son zuwa gida me yasa? cikin kuka tace"shikenan mu kuma acen zamu k'are bazamu dawo k'asarmu kusa da danginmu da iyayenmu ba Umma kinsan bani da ra'ayin karatun waje Abba ne ya takuramin gashinan silar haka ya jefa rayuwar Yah Saif cikin wani mummunan ha....Umma ta katseta ta hanyar d'aga mata hannu tace"kinga kad'an daga cikin halayenki ko?yanzu Yayan naki kike son jawa wani mugun alkaba'in?yaro yana cen ya mayar da hankali ga karatunsa ba irinki ba,sosai Rihah ke hawaye tana girgiza kai zatayi magana Umma ta d'aga mata hannu"Raihanatu bana son kiyi wata magana anan bazaki jawa yarona wani abunba waike mai yasa baki fad'an alkhairi ne." tana kaiwa nan ta wuce tana mita."
Riha zamewa a gurin tayi tana hawaye cike da takaici hali irin na iyayenta,sosai take kuka aranta tanaji ina ma basu suka haifeta ba,tashi tayi ta fito,chekk ta tsaya ta zubawa part d'in da take tsaye gurin ido sosai hawaye suka fara zubo mata kamar kullum ko da yaushe idan tazo k'asar sai ta shiga ciki duk da a yanzu babu kowa a ciki,sai dai komai nasu yana nan tsaf yarda yake domin Kakansu yana sawa a gyara part d'in duk bayan sati guda,kai tsaye d'akin 'yar uwarta aminiyarta k'awarta masoyiyarta ta shiga,zaunawa tayi bakin tangameman gadonta tana kuka tace a fili "Abbu Ammi da aminiyata ta fad'a cikin kuka mai tsuma zuciya,wani pic dake saman gadon ta d'auka,Abbu da Ammi sai wata matashiyar budurwa a tsakiyarsu duka sun rik'eta cikin murmushi sosai sukayi kyau,rungume pic d'in tayi tana kuka,ta kusan awa biyu a bedroom d'in sannan ta sake gyara d'akin tafito tana waiwaye da hawaye a idonta,part d'in Kakansu ta wuce tsoho mai ran k'arfe hakimin Katsina duk da yanzu ya tsufa d'ansa na biyu ne ya gajesa mai biwa Alhaji Tafida dominshi Abban su Rihan yace"sarauta bata gabansa siyasa ce gabansa,da sallama ta shiga ciki da fara'a ta nufi tsohon wanda ta iske zaune a parliunsa sai hadimansa dake masa komai cikin fara'a yace"wacece na ke gani kama RAIHANATU tsohuwar matar hakimi,sosai ta saka daruya da k'arawa gabansa tana son tsohon nan sosai cikin shagwa'ba ta ce.....
[10/10, 4:01 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._


_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._


*UMMU AFFAN*🤏


🅿️ 9️⃣ & 🔟


Ta ce, "Ni ba tsohuwa ba ce kaine tsoho"
"Kina gani na yaro sabon jini ki kirani wani tsoho? To ke kan ki kin mini tsofa."
Gaba d'aya suka saka dariya, zaunawa tayi ta ce,
"Kaka ina wuni'' ya ce"Lafiya k'alau ya karatun naku" "AlhamduLillah Kaka." Zaunawa tayi sukayi hira sosai domin haka yake mutum ne mai sakin jiki da son jikokinsa."

Kusan awarta biyu a gurin tsohon suna hira, yana son Rihah a cikin jikokinsa saboda kyawun halinta yarinya ce k'ara amma tana da k'wak'walwar manya, jin kiran sallah ya tasar da ita ta ma shi sallama sannan ta wuce part d'insu.

Sallah tayi sannan ta sake fitowa ta nufi sauran sassan gidan k'annan mahaifinta su biyu Alhaji Kamalu wanda shine MAGAJIN GARIN Katsina sai Alhaji Auwalu, dukansu suna da mata da yara kuma duk anan gidan suke da zama kowa da part d'insa.
Tafiya take tana tunanin rayuwa da abin da ya faru baya duk da lokacin ba wani wayau ne da ita ba amma tana tuna wasu abubuwan, tsayawa tayi cheek lokacin da idanuwanta suka kai ga wannan ginin na cen k'arshen gidansu k'urawa gurin ido tayi zuciyarta cike da zullumi tun da ta taso take ganin wancen ginin ada dai tasan na hadiman gidan ne amma a yanzu Abbanta tuntuni ya kulle gurin kuma babu me shiga dagashi sai amininsa abun na damunta sosai tana son sanin me suke shiga yi domin ita kad'ai ce bata yarda da shi ba, shi kan shi Abban ya sani don dodonsa ya sanar masa komai dalilin da yasa bai son zamanta k'asar kenan, ta ra sa dalilin da yasa sam k'annan mahaifinta basa magana akan hakan duk da tana ganin take-taken Abban nasu kamar yayi wani abun a kan hakan, a hankali ta fara takawa k'irjinta na bugawa sosai, tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki,da haka har ta kusan k'arasawa,Mahaifinta ne ta ga ya fito daga ciki,da sauri ta juya tayi kamar ba gurin take nufa ba,ya ganta amma bai ce mata komai ba,da haka ta samu ta k'arasa part d'insu tana shiga kai tsaye bedroom d'inta ta wuce ta fad'a saman bed tare da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta nad'e guri guda ta cure tana kuka sosai jin muryar mahaifinta yasa ta tsayar da kukanta chek"Riha "Riha "Riha kina ina ne?" Jikinta har rawa yake ta fito kan ta a k'asa bata yarda ta d'ago kai ta dubeshi ba,cikin tsananin masifa ya ce"Raihanatu ki kiyayeni ki fita sabgata idan ba so kike kema ki shiga cikin taskona ba,ina mai umartarki ko hanyar da zaki BQ kika sake bi wallahi ranki sai ya 'baci zan iya sallamaki wallahi idan har naga zaki kawo min matsala." Hawaye ne ke bin kuncinta cikin sanyin murya ta ce"To Abba." Mtsuuw!yaja tsaki tare da barin gurin yana mita,a gurin ta zube tana kuka sosai Umma ta fito ta ce"Ke dai wannan yarinyar ban san halin wacce kika gado ba,ni dai ba haka nake ba ubanki ma mai zafi ne sai dai a cikin danginsa kikayo gado ni dai ba haka nawa dangin suke ba." Tana gama fad'a tabar gurin Riha ta sake sakin kuka cike da tausayin kanta da na familynsu.
*********
"Zarah! Zarah!!" Habu ne ya shugo yana k'wala mata kira,fitowa tayi daga d'aki fuskar nan tata a d'aure,ta ce"kai Habu lafiya kake min irin wannan kiran kamar kana bina bashi,ya ce"ke dalla karki raina min wayau ta samu ne idan zaki iya? Su Alhaji Tafida ke son 'yan mata za su musu wani aiki shine nace zan nemoki" Wani kallo ta mashi da Ƙwalawa da rainin hankali ta ce"Waye hakan?" ya ce"Ubangidanmu ne shi nakewa aiki yana neman gwamnan jaha ne, amma kuma ma na tuna ba ke ya kamata na saba Feesu zatafi iyawa ke kina abu kamar maza ma taya zaki iya." Mtsuuww taja tsaki ta ce"Kuje kuyi ta musu aiki kuna shan bak'ar wahala sun raina yaran talakawa nasu yaran sun killace su,ku ne da musu bauta idan sunci su manta daku dagasu sai matayensu da yaransu kune shashashai suna amfani daku suna baku kayan maye da makamai wallahi Habu kayi hankali 'yan siyasar nan ba k'aunace suke nuna muku ba!" ,ya ce"dalla rufemin baki ke ina ruwanki tun da bazakiyi ba kinji nace miki dole?" Yayi ficewarshi yana tan gad'i. tsaki taja tare da shiga d'akin Hanne.

Hanne da ke d'aura kulle-kullenta da take sayarwa,su kuka,ku'bewa busassa,su gishiri,da maggi d'an kulli,ta d'ago tana kallo Zarah,wacce ta sami guri ta zauna bakin tsohon gadonta. Hanne ta ce"yanzu na gama gyara gadon sai kizo ki zauna ki 'bata min saboda ga marainiyar wayonki?" Zarah ta kad'a kai ta ce"ko mai zaki ce sai dai ki ce, ni nazo in tambayeki ne, gyara zama tayi tana gallawa Zarah harara ta ce"Ina jinki don idan ma kud'i ne wallahi kar ki soma tambayata don ban da su, ke ko ina dasu bazan baki ba." ta ce"ni nace miki kud'inki na ke so?me kike dashi da zaki bani Hanne?,tsuke baki tayi kafin a hankali ta ce"naji bani da shin kiyi tambayarki ki tashi ki bar min d'aki." Zarah ta ce"daman tambayarki zanyi mai yasa baku bamu tarbiyya ba?me yasa ku ba iyaye bane kamar sauran wasu iyayen." Kama ha'ba Hanne tayi da zaro ido ta ce"oh! kinzo ki tuhume ni ne?to ban sani ba,kuma ki tashi ki bar min d'aki." Mik'ewa Zarah tayi ta ce"ko ba kice in fita ba daman fita zanyi ni wallahi ji nake ina ma baku ne iyayena ba." Sosai Hanne ta zaro ido tare da mik'ewa tsaye ta zuba ma Zarah ido wacce ke yarfe hannu da ciccijewa wai irin bonsewar nan,Hanne ta ce"to don ubanki ki canja iyayen mana." Zarah ta ce"da a kwai halin haka da nayi" tana fad'a ta fice."
Tsuww!!! Hanne taja tsaki taci gaba da aikinta tana mita,Zarah d'akinsu ta wuce tayi shirinta domin fita gurin aiki a ranta tana mai jin haushin iyayen nata,babban abun takaici tana fita taga an kawo Musa jane-jane da jini wai sunyi fad'a garin gaddamar cha-cha,kamar ta wuce amma ganin halin da yake yasa ta tsaya ita ba tausayinsa taji ba domin sam bata da tausayi idan akan k'arya ne,wani a ciki ya ce"yauwa Zarah gara da kika fito gashi nan ku kaishi asibiti idan ba haka ba kuwa akwai matsala." Wani hura hanci tayi ganin sun jibgeshi gabanta kuma sun wuce. Ciki ta shiga tare da kiran Hanne wacce tana ganinsa ta rud'e ta fara kururuwa bayan da zai fita da fad'a suka rabu (Allah sarki akace tsakanin mata da miji sai Allah),harara Zarah kawai take aika mata kafin ta ce"to ke ya za'ayi yanzu?kin tsaya kinawa mutane kuka." Habu ne ya iso gurin kallonsu yayi yana rangaji "me ke faruwa ne?" ya fad'a cikin muryarsu ta mashaya da daba,Hanne cikin kuka ta ce"Habu ina zan sani ni dai gani nayi Zarah ta kirani na gansa anan" Kallon Zarah yayi ya ce"ke kuma ya akayi ne kin zuba min ido sai kace na mujiya.'" harararshi tayi dacewa"Ai gara nawa akan naka ni dai nasan na gaba yayi gaba, na baya sai labari." ya ce"to naji me ya sami wannan mutumin?" Ya fad'a yana nuna Musa wai mahaifinsa ne mutumin. ta ce"su Saminu ne abokinsa suka kawosa wai sunyi fad'a akan gardamar chacha kuma idan ba'a kai shi asibiti ba da matsala." aljihu yasa hannu sai gashi ya fito da dubu biyar ya ce"yaci sa'a yasin daga gidan Alajina nake na sami kud'i da sai dai ya mutu a haka" Hanne ya ba mawa ya ce"ku kaishi asibiti,Sannan ya shige cikin gida kamar zai kifa. Zarah ta kira mai napep sannan ya taimaka musu suka shigar dashi ciki sannan suka wuce asibintin genaral. Bayan an masa 'yan gwaje-gwaje suka ce kwantar dashi zasuyi, bayan sun basa gado aka d'aura masa k'arin ruwa,mik'ewa Zarah tayi bayan likitocin sun fita,ta ce"Hanne yau na makara zan wuce Allah ya k'ara sauk'i" ta ce"to yanzu idan ya farka mai zan bashi? ni tsorona d'aya ma kar likitan nan ya cika mana kud'i kin ga dubu biyar Habu ya ba mu." Ta ce"ki tambayeshi idan ya farka shi kansa ba zai rasa kud'i ba kin dai san halinsa sarai." tana kaiwa nan ta wuce,mutane sai kallonta suke ganin yarda take tafiyar maza wasu har dariya suke hakan bai dameta ba ta sami d'an a cha'ba ta hau ta wuce."
...........................
"What!?Daddy kasan abin da kake fad'a kuwa?" Murmushi yayi ya ce"na sani Ahamaduna kuma nasan kai bazaka bani kunya ba zaka iya sai ma ka fini iyawa." Girgiza kan shi Ahmad ya ke ya ce"Don Allah Daddy ka dena wannan maganar please." Murmushin yak'e Daddy yayi ya ce"Ahmad ni kad'ai nasan yarda nake ji ban san mai yasa mini hakan ba ko iyayenka na kasa sanarwa amma ina jin jikina wani iri." Hannayensa duka biyun Ahmaf ya rik'e ya ce"babu abin da zai sameka Daddy abin da kake d'aurani a kai yafi k'arfina bazan iya ba." wani murmushi yayi tare da shima rik'e hannayensa da kyau ya ce"zaka iya Ahmad." sosai jikinsa yayi sanyi,duk maganar nan suna yinta ne lokacin da Ahmad shi da mutane da yawa suka rako Alhaji Mahmud mai abaya da matemakinsa da wasu manya a k'asar nan Air port domin zasuje wani taro ne Abuja shugaban k'asa da kansa ya kirayi duka gwamnonin k'asar nan. Ahmad yaso raka mahaifin nasa sai ya nuna masa babu yuwur hakan,haka suka shiga jirgi shida wasu manyan mutane da 'yan sanda da dama,Ahmad shida matemakin mahaifinsa basu koma ba sai da sukaga jirgin ya tashi sannan suka wuce"a duk lokacin da Ahmad ya tuno maganar mahaifinsa sai hawaye sun zubo masa gashi haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi sosai,masallaci ya wuce domin sallar magrib sai da yayi isha'i sannan ya shiga gida domin ya d'auki Hafsat su wuce" Dukansu suna zaune parlour suna kallon labarai,dai-dai shugowarsa aka nuno abin da gaba d'aya ya tayar musu da hankali a BBC News,lokaci guda Hajiya Batula Hajiya Anty da Hafsat suka mik'e Ahmad kuwa mutuwar tsaye yayi.... .[10/11, 6:22 AM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._



_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA✌️._


*UMMU AFFAN.*🤏



🅿️ 1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣


...Ba komai ba ne sai ganin jirgin da su Alhaji Mahmud mai abaya suka hau a tafiyar da su ka yi, Ya fad'o daga sama ya k'une wanda ba asan dalilin hakan ba, kafin ya yi wani k'wak'k'waran motsi sai jin muryar mutane suka yi a waje, ana ta hayaniya. Mataimakin gwamna ne Alhaji Sani ya shugo hankalinshi a matuk'ar tashe domin mutum ne mai adalci kusan duka halayensu d'aya da mahaifin Ahmad.

Da sauri Hajiya Batula ta k'arasa gaban shi. Cikin wata irin murya ta ce "An ciro su?" Ta fad'a cikin kuka.

Hawayen da ke zubo mashi ya sa hannu yana gogewa, ya kasa magana hannun Ahmad kawai yaja suka fita. Hajiya Batula kuka ta fara tare da zubewa a gurin jiki a sanyaye Hajiya Anty ta k'ara so gurin itan ma kuka take ta dafa ta sukaci gaba da kuka.
Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, kullu nafsin za'ikatul maut dukkan wani mai rai mamaci ne Allahu akbar sanadiyyar hakan Alhaji Mahmud mai abaya da duk wanda ke cikin jirgin Allah ya amshi rayuwarsa, duka jahar Katsina tana cikin wani yanayi na alhini harma da gwamnatin tarayya da sauran jahohin Nigeria domin shid'in ya yi suna wajen aikin alkhairin da ya kewa jaharsa, lokaci k'ank'ani gidan gwamnati ya cika mak'il da mutane manyan k'asar nan da sauran mutane. Ahmad kuwa ya zama kamar mutum-mutumi shi dai gashi nan ba ummm ba uhmmm uhmmm aka ce kukan zuciya yafi na fili ciwo, to tabbas Ahmad kukan zuci yake.

Haka aka suturta duk wanda ya rasu aka kai su gidajensu na gaskiya, Allahu akbar duk wanda ya mutu shi kenan kuma sai addu'a amma a wannan lokaci jahar Katsina tayi sanyi tayi shuru duk inda ka ratsa maganar mutuwar ake kowa matan alkhairi suke masa domin a tarihin jahar ba'a ta'ba samun gwamna mai adalci irinsa ba.

Hajiya Batula da Hajiya Anty suna cikin wani hali duka dangi da 'ya'yansu dake gidajen mazajensu sun zo haka surukarsu Hafsat, gidan har akayi kwana goma bai rabu da jama'a ba har akayi arba'in, tuni kuwa mataimakin gwamna Alhaji Sani ya maye gurbin gwamna yana rik'on kwarya kafin ayi za'be. Ahmad bayan nan sai da aka kwantar dashi asibiti saboda bai magana kallon kowa kawai yake yi amma daga baya ya dangana, don yasan mutuwa dole ce tana kan ko wanne bawa.
...........................
Sosai ake shagali, buzumin Sa aka yanka aka gasa shi tare da shimfid'eshi saman wani babban tebur ga kayan shaye-shaye wato lemuka na kwali da na robobi dana kwalba kala-kala, babu abin da ka ke ji sai sauti mai sanyi yana tashi. Alhaji Kabiru Tafida kenan da mutanansa suna murnar mutuwar gwamna mai ci a yanzu inda ya shirya musu wannan liyafar domin nuna tsantar murna da farin cikinsu, babu abin da suke sai dariya Alhaji Mudi ya rad'a masa a kunne cewa"Mutumina babu babban shege irinka." Cikin farin ciki da fara'a ya ce"Ni d'in ai ba na wasa bane, Wallahi faɗa da aljani babu ƙyau, duk wanda yaci tuwo da ni daman ya tabbatar miya ya sha. Dole ne nayi gwamna ko ank'i ko anso sai naci, kai bari kaji wallahi akan siyasar nan babu abin da bazan iya ba dole ne na yad'a manufata." Tafawa su ka yi suna sakin dariya, tare suka mik'e gaba d'aya kowa da k'aramar wuk'a da chokali mai yatsu a hannunsa suka zagaye teburin da ke da wannan gasasshen San. Ɗaga hannu sukayi da cewa"PRP koresu PRP koresu PRP sai ta korasu ko basa so." suka saki dariya mai k'arfi sannan suka fara yanka suna ci cikin tsantsar farin ciki da annashuwa.
Da haka wannan taro nasu ya k'are cikin farin ciki.

Rihah ce zaune a parlour ta takure abin duniya duk yabi ya isheta domin cikin kunnanta taji abin da ya furgita tunaninta wai da sa hannun mahaifinta aka saka bom a jirgir da gwamnan jahar nan. A duk lokacin da ta tuno wannan mitin da mahaifinta ya yi da wasu mutane sai gabanta ya fad'i, sannan ta saki kuka wannan wacce irin rayuwa ce har kasa a kashe rai haka kawai saboda mulki da siyasa tabbas mahaifinta yana da tarun zunubai masu yawa, wayarta ta d'auko da niyyar kiran Yayanta Saif da sauri ta fasa domin tuno halinshi kusan d'aya da mahaifinsu idan ma ta fad'a masa tasan asiri zai tona mata, kanta ta saka tsakankanin cinyarta tana kuka sosai.

Umma ce ta sakko daga sama bin 'yar tata tayi da kallo tana girgiza kai, ta k'arasa kusa da ita tare da zama, da sauri Riha ta bud'e ido jin motsi. Tana ganin Umma ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, Umma ta fara shafa bayanta alamar rarrashi dacewa"Haba Riha ya kike son jefa rayuwarki cikin wani hali har ki haifarwa da kan ki damuwa?" cikin kuka ta ce"Umma me yasa kika kasa fahimtata? Ya dace ace kece ta farko da zaki fahimce ni da amshi uzurina.''

Ta ce"Akan wanne irin dalilin? Rihah idan kina son kwanciyar hankali to ki fita daga sabgar mahaifinki! i
Idan ba haka ba kuwa wallahi zaki sha mamaki ni dai ba ruwana na sanar miki" Hawaye masu zafi suka gangaro a kuncinta gyad'a kai kawai tayi alamar "To" domin ta kasa magana saboda damuwa da takaici. Umma ta fara share mata hawaye ta ce"Ki fara shiri kin san dai jibi zaki koma England" ta ce"To Umma."

Da haka ta tashi tabar gurin zuciyarta cike da zullumi.
..............................
Musa sosai ya sami lafiya domin yana farkowa ya fara zage-zage sai da Hanne ta rik'eshi, ya ce"Kai lafiya wa ya kawo ni nan?" Abin da ya faru ta sanar dashi ya ce"wallahi tallahi bazan rabu da shi ba sai na rama ki kiramin likitan su sallame ni" Dai-dai nan Zarah ta shugo hannunta d'auke da take away
Showing 9001 words to 12000 words out of 22503 words