sai su yi tare.

Shuraim a zuciyarshi ya ji ya sake jin k’aunar Hudan, yadda ta tsaya take k’ok’arin taga yayi farin ciki hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba.

Karb’a yayi ya fad’a toilet d’in
ita kuma ta jona ps ta fara yi musu settings…
Sai a lokacin Ummi ta bar bakin d’akin tana rik’e kukan da ya taho mata...
Tana shiga d’akinta ta saki kukan, tabbas tayi kuskuren da ita kanta ba zata tab’a yafewa kanta ba!
Kalla fa yadda Hudan take da hankali take k’aunar jininta
amman haka nan tayi depriving d’inta childhood mai dad’i! Ta rabata da Mahaifinta! Ta sanyata ita da uwarta a k’unci basu ji ba basu gani ba duk saboda So da Burin mallakar Mijin da
a yanzu ta riga ta hak’ura dan ta san ba zai tab’a accepting d’inta ba….
Ummi ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita, tabbas zata samu lokaci ta ware ta rok’i Abba ya barta ta je taga Mama ta nemi yafiyarta sannan zata ta nemi yafiyar Hudan itama dan kwata kwata ta kasa sukuni tana jin
zafi da dana sanin abunda ta aikata a baya
Inama ana dawo da hannun agogo baya.......


Abba Yana fita direct side d’in Daddy ya nufa, yana shiga ya tarar da su suma suna dinner su uku abunsu.
………Yanzu Mom ta samu sauk’in Jalila biyayya take yi mata kamar zatai mata sujjada!
Duk abinda tace shi take yi sannan ta maida kanta k’asa kamar wata y’ar aiki, yau ma
ana gama abinci ta d’iba ta wuce d’akinta har da cewa
Mom d’in ‘ko akwai aikin da take so ayi mata?’
Murmushi kawai Mom d’in tayi mata sannan tace ‘ba komai’
already a ranta ta riga ta gama shiryawa akan gobe gobe za tayi mata korar kare!
In sha Allah…….




Kujera Abba ya ja ya zauna kusa da Daddy.
Duk da ya k’oshi amma sai da Daddy ya saka shi yad’an tab’a wani abun.

Auwal ne ya fara mik’ewa saboda yana da tulin aikin da yake son yi and yanaso yau ma ya sake gwada sa’ar shi ko Allah zai sa Sakina ta amsa wayarshi.
Dan haka yayi musu ‘sai da safe’ ya wuce sama.

Daga nan itama Mom ta mik’e suka fara tattare dining d’in ita da mai aikinta..
Tana shigewa Abba ya dubi Daddy yace
“Daddy magana na zo mu yi akan Maryam!”

Juyowa Daddy yayi ya bashi dukkannin attention d’insa kafin yace
“Ina sauraronka, what about her?”

Soundin so worried and disturbed Abba yace
“Har yanzu bata d’aukar waya ta! Bata replying messages d’ina..
I think kawai mu je mu samu su Abba Madun maybe shi zai iya bata shawara ta d’auka”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace “Abba,
I know what you are going through amma sai nake ganin kamar Maryam tana buk’atar more time kafin komai. Ka duba kaga irin abunda Mijinta yayi mata sannan na san ta san Granpa ya sallame mu daga estate saboda Huda
kuma na san yanzun ma Huda zata iya gaya mata ya sake korarta!
Gaskiya bana jin su kansu su Abba Madun za su goya mana baya ko da ace mun je mun same su da wannan maganar.
Let’s assume ma sun goya mana bayan ni na san
Maryam ba zata tab’a yarda ba a yanzu, kuma kaga idan suka bata shawara itama ta basu nata uzuri dole fa in aka auna aka duba za a ga ta fimu gaskiya ne.
Sannan Granpa!
Allah kad’ai ya san irin yawan y’an kallon da zamu kwasa da shi idan Maryam ta dawo gidan nan a yanzu!.

Bawai zan yi backing out bane in daina goya maka baya ba
not at all Abba, all I’m saying shine
Ka kwantar da hankalinka
mu d’an jira kad’an tukunna, na san dole Granpa zai sauk’o kwanan nan tunda yanzu case d’in ya shafi har Aslam, kaga daga nan sai mu san abun yi”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace
“Na ji kuma na fahimceka.
Amman nima inaso ka fahimceni…
Daddy, Idan akwai abinda na sani wanda yake dahir! To shine
ko da ace Granpa ya huce mun koma yayi accepting d’inmu da Huda to fa ba zai tab’a accepting Maryam ba
kuma idan aka taso da zancen
wani sabon case d’inne zai kuma b’ullowa, kaga
kenan an koma square 1!
So ni a gani na this is the right time da ya kamata muje ayi magana a gyara komai,
In yaso idan ma ya hak’ura kaga already Maryam tana nan so babu yadda zai yi.
And another thing is
wannan Usman d’in!
Na san yanzu baya nan saboda iyayensa sun ce ko k’afar gidan da Maryam take kar ya taka amma fa su suka haife shi, shekarun baya Maryam d’in ta tab’a bani labarin yadda Mahaifiyarsa ta murzawa idanuwanta toka ta fifita farin cikin d’anta akan na kowa, so yanzu idan ya dawo ya nuna musu bai hak’ura ba na tabbata hak’uri kawai za a bayar kuma na san Maryam ba zata iya ce musu a’a ba..

Waennan dalilai Daddy su saka sanya kaga hankalina duk ya tashi!
I don’t want to loose her again.”
Ya k’arashe maganar kamar zai yi kuka.

Gaba d’aya sai tausayinsa ya rufe Daddy dan haka yace
“Ba komai,
In sha Allah ba zaka rasata ba.
Za muje d’in,
in Allah ya kaimu ko gobe da yamma ne idan na tashi a aiki zan biyo company d’in naku sai mu wuce.”

Sai a sannan Abba yayi murmushi yace
“Thank you Daddy”

Murmushi shima Daddy yayi
daga nan suka shiga tattaunawa…….


Tunda suka fara magana Mom ta lab’e a kitchen, babu
abunda bata ji ba, gaba d’aya
ta hada gumi kamar ita akace za a k’arowa kishiya.
Sai da su Daddy suka bar dining d’in tukunna ta samu ta fito ta haye sama da niyyar d’aukar mayafinta ta nufi wajen Ummi amma sai
aka yi rashin sa’a Daddy ya rik’e ta, ta so ya d’an
fita ko ita ya barta taje ko parlour ne tayi waya
amman k’iri k’iri ya kafa ya tsare yayi kane kane!
Ba yadda ta iya haka ta hak’ura ta bari akan gobe suna fita office zata je ta samu Ummin….


Sai da Sudais yayi bacci tukunna suka yi sallama da Shuraim wanda zuwa yanzun ya ware kamar ba shi ne yake ta kuka d’azu ba!
Haka nan ta fito ta barshi yana game d’in.
Ta so ta wuce d’akinta kawai
amman sai akai rashin sa’a suka had’u da Abba tana fitowa daga parlourn nasu.

Ajiyar zuciya ta sauk’e
dan daman tana son ganinshi, duk da bata san ta Ina zata fara ba but they need to talk.

Kallonta yayi ya kalla inda yaga ta nufa, da sauri
ta fara kame kame
“Um daman zz n”

Cikin katseta yace “It’s late,
bara in je In kwanta.
Good night.”
Har ya wuce yaji tace
“Abba”
Juyowa yayi yana kallonta
fuskarsa ba yabo ba fallasa.

K’arasawa tayi inda yake a tsaye tana wasa da fingers d’inta.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Talk mana, Um?”
Yana mai bata full attention d’insa.

Da kyar ta iya ce masa
“Abba daman it’s about Ummi”

B’ata rai yayi sosai kamar bai tab’a dariya ba!

Kamar ta sani dama tak’i yarda ta kalleshi taci gaba da magana
“Abba dan Allah ka daina yi mata abunda kake yi, ka dinga
kulata please Abba kar..”

Cikin katseta yace
“Ita Ummin tace miki bana kula ta?”

Da sauri ta d’ago ta hau girgiza kai kafin kanta tsaye
tace “Shuraim ne, d’azu
ko abinci bai k’arasa ci ba ya bar dining d’in.
Ina hawowa na ganshi yana ta kuka, da kyar na lallab’ashi..
Abba if this continues
zamu iya samun matsala da brothers d’ina a gaba musamman ma idan suka k’ara wayo suka fahimci duk ata dalilina ne kake yi mata hakan.
Dan Allah Abba ka daina
Ubangiji ma ana yi mishi laifi ya yafe Ummi ta gane kuskurenta..kalla yadda
take yi min, Abba please
ko dan neman zaman lafiyarmu ni da su Shuraim ka dai na yi mata haka, no
matter yanda muke ni da su
uwa uwa ce!
Ko ni idan naga ana yiwa Mama haka akansu ba zan ji dad’i ba.
Please Abba dan Allah”
Ta fad’i hakan tana me matsowa ta kama hannunshi a nata ta rik’e.

Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e
...Tabbas abunda Huda ta fad’a gaskiya ne, shi kansa saboda su Shuraim d’inne ma yasa yake sassauta mata abubuwan da ya shirya zai yi mata tunda ta nace sai ta zauna da shi!
Ummi tayi masa abubuwan da baya jin zai iya yafe mata, yana so ya yafe amman ya kasa, but
kamar yadda Hudan ta fad’a
kar aje a samu matsala ya raba kan y’any’ansa da kanshi dan haka dole zai dinga danne zuciyarsa……
A hankali yaji Hudan ta sake cewa “please Abba”
Kamar zata yi kuka.
Murmushi yayi ya zare hannunsa a nata ya shafa kumatunta
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya..
Baya jin akwai uban da yake yi wa y’arsa irin son da yake yiwa Huda, she’s just like her Mom
everything hatta halayyersu iri d’aya ce! Kalla yadda take yiwa kishiyar Mamanta campaign dan kawai kar ayi hurting kowa.

A hankali yana kallonta yace
“Naji na daina I promise”

Murmushi ta fara mai had’a da dariya kafin tace
“Thank you Abba”

Jingina kai yayi shima yana murmushin yace
“Ai kin iya campaign dole in hak’ura, amma inaso nima kiyi min campaign a wajen Mamanki!”

Da sauri ta sunkuyar da kanta dan ita kunya ya bata.

Dariya yayi kafin yayi kalar tausayi yace
“Please princess
Tak’i d’aukar wayana.
Ko bakya so ta dawo nan ku zauna tare?
Kin fi so koma gidan Usman?”.
Da sauri ta girgiza kai.
A hankali yace
“Then you have to do something Huda ina
buk’atar taimakonki, kin san
Mamanki da kafiya dan haka dole sai mun taru akan ta tukunna za muyi nasara saboda ba zan iya shawo kanta ni kad’ai ba.
I need your help”.

A hankali ta d’aga kai,
ckin tsananin jin tausayin Mahaifin nata tace
“In sha Allah Abba,
I’ll try my best”

Murmushi yayi yace “to shikenan, na gode.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tana tunanin ‘tabbas idan fa akai sake Mama fa zata iya komawa gidan Baba anytime from now, dan tana da labarin yadda Shuwa tayi kawaici a farko ta bi bayan Baba akan Abba. Sannan itama Mama a yadda suke yanzu da Baaba Talatu tsaf zata iya yin kawaici ta koma masa, ko lokacin bikinta sai da taji Baaba Talatu suna magana da Anty Zainab wai tunda Baba ya tafi port harcourt bashi da lafiya!
Bara a gama biki zata samu Kaka da Abba Madu da maganar!
Kar fa ace tayi hak’uri ta koma zai shiryu tunda gashi har rashin lafiya yake yi which definately ta san akan Maman ne!
Komai yana kanta daram! Na yadda Mama ta sha azaba a gidan nan, ba zata tsaya ta zuba ido a sake maida Mahaifiyarta cikin uk’uba ba
besides ita dama ta dad’e tana da burin taga an maida auren iyayenta! Tana son ganinsu tare……’
“Good night, ko?”
Muryar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

D’agowa tayi tace “Good night Abba”
So take ya wuce tayi d’akinta amman sai taga ya tsaya..
Dakewa kawai tayi ta juya ta nufi side d’inta.
Murmushi ya yi mai had’e da y’ar dariya kafin yace “A fatherly advice…kema ki
daina gudun Aslam!”

Runtse idamuwanta tayi da mugun k’arfi! Wata kunya ta lullub’eta…sai da tayi dana sanin nufar d’akin nata da tayi.

Tafi minti biyar a tsaye, k’arshe
tayi kalmar shahada ta juyo!
Kamar yadda tayi zato bata ga Abba a wajen ba.

Kamar wadda akace mata zai fito haka ta zo ta wuce da sauri ta nufi hanyar k’asa ko
globes d’in bata tsaya kashewa ba....

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
60


Tana sauk’a k’asan ta ga shiru ba kowa. Da alama ma har masu aikin sun tafi side d’insu dan har an rufe main door
sannan an kashe globes.
Hasken fitilun barander waje da suka ratso ta windunan parlourn ne suka taimaka mata ta k’arasa bakin k’ofar d’akin nasu.

A hankali ta d’anyi knocking, ita bama ta yi tunanin za aji ba amma sai taji yace
“Come in”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sa kai ta shiga…

A zaune kan sofa ta sameshi, da alamun wanka yayi
dan ya chanja kaya zuwa wata jallabiya ruwan zuma mai dogon hannu da hula, bai
sanya hular ba ya barta ta fad’a baya…ba k’aramin kyau yayi ba.
Yana a zaune yana latsa computer ga tea a gefe kan d’an stoll d’in da ya d’aura computer.
Gaba daya hankalinsa yana kan aikin da yake yi
shiyasa ta yi mamakin ta yadda ya ji d’an mitsitsin knocking d’in da tayi, kuma
kamar ma ba shi ya amsa ta ba dan tunda ta shigo be ko kalli inda take ba! Haushi abun ya bata yadda ko d’agowa bai yi ya kalletaba kamar ba d’an Adam ne ya shigo d’akin ba
dan haka itama ta d’auke kai bayan ta d’an hararesa ta shige tayi wucewarta….
Inda ta ajjiye akwatinta ta nufa
cikin closet, ga mamakinta sai taga wani akwatin wanda
ta tabbatar nasa ne!
B’ata rai tayi kawai ta hau zabgawa akwatin harara wanda ita kanta bata san dalili ba..
Sai da tayi me isarta tukunna ta d’auki inner wears, toothbrush, tooth paste, hijab da sleeping dress ta shiga toilet d’in…
Wanka tayi ta d’auro alwallah, a nan cikin toilet d’in ta chanja kayanta..sai kuma ta fara tunanin a ina zata shanya bra da pant d’inta (waenda ta wanke yanzun) inda ba zai gani ba.

Babu inda bata duba ba amman ta rasa mab’oya, k’arshe dai shanyawa kawai tayi a wajen shanya
sannan ta d’aura hijabinta akan rigar barcin jikinta ta fito.

Still yana zaune a yadda yake har yanzun..
Tsayawa tayi dan so take ya tashi ta kwanta!
Tafi minti biyar a tsaye
chaan! Ta tsinkayo muryarsa
“Kina buk’atar wani abun ne?”
Yayi mata tambayar ba tare da ya kalleta ba…

‘Itafa gaskiya ya fara k’ular da ita! Ta tsani ayi mata magana ba tare da an kalleta ba, wato ba ma ta kai ya kalletan ba kenan ko me?’
Huda ta aiyyana hakan a ranta.
Gani tayi kawai ya d’ago kyawawan idanuwansa ya zuba mata su!
Da sauri ta sunkuyar da kanta a ranta tace
“Ko dai a fili na yi maganar??”

Shi kuma Aslam
shirun da tayi ne yasa ya d’ago ya kalleta, ganin ta sunkuyar da kanta ne still bata ce komai ba ya sanya shi kiran sunanta,
a hankali taji yace “Huda”

Da mugun k’arfi k’irjinta ya buga! Saboda yanayin da ya kira sunan nata da muryarsa mai mugun dad’in sauraro
sannan very calm kamar baya son maganar ta fito.
‘Ita kam, tunda take anya akwai wanda ya tab’a kiran sunanta da dad’i kamar haka kuwa?’
Ta aiyyana hakan a ranta.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e
kafin ya rufe computer ya mik’e
ya nufi inda take tsaye….

Tunda ya mik’e ta d’ago ta fara kallonsa, ganin ya nufota gadan gadan yasa ta rikice tashi d’aya, da sauri tace
“sofa, sofa! Sofar nake buk’ata zan yi bacci”
Kafin ta rufe bakinta ma already ya riga ya k’araso inda take!
Da kyar ya iya danne dariyarsa, yana kallonta yana mamakin yadda duk ta duburce kamar ba ita ta gama zuba masa harara yanzunnan ba.
Hannunsa yasa ya kamo nata!
Da sauri ta d’ago ta na kallonsa, shima itan yake kallo
ido cikin ido!

K’asa tayi da kanta tana jin
yadda zuciyarta take bugawa!
Haka kurum taji hawaye sun tarun mata a ido….Tunda take da Ya Arshaad ko da wasa bai tab’a kama mata hannu ba
4 years! Amman shi wannan she just knew him amma
bashi da aikin da ya wuce ya shafa mata kumatu ko kuma ya kama mata hannu..
Tabbas! Ta san akwai difference tunda shi
wannan Mijinta ne
amman kuma duba da yanda basu wani saba ba sannan kuma basa k’aunar juna
ai bai kamata ace yana saurin tab’ata haka ba!
Ko da yake ai ance daman a uk ya girma…ta tabbata inda Ya Arshaad ne aka yi musu irin wannan auren had’in da shi da ba zai tab’a yunk’urin rik’e mata hannu ba har sai ya
bari sun d’an saba tukunna…..
A take case d’in Jalila ya fad’o kanta, ta tuna yadda ta d’aura masa laifin da ba nasa ba
bawan Allah har da AlQurani ya zo zai rantse mata
gaskiya Ya Arshaad yana sonta ba kadan ba!……
Tana cikin wannan tunanin bata yi auni ba kawai taji kuka ya kufce mata!.

Ajiyar zuciya taji Aslam yana ta faman sauk’ewa akai akai
kamar shine yake kukan!
Be hanata yin kukan ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru….

K’afafuwanta har sun fara zafi saboda tsayuwa.
Har tayi shiru bata ji ya daina sauk’e ajiyar zuciyar ba, chaan, taji yace
“Ki tabbatar duk lokacin da tunanin Arshaad yazo miki, kika yi, kin yi istighfari!”
Yana gama fad’in haka ya ja hannunta ya kaita har kan gadon sannan ya ajjiye ta yace “sleep”
daga nan ya juya.



Huda gaba d’aya tsoron sa ne ya rufeta!
A ranta tace “Anya wannan ba alhaji bane ba kuwa?”

Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo, ganinta yayi still a zaune
bata da niyyar kwanciyar..
Yunk’urowa yayi zai yi mata magana kawai yaga da mugun sauri ta juya ta d’aura k’afafuwanta akan gadon ta kwanta ta lumshe ido…
Tabbas ya san me ta tuna
dan haka kawai ya girgiza kai ya juya ya koma yaci gaba da aikin shi…
Itama Hudan a tunaninta kwantar da ita zai yi k’arfi da yaji kamar yadda ya durk’usa zai kinkimeta ranar a asibiti
shiyasa ta shafawa kanta ruwa ta kwanta tun kafin ya sake matsowa kusa da ita zuciyarta ta tarwatse! Dan har yanzu bata bar uban bugun da takeyi ba.

Bata san lokacin da yayi bacci ba dan ita kam tana kwanciya bacci ya kwasheta.


Ta riga sa tashi dan tun kafin assalatu ta farka ita…
D’akin da duhu ba kamar yadda tayi bacci ta bari da haske ba. Jinta ta yi a lullub’e cikin lallausan bargon da ta gani a gefe kan gadon.
A hankali ta karanto addua kafin ta mik’e ta zauna sakamokon kiran sallar farko data fara ji, dan ita da a tunaninta ma farkawar tsakar dare ta yi.
Sai da baccin yad’an ragu a idonta sannan ta yaye bargon ta mik’e bayan ta d’auki wayarta.

Flash ta kunna sannna ta nufi hanyar bathroom..idanuwanta ne suka sauk’a kan Aslam wanda yake kwance akan sofa!
Dogo ne shi d’in sosai shiyasa sofar tayi masa kad’an, saboda kujerar ba wata mai girma bace ba dan
da kyar In tafi 3 seater.
Ya tankwashe k’afafuwansa akan sofar
Showing 18001 words to 21000 words out of 100703 words