farhat na kurya.

iPad din hannunta yazame ahankali tareda ajiyewa gefe ya janyo bargo ya gyara musu lullubinsu har zuwa kurji.

Fuskarta data juyo gefensa ya kalla zuwa wuyanta dake bayyane ya feso Masa kamshinta direct cikin hancinsa  sai dumin numfashinta dake sauka ai tsaye kan hannunsa ya rintse ido ya bude ahankali sukai ido biyu da ita qamshinsa daya cika hancinta ya farkar da ita saidai Bata motsaba idanuwan kawai ta zuba Masa.

Kallonta yake ta lumshe ido tasake budewa cikin yanayi na daukan hankali sbd bacci baccin dabai saketaba duka.

Hakan datayi yasashi hadiye wani Abu dayasa maqoshinsa yin sama yadawo qasa tana gani sai hakan yasata Jin tsananin kunya baccinta na sakinta gabaki daya ta motsa ahankali zata juya ya Dora hannunsa cikin wuyanta tareda tallafo fuskarta daf da tasa tayi saurin lumshe ido daga kallonsa numfashinta na sauyawa ta matso da kirjinta ya mannu da nasa sosai take ya sake zuba Mata idanuwansa yanakai dayan hannunsa cikin rigarta ya shafi cikinta dayasata dauke wuta take tana qanqamesa tareda sake mannuwa dashi.

Bude idanuwanta tayi ahankali har lokacin fararen idanuwansa na zube akanta fuskarsu na Dab data juna sosai Dan dogayen hancinsu gugar juna sukeyi duk numfashinsa daya da qamshin spraymintt na Baki take shaqa Ahankali ta bakinsu sukazo daf da juna har lokacin cikin idonta yake kallo idanuwansa na sake rurrusa kuzarin jikinta ta sake Masa gabaki daya cikin jikinsa tana matse dashi.

Kallon bakinsa dake daf da nata tayi sbd lips din kusan suna gugar juna ta lumshe ido tana tunowa a dakin farhat ne Kuma farhat na tashin dare Shan ruwa Dan haka zata iya tashi kowane lokaci Dan haka ta dago idanuwanta ta kallesa ta motsa zata bude Baki tayi magana bakinsu ya hade saijin farhat tayi tana Kiran sunanta cikin bacci.

Wani irin mummunan sanyi jikinta yayi takasa dagowa ta kallesa hakama takasa fitowa daga jikinsa tanaji ya zameta tareda Miqewa ya fice batareda ya waiwayo ba tabi bayansa da kallo jikinta na sake mutuwa Dan bama zata iya tashiba yanzu daukowa farhat din ruwa kafafunta bazasu iya daukanta ba.

Tana kokarin tashi taji bude kofar dakin tana dagowa Yana aje Mata ruwan roba biyu agabanta ya juya ya fice mamaki na shirin shideta ta kalli ruwan da sauri tadago tasake kallon kofar daya fice mamakinta na sake ninninkuwa.
Da sauri ta dauki ruwan ta Dora kan jikinta saiga wani siririn murmushi ya sauka kan innocent face dinta tana waiwayawa ta kalli farhat da batama farka ba har lokacin wato dazun motsawane kawai tayi cikin bacci takira sunanta.

Bude ruwan tayi ta 'dan Sha daya ta rufe ta ajiye har lokacin Dan boyayyan murmushinta Yana kan fuskarta ta zame ta kwanta tana lullubewa tareda rufe idanuwanta.

Washe gari sai 9 ta fito tana Yar miqa sbd tayi bacci me nutsuwa da qarfi ta nufi dakinsu ta shige Kai tsaye ta nufi toilet sai datayo brush tafito tazo gurin afia suna gaisawa tace"

Afia yaushe zakije siyayya akwai abubuwan danake buqata infact inason zuwa saloon yaushe zamuje?

Nima inason gyara kaina da qafafuna siyayya Kuma zanmana online shopping.

No banason online akwai abinda nakeso naje da kaina na siya dole sainaje da kaina.

Me kike buqatane?"afia ta fada tana zare dogon wandon baccinta Dan tubewa tashiga wanka.

Nighties Dina sun tsufa ina buqatan wasu and makeup stuff dai sai perfume danakeson sauya brand.

Ok Nima dai kusan duk buqatar dayace why not muje anjima.

No kikuma dai gobe ba.

Alright shikenan"afia tace tana qarasa cire kayanta ta nufi toilet tashige.

Bayan shigarta toilet din kenan wayarta tayi ringing NURU dake kusa ta dauki wayar zata daga tana dubawa taga sunan MUM baro baro akan wayar ta ajiye batareda ta daga din ba qarshema ta miqe ta fara gyara musu dakin tana kallo lailan nata Kira kusan ko bakwai kafin ta hkr zuciyarta na can na tafarfasa.

Wurgi da wayarta lailah tayi tana miqewa tsaye daga zaunen datake cikin bedroom dinta na qaton gidanta dake LA wanda zata Bari sbd hardashi duk ta rasa batason kowa ko duniya tafara sanin halinda take ciki shiyasa takeson lallabawa takomawa MALEEK batareda koshi yasan hakanba sbd mutane shegu sun nuna Mata wani abin Saida connection da zamanka wani sananne akeyi dakai,
Da farko farkon fitowarta kowa son huldar aiki yake da ita sbd zamanta da saninta Matar MALEEK UBAYD Amma tunda aka fara sanin sun rabu duk manya manyan mutanen datake taredasu sun janye sun nuna Mata sbd maleek ne wani abin shiyasa Dole yanzu Takoma Masa tunda dashi zata cigaba da amfana hartayi sunan da matsayin datake so Amma gashi wannan shashashar Yar tata da batada wayo tana Mata shirme sai ansan metake ciki gashi gidanta ma data saka acikin dukiyar Dan investment data shiga yashige ciki gashi bazata taba iya tambayar kowa kudi ba ayanzu sbd ba girmanta bane bazata taba Bari kowa yasaniba bare raini yashigo tana matsayin Matar maleek guda.

NURU bayan tayi wanka sunyi breakfast tareda maleek ba sukasan baya gida suna gamawa tadawo Palo ta zauna tana Dan dudduba chats na wayarta bayan tagama waya da abal dinsu akan har lokacin su padima Bata isoba dayake tayi waya da jekadi akan sun Isa lafiya saita fada Masa sun Isa suna gizah padiman zata dawo idan suka huta a gizah aka sallameta da Haka suka bar zancen padiman suka danyi fira tsakaninta dasu aka Bata meryam sukai fira kafin ta kashe tashiga chats din.

Doorbell ne yayi qara tanaji ta Dan dago ta kalli kofar kafin taci gaba da chats dinta mum Sarah tazo ta bude
Mr Omar ne mum Sarah tabashi hanya ya shigo ya nufo gurin NURUn cikin girmamawa ya tsaya tareda Dan dagowa yace"

Maleek daga office zamuyi tafiyan kwana biyu zuwa Los Angeles.

Dagowa tayi ta kallesa batareda ta iya cewa komaiba harsaida yakuma maimaita Mata kafin ta gyada Kai ahankali tace"

Allah yakai lafiya adawo lfy.

Idan kaje ka sanar zamuje saloon tareda afia.

Kamar wani munafuki Mr Omar din ya boye Dan guntun murmushinsa yayi gyaran murya yace"

Duk inda Zaki anbaki dama Banda zuwa asibiti.

Kallon Mr Omar din tayi fuskarta na sauyawa ga tarin mamakin shine yake Bata damar fitar ne kokuwa
ganin hakan yayi saurin seta murya yace'

Saqo ne daga maleek ranki ya dade.

Shiru tayi kafin ta gyada Kai tace"

Nagode shikenan Allah ya tsare.

Juyawa yayi ya fice mum Sarah tabisa ta rufe kofar Takoma kitchen gurin aikin dasukeyi.

Kasa chat dinma tayi ta ajiye wayar gabaki daya tareda Miqewa ta koma daki ta kwanta.

Baccin Rana tayi sai bayan dawowar farhat da dadewa ta farka ta tashi tayo alwala tafarayin sallah tukuna ta fito taci abinci kadan tadawo gurin Islamic class da ake zuwa anayiwa farhat din kullum ta zauna sunayi da ita.

Sai dare dasuka kwanta NURU tasamu tayi bacci daqyar sbd 'yar damuwar datakeji hakanan kawai.

Washe gari fes ta tashi ranta ba damuwar komai sukai duk abinda zasuyi guraren karfe biyu suka fice zuwa inda zasuje Amma driver ne yake jansu.

Gurin shopping kayan make-ups da turaruka ta dauko ita saida sukaje bangaren kayan bacci suka daddauka set kaman yanda yawanci suka Saba me guda uku suda farhat saidai NURUn taqara da wasu wainda itama daqyar ta iya daurewa ta daukesu agaban afia din wadda takusa suman tsaye sbd mamaki da firgici Amma ta danne Bata nunawa NURUn ba sbd Bata tabbarda mezayi da irin wainnan sexy kayan baccinba wainda kwata kwata basa sakasu.

Daganan saloon suka tsaya acan suka Dade sai yamma lis suka dawo gida NURU na waya da abal dinsu cewan shi ko numbern padima baya samu tace Masa yabari zatakira jekadi taji meya Hana padiman komawa haryanxu.
##MAMUH#


_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899
*_Mamuhgee 34_*


_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_


********************
Suna shigowa gidan farhat tafara tarbonsu da gudu ta fada jikin afia tana Dan bayyanarda tsoronta afili tace"

Afia mum tazo tana ciki tundaxu da kuka fita......

NURU data jefa qafarta Palo ta tsaya cak Jin abinda farhat tafada zuciyarta na dakatawa na 'yan mintuna kafin ta daga fuska tana kallon cikin palon da Babu kowa ta danne tashigo tareda nufar dakinsu direct tana shiga ta sa sauke ajiyar zuciya ahankali tareda fitarda numfashi ta nufi table din dake tsakiyar sofas din dakinsu ta ajiye shopping bags din hannunta ta zare qaramin gyalen dake kanta ta cire kayanta ta dauki towel ta nufi toilet tayo wankanta tareda alwala ta fito tashirya cikin riga da wando dogo marasa nauyi tazo ta tayarda sallah har lokacin afia Bata shigo dakinba.

Saidata idar da sallah tayi adduointa ta miqe ta kwashi bags din tasaka cikin wardrobe ta dauki hula tasaka akanta ta fice zuwa kitchen neman abincin tana Dan Jin yunwa.

Kodata fita Palo farhat na zaune ita kadai tana ganin NURUn ta taso tana cewa'

Aunt yunwa nakeji.

Da kulawa ta waiwayo ta kalleta tareda Kama hannunta suka nufi kicin tana cewa"

Sweetie Nima yunwa nakeji muje muga me Fana ta dafa.

Suna Shiga ta dudduba taga tuni angama jere komai a dining ta dauko musu melon drink suka dawo dining din suka zauna tafara zubawa farhat kafin tazuba suka faraci tana kallon yanda farhat din keci alaman taji yunwa sosai ta zuba Mata drink din a cup ta miqa Mata tana cewa"

Sweetie tunda Kika dawo school bakice abinci bane?

Gyada Mata Kai kawai tayi tana cewa"

Dana dawo mum Sarah zata kawomin saiga mum shine tace ta ajiye komai taje ayi Mata gyaran dakinta daganan banci komaiba.

Murmushi NURU tasaki tana cewa"

Shikenan yanzu kici abincin bazan qara Bari kiji yunwa hakaba Inshallah baby.

Suna cikin ci wani sabon qamshi ya doso dining room din Wanda ta tabbatarda kila lailah ce ke zuwa Dan haka saita dauki ruwa Tasha dama tagama saita miqe tana cewa farhat"

Sweetie nagama idan kingama kisameni Palo muyi kallon cartoon.

Juyawa tayi daidai shigowan lailah sanye cikin wata straight doguwar riga data tafi daidai tabi jikinta kanta a daure da band tana zuba kamshi hankalinta kwance tashigo tana ganin NURUn ta tsaya kallonta daga qasa zuwa sama sbd NURUn riga da wandone ajikinta dasuka sake maidata yarinya qarama sbd rigar Kamar shimi take sai wandon daya wuce gwiwa sosai Amma bekai qasa ba,
Fuskarta ta kalla taga yanda take wani maiqon kyan fata da gyaran datake samu tareda nutsuwa datake ciki datake qarawa mutum kyan fata.

Kallonta NURU tayi fuskarta Babu wani sauyi akai tace"

Barka da zuwa.

Kamar lailah bazata amsaba saidai ta dakata tareda juyowa ta kalli NURUn tace"

Karki sake zuwa dining cin abinci dagani sai 'yayana da mijina muke hawa dining a gidan Nan
Idan ada kina hawa yanzu nadawo banason tarkacen da hayaniya ki tsaya inda bazan ganki ba kafin me MALEEK din yadawo kisan matsayinki.

Tana Gama fadar hakan ta wuce ta nufi dining din tana cewa farhat ta tashi taje takira Mata fana tazo tayi serving dinta.

Aje spoon farhat tayi ta sauka daga kan dining din ta nufi dakin mum Sarah tafada Mata sbd Bata taba bi ta hanyar kicinba taje bangaren masu aikinsuba tunda take.
Daga gurin mum Sarah sidadawa tayi Takoma dakinta Bata koma dining ba.

NURU kuwa tunda Lailah tagama maganganunta ta juya ta fice Bata ce kalaba ta nufi Palo tayi zamanta tana kallo tana gani farhat tazo ta wuce dakinta batai yunqurin bintaba sbd gudun mum dinsu tace Kuma ga wani salon saitaci gaba da kallonta tana kallo afia ta fito ta nufi dining fuskarta ba wani walwala da alamar itama mum din batai Mata da Dadi ba.
Tana Nan zaune lailah tagama tafito ta wuce sama batareda ta lura da NURUn a Palonba datayi magana kila.

Sai guraren goma ta miqe ta nufi dakinsu tayi tayi duk abinda zatayi tazo gefen afia ta kwanta tareda rage hasken dakin sosai tanajin motsin afia din wadda da Alama batai bacci ba kwancen kawai take.
Bata Jima da kwanciyarba bacci ya dauketa Bata farka ba sai bayan asuba har gari yafara haske ta tashi tana miqa ahankali ta wuce toilet tayo brush da alwala tafito ta tada sallah.

Bayan tagama ta miqe ta nufa dakin farhat ta tada ita tayi sallah kafin tafara Mata Shirin makaranta suka Gama ta fito ta nufa kicin ta hada Mata breakfast dinta sukaci tare kafin aka tafi Kai farhat din school itakuma takomawarta daki ta kwanta ta shige bargo ta Dora sabon bacci cikin kwanciyar hankali.

Har Rana tayi Fana na aikin abincin safen aikin yaki karewa sbd kalolin abincin da lailah tasaka a daddafa din Wanda tasaba idan zataci abinci tafison ayisu kalolo daban daban sbd taci Wanda taga tanada raayinshi sukuma yanzu sun Saba aikin abincin gidan akan kaida akeyinsa tunda NURU tafara Aiko a kicin din gashi tun bayan tafiyar maleek NURU ta cire hannunta a aikin abincin iyakacinta ci idan anyi kamar kowa.

Koda ta farka ta bude idanuwanta taga afia zaune a dakin tanashan Cocoa Krispies da Madara ta mamaki take kallonta tana tashi zaune tace"

Afia yanzu da Rana kike Shan Krispies nagama bakyashansa be damekiba.

Kallon NURU afian tayi tana Kai spoon bakinta tace"

Yunwa nakeji ne sosai kodana tashi kaman naci Rami acikina sbd jiya da daddare banwani ci abinci ba juice kawai nasha bayan hakama ace haryanzu a gidan Nan ba'a Gama breakfast ba sai kace wasu celebrities dakecin abinci akan lokacinda suke zabarwa kansu bazan iya jiraba.

Murmushi NURU tayi tana cewa"

To kodai fana batada lafiya ne da aikin yakaita haryanzu?
Pass 11 fa.

Sanin dalilin hakan yasa afia batace komaiba taci gaba dashan abindake gabanta tana cewa idan nagama asibiti zanje Nanda 4 days zamu fara zuwa session training dinmu yaushe ne naku?

Tana saukowa gado ta nufi mirror tana cewa"

Namu sai next week Nanda kusan 10 days ma Amma Nima may b kwanakin Nan nafara lekawa court din.

Toilet ta nufa tashige tana cewa idan kinfita zanmiki texting din sunan wani littafi kizomin dashi idan Zaki dawo.

Wanka tayi tana fitowa daureda towel tana goge kanta da ruwa yadan jiqa ta alamar afia din ta fita ta nufi mirror kenan zata zauna aka shigo dakin ta Bata waiwayoba ta cikin madubin taga lailah wadda takusa hadiyar zuciya ganin NURUn a Haka sbd fatarta dake wani irin daukan ido sbd zamanta fresh ta kanne tareda dan yamutsa fuska ta kalli cikin dakin taga afia Bata Nan ta maido ta kallonta kan NURU dake abinda ke gabanta tace"

Karkicemin anan dakin kuke zama tareda afia?

Waiwayowa NURU tayi ta kalleta sai tace mata"

Barka da shigowa"tayi skipping wancan tambayar tana kokarin dauko Kaya tasaka ajikinta.

Sake kallonta lailah tayi tana cewa"

Wane irin toshewar Kai ne zaisa ki zauna a dakin AFIA bayan dakunan dake gidan Nan gasucan kusa Dana Sarah Amma kinzo nan kin gwamutsa ta Yaya mutum biyu zasu zauna daki daya a matse wani na shaqan numfashin wani wannan masifa ne cuta na shigowa ciki.

Wannan karon tsayawa NURU tayi kallonta sbd tasamu fahimtar me mum dinsu afian ke nufi Dan dai ita abin yafara gundurarta Matar tacika tsirfa.

Fara hasala da kallon da NURU ke Mata Kamar wawuya lailah tayi tace"

Ba'a kallo Haka idan Ina magana ba sa'arki ke magana ba Matar uban gidankice ke mgn.

Hakan data fada yasa NURU kallonta gabaki daya saidai har lokacin Bata ce komaiba kafin ta juya ta dauki kayanta tafara sanyawa lailah taqara harzuka sbd ganin Kamar NURUn ta maidata hauka kawai takeyi saita dauki towel din afia ta riqo hannun NURUn dashi tajawota ta fito da ita dakin tasawa dakin key ta zare ta kalli NURUn tana Dan yamutsa fuska tace"

Next time idan Ina mgn saiki saurareni da kyau,
Kije dakunan dake kusadana Sarah ki dauki daya wannan banason tarkace ko gwamutsetse atareda yarana ciwo zai iya shiga.

Wucewa tayi tabar NURU a tsaye daga ita sai towel tayi shiru batareda tace komaiba har lokacin sai kawai ta juya ta nufi dakin farhat tashige Allah yasa tanada wasu Kaya adakin na farhat saita Sanya duk Dana shan iska ne saita fito taje kicin ta dauko drink da biscuits tadawo daki taci tayi sallah ta haye gadon dakin tana juya wayarta tanason kiran jekadi Amma saita fasa ta ajiye wayar.

Sai yamma afia tadawo ta tararda dokar mum dinta ta girgiza matuqar gaske ta kalli mum din zatayi magana mum din tayi Mata wani kallo tana numa Mata kofa sbd batason dogon zance bare hayaniya.

Koda afia ta fito dakin farhat ta nufa Kai tsaye sbd tasan NURUn na can tana shiga ta taddasu zaune kan kujera suna game da farhat hankalinsu kwance suna dariyarsu.

Wani iri taji na rashin Jin Dadin abinda mum dinta tayi Amma bazata iya take maganartaba sbd duk yanda take kaunar NURU mum dinta mum dintace saita kasa shigowa ta juya zata wuce NURU data lura da ita kalleta tace"

Charger na kawai nake buqata a dakin sai laptop Dina.

Tsayawa afia tayi tareda juyowa ta kalli NURUn taga ba damuwar komai akan fuskarta ta dake itama tace"

Ok zan Aiko mum Sarah takawo miki."tajuya ta tafi tabar gurin suka cigaba da abinda sukeyi zuciyar NURUn a dake Taki Bari abinda takeji ya rusata.

Koda dare yayi daqyar NURU ta iya rintsawa sbd dokokin lailan sunfara tsauri sbd ko dining din suna Gama cin abinci aka rufesa
Mum Sarah duk hankalinta ya tashi NURUn ta nuna Mata bakomai kadata damu Takoma daki ta kwanta.

Washe gari bayan tafiyar farhat school ma haka tashiga wani sabon cin zarafin ta daure dai Bata cewa komai bare ta tanka qarshe dai futa tayi taje restaurant taci abinci dagacan tace driver ya wuce da ita wani guri acan ta wuni sai qarfe bakwai tadawo gidan tana dawowa ta shige sbd komai na gidan
Showing 63001 words to 66000 words out of 104202 words