duk dan ta ishesa
amman duk da haka a takure yake da alama kuma sanyi yake ji, gashi taga kamar blanket d’aya ne a d’akin kuma ya rufa mata Pillow kawai ya d’auka ya kwanta a kai
ya turo k’ananan throw pillows d’in sofar k’asa…….

Hasken fitilar ta ne ya farkar da shi….ya farka amman bai bud’e ido ba.

Tsintar kanta tayi da komawa gadon, a nan ta ajjiye wayarta still bata kashe flash d’inba (dan ta ga haske) ta d’auko blanket d’in ta dawo wajen da yake kwance.
A hankali gudun kar ya farka
ta d’an sunkuyo ta lullub’a masa blanket d’in tun
daga k’afafuwansa har zuwa wajen wuyansa…
Ajiyar zuciya taji ya sauk’e dan haka ta yi saurin kallon fuskarsa a tunaninta ko ya
farka ne amma sai taga baccinsa yake yi peacefully..
Gaba d’aya sai taji tausayinshi ya rufe ta…ta tabbata d’umin ne ya sanya shi jin dad’i har cikin baccinsa yana sauk’e ajiyar zuciya…ya san yana jin sanyi amman ya hak’ura ya lullub’a mata shi ya kwanta a haka…
A hankali take nazarin tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
Durk’usawa tayi sosai a gabansa kamar mai zaman
tahiyya.
A hankali ta shiga kallon fuskar tasa tun daga kan sumar kanshi zuwa straight girarsa..duk da idanunsa a rufe suke amman hakan bai hana ta ganin kyawun da idanun suka k’arawa fuskar tasa ba, ga wasu kyawawan zara zaran lashes, dogon hancinsa ta kalla tana mamaki da girmama kyawun halittar Ubangiji……….
Ta dad’e tana kwad’ayin son ta yiwa fuskarshi nutsatstsan kallo saboda ita har ga Allah
tunda take a rayuwarta bata
tab’a ganin kyakkyawan Namiji kamar Ya Aslam ba! Komai nasa mai kyau ne, ga
muryarshi idan yana magana kamar kar ya daina……….
Kallonsa kawai take yi sosai tana nazarin, dan har
d’an matsawa ta yi kusa da shi sosai ba tare da ita kanta ta sani ba!
So take ta gane me yafi kyau a fuskarsa! Hancinsa ne ko kuma idon ko cikakkaiyar straight brows d’insa, amma ta kasa, taso ace idanunsa
biyu ta samu ta yiwa idanuwan nutsatstsen kallo kamar haka.

So take ta d’auke kai ammman kwata kwata ta kasa…
A hankali take bin skin d’insa da kallo, fuskarsa tass
babu alamar k’urji ko zanzana ko wani tabo! K’ayataccen sajensa ne kawai ya bambanta fuskartasa da ta babies.

Ahankali idanuwanta suka kai kan d’an mitsitsin pink lips d’insa wanda yake a zagaye da lallausan siririn saje!
Ta jima tana kallo chan ya ji
tace “Astaghfirullah!!”
kafin tayi saurin runtse idanunta sai kuma ta mik’e da sauri ta juya ta fad’a toilet ko wayar tata bata d’auka ba!
Tana shiga ta banko k’ofar!.

Sai a lokacin Aslam ya bud’e idanunsa, yana wani sassanyan murmushi mai had’e da dariya…

Ta jima a toilet d’in kafin ta fito.
A zaune ta sameshi this time around da waya a hannunsa, a
ranta tace “sai kaje garin daddanna na’ura ka lalata idon”
Wucewa tayi ta d’au hijabinta ta zura ta fara k’ok’arin gabatar da nafila shi kuma ya mik’e ya nufi band’akin
da gudu ta k’arasa ta shige toilet d’in kafin shi ya shiga ta rufo k’ofar! Chaan, ta bud’e ta fito ta wuce ba tare da ta kallesa ba..
Bayanta ya bi da kallo kafin ya girgiza kai kawai yana murmushi ya shige toilet d’in,
kamar ance ya d’aga kai, yana
kallon wajen dariya ta kufce masa, abunda bata sani ba shine
jiya already ya rigada ya gani
dan kafin ya kwanta sai da ya shigo yayi alwala..
Yana dariya yana murmushi shi kad’ai haka yayi wanka cikin farin ciki da annashuwa dan shi kam Hudan already made his day yau before
it even begins.

Da towel ya fito d’aure a k’ugunsa lokacin
ita kuma juya baya tana sallah.
Cikin nutsuwa ya hau shiryawa, tana cikin sallar hancinta ya fara jiyo mata wannan azababben k’amshin turaren nasa yana k’aruwa akan wanda already ya riga kama d’akin.
Tana idarwa tayi addua ta shafa, ta gyara zamanta a nan gaban gadon kan kafet ta na jira a kira sallah.
Takun sa ta ji a hankali yana k’arasowa inda take..
Lumshe idanuwanta kawai tayi tana shak’ar k’amshinsa tana kuma sauraron yadda bugun zuciyarta yake k’aruwa dede da takun nasa.
A hankali taji yace
“Gyara in yi nafila”.
D’agowa tayi suka had’a ido..
Sanye yake cikin jallabiya bak’a mai shek’i amman
ta k’asan jallabiyar tana iya hango dogon wando bak’i
kamar na suite saboda
jallabiyar bata ida rufe duk k’aurinsa ba.

Da sauri ta mayar da kanta k’asa ta mik’e ta koma kan gado.

Yana idar da nafila ana tadaa iqama a masallaci dan
haka ya mik’e ya nufi k’ofa..
Har ya kama handle zai murd’a
sai kuma ya juyo ya kalleta, yace
“Zan fita yau da wuri.
Ina da bak’i tun jiya cikin dare suka zo kuma yau da safe suke son komawa..
Get me something simple to eat, please. Kafin in dawo a masallaci.”
Bai jira jin me zata ce ba ya murza handle d’in ya fice.

Shiruu, tayi na y’an mintuna
chan kuma ta mik’e ta tada sallah.

A nutse ta gabatar da sallarta.
Sai da ta idar ta yi azkar
tukunna ta mik’e ta d’au wayarta ta fita a d’akin.

Tana shiga kitchen d’in ta nemi globe ta kunna, ta
fara k’arewa kitchen d’in kallo
dan ita bama ta san ta ina za ta fara ba.
Ganin babu lokaci yasa kawai
ta soya omelet ta
had’a salad ta d’auko bread da kifin gwangwani ta had’a masa sandwich da tea.

Tray ta d’auko ta jera akai ta d’aura cup da tea flask d’in da su madara da sugar da teaspoon ta ajjiye dik a kai sannan ta d’au tray d’in ta fita.

Tana fita ta gansu akan dining shi da Abba duk sun shirya,
da wasu takardu suna dubawa.

A hankali ta k’araso ta ajjiye tray d’in sannan ta d’an rissina tukun tace
“Abba Ina kwana”
Tunda ta fito Abban yake kallonta yana murmushi, ba k’aramin dad’i yaji ba
“Lafiya Alhamdulillah”
Yace da ita yana murmushi yana kallonta.

A hankali ta d’an kalli Aslam tace
“Ina kwana”.
Sai da ya d’ago ya d’an kalleta tukunna yace
“Lafiya”
Sai kuma ya mayar da kanshi kan tray d’in yace
“Thank you”
Daga nan ya maida kallonshi ga takardun….

Abba ne yace
“Princess yau abun son kai ne?
Ina nawa cup d’in?
Da alama ma breakfast d’in baku yi da ni ba”

Gaba d’aya kunya sai ta rufeta
cikin shagwab’e fuska tace
“Abba ai ban san kaima zaka fita da wuri ba”
Tana gama fad’in haka
ta koma kitchen ta d’auko cup ta kawo da tea spoon.
Har zata sake komawa sai yayi sauri yace
“No wannan zai ishemu, wasa
nake miki”

Murmushi tayi daga nan ta juya ta wuce d’akin nasu.

Tana cikin karatu taji fitarsu, sai da ta ida tukunna ta tashi dukda cewar d’akin bai yi wani datti ba amman sai da ta goge ta share ta wanke toilet, ita kad’ai tana ta
mitar Aslam bashi da kunya wai k’ato da shi amman ya wani shanye mata boxes tazo ta gani ma shi bai damu ba kenan!……….

Sai wajen 9:00am sannan ta fito, lokacin gidan ba kowa daga ita sai Ummi.

A cikin parlourn ta hango ta
amman da alama ma bata san ta fito ba! Ta rafka tagumi tana kallon gefen tv d’in da take ta faman aiki ita kad’ai…
Sai da Hudan ta zo inda take ta ce “Ummi ina kwana”
Tukunna tayi firgigit ta juyo, suna had’a ido ta fara murmushi, kafin tace
“Lafiya, Alhamdulillah daughter. Ya kika kwana?”

“Alhamdulillah” itama Hudan tace tana me zama a kujerar gefenta 1 seater.

“Ki yi breakfast mana”
Cewar Ummi.

“Ok” kawai Huda tace

sannan ta mik’e taje tayi, har
ta gama ta dawo ta zauna
Ummin tana wajen bata ko chanja yana yin zama ba.

A hankali ta zauna kafin tace
“Ummi tunanin me kike yi?”



Kallonta Ummin tayi kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace
“Huda, gaba d’aya har yanzu na kasa yafe wa kaina.
Sannan guilt yak’i barina In samu peace of mind!
Ki taimaka ki yafe min sannan
inaso ki rakani wajen Mamanki In nemi yafiyar ta na san
na zalunceku”

Da sauri Huda tace
“Ummi dan Allah ki daina.
Ni kam wallahi na yafe miki duniya da lahira
Mama itama na san ta yafe miki.
Ki kwantar da hankalinki
ki daina yawan tunani, please.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Huda dukda cewa na san kina da kyakkyawar zuciya ba lalle ki aikata irin abunda na aikata ba, amman still ina me baki shawarar ki rok’i Ubangiji ya tsareki daga aikata aikin dana sani’
Guilt d’in bashi da dad’i kwata kwata na rasa sukuni, nan san
tayaya zan yafewa kaina ba.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Ummi, ki saka
a ranki da ni da Mama mun yafe miki har abada!
Sannan bamu rik’e ki a zuciyoyinmu ba ko kad’an!
Mun yafe miki har gaban abada kuma ganin ki ne kamar
komai bai tab’a faruwa ba!
Ta hakan ne zaki iya yafewa kanki.

Wallahi Ummi kinji dai na rantse miki
har k’asan zuciyata na yafe miki kuma ban rik’e ki a zuciyata ba kwata kwata”.



D’an guntun murmushi Ummi tayi tana jin k’aunar Hudan na sake shigarta, a hankali tace
“Na gode Huda but
some facts will never change, Ina jin kunyar Abba sosai
Ina jin kunyar sa…”

Hudan ta bud’e baki zata yi magana kenan! Suka fara jiyo kuka a waje…
Da sauri suka kalli juna sai kuma suka mik’e suka yi wajen….

Kaya suka gani a zuzzube
gefe guda kuma ga Jalila tanata kurma kuka tana tattare kayan nata.
Tana ganin Hudan tayi saurin k’arasawa inda take ta rik’e mata hannu tana cewa
“Huda dan Allah ku taya ni bata hak’uri, ni gani nake ma kamar ba ita bace ba ko
kuma aljanuntane suka tashi!
Lokaci d’aya kawai tace wai In fitar mata a gida!
Dan Allah Huda kar ku bari ta kore ni…”

Dede nan Mom ta fito
ba tare da ta kalle su ba ta k’arasa ta finciko hannun Jalila ta wulla ta gefe sannan tace “oya! Tattare ki fice kafin In kwace kud’in motar da na baki”

Da sauri ta mik’e tsaye ta share hawayenta ta k’araso inda Mom d’in take tsaye tace
“Mom dan Allah kiyi hak’uri,
wallahi ko wanke wanke da shara kika ce zan yi please Mom, dan Allah ki ara min kwana 7
Na yi miki alk’awarin nan da sati d’aya zan tafi wallahi.”

Cikin b’acin rai Mom tace
“Nan da kwana bakwai na san me zaki yi???
Na san kalar asirin da zaki k’ulla?
Na san akircin da zaki shirya?
Eh Jalila?”
Ta yi mata tambayar tana kallonta. Bata jira jin amsarta ba taci gaba “Kinga, wallahi tallahi tun muna sheda juna ni da ke! Ki fice mini a gida”
Da sauri Jalila ta rik’o hannunta tace
“Momina dan Allah dan annabi...”
Tass!! Mom ta d’auke ta da wani gigitaccen mari, cikin fushi tace “idan kika sake ce min Momin ki sai na datse miki harshe billahillazi. Ki kwashe tsummokaranki ki kama gabanki tun kafin raina ya ida b’aci!”
Mom d’in ta k’arashe maganr cikin fushi da tsawa.


Tun da ta kifa mata mari ta dafe wajen tana kallon k’asa, bata motsa ba! Sai da
ta bari ta kai aya tukunna ta d’ago manyan idanuwanta da suka yi jaaa tana kallon ta!
Cikin dakiya ta b’acin rai tace
“Babu inda zan fita inje Adama.”
Dariya Mom ta kwashe ta ita
kafin tace
“Perfect!” tana me gwadawa da hannunta sannan ta ci gaba
“Wannan Jalilar dama nake so ta fito ba wachchar ba!.
Yanzu zaki ga yadda ake hauka da rashin mutunci a cikin gidan nan!”
Tana gama fad’in haka ta nufi gate….
Wani christian mai gyaran fulawa ta nemo da wani soja
ta had’o su su biyu ta dawo.

Tana zuwa ta kalli Jalila tace
“Jalila ba da ni za kiyi wanann rashin kunyar taki ba da waennan za kiyi”
Tayi mata nuni da k’artin bayanta, sannan cikin bada order ta juya ta kallesu tace
“Mai aikinta ce tayi mata sata,
so ta sallameta ta koreta amman tak’i tafiya dan haka su fitar mata da ita idan
tayi turjiya su yi mata dukan mutuwa!”

Jalila ba wani turancin kirki ta iya ba amma ta fahimci me Mom d’in tace.
Ganin sojan ya tunkarota ba alamun annuri a fuskarsa yasa ta durk’usa da sauri ta fashe da kuka, tace
“Wallahi tallahi kika saka aka fitar dani sai naje na tona muku asiri ke da d’anki a wajen Granpa.”

Dakatar da sojan Mom tayi kafin a hankali ta k’arasa inda take durk’ushe. Durk’usawa itama tayi sannan ta saka yatsa ta d’ago fuskar Jalilan..
B’ata rai tayi ta yamushe fuska kalar tausayi kamar wadda zata fashe da kuka kafin a hankali yadda ta tabbatar babu mai ji tace
“Ayyah Jalila!
Wajen Granpa zaki je?
Bismillah to ki je. Amman inaso ki san
ko da ace kin je wajensa baki da wata shedar da zaki iya nunawa against ni ko Auwal!
Mai yasa kike tunanin na barki kwana uku?”
Bata jira jin me Jalilan zata ce ta bata amsar tambayar da tayi mata da kanta tace
“To get rid of all the evidence!
Sannan ta ci gaba da cewa
“Sannan tun farkon zuwanki
ranar cewa nayi
Inna tayi min message
tace min wata zata zo ta tayani y’an aikace aikace saboda an saka ranarta so tana buk’atar kud’in kayan d’aki, kinga yanzu In aka kira Inna tunda ba ita ta turo ki ba zata ce bata sanki ba ba kuma
ta san da zancen ba!
Nima kuma daman kinga Innar nace ta had’ani da ke…
Questions d’in da zasu fad’owa y’an estate d’innan a karon farko shine
“Wacece ke?
Mai yasa kikayi outsmarting d’inmu?
Tayaya kika iya hacking wayar Innaa?
Sannan me kikeso me ya kawoki?
Waye kuma ya turoki gidan nan?.
Jalila bincike In yayi bincike believe you me har sharrin y’ar boko haram sai na d’aura miki wallahi!

Family d’innan is a well known family so dole muna da mahassada da masu son cutar da mu so kinga kema a wannan sahun za a jefaki
ta yiu ke kika zo da kan ki ko kuma wanine ya saka ki kizo
gidan nan kiyi aiki ko bincike ko wani abun wanda Allah kad’ai ya san na menene!

Granpa kuwa kinga dole ya tashi tsaye yayi bincike in ta kama a hukuntaki hukunci mai mugun tsanani
Idan anyi miki mai sauk’i shine
a kaiki cell ayi ta laftarki ace sai kin fad’i waye ya turoki...
Shawara ta gareki shine
Ki guji mutumin da kika ga Auwal yana mugun jin tsoronsa!
Ki duba kiga fa
surukan gidan nan ne mu
amman da muka yi laifi ya aka yi da mu?.

Sanann maganar ciki
Already tun a ranar na biyasu
y’an asibitin sun goge history d’inki! So kinga ko kince aje chan kina da evidence
to nan d’in ma sai dai ki sake k’ulle kanki infact duk inda kikaje ma Jalila kud’i kawai zan bayar amaida lefin kanki.
Sannan hatta chat da number Auwal duk na goge wani evidence a wayarki d’azu d’azun nan da nace miki ki ara min wayarki already kuma na san pin d’inki ba tare da kin farga ba shiyasa komai ya zo mini da sauk’i…baki da wayo Jalila sannan baki iya takun ki ba dan haka baki ta evidence ko
wani abu da zaki nuna against me…
So be a good girl!
Ki kwashe tsummokaranki
ki yi gaba tun kafin waennan k’artin su miki illar da na san ko kud’in magani ma ba lalle ki samu ba!”
Tana gama fad’in haka ta cika mata hab’arta ta mik’e ta
bar gurin tana karkad’e hannunta.


Still sojan ne ya sake nufarta yace “Stand up and leave!”

Banza tayi da shi tana wani kalar kuka mai cin rai.

K’afarsa ya d’aga yayi wani mahaukacin ball da ita
wanda sai da ta hantsila sau biyu!

Da gudu Ummi da Huda suka k’arasa wurin suka dakatar da shi dan har ya sake nufar ta.

Ummi tana duba ta taga gefen kanta ya fashe saboda yadda ta kifa a kan interlock d’in. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago ta cewa Mom
“Haba Adama!
Meye haka?
Kin san fa ba ita kad’ai bace ba. Yanzu na tabbatar ko mik’ewa ma bazata iya yi ba
balle ta fitar miki a gidan da kike ta faman ik’irari!”

Tab’e baki Mom tayi
sannan ta kalleshi cikin harshen turanci tace
“Jata ka fitar idan ba zata iya tashi ba.”

Ummi tana rik’e da hannunta amman mutumin nan bai damu ba haka ya kamo d’ayan hannunta ya fara janta kamar ba mutumba….
Sai da suka yi kusan rabin gidan tukunna Ummi ta hak’ura ta daina binsu rik’e da hannun Jalilan tana masa magana dan har ta fara haki.

Haka nan ya jaata ya fitar da ita kamar kayan wanki ya jefar a bakin gate!

Mai gyaran flowers kuma ya watso mata kayanta waje suka ja k’aramar k’ofar gate d’in suka rufe gidan......

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
61

Mikiya Writers Association.
Rai a b’ace Ummi ta koma inda Mom take ta rufeta da fad’a.
Ita babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda aka jaa Jalila a k’asa despite the fact that she’s pregnant, ai ko ba komai de d’an Auwal ne k’unshe a cikinta!.

Mom bata ce wa Ummi k’ala ba
har tayi ta gama ta wuce ciki.

Tana wucewa ta bi bayanta
suka bar Hudan a nan tsaye tana mamakin rashin mutunci da rashin tausayin irin na Mom
tabbas a wajenta Auwal ya kwaso duk wasu bad habits nasa daga gani kuma
ita ta b’ata shi tun farko
dan wannan uwar ba zata tab’a iya yin tarbiyyar da ta kamata a Yaro ba.
Kamar ta bi bayan Jalila
haka taji, to kuma kar Jalilan ta ganta tace zata zauna a wajenta taje sabon case ya b’ullo tsakaninta da Mom
sannan Mama ta ja mata kunne akan ta fita harkar case d’in Jalila da cikin jikinta da duk wani abun daya shafeta..
Shiyasa kawai ta share hawayenta ta wuce ciki
tausayi da k’aunar Arshaad suna sake shigar mata zuciya dan maganganun Jalila Mom da Ummi sun sake tabbatar da
ciki dai na Auwal ne.


Sai da Ummi ta kusan kaiwa d’akinta tukunna ta lura da Mom na bayanta.
Juyowa tayi tana kallonta kafin tace
“Adama baki da bakin yi min magana yanzu, ba zan
saurareki ba dan haka
kawai ki juya ki tafi.
In wulak’anci abun yi ne
ki je kiyi.
Kuma kin san Allah ki guji had’uwar ki da Auwal
saboda duk tsiya dai
cikinsa ne a jikinta kika yi mata wannan rashin mutuncin….”

Matsowa Mom tayi tana mai sauk’e ajiyar zuciya
tukunna tace
“FYI Cikin ya zube.
Ta fad’o daga bene ya zube 3 days ago”

Shiruu Ummi tayi tana kallonta
ta
Showing 21001 words to 24000 words out of 100703 words