kuwa? anya ni na haifeki matukar nine ubanki bazaki aikata Abunda kika dade kina aikatawa ba,saboda ko banza jinin Azeema na yawo anaki,wlh indai nine ubanki na gaskiya Nayi tir dake Azeeza haihuwarki bai ja zamin komai ba sai Danasani da nadama.."Yafada yana Fashewa da kuka Inna Ramatu itama dake kukan Fadi take"Haba mallam karkace hakamana,wlh Azeeza diyarkace ta halak kawai irin zuciyarta kenan.."mallam lawal yace"Ai banyi musu ba,ammh kuma banyi mamaki ba,sanin mugun nonon datasha wlh Ramatu duka mugayen halinki ne Azeeza ta dauko,Dama ance mgaji mafiyi,toh dake da ita dukkanku Allah ya isa ban yafemuku ba.."Yake Fada yana Share kwallah.

Azeema tana daga baya tana Sharban kuka,jabir yace"Baba kadaina kuka don Allah,kabar bata bakinka mu zamu tambayeta.."yafada yana wurgama Azeeza harara ko kafin ma yayi mgana Tuni Aliyu yayi tattaki ya isa gareta baiyi wata wata ba ya saka duka hannuwansa yashiga zabgamata Tafi Dama da hauni,duk marin dayayi mata sai ta hade da garu,Muneera dake gefe tace"Wlh kamata dukan mutuwa don agabanmu tace Tafi mahaifiyarka Sonka,so zata iya kashe kowa,bayan Azeema har goggo zata iya kashewa.."dafe kirji goggo tayi tana riko Muneera tace"Da gaske kike yan"nan.."Juyowa Muneera tayi idonta ya ciko da kwallah tace tana kallon goggo da Azeema wacce ke kuka Wurjajan tace"Da gaske ne goggo,don Allah kiyafemana,kinga watanan yarinya ko shedan na Tsoronta,ita.....nan Muneera ta kwashe komai Tafadama goggo takarishe da dukawa dukkansu ita da Ni"ima suna Fadin"gamu gabanku keda Azeema ku yankemana duk hukuncin daya dace damu,ammh wlh bazamu bar nan wajen ba sai mun tabbatar da an damka wannan Shegiyar yarinya ga hukuma"Baki goggo takama tana mamaki,balle Azeema wacce ke ganin jiri,wani ihu sukaji Azeeza ta yanke,suna waigawa suka ga Yadda gadanga ke kwallo da ita gabadaya jini ya wankemata Fuska,jabir ya rikeshi yana Fadin"'kyaleta Dude kada ka kasheta,barta hukuma ta hukuntata..",Huci yake yana wani Tiriri Inna Ramatu tana ta kuka ammh ba bakin mgana Shiko mallam lawal Fadi yake"Ka barshi yakasheta gwara naga gawarta dana ga gawar yar"uwata kuma Anunata amtsayin wacce ta kasheta..'Azeeza dake yashe akasa ta dago tana Kallon mutane dake wajen idonta digan jini yake,Mirmishi ta saki mai ciwo tana Share jinin dake zubomata ta hanci tace cikin Raunin murya.."Karku ga Laifina na,laifin zuciyata datake matukar Sonka yaya captain,eh..Eh..Da gaske nace zan kashe Adda Azeema ammh bawai don ta min wani abu ba.,A"a sai don ka Aureta kuma kana zaune da ita,kai ne Sila,kai ne Silan duK Abunda yafaru,wayace kafara Son Adda Azeema bayan gani,wayace ka Aureta bayan gani..Arm...Wlh bazan daina Sonka ba,har na Mutu,ko dukan mutuwa zakamin digon sonka bazai tabq Ragu araina ba..INa....Ina...So..SoN..."Bata karisa ba mallam lawal ya kifeta da mari yana saka kafa ya Shurata gefe yake Fadin"Tir dake Azeeza wlh nayi nadamar haihuwarki Allah dai ya Tsi......'A'a Baba.."Azeema ta Fada tana Rufemai baki,kafin ta Fada jikinsa tana kuka Riketa yayi yana kwallah yake Fadin",barni na Karisa Azeema yau ina zansaka kaina ace wai diyata ta cikina ke son mijin yar"uwanta harda ikirarin kasheki haba Azeema niko banayi Tir da haihuwar Azeeza ba.."Azeema kuka yaci karfinta tace"Baba kaddarace babu yarda zamuyi don Allah kabar jifanta da mummunan kalamai"Runtse ido yayi yana Tsiyayan hawaye,Jiniyar Yan sanda sukaji ta cika wajen ko kafin suyi wani yunkuri Tuni yan sanda akallah zasu kai su bakwai suka Shigo suna Shigowa suka kame gabadayansu kafin babban cikinsu ya Fito da Id card dinshi yana Fadin"Sunana *DSP MALEEK KABIR KUMO* my next novel ohh💃An turomu ne daga babbar headquater mu,munzo Tafiya damai laifi ne,sakamakon muke da alhakin Hukunta duk wani mai laifi dake wannan jahar.."

jabir da Aliyu suka bisu da wani kallo,da hanzari Ni"ima tace"Ni nayima Daddy waya nace ya Turo hukuma tatafi da ita,ammh kuyi hakuri in nayi kuma katsaladan..'ajiyar zuciya Aliyu ya sauke jabir ya Saki hannu yana fadin"ok go ahead dama,chan dole ku xamu damkawamawa,ku Tafi da ita Tanada laifuka da yawa babban ciki shine yunkurin kisan kai,"Gyada kai Dsp Maleek yayi kafin yace"Zamu Rubuta Statament dinta,kuje ku sakamata ankwa.."Yafada da kakkausan murya da hanzari wata mace tatafi ta dago Azeema kafin Namiji ya matsa yabata ankwa ta sakamata,saboda yadda ta daku bata iya Tsayuwama dakyau,sai dai yar sandan ta Shiga janta,Inna Ramatu ta rike kafan Azeeza tana fadiin"Ina zaku da ita,don Allah kiyu hakuri don Allah.."Take Fada tana kuka.

Ba wanda yama Saurareta haka aka yi ta jan,Azeeza itako ta kurama Aliyu ido tana kallonsa da bakinta yana zubar da jini,sai da yar sanda takara janta lokaci daya dakifamata mari,ta fice da ita Inna Ramatu ta bisu tana ihu,Musabaha su Aliyu sukayi da Dsp maleek kafin yafice sauran suka Mara mai baya,awaje anguwa tacika tayi makil da ita,hadda mata sun Fito bama idonsu abinci agaban idon kowa aka Fito da Azeeza ,wacce bakinta da hancinta ke zubar jini nan fa waje ya kaure da cecekuce,don ma da Sojoji shiyasa ba wanda ya matso kusa har aka saka Azeeza amota aka Wuce da ita,inna Ramatu na ihu tana bin motar tana kururuwa,kowa na fadin albarkacin bakinshi sanin halin Azeezar na Rashin da,"a wasu na zargi kila wani bala"in taje ta jawoma iyayanta.


Itako Azeema ana Fita da Azeeza taji kanta na juyawa tadago daga jikin mallam lawal karaf suka hada ido da Gadanga wanda yaketa kallonta ta cikin bakin gilashinshi,ganin yadda tayi Rama yake,ga wani Fari data kara,Kallonsa take kuka na zuwarmata kafin ta kauda kai,tafara Tafiya daniyyar tabar wajen kawai taji kanta na juyawa kafin ta kara wani motsi Tuni tajita luu,tatafi sai akan kirjin gadanga Tafada wanda ke lura da ita,yana ganin sadda ta dafe kai,idonta na Rufewa da wani hanzari ya isa gareta Tafada jikinsa idonta yarufe a Harzuke ya shiga jijjigata yana fadin"Azeema...Azeema.."ammh shuru goggo ma takariso tana Jijjgata hankalin Aliyu ya tashi ya kalli Jabir yana fadin",bring d car.."Yafada yana riko hannunta Ficewa Jabir yayi da Sauri Shiko mallam lawal Addu'a yake ta tofamata yana fadin"Dole ta suma taga Abunda bata taba gani ba...'






*Janafty*
[12/24, 22:26] +234 810 307 8468: *ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


        *Chapter 28*

     Aliyu da kanshi ya dauki Azeema da hannunsa ya sakata acikin mota goggo ta Shiga baya,jabir na Driving,su Muneera ma Motarsu, suka Shiga suka Mara musu baya,Mallam lawal Bai bisu ba,yadai bisu da addu"ar Fatan samun lafiya,general Hopital suka kaita,suna zuwa aka karbeta da gaggawa,likitan yana ganin yadda take yafara Sakamata drip tare da wasu Allurai,domin yace ba Suma tayi ba,jikinta ne babu karfi sam,Jininta aka diba First,aka tafi dashi lab,domin gwadawa,itakuma Dama Ruwan daya samata saboda yataimakamata wajen samun karfin jikinta.

  Gwajin Farko ya Tabbata da Samun ciki Azeema na Tsawon Sati Takwas koda Resuilt din ya Fito Gadanga aka Damkawa murna kamar bakinshi zai zage,Rumgume jabir yayi yana godiya ga Allah,goggo ko mirmishi take na Farinciki,domin dama Tuni Ta Fahimci ciki ne da Azeemar,itako Azeema batasan wainar Da ake toyaba,tana kwance duk jikinta ba karfi,bata dade ba ta Farka tana Fadin"Goggo Ruwa..." da hanzari Goggo ta bata Ruwa,kafin ta taimakamata tatashi Tana tashi idonta na kan Aliyu wanda yakafeta da ido,yana kallonta lokaci daya da mirmishi bisa Fuskarsa,kauda kai tayi tana amsa Sannun da Ni"ima da Munnera suke mata,amsa musu tayi da kai,tana Kara kallonsu,ita Ni"imar nema ke bata Tsausayi,jabir ne yayimata sannu takarba dakai,Aliyu dayake tsaye chan gefe sai ya matso kusa da ita yana fadin"pretty ya jikin?Kura masa ido tayi tana Tuna sanda yayi Shuri da ita,Runtse ido tayi hawaye na kwararomata,kauda kai tayi tana cije bakinta,ganin haka yasa goggo ta Girgiza kai ta saka kai Ta fice,Jabir ma yabi bayanta Ni"ima ce ta karisa gaban Gadon Azeema tace"Zamu Tafi Azeema,Allah ya baki lafiya.."

     "Gyada kai tayi kafin tace"ngd..."Dakyar cikin muryan ciwo,kallon Aliyu tayi kafin tace"Captain zamu Tafi,ina Fata dai An yafemana kuran damuka aikata.."Tafada idonta na cikowa da kwallah,Mirmishi yayi yana kallonta kafin yace"Bakomai Ni"ima buh next time Kada hakan takara Faruwa ko ba akaina ba,ku koyi yaki da zuciyarku don Allah..."

gyada kai tayi kafin ta Share kwallah Tana Fadin"Insha Allahu hakan bazata kara Faruwa ba.."Gyada mata kai yayi yana Fadin"Toh Yayi kyau naji dadin haka,share hawayenki kibar kuka hakanan,komai ya wuce.."Mirmishi tayi batayi mgana ba,sai ta waiga tana kallon Azeema wacce ta Runtse ido ammh kaf Abunda suke Fada akunnanta ne,Dafata tayi tana fadin"Congratulatino Sisto Allah ya inganta.."Daga haka tajuya,muneera dake tsaye itama tayi Fatan samun lafiya kafin su Fice,awaje sukayima su goggo sallama,suka Tafi suna jin zuciyarsu tayi sanyi Tunda komai ya Wuce yanzu.

   Suna Fita ya karisa gareta lokaci daya yana harde hannuwansa bisa kirjinsa kallonta yake dakyau yadda Fuskarta tayi Fayau tabashi Sha"awa,Sunanta yakira ahankali.."Pretty..." Tana jinsa tayi mishi banza harda dan nishinta alamar barci takeyi,yana kallonta yar dariya ta kamashi,sai ya saka hannu ya dan,matse hannun Da aka sanyamata Drip,taji zafi da hanzari tajaye hannunta tana Fadin"Wash.."tafada tana Jaye hannunta bata bude ido ba,ta mirgudamai baki,dariya ta kamashi sai ya Rankwafa yana lakucemata hanci yake Fadin"Matar Sunnah bata Fushi da mijinta,kuma in yayimata laifi yakamata ta Sausautamai,koyasamu damar bada hakuri..",tana jinsa tayi mishi banza,sai ma juyamai baya datayi,Kai ya dafe yana Saka hannu abaki,kafin ya Sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan ki Adanamin duka Fushinki pretty har na dawo,nayi alqawarin daukan kowani mataki kika Dauka akaina,ammh i want to u to know one Thing i relly miss u so much,and kinbiyani Tunda kikayi Saurin Cafkan sako na,Adaren Farkomu,Allah ya saukeki lafiya.."Yafada kafin ya duka ya bata kissa Ahannunta,ya saka kai Yafice yana mai jin Farinciki,Sai da ta tabbarta da yafita kana ta bude ido tana Dafe kirji tace"Ina da cikin yaya captain yanzu a wannan cikin? tafada Tana dafa cikinta lokaci daya tana Sakin mirmishin Farinciki,hawaye suna zubomata ta sanya hannu ta Share Tana fadin",Allah na godemaka..Ni nan da wata Tara nazama mama"Tafada kafin ta saka dariya ita kadai,shafa cikin take tana mirmishi ita kadai,kafin chan kuma ta Tura baki tana fadin"Ina Sonka,ammh ina Fushi da babanka,duk da kewarsa da Soyyyarsa bazata taba barina Fushina yayi Tasiri Akanshi,Alhamdulillah Allah nagodema.."take Fada tana mirmishi ita kadai.

Shiko Aliyu achan waje,har kasa ya dukama goggo kafin ma yayi mgana tayi Saurin dagoshi tana fadin"Tashi gadanga,Har Abada goggon gadanga bazata yi Fushi dakai ba,konayi baya zuwa ko"ina na yafema Tunranar da naje mkrantansu Azeema Shugaban mkrantar ke Fadamin kagama biyanmta komai,Tun wajen nace na yafema nayita sakamaka albarka,duk da dai Ja"irin ka batamin Rai ammh kadan.."Tafada tana mangaremai kai,dariya yayi kafin ya Fada jikinta ya Rumgumeta yana Fadin"Nayi kewarki goggo.."Kunnensa ta murda tana Fadin"Karya kayi dai kewar matarka ko? ammh bani ba.."Dagowa yayi yana kallonta Kafin ya Shagwabe yana Fadin"Ni Allah goggona nayi kewa.."Dariya tana fadin"Toh naji Nima nayi kewar gadanga ko Tsiyar damuke ankwana biyu ba"a hadu ba..",Dariya suka saka gabadaya kafin Gadanga yace"Goggo zamu koma bakin aiki.."Jinjina kai Goggo tayi kafin tace"Basai kamin bayani ba,yanzu Jabir yagamamin bayanin komai Kuje Allah ya Tsare yakuma bada Sa"a Azeema kuma zan kular maka da ita har kadawo nayi alqawari.."Da Ameen suka amsata mata kafin Suyi mata sallama Su Tafi,daganan Asibitin hanyar gombe suka dauka,dama tawagar da sukazo Tare Tun Sadda zasu kai Azeema Asibiti suka basu Umarnin juyawa gombe,toh Tuni sun damki hanya kilama Sun isa Tundazu.

  Koda goggo takoma wajen Azeema tayi barci lokaci,tatasata tayi tana ta zuba godiya Ga Allah,har saida Tafitar da kwallah,Allah sarki Gadanga,shifa Tunda yatashi baisan dadin wani Dan"uwa ba,sai Hisham,wanda kusan yanayin aikin banki da Tsanani da Takura gashi ba sakewa so basu cika haduwa ba,sai dai awaya,haduwarsa da Jabir yasa yasamu aboki sosai,gashi Allah ya ba matarsa Ciki tana Fatan cikin ya zamanto Silar Farincikin gadanga dasu gabadaya.

Kwanan Azeema daya aka sallamota ta dawo gida,bayan an kafamata dokan banda aiki mai yawa,ba daukan Abu mai nauyi,kuma anbata mgungunar Kara jini,dana saka cin abinci don goggo tace bataci,sai cika ciki da goriba,ba"a hanata cin kayan kwalamanta ba,ammh ance ta dinga cin Abinci sosai,tadai Samu ishasshen Hutu da Lokaci mai Tsawo,goggo ko duk taji bayanan likita Shiyasa suna komawa gida ta zage tayimata Tuwon Semo miyar Kubewa dayan,wacce aka daka kifi aciki,duk da bataci dayawa ba,ammh taci sosai,daddaren Mallam lawal ya Shigo duba Azeema yadade yana mata nasiha hakuri da rayuwa,tare da mata gargadin ta rike mijinta da Amana,nan yake Fadamusu Inna Ramatu tun jiya take kuka da Hajijiya tana Rokon don Allah asakomata Azeeza tatuba tabi Allah,yacema bayan Tafiyarsu saiga Baba Ade tazo,har yara Sun kaimata lbrin Abunda yafaru tazo da kukanta ni nayita bata baki,gyara zama goggo tayi tana fadin"Allah sarki ai tabar kuka,don ta kusa samun megida ko Amarya kai kuma Mallam ka Shiryafa jika na zuwa.."Washe baki yayi yana saka albarka yana kallon Azeema,itako Rufe Fuska tayi Duk kunya ya kamata,Mallam lawal yayi murna Sosai yayita Addu"ar Fatan Allah ya Raba lafiya.


__________________

_Kaduna_

  Yau kimanin kwana hudu kenan da zuwansu barikin baitaba yin nesa daga Sansaninsu ba,iyakarsa Dan haraban wajen,sai jiya kuma da Sukaje bayan bariki sukayi Atisayen Harbi,yau Tunda yatashi yakejin sha"awar zagaye barikin nan duka duk da baisan ko"ina ba yasan baya bata ba,cikin Kakinsu na chan ya Fito yafara Tafiya duk inda yabi yana Daukan Hoto ko video din wajen da Rantsatsiyar Wayarsa kirar Samsumg,Duk inda ya Shiga sai Binsa ake da kallo Abunda yabashi mamaki Wasu Sojojin jahar ta Nageria har kamemai Sukeyi Saboda Su bihakki da gaskiya Dauka Suke Captain Aliyu ne,duk da kuma da bambamcin Uniform din da Suka gani,Abun ya Daureshi mishi kai,sai yakoma daya Hadu dasu yaga sun Kamemai Sun Saramai,kawai sai ya Daukesu Selfe ya wuce yana dariya,suko suyi ta mamaki don Asaninsu Captain Aliyu baya dariya Sai dai mirmishi ko kaga yadan murmusa kumatu kadan.

Yana Tafe yabada baya yana Daukan wani lafiyayyan Titin daya Shararo,wajen ya burgeshi yadda kasan ba"a Nageria ba,kamar akasar Turai saboda Haduwansa gashi so quit,ga wasu Fulawoyi dasuka kawata wajen,sojojin dasuke wucewa kadan kadan ne,sakamakon Lokacin da Safe ne sosai ba'a Fito Training ba.

Jiyayi ya bangaji Mutum harsaida wayar dake hannun Wanda sukayi karo da Umar din,tafadi kasa da hanzari Umar ya sanya wayarsa a aljihu ya duka ya Tattaroma mutumin wayarsa wacce ta watse yana fadin"Am so Srry did know u are coming Srry...",Yafada yana dagowa karaf ko suka hada ido da Jabir wanda ke Tsaye yana karemai kallo sama da kasa kafin ya zaro ido yana Rike baki yace"Kambu Dude,basaja kakoma kuma,yau Abun naka harda komawa Sojan Niger.."Yafada yana Dariya galala Umar yayi rike da waya yana kallonsa bakinsa na motsi yace"ni..Ni..Bansan meka ke mgana akai ba fa? Kafadansa Jabir ya daka da karfi yana fadin"Kai Dude dawo hayyacinka kasan dai ni bazakamin layan zana bako?any why yau fa kasan akwai Atisayen gudu ina kuma zaka naganga ta nan? Umar ya lumshe ido kafin ya bude,baiyi mgana ya Rike hannun Jabir ya damkamsa wayarsa yana fadin"Ba wanda Kake Tunani bane,Ni Sunana Leuitenant Umar Abdulnaseer Tambari buzu ina daga cikin bakin Sojojin da suka sauka Shekaranjiya.."Kuramsa ido Jabir yayi kafin ya warci wayarsa yana Fadin'Kajimin dan iska,Umar kuma kakoma? Toh in bakai bane waye,Nikaga Tafiyata mallam,dama kai baka Rabo da Maida mutane yan iska..",Yana Fadin haka ya juya ya cigaba da Tafiya ko waigowa baiyi ba,Galala sake da baki Umar ke binsa da kallo kafin ya rike baki yana Gyada kai,mamaki yakamashi,ammh sai bai ba Mamakin matsungunni ba,juyawa yayi yakoma,ammh kuma Abunda yafaru ya tsayamai Aranshi.

  Jabir da hanzari yakoma barayinsu yana zuwa kofar Apartment din Aliyu ya ganshi ya Fito sanye da kayan gudu,cogewa yayi agabansa yana kallonsa Abun ya bashi mamaki,toh wannan Aljanine,yanzu fa ya ganshi Aliyu dake tsaye yaga yadda Jabir ke kallonsa Tsaki yaja yana Fadin"Kai fa dan iskane lafiya kawani kuramin ido,bafa wannan kwailar budurwantaka bace"Yafada yana hade rai,Hararansa Jabir yayi kafin yace"Durun uwar kwailar,Ai kwaila bata Wuce Azeema ba.."Dirowa Aliyu daga saman Apartment dinshi ya Naushi Jabir agefen ciki kafin yayi gefe yana fadin"Ai Azeema Ta wuce kwaila Tunda ta iya daukan Nauyi na,har gashi tana Dauke da ciikina,kuma wannan ne last time dazaka kara kiran Sunan matata gatseai ba sakayawa,Tunda ba sa"arka bace.."Jabir dake duke yana rike da gefen cikinshi ya dago yana Fadin"Allah ya isar min mugu kawai,don kaga kai ka fara kokarin ijiye kwanka aduniya Shine ni zakamin mugunta Rasa nawa,ta Allah bata mutum ba.."dariya Aliyu ya saka mai kayatarwa yana Fadin",Au kudai zauna yanzu nagama yima gayen nan Hisham,nace ya zauna aikin banki ya daskararmai da kwan haihuwa,ko kuwa zama waje daya da Wuni cikin Ac,ya Lusarar dashi,sai bayan anyi Aure aji mata ta gudu taga ba bayani"Dashi da Jabir din suka saka dariya atare harda Tafawa Jabir yace"Kai Dude kasan kan Tsiya fa"Yafada yana Fada kadafadansa kafin yace'Kai Dude Seroious Fa,kana aiki da Aljanune,yanzu fa naganka sanye da kakin Sojin Niger,yanzu kuma na ganka da kakin Sojan Nageria kuma banga sanda kadawo harka chanza kaya ba,wai kodai layan zana gareka.."Kallonsa Aliyu yayi yana Fadin"Tsiyana dakai kwakwalwarka bataja,Ni da yanzu Fitowata kenan,kuma banda Abunka meya hadani da Sojojin Niger da har zan sanya kakinsu,..? Rantsuwa Jabir ya jero yana Fadin"Wlh da gaske,wai bakai bane Harfa kacemin Sunanka Umar Abdulnaseer Tambari buzu fa? Har Aliyu ya juya Yafara Tafiya jin sunan da Jabir ya ambata sai dayaji yanayin jikinsa ya chanza,waigowa yayi yana fadin"Ni kuma? kai mallam kafara Rudu wlh,bani bane kaji na Rantse maka ma,yanzu dai duk ba wannan ba kashiryo kazo muje Atisayen gudu da za"a gudanar yau.."Yana gama Fadin haka yayi gaba da dan gudunsa.

Tsaye Jabir yayi yana mamakin wannan al"amarin Hannunsa bisa baki yana fadin"Bashi bane to waye? yafada yana kada hannu Alamar Abun yabashi mamaki,tsaki yaja kafin yace"Mtsewww shege shine fa,so yake yayi Wasa da Tunanina"Fadin haka yasa ya juya yashiga part dinshi da gudu domin Shiryawa domin Atisayen na yau na musamman ne,domin Duka Shuwagabannin kowani bangare zasu Koyar da Atisayen na yau,duk acikin salon Dabarun yakin daza"a koya musu ne, na Tsawon Sati daya duk da su sun dade da kwarewa game da Aikin,ammh dalinlin bakin Sojojin dakuma Turasun da gwannatin Nageria zatayi zuwa wajejen da yan boko haram suka mamaye.



*JANAFTY*😘
[12/24, 22:26] +234 810 307 8468: *ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

           

           *Chapter 29*

    ""Har aka gama Atisayen gudun
Showing 66001 words to 69000 words out of 88299 words