kika canja wannan matsalar tawa ta k'yak'yk'yawar siga, cikin hikimarki da ilimin da ALLAH yabaki, da kasancewarki mai tarbiya, Dan kowanne tsuntsu da gaske kukan gidansu yakeyi, nasha gwadaki akan abubuwa daban-daban amma kina cinye wannan gwajin nawa saboda zuciyarki a tsarkake take, please ina rok'onki a karon farko ki yafemin, kiyi hak'uri kiyi hak'uri kiyi hak'uri, nimai laifine amma mai nadama, tabbas zanji ciwon wani ya k'ulla alak'ar aure da Samha ma ba Amaturrahman ba ta sigar dana k'ulla dake, amma wlhy inhar kince naje gabansu Abba na sanar dasu komai zanje, nidai karki bari aurenmu ya girgiza koda da igiya d'ayane, namiki alk'awarin samuna fiyema da yanda kike tsammani matata”.
Idanu Munaya ta d'ago tana kallonsa, ya jinjina mata kai da lumshe idanu alamar tabbatarwa.
Batace komaiba ta maida kanta k'asa.
Hanunta ya saka anashi yana matsawa, a marairaice yace, “Kokinason Muhammad Sameer yamiki kukane Munaya? Sannan ki yarda nayi nadama? Wlhy nayi nadama da gaske”.
Jikinsa kawai ta fad'a takuma sanya masa wani kukan, shima ya rungumeta yana sakin wasu mugayen ajiyar zuciya, jiyake kamarma ya had'iyeta gaba d'aya ya huta, suzama abu guda d'aya kawai.
Momma dake bayansu tashiga tafi tana takowa cikin d'akin. Da sauri Munaya tabar jikinsa tana 6oye fuska, shikansa Galadima yaji kunya, yay k'asa da ido tana murmushi.
Momma ta zauna tana fad'in “Alhmdllh ya Ubangijin talikai na gode maka, ALLAH ka d'orar da wannan zama har'a aljanna”.
A saman la66a Galadima ya amsa da amin. Munaya dai kunya ta hanata kallon kowa.
Momma tace, “Nima yau zan sanar muku abinda baku saniba”.
Daga Galadima har Munaya kallonta duk sukayi.
Ta gyara zamanta tana murmushi. Tace, “Tun farkon Aurenku nasan komai”.
Da mamaki duk suka kalli juna sannan suka maida kallonsu ga Momma.
Murmusawa takumayi, “Lokacin da Muh'd ya yarda zai auri Munaya amatsayin auren contract Muftahu ya sameni ya sanarmin komai, danshi burinsa Muh'd ya Auri Munaya ne aure na gaskiya tamkar kowa, a lokacin kuma yasan cewar Gimbiya Zulfa itace ta saka aka muku wannan 6atancin, domin 6atama Muh'd suna, abinda yasa Munaya ta shiga matsalar ranar da kuka had'u a filin idine, shikuma Erfan dayazo miki da suna Fu'ad an sakashi sakama Muh'd idone, saikuma ya ganku tare, duk zatonsa akwai alak'a a tsakaninku shiyyasa yayta bibiyar lamarinki harya kaiku plaza, saidai kuma ya rikice yagaza banbanceku lokacin daya fahimci sewar Ku y'an biyune, shi Muftahu a lokacin bazai iya tunkarar Muh'd da ainahin gaskiyar abinda ya saniba gameda Gimbiya Zulfa da Harun, shiyyasa yayta cusamasa ak'idar aurenki a zuciyarsa, Dan aganinsa hakan zai girgiza zuciyarsu gimbiya zulfa, maybe su aikata abinda Muh'd zai iya farga dasu, ammashi sai rashin yardarsa ta tsiya ta hanashi aminta dake kanki. Gudun karta kwa6e agaba yasaka Muftahu zuwa ya sanarmin komai, yakuma fad'amin nagartarki data ahalinki, ya tabbatar min sai kowa yayi alfahari dake acikin masarautarnan, dansu suna ganin idan Muh'd ya auri y'ar talaka zai k'ask'anta bazaiyi sarauta ba, sun manta ALLAH shine mai komai da kowa. Muh'd yanada tausayi sosai Na tabbata inhar wani Abu ya shiga tsakaninku bazai ta6a sakinki ba, wannan dalilin ya sakani bama Muftahu pills ya saka muku, Dan ta wannan hanyar ne kawai zaku iya zama Abu guda”.
Munaya da Galadima duk suka kalli Momma da mamaki, saikuma sukayi k'asa da kai saboda kunya.
Murmushi Momma tayi. Tace, “Yes nice nabashi danna kafeku a waje d'aya, nakuma san Munaya zata iya bore akan ka saketa, shiyyasa a washe garin faruwar abin nasaka ka tilas ku taho nan, wannan shine mataki na biyu, mataki na uku saka Munaya tak'i kwantar maka dakai dannasan halinka da bak'in rashin yarda Muh'd, wannan na kula itakuma bata d'aukar saita kwana, shiyyasa abin yamin dai-dai, nadad'e da fahimtar son dakake mata, amma na shareka harsai ka gano dakanka ka fad'a mata. Cikin Munaya shine babbar ribar danaci, wadda nakema ALLAH godiya akowace dak'ik'a ta rayuwata, nake kuma jin k'aunarta har cikin jinina, badan na rabaku na rik'e Munaya ba, nayine dama danna tabbatar da nadamarka, itama ta kuma tabbatar da lallai da gaske kana k'aunarta, ta daina kokwanto a ranta, ALLAH yayi muku albarka, ya k'ara baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yabama Sauban mace tagari shima irin Munaya, itama Haneefa yabata miji nagari kamar mijinta daya bar duniya koma Wanda ya fishi, jikata Samha itama ALLAH yabata miji nagari Wanda zai rik'e mana ita”.
Atare muka amsa da amin.
Galadima zaiyi magana Momma tace, “kaga d'auka matarka ku tafi dare yayi, da safe ma k'arasa, nikam barci nakeji”.
Kunya ta kama Galadima da Munaya, amma Momma saitayi tamkar batasan sunaiba.
Tamkar munafukai haka suka mik'e sum-sum suka fice a d'akin, yanda basuyi yink'urin d'aukar yaro ko d'ayaba haka Momma bata tuna musuba itama🤣👍🏻...................✍🏻


*_Masoyan Raina kama amin afuwa dajina shiru, wlhy abubuwane sukaimin yawa, amma Alhmdllh yanzu nafara daidaita, kuma zanyi k'ok'arin gamawa nan kusa da izinin ALLAH, ina muku barka da salla baki d'aya, inakuma jiran naman layya😅🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀._*


_wad'anda suka tura hoto kuma Na yafe muku wlhy har zuciyata, wancan write up nayisane lokacin raina a matuk'ar 6ace, yanzu kuma Na huce😅, nayi HAK'URI bisa koyarwar manzon ALLAH, Maman Haneefa ngd kema sosai ALLAH yabar zuminci, yakuma yafe mana baki d'aya, dama raina ya 6acine saboda bansan iya inda hotunan zasu kaiba, idan wani ya gani da k'yak'yk'yawar zuciya wani zai iya munanani ta mummunar hanyar dabanjiba ban ganiba, duk mace tagari bazataso pictures nata suke yawo a social media ba, musamman ma mai aure, kobaka da aure mace darajane da ita, saikuma mutunta kanka ALLAH zai kareka, masu ganin Abu kuna yad'awa jikinku Na rawa kubari wlhy, kokad'an hakan bashida k'yau, Dan kuma bazakuso hakanba, ALLAH ya k'ara mana hak'uri baki d'aya._👏🏻😘😘






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
______________________

Gaisuwa da fatan alkairi.😘👌🏻

*_Takwara Billy Badaru, Maman Haneefa, Jameesha, my Hussy, my Dee.., Maman sayeed, Maman Sa'eed, Rahila Abba, Umman Murtala, lalai, Melerh zbi, Rally garba, Nana yakaku, Aysha Umar Abubakar, Aysha Galadima, Aunty Fareeda (ta group d'in Rano) Ameerah Ibraheem, xeecul, Bilkisu Ogun, Maman Mu'allim, zaujatu takwara Hussain 80k, Dan Mom._*

Masha ALLAH akwaiku da yawafa my sweet sister's and brothers😅😘😘👍🏻
______________________

*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣7⃣


....................Koda muka fito daga d'akin momma tamkar kwai ya fashemin a ciki haka nake tafiya, yana gaba ina binsa a baya, yayinda yafara taka steps d'in saiya juyo yad'an kalleni, k'asa nayi da kaina, yayi wani miskilin murmushi mai cike da ma'anoni, oho bansan yanaiba.
A step d'in k'arshe ya tsaya yana nunamin hanya wai Na wuce, ra6awa nayi ta gefensa na shige, yanzu kam ina a gaba yana bina a baya buka shiga bedroom d'in, yana nan yanda Na sanshi cikin k'amshi da tsafta, Na zauna a saman sofa ina sauke numfashi.
Tsaye yay kawai yana kallona, nikuma nakasa d'aga nawa idon Na kallesa, saima naji Na takura kallon dayakemin d'in. Kusan mintuna biyu sannan ya zauna a teble d'in dake gaban sofa d'in, ya kamo hannayena danake wasa da gefen siririn gyalen kaina. Cikin wata tattausar muryarsa mai cikeda nutsuwa da tarin k'asaita yace, “My Mata”.
Kasa d'ago idanu nayi Na kallesa, saida Na amsa a sanyaye.
Yad'an murmusa tareda saka hannunsa a ha6ata ya d'ago face d'ina. Kallo d'aya namasa Na risinar da idanuna, murmushi yayi mai sauti, yakuma sanyaya murya tamkar mai rad'a yana fad'in “Kin huce?”.
Kamar bazance komaiba dai saina d'aga masa kai siraren hawaye na ziraromin a kumatu.
Baice komaiba sai zubamin ido da yayi kusan seconds 30, ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya yana saka hannayensa biyu ya tallafe fuskata a cikin tafin hannun, ya gogemin hawayen da babban d'anyatsansa guda biyu.
“A d'an kalleni mana my Queen, a kuma min murmushi ko kad'an na tabbabatar an huce d'in”. Yay maganar yana Raba idanu akan fuskarta.
Yanda ya marairaice sai bansan lokacin da murmuahin ya kufceminba ma.
Shima murmusawa yayi da d'an jan hancina, “Haba kokefa my heartbeat”.
Hannu na saka na kare fuskata saboda naji kunya.
Yawani lumshe idanu da sakin murmushin gefen baki, tareda maida kallonsa ga k'aramin agogon dake bisa dirowan gefen gadon. Time yaja Sosa, kallonsa ya maida ga Munaya data kasa kallonsa. “tashi kiyi shirin barci mu kwanta, ga dare na Neman rabawa”.
Kallonsa nad'an sata ina janye idona. Nace, “To yaranfa?”.
Bai amsaminba saida ya mik'e tsaye, “karki wani damu kanki, tunda kikaga Momma bata bamuba aikinsan ranar ta musamman Ce yau”.
Ban sake maganaba danjin ya kamo wata tashar, na mik'e tsaye zuwa wardrobe na d'auka kayan barci.
Duk abinda take idonsa a kanta, yana zaune a bakin gado yana binta da kallo.
Ina juyowa muka had'a ido, nai azamar janye nawa, shikuma ya jehomin tambaya.
“Wad'annan kayanfa?”.
Kallon kayan nayi sannan Na kallesa da mamakin tambayar tasa, idonsa a kaina Dan haka Na janye nawa.
Nace, “Zan sakane”.
Baicemin k'alaba, sai mik'ewa da yay ya tako gareni cikeda izza da k'asaita, saina samu kaina da fad'uwar gaba, jinake tamkar nama zura da gudu. Kayan ya kar6a yana matsowa jikina, nad'anja baya amma saiya taro k'uguna da hannunsa yana kallon fuskata, cikin magana rad'a-rad'a daf da fuskata yace, “basu nake buk'atar ki sakaba yau, ke kad'anki nakeson gani babu wani shamaki a tsakaninmu”.
Da mamaki na kallesa saiya d'agamin gira, nai azamar janye idona ina marairaice fuska. “ALLAH nidai bazan iyaba yalla6ai”.
Kuma rank'wafowa yay kaina yana fad'in “Zaki iya my Queen, inhar da gaske kina son farin cikin mijinki, ni haka nake buk'atar ganin matata aduk lokacin kwanciya barci, ni kad'aina na isheki riga da bargo OK?”.
Yanda ya k'are maganar saida tsigar jikina ta tashi, babu shiri na d'aga masa kai alamar amsawa, dan inhar nabari muka cigaba da kasancewa a haka wlhy za'a iya samun matsala.
Harna fara tafiya ya rik'o hannuna, cak na tsaya batareda na juyoba. Yace, “nazo na tayaki wankan?”.
Ai babu shiri na juyo ina kallonsa cikin waro idanu, saiya kashemin ido d'aya yana cizon lips. Zare hannuna nayi nai gaba da hanzari, saida naga na rufe k'ofar bayin na jingina sannan na sauke ajiyar zuciya, lallai naga takaina da Galadima, dama haka yake? Sumi-sumi dashi, idan ka gansa saika d'auka bazai iya ko kallon macenba, amma humm.

Shima tana shigewa ya murmusa yana shafa sajensa zuwa gemu, takawa yay zuwa gaban gadon ya zauna, zuciyarsa na kuma tsunduma a k'aunar matarsa da ayyukanta, waya ya d'auka yana danne-danne, kusan wasu mintuna sannan ya mik'e yana ajiye wayar, kayan jikinsa ya cire, dagashi sai boxer ya haye gadon tareda jan bargo ya lullu6e jikinsa yana kwanciya, luf yayi tamkar mai barci.

Sosai na nutsu na gyara kowane lungu da sak'o na jikina, nasha turarrurukansa dake bathroom d'in, kunyar fita nakeyi da towel wlhy, Dan haka naja rigar wankansa na saka, ahankali na bud'e k'ofar, saida na fara lek'a kaina na hangoshi kwance akan gado da alama ma yayi barci. Ajiyar zuciya na sauke kafin na ida fita cikin sand'a.
Duk abinda takeyi Galadima na kallonta, ya had'iye dariyar dake taso masa da k'yar yana kuma yin luf.
Cikin tafiyar sand'ar tazo har gaban madubi, bai motsaba harta gama shafe-shafen turarenta da lips gloss, ta tako a hankali gaban gadon zata d'auke wayarsa data kusa fad'owa k'asa, wadda ya ajiye dama matsayin tarko, yasan inhar tagani bazata wuce ta bartaba saitayi yunk'urin d'aukewa.
Caraf kuwa ya damk'e hannunta, gabanane ya fad'i, ina k'ok'arin ja da baya ya kamo igiyar rigar wankan danaima d'aurin zarge, aikam lokaci d'aya ta warware, nai saurin rik'ewa Dan karta bud'e, amma ina saiya jawo igiyar ya fisgoni na fad'o jikinsa, bargon ya d'aga ya turani ciki yana murmushi mai sauti.
Ya zare wayarsa dake cikin hannuna yana fad'in, “Dukfa wayon amarya.....”
Shiru nayi nakasa magana danni tsoronsa ma kuma mamayeni yakeyi, ban ankaraba naji yana zare bathrobo d'in.
Cikin marairaicewa nace, “please yalla6ai kayi hak'uri kabarni da rigarnan akwai sanyi fa......”
Yatsansa d'aya ya d'ora saman la66ana, yaymin alamar nayi shiru, banida za6in daya wuce bin umarninsa.
Yace, “Nifa ba komai zanyiba, bashina da akaci za'a biyani, sanyi kuma nine bargonki ai”.
“Ni yaushe naci bashinka?”. Nai maganar a raunane”.
“Uhyim, in maye yaci ya manta ai maid'a baya mantawa, kedai kawai ki mik'a wuya, wahalar da aka bani yau duk saina fanshe kayana”.
Maganar danayi yunk'urinyi bansami lasisin kammalata ba ai, sai a cikin b.....🤭


(😝ba ruwana nayi nan⛹🏻‍♀).



********************

Yaudai kam Na tabbatar nashiga hannun manya, babu ga6ata da bata ciwo, nayi ligif saboda jikagata, baiyi k'aryaba kam, ya fanshe haushinsa harda gyara, da asubahi saida taimakon ruwan zafi nasami k'arfin jikina, Dan saida nagasa jikin, ga6o6ina suka d'an mik'e, bai fita masallaci ba, shiya jamu jam'i.
Sosai barci ya d'inga cin idanuna, muna idar da sallar Na zame a wajen Na kwanta, baice dani komaiba, saima Qur'an daya d'auka yafara karatu cikeda nutsuwa da kwarewa, tun ina saurarensa sama-sama har barci mai nauyi yay a won gaba dani.

Bai dad'e yana karatunba ya ajiye Qur'an d'in, Dan shima barcinne taf idonsa, kallon Munaya dake k'udundune cikin hijjaf yayi, yad'an murmusa yana shafa fuskarta, shikansa yasan jiya ya wahal da ita, amma soyayyartace duk ta jawo hakan, ya duk'a yana sumbatar goshinta da kumatunta, mik'ewa yay ya cire jallabiyar jikinsa sannan ya dawo inda take, itama cikin dabara ya cire mata hijjab d'in sannan ya d'auketa cak zuwa gadon.
Tad'an bud'e ido ta kallesa ta maida ta lumshe. Murmushi yay da sake sumbatar la66anta sanan yaja musu bargo, ya rungume yalla6iyarsa suka sake komawa duniyar barci.😘👌🏻



★★★★★


Tun Momma Na zuba idon sakkowarsu har abin yafara bata mamaki, gasu Abdurrahman sun farka tun d'azun, sai faman banka musu ruwan zam-zam mai had'eda Zuma take dasunyi kuka, da alama yunwa sukeji, amma takula iyayen nasuma sun manta dasu.
Aunty Mimi dai nata k'umshe dariya, har sukayi breakfast babu su munaya babu labarinsu, yaranma sun kuma komawa barcin dole.

Barcin yaran baiyi wani nisaba suka kuma farkawa da kuka, Dan yunwa ta hanasu barcinma.
Momma tace Samha tahau saman taga idan sun tashi.
Da to ta amsa tana hawa saman. Amma saita iske ko ina tsitt, babu alamar motsin mutum. Dawowa tayi ta sanarma Momma basu tashiba, ga Abdurraheem harwata shid'ewa yake saboda kuka, shi dama baida jimirin yunwa, sauran y'an uwansa sunfiahi hak'iri, ga matsalar ciwonsa da ba'aso ya yawaita kuka.
Babu shiri Momma ta jawo waya, zata kira Munaya saita tuna ai wayartama Na d'akinta, Dan haka ta maida akalar kiran ga Galadima.

Cikin barci yaji wayarsa Na ring, da k'yar ya iya mik'a hannu ya d'auka yana guntun tsaki, shi baima San a Yaya yay picking call d'inba, yadai saka a kunne kawai cikin yanayin barci yace, “waye?”.
Mamaki ya kama Momma, wato bama su tashiba?. Tace, “Kabarmin yarinyata tazo ta shayar da yara kaji malam”.
Babu shiri ya watsakke, saidai kafin yace wani Abu wayar ta yanke, kansa ya dafe danjin Momma Ce Ashe, ya kalli Munaya dake barcinta har yanzu, harga ALLAH tana buk'atar hutu, baison tashinta, saiyaji inama yabari yaran sunashan madara tun farko, aikam yanzu dolene ya nemota, Dan can zasu dinga kwana wajen Momma.

🤣yanzu kuma.


Aunty Mimi tace, “Momma kibata kawai takaisu, Dan wad'annan sakkowarsu aikice kam yau, yarannan kuma yinwa sukeji, ai maganinsa ma, bashine ya hana abasu madara ba, ai da yanzu sai a basu susha su k'oshi”.
Momma tai kwafa tana fad'in, “Ai dolensa ya nemota yanzu, Dan bazan iya wannan shelarba kullum nikam, indai yaran nada abinda zasuci sukam su shekara basu fitoba ina ruwan wani, yunwama ta ishesu”.
Aunty Mimi dai da jakadiya dariya suketa sha.
Samha ta d'auki Abdurraheem ta
Showing 84001 words to 87000 words out of 115198 words