Sati Allah ya bayyanamin Fuskarki amafarkina Suwaiba ina ganinki na Tuna,bayan na Farka ina kiran sunanki,Sai matana da mahaifa suke ganin kmar nayi gamone,kwana biyu akwance ko Fada bana zuwa,ina zurfafama kaina Tunanin kozan iya Tuna awani gari muka zauna dake,ammh tabbasa na tuna kedin matatace,toh ina cikin wannan halin sai na samu kiran Da'na Yarima umar ya sanar dani Ragowar Abunda ya Shigemin Duhu,na ganin yaron da kika haifamin,bayan Tsananin kamaninsu kuma suna amfani da sunan mahaifi daya tare da sunan Masarauta,Aranar hadda Bala munyi mgana bayan ya tabbatarmin da kina raye,ni na hana agayamiki komai nafison nazo dakaina ki ganni na ganki bayan na baki lbrin duk Abunda yafaru Shekarun baya,Wannan itace mahaifiyata yafada yana nuna Ummah mai babban daki sai Matata ta fari Gimbiya Fasilatu ita ta haifarmin yaro namiji mai suna Umar gashinan,sai gimbiya Razeenah mahaifiyar su Zafira da Safaratu kenan,Bayansu bankara haihuwa ba,bani da wasu ya"ya bayansu,ina Fata da wannan bayanin zaki dubeni da idon Rahama Suwaiba ki yafemin barinki danayi na tsawon lokaci batare dana waiwayeki ba.._



Gabadaya wajen yayi tsit harda masu kwallah irinsu madina da mardiya da Ummah,Goggo kuwa kanta na bisa kafadan Kawu tana Fitar da kwallah,hatta Azeema sai ta koka,Maimartaba ma kukan yake ammh yana saka gefen Rawaninsa yana Sharewa ammh idonsa kur akan Suwaiba,Ummah mai babban daki ta mike ta isa ga Suwaiba ta dafa kadanta tana Fadin"Dago kanki Diyata...",Jiki asanyaye ta dago tana kallon Ummah mai babban daki wacce idonta ya cika da hawaye tana Fadin",wlh tallahi duk tsawon wannan Shekarun Abdulnaseer baiyishi cikin kwanciyar hankali ba,muma namu hankali ba"a kwance yake ba,kullum rokom Allah nake ya bayyana mai koma miye shi,gashi yau Allah ya amsa rokonmu kiyi hakuri kiyafamai nayi miki alkawarin bazai kara barin ki ba.."Tafada hawaye suna zuraromata Goggo da jikinta yayi sanyi ta dago tana kallon maimartaba wanda yake kallonta da tsausayawa kafin ta maida hankalinta kan Gadanga wanda ya hada hannayensa yana nuna mata alamar roko,Komawa da kallonta tayi kan su Madina taga suna gyada mata kai,balle kawu dayake ta murza kafadanta alamr lallashi,Kanta ta mayar kasa kafin ta share hawayenta tace"Shikenan...Na yafemai Duniya da lahira.."Ummah ta rumgumeta tana dariya Gabadaya wajen kowa ya sauke ajiyar zuciya harda maimartaba wanda yaketa maimaimata Alhamdulillah Aransa ashe afili yakeyi,gadanga ke kallonsa yana kunshe dariya.

Ummah mai babban daki ta dago Fuskar goggo tana fadin"Sai wata alfarma daya danike rokonki Suwaiba.?."Akunyace goggo tace"Mene ita..? Ummah na kallon Fuskar maimartaba tana Fadin"Ki Amince amaida aurenku da Abdulnaseer,In zamu koma Masarauta kibi mijinki ki koma tare dashi..."Gabadaya wajen aka Tsurama goggo ido,wacce kunya ta kamata kamar ta nutse,gimbiya Fasilatu kuwa kamar ta mutu saboda bakin ciki da kishi,Gimbiya Razeenah kuwa mikewa tayi ta isa ga goggo tana zauna tana riko hannunta take fadin"Kiyi hakuri karki ce A"a domin Maimartaba hankalinsa bazai taba kwanciya ba,balle har ya iya zaman Fada ba balle har ya gudanar da sha"anin mulki ba sai dake,don Allah ki amince amaida aurenku in zamu koma mutafi dake masarauta muzauna mu Rumgumi mijinmu don Allah..."Tafada tana kallon kwayan idon goggo,wacce saboda kunya kamar ta nutse,in tace bata son mijinta tayi karya,Shiko maimartaba idonsa na kan goggo gabansa na Faduwa kada Suwaiba tace"A'a..."


goggo ta dago kanta ta bude baki zata yi mgana kenan su gadanga dasu madina suka hada baki suka ce",Karki ce A"a goggo..."Suka Fada kamar zasu kuka,kawu yace"Toh kinji suma ya'yanki suna miki sha"awar komawa Rayuwar aure wacce zaki rabauta da ita har gobe kiyama.."Yafada cikin siyasa Ummah dake gefe ta dinga Kyaftama goggo ido😂wai ta yarda goggo na jin kunya ta dago tana kallon maimartaba wanda ya Langwabe kai,alamar ki yarda dani,Saurin kauda kai tayi tana Fadin"Na Amince..."Ai gabadaya wajen ya dau ihu,Ummah ko ta ware ta dafa hanci ta saki guda,suko Fadawa nan suka fara busa algaita suna Fadin"Angaisheki giwar sarki,Angaisheki Gimbiyar Sarki...Sarkinmu na godiya ga Amincewarki Allah yabar soyayyah..."Dariya akasa gabadaya Goggo ko kunya kamar ta nuste,shiko mai martaba dariya yake har hakoransa suka bayyana waje yana kara godema Allah,addu"a Gadanga yayi aka Rufe taro da addu"a kafin abude shashenshi su Maimartaba aka Saukesu anan,itako Ummah mai babban daki tana dakin goggo ita da jikokinta ana shan hira da dariya,Ita dasu jabir da Haisam suna Fadin suma fa dole su garzayo masarauta sunga iri😜😿Ummah mai babban daki tana Fadin ba wanda zata bamawa,Suko su Zafira suna makale da Azeema wanda suke tare dasu Anty madina,Ummah ko natare da goggo wacce gimbiya Razeenah ta Shige cikinsu ana hira,Shiko maimartaba yana shashen gadanga,suna hira shida Kawu da Mallam lawal wanda kawu yake bama maimartaba lbrin Abunda ya Faru bayan tafiyan shi da dalilin barowarsu zaria yazo ya saima goggo gida anan,Maimartaba ya jinjina al"amarin kuma nan take yace zasu zaria har anguwan da suka zauna,dagachan sai ya wuce Fadar maimartaba Sarkin Zazzau,Gimbiya Fasilatu kuwa tana dayan bedroom din Gadanga tana Fama da bakinciki,Bayi kuma mata,dakin dake tsaKar gida aka Saukesu Maza kuma akwai wani daki a shashen gadanga ammh yana da kofa ta waje shi aka bude musu,inna ramatu tanajin sadda goggo tace ta amince da Auren sarki ta sulale ta fita tana zufa kafin kace kwabo tabi anguwa ta yada lbrin mahaifin gadanga Ashe sarki ne,goggo kuma matar sarki zama amaida aurensu tabishi chan masarauta.

Shiko kawu ta waya yayi mgana da kwamishinar yada lbrai na jahar gombe yayi Narrating komai ya sanar dashi yace yana so,abuga lbrin akowacce jarida bayan afitar da sanarwa akowani kafafan yada lbrai,harta kaduna sai da yayi waya ya sanar kuma yace kafin gobe yake so lbrin ya karade duniya gabadaya Maimartaba yaji dadin haka sosai,saboda masu son Shegenta masa da,yau sun sani cewa Captain Aliyu ba Shege bane yanada cikakken Asali,kuma Asalin ma daya fi na kowa.


Anty madina da Anty mardiya da Azeema da su Zafira suka Fada kichen domin yin girki saboda yau dai Ahalin yayi albarka sai wanda ya gani.




_*Ina bukatar Addu"anku daga bakunanku masu albarka,ina cikin damuwa,tare da Fuskarta wata jarabawan Rayuwa,kumin Fatan Allah ya bani ikon cinye jarabawata,in kuma Alherina ne Allah ya Tabbatarmin dashi ya kauda duk wata Fitinar dazai Tunkari al"amarin*_🙏


    
*JANAFTY*
 *ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

    *Chapter 36*

  "Washegari Sojojin suka yima Dajin Sambisa tsinke,wannan karon harda manyansu atare, dasu bayan su Umar da Jabir da Sauran wasu jajiratattun Sojojin,Ta jirage ne wadanda ke da Na"irorin Daukan Hoto ta kasa,ma"aikatan dake cikin Helecopter din suna ganin duk wasu kananan Abubuwan dake cikin dajin,ta Na"urorinsu,cikin ikon Allah suka tarar da wani sansani na yan boko haram din acikin chan kuryan Daji,Umarnin yin kasa akabama Jiragen bayan kowani Soja ya saka rigar iska,sun Fara sulalo wa kasa,Mamaya suka yi musu ba Shiri kawai sai dai sukaji tashin harbi kokafin su Fito da Makamansu sunyi musu kwanya harbi kota ko"ina domin Sojojin suna dayawa Suma,nan Fa akaita bata kashi har na tsawon Mintina Talatim kafin sojojin su samu Nasarar kashe wasu ammh duk da haka akwai wadanda suka kara Nausawa dajin,suma acikin Sojojin an samu Wadanda suka Raunata,ammh ba!a samu rasuwar rai ba,nan da nan suka kafa sansani bayan an Fitar da masu Rauninka likitocin cikinsu na basu Taimakon gaggawa.

Cikin katon sansaninsu da Sojoji sukayi watsawatsa dashi aka gano Sauran Sojoji 8 daga cikin wadanda suka bace,suna daure dukkansu da kacha,duk sun rame sun lalace,dukkansu babu riga ajikinsu,ko"ina tabon bulalane da sara alamar dai Suna cikin wata rayuwa,cikin azama aka kwance su aka daukesu zuwa sansanin sojojin domin basu Taimakon gaggawa Major Sadeeq Amfani ne ke Fadin!where iz Captain Aliyu Naseer..'?yake Fada Ahankalinshi take,sai alokacin Sauran Sojojin suka Fahimci babu Aliyu aciki,nan fa hankalu suka Tashi nan da nan akace su Jabir su sake bazama cikin dajin domin sake dubawa kila a dace su ganshi.

Aikuwa hakane ta Faru basuyi nisa ba,suka iske wani sansanin ammh babu kowa aciki,koda suka Farma wajen sai suka tarar da wani mutum Daure daga saman hannayensa da kasa ma an Dauremai kafafu,Shibai kai tsakiya ba,shikuma bai sauko kasa ba,kansa na sunkuye ne jina na zuba ta hanci ta baki,bayan Kafarsa ta dama daure da wani kyalle,ammh haka jini ke zuba awajen,gashi ta kumbura,Tsaye sukayi cak suna bin Mutumin da kallo,Abu daya yasa su ka gane wannan nasu ne,wandon Sojan Nagerian dake jikinsa,wanda yachanza kala saboda jini,Jabir daje tsaye yayi kukan kura yana Fadin"Dude...."Yafada da duka muryansa bude,wanda harsaida Dajin ya amsa,hatta sauran Sojojin dake baya da suka ji suka Biyosu aguje dauke da makamai.

Umar najin haka ya karisa garesa suka rikosa baya Numfashi alamar ma Asume yake,wasu daga cikin Sojojin suka fara Zagaya wajen suna dube dube,wasu kuma suka isa wajen suna kokarin kwance Aliyu,awurin kwancensa ne suka Fahimci yana da karaya biyu Akafadansa ta
dama,bayan kafarsa ta dama ta Dauke da harbin bindiga,ammh an cire harsashinsa,sai kafarsa ta hagu itama tana Dauke da karaya,sai wasu kananun gocewar kashi,kuka reras Su Umar keyi na tsausayin Halin da Aliyu ke ciki,haka suka Daukosa ko"ina na jikinsa ya saki kamar gawa,suna Fito dashi manya sojojin suka karisa garesu da hanzari Jabir ne yake sanar dasu irin Rauninka dake jikinshi,nan da nan Major Sadeeq  Amfani yasa su Jabir da Sauran Sojojin su cikon 8 din da kuma wadanda suka jiggata su shiga jirgi tare da Likitocin cikinsu su koma chan Asbitin Federal Ta Abuja,domin basu Taimakon gaggawa,su in sungama tararra komai zasu zo daga baya.

Cikin kankani lokaci aka sakasu cikin jirgin suka lula sararin samaniya,tun acikin jirgin Likitocin sojojin ke bama Aliyu taimakom gaggawa,ammh har zuwa lokacin bai farfado ba,sun dai samu daman warware kafar data keda harbi sukayimata dressing kafin su isa Abuja,shiko Chaif Amry of Staff tun suna chan lbrin ya sameshi cewa an ganosu,nan da nan suka sanar da kafafen yada labarai na Gano wadandan Sojojin dasuka bata ayayin kwantar da tarzoma agarin na maisuguri.

Suna isa Abuja direct asibiti aka wuce dasu,wanda yafi jin jiki Aliyu ne domin Shine baya cikin hayyacinsa,suko Sauran Tun acikin jirgi suka dawo hayyacinsu,Emagency aka shiga dashi domin bashi taimakon gaggawa da kuma daure karayan dake tare dashi,ga kuma harbin bindiga wanda ya dade ajikinsa don ma dai Allah yasa Tun lokacin da Abun Yafaru an cire harsashin.

Lokacin da lbrin kuboto da Sojojin dasuka bata ya zaga Duniya gabadaya Mutane nata murna,ciki harda Ni"ima wanda Tun sadda taji harda captain dinta awanda ake nema,ta Shiga tashin hankali,sai kuka ta addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya,jin dawowarsu har saida tayi sujjudan godiya ga Allah,duk da ba"a Fadi Ahalin da suke ciki ba,an dai ce Sun samu Raunika ammh ba na tada hankali ba,suna babban Asibiti dake Abuja suna amsan Taimakon gaggawa.

  Kawu Shine kan gaba wajen samun lbrin wayar Umar yakira Shiyake labartamai halin da Aliyu ke ciki hankalinsa ya tashi nan take ya biyo jirgi zuwa Abuja,Shiko Umar suna gama waya da kawu ya kira Maimartaba ya Fadamai Halin da"ake cki..Wai Fadar irin tashin hankalin da Maimartaba ya Shiga Fade bata baki ne,salati kawai yake yana kiran Sunan Allah,lokacin dayake sanar da goggo zaman ya bori tayi hannu bisa kai tana kuka,maimartaba na bata baki,gimbiya Razeenah da Ummah mai babban daki da Baba Ade sai gimbiya Fasilatu kadai sukaji lbrin Abunda ke Faruwa,sai waziri da shamaki wanda maimartaba yabada Umanin ashirya musu Tafiya zuwa Nageria.

Goggo tayi kuka tana Fadin in Aliyu ya mutu ne asanar da ita,ammh maimartaba ya dagemata bai mutu ba da Ranshi,Azeema kuwa babu wanda yake da karfin halin Sanar da ita,saboda yaya lafiyarma kura balle tayi zawo,bata da aiki kullum sai kuka tana Fadin Yaya captain ya mutu ne ba"a san gayamata ne,ga cikinta daya shiga wata na Takwas,yayi girma sosai ta kumbura tako"ina gashi yana neman Rinjiyarta in ka ganta sai ka tsausayamata Saboda yadda ta rame ta lalace kamar ba Azeeman Kaduna ba,Su Zafira na iya bakin kokarinsu na kada Azeema ta damu ammh ina Ita bata su take,kewa tare da zafin ciwon mijinta kadai ya isheta,tayi kuka kamar zata mutu ammh kullum hakuri ake bata,akwai likitar datake duba matan maimartaba ita ke kula da Azeema,duk sati sai tazo ta dubata tare dayi mata Fadan,ta rage saka damuwa aranta don hatsari ne mai tsohon ciki tana da hawan jini,kuma baya kasa kullum saima karuwa dayake,Azeema kallonta kawai take aranta tana Fadin"kaji mata,wato na zauna nayita kwanciyar Hankali mijina ya tafi yaki bai dawo ba,lalle ma wannan kwakwalwarta tatabu toh jinin yayi ta hawa ai badai Ranar sauka sai Muradin Ranta yadawo,Ko Zafira da Jabir ya kira ya sanar da ita Gargadi yayimata na koda wasa karta gayama Azeema,saboda ba"a ce asanar da ita ba.



Washegari Maimartaba da Waziri sai Goggo da Gimbiya Fasilatu Suka nufo kasar Nageria cike da alhini tare da tararradin Halin da zasu iskeshi ciiki,gimbiya Razeenah anbarta ta zauna Da Azeema ita da Baba Ade da Ummah mai babban daki,wanda sukama Azeema karya Da cewa zasu wani bikin masarautar yanki dake gabas dasu ne,kwana biyu zasu suyi dawo,bata damu ba don yanzu Abubuwa dadama basa burge Azeema,ita burinta Allah ya bayyana mata mijinta tare da Fatan Allah ya sauketa lafiya.

Koda kawu Bala ya isa Abuja dakyar aka barsa yaga Aliyu bayan Anfito dashi daga Emegency,wlh sau daya ya kalleshi bai kara ba,saboda yadda yaji kwallah sun tahomai,yanzu Gadangan goggon ne ya dawo haka gabadaya kafafunsa sagale cikin wani karafa,duka kuma nannade da bandeji,bayan Kafadansa shima daure a wuyansa,shima nannade da bandeji domin Shima karaye ne awajen,sai goshinsa wanda shima Wani katon Rauni ne awajen,gabadaya dai Abun Tsausayi,har kuma zuwa lokacin bai Farka ba,tun bayan Farfadowan da yayi lokacin ana Gyaramai Dauri,Kawu waje ya Fita yana Share kwallah,bai dade da zuwa ba,sai ga Haisam,ai Shi yana Shiga ya kame atsaye hannuwansa dafe da kai yana salati su Umar ne suka rikosa ganin yana neman Faduwa fadi yake su Fadamai gaskiya anya Gadanga na raye kuwa,?Sun tabbatar mai dayana raye,kawai dai ya jiki ne.

Sauran Sojojin dasuka dawo hayyacinsu suke bada lbrin Abunda Yafaru Ashe lokacin da yan boko haram din suka kawo masu Farmaki,suka yi ta bata kashi,toh lokacin da aka samu Rabuwa Sojojin acikin daji,harda su Aliyu aciki wanda sakamakon haka suka harbeshi akafarsa ta dama,Faduwa yayi akasa,ammh sai yayi kokarin mikewa,ganin ya kasane yasa ya Fito da karamar wukar dake kugunsa ya yaga daidai inda Harsashin ya Shiga ya saka wuka ya tsaka ya cillo shi waje yana ihu yana komai,saboda azaba,haka ya saka wani kyalle ya Daure wajen,ya mike yana dingishi ya cigaba da gudu yana rike da bindigarsa,ganin bai da wani karfi ne yasa suka mamayesa suka kamasa,suka kuma saka Sauran Sojoji 8 dake tare dashi su Mika kansu ko kuma su kasheshi,toh wannan Shine dalilin dayasa suka Ajiye makamansu suka mika kansu,shine fa suka ijiyesu anan sunata musu Azaba,dama sunce lokaci kawai suke jira dukkansu zasu kashesu,lura da sukayi kamar Aliyu ne Shugabansu yasa suka ware shi dabam suna mai Azaba kala kala,shine fa har yasamu wadanan Karayan da kuma Sauran Rauninka,suna kokarin cinye wa!adinsu na kwana biyun da suka diban musu na zasu nunasu Afaifan Vidiyo,su bada sanarwa cewa ko gwannatin Nageria su sakarmusu mutanesu suma su sakin musu Sojojinsu,in kuma sunki yarda toh suma zasu kashesu Dukkansu,toh Ana cikin hakane Sojojin sukazo suka Farmusu kuma Allah yabasu Nasara.


*****************

Maimartaba basu samu isowa ba sai Washegari,lokacin da suka Shigo cikin asibitin sun tarar da Kawu Bala da Haisam,sai Umar da Jabir,sai wasu Security dake tsaronsu,Yanayin yadda goggo taga kawu tun anan jikinta yayi sanyi kafafuwanta sukayi Nauyi,lura da Halin datake ciki ne,yasa maimarta riko hannunta ya matse alamar Karfin gwiwa kallonsa tayi wasu hawaye na gangaromata,likitocin sunyi complain Majinyacin baya bukatar hayaniya,saboda Baida de da Farkawa ba,ganin kimar Maimartane yasa aka barsu suka Shiga inda Aliyun yake,kai kodaga ganin yanayin dakin,gabadaya glass ne,zaka Fahimci saima Mutum yaji kamshin mutuwa ake kawosa irin wannan Dakin😅,lokacin da suka Shiga Dakin goggo na rabe bayan maimartaba Gimbiya Fasilatu ce kan gaba sai Waziri sai kawu bala dasu Umar,su goggo suna bayansu,Waziri keta salati yana kiran Sunan Allah lokacin dayayi Tozali da Aliyu,itakanta gimbiya Fasilatu da damuwar Abun baiwani dameta ba,sai da tayi baya tana dafe kirji idonta ya kawo kwallah,wani imani yakara Shiganta lokaci daya,yanzu Aliyu ne yakoma haka? ganin haka yasa maimartaba karisawa bakin gadon na Aliyu yana kallonsa da duka idanuwansa waje,Goggo dake bayansa tayi Saurin Rufe bakinta wanda kuka kenan Kwacemata hannu maimartaba ya sanya ya cire gilashinsa mai karamasa karfin ganin,hawaye suka taru acikin idanunsa,har sai da suka kwaranyo bisa hannun Aliyu wanda yake da lafiya,jin sanyin hawayen maimartabane yasa ya motsa hannunsa,lokaci daya da bude kumburarrun idanunsa,dishi dishi yake gani,ammh duk da haka sai da ya gane goggo da maimartaba dake gabansa,bakinsa ne yafara motsi,shiyasa da hanzari goggo ta duke gaban gadon tana Riko hanunnsa take Fadin"gadanga...."Tafada tana kuka kallonta yake,shima hawaye suna zubomai ta gefen ido,dakyar ya Furta"Na"am goggota..."Yafada murya shake,goggo Runtse ido tayi tana Rumgume hannunsa take Fadin"Allah ya Tada kafadunka Gadanga,Allah yabaka lafiya.."Take Fada tana wani kuka,wanda duk wanda ke wajen sai ya tsausayamata,Umar da jabir dake gefe banda Share kwallah babu Abunda sukeyi,Haisam ko waje yakoma don yadda kuka yaci karfinsa,Maimartabane yayi Saurin Ficewa da hanzari,Waziri ya maramai baya Shida Kawu Bala.


Gimbiya Fasilatu da Tsausayin goggo ya cikata ta Durkusa tadafa kafadanta tana Fadin"Ki bar kukan Suwaiba,kuka bazaimana mgani ba,addu"a zamu tayimai Allah ya bashi lafiya.."Goggo na jin haka tamike da hanzari,itama gimbiya Fasilatu ta mike,saboda yadda goggo take jikintama babu karfi saboda kuka,shiyasa kawai Tafada jikin gimbiya Fasilatu takara Fashewa da kuka mai cin rai,itakuma ta riketa tana lallashinta,Aliyu na kwance yana jinsu shima kukan yake,yana so ya tambayi,goggo ina Azeema ta haihu ne?ko haryanzu da Saura ammh kuma bakinsa yayimai Nauyi bazai iya mgana ba

Ashe Fitar su maimartaba sukayi Office din likitan yaje,yace ya Rubuta musu takarda yanzu zasuyi Transfer din Aliyu zuwa wani babban Asibitin kashi dake kasar india New Delhi,nan fa sukace basu san dawannan mganar ba,saboda gwannatin Nageria karkashin Sojojin kasa,ita keda alhakin kula da Aliyu Ahalin yanzu,kuma yana karkashinta babu yarda za"ayi su basu shi su tafi dashi,batare da gwannatin Nageria tasaka hannu ba jin haka yasa nan da nan Akayi waya zuwa ga *BRIG.GEN.S.U KUKA SHEKA* Shiya sanar da maigirma Chief Amry of Staff *LT.GEN.Y.T BURATAI* Abunda ke Faruwa babu Bata lokaci sai
Showing 81001 words to 84000 words out of 88299 words