wato baki da lafiya amma bazaki bar fitsara ba ko? Dakyar ta ture hannunshi tace bafa ni da lafiya😞tai maganar cikin shagwaba, salman yai dariya tare da bud'e drawer yace mike kisha magani, tace uhm uhm yace kin tashi ko kuwa? Ta juya baya tace ni ba ruwana dakai, yai murmushi yace naji amma tashi kisha magani, ganin taki tashi yasa ya d'agata tare da miko mata magani ta amsa sannan yabata ruwa tasha, yakalleta zai yi magana yaji ana knocking ya kalleta tafara kokarin tashi, yace let me check, yai hanyar kofa.




Yana budewa yaga farha, da mamaki ya kalleta yace farha ya akai? Salma dake zaune tanajin sunan taji gabanta ya fad'I, farha ta kalli salman tace yaya so nake ka rakani gidan dangin dad d'ina, salman yace bazaki iya zuwa ke kad'ai ba? Tace yaya kaima kasani fa😰 tafad'a tare da share kwalla, salman yace shikenan amma yakamata ki saba dasu farha, salma dake kwance ta mike, fita zasuyi tare? Kafin ta nemo amsar tambayoyinta taji salman yace bari nad'auko key, salma dake kwance kamar tai ihu.

Salman ya shigo d'akin ya kalli salma yace zan fita, salma ta sauko daga kan gadon tace nima zani🙄salman ya kalleta yace ina? Tace nagani da kwanciya so nake in fita☹salman yai wata dariya yace bafa ki da lafiya? Tace ai na ware, yace don't tell me kishi kike🤔 dasauri ta juya tace wa? Ni? Inji wa? Yace to meye na mikewa kice xaki fita? Tace bana fad'amaba😞 yace shikenan muje tai murmushi ta gyara fuskarta sannan ta yafa mayafinta.


Farha na zaune tana auna yau intaja salman sai 11, motsin kofa taji, ta mike da sauri sai dai me? Salma tagani da salman😳cikin jin haushi da kishi tace yaya meye hakan? Salman yace me? Tace yanaga in_law? Tafad'a tana kallan salma, ya hade rai yace kin manta matatace? Tana da right?farha tace ba haka nake nufi ba amma....yace inzaki muje in bazaki ba to.


Farha ta kalli salma dake murmushi jitai kamar tasa ihu, salman yace ke nake jira, tace zani mana yaya😕 yace muje to, nan sukai waje.


Salman ya bude mota ya shiga ga mamakin salma gani tai farha tashige gaba, tsayawa tai tana kallan ikon Allah, jitai salman yace bazaki shigo ba? Salma ta makama farha harara tare da bud'e baya tunani take ko ta jawota?sai dai akwai fadawa a gun, hakan yasa ta daure ta shiga ba.



Zama tai ta jingina da jikin kujera, ta hade rai, farha ta kalli salman tace yaya kasan me?yace a'a tace kullum sai naje shagon nan dakake siyomim ice_cream, salman yai murmushi yace amma yanzu kindaina shan ice_cream sosai ko? Tace eh mana tafiyarka tasa na rage dolena, tai maganar cikin wani salo.


Salma kamar ta mutu, ta kalli salman taga yana murmushi jitake kakar ta fita daga motar, salman ya kalli salma ta mirror yace jikin ne? dakin kwanta, ta kalleshi tare da daurewa ta saki murmushi tace muna tare a mota ina kallon gari inafa zan kwanta? Salman ya kalleta cike da mamaki, amma sai ya danne yai murmushi, farha zatai magana salma tai saurin cewa nikam a bayan nan bana ganin komai sosai,salman yace meyasa to baki zauna a gaba ba? Ta harari farha tace kanwata ta rigani shiga yazanyi? Salman ya kalli farha wacce kalaman salma sunzo mata wuya, wai kanwa? Tama raina mata hankali, tasani sarai ta girmeta, salman yace farha fa ta girmeki duk da bansani ba, salma tai murmushi tace ai ni matar wanta ce ko? Tafad'a tare da dafa farha, murmushin yake tai tace haka ne, salman yai murmushi yace lalai, salma aranta tace nadaina yarda kima min iskanci, ke ba kishiyata ba bare ince.....



Sun iso wani makeken gida, salman ya isa gun parking sannan suka fita, salma ta zauna a mota, salman dake waje ya leko yace me kike? Tace naga bataso inzo, kuje kawai, salman yace wasa take kamar baki santa ba? Tace bansanta ba😏 yace in barki anan kike nufi, tace eh, salman ya fito tare da kallan farha yace muje ko? Tace in_law fa? Yace muje kawai, harsun yi gaba salma tai tunani yanzu tana nan in farha ta fara ma salman kisisina fa? Dasauri ta mike ta fito.


Sun kusa shiga bangaren farha ta hango salma da mamaki tace yayana ka ga? Salman ya tsaya har ta iso, ya kalleta baice komai ba, tace nafasa zaman motar, ganinai gwara muje nima nagaidasu, salman yai murmushi yace kin kyauta dan kuwa har biki sunzo, itama murmushi tai tace kanwata muje 😊 farha ta harareta tace to.



Ishaq ne zaune kusa da fulani, ya kalleta yace umma dagaske kike salmata ita taje gun sarki ta kare salman? Fulani tace
Wani zancen banza
Ne wannan salmata?baka da tunani ko? In wani ya jika fa?yace wake zancen wannan kina ganin alama ne na tafara san salman bayan ni yakamata taso? Fulani taI tsaki tace shiyasa haryanzu Abbanka bai daina tunanin salman zai gaje shi ba dan sam kai baka san rayuwa ba, ishaq ya mike cikin b'acin rai yace nafad'amiki kidaina had'ani da wannan yaron tun ina karami, ke komai sai kice salman yafini😡ya juya azuciye yai waje, tsaki tai tace tunda nake bantaba ganin salman ya nuna bacin ransa a waje ba ko ran nasa ya baci amma wannan...?I wish ishaq ne salman😕...




Nikam Ayusher dariya fulani ta bani, nace stop dreaming😂😂




By Ayusher Mohd📚


☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.3⃣4⃣

Suna isa farha ta dana kararawa, ba'afi 2min ba akazo aka bude, daga ganin wace ta bude mai aiki ce ta gaishesu tare da tambaya, salman yace hajiyar nanan? Tace a'a ta fita sai mami dasauri farha tace a'a yaya ma dawo wata ran, ya kalleta yace Baffan fa? Tace tare suka fita da hajiyar, ya kalli farha tace a'a yaya kasan halin mamin nan, muje kawai madawo daga baya.



Juyawa yai batare dayace komai ba, salma ta kallesu aranta tace mekenan? Itama dai batai maganar ba har suka isa mota, farha ta bude gaba zata shiga salma ta rike kofar tace kanwata kin manta? Farha ta mata wani kallo salma itama ta harare ta, tunani take wanda da kishiyarta ce yazatai?itama farha tunani take lalai inta auri salman sai ta gyarama salma zama, salman ne ya kallesu yace ke farha ki koma baya mana dolene sai kinzauna anan? Tace yaya ni nafisan zama kusa dakai☹salma tasa dariya tace me? Salman yai tsaki yace bansan iskanci ki wuce baya itaba matata bace? Farha ta bude baya tana turo baki, salma ta shiga tare da hade rai, salman yaja mota, sun dade suna tafiya a haka kafin salman yace kinga gari? Salma ta daure fuska tace hm yace ke kuma wannan cin maganin fa?ta kara hade rai yace jikin ne? Yafada tare dayin gefen titi, salma batai magana ba,parking yai tarr dasa hannunsa a goshinta, ya kalleta tare da hararar wasa yace ai bama zazzabin yanzu, ta kalleshi batare data ce komai ba, farha jitai kamar ta shake salma ganin sai wani hade rai take shikuma yana wani lallabata bayan ita akama abu amma bai kula ba😠.



Yafara tuki takalleshi tace tunani nake yace name? Tace mun fito bamu tambaya ba kar yazama wani abun, salman yai tsaki yace ki daina damun kanki da wad'an nan abubuwan,ace mata da miji basu isa su fita ba sai sun tambaya? Har kasan ran salma taji dadin mata da mijin dayace amma a fili tace amma ai dokace☹ yace I don't care about that, yafad'a tare da kallan titi, farha kamar tai kuka in ta kallesu.



Sun isa gida suka fito dukansu, sai dai suna sauka ishaq ya karaso gun, cikin bacin rai ya kalli salman yace kaifa bakada mutunci, salman yai murmushi yace badai sai yanzu kasani ba😉 ishaq yace mu bar nan muje bangarenka dan yau bazan kyaleka ba, salman yai wani murmushi yace ahhh I hope bazaka canza kudirinka ba😏.


Sun isa bangaren su
Farha ta kalli ishaq tace ya.....wata harara ya maka mata yace dalla fita daga nan, a zuciye ta juya tana kunkuni, ishaq ya kalli salman yace kaji asara wlh dazakasa baiwar Allah karya akan wata lalata dakake, salman yace ahh badai baiwar Allah daka fada tana nufin matata ba?salma da sauri tai hanyar kitchen, ishaq yace ita mana to wlh bazan.....salman ya katseshi yace matata? Ba matar ishaq ba ko? Nad'auka haa zancen yake? Ishaq yai shiru yana huci, salman yai murmushi yace yaya ina tausayin ka dasan shiga zancen ma'aurata😞 yazanyi in kaje kai baban laifi🙊? Ishaq yagama kuluwa jiyake kamar ya mutu, salma dake kitchen tai murmushi tace amma salman😀.

A hankali salma ta fito dauke da ruwa da lemo, sannan ta kalli ishaq tace kazauna😊 wani sanyi ya kamashi nan yazauna yana kallanta kamar ya had'iyeta, salman ya kalli ishaq ganin yanda yake kallanta yasa yace yaya kasan me? Yace me😡? Yace akwai wani kare da ya takuramin, bayan nasai wani abu mai kyau sai na kua karan yasamin ido, burinshi yaga ya d'au abin nan, ishaq yace a ina karen yake? Salman yai murmushi yace kanaji? Yace eh, salman yace kasan menama karen? yace a'a, yace zuwa nai nasashi a kejin daba mai budeshi har karshen rayuwa🙂 ishaq ya tabe baki yace ka kyauta, nifa karnuka basumin ba, salma dake tsaye tasan lalai magana salman yake dankarawa ishaq amma mamakimta shine badai ishaq ne karan ba ko? Salman ya saki murmushi ganin ishaq baisan mema yace ba, yace yaya inkaje ka tambayi fulani labarin karen ita tasani ai, ishaq yace to tare da kallan salma.



Yana fita salman yai tsaki tare dayin d'aki dan yafarajin kansa na sarawa, dasauri ya had'iyi magani ya kwanta, salma ta shigo tare da zama kusa dashi tace labarin karen nan? Ya kalleta, tace badai dashi kake bako? Yai murmushi yace ashe kina gane maganar boye? Ta tabe baki tace me ka d'auken? Yace ummm bari muga....tasa hannu ta mintsineshi a ciki, hannun ya kama tare da jawota jikinsa yace umm ina tashi ramawa me kike tunani?ahankali tad'ago tace to ai kaid'in ne☹yace ni me? Tace wato bama kasan me ka d'aukeni ba🤔 habarta ya rike da hannu d'aya yafara juya fuskarta, yana cewa bari inga, ture hannun tai tare da mikewa, dasauri ya jawota, ta fad'a kanshi sunyi shiru na wani lokaci banda zuciyoyin biyu da suke bugawa, cikin wata irin murya salman yace haushi kikaji? A hankali itama tace um, wani sansanyan murmushi sukama juna yace bada wani abun na fad'aba, tace nasani yace then? Tace bantabaji kaba wani hakuri ba tunda nake, yace so?tace meyasa? Yace kawai, tace ummm nagane, yace bansan kid'inga zuwa inda kikasan ishaq na zuwa, in gurin fulanine kibari muje tare, tace y?yace kawai, ta tabe baki sannan tace to amma menene abu mekyau da kake magana d'azu? Yace u don't have to know tace shikenan😞naji.



Zaune suke akan dinning suna lunch, salma ta kalli salman tace bayan tafarnuwa meye bakaso?yace bangane ba? Aranta Tace banason wata tazo ta dinga nunamin tafini sanin mijina, tabude baki zatai magana taga salman na dariya, tace meye kuma😞 yace kedai zuba abinci, wato da farha kike ko? Tace mene? Yace wace zata nunamiki ta fiki sanina😉 dasauri ta rufe fuska dama yaji? Ahh kunya ya kamata,murmushi yai tare da matsowa kujerar kusa da ita, ahankali ya zare hannunta tai kasa dakai yace uhmm bari in tashi nama daina jin yunwar, dasauri ta rikeshi tace a'a muci dan Allah, yai murmushi tare da kallanta itama shita kalla, yamata alama da kai ta zubamai taI murmushi tare da jawo plate.........


Ummmmm nikam nace tunda abin ba tayi bari nai nan🏃🏼🏃🏼


By Ayusher Mohd📚



☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.3⃣5⃣


Ishaq zaune a kusa da fulani ya bata labarin kare, ranta ya baci ta mike a fusace tace kai amma kazama babban shashasha kana zaune salman ya gane kanama salma wani kallo, ishaq yace to sai me? Tsoranshi nake? Tace to kasan waye karen?

Ishaq yace bayace kinsan karen ba? Haushi ya kamata a fusace tace to kaine karen dakai yake banza, tafad'a tare dayin d'aki, ishaq ya mike yace ni? Nine kare? 😖😡 amma salman yagama cimin mutunci kuma wlh sai na hukuntashi sai yasan nidin kare mai cizo ne😡.






Salman kwance a d'akin najib yayi rigingine tare da dora hannunsa a a goshi, najib ya kalleshi tare da girgiza kai yace prince dagaske bazamu fitan ba? Salman yai shiru, najib yace prince wai menene?

Tun d'azu kazo kawai ka kwanta, salman ya mike da sauri yazauna akan gado yace najib, zo ka tab'ani kaji ko dai ina zazzabine? Najib ya matso tare da sa hannu a wuyansa, yace lafiyarka kalau🤔salman yace to meke nan? Najib yace wai me? Salman yace kai inaji gun likita na zani ina bukatar amsa, najib yace jikin ne?

Salman yai tsaki yace haka kawai tunda nafito nake tunanin salma sannan daga na rufe ido sai indinga hangota, gashi in muna tare in tai wani abun sai inga kamar ita kad'ai nake gani a duniya, abinda yafi damuna in ta matso kusa dani ko na matsa sai injo zuciyata na bugawa, najib baka tunanin yakamata inga likita? Najib ya kwashe da dariya harda rike ciki, salman ya hade rai tare da mikewa yace wani sabon iskanci ne wannan kuma?

Najib ya tsagaita yace salma dana d'auka kana masifar san farha me kenan? Salman yace insanta mana kamanta tare muka taso? Najib yace kundai shaku amma ba soyaya ba, salman yace bangane ba?

najib yace prince yanzu kafara soyayya bada ba ai😂salman yace bansan iskanci meye hakan? Najib yace ayya prince salma ta gama da zuciyarka indai har ka kai wannan stage din😀gaskiya ina tayata murna da alama ya kamata in kirata muyi party😬 yafad'a yana d'aukan wayarsa, salman daya tsaya kamar sanda yana nanata kalaman najin, ganin najib yad'au waya yasa ya fizge wayar yace wani iskanci kake hakan?

Najib yace abin murnane ai, salman yace ba wani soyaya so kake inka fad'amata tarainamin hankali😠najib yace kaifa matsalata dakai kenan, salman yace tashi mu fita, najib ya mike tare dacewa abokina ina tayaka murna😉, salman ya makamai harara yace kamanta, wannam d'in abun murnane kaifa bakada aikinyi😏.




Salma na zaune a falo rike da littafinta,ganin mutum tai agabanta tasauke littafin tare da kallan wacce ke gurin, farha ce sanye da riga da wando, salma ta mata wani kallo tace na sallama? Farha tace ina yayana?

salma tai wani murmushi tace menene? Farha tace meya dameki? Salma ta mike tare da d'aukan littafinta tace inkin fita ki rufe kofar ni nayi nan, farha tace kina nufin anan zaki barni😠?


Salma tace naga ba guna kika zo ba kuma Wanda kike nema bayannan kinga sai kijira a falo inkin gaji sai ki tafi ko? Farha tafara muzurai salma takalleta tare da tura kofar d'akin.



Tana shiga ta zauna akan gado ranta duk a bace tace what? Yayana😏? Tanaji farha ta fita tai tsaki tace yarinyar nan tama gama rainamin hankali.



Falo ta fito dan ta bar wayarta acan, sai dai me?
Muryar farha taji a waje da mamaki ta leka, salman taganj da farha akan kujerar gun suna hira, jitai kamar zata fashe dan kishi dakyar ta saisaita kanta ta fito wajen,salman tunda yaji motsi ya juya yaga salma ya zuba mata ido, yakasa d'aukewa, farha ta kalleshi tasa hannu ta taba hannunsa ya juyo tace yaya ina baka labarin skul, yace oh inaji, yafad'a tare da kallan gun da salma take, salma takaraso gun tace ashe kana nan? Salman yace eh yanzu na dawo, wani abun ne? Haushi yakama salma wai wani abun ne? Tahade rai tace ba wani abun🙄 tafad'a tare da juya,baisan sanda ya kama hannunta ba tad'an yi murmushin farin ciki sannan ta juyo, tace menene☹?



salman daya rasa mai zaice yace umm dama ce miki zan kid'aukan earphone d'ina, salma ta kalleshi sannan ta kalli farha datasaki murmushi ganin kallan da salma tamai yasan taji haushin maganar, fizge hannunta tai wtare da juyawa, salman ya kalleta sannan ya kalli farha yace nashiga ciki tace yayana ba.....kasa karasawa tai ganin yayi gaba, haushi ya isheta ta mike tai d'aki a fusace.





Salman na shiga d'aki yaga salma azaune akasa tad'aura kanta a gado, jikinsa yai sanyi, yakarasa gunta shima ya zauna a gefenta yasa kansa a jikin gadon yana facing d'inta, kallansa tai idanunta taf kwalla,yace haushi kikaji? Tace haushin me? Yace shikenan amma miye na tahowa? Tace mezan muku agun? Yai shiru tace kagani ko? Nasani ai, yace me kika sani?



Tasa hannu tashare kwallar data zubo mata tace shikenan, salman yasa hannunshi a kuncinta tare a shafa kanta yace bakisan komai ba, dan haka kiyi shiru, ta kalleshi sai dai yanda yake kallanta yasa takasa magana,shima kallanta yakeyi ahankali ya matso yakai bakinshi kan goshinta yai kissing, salma ta lumshe ido jitake zuciyarta kamar zata fashe, jawota yai ya rungumeta tsam ajikinsa tare da sakin wani nannauyan ajiyan zuciya, salma tai luf akirjin salman wata kwallar dadice ta zubo mata.......


Nikaina jinake kamar inyi kwallar amma ni ta bakin ciki dan can na hango farha a zuciye tayi d'aki tare da rufo kofa dakarfi da alama kuka zatai🤕😥

By Ayusher Mohd📚



☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.3⃣6⃣

Fulani zaune a kilisarta bakar maganar da salman ya fad'a wa d'anta ta dameta dayawa wata baiwa tasa ta kira mata ishaq ganin yau sam bai shigoba da alama shima haushin abinda fulani ta fad'a yake.


Salma ta shirya tsaf, dan salman ya fita makaranta kuma tafad'amai zataje gaida fulani, sun fito itada hanne, azahirin gaskiya gani take kamar bai kamata ace sai lokaci_lokaci take gaida fulani ba, ganin matan gidan kusan kullum sai sun gaidata, tana tsoron kar hakan yaja ma salman wani abun.




Sun isa bangaren, wata baiwa tace kishiga tana kilisarta,tace duk bayin su fita amma ke ai ba matsala, salma tace tom tare dayin hanyar.


Fulani zaune itada ishaq takalleshi tace wai haushi kaji? Yace umma ni narasa me kikeso inyi ki yabeni? Tace ina yabonka ishaq kawai banaso ne kadinga zama na karshe in aka had'aka da salman,ishaq yace nifa umma na tsani ganin yaron nan dan yana takuramin, daidai nan salma tazo shiga sai dai tasa hannu zatai knocking kofar taji fulani tace kodai musa amaidashi kasar waje? Ishaq yace ko? Tace eh mana ni kaina na tsani
Showing 30001 words to 33000 words out of 36779 words