Katsemin tunani yayi da fad'in “Manma nizam shafa?”. A hankali yayi maganar, kuma fuska babu walwala.
Ni mamakima yabani, amma to da banzo ba waye yake shafa masa?, bance komaiba na zauna kusa dashi ina zuba man atafin hannuna da mutsukashi, kunya tasa narasa dama ina zan fara?.
Lura da hakan dayayi saiya mik'amin hannu kawai, banida za6in daya wuce cika umarninsa, anutse na shafa masa man dan banida yanda zanyi.
Kaya na d'auka masa marasa nauyi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi ya saka, nidai kauda idona nayi gefe harya gama.
Natashi na had'a masa tea d'in da ruwan kayan k'amshinan, yana zaune akan sofa ya zubamin ido saikace wata television, dana mik'a masa mug d'in saiya had'a harda hannuna ya rik'e, da ido namasa alamar da zafifa cikin marairaicewa.
Shima saiya min nasa salon da ido alamar da gaske.
Nakuma narke fuska tamkar zanyi kuka, zame mug d'in yayi yana wani miskilin murmushi.
Ya d'ora cup d'in akan bakinsa yana kallon yanda take tatta6a tafin hannunta, a ransa yace hajiyar tsiwa kenan, andawo koya kuma zamu kwashe?.
Tea d'in yamasa dad'i, Dan saiya tuna masa da inno, itace kan masa wannan had'in inhar yana mura, yanasha yana kallona a k'asan ido, saika rantse kuma ba kallon nawa yakeba, amma ni inaji a jikina.
Knocking k'ofar da akaine ya sashi kallon cctv, ganin Muftahu da Dr jalal sai ya juyo ya kalleni da alamar tuhuma. Uffan bance da shiba, na mik'e da nufin fita na bud'e musu saiya dakatar dani ta hanyar d'agamin hannu.
Komawa nayi na zauna, shikuma ya mik'e rik'e da mug d'in ya fita.
Ajiyar zuciya nad'an sauke ina binsa da kallo.

Saida ya zauna cikin kujera sannan yabama su Muftahu izinin ahigowa.
Duk suka zauna suna masa sannu, ya amsa musu cikin d'aga kai da basu hannu sukayi musabaha.
Magunguna Dr jalal ya bashi na mura. Sannan ya buk'aci yimasa allura, amma saiya nuna bayaso.
Cikin dafe kai yace, “bar Allurarnan Jalal, bara nasha maganin kawai”.
Murmushi Dr jalal yayi, Dan yasan dama Galadima bayason allura. Basu wani dad'eba sukai masa sallama suka fita.
Fitarsu dana gani yasani fitowa falon, kallonsa nayi ina zama, shima idonsa a kaina, da hannu ya nunamin ledojin da Muftahu ya ajiye.
Bance komaiba na bud'e, d'aukar d'aya nayi na fita, na kaima laraba dakema su Abdurraheem shirin barci.
Cikin tsokana tacemin “kodai murufe d'akinmu kawai”.
Dariya nayi na fita ina fad'in “kai iya yanzufa zan dawo”.
Inajiyo dariyarta daga falo. Nidai nashiga kitchen na d'auki plate da spoon na koma wajensa.
Farfesun kifi na zuba masa, dan zaifi masa sauk'in ci, da farko ma cayay bazaiciba, saida naita rok'onsa harda kwalla sannan ya amince nabashi da kaina, yad'anci babu laifi, nabashi drugs d'in da Dr jalal yabashi”.
Koda yagama sha saiya jingina jikinsa da kujerar yay shiru, yad'anji dad'in jikinsa kam ba laifi, falon saiya d'auki shiru, muna a hakane kiran Momma ya shigo wayarsa.
Yabud'e idanu yana d'aukar wayar, yay picking, gaisawa sukayi, bansan mitace da shiba daga can najidai ya amsa da “Insha ALLAH goben muna hanya”. A hankali yake maganar saboda kansa, bama su dad'eba ya yanke wayar ya mik'e, hannu ya mik'omin alamar na kama.
Banyi musuba na saka hannuna cikin nashi ya mik'ar dani, bedroom d'in muka koma, ya zaunar dani bakin gadon sannan ya cire kayan jikinsa, ya hau gadon ya kwanta.
Nidai k'in kallonsa nayi, saida ya kwanta sannan ya kirayi sunana a hankali can k'asan mak'oshi, kallonsa nayi.
Yace, “Please mammatsamin jikina kozai rage ciwon da yakemin”.
Tausayi yabani, dan haka banyi musuba na hau gadon sosai nafara masa tausa a nutse, idonsa ya lumshe yanamai jin dad'in tausar, ahankali drugs d'in dayasha yafara cin k'arfinsa, barci mai nauyi yay a won gaba dashi, saida na tabbatar barcin yayi nisa sannan naja bargon na kuma lullu6a masa har saman kafad'a, nai masa addu'a na mik'e Na lalla6a na fita a d'akin bayan na kashe masa fitila.

Koda na koma d'aki laraba har tayi barci, nima shirin kwanciyar nayi kawai na kwanta, cikeda kewar y'an uwana da jiya iyanzu duk muna a tare😔.


********************

Iyayen Su Munaya maza sunyi farin ciki da labarin da Abba yabasu akan dangin inna, dan suna tausayinsu sosai, innaro ta tarasu duka tasa aka kira mata inna, harda hawayenta tana Neman gafararta bisa ga abinda tamata tsawon shekaru.
“Kiyafemin Ai'sha, dan lallai son zuciya ya rufe idona ruf, banason ara6i y'ay'ana koni saboda abin duniya, nata k'ask'antar dake agaban wad'anda duk kin rigasu zuwa gidan, wlhy wani lokacin su mero ne suke zugani, dan ALLAH kiyi hak'uri, nasan dai da wuya ki yafemin ma.....”.
Da Sauri inna tace, “Wlhy na yafe miki nikam, dama ban ta6a rik'eki a raina ba, dan matsayin uwa mahaifiya nake kallonki, inhar bazan iya musawa mahaifiyata magana ba ko jin zafinta to lallai kema baki cancanci na musa mikiba, ni dukanku ma na yafe muku wlhy, ALLAH ya kare gaba, yakuma yafe mana baki d'aya”.
Su Abba duk suna amsa da amin, kowanne yanajin dad'i har cikin ransa, lallai idan kaga halin girma to daga tsatson d'an masu girma ya fito, duk cin kashin da innro tama innarsu Munaya hakan baisa ta gagara yafe mataba, ya rabbi kabamu k'yak'yk'yawar zuciya gaba d'aya.
Masu samun fawar cin zarafin inna a wajen innaro duk sai suka nutsu suma, dan yanzu kam babu dama.
Haka su inna sukaita rabon tsaraba akaita rabo, har gidajen iyayen su Maman safara'u duk saida aka kai, kafin kacemi labarin tushen inna yabaje anguwa, mutane sai mamaki da al'ajabin hikimar ubangiji sukeyi, lallai Maman biyu tazamema matan gidansu RAINA KAMA, su sunata hura hanci y'ay'an wasune, da mata gorin rashin dangi Ashe gaba da gabanta, aifa matan anguwa suka dinga shigowa mata murna da sannu da zuwa.

Matan gidansu Munaya bak'inciki tamkar zai karsu, saidai babu damar koda yin tari, saidai kukan zuci da bak'incikin hassada mai cinye farin cikin Bawa.


******************


Washe gari Galadima yatashi dad'an dama-dama, dan babu zazza6in sai ciwon kai, shima bamai tsananiba irin na jiyaba.
Da safen yake sanarmin nayi shiri wai zamu koma, mamaki ya kamani, wannan wace irin tafiyace haka babu shiri, bayanma naji yanata kukan rashin kud'i a tsakaninnan, saidai banida damar Musawa, dan inason zuwa naga jikin Abie nima.

Da yake tafiyar saida yamma, tashin hantsi muka shiga cikin gida gaida mutane, fada Ce kawai bamujeba, sai yaran aka kai can, kowa yana yaba k'yawu da girman da yaran suka k'ara, gimbiya zulfa dai bata yarda mun gantaba, wai batada lafiya tana kwance.
Bamuce komaiba muka fito, mun iske Galadima yana fada, dan haka muka cigaba da shirye-shiye, sai a waya na kikkira mutane mukayi bankwana, naso had'uwa da Aunty Salamah dan inason ta warwaremin wasu tambayoyi, to amma hakan bata samuba, ko gidansu baba mai k'anwa ban lek'aba, kuma wlhy naso hakan matuk'a, to amma ga ayanda tafiyar tazo babu shiri.

K'arfe 2:00 mukabar masarautar gagara badau zuwa masarautar su papi, tarba akai mana ta mutunci, ina mamakin yanda suke matuk'ar k'aunar Galadima, Sauban tamkar zaiyi rawa dan dad'i, ammafa yayi 6ul-6ul dashi alamar yanashan gata, dukda lokacinmu k'urarrene munsha fira, inno tsohuwar mutunci, yanda take jana ajiki abin ba'a magana.
Galadima ma tunda suka gaisa da papi da mutane saiya shige cikin d'akin inno ya kwanta, dan bayason yawan hayaniya, saida akayi magrib muka baro masarautar cikeda d'unbin alkairin wad'annan bayin ALLAH, alkairi sosai Galadima yay ma laraba, harda hawayenta nima haka, dan munyi sabo sosai, bansan miyasa Galadima baice mutafi har itaba, kokuwa matsalar kud'ice oho, lallai na yarda sabo Turken wawa, shi akema kuka ba mutuwaba. Nuren ya d'auke mu.
Mun biya gidan Mom, itama dai haka tasha hidima damu, saidai akwai yarinyarta ta biyu nakula tun a wancan zuwan bata yina, dan ko gaisheni bama yi takeba, tata yatsine-yatsine kenan, a wancan zuwan abin yad'an dameni, amma yau ko a jikina, dan abinda na lura dashi son Galadima takeyi, dan haka na watsar da lamarinta ko kallo bata isheniba, babu mai takani na zauna, babu ruwana da arzik'inka ko ahalinka, ka mutuntani nima na mutuntaka saimu zauna lafiya.
Wanda takeyi donshi d'inma ko kallo bata isheshiba, dan baya sakar musu fuska, duk shakkarsa sukeyi har babban wan nasu gaba d'aya, dan ko sauban ya girmeshi balle Galadima.
Bamu bar gidanba saida time d'in tashin jirginmu ya matso, dan tacan zamu wuce, dukansu gidan sukai mana rakkiya har airport, har saida sukaga tashin jirginmu.


**************

Abin ya had'emin da yawa kam, ga yara ga babansu daba lafiya, sauk'inama basuda yawan rigima, Abdurraheem ne dai idan yaji ya takura babu zaman lafiya, Alhmdllh ALLAH dai ya taimakemu mun Isa lafiya, Khumar da Samha, aunty Mimi sukazo tararmu, bama tamu sukeba ta yaran sukeyi, ganin haka Galadima yaja hannuna muka shige mota, saida suka gama murnarsu sannan suka shigo, aunty Mimi na fad'in, “Oh shine kuka shige mota?”.
Galadima yabata amsa da cewa, “Tunda batamu akeba mizamu zaunayi”.
Dariya ta sanya da fad'in “yau naga kishi, to kuma dai sannunku badan halinkuba”.
Murmushi nayi ina gaisheta, Samha ta mak'alk'aleni.
Haka dai muka k'arasa gida.
Momma da jakadiya duk suna a harabar gidan da sauran hadimai mazan da mata. Kowa burinsa yaga yaran. Momma dai Nita rungume tanamin oyoyo. Kunya dukta kamani, ina k'aunar wannan baiwa har cikin raina wlhy.
Galadima kam jingina yay da mota kawai yana kallonsu cikeda jin dad'in yanda kowa ke farin cikin dawowar iyalansa.
Saida muka shiga ciki sannan Momma kecewa “Ina uban gayyar wai?”.
Galadima dake shigowa a k'arshe yace, “gani a anan, naga batani akeba Momma shiyyasa naja gefe”.
Duk dariya mukayi, yayinda bayin sukai k'asa da kai duk suna k'umshe tasu, dan babu damar yi.

An shiga gaishe-gaishe damana sannu da zuwa, hadiman gidan duk suka fice aka barmu mu kad'ai.
Momma duk tana rungume da jikokinta wad'anda suke rikid'ewa ruwa biyu, kamannin Galadima da Munaya, Khaleel ma yabi ya mamuk'e mata.

Galadima ya mik'e ya haye sama, danya d'an watsa ruwa, gashima magrib tagabato anan.
Momma harda hawayenta najin dad'i da farin ciki.

Tofa lamari ya canja salo, a wannan karon dai maimakon Momma tace nabi mijina saitace na shiga d'akinta nayi wanka na huta, aunty Mimi kuma ta kwashi yaran da taimakon Samha zata musu wanka.
Nikam hakan yamun dad'i, dan dama banason zama d'aki d'aya dashi. A d'akin Momma nai wanka na canja kayana, ina shirin kwanciya Samha ta shigo kirana wainazo naci abinci.

Galadima yay ta zuba idon shigiwar Munaya amma saiyaji bulum. Da farko bai kawo komai a ransaba yashiga toilet danya watsa ruwa, jikinsa babu k'arfi har lokacin, dayake d'akin tsaf yake an gyara ko ina fes yanata k'amshi.
Mamaki yakuma kamashi daya fito har sannan babu Munaya babu dalilinta, ko mai bai shafaba ya zura jallabiya ya sakko, Momma na zaune a falo, harya gama sakkowa idonta na kansa, duk sai ya rame mata a ido, ga hancinsa yay jajir alamar mura tamasa ligif, tissue d'in hannunsa ya ajiye sannan ya zauna.
Momma tace, “Sannu Muh'd dukka rame, mura na wahalmin da kai wlhy”.
Murmushi yad'anyi yana shafa sajensa. Yace, “My Sweet Momma to yaza'ayi, yanzu hakama kaina ciwo yake, ya muka sameku?”.
“Lafiya lau, sai kewarku, ya kuka baro manasu da autana?”.
“kowa lafiya, Autanki nacan nama inno ta6ara, bakiga yanda yay k'iba ba ma”.
Momma tayi dariya tanacewa, “Ja'iri, da yanata zum6ure-zum6ure bazaijeba, bagashi haryaci wata kusan uku ba, kwana nawa zai gama”.
“Dama ai shagwa6ace Momma”.
Momma tayi murmuahi tana maida kallonta ga jakadiya dake maganar ga abinci.
Sannu Tamata, ta kalli Galadima daya jingina da kujera ya lumshe ido.
“Muh'd tashi ga abinci ko, kasamu ka kwanta ka huta”.
Idonsa ya bud'e yana mik'ewa, saiga Samha da aunty Mimi sun fito suma. momma tace, Samha ta kira Munaya tazo taci abinci.
Galadima yanaji amma baice uffanba, saima maida hankalinsa yayi ga abincin da Aunty Mimi ke zuba masa.

Ya faracin abincin Samha da Munaya suka fito, kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa zuciyarsa na mamakin miya kaita d'akin Momma?.
Duk Momma na kula dashi.
Itama Munayar kallonsa tad'anyi ta d'auke kai.

Haka akaci abincin duk hirar dasu Momma sukeyi da Munaya Galadima baice uffanba, cin abincin sa kawai yakeyi, baima wani ci da yawaba ya matsa gefe alamar ya k'oshi.
Aunty Mimi tace, “my K'ani Yaya dai?”.
Yad'an yamutse fuska da fad'in “Alhmdllh ya isheni”.
“Ai kai dama tsiyar murarka kenan wlhy Sameer, ta jigataka ta hanaka cin abinci, ALLAH ya kara sauk'i”.
Cikin lumshe ido ya amsa da amin a saman la66a.
Muma duk sannu mukai masa, ya d'aga mana kai kawai.
Koda muka had'a ido saiya zubamin wata harar gargad'i, murmushi nayi na kauda kaina gefe tamkar ban ganiba.....................✍🏻







*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻




[8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣6⃣


.................Momma dai ta kasa ta tsare ta hanani hawa sama, idan abu Galadima ke buk'ata saitace Samha ta kai masa, tsakanina dashi saiya sakko gaidasu ko zaije massalaci, ya kumak'i nuna hakan ya damesa, sosai mamaki ya kamani, dan kwanakinmu hud'u kenan da dawowa, da farko na d'auka kawai shariyar tasa ta k'asaitace ta motsa, amma zuwa yau dayake shirin zuwa Kashmir sai abin yafara bani tsoro, dan ina zaune bakin gadon Momma ina shayar da Abdurraheem ya shigo, Momma ta fita kitchen.
'Dago ido nayi ina amsa masa sallamar da yayi, amma saiya d'auke kai tamkarma bai ganniba, ya k'araso kusa dani ya rissina ya d'auki Amaturrahman dake kwance tana motse-motse.
Duk'owar dayay saitasa k'amshin turarensa bugomin a hanci sosai, na lumshe idanuna sannan na bud'e akansa, magana yake ma Amaturrahman ahankali cikeda k'asaitarnan tasa, saikace wata babba.
Da kamar nima zan shareshi, saidai na daure nace, “Ina kwana”.
“Lafiya”. Ya amsa batareda ya kalli inda nakeba.
Hakan yamin ciwo a rai, na dangwarar da Abdurraheem d'in akan gado batareda ya k'oshiba, aiko saiya saka kuka, banbi takansaba na shige bathroom abuna.

Da kallo Galadima ya bita cikeda takaici harta shige, ya cije lips nashi tamkar zai huda da hak'ori, idanunnan harsun kad'a da 6acin rai. Yana k'ok'arin tashi ya d'aukeshi Momma ta shigo d'auke da k'aramin Kofi ma Magani daza'a basu. K'arasowa tai dad'an hanzari tana fad'in “shikuma wannan mi akai masa?”. Ita bama ta lura da Galadima ba, amma taji k'amshin turarensa.
Kwafar da yayi yasaka Momma juyowa ta kallesa bayan ta d'auki Abdurraheem d'in. “Wai dama kana d'akin amma yake kuka? Ina Munayar ne?”.
Baice komaiba sai bayi ya nuna mata da hannu, hakan yasata fahimtar ransa a 6ace yake, ta zauna tana shafa bayan yaron, yayinda shikuma ya daina kukan.

A kausashe Galadima yace, “Momma idan bazata iyaba na nemo masu kulamarmin da yara, dan bazan d'auki wannan wulak'ancinba, ta k'auracemin na k'yaleta tayi duk yanda ta gadama, shine yanzu kuma abin akan yarana zai dawo, nifa wlhy......”
Dakatar dashi Momma tai ta hanyar d'aga masa hannu, “ya Isa haka Muh'd, Munaya dai matarkace, kuma lafiyar ALLAH kuka dawo k'asarnan, aganina tun washe garin dawowarku kaga batazo inda kakeba yakamata ka tambayeta miye dalili? Amma ka share tamkarma hakan bai damekaba, shin mulki haukane Muh'd? Indai kace zakaima mace izza da
Showing 78001 words to 81000 words out of 115198 words