ππ GARWASHIππ
Page
1
Hadiza Bara'u gidan iko
Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne
Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Ubangiji Allah kayi musu Rahama kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH don girman shaffakin manzon Allah kasa ADDU AR da sukayi garemu karbabbiya ce
Har kullum Ina godewa masoyan Rubutun Gidan iko bani da Bakin godewa sai dai nace Ubangiji yafi Ni yabawa son so nake muku Yan uwa Allah ya hada mu a ALJANNAHπ₯°
Godiya ga Ubangiji da ya yarda har na sake dawowa da wata firar Mai take GARWASHI Allah yadda kake taimako na a ko yaushe ka ci gaba da taimako na har karshen numfashi nayi ta yin nasara a komai na Fara lafiya na Gama lafiya
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
........"Kaddara sunanta guda Daya ne Amma ma anarta da harsunan ta sunfi gaban a kidaya bare a iyakance. A yadda na fahimci kaddara da Kuma sunanta sai na kalli Duniya da abinda ke cikinta duk a matsayin kaddara. Idan nace kaddara to Ina nufin kaddara. Sai dai yadda Ni na fahimci kaddara akaran kaina ba Haka sauran mutane suke kallon kaddarar ba. Domin ko mun samu banbanci kwarai da gaske. A gareni kaddara itace komai ya samu bawa kaddara ne Dadi da wuya. Samu da Rashi Rayuwa da mutuwa ita kanta DUNIYA da abinda ke cikin ta kaddara ne . Zuwan bawa Duniya ma kaddara ne Amma sai na fahimci mutane Abu guda Daya Tak suke Kira sa kaddara shine wani Abu da ya samesu marar Dadi shine kawai kaddara ban sani ba Ni fahimtar da nayiwa kaddarar ko don ya kasance gaba Daya Rayuwa ta kaddarorin ne sukayi Mata zobe ne yasa na fahimceta Haka? Koko nawa zaton ne dai Haka ? Oho.
A wannan labarin ma da Zan baku ma babu komai a cikin sa sai tarin kaddarorin da suka faru akaina da iyayena da ma Yan uwana kwara biyu da muka Rayu a wannan kuntatacciyar Duniyar marar tagogin da zasu bamu iskan da zamu Shaka bare mugane Yan cin dake cikin Duniya Wanda har na kirawa kanmu GARWASHI domin ko gara zama a cikin GARWASHIN WUTA da irin kaddarar da kaddarar ta Miko Mana dolen mu kuma muka Mika hannu muka karba har ma muka bita da godiya duk da babu murmushi yayin godiyar sai ma tarin HAWAYE Mai radadi a garemu musamman ma Ni yarinya Fatima Zahra da duka duka shekaruna Sha biyar ne kacal Amma kaddara Bata tausayawa kuruciya ta ba kamar yadda bata tausayawa mahaifiyata ba Akan Rashin dangi da Yan uwa tayi aikin ta Akan muπ
Ku shirya ku Kuma gyara Zama kuji yadda kaddara tayi sukuwa ta kumayi zamiya Akan mu Wanda karfin imani ne ya Hana mu hadiyar zuciya mu kauce daga cikin Duniya da Rayuwa...........
*** *** **** **** ****
GARWASHI
Karfe 12:09 am ta buga Mana muna tsakiyar filin jirgin marigayi malam Umar Musa yar Adua a garin katsina motar da mahaifiya ta ke ja kirar marcendy ce 3400 muka SHIGA filin jirgin Wanda yayi daidai da Jin Rigugin jirgin AZAMAN Yana Shirin sauka Alamar dai ba wani dogon jira zamuyi ba Daddyn zai iso nayi murmushi Mai sauti yayin da ammi ta tayani wurin fadin
"Munzo a daidai ga abin Sona Nan Zuwa
Ta fada itama tana Kara fadada murmushin ta Wanda yayi daidai da parking din motar da tayi a daidai parking space da sauri na balle murfin motar na fito ina daga kaina sama Ina kallon jirgin da Yake shawagin sauka kasa cikin wani salo Wanda ya dauki hankali na
Na daga tafin hannun na Ina Kare Ranar dake kashe min ido don na kalli jirgin da Wai buwar da yakeyi idan zai sauka da kyau har ma in bawa Yan uwana labarin da nagani
Ammi tana Raba Mana kallo Ni da jirgin da ya dauko abin sonta cikin murna da farin ciki har zuwa lokacin da jirgin ya Soma saukowa kasa Yana tsillawa aguje kamar ba sauka zaiyi ba kafin ya zuro tayoyin shi da nagan su ya mitsimitsi kafin ya diresu a kasa fankokin shi na wulwulawa inda kuma wata mota Mai dauke tsani wato kwarangar da matafiyan zasu tako zuwa kasa
Na finciki hannun Ammi Wai ta taho itama da sauri ta biyo Ni inda Kuma Naga kamar bata sauri don Haka na saki hannun ta na sheka aguje da nufin idan Daddyn ya fito in fada jikin shi na Rungume shi nayi mishi oyoyo shi Kuma ya sureni yayi sama Dani Yana cillawa sama. don gaskiya Ina son Daddy na fiye da ammi don shi Kam biye min Yake Kuma duk abinda nake so shima shi Yake so yayi wasa Dani yayi dariya in fada mishi damuwa ta yayi min magani akasin ammi da ta Fi bawa Yan uwa na maza kulawa musamman Yaya Abdullahi da kanena sulaiman muhimmanci fiye Dani Ni Kuma Daddy yafi bani muhimmanci abinda ban sani ba shine kaddarar farko kenan da Zan Soma dandan Akan harshena da idanuna da Kuma zuciya ta Akan Daddy na Mai bani kulawa
Muna tsaye muna jiran a bude kofar jirgin don inyi ido Hudu da Daddy na koma in fada jikin shi muji dumin ya da mahaifi da nafi kowa muradin hakan
Kofar jirgin ta bude inda na Fara ganin aminin Daddyn ya Fara fitowa fuskar shi Babu sassauci kafin wani mutum ya biyo bayan shi sai Kuma wasu fuskoki da ban San su ba ban taba ganin su ba suka fito suka dauke da wani Abu Mai kamar gadon tura marasa lafiya wani Abu Wanda aka nade cikin farin yanki kwance Akan gadon kamar gawa........
Gabana naji yayi wata irin sarawa har naji kaina na neman daukar ciwo na juyo Ina kallon Amma wadda ta taho aguje tana bude fuskar Wanda ke kwance Akan gadon Nan fuskar was Zan gani? Daddy na ne babu Alamar motsi ko numfashi a tare dashi
Kafin na tambayi aminin Daddyn wato Alh Mustafa abinda ke faruwa Akan Daddy na sai Jin kukan mahaifiyata ammi naji cikin wata murya da ban zaci Tata bace...........
Littafin GARWASHI na kudine ga me son Jin cikakken labarin zai biya dari uku ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko katin MTN Akan wannan layin 08035191669
Labarin GARWASHI daban yake da sauran labaran gidan iko kasance da shi don Jin yadda kaddara tayi Aikin ta Akan wadan Nan bayin AllahππΏ
Kar ku Bari abar ku baya
Gidan iko shine sunanan ke cewa saduwar ALHERIπ₯°
π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€
πππ GARWASHIπππ
Page
3//4

Godiya ga Ubangiji madaukakin sarki Mai iko Kan komai da kowa da yake aminta har komai ya zamo cikin falalar shi ta kasance kun fayakun Allah ka saka mu a cikin kun fayakun Dinka Duniya da lahira
Gaisshe da haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria tare da girmamawa
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
..........Kukan da Naga Ammi nayi ne ya fahimtar Dani wani Al amari Mai girma ya faru ko Kuma Yana Shirin faruwa Wanda ban shirya ji ko gani ba bare daukar shi a zuciya ta.
Har ga Allah ban kawo mutuwa Akan Daddy ba abinda kawai Rai na ya bani bashi da lafiya tuna hakan da nayi ma ya kara jefani a cikin Rudani da tashin hankali don ban bawa Daddy mutuwa a wannan lokacin ba sai yayi min Aure har Ya'ya na sai ya dauka Amma fa a yadda na tsara kenan ban San nayi daban da tsari na da tsarin Ubangiji ba. Wannan kaddarar itace ta zamo masomi ko nace mafari duk da Akwai wata dadaddiyar kaddarar da na baro muku ita a baya Akan Daddyn da ammi wadda itama zakuji sanadin kaddarar da ta hadasu Wanda haduwar ce kuma ta sake bada wata kalar kaddarar duk shi Ubangiji babu Ruwan shi idan zaiyi Abu ba don aso ko aki ba a mutu ko ayi Rayuwa shiyasa ma akace alkalamin kaddara zanen shi baya gogewa to hakan take Akan mu shiyasa muke ta biya kaddarar mu da Bakin mu muna kuka ko muna dariya......
Kukan da Ammi ke Rerawa cikin fita hayyaci da kalaman dake nuna mutum yaji dukan da mutuwa ke barwa Wanda tayiwa ta adi wato sambatun radadi na Soma jiyo abinda take fadawa Daddy......
"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un yau Ni Ina Zan saka kaina faruk me yasa kayi min Haka? Ina Alkawarin da kayi min na zaka zamo min Uwa Kuma Uba?
Ga wa ka barni bayan kasan bani da kowa sai Allah sai Kuma Kai ba don na Rasa Ahali da dangi da Yan Uwa ba? Don Allah ka tashi Kar kace min ka tafi ka barni da yaran ka da Basu da gata sai Kai. Don Allah Umar ka tashi ka ci gaba da kasance wa farin ciki na kamar yadda kayi min alkawari kafi kowa sanin bani kowa sai Kai Yan uwan ka zasu samu damar keta Ni . Iyayena zasu kasheni in suka tabbatar babu Kai a Duniya kayi min Rai kayi min gata Kar a tarwatsa min farin ciki don Allah ka tashi faruk kace min baka mutu ba kana Raye
Yadda take jijjiga gawar mijin nata ne ya sake fahimtar Dani lallai munzo gabar da wasu mutanen suke so muzo don su wulakanta mu musamman Ammi da Yan uwan Daddy basu kaunar ta don kawai ta kasance ahalul kitabi kafin Auren Daddyn shikenan suka Dora Mata kahon zuka sai gashi yanzu Daddyn da ya zamo Mata garkuwa yau Babu shi duk da ban San komai Akan abinda zuciyar ammi ta kunsa ba Zan iya cewa zafi biyu takeji a yanzu
Zafin Rasa mijin da yayi Mata gata da Kuma zullumin abinda zai biyo bayan mutuwar mijin nata daga bangaren Yan uwan shi
Tunda na tsinci kalmar mutuwar Daddyn a harshen ammi nake Taya ta kukan Rashi ko nace nake Taya ta tausayawa kanmu don nice nayi Rashi tayani kawai takeyi
Mun cika filin jirgin da kukan mu Ni da Amma kafin aminin Daddyn wato Alh Mustafa ya katse ammi da wata tsawa Yana zare Mata idanu abinda yayi matukar Bata mamaki don ta hango wani Abu Mai Kama da tsanar ta fal idon shi abinda Bai taba nuna Mata a lokacin Rayuwar mijin ta ba akasin zolaya da kambama ta wurin iya kula da abokin shi.......
"Ke da Allah saurara Mana Haka Nan tsiyar tubabbu kenan ko zasuyi shekarun Annabi huhu a cikin musulunci sai sun nuna maka asalin su da jinin jikin su mu a addinin mu na musulunci kukan mutuwa haramun ne kar ki sake daga Mana murya anan ja daga baya ki Kuma matso da mota mu saka shi mu wuce gida dubi da Allah yadda Kika Tara Mana mutane sai kace akanki aka Soma Rasa miji
Ni da ammi muka bishi da jajayen idanun mu cikin wani madaukakin mamaki kafin jiki a sanyaye ammi ta Mika mishi key din tana fadin Bata da nutsuwar iya tuki don Haka sai ya amsa ya matso da motar aka sako gawar mahaifina muka shigo mota ya tuko shi da wannan mutum da bamu San ko waye ba muka nufo gida muna sake sabunta kukan mu
A falo aka shimfide gawar Daddy inda Alh Mustafa ya cewa ammi ta buga waya can kauyen su Daddy ta sanar dasu
Jiki na kyarma tare da bugun zuciya ta Soma neman layin yayar mahaifina wato Yaya Badura cikin sa a Kuma ta sameta Amma sai da tayi Ringing sau biyar kafin Yaya Badura ta daga tana fadin
"Waye? Ammi taji wani sabon kuka ya kwace Mata tace
"Yaya Badura nice Aminatu........
"Na Gane muryar ai meye Kuma kike min shaken hanci (kuka)?
Ammi ta Kara saka kuka tana fadin
"Faruk ne Yaya Badura don Allah kuzo kuce mishi ya tashi Kar ya tafi ya barni bani da gata sai Allah sai Kuma shi.........
"Ke aniyar ki ta biki yar arnan dawa fatan da kike mishi kenan ya tafi ya bar Miki dukiya ko? To ki kwana da Shirin ciwon Kai idan ya samu ummaru na Rantse Miki sai kin bar Duniyar Nan bakar kaddara kawai. Kukan ammi ya Kara tsanani saboda Jin masifar da Badura ke Mata ita Kam Tata ta sameta
Badura tana sabe da wayar a kunnen ta tana sauraren kukan Ammi Bata kashe ba sai da ta tsinto muryar Alh Mustafa Yana waya Yana fadin Alh faruk ne Allah yayiwa Rasuwa sai kawai Badura ta kwantsama uban ihu inda mutanen gidan suka taru kanta tana fadin matar ummaru ce ta kirata tana kuka Kuma taji ana fadar ummaru ne Allah yayiwa Rasuwa.
Kan kace me ? Sai gasu kwai da kwarkwata sun ciko mota mazan su da Matan su Yara da manya sunyi dirar mikiya agidan Abu ga jahilcin kauye sai gidan ya amsa sunan shi wato gidan makoki don kewaye gawar sukayi suna ta gurzar kuka har da masu tashin aljanu wato Yaya Badura Wai ta Rasa Dan uwa me kaunar ta da daukar takalifin ta
Ahaka aka shirya Daddy akayi mishi sutura aka yi nufin sada shi da makwancin sa har aka bukaci ammi tazo tayi mishi sallamar bankwana. Ta kuma taho idonta na zubar HAWAYE ta sunkuya tana mishi ADDU AR samun kyakkyawan makwanci da samun Rabon Duniya da tana Kuma fatan can tafiye mishi wannan kuntatacciyar Duniyar marar mutane masu Adalci Adalcin da suke kasa yiwa kawunan su bare suyiwa wani.....
Kawai sai ji tayi an finciko ta an cillo waje
Ta dago idonta tana Kuma Jin zafin hannunta da ya bugu da Bakin kofar ta kalli yagana sai bude manyan hantunan ta takeyi Wai afusace take
"Uban me Kika sani acikin musulunci da musulmai da har kike wani mimi mi da Baki ADDU A kike son nuna Mana kin iya ne? Ai Baku gada ba bare kiyi abin kuzo mugani tuban Taki ta muzuru tuban ganin abin Duniya? Da Allah fice anan Kar kisa ayi mishi azaba akan tsayuwar ki Akan shi kayan kazanta dake iyalan oduduwa da fafaroma
Jin abinda ya kumbo na yagana ke fada tana tada murya yasa na kamo ammi dake HAWAYE muka fito yagana na Rako mu da wani matsiyacin tsaki
Sallamar bankwana da banyi da mahaifina ba sai dai na Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa don lokacin da Naga an fito da mankarar dake dauke da gawar shi ban sake sanin abinda yayi kantafi da Rai na da nutsuwa ta ba sai dai farkowa nayi naganni a Kan cinyar ammi tana shafawa fuskata Ruwa na kumayi nasarar ganin fuskar ta da ta kumbure saboda kuka Kuma har yanzu idaniyar ta Bata kafe da zubar Ruwan HAWAYE ba.............
Wannan labarin na kudine ga Mai son cikakken labarin zai biya 300 ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669
Labarin GARWASHI daban yake da sauran littatafan gidan iko Kar ku Bari abaku labari
Gidan iko sunan ke muku fatan ALHERIπ₯°ππΏ
π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€
πππ GARWASHIπππ
Page
5//6
Hadiza Bara'u Gidan iko

Har kullum godiya ga Ubangiji ta zamo Dole Akan yadda ya sauwake Al amura masu yawa agareni Allah ka Kara dubun dubatar salati ga shugaban halitta Wanda nake fatoh shiga cikin ceton shu Ranar alkiyama
Masoyan Rubutun Gidan iko babu yadda Za ayi na manta ku kun Kai har kun wuce a gareni ba don na iya ba kuke yabawa tare da ADDU AR fatan ALHERI gareni har da iyayena ko nayi nufin aje alkalamin don bawa kwanya da zuciya hutu sai naji fatan ALHERIN ku nake bukata sai na girgije na Soma sabon typingπ₯°
πΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
..........Zaman makokin mahaifina shima wata makaranta ce guda da za a dauki Darasi Kuma irin Darasin Nan da Duniya ce kadai Kan koyar da irin shi Amma ba Wai mutane irin dangin mahaifina ba
Zaman makokin ya kasu Kashi biyu NE a cikin gida yayin da akeyin guda Daya a waje wurin mazan...
Ko dayake can din ma biyu NE akeyi inda dangin mahaifina suka kafa majalisar su ta Yan uwa Kuma dangi yayin da Alh Mustafa ma shi da jama ar da suka San shi da marigayin mahaifina da mu amalar su suna kammale wurin Alh Mustafa inda Kuma su kawu madu da kawu gide suke tasu majalisar ta Yan uwan Daddyn in sunzo wurin su suke sauka kamar yadda a Nan ma cikin gida zaman ya kasu Kashi biyu . Su Yaya Badura da yagana suna falon Daddyn inda yagana ce tazo ta ce da ammi ta Bata key din dakin Dan uwan ta Bata Kuma ja ba ta Bata sai dai da Yake Kan nasu babu komai sai handama da babakere babu Arabi ba Boko sai hadama da son Azurta Kai yasa basu waye da komai na maraya ba kasancewar ko acan garin nasu na Maiduguri kauye ne sosai shiyasa ma da yagana ta karbi makullin ta kasa bude uwar dakin Daddyn sai suka tare a falon yayin da ammi ke falon dakin ta Kuma makotan tane Wanda suke gaisuwar mutunci tare da ita musamman mama da suke ga gida ga gida Kuma ta mayar da ammi yarta saboda ko shawara da ita ammi keyi shiyasa take tare da ita Kuma mutanen unguwa ma duk da kasancewar unguwar ta G R A ce irin Rayuwar kowa tashi ta fissheshi ake ba Ruwan kowa da kowa yasa dai daiku sukan gaisa ayi barka ko gaisuwa inda can Kuma wurin su Badura duk Wanda zaizo daga Maiduguri Kai tsaye wurin su yake yada zango
Ranar farko ta mutuwar Badura da yagana ne a cikin kichen suna faman dorawa da saukewa na abinci Wanda yagana ta karbo Dan makullin store Wanda ke shake

Book Chapters
Chapter 1 Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11