iya Shuru yace"Wai yau naga bariki umar,yanzu Kaduba gayen nan,duk Wahalan damukayi dashi baitaba nuna damuwarsa ba inzamu koma masauki,ammh yau Azeema tazo harda tada rigiman kota dinga kwana dashi ko asallameshi yadawo gida? hararansa Aliyu yayi yana Fadin",Eh din,to daman ku gardawa dakune zan so ku kwana dani,Allah kyauta kai ni ko yanzu kuka tattara kuka tafi,Ayashe ta gaida Assha ko pretty? yafada yana kallon Azeema,wacce ke kunshe dariya ganin yadda Jabir ke hararansa,Jabir ya yi kuri yana kallonsa kafin yace"Toh ai ba damuwa ba basai ka koremu ba,zamu tafi kuma wlh zaka nemi ni banza mara mutumci kawai.."Dakin ne akasa dariya gabadaya ganin yadda Jabir yaji zafin Abun,Waje yafita yana ta zagin Aliyu shiko hardamai gwallo,Zafirace ta lallaba ta bi bayan Habibitan,Su ummah ko Aliyu sukayita ma Tsiya shiko ko ajikinsa don Abun yanzu ne yayi mai daidai.



Azeema duk da tsohon cikinta bata nuna kiyuwa wajen kula da Megidanta Aliyu,itace bashi abinci,goggemai jiki sabida yaji dadin jikinsa saboda Rashin wanka,akwana hudun da zuwansu garin aka kwance Karayan hannunsa,kuma Alhamdulillah komai yayi kyau masha Allah,sai da kokarin yafara anfani da hannu,wanda wannan aikin Azeema ce,itace keta kokari kan haka kuma yana kokarin motsa hannu,koda daukan Abune na mara karfi,itama Asibitin suna kokarin kula da ita amtsayinta na mai ciki,tunda duk sun saba da likiticin kamar DR khan sun Shaku dashi,inkaga yadda suke hira da Aliyu sai kuce sun shekara aruaru da haduwa ne.


Sati Daya su Gimbiya Razeenah sukayi suka koma,harda Jabir da Umar,Ummah mai babban daki tace ko ba inda zata zata,har sai Azeema ta haihu Aliyu ya warke kana ta biyosu su dawo,saboda itama ta kula dasu,toh ya suka iya dole suka barta sai Gimbiya Razeenah Tabisu suka koma tare,Ita kuma Ummah Dr khan yace ba"a barta ita kadai ahotel ba,gidansa dake cikin Asibitin nan Yakai Ummah mai babban daki,tazauna ita da matarsa mai Suna KAREENA,suna da kirki sosai,duk da Ummah batajin Turanci tana jin labarci,sukuma sun iya saboda sun zauna da larabawa sosai saboda yanayin aikin Shi Dr khan din,itama kuma Azeema aka barta ita da mijinta tana kara kula dashi..



_________________

*BAYAN WATA DAYA*

Sauki tare da cigaba yana samuwa abangaren Aliyu,wanda har an kwance duka aikin da"akayimai akafafunsa,hannunsa kuma Tuni ya yawarke garas,in ka ganshi bazakace yataba samun Rauni ba,Kafafunsa kuwa haryafara koyon Tafiya dasu Duk da tafiyan bata nuna Sosai ba,ammh sakamakon sanduna guda biyu,suna taimakamai Sosai wajen Nunar da Tafiyar nashi,kullum safe da yammah Azeema ke Fitowa dashi suna zagaya Haraban Asibitin,suna tafe suna soyewarsu babu Ruwansu da kowa,Tuni sukebama duk wanda ke asibitin sha'awa ganinsu bakaken Fata,ammh kuma suna mutumta soyayyah da daraja Aure haka,Ba yadda Ummah mai babban daki batayi ba,akan Azeema tadawo tahuta Tunda cikinta ya isa haihuwa ammh fafur taki,wai Tunda lafiyanta kalau ita bazata ta zauna ba,dole ta zura mat ido toh yazatayi Allah ya hadata da yaran zamani.


Awani dare Azeema tatashi da Nakuda,Hankali Aliyu yayi bala"in Tashi ganin halin datake ciki,ko kafin ya danna Madannin kiran likita Azeema tafara Wani irin nishi,ko kafin Nurses din su kariso Azeema tayi wani nishi mai karfi sai ga Kan d'a ya Fito,Allah ya taimake Nurses din suna shigowa Kan Da'n na Fitowa da hanzari suka karisa suka saka hannu suka jawosa,ai basu bar wajen ba,Azeema ta bankare tana salati nishi take mai karfi sai ga wani kan yakara Fito,suka saka hannu suka jawosa,Aliyu dake gefe yahada zufa kota ko'ina yana rike da Azeema,wlh har sai da yayi mata kwallah,ai suna jawoshi,takoma takwanta tana maida numfashi,Ihu suke suna daga ya"yan suna bugasu,nan da nan suka chanyara kuka atare,Azeema dake kwance hannunta kamkame dana gadanga taji cikinta yakara murdawa Nishi take saki tana Fadin"Yaya inaji fa akwai wani acikin cikin?Tafada tana wani nishin mai karfi,Wata nurses ce ta ankare da hanzari ta kariso tana kara ware kafafun Azeema take Fadin"Anoder one..."Take Fadi tana ihu"push oya push..."take Fadamata Azeema ko jitayi kamar zata Shide saboda azaba,dakyar ta iya wani nishi mai karfi,wanda ya Fito da kan Da'n Suka sanya hannu suka jawoshi,suna murna gabadaya dakin ya gauraye da kukan jariran wadanda Nurses din suka dagasu suka zube bisa jikin Azeema suna dariya,jikinsu duk jini ammh haka Azeema ta rikesu tana dariya lokaci daya da kwallah,Aliyu ko kamar yasuma saboda dadi,Dakyar suka koreshi waje suka kwashe mabiyan Azeema suka gyara wajen gefe daya kuma wasu suna kokarin gyaran yaran,duk da asibitin na kashi ne,ammh Nurses din sun san Abunda sukeyi,shiyasa karban haihuwan Azeeman bai basu wahala ba,duk da Abun yazo da Sauki.


Koda gari ya waye sai dai Asibiti ta cika da lbrin Majinyacin Sojan nan da"aka kawo daga Nageri,matarshi tahaifi Tripple,Mata biyu Namiji daya,kuma dukkansu sun zauna amahaifa dayane domin ko Azeema da Aliyu haryanzu sun kasa gane bambamcinsu,duk da kwana sukayi suna kare musu kallo,sun Rumgume yafi sau Biyar suna kara godiya ga Allah daya Basu wannan kyautar,Ummah mai babban daki sai dai Da Safe Dr khan ya sanar da ita haihuwan Azeema,duk da shima baya Asibitin waya akayi masa,jiki narawa suka nufa cikin Asibitin,sai dai suka tarar da Azeema zaune bisa gado tayi Ras da ita kamar ba ita ta haihu ba ga Gadanga a gefe bakin nan kamar zai yage,saboda murna Ummah mai babban daki ita takira Gida ta sanar dasu,gabadaya masarauta ta rude da murna Jikoki uku alokaci daya lalle Allah Abun godiya,Goggo ita ta kira kawu da kanta ta sanar dashi kafin kaceme haihuwan Tripple yazaga Duniya,Haisam na kano yaji lbrin ai sai ya kira jabir yana sanar dashi da zarar komai yayi daidai Aliyu ya dawo gida zasu fadama maimartaba suna so suma ayi bikinsu nan da wani lokaci domin zamowar Aliyu baban yan uku tabbas barazanane ga rayuwarsušŸ˜‚

kwana biyu da haihuwan Azeema gimbiya Fasilatu da gimbiya Razeenah suka dira a india,murna ba"a mgana,ai gimbiya Fasilatu batayi shawara da kowa ba tayi saranda Taba goggo dama,Domin ta Fahimci tafi karfinta nesa ba kusa,domin tsakaninsu kamar tsakanin sama da kasa ne,duka duka Sati daya suka kara gabadaya aka Rubutama Aliyu gadanga sallama lokacin yana da wata biyu a asibitin,domin yaji sauki sosai koma nace ya warke,domin kafafunsa sun mike da kanshi yake takawa batare da Taimakon sanda ba.



Asibitin sunsha kewa love birds,Azeema da Aliyu ga kuma Tripple masu shiga rai da Ban sha"awa,haka sukayi ta hotuna da likitocin da Nurses,suna bankwana da sabo suka rabu,Azeema harda kwallaar rabuwa ita da Ummah mai babban daki sunji dadin india,sosai Dr khan kuwa sunyi exchanging din Phone number da Aliyu,da cewa da zarar ya shigo Nageria zai nemesa,haka suka rabu da matarsa kareena wacce suka shaku da Azeema da Ummah.

Ranar da suka baro india zuwa Masarautar Tambari buzu,sukowa ana chan ana gudanar da shagulgular murnan dawowar Aliyu da kuma murnan haihuwan yan"uku ,wanda ba"a tabayi ba tun sadda aka gina masarautar,Mutanen Nageria kuwa Sun dade da isa zuwansu Aliyu kawai suke jira,Hatta da jabir wanda yazo Shida Maminsa da Daddynsa,da Haisam ba"a barsu abaya ba domin sunce wlh wannan karon bazasu koma Nageria ba sai da matansu sun gaji suma,suna bukatar gwada karfin mazantakansušŸ˜‚ wannan karon ma kawu da duka iyalansa,harda su Anty madina sunce wlh suma baza"a barsu abaya ba,tab uwa uba kuma ga shi Sunan yan ukun za"a hadashi ne da bikin gwagwaran biyu Wato Jabir da Haisam,kawu ya roki alfarman kuma Maimartaba baiyi gaddama ba,sakamakon yadda yake cikin Farinciki na dawowar Aliyu,ga kuma wani kyautan daga Allah.



*Ina godiya sosai masoyana ina ganin duka comments dinku daga mabambamta group dadama,bana samun binku daya bayan daya na yi muku reply,saboda ina cikin busy ne ko Typing din ma kokari nake mu kareta mu huta hakanan Shiyasa,ngd sosai kujigaba da hakuri dani Allah ya bar zumunci Ameen*


_*Sisinah Aisha Alto,keda Sahibata Hafsat Hafan ina kai gaisuwašŸ™‹ Alherin Allah ya lullubeku aduk inda kuke*_


*D'IYATA LADINGO GA SAKON JINJINATAšŸ‘Allah yayi ma Rayuwarki Albarka can love u less diyar kwarai*



*Janafty*
Showing 87001 words to 88299 words out of 88299 words