shekara ɗaya da rabi kafin mahaifina ya rasu sanadin haɗarin motar da ƴan fashi masu tare hanya suka jawo.

Itama inna ta ban ciki shekaru biyu cikakku ba ta haukace ƴan uwan mahaifina suka dinga faɗin rashin tawakkali ke gare ta, wai ta kasa dangana da rashin babana ne.

Wasa wasa abu ya zama sedai a rufe ta a ɗaki ga ba me kula da ita se tsohuwar kakata da nake kira biba dan lokacin ban iya baba sosai ba haka kuma kula dani se abin ya taru yayi mata yawa to abu ga jikin girma, wannan yasa yunwa, ƙishirwa da rashin lafiya yaci ƙarfin Inna ta se wayar gari aka yi aka tsince ta amace.

Ba wanda ya damu da mutuwar se kaka ta dan da ƙyar dangin babana suka sallaci gawar bayan kaka tayi iƙirarin tsine musu a cewar su wai haram ne sallatar gawar da ba'a san asalin ta ba.

Tun daga lokacin na zama marainiyar ƙarfi da yaji amma biba bata gaza akai na ba, kullum idanun ta na kai na tunanin ta nice da rayuwata har aka wayi gari ta makance dan dama tana fama da ido ga kuma shekaru dan a ƙalla a lokacin tayi saba'in da hawa dan se da ta shekara sha ɗaya da aure kafin baba Habibu yazo duniya.

Haka tana ji tana gani ba yadda zata iya ta baiwa baba Habibu ni bayan ta jaddada masa amana ce ta basa kuma Allah ya kallon sa, da farko zaman kamar abin arziƙi kafin daga baya komai ya kwaɓe, a ƙananun shekaru na na huɗu a lokacin haka ake sani wanke wanke, shara, ɗebo ruwa kai har ma da wanki wani sa'ilin bayan ƴaƴan sa har da me aure ciki banda ragowar matasa da ƴan matan da ke cike.

Duka kuwa kamar baiwa sedai in ban kuskure umarnin su ba daga ƴaƴan har iyayen, wani sa'in biba ta jiyo Ni wani sa'in Bama ta sani nima kuma bana faɗa saboda irin tsoratar dani da Inna uwale dashi baba Habibun suka yi.

Haka nayi ta shan wannan baƙar azabar har na kai shekara bakwai wanda ina shekara biyar Allah ya ɗau ran kakata biba, ba ciwo ba komai ajali ya sauka se fatan dacewa kawai, a lokacin duk da banda shekaru amma ina da wayo da kaifin basirar da maraici ya koya min dan haka nasha kuka sanin ragowar gatana babu dan duk wannan labarin na same shi ne wajen ta gaf da zata rasu, in na gama aiki na se in gudu can muyi ta hirar mu shine fa na taɓa tambayar ta ni ina babana da Inna ta shine ta sanar dani.

A shekaruna na bakwai na iya raino fiye da zato dan hatta da wankan jarirai yi nake, kai a aikin gida ko kula da ɗa ba abinda ban iya ba lokacin haka kuma azaba ba wadda ta ragu wajen uwale matar baba Habibu.

Se da na kai sha biyu sannan suka maida ni wajen kawu iro kan cewar suma su amfana dan lokacin ita uwale bata da ƙananan ƴaƴa, shi kam kawu Adamu ko da aka yi masa tayi cewa yayi a'a dan shima ba shida ƙanana se matasa, haka na koma hannun kawu iro na cigaba da wahaluwa wajen Inna mariya.

Ban san wadda tafi wata rashin imani ba cikin matan biyu wato uwale da mariya dan ita uwale da wuta take min azaba ita da mijin ta ita kuwa Inna mariya cewa tayi kowane sassa na zan dinga musu ayyuka.

Sauƙin abin ɗaya da mai gari yasa dole aka bar ni nake makarantar boko ganin yadda nake sha'awar na ƴaƴan shi dan haka tun ina shekara tara na fara haka kuma karatun makarantar gwamnati ba wani nursery daga primary ne kawai.

Ko da na gama ban yi sanya ba na garzaya na faɗa masa buƙata ta na ɗorawa ta kuwa same su da maganar kuma dole suka yadda, farin cikin da nayi lokacin da na sami makarantar kwana ba zai bayyanu ba dan ina ɗaukar makarantar da wajen da zan fake in ji sanyi a raina.

Duk irin wahalar da ake faɗa na makarantar kwana ban damu ba dan a wajena bata kai ko rabin ta gidan mu ba, haka kuma in naga ƴaƴan masu dashi ko rufin asiri na ciye ciye bana ɗorawa kaina sanin ni ko shege ƙanzo ba a haɗa ni dashi ba hasalima Ni na kai kaina makarantar a ranar farko da kowane iyaye ke kai ƴaƴan su.

Tun a lokacin principal ɗin ta kafe ni da kallo alamun tana nazari ne a kaina kafin kuma ta bani komai na buƙata tace naje aji bayan ta haɗa ni da wata ɗaliba.

Washegari se gashi ta aiko an kaini har gidan ta dake quarters ɗin Malamai ta tambaye ni tarihina bayan ta bani abinci naci ganin alamun yunwa a tattare dani.

Kamar yadda nake faɗa miki haka na sanar da ita inda se da ta koka min, haƙuri ta shiga bani kamar ita ce mai laifi kuma tun daga lokacin ita ke kula da komai na na karatu har mamaki nake yadda bata ƙyashin kashe kuɗin ta a kaina, hatta tsangwar da ɗalibai suka so ɗora min ita tayi tsaye taga ta hana duk dan naji daɗin Makarantar.

Ina aji na biyar muka yi aure da wani malamin mu da yazo bautar ƙasa batare da sanin dangi na ba dan nasan ba zasu yadda ba ni kuwa ba zan iya haƙura ba dan gani nake auren ne kawai ze sama min sauƙi na dindindin, wata biyar da auren na samu juna biyu.

Mama Hadiza wato principal ke kula dani dan ta shaida aurenmu.

maigadin mu na aika da izinin Mama yaje ya sanar musu ba zan dawo hutun zango na biyu ba zamu shiga lesson na jarrabawar ƙarshe dan haka zan zauna a makaranta, ba wanda ya ko kula zance na dan tuni suke min kallon wata mara amfani kuma ba tsatson su ba.

Wata daya kafin fara jarabawar mu na haife su, muna gama jarabawar da ta ɗauke mu wata ɗaya da rabi ne muka koma gida shine suka shegan ta min ƴaƴan suka koro mu saboda bamu je da baban su ba an masa canjin waje aiki ya bar mu akan zeje ya dubo inda aka tura shi muka yi dashi wata biyu ze dawo yanzu kuwa kwana huɗu kenan a cikin satin farko".

Ƙura mata ido Inna tayi tana kallon yadda yarinyar ke sharar hawaye gwanin ban tausayi.

"Baki kyauta ba da kika yi aure ba tare da sanin dangin ki ba ko ya suke kuwa kuma ko me suke yi yanzu dai dubi yara kyawawa wanke hannu ka taɓa amma ana yaɓa musu baƙin fenti kamar wasu mara sa galihu.

Amma me yasa ba kuje gida da ita shugabar makarantar ta ku ta musu bayani ba?".

"Tare da ita muka je Inna sedai duk sun ƙi yadda wai se mijin yazo shi ba waya ba balle mu kira shi, shiyasa bana son yin nisa kar ya dawo be same ni ba".

"Wannan gaskiya ne, tun da haka ne me ze Hana ki zauna tare da mu zuwa ya dawo ɗin se ki tafi, ina ganin ba matsala ai ko".

"Babu Inna, nagode ssae Allah ya saka muku da alkhairi ya raya muku zuri'a, amma ragowar ƴan uwan ki zasu yadda tun da ba sani na kuka yi ba kuma naga al'adun ku da Yaren ku daban da nawa?".

"Sam kar ki damu, ba su da matsala akan haka, mu ɗin wani yanki ne na Larabawan ƙauyen Sudan, anyi yaƙe yaƙe a kusa damu har aka cimmana yasa muka haɗa kan mu da muka rage muka gudo ƙasar nan, Allah da ikon sa be nufe mu da zama a ko ina ba se nan da muka kafa wannan ɗan ƙaramin garin da kike gani, wasu daga cikin mu sun yi ilimi daga na addinin har na boko, wasu ko iya na addini ne kamar dai ni dan babana liman ne a can garin mu na ainahi".

Inna ta faɗa cikin alhini na tunawa da dangin su da aka kashe musu, dukiyoyin su da aka lalata wasu kuma aka kwashe.

"Allah ya jiƙan wanda suka rasu ya tsare ku ku da ke da rai ya amfanar daku".

"Ameen ƴata, kinga ni sunana Husaila".

"Kuma sunan ki me daɗi irin na ƴan gayu, ni kam daga yau baba Husaila zan ke ce miki".

Dariya suka yi duka yayinda baba Husaila ta miƙe tare da faɗin tana zuwa ta fice.

Bata daɗe sosai ba ta dawo hannun ta riƙe da wasu garin magani a jiƙe a kofi ta miƙa mata tace ta shanye, bata yi gardama ba ta kafa kai ta shanye duk da baurin maganin, wani abu me kauri kamar koko ta bata shima a kofi da kuma garin magani shima ta sa ta shanye.

Tun daga ranar haka take bata jiƙe jiƙe dan hatta ruwan wankan ta kullum se an sa masa wasu saiwoyi da garin magani har kwana huɗu.

Shigowar baba Husaila yasa ta ɗagowa tare da cire hannun ta daga shafa ƙirjin ta da suka cicciko da ruwa da take yi ta maida hankali kan ta, yamutsa fuska tayi ganin yanzun ma dai wani haɗin ne dai sedai bata ƙi ba ta karɓa ta shiga sha tana runtse ido dan ta san komai take yi dan taimakon ta take yi da kuma ƴaƴan ta dan ita ma zata so ace tana shayar dasu tun da ba kuɗin siyan musu abu ne inganci da ze gyara jikin su ya ƙara musu lafiya gare ta ba.

Da hannu ta ringa share zufar da take yi dan damun kunun gyaɗa ne mai zafi aka sa masa magani aka baya tasha, seda ta gama tas kafin baba ta karɓi kofin ta fita dashi ta dawo hannun ta riƙe da Hassana da wata matashiya ta amsa ta fita da ita zagaye dan kowa so da ƙaunar yaran yake dan sha'awa suke bawa Kowa hatta matasan cikin su shiyasa yanzu kaya kam suna dasu gwargwado da suke siyo musu.

Ɗora mata ita tayi kan cinyar ta ita kuma ta shiga yi mata wasa yarinyar kuwa ta shiga murmushi dan har sun gane fuskar ta dan ko kuka suke tana karɓar su suke shiru musamman uwar rigima Ussaina.

"Maza bata tasha dan nasan zuwa yanzu ruwan yazo gashi nan yana ta lema ta cikin zanin ki, gyara ki bata dan tafi yar uwar ta haƙuri, in waccan acicin ta riƙe nasan ba saki zata yi ba".

Murmushi tayi dan dama baba Husaila da Ussaina basa shiri saboda rigimar ta, a hankali ta janye zanin daga ƙirjin ta tare da matsar da fuskar yarinyar gaban ta na dukan tara tara na rashin sabon abin da baka taɓa yi ba ita kuwa baba se ta fice a tunanin ta ai ta iya.

Da sauri Hassana ta cafke tana sauke ajiyar zuciya dan rabon su da nono tun rabuwar su da mahaifiyar su sati da kwanaki kenan.......................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.


☑️Ote, Comment and share please.











Ouummey 05 [ 11/27/2022 9:24 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*







₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.









                    FREE PAGE 005










_________________________📖 A sittin ta runtse ido tana taune leɓen ta sabida zafin da ya ziyarce ta ita kuwa Hassana da zaƙuwa take zuƙa tana sauke ajiyar zuciya har ta ƙoshi kafin ta saki.

Se lokacin ta buɗe idon ta da ya ɗan canja kala ta kalli yadda yarinyar ke numfashi a hankali a hankali tana ciccilla ƴan ƙafafuwan ta tare da wasa da hannayen ta se ta ji wani sabon farin ciki ya kamata har ma taji zafin ya tafi.

Zanin ta ta gyara a ƙirji ta miƙe ta saɓa ta a kafaɗa ta shiga jijjiga ta dan tayi gyatsa, a haka baba Husaila ta tadda ta se ta kwantar da Ussaina ta karɓi Hassana ta fita da ita a kafaɗa ita kuma ta koma ta zauna tare da ɗaukar Ussaina.

Haka ta shayar da ita itama sedai ba kamar Hassana ba Ussaina akwai ci dan se da ta daɗe kafin ta ƙoshi hakan ma se da ta canja mata ɗayan shiyasa gaba ɗaya ƙirjin nata ya ɗume da zafi.

Tun daga lokacin take shayar dasu amma duk da haka baba Husaila na haɗa musu da ƴan dabaru musamman Ussaina da ta fahimci yarinyar akwai tsotso in aka barta bata ƙi ta wuni da nono a baki ba.

Iya ƙauna da mutuntaka baba Husaila da ƴan uwan ta sun gwada mata, Abinci da abin sha bata taɓa rashin su ba, ga kula da ita da ƴaƴan ta da suke yi tun bare baba dan ko rigimar Ussaina ce ta tashi da dare bata bari ta tashi cewa take ta koma tayi kwanciyar ta ita kuma tayi ta fama har se tayi bacci tukunna hankalin ta ze kwanta.

Ruwan wankan su kuwa kullum se ta sa musu magani shiyasa alhamdulillah jikin su yayi ƙwari se fatar su da ta ɗan dafe saboda zafin ruwa da kuma kalar magani duk da yanzu sun fara sabawa da zafin ruwan.

Sannu a hankali har ta cinye wata ɗaya tare dasu basu ankara ba saboda zama da yayi daɗi, jakar ta kuwa baba ta adana mata dan ce mata tayi da su ne za'a bar ta ta shiga makarantar in taje, yadda ƴan uwan baba ke son ta ita abin har mamaki yake bata, wai yau ita Salame da kowa ke gudu itace yau ake so ko da yake ai ba ita ake so ba ƙaunar ƴaƴan ta ce ta shafe ta dan haka be kamata tayi wani kauɗi ba.

Mace ɗaya ce ta taɓa son ta a Karan kanta yadda take wato Hajiya Hadiza principal ɗin su, Allah ya sani tana son matar a ranta irin son da bata san yadda zata kwatanta shi ba.

Ta so ta a lokacin da kowa ya ƙi ta, ta bata gatan da bata taɓa zaton samu ba, a bayyane yake badan ita ba da ba zata taɓa samun damar karatun da take so ba, ita ta ɗau ɗawainiyar komai na makarantar ta, kuɗin PTA, uniform, littattafai, takalmi, Safa, abinci da komai da zata buƙata a makaranta tun da ta fara kuwa bata gaza ba har wata ɗaya da kwanaki baya da ta gama, ita kuwa ai sedai tace da ita Allah ya saka da kuma ya zame mata wajibi ta so ta.

Kallon baba Husaila dake zaune gaban ta tana mata lissafi kawai take yi yayin da idanun ta suka tara ƙwalla, kuɗi ne daga kan ƙwandala zuwa na takarda wai wanda aka haɗa mata dan tafiya makarantar su da zata yi duba mijin ta in yazo (kamar yadda tace musu).

Hannu ta sa ta share hawayen

"Dan Allah baba ki maida musu kuɗin nan kin ji, zan fa iya zuwa da ƙafa".ta faɗa murya na rawa

"Amma dai salamatu baki da kirki, ya za'a yi mutum yayi alkhairi a maida masa, to kul kar in Kuma ji ko ke kin yi hakan kin ji ko?".

Da kai ta amsa wa baba kafin ta shiga yi musu godiya da addu'a kamar Allah ne ya aiko ta har se da baban ta gaji ta fice ta bar mata ɗakin.

Tuhumar kanta take kan me yasa tayi masu ƙarya gashi su kuma sun yarda da ita sun zauna da ita da zuciya ɗaya, jaddada wa kanta take Allah ma ya sani ba'a san ran ta tayi ƙaryar ba, bata so a raba ta da yaranta ne kawai.

Da wannan ta tattara kuɗin da suka tasamma dubu ɗaya ta zuba cikin jakar makarantar ta, ta kuma haɗe kayan ƴan biyu ta ninke ta zuba cikin jakar su ta rakuɓa nata kala huɗu da take dashi.

Kashegari tayi sallama dasu cikin rashin daɗin rai dan har da kukan ta haka ma baba Husaila da ta zauna wajen ta, ji take kamar yarinyar ta dawwama tare da ita dan bata da matsala sam, yarinya ce me kirki ga ladabi da biyayya, gata ba har dama, ga nutsuwa da rashin ƙyuya, duk sanda taga ta tashi aiki bata bari tayi komai se karɓe ta shiga yi shiyasa so da yawa ma bata tashi yi saboda tasan ba zata bari tayi ba.

Su kuwa ragowar ƴan gari da matasan su ƴaƴan ne suke jin kamar su ƙwace ta tafi ita kaɗai dan sun shiga zuciyoyin su barin ma Hassana da bata da rigima, in aka fita da ita har se an tausaya an dawo da ita dan bata kuka se dai in ko Bata da lafiya ko kuwa ta kai maƙura wajen jin yunwa, toh haka dai aka rabu kowa na mararin kowa, rayuwar kenan!

Ganin tana da isassun kuɗi a hannu se kawai ta tare mota bayan ta fita sarari, sunan Makarantar su ta faɗa masa suka yi ciniki ta hau ya kai ta har bakin gare kuwa.

Wajen baba megadi ta bada ajiyar jakar kayan su ta wuce office ɗin Hajiya Hadiza wato principal, ba abinda ya dawo da ita makarantar illa son karɓar sakamakon ta tare da certificate ɗin kammala karatun ta dan tana so a duk inda taje ta ɗora karatun ta dan shine burin ta tun bata san ze iya cika ba ko kuwa ze rushe ne har zuwa lokacin da ta fara hasashen cikar sa wato da maigari ya sanya baki a kan karatun.

Ba kaɗan ba Hajiya Hadiza taji daɗin ganin Salame wadda ke amsa sunan Salama kamisu a makarantar, cikin nutsuwa ta bata takardun ta da WAEC result ɗin ta dan dama alƙawari ne tayi mata ana sakin result zata bada a
Showing 9001 words to 12000 words out of 27225 words