Yana yawo Akan screen din waya ta na yi saurin nunawa nafisat nace Mata gashi Nan ma Yana kira tace dauki Kar ta tsinke shima dai ga Alama ya kamu sai dai kafin na daga har Kiran ya tsinke Amma ba a Jima ba wani Kiran ya sake shigowa na daga Ina mishi sallama ya Kuma amsa Yana fadin Ranki yadade Justina shikenan kin barni ina ta jaje har gidan Redion BBC? Nayi murmushi nace ai kuwa baka Zo gidan mu ba da baka Kai Cigiya ba.....
"To ai ban San gidan naku ba tunda Baki fada min ba don Kar na kawo Miki ziyara......

"Idan kuwa zaka Zo me zai Hana na baka address?
"To abani address din sai nazo tunda ke kin min yaji. Murna ta cikani na Kuma tura mishi address din ya Kuma fada min Ranar da zai Zo zai kirani
Kawaye na sun bani shawarwari Akan kame kaina da Kuma kiyaye abinda zaisa Umar faruk ya janye jikin shi akainan don yadda sukaji muryar shi da kalaman shi kamar Babu yaudara Ni Kuma sai na fada musu sanadin haduwar mu dashi da irin taimakon da ya bani inda su duka sukace zasu so ganin shi don ya burgesu da Haka dai muka Rabu na dawo gida Ina ta dokin Ranar da Umar zai kirani yace min gashi Nan Zuwa don ban San irin tarbar da zanyi mishi ba
Kwana biyar da yin hakan sai ga Kiran nashi ya shigo waya ta na dauka Ina gaishe shi Ina Kuma tambayar shi Allah ya sa dai yau zai Zo? Ya Kuma tabbatar min da kwarai kuwa yau zaizo da misalin karfe biyar na yamma nace to Ina jiran zuwan shi

Karfe biyar kuwa na bugawa sai ga manyan motocin gidan igwai yarima Gibson ya karaso kawo min ziyarar ba zata a zatona bakona ne Umar faruk don Haka na fito tarbar shi cikin murna Amma Ina zuwa sai Naga Akasin hakan wato yarima Gibson cikin SHIGA ta nuna shi din jinin sarauta ne saboda kurewa da cinyewa ta fannin kyau da gayu inda Kuma naji kamar na fasa ihu ko in Fadi kasa In ta Rusa kuka .......















Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669








Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu











Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ₯°πŸ’ƒπŸΏπŸ˜‚
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€





πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
33//34
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne


Godiyar har kullum ga Ubangiji Wanda ya yarje min komai cikin sauki da fuwacewa salati da Aminci da taslimi ga Annabi MUHD S A W da Ahalin gidan sa madaukaka da duk Wanda yabisu da kyautatawa


Tukwici ne ga Hafsat Bara'u ba Duhu Allah ya bada ilimi me Amfani

Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


..........Duk murmushin da yarima Gibson ke jifata dashi na Jin Dadin ganina hakan Bai sa naji nayi farin cikin ganin shi ba sai ma wani turiri da naji zuciya ta nayi don Ina ganin zai kawo min cikas akan zuwan Umar

Ina tsaye Ina kallon yadda ake faman tattare mishi Riga da shimfida mishi dogon kafet din da zai taka shi kuma Yana ta jifa na da murmushi
Ya karaso Yana me Rungume Ni Yana fada min wasu kalamai Wanda Rashin sa ar da ya tako Bai taba burgeni ba bare naji son a zuciya ta bare Kuma kalaman shi suyi min Dadi. Ya saka tafin hannun shi cikin nawa hannun ya Runtse Yana ci gaba da rada min kalaman kauna a kanne na Yana Kara Rungume Ni tsam a jikin shi yayin da tsanar shi ke Kara zagaye jikina da zuciya ta na Soma zare hannu na daga nashi hannun Ina Shirin zare jikina naji Amaka ta iso tanawa Gibson barka da zuwa tamkar zata mayar da shi cikin ta ta sake haifar shi inda Kuma naji waya ta ta dauki tsuwwa na duba na kuma ga Umar faruk ne na daga da sauri inda Yake fada min ya karaso
Gaba na yayi masifar faduwa don lamarin ya Zo min da Zaki da madaci da ace Amaka Bata karaso ba to da na sulale na fice zuwa wurin Umar faruk Kuma yadda na kula tana ta bare baren murnar zuwan Gibson idan nace Zan fita komai zai iya faruwa Kuma banajin Zan iya Barin Umar a waje na shanya shi don zuwan wani Gibson da bana kallon shi a wata tsiya sai Wanda ya nemi katse min kwanciyar hankali da shiga Rayuwa ta ta karfi da yaji

Na daga wayar Umar Ina mishi sannu da Zuwa na Kuma tambaye shi ya karaso? Yace min gashi a kusa da gidan mu nace gani Nan Zuwa

Amaka ta kwada min harara Wai ban sauki Gibson ba na barshi a tsaye . Na SHIGA laluben yadda za ayi na sulale na fita wurin Umar ba tare da Amaka ta nemi kunya Tani a gaban Gibson ba sai Kuma na Gane in ba tarairayar Gibson nayi ba to kuwa ba Zan samu na fita ba don Haka sai nayi nufin karrama shi

Na sauke shi a falon saukar Bakin Maazi Nkem na Kuma kawo mishi abin tarba dangin Ruwa da nau ikan namo mi da abinci irin na girma da kasaitacce irin barasake Gibson

Amaka kuwa sai barin jiki take tana fito min da Kaya na garari Wai inyi kwalliya don har da murjanai ta fito min dasu Wai nayiwa yarima Gibson kwalliya

Nayi hikimar cewa Amaka Zan karbo abu wurin grace wata yarinya ce Nan makociyar mu inda Amaka tace nayi maza na dawo nayi wanka Kar ya tsaya jirana
Aguje na fita na hango Umar a bangon gidan su grace Yana tsaye cikin fararen Kaya Wanda suka Kara fito da kwarjinin shi naji kamar na Rungume shi don tsabar kyan da yayi min a ido

Bakine kalar fatar jikin shi ba Kuma Baki sosai ba irin kalar Nan da ake cewa cokulat kala shi ba Baki ba shi Kuma ba fari ba wankan tarwada. Dogo ne sosai Kuma Mai murdadden jiki Yana da fadi a kirji da Kuma dogon wuya sai idanun shi matsakaita da tattausar suna irin ta labarawan Maiduguri wato shuwa sai sajen fuskar shi da hancin shi mikakke dodar a Kan dakalin fuskar shi sai Kuma wani annuri a goshin sa Mai Kama da an diga mishi bakin Abu a tsakiyar goshi

Na karasa gareshi Ina murmushi nayi mishi barka da zuwa shima yayi min murmushi Yana kallon tsakiyar idanu na kunya ta kamani na sunnar da kaina kasa.

"Shikenan Kuma sai na Rabu da jinki Justina? Na tsinto maganar tashi Akan kaina

"Kayi hakuri ban San zaka nemi Ni bane
Na fada inajin kallon Nan nashi har jinin jikina.

"Gani to na neme ki Kuma Zan gaida mama da Baba.....
Rudewar da nayi har shi ya fahimci hakan don Haka sai nace mu SHIGA gidan su grace zanyi wanka yanzu Kuma na kawo mishi Ruwa
Muka SHIGA gidan su grace na sauke shi a parking space na karbo fararen kujeru wurin maman Grace na Kuma fada Mata na sauki bako na a parking space tace ok

Na fito na aje Mana kujerun na Kuma ce mishi ya bani minti goma Zan dawo
Na fice zuwa gida na fada wanka na fito na saka kayan da Amaka ta fito min dasu ita da kanta ta SHIGA tsara min kwalliya kasancewar ta kwararriya a fannin make up don har kanti ta bude inda ake tsantsara kwalliyar kanti. Ta daura min murjanai ta Kuma fesheni da turare kala kala na nufi inda Gibson Yake Amma Kuma zuciya ta tana wurin Umar Wanda nayi fatan ace wurin shi na wuce Kai tsaye Amma Kuma ban Isa ba koda kuwa na Sha giyar wake

Fadawan dake gadi a kofar inda Gibson Yake suka sunkuyar da kawunan su Wai don kar su kalleni na wuce su Ina Jan tsaki Araina

Na shigo na same shi Yana kishingide irin kwanciyar jinin sarauta Amma Yana ganin na shigo ya taso ya tarbeni Yana bani hot kiss abinda ya ke bakan ta min Rai shi Kuma Yana ganin ta Haka NE zai nuna min yadda yake jina a zuciyar shi
Muka tsurawa juna ido muna kallon juna a tsakiyar ido kafin ya zaunar Dani dab dashi na Kuma kula da bai taba komai ba don Haka na Soma service din shi da nau ikan abin da aka Tara mishi Kuma ya dan taba kadan daga cikin abinda na zuba mishi Yana ci kuwa yana kallo na

"Ina fatan dai ke kikayi girkin Nan? Ya fada Yana Ruko tsintsiyar hannu na na kada mishi Kai Alamar bani nayi ba sai ya mayar da Naman da yakai Baki Yana gutsura kamar Dan yaro
Ya yagi tissue paper Yana goge hannun shi da Bakin shi ya Dan kurbi lemun Dana zuba mishi a tanbulan sai kawai Naga ya kwanta Akan cinyoyi na Yana Riko hannun na Yana matsawa Yana Kuma kallon idona Yana fada min nayi mishi girki kafin ya tafi don yaji irin dandanon hannuna Wai ta dandanon girkin mace ake ita din wacece a cikin Mata
Maganar tashi ta bani haushi ba kadan don Haka na tambaye shi yaushe ne zai tafi? Yace 4:00 na yamma na dubi agogo Kuma 2:51 ne don Haka nace to ya jirani na SHIGA kichen yanzu nayi mishi girki don har coice din shi na tambaya don nasan na Gama samun damar da nake ta neman samu ta zuwa wurin Umar

Na fito nacewa Amaka yace girki na Yake so nayi mishi Amaka tace to na SHIGA kichen Mana nayi mishi me shegen dadin da zai manta da kunnen shi

Na SHIGA kichen Ina hada slinder na kuma Dora tukunya da sauri Kuma na fice zuwa wurin Umar Wanda nayi dabarar fito mishi da Ruwa da lemu har da nama

Muna ta fira Yana fada min shi Yana so ne yayi min silar da Zan Rabu da ciwona na bugun aljanu don abin Yana Ranshi idan ya tuno da yadda abin ke samu na. Ban boye mishi ba na sanar dashi yadda nake son karatun Alkur ani da Kuma mafarkan da nake yawan yi Wai Ina salla har na Fara tunanin yadda Za ayi na taka tsanin da Zan zamo Ina yin sallar Nan shi Kuma Yana Kara fada min girman iyaye da hakkin su na ayi musu biyayya hakan ya Kara jefa Ni cikin Rudani don na Rasa ta Ina Zan Fara?

Mun Dade muna fira har bamu San lokaci yaja ba sai da Rutu Mai aikin gidan mu tazo take fada min wai sanwar da na Dora ta kone har ta so haifar da gobara don Haka na biyo Rutu muka taho inda na iske Amaka ta cika ta batse kadan ya Rage ta fashe muna shigowa ta wurgo min wata matsiyaciyar harara tamkar idanun ta zasu zubo kasa.................













Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669









Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran









Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ₯°
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€





πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
35//36
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne



Sadaukarwa ga Anty Jamila Yusha u ma aikaciyar Rema sokoto Anty j Allah yakara daukaka na gode kwarai da kaunar Rubutu na Allah ya shirya ZURIA


Fatan ALHERI ga mahaifiyata haj Rabi atu Abubakar magaji Yar Adua Allah yayi Miki sutura cikin suturar da yayiwa ma aiki S A WπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°



Yabawa ga haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria har muddin Rayuwa da numfashi Allah yasa har gidan ALJANNAH


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



"Wane irin wulakanci ne kike Shirin yi Mana? Cewar Amaka da tayi furucin a fusace. Dama kin shirya kunya ta mu ne a cikin Ahalin igwai? Yaron Nan ya Sanya ki Aiki kin Kama kin fice har ya Soma gajiya Wai me kikeyi ne agidan su Grace din? Na tura Baki gaba Alamar Raina ya baci da tijarar da Amaka ke min saboda wancen shashashan wato Gibson

Jin ban Bata amsa ba yasa ta tubi Rutu tana tambayar ta Wai me nakeyi agidan su Grace din?
Rutu ta bude Baki Wai zata fadawa Amaka abinda ta Tara's inayi wato fira da Umar Amma hararar da na watsa mata ne yasa tayi gum da Bakin ta ta SHIGA kame kame Ni Kuma nayi cikin kichen Ina duba ta adin da girkin nawa ya jawo
Amaka sai masifa take min kamar zata Rufe Ni da duka Ni Kuma duk Raina ya baci saboda firar da Umar yake min tafi komai muhimmanci a gareni gashi kuma Amaka ta Rabo Ni daga gun sa ita a Dole sai na tarairayi Dan gidan igwai....


Muna a Haka Amaka na fadin sai na sake Dora mishi wani sabon girkin sai ga Gibson ya fito da niyar tafiya don har biyar ta kusa bugawa

Amaka ta Soma fadin zai tafi Bai jira sun gaisa da Maazi Nkem ba Kuma baici abincin ba? Yace yayi maraice ai zai dawo gaishe da Maazi Nkem din girki na kuwa ai gajen hakuri ne yayi tunda Zan Zo zaman dakin shi kafin bikin Auren mu ai zaici

Ya Riko hannun na muka bishi wurin da motocin shi suke Yana Rungume Dani a gefen kafadar shi Yana Rada min wai nayi mishi Rowa ta girki na Wanda yaso ya dandana yaji zakin hannu na Wanda inda yaji zakin hannun nawa to da kwana yayi Amma yanzu zaije ya fadawa igwai Yana son nazo nayi mishi Zaman daki sai yaji girkin nawa...

Nayi maza na hade fuska don nasan abinda Yake nufi da zaman dakin da zanje nayi mishi wato dai inje in samo ciki Wanda zai tabbatar da Auren mu kamar yadda Al adar take abinda kuma nakejin ba zai taba yuwa ba Kuma zai yuwu ba don Haka nace mishi

"Ba Zan Zo yi maka zaman daki ba karma kace Haka in dai girki ne zanyo shi na sako maka mota akawo maka shi har gida.......

Ya katse Ni Yana murmushi
"Ai ba girkin kawai nake so daga gareki ba my love ganin da nayi Miki a yanzu ya nuna min kuskuren da nayi Ina da kamar ki Amma ace na barki kina nesa Dani sai dai nayi ta ganin ki a cikin bacci na da mafarki na? Ki saurari aike na cikin satin Nan Zaki iso min zaman dakina ya Miko min wata jakar fata me zanen Ado irin na tambarin sarautar su yace igwai ne ya ce akawo min kafin ya Kuma Miko min wata ita Kuma jakar Leda ce ta wani kamfani ita Kuma mamar shi ce tace ya kawo min shi kuma hannu na ya Kama ya saka min wani tsadadden zobe na zinariya Mai Daraja wadda itama ajikin zoben tambarin sarautar tasu ne amma anyi wa zoben harafi guda biyu na farkon sunan mu wato j & g don Haka ya fada min shi Kuma ga tashi kyautar Nan ya Kuma sumbaci yatsun nawa bayan ya gama saka min zoben
Fadawan dake biye dashi a baya suka kwashi kayan nawa suka Rike Wai su Kai min gida
Har na juya Zan koma gida don hankali na Yana wurin Umar bayan nace mishi yayi min godiya wurin mama da Kuma igwai akan abinda suka bani sai kawai naji ya Ruko min hannuwa Yana min kallon tsakiyar idanu Wai Haka Zan barshi Ni ba Zan bashi abinda zai Rika tunawa Dani ba?
Na bishi da manyan idanu na don ban San abinda Yake nufi ba sai kawai naji ya jawo Ni cikin motar Yana hada tsinin hancin shi da nawa inda na Gane abinda yake nufi Wanda Kuma banajin zai sameshi don ba Zan iya yi mishi yadda zai gamsar dashi ba tunda banayin shi Amma ko hakan da na Raya a zuciya ta ya juyo Koko Alamar hakan ya gani shiyasa Bai Bata lokacin jira na ba ? Oho sai kawai na tsinto bakina a cikin nashi na Kuma kasa kwacewa sai da ya sakeni Don ya so hakan. Na fito motar Ina Jin wani Abu Yana min yawo a jiki saboda irin hakan bata taba faruwa Dani ba a son Raina ko Akasin hakan irin na yau don Haka wannan Rayuwar bakuwa ce a gareni

Wannan shine bankwanan da mukayi da yarima Gibson ya tafi Yana min wani kallo Wanda nakejin don ya cuceni ne ya hada bakin shi da nawa yake min shi


Na kawowa Amaka kayan da ya bani da zoben shi da kyautar igwai da kuma ta mah wato uwar yarima Gibson

Amaka ta Rafsa guda Mai tsananin karfi tana Rawa Wai anyi min kyauta sai Kuma ta SHIGA budewa tana gani inda Ni Kuma na sulale zuwa wurin Umar Wanda na hango shi ya fito daga gidan su Grace Yana tsaye jikin bangon gidan Ina karasowa ya Soma fadin wannan Kuma waye Haka yazo wurin ki Justina? Gaba na ya Fadi Jin Ashe yaga duk abinda ya faru tsakani na da Gibson sai ban boye mishi ba na sanar dashi shine Wai mijin da iyaye na suka zaba min....

Ya dube Ni Yana Fadin Ashe Ni Kuma igiyar Ruwa na Kama kenan Justina tunda har anyi Miki miji?
Nima na dube shi nace
"Kana Sona ne kenan? Yace kwarai kuwa sai dai nasan Babu ta yadda Za ayi na sameki tunda har iyayen ki sunyi Miki miji Kuma ko da basuyi Miki miji ba ba lallai ne su bani Auren ki duk da tazarar dake tsakanin mu Amma nayi nufin na fahimtar dasu idan suka ki bani Auren ki saboda tazarar mu to Kuma gashi
Showing 24001 words to 27000 words out of 30837 words