mu har Kuma zuwa yau din Nan da muke tsaka da garari a cikin Duniya don Haka ku biyo Ni kuji haduwar mahaifina da mahaifiya ta da irin kaddarar da ta taka Rawar da har suka Zo Kan gabar Aure da haihuwar mu muka Kuma shigo Duniya cikin wani mashahurin gata Amma dare Daya Ubangiji ya sauya komai duk dai acikin waccan kaddarar da take Rubutacciya


Kamar yadda Ammi ta sanar Dani sunanta Justina............







Labarin GARWASHI na kudi ne ga duk me bukatar jin cikakken labarin zai biya dari uku 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669





Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin daban yake da sauran







Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ’ƒπŸΏ
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€




πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
19//20
Hadiza Bara'u Gidan iko




Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Tukwici ne gareku
Nafisa Rabi u Umar Mrs Abdul
Rukayya GAWATA
Hadiza D Auta
Wasila ummu Aisha
Bilkisu h muhd
Haj Jamila Dan fajo
Rabi atu Bashar Abdullahi
Fedyn bash
Nagode muku kwarai

Gaisuwar girmama wa ga haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria

Yan Uwa na maza da Mata Ahalin gidan Alh Bara'u Sani majema Ubangiji ya Kara daukaka

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


............Justina shine sunana Yar gidan wani mashahurin me kudi Mai suna maazi Nkem . Ma azi Nkem hamshakin Mai kudi ne Wanda ya Tara dukiya Mai dumbun yawa saboda shaharar shi ta fuskar kasuwanci komai saidawa yake in nace komai to Ina nufin komai Domin ko Maazi Nkem har gidan giya gareshi bama guda Daya ba don Haka komai da Ruwan ka ne don mu a Al adar mu Dole ne ma mutum yayi kudi na kecw Raini don Babu abin kunya agaremu irin mutum ya Rayu cikin talauci Kuma ya mutu cikin talauci har Diyan jikoki sai an gorantawa ace Basu da k'ashin arziki don haka NE maza ke zagewa su nemi kudi ba sai lallai ta hanyar Sana a ba ta kowace fuska dai kayi kudi don ka kaucewa talauci Akasin wasu dake fita bakin Rai bakin fama su sata ko suyi kisa su kwashe koma su bi Dare su fasa gidaje ko shaguna Akasin Maazi Nkem Wanda shi Sana a ce ta Tara mishi kudin shi kowace iri ce kuwa zaiyi ya samu kudi inda ya Auro mamata madam Amaka ita Kuma ma aikaciyar Yar Boko ce don har Aiki ta Fara Amma ganin Maazi Nkem da kudin shi shi ya hanata Aikin Kuma ta yarda ta hanu.

Rayuwar gidan mu abin burgewa ce don mu uku iyayen mu suka haifa maza biyu mace Daya Kuma dukkan mazan biyu yayu nane nice karama Kuma mace Daya don Haka fasalta yadda Zan kasance a tsakanin iyayena

Idan nace sunaji da Ni naso Bata yawun bakina ne kawai ba garesu iyayena ba Baga Yan Uwa na ba guda biyu Sony da Emmanuel wadan da suke tsare da wasu bangarori na dukiyar Maazi Nkem

Wani Abu Kuma da ke burge mutane akaina shine Ni din tamkar ba jikin Amaka da Maazi Nkem na fito ba don ko kusa banyo kalar kowa ba tamkar ma ba Yar Nigeria ba nafi Kama da black American sai dai Ni farace tas irin farin Maazi Nkem Amma bayan wannan komai nawa daban ne kuma na musamman ba irin na Yan Matan garin mu ba. Manyan idanu da dogon hanci me idanu irin na yankan kifi lumsassu gashin kaina har kafada bakina Dan karami Wanda a gefe Kuma Ramin kyau ne (dumple ) da nayi murmushi sai ya loba
Kirjina daidai Ni da shafaffen ciki da budadden kuturi daga kasa ta ko Ina nayi daban da Matan yankin mu don za a Tara dari sai sa a mukai uku hatta d yatsun hannuna daban suke Kuma abin kallo ne wurin mutane mussamman maza sai Kuma akayi sa a bana son kallo da na kula ana kallo na yanzu ne zan fashe da kuka Kar ma ace tare nake da Amaka ko Maazi Nkem Wanda Yake alfaharin sakani gaba nayi mishi Rakiya duk inda zaije kuwa Akasin yasa ka babban Dan shi gaba suje wato Sony sai nice yake sakawa gaba muje

Duk wani Abu da Zan nema a gidan mu Zan sameshi wurin Maazi Nkem ko Amaka ko su Sony da Emmanuel kowa Yana min abinda nake so hatta makaranta ta kudi aka sakamu a komai sai an kure adaka ake Mana


Sai dai Kuma a gefe guda iyayena sun tsani nayi mu Amala da bahaushe Kai ba Ni kadai ba ko su Sony aka gani da aboki bahaushe yanzu zakaji bakin Amaka don tafi Maazi Nkem kin hausawa da ma addinin da sukeyi wato musulunci don Amaka ko siyayya batayi wurin musulmi bisa Dole su Sony suka hakura da abokai musulmi sukeyi da Yan jinsin su Wanda yaren da addinin Yake Daya


Sai dai Kuma Ni a wurina abin ba Haka yake ba don na Fi son nayi kawance da hausawa Kuma Ina masifar son mu zauna fira da su muna Labari don nagane su din suna da wayewa sosai kuma basa nuna min kyama Akasin wasun mu dake nuna kyama ga hausawa irin dai Amaka
Ni Kuma sai ya zamo kawaye na kaf hausawa ne Kuma musulmai Ina Kuma Jin dadin taraiyar mu da su don babu kyashi bare mugunta a tare dasu sai nake Jin dadin kasancewa dasu har bana son ayi hutu don kar mu Rabu harma nakan ziyarci wasun su a gidajen su Amma fa Ni ban taba gayyatar wata zuwa gidan mu ba don nasan yadda nake zuwa gidajen su iyayen su na faram faram Dani su idan sukazo gidan mu kunya kawai zasu Sha don nasan ba karamin aikin Amaka bane ta Rako su da bulala

Na kasance me lalurar aljanu Wanda ban mance mafarin cutar tawa ba wata kirsimeti ce munje gida can jihar imo kasancewar su Amaka duk Yan jihar imo ne ana ta bukukuwan crismeti mun nutsa daji Ni da kawaye na kasance wa ta me son korayen tsiro na SHIGA Ina ta tsinko duk kalar koren tsiron da yayi min sai Kuma na hango wani wuri fetal babu komai a wurin tamkar an share ko haki guda Daya Babu abin ya bani mamaki ganin daji ne babu kowa Amma Wai wurin kamar an share tas tas sai kawai naje na zauna a wurin yayin da su coma suke can saman bishiyar kwakwa zasu Ciro Mana Ni Kuma Ina Zama a wurin Nan sai naji wani Abu Yana hau min Kai tamkar Yana tilasta Ni Rufe idanu inda Kuma naji coma na kwala min Kira Wai na tashi daga inda na zauna baban ta yace Kar su sake su taka ko da kafa ne bare su zauna .

Sama sama najiyo ta ban Kara sanin abinda ke faruwa Dani ba sai dai farkowa nayi na ganni Akanyar Amaka suna ta Rusa ihu Nima sai na Soma Rusa ihu inda aka kwasheni zuwa gidan Mai magani akayi ta banka min sauyoyi magani da hayaki

Haka muka dawo gida ba tare da tunanin cewa akwai wats sauran matsala Akan wannan ciwon ba don magani daban akayi ciwo daban. Sai ya zamo ba a Rufe kwanan wata ba tare da ciwon Nan ya tashi ba Kuma Haka akayi tayin magani daban ciwo daban har waje dai an kaini Amma babu wani sauyi sai bankar maganin bature nakeyi da neman sauki Akan ciwon tashin aljanu


Wata Rana a makaranta kawata sumayya Ahmed yabo ke fada min da ciwon nawa ya tashi a makaranta cewa ciwona fa ba na Asibiti bane warakar shi tana cikin Alkur ani don dai bamu sani bane

Sai naji kwarai na gamsu da maganar sumayya Ahmed don inda ciwon na Asibiti ne ai har waje an fidda Ni Amma dai ana Nan jiya iyau
Da na komo gida nake fadawa Amaka cewa ciwona ba na Asibiti bane sai tayi maza ta tareni tana fadin....

"To na Ina ne? Na fada Mata yadda sumayya Ahmed ta fada min wai warkewar tana cikin Alkur ani ai kuwa ban Rufe bakina na Amaka ta gaura min Mari tana Sababi...............














Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669







Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan labarin na daban ne




Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunan ke cewa saduwar ALHERIπŸ’ƒπŸΏ
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€




πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
21//22
Hadiza Bara'u Gidan iko




Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne


Sadaukarwa gareku
Anty Aisha Bara'u
Anty Maryam Bara'u
Anty Zabbau Bara'u
Anty Binta Bara'u

Fatan ALHERI ga Uwa ta haj Sa adatu lawal Ade Allah ya Kara sutura da lafiya

Kyautar wa ga iyalan haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria mazan su da Matan su Allah ya daga lamarin ku


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


............."Ba Zaki Rabu da masu sallah ba ko? Bance Miki Kar ki kuma Zama kusa dasu ba? Ta fada tana zaro min idanu inda nake turo Baki gaba Ashe bansani ba na Kara bawa Amaka haushi sai kawai naji ta zaune Ni akaina da manyan kuturanta Wai naji nauyin ta akaina

Ta kuwa zaune Ni Tana fadin "Ai tunda dai na Raba ki da mutanen Nan mayaaudara masu tallatawa mutane Addinin su ko Bai nema ba matukar Baki Rabu da mu Amala dasu ba to Zan saka wuka in yanke kine matukar na karajin kinyi magana da masu salla


Sai da ta gaji don kanta kafin ta daga Ni Amma ko kadan banji Ina son in Rabu da kawaye na ba sai dai duk yadda Amaka zatayi sai dai tayi

Haka na ci gaba da Rayuwa cikin ukubar matsalar jinnu sai dai duk Ranar da ciwon ya motsa sai dai mu tare a Asibiti mu Kashi kudi mu dawo

A lokacin da na Gama karatu Maazi Nkem ya siya min mota me tsada na Soma SHIGA gari a kuma wannan lokacin ne na some tsanar zuwa coci inda Amaka ke Mika kokon barar ta ga malaman cocin Akan ciwona inda ake ta min ADDU A yayin da Maazi Nkem Yake bada kyautar kudi da Kaya ana kawowa coci yayin da Ni Kuma naji kwata kwata bana son zuwa cocin a duk Ranar lahadi Amaka Kan tusa Ni gaba muje wani lokacin ma a mota ta muke zuwa inda Kuma na Soma kalula da karyar ciwona tun Amaka Bata farga ba har dai ta gane son zuwa ne banayi ta Kuma ce ban Isa ba bisa Dole take tasani gaba muje Amma da mun Isa sai na fakaici idon ta sulale na bar cocin na koma gida


A cikin wannan lokacin ne Kuma na samu adimition din jama ar Legos a matakin farko inda Kuma muka sake hadewa da kawaye na na baya wato sumayya Ahmed yabo da fauziyya Yar Amana muka sake kullewa fiye da Baya
Zuwa wannan lokacin na farajin Ina Sha awar irin kayan da suke sakawa musamman hijabi da dogayen Raguna amma na San ko giyar wake Nasha ban Isa na Kai su gida ba bare Amaka ta gani bare na kaisu jikina


Na dubi sumayya bayan mun fito daga lacca nake duban ta cikin Sha awar shigar ta ta atamfa da katon hijabi harma da Nikabi
"Wai sumayya kin taba fada min ciwona bana Asibiti bane na Alkur ani ne ko? Tace Eh haka ne Justina hakan NE kawai zakuyi ki Rabu da ciwon ki don aljanu ne fa suke shigar mutum Kuma sunfi shigar Mata mafi yawan lokuta Matan dake yawan Zama babu Dan kwali ko Babu suturar kirki Suma Wai Sha awar Matan suke ku Kuma ba zaku iya saka irin kayan mu ba
Nace
"To Ni yanzu yaya zanyi da Alkur ani in warke ne sakawa ake a Ruwa koko yawo Zan Rika yi dashi? Sumayya tayi Dariya tana fadin
"A a karanta Miki za ayi sai kiga kin samu sauki Amma fa sai Allah ya yarda kinsan komai Allah ne ke yin shi

Nayi shiru don nasan Amaka ba zata yarda da hakan ba Dole nayi shiru Amma a Raina Ina tunanin Yaya za ayi ayi min karatu?

Haka na kasance Ina ta fama da ciwo in ya tashi Nasha maganin bature in Kuma lahadi tayi na sulale Amaka tayi ta Sababi tana fadin ba zanje ayi min ADDU A ba to Allah yasa asake wata lahadin bakije ba kiga abinda zai faru

Ban damu ba Ni fatana kawai na samu Wanda zaiyi min karatun Nan don kullum abin ci gaba yake akasin da nake kwanciya ciwo yanzu bugeni ake na Fadi tamkar matacciya magani kuwa babu Wanda ba a Nemo min ba Amma babu wani ci gaba

Mun Isa jihar imo inda ake bikin Yar sarkin imo wanda ya kasance sarkin garin mu Kuma Wanda Maazi Nkem Yake matukar girmamawa tamkar ya duka ya bi ta kanshi ya wuce . Wannan girmamawa da Maazi Nkem yakewa sarki yasa suke matukar mutunci Wanda Nima na samu SHIGA a gidan nashi harma na zamo kawar onye wato Amarya don Haka da bikin ya tashi Maazi Nkem ya kwashemu har Amaka muka tafi halartar bikin gidan sarauta a jihar imo

Kai tsaye fadar sarki muka Fara Isa mukayi gaisuwa inda sarki ya dafa kaina Yana yabawa kyauwuna Yana Kuma yi min ADDU A cikin yabawa da nuna kauna

Aka Soma gudanar da shagalin biki irin na gidan sarauta inda Amaka ke can wurin matar sarki suna ta gudanar da nasu shagalin Nima Ina cikin su onye amarya wadda na ji Wai Dan sarkin aber ne zata Aura
Duk wasu Kaya na shagalin bikin an tanade su an Kuma Rabawa mahalar ta bikin Wanda Nima na samu kasona na wata Riga doguwa Mai hannun shime wadda aka Dan Rufe kirjin ta da wani less me shara shara Kuma aka tsuke kasan ta ta yadda ta bayyana kuturin Wanda ya sakata

Wurin da za ayi taron katon filine Wanda ya ke a cikin gidan sarautar inda Kuma aka hada wasu manyan manyan itace aka hada wuta tana ci ganga ganga . Shi dai wannan taron sunan shi agare amarya ce za a bawa namijin tantabara shi Kuma Angon abashi macen tantabara su fito fili inda wutar Nan take ci idan Amarya ta taba sanin wani namijn kafin Angon nata to tantabarin hannunta zai mutu idan kuwa Bata taba sani kowa ba to na tantabarar hannun Angon nata zata mutu..............












Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669






Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan Labari daban yake da sauran







Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERIπŸ’ƒπŸΏ
πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€πŸ–€




πŸ’πŸ’πŸ’ GARWASHIπŸ’πŸ’πŸ’
Page
23//24
Hadiza Bara'u Gidan iko





Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne


Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Allah kayi musu Rahama kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH madaukakiya da dukkan musulmin duniya


Yabawa ga masoyan Rubutun Gidan iko musamman masu comment sannun ku da kokari son so πŸ₯°

Tukwici ne ga Anty Amina maman muhmd da Anty A'smau maman maama

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


.............Muna tsaye a filin Ina hagun onye dake Rike da tantabarar ta yayin bici ke ke damanta yayin da shima Ango Peter yake tare da abokanshi yarima Gibson Yayan Amarya Wanda ya zuba min ido Yana kallo na abinda na tsana kenan

Hatta Ahalin gidan sarkin sun fito filin don su ga yadda Wannan taro zai Kare Amma fa fuskar Uwar Amaryar cikin tsoro da zullumi don in har ya kasance yarta ta taba sanin wani namijn to karshen abin kunya ne a garesu Kuma abin kunya ga sarki da Ahalin gidan sa ace Yar gidan shi ta lalace kafin Aure don Haka kowa ke cikin taraddadi domin ko in har aka samu akasi shima Angon ba zai taba Auren ta ba don Haka acikin filin ma ba iyayen Amaryar ne kawai ba har da Ahalin gidan su Ango Peter kowa zuciya na bugawa musamman uwar amarya

A gefe na kuwa bana tare da komai sai nishadi don bikin ya kayatar Dani Kuma wannan Al ada tana burgeni ko Babu komai dai zai zaburar da Yan Mata kame kansu ko don irin wannan Rana da suke gudun fallasa ban sani ba ko don Ina tare da kewaye hausawa ne masu nuna min watsewar da ake a Jami a da Kuma na cikin gida yasa wannan Al adar ta burgeni? Ko ko dai don bana Ra ayin watsewar ne ? Oho Amma Kuma da yawa daga cikin yaren namu suna tur da Allah wadai da wannan tonon Asiri don da dayawa daga cikin Yan Matan dake Rasa budurcin nasu su Samarin ne ke batasu da Romon bakan su zasu Aure su wasu Kuma Yan uwan su NE na jiki ke karbe musu budurcin da ko mu muke girmama matar da takawo wa mijinta shi a gidan shi batayi saken da ta Rasa shi tun a waje ba

Kuma shi wannan tonon Asirin ba Wai sai a irin gidan sarauta ake you shi ba ko a gidajen talakawa suna alfahari da shi don suna ganin hanyace da ake wanke zukata daga zargi Ango zai karbi matar shi babu zargin ta zaga yawo ko wani ya Rigashi samun budurcin da suke wa kulafuci. Suma Kuma iyayen ta zasu San Basu bawa yarsu tarbiyar banzaba kowa dai zai Gane Babu cuta a cikin Auren su bare zargi.


Sai dai Kuma a gefe guda akwai wata Al ada
Showing 15001 words to 18000 words out of 30837 words