nayi alkhawarin baka koma menene matuk'ar zanyi kud'i zanyi mulki." Hhhhhhhhhh hhhhhhhhhhh hhhhhhhhhh dodon nan yake dariya kafin yace"Alhaji Mahmud!! Mahmuda!!! Mahmuda!!! Mai Abaya!!!!!,duk da jikin Alhaji Kabiru Tafida yayi sanyi da jin abinda dodonsa ya kira amma haka ya k'arasa jikin wannan mutumin dake zindur ya bigi kansa da k'arfi yanayin wasu surutai sai kud'i suka dunga 6ul6ulowa ta cikin bakinsa,saida ya jika jaka guda sannan ya d'auki wata kwalya da ta bayyana jini ne a ciki sha yayi sannan ya kinkimi jakar ya fita."
Har lokacin tana parloun tana hawaye ya fito,wani kallo ya mata ya nufi hanyar fita,cikin kuka tace"Duk abinda kake shukawa k'arshenka na nan zuwa,Allah ba azzalimin bawa bane Alhaji Tafida Allah ya tona maka asiri!!!,ta idasa cikin k'ara da kuka,juyowa yayi tare da sakin wata dariya "Hahhahhhahhhahhhhahhh!! Falmata har abada inaso ki sani asirina bazai ta6a tonuwa ba yana nan a rufe har k'asa ta tashi,cikin kuka tace"mulki da siyasa ne burinka kuma har abada bazaka samu ba kasa wannan a zuciyarka mugu azzalumi,K'arasowa yayi ya sakar mata wani wawan mari kuka ta saka da k'arfi tare da zubewa gurin tana kuka kamar ranta zai fita,k'afa yasa ya fita cikin gidan,yana fitowa ya saka key ya rufe ko ina na ciki,abun ya bani matuk'ar mamaki da naga wannan yanken shine k'arami a cikin part-part dake gidan kuma shine a baya cen k'arshen gidan da alama babu wanda ke zuwa gurin domin sai anyi tafiya mai tsawo sannan za'a kai wajen shi kansa a mota yazo,bud'e bayan motar yayi tare da chilla jakar ciki sannan ya shiga ya tana motar,babban part d'in da yafi ko wanne girma a ciki naga tsaya domin rassa ne har guda biyar a gidan gida ne na family yana parking ya fito tare da shiga ciki nan had'imai suka fara gaishesa ko kallonsu bai yiba bare su saka ran zai amsa gaisuwarsu,sama ya nufa Hajiya Balaraba zaune hamshak'e cikin shiga ta alfarma ga zinarai da gwala-gwalai a wuyanta sai shek'i suke,yana shugowa ta dubesa da murmushi zaunawa yayi yana maida numfashi tace"lafiya na ganka cikin damuwa Alhaji?yace"uhmmm Hajiya kedai bari kawai,mik'ewa yayi zai shiga ciki tace"amma kuma Saif ya kirani da ba kanan,Cheek ya tsaya tare da komawa ya zauna yace"meke damunsa?tace"maganar gizo bata wuce ta k'ok'i maganar kud'i ce,yace"to meye amfaninsu tunda ina dasu ai amfaninsu kenan bawa d'ana duk abinda yake so,waya ya ciro tare da kiran wayar Saif wanda yake k'asar Englang yana karatunsa ko ince shak'iyanci a gurinsu yana karatu ne amma babu abinda yake sai shagalinsa da matan turawa manemin mata ne na k'arshe da shaye-shaye d'an hutu ne mahaifinsa na k'aunarsa fiye da zaton mai karatu zai iya yin komai akan soyayyar d'ansa komai yake so bai rasaba babu abinda ya nema ya samu yana d'aya daga cikin abinda ya lalatashi shida k'anwarsa Raihanatu da suke kira Rihah dukansu a k'asar waje suke karatu mahaifinsu ya killacesu baya son komai ya samesu hakan yasa tun daga secondry a waje suke karatu har zuwa yanzu da Saif ke karatun masters d'insa ita kuma Riha a SS2 take hutu kawai ke dawo da Rihah gida shi kuwa Saif sai yaso yake dawowa domin sosai ya tsani Nigeria,Saif ne ya d'aga kiran mahaifinsa wanda a lokacin rungume yake da wata cika dukansu tsirara yace"My Dad ya kake?,yace"ina lafiya my son ya karatun?"Alhamdulillah,ya basa amsa sannan ya d'aura da cewa"Dad Mum ta sanar da kai buk'atata,yace"yes yanzu zan maka transfer ta account d'inka karka damu danku nake neman kud'in nan idan har kai da 'yar uwarka da mahaifiyarku za kuji dad'i to kowama kar yaji,yace"wow Dad shi yasa nake sonka."duka suka saki dariya yace"Dad yanzu zan shiga lucture zan kiraka anjima ka turon kud'in yanzu,yace"ok my son kayi karatu da yawa,da haka ya yenke kiran,Hajiya Balaraba tabi mijin nata da kallo cikin sakin murmushi naji dad'i tana son yarda yake nuna tsantsar k'auna a garesu,tashi yayi ya wuce sama yana danna kiran Alhaji Mudi bayan ya d'auka yace"Naje d'akin dodo na d'auko kud'in ina son ka turo a amsar maka da kud'in nan a sayo makamai da bindigogi da kayan maye wad'anda za'a bawa yaran nan 'yan bangar siyasa,Alhaji Mudi yace"ok hakan yayi sannan ya yanke kiran turawa Saif dubu d'ari uku yayi sannan ya kwanta cike da tunanin hanyar da zasuci gaba dayi domin ganin sun sami mulkin nan ta halin k'ak'a da ganin yarda zasu dakatar da Alhaji Mahmud Mai Abaya gwamnatin dake ci yanzu."
.................................
Ko da Zarah ta koma wajen aikinta cike take da mamakin dalilin da zaisa Hisham ya mata haka,sai yanzu zuciyarta ta bata"Zarah wancen fa mafarki ne wannan kuma zahiri,uhmmm taja numfashi da haka har na kammala aikinta ta dawo gida wanka tayi tare da d'aura alwala kamar kullum,Musa ya shugo cikin gidan yana k'wala mata kira,"Zahra'u"Zahra'u,ta shi tayi tana niyyar fitowa sai gashi ya shugo sai ta komo ciki ta sami guri ta zauna kallonta yayi da cewa"Zarah wata gasa zamu shiga akan chacha duk wanda yaci a cikinmu shi keda dukiya kinga dole sai kowa ya bada kudi shine akace ni na mata dubu d'ari shi kuma abokin takarar tawa zaibada dubu dari biyar kinaji ko idan ni nace zan had'e duka na rik'e haka idan shi amma yarda nake da sa'a ban ta6a chacha aka cini ba don haka wannan ma bana ganin za'a cini,cikin maganarta ta kwalawa tace"yo toni ina ruwana a harkarka da zakazo min da wannan maganar,gwara murya yayi da samun guri ya zauna cikin sanyin murya yace"Zarah akwai ruwanki kinga ke kina aiki kuma zuwa yanzu nasan kin tara kudi fiye da dubu d'ari shine nakeso ki rantamin idan munyi zan baki d'ari biyu kinga na nunka miki,wani kallo ta masa tare da mik'ewa tace"amma fa kai Musan nan ka iya rainin hankali nice zan baka aron kud'i?,yace"eh mana Zarah nace miki zan nunka miki ne idan naci,tace"to idan bakaci ba fa?,yace"haba Zarah ya zakimin wannan fatan zan ma ci,tace"to ko ina dasu bazan baka ba bare ma banda su,k'ara sanyin murya yayi yace"haba Zarah kiyi hakuri ki aramin,d'aga murya tayi"yasin ka fitar min d'aki kafin na kira maka 'yan sanda ince zaka min sata,Feesu ce ta shugo wani kallo banza ta masa tace"Musa mai ka shugo ka mana a d'aki?,yace"wallahi duk na haifi 'yan iskan 'ya'ya wai bani ne ubanku ba da kuke kiran sunana kai tsaye?,Feesu tasa dariya tace"kaine amma kaida kanka ka koya mana kiranka da Musa ita kuma matar da Hanne don haka baku koyar damu kiran Baba da Mama ba da zamu kiraku da hakan,Zarah tace"ai kuwa don kuwa barewa bazati gudu d'anta yayi rarrafe ba,fita yayi yana mitar tau dai mun aifi bala'i,Feesu tace"kaine zaka gansa bala'in."
Zarah shinfind'a dadduma tayi ta fara sallah,fisu handbag d'inta ta d'auka ta fice,Yau indomie taci da ta dafa yanzu da kwai sannan ta d'an dad'e a zaune ta kwanta,Kamar kullum yauma sai ganinsa tayi ya bayyanar mata.
[10/10, 3:56 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*


_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._


*UMMU AFFAN*🤏


🅿️ 7️⃣ & 8️⃣


..."Hisham!!!"
Ta kira sunanshi cikin sauti, murmushi d'auke a fuskarsa ya ƙara so ya ce, "Eh ni ne"
Girgiza kai ta fara da fad'in "A'a!a'a!!a'a!!!!!" Sai ta farko a matuk'ar gigice waige-waige ta fara.
Duhun dare ya tsala sosai gata ita d'aya a d'akin kamar mayya, bata taɓa jin zuciyarta ta karaya ba irin na yau.
Hawaye take ita da abu da yawa bai sata kuka kai ita fa duk tausayin da abu ya bata da wuya tayi kuka amma yau ita ke kuka, ganinsa tayi tsaye gabanta, baya ta fara tana girgiza kai, shima k'ara kusanto ta yake sai da yazo daf da ita sannan ya sami guri ya zauna kama hannuwanta ya yi ya ce, "Ki dena kuka masoyiyata wani ma bana so ya saki kuka balle ni, kukanki na d'aya daga cikin abin da zai tayar min da hankali zan iya jure komai amma ban iya jure ganinki cikin damuwa da tashin hankali." Cikin kuka ta ce"Ni ka rabu dani bana sonka ba na son ganinka!!" Da k'arfi ya rumtse idanuwansa sannan ya bud'e ita kan ta sai da ya bata tsoro ganin yarda lokaci guda idanuwan nasa suka chenja kala, juyewa da farare zuwa baƙaƙe ba ma ja ba, abin da furgitarwa, ya ce"ban ce lallai ki soni ba amma ni ki sani ina sonki! ina sonki!! ina sonki!!! da k'arfi ya jawota jikinsa tare da had'e bakinsu guri guda,turesa take amma jinsa take kamar tana ture k'arfe ko wani gumgume man dutse,sai da ya gaji don kansa sannan ya saketa amma har lokacin bai bari tabar jikinsa ba,ya ce"na ta'ba fad'a miki ako da yaushe ina tare da ke babu wanda ya isa ya rabamu dake,ta ce"jiya na ganka da matarka ai" Zaro ido yayi sosai sai kuma yayi shuru ta ce"eh na ganka naji ta kira ka da mijinta kuma kun hau mota kun je gida mai yasa a lokacin da na maka magana baka kulani ba kace baka sanni ba!?" Girgiza kai yayi da sauri yace"Ba ni bane, ni Hisham sunana!" ,ta ce"k'arya kake kaine na gani,ya ce"bani bane wancen bil a........sai kuma yayi shuru ya ce"bani bane!bani bane!!! 'bat ya 'bace sama ko k'asa a furgice ta farka duk ta had'a zufa,ashe wacce farkawar ta farko duk a cikin mafarkin tayi ta,kurma ihuww tayi da k'arfi sai ga Hanne ta shugo"ke lafiya?ta tambayeta sai a lokacin ta bud'e ido,Hanne ta ce"kusan kullum ke haka kike barcinki me ke faruwa dake ne?" girgiza kai ta fara ta ce"ba komai" zaunawa Hanne tayi tare da dafa kafad'ar Zarah ta ce"ki sanar dani abin da ke damunki Zarah?" girgiza kai tayi"ba komai,ganin Hanne na niyyar takura mata sai ta tashi ta bata guri wanka taje tayi wajen tara na safe sai lokacin take sallah,bayan ta idar ta dad'e zaune tana tunani amma zuciyarta ta kasa tunano mata komai,tashi tayi ta shirya zuwa wajen aiki ko karyawa bata iya yiba,tana fitowa taga 'yan makarantar islamiyya suna wucewa kasancewar ranar Asabar ce,gabanta taji ya fad'i tabi su da kallo har suka 'bace sannan taci gaba da tafiya.Ta wajen da su Musa ke chacha ta wuce,ko kallonsu batayi ba bare ta gaishe su,wani cikin mazauna gurin yana hura sigari yace"Musa waccen ba Zarah bace ta wuce?Da sauri ya d'ago kansa yace"ita ce mana ina ruwanka da ita?yace"daman ni bance wani abuba ko gurinta kaga naje kawai dai kai dai yaranka basu da tarbiyya da d'a'a ace suka abokan ubansu amma suk'i gaishe su,yace"ai kai naka yaran naga tarbiyyar gare su,nan fa abu kamar wasa ya kaisu ga chachar baki harda k'ok'arin dambe da k'yar aka rabasu."
..............................
Hafsat ce kwance a saman k'irjin mijinta a hankali yake shafa bayanta,ya ce"gobe ne Alhaji ya sanar dani zamuje Bakori yak'in neman za'be akwai wani babban taro da za'ayi a cen,k'ara shigewa k'irjinsa tayi tace"bana so kana nisa dani Honey,a hankali ya kai hannu saman cikinta yace"yaushe zaki haifa mana baby?,zaro ido tayi tace"baby kuma?tun yanzun?cike da mamaki ya kalleta yace"to idan ba yanzu ba sai yaushe?,murmushi ta sakar masa tace"kana son na haihu Ahmad?,ya ce"kin san ina son yara ko?,har yanzu murmushi take ta ce"shi kenan a yau ka bani yaro,d'an murmushi yayi ya ce"kice dai Allah ya bamu,a zuciyarta ta ce"ba amin ba,a fili kuwa murmushi tayi,babu a binda ta tsana a yanzu irin haihuwa duk da kimanin shekaru biyu kenan da auransu,tunda akayi auransu ta fara planning don sau biyu kenan tanayi na shekara-shekara take allura da farko tayi ana gobe bikinsu sannan kuma data shekara ta koma yanzu haka ta kusan komawa tayi wata Allah ya gani yarda take son mijinta da son more rayuwa bata jin zata haihu anan kusa domin gani take da ta haihu shikenan Ahmad zai juya mata baya ita kuma ta tsofe,shiyasa bata shiryawa haihuwa nan kusa ba,duk wata hanya da tasan zai gane ta tosheta shiyasa ma tafi yarda da allura akan kwaya."
Ta'bata da yayi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka,Sajensa ta fara shafawa a hankali,ya ce"tunanin me kike?tace"haihuwa Ahmad haihuwa ta Allah ce don Allah kar kaga ban haihu ba ka juya min baya ko kace zaka min kishiya." Jawota yayi jikinsa yana shafa bayanta yace"karki damu Hafsat ni ba wai na damu bane duka yaushe mukayi auran da har zan d'aga hankalina kawai dai na fad'a miki ina son yara ne sai ki shirya haifa min kyawawan yara kamarki,cikin shagwa'ba ta ce"kamarka dai ni har wani kyau gare ni da za'ace kamata,ni nafi son kyakkyawan yaro kamarka,ya ce"shi kenan sai muyi anko da masu kama dake da masu kama dani,murmushi kawai tayi tare da k'ara shegewa jikinsa."
*BAKORI k'aramar hukumar jahar Katsina*
Sosai mutane suka cika,inda ake ta d'agawa gwamna Alhaji Mahmud mai abaya hannu *Ahmad Mahmud mai abaya* shine saman mumbari yana bayanin manufofinsu kamar yadda mahaifinsa ya basa dama,cikin k'wararran turancinsa yake magana ya ce" wannan gwamnati dai ita ce akan mulki sannan ko talakawa kun fi mu sanin meye manufarmu domin kuna gani a k'asa aiyukanyi matasanmu sun sama domin gina masana'antu da gwamnatin nan tamu tayi fannin noma muna bakin k'ok'ari domin ganin mun bawa manobanmu tallafi domin noman zamani ba wannan ba duba da yarda muka gina makarantu da kasuwanni domin ci gaban da samar da ilmi a jaharmu,muna kira gareku daku k'ara bamu k'uruk'unku domin mu idasa aiyukan da muka faro.ihuww da tafi aka saka mai abaya babu abinda yake sai murmushi ta k'ara jin alfahari da d'an nasa,wanda ya amshi abun magana ne bayan Aliyu ya koma ya zauna yace"ANPC jama'a suka amshe da NASARA SA'A *ANPC* suka sake cewa NASARA SA'A CHENJI, *ANPC* nasara sannan yaci gaba da bayaninsa duk akan aiyukan da suke da son samun k'uruk'un jama'a."
...........................
Alhaji Tafida ne zaune da amininsa Alhaji Mudi,akan kujeru ga taron matasa gabansu da kayan sara suka su adduna wuk'ak'e bindiga da sauransu sai gayan maye taba wiwi shalaso da hudar iblis.

Ogansu wato Habu shine ya tashi ya fara rabawa kowa nashi,sosai sukasha kayan mayen a gabansu Alhaji Tafida ba 'abin da suke sai hirarsu sun tara yaran talakawa suna basu kayan maye da adduna nasu kuwa sun killace su sun fitar dasu k'asar ma ko kud'a masa burin ya ta'basu,bayan sun gama sannan suka d'unguma dukansu domin zuwa yak'in neman za'be,sosai suma suka tara jama'a ba abinda suke sai rabon kud'i damansu nasu na rabon kud'i komai suna yinsa cikin nera"PRP jam'iyyar hamayya kenan ko ina photunan Alhaji Tafida ne ana faman bi ana lik'a fad'i suke"Sai kayi gwamna sai kayi,ba abinda ya ke saki sai murmushi yana d'agawa jama'a hannu da d'aukar musu alkhawarin idan suka za'besa zai musu aiki mai nagarta wanda gwamnatin dake kai takasayi inda suke sukar gwamnati maici yanzu da cewa idan har suka bari wannan gwamnati ta maimaita to sai dai azo ana d'aukar talakawa matattu a gidajensu domin yunwa da rashin arzik'i da abinci da ake fama dashi yace"meye a cikin wannan gwamnatin bayan son kansu da 'ya'yansu ba sama talakawan da suka za'besu komai ba gyara harkar ilmi ta lalace idan har kuka za'be mu 'ya'yanku zasuyi karatu kyauta harkar noma zata bunk'asa zamu gina muku makarantu da masana'antu kowa zaiji dad'i shine fatanmu,tafi aka fara rab-rab-rab da ihuww murmushi kawai yake saki,fatansa da hangensa ganin ya tsallake wannan za'ben dake tunkarowa."
"Ni kan Zarah yau lafiyarki k'alau kuwa? cewar Abida wacce suke aiki tare idan ma bazata wuce sa'ar Zarah ba suna gaisawa sosai don zan iya cewa a gurin tafi shiri da Abida saboda yarinya ce mai natsuwa,gyara tsayuwarta tayi tace"a kwai wani abu da na manta da ya faru dani a rayuwata amma sam na kasa tunawa,murmushi Abida tayi tace"to ke dole sai kin tuna kawai ki bar komai karki takurawa k'wak'walwarki idan lokacin ki sanin yayi zaki sani." Dariya Zarah tayi tace"dad'ina da ke kanki naja 'yan mata." kama hannunta tayi suka fara aiki, Abida tace"amma Zarah na tambayeki badamuwa?,Zarah na gyara kwalar rigarta tace"ina jinki,d'an shuru tayi sai kuma tace"am me yasa kike saka kayan maza?me yasa kije magana irin ta maza?,da sauri Zarah ta kalleta sai kuma tayi murmushi tana buga bayanta tace"karki damu da wannan,ta fad'a har ila yau cikin maganarta ta d'aura da cewa"kawai ki share,haka sukaci gaba da aikinsu k'arfe uku da rabi Abida ta musu sallama domin lokacin ita take tafiya Zarah tace"amma me yasa kike tafiya tun yanzu?,tace"eh saboda islamiyya nake zuwa da k'anne na k'arfe hud'u zanje na shiryasu nima na shirya sai muwuce,gyad'a kai kawai Zarah tayi tabita da kallo sannan ta koma ciki."
..................
"Hafsat"Hafsat"Hafsat ki tashi lafiya?wai meke faruwa ne? kusa da ita ya zauna tare da d'agota jikinsa,sai kawai yaga ta bud'e ido tana dariya,ajiyar zuciya ya saki tare da cewa"wannan wane irin wasa ne please ki dena,hannunta tasa ta sak'alo wuyansa tare da had'e bakinsu guri guda tana tsotsa,zuwa cen ta saki ta kuma sake mayarwa tana tsotsa a hankali ta saki bakinsa idanuwanta akan la'b'bansa tace"ban gaji bane." da me? ya tambayeta tace"kafini sani ai "ta fad'a tana sake jawosa jikinta,murmushi kawai yayi aransa yana mamakin jaraba irin ta Hafsat,yace"ki shirya yau zamuje gida,tace"bayan mun gama ko? harararta yayi ta saki dariya nan suka fad'a saman bed."
Sun sami Mai abaya da bak'i hakan yasa kai tsaye suka wuce cikin gidan gwamnatin,Ita kanta Hajiya Batula cikin shiri take domin zasu fita wajen k'addamar da wata k'ungiya ta mata sai Hajiya Anty don a tsaitsaye suka gaisa ta fita,sai gurin Hajiya Anty ta tauza suka d'an ta'ba hira shi kuwa Ahmad tuni ya fita wajen Daddynsa."
..................
"Wai ke Rihah ko d'anya kuka sami hutu sai kin taho,amma nace miki hutun da baifi sati biyu ba ki dunga zamanki cen meye amfanin gidan da na saya muku keda yayanki Saif,hawaye ne kwance a idaniyarta amma bata bari sun zubo ba tayi k'ok'arin mayar da su tace''kayi hak'uri Daddy laifi ne don 'ya taso ganin iyayenta?,yace"ba laifi bane Rihah amma ina son inga kunyi ingantaccen ilmi da babu kamarsa ina son naga kunfi kowa,tace"na sani Daddy kayi hakuri,ransa 'ba ce yabar gurin,hawayen da take 'boyewa suka zubo jiki a sanyaye ta koma kusa da Ummanta tare da d'aura kanta akan kafad'arta Umman tace"Rihah Abbanku yafi son ganinku acen kuna karatunku ke kuma kina
Showing 6001 words to 9000 words out of 22503 words