glass manne akan kyakkyawar fuskarshi, mai fitar da annuri.
Cup d'in glass mai kyawun gaske ya d'auka ya kai daddad'an shayin bakinsa, ya kurb'a ya ajiye.
Da tsinin ido yake kallon yadda Raiyana ta k'ure shi da ido.
Hankalinsa ya maida wajan Jaddatu ya ce“Ummi Afuwan wlh tinda na fito daga sallar isha nayi bak'o daga Jos ta Nigeria dole zanji da shi, ba kiga sai Kira nai aka kai masa abinci, kuma yau ya juya yanada kyau dukkan mutumin da ya d'auko k'afar shi yazo daga wani garin ko wata k'asa ka saurare shi ka masa tarba mai kyau, sabida kai ma gaba bakasan ko zaka nemi wani temakon wajansa ba ko wajan wani shak'ik'insa, bare wannan harakar kasuwanci ta had'amu. Uhmm! Bari naje biko Baby Ummi, na mata bayani yanda zata fahimceni, ba lallai ta yi baccin kirki anata fushi da Abienta, na rasa wa baby ummin ta biyo rigima?â€
Raiyana aranta ta ce“Wannan gyatumar taka mana, kaima ai kanada kuji shi d'an ak'ida kawai, sai na cinye jarabawarka, insha Allah.â€
Jaddatu ta ce“Jeka maza, nima bari naje na kwanta.â€
Hannun mahaifiyarsa ya kama suka nufi b'angaranta.
Sai da ta kwanta ya ce“Abokiyar kwan naki dai jibi zata dawo.â€
Dariya Jaddatu tai ta ce“Ai kam asha rigima Allah ya nuna mana da ran da lafiya.â€

Baiga Raiyana ba a falon sai Tv take surutu, ya rufe dukkan k'ofofin ya kashe Tv da fitulun falon, ya d'auki system da wayoyinsa ya haura sama, kai tsaye beni na 2 ya wuce wajan Rahma bai tsaya ajiye kayansa ba!..._*Yar Ajin Tubarkallah🥰*_



*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*


TSINTACCIYA
Nimcyluv

SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA



Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/2/22, 09:18 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_


*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_
🔥FITATTU HUƊU🔥*


_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_


_Labarin nan zan iya kiransa da *BAKANDAMIYATA🥰* tabbas. Kusan meyasa nace hakan? Humm! Muje zuwa. Tabbas salon labarin cike yake da zallar k'auna da soyayya mai rikitarwa, shak'uwa iya shak'uwa, akwai rikita-rikita, da_ chakwakiya _wacce duk iya tunanin mai tunani ba lallai yaje inda nake son zuwa ba. akwai abubuwan k'aruwa darusan rayuwa salon love mai tsafta mai_ _tsuma zukata, hajiya karki yi jinkiri wajan siyan labarin nan, ki cije ki shigo daga ciki adama dake, ni dai bakina da taba, tabbas bazan baku k'aran hasken komai ba ayanzu, kune za ku d'auka alokacin da free page yazo gangara,👌ðŸ¼latsa nan hajiya kai tsaye ki sadu da marubuciyar_ *dattijon arzik'i🥰*. Don girman Allah idan ba siya zakiyi ba karki tab'oni.ðŸ™ðŸ¼
👇ðŸ¼
*Http://wa.me/+22796515805*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


_*cнapтer 9&10*_

A k'ofar d'anki ya tsaya ya na knocking, had'i da kiranta, cike da tausasa muryasa me nutsuwa da kamala.
“Baby Ummina bud'e ga Abienki yazo ya lallashe ki.â€
Rahma wacce take kwance saman tamfatsetsan royal bed d'inta, ya sha lafiyayyar shimfid'a sanye take da riga da wondo na bacci, wandon iya guiwarta rigan doguwa har k'asa, mai bud'add'an gaban.
Wani irin kyau ta yi, dogon gashinta mai samtsi da laushi, ya baje saman k'aton pillow'n yayin da rabinsa ya rufe mata fuska.
Ahankali take jin sautin daddad'ar muryar Abienta na ratso ta falon ta, kai tsaye ya zarce har bedroom d'inta, ta shige dodon kunnenta.
D'an k'aramin bakinta ta turo gaba, had'i da muskutawa, yayin da ahankali ta fara qoqarin bud'e k'ananun kyawawan shanyayyun idanunta, wanda sun b'ata lokaci a lumshe, tana aikin janyo numfashinta wanda yake sama yana qasa.
Tar ta bud'e idanunta had'i da yink'urawa ta zauna saman bed d'in, jin har yanzu daddad'ar muryan Abienta na ratso dodon kunnenta.
Gashinta da ya rufe mata fuska ta janye gefe, ta yink'ura ta sauko, ta d'aure rigar baccinta da igiyoyin gaban rigan, ta sanya silipas ta nufi hanyar falon tanata qoqarin fizgo numfashinta wanda yake ta mata farazanar d'aukewa ba tare da k'wak'waran dalili ba.
Key ta murza ta bud'e k'ofar, ba tare da ta kalli Abien nata ba, ta kalli k'asa tana wasa da zara² fararen yatsunta wad'anda suka Sha zanen Jan lalle.
K'afafun Abienta ta kalla farare tass sanye da silipas, dab da su system d'insa ne ya ajiye ya d'ore wayoyinsa a sama.

Abdul Majeed ya zubawa 'yar tasa narkakkun idanunsa, ya saki wani irin guntin smile, ahankali ya tako zuwa dab da ita, wanda fitinannan k'amshinsa ya buwayi hancinta.
Tattausan hannunsa ya sanya ya janye mata dogon gashinta,wanda ya rufe mata kusan dukkan fuskarta, ya d'an rankwafo ya lek'o fuskarta, yana sakin smile.
idanunsa akanta ya kusanto fuskarshi dab da tata, har suna jin hucin junansu atausashe ya kirata “Baby ummina! Oya zo naji me Abien ya yi um? D'ago mana baby ummiterh.â€
Jin muryasa dab da kunnenta daddad'an k'amshin da yake fitowa daga bakinsa, ya mamaye mata dukkan k'ofofin hancinta.
Dad'in k'amshin ya sanyata jan wani irin wahalallan numfashi, wanda taji lokaci d'aya yana qoqarin barin gangar jikinta. Da iya kacin k'arfinta take janyo numfashinta da yake son tsaya iyakacin k'arfinsa.
Hakan ya sanya zuciyarta wani irin matsanecin rauni, wanda ya janyo zuciyar ta fara bugu da dukkan iya k'arfinta, jikinta ya fara wani irin b'ari, yayin da wani irin fitinannan sanyi ya kawoma dukkan illahirin jikinta farmaki, lokaci d'aya, sanyi ya fara bin gab'ob'in jikinta, da dukkan wata k'ofar mahudar gashin jikinta, sannan tin daga cikin tafin k'afarta zuwa har k'wak'waluwarta, sanyin yake ratsa.
Abienta ya ce“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ummina! Bakida lafiya ne?â€
Ya k'arashe maganar ya janyota cikin jikinsa ya rungumeta k'am-k'am, ya d'ago fuskarta yana shafawa yana hura mata d'umamanmiyar iskar bakinsa mai fitar da wani irin d'umi had'e da k'amshi marar misali.
Numfashinta da yake barazanar tsayawa ta fizgo da k'arfin gaske tana sanya dukkan hannayenta ta zagaye bayansa, ta fashe da wani irin rikitaccan kuka, cikin fizgo numfashi ta kirasa.
“Abiena zan sha ruwa mai d'umi.†ta k'arashe mgnar cikin shashek'ar kuka.
Abdul Majeed ya rikice yana famar buga bayanta ya ce“Ya Ilahi! Baby wai me na miki? ji yadda zuciyarki take bugawa. Ok naji muje na had'a miki tea me zafi, don Allah ki daina min kuka zo kiji yadda zuciyana ke bugun uku².â€
Ya k'arashe mganr yana kamo lallausan hannunta ya d'ora tsakiyar faffad'an k'irjinshi.
Rahma jin yadda zuciyar Abienta yake bugawa iya k'arfinta, ya sanyata tattaro nutsuwa ta k'arfi ta fara shafa k'irjin nasa ta tura kanta tsakiyar k'irjin nasa, tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta kira shi asanyaye.
“Abiena!â€
Ya amsa da “Na'am zuciyar Abienta! ke d'aya k'wal ubangiji ya mallaka min aduniya, banga anfanina ba idan har zan barki acikin damuwa.â€
Ya k'arashe maganar ya na d'aukarta cad'ak kamar baby ya juya ya fara taka matattakalar benin.
Rahma ta had'iye kukanta sbd kalamansa sun saka mata tausayinta, ta tura kanta tsakiyar k'irjin Abienta tana sauke ajiyar zuciya, ajere².
K'asa ya sauko da ita ya zaunarta saman kujera, ya manna mata kiss saman kumatunta, yaje ya kunno fitilun falon masu haske, ya shige kitchen.
Rahma ganin bai dace tabar mahaifinta ya yi mata aiki ba ya sanya ta mik'e cikin sauran d'an kuzarinta da ya rage mata ta iskosa kitchen.
Ashagwab'e ta ce“Abiena kawo na had'a.â€
“No! Ummina!â€
Kai ta d'ago ta kalle shi tana kwab'e fuska, gira ya d'aga mata yana sakar mata lallausan murmushi.
Itama murmushin yak'e tai dan ta rasa abinda yake damunta, bayan abinda Raiyana tai wa mahaifinta tabbas akwai damuwar da ta kasa gano meye.
Tayi nisa cikin tunani taji tattausan hannun Abienta ya rik'e nata yana janta tare da fad'in.
Muje naji me ke damun ummina.â€
Zaunar da ita yay ya zauna dab da ita, yana hura mata had'add'an tea d'in da ya mata da bakinsa.
K'ananun kyawawan idanunta ta zuba masa, tana sanya yatsarta aramun dimple d'insa, wanda yake lob'awa, sbd yadda ya dage yana hura mata tea d'in da Iskar bakinsa yana murmushi, ya ce“ Oya zo ki sha.â€
Ya k'arashe mgnar ya na tallafo gefen fuskarta, ya kafa mata cup a mitsitsin bakinta.
Marerece fuska tai tana kallonsa.
Fuska ya had'e ya ce
“Oya.â€
Luf ta lab'e ajikinsa ta lumshe k'ananun fararen idanunta tana shan tea d'in, cike da nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta samu ayanzu², wanda take ta tafi duniyar tunanin abun da batasan meye shi ba.
Dariyar Abienta ta dawo da ita daga duniyar tunanin.
Kyawawan k'ananun idanunta ta bud'e ta tsurama kyakkyawar fuskar Abienta ido yadda yake mata dariya yana rik'e da fuskarta, ya nuna mata cup d'in vide ma'ana ba komai, ya shanye tea d'in amman sai famar rik'e hannunsa take tana kai cup d'in bakinta.
Fuska ta kwab'e tana tura yatsarta a ramin dimple d'insa, tana matsar k'ananun lumsassun idanunta.
“Sorry mah baby ummina muje ki kwanta, yau busy nayi dayawa ba shareki nayi ba kinji bugun zuciyata ummina.â€
Rahma ta zumb'uro k'aramin bakinta gaba, cikin sanyita da rauninta akan Abien ta ce“Abiena! Ko kirana baka d'aga ba fa! Ga shi gobe zaka tafi tsawon kwanaki ban ganka ba Abiena!â€
Ta k'arashe mgnar cike da rauni wanda ya bayyana qarara akan kyakkyawar fuskarta, har k'walla sun fara taruwa, tai saurin mayar da k'wallar, ta daure batayi kukan ba!
Wani irin wahaltaccan numfashi ya janyo da k'arfi, ya feso da iskarsa waje, saman fuskarta, tare da shafa fuskarta a raunace cike da tausayin 'yarsa d'aya tilo kamar tsoka d'aya acikin miya, ya ce “Afuwan Baby ummiterh zanyi qoqarin dawowa akan lokaci domin na baki dukkan kulawar uwa da uba suke bawa d'ansu,na ji dake na tarairaye ki na baki lokacina fiye da kowa har sai hutunki ya qare kin koma Espagne, oya muje ki kwanta kinji Babyn Abienta.â€
Cike da rauni ta jinjina kanta tana janye jikinta.
Kama lallausan hannunta yay suka nufi wajan kashe makullan fitulun falon wanda k'wayayen sun kai guda 12 kala² hannunta ya sanya saman ma kashin fitulun ya danna yatsotsinta falon ya gauraye da duhu, yay murmushi k'asa² ya ce“Oya dodo Kama ummina...â€
D'an guntun qara tai ta fad'a jikinsa ta k'ank'anme shi cike da zallar shagwab'a ta ce“A'a fa dodo oya tafi sha'aninka Baby na tare da Abienta ba wani abin cutarwa da zai iya cutar da ita.â€
Ta k'arashe mgnar tana murmushi.
Ba sake mgna ba yay murmushi ya kunna fitilun haske ya bayyana, janyeta jikinsa ya kama hannunta suka nufi sama.
Ak'ofarta ya saki hannunta ya mata kiss agoshi ya ce“Oya ummina bacci mai dad'i ki kasance cikin amincin Allah har zuwa wayewar gari.â€
Ya k'arashe mgnar ya d'auki wayoyinsa da system d'insa.
Rahma ta ce“Abiena kaima ka kasance cikin duk abinda ka lissafomin fiye da hakan, I love u Abiena bye.â€
Ta d'aga masa hannu tana shigewa ciki ta murzawa k'ofar key.
Juyawa yay ya fara tafiya wani irin sihirtaccan murmushi d'auke akan fuskarshi.
Yana saukowa daidai k'ofar d'akin Raiyana yaji motsi, hakan bai saka shi waigawa ba, ya gifta ya ji muryan Raiyana, tana kiransa.
“Abien Ummi inada mgna.â€
Waigowa yay ya fad'ad'a murmushin fuskarshi, ya ce“Ok inajiâ€
K'arasowa tai tana danne mugun haushinsa da takeji, ta marere fuskarta kalar tausayi, ta ce“Sbd Allah tin yaushe wajan Ummi kake? amman ni kuma kamar ba matarka ba? Gsky gatan da kakewa...â€
Da sauri ta had'iye abinda zata fad'a ta waske ta gyara kalamanta ta ce“Allah ya qara maka lfy ya barma kai nida Ummi babba da Ummi 'yar lelen Abdul Majeed, kana son 'yar dayawa gaskiya, nima Allah ya bani haihuwa da kai.â€
Ta k'arashe maganar tana qoqarin rungumeshi.
Bai hanataba ta wani shige jikinsa ta k'ank'ameshi tana shak'ar daddad'an ni'imataccan turarensa, wanda ya gauraye da turaren Rahma.
Can k'asa ya ce“Hankalinki ya kwanta? sakeni toh, Sam bakida kunya har kin manta tijaran da kika min?â€
Ya k'arashe mgnar yana zamewa ya juya ya nufi bedroom d'insa.
Raiyana sororo ta tsaya tana kallonsa har ya shiga ya rufo k'ofa.
“Hummm Abdul Majeed zaka shigo hannune da izinin Allah.â€
Ta fad'a tana shigewa ciki.
Rahma kai tsaye saman bed ta fad'a ta shige wani irin lallausan bargo mai fitar da sihirtaccan k'amshi,ta rungume k'atuwar Teddy d'inta, tana mai karanto addu'o'in bacci.
Minti 7 bata cike ba wani irin dadd'an bacci yay awon gaba da ita.
Abdul Majeed yana shiga, shirin bacci yay ya shirya cikin wasu kayan bacci masu masifar kyau da laushi, ya kashe dukkan wayoyinsa yabi lafiya royal bed d'insa, bakinsa bai daina karanto addu'a ba har bacci ya d'auke shi mai cike da nutsuwa.

*Washegari.*
Niger Diffa

K'arfe 5 saura na asuba bus d'insu Ja'afar ta cira daga garin damagaram zuwa Diffa.
Tafiya ta tsawon 7 hours sukayi acikin bus, kafin su iso garin Diffa.
Suna sauka daga gidan bus suka shige rumfuna da aka tanada dan bak'i, suka zazzauna bayan sun huta sunyi abinci sunyi sallah, sun nutsu.
Ja'afar ya kalli wayansa yana jujjuyata zuciyar ba dad'i tun jiya, dan tabbas yasan Ibtisam d'insa tana cikin damuwa.
Manyan idanunsa ya lumshe ya bud'e ya kalli Yahuza da Harisu abokan tafiyarsa, sai hirasu suke cikin walwala, sunata dariya.
Tsuki yay ya shafi sumar kansa, ya ce.
“Kufa ku tashi musan nayi hutun ya isa haka.â€
Harisu ya ce“Uban gidana kak'i fad'in garin da zamu dosa kai tsaye, tsakanin Tchad da Cameron? Ko muje Tchad idan baja sai mudawo Cameron ko?â€
Ja'afar ba tare da ya kallesu yana danna wayasa, yay dialing d'in number Baaban sa, ya ce“Inaga muje Tchad zaifi ko?â€
Yahuza ya ce“Wlh nima nan nafi kwad'aituwa, Allah yasa mu samu aiki na k'warai acan.â€
Ja'afar ya amsa da
“Ameen. Oh! Na rasa Baabaâ€
Ya fad'a yana sake kiran number mahaifinsa bata shiga.
Harisu ya mik'e ya d'auki jakarsa ya ce“Muje zama ba namu bane.â€
Basu musaba suka mik'e kowa ya d'auki jakar matafiyansa suka fito nan k'ofar sonef suka shiga keke napep.
Ja'afar yace ma me napep.
“Yauwa don Allah tashar mota zaka kaimu inda zamu samu motar Tchad. â€
Me napep ya ce“Akwai kuwa amman yanzu kwanan hanya zakuyi dan akwai tafiya.â€
Ja'afar ya ce“Ok muje mun gode fatanmu mu sauka lafiya shine kawai.â€
Nan me napep ya nufi babbar tashar motocin, ya kaisu har layin motocin Tchad, cikin ikon Allah mutum ukune daman suka rage sai ga su Ja'afar. Nan suka shiga mota kamasho ya amshi kud'insu ya sallami direba nan mota ta tashi jama'ar ciki kowa na addu'a, cikin nasara yanzu Ja'afar ya gwada kiran mahaifinsa ya sameshi.

*TAHOUA*
Unguwar Moray

Malam Adamu yana tsakiya da cin abinci, wanda kullun sai yayi sallar azuhur 2 yake zauwa cinsa agida, ko kusa baya cin abinci wajan sana'arsa.
Kiran da ya shigone ya sanya shi saurin kai lomar abincin bakinsa, ya d'auki wayan da take gefensa ajiye.
Ganin Ja'afar ne ya fad'ad'a fara'arsa, ya d'aga kiran tare da sallama, yana fad'in.
“Ma Sha Allah Ja'afar yanzu kuna ina? Tin jiya wayan take kashe na barta a chaji yanzu na cirota.â€
Ja'afar wanda motarsu ta fita daga cikin Tasha, ya ce“Baaba ina yini? Asamu cikin addu'a gamu zamu Kama hanya, abani innata idan tana kusa.â€
Malam Adamu ya ce“Allah ya saukeku lafiya ya rabaku da sharrin dukkan abin k'i Allah ya baku sa'ar tafiya, bari na kaiwa Hansatu wayan.â€
Daga can Ja'afar ya ce“Ameen Baabana Ngd. â€
Malam Adamu ya fito wayan akunnensa sai addu'a yake jeroma Ja'afar.
Inna Hansatu tana zaune a inuwan dalbejiya, ita da Deluwa tana lissafin ribar da ta hayo mata ayau sai washe baki take, sabida kusan d'ari uku taci riba, ta ce“Ina laifi sbd Allah ga shi anata cin ta sadaka agida ai na zaune baiga gari ba wlh.â€
Deluwa ta ce“Allah ya qara albarka hannu ya kuma k'aro kasuwa. Hansatu kinyi mgna kuwa da Ja'afar?â€
Inna ta ce“Ameen fa kam tinda ana cin ta sadaka sosai. A'a wlh ni da wayana taci battery sai an siya, kekuma an sace taki, sai ta Malam...â€
Isowa yay yana fad'in.
“Yauwa ga iyayan naka zaune, anata lissafi, Delu amshi ki masa fatan alkhairi.â€
Deluwa ta amsa tana kara wayan akunnenta, tare da sallama.
Ja'afar ya gaisheta, ta amsa tana masa addu'a, ta bek'awa inna mai waina.
Inna bayan ya gaisheta ya fad'a mata suna hanya, ta shiga kwararo masa addu'a akan Allah ya had'asa da mutanan arzik'i inda shima zaiyi arzik'in.
Sai da ta idar da masa addu'ar arzik'i ta ce“Allah ya kaiku lafiya bak'in buzuna.â€
Ja'afar ya girgiza kai yana murmushi ya ce“Ameen innata Ngd ban Baaban.â€
Wayan ta ba Malam tana fad'in.
“Gaskiya Malam ka siyo min battery d'in waya domin Allah fa.â€
Deluwa ta ce“Ni kuma ko rakani Masai ce asiyo min.â€
Dariya ya musu yace“Insha Allahu zan siya muku Allah ya mana bud'i na alkhairi.â€
Ya k'arashe mgnar yana komawa d'akinsa.
Inna mai waina ta tab'e baki ta ce“Wai Deluwa meyasa kikeda bin gasane? Mufa ba yara bane.â€
Deluwa ta ce“Ameen Malam mun gode. Allah baki hkr ai gaskiya ce ke mai sana'a ma kin roqa bare ni mai zaman banza.â€
Inna ta ce“Akoyi Sana'a zama zaunewa deluwa, au kice saa'ar waina abaki take?â€
Deluwa dariya tai ta ce“A'a wlh ni kam sai dai na biki da fata alkhairi.â€

Unguwar geban zogi
Ibtisam tin jiya batada wani sukuni arayuwarta, yau tin safe zazzab'i ya rufeta, sai da Tanko ya kaita asibiti wajan 9 na safe aka mata allura gudun karta rikice musu, dan bata iya ciwo ba. Alhmdllh jikin ya yi sauqi.
Zaune take arumfar k'ofar d'akinsu,tana shan lemon zak'i, Aydah na ma Nadra tsifa sai zungurata take, Fu'ad na musu dariya, yayin da Taslim mai bin Ibtisam 'yar kimanin shekaru 14 tana famar qanqaran farce.
Ramadan ne kad'ai baya gidan, duk k'anen Ibtisam ne.
Sanye take da riga da siket na atamfa mai sauqin kud'i, amman d'inki ya mata kyau, fuskarta ta rame kamar ta tashi daga jinya.
Laraba ta kalleta ta ce“Don Allah Ibtisam ki ajiye hankalinki ki manta da waccan yaron ki tsaya ki saurari mazan kirki masu sonki da alkhairi.â€
Taslim ta ce“Haba Anna ki barta mana ai ba'asan abinda Allah ya shirya atsakanin su ba.â€
Laraba ta ce“Iyeee! Taslim duk nawa kike har kike shiga mgnar masoya? Wlh zanci ubanki.â€
“Toh Allah ya baki hkr Anna amman wlh banson ki matsa...â€
Wani guntin ice ta jefo mata ta mik'e aguje ta shige cikin d'akinsu.
Ibtisam batace komai ba ta mik'e kamar an tsikareta, tana zumb'uro baki gaba tana diddira k'afafunta.
Laraba ta ce“Zanga yadda za ki aure shin dan ubanki....â€
Tanko da yake shigowa mak'ale da waya akunnensa ya ce“Yauwa d'ana munata muku addu'a kaga ganima agida na shigo bari na baka k'anwar taka Ku gaisa, nasan kana son tambaya nauyi ya Hana. Ke Ibtisam taho amshi kuyi bankwana sun d'auki hanyar Tchad. â€
Ibtisam ta langwab'ar da kanta ta fara rau-rau da idanu ta ce“Wayyo Baba Wa?â€
Tanko ya ce “Amshi manaâ€
Ibtisam ta amsa ta kara akunnenta.
Jin murya Ja'afar ya saka ta nufi d'akinsu aguje.
Laraba ta
Showing 9001 words to 12000 words out of 164819 words