ta fito dasu wannan karon kanta a daidai tana bin su da kallo har ta kai gaban su ta sake tsugunnnawa, a yanzu kam Inna A'i da kallon da take bin su dashi ya ɓata wa rai itace ta kai mata duka a fuska, ba wai mari ba dan ba kuncin ta ta nufa ba kuma ta na sane ta kuma same ta a idon ta na dama, duk yadda idon ya ɗau raɗaɗi bata ko motsa hannun ta da niyyar taɓa wa ba.

Ta daɗe da sanin idanun ta na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo mata tsana, kyara da tsangwama a cikin gidan, wato wani irin ido Allah ya halitta mata me kamar na maciji ko mage za'a ce, dan ƙwayar idon ta ba baƙa bace haka ma ba brown ba, wata color so similar to golden, sedai golden ɗin irin me ɗan duhu kaɗan.

So da yawa su kawu, matan su ko ƴaƴan su sun sha goranta mata yanayin idanun nata duk tayi laifi, kai koma bata yi ba indai zasu haɗa ido se sun tanka mata, shiyasa tun lokacin da malamin Islamic studies ɗin su yayi musu addu'o'i ciki har da na baki shikenan ta ke yi, la haula kuwa kowane dare se tayi adadin da bata sani ba dan ba carbi ne da ita ba ta shafa a fuskar ta kafin ta kwanta haka kuma da asuba in ta tashi.

Bata san a wajen wa ta gado irin wannan idon ba cikin iyayen ta dan bata yi wayo da ko ɗaya ba sedai da alama ba wajen babanta da yake ƙanin baba Habibu da baba Adamu wa ga baba iro ba ne, tafi kyautata zaton wajen mahaifiyar ta ta gado ko kuwa dai Allah ne yayi mata nata halittan daban, ko a makaranta seda hakan yaso ya zame mata barazana dan har se da shugaban makarantar ta tsawatar tukunna shiyasa har tayi ta gama bata da wasu cikakkun ƙawaye sedai na gaisuwar mutunci, kowa gudu da tsoran ta yake saboda kalar idon ta da ba'a saba gani ba cikin jama'a, tun bata saba da hakan ba har ya zo ya zame mata jiki ba ta ma damuwa.

Zama suka yiyyi kan tabarmin da ke shimfiɗe a fadar me gari kafin suka shiga kai gaisuwa shikuma dattijon dake amsa sunan maigari na zaune kan kujerar ƙarfe kan sa ɗaure da rawani yana amsa musu.

Kafin kace me jama'a sun fara ciki dan haka ake wa duk ƴaƴan da suka yi ciki a garin amma fa marasa galihu dan da Allah yasa ƴar maigarin tayi shiru kake ji wai maye yaci shirwa, karuɗuf ƴar magulmaciya tayi ciki, ba wanda yasan da zancen seda faɗan kishiyoyi ya haɗa shima kuma har rana wata yau ba'a yi irin wannan zaman a kanta ba gashi har ta haife tuni.

Seda fadar ta gama cika sannan maigari ya fara sanar da abinda ya tara su wato dai batun cikin da Salame tayi ta haife batare da sanin su ba har gashi ƴaƴa sun kusa rufa watanni uku, hayaniya ce ta shiga tashi inda mutane da yawa ke Allah wadai da ita yayinda ƙalilan da abun ya faru kan ƴaƴan su suma suka shiga yi mata fatan Allah ya shirya a ganin su ai hakan ƙaddara ce (saboda ya faru ga nasu).

Se da gurin ya lafa kafin maigari ya shiga jawabin sa kamar yadda ya saba

"Bisa ga tsari na wannan gari bamu yadda da abun kunya ba ko yaya yake kuwa dan haka zamu aiwatar da abinda muka saba yi duk sanda aka samu irin wannan san zuciyar, a yanzu haka zamu karɓi ƴaƴan a kai su can nesa inda ba wanda ze san nata ne balle ayi mana gori kamar yadda muka saba tun da wannan shine karon ta na farko, da na biyu ne kuwa ko sama da haka to fa kun san hukuncin kora ne a kanta".

Yana gama faɗar haka wasu fadawan sa suka nufo ta da zummar amsar yaran inda ita kuma cikin matsanancin firgici da tashin hankalin jin abinda ake kiran ze faru ta sake ƙanƙame ƴaƴan ta ta shiga kurma ihun ba ta yadda ba ba zata bayar dasu ba, kowa a gurin ya shiga mamakin abinda tayi, a ganin su ƴaƴan shegen take ihu dan za'a raba ta dasu, to meye abin so cikin ɗan shege?!.

Muryar Salame da fiye da rabin ƙauyen zasu ce basu taɓa ji ba se gata ana jiyo ta tun daga farkon hayin maigari saboda yadda take ihun da iya ƙarfin Muryar da Allah ya bata, duk irin tsawa da zagin da babannin ta ke mata bata ma san suna yi ba balle ta saurare su ta daina ihun har se da maigari yasa fadawan su janye daga kusa da ita kafin tayi shiru ta sake matse ƴaƴan tana sauke numfashi sedai sam hankalin ta be kwanta ba dan tasan ba wai an ƙyale ta bane.

Seda megari ya gama ƙare wa jama'ar wajen kallo kafin ya muskuta yana zarar ido

"Tun da har wannan yarinya taƙi yadda da hukuncin mu to mun bata zaɓi biyu kuma a yanzu a nan gurin zata bayyana mana wanne ta ɗauka, na ɗaya ko dai ta bada yaran nan ayi kamar yadda aka saba dasu ko kuwa na biyu ta tattara ta bar mana garin ma'ana mun kore ta daga ita har ƴaƴan haka kuma duk sanda muka sami labarin shigowar ta to tabbas hukunci mai tsananin tsauri ya hau kanta, wannan sune zaɓin".

Shiru kowa yayi kallo ya koma kan Salame da take jin komai da aka faɗa haka kuma ba tare da second thought na halin da ita ko yaran zasu shiga ba sanadin zaɓin ta ta buɗe baki ta zaɓi abinda take ganin ya fiye mata

"Ba gari ba ko ƙasa ce zan iya haƙura in bar ta akan ƴaƴana dan haka na zaɓe su akan komai da nake dashi ciki kuwa har da asalina".

Kusan a tare duk su baba Habibu, baba Adamu da baba iro suka miƙe jin abinda ta faɗa, wato ta zaɓi ta bar garin saboda ƴaƴan ta haka ta zaɓe su akan Asalin ta wato su dangin ta kenan.

Shi kan sa maigari ba haka yaso ba dan a tunanin sa zata zaɓi bayar da yaran ne tun da in ta bar nan wa ta kama?, Bata da kowa banda dangin baban ta, mahaifiyar ta kuwa bama ƴar nahiyar bace, a yawon tuƙin babban mota baban ta ya auro ta dan haka ba wanda yasan komai a kanta kamar yadda basu faɗa wa kowa komai game da ita ba har kuwa ranar da ta bar duniya sanadin hauka da aka sa mata da ya kai sedai a ɗaure ta a ɗaki.

Umarni me gari ya bayar kan dogarawa su bita gida ta ɗebi abinda zata ɗauka a rakata bakin gari ta tafi sedai fir baba iro yace ba abinda ta aje a sassan sa bare ta koma ɗauka dan haka su rakata bakin garin kawai, bata Musa ba ta shiga gaba dogaran na binta a baya dan tun da ta shafa taji jakar makarantar ta na jikin ta hankalin ta ya kwanta.

Seda suka tabbatar tayi nisa da gari kafin suka juya zuwa gidan maigari suka sanar dashi an cika umarnin sa inda ya amsa da cuskunenniyar fuska dan ba haka yaso ba.

Abinda mutanen garin basu sani ba shine maigari siyar da jarirai yake wa ƴan birni da suka rasa haihuwa da kuma masu aikin asiri though be san me suke dasu ba, shidai kawai a bashi kuɗi shikenan, da an samu yarinyar da tayi ciki se ya hana a zubar yace ta haife shi kuma ya sami ƙarin jari.

Lokutan da kuma ba'a samun na banza hatta na sunna kaiwa yake dan akwai ungozomar da suka haɗa kai in ba na shege se a kai na sunna, yadda suke yi kuwa se an gama haihuwa lafiya lafiya se ta shafawa yaron wani magani da ta samo a wata asibiti dan ta taɓa zaman birni shikenan yaro se ya birkice da koke koke, ƙin kama nono da sauran su daga nan se a nufi wajen babban me maganin da suka yadda dashi da dukkan imanin su, dake shima nasu ne se yace ai ɗa ko ƴa na aljanu ne sun ɗauke naki sun musanya miki dan haka maza maza akai daji kaza daidai wuri kaza a ajiye musu kayan su, se an kai an ajiye ita kuma tabi dare ta ɗauka ta kaiwa maigari cikin gidan sa na sirri dake can bayan gari gefen dajika inda yake harƙallar sa.

Guri ta samu ta zauna tana haɗiyar busasshen yawu dan gaba ɗaya bakin ta ya bushe da ƙishirwa, tafiyar ƙafa sabon tace dan haka ba zata ce ta gaji ba sedai rashin ruwan ke neman kassara ta ga kuma ƴaƴa har biyu gaba da baya ga jaka me nayi se abin yayi mata yawa.

Mutsu mutsun Ussaina da taji yasa ta san ta farka dan haka ta sauke ta dan ta ɗan huta da goyon sedai ita ba hutun take nema ba abinci take nema da bata samu ba kuwa ta buɗe baki ta shiga canyara kuka da ƴar Muryar ta na jarirai, kukan Salame ta shiga yi itama dan abin ya haɗe mata goma da ashirin.

Haka Ussaina tayi kukan ta har ta gaji baccin yunwa ya ɗauke ta kafin itama ta haƙura ta goge fuskar ta ta maida ta baya dan ba zata iya riƙon hannu ba ta cigaba da tafiya.

Se da rana ta faɗi gaba ɗaya kafin ta shiga wani ƙaramin ƙauye dan gaba ɗaya gidajen dake ciki basu fi a ƙirga ba haka kuma daga ganin gidajen su kasan har yau su kam suna cikin duhun rayuwa wato ba wayewa ko ta misƙala zarratin dan duk bukkoki ne ba gidan ko ƴar jar ƙasa ɗaya.

Kan wani kututturen dabino ta kai zaune tana ajiyar zuciya tare da numfashin ta dake fita ɗaiɗai saboda wahala da jigatuwa, nan take zaune har se da wani tsoho ya zo wucewa ya ankara da ita kafin ya ɗan matsa nesa da ita ya shiga ƙare mata kallo Sannan ya gyaɗa kai ya wuce.

Be daɗe ba ya dawo dashi da wasu dattijan da kuma matasa suka dinga magana da Yaren su da bata san wanne bane kafin ɗaya daga cikin matasan ya nufi ta.

Tambaye ce daga ina take, me ta shigo nema a shiyyar su, me take buƙata haka dai, amsa ta bashi da sunan garin su wato BA MUNI wanda sunan ya samo asali ne daga yadda duk wani ɗan garin yake kyakkyawa sedai wani yafi wani amma mummuna kam babu sedai ko baƙo shiyasa suke saurin gane baƙo a cikin su.

Iyayen sa ya koma ya sanar da amsar da ta bashi, sunan garin su da kuma taimakon da tace ta zo nema, seda suka kuma sake zantawa cikin dai Yaren nasu kafin wani saurayi ya tafi be daɗe ba ya dawo da wata tsohuwa sedai ba tukuf ba, nuna mata ita suka yi inda ita kuma ta ƙarasa ta kamata ta miƙe kuma cikin fara'a tace mata

"Kunto min jikokin nawa mana, da alamu sun daɗe a goye".

Bata ƙi ba ta kunto Hassana ta bata ta bar Ussaina

"Ita ma sauko ta ta huta hakana".

"Tana da kuka ne Inna".

Murmushi innar tayi alamun ta gane kafin suka shiga tafiya hannun ta dafe da zanin ta dan cikin sa ta ɓoye jakar ta da zasu je wajen Maigari ashe Allah ne yayi suna da rabo da yadda kawu iro yace ba zata koma masa gida ba shikenan sun salwanta.

Bukka ce me ɗan girma suka shiga sedai abin mamaki har dasu gadon ƙarfe a cikin ta, fita Inna kamar yadda ta kira tsohuwar tayi bayan ta kwantar da Hussaina tsawon lokaci tukunna ta dawo da bahon katako a hannu, ruwa ne masu zafi a cikin sa haka kuma ba fari bane da alamun an zuba wasu abubuwan banda kuma ganyayyaki dake ciki, tuɓe Hassana tayi ta mata wanka da yasa yarinyar ta ringa sauke ajiyar zuciya a jejjere, Ussaina kam ta sha ihu da ana yi mata dan alamu sun nuna ba su taɓa shiga ruwa masu zafi haka ba.

Se da ta tabbatar sun gasu kafin ta ɗau abin ta fice inda Salame ta yi saurin isa ta ɗau yarinyar ta shiga jijjiga da lallashi har tayi shiru,

"Ga can ruwa ki je kiyi wanka kema ko kya watsar da gajiya".

"Toh Inna".

Tace tana kwantar da Ussainar a hankali gudun kada ta tashi daga ɗan baccin da ya fara sanɗar ta............................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.














Ouummey 04 [ 11/26/2022 9:17 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*







₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.






                     FREE PAGE 004







________________________📖 Ba ƙaramin daɗi taji ba da tayi wankan, wani irin mulmulallen sabulu ne da bata san wane iri bane Innar ta ɓata tayi wankan dashi ga kuma ruwan zafi da har yake tashin tururi.

Gaba ɗaya se take jin kamar an kwashe rabin ta an yar haka kuma wata daddaɗar iska ke ratsa fatar jikin ta tana shiga har cikin ruhin ta.

Bata san ina ta samo kaya ba se gani tayi ta kawo mata har kala biyu, duk da tsofaffi ne sedai ai basu kai nata mutuwa ba dan haka ta shiga godiya kamar zata ari baki.

Hankalin ta ta maida kaf wajen Inna da tace zasu yi magana

"Ƴar nan nace yaran nan zasu yi wata nawa ne yanzu?".

"Watannin su biyu da rabi".

Ta faɗawa Inna tana tabbatar wa kanta ba zasu fi hakan ba ko zuwa uku.

"Amma na lura ba kya son shayar dasu tunda seda nayi ƴan dabarun mu na tsoffi na samu abin baiwa Ussaina tukunna itama Hassanar ta samu".

Ɗan jim tayi gaban ta na faɗuwa na sabon batun da ya Kunno Kai, ita kanta ta san a kwana da wuni da suka yi a hannun ta sun rame saboda yunwa sedai bata san yadda zata yi musu ba haka kuma wannan na cikin tunanukan da ke kai kawo a kanta dan su ɗin ƴan ƙauye ne so sun san muhimmancin nonon uwa ga jariri

"Dama...dama haka kawai ya ɗauke shine ban san yadda zan yi ba".

"Ikon Allah, abinda mamaki amma mafita ba zata gagara ba sedai kafin nan ina son sanin wacece ke da abinda ya rabo ki da garin ku dan mu samu kwanciyar hankali da yardar zuciya akanki cewar ba me cutar wa bace, haka kuma kiji tsoron Allah ki faɗa mana iya gaskiyar ki".

"Isyaku Maƙeri Dattijo ne da yayi suna a garin BA MUNI ba dan komai ba se dan sana'ar sa ta ƙira da Allah ya sanya masa nasibi akai dan yana iya ƙera duk kalar abinda ake so kama daga kan makami har zuwa kayan amfanin yau da gobe na gida da na waj   en sana'a.

Matar sa ɗaya har yayi rayuwar sa ya koma ga Allah wadda ƴaƴan ta ke kira Kulu d an Asalin sunan ta Hauwa'u ne, ƴaƴan su biyar rayayyu dan tayi ta haifa suna mutuwa se biyar ɗin ne suka tsaya suma ba a jejjere ba, Baba Habibu shine babba se baba Adamu duk da akwai ratsin matattu biyu tsakanin su se kuma babana wato kamisu shi kuma matacce ɗaya ke tsakanin sa da wan nasa, daga shi se gwaggo Larai se kuma auta baba iro.

Dukkan su suna zaune a madaidaicin gidan gadon da mahaifin su ya mutu ya bar musu ne sedai kowa da sashen sa inda ya killace suke rayuwa da matar sa da ƴaƴan sa, sedai banda gwaggo Larai dake aure a can wani ƙauye me nisa da namu shiyasa ma se ta shafe watanni bata zo gida ba.

Babana direban babbar mota ne inda Allah ya taimake shi ya shiga makarantar yaƙi da jahilci har ya samu abinda ba'a rasa ba na ilimin zamani dan yaga komai seda ilimin ko yaya ne hatta ko da tuƙin.

A can wajen sana'ar sa ta zuwa gari gari ya taho da mahaifiya ta daga garin da bamu san ina bane bayan ya aure ta sedai kawai ganin sa da mace ƴan uwan sa suka yi yace matar sa ce.

An sha rikici da shi kafin ƴan uwan su haƙura su bar shi da ita dan se da uwar su ta nemi yi musu baki akan maganar dan ba ƙaramin so take yi wa babana ba kasancewar sa mutum me kyauta da tausayin iyaye hakan yasa duk ciki ya fi kyautata mata.

Cikin wannan hali rayuwa ta cigaba da gudu har iyayena suka shafe shekaru tare amma haihuwa shiru, tun abin baya damun Inna ta har ta fara yiwa babana kuka sedai ya bata haƙuri duk da shima yana damuwa dan habaici da baƙar magana duk yana kwasa wajen ƴan uwan sa da matan su sedai bata kulawa dan shi ba me san rigima bane.

Ba'a daɗe ba Baba iro da yayi aure bayan su ya haihu shima wannan ya ƙara wa iyayena damuwa, a taƙaice dai seda suka shekara biyar sannan Allah ya basu cikina, murna kuwa a wajen su ba yasu a lokacin su da kakata bayan su kuwa ba wanda yake farin ciki dan ba wanda yake so a haɗa musu zuri'a da Inna ta a cewar ƴan uwan sa tunda basu san asalin ta ba.

Cikin ikon Allah Allah ya sauki inna ta lafiya ta haife ni, ƙauna da soyayya na same ta ɗaga kowane ɓangare na iyayena da kuma kakata har na kai
Showing 6001 words to 9000 words out of 27225 words