su Abdallah kawai a waje.
     Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ɗan gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
       Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ɗaya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ƙa'ida bana waje ɗaya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in taƙaice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”.
          Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “ALLAH yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ɗiyar ɗan uwan nasu dama ɗan uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.

        Kamar da wasa sai ga su Abbah sun shafe fin awanni bakwai amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. Shigar lokacin sallar la'asar ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
       Wata cikkakkiyar awa biyu suka sake sharewa gangariya, Abban Abdallah na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor ɗin nan mace mai suna Doctor Ai'sha yaji yaya ake ciki? sai ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta washe da murmushi.
      Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo.
          Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
       Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Nu'aymah da ke a hannunsa yana dubawa. Ya ɗan rame, hakan ya saka sake fiddo hasken fatarsa da ƙyawun da ALLAH yay masa. Ga wani annuri na hasken ibadar ALLAH tattare da shi, wanda ya sake ɗaukaka ƙwarjininsa da cikar haiba kai kace farin watane ɗan daren sha biyar. Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Coffee color, sai farar shirt da ke a ciki babu necktie, dan maɓallan Shirt ɗinma kusan uku a buɗe suke.
        Doctor Aysha na daga gefen damarsa duk da yaɗan zartata kaɗan a tafiyar kasancewar ya fita tsayi, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Solomon dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Sa'ad da wasu likitoci biyu da Nurse kusan huɗu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abban Abdallah bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Nu'aymah ke ciki suka ja birki, su Abdallah da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin.
        Iya shi da Doctors ɗin suka shiga, yayinda Solomon da Nurses ɗin suka ja birki a bakin ƙofar.
      Sai da ya ƙarasa gab da gadon da Nu'aymah ke kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin tsirgawa zuciyarsa tayi ba, amma saboda son sake gaskta abinda yake tunanin sai ya zare Glasses ɗin idonsa da ya ƙara ƙawata fuskar tashi. ‘Kamar dai itace’ ya ayyana a zuciyarsa cike da kokwanto.
        A fili kam sai yay saurin maida mata na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na vibration har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Aysha a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shiga matakin ƙarshe, ina mamakin yanda mutane suke abu tamkar basu san muhimmacin lafiya ba. Mtsoww!!. Su Iyayenta fa?”.
      Dr Sa'ad ne ya bashi amsa da “Haka suke wlhy Doctor, sai kuma an mutu suce likitoci ne da sakaci bayan tun farko sune da matsalar su.........”
         Cikin sauri Dr Aysha ta katse Dr Sa'ad ɗin dan bata son ya sake tunzura Dr Yoohan, “Ayi haƙuri sir, duk family nata suna waje, duk da kasancewarsu manyan mutane suna tare da ita tun ɗazun fiye da awa tara wlhy”.
      Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Nu'aymahn, sai kuma yay azamar ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yay zai fita. Doctor Aysha tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye su ka sake bin bayansa ita da su Doctor Sa'ad da ke ta faman cika yana batsewa saboda haushin kare dangin Nu'aymah da tayi.
       Yanzun ma bai duba kowa ba a cikin su Abdallah yay wucewarsa. Duk da kallo suka sake binsa suma, yayinda Abban Adawiya yaso gane sa, sai dai baiyi magana ba jin suma su Abban Abdallah basu ce komai ba.
        Da ga shi sai Solomon suka shiga office ɗinsa, komai ƙal yake, dan tunda Dr Aysha ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa'ida kullum sai an share an goge. Ƙaramin ɗakin hutun dake cikin office ɗin Solo ya ƙarasa. Ganin nanma komai dai-dai yake yanda yasan Yoohan ɗin na buƙata sai ya ajiye jikkar ya fito.
      Tsaye ya iske sa yana ƙoƙarin zame rigar suit ɗinsa, har Solomon ɗin ya kai ƙofar fita ya tsinkayi muryarsa ya na faɗin, “Kiramin Dr Aysha”.
       “Okay sir”.
     Solo ya faɗa da sauri yana ficewa. Hanging ɗin rigar yayi bayan kujerarsa ta zama, sannan ya fara ƙoƙarin kunna Computer ɗin da ke a saman desk ɗin na sa. Yanda yay matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Aysha ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, dan tasan ba lallai ta samu amsa ba musamman a irin wannan lokacin da ta tabbatar hankalinsa gabaki ɗayansa nakan patient ɗin da ke jiran taimakonsa.
      Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin theatre yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”.  Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta ko mijinta. Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
      Ɗan jimm Dr Aysha tayi. sai kuma komi ta tuna oho, ta gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice shi kuma ya miƙe ya nufi ɗakin da ke a cikin office ɗin.........✍

         
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 37

............A tsaitsaye ta iske su Abba gaba ɗaya yanzun kam. Cikin girmamawa ta ƙarasa garesu. Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”.
     Cike da jin daɗi suka shiga faɗin Alhmdllh.
       Da ga haka ta buƙaci magana da su Abbah. Babu musu suka bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu da Dr Yoohan ya sanar mata, Abba Musbahu ne ya nuna ai suma iyayen Nu'aymah ne idan sun saka hannun babu damuwa, tunda yayansu baya a kusa, gashi kuma tace za'a shiga aikin ne da gaggawa........
     Ita dai kasa ce musu komai tayi dan suna da girma da kima a idonta, sannan kuma ta tabbatar tunda Dr Yoohan yace a cikin ukun ɗaya ake buƙata dolene hakan za'ayi. Ganin shirun da tayi ne ya saka Abban Adawiya fahimtar akwai matsala, dan haka sai ya kalli ƴan uwansa, “Inaga kawai mu kira Yayan kamar zaifi fa'ida, dan sun fimu sanin muhimmancin sharɗanta hakan”.
    Duk sun gamsu da bayaninsa. Abban Abdallah ya ciro waya yay kiran Baba malam. Kirannasa ya shiga wayar baba malam ɗinne dai-dai lokacin da Umm da Hajjo ta shafama ruwa a fuska ta kawo nannauyan numfashi alamar dama suma tayi. Kusan a tare duk suma suka sauke numfashin, musamman ma baba malam da ke jin kamar an tsundumasa a aljanna.
    Ba ƙaramin faɗuwa kuma gabansa yayiba ganin kiran ɗan uwansa, amma sai yay ƙarfin halin ɗagawa ya saka a kunne. “Rudwan ta rasu ko?”.
    Da dauri Abban Abdallah yace, “A'a Yaya tana da ranta”. Da ga haka yayma baba malam bayanin halin da ake ciki. Kamar baba malam bazaice komaiba. sai kuma ya nisa kaɗan da faɗin, “Shike nan ina zuwa”.

★★★★
   
             Bayan saka hannun baba malam Yoohan da wasu likitocin biyu sai Dr Aysha ta uku suka shiga theatre room da Nu'aymah da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.
     Tun suna irga mintuna har suka koma awanni, dan anyi sallar magrib har isha'i su Yoohan basu fitoba. Duk jikinsu ya kumayin sanyi. amma saboda ƙarfin hali irin na baba malan haka ya bama matan da samarin ƴaƴan nasu umarnin suje gida su huta haka nan. Basu da ikon masa musu akan hakan, amma a kallo ɗaya zaka fahimci ba haka suka so ba, dan Abdallah kasa daurewa yay kansa a ƙasa yace, “Abba da ku kuje kawai, ni zan zauna har su fito insha ALLAHU”.
     Da sauri Naser shima yace, “Abba nima ina nan harsu fito dan ALLAH”. Ta ƙasan ido Abdallah ya ballama Naser harara, amma dai baice komai ba.
       Shiru kawai baba malam yay yana dubansu, dan shi harga ALLAH tausayi suke bashi. Kafin baba malam yace wani abu Hajjo tace, “Ai mu duka ma tafiyar tamu bamai yuwuwa bace ba, dan ya kamata muga fitowarsu ko ma tafi da ɗan ƙwarin gwiwa. ALLAH dai ya bata lafiya”.
      Duk da Amin suka amsa mata. Daga haka kuma babu wanda ya sake cewa komai, suka sake cigaba da zaman jiran tsammani.

       Sai kusan ƙarfe tara na dare dai-dai su Yoohan suka fito, duk su baba malam suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki?  Su Doctor Aysha ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Yoohan yana ɗakin bai fito ba tukunna.
      A tare suka shiga faɗin Alhmdllhi, Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Nu'aymahn ta tashi garas bane ba.
        Su Dr Aysha da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Nu'aymah a yanzu, hasalima ba'a buƙatar kowa a gareta.
          Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Mubarak ɗin, dan haka baba malam yace su wuce ɗin kawai, dama gashi sun baro Umm ita kaɗai a gida sai su Hajarah da ke a tare da ita.

          ★★★★‡★★★★

      Kamar jiya yau ma baba malam ba shine yaja salla a massallaci ba, hakama bayan an idar bai zauna wajen karatu ba ya shiga gida.
          Tun a daren jiya ya gama yanke shawarar da ta dace akan wannan al'amarin, dan haka koda ya shigo gidan waya ya ɗauka, ya rubuta gajeren text massege ya tura. Umm na zaune na azkar tana kallonsa. Yanda baice mata komaiba itama batace ɗinba har sai da ya kammala ya ɗago yana kallonta.
      Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, “Ki ƙara haƙuri Jannat kinji, nasan kina cutuwa matuƙa, amma inason ki ɗauki komai matsayin jarabawa, kinsan ita duniya dama UBANGIJI bai yita dan ta kasance abin jin daɗin ɗan adam ba a kullum”.
         Ƙwallar da suka cika mata idanu ta haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Insha ALLAHU, ALLAH ya bamu ikon cinyewa”.
       “Amen ya rabbi” ya amsa mata shima.
        Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa, a haka har gari ya ƙarasa wayewa tangaran. Duk da Umm bazata iya aiki ba haka ta fita cikin dauriya ta lissafama Rabi abinda zatayi. Ita kuma ta koma ɗakin baba malam inda ta tarar zai shiga wanka.

★★★

       A ɓangaren Abdallah kam tun a daren jiya ya karɓa Number Yoohan a wajen Ahmad. Babu irin tambayar da Ahmad ɗin bai masa ba akan mizaiyi da Number amma yaƙi faɗa masa. Dan haka ya ƙyalesa kawai yay kwanciyarsa.
        Tun a daren ya fito harabar gidansu ya kira wani abokinsa SSS, bayani ya kora masa akan taimakon da yake son yay masa, babu musu kuwa ya amsa zaiyi. ya buƙaci Number Yoohan a take ya tura masa ita da ƙara jaddada masa dan ALLAH zuwa gobe yake buƙatar result.

       A safiyar yau kam kusan ƙarfe bakwai da kwata sai ga kiran abokin nasa. Bayan sun gaisa da ɗan tsokanar juna kamar yanda suka saba ya sanar masa aikinsa ya kammala, yaya yakeso ayi?.
       “Wow gaskiya na gode matuƙa Mahmood, amma nayi mamakin jin mai Number wai yana a kano, kasan a yanda naji Abuja yake da zama”.
       “Eh to, zata iya yuwuwa kanon yazo, dan a yanzu hakama sai da na sake tabbatar da yana a inda muka gansa jiya sannan na kiraka, dama wannan shine amfanin tracing ɗin ai”.
         “Gaskiya kam, aiko nagode sosai. Abu nagaba shine zanzo mu haɗu yanzun, dan ina buƙatar a kama min shi ne”.
      Dariya sosai Mahmood ya keyi, yace, “Shegen sama mi yayi maka ne? Halan wata harƙallar kuka ƙulla ya doje?”.
        “Ai harƙallar dake tsakanina da wannan shegen ta wuce duk yanda zakai tunani wlhy Mahmood, kai dai faɗamin inda kake nazo na sameka kawai”.........

     
   ★∆∆★

          Sai ƙarfe shida da wasu mintuna ya farka na safiya. ya tashi a ɗan firgice bakinsa ɗauke da addu'ar barci da ALLAH ya bashi ikon riƙewa a lokaci ƙanƙani kamar yanda baba malam ya koyar da shi. Tunda ALLAH yasa ya musulinta yau ne karan farko da zaiyi sallar asubahi a makare. Dan alarm yake sakawa gudun karya makara. Sannan kuma baba malam duk asubahi sai ya kirasa ya tadashi. Hakan na masa daɗi, yana kuma ƙara masa ƙwarin gwiwa. Dalilin makarar tasa ta yau ma dan bai kwanta da wuri bane, dan tun bayan fitowarsu theatre ya duƙufa ne akan binciken matsalar Nu'aymah. Dalilin binciken nema ya sakashi kwana a asibitin, Solomon ne kawai yaje Hotel ya kwana.
        Bayi ya shiga ya ɗauro alwala ya fito, ya buɗe jakka ya ciri sallaya da yanzu bai rabo da ita a kayansa duk inda zaije, shimfiɗawa yayi sannan ya zura jallabiya ya tada salla. Yana idarwa saƙo na shigowa wayarsa, sai dai baibi takai ba ya miƙe ya fita dan yana son duba patient ɗinsa.
       Kusan mintuna ashirin ya ɗauka a ɗakin da Nu'aymah take sannan ya fito ya koma office. Yanzunma baibi takan wayarba dai ya shiga wanka. Bayan ya fitone ya ɗauka wayar saboda ganin screen ɗin yana haske. Missed calls ne har uku yaci karo da su duk na Mumynsa. Bai kirata ba sai ƙoƙarin duba saƙon da ya gani yay cike da mamakin ganin baba malam ne.
         Yana gama duba saƙon yay ƙoƙarin kiran baba malam ɗin. Cikin sa'a kuwa ya ɗaga. Tamkar yana a gabansa haka ya rissina da girmamawa ya gaida shi, shima kuma da ga can baba
Showing 126001 words to 129000 words out of 303604 words