an farane da fada.
Yau itace ranar farko da Munaya ta shiga Fadar sarkin ta, yaukam taga abin mamaki, musalta yanda wannan fada ta k'awatu ai 6ata lokacine kawai, ammafa lallai komai yaji, ga Sarki hakimce bisa garagarsa cikin kwarjini irinna mutuntakar mulki, sarkinmu kenan kuma sirikinna ta wani fannini, daga ni sai aunty Mimi da kuyangi ukune muka shiga, kowanne d'auke da yaro d'aya a hannu.
Fada cike take mak'il anata fadanci, Su Wanbai da talba duk ana ciki, hakimai da masu manyan muk'amai Na masarauta da wajen masarauta duk an hallara, kasancewar shine zaman farko Na wannan makon, kuma ana saka ran zuwan Governor ne da zaizoma mai martaba jajen abinda ya faru Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zagaye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma).

Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa.
Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi.
Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki.
Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci🤸🏻‍♀😂, ga irin naku manyan mata👍🏻)

To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki.
Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina .
Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Munaya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya.

************

Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Munubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma.
Nanfa matan gidan suka fara k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro🤣.
Oho innarsu Munu ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (🤦🏻‍♀gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da irin wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai).



******************

Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai yayi yashige bayi.
Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci yay gaba dashi.
Munaya batasan ya dawoba, d'okin zuwa gida ya hanata barcin ranarma ita, sai yawan duba lokaci takeyi😂👍🏻.


*_3:35pm_* Galadima ya tashi, saboda kiran wayarsa da akayi, idonsa a lumahe ya d'aga, a haka suka gaisa da Momma, ya tambayi Abie tace barci yakeyi, sunyi wayar kusan mintuna 15 haryaso makara fita sallar la'asar.
Bayan yadawoma papi ya kira suka tattauna, sannan yakuma sabon shiri cikin Orange d'in yadi anmasa kwalliyar bak'i kad'an, yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshi yakeyi, saidai fusakar kam babu alamun yasan miye dariya.
A haka ya iso sashen Munaya, babu kowa daga ita sai yaranta da Khaleel dake barci a gefensu, itako wayama take latsawa, da alama game takeyi Kodai wani Abu.
Sallamarsa ciki-ciki da k'amshin turarensa ya sakata d'ago ido suka kalli juna, yawani Basar yana shan k'amshi, hakanne yasaka Munaya sake kama kanta, ta gaisheshi, sau d'aya ya amsa ya zauna a bakin gadon yana shafa kan yaran d'ai-d'ai harda Khaleel.
Handbag d'inta da mayafi dake ajiye alamar lokaci take jira kawai ya kalla, baki ya ta6e ya d'auke kai.
Key d'in mota guda biyu ya fiddo a aljihu ya jefa min akan cinya.
Ni harma Na tsorata na kalli keys d'in sannan Na d'ago na kallesa.
d'auke Kansa yay daga inda nake, cike da k'asaitarnan tasa yace, bak'in kibama Abba, d'ayan kuma ki ajiye a wajenki, motar tana can, saboda ko wani abu yataso musamman kai yara asibiti sai wani ya kaiki cikin yayyenki, ki kulamin da yara, kuskure d'aya kikayi a kansu zand'au mataki mai tsaurine, duk abinda zuciyarki batayi na'am dashiba ki gaggauta kirana na sani, ki kula da Abdurraheem sosai, banda barinsa yana dogon kuka saboda doctor ya sanar mana yana d'auke da ciwon......”.
Saikuma yay shiru yana furzar da iskar bakinsa.
Masifar tsura masa ido nayi zuciyata Na bugu tamkar zata fad'o dan tsoro, sai tsuma nakeyi, babu shiri na taso na dawo inda yake, durk'ushewa nayi gabansa tamkar mai neman gafara, “Yalla6ai ciwon mi? Please ka k'arasa fad'an dan ALLAH”.
lumshe idanunsa yayi yana cizar lips, “Ba abin tada hankali baneba ai, domin ALLAH daya d'ora mana yafimu sanin hikimar hakan, bagashi ni nakai lokacin da Magauta basuyi tunaniba”.
Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”.
Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya kuka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani hakan, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.
Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi.
Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.
Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.
Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.
Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......”
Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.
Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.
Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.
Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.


**************

Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.
Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.
Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.
Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.
Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.
“Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.
“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.
Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.
Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.
Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.
Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.

Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba🤣.
Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.

Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.
Samha da khaleel harda kukansu.


**************


Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama.
Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............✍🏻











*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*


[7/25, 9:07 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻7⃣➖8⃣


..................Momma tayi farin cikin dawowar yaranta da jikoki, hakama Abie, wanda su Galadima sukai matuk'ar rikicewa da murnar ganin cigaban jikinsa, babu wanda baiyi hawayen farin cikiba, nanfa su Samha suka shiga nunama Momma da Abie hotunan yara da Munaya, Abie dake murmushi ya kalli Galadima da shima yake zaune ya hard'e hannaye a k'irji yana kallonsu da Murmushin, da ido Abie yamasa magana ya matso gareshi.
Galadima ya tashi daga inda yake ya matsa kusada gadon, Aunty Mimi tabashi kujera ya zauna, hannunsa ya saka cikin na Abie yana d'an matsa masa, ada komi zakayi awani sashe Na jikinsa bayajin komai, koda zakaita dukansane bazaijiba, amma wannan hannun da aka samu canji da k'afarsa d'aya yanzu ko Yaya aka ta6asu saiyaji, yanda Galadima yake matsa masa hannun a hankali sai yakeji tamkar tausa, yad'an lumshe idonsa cikin jin dad'i yace, “ALLAH yay muku albarka gaba d'aya Muh'd Sameer, Na taya kaina farin cikin samun jikoki a tsatsona biyu, nakuma tayaka murna da samun y'ay'a a karo Na farko, bazan 6oye makaba ina k'aunar matarka, ina jinta a jikina tamkar kud'innan, tun randa Na fara ganinta ALLAH ya samin k'aunarta amatsayin d'iya, ina fatan ALLAH ya cigaba da saka albarka a cikin aurenku, ALLAH ya d'orar dashi har mutuwa”.
Babu abinda zuciyar Galadima take sai lugude, auren dake gab da tsinkewa akema wannan doguwar addu'ar? Shikam yaga ta Kans.......
Girgiza hannunsa Abie yay ganin ya fad'a duniyar tunani, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin yak'e da fad'in Amin akan la66a.
Sun jima a haka Abie nata masa hira, kunsan dai halin mutumin naku, saidai yayta zuba murmushi, inda ya dace ya bada amsa kuma ya bayar, sun dad'e a asibitin kafin su koma gida, amma su aunty Mimi sun riga Galadima tafiya, danshi saida yaje Asibitin su namasu ciyon zuciya yaga likitansa, saboda a tsakaninnan dauriya kawai yakeyi, amma bayajin dad'in jikinsa. Duk wani abinda ya kamata Doctor Subash yamasa, Yakuma k'ara masa da Shawarwari.

Lokacin daya iso gida har Samha ta gyara masa samansa da taimakon Sauban, ko ina yayi fes, dama suna sauka asibiti suka wuce, saboda d'okin son ganin jikin Abie.
Ya fara zame kayansa idonsa bisa Sofa, ya lumshe ido yana cizar lips d'insa, bai kuma kallon sofar ba ya shige bayi, acanma dai bata sauya zaniba, dukkan abinda Munaya ta ajiye Na amfaninta irin Na mata idonsa Na wajen, haka dai yay wankan ya fito yana goge fuskarsa, sallar zuhur yafara gabatarwa sannan yadawo bakin gado ya zauna, wayarsa ya had'a, ya maida dukkan layikansa Na k'asar aciki.
Knocking k'ofa da akayine ya sakashi kallon k'ofar, batare daya tankaba ya d'auke kai, aka kuma knocking, gutun tsaki yayi kafin yabada izinin shigowa.
Samha ce d'auke da babban tire, kallo d'aya tamasa ta d'auke kai saboda ganin yanda ya d'aure. itadai ta ajiye ta lalla6a ta fice abinta. Yaja wasu adadin mintuna kafin ya mik'e zuwa wajen abincin, bubbud'ewa kawai yayi, yad'an ta6e baki yana rufewa, sai yama fice daga d'akin gaba d'aya zuwa d'akinsa na sirri.
Komai yana nan yanda yabar kayansa, sai y'ar k'urar daba'a rasaba, amma dukda haka saiyaji yana k'yank'yamin d'akin, fita yay ya sauka k'asa, babu kowa a falon, da alama kowannensu gajiya ta kadashi, tsayawa yay yana tunanin wama zai tado? idonsa ya tsaya d'akin Sauban, can ya nufa, Sauban na kwance a gado yana danna lap-top Galadima ya Shiga da sallama ciki-ciki, tashi yay zaune da sauri, “Yaya Sam lafiya dai?”.
“Shi wancan d'akin laifin mi yamuku dabaku gyarashi ba?”.
Sauban ya marairaice kalar tausayi “ALLAH yaa Sam bayana ciwo, duk mun gajine”.
Hararsa yayi, yana masa nuni da k'ofa, ya juya yay ficewarsa.
Sauban yad'an tura baki yana sakkowa a gadon kamar zaiyi kuka, cik'in k'unk'uni yace, “shi Yaa Sam d'inna yanda yake aiki kamar wani ingi baya gajiya ya d'auka kowama haka yake”.

Sanda ya fito har Galadima ya koma sama, shima hawan yay yanata kunkuninsa, a falo ya iskeshi zaune ya zubama wata kujera ido, baiyi maganaba ya shige d'akin, saida ya Shiga sannan ya Sanya dariya, dan ya kula kujerar da Munaya ke yawan zamace Galadima yakema kallon har hanji😂.
Tsaf ya gyara ko'ina sannan ya fito, yanzu kam a kwance ya iskesa ido a lumshe, yace, “yaya Everything is done”.
Hannu kawai ya d'aga masa, Sauban ya wuce abinsa, saida ya sauka ya juya ya kalli benen yana fad'i “Chiii yaa Sam He is too stubborn wlhy”.
Aunty Mimi dake bayansa bai saniba tai dariya, “kadage ya jika dai, kasan ko kurar wasa saita fika gata agidannan”.
Juyowa Sauban yay ya kalli aunty Mimi yana dariya shima, “Aunty babba ai lamarin boss ne sai addu'a” ya matso kusa da ita yana rage murya alamar gulma, “kinsan mineme kuwa?”.
Kanta ta girgiza masa.
Yacigaba da fad'in “Wlhy Ku taimakemu Ku amso masa matarsa da wuri, dan yafara rikid'ewa zai koma asalin Muhammad Sameer d'insa saboda kewarta”.
Idanu Aunty Mimi ta zaro waje, cikin sakin baki da tafa hannaye tace, “Sauban! Yaushe ka fara sanya masa ido?”.
Showing 9001 words to 12000 words out of 115198 words