[10/10, 3:42 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon Salo._



©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN


_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA BIYU._✌️🔥



*Godiya ta tabbata ga Allah da ya sake bani dama da iko na kawo muku wani sabon labarin sabon takun kuma sabon salo, Allah ka ƙara bani iko da aminci lafiya da basira incigaba da kawo muku gawurtattun labari. Dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halittu Annabi Muhammad S A W.*


_Wannan karon ma labarin ƙirƙirarre ne, da fatan zaku bani haɗin kai domin fahimtar inda ya dosa, sannan ban yadda a juya mini labari ta kowacce irin siga ba ba tare da izini na ba, idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne._


_MASU SO NA ƊAURA MUSU TALLA A PAGES NA LITTAFINA ZASU IYA MAGANA CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, MAI TALLA SHI KE DA RIBA 08104335144._


*_Bismillahir rahmanir rahim._*



🅿️ 1️⃣ & 2️⃣


...Sosai ta ke juyi a saman gadon tana girgiza kai da fizge-fizge kai da ka kalleta kasan tana cikin wani yanayi kuma a hakan idanuwanta a rufe suke kamar mai bacci, cikin wata irin murya mai ɗan ƙara da sauti ake mata magana "Zahra ina sonki kuma har abada ba zan iya rabuwa da ke ba ke tawa ce ni ɗaya."

Bin shi take da kallo ta kasa magana shi kuwa ta kowa yake gareta har ya ƙaraso bakin gadon. Zaunawa yayi tare da ɗagota jikinsa ya fara sarrafa ko ina na jikinta, ita dai ga tanan kamar mutum-mutumi ta kasa ko da ɗaga ɗan yatsan hannunta, bakinsa ya saka cikin nata yana tsotsa kamar ya sami lollipop, sun daɗe cikin wannan yanayin a hankali ya ɗago rikitattun idanuwanshi ya ce, "Zahra ke tawa ce har abada." Wani irin haske ne ya bayyana wanda ko idaniyarka ba zaka iya ɗagawa ka kallaba saboda tsananin hasken, bayyanar hasken shi yasa kamar anyi walƙiya sai kuma d'uf!! Ya ɓace kamar anyi ƙiftawar ido. Hasken ne yaci gaba da matsota.
A matuƙar hargitse ta farko daga baccin da take wanda in har zata kwanta sai tayi wannan mafarkin, kasancewarta mara tsoro da kuma da kakkiyar zuciya yasata zaunawa akan gadon tana tariyo abin da ya faru *Hisham!* ta kira sunansa kamar yadda ya sanar mata a mafarki, sai ji tayi kamar daga sama an amsa mata _Na'am Zarahta abar sona a ko da yaushe kuma ako wane lokaci ina tare da ke_ da sauri ta fara waige-waige a cikin ɗakin amma ba ta ga kowa ba.

Tsuww!!! ta ja tsaki tare da miƙewa, riga da wando ne a jikinta sak na maza domin jeans ne da t-shirt mai kwala irin ta maza kanta hula ce ta tusa gashin kanta ciki, fitowa tayi tsakar gida daidai fitowar Hanne daga ban ɗaki wato mahaifiyarta, kallonta tayi tana hura hanci "Yo Hanne me zan samu ne ko an jiƙa kwakin ne ko yau an sami garau-garau!"

Wata harara ta banka mata ta ce"Sannu Baabata kin san dai kowa tasa ta fishshesa akeyi a cikin gidan nan don haka idan kina da kuɗi sai ki saya kici. Zarah ta kalli Hanne da ƙyau ta ce"Allah ko?" Cikin maganar kalar ta maza nigogi. Hanne taja tsaki tare da cewa"Ƙyayi kuma ai" Feesu ce ta shugo cikin shigar ƙananun kaya kan nan nata yasha ƙarin gashi hannunta riƙe da leda, guri ta samu ta zauna da sauri Hanne ta ƙaraso ta ce"Nafisatu sannu da dawowa" Harara ta banka mata ta ce"Yo wanne dare ne jemage bai gani ba? Dole kice min sannu da dawowa Hanne tun da kin ga leda a hannuna kuma yasin kin bar cinshi nima fita nayi aka amfanu dani sannan har na samu na saya." Girgiza kai Zarah tayi ta ce"Matsalar talauci kenan matsiyatan banza kawai ke Hanne ba yanzu kika gama cewa kowa tashi ta fissheshi ba to kema taki ta fishshe ki" cikin maganar nigogi tayi maganar tare da damsewa tayi hanyar waje a hakan babu hijab balle mayafi, tana tafe tana cilla ƙafa yadda dai maza nigogi ke yi. Kai tsaye bakin kasuwa ta nufa gurin da Hajiya Sa'a me sayar da abinci take, tana zuwa ta fara gaisawa da jama'a cikin fara'a domin kowa yasanta da fara'a da sakin fuska take, gurin Hajiya Sa'a ta ƙarasa,ta ce"Hajjaju ya garin?ya yau?" dukkan maganarta ta nigogi maza take yinta. Hajiya ta ce"Zarah yau kin makaro don haka ki koma gaskiya bazan ɗauke ki ba, bayan na sanar miki ƙarfe tara na safe zakizo yanzu fa sha ɗaya ta kusa" Zarah ta ce"Haba-haba Hajjaju aike tamu ce karki ji komai ai ana tare ko ba haka ba?" Ta idasa maganar tana karkata baki da ɗaɗɗa hannu tana yarfewa irin na gayu. Hajita Sa'a ta ce"gaskiya kina cin sa'a ta fa Zarah kije ki mimmiƙawa waɗanda suka saya tukun kafin kici abincin" "Yawwa Hajjaju tamu ina yinki fa a gaskiya ina yinki." Wucewa tayi zuwa cikin rumfar ta fara miƙa musu, zaune ta hangesa cikin kujerar yana murmushi da kallonta, chek ta tsaya tana kallonsa cikin sanyin murya tace" *Hisham!* murmushi yayi ya ce"eh ni ki ƙaraso gare ni masoyiyata!" Waiwayen bayanta tayi babu mai kallonta sai ta girgiza kai kawai ta koma ciki. Har ta kammala aikinta na ranar Hajiya Sa'a ta sallameta sannan ta juya zuwa gida, tana tafe tana daga ƙafa dai-dai wucewarta ta gungun samari matasa ta ce" yah Baaba ya kuke?duka suka d'aga mata hannu da cewa "Lafiya." Wucewa tayi shago zata sayi kayan shayi sai kawai Bala ya ce"daman yanzu mutumin nan ya fita ga abinda ya ce na baki" amsar ledar da Bala ke miƙo mata tayi,leƙawa cikin ledar tayi kayan shayi ne da bread duk dai abinda tayi niyyar saya komai ta gani a fili ta ce"Wai wa?" ya ce"wannan dai da yasa ba bani na baki." bakinta ne taji ya furta *Hisham!* wucewa tayi gida Hanne riƙe da kwalar Musa wato mahaifinsu suna surfawa juna masifa yana cewa "Hanne ki sake ni na wuce" tana cewa"Baka isaba mashayin banza yau sai ka bamu na abinci kai kenan kullum bazaka ciyar da iyalanka ba" Tana shugowa Hanne da Musa suka zuba mata ido Hanne ta sake shi ta ce"Yauwa 'yar albarka sannu da dawo ni nasan Zarah bazata barmu mu kwana haka ba." Wani kallon kwalawa ta mata tace"kika ce me?to kiji da k'yau wallahi kowa ta bisshesa babu ruwa." Tayi shigewarta ciki tana ta6e baki da cewa"sai dai kuyi tayi,Musa kuwa tuni ya fece Hanne ta bisa har ƙofar gida tana masifa shi dai ya samu ya gudu.
*****
Wasu ƙyawawan motoci ne jere reras a saman titi kusan guda goma, manyan motoci masu matuk'ar k'yau da tsada gaba da police baya ta police da alamar wani babban mutum ne zai wuce, jama'a sosai sun taru sai d'aga masa hannu suke, shid'in ma cikin fara'a yake d'aga musu hannu, gwamnar jahar Katsina kenan mai ci a yanzu His-Excellency Alhaji Mahmud Mai Abaya gwamna mai k'warjini da kamala haka yayi ta jagaye jama'a cikin sakin fuska yana d'aga hannayensa gefe guda babban d'ansa ne shima tsaye yana d'aga hannu da ka kallesa kasan fara'arsa akan dole yake yinta lokaci-lokaci ya kan d'an ja tsaki domin hayaniyar mutane sosai take damunshj shi mutum ne mara fara'a da rashin son mutane siyasa sam bata ra'ayinsa kamar yarda mahaifin nasa ke burin ganin d'an nasa ya fantsama harkar ta siyasa, a haka dai suka kammala kamfen nasu domin ana gab da fara zaɓe Alhaji Mahmud mai Abaya yana son cigaba da gwamnan sa 4+4 kamar yarda jama'a ke k'aunarshi da haka suka gama, suna komawa gida ya wuce part d'insa yana sakin tsaki wai a kan me mahaifin nasa zai takura masa akan lallai sai ya shiga harkar nan ta siyasa shifa baya son hayaniya ko kad'an burinshi na zama Low ne amma mahaifin nasa yasa shi karantar fannin siyasa domin faranta ran mahaifinsa haka ya daure yayi yanzu ya kammala taya zai sa shi ta dole sai ya shiga siyasaa *Ahmad* Kenan babban d'a a gurin Gwamna mai ci yanzu Alhaji Mahmud mai Abaya." Dafe kansa yayi da ke barazanar tarwatsewa saboda hayaniyar da yasha ta samasa ciwon kai. Hajiya Batula ce ta shugo part d'insa wato mahaifiyarsa cikin shigar alfarma wani d'ank'areran les ne a jikinta tasha make up ta yafa mayafi kalar leshin k'afarta da takalli mai kyau cikin fara'a ta dubesa "My Son Mahaifinka ya shugo fa yana jiranka." d'agowa yayi cikin da kushewar murya ya ce"Haba Mum akan me Dad zai takura min dole sai nayi abinda bana so Nifa Siyasa bata cikin ra'ayina." Zaunawa tayi tare da d'ago kansa ta d'aura saman cinyarta cikin taushin murya ta fara magana"My Son ina son kayi hak'uri kaso abinda mahaifinka ke so nan gaba zaka ga amfanin hakan, kace ni na fad'a maka." Cikin damuwa yace"Mum bana son damuwa ne da nuna hamaiya irin ta siyasar k'asar mu" ,ta ce"Weldone *Ahmad* karka damu in sha'Allahu siyasa Alkhairi ce a gareka." Murmushin yak'e kawai yayi, tare da mik'ewa ta kama hannunsa suka fita."
*****
Zarah ce zaune tana kallon Yayarta Feesu da Hanne suna fad'a dai-dai shugowar Habu, hannayenshi rik'e da adda da sanda domin riƙaƙƙan ɗan daba ne. Kallonsu ya ke wani irin a shawu yana rangaji saboda shaye-shayen da yake na wiwi da taba sigari, Feesu cikin rashin kunya da fitsara ta ce "Wai kai Habu mene ne haka zaka shugowa mutane ko sallama babu?" Ɗago jajayen idanuwansa yayi ya ce"Ke wallahi yanzu zan sassara miki jiki, idan kika nemi ki mini rashin kunya, ni tsaranki ne?" Tsaki taja mtsuww!!! Zata wuce ya jawota da ƙarfi har sai da ta faɗi ya ɗaga wuƙa zai sara mata, sai ganin Zarah aka yi ta riƙe hannunshi da ƙarfi don har Feesu ta sadaƙat. Ta ɗauka shi kenan ta mutu, da ƙarfi ta saki ƙara jin shuru yasa ta buɗe idanuwanta sai ganin Zarah tayi riƙe da hannun Habu cikin zafin nama. Da sauri Feesu ta tashi daga ƙasan da ta faɗi duk da haka bakinta bai mutu ba ta ce"Wawa jaki kawai." Zarah ta ce cikin irin maganarta ta maza "Haba Baaba meye hakan kai sai kace ba namiji ba ai ba a biyewa mata." Cikin maye da maganar mashaya ya ce"Ai da kin barni na koyawa 'yar iska hankali tun da bata da kunya." Hanne ta ce"Ku dai yaran nan dukanku babu na ƙwarai, ni da Musa mun haifi bala'i yanzu daga mashayi sai karuwa sai ke Zarah da muka kasa gane kan ki macece ko namiji. Gaki nan dai sai kace mai *Ruhi biyu*" Zarah ta ce"Ai kun fini sani tun da ku kuka haife ni, kuma abu a duhu ina jin dai Ruhi buyu ne a jikina. Sannan yadda kika ce mu bala'i ne kuma bala'in kan ku ne chen da yawarki Hanne." Ta wuce tana kaɗa ƙafa da bonsin irin na gayu. Kasancewar magrib ake kira alwala tayi ta fara sallah bayan ta idar fita tayi da chenjinta gurin Bala mai kanti don juice da biskit zata saya taci ta kwanta saboda dare kuma rishonta babu kalezir bare ta dafa indomie. Tana shiga ya ce"Yawwa Zarah kamar kin san yanzu nake cewa zan aika miki don saurayin nan naki ya bani na baki." Kallonshi take bakinta a sake kafin ta miƙa hannu jiki a sanyaye ta amsa Juice ne da biskit kamar na yadda zata saya. ta ce"Amma Bala me yasa idan yazo baka kirana sai ya tafi." Murmushi yayi ya ce"Na sani ko lokacin baki gida karna aika baki nan." Juyawa tayi tana faɗin "To na gode" Bayan ta koma gida sallar isha'i tayi sannan ta zauna bakin ƙaramin gadonta ta ciro ta faraci. Feesu ce tsaye ke shirinta cikin ƙananun kaya riga da wando tayi matsu sosai, ta feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki jakarta tayi hanyar fita. Zarah ta ce"Feesu wai ke kullum kina hanyar fita baki zama gida ki kwana." Wani kallo ta mata kafin ta ce"To idan ban fita na nema ba kece zaki ciyar dani? Kina jin dai iyayenmu da kansu suka ce ko wacce ta fita ta nema ta ciyar da kanta to akan me zan zauna da yunwa gara naje na sami abin da na sama cikina." Tana kaiwa nan ta fice gyara kwanciya Zarah tayi tana cewa"Bazan biye miki ba gara na kwanta ƙarfe tara Hajjaju ta ce na fita ke ce gantalalliya. Kamar kullum cikin barcinta ta fara jin mutum kusa da ita, *Hisham* ta kira sunansa cikin cool voice kallonta kawai yake yana murmushi ta ce"Please kai waye me kake nema a gurina? Zaunawa yayi kusa da ita tun da take ganinsa a mafarki bata taɓa iya masa magana ba, wannan maganar da tayi ma a zuciyarta tayi sai dai ga mamakinta sai ji tayi ya ce"Zarahta a sannu zaki gane ko ni wane ne, abin da kawai nake so da ke kisa ni a zuciyarki karki bari wani ya ce zai raɓeki shine babban kuskure da zai yi a rayuwarshi" kallonsa kawai nake ko kiftawa babu gashi ko yatsana na kasa d'agawa magana nake son masa na kasa,d'agoni yayi juwa jikinsa sannan ya ce"Duk wani abu dake zuciyarki na sani nasan kina da tarin tambayoyi gami da ni lokaci shi zai nuna hakan zaki san koni waye" had'e fuskarsu yayi guri guda tare da zaro harshensa yana lasar hancinta zuwa cen ya sauka a bakinta ya fara tsotsa a hankali har izuwa wiyanta. Magana take son yi amma ji take kamar an d'aure mata harshenta, gangarowa yayi wuyanta yana lasa, k'ara ta saki da k'arfi tana kurma ihu dai-dai shugowar Hanne tana cewa "Lafiya?" Jin muryar Hanne ta bud'e idanuwanta a hankali rana ce ta kashe mata ido,ajiyar zuciya ta saki ganin har gari ya waye,tsohon agwogwonta ta kalla ganin goma saura ta tashi a furgice wanka tayi tare da sallah sannan ta fice,tana zuwa Hajiya Sa'a tace"wallahi Zarah baki isa ba,ni bazan iya ta bauta dake ba bayan ke baki min abinda nake so ce miki nayi tara na safe zaki dunga zuwa yanzu har goma da kwata,gyara tsayuwarta tayi tare da yarfe hannu tace"kin san dai bamu haka dake Hajjaju." "Daga yau sai mu fara." Hajiya Sa'a ta fad'a tana ci gaba da aikinta,juyawa Zarah tayi ba tare da ta sake cewa komai ba,har tayi d'an tafiya taji Hajiya Sa'a ta saki k'ara domin gama d'aya tukunyar girkinta ta 6are lokaci guda kamar an ture,ko da Zarah ta juyo ta gani murmushi tayi tare da bonsiwa tace"an gaya miki ni d'in tawasa ce,kawai ta wuce amma har cikin ranta take mamakin ya akayi tukunyar ta turgud'e ta6e baki tayi tare da d'aga kafad'a irin ko a jikinta d'in nan." Tunani take ina ya dace taje ta fara wani aikin domin dole ne tayi inhar tanason taci abinci don idan zata zauna babu aiki ba ruwan Musa da cinta bare Hanne,ji tayi kamar an d'agata sama sai ganinta tayi tsaye bakin gidan wani abinci na masu kud'i duk wanda zajaga yazo gidan abincin nan to wani k'usa ne a k'asar nan domin na manyan mutanene,hango ma'aikatan gurin tayi kowa da uniform d'insa gaba da bayanta ta kalla ita sam bata san ma ina ne nan ba."


08104335144
_Somin taɓi kenan, taɓa ka lashe._
[10/10, 3:49 PM] Sadfat: *SANDAR MAKAUNIYA...!*
_Sabon salo._


_GAWURTATTU BIYAR TAKU NA BIYU._✌️



*UMMU AFFAN*🤏


🅿️ 3️⃣ & 4️⃣


...Tunani da tambayar kan ta take ta shiga ko ta tsaya? Ganin irin motocin da ke shige da fice a gurin yasa ta ji a zuciyarta kamar idan ta je ma korota za a yi, sai kawai ta ji zuciyarta na hankad'ata ita dai bata san yadda a ka yi ta shiga ba sai ganinta tayi a ciki.

Gurin shugabar wajen ta nufa tun kafin tayi magana matar cikin fara'a ta ce, "Ƙwarai ke ce daman Yayanki yazo tun d'azun ya sanar min ina ganinki na gane ki, domin sak ya zayyano min yadda ki ke." Murmushi ne ya suɓucewa Zahra ita dai ba tasan ko na miye ba, nan matar ta fad'a mata aikinta a wajen kai wa kostomas abinci da tambayarsu abin da suke so.

Zahra tayi godiya sannan ta sanar da ita albashinta tare da bata uniform ta ce"Kije gida gobe sai ki dawo" Mik'ewa tayi"To na gode." Da haka ta fita wajen tana ta waige-waige."
..............................
Alhaji Kabiru Tafida shine d'an takara a babbar jam'iyyar hamayya ta PRP babban attajiri mai ji da dukiya da sarauta domin jinin sarauta ne shiyasa yake da *IZGILI*(Sunan book d'ina)da k'asaita mutum ne mai nuna mulki da d'agawa jinin sarauta ne amma Allah ya d'aura masa k'aunar siyasa ya shiryayin gwamnar jahar Katsina ko ta halin k'ak'a,tare sukayi da kara da ANPC Jam'iyar dake mulki a yanzu inda Alhaji Muhmud Mai Abaya ya kayar da shi da k'uruk'u masu dama,shiyasa a wannan karon ya shirya sosai domin sam baya son gwamnati mai ci tayi 4+4 burinsa ya tuntsirasu da k'asa koda ta hanyar satar k'uri'a, domin tuni suka shiryawa hakan ta hanyar shiga gidajen talakawa a kai musu kayan abinci bai wuce taliya kwaya da'aya da makroni d'aya da su maggi da bai wuce na nera hamsin ba sannan omo shima hakan da musu dad'in baki akan inhar suka dangwalawa jam'iyar PRP zasu sami abubuwa da dama,wanda shi kuma Alhaji Kabiru Tafida ba wannan ne a cikin zuciyarsa ba shi dai hangen mulki yake ta hanyar da zai tara kud'i da kuma mulki domin yanzu siyasar tamkar kasuwanci wasu daga ciki suka d'auketa."

Tsaye suke tare da gungun matasa 'yan bangar siyasa Alhaji Kabiru Tafida ya ce"Abin da nake so daku shine ku shirya gobe zamu fita yak'in neman zaɓe,sannan naji wancen banzan gwamnan Mai Abaya wai yau zai fita, ina son ku ta da musu hankali kar a sake abarsu suyi cikin lafiya, Ihuww suka saka Habu ne mai cewa"sai kai babba d'an gidan babba ba gudu baja baya ko ank'i ko anso sai ka lashe indai muna tare da kai sai kaci,murmushi kawai yake domin yana son yaji ana masa kirari nan ya ce"A bashi dubu goma" Ai Habu jin haka nan ya
Showing 1 words to 3000 words out of 22503 words