kallonsu batayi ba,bare tasan da zuwansu JABIR ne yace sannu MARIYA harara ta gallamai ta mik'e tayi bedroom d'inta .

AFRAH ko da maganar tafi k'arfinta wucewa tayi taje ta cire kayanta ta shiga wanka bayan ta fito ne JABIR ne yashigo ya d'auketa ya kwantar da ita a gado yafara sauya labari nikuma na fito na barmusu d'akin ganin suna harara ta.


Yaune JABIR ze koma d'akin MARIYA kwata kwata bayason tafiya yabar AFRAH ita kad'i .


Bayan sallahr isha,I misalin k'arfe tara na dare yashigo da sallamarshi MARIYA ko kallonshi batayi ba tashi tayi zata bar gurin dayake JABIR d'in ba kanwar lasa bane ya rik'ota ta fad'o jikinshi be nuna mata ta 6atamai rai na k'in zuwa duba AFRAH a hospital ba .

Cakul kuli yadiga yimata seda tayi ta dariya tukun ya barta".


Washe gari MARIYA ta ,tambayi JABIR anguwa tayimai k'aryar zataje gidan su duba momyn ta babu .

Bayan ya barta shiryawa tayi ta d'auki isashen kud'i shima JABIR d'in yabata dubu biyar tabawa momynta , tayi farinciki har ,rungume JABIR d'in tayi ta fice ta barshi a gurin yana shirin fita aiki.


Jamila ce takirawo ta a waya take tambayarta akan ta shirya ?eh tace mata kana ta d'auki hand bag d'inta ta fice a gidan tabar yara da mai ,aikin datasa aka kawo mata .


Samun jamila tayi kusada layinsu bakin titi suna nufa wanan karon bada driver sukatafi ba motar haya suka dauka akan ze kaisu ya dawo dasu .

Bayan sun isa cikin jejin suka duba babu ,boka babu dalilin shi se wasu mata suka gani suna tafiya cikin jejin daka gansu kaga yan gidan masu kud'i saboda sunfi JABIR kud'i shima JABIR d'in nada kud'i amma kana ganin kayan dake jikinsu ,seka rik'e baki .

Jamila ce tacewa MARIYA kodai muyiwa wa ,inan mutanen magana ko sunga boka anan gurin .


MARIYA ce tace dan Allah kiyi musu magana ko lokacin da sukazo sun ganshi, jamila ce ta k'arasa zuwa gurin matan guda biyu da a k'alla sun haifeta tace sanunku dayar ce tace yauwa barka jamila ce tace dan Allah ko kunga boka dayar ce da tunda jamila tazo batayi magana ba tace bokafa ya tashi kuma bamusan inda yanufa ba amma idan kunason aikin hatsabibin,bokan dake can gaba Ku biyomu can zamu tafi.......


*✍️mom Islam ce*🥰
[12/1, 6:31 AM] Zainab Abu: *🥀🥀ZAZZAFAR KISHI!!!🥀🥀.*
_labar me ɗauke da makirci cin amana da soyayya_




*NA*
*ZAINAB HABEEB.*
*MOM ISLAM*




*MARUBUCIYR*

*ZAINABU ABU*


*AND NOW*

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*


*page* 9_10


_____Binsu su ka dingayi cikin jejin da ba'ajin kukan kowa sai na tsintsaye can suka hango wani mutum yafito ya 6ace d'ayar matar ce ta dubi Jamila tace"kunga wanan bokan aikinshi babu yaudara ko kisa yanayi "MARIYA a tsorace tace a,a muk'arasa dai amma banda maganar kisa k'arasawa sukayi gani nayi sun juya baya suna tafiya da haka har suka iso gurin bokan yana zaune yana d'aga wani ganye me layoyi a jiki matanne suka fara zuwa bokan yadubesu kana yace ga wanan kusa mata a k'arkashin filo tana kwanciya se gawarta matar ce ta tsorata tace boka to idan akaga gawar layarfa " tuntsirewa yayi da mahaukaciyar dariya yace laya tamuce zamu d'auke abarmu suka tashi bayan sun ajiye mai kud'in jamila dajin haka tafara murmushi hak'ika wanan bokan bana wasa bane"

MARIYA ce ita da Jamila suka k'araso gurin bokan tun kafin su zauna zasu fara magana ya dakatar dasu "yace nasan meke tafe daku ya nuna MARIYA yace kishiya ce dake kuma bakison ta ,tana d'auke da ciki kuma namiji zata haifa" .

*nikuwa nace boka kasan gaibu*

MARIYA ce tace eh,hakane boka yasa dariya kana yace mekikeso ayi mata,ko a kasheta kokuma a samata warin ja6a kokuma a maidata mahaukaciya tabar garin "MARIYA ce ,tace banason a kasheta a turata jeji kokuma wani garin nidai burina a barni ,nida mijina " bokane yace angama kud'i ya yanke musu dubu ishirin bayan tabashi kud'inne yaciro wata tsuntsuwa a cikin wata bak'ar rijiyar dake gabanshi wurgata yayi sama tunda tsun tsuwarnan ta ,tafi bata dawo ba MARIYA tace boka inason arufewa kowa baki hatta minjin yazamo tunanina yakeyi"kuma azubar da cikin dake jikinta jamila ce ,tace a,a kar azubar gara abarta tasha wuya kinga ta hakane za,a d'auka cikin shege ne bokane yace mijinnan naki magani baya cinshi amma ga wanan kisamai a ruwan wanka ".

Kafin su tashi sukaga babu boka babu alamarshi a tsorace suka koma cikin jejin suka nufi bakin titi " bayan sun sami abin hawa jamila tace k'awas yau zanbiki ,inga inda shegiyar nan zata k'are MARIYA ce, tace dakin kyauta kuwa bayan sun biya hotel sunci abinci suka wuce gida samun AFRAH itada JABIR tayi suna kallo a TV ita kuma AFRAH na kan cinyarshi sallama sukayi kamar mutanen kirki amsawa yayi yana tambayar MARIYA cewar ya jikin momy da sauki tace fuskarta babu yabo ba fallasa "jamila ce ta gaida su AFRAH amsawa tayi daga nan jamila ta mik'e tadubi MARIYA tace wlh inajin fitsari MARIYA ce,tace muje inrakaki " bayan sun isa d'akinne jamila tadubi MARIYA tace naga haryanzu maganin befara aikiba MARIYA tace kwantarda hankalinki ai yau d'innan seta bar gidannan suna cikin haka suka jiyo ihu dagudu suka yo waje AFRAH suka hango ta fice dagudu JABIR yabita cikin tashin hankali yakasa cimmata mutane yagani sunata wucewa yana kutemakamin dan Allah babu wanda ya kulashi shikuwa se kuka yakeyi yana gudu amma babu AFRAH babu alamarta ........✍️✍️✍️




Mom Islam ce ✍️✍️🥰
[12/1, 6:32 AM] Zainab Abu: *🥀🥀ZAZZAFAR KISHI!!!🥀🥀.*
_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_




*NA*
*ZAINAB HABEEB.*
*MOM ISLAM*




*MARUBUCIYR*

*ZAINABU ABU*


*AND NOW*

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.



*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*


*page* 11_12


_____tsabar gudun daya sha"har yana ganin jiri na d'ibar,shi,bayan yasami guri ya zauna wasu hawaye masu zafi suka zubo'mai yana tuna cikin dake jikin AFRAH"gashi bata san ko'ina ba ,a kano,mik'ewa yayi ya,nufi hanyar koma,wa gida tafiya me nisan gaske yayi sanan ya isa gidan ya mance da sallama yashige babu kowa a palon "direct d'akin MARIYA ya wuce " samun'ta yayi tana kwance a gado tana charting tun bayan tafiyar JAMILA bata mik'e daga inda take zaune ba JABIR ne yadubi MARIYA yace amma baki'da imani kina ganin y'ar mutane tabar gidan ,nan".


Tunda ya, fara magana MARIYA ko d'ago kai batayi,ba "bare ta bashi amsa ranshi,ne yakuma 6aci tabbas da yana duka babu abin'da zesa be yiwa MARIYA duka ba"ficewa yayi ,yanufi d'akin AFRAH" hijab d'inta ya d'auko ya rufe fuskar,shi yaji kuka na zuwa'mai yarasa ya zeyi da rashin 'imanin MARIYA".

Washe gari AFRAH na hango,tsabar tafiya na kwana d'aya ta jigata tayi bak'i"tafiya takeyi babu wai, waye d'an kwalin kanta ma cireshi tayi yana hannun,ta"surutu ,takeyi wanda ba kowa zegane maganar taba "wani mutum ne a cikin wata bak'ar mota yayi parking" dai'dai saitin gurin,da AFRAH ta ,tsaya "rage tsawon bak'in gilashin daya rufe motar" saboda,na waje baze,ga na cikiba "lek'o da kai yayi waje AFRAH nata suru tanta bata kulashi ba" k'awala mata kira yayi da ke mahaukaciya ga sadaka a zabure ta mik'e ta cakumo wanan mutumi tana kuka tana kiran sunanda se mutum ya nitsu ze gane sunan wa, take kira'JABIR take cewa da wata iri,yar murya wace ta dashe tsabar ihu"bak'in mutumin ne yace da alamu dai wanan yarinyar harka take so janyota yayi ,ya tura ta cikin motar'shi ya,nufi wani katafaren gida" in kaga gidan kamar ba,a Nigeria ba "horn yayi me gadi ya bud'e mai get kutsa motar yayi a hara,bar da wasu tsala tsalan motoci suke" lokacin daya shigo AFRAH tayi baci, a motar d'auko,ta yayi kamar k'aramar yarin,ya" shigewa yayi da ita, cikin gidan babu kowa a gidan se megadi "bacci takeyi hankalin,ta kwance babu damuwar komai" wani tsara,ren palo yashiga kai tsaye, fad'ar irin tsaruwar da palon yayi 6ata lokaci,ne bedroom d'in dake cikin gidan" ya wuce da ita ya kwantar da ita a makeken gadon ,da ya k'awata d'akin ".

Wanka yayi ,yafito daga shi se gajeren wando da farar riga me gajeren hannu" sufa yayi a gadon kana ya rungumo AFRAH da,keta bacci ,rungumeta yayi sosai "acikin ranshi yana ai,yana irin kiwon da zeyi mata baze fara kusantar taba har seya bata wani abu" da shi,kad'aine yasan ko menene".

JABIR na d'akin AFRAH yana bacci yaji ringin d'in wayar AFRAH" gabanshi,na fad'uwa ya d'aga wayar da sallama ji,yayi ance AFRAH nake nema" seda ya nisa kana yace,tafita anguwa"mamin AFRAH da take ganin kamar JABIR ba gaskiya yake fad'a mata ba "tace, JABIR meyasa zakayimin k'arya kodai AFRAH bata,da lafiya ne kake 6oyemin¿" rasa meze ce yayi can kuma hawaye ya zubomai sharewa yayi ,murya me alamun anyi kuka" yace mami wlh bansan inda AFRAH ta ,tafi ba kukan daya,zomai lokaci d'aya ne ya hana,shi k'arasa maganar"mami ce da gaban,ta ke mugun fad'uwa "a zabure ,tace ina ka,kaimin yarin,yata" kuka, mami takeyi kamar k'aramar yarin,ya "JABIR ne yaji kamar yau AFRAH ta 6ace a zabure ya mik'e sekuma yadawo ya zauna".


Yarasa inda zesa kansa "

MARIYA ta rasa abin,da
ke damuta ,tun tafiyar AFRAH ta,rasa gane kan JABIR" JAMILA,takira akan tazo sutafi ,gurin boka" JAMILA ce ta duba lokaci k'arfe d'aya na rana"tace gaskiya yanzu,ina da bak'o sedai zuwa k'arfe hud'u" MARIYA ce ranta ,yakuma 6aci ,tafara tunani"gashi ta ,kori AFRAH gashi JABIR bashi,da wata magana inba ta AFRAH ba"mafita ,tafara'nemowa k'arfe hud'u dai,dai JAMILA ta iso "samun MARIYA tayi a Palo .


JAMILA ce ta,dubi MARIYA 'tace muje ko¿" eh tace, suka 'kama hanyar waje"batare da, ta'tambayi JABIR,ba ta'fice daga, gidan direct motar,ta "ta d'auko suka shiga" se gurin boka".


Tunda suka fara shiga jejin"suka jiyo wani ,irin kukan tsun'tsaye hak'ik'a sun tsorata,matuk'a"MARIYA tsabar ,tsoro har tana fad'uwa "JAMILA ceta ,temaka mata'ta mik'e"

Tafiya me nisa,sukayi ,suka iso jejin sun sami bokan'na zaune yana wasu surutai na tsafi "tuna dokar shiga gurin ,bokan sukayi"juyawa sukayi,kana suka k'arasa gurin bokan" bayan sun zauna yafara gayawa MARIYA abinda yake tafe da ita.....✍️✍️✍️


*mom Islam*✍️✍️
[12/1, 6:32 AM] Zainab Abu: *🥀🥀ZAZZAFAR KISHI!!!🥀🥀.*
_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_




*NA*
*ZAINAB HABEEB.*
*MOM ISLAM*




*MARUBUCIYR*

*ZAINABU ABU*


*AND NOW*

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*


*page* 3_4


_____wai dama haka auran me mata yake¿ take tambayar kanta ,seda ,dare yayi sosai duka yaran suka wuce part d'insu lokacin da suka tafi karfe 10:20 pm na dare AFRAH ce kwance a makeken bed d'inta tana shirin yin bacci tayi alamun ana nocking tashi tayi taje ta bud'e k'ofar JABIR ne sanye da kananun kaya ganin shigar da AFRAH tayi ya d'auki hankalin shi sleeping dress ne a jikinta da be wuce cinyarta ba k'arasowa yayi ya bud'e hannayen shi a kunyace ta zo ya rungumeta...

Rik'e da hannun juna suka fad'a gado rufe k'ofar yayi daganan yafara sauya labarin tunda yafara sarrafa AFRAH yanemi tunanin shi ya rasa yana cikin cirewa AFRAH kayan jikinta sukaji ana nocking.

A fusace yamik'e yanufi k'ofar bud'ewa yayi MARIYA ce dafe da goshi tana kuka hankalin JABIR ne yatashi cemata yayi jeki d'aki ganinan zuwa mutafi asibiti wucewa tayi dafe da kanta .

Tana zuwa d'akinta ta buga tsalle ta kwanta tana kuka likitan ta ,takirawo tanajin ya d'auka tace doctor gamunan zuwa nida alhaji kasan menakeso dakai ¿sonakeyi ,idan munzo kace dole se anbani gado saboda ciwon babba ne doctor Ahmad ne yace karkidamu hajiya angama bakida matsala.

JABIR na shiga d'akin AFRAH ya kamota ya d'orata a kan cinyar shi yace AFRAH dan Allah kiyi hakuri kinga MARIYA batada lpy ,yanzu zan kaita hospital AFRAH da idanunta suka kasa 6oye kukan datakeyi tace sekun dawo .

Jallabiya ya zura kana ya d'auki mukulin motarshi yaje d'akin MARIYA a kwance ya sameta tanata nishi alamun zazza6i na damunta sosai Sannu yadinga jeramata ya sukuceta ya kaita mota ya rufo motar .

Komawa d'akin AFRAH yayi samunta yayi tana kuka rarrashin ta yashiga yi seda tayi shiru yace mata ga yara nan bansan ko zamu dawo yauba to tacemai ya ciro kud'i masu yawa ya bata kar6ba tayi tace Allah yak'ara bud'i .

MARIYA ce a mota ta kirawo wata aminiyarta kawar tatace ,,tace shegiya aikin ki yana kayu yanzu ya ake ciki MARIYA ce tace ai nad'au alwashin JABIR nawane ni kad'ai wata mace bata isa tace zamu dinga sharing miji ba koda munyi sharing d'in to baze kwanta da itaba balle har ta sami ciki tazo aihuwa cabb suna cikin magana ta hango JABIR na zuwa kashe wayar tayi daganan yashigo motar suka nufi hospital d'in.

Alokacin dasuka isa hospital d'in karfe 12 na dare direct baban oficin likitan suka wuce daganan aka kaisu d'akin da ake wantar da marasa lpy .

Doctor Ahmad ne yayi, yan gwaje ,gwajensa yace gaskiya madam tana famada ciwon zuciya kuma se mun bata gado saboda za,a k'ara mata ruwa da sauransu .

Inda JABIR yaga dare haka yaga rana itakuwa MARIYA nata shek'a baccin ta misalin k'arfe hud'u na asbah MARIYA ta farka tanata kuka had'i da ihu dagudu JABIR yafice yaje office d'in likitan segasu ,sun dawo tare allura aka yimata dagan ta koma bacci .

Washe gari da safe AFRAH ta ,tashi tayiwa yaran wanka ta shiryasu tayi musu breakfast sun k'arya daganan tashiga wanka tafito mai tashafa bata tsaya yin wata kwaliyaba ta d'auko kayanta doguwar rigace pink me adon flowers masu kyau se d'an kwalin rigar tasa hijab .

Abincin dazata kai hospital d'in ta d'auko suka fito da yaran da BILLY da KHALIFA da MAMA itace k'arama .

AFRAH ce ta aiki BILLY takirawo driver bayan takirawo shi tashigo tace anty yace wai mufito.

Motar suka shige suka wuce hospital d'in basu san d'akin ta aka kwantar da MARIYA ba number JABIR tashiga kira yanajin wayar tafara ruri ya d'auka amsawa yayi da room 5 muke to sekun k'araso MARIYA najin haka seta shiga bacin k'arya .

Da sallama suka shigo nuni yayi musu da kujera zama sukayi AFRAH ce ta durk'usa tace barka da safiya JABIR ne yace kintashi lpy ,lpy Lou tacemai a tak'aice yaranne suka taho kusadashi sukace good morning dady amsawa yayi da dafatan kun tashi lpy fine suka ce AFRAH ce tadubi gadon da MARIYA take kwance .

JABIR ne yace mekuka zo mana dashi AFRAH ce tace abinci ne tashi tayi taje ta zubomai yanata santin girkin AFRAH ran MARIYA in yayi dubu ya 6aci yink'urin mik'ewa tayi JABIR ya taho da sauri ya rik'eta bud'e ido tayi a hankali .

AFRAH ce tazo kusada gadon tace anty kintashi lpy MARIYA ce ta zabga mata harara tace daban tashiba zaki ganni ne munafuka .

JABIR ranshi a 6ace yace wlh MARIYA kina bani mamaki baki d'auki duniya da sanyi ba.

AFRAH ce takoma gefe ta fitoda wayarta tana danne danne can anjima tace nizan tafi yaran sukace mu zamu zauna a gurin momy sallam tayi musu MARIYA tak'i kulata .

Bayan ta fice JABIR ze bita MARIYA tafara kukan munafirci haka yadawo yarungumeta yana rarrashinta tunda yaji ance tanada ciwon zuciya yake gudu 6acin ranta.
Bayan takoma gidan tarasa mekeyimata dad'i tafara tambayar kanta wai wane irin miji ta aura ¿.

Satin MARIYA d'aya a hospital aka sallamo su se abinda takeso shi za,ayi a yaune AFRAH tacika one week a gidan JABIR kuma yaune ze koma d'akin MARIYA .

Duk wani maganin mata dazesa ta mallake zuciyar JABIR tana amfani dashi dakuma uwa uba makirci wanka tayi tasa sleeping dress masu shara,shara iya cinyarta turatuka masu d'aukar hankali ta shafa ta d'auko cingom me kamshin strawberry ta jefa a baki.

K'arfe nine o'clock tasa yaran sukaje suka kwanta tana cikin gyra gashin kanta segashinan ya shigo dagudu taje tarungumo shi d'aukarta yayi ya wurgata kan gado.

Rad'a mai tayi a kunne I miss you my JB k'ara rungumeta yayi daganan naga suna hararata na fito daga d'akin.

Washe gari AFRAH batasa JABIR a idanun taba bare yaran nasu .

Damuwace ta,taru tayimata yawa tarasa wazata gayawa damuwarta maminta ce tafad'o mata har tad'auko waya zata kira kome tatuna sekuma ta fasa kuka ta fashe dashij me tsuma zuciya .


✍️Mom Islam ce🥰
[12/1, 6:33 AM] Zainab Abu: ________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*🥀🥀ZAZZAFAR KISHI!!!🥀🥀.*
_labar me ɗauke da makirci _cin aman da soyayya_




*NA*
*ZAINAB HABEEB.*
*MOM ISLAM*




*MARUBUCIYR*

*ZAINABU ABU*


*AND NOW*

*ZAZZAFAR KISHI!!!*.



*BISMILLHIR RHMNIR RAHIM*


*page* 13_14


_____Bokan yace kinason a sawa mijinki mantau ko¿"eh MARIYA tace bokane yacigaba da surutu ,can ya 6atarai,yadubi su JAMILA yace gaskiya mijinki yanzu baya wasa da sallah kinga ko anyi baze kamashi ba "itama wacan din beshigeta sosai ba ,dan tana tunawa da mijink ta MARIYA da gumi ya wanke mata fuska lokaci d'aya tace to yanzu boka menene abin yi, wata irin dariya yayi kana yace kugak'ura zedawo dai,dai " to tacewa boka suka mik'e suna tafiya tana masifa ,wallahi danasan wahalar banza zansha da banzo ba "JAMILA ce tasa dariya tace koni dazance karmu taho bazaki yarda ba.

Mamin AFRAH ce ta iso garin kano ,misalin k'arfe 11am na safe kiran wayar AFRAH tayi, ringing takeyi amma ba'a d'aga ba" k'ara gwadawa tayi cikin sa'a aka d'aga" jin muryar JABIR yasata k'ara shiga damuwa" tace kana nufin da gaske AFRAH na batanan¿"shiru yayi dan bashida amsa"cikin she,shek'ar kuka mamin tace to gani a kano kazo ka d'aukeni, cikin fad'uwar gaba yace to ganinan "wucewa d'akin MARIYA da bata dad'e da 'dawowa daga gidan bokanta ba" sallama yayi ko kulashi batayi ba ,bare yasa ran zata amsa masa, zama yayi kusad,ita kana yace MARIYA yau zamuyi bak'i daga Kaduna ,nanma bata kulashi ba ,tsawa yadaka mata yace ,duk iskancin,ki da rainin hankalinki wlh sena gyra miki zama ,MARIYA ce ta sake baki tana kallon shi ,cikin jin haushi JABIR yace wlh hardai,matar nan tazo kika wulakan tata to abakin auranki "MARIYA ce ta mik'e a fusace tace to wlh baka isa ,ba kuma koma wacece
Showing 3001 words to 6000 words out of 12971 words