ta saka hannu tana taba jikina.
"Sannu mamah na ji babu fever". Ta fada cike da kulawa.
Na murmusa kadan duk da idanuwana sun yi kozai kozai na ce "Da sauki sosai Amrah. Ina Dady?"
Ta ce "ya ce na taho aiki ya rike shi"
Na ce "Tom ki je ki samu wani abu ki ci, nasan kun yi sallah".
Ta mike ta ce "Bari na fara yin wanka."
Na bita da ido ina sake shaidar tsananin kamannin da take yi da Sahal. Hatta tsayinsa duk ta kwaso, tana aji hudu a sakandire yanzu.
Na yunkura na mike cikin k'arfin zuciya na fara zagaya dakina ina ta kokawa da sashin zuciyata da yake kalubalantar Babanta akan da Hawwa ya fita ya kashe mata kudin da suke nawa ne. Kudin da ba'a b'agas nake samunsa ba, sai na shafe kwanaki ashirin da biyar ina sammakon barin gidana duk sanyi, duk zafi ko damina, haka nan yini nake ina fama da alli da biro hadi da marking bayan bata lokaci wajen yin nazari tare da bitar yadda zan dinga koyarwa cikin hikima ta yadda dalibaina zasu fahimci darasin da kyau. Ba dan komai ba sai dan na tabbatar albashina halal ne. Sai ga shi duk wannan fadi tashin ina yi ne, wata tana ci a b'agas cikin dabara da hila.
"Tirkashi." Kalmar ta subuce mini ba tare da na shirya hakan ta faru ba.
Na cigaba da zagayen amma sai na tsinci kaina da ambaton "Rabbi inni lima anzalta ilaihi mini khairun fakeer!
Yi nake yi a fili tare da nufin na samu saukin matsalolin da suka dabaibaye zuciyata da tunanina.
Da yake alkawari ne na Ubangiji idan ka nemi taimakonsa cikin yarda da gasgata shine mai yi, zaka ga taimakonsa kuwa ta inda baka yi zato ba.
Sannu a hankali na ji saukin zuciyata dan haka sai na fita zuwa falo dan kada na cigaba da zama tunani da bakinciki su kassara ni.
Ina zama kuwa su Yaya Faruk suka shigo.
Farha da bata yarda ta girma ba, ta taho ta fada mini na d'agota na tsinci kaina da kallonta, irin kallon nan mai tsananin gaske. Gabadaya kammanin Yaya Sulaiman ne akan fuskarta, wadanda basu san shi ba, sai suce da ni take kama tunda babu shakka ni da shi kamarmu har ta b'aci.
Ta yi murmushin da irinsa Abida take yi ta ce "Mamah na fada miki bana son Alawiyya ta zo daukarmu!
Na jata jikina na ce "Ai ba ni da lafiya ne Farha"
Nan da nan ta ce "Oh sorry mahmah ya Jiki?"
Na amsa mata da ce wa " sauki."
Na ce "Maza je ki Yaya Amra ta watsa miki ruwa kafin ta fito tana dakinku."
Da sauri kuwa ta dauki jakarta ta yi daki nsu, sai lokacin na mayar da hankalina kan Faruk da yake tsaye na ce "Kaima ka je ka watsa ruwa ka kuma tabbatar ka fito kayan nan ka bazasu a baya. Idan ka dawo daga masallaci anjima ka hada da na Farha ka wanke muku, kasan Yaya Amra ta ce ta daina yi Maka wanki tunda ka mata rashin kunya."
Ya wuce yana kunkunin ta daina yi din mana. Tunda a washing machine ne Ai ya iya shima.
Har muka kammala dinner babu shi babu duriyarsa. Bai dawo ba sai karfe tara na dare.
A falo ya tarar da ni ya yi matukar kaduwa domin bai yi zaton zai ganni a falo ba.
Yara suka yi masa barka da dawowa san nan suka tafi suka kwanta domin mun riga mun sabar musu 9 suke kwnaciya duk dare.
Ya zauna daf da ni. Turarensa ya cika mini hanci.
Cikin nutsuwa ya ce "Ya jikinki?"
Murya babu amo na ce "Na warke"
Na tsananta kallonsa ganin haka ya shigo hannu rabbana. Hawaye ya cika mini kwarmin idona. Tabbas a wajen yarinyar nan ya shantake ya yi dare bayan ya gama kashe mata kudaden da yake mallakina ne, ni kuma ya bar ni ko oho duk da ya bar ni a yanayin na rashin lafiya da sukuni sosai.
*Alhamdulillah!*
*Mu je ga book 2.*.
*Book2&3 na kudine wanda za'a kammala cikin kwanakin k'alilan a Telegram da arewa.*
*Kunsan dai marubuciyar bata jan rai wannan karon ma ba zata ja muk rai ba.*
*Menene matsalar da ta tarwatsa ahalin su Bilkisu duk da irin k'arfaffen. zumuncin da suke gudanarwa?*
*Wacce irin rayuwa da sadaukarwaka ta yi da mijinta ne?*
*Dukkan karatun da kuka yi , bamu kutsa cikin danbarwa da rikitarikitan da suke cikin labarin ba*
*Sharar fage kawai muka yi*.
*Ku gyara zama zaku sha karatu cikin nutsuwa babu jan rai in sha Allah*
*Za ku yi nishadi, takaici, mamaki tare da alajabi cikin wannan labarin*
*Ku biyo Bilki sannu a hankali har zuwa lokacin da zata cigaba da hakaito mana labarinta yadda zare da abawa zasu warware mana*.
✍️✍️
Showing 42001 words to 42772 words out of 42772 words

*Ku biya 1k ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.
*Menene matsalar da ta tarwatsa ahalin su Bilkisu duk da irin k'arfaffen. zumuncin da suke gudanarwa?*
*Wacce irin rayuwa da sadaukarwaka ta yi da mijinta ne?*
*Dukkan karatun da kuka yi , bamu kutsa cikin danbarwa da rikitarikitan da suke cikin labarin ba*
*Sharar fage kawai muka yi*.
*Ku gyara zama zaku sha karatu cikin nutsuwa babu jan rai in sha Allah*
*Za ku yi nishadi, takaici, mamaki tare da alajabi cikin wannan labarin*
*Ku biyo Bilki sannu a hankali har zuwa lokacin da zata cigaba da hakaito mana labarinta yadda zare da abawa zasu warware mana*.
✍️✍️
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15