matukar tana raye Abun sonta bazai dawo gareta ba,Mganar su Ni"ima kuma bata da mtsala dasu don su aikinsu ya kare,dama wannan fa on none ne,bata da wani madafa,so dama tayi amfani da itane Burinta yacika yanzu kuma ita da kanta zata karishe Sauran aikin,Ranar dakyar Azeeza ta iya barci saboda Farinciki,harda mafarkin sunyi Aure da yaya captain wai Sun Tafi Canada honeymoon😛😜koda tatashi da Safe,sai tayi karyan ciwon ciki taki zuwa mktanta sai da mallam lawal ya Fita,itakuma inna Ramatu ta shiga makewayi wanka ta saka hijabi ta Fice salaf salaf,azauren gidansu ta make tana leken gidan goggo,tasan Dole goggo zata Fito yau domin yau Surukar Hajiya goshi Ake Sunanta,kuma suna mugun Shiri da goggo tasan dolene zata Shiga gidan,itama inna Ramatu nan take Rawan jikin zuwa Tunda tasan gidan akwai maiko,don Wani Tamkamemen gidane mai get chan bayan gidansu goggo,Tana nan ko  sai ga goggo ta Fito sanye da hijabi,ta Wuce zuwa gidan Hajiya goshi,Tana ganin Fitarta tayi tsallen murna Sai da tadan Wuce da wasu Mintina kafin ta Fito tana waige waige,sai kuma tayi zaraf ta Shige gidan goggo,sai da ta tsaya azaure ta gyara kanta kafin ta rafka sallama ta Shiga.

  "Salamu Alaikum..."Tafada da muryanta da karfi,Azeema dake kwance cikin bargo acikin bedroom din goggo ta dago kanta jin sallama,domin Tunda tazo kullum da zazzabi da ciwon kai take kwana,Dakyar ta mike jin ankara sallama Saukowa tayi tana amsawa kafin Ta fito Falon tana fadin"Waye..? da muryanta wacce ta shake saboda kuka jin muryanta yasa Azeeza tayi Wuf ta fada dakin,Azeema dake kokarin Fitowa sukaci karo da juna baya taja da Sauri tana kallon Azeezar wacce itama take kallonta daga sama har kasa tana wata karamar dariya,gaban Azeema ya Fadi tayi kasake tana kallonta da idanuwanta da suka Shige ciki saboda kuka,zagayata Azeeza ta Shigayi tana mata kallon sama da kasa duka hannuwanta suna harde bisa kirjinta.

  Azeema Ta dago da idanuwanta tana kallon Azeeza kafin tace"Lafiya kika Shigoma mutane gida,kina musu dariya.."?Tafada cikin kakkausan murya wata dariyan Azeeza ta sheke dashi kafin ta Shiga Tafa hannu tana Fadin"Dole na Shigo nayi miki kalan tsab,ina dariya ai nasan dama zaki dawo ko kinmanta nafadamiki ban Yarda makamai na ba,zan dawo gareki kuma ina da tabbacin Tarkona wannan karon ya kama kurciya don daga alamunki ya nuna Keda kaduna kuma sai dai da wucewa.."Tafada tana kara saka dariya Baya Azeema tayi tana dafe kirji Duka idanuwanta awaje kafin tace"Dama..Dama..Ke kika kullamin wannan Makircin Azeeza..?

  Duk da Azeeza batasan kowani makirci bane su Ni",ima suka kullah ma Azeema ba,ta tabbata bamai Sauki bane,mirmishi tayi kafin tace"Kwarai ma dagaske,Toh dawa kike Tunani Ada,ai babu wanda yakeson ganin bayanki Azeema bayan ni,kuma naci Nasaran rabaki da Aurenki yanzu Abu na gaba,shine zan Rabaki da duniyar gabaki dayanta yadda mafarkina zai Zama gaskiya.."Azeema data kame saboda mamaki batasan sadda hawaye suka zubomata ba tashiga Nuna Azeema tana Fadin"Kinyi kuskure Azeeza,ada na dauka kuruciya ke damunki,ashe ke da gaske kike,Toh barikiji na sanar dake Abunda baki sani ba,Aurena da yaya Captain mutuwace kadai zata iya Rabata duk makircinki Azeeza sai dai kiyi gama,ayau nayi nadamar hada jinin mahaifi dake Azeeza wlh na Fara Tunanin kila keba diyar baba  bace Ta halas.."Baya Azeeza taja tana huci tace"me kike nufi..? Dariyar Rainin hankali Azeema tayi mata kafin tace"kinfini sani,banza sakarya wacce iliminta bai amfana mata komai ba.."Azuciye Azeeza takaima Azeema mari,caraf ta rike hannunta kafin ta yarfe hannun ta dage iya karfinta ta zabgamata maruka har guda biyu tana fadin"Na bar kara ragamiki Azeeza don ke ba yar"uwata bace daga yau,kuma wlh ni dake mu zuba mugani Shege ka Fasa.."Tafada tana ingizata har sai da Tafada kan kujera,dafe kuncinta Azeeza tayi tana kallon Azeema wacce ke kanta tana huci mikewa tayi tana dafe da Kuncinta tace"Tunda dai kince mutuwa ne zata Rabaku da yaya captain niko yau zan gayyato miki mutuwarki har gida,kinga kin saukakamamin al"amaruna.."Tana gama Fadarka tayi kukan kura bisa wuyan Azeema ta shaketa kam,Azeema ta sanya hannu tana kokarin kwacewa Azeeza tasaka jikinta ta ingixata kan kujera ta tafi ta Fada,itakuma ta bita ta Danne,hannunta kuma bisa wuyanta ta shaketa da karfin tsiya dayake Azeeza nada girman jiki tuni ta sakarma Azeema gajiya tagagara kwace kanta ga idanunta sun zaro waje tana kakari,idanun Azeeza ya Rufe mutuwar Azeema kawai take son ganin,Jin alamun kamar motsi ne,yasa tayi hanzarin sakinta tana huci Azeema ko hannunta na wuyanta tana hawayen Wuya kallonta Azeeza tayi kafin tace"Kin ci sa"a akaro na Farko ammh wlh karo na biyu ko ni ko ke...!"Tana gama Fadin haka ta Fita da Sauri alamun Shigowar goggo taji,da hanzari ta makale bayan kofar gidan,sai da goggo ta Shige kana Ta fita aguje tana haki,Itako goggo tana Shiga taga Azeema kwance tasha wuya hannunta na bisa wuyanta tana kuka,Koda ta tambayeta kin Fadamata tayi sai tace Ta fado daga kan gado ne sadda take barci ,gyada kai kawai goggo Tayi Domin bata yarda ba,itako tama Rasa mezatace ne,Azeeza na son kasheta? kuma itace silar dawowarta gida? ina wannan Fadan natane ita kadai dole itama tamike Tsaye takama jikinta suyi Fito na Fito da Azeezar.


*Get Ready Fa,gobe ne fa💃💃 gobe ne fa💃💃 gobe ne fa Jirgin daya Dibo sojojin hadin gwiwan Gwannatoci hudu zai yada zango a Abuja*😜


*Intelligent writers asso*
*Janafty....*
[12/24, 22:26] +234 810 307 8468: *ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 26*

    *After 1 week*

    Bayan Sati daya da dawowar Azeema gombe,har kuma yau basu ji wani mgana daga bakin Gadanga ba,koda goggo ta gaji da Fushinta ta kirashi wayarsa bata Tafiya,Itako Azeema bata gayama Goggo Abunda yafaru Tsakaninta da Azeeza ba,saboda batasan taya zata kama lbrin ba,ammh tabi Shawaran goggo ta maida lamarinta ga Allah Shine zai warware komai cikin Sauki,Azeeza kuwa Aranta tana mata Fatan shiriya,Yanzu ta rageyawan kuka da damuwa ammh ba kewa  Tare da kaunar gadanga bai bar Ranta ba,kullum dashi take kwana take tashi,gashi Tunda tazo take Fama da zazzabin dare,dakuma gari yawaye sai ta nemi zazzabin Tarasa,gashi bata cikin kwanciyar Hankali ammh taKara haske sosai Fatarta tayi kyau,Kullum sai dai Tasha paracetamol ta kwanta,itama goggo Abun na damunta ammh Sai Azeema tashashantar da zencen Zuwa asibitin,mganar cin abinci kuma bata cika ci ba,sai da yanzu Tafi kauri wajen kayan kwalama,irinsu goriba,wainar Fulawa ta manja,da kuma Danwake wanda kullum cikin yinshi take,goggo dai kallonta kawai take ammh kasan zuciyarta tana zargin wani Abu,Allah yasa hasashenta yazama gaskiya,Shiko mallam lawal kullum zai Fita kasuwa sai ya Shigo sun gaisa da goggo yaga kwanar Azeema,in ko yadawo sai ya Shigo yakawo mata Sakonta nasu goriba da dan Ta matsitsi tunda ya lura tana so sosai,Sune yanzu Abun shanta da Tsamiyar biri,Daga goggo har Mallam lawal sun tabbatar da hasashensu kan Azeema domin alamomi dadama sun bayyana zarginsu.

Ranar Asabar sai ga Kawu bala Shida Ummah suka diro gombe,Murna wajen goggo ba"a mgana tarasa ina zata sakasu saboda murna,kawo musu Wannan kawo musu wanchan,Sai da suka huta sukaji abinci kafin su shiga tattauna Abun yakawosu Goggo tana Fada tana gayama Kawu bala cewa gadanga bai kirata ba,kuma takirashi akashe,mirmishi kawu yayi yana fadin"Kiyi hakuri Suwaiba komai zai Wuce,ninaje wajenshi har cikin barikin na sameshi,kwance baida lafiya abokinsa na kula dashi,ammh yaji Sauki sosai,yace aiki ne yayi musu yawa,tunda Sojojin hadin gwiwan da"a ke sa ran zuwansu gobe ko jibi su zasu bi Tawagar Cheif Army of Staff,suje Abuja su Taho dasu nan barikinsu Tunda kinga babban bariki ne,mai wakiltan Arewacinmu na Nageria,shiyasa ,kuma komai fa Ahankali zamu bi Suwaiba Har Allah ya warware komai"Jinjina kai goggo Tayi kafin tace,"Shikenan yaya Allah ya Shigemana gaba.."Da Ameen suka karba kafin Kawu yace"Suwaiba kiramin Azeeman nayi mgana da ita.."Tashi goggo tayi tashiga ciki takira Azeema wacce ke zaune ta zabga Tagumi,koda Tafito sanye da dogon hijabinta kasa ta durkushe tana kara gaishesu domin sun gaisa sanda sukazo,hakuri ya Shiga bata tare dayimata nasiha mai Shiga jiki,Tare kuma da Umartanta datayi hakuri tadauka wannan Jarabtane daga Allah,gyada kai Azeema ketayi tana Tsiyayan Hawaye,Ummah dake kusa da ita,tajata kan jikinta tana lallashinta kawu ya kalli Goggo yace"Suwaiba mganar jarabawarta zan baki kudi Ranar monday Ki dauketa kuje tare,kiyimata Rigistration Din,Allah ya Rufamana Asiri yakuma bada sa"a.."Da Ameen goggo ta karba tamai godiya,Itama Azeema tashiga mai godiya,yana girgiza kai baice komai ba.

Basu Tafi Aranar ba ,sai washegari da safe suka koma,bayan ya cika goggo da kudi da kayan Nau"in Abinci kala kala,Mallam lawal ma yasamu nashi kason,don daya dawo daga kasuwa yaShigo nan suka hade da kawu,suka Shiga hirar yaushe gamo,Tare sukaci abinci sai wajen goma ya Shiga gida,Aljihunsa cikeda kudin da kawu ya bashi,koda inna Ramatu Tafara Tsiyarta yana gayamata inda ya tsaya da kudin da kawu yabashi harda kayan abinci,washe baki Inna Ramatu tayi tana Murnan sun samu kudi,domin dama idonta fa Anaira yake,Dubu biyu yabata harda dari biyar,sai kaji baki ya mutu ta kalmashe kafa tana mai Hira harda Cemai in Azeema zata koma zata bita taga dakinta,jinta kawai yake yana jinjina son Abun Duniya irin na Ramatu sam bata iya boye kwadayinta.

Ranar monday Tun karfe 8:00am tayi masu goggo a office din principal din mkrantar su Azeema,koda tafadi Abunda ke tafe dasu,Har an bude Littafi za"a Rubuta sunan Azeema,aka Tambayi Sunan dalibar, Azeema tace"Azeema lawal bature.."Cike da mamaki principal ke kallonsu kafin yace"Ai Yayanta yakirani awaya mun gama mgana dashi,haryama Turo da kudin Rigistratin din na both WAEC AND NECO,gashi ma Monday mai zuwa zasu Fara WAEC,gama Time dinta.."Yafada yana zaro wata paper agefensa ya mikama Azeema,Tasa hannu biyu ta karba,Mirmishi goggo tayi kafin tace"Ayyah dana ne,munyi mgana dashi,toh nazata baisamu lokaci bane,dayake yana chan kaduna yana aiki ne,kasan Soja ne.."principal din ya gyada kai yana Fadin"Allah sarki.."Kafin ya gimtse Fuska kadama goggo taga damar kara wata mgana,dariya takusa kama Azeema,da hanzari ta riko goggo suka Fice tana fadin"Tanque Sir..."Goggo ko ajikinta tana tafe tana sakama gadanga albarka harda Fadin da tanajin Haushinsa ammh yanzu ya wankemata Ranta Fes ta yafemai,Azeema ta hadu da yan class dinsu suka tsaya suka gaisa,cikin kulawa wasu kuma sunata mata murnan Aurenta duk da bata gayyacesu ba,goggo ce ke karbewa da cewa",Ai Abun ne yazo a kurarran lokaci,..."Dahaka take kashe bakinsu basu bar mkranta ba,sai wajen goma,sai da suka biya kasuwa goggo ta siyo ogun da alayyahu,wai yau miyar ogun takejin ci,itako Azeema Goriba ta siya da uban yawa,har goggo na mata Fadan yayi yawa,kada fa hakoranta su Mauje Saboda cin Goriba,dariya kawai tayimata kafin suhau Adaidaita su koma gida,Ranar Azeema Wuni tayi cin goriba,sai danwake wanda goggo tayimata,itadai Tuwon Shinkafa tayi da miyar ogun dinta,Azeema ko warinshi bataso sai dai ta shige daki tana Toshe hanci,goggo na dariya tace"Topha Shikuma wannan Audin da Tsirfar dayazo kenan,aiko sai da yayi hakuri don Tuwon kwana uku nayi wlh.."😹

   ••°°••°°••°°••°°••°°••°°

_Nnmadi Azikiwe International Airpor Abuja_

   "Misalin karfe 5:30pm na Ranar Laraba,Jirgin gwannati wanda ke dauke da Sojojin Cameron,chadi,da Niger ya yada zango a babban Filin jirgin Na Nmandi Azikiwe dake Abuja,acikin masu Tarbansu akawai mataimakin Shugaban kasa *PROF. YEMI ASINBANJO..*sai Shugaban Army Of Staff na Nageria gabadaya Wato *LT.GEN.Y.T BURATAI..*,tare dashi akwai *BRIG.GEN. S.U KUKA SHEKA..* Bayansu akwai wasu manyan Sojiji daga Tawaga Tawaga ciki harda Manyan Sojijin da kananun dake *I DIVISION NAGERIA ARMY KADUNA..*Domin suke da alhakin jagorantansu zuwa Kaduna chan barikin,acikin wadannan Sojojin akwai Irin su Captain Jabir da Captain Aliyu Tambari buzu,wanda kowa yasan kwarewarsu wajen aiki da kawoma kasa cigaba,cikin bakin Sojojin da suka sauka harda *LIEUTENANT UMAR ABDULNASEER TAMBARI BUZU..*yarima mai jiran gado.,daganan Filin jirgin sai da suka isa Fadar Shugaban kasa Wato villa, mai Girma Shugaban kasanmu *GEN. MUHAMMADU BUHARI* yayi musu jawaban barka da zuwa tare da mika godiya sosai zuwa garesu mussaman ma Shugabanninsu daga kowani yanki,an Shirya liyafar ban girma acikin Villah fa,wlh anja kaya sosai ba karya anyi Shaye shaye na lemuka kala kala,abinci kuwa anyi yafi na kala dari,kundai san Villa babbar waje ne,so dole ayi babbar Harka,yan TEAM AZEEMA GADANGA Kuwa da suka biyoni Tuni Security suka hanasu Shiga nima din dakyar na samu rabawa,Allah sarki suna waje suna raba ido 😂😹😛Srry in zamu Masarautar Tambari buzu a sakaya ku😂Nan suka kwana sai washagari Suka sake hawo wani jirgin zuwa Kaduna.

 
__________________

    inda suka Faka motarsu wanchan karon,wannan ma anan suka ijiyeta,wato gaba da gidan goggo da kadan,Sun Fito daga motar suna waige waige neman wanda zasu Tambaya don lokacin wajen sha biyun Rana ne,babu kowa alayin,sai ga wani dan yaro wanda bazai Wuce shekara goma ba,da kayan mkranta ajikinsa da alama dai daga mkranta yataso,harya gota su Muneera tayi Saurin kiransa.

"Kai yaro zo nan.."Waigowa yayi kamar bazai zo ba,ganinsu yan gayu sai kuma yaje,ammh sai ya tsaya daga baya baya,mirmishi Muneera tayi kafin ta bude Yar karamar jakar dake hannunta ta zaro Naira dari tamikamai Tana fadin"Karbi dama tambayarka zamuyi.."Da hanzari ya karba yana washe baki,muneera tace"Gidansu wata yar budurwa mai Suna Azeeza,zaka ganta wata mai kiba Fara,idonta asama.."Shuru yaron yayi kafin yace"La Anty Azeeza kanwar Adda Azeema wacce ta auri yaya sojan nan gidan.? yafada yana nuna gidan goggo da hannu,Faduwar gaba ya ziyarci Ni"ima da Muneera atare,Suka kalli juna kafin su kalli yaron Muneera tace"Au dama yayartace ta Auri sojan nan gidan? yaron ko yawashe baki yana fadin"Eh mana gama gidansu Anty Azeezar nan,innansu kawar innanmu ce fa.."Zaro ido muneera tayi kafin tace"Toh mun gode jeka.."

  yako zura aguje yana murnan kudin da suka bashi,Hannu muneera ta saka bisa kugunta tana Fadin"Sweetheart anya ba gadar zare yarinyarchan ta Shiryamana ba,kiji fa ance yar uwartace ta Auri captain fa,? ni zuciyata na bani wani Abu dabam..'ajiyar zuciya Ni"ima ta sauke kafin tace"Nima Abunda ya Dauremin kai kenan,ammh karmu yanke hukunci mu Shiga gidan mugani,ammh da mamaki ace in har yar"uwantane kuma taso ganin bayan Aurenta.."Muneera batayi mgana ba,tayi gaba Ni"ima tabiyo bayanta suka Rafka sallama acikin gidansu Azeeza,wanda suka samu inna Ramatu tana Tsakar gida tana gyaran Shinkafa suka Shigo koda ta amsan sallaman tadago tana kallonsu da mamaki don ganinsu yan gayu dasu,mikewa tayi tana musu maraba bakinta duk abude,taga irin Naira,Sannu da zuwa take jera musu Suko suna binta da gidan gabadaya da kallon banza,Tabarma inna Ramatu tashiga daki ta daukomusu Tana kokarin Shimfidamusu Muneera ta dakatar da ita da Fadin.

"No barshi baiwar Allah ba zama yakawomu ba,don Allah mahaifiyar Azeema muke nema matar captain.."Bata Fuska Inna Ramatu tayi ganin Irin yadda suke kallonta tace"Au ita taturo ku kuzo kumin Rashin arziki? kokuwa kunyi batan kaine,ni ba Uwarta bace,uwarta tadade da mutuwa,ni matar ubantace uwar Azeeza,in wajenta kukazo to ku juya ku Shiga wannan gidan na gaba nan take zaune wajen Uwar mara Asalin.."Tafada tana zaro musu ido,Mirmishin Takaichi Muneera tayi kafin tace"Ai dama Azeeza muke nema munyi batan Sunane.."Tafada tana kallon Ni"ima wacce Tun yanzu Nadama suka dirar mata.

Azeeza dake barci adaki sama sama takejin hayaniyar Inna Ramatu,tsaki taja kafin ta Fito daga ita sai wata doguwar Rigar Atamfa bako kallabi,tana hammah da mika atare ta bude labule tana Fadin"Kai inna waike dawa kike Masifa da Rana tsa...."Bata ida mganarta ba idonta ya sauka kansu Ni"ima da Muneera wadanda ke jifanta da wani kallon banza nazakici ubanki din nan.

  Inna Ramatu tace"Nida wadanan yan Rainin arzikin ne,wai da Farko sunce wajen Azeema sukazo,sai da sukaji na balbalesu kana suka dawo sukace wajenki sukazo,kiji fa rainin Hankali ina kika sansu ma.."Tafada Hankalinta kwance,Azeeza wacce ta Razana da ganinsu Ni'ima ammh sai ta boye Razanarta Ta Fito tana fadin"kyalesu inna Wajena sukazo na sansu yan sch dinmu ne.."Inna Ramatu ta washe baki tace"Oho ai sai kuyi bayani,kuyi hakuri fa,ke Azeeza kishiga dasu ciki mana sannunku da zuwa.."Tafada tana mikewa zata kawo musu Ruwa,yake kawai Azeeza tayi kafin takoma daki tana fadin"Ku Shigo.."Ai bata gama Rufe baki ba Muneera ta bankada dakin da Sauri Ni"ima tabi bayanta suka tsaya cirko cirko suna kallon Azeeza wacce ke tsaye tana jifansu da wani kallon uku saura kwata,suna tsaye sai ga inna Ramatu ta Shigo da Jug da Ruwa hade da kofuna ta ijiye tana fadin!ku zauna ga Ruwa kusha.."yake kawai Muneera tamata tana Fadin"Toh...Inna bata kawo komai Aranta ba,ta Fice zuwa waje.

   Muneera ce ta katse kallon da Azeeza ke binsu dashi tana Fadin"ke baiwar Allah nasan kinsan meke Tafe damu ko,and wht all dis ya akayi kika samu aiki,kuma alhalin Azeema matar captain yaya take gareki,and abubuwa dayawa da bamu gane ba plz u need more explanation fa"Tafada da kakkausan murya,Baya Azeeza taja kafin ta tuntsire da dariya harda dukewa Ni"ima ta kalli Muneera idonta na cikowa da hawaye,itama muneera ita ta kallah,kafin ta maida hankalinta kan Azeeza tace"Lafiyanki kika tasamu kinamana dariya..? tafada tana bin jikinsu da kallo,dariyan Azeeza takara kecewa kan ta tsagaita tana fadin"oh don Allah kiyi hakuri,wlh ba Dariyan komai nake ba,sai dariyan gaku ridaridan yan mata,ga kyau ga iya wanka,ga kudi ga ilimi ammh sam kwakwalwarku bata aiki daidai ko nace ta wawaye ne wlh.."Tafada tana Tafa hannu tana cigaba da dariya,Zaro ido sukayi suna mamakin Furucinta Ganin yadda sukayine yasa Azeeza tacigaba da cewa"Yo eh mana banda Wauta da Saunanci daga ganin mutum yace,kayi Abu kaza,kaikuma dayake gabo ne,sai kayi jiki na rawa,koda yake duk acikin son dakikema captain din ne ko,?don naga Tun kwana hudu da mganarmu Aka sako Azeema tadawo gida duk da ba"a Fallasa Abun ba,inaji nace lalle kinyi kuskuren yarda dani,domin wannan Abun dana sakaki kika aikata na saki ne saboda nakara nesanta yaya captain dake,bayan kin kashe auren Azeema kinga na jefi Tsuntsu Biyu da Dutse daya kenan.."Tafada tana daga musu gira,Muneera da Ni"ima sukayi wani slow suna bin Azeeza da kallo yarda karamar yarinya ta iya Wasa da hankalinsu Ni"ima ce bakinta na Rawa tace"Toh sa..saboda mene...?

  Daure Fuska Azeeza tayi kamar ba ita ke dariya ba tace"Ko baku Tambayaba,dama yakamata kuji koda jin bazai muku amfani ba,Yaya captain nawane nikadai,nafi kowa sonshi harda da uwarsa nafita sonshi,Duk duniya bani da wani buri sai na yau na ganni amtsayin matar Yaya captain,nasoshi Tun banso mai ake kira soba,Na rayu da Sonshi na girma da Sonshi,kullum mafarkina na Aureshi,sai gashi kwatsam Adda Azeema tafim Shigar Sauri,saboda shi na tsani yar"uwanta naji bana  kaunarta balle nakaunar ganinta da Abun
Showing 60001 words to 63000 words out of 88299 words