tace tashi ku gaisa da baffanki tace to tare da mikewa.
A falo tagansu ta gaishesu suka amsa cikin farin ciki mustafa yakaleta yace salma inaso kisan duk abinda yafaru dake to ba shakka mukaddarine sannan mahaifinki dani masu sanki ne bazamu yanke hukunci akan abinda mukasan bazai taimakeki ba tace hakane baffa, Abba yace ungo nan ya mika mata d'ari 500 yace kije kisiyoma baffanki lemon fata da ayaba tace to tare da fita, taxo fita taga goggo tadawo nan tagaisheta ta wuce.
Haka ta tafi tana murmushi haka kawai tunda tai mafarki takejin farinciki.
Can bakin titi taje tana tafe cikin nikaf tana murmushi.
Mustafa shi dakanshi yazaunar da umma da goggo da matarshi dake ciki time din batasan meke faruwa ba ya musu bayanin halin da'ake ciki, Goggo kam tayi murna ta kuma yi bakinciki.
Tana murna salma zatai aure sai dai tana kishin auran d'an sarkin dazatai sai dai yaxatayi? Tunda batada 'da.
Hafsa matar mustafa tace amma kamal.....dasauri mustafa ya katseta yace inhar kamal yadamu da salma da tuni ya dawo sannan daya dinga nemanta ta hanyoyi daban daban amma ina sane baya nemanta, umma kam batace komai ba.
Abba yace kada kowa yafad'ama salma halin da ake ciki yanzu harsai bikin yazo kusa gudun kar sanda takema kamal yaja mata matsala sukace to.
Salma tadawo gida tawuce d'aki tare da d'aukan hoton kamal tace yaya inaji ajikina munkusa fara rayuwa tare ganin irin mafarkin danai.
Nace toh faπ€ anya kuwa?.
Fulani dakanta ta kira Zainab da Zeena 'ya'yanta manya masu aure kuma sune kesan salman nagaskiya, nan ta sanar dazu umarnin sarki na lefem salman da zasu hado, murna sosak sukai, fulank tace sai dai yarinyar yar talakawa ce dan haka kusan irin kayan dazaku hado? Cike da mamaki zeena tace bangane ba? Dan zai auri talaka sai akace ita ba mutum bace? Zainab tace mudai zamuyi abinda muka saba, fulani tace kukuka saniπ sannan ance kar wanda yama salman zancen auran.
Zainab tace bangane ba?baya santa ne ko me? Tace nidai nafad'a muku umarnin mahaifinku ne.
Suka kalli juna cikin mamaki.
Shirye shiryen biki ake sosai agidan sarki an tsaida lokaci nan da 3weeks, salman kam yafahimci akwai shirin biki da ake a gidan sai dai ganin ba wanda yamai maganar yasa shima ya basar ya nuna baisan me sukeyi ba.
Haka gidansu salma ita ba makaranta take zuwa ba sai dai itakanta batasan shiga da fitar da ake a gidan ba gashi kullum goggo sai ta kawo mata abu a kofi tace tasha intai magana sai tace bayam inakallan yanda kikeyi da jiki gabadaya shawara da basir sun kamaki, shiyasa ko makaranta bakya iya zuwa tace hmmm.
Yau saura sati 1 biki haka kuma yau ne sarki ya kira salman da daddare suka zauna a turakarsa, sunyi shiru na wasu lokutan sannan sarki ya nisa yace salman menene matsayina agunka? Salman ya d'ago da mamaki yace Abba yazaka tambayi 'da matsayin uba a gareshi? yacigaba Abba bani da kamarka aduniya, sarki yai shiru can yace nasani salman sai dai inasan intunatar dakaine yanda kakejin matsayin na agunka nima haka nakejin matsayinka aguna.
Salman yai kasa dakai idansa ya kad'a yai jaa, Sarki yacigaba salman na maka mata ina fatan kuma zakamin biyaya a matsayina na wanda bakada kamarsa, cikin kid'ima salman yad'ago ya kalli sarki yace Abba mekake nufi da mata? Sarki yace eh salman wannan shine my first and last request to u a matsayina na mahaifinka, salman bakinsa yashiha rawa kanshi yafara zafi samun kanshi yai dacewa bakomai Abba, sarki ya saki murmushi yace nasank sarai bazaka bani kunya ba.
Salman yai kasa dakai, sarki yace gobe ka shirya Mannir ya rakaka yace a'a nikadai zani, sarki yace a'a ko ishaq to kad'auka yacd zanduba, harya mike sarki yace nan da kwana 6 za'a d'aura auren ragowar sha'anin biki sai ta tare za'ayi tunda ba hali garesu ba, haushi yakamashi talakace ma kenan? yace da wuri haka? Abba yace mezamu jira salman? Kannanka fa sunyi aure yai murmushin yake tare da mikewa.
Salma kam tanata sharar dakuna dan yau tun safe 'yan gidan suka tafi gidan baffanta, tagama da d'akuna tashiga falon Abba ta share sannan tad'auko tsinma ta fara goge_goge tazo goge gun tv taga invitation Cike da mamaki tad'aga dan ganin auran wa za'ayi? Mamaki ya kamata ganin sunanta daro_daro wai ana gayyatar walimar bikinta ranar juma'a da misalin karfe 4, takalla dakyau basunan namiji, tace mekenan? Badai yaya kamal bane zai dawo akaki fad'aminπ¬.
Jitai ana kwamkwasa kofa tafi to dasauri makocinsu ne tagaidashi yace babankine yakirani wai inkawo miki waya zai kira tace to.
Basu dadeba Abba yakira tad'aga yace salmah kiyi hakuri naso in nadawo nafad'amiki wata muhimmiyar magana sai dai I am too late, tace na me fa? Abba yace ki shirya zakiyi bako sannan dan Allah inhar kinsan darajata karki wulakantamin bako, da mamaki tace to amma bakon guna zaizo? Yace eh ki tambatar kin shirya sannan karki manta karki wulakantashi indai......ta katseshi da sauri to Abba najiπ.
Yace kin yarda dani aiko? Tace in banyarda da Abba na ba dawa zan yarda yace good dan haka kitaimakeni karnaji kunya nida yayana tace Abba karka damu, nan sukai sallama.....
Hmmmmmπ±
βββββββ
π₯ *NI DA PRINCE*π₯
βββββββ
*NA AYUSHER MOHD*
NO.9β£
Wanka salma ta shiga bayan tagama komai ta shirya cikin less d'inta na sallah haka kawai ta kosa taga bakon da Abbanta yake magana.
Salman ma ya shirya cikin kayansu na sarauta shida bawanshi suka fito dakuma driver, su biyu suna gaba shikuma yana baya rike da waya yana dane_dane, sam bai kula da inda suke shigaba dan driver dashi akazo ganin gidan tun farkon zancen auran, salman jin ana jugub_jugub a mota yasa ya dago kai, cikim tsananin mamaki yake kallan dan lokon da suke shiga, cike da mamaki ya kalli driver nasa yasa mamman ina kake kaini? Yace yalab'ai kayi hakuri mun kusa zuwa, cikin b'acin rai yace Mun kusa zuwa inaπ‘? Mamman yace gidan matar taka, salman da sauri ya juya baya tacikin glass yana kara kallan unguwar yace anan unguwar take? Yace eh tare dayin parking awani karamin gida salman yace me kenan? Yace an iso ga gidan nan, ya nuna wani karamin gida mai kofa karama salman yashiga yin wata dariya mai karfi, wanda hakan yasa suka razana bawan yace Ranka ya dade menene?salman yace bakuda hankali ne kuka kawoni nan? Mamman yace yallabai ai.....da karfi salman ya katsesu yace kuyi gaggawar fitar dani daga unguwarnan kafin kwalara takamani, mamman yace yallabai bakaga matar taka ba ai, yace wace mata kuma? Nace ku fita dani ko? Bawan yace to yallabai amma bari in ajiye mata sakon da sarki yabada yace aikin banza, ka fita ka kaimata inyaso ka taho daga baya yace yahkri yallabai ajiyewa kawai zanyi intaho yace komadai meye to kayi saurin dawowa inka wuce minti 5 tafiya zamuyi dasauri yace to yallabai.
Boot din motar ya bude ya dauko manyan jakukuna guda 3 ya nufi gidan ya kwankwasa ciki sauri salma ta bude, sanye take da hijab amma batasa nikaf ba, kallanta tare da sakin baki, tadaure ganin kayan fadawa ajikinsa tace sannu? cikin in_in na yacs yauwa dan Allah hajiya salma nanan? Tadan kalleshi da mamaki tace nice salma tafad'a tare da nuna kanta, yace hmm gashi ance inkawo miki tace ni kuma? Yace eh kiyi hakuri ya shirya zuwa kuma sai wani uzuri yataso mai, tace wafaπ€?Zaiyi magana yaji anmai horn dasauri yajuya yace eh, tabishi da kallo tare da cewa shine bakon Abban? Sai kuma ta d'an daga kafada tare da kallan waje can taga motar ta kulle tad'au jakukunan ta shiga ciki tare da ajiyewa a falon Abba takoma d'aki ta kwanta, tunani take me katin bikin nan yake nufi?
Bafaden kam na shiga mota yai ajiyar zuciya tare da cewa kai yallabai kayi sa'a wannan ita kad'ai ma kyanta ai ya isa ka wuni kana kallanta, salman ko kallanshi bai ba asari ma ranshi ne yakara b'aci.
Sanda yana yaro mahaifiyarsa ta rasu, matan babansa basanshi sukeba haka 'yan uwansa, sannan yanzu matar dazai aurama maimakon abarshi yasamu wacce zataso shi shima yasota amma sai abashi auran kara buta? Lalai zai d'au mataki bayan auran nan.
Salma kam duk abin duniya ya dameta tanajin motsin Abba ta mike da sauri taje ta gaidashi ya amsa tare da cewa kinga bakon? Tace eh wani bafadene yace wanda zaizo din wani uzuri ya hanashi zuwa, Abba yace tohπ³? Yaza'ai haka? Tace gashi wanda yazo ya ajiye, Abba yace toh da alama uzurin mai karfine tunda ansanar dani ya fito daga gida, salma tace Abba katin can kamar na biki, Abba yace salma matso nan ta matso kusa dashi tana murmushi yace ki nutsu zan fad'a miki wata magana mai tace to Abba.
Yace dani da yayana mun yanke hukunci yi miki aure tad'ago da mamaki tace aure kuma? Yace nasanki salma yarinyace mai biyayya kadaki bani kunya, idanta ya ciko da kwalla tace Abba yaya kamal fa? Yace salma kibar zancen kamal dan mahaifinshine yafara ansar maganar auran, tai shiru zuciyarta sai bigawa take, yace wannan juma'ar za'ayi yini da d'aurin aure da daddare akaiki saidai bansan koda wani abu dazakuyi keda kawayenki ba, tace Abba juma'a?yace eh salma kada ki manta ni mahaifin kene bazan tabayin abinda zai cutar dake ba sannan inaji ajikina auran nan alheri ne.
Hawaye take sosai yace salma Allah yamiki albarka ta runtse idanta da karfi meke shirin faruwa da ita? Mafarkin datai dama na rabuwa da kamal ne?ππ.
Abba yace bazaki tambayi sunan mijin ba? Tace basai naji ba Abba tunda kun amince dashi ai shikenan yai murmushi tausayinta yakeji sosai.
Mikewa tai tashiga d'aki ta hau kuka, umma najinta amma batako shigo dakin ba ga batare suka dawo da goggo ba ta dawo ba.
Yau laraba gida ya fara cika salma kam na kwance ba lafiya sai dai hakan baisa an daina hidima ba, tun safe aka kwashi 'yan uwan umma da Abba suka tafi gidan mustafa acan za'a anshi lefe.
Salman zaune a gaban sarki, mai martaba yace za'a kwashe kayan bangarenka a sake wasu ko kana bukatar wani abun? Salman yace a'a duk yanda kuka gani, sarki yace inafatan kaje gun yarinyar kaji ko tana bukatar wani abun na biki? Salman yaji gabansa ya fad'I amma yad'aure yace tace bata bukatar komaI, sarki yace zancen banza kenan kai bakasan kawaici ba? Ko kataba ganin inda amarya tace bata bukatar kudi? Salman yai kasa dakai yace zan aika mata wani abun, sarki yace dakanka zaka koma, salman yadaure yace to Abba.
Lefen da aka kai sai daya tsorata duk yan uwan dasukaje, mamakin irin kayan da aka zuba suke, kamar ba'a talauci a duniya? Kanwar maman salma kam kasa jurewa tai tace kai JAMA'A kayan nan ai sunyi yawa, zainab tace haba hajiya bakomai ai nan kowa yashiga jinjina wa salma lalai kam tagama warkewa, dan gidan sarki? Hmmm.
Zeena kam zaune kawai take amma sam ranta badadi yama za'ayi ace salman guda a aura masa yarinyar da iyayenta basufi bayin gidansu baπ‘ nan suka ajiye kudin dinkin amarya dana kwalliya, dubu dari biyu mamaki yakama mutane nan aka shiga gulma daga gani Abba saida 'yarsa yai inba haka ba wannan kudi da kaya haka? Shiyasa ma bikin ba'a wani ja shi ba, sudai 'yan kawo lefe nan suka tafi suma suna gulma.
A gidan akabar kayan dan kamwar maman salma tace in aka kai kayan can gulma yawa zatai, nan suka debi d'inkakun kaya a karamar jaka suka fita.
Salma na kwance zazzabin jikinta yafara raguwar dan bacci ya d'auketa taji guda a saitin kunnenta da sauri ta mike a zabure, dangin mamanta ne suke guda, wata daga cikinsu tace kai yarinya tayi goshi irin wannan al'amura haka? Salma kam kallansu kawai takeyi Asabe kanwar mamansu tace tashi kiyi wanka dalla kinwani zauna kamar wacce za'a kaita gidan marii, salma tace nifa.....Asabe tace so kike kibamu kunya?kin tashi ko sai na miki wanka dakaina? Salma ta mike tare da turo baki tai waje, nan aka shiga guda.
Suna zaune ita da kawayenta 'yan uwa, sun sata agaba suna tsokana idanta duk ya cika da kwalla, Asabe tazo tace wai ma taci abinci? Sukace anya kuwa? Nan ta kama hannun salma tai dakin umma da ita tasa aka siyo maltina da madarar ruwa ta juye a kofi tace kafa kai? Salma tace nifa banajin yunwaβΉ tace kin kafa kai kosai na mareki? Nan salma ta amsa tana sha tana kuka inta tuno kamal sai taji kamar ta kwalla ihu.
Ran Alhamis da safe gida ya cika taf salma na kwance zazzabi yadawo sabo, jin gobe za'a d'aura aure kuma akaita, wank yaro ne yai sallama yace wai ana sallama da salma, Asabe ta shigo d'akin tace tashi kiji inaji angon ne salma ta hade rai takuma ki tashi, asabe tace kin tashi ko kuwa? Salma ta mike ta yayimi hijabin sallarta ta zura tai waje Asabe na kiranta amma ina hartakai kofa, zuciyarta taf take da masifa, sai dai me? Tana zuwa taga wannan bafaden na rannan, yana ganinta ya zube a kasa yashiga jera gaisuwa ita abin ma mamaki ya bata dakyar tace menene hakan? Yana tsugunne ya miko mata envelope takalleshi tace namiye? Yace aikoni akai inkawo miki, tace inji wa fa? Yace mai gidana, tace ina nasanshi?yace wanda zaki aurafa? Sai yanzu ta gane, haushi ya isheta tai tsaki tace kamaidamai kudinsa kace bana bukatar wannan, in yanaso ya birgeni to ya......tunowa tai dakalmar mahaifinta dayace nasani bazaki bani kunya ba, idanta ya ciko da kwalla tace ka maidamai kudinsa bana bukata tana fad'a tai ciki da sauri.
Tana shiga kowa ya shiga kallanta ana tsokana, wato dan rashin hakuri shida za'a kaimasa ke gobe shine sai daya aiko aga lafiyarki?haushi ya kamata ko kulasu batai ba tai d'aki ta shiga bargo tasaki kuka.
Salma kam hidimarsa yake kamar ba aurensa za'ayi ba su Amir ma abakin mannir sukaji zancen auren.
Yau juma'a tun safe gida ya cika makil, salma kam tana d'akin goggo a kwance, Abba ne ya shigo tana kwance idanta duk ya kumbura, ahankali yakalleta tare da zama kusa da ita.
Idanunta ta bude ganin Abba yasa ta kakaro murmushi tace Abba, tafad'a ta a kokarin mikewa hannu yasa a kafad'arta yace yi kwanciyarki salma, ta kwanta tare da yin shiru, yace salma ni najamiki ciwon nan ko? Tace a'a Abba, yace nasani salma kiyi hakuri laifinane dana bari yaya ya amsa tun farkon maganar, dasauri tace haba Abba ai nasan dan kun isa danine yasa kuka amsa, yace to meya saki zazzabi? Aranta tace ko mijin fa bansani ba? Nadaisan yana da hadi da gidan saraura tunda taji 'yan uwa nazancen, sai kuma bafaden nan data gani, amma afili tace cutace kawai, Abba yace salma Allah yamiki Albarka, da izinin Allab bazakiyi danasanin wannan auran ba, tai murmushi tare da cewa yaya kamal ya sani? Abba yace ai kamal sam ko babansa yakirashi baya d'agawa bamusan me yake tunani ba, tai shiru.....
Abba yace da daddare za'a kaiki nasani ke yarinyace tagari amma gidan dazaki sai kinyi hakuri, tace wani iri ne? Yacr gidan sarauta tad'an juya kai kodai d'an gidan waziri zata aura? Abba dakanshi yasa aka kawo mata koko da kosai taci.
Auren in anyi sallar juma'a ne hakan yasa Massallacin gidan sarki ya cika taf da mutane, manyan mutane na sarauta da kuma na milki.
Salman na kwance a d'aki yana sharar baccinsa, sai nemanshi akeyi, najib ne ya shigo dakin kamar wasa dan baiyi tunanin zai ganshi anan ba,mamaki ya kamashi ganin salman daI_dai akan gado yana bacci karasawa yai kusa dashi tare da tabashi, cikin abin bacci salman ya bude ido, Najib yace prince me kakeyi hakan? Salman yace don't u see? Najib yace anacan ana nemanka amma kana nan kana bacciπ³? Salman yace oh!!! Lokacin auran nasu yayi ne? Yafad'a tare da duba agoggon bango na d'akin, najib yace auransu ko auranka? Salman yai tsaki yace ni wannan shirman auran badamuna yai ba yarinyarce koma wacece kawai ina tausayinta, sannan ina tausayin kaina dan za'asani sharing din daki da wata kucakaπ‘ ko dayake servant zansamu, Najib yace salman kasan me kake fad'a kuwa? Yace malam kyaleni, najib yace naji amma tashi ka shirya kafin ran mai martaba ya baci, salman ya mike yasaki kwafa irin ta muguntarnan.
By Ayusher Mohdπ
[10/16, 11:17 AM] βͺ+234 803 681 7247β¬: βββββββ
π₯ *NI DA PRINCE*π₯
βββββββ
*NA AYUSHER MOHD*
NO.1β£1β£
Haka salman yashirya cikin dakakun kayan sarauta da Mai martaba ya aikomai dashi, shi kanshi yasan yayi kyau najib sai kodashi yake, yai dan karamin tsaki yace I wish wannan auran da budurwar danakeso akeyi,amma meye amfanin kwalliyar? Najib yace zaka fara ko? Dan Allah kazo mu wuce, turarensa ya fesa sannan yasa hula da takalmi ya fito cikin kasaitarsa.
Tunda ya fito bayi da 'yan uwa kemai sannu da Allah yasanya alkairi amma kasaita da jin kai irin na salman ba wanda ya amsawa sai najib ne yashiga amsawa.
Yana zuwa hanyar fada wasu bayi sukazo suka kewayeshi yace kun fara ko? Najib yace wad'annan fa? Salman yace ai aiki yaganka dan hakannan zasuyi tabinmu har agama, najib yace lalai kace alamace ta ango ya taho, salman ya juya kai ba tare dayai magana ba.
Guri yacika sosai su Abba kam suna wani guri da aka ware musu, tsoro ya fara kama Abba shikanshi yafara tunanin kodai saida 'yarsa yai?.
Salman haka yai ta ratsawa cikin manyan mutane suna gaisawa, basu dade ba aka shiga huduba ta sallar juma'a, bayan anyi sallah ne aka d'aura auran *SALMAN DA SALMA* akan sadaki dubu hamsin, dan Abba yace sadaki kad'an yafi daraja a aure duk yanda sukaso ko dari abada amma yaki yace hamsin ya isa hakan yasa aka hakura aka bada hamsin.
Salman kam baimasan an d'aura auran ba yana waje suna hira da Amir da Najib sai dayaji masu busa da kirari sun matso kusa dashi sunayi nan fa mutane suka zagayeshi, haushi duk ya isheshi jin wai sunan matar salma, wato salman da salma kenanπ‘? Inama ace wacce yakeso ne take da wannan sunan kuma sukai aure? Da baisan irin kyautar dazaiyi ba yau.
Najib ne yaja hannun salman yakaishi gunsu Abba, har kasa salman ya tsugunna yagaidasu, Mustafa yace
Showing 6001 words to 9000 words out of 36779 words

[10/16, 11:16 AM] βͺ+234 803 681 7247β¬: βββββββ
π₯ *NI DA PRINCE*π₯
βββββββ
*NA AYUSHER MOHD*
NO.1β£0β£

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3 Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13