bak'ik'k'irin sosai gabansa ya buga musamman jin dodon yana amsa kuwwur kiran sunansa"Tafida!"Mudi!rayuwarku tana cikin had'ari idan har bakuyi gaggawar raba shi da ita ba, Sannan siyasarku na cikin tan'bele idan har baku rabasu ba, Sannan muna buk'atar jini!,dukansu idan ban da zufa babu abin da suke don sun kasa gane ma abin da yake nufi a raban da haka suka lalla'ba dodon cewa zasu kawo jinin sannan suka fita, har lokacin Falmata na gurin saboda rud'in da suke ciki basu tanka mata ba duk kuwa zagi da addu'ar ta'bewa da tabisu da ita, bayan sun kulle ko ina suka hau mota suka koma cen cikin gidan, dukansu shuru suka yi bayan Mudi yayi parking zuwa cen Tafida ya ce"komai zamu iya ganin ba mu samu ko wacce irin targard'a ba amma kai mai ka fahimta?ya ce"Me kuwa na fahimta duk d'aya muke babu abin da na gane" Tafida ya ce"A sato yara kai ko manya ne asamu dodo ya sami jinin kafin musan inda d'ayar maganar ta dosa" Da haka sukayi sallama.
..............................
"Hafsat manyan mata matar babban mutum gwamnan gobe" Murmushi tayi mai k'ayatarwa tana wani hura hanci tana son a yabeta ko a fasa mata kai da kalamai ta ce"Shukra kenan ko baki fad'a ba maganar haka take" Shukra tayi murmushin yak'e tana bin k'awar ta ta da kallo cike da jin haushin irin jin dad'in da Hafsat d'in take ciki ta ce"k'awata kenan kina jin dad'inki fa,"To ya son ranki?" "Fari sol ai abin farin cikinmu ne ganinki cikin jin dad'i."
Ahmad ne yayi sallama suka amsa kai tsaye sama ya nufa, Hafsat da Shukra suka bisa da kallo, daga bisani ta mik'e ta ce"kin ga bari naje gurin mijina, maganar gaskiya ba yanzu zan fito ba idan zaki tafi ne to ki gai da gida kin ga tafiyata" ta idasa fad'a tana hawa matattakala.
Shukra ta bita da wani kallon takaici da hassada ji take kamar ta fincikota ta fad'i K'asa ta dad'e a gurin kafin ta mik'e jiki a sanyaye a ranta ta ce"wallahi duk wani shirinki ina sane kuma sai na tona asirinki" ta fice daga gidan ranta a 'bace.
Ahmad babu abinda ya ke sai juyi a bedroom daga ganinsa zaka gane cike yake da damuwa, Hafsat wacce ta shugo ta dubesa cike da alamar tambaya kamo hannunsa tayi suka zauna bakin bed ta ce"Honey lafiya?me ke faruwa?,numfashi ya ja ya ce"har kar siyasa abu ne mai girma tabbas Alhaji Tafida ya d'auki abin da zafi da girman da ya wuce misali amma abin nasa yayi yawa" "Mai kuma ya faru?,bai bata amsa ba ya d'aga wayarsa ya kira number d'in abokinsa Usman wanda sukayi karatu tare da shi a fanni guda Usman d'an asalin jahar Kebbi ne amma aiki ya dawo da shi Katsina bayan kammala karatunsu, Ahmad da Usman abokan juna ne sanadiyyar abotansu karatunsu da sukayi tare jininsu ya had'u har suka k'ulla abota yanzu haka shima Umar yana da mata Zainab har da yaransu uku Jiddah Shuriem sai k'aramin Suhail,sam Hafsat da Zainab basa k'awance wai irin na matan abokan nan domin ra'ayin ko waccensu da ban Zainab tana da k'yirki sosai yayin da ita kuma Hafsat ke da d'agawa ko haihuwa Zainab tayi Hafsat daga barkar da suke zuwa da Ahmad to bata k'ara komawa bare taje suna,Ahnad yayi k'ok'arin ya had'asu ganin Hafsat bata son k'awance da Zainab sai ya rabu da ita duk da bai ji dad'in hakan ba don yasan Zainab ba dai k'yirki ba ko da girki ne ta koya amma girman kai irin na Hafsat bazata bari hakan ta faru ba.
Usman ne ya d'aga kiran Ahmad. cikin wasa da zolaya yace"Ahmad gwamnanmu na gobe in sha Allah da girman kujerarka" Ahmad ya ce"duk ba wannan ba kana ina ne?ya ce"ina gida mai ya faru ne?ya ce"nazo na same ka yanzu ko zaka zo?,cikin zolaya ya ce"kai da kaji kiran manya kasan da magana to ya na iya gwamna guda dole na amsa kira" Duka murmushi sukayi sannan sukayi sallama,Hafsat tana yatsina fuska ta ce"me yasa ni bazaka sanar min matsalarka ba sai ka kirasa,? Nifa Usman d'in nan wani lokacinma haushi yake bani halinshi d'aya da matarsa." Wani kallo ya mata ya ce"aminin nawa to na gode" matsowa tayi kusa dashi tare da rik'e hannayensa ta ce "nifa ban fad'a da wata niyya ba gaskiya ce kawai" "uhmmm a wajenki ba take gaskiya" jin kiran Usman ya amsa yana fita daga ɗakin. ta'be baki Hafsat tayi da cewa sai na rabaku.
...........................
A hankali ya ke gangaro da motarsa zuwa cikin layin domin duk hanyar babu kyau Usman ya ce"Ka gani ko don Allah dubi halin da talakawa suke ciki? Ahmad saboda tausayi har 'yar kwalla yayi shi mutum ne mai tausayi, Usman ya ce"dole ne fa ka dun ga basaja idan ka zama gwamnan nan domin ka din ga ganin halayen da talakawanka ke ciki domin sanin matakan d'auka domin ci gaban jaharka da kuma sauke nauyin da ya rataya akanka" Parking Ahmad yayi suka fito suna tafiya a k'asa suna kallon unguwar yadda kowa ke harkarsa daga gani kasan suna cikin kuncin talauci da tsadar rayuwa. Ahmad ya ce"maganarka gaskiya ce Usman Allah dai ya bamu ikon rik'e nauyin da zai rataya a kan mu." Da amin Usman ya amsa.
Zarah ce ta fito daga gida ganin mutane tsaye k'ofar gidansu ta k'arasa, tare da tsayawa gabansu, daga Ahmad har Usman suka zuba mata ido,ganin Aliyu ya sata zaro ido tace"laaaah kai ne?,d'aure fuska yayi yana bin ta da kallo ganin shigar dai tata tana nan ta maza har maganar,ba wanda yayi magana shi dai Usman cike yake da mamakin ina Ahmad yasan yarinyar nan mai siffar maza. Zarah ta ce"kayi hakuri kwanaki na ganka nace kai ne Hisham da muka had'u ya ce ba kai bane, amma na kasa yadda kai ne dai Hisham domin ni ban fa wani banbanci da zanƙi yadda ba!" bai mata magana ba ya kalli Usman ya ce"muje" Da sauri tasha gabansu ta ce"haba Baabaa magana fa nake to mutum bai kuskure ne kuma nace fa kayi hakuri duk da nasan kaine, kana dai ɓoye mini ne saboda wancan lokacin kana tare da matarka yanzu kuma da abokinka, abin da a tarihina ban ta'ba yi ba kenan bawa wani hakuri ko da kuwa shine mai gaskiya."ya ce"ok to yayi" ta ce"amma ina wannan matar taka wacce tafika girma wallahi sam-sam-sam baku dace ba." ta fad'a tana yarfe hannu, zaro ido daga Ahmad har Usman sukayi suna kallonta, d'an murmushi tayi ta ce"ni fa bana 'boye gaskiya idan tazo fad'inta nake kowa ya sani ma" Usman murmushi ya yi domin sosai yarinyar ta burgesa ya ce"mene sunanki?ta ce"Sunana Zarah" "Da kyau Suna mai dad'i" Murmushi kawai tayi tana kallon Ahmad da ya d'aure fuska bata san me yasa ya ke mata kwarjini ba kuma haka kawai take jin tana son sa har cikin zuciyarta. Ahmad yac e"Idan ka gama sai mu wuce" Da sauri Zarah ta ce"Amma don Allah me kuka zo yi layinmu?" Wani kallo da Ahmad ya mata yasata saurin shuru Usman ya ce"Kawai mun zo ganin gari ne" ta ce"uhmmm amma don Allah uhmmm da man uhmmmmm" Duka suka zuba mata ido Usman ya ce"daman me?,ta ce"daman wai zance ne..sai kuma ta ce"ko da yake babu komai,Tsaki Ahmad yaja mtsuww tare da fuzgar hannun Usman suka wuce, murmushi kawai tayi tare da bin su da kallo har suka 'bace ma ganinta sannan ta wuce daman wajen aiki zata,ranar haka ta kasance cikin farin ciki da ta tuno Ahmad sai tayi murmushi.
Usman kuwa bayan sun shiga mota ya ce"wai ni kuwa ina kasan yarinyar nan?" Nan Ahmad ke basa labari har da biyosu gida da tayi ya d'aura da cewa"Da alamar bata da hankali da tarbiyya" Usman kuwa mai zai yi ba dariya ba ya ce"kai amma wannan abu ya bada citta gaskiya zanyi abota da ita da alama kanta fa yana ja" Da sauri Ahmad ya ce"da wannan kuchakar zakayi abota baka ga unguwarsu ko gidansu bane?" Murmushi yayi ya ce"na gani mana a hakan nifa ta burgeni ne kuma wallahi kunyi macin fa" da sauri ya zaro ido ya ce"bana so Usman wannan wace irin magana ce" Sun yi tafiya har sun bar zan cen sai Usman ya tun tsire da dariya Ahmad ya ce"Lafiya?" cikin dariya ya ce"amma ina wannan matar taka da ta fika girma sam-sam-sam baku dace ba"maganar da Zarah tayi d'azun ya maimaita tuni Ahmad ya d'aure fuska ya ce"wai Usman meye hakan ne ko kaima ka koma ita ne?bai bar dariya ba har ya saukesa gida shi kuwa ya wuce cike da k'uluwa da k'udirin duk ranar da suka kuma had'uwa sai ya gyara mata zama.
..............................
Cike da mamaki Zarah ta fito daga gidansu wai ana kiranta waje ita abin ma wani banbara k'wai ya mata sanin tun da take ba'a ta'ba zuwa gurinta da sunan zance ba,ita kuwa Hanne sai murna take wai 'yar tata ta fara zama mace tun da har an fara zuwa nemanta,ganin Saif cikin had'ad'd'ar motarsa abin ya bata mamaki matuk'a da gaske acewarta Hisham ne,da sauri ta k'arasa tana harararsa ta ce"wai Hisham ba nace ka rabu dani ba,murmushin yaudara yayi ya ce"da zaki kira ni da Saif ko Saifuddeen da nafi jin dad'i akan Hisham" ta ce"koma me nene ni bai dameni ba,ya ce"da zaki shugo da yafi wata magana zan miki",ba tunanin komai ta shiga motar,wani sanyi yaji aransa ya ce"yauwa ko kefa",ta ce"Sai ka fad'a,mai maimakon yayi magana sai kawai naji ya chachimeta da sauri ta zaro ido ta ce"lafiya?numfashi yake saukewa da k'yar nan take idanuwansa suka sauya kala,k'ok'arin k'wace kanta take amma ta kasa domin sosai ya matseta,jin hannunsa cikin rigarta yasata zaro ido da sauri domin tun da take da Hisham bai ta'ba zura hannu cikin rigarta ba sai yau,jin yana k'ok'arin fito da dukiyar fulaninta yasata saurin bige hannunsa amma ta kasa sosai yake chakud'asu ta kusan fita haiyacinta gashi ya had'e bakinsu sai wani fitar da numfashi yake,turesa take amma kamar tana ture dutse ta kasa, Saif kuwa tuni ya fita cikin haiyacinsa.......
*Na kusa da na ƙarshe a free pages, ƴar uwa hanzarta kar ayi tafiyar gawurtattu biyar baki ciki.*
[10/11, 3:32 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._
_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA.✌️_
*UMMU AFFAN*🤏
🅿️ 1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣
_Last free pages._😇
...Sosai ya ke yamutsata son ran shi. Allah ne ya bata sa'a ta samu ta tunkud'esa da k'arfi domin duka jikin shi ya gama mutuwa. Bin ta ya yi da kallo kamar d'an mayu. Ta ce"Amma kai d'an akuya ne?" Sosai ya ji zafin Maganarta taya wannan k'azamar yarinyar zata kira shi da haka? Ɗaga hannu ya yi zai mareta sai kuma ya sauke da ya tuno k'udurinshi a kan ta, cikin wahalalliyar murya ya ce"Zahra kin san ina sonki fa" Ta ce"Ni kuma kasan bana sonka don Allah ka rabu dani" ya tsani ta ce bata son sa aran shi ya ce ke idan ban da ina son na huta da ke mai zai kawo ni cikin wannan unguwar taku ma balle har na kulaki baki san waye ni ba. Ya ce"Zarah komai kike so zan baki kud'i ke idan ma zaki bar aikinki ni a kullum zai iya baki fiye da abin da ake baki a duk wata ni kuma a kullum." Wani kallo ta masa ta ce"Ohh haba Baabaa" ta fad'a cikin maganar kwalawa. "Hisham ni zan wuce" ya ce"ki ce min Saif" hannu yasa aljihu ya ciro kud'i ya mik'a mata. "Ga wannan" kud'in tabi da kallo sai kuma ta girgiza kai ta ce"A'a na gode" zata bud'e motar ta fita da sauri ya damk'i hannunta yana girgiza kai ya ce"No Zarah" ta fin hannunta ya bud'e ya saka mata kud'in sannan ya manna mata kiss ya ce"Sai na sake dawowa da fatan zaki sakar min jikinki nayi yarda na ke so" Da kansa ya bud'e mata, fita tayi ta tsaya tana kallonsa har yaja motarsa ya wuce. Kud'in hannunta ta duba da ya bata kusan dubu ashirin, Feesu ce ta k'ara so tana bin bayan motar da ta ga k'anwar tata ta fito ciki sannan ta k'araso tare da kallon hannunta cikin alamar tuhuma ta ce"Zarah waye wancen?" Ɗ'an yatsi fuska tayi ta ce"Wani ne" sannan taci gaba da tafiyarta.
Bin bayanta Feesu tayi, yarda ita ta lalata rayuwarta bata son ita ma Zarah ta kasance cikin irin halin da take ciki. Hanne tana ganin ta shugo ta ce"Iye-iye 'yan matan Hanne a yau na yarda mace na haifa ba mata maza ba." Feesu ta d'aure fuska ta ce"Wai Hanne me ke faruwa ne?cikin murna ta ce"Saurayi ne fa yazo yana sonta wannan abun farin ciki har ina?" Feesu ta zaro ido ta ce"saurayi kuma?kallon Zarah tayi ta ce"Zarah wallahi ki natsu karki kuskura ki biyewa samarin zamani basu da imani." Hanne ta fara tafa hannu ta ce"Yau na shiga uku bak'in ciki k'iri-k'iri ba tsoran Allah to wallahi Feesu kiji tsoron Allah ke dake da samarin kwando-kwando ita sai ki mata bak'in ciki?"
Tsaki Feesu ta ja ta ce"Ke ce zance kiji tsoron Allah karki jefa rayuwar 'yarki cikin garari." Zarah ta kama hannun Hanne ta zuba mata kud'in ta ce"Ga abin da ya bani" Ai wata bud'a da Hanne tayi yasa Musa k'arasowa da sauri yana tambayar lafiya" Hanne ta ce Musa ta yani murna Zarah tayi farar k'afa tayi goshi daga zuwan farko saurayi ya bata dubu ashirin nan gaba kuma sai hamsin, ai nan fa suka kama murna harda taka rawa, Zarah ta girgiza kai kawai ta wuce ciki. Feesu ta ce"Wallahi kun dai ji kunya bamuyi dacen iyaye ba mu kam." Musa ya ce"Cen da ya warki ke dai bak'in ciki kike" Hanne ta ce"Ai kuwa kuma sai dai y'an bak'in ciki su mutu" cike da takaici Feesu ta wuce ciki tanawa Zarah masifa da fad'an karta kuskura wani namiji ya rabata da 'yan cinta mutumcinta.
D'an murmushi tayi ta ce"Haba Feesu ai daman ni ba irinki bace duk abin da kike tunani ni bazan ta'ba aikata hakan ba" Wani sanyi Feesu taji aranta don harga Allah bata son rayuwar k'anwarta ta shiga irin tata rayuwar.
.....................
Rihah ce zaune tayi tagumi abubuwa da yawa ne ke dawo mata, tana son ta zamo sila kuma sanadiyyar warwarar matsalar da tawa danginsu ka tutu, amma ta ina zata fara?ta tambayi zuciyarta domin abubuwan akwai rikitarwa mahaifinta yasan ita d'in tasan wasu abubuwa da yawa cikin lamarinsa amma ta inda zata fara ne matsalar har cikin zuciyarta tayi da nasanin kasantuwarta 'ya a gurinsa sai dai bata da yarda zatayi haka Allah ya tsara, shugowa yayi gidan ransa a 'bace, a hankalin ta d'ago ido ta kallesa gurinta ya k'ara so da sauri.
"Sannu da zuwa Daddy" ta fad'a ganin ita yake tun karowa, d'aure fuska yayi sosai ya ce"Rihah yaushe ne zaki koma England kin san dai ko Secondary baki kammala ba" Hawaye ne suka fara zubo mata tayi k'asa da kai cikin takaici. Ya ce"tambayarki nake kin yi shuru yaushe hutunki zai k'are?" A hankali ta d'ago ta ce"Daddy me yasa ba ka son zama na kusa da ku? Ni fa 'ya macece ya dace ace ina kusa da ku" zai yi magana Saif ya shugo. Umma kuma ta sakko daga sama, Saif ya zauna kusa da Rihah tare da d'ago fuskarta ya ce"Rihah me ke faruwa kike kuka?" Kallon Daddy tayi kafin ta ce"Yaya Saif tun da ka kammala karatunka me zai sah Daddy ba xaiyi hakuri ba ni ya barni naci gaba da karatuna anan ba, ni bana son komawa ni kad'ai, ni fa macece mai yasa Daddy bai duba da hakan?" Ta k'arashe cikin kuka, duka jikinsu yayi sanyi musamman Umma ta ce"Alhaji kayi hakuri kawai ta ci gaba da karatunta anan ni bana son abin da zaije yazo" Saif ya ce"Haka ne nima abin da zance kenan tun da ta nuna bata so Daddy ka hakura kawai." Duka kallonsu yake zuciyarsa na hasala bai ce komai ya nufi sama, Saif ya fara share mata hawayenta ya ce"Kiyi hakuri Little Sis" Hawayenta sun kasa daina zuba ya ce"Rihah anya kukan nan na iyakar barinki karatu anan ne kuwa?" Kallonsa tayi Cikin zubar hawaye ta ce"Me yasa Daddy baya son barinmu k'asar nan?Yah Saif ina batun Abbu Ummi dasu Yaya Sadik? Me yasa Daddy bai son ayi maganarsu?me yasa duka 'yan gidan nan kowa yayi burus da batun?zuciyata ta kasa yarda ta kasa aminta da wannan curarren al'amarin." Ta idasa da sakin kuka, sosai jikin Saif ya yi sanyi ya ce"Nima ina tunanin hakan amma me yasa tun da Daddy baya so bazaki bar zancen ba" Da sauri ta kallesa ta ce"Ada family d'inmu ba haka suke ba, na fika sanin komai tun da na fika zama kai ko a 'yan gidan nan ba kowa ka sani ba amma ni na son kowa nafika son mutane da shiga cikinsu. Yaya Saif idan har za a ci gaba da zama a haka akwai babbar matsala" Dafe kansa ya yi ya ce"Rihah kema wani lokacin kina da matsala, wai ina ruwanki da damuwar wasu?Kiji da kanki mana" mik'ewa ya yi ya ce"Haka kawai ina cikin farin ciki kin zo zaki bani damuwa, ni dai ina shawartarki ki mance da kowa da komai idan kina so ku zauna lafiya da Daddy tun da ya nuna min baya so kin ga na sake maganar?" Hayewa sama ya yi ya bar Rihah a gurin. Binsa tayi da kallo tana share hawaye a fili ta ce"In sha Allahu sai na gyara komai ni bazan bari hakan taci gaba da faruwa ba ko da kuwa zan rasa raina ne." Ta idasa da shasshek'ar kuka muryarta cike da rauni.
........................
Ahmad yanzu abubuwa sun masa yawa ko lokacin Hafsat bashi dashi, ita kuma sosai ta damu da hakan ta kasa samun mafita tun farko da tasan hakan zai kasance da bata yarda ta k'arfafa masa guiwar yayi siyasar nan ba tun da bashi da ra a yi amma yanzu mutane sun cusa masa ra'ayin yafi damuwa da damuwar mutane akan tata shi kenan baya zama, bayan wasu 'yan siyasar da yawa kullum suna cikin
Showing 18001 words to 21000 words out of 22503 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8