Kai acikin ta Amma da Yake jarumi ne sai ya nuna min bafa komai bane wannan duk na lokaci ne Kuma zai wuce da yardar Ubangiji shi lamarin Rayuwa guda biyu NE ko dai ya wuce ya barka ko Kuma Kai ka wuce ka barshi

Haka ya fada min a lokacin da nake kokawa halin da Naga ya SHIGA na wani sauyin saboda sanin da nayi mishi na Bai taba SHIGA wani hali na Rayuwa irin wannan ba bare nayi tunanin sabo Amma Kuma Dole na gamsu da bayanin da yayi min don a sanin da nayi mishi Yana fatan ganin ya fita hakkin mu Akan komai Kar dai muce muna son kaza to kuwa zaiyi kokarin sama Mana abinda muke so inda Kuma na Gane a kokarin Yaya Abdullahi so Yake a Dole sai ya maye Mana gurbin Daddy da muka Rasa Nima sai naji zanso hakan Amma Kuma gaskiyar magana nafi son naga Yaya Abdullahi shima a huce Amma ba cikin wannan wahalar ba to Amma ya muka iya tunda haka alkalamin kaddarar mu ya zano Mana?


Na dawo makaranta kenan na iso kofar gidan mu inda na hango motar Yaya Abdullahi a kofar gida inda na SHIGA tunanin yau kuwa ya dawo da wuri na SHIGA gidan da karsashi na inda na samu Ammi ta zabgo tagumi cikin damuwa sai naji hantar cikina ta kada

"Anmi lafiya dai ko ? Na fada murya ta na Rawa don naji ajikina ba lafiyar da na tambaya ba......


"Lafiya Lau Zahra Abdullahi ne dama ya dawo babu lafiya Kuma gashi babu kudi a hannu na bare na Kira likita Amma tashi kije gidan maman Nana ki aro min ko dubu Biyu ne dama gareshi nake saka Ran samun kudin idan ya dawo to jiki da jini yau lafiyar Taki......

Kafin ma Ammi ta gama zancen ta na wuce kuryar dakin Yaya Abdullahi Wanda na samu Yana ta kelaya uban Amai tsanwa Shar Alamar kumallo ne babu komai a cikin sa

Na matsa kusa dashi Ina mishi sannu kafin na Kama shi na jingina shi jikin filo na fito da sauri na dauko kokon da na Rage da safe na kuza mishi Ruwa ya Zama farau farau na dawo na bashi ya dan Kora ya koma ya kwanta na kwashe Aman kafin na fice zuwa gidan mama na fada Mata sakon ammi ta kuwa bani kudin har ma ta zubo abinci Mai yawa a kula tace na kawowa Yaya Abdullahi Kuma nace tana duba shi kuma zata Zo duba jikin nashi

Na kawo wa ammi kudin da sauri Kuma tace na Kama Mata Abdullahi mu Kai shi Asibiti
Na kamo shi muka fito ammi ta bude motar muka SHIGA kasancewar ta iya mota yasa Kai tsaye muka nufi Asibiti aka duba yaya Abdullahi akayi mishi gwaji sakamakon na malairia ne da da Kuma Rashin Samun hutu sai Kuma ulcer dake neman Kama shi don Haka aka shawarce mu da bashi cikakkiyar kulawa da Kuma samun hutu kafin aka Rubuto magunguna muka dawo gida

Dole Yaya Abdullahi ya zauna a gida ba don ya samu hutu ko kullawar da likitan ke magana akai ba sai don ya samu afuwar jiki ya koma bakin aiki a ganin shi talaka irin shi wane hutu zai nema Wanda sai ya fita ya samo ake bukatun Rayuwa.

Zuwa wannan lokacin duka duka shekarun shi fa ashirin da biyu NE don dai Jin Dadi da kuma jikin girman yasa ya Zama wani babba Amma yanzu da Rayuwa tayi sauyi duk wannan jikin nashi ya zube ya koma Dan kadan don shekara bakwai ne tazarar dake tsakanin mu Ni da kaina na Gane Yaya Abdullahi Yana bukatar hutu don Haka sai zaman jinyar shi ya Kara budo Mana wasu shafukan a cikin littafin da Yake Rubuce da tarin kaddarorin mu inda Yake Shan magani Amma sauki sai ga Ubangiji da Kuma godiyar Nan dai a gareshi


Muna cikin jimamin jinyar Yaya Abdullahi sai ga haj ladi matar da muke haya a gidan ta ta doko Mana sallama har ga Allah mun manta da cikar wa adin kudin ta saboda jinyar Yaya Abdullahi


"Masu gidan suna Jin sallama ko kuwa duk cikin Rainin da ake shirin kawo min ne anaji na Ina kwada sallama ake yi min banza?

Ammi ta amsa Mata da bamuji bane hajiya sannu da Zuwa shigo ciki......

"A a ba sai kin sakani a daki ba don ba dogon turanci ne ya kawo ba kudina na biyo karba bani kawai na wuce in har Babu Raini a cikin lamarin naku

"Kiyi hakuri hajiya Wallahi babu Raini a tsakanin mu yaron wajena ne babu lafiya kingan shi Nan kwance dama shine me biyan kudin don Allah hajiya ki Kara hakuri Zan kawo Miki kudin ki har gida da Ubangiji ya yaye wannan ciwon ne ya kawo hakan...

"Ke Yar Nan Kar kice Zaki kawo min kalaman karya ki fake da karsana ki harbi guzuma
"Don anji nayo sallama ne ake nadewa a gado ace ba a lafiya? In dai lafiya ce waye Mai lafiya a yanzu? Nima ba ita gareni ba Amma nake mazewa nayi harkokina Ni da har hauhawar jini ma gareni Amma ban nade a gado ba sai wannan katon ne akwance Wai baya lafiya? To ki kiyaye Ni don bani da Dadi ko da gishiri Zan Baki watan gaba ki kawo min kudina don ba Zan lamunci a zaune min gida akasa biyana haya ba yo yaushe ma ake haka ? Nan gaba kuwa ai mutum zai iya cewa gidan nashi ne to a fita idona na Rufe don in na Rufe da mutum a ciki ba zai fito ba yayi ta Zama kenan

Da haka ta fice daga gidan tana zuba Ruwan tijara

Ammi ta dafe kanta tana SHIGA wani zuzzurfan tunani Haka na fice zuwa makaranta zuciya ta a kuntace ban iya dorar da duk wani darasi da akayi a makaranta ba saboda zuciya ta tana wurin daban Akasin gangar jikina dake cikin ajin amma zuciyar Bata cikin ajin Haka na dawo inda na iske motar Ammi dake kofar gidan mu an Mata pentin taxi Amma sai ban dauka wani Abu ba azatona ma ba motar ta bace na SHIGA gida na iske Yaya Abdullahi Yana ta amai inda ammi ke fada min magungunan shi ne suka Kare babu Kuma kudin siyen wasu shiyasa ciwon ya koma sabo Dal Dole aka SHIGA kame kame

Washe gari naji Ammi na cewa sulaiman Kar yaje makaranta ya tsaya ya kula Mata da gida da Kuma Yaya Abdullahi. Ban tambaye ta inda zataje ba NASA Kai na fice zuwa makaranta inda yauma ban kula da kalolin darussan da aka koyar damu ba saboda tunanin Rayuwa har aka tashi na taho Ina zancen zuci har na kawo bakin titi Zan tsallake Ina hanga dama na da hagu na don kiyaye ban fada wa abin hawan da ke son wucewa ba inda Kuma na hango wata taxi tayi parking a gabana Ina dubawa sai Naga Ammi a mazaunin direba sai wasu Mata dake baya da Kuma wata mace a gaba

Gabana yayi masifar faduwa inda najiyo Ammi na fadin
"Shigo muje Zahra har an taso? Na bude bayan inda ke da wurin zaman mutum Daya na zauna na Rufe motar Ammi taja motar muka wuce Ina cike da tarin tambayoyi shin ammi mota ta koma ja ne? Ko kuwa wadan Nan matan Ina zata kaisu?

Matan Nan na cikin mota suka katse min tunani ta hanyar fadin

"Ai Ni Wallahi baiwar Allah kin burgeni don wannan Rayuwar babu nakasasshe sai kasasshe Haka Kuma Babu maraya sai Rago tunda har Ubangiji ya Azurta ki da motar nan Taki ce ta kanki da ki tsaya bawa mutanen wannan zamanin marasa Amana suna cutar ki gara ki tuka abinki tunda ma Allah yasa kin iya don Ni Wallahi zaburar Dani kikayi don Zan cire tsoro Nima na koyi motar Nan don tsaro ba don tsoro ba . Dayar matar dake gaba ta karbe maganar da cewa

"Ai in Gaya Miki Aisha Mata na ganin tasku a Duniya Kar ma ace Allah yayiwa mijinki Rasuwa wayyo Allah na taba SHIGA wannan siradin na Rantse Miki da Allah aduk yawan yan uwan mijina aka Rasa samun zakaran da zai tallafa min da kwayar hatsi ke sai a shekara ma ban saka dayan su idons ba ga Yara har biyar baccin Sana a ta ai da Asiri ya tonu shiyasa yanzu da Naga baiwar Allah Nan tana Jan mota sai tausayin ta ya kamani don nasan akwai wani Al amari da ya sata hakan

Ammi tayi murmushi daidai da ta kawo su bakin babbar kasuwar central market ta gyara parking suka fito suna Miko Mata kudin ta suna Kuma binta da ADDU A ta fatan ALHERI ga Kuma kiyayewar Ubangiji ta karba tana godiya ban San lokacin da HAWAYE ya balle min ba na kife kaina a cinya ta Ina kuka inda najiyo Ammi na min magana cikin sanyin murya ..............













Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669






Labarin daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku


Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ’ƒπŸΏ
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€




πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
17//18
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne


Sadaukarwa ga daukacin ZURIAR dake Rike zumunci tsakanin su da Allah ba don abinda suka hango ba ko Wanda zasu samu don yanzu zumunci ya zamo jari hujja

Gaisuwar girmama ga Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


............Muryar Ammi najiyo akaina cikin wata murya da na Gama fahimtar cikin Hali tayi maganar

"Kiyi hakuri Zahra komai Kika ga ya faru ga bawa Rubutacce ne bawa Kuma Bai Isa ya sauya shi ba. In ba Allah ba wa ya Isa yayi hakan? Nasan kinajin zafina Akan wannan hanyar da na dauko wadda nake ganin itace mafita Domin ko ya zame min Dole na tashi na Kare mutuncin ku tunda Dani a cikin Wanda sukayi sanadin zuwan ku Duniya Ashe ko ya Zama Dole na SHIGA na fita don ganin ba kuyi kukan Rasa wani Abu ba . Ba Zan sake Barin Abdullahi ya komawa aikin Nan Mai wahala ba nice ya kamata nayi tukin mota Amma ba fita garuruwa ba iyakata Nan cikin gari kawai na Kuma yi Miki alkawarin Kare mutunci na da naku in Sha Allah duk Runtsi duk wuya inaji ajikina Zahra akwai lokacin da komai zai zamo tarihi kamar ba ayi ba don Haka Daina kuka kinji ? ADDU A nake Rokon kiyi min Allah ya tsare Ni sharrin karfe da Kuma sharrin mutum da aljan

"Ammi ba haushin ki nakeji ba illa tausayin ki Ammi ban taba ganin mace na tukin taxi ba shiyasa nake tausaya Miki Kar kema wahala tayi Miki yawa irin wadda ta riski Yaya Abdullahi.....


"Babu komai Zahra Allah ya Rufa min Asiri don na lura Ubangiji ya saka min nasibi don kusan Dubu biyar na samu bayan na fidda Dubu biyun Mai da na siya kinga sai mu biya haj ladi kudin ta abinda na samo gobe Kuma sai mu siyo abinci mu aje in Sha Allah wahalar mu ma tazo karshe

Haka kuwa Ammi ta zage fita Aikin tuki Kuma tana samo kudi sosai inda na Gane shi Ubangiji da ka tashi da nufin kana son ya taimake ka to zai kuwa taimake ka sai dai Kuma Yaya Abdullahi dake kwance Bai San hakan ba Kuma ammi tace Kar mu sanar dashi don da yaji ba zai yarda ba Kuma gashi ba lafiya gareshi ba


Tuni aka biya haj ladi kudin hayarta muka zauna lafiya har ma Ammi ta samu kudin da ta siyawa Yaya Abdullahi magani ta Kuma siya Mana kayan abinci Wanda Rayuwa ta koya Mana cin dangogin su Wanda bamu waye su ba amma dole muka Saba tun muna ci cikin mu na baci muyi ta zawayi har muka Saba daga wannan sabon sauyin zuwa Wanda Muka sani muka Kuma Saba

Jikin Yaya Abdullahi yayi sauki har ya Soma tambayar kanshi yawan fitar da ammi takeyi Amma dai Bai tambaye ta ba Bai Kuma tambayi kowa ba inda a yau ya fito waje Yana zaune Yana kallon yadda mutane ke ta Kai kawon su kawai sai yaga Ammi ta shawo kwana cikin motar da aka mayar taxi Kuma ga Alama kamar garin take zaga wa

Ya taso ya karaso daidai da tafito Rike da ledar da ta siyo Dan Raba Mana dangin makulashe ya karbi ledar suka shigo ciki Yana mata sannu da Zuwa ita Kuma tana murnar ganin ya Soma fitowa waje Alamar sauki ya samu

"Iska kake Sha ne Abdullahi? Masha Allah Allah ya Kara lafiya kaji ? Ya amsa da Ameen Ammi Amma ya Naga motar Nan anyi Mata fentin taxi? Ya fada Yana kallon Ammi wadda ta shiryawa tambayar tashi
"Sai dai kuyi hakuri Abdullahi Amma ai ya Zama Dole na Mike tsaye don na ga Baku yi kukan Rashi ba in kun Rasa Uba jajirtacce to tabbas Baku Rasa jajirtacciyar mahaifiya ba don Haka Kai ma inaga makaranta ya kamata ka koma don yadda na samu sa ar Nan abubuwa suna tafiyar min yadda ya Dace kaima na yanke shawarar ka koma karatu kawai.......


Ya Soma kada kanshi Alamar A a ba zai iya Barin ta da wannan dawainiyar ba. ......

"Ammi nine fa Ubangiji ya baku don kuyi alfahari da haihuwa ta . Nine Wanda Ubangiji ya kawo muku don na dauki takalifin ku keda Daddyn mu da Kuma kanne na to tunda Ubangiji Bai yarda Daddyn yaga Haka ba sai ke don me Zan Bari kiyi ta wahala Haka ? Don Haka don Allah don Annabi kiyi hakuri da fitar Nan nine Zan fita na Nemo muku duk abinda kuke so tunda na samu lafiya dama sai da wani ya fada min ulcer ce ke neman kamani da na fada mishi abinda nakeji shi Kuma yace akwai maganin Hausa da zai bani Zan Rabu da ita Yana a funtua ne in naje Zan neme shi ya bani shikenan Ammi don Allah don Annabi kar kice A a idan Kika ce a a kamar Baki yarda Zan zamo Miko abin alfahari ba....


Ammi bata yarda ba daga farko don cewa tayi bashi da lafiya ya Bari ya Kara samun sauki tukuna shi Kuma ya CE baya son yaga tana fitan ne don Haka ta hakura da fita shi Kuma ya zauna zaman shanye maganin shi kafin ya koma bakin aiki

Sati guda Daya Tak ya koma aiki inda Ni da kaina naji gaskiya bana son aikin Nan na Yaya Abdullahi hankali na ya Fi kwanciya Akan na ammi ban San Dalili ba ko da Yake dalilin ba zai wuce na kaddara ba wadda Ubangiji ke darsawa wasu Jin wani Abu da zasu yarda dashi ko Akasin hakan Wanda matukar suka bibiyi abin Nan da Basu yarda dashi ba sannu a hankali sai su Tara's da kaddara acikin shi kaddara kuma me ciwo a zuciya

Aikin Yaya Abdullahi ya Dore don yanzu har wata Yar kiba ya somayi bayan ya karbo maganin ulcer ya Kuma yi amfani dashi har ya warke daga cutar ulcer harkokin shi suka tafi daidai komai namu ya tafi daidai kamar dai irin Rayuwar da ta samemu a tsakar Rana guda Daya Tak

A dangin mahaifina kuwa shiru babu Wanda ya neme mu bare yaji ya muke Rayuwa ya muka Fadi ya muka tashi ko da Yake naso na yaudari kaina idan nace so nake Wai wani yazo da sunan duba mu ai ko a mafarki naga hakan Zan karyata suna wurin su muna namu sai ma Nana CE ke fada min wai Yan uwan Daddy sunzo Kan maganar gidan mu har ma sun saida shi Wanda ya siye shi ma yace Rushe shi zaiyi ya sake sabon Gini

Kasancewar makarantar mu daya da nana ta gidan mama kusan ma itace kawata ta kusa kusa don a tare ake kaimu makaranta a wani lokaci can da ya Jima da shafewar tarihin shi
Wannan magana ta Nana ta kadani ba kadan ba don da nadawo gida ma sai da na sanarwa ammi abinda nanar ta fada min

"To ya za ayi Zahra in ma Basu saida shi yanzu ba zasu saida shi Nan gaba Allah ya Baku mafiyin abinda kuka Rasa Ina Rokon Allah yayi muku gata fiye da Wanda mahaifin ku yayi nufin yi muku na amsa da Ameen ya Rabbil Alamin

Da na kebe ma sai naji Ina son yin dogon nazari Akan shin Wai mu kadai ne muka kuskuro shigowa Duniya da Rashin Dacewa Akan Yan uwan Daddy ko ko Ammi da Ubangiji yayiwa nasibin shigowa hasken musulunci? Yan uwa da dangi dai ta bangare biyu ake alfaharin samun su wato Uwa da Uba shi Daddy nashi Basu da kirki suna kin Ammi ne don kawai ta kasance ahalul kitabi suke kinta to su Kuma dangin Ammi fa? Su Kuma meye matsalar su damu da suka yada mu basa son mu Basu rabar mu ? Da na nutsa sai Nagano yadda Ammi ta sanar Dani shigarta cikin musulunci ya bar baya da kura Wanda har nemanta suka Rakayi don su kasheta Allah ya kareta Daddy ya dauke ta suka bar kasar Baki Daya shine fa ta tsira daga harin da ake kawo Mata Amma Kuma sai Naga indai Haka akayi Rabuwar to Babu dalilin da zasu neme mu don a fahimta ta ma yadda su kawu gide suka tsani Ammi saboda ta fito daga wata kabila da yare akasin nasu suke kinta to su Yan uwan Ammi na tabbatar da sunfi su kawu gide kinmu tunda su neman Ammi suke ma su kasheta Akasin su kawu gide da basu nemi kisan ba don Haka kuwa Ashe yaudarar Kaine ince zasu tallafe mu don Haka sai Naga Bari na koma baya na hasko muku madubin kaddarar da ta haske Akan Ammi da Daddyn mu Wanda haduwar su CE sanadin kaddarar
Showing 12001 words to 15000 words out of 30837 words