ta?".

"In shi kuma yaje ya jiyo abinda mu bamu sani ba a kanta ya riƙe matsayin makamin hana auren fa?".

"You so stupid man, ya Ina tambayar ka kana maida min tambaya matsayin amsa?".

"And what did I say wrong?".
Dunƙule hannu Haisam yayi ya kai masa duka a kafaɗa shi kuma ya goce yana sakin silent smile na ganin yadda ya harzuƙa Haisam ɗin wanda ba wanda ke iya tolerating halin sa se shi kaɗai da Allah ya sallaɗawa so da ƙaunar sa.

"Please bawan Allah let's be serious, kaga wannan auren ina so ya faru at all cost ko banda hatsaniyar jaridar nan har ma da jama'ar gidan ku, na rasa gane wace irin cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa ce ke faruwa a gidan ku, da na zauna nayi tunani dole se da mace a tare da kai zamu fahimci kome ke tafiya dan na tabbatar wanda suka farmaki nafisa zasu sake yunƙurowa tun bare ma in ya zama kai ka samo matar da kanka".

"Rayuwar gidan mu bahaguwar rayuwa ce da hatta ni da nake cikin ta ba komai nake fahimta ba, abu ɗaya na sani shine kowa mara gaskiya ne, kowa macuci ne haka kuma kowa mugu ne shiyasa na zaɓi na rayu on my own haka kuma bana don shigar da kowace ƴa cikin haɗarin dake tattare da rayuwa ta dan maharana suna da yawa Haisam, dalilin kenan da na haƙura da aure amma for now ya zama dole in miƙe in har zata shiga rayuwa ta ko da na kwanaki ne kuwa".

"Me kake gani, mu bata hutu zuwa lokacin da komai ze tabbata ta fara amsa sunan matar ka ko yaya?".

Relaxing yayi cikin kujerar da yake kai yana lumshe ido

"Kasan meye damuwa ta?, Ƴaƴan ta, bana san a cutar da kowanne saboda ni, bana a ringa cutar da yaran da basu ji ba basu gani ba saboda wani ƙiyayya da ake min".

Ya ƙarashe yana buɗe idanun sa da lokaci guda suka canja kala zuwa jajaja brownish

"It hurts, it deeply hurt Haisam".

Ya faɗa yana dafe ƙirjin sa ɓangaren hagun sa alamun yana masa ciwo

"Calm down Abu Aulad, calm down insha Allah ba abinda ze same su".

Rufe idon sa yayi tare da kife kan sa kan table ɗin gaban sa ya shiga ajiyar zuciya akai akai tare da haɗiye wani ƙullutu me matuƙar ɗaci da ke taso masa duk sanda ya tuno yara, yana matuƙar san yara a rayuwar sa hakan yasa ake masa Indiya da Abu Aulad tun yana saurayi, da ya zama magidanci kuwa yayi aure burin sa da fatan sa ya haihu ne kawai, lokacin da Allah ya bawa matar sa ciki irin murnar da yayi ba me misaltuwa bace sedai Allah be nufa rayayyu bane daga uwar har ƴaƴan.

Miƙewa yayi ya zafi key ɗin sa ya fice da sauri kamar ze tashi sama haka ma Haisam ya bi bayan sa, yau dai kam ba abinda suka tsinana....................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.




☑️ Ote, Comment and share fisabilillah.













Ouummey 08 [ 11/30/2022 3:14 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*







₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.







FREE PAGE 008












_________________________📖 Gaban tanƙamemen gare ɗin gidan ya tsaya yayi horn, cikin sakanni gate ɗin ya fara zugewa da kan shi har ya gama ya tura hancin motar cikin babbar harabar gidan.

Daga kallo ɗaya in kayi wa cikin gidan zaka san gidan family ne ma'ana gida ne da ya kasu kashi kashi (parts-parts).

A lot ya kashe motar ya fita cikin cikakken takun sa da yake da ƙarfi ya nufi sashen mahaifin sa, a yanzu base anjima ba yake san isar da saƙon sa gare shi.

Yana yin sallama ya ɗaya labulen ƙofar tare da shiga falon, zaune kan kyakkyawar shimfiɗar da ta kewaye falon gaba ɗaya yake zaune tare da dattijuwar matar sa, dattijo ne da kallo ɗaya zaka masa kasan shekaru sun tura amma ba alamar yanƙwanewa ko wani rashin ƙarfi tattare da shi.

Zama yayi gaban sa bayan ya tanƙwashe ƙafafun sa ya gaisar dashi cike da ladabi sannan ya ɗora da batun da ya kawo shi batare da ya dubi tsohuwar dake zaune ko ya nuna ya san da ita ba.

"Na samu matar da nake son aura har ma mun gama daidaitawa, nasan an kawo maka wata jarida game da ni to yarinyar jiki ce zan aura ɗin, sunan ta Salma, magabatan ta na garin BA MUNI bana san a ɗau lokaci sosai ne, ba budurwa bace ta taɓa aure da yaran ta biyu".

Tun da ya fara magana wani irin firgicin ya wanzu kan fuskar matar har hannun ta ya fara ɓari wanda se da ta jimƙe shi tukunna ya tsaya, da sauri ta maida duban ta ga mijin ta dan jin me zece

"Amma ai ka bari ayi bincike a kan ta ko, banda rashin hankali irin naka Abu Aulad ka rasa matar da zaka aura se wadda hotunan ta ya gama zaga gari da sunan ɓatanci, to sam ban lamun ta ba ma, hakan ba ze taɓa yiwuwa ba, ga nan babar ka ta daɗe da sama maka mata tsoron halin ka yasa ta kasa faɗa maka amma ni yanzu na sanar da kai kuma sati biyu masu zuwa za'a yi auren".

Wannan karon gaba ɗaya ya ɗago yana kallon mahaifin sa cikin yanayin ba fa zan yarda ba

"Sam hakan baze yiwu ba Baba, a wancan karon ka kawo min nafisa ban yi musu ba amma a wannan karon kam bana jin akwai wanda ze dakatar da ni, bincike akan yarinya ni duk na gama shi, hotuna kuma nawa da nata ne sukai yawo dan haka ba matsala mata da miji dan sun zaga gari an san su, batu na wata ƴa kuwa bani da uwa balle ta zaɓar min, infact babu wani mahaluƙi da ya isa ya min auren da bana so a wannan karon, ka samin albarka dan a gobe zan je in auro ta Dan addini ya bani damar nemawa kaina aure kasancewa ta namiji, se an jima".

Yana gama bayanin sa ya miƙe tare da ficewa da sassarfa, yana fasa bari nan da sati ɗaya tun da ya fahimci abin iskanci ne, a gobe ze je ya auro ta ya ga wanda ya isa yace ya sau ta in akwai shi.

Dan anga yana yin shiru se a dinga maida shi wani soko ko wanda be san kan sa ba, to an shigo da'irar da ba ragayya tsakanin sa da kowa yanzu, ze fubi ifon kowane mahaluƙi da yanemi shiga hanyar sa sannan ya kawar dashi.

Waya ya ɗauka ya shiga kiran Haisam da tuni ya wuce gida tun lokacin da ya tabbatar gida ya nufa, ringing bitu ya ɗaga

"Ka fito bakin titi gani nan zuwa, ina nufin a ƙafa".

Ya faɗa batare da ya jira jin me Haisam ɗin zece ba haka be tsaya sauraren me ze faɗa ba bayan ya gama bayanin sa ya kashe wayar.

Kamar yadda ya faɗa a titin ya same shi, gefen sa Haisam ya shiga yayi wa mota wuta batare da ya sanar dashi ina suka nufa ba, shima tun da yaga yanayin sa se be tambaya ba.

Gudu ya dinga tsugawa a titin har suka fara fita gari, be tsaya ba seda aka kira sallar Azahar suna idarwa kuma suka sake ɗaukar hanya.

Ƙarfe biyar sannan suka shiga ƙauye BA MUNI, kai tsaye gidan me gari ya tambaya aka nuna masa ya wuce, suna zuwa suka fita sannan ya kalli Haisam

"Auren yarinyar can muka zo nema, gobe zamu dawo a ɗaura aure".

Baki sake Haisam ya bishi da kallo jin wani sabon tsari kafin kuma ya bi bayan shi ganin har ya kusa shigewa fadar me garin.

Kan shimfiɗun wajen suka zauna maigari kuwa se rawar jiki yake yaga ƴan gayu cikin kaya masu kai da walƙiya, cikin ƙanƙanin lokaci ya sanar dashi abinda ke tafe dashi aikuwa da sauri maigari ya tashi ɗan aike aje a taho da su kawu iro.

Ba'a daɗe ba se gasu sun bayyana gaban maigari kowanne futu futu dan yawancin su dawowar su kenan daga gonaki da wajen aikin ƙira.

Baɓata lokaci maigari ya sanar dasu dalilin kiran, baba Habibu yayi tsalle yace shi ba shi a cikin maganar yarinyar da ya zaɓi shegun ƴaƴan ta akan su haka ma baba iro.

Baba Adamu ne yayi sassaucin cewa sun bayar a ɗaura yanzu in har da gaske yake kawai dan shima ba ze yadda a Kuma tado shi daga wajen sana'ar sa ba gobe kan batun auren wata can wai Salame.

Ba ɓata lokaci kuwa aka ɗaura auren Salma Khamees da Abdallah Abdulsalam Gamji bisa sadaki dubu hamsin da ya bayar lakadan ba ajalan ba a fadar maigari.

Basu kuma jiran komai ba suka juyo da ɗimbin goron da suka siya a garin na ɗaurin aure, basu kai gida ba se wajejen goman dare, Haisam ya fara saukewa kafin yayi masa godiya ya wuce gida shima.

**********

"Ina sam ba zan bari haka ya yiwu ba wallahi, taya ya yaran nan ze shammace ni haka bayan ina nan ina shirin aura masa shuraiha, kai dole ma ita ce aura dan ba zan yi sanyar ya ɗauko wata a waje ba, nasan duk ma wannan fuffukar ta banza ce dan haka bari gobe tayi zan yi wa tufkar hanci, auren nan da sati za'a yi inga ta tsiya".

Hajiya Babba ta faɗa wa kanta cikin tabbatar da abinda zata iya taba kaiwa zaune cikin sauke ajiyar numfashin samo mafita da tayi, ta daɗe tana zaune ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa ciki sake zurfafa tunani har dare yaja kafin ta haƙura ta kwanta bayan ta sake maimata shawarwarin da ƴaƴan ta suka babbata ta ɗau na ɗauka ta watsar da na watsarwa.

********

"Anna da zafi zafi fa akan daki ƙarfe ya kamata gobe kije ki sami baba ki Masa magana kan meze hana na maye ɗakin yaya ta, kinga wancan karon shi ya Abdu yace a bar zancen tukunna amma yanzu ai yaci ace a tada maganar, shekara takwas za'a shiga ta tara da muke, kar mu tsaya garin kallon ruwa kwaɗo yayi mana ƙafa".

"Bari haka za'a yi, shi Abdallahn zan fara kira nan nayi masa kuka ta yarda baze Musa min ba kinga da kan sa ma se ya kai zancen naku can wajen baban nasa ta yadda ba wanda ze zargi ni nake son tusa ƙi ko".

"Sosai ma kuwa Anna, wannan idea ɗin tayi, bari in je in kwanta Allah ya kaimu goben da rai da lafiya".

Da Ameen Anna ta amsa mata yayinda ta shige ɗakin kwanan ta dake part ɗin marigayiya yayar ta nafisa da suka gaje tun bayan mutuwar ta.

A can kuwa baiwar Allah salma ta tasa ƴaƴan ta a gaba tana kallon yadda suke bacci hankali kwance ba abinda ke damun sa yayinda ita take cikin damuwa, damuwar da bata san dalilin ta ba wadda haka kawai take samun faɗuwar gaba duk ta tuno boss ɗin ta da auren da yake batun zasu yi, aure kuma kwana kusa in less than two weeks abinda bata taɓa shiryawa ba balle ta zauna tsara yadda ze kasance.

Alwala ta ɗaura ta shimfiɗa sallaya ta shiga nafiloli tana kaiwa Allah kukan ta kan ya shige mata gaba, seda ta gaji kafin ta zauna ta ɗau ƙur'ani ta shiga karatu har seda ta ji bacci yaci ƙarfin ta kafin ta rufe tayi addu'a ta kwanta.

Safiyar Laraba yazo wa mutane da dama cikin wani irin yanayi, ga salma wani irin nauyi take ji a ƙirjin ta da kanta kamar wadda ta aza dutsen dala a kanta, yaran kansu da ƙyar ta iya shirya su dan har se da suka makara yau, jiki ba ƙwari ta rakasu ajin su ta koma ta tare wani napep ɗin zuwa wajen aikin ta.

Ko da taje ta tabbatar boss ya rigata zuwa amma yau bata ji wannan fargabar ba illa wani nauyi da ta tuno sunan sa da abinda ke ƙoƙarin shiga tsakanin su.

Seda ta ajiye jakar ta da files ɗin hannun ta ta gyara wanda zata kai masa Sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar, amsa mata da akayi tareda bata izinin shiga ya sa ta buɗe ƙofar ta shiga ta ƙara sa gaban table ɗin sa ta ajiye masa files ɗin duk da bata gan shi a kan kujerar sa ba, juya tayi da zummar fita amma ya dakatar da ita daga cikin inner office ɗin sa kan ta zauna ta jira shi, zama tayi ta shiga bin office ɗin da kallo a hankali cikin admiration, office ɗin ya daɗe yana birge ta ba tun ba yau ba yadda ba'a cika masa shirgi da hauragiya ba amma komai a tsare fes wajen da ya kamata.

Cikin haka ta sauke duban ta kan ƙofar inner office ɗin dake buɗe ko kafin ta kai ga ɗauke idon ta tuni ya bayyana cikin shadda riga da wando ɗinkin tazarce sedai maɓallayen wuyan a buɗe suke yana gyara su, haɗa idon da suka yi yasa ta maza ta sauke nata gaban ta na faɗuwa, iya zaman ta a Companyn zata iya rantsewa yau ne ƙwayar idon su ta shiga cikin na juna dan indai tana gaban sa kanta ya kan kasance a ƙasa ne har se sanda ta bar wajen sa shiyasa ba zata iya cewa ga cikakkiyar ainahin kamannin sa ba dan kwarjinin sa kaɗai kan hana mutum iya kallon sa fuska da fuska.

Idon sa a kanta ya shiga takawa har ya ƙarasa ya ja kujerar opposite ɗin ta ya zauna tare da ɗaukar wayar sa ya shiga kiran Haisam

"Kasan tafiyar da zamu yi da tsawo amma kabar mutane na jira?".

Yana gama saurarar abinda yace ta can ɓangaren ya kashe wayar tare da ajiyewa ya shiga gyara agogon hannun sa, files ɗin ta jawo ta shiga yi masa bayani cikin mamakin yau kam be da niyyar zama kan kujerar sa sedai tuni ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu se kuwa taja bakin ta ta tsuke.

Ƙwanƙwasa ƙofa masinjan sa yayi ya bashi izinin shigowa, leda ya ajiye masa cike da girmamawa sannan ya juya ya fita, ledar ya jawo ya buɗe tare da kallon kayan ciki sannan ya tura mata gaban ta

"Ki shiga ciki ki canja wannan uniform ɗin dan ba zan iya tafiya dake dasu a jikin ki ba".

Binsa tayi da kallo har ya fice kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta canja kaya to akan me, ina ruwan sa da kayan jikin ta ko basu ne suka bata a matsayin kayan aikin ta ba da yau ze kawo mata wani sabon sanaben ta canja.

Haka dole ba dan taso ba ta ɗau ledar tare da shiga toilet ɗin sa ta cire kayan jikin ta ta maida wannan, doguwar riga ce ta mata se mayafin ta, kayan coffee and milk se suka yi mata kyau sosai dan tana da hasken ta daidai gwargwado.

Cikin ledar ta fito tana ninke uniform ɗin ta zuba su ta sake neman kujerar da ta tashi ta zauna

"Mrs Gamji bismilla ko".

Haisam ya faɗa daga ƙofa bayan ya buɗe, da rashin fahimta take kallon sa jin sunan da ya kiraye ta dashi yau

"Muje salma, inda zamu ba nan kusa bane".

Jiki ba laka ta miƙe ta bi bayan shi dan har ya fita, Allah ya sani bata san zuwa ko ina da su tunda ba muharraman ta bane haka ba wani cikakken sani tayi musu ba banda na wajen aiki yanzu kuwa mutum abin tsoro ne bare ma ita da bata da galihu ba wanda ze tdaya mata in wani abu ya same ta.

Gaban mota Haisam ya buɗe mata, cikin ɗarɗar ta shiga tana me karanto addu'a a bakin ta, wani irin sanyi ne ya ratsa fatar jikin ta na Ac dake tashi yayinda hancin ta ya shaƙo mata daddaɗan ƙamshin turaren motar da na jikin sa da suka gaurayu suka bada wani launi na ƙamshi daban.

Rufe murfin Haisam yayi ya koma ya buɗe bayan motar ya shiga, tada motar Abu Aulad yayi suka fita daga Companyn yayinda ma'aikata ke aikin kallon su sedai shi kam ko mutum ɗaya be nuna yasan da zaman shi ba balle ya kalle shi.

"Garin ku fa zamu je Madam".

Da sauri ta shiga ta kalli Haisam da yayi maganar kafin ta juyo ta kalli Abu Aulad da idanun sa ke bisa titi, bakin ta na ɗan rawa ta furta

"Taraba, suna school, ba wanda ze je ɗaukan su".

"Ba ze yiwu muje mu dawo kafin su tashi ba?".

Da sauri ta girgiza kanta,

" ƙarfe huɗu suke tashi".

"Ze yiwu muje har mu dawo". Da sauri ta shiga girgiza kanta

"A'a nidai mu tsaya a ɗauke su, ba zan iya tafiya in bar su ba, pleaaseeee".

Ta faɗa wannan karon directing to Abu Aulad

"Ya sunan Makarantar?".

"Star light Academy".
Be Kuma cewa komai ba ya saki hanyar da yake kai ya ɗauki wadda zata kai shi makarantar da ta faɗa.

Har ciki ya shigar da motar sannan ta fita zuwa wajen principal, uzuri ta bayar kan dalilin da yasa za'a ɗauki yaran, be Musa ba ya yarje mata dan yaran ta are one of their daily and punctual students da basa fashi sake da ƙwaƙƙwaran dalili.

Rungume su tayi a tare lokacin da suka fito daga aji kafin ta ja hannun su zuwa wajen motar suna ta yi mata surutu.

Tun da suka tunkaro su ya kafe yaran da ido cike da sha'awa da muradi, sha'awar dama nasa ne, muradun samun kamar su ya cike ransa.

Buɗe musu bayan motar tayi suka shiga a hankali sannan ta sa musu lunch
Showing 18001 words to 21000 words out of 27225 words