar zani domin da duba daya suka yanki kati sauran canjin Zarah ta fita dasu k'ila dasu ta musu wannan siyayyar,ta ce"to amma idan suka kama mu fa?" ya ce"ke dai idan zaki gudu kizo muje" bayansa tabi sukawa yi waje da yake su uku ne a d'akin masu lalurar biyun duk bacci suke su kuwa 'yan jinyar suna waje, da haka suka samu suka bar asibitin.

Suna fita suka fara gudu kai da ka gansu ka ga munafukai, da haka suka koma gida bayan sunyi nisa da asibitin suka sami keke napep suka koma.

Sosai Hanne ke murna ganin ta sami kud'inta har dubu hud'u lallai tana cike da farin ciki da murna hakan yasa bayan ta tabbatar Musa ya fice ta je shagon Bala me kanti ta sayi katon buredinta ta sayi lipton milo madara da siga sannan ta sayi kwai guda biyar, sai da ta k'arar da dubu biyu sannan ta dawo cike da murna tasa ruwan zafi tana wak'arta"Ladi mai kid'an kwarya asha kid'a asha dad'i ari!!!waiwaya baya ari!!!ta saki dariya tare da turo mazaunai baya ta buga cinya tace"Ari!!!Hhhhh ta 'ba'b'aka dariya,haka tasha abin ta ta more tana jin dad'inta.
..............................
Wani muhimmin zama 'yan majalisa sukayi akan wannan za'be da zai gudana Ahmad zai fito a matsayin d'an takarar gwamnar jahar Katsina a jam'iyyar ANPC inda sukayi tunanin ya cance
Anta kuma yaro ne mai dattako domin tun bayan rasuwar mahaifinsa mutane da dama suke masa tayin yayi siyasar,haka a gidajen Telavision da Radio babu maganar da ake sai suna son Ahmad Mahmud mai abaya A.M.A ya fito a d'an takara suna son shi suna goya masa baya.

Wannan lamari yazo wa Ahmad tamkar a mafarki, sosai abin ke basa al'ajabi sam tun da ya ga mahaifinshi ya rasu ya cire wata siyasa da burin da mahaifinshi ya d'aura akan sa, har gida wasu k'usa a jahar suka kawo masa ziyarar ban girma da bazata da kuma mik'a k'ok'an bararsu akan ya tsaya a d'an takara,da kuma k'ara masa ta'aziyya,yayi farin ciki da zuwansu sannan ya ce"zaiyi tunani,mahaifiyarsa ya sama da maganar ta nuna farin cikinta ta masa fatan alkhairi,ya ce"Mum da ni bazan amince ba ina tsoran siyasa" murmushi tayi tace"Ahmad a lamu sun nuna cewa baka son mulki, kuma irinku ne ya dace ku mulji ƙasa da jaha, sannan tabbas daman ai ba wanda yake so ya da ce yayi mulki
ba wanda mutane suke so shi yadace."

Ya ce"amma Mum baki ganin nayi k'ank'ata da wannan muk'amin?",ta ce"Saura kad'an fa kayi arba'in ko ka manta ne?" girgiza kai yayi yana murmushi da cewa"A'a" ta ce''to zaka iya nasanka da adalci, ina maka addu'a da fatan alkhairi a duk kan abun da kasa gaba."

"To na gode Mum,Allah ya k'ara girma" ta amsa da "amin" sannan ya mata sallama bayan yaje sun gaisa da Hajiya Anty ya wuce.

Alhaji Sani wanda a yanzu shine gwamna,yayi farin ciki da hukuncin da 'yan majalisa suka zartai domin shi kansa ya ta'ba tunanin hakan balle da ya tuno irin burin da mahaifin Ahmad yaci akan sa duk kan siyasa sai ya bada kai buri ya hau yayi fatan alkhairi domin yasan Ahmad zai fi shi adalci sosai ya k'arfafa masa gwiwa akan hakan.

Hafsat kuwa k'awayenta ta gayyato domin atayata murnar mijinta zai yi takarar gwamna sai wani felek'e take da nuna yanzu ina ta zama matar gwamna domin haka dole tun yanzun su fara bata girma,babu abinda kakeji idan ba tashin kid'a ba,haka sukaci suka sha sannan ta sallami kowa ta gyara gidanta ta saka turare sannan ta saki wak'ar Umar M Shareef ta bazan rayu in babu ke ba,baitin take " _Kaine masoyi na farko,Idan babu kai gani fanko,Kai zana damawa koko,Kasha da dad'i a k'ok'o,Idan na shige ba fitowa ni amarya ohla shakka kai zana cewa angona_.

Sosai take jinta cikin nishad'i gani take kamar gata can ta zama matar gwamna har ta hangota tana magana saman munbari ga maza da mata turmus a k'asanta sai tafa mata suke,wani ihun dad'i ta saki duk da ita ma mahaifinta babba ne domin ita ma d'an siyasa ne mahaifinta a can jahar Kano iyayenta suke karatu ne ya had'asu da Ahmad har sukayi soyayya daga k'arshe ta kaisu ga aure.

Dai-dai lokacin da tayi ihun nan Ahmad ya shugo da sauri ya k'arasa ya d'auka ko wani abunne ya sameta,sai ganinta yayi tana tik'a rawa,sakin baki da mamaki yake dubanta,tana ganinsa ta k'araso da sauri ta rungumesa tare da d'aga hannunsa ta shiga k'asa ta juya,murmushi yayi ya ce"Hafsat na lura kina cikin nishad'i?" kashe sautin tayi sannan ta dawo ta rungumesa ta ce"sosai kuwa,ina cikin murna da farin cikin mijina zaiyi takarar gwamna."

Zuba mata ido yayi har sai da ta hura masa iska tana d'aga kai ta ce"ya lafiya?ya ce"Mulki fa abu mai girma ne Hafsat ke baki min hangen halin da jan shiga ranar gobe k'iyama idan banyi adalci ba kawai ke hangenki na duniya ne" ,Kwantawa tayi jikinsa tana shafa kwantaccen gashin k'irjinsa ta ce"nasan mijina mai adalci ne in sha Allahu zakayi adalci" shafa gefen fuskarta yayi yace"idan ma an za'beni kenan?tace"zama a za'beka kana da farin jini fa Nawan,jan kumatunta yayi dacewa"bari na watsa ruwa"ok muje na taimaka maka"baiyi musu ba ta fara cire masa takalmin k'afarsa sannan ta zame wandon shi kuma ya cire rigar,dagashi sai boxer da singlet,tasowa tayi ta k'amk'ameshi tana sakin ajiyar zuciya idanuwanta kuwa tuni suka cenja kala domin Ahmad badai k'ira ba mutum ne cikakke da ko wacce lafiyayyar mace ta kallesa sai taji wani abu ga kamala da kwarjini,ta ko ina take aika masa da sak'on ninta inda shima ya d'auka,daga nan suka cilla duniyar ma'aurata.
.................................
Wannan lamari sosai ya tada hankalin Alhaji Tafida ya ce"wannan rainin hankali na majilisa har ina me yaro kamar Ahmad zai iya a siyasar k'asar nan?! Alhaji Mudi ya ce"sannan yaro ne da ya karanci wannan harkar ta siyasa wallahi kanaji ko har yafi ubansa k'warewa kasan ita kuma siyasa iyawa ce wallahi ya tafi da hankalin mutane da yawa,idan kaji yarda yake sarrafa maga wallahi ko kai saika sallama masa jiya akayi hira dashi gidan Radio kai kaji tsari da iya zance na siyasa?Sosai idanuwan Alhaji Tafida suka fito yace"ai jin da nayi ne yasa na maka maganar amma idan yasan wata bai san wata ba,wallahi sai nasa mutananmu sun je gidajen Radion sun zauyano k'arya da k'arerayi nasa wasa ne yanzu muka fara Siyasar wallahi sai na zubar masa da duk wani k'udurinsa.
.....................
Saif ne kwance bisa kujera a k'asar ta England gefe da gefensa mata ne su biyo turawa babu abinda suke bayan ta'ba ko wanne 'bangare na jikinsa ya tsotsi wannan ya juyo ya tsotsi wannan haka suke cikin wannan mugun halin ga kwalaben giya reras gabansu,dai-dai shugowar Rihah tana ganinsu a haka ta saki k'ara da kuka gaba d'aya suka dawo haiyacinsu......
[10/11, 6:25 AM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._



_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA.✌️_


*UMMU AFFAN.*🤏


🅿️ 1️⃣3️⃣ & 1️⃣4️⃣


...Gurin ta duk'e tana ci gaba da kukanta mai ban tausayi, da sauri ya sallame su tare da k'arasowa gabanta, ya ce"Am sorry my Sister!" Hawayenta bai dai na zuba ba ta d'ago jajayen idanuwanta ta ce"Haba Yaya Saif, wannan ba al'adar duk wani d'an musulmi bahaushe bane, me yasa ka ke son 'batawa zuriarmu suna?" Hannu yasa tare da d'agota tsaye ya ce"Bazan sake ba kin ji 'yar k'anwata." Hawayenta bai dai na zuba ba ta ce"Na nawa kuma? Sau nawa ka ke cewa ka bari kaci gaba. Kuma ni dai addu'ata a kullum Allah ya shirya min big bro d'ina" Hannu yasa ya share mata hawaye ya ce"Yawwa sis addu'arki nake buk'ata." A kwatinta ya fara ja hannunshi rik'e da nata zuwa bedroom d'inta, bakin bed ya zaunar da ita shima ya zauna tare da cewa"Ya kika baro mutanan Kt?" ta ce"Kowa lafiya suna gai sheka" D'an murmushi ya yi"Ok ina amsawa, kici abinci ki huta Sis bari na wuce School." "To Yaya sai ka dawo" Fita yayi ita kuma ta cire hijabinta tana linkewa a ranta tana nemarwa Yayan nata shiri domin abun nasa yayi yawa.

*KATSINA Ta dikko d'akin kara.*
"Wai ni Hanne lafiya kuwa tun da na dawo aiki na lura yau kina cikin farin ciki?" Murmushi tayi ta ce"Yo ke Zarah da so ki ke kullum ki din ga ganina cikin bak'in ciki to aniyarki ta biki." Ta ce"Dad'ina da ke baki ga ne wa, ke 'yar yawa ce daga tambaya kuma." Ta ce"Ai tambayar taki ce ta zallar rainin wayau." Mik'ewa Zarah tayi ta ce"Ke kika sani kowaa tashi ta fissheshi!" "Yo daman ai ko baki fad'a ba."
D'aki ta shige tana cewa"Sam Hanne baki da ganewa." Daman da alwalarta sallah tayi sannan ta zauna tana tunanin su ko nefar nan ba su da ita balle kayan kallo har kayi ya rage maka zama waya kuma bata cikin ra'ayin Zarah ko Feesu da ta gani da babbar waya bata ra'ayi ko mu gani bata ta'ba cewa ba. Ta dad'e zaune kawai tunanin mutumin da suka had'u shi da matarsa take, sai yanzu take hangen rashin kamarsu da Hisham shi wancen bai kai tsayin Hisham ba sannan ya d'an fisa kaurin jiki amma ta rasa me yasa daga kallon farko ta gansa tamkar Hisham zuciyarta ta bata amsa saboda shine a zuciyarki, Girgiza kai ta fara, tare da furta "Kamarsu ɗaya, me yasa zuciyata da ƙwaƙwalwata kuke yaudarata? Shin aljani ne ko mutum? Tambayar da kullum sai ta aiyanata a zuciyarta sai dai bata da amsarta." Shuru tayi karon farko da tayi tagumi wacece ita? Su waye iyayenta? Wato Musa da Hanne abin da ya fad'o mata a zuciya kenan.

Gyara kwanciya tayi da niyar da safe ta tambayi Hanne, kamar kullum Hisham ta gani tsaye gabanta ya ce"Zarah me yasa kike wannan tunanin haba ya masoyiyata! Ba na son ganinki cikin damuwa sannan bana son ki tambayi Hanne ni da kaina zan sanar miki ko ke wacece kin san dai Hanne ita ce mahaifiyarki." Zuba mashi ido tayi tare da tashi zaune ganin haka ya k'araso gareta tare da zaunawa kusa da ita ta ce"Hisham me yasa baka son na tambayeta?" Rik'e hannayenta ya yi cikin nasa yana murzawa ya ce"Ni nasan dalilin nasan abin da ke baki sani ba don haka ki bar komai a hannuna." "To waye kai?" Murmushi ya yi"Zaki sani duka idan lokaci yayi Zarahta" Sadda kai k'asa tayi tana tunanin wannan curarran abu kuma chakuɗaɗɗan al'amari. Hannu yasa ya d'ago fuskarta tare da girgiza mata kai, ya had'e fuskarsu saitin bakinta ya ce"Zarah ina sonki soyayyar ta jazamin abubuwa masu girma akan soyayyarki na shiga had'ari mai wuyar fita wanda har yanzu nake cikinsa, Zarah kema ki soni ko kad'an ne." Kasa magana tayi sai bin shi da ido domin yanzu ji tayi kamar an d'aureta, zubawa bakinta ido yayi ya ce"Bakinki yana da kyau Zarah ina son shi sosai musamman lifs d'inki masu taushi" A hankali ya kai bakinshi cikin nata yana tsotsa hannayensa saman nonuwanta yana murzawa, ko k'wak'k'waran motsi ta kasa sai dai jikinta da takeji gaba d'aya ya saki wani irin yanayi take jinta mai wuyar fassara wanda bata ta'ba jin makamancin irin na yau ba, sosai hankalinta ya tashi gashi ta kasa magana musamman kan nipples da yakewa wani mugun tsotsa da yasata jin zafi amma ta kasa tanka mashi ,"Zarah! Zarah!! Zarah!!!" Muryar Hanne ke kiranta sai gani tayi 'bat Hisham ya 'bace a d'an razane ta juyo. Hanne ta ce"Wannan wanne irin bacci ne kike Zarah goma ta wuce ko bazaki wajen aiki ba ne?" Zarah da taji kanta na wani irin sara mata ta ce"Hanne bana jin dad'i yau ba zani ba.! Hanne fita tayi tana "To Allah ya sawak'e gashi ni ko taro da sisi bani dashi balle na siya miki ko Panadol ne na nera goma to bani da kud'i Allah ya baki lafiya." Bargo Zarah ta jawo ta rufe jikinta sosai take jin sanyi jikinta sai rawar sanyi yake, sannan babu abin da k'irjinta yake irin bugawa da ta tuno abin da Hisham ya mata yau sai ta k'ara k'amk'ame jikinta da k'yar tayi sallah ranar. (Baku tunanin abin na Zarah ko harda rashin sallar asuba a lokaci? To Allah ya kyauta, Muje dai zuwa🙊).

Tana kwance nan har Feesu da wata k'awarta Nana suka shugo, ganinta lilli'be Feesu ta ce"Zarah lafiyarki kuwa?" Cikin rawar murya ta ce"Feesu zazza'bi nake." K'arasowa tayi tare da ta'ba jikinta ai kuwa zafi sosai ta ce"Allah sarki sannu, bari na amso miki magani." Tare suka fita da Nana saj gata da Malam Shehu mai chemis, dubata ya yi sannan ya ce"Za a mata allurai ne da magunguna."

Idan kuma da hali ma har ruwa sai an k'ara mata domin taji k'arfin jikin, ba musu Feesu ta basa kud'in da za'a buk'ata ta ce Ya je ya kawo ya sa mata." Mintoci kad'an aka mata duk wani abin da ya dace wani wawan bacci mai nauyi ya d'auketa. Habu da ya shugo da yamma sosai yaji tausayinta shi mutum ne da ke son 'yan uwanshi sosai yana son Feesu da Zarah matuk'a komai zai iyayi akansu in har yana da halin da zaiyi hakan, shaye-shaye ne kawai illarsa da sara suka ko da yake babbar illa ce, ganin halin da take ciki sosai ya tausaya mata fita yayi ya sayo mata kayan shayi da na marmari har da rabin kaza ya kawowa Feesu wacce yau ta kasa fita ganin 'yar uwarta babu lafiya ta zauna domin ta kula da ita. Sosai take son Zarah a cikin zuciyarta tana son ganin suna kwana tare amma bazata iya ba saboda dole ta fita domin idan bata fita ba babu ta yadda za'ayi ta sami abin da zata ci amma har cikin zuciyarta bata son barinta ita d'aya a d'akin.

Habu ma zaunawa ya yi har lokacin da Zarah ta farko ba laifi jikinta yayi sauk'i don sai zufa take, Feesu ganin ruwan ya k'are taje ta kira Malam Shehu yazo ya cire mata ruwan sannan ya bata wasu magagungunan sannan ya musu sallama.

Abinci ta bata bayan ta wanke mata bakinta kasa ci tayi Habu ya ce"Ki had'a mata tea ko zata sha" Ganin suna da ruwan zafi sai ta had'a mata shi d'inma da k'yar tasha kusan rabi sannan tasha magani ta koma ta kwanta.

Habu tashi yayi ya fita ita kuma Feesu ta gyara d'akin. Musa ne ya shugo yana k'walawa Zarah kira, Feesu ta fito ta ce"Bata lafiya." Zaro ido yayi ya ce"Bata lafiya kuma mai ya sameta?" "Zazza'bi ne ke damunta." Ya ce"Assha-assha to Allah ya k'ara lafiya." Hannu yasa aljihu sai ga nera ashirin ya ce"Gashi mik'a mata ta sayi panadol tasha Allah ya bata lafiya.

Girgiza kai Feesu tayi ta ce"A'a ka rik'e kasha sigari ta riga tasha magani" ya ce"Kin gani ko, Nafisatu ke baki neman albarka ne?rainawa kika yi kenan? Ke idan ba ma don Zarah ce ba lafiya ba zan kulaki ne? To ita d'iyar albarka ce tana k'ok'arin faranta min shiyasa na bata ta sayi magani." Ta ce"To bata so ka rik'e abin ka." Ta na fad'a ta shige ciki ya tsaya nan yana jaraba. Hanne ta fito daga d'aki"Wai lafiya Musa kai da waye?" Ya ce"ni da wa fa bayan wannsn 'yar iskar 'yar taki Nafisatu wai nabawa Zarah nera ashirin a siya mata magani take min rashin kunya." Ta'be baki tayi"to ina laifi nima nace da ina da nera goma da na bata ta saya ka bata ashirin ai kuwa ta sayi magani."

Ya ce"to rabu da gantalalliyar har zata gaya min maganar banza." Mik'a hannu tayi ta ce"kaga bani na aika a siyomin omo nayi wanki." Ya ce"kunji wata jaraba kuma omon ashirin zai isheki wanki to nak'i tun da bata amsa ba gara na rik'e sun k'ara auki." Yana fad'a yayi wucewarsa Hanne ta ce"kai ne matsiyaci ni nafika arziki." Mtsuww!taja tsaki tare da shiga cikin d'akin Feesu zaune ta raba kazar da Habu ya siyo ma Zarah tana ci, ganin kaza da sauri ta k'arasa tare da samin guri ta zauna ta ce"Allah sarki Nafisatu kinata k'ok'ari da k'anwarku wallahi aiyuka ne suka min yawa ban shigo ba sai yanzu" d'aure fuska Feesu tayi da cewa"to naji." Hanne ta d'an sosa kai ta ce"bacci ma take"eh" Feesu ta amsa, ta sake cewa"uhmmm nama kike ci?" Idanuwanta k'ur a kai "eh kuma bazaki ci shi ba." D'aure fuska Hanne tayi ta ce"dad'ina dake Feesu rowa waini uwarki kikewa to idan banci ba ubanwa kike so yaci?" ,Feesu ta ce"shima uban nawa bazan iya basa ba." Sakin baki tayi dacewa"Feesu!"Feesu!!"wallahi Feesu ki kuka da kanki uwwarki ce ni fa kazar banza kashi fa zakiyi da kinci"ta ce"to wai ina ruwanki ne?nima kazar nan Habu ya sayawa Zarah shine fa na d'an yanka ina ci shine." Hanne da sauri ta jawo ledar ta ce"ke kinci ubanki daman bake kika saya ba kike gaya min maganar banza." Ta yagi cinya a baki cikin tauna ta ce"Zarah da ko tashi tayi bazata iya ci ba tun da bata da lafiya" sakin baki Feesu tayi kamar zata bigeta saboda haushi.
...........................
Sosai ake ta watsa mutane gidajen Radio suna zagin jam'iyyar ANPC da cewa Matashi kamar Ahmad
Showing 12001 words to 15000 words out of 22503 words