k'ara d'aga murya da kirari. da haka suka koma ciki, Alhaji Mudi wanda shine idan sun ci yake mataimakin gwamna. ya ce"Ni wai Alhaji Tafida ko kaji wani batu? Kallonsa ya yi da k'yau ya ce, "Wanne batu?" Akan yak'in neman zaɓe da Mai abaya zai fita wai harda babban d'ansa da yake burin shima yayi siyasa,wata dariya ya saki mai k'ara yace"ohh d'an nasa ke son ya gajesa kenan to muzuba mu gani shi babban mutum ma mun iya dashi bare d'ansa yaro k'arami" ya ce"Babban d'ansa nake maka magana d'an nasa fa zaiyi 35y yace"to sai me?ba yaron bane?ko kai baka haifi d'an 35y ba?" ya ce"Haka ne,dafasa Tafida yayi yace"Mudi wallahi kaji na rantse maka ko ta halin k'ak'a sai mun mulki jahar nan tamu son mulki irin na siyasa a jinia yake kuma na rantse da Allah sai nayi,yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki."
...........................
"Dad ban san me yasa jikina yayi sanyi da fitar nan tamu ta yau ba, don Allah ko za'a cenja tsari zuwa gobe,dafasa Alhaji Mahmud yayi yana murmushi ya ce"Yarona ka zama gawurtacce mana kasan kuma fa ina burin nan gaba na ga ka zamo shugaban k'asa ba ma gwamna ba, zaro ido yayi fuskarsa da murmushi ya ce"Dad haka kawai naji jikina yayi sanyi bana son wani abu ya faru da kai mu bari gobe mana, ya ce"ba abinda zai sameni sai alkhairi sannan naji labarin gobe Alhaji Kabiru Tafida zasu fita kaga yau ne dai ya dace mu fita,gyad'a kai yayi da cewa"shi kenan Dad bari naje na shirya,cikin jin dad'i da alfahari yace"Allah ya maka albarka ina alfahari da kai yarona,bari nima na isa gurin wad'anda zamuyi gangamin suna waje." Murmushi kawai yayi ya fita,da har zai shiga part d'insa dake cikin gidan domin ya shirya sai kuma yayi tunanin bari yaje gidansa." Gida ne mai k'yau da tsari na 'ya'yan manya hune yayi a bakin gate mai gani yazo ya bud'e masa ya shiga ciki tare da samun guri yayi parking jiki a sanyaye ya fito zuwa cikin gidan, zaune take a parlour taci kwalliya sosai tayi kyau cikin wasu riga da siket da akawa d'inkin wulak'anci gaba d'aya saman nonuwanta a waje suke babu abinda ba'a gani taci kwalliya domin 'yar k'walisa ce ta k'arshe Hafsat kenan mata a wajen Ahmad ko kallon inda take baiyi ba ya nufi hanyar bedroom,kallonsa take cike da mamaki da sakin baki tasanshi yana son ya ganta cikin wannan yanayin to ko lafiya?ta tambayi kanta tashi tayi tabi bayanshi, gani tayi yana kiciniyar cire kaya da alama wanka zai shiga da sauri ta iso garesa tare da rungumesa ta baya gama d'aya nonuwanta a saman bayansa wani yarrr yaji ya juyo da ita ta gabansa a jikinta babu abinda yafi k'auna sama da nonuwanta sa hannu yayi a hankali yana shafasu, kallonsa tayi ta ce" Ahmad lafiya naga ka shugo cikin wani irin yanayi?kasa ce mata komai yayi ya had'a bakinsu waje guda na aika mata da wani hot kiss itanma biye masa tayi sosai suke romancing junansu ganin tsayuwa bazata yuwuba suka isa bed sosai yake ya mutsata son ransa kamar yadda ita ma take masa sun d'auki tsawon lokaci a haka wayarsa ce tayi k'ara sai lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa d'aukar wayar yayi ganin sunan Dad da sauri ya watstsake ya d'aga, muryar Dad yaji yace" *Ahmad* kana ina ne kai fa muke jira, da hanzari ya ce"Dad ina zuwa yanzu in sha Allah,da sauri ya saki Hafsat ya fad'a bathroom ita kuwa binsa tayi da wani mayen kallo gaskiya a yadda take mayyar Sex idan har Ahmad bai kusanceta ba akwai matsala tashi tayi cikin wani irin mayen yanayi ta bisa bathroom d'in. Bakin k'ofa ta tsaya ta zuba masa rikitattun idanuwanta,kallo d'aya ya mata ya kaida fuska yaci gaba da wankansa,bayan ya gama tawol ya d'aura yazo ya ra6ata ya wuce,tasan halinsa duk domin kallon da ya mata ta san abinda yake nufi,jiki a sanyaye ta dawo bakin bed ta zauna tana kallonsa har ya gama shirinsa cikin manyan kaya wato d'inkin shadda har da malum-malum tuni daman duk wata shigar k'ananun kaya ya dena sai lokaci zuwa lokaci saboda girman nan da mahaifinsa ya k'ak'a ba masa,sai da ya gama saka turarensa sannan yazo ya shafa gefen fuskarta murya cen k'asa yace"am sorry dear sai na dawo,ji tayi kamar ta kamosa jikinta haka ya fita ya barta cikin wani irin yanayi,tun farko shi ya sabar mata gashi yanzu jar tana neman ta fishi jaraba jinta tayi cikin wani felling sosai,a hankali tasa hannu k'asanta tana d'an murjawa a hankali tana sakin 'yar k'ara ganin hakan bazai mata ba tashi tayi ta shiga bathroom ta tara ruwa ta shiga ciki tare da bud'e k'afafunta sosai take jin kewar mijin nata ita macece mai son sex da soyayya duk da mijin nata ya koyar da ita amma yanzu jarabarta tafi tasa bata iya shige-shige ba duk jarabarta akan mijinta take k'arewa sai dai yau ji take kamar me ji take idan namiji bai kusanceta ba akwai matsala,ta dad'e cikin ruwan sannan ta fito d'aure da tawul tana goge jikinta shiryawa tayi cikin wasu shegun kaya sosai suka mata kyau fitowa tayi parlour 'yar aikinta ce ta kawo mata abinci amsa tayi tanaci a hankali tana tunanin mijinta,wayarta ta ciro tare da danna kiransa,lokacin kuwa sosai suke cikin jama'a domin saboda hayaniyar mutane sam baiji kiran nata ba,ta kira har sau uku daga k'arshe cilla wayar tayi ta fara hawaye cike da kewar mijin nata,acen kuwa taro yayi taro sai gudanar da al-amura suke yadda ya kamata,mutane sosai suka taru suna d'aga hannu ga kalandun gwamna Alhaji Mahmud mai abaya nan ta ko ina an lik'a wasu yanzu ake lik'awa abin nasu yayi kyau sosai mutane ke k'aunarsa saboda tausayin talakawansu,cikin sauti na sifik'a yake magana"jama'a da farko Assalamu alaikum." Gaba d'aya suka amsa sannan ya ci gaba da cewa"kamar dai yadda kuka sani wannan jam'iya itace mai mulki a jahar nan harma da k'asar nan,muna so kuci gaba da bamu goyan bayanku kamar yarda muka faro ga sauran aiyuka namu da bamu kammala ba insha'Allahu da zarar anyi za6e zamuci gaba da aiyukanmu." Ihuww aka saka ana tafa masa wasu nace"gwamna sai kayi gwamnanmu sai ka sake." yace"to madha Allah mudai wannan jam'iyya tamu cigaban talakawa shine takenmu domin samawa matasanmu aikinyi,tafi tafff-tafff-tafff ake,wani ne ya amsa sannan gwamna ya koma gurin zamansa,mutum da k'arfi yace"ANPC,Jama'a suka amshe da "Nasara chenji."ANPC."Nasara chenji."ANPC.Nasara chenji,sannan yaci gaba da bayaninsa,ana cikin haka saiga 'yan ta'adda bangar siyasa,sune suka fasa taron inda suka fara sare-sare nan fa kowa yayi takansa sosai ran gwamna ya 6aci da wannan abun kuma yasan 'yan babbar jam'iyyar hamayya ne suka turo,amma dai yasan duk siyasa ne da hamayya hakan yasa dai kowa ya watse inda akabar nasun 'yan bangar suka had'e da juna. Su kuwa tuni suka wuce ran Ahmad ya ɓaci sosai wai a hakan mahaifin nasa ke son ya fad'a harkar gadan-gadan?
..............................
Zahra ta fara zuwa aikinta wannan gidan abinci na masu kud'i, ba laifi tana samu sosai hakan yasa idan ta kwashi albashi tana sayawa Hanne kayan abinci Shinkafa da garin tuwo sai kwaki da su maggi tace tayi cefane, ita kuwa daman idan ta karya da shayi da breadinta idan taso har kwai take toyawa sannan ta wuce acen take cin na rana da sunce idan tanaso zata iya kwana amma tace"a'a tafi so ta dunga kwana a gida hakan yasa da yamma ta ke komawa gida wataran ma harda abincinta take tahowa,idan tayi niyya ta d'ibarwa Hanne tunda Feesu daman ba gida take kwana ba,yau a gajiye ta dawo wanka tayi tare da d'auro alwala jin an fara kiran sallar magrib mai ta shafa da yake daman ita mai kawai take shafawa wataranma bata shafawar don komai nata na maza ne,sallah ta farayi sannan ta jawo take away d'inta ta faraci babu abinda k'irjinta keyi sai bugawa,ta rasa dalili amma saboda da kakkiyar zuciya irin tata ko gezau babu alamar tsoro a tattare da ita,bayan ta gama tashi tayi ta fita jin ana kiran sunanta *Zahra!* *Zahra!!* *Zahra!!* inda take jin sautin kiran take bi har zuwa d'an katin Bala, chek!!! ta tsaya ganin Hisham a bakin k'ofar da alamar Balan ya tafi, don shagon a rufe yake, babu abin da yake sakar mata sai murmushi, Aljani ne ko mutum? Ta tambayi zuciyarta sai kuma ta d'aure fuska sosai tare da cewa"Waye kai?." har lokacin murmushi ne kwance a fuskarsa ta kowa yayi har zuwa inda take ita kuwa ko gezau tana a tsaye bata matsaba har ya k'araso cikin very sweet cool voice ya ce da ita"Har yanzu lokaci bai yi ba,da sannu zaki gane Aljani ne ko mutum, nazo gurinki na tayaki hira ne idan babu damuwa?" Juyawa tayi da niyar komawa gida,sai taga wani siririn mutum da kwala-kwalan ido da k'aton kai harda k'aho,sake juyowa tayi ta kallesa har lokacin ita yake kallo fuskarsa da murmushi ya k'ara takowa gareta tare da rik'e hannayenta sai taji sam ta kasa kwacewa,yasa hannu yana shafa fuskarta yace"ke tawa ce ina so ki soni,kasa magana tayi domin ji tayi kamar an d'auke mata komai najikinta sosai jikinta ya mutu ko yatsa ta kasa d'agawa,rik'e fuskarta yayi tare da had'eta da tasa ya hura mata iska a fuska,lumshe idanuwanta tayi,muryar Musa mahaifinta taji yana cewa"ke Zarah me ki keyi a gurin nan? da sauri ta bud'e idanuwanta babu shi daga ita sai Musa, waige-waige ta kama,ya ce"ke Zahra lafiya? Bata ce komai ba ta nufi hanyar cikin gida har tana tuntu6e,shima bin bayanta yayi yana banbamin fad'a"kawa yarinya magana amma ta shareka saboda tsabar rainin wayau,duk da haka bata kulasa ba har takai d'akinsu zaunawa tayi bakin gado tare da lumshe idanuwanta tana hangenshi, "Waye shi?meye had'inta da shi? Sai yanzu zuciyarta ta fara raya mata anya mutum ne shi?,girgiza kai tayi ganin tunani bazai fishsheta ba tashi tayi ta sake alwala tanajin hayaniyar su Hanne aranta ta ce"Aikin ku kenan kullum ko gajiya bakuyi."Bayan ta idar da sallah sannan ta kwanta."
Kwance take saman faffad'an k'irjinsa tana wasa da kwantaccen gashin dake k'irjin nasa mai yawa da kyau sai kwalli yake cikin murya k'asa ta ce "Honey ina sonka da yawa inason kasancewata tare da kai bana gaji da kai ko kad'an." Bai ce komai ya ci gaba da aikin da yake a computer duk da tana jikinsa amma hannunsa d'aya da computer d'ayan kuma na saman k'irjinta,tace" Ahmad a yarda nake sonka bazan iya taɓa jure inganka tare da wata ba bayan ni ina da kishi mai tsanani musamman akan ka." Murmushi kawai yayi don maganarta dariya ta basa sai ya ce"To dawa zaki ganni?" Ƙank'ameshi tayi tare da zura harshenta a kunnansa sannan a hankali ta ce"Bana tsammanin ganinka da kowa don Allah ka mini alkhawari bazaka min kishiya ba." Zuba mata ido yayi sai kuma yayi d'an murmushi yace"Hafsat me kika dafa mana yunwa nake ji." Ya fad'a domin gusar da waccen maganar,tace da sauri"am sorry honey ban d'aura ba tukun bari na tashi nayi." Ya ce"Gaskiya yunwa nake ji sosai bazan iya hak'uri har kiyi girki yanzu ba." ta ce"Ai ban ji dad'in tafiyar da Talatu mai aiki tayi ba jiya ga irinta nan,don Allah ka k'aro mana 'yan aiki." Ya ce"Karki damu yanzu shirya dai ki tashi muje gidan abinci." Zaro ido tayi ta ce"Kamarka a ganka gidan abinci ko ka mance da burin Dad akanka ne, d'aga kafad'a yayi da cewa"To idan an ganni wa yasan ni ne?sau nawa ina zuwa kuma." Murmushi tayi ta shirya da sauri, ya d'auki mota suka bar gidan sai gidan da Zahra ke aiki domin Ahmad yafi son sayen abinci ko drinks a gurin saboda suna da tsafta sosai da iya girki.
[10/10, 3:51 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._


_GAWURTATTU BIYAR._✌️


*UMMU AFFAN*🤏


🅿️ 5️⃣ & 6️⃣


Guri suka samu suka zauna, akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ta na da domin masu sayen abinci zaunawarsu ke da wuya Zarah ta iso, hannunta d'auke da takaldar da ake mik'awa domin ka zaɓi abin da zaka saya, tun daga nesa yake kallonta cike da mamakin ganin kamar macece amma take abu na maza har ta k'araso idanuwansa na kan ta. Ɗago fuskar da zatayi ta kallesa, shi d'inma ita yake kallo zaro ido tayi tana so ta tuno inda tasan fuskar zuwa cen ta ce" *Hisham* Eh kaine *Hisham* daga Ahmad har Hafsat kallonta suke cikin k'uluwa kafin Hafsat ta ce"Ke dak'ik'iyar ina ce zaki kalli mijina ki kirasa da wani sunan daban?" Gyara tsayuwarta tayi ta ce"Mijinki? Eyhy lallai mijinki, idan har mijinki ne me yasa yake zuwar min a barcina?" Cikin maganar maza tayi maganar kamar dai yadda take yin maganarta. Cikin huci Hafsat ta ce"Ƙarya ki ke? Jahila wallahi mijina ya fi k'arfin yazo a barcinki yazo ya miki uban me? A matsayin mace ko namiji? Mata maza dake!!!" ,Zarah bata taɓa jin haushin kanta da d'abi'unta ba sai yau da matar nan ta kirata mata maza, cikin dakiyar murya da rashin tsoro ta ce"Naji ni mata maza ce ke kuwa da kika rako mata duniya fa?" A zafafe Hafsat ta d'aga hannu zata mari Zarah da sauri Aliyu ya rik'e mata hannu tare da girgiza mata kai ya ce"No Hafsat." Hawaye ne suka wanke fuskarta ta ce"Amma fa kana jin abin da ta ce? Wai kai mijina take gani a gurin bacci saboda tsabar ta raina mana wayau" ya ce"Naji to ya isa." bai sake kallon Zarah ba,ya zaunar da matarsa sannan ya kira wata a ma'aikatan gurin ya ce ga abin da suke buk'ata. Nan aka kawo musu amma Hafsat ta kasa cin komai saboda zafin da taji zuciyarta na mata,Zarah kuwa tana gurin tak'i tafiya babu abin da take sai kallon Aliyu da take kira Hisham tabbas a haka ya ma fi kyau ba kamar a baccinta ba, to amma me yasa shi bai ganeta ba bayan kuma yace yasan duk wani abu dake zuciyarta kuma ako da yaushe yana tare da ita,kallonsa kawai take,shima ta gefen ido yake lura duk da ita shi dai a zahirin gaskiya bai ta6a ganinta ba hasalima yanayin da ya ganta abin mamaki ya basa yasha ganin 'yan daudu maza dake mayar da kansu mata amma bai ta6a ganin macen dake mayar da kanta namiji ba sai a kanta."
Ganin Hafsat tak'i cin komai yasa dole ya ce amata take away,bayan ya biya komai suka fita,Zarah bin bayansu tayi tana ganin sun shiga mota hau acha6a tace duk inda sukayi ya bisu,Aliyu ya lura da ita sosai yayi mamakinta to me take nufi?,ya tambayi kansa bashi da amsa,kai tsaye gidansa ya nufa bayan yayi hune mai gadi ya bud'e masa ya shiga,Zarah sauka tayi daga babyur bayan ta biyasa ya wuce,kai tsaye gate d'in ta nufa ta fara bubbugawa,Mai gadi ya lek'o,kallonta yayi sama da k'asa yace"lafiya?cikin maganar tata tace"haba Baaba ka bani guri na wuce gurin Hisham nazo,kallonta yayi tare da d'aure fuska yace"wuce ki bamu guri 'yar dauduwa nan ba gidan sakarai bane." Matsowa tayi kusa dashi tare da chafkar wuyansa ta shak'e sosai yaji tsoro domin itan kanta Zarah bata san tana da k'arfin hakan ba tasan dai duk abinda yazo zuciyarta tana ai watar dashi ne tace"zaka bud'emin ko sai kajika barzahu?,da sauri ya gyad'a kai,dai-dai fitowar Aliyu da sauri ya k'araso tare da bige hannunta a wuyan mai gadi da sauri ta sakesa,cikin fushi yace"wai meye damuwarki da ni ne?me ya kawoki gidana?,matsowa tayi kusa dashi da sarauni kuma ta matsa abinda wani mutum bai ta6a mata ba shine Aliyu ya mata wato kwarjini sai ta kasa magana,yace"maza kija k'afarki ki barmin gida kafin nasa securitys su fitar min dake,sosa kai tayi sannan tace"amma Hisham ka bani mamaki da ka kasa gane ni amma yanzu zan tafi kamar yadda ka buk'ata sai dai ka sani zan dawo,cilla k'afa ta bara tare da bonsewa ta fara tafiya,daga Aliyu har mai gadi baki bud'e suke kallonta,kafin yaja tsaki ya koma ciki shima mai gadi yabi bayansa da sauri don ji yayi kamar zata(Matsoraci🤪).
...........................
Da sallama ya shugo cikin katafaran parloun da ya tsaru iya tsaruwa an kashe mak'udan kud'i wajen tsarashi da kayan alatu na zamani,wata Hajiya ce wacce bazata haura shekaru 45y ba zaune kan d'aya daga kujerun alfarma dake parloun,ko da ya shugo baibi takanta ba da sauri ya nufi cikin wani kad'i wanda shi kad'ai ke shiga d'akin sai kuwa Alhaji Mudi amininsa,binsa tayi da kallo lokaci guda wasu hawaye masu zafi suka zubo mata Hajiya Falmata kenan mata a gurin Alhaji Kabiru Tafida mai neman takarar kujerar gwamna,jagwab ta koma ta zauna hawayen basu dena zuba a fuskarta ba,yaushe xata dena kuka?yaushe hawayenta zasu tsaya?har abada zuciyarta ta bata amsa,sosai ta fashe da kuka tare da d'aga hannuwanta sama tace"Allah gani gareka kasan irin halin da nake ciki Allah ka kawo min a gaji cikin gaggawa." Ta fashe da kuka sosai,shi kuwa Alhaji Tafida yana shiga d'akinsa dake dund'un ya fara wata magana ta sulkulle kafin wani haske ya bayyana,ai abubuwan da na gani sauran kad'an birona ya fad'i domin fitsari naji ya fara zubomin lolx,Wani mutum na gani zurdur haihuwar uwarsa a tsaye kansa an masa aski yayin da duk jikinsa wasu irin zanene a cikinsa da ja da bak'i idanuwansa duka a bud'e yayin da hancinsa ke fitar da wani hayak'i haka bakinsa a bud'e yake sosai,gefe guda kawunan mutane ne a k'asa harda gangar jikin wasu ga dai abubuwa nan babu kyawun gani,daga k'asan mutumin wani bakin mutum ne bak'i sosai kaine kawai ba jiki shine ya fara magana cikon wani irin yanayi,murya mara dad'in sauraro da alamar shine dodon nasa yace"Tafida baza ka ta6a mulki ba idan har baka bamu jinin wanda muka buk'ata ba jininsa kawai ne zaiyi tasiri da samun kwarjininka a gurin jama'a har su za6eka,jikin Alhaji Tafida har rawa yake yace"Dodo nayi alkhawarin baka ko ma jinin waye tunda na baka mahaifiyata na baka wasu daga jinina waye ma bazan iya baka ba,ni jinin sarauta ne bana buk'atar sarauta sai mulki irin na siyasa
Showing 3001 words to 6000 words out of 22503 words