ma Ashe an bada ke ga Dan gidan sarauta Kinga kuwa abinda ba zai taba yuwa ne ba su tada wannan alkawarin.....


Nayi saurin tarar shi Ina fada mishi nifa dama ba Wai son Gibson nake ba Ni shi kadai nake so don nayi alkawarin ba Zan taba Auren Wanda muke addini Daya dashi ba sai Mai salla Zan Aura ko da banyi salla ba ina son anayin salla a gabana Kuma ma Ni gaskiya Al adun da akeyi ne wurin Auren mu ba suyi min ba da ya nemi ba asi na Kuma fada mishi ya Jima Yana kallo na kafin yace zamuyi magana yanzu na SHIGA gida tunda yayi maraice zamuyi waya.

Na Raka shi har Baki hanya inda Kuma muka gamu da Maazi Nkem ya karyo kwana ya Kuma ganmu Ni da Umar sai dai da sauri nayo baya umar Kuma ya tafi abinshi

Kayan da Maazi Nkem ya Tara's Amaka ta baje tana ta kambama su su suka dauki hankalin shi inda Amaka ta sanar dashi zuwan yarima Gibson Wanda ya kawo min wannan kayan sai ya Kira wayar igwai yayi godiya ya Kuma ce wa sarkin bashi gari ne sai yanzu ya dawo ya samu sako in yarima Gibson ya dawo ayi mishi sannu

Ban san yadda suka Kare ba Maazi Nkem da Amaka da kayan Gibson

Washe gari da naje makaranta nake fadawa nafisat da fauziyya yadda mukayi da Umar Wanda yazo takanas don ya fada min Yana Sona amma Kuma Yana tsoron iyayena mussamman da na fada mishi an bawa yarima Gibson Aurena lokaci kawai ake jira
fauziyya tace gaskiya Justina Lamarin ku fa yazo da Rudani ke ba Kya son yarima Gibson su Kuma iyayen ki shi suke so Umar kike so Umar kuwa Babu ta yadda Za ayi iyayen ki su bashi Auren ki yaya zakuyi kenan? Nima abinda nake tunani kenan a Rai na Ina son nayiwa iyayena biyayya Amma Kuma gaskiya bana son Auren Gibson sai Umar Wanda Kuma na tabbatar iyayena ba zasu taba yarda da Auren mu ba Koda kuwa shi shi kadai yayi saura a Duniya Yaya zamu Kare kenan? Dukkan su sun bani shawarwari Akan nayiwa iyayena biyayya kuma na Roki Allah ya zaba min ALHERI

Na dawo gida jikina a sanyaye inda na makala hearphon a kunne na Ina sauraron karatun Alkur ani Wanda na ji nutsuwa tana sauko min har ma bacci ya kwashe Ni kuma cikin Rashin sa a wayar hearphon din ta zare daga jikin wayar Wanda Ni na zare ta saboda matsewar da nayiwa wayar garin bacci ai kuwa Kira ar ta fito tar ta cikin bututun sauti na wayar Amaka dake zaune kusa Dani ta dubeni ta Kuma dubi wayar dake ta amayar da sauti cikin fusata Amaka ta fincike wayar ta kwantara ta da kasa ta watse Ni Kuma ta sharara min Mari Wanda na farka a gigice Ina zare idanu


"Wato Ashe Baki Daina sauraren wake waken Nan ba ko? Nace Mata karatu ne fa ba wake wake ba....
Ta Kuma kwada min Mari kafin ta shakeni tana fadin Wallahi kasheni zatayi ba Zan jawo Mata abin kunya ba tunda dai na zabi dabi ar masu salla nace ita ta burgeni to gara kawai ta kasheni ta huta don Bata da idon duban Yan uwan ta da suka Rayu cikin addinin su Kuma Wai ace Ni Yar da ta Haifa na ce addinin ta ba na gaskiya bane gara ace ita din ta kasheni da dai nayi Mata wannan wulakancin

Ai kuwa da gaske Amaka take don tun Ina iya shaida abinda ke faruwa har naji numfashi na Yana kokarin daukewa daga gabgar jikina zuwa wata Duniyar Wanda ban santa ba
Ban San ya akayi ba sai naji Emmanuel Yana kwata ta daga hannun Amaka Wanda tace dawa Allah ya hada ta ba dashi ba? Sai ta Rufe shi da duka Wai shike Goya min baya don Haka gara ta kashemu Ni dashi sony kadai ya isheta Rayuwa tunda shi ai me son addinin nata ne. Emmanuel dai dayake namiji ne ya kwaci kanshi hannun Amaka ya Kuma fice ya bar gidan inda Maazi Nkem ma ya dawo yaji labarin abinda na aikata bindigar shi ya kafa min a goshi Yana fadin zai kasheni wallahi da dai ace musulunci nake kwaikwayo . Da kyar baban Grace ya Basu magana suka hakura Amma fa Nasha jibga wurin Sony sai da yayi min laga laga kafin ya barci jiki duk jini da cuwuka Amma wani abun mamaki da na kwanta bacci sai gani dai wurin Nan Ina salla har ana Miko min kyautar littafin da naga mafi yawan su suna budewa suna rero Kira a irin wadda nake so da saurare abinda Kuma yasakani kudurewa lallai sai nayi sallar Nan Kuma sai nayi karatun Nan da nake yawan saurare sai kawai na diro daga Kan gadon nayi wanka da Ruwan zafi na gasa jikina ko Mai ban saka wa cikina ba na fice daga gidan...................
















Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669










Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran












Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunana ke cewa saduwar ALHERIπŸ’ƒπŸΏ
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€





πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
37//38
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne



Sadaukarwa ne ga duk inda masoyan ANNABI MUHD S A W suke afadin Duniya Allah ya karawa ANNABI Daraja da wasila da fadeela


Sadaukarwa ga iyalan marigayi Alh Ali Mai chanji marnar gangare Allah Ubangiji yayi mishi Rahama yasa kwanciyar shi hutawa dashi da dukkan musulmin duniya


Fatan ALHERI gareku masoyan Rubutun Gidan sannun ku da kokari littafin GARWASHI na jinjina mukuπŸ₯°


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


..........Kai tsaye gidan su fauziyya na nufa da dai wurin Umar nayi nufin zuwa sai nayi wani tunani sai kawai na nufi gidan su fauziyya

Duk yan gidan su sun sanni muna Kuma girmama juna don Haka da na SHIGA sai da muka gaisa da kowa kafin fauziyya ta kaini wurin maman su na gaida ita cikin sakin fuska ta amsa min na kuwa ji dadin yadda suke karbata babu nuna kyama bare suyi min daukar hanci irin Wanda Amaka kewa hausawa da musulmi Amma su Babu Ruwan su Basu Kuma tallata min addinin su ba kamar yadda Amaka ke zargin Wai hausawa ne ke neman jana na SHIGA jikin su shiyasa take Hana Ni mu Amala dasu


"Daga Ina kike haka Justina cikin uwar Ranar Nan? Na dubi fauziyya Ina Fadin. "Don Allah fauziyya wata Alfarma nake nema Kuma ya zamo sirri a tsakanin mu don bana son kowa yaji maganar nan Kuma ke nasan Zaki Rufa min Asiri ko ba Haka ba? Fauziyya Yar Amana tace kwarai kuwa Justina ai tsakanin mu Babu tonon Asiri ai mun wuce wannan wurin ki Kara sakawa Ranki mu fa musulmi muna da Amana fiye da zaton ki don Haka fada min abinda kike so nayi Miki Alfarma ko mamana ba zataji abinda Kika yarda Dani Kika fada min ba Zan tayaki boye sirrin ki daga Ni sai ke Sai Allah. Na Kuma gode da Kika zabeni a matsayin wadda Zaki fadawa sirrin ki.

"Na ce na gode fauziyya don Allah salla nake so na Fara Amma ban San ya zanyi ba Kuma bana son iyayena su San na Fara salla shine Naga ke kadai kike fada min yadda addinin ku yake Kuma na Faye mafarkai Akan Ina salla da karatun Nan da nake yawan saurare shine kawai na yanke shawarar in Fara salla don naji zuciya ta tafi aminta da salla fiye da abinda mukeyi a cikin addinin mu ko Babu komai addinin ku ya koyar daku Adalci ya koyar daku yiwa Wanda ma ba addinin Yake ba Adalci Kuma ya koyar daku saka kaya masu mutunci ya Kuma koyar daku ibada wadda zuciya ke nutsuwa idan anyita don Haka fauziyya na San iyayena ba zasu so na bar addinin su ba Amma Ni gaskiya nafi son musulunci fiye da addinin da na gada don da shine gaskiya da ban Faye mafarki dashi ba tunda ku ai ba kwa mafarki da namu addinin ko kunayi? Na tambayi fauziyya ta Kuma kada min Kai Alamar A a basayi nace to kin gani ?

Fauziyya tayi kabbara tana fadin "ALLAHU Akbar kabeeran Kai Amma nayi Miki murna Justina sai dai Kuma Ina tsoron abinda zai biyo baya idan mahaifan ki suka fuskanci kin bar addinin su don gaskiya bana son ki samu matsala da iyayen ki.........

"Fauziyya na shiryawa komai Koda kuwa zasu kasheni ne kamar yadda suke fada banajin zanyi nadama da mutuwa ta ke dai taimakeni ki fada min yadda zanyi ki Kuma Rike min sirrina Kar ki fadawa kowa

Fauziyya Yar Amana ta lakana min kalmar shahada tana karanta min Ina maimaitawa ta Kuma karanta min kadaitakar Ubangiji da tsarkake shi da matsayin sa shi Daya Tak bashi da abokanshi taraiya da Kuma shaidawa shi kadai Yake Haka Kuma Annabi MUHD S A W bawan ne Kuma manzon sa
Duk na biya Kuma naji zuciya ta ta yarda da abinda na biya din inda Kuma fauziyya ta fada min sai nayi wanka na SHIGA musulunci da kuma yadda ake wanka idan period tazo da Kuma wankan tsarki na zahiri da Kuma na mafarki duk ta koya min yayin da ta Soma sanar Dani salla da bangarori da ke gareta irin abinda Yake Dole da Wanda akayi sauki da Wanda akayi sassauci wato farali sunna mustahabbi duka dai inda tace sannu a hankali zata ke sanar Dani Kuma in fadawa Umar shima zai taimaka min ta wata fuskar don Haka Ina gidan su fauziyya akayi sallar zuhur muka tashi fauziyya ta fada min niyar daga cikin zuciya ta Zan kudura ta ta Kuma ce na kalli yadda zatayi Alwala duk abinda Naga tayi Nima nayi. Haka kuwa akayi muka yi salla ta Kuma fada min sai na Rage saka kayan da zasu Rika fidda min part din jikina wato masu bayyana tsiraici


Haka na dawo gida zuciya ta tamkar anyi Mata wanki babu komai nakeji Sai farin ciki da wani irin iska Mai sanyi Yana kada Ni sai najini tamkar bani ba don har nauyi sai naji na Rage na koma wata Yar shafal

Aduk lokacin da Zan duba Inga ya Kai Wanda fauziyya tace min nake salloli sau biyar azuhur da la asar magaruba da Isha I Sai subahi kowane ta fada min lokacin su duk da tace lokacin Yana sauyawa musamman idan yanayi ya sauya irin zafi zuwa sanyi ko damuna Amma tace idan ma yanayin ya sauya zata sanar Dani

Aduk lokacin da zanga lokacin sallar yayi Zan SHIGA dakina na Rufe na fada toilet nayi Alwala na zaro katon hijabi na Wanda nasiyo don salla na zurma nayi salla ta wadda duk lokacin da Zan gamata sai naji wani Dadi da farin ciki kafin na zauna Ina tunani sai Kuma in boye hijabi na kafin na bude dakin in fito Ina makale da hearphon a kunne na Ina sauraren karatun Alkur ani Mai girma Kuma Alkur anil Kareem Haka Yar Amana ta fada min sunan shi wato Mai girma


Nayi Shirin SHIGA kasuwa inda Zan fanshi Alkur ani don Ina son na Fara koyon karatun sa don Haka nayiwa Amaka bankwana na SHIGA kasuwa sai da kyar na samo shi don Haka kai tsaye na nufi wurin Umar don shigar da na fito da ita daga gida ba itace na shigo kasuwa da ita ba hijabi na Yana jakata Ina fitowa na zurma kayana don Haka Umar ma da ya ganni cikin hijabin sai da mamaki ya Kama shi ya zuba min ido Yana kallo na cikin kaunar da bata boyu ba yana ta murmushi Ni kuwa kunya ta kamani ganin irin kallon da Yake bina dashi. Ya kasa tankawa sai dai kallo na yake Bai Kuma fita daga mamakin da Yake ciki ba na Kara kashe shi da wani mamakin inda na fiddo Alkur ani daga cikin hijabina nace mishi nazo ne ya koya min karatun Alkur ani. ALLHU Akbar kabeeran Ni Kuma nayi maza nace Asshhadu An Lailaha illallahu wa Asshhadu Annan Muhammaur rasulullahi S A W

Umar Bai boye farin cikin da yayi ba da Kuma Jin abinda na furta Amma Kuma sai ya tambaye Ni ta Yaya hakan ta faru?
Na Gaya mishi duk yadda akayi da Kuma yadda mukayi da fauziyya har zuwa abubuwan da ta fada min Akan salloli da dukkan abinda ya shafi musulunci Ni Kuma nace Zan siyo Alkur ani nazo ka Fara koya min Kuma kaima Zan Roki Alfarmar ka Rufa min Asiri Kar ka fadawa kowa

Shima yayi min alkawarin Rike min sirrina Kuma yayi min alkawarin Zama min Dan uwa Kuma zai Dora Ni akan dukkan abinda ya shige min Duhu fiye da Wanda fauziyya tayi min tun daga wannan Rana ya Soma da koya min Alkur ani tun daga basmala zuwa fatiha da kula uzai Wanda tuni Yar Amana ta koya min su Kuma na iya tun da dasu nake salla Kuma yace Yana son ganin fauziyya Yar Amana don itace macen da ba zai taba mantawa da ita ba Wai don ta Kara taro mishi masoyiya . Na Rufe fuskata Ina Fadin yanzu ne kake Sona ko kuwa tun tuni? Yayi murmushi yace ai tun daga Ranar da na Fara ganinki kin Fadi na kamu da kaunar ki don a Ranar banyi bacci ba ke nayi ta gani sai dai Ina zullumin yadda Al amarin mu zai kasance sai gashi Allah da ikon shi kin zamo yadda nake Kinga kuwa ai Dole na godewa Allah na Kuma yabawa Yar Amana. Kunya ta hanani Zama na taso Ina Fadin Ni dai Zan tafi gida ya taso ya biyo Ni Wai yayi min Rakiya har bakin motata ya kawo Ni ya Kuma bude min Yana fadin Wai Baki ma fada min sunan da Kika canja ba ko ita Yar Amana Bata fada miki komai Baki ya canja na yanzu? Nace ta fada min kawai dai ban San sunan da Zan amsa bane.....

"Ai na zaba Miki shi tun tuni tin kafin yau din Nan sunan ki Aminatu idan Kuma munyi Aure sai na kiraki da abin Sona kunya ta kamani inda naji lallai sunan Aminatu ya burgeni sosai na Kuma yarda sunana kenan nayi mishi godiya nace Nima zabin nashi yayi min da haka mukayi sallama Yana Kara fada min lallai gobe goben Nan na kawo mishi Yar Amana yayi Mata tukwici nace mishi Zan kawo ta kuwa. Naja motata na nufi gida



Ina karasowa na hango motocin Nan da sukazo tare da yarima Gibson inda naji gaba na ya Fadi ban tsinke ba sai da na SHIGA gida bayan na cire hijabina na boye a mota na SHIGA gida na samu Amaka ta hado min akwatina Wai dama yanzu take nufin kirana don yarima Gibson ya Aiko a daukeni don naje nayi mishi Zaman dakin da Zan dawo da ciki Wanda suke fatan a zaman wata uku kadai na samo shi ba sai nayi zaman wata shida ba don Auren namu kusa kusa za ayi shi ba lokaci za a ja ba..............

.












Labarin GARWASHI na kudine ga duk Mai bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669












Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran














Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ₯°πŸ’ƒπŸΏπŸ˜‚
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€





πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
39//40
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne


Sadaukarwa ga dukkan musulmin duniya wanda suka yarda da kaddara suka Kuma yarda Babu Mai yi face Allah suka Kuma dogara ga Ubangiji Allah ya kabamu mafita


Fatan ALHERI ga mahaifina dake kwance kushewa Allah kasaka Rahamar ka Akan sa da dukkan musulmin duniya Kuma muminai maza da Mata


Kyautar wa ga Anty Aisha Bara'u Allah ya Baki lafiya yasa kaffara


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹



...........Nayi turus Ina kallon Amaka da ta jido min akwatuna tamkar wadda zata bar garin gashi Kuma a yanzu babu abinda nake bukata irin sarari don na Rabi Umar na Kuma Kara sanin yadda Zan bautawa Ubangiji sai gashi Wai Amaka na fada min wai Zan tafi wani gari inda Zan kwaso zunubi Wanda Wai Zan tare a dakin wani Kato tamkar matar Auren shi ba Kuma Zan dawo ba sai da cikin shege Wanda su Kuma wannan cikin shine abin alfaharin su
"Kizo Mana kiyi wanka Kika tsaya Raba Mana kallo ko ko me kike nufi ne naga bakya murna da zuwa zaman dakin yarima Gibson?
Amaka ta katse Ni da fadin Haka Amma nayi shiru ban tanka Mata ba


"Wai bakiji abinda nake fada bane kike min shiru? Na fa kula da take taken ki Akan yaron Nan Dan gidan igwai Banga kina Rawar jiki akan shi ba halan Baki da labarin har Mata ke mutuwa saboda son shi?
"Wahala ce Bata ishi wadda ta mutu Akan shi Ni a idona Banga abin Rawar jiki Akan shi ba....

Ban Rufe bakina ba naji Mari Amaka ta kwado min
"Ai dama tuni nagane abinda kike nufi akan yaron Nan to Kuma kinyi karya Wallahi sai kin Aure shi Koda Zaki mutu sakaran banza marar tunani Baki San Rabo bane Aure a gidan igwai? Yar iska ki haifo Mana princess ba alfahari bane? Tashi maza kiyi wanka na kaiki in Kuma Roki ayi Miki ADDU A ki SHIGA da sa a kina zuwa ki samo ciki ko haihuwa ba Zan Bari kiyi a gaba na ba za ayi bikin ku ki haihu a can don su tabbar da ke din irin haihuwa ce

Haka nayi wanka Ina kuka na
Showing 27001 words to 30000 words out of 30837 words