ya tsaya sai taji kamar taje ta Rumgumeshi,har wani lumshe ido takeyi tana lasan baki tsawan daya kara daka musu ne ya fargar da ita,gabadayansu suka je,kowacce taje ta cika botiki daya,na mutanen dake wajen suna gamawa yace kowacce ta dauko akanta tazo nan,haka suka dauko suka zo,suna zuwa yace"Kowacce ta kalli yar"uwanta..,Bayan sun kallah yace"Kowacce ta juye Ruwan jikin nakusa da ita..."Kwalalo ido sukayi suna binsa da kallo,tsawa ya daka musu yana fadin"in na kirga uku bakuyi Abunda nace ba,zan sauya ra"ayi daga wanka Ruwa zuwa na kasa kuma wlh zanyi Abunda nace.."Yafada kai tsaye,ah bai gama Rufe baki sukayi ma kansu wanka da Ruwa,kallonsu yayi yaga kowacce tayi tsamo tsamo kamar wasu zakaru Dariya ta kamasa,ammh sai ya matse da kallo ya bisu kafin yace"Yauwa kun warware gajiya by now kowacce tasaka gwiwanta akasa ammh kuma ta juya ta kalli hanyar gidansu.."yafada yana mirmishin mugunta,Zubewa sukayi kowacce na kuka harda majina,domin ji suke tamkar gangar jikinsu bazai iya Daukansu ba.

Wucewa yayi yafara tafiya kafin yace"Kowacce tafara jan gwiwa har zuwa gidansu,wlh tallahi duk wacce tatashi na ganta ko na kamata,yau sai ta zagaye anguwan nan tana jan gwiwa,toh tun kuna son kanku da Arziki kuyi yadda nace,dis one na small one,duk Randa kuka karama matata Rashin kunya  zanyi Doubling din hukunci danayi muku yau,so be carefull.."Yafada yana wucewa kafin yace"1,2,3...Start..."Da hanzari kowacce ta fara suna jan gwiwa suna kuka wiwa,Inda Allah ya taimakesu duk yan wajajen nan,gidajensu babu nisa sosai,nan kowacce ta nufi gida da jan gwiwa tana kuka harda majina,Shiko Aliyu gida ya shige ko ajikinsa,shiko Sulaimam bai Tafi ba sai da akaci aka sude sai dariya yake Ransa fes anyi maganin marasa kunya.

  Sai ga inna Ramatu da kanta ta fito tana hada Kulin Alalan tanayi tanama Azeema Allah ya isa,sai ga Azeeza ta shigo da jan gwiwa tana kuka Fuskarta ta hade da majina da kuka,ga jikinta ajike da Ruwa da hanxari tayi Wurgi da ludayin hannunta tana fadin"Na shiga Tara ni Ramatu Azeeza gamo kikayi kokuwa karo kikayi keda mai akori kura,yayi miki wannan damejin da jiki..."Tafada tana karisawa gareta tana riko Azeeza,gocewa Azeeza tayi ta zauna dirshan Tana kuka gwiwanta duk sun sale saboda janta datayi akaasa,Kafafunta kuwa ciwo suke matw kuka take tana hadawa da ihu tana fadin"Wayyo inna wlh kafata zafi takemin kuguna,ya rike ban iya mikewa saboda azaba.."Tafada hawaye suna zubomata,Azeema dake lekensu ta window ta kece dadariya tana kama bakin ganin yadda Fuskar Azeeza ta dawo kamar wacce akayi wasan kura da ita,kallonta inna tayi tana fadin"ke wai tsaya Hatsari kikayi ne komiye..?"Azeeza na kuka tace"Wani hatsari inna,ba yaya captain bane saboda naje kiran Azeema tazo in jiki ba,sai ta dauko Ruwa tazo zata wuce shine santsi ya kwasheta tafada kwata,shine shine fa,yazo ya hadamu nida su lantana,yasakamu tsallon gwado bayan mungama yasa mukama junanmu wanka,duk hakan bai ishesa ba,sai da yasamu kowannenmu yaja gwiwansa zuwa gida..",Takarishe tana yaye zanin jikinta gwiwanta ya bayyana Duk ya sabe,baya inna Ramatu taja tana salallami take fadin""Kutmar ubanchan,yanzu Shi yayi muku hakan?gyada kai Azeeza tayi tana fyace majina,Haba Inna ta rike tana fadin"Lalle ya cika mara mutumci ai sai ki tashi ki gasa jikin ki,kiyi hakuri.."da mamaki Azeeza ke kallonta kafin tace"Inyi hakuri fa kikace inna,nazata zaki Ramamin kan Adda Azeema tunda akanta ne yayi mana haka.."baya inna taja tana fadin"Wa ni? Rufamin Asiri nima bai dade da fita daga gidan nan ba,yamin kashedi sosai kan Azeema yace duk Randa na saba umarninsa,sai ya saka ansace,na kwana afiriza mai maida jikin mutum kankara,kafin ya hadani da sojoji suyi wasan kura akaina,.."Tafada tana waigen kofa,zaro ido Azeeza tayi tana fadin"da gaske inna..."Gyada mata kai tayi tana fadin"Wlh kinga kuwa ko saceni yayi babanki bazai damu baTunda yafi son Wanchan sakaryan Akanmu.."Shuru Azeeza tayi batama inna mgana ba,Tunaninta yatafi kan Tunano Fuskar Abun kaunarta,Inna da hanzari taje ta hura wuta ta saka Ruwan zafi kafin tazo ta ciccibi Azeemar zuwa kofar dakinta inda ta Shimfida mata tabarma,Azeezar sai wash wash take saboda azaba ammh kuma ko Ranta batajin Haushin Captain ba,saima tsanar Azeema daya kara cika zuciyarta ta kudiri niyar ko ta halin kaka sai ta mallaki muradin Ranta.

Inna Ramatu ita tagasa Ma Azeza jiki tana gasata tana kukan zafi bayan tagama ta shafe mata jiki da Man zafi,hakama Sauran kawayenta,kowa yaji Captain ne,ko ya taso da zafi sai yakoma don ba"a ma Soja wargi,Ballema kowa yasan waye captain kaf,anguwan nan Ansan baya da wasa yaci kaniyarka bawani abu bane awajenka,Azeema ko cikin dakinsu tana kashin dariya domin Ranar tayau ta mata dadi,kota tafito Diban Ruwa tayi wanka daga Azeezar har Inna ba wanda ya Tankata haka ta shige bayi tana dariya,wani Farinciki na Fizganta bata san dalili ba,ammh ko Fuskar captain Tatuna sai taji wani Sanyi ya Shiga Ranta,ita kadai ta Furta. *YAYA CAPTAIN NAGODE*


_______________

Ranar da Aliyu ya taho Gombe Aranar Ni"ima ta dira akaduna,Taji matukar takaichi da Bakinciki lokacin da captain jabir ke fadamata Cewa Aliyu ya taho gida,kuma bayajin zai dawo cikin satin nan,sai sati na sama,Kuka wurjajan Ni"ima takema Jabir kan yabata nombar wayar da zata samu Aliyu,dariya jabir yayi mata yana fadin"Bayajin cewa Aliyu ya chanza layi buh Abu daya yasani cewa ya kulleki ne,da zata tafi yace"Shawara mai kyau karta kuskura taje gombe wajen Aliyu in ma zata dawo ne tabari ya dawo kaduna yayimata alqawarin fadamata,taji dadi sosai Kafin tatafi sai da sukayi exchanging din Phone number,Direbanta ne yakawota Domin karya tayima mami wai zata raka Muneera biki sai yammah zata dawo Shiyasa har ta dawo gida mami batasan ina taje ba.


   *************

  Bayan kwanaki da Faruwan Abun,Azeema tasamu sauki sosai ta bangaren inna da Azeezar ita kanta bamai Shiga harkanta,ko aiki bamai sakata,Ammh dayake Azeemar ta riga ta saba shiyasa bata iya zama,duk Abunda tasan aikinta ne tun safe zata tashi tayi Mganar aikenta kuwa ba"a kara yi ba tun Ranar da Captain yayi mgana in ka ganta waje toh Mkranta zata ko Allo,itako da Azeeza ko mgana bata mata,in tayimata ma bata karba mata shiyasa tafita harkanta,Dayake bata zuwa mkranta tana jinyan kanta saboda kugu ya rike😂,Shikanshi mallam lawal yayi mamakin ganin chanji agidan,bai dai yi mgana bane,sai yaji dadi Aransa yana fatan ya sa Ramatun ta gyara halinta ne,itako Inna Ramatu mganar saceta a kaita barikin shine ke dagamata hankali,shiyasa ko taso yin wani Abu takejin Jikinta yayi sanyi,toh tafaa sani tsab Aliyu zai iya don ba mutumci ne da shi ba.

Goggo batasan wainar da"ake toyaba ,don yanzu bata cika ganin Azeemar ba,saboda dawowar captain sai dai da safe in zata mkranta kan yatashi take shigowa su gaisa da goggon ta wuce agurguje,Shiko Captain haryanzu goggo batamai mganar data kirasa akai ba,Shikuma bai mata mgana ba,yana jiran yaji mezatacemai,Shima yana Tunanin Dauke  Azeemar  daga wanchan Rayuwa zuwa wata rayuwar mai inganci.


**************

Yanasanya mota kenan Cikin garejin yana Sauri yasamu jam"in sallar isha"i yaji maganganu daga kofar gida,koda ya fito dayake akwai wuta,kuma haske ya wadata kofar gidan,Kallonsu yayi suna tsaye Azeeza takalli Azeema tace"Gaskiya Adda Azeema kidaina sakamin ido,ina Ruwanki dani,wato ke kinyi Aure,kina bakin ciki ni kar na tsaya na nemi nawa mijin,da anyi mgana sai kice,Baba yahana,don Allah kibarni naji dadin rayuwata.."tafada tana saka hannu ta ture Azeema dake tsaye sai da ta fadi,tsautsayi yasata tafadi ta gefen hannunta sai da yayi kara,dan Ihu Azeema tayi tana dafe hannun saboda azaba,Hawaye na shatata bisa kuncinta

  Kallonsu yake cike da mamaki,kamar ya basar ya wuce,sai kuma ya tsaya yana kallon Azeezar harta kariso kusa dashi bata lura dashi ba,sai da taji ya dakamata tsawa yana fadim'"U Stupit,Come here.."Yana fada yana gyara tsayuwarsa,ba Azeeza da"aka dakama tsawa ba,hatta Azeema dake gefe saida ta razana,jikin Azeeza na rawa ta kariso tana kallonsa kafin tace"Gani.. YAYA CAPTAIN.."Ko kallonta baiyi ba,sai ya juya kan Azeema yana fadi cikin tsawa.."Au ke bazaki zo ba,jira kike na kiraki ko?i swear in kika bari nazo na sameki sai kin zagaye anguwanan kina tsallen kwado,wawiya kawai.."Yafada yana hararanta,ai Tun kafin ya rufe baki,ta kariso gabanshi jikinta na kyarma,hawaye na zubomata,Azeeza kuwa kuramai ido tayi tanajin wani dadi kamar ta rumgumeshi,hartana wani lumshe ido saboda yadda Shaukin ke Fuzgarta

Kallon Azeema yayi kafin yace"In kika bari hawayen ki ya zuba akasa,wlh sai kin duka kin lasheshi tas.."yafada ba alamar wasa atare dashi,Azeema da hanzari,ta hadiye kukan nata,tana share hawayenta,tsawa ya dakamusu yana fadin"Daga ina kuke Don ubanku yanzu dadddaren nan?.."Azeema bakinta na rawa tace",Da..daga Mkrantar Allo.."Sauke idonsa yayi kan Azeeza wacce tayi zurfin cikin Tunani,kuramata ido yayi yana ayyana girman Rashin kunyar yarinya,kara tamke fuska yayi kafin yace yana kallon Azeema"Waye ya girmi wani acikinku..? Da rinannun idanunta ta dago ta kalli Azeeza,wacce take wani mirmishi,Daka musu tsawa yayi yana fadin"Wai bada ku nake,mgana ba,ok so kuke yanzu jikinku yagayamuku inaga."Yafada yana kokarim zare belt,da hanzari Azeema tace"Nice,na girmeta..."Wani banzan kallo yayi mata kan yace"oh kece babba ammh kina zaune,yar kanwarki na miki Raini,harda tureki,kekuma dayake sakaryace mara wayau,har kina mata kuka ko"?yafada yana sakarmata ido
 

Jikinta na rawa kuka na neman kwacemata tafara ja baya,"Tsaki yaja yana fadin"bantaba ganin sokuwar yarinya irinki ba.."yafada yana maida hankalinsa kan Azeeza,Yaga yadda ta saki baki da hanci tana kallonshi nan da nan ranshi ya baci bai yi wata wata ya saka hannu ya shareta da mari lokaci daya ya sanya kafa yayi ball da ita,Azeeza dataji saukan mari abazata dakuma yadda ya hambareta tayi gefe tana fashewa da kuka"Nunata yayi da yatsa yana fadin"Shhiii..In kikayi Min kuka wlh Sai nayi miki bulala dari,don kaniyarki sa'arkice dazaki dinga dagamata murya,harkina dukanta, wato Abunda yafaru Ranar bai Tsorata ki ba ko?wlh na kara ganin kin mata rashin kunya,sai na saki cikin kankara kin kwana biyu,Try me an See.,Bacemin daga gani,tunkafin nafara kwallo,dake bush girl mai kama da monkey.."Da gudu Azeeza tamike ta shige gida tana kurukuruwan  ihu,kallonsa ya dawo kan Azeema dake gefe tana sharan hawaye,Wani kulilin takaichi ya tokareshi,yanzu wai wannan wawiyar itace matarshi,gaskiya goggo bata kyautamai ba

  Wucewa yayi yana fadin"Kema bita,kafin na chanza mind dina,inyi kasa kasa dake,kuma Nakara ganin kina mata kuka,sai na prison ya fiki jindadi,ko mganar banza ta fadamiki slap her,beat her,yadda zata kiyaye ki,kinji ko bakiji ba..

Da wani Rawan jiki dana baki tace"Na..naji...'" Better.."yace yana wucewa massllacin cikin sassarfa,da hanzari Azeema tafada gidan Goggo don tasan tana Shiga gidansu to tabbas sai Inna Ramatu Tarama ma Azeeza dukan da yaya Captain yayi mata,duk da yanzu tana shakkar yimata wani Abun saboda shi.



*Am Srry For d late update Na mantane ban hidi muku ba,Zaku dinga samu update din Ali gadanga duk bayan kwana daya ne,cuz am busy wlh Abubuwa sunman yawa Akwana dayan ma,karfin hali nakeyi..Masu comment da sharhi duk nagani kuma ngd sosai Am srry bansamu maida Reply ba,saboda wasu abubuwa dasuka shamin kai buh duk nagani kuma ina godiya Allah ya bar Zumunci Amin..*



    
      *#Comment share,and vote...#*
      *#Intelligent writer's asso...#*
      *#Janafty....#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


*NOT EDITED*💥

        *Chapter 11*

  """Goggo na cikin kichen taji Sallaman Azeema,da hanzari ta fito tana fadin"Ah Azeema,kice kamar daga sama da daddaren nan? Tafada tana kallonta,Sunkuyar dakai Azeema tayi tana kokarin dukawa ta gaida goggon saurin Rikota tayi tana fadin"A"a tashi kada muyi haka dake,bama wannan ba,miye naga kina wani zare ido,gabadaya kamar atsorace kike,gayamin badai wani lalatattace bane ya biyoki yanzu na fita naci ubanshi,kokuma na hadashi da gadanga wlh yaci uwarshi yanzu nan fadamin waye ya biyoki naga kin Shigo a Tsorace"Dan waro ido Azeema tayi kafin tace"Ba kowa bane fa inna Dama yaya captain ya daki Azeeza saboda tamin Rashin kunya,shine na shigo nan kada na koma gida inna ta huce akaina.."Galala Goggo ta kalleta kan tace"Ai yamin daidai wlh,kema dai Azeema wlh ki kamma jikinki,in dai kina wannan sokanci wlh bazaku Shirya da gadanga ba,shi mutum ne dabayason wargi balle shashanci yo in ma kinaso sace zuciyarsa ne,na baki satan amsa ki zama mace Tukunnah bayan kinkam jikin ki Atoh.."Tafada tana Riko hannunta,Baki Azeema takama tana yar dariya,Mangare mata kai goggo tayi tana fadin"Au dariya na baki ko?yo ai gaskiya ne,ammh wani lokacin in kina wani Abun sai ki dinga Tunamin da Mahaifiyarki Fatima,wlh Azeema yadda kike da hakuri da kawaichi to Fatima ta fiki.."Tafada cikin sanyi,nan da nan idon Azeema ya ciko da hawaye,dafa kanta goggo tayi tana fadin"Karki damu Azeema wlh Tamkar Aliyu haka nake kallonki da izinin lahi sai kin zama Abun alfahari,da kin Tuna da mahaifiyarki karkiyimata kuka kiyi mata addu"a da Fatan tana kyakyawan mtsayi kinji ko? dakai Azeema ta amsa tana share,kwallah hijabin jikinta goggo ta ciremata bayan ta amshi al"qur'anin tana fadin"Maza shiga shiga ciki ki dauro alwala kizo muyi sallah sai muci abinci yanzu na gamashi da zafinsa,ai ni nagodema ja"irin nan gadanga daya bugemin Mara kunyar yarinyarnan gashi sanadin haka yata tazo wajena,duk da yanzu wasan buya ake dani Tunda Megida yadawo.."Tafada tana kyabe baki,Tura baki Azeema tayi tana fadin"kai goggo ba ina zuwa ba,kuma ni yaushe nace haka.."Goggo tayi yar dariya tana fadin"Au hakane fa,to naji baki ce ba,maza shiga kiyo ki fito an kusa sallame salla daga masallaci.."Tafada tana Ficewa daga Falon,itako Azeema dan mirmishi tayi kafin tafada bedroom din na inna wanda in ka gansa ko na wata amarya albarka saboda yadda yasha wani ubansu royal bed mai kyau da tsari gashi yana malale da capet mai kyau da tsari,da makeken wardrope dinta sai madubinta dake shake da kayan shafa na mata,wanda goggo banda kwalli bata shafa komai,ammh kullum taramata Ali gadanga yake,Tunda kawu ya daukemata Nauyin komai.

Tare sukayi jam"i da goggo suna gamawa goggo ta zubomusu abinci Shinkafa da miya sai slat datayi musu goggo fa,ba baya ba,akwai iya girki sosai kamar ka tsinke hannu,nan suka zauna Dole tasa Azeema sakin jiki don goggo dai kun santa dole ma mutum ya saki jiki da ita,da farko Azeemar kin ci tayi,aiko goggo tayimata barazana da zata kira Aliyu yanzu yazo yayimata dure,kila taci jin haka yasa taba goggo hakuri ta hau cin abinci dama yunwa takeji sosai domin tun karin safe rabonta da Abinci,Ammh tanayi tana waige da sauraran waje kada Yaya captain yazo ya Ritsata.

  Itako Azeeza tana shiga gida da ihu Ta iske mallam lawal atsakar gida shida Inna Ramatu,jin ta shigo da ihu yasa Inna mikewa tana fadin"Ke lafiyanki kuwa keda wane.."gabansu Azeeza ta zube tana fadin"Inna wlh In baki dauki mataki kan Adda Azeema ba,ni zan dauka dakaina.."Tafada tana hawaye,wanda bana zafin marin da yaya captain yayimata bane,a"a takaichi yadda taga kamar yana tsausayin Azeemar ne,wanda ita ba burinta kenan ba,burinta kafin yafara son Azeemar ita ta riga ta mallake zuciyarsa Allah barshi ya dankarama Azeemar sakinta ta kara gaba.

Inna tace"Toh me tayi miki ne,nifa bangane ba? Kyabe Fuska Azeeza tayi tana fadin"Ba ba kawai mundawo daga Mkranta bane zamu bi ta kofar gidansu yaya captain Tunda Adda Azeema ta ganshi shikenan ta nufi wajensa,bansan metacemai ba,naga dai Tana ta nunoni,ban ankara ba yazo kusa dani kawai ya mareni,kuma ya saka kafa yayi Shuru dani.."Tafada tana kara barkewa da kuka kamar gaske
  

  Kutmar ubanchan.."Inna tafada Tana rike kugu kafin ta waiga tana fadin"Ammh dai kaji Abunda tsinanniyar yarka tayi ko? ammh naga kayi Shuru bakace komai ba"Ko kallonta baiyi ba yace"Nidai ban Tsinema yata ba,sai dai in ke kika Tsinema taki,mganar kuma da makaryaciyar yarki ta fada ba gaskiya bane,na tabbata Azeema bazata kulla miki sharri har Aliyu ya dakeki ba,sai dai in rashin kunya kikamai ya hukuntaki.."Yana gama fadar haka ya mike yana kakkabe rigarsa yake dakama Azeexa tsawa yana fadin"Tashi kiba mutane waje,matukar baki zama mutum ba,har abada ni dake bazamu Shirya ba.."Yafada yana Shigewa daki.

Da kallo inna ta bishi kan takoma ta zauna tana fadin"Eh na yarda tabbas Watarana Azeema zata kashemun aure,toh kan ta kashemun ni zan mata dukan mutuwa dasai ta gwammace kida da karatu,wlh tallahi sai dai duk Abunda zai Faru ya faru..",Tafada tana huci,ganin haka yaasa Azeeza tashiga zigata na taci uban Azeemar in tadawo itako inna huci kawai take kamar wata macen zakanya.

Shiko gadanga yana idar sallah yadawo gidan,yana shigowa yaji muryan goggo tana hira cikin hiran natane yaji ta ambaci Azeema jin haka yasa yayi burki zuwa dakinsa cuz bayasan ya mtsama yarinya Tunda ya lura tsoransa takeyi,bai cika cin abinci mai nauyi ba da daddare,shiyasa goggo bata damu da nemansa ba,balle ta kaimai Abinci,har wajen goma Azeema na gidan sai lokacin tace zata koma gida goggo tayi tayi ta tsaya ta kwana ammh taki dole ta kyaleta ammh aranta tana addu"ar Allah ya hadata da gadanga ya warfatota tadawo akwai illai tana Fitowa tsakar gida cikin sanda Ya hangota dama yaji karan bude kofa,Fitowa yayi yana kallonta tana tafiya ahankali Gyara tsayuwa yayi sai da takusa isa ga kofar gidan daya kulle Tun dazu kan yace"Ke...",yafada cikin sanyi,Cak ta tsaya jikinta na rawa jin muryansa kafin ta waigo Arazane kallonta yayi kafin yace"Ina zaki.."?Bakinta na rawa tace,"Gi...gida...Za..zani.."harara ya zabgamata kafin yace"dallah wuce kibama mutane wajen gidan wa zaki Da daddrenan.."Yafada yana kokarin komawa daki,kin tafiya tayi ganin haka yasa ya dakamata tsaawa yana fadin"Au zaki wuce ko sai nazo na tattaka ki anan wajen ne.."Jin haka yaasa tayi dakin goggo da gudu tana rawan jiki,gyada kai kawai yayi ya rufe kofa ya koma ciki,tana shigowa daki taga goggo na mata dariya tana fadin"Allah yamaka albarka gadanga..."Take fada tana ma Azeema dariya,Azeema tayi nakwa nakwa da Fuskar kamar zatayi kuka da sauri goggo ta rikota tana fadin"Yi hakuri kema Allah miki albarka Azeemata muje mu kwanta kinji.."Tajata zuwa kan makeken gadon nata ta kwantar da ita,tana shafa kanta tace"Toh kwanta kiji gobe da safen zan rakaki har gidan kinji ko? gyada mata kai Azeema tayi tana dan mirmishi Aranta tanajin son goggo na ratsata saboda yadda take kula da ita.

  Shiko mallam lawal koda dare ya tsala Azeema bata dawo ba,haka inna ramatu tazo kansa tanata jaraba wai Azeema bata dawo ba,tatafi gantali kuma wai nan matar aurece,hartana cewa bataga amfanin wannan Auren ba,shisshigi ba kwarjini,sai Tusa kai suke ana gwasalesu,shidai yana jinta kanzil baicemata ba,saboda yana da tabbacin Azeema na gidan goggo kuma yasan darene yayi Suwaibar tahanata dawowa,juyamata baya yayi dole datagaji ta
Showing 21001 words to 24000 words out of 88299 words