jinjina lamarin a zuciyarsa, shi dama baba Rabilu ya fad'a masa kafinsuzo, kafin Galadima ko Muftahu su sami damar magana baba Rabilu ya fara fad'in “Lallai kamar yanda na sanarmaka randa nazo gareka ranka yadad'e d'an uwanane shi wannan daya bada camera d'in, da ni da shi duk aikinmu d'ayane, bayan yakai wannan camera ga mahaifin Badi, gidana ya zarto, amma saiya iske ban dawoba sai iyalina kawai, yabar musu sak'on wasik'a da address d'in inda zan sameshi, wato k'oramar bakin gari inda shi Badi ya gammu, inayin sallar asubahi kuwa na nufi wannan wajen dan ya rubutamin Cewar yana cikin mawuyacin hali, yana tsaka da fad'amin abinda ke faruwa saiga wad'annan mugaye sun biyomu, bansan a ina sukaji muna canba, na gudu ne a tunanina shima Habu ya gudu, Ashe sun kamashi, saida na fara jiyo sautin muryarsa dake amsa kuwwar karmu tsaya mu gudu, badan nasoba na gudu nabar Habu a hannunsu, wasu a cikinsu sun cigaba da bina, amma wani mai lambu ya taimakeni ya 6oyeni, kwanana biyu a cikin lambun, saida mukaga komai ya d'an natsa sannan na fito Na koma gida, duk tunanina ai basu ganniba, shiyyasa nacigaba da y'an hidindimuna domin 6adda kama, a 6oye kuma na shiga binciken wanda Habu ya bama Camera d'in, dan ya gayamin tana masarauta wajen mai kula da barga, Labarin mutuwarsu tazomin shida matarsa a bisa bincikena, saidai a masarauta ance d'ansu Badi shine ya kashesu, Sam ban aminceba, wannan ya sakani Neman Badi domin na kar6i camera d'in hannunsa, inada tabbacin shine Habu ya sanarmin cewa gashi can alokacin da mutanen nan suka iso, saidai kallo d'aya namasa muka fara gudun tsira, daga nan kowa ya kama tsaginsa. Dole na ajiye aikina saboda tsaro, na kawo rigar siyasa na sanya dan nema ma kaina girma, shekarata 6 a rigar siyasa akayi yunk'urin kasheni, ba kowa bane da wannan aikin face Alhaji Shehu Adamu Darma, har gidana ya saka aka satoni, nayi mamakin ganinsa, dan jam'iyyarmu d'aya, wani sa6ani bai ta6a shiga tsakaninmu ba, dan haka na nemi dalilin sanin miyasa zaisa a d'akkoni cikin iyalina? bayan mu y'an jam'iyya d'ayane. Ya kwashe da dariya yana nunani da fad'in lallai Alhaji Rabilu fanisau bakada hankaki, a tunaninka dukkan 6addamin da zakayi bazamu ganoka ba? yanzu dai dukma ba wannanba, ina camera?. Nace wace camera kuma? Wani wawan duka yaronsa yamin, na dafe wajen saboda azaba, Darma yakuma cemin ina camera d'in da Habu idris ya bani? nanma na sanarmasa ban saniba, wannan ne yasakashi kar6ar k'arfe ya kwad'amin a kai saboda haushi, daga nan na fad'i a wajen, ashesu duk sun d'auka a lokacin dukna mutu, shiyyasa suka jefar dani gefen hanya suka tafi, wani bawan ALLAH ne ya d'aukeni yakai asibiti, abinda yasa su Darma basuji labarina ba wanann mutum ba d'an nan yankinmu baneba, fataucine ya kawoshi, daya d'aukeni kuma saiya bar nahiyar wannan yanki dani gaba d'aya, nayi jiyyar shekaru biyu, kafin na dawo dai-dai, duniya sukta d'auka na mutu, saida na d'au shekaru bakwai banzo wannan yankinba, dan bawan ALLAHn nan yazo har nan ya kwashe iyalaina ya kaimin, bayan yamusu bayanin dazasu fahimta, bayan shekaru bakwai nakanzo nad'anyi bincikena na koma cikin 6adda kamanni, a wannan yanayinne na farga da Badi, ban sanshiba gaskiya, amma ganin yanayinsa tamkar mai lek'en asiri shine na fara bibiyarsa harna fahimci wanene shi, hakama waziri da d'ansa, na lura kullum cikin bin diddigin yalla6ai Galadima suke suma, nima wannan abun shine abinda na sani, kunji dalilin Darma na kirana Fatalwa”.

Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar Galadima ya iya bud'e baki cikin muryar tsananin damuwa yace, “waishin minene a cikin camera d'in nan? Yanzu kuma wanene ke rik'e da ita?”.
Baba Rabilu yace, “Duk wannan muke son sani ranka ya dad'e, yanzu haka muna kan neman wanda badi yabama wannan Camera, dan na sanar masa har yanzu batazo gareka ba”.
Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana cije lips, idonsa yayi jazur, ya kalli Muftahu sannan ya kalli Badi dake zaune kansa a duk'e, “Badi yanzu idan ka gansa zaka iya ganesa kenan?”.
“insha ALLAH ranka ya dad'e zan iya, saidai idan har ya mutune, bakuma ma fatan hakan”.
Shiru dukansu sukayi kowa na nazari, Galadima sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa, shi kad'ai yasan mi yakeji, ya kalli Muftahu yana fad'in “Sarkin mota ya shigo, dan nasan baisan matsayin Badi a wajensa ba”.
Muftahu ya amsa da “to ranka ya dad'e”.

Cikin y'an mintuna saiga Sarkin mota tare da Muftahu sun shigo, a k'asa ya durk'usa yana musu sannu, Galadima ya kallesa yana nuna masa Badi, “kasan wannan?”.
Badi da Sarkin mota suka kalli juna, a lokacin ne Muftahu da Galadima sukaga kamannin su, saidai shi Badi tsufa ya 6oyesa kad'an.
Ganin sun shagala da kallon juna kowa yakasa magana sai baba Rabilu ya katsesu da fad'in “Badi kamasa bayani mana”.
Dattijo badi ya kamo hannun Sarkin mota kusa da shi, yana zubda hawaye yace, “matso gareni Yunusa, nine babanka yayan mahaifiyarka, Badi ya rungume Sarkin mota suka fashe da kuka, a haka yake bashi labarin alak'arsu. Saida kwalla ta cika idon Galadima, hakanne ya sakashi tashi ya fice daga falon, Muftahu da tausayinsu ya kamashi shima ya bi Galadima da hanzari.
A tsaye ya iskeshi ya tsurama flowers d'in da akama gidan ado dasu ido, hannayensa biyu duk cikin aljihu, gaba d'aya bugun zuciyarsa ya fara canjawa, sai had'iye yawu yake da k'yar, wayarsa ya zaro daga aljihu, rasa wanda zai kira yayi, sai bin numbers d'in yake da idanu yana canki canka, ya tsansa dai ya sauka kan number Munaya.........



**************************

Fitowata daga wankan yamma kenan Munubiya ta shiga, yau kwana biyu duk zuciyata babu dad'i, hakannan na tsinci kaina cikin 6acin rai, harzan fara shafa mai Aryaan ya shigo d'auke da Abdurrahman yana kuka, dole na ajiye man na kar6esa, na ta6a jikinsa da har yanzu zafin zazza6in daya yini da shi bai saukaba, saboda tunda asuba ya farka da kuka cibiyarsa na ciwo, kashinsa harya canja kala, saida innaro tazo tabashi magani sannan muka samu nutsuwa, daga nan kuma sai zazza6i, shine har yanzu nake d'an jin jikin nasa da zafi kad'an, nono na saka masa a baki kozai kama, dan duk yinin yau bai shaba, na sauke ajiyar zuciya ganin ya kar6a, ina shafa kansa idona na kallon fuskarsa data fara rikid'ewa zuwa kamannin mahaifinsa wayata ta shiga Ring, d'auke idona nayi daga kan Abdurrahman na maida ga wayar, nayi mamakin ganin yalla6ai, danna canja sunan tun a waccan ranar, na daiyi picking a d'arare na saka a kunne. yau dai banjira k'orafinsa ba nace, “Ina yini”.
A yanda ya amsa min sallamar da gaisuwar saida gabana ya fad'i har na cire ma Abdurrahman nono ban saniba, aikam ya fashe da kuka.
Hakkane yakuma rikita Galadima daga can, yace, “miya faru? Waye ke kuka?”.
K'aramin tsaki naja, nace, “Abdurrahman ne, wai dama ka dawo?”.
Bai amsa min na k'arshen ba saina farkon, yace, “mi'akai masa?”.
“Babu komai, bayajin dad'ine kawai”.
Lips d'insa ya cije yana fad'in “yanzu zanzo gidan”. Bai jira cewar Munaya ba ya yanke kiran.

Sororo nayi ina kallon wayar, kai kace zan ganosa a wajen ne, Munubiya data fito ta katseni da fad'in “mikike kallo haka? ga ruwan nono kin bari yana zuba a jikin yaro”.
Ajiyar zuciya na sauke, sannan na gyara ina kwantar da Abdurrahman d'in dayay shiru.
Munubiya dai takuma tambayata, fad'a mata zuwan Galadima nayi, tace, “oh shine kikema wannan mamakin ko miye?”.
'Dan hararta nayi, amma bance komaiba, itama ta ta6e baki tana kamo hannuna ta zauna a stool d'in Mirror. Wai sai tamin kwalliya.
Da faro k'in yarda nayi, saida naga ta 6ata rai sannan na hak'ura dai tamin inata tura baki gaba.....................✍🏻






*_ALLAH Sarki, wlhy harna fara missing d'inku, waya tamana tsiya😢, yanzuma da wayar Oga nayi typing, koba komai Comments naku na sakani nishad'i, I Miss you so much all😔😘😘😘❤❤_*


Insha ALLAH vary soon zan dawo gareku😂.






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
[7/29, 5:47 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣1⃣➖1⃣2⃣


.............Mintuna basufi 20 da gama kwalliyar ba saigasu Aiyaan sun shigo dad'an gudunsu, Munaya na cikin d'aki tak'i fitowa, wai kunyar su inna suganta da kwalliya takeyi.
Inna ta dakama su Aryaan tsawa saboda batason wannan gudun.
Nutsuwa duk sukayi.
Tace, “Gudun mi kukeyine?”.
Y'ar rige-rigen fad'a suka fara, kowa yana ture d'an uwansa akan shine zai fara fad'a, ana cikin haka Yaa Anas yay sallama.
Hayaniyar su Aiyaan ta hana aji, sai laraba ce ta farga dashi, shine Yakuma yimasu Aiyaan tsawa suka nutsu, kowa ya zauna gefe yana tura baki.
Yaa Anas ya gaishe da laraba da innarsu munaya, Munubiya ma ta gaisheshi, ya Amshi Ameen dake hannun inna yana fad'in “inna Yalla6ai Galadima ne fa agidan namu, gashi kuma duk su Abba basa nan, shine nace ko'a kawoshi nan ne”.
Inna tace, “A'a Anas, ai ba'ayi hakaba, bara na d'akko makullin d'akin Abbanku saika bud'e masa nan ya shiga”.
Anas yace, “to inna”.
Laraba dake taya Munubiya shirya su Amaturrahman tayi murmushi, a ranta tana yaba yawan karamci na ahalin Munaya, mutanene masu dattako da sanin darajar d'an Adam, shiyyasa kullum take kuma taya Galadima murna da samun tsatson wannan mutane.......
Tunaninta ya katse lokacin da inna tadawo da key ta bama Anas, Ameen ta kar6a a hannunsa shikuma ya fice.
Munubiya tace, “innarmu ajiye wannan ki k'arasa sama Abdurraheem kayan Dan ALLAH, sainaje na had'ama Abbansu abincin, nasan yanzu yayi”.
Inna ta harareta, “kai nifa kunma maidani Nanny d'inku, nizan ke muku hidimar y'ay'ane?”.
“please mana innarmu, basune masu kawo miki kaza kina ciba sannan kin tsufa”.
Laraba tayi dariya tana fad'in “Gaskiyarki kuwa Maman 2, ALLAH dai yaja da rai”.
Inna tace, “iya kema biyema shirmennan nata zakiyi?”.
Laraba takuma darawa tanama Abbdurrahman rawa.
Itadai Munubiya ta fice tabarsu, laraba na bama inna amsa.

Duk ina jiyosu daga d'aki, haka kawai sainakejin wani iri, yanzu dole ta gaban su Innarmu zanbi natafi wajensa? Na kalli kaina a mirror kunya ta kuma kamani, dukda Simple kwalliya Munubiya tamin nayi k'yau, dan d'aurin kaina ya zauna dak'yau, fuskata ta kuma nutsuwa, har rantsuwa tamin inhar na canja wani Abu saitayi 2weeks batamin maganaba, nasan kad'an kenan daga abinda Munu... Zata iya, shiyyasa dole na hak'ura na bari.....
Shigowar Munubiya yasani waigawa na kalleta, ta harareni tana matsowa tamin kallon tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska, “Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi”.
Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in “to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki”.
Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo.
nace, “haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH?”.
“Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni”.
Baki na murgud'a mata.
Tace, “oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba”.
Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito.
ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina.

Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar.
K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido.
Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba.
Munubiya tace, “To Abban 3 gatanan nakawo maka”.
Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Thanks you Auntynmu”.
Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in “Su twins rowarsu akemin?”.
Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa, “A'a Abban 3 zasuzo su gaida abbansu insha ALLAH”.
Baice komaiba sai murmushi daya sakeyi.
Ta harareni sannan ta fice, Nina ramawa nayi.

Koda Munubiya ta fice saiya kuma maida hankalinsa ga yaran ya shareni, abin yabani haushi, jinaima kamar na fice abina, amma na danne zuciyata na matsa gabansa. Wajen tiren abincin na durk'usa, na d'auki jug d'in zo6on na zuba a k'aramin cup, d'agowar da zanyi na kamashi yana kallona, amma saiya basar, baki na tura kad'an, na mik'a masa cup d'in.
Bai kar6aba, sai wani bina da kallo yake tundaga sama har k'asa, a raina nace rainin wayo.
Idonsa ya janye daga kaina, ya fara kwantar da yaran d'ai-d'ai a gefensa, saboda a doguwan kujera yake.
Saida ya gama nakuma mik'a masa cup d'in, hannuna ya had'a da kofin ya rik'e, na d'ago ido muka kalli juna, duksai na daburce, danya cire eyeglasses d'in, kamar mai koyan magana na had'o kalmomin gaisuwar da gyar.
Nace, “i...na..yini”.
Wani Munafukin murmushi yayi yana lumshe idanu, ya kuma bud'esu a kaina yana d'age girarsa d'aya da cizar lips, a hankali ya furta “ke matsoraciya Ce, miye na rikitar daga kallo uhmyim?”.
Idanuna nad'an juya nace, “Tab badai niba”.
Ya ta6e baki kad'an, idonsa akan hannunmu dake had'e waje d'aya akan kofin.
Nima saina kalli hannun, cikin sanyin muryar dabansan nayiba nace, “da sanyi fa”.
“Really?”.
Shiru nayi ban amsashiba, ya zame kofin a hankali, sannan ya koma jikin kujerar ya kwanta yana hard'e k'afafu.
6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, bansan miyasa inhar Galadima zai kasance kusa dani daf irin haka koya kafeni da ido nake rikicewa ba, haka kawai sainaji jikina yana tsuma...
Yay wani luuu da idanu saboda ajiyar zuciyar da tayi, zo6on ya kai bakinsa ya kur6a kad'an, dad'insa ya sakashi lumshe idanu ya had'iye.
Da hannu yamin nuni da kujera, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki na mik'e, harzan bar wajen naje ta nesa dashi saiya rik'o hannuna. Juyawa nai na kallesa, ya nunamin kujerar kusa dashi da ido cikin tsare gida.
Banida za6in daya wuce bin umarninsa, na zauna tamkar mai shirin guduwa da ance ar.
Zo6on yakuma sha yana kallona, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Ganin haka sai nace, “yaya jikin Abie? dasu Momma?”.
Yaji dad'in ganin ta damu da ahalinsa, ya ajiye kofin yana gyara zama, yace, “jikin Abie Alhmdllh munata k'ara ganin haske, duk since na gaidaki dak'yau”.
Nace, “ina amsawa”.
Daganan mukai shiru, kowa yana tattaunawa da zuciyarsa, Idan ka gammu saika d'auka wasu saurayi da budurwane, irin had'uwar farko d'innan😂.
Abimda na fahimta dai kamar yana tattare da damuwa ma, nad'an kallesa ta gefen ido, idonsa nakan yaransa, nace, “Abinci fa?”.
Maido da kallonsa yay gareni, yad'an yamutsa fuska yana girgiza kai.
Kallonsa nayi, cikin marairaicewar da bansan nayiba nace, “please mana yalla6ai, yanzu haka bakaci komaiba ka fito gida”.
Wani Abu dabaisan miyeba yaji ya tsarga cikin kansa har zuwa tafin k'afa, idonsa k'yam akan Munaya ko k'yaftawa bayayi,
Showing 18001 words to 21000 words out of 115198 words