Allah yau kam duk addu'arta ta salman ce, bayan ta idar ta mike tai kitchen.



Kitchen din ta shiga dubawa, taga ba kayan abinci sai wasu ledoji akan dinning nan takarasa ta bude, take away ne, da alama salman dazu dasu ya shigo ta bude d'ayar ledar, kaza ce da dankali, sai dayar kuma lemo.


A hankali tadau ledojin takarasa kitchen ta dauko plates tafara wankewa, salman ya karaso inda take yasa hannu a kugunta tare da turo kansa ta wuyanta, yace beauty me kike? A ranta tace beauty? Ta juyo ta kalleshi da mamaki kafin tai magana ya manna mata kiss a kumatu, yace ba dream bane😉 murmushi tasaki sannan ta maida kanta gun wanke_wanken, tace andaina stubborn d'in? Kara kankameta yai yace sosai ma😊 ta turo baki ta juyo ta kalleshi tace ba wani bayan a wayarka haka aka sa? Yace oh ashe fa hakane, shan yace wait......kefa? Dasauri ta maida kanta tace umm nikam dama d'azu da abinci kataho? Baka fad'amin ba? Ya kwanta a bayanta yace inafa na tuna🤔? Ta gama wanke wanken ta goge dinning d'in sannan ta jera ta kalleshi tace abinci, yazauna tare da kallanta, itama tazo ta zauna a kujerar kusa dashi, ta zubamai abincin, nan suka fara ci,sai dai insuka had'a ido sai duk suyi murmushi, sun gama suka mike, salman ya kalli yanda take d'ingisa kafa, karasowa yai inda take kawai sai jitai ya d'agata da sauri takalleshi 😳 Ya juya kai tare da cewa tunda nina saki d'ingishi I have to take responsibility, tai murmushi tare da cewa ahh ni kunya nakeji🙈 ya fara tafiya tare da cewa toh yaza'ayi? Gashi nikima banasan mace mai kunya 🤔 dasauri ta bude ido, tace naa daina, dariya yasa tare da zama akan kujerar da ita, yakalleta yace wai daga fitata kikai duk wannan aikin?



Tace yayi yawa ne? Ko tayani zakai? Ya kalleta yace ahh sai dai inmiki sannu dan inaji tunda nake ban tab'a rike tsintsiya ba bare shara, salma tace na sani ai basai an kara sanar dani ba☹ ya ja kuncinta kad'an yace umm haka nakeso, tace bafa kayan abinci? Yace toko muje a siyo? Nikaina ina kwad'ayin cin abincinki, tace in kuma ba dadi fa? Yace anya kuwa? Bayan inaji ajikina ta iya? Salma ta mike daga cinyarsa tace yallabai muje? Tafad'a tare da kallansa, salman ya kalleta tare da had'e rai, tace menene kuma? Yace waye yallaban? Tace bafa suna bane☹kawai fad'a nai yanzu, yace au sannan ya mike yai gaba tabi bayanshi da kallo tace oh ni.



Sun shiga mota sun zauna salman ya d'au waya tare da yin dialling sai dai salma dake zaune taji wayarta na ringing awajen radio ta ajiye wayar a tare suka kalli wayar da salman sai dai me? *My Prince* yaga ya fito a jikin wayar, kallansa tai tare da saurin d'auke wayarta, yai murmushi tare da kunna motar.





Sunyi siyayya sannan suka koma gida, a falo suka zauna salman yakalli salma yace jikin fa? Tace da sauki, salman ya sauko kasa sannan yakalli salma dake kan kujera ya miko mata hannunshi, kallansa tai sannan ta mika mai nata,tare da sauka in da yake, sunzauna daf da juna dan rabin jikinta ma a jikinsa yake, hannu yasa ya kwanto da kanta jikinsa, ta gyara kwanciyar tare da lumshe ido, salman cikin magana mai rad'a yace baza'a fad'amin sunan nawa ba? Ta kara shigewa jikinshi, yai gyaran murya yace ahh nikam bansan mace mai kunya, salma tai shiru, ahankali yaji tace my prince🙈 yai murmushi tace ahh nikam banjiba🤔 tad'ago tace Allah kaji☹kiss ya manna mata abaki yace beauty daga yanzu kid'inga kirana haka, tace naam😳? Yace me? Bakyaso? Dasauri tace a'a bafa haka nake nufi ba, yace to me kike nufi? Tace sai dai in muna mu biyu, yace banyarda ba to in muna cikin mutane sai kice salman? Tace ahh ni? Yace to me zakice? Tace to ai in a cikin mutane ne bana fad'ar suna, yace ohh sai kice kai? Tace 🙊 ni? Ban isa ba, salman ya kwantar da kansa akan kujera yace shikenan.



Murmushi tai tare da sako fuskarta inda kansa yake tace zan d'inga fad'a kaifa? Yace wa? Ni? Ke kina tunanin ni zan kasa yin abinda naso? Tace ina fa? Rungumeta yai, salma tai ajiyar zuciya tace prince? Yace umm tace ban iya san abu ba, ina tsoron kar sanka yamin yawa in rasa ya zanyi? Kara kankameta yai dadi yakeji har ransa yace nabada dama kisoni harsai zuciyarki takai yanda bazaki iya rabuwa dani ba, tace I am afraid😞 ahankali ya d'agota yace of? Tace you, yace me? Tace eh, kara rungumeta yai baice komai ba, hawayen dasuka taru a idanta ne suka zubo.



By _```AYUSHER MOHD```_📚
Showing 36001 words to 36779 words out of 36779 words