ya kamo ya dibeta a tsanake yace"zahra ni kikeso?"yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace "Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har raina"ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace"zahra to ya zakiyi in kika fahimci ba matsuguninki a zuciyata?"

"addua zanyi,wataran zaka soni"ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace"to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so fa?"

"Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu"tabashi amsa.

"to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?"

"wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga shine kawai dalilin daze hanaka aurena"ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace"to naji zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,"

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*10*


Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace "ɗiyata sauƙi yasamu kenan?"
Murmushin itama zahra tayi ta sunkuyar da kai ƙasa,
Daddy ne ya ƙaraso gurin ya zauna sannan yace"dama wannan lokacin nake jira kuma gashi Allah ya kawo mu,zamu so ki sanar damu ko ke wace ce,dan musan taya zamu taimakeki ki koma ga danginki"

Hawayene ya zubowa zahra tasa hannu ta goge,sannan tace"ni bani da dangi,baffana yayi hatsari ya mutu,innata ƴan bindiga sun kasheta,tade taɓa shaidamin muna da ƴan uwa a gombe,kawu modibbo amma sun bar gomben kuma batasan inda zata gansu ba"

Kallon kallo suke tsakanin hajiya da Alhaji,bakinsu har rawa yake gun jefo mata tambayar"ya sunan innar taki na Aynihi?"

"hauwa'u sunanta"ta basu amsa.

Rungumota hajiya tayi jikinta tana hawaye tace"tunda nake kallon fuskarki naga kamar nasanki,amma na kasa gasgata hakan,ashe ko ikai fuskar hauwa nake gani ataki fuskar,Allah mungode maka"

Daddy sosai yake murna da ganin ɗiyar ƴar uwarshi,hotunan inna nada ya nunawa zahra ayko murmushi take tana faɗin"innata ce wannan dama kunsanta"

Daddy ya gabatar mata da kanshi da iyalinshi a matsayin dangin nata yamata bayanin komai,ayko itama kuka tasa najin daɗin ganinsu.

Shide Muhammad abun koma masa yayi kamar a film,daga neman shawarar akaita gidan mahaukata shikenan abu ya juye ta komo ƴar uwarsa.

Basu bar falon ba se da dare yayi sosai anata hira,sosai daddy yasaki jiki da zahra wacce yake kallo amatsayin sauran danginsa da suka rage masa a duniya.

Washe gari da safe bayan muhammad ya duba zahra,cire safar hannunshi yayi ya janyo kujera ya zauna yana fuskantarta,ita de tunda ta fahimci shine ke dubata kunyarshi takeji,da ƙyar take iya haɗa ido dashi.
"zahra kin bada labarin komai naki,amma baki sanar damu wanda kuma ya miki fyaɗe ba?wanda a matsayinmu na ƴan uwanki zamu so musani"muhamnad yace cikin tattausar murya.

Hawayene ke biyo idonta a hankali tace"na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata"ta faɗi cikin kuka.

Taɓe baki yayi sannan yace"bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faɗa min ba dole zaki faɗawa mijinki ay"yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Hankalin zahra yayi ƙololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duƙar da kanta tayi ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.

A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace"mummy yanzu rayuwata a haka zata ƙare kenan,bazan taɓa aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaɗe? inde hakane nida aure har abada"ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daɗi,da ƙyar tayi shuru.

Mummy ɗakin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace"hajiya lafiya kuwa?"

Cikin damuwa tace"Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaɗen da aka mata, baka ganin akwai buƙatar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?"

Shuru Alhaji yayi na ɗan lokaci sannan yace"nemo ko waye beda wani amfani,fyaɗe de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaɗai ze rufa asirinmu"

Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ƙara bashi kan ƙudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuƙa.

Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaɗanne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace"daddy don Allah kayi haƙuri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba ɗaya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min ƙanƙanta daddy pls"
Yafaɗi kamar zeyi kuka.

"muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faɗa maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba ɗaya" daddy ya buƙata cikin haɗe rai.

Jikin Muhammad a sanyaye yace "wata guda"

"nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na ɗauke maka komai,kaje ka fara shiri"daddy ya faɗi sannan ya miƙe yabar gurin.


Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.


Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*12*



A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office ɗin aminin nasa.

Da sallamarsa ya shiga office ɗin cike da fara'a ya taso suka rungume juna,suna ɗan dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.

Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa"Abokina ina cikin damuwa fa,?"

"wacce irin damuwace wannan,?"abokin nasa ya buƙata cike da kulawa.

"jibi daddy ze ɗauramin aure da wata ƴar ƙanwarsa,na rasa inda zan tsoma raina".

A razane ya miƙe tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce kamar wanda yacewa gobe ze mutu.

Cikin kakkausar murya yace"HAMMAD kana nufin alƙawarin auren ƴarfillo daka lalatawa rayuwa yatashi a banza kenan?"

Miƙewa muhamnad yayi ya ƙaraso kusa da abokin nasa ya dafa kafaɗarsa yace"JAMEEL kafi kowa sanin irin son da nakewa ƴarfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan ƴarfillo zan iya ɓata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da itan,kwatankwacin kaddarar data faɗawa ƴarfillo itama hakanne,wallahi zan auri yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin ƴarfillo na cikin sauƙi,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata"muhammad yayi maganar kamar zeyi kuka.

Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace "b haka bane hammad ay kai mijin mace huɗune,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da ƴarfillo shine yasa"

"har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda ƙarfina ya ƙare"Muhammad yafaɗi cike da tabbatarwa.

Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo ƴarfillo ya amince ya aureta.

Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana dariya"wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi ɗaya a baya,sega resigning letter wallahi ka bada maza,ay gashi nan ka ƙare a kallewa mata al'aura,da wuri zaka makance"ya ƙarasa maganar yana dariya.

Duka jameel yakai masa yace"ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da ƙyar zan bari a ƙarasa ni,kaima kaga zaka iya ne shiyasa baka fita ba"

"bazan taɓa barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da ƴarfillo to tabbas zan fita".

Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga ƴarfillonsa.

To bari mu waiwaya baya😄

Kowa ta turo data se in ci gaba😎


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*Ummu Airah,Asmau shareef,mmn minister,mahaƙurci mawadaci,da sauran wainda suka turomin kati da data,nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,ya ƙara buɗi na alkhairi,naji daɗi*.


*13*



Bayan Mahaifin Hammad ya ɗaukeshi zuwa nema masa magani a ƙasar rasha,anci baƙar wahala kamin asamu kansa ya dawo seti.
Cikin nasara akai masa aykin ido ya samu sauƙi,watanni bakwai suka kwashe a ƙasar sannan ya warware suka dawo gida nigeria.

Koda wasa Hammad be taɓa faɗawa kowa abinda ya ayƙatawa ƴarfillo ba,sede kullum cikin nemanta yake,be taɓa gajiyawa,sadaka sallah da addua cikin yi ike.

Jameel sojojin agajin gaggawane suka tsamoshi aruwan daya faɗa,taimakon gaggawa suka bashi,nunfashinshi yadawo,oxygen suka sa masa sannan akasashi a mota zuwa babban asibitin sojoji dake kaduna.

Cikin nasara akai masa ayki aka cire bullet din da aka harbeshin.yasha jinya kan yasamu ya warke,shiyasa yana warkewa ya ajiye aykin soja.

Tare sukai karatu da amininsa a turai fanni ɗaya,shiyasa jameel ya koma inda yafi wayau.

Hammad hospital asibitine da mahaifin Hammad ya gina masa tun yana turai karatu,azuwan yana dawowa seya fara ayki,amma fafur Hammad yace soja zashi beson asibitin.

Haka Mahaifinsa ya haƙura,aka rufe asibitin,badan yana so ba sedan ba yadda zeyi.shiyasa da jameel yabar aykin sojan ya miƙa masa asibitin domin yaci gaba da kulawa dashi.

Hammad sunan yasamo asaline daga wani abokinsa bature,da be iya faɗin Muhammad ba se dai yace Hammad,mutuncin dake tsakaninxa dashine yasa Muhammad maida sunan nickname ɗinsa,sabida kar ya mance dashi,

Asalinsu ƴan gombe ne amma yanzu a abuja suke zaune,sabida harkar kasuwancin mahaifinsa.

*Cigaban labari*


Shawarar da jameel ya basa tasa yasamu sassauci dan haka yanzu ya rage damuwa aransa,amma zullumin be bar shi ba.

Yau dandazon mutane suka shaida auransa da Zahra,ko ina kaduba jama'ar annabi ne,Hammad hannunsa har ciwo yafara sabida gaisawa da mutane.

Taro be watse ba se wajen magriba,a gajiye ya shiga ɓangarenshi bayan ya raka su jameel,wanka yayi sannan yazura kayan baccinshi ya nemi kan doguwar kujera ya ɗan kishingiɗa.

Amarya Zahra ko kamar wata balarabiya dan kyau,dan surayya ƙanwar hammad wacce ta iso jiya da dare daga malesia inda take karatu itace ta tsantsarawa amarya kwalliya ta ƙin ƙarawa.

ko ina ta gifta mutane se yaba ta akeyi,sabida taron mata ma cika gidan yayi ,yayi danƙam,da mutane.

Bata samu sakewa ba seda taro ya watse,a waya Hammad ya kira mummy yace a shagwaɓe"mummy jinjirinki fa yunwa yakeji,rabona da abinci tun safe,kisamamin abinda zanci,"

"subhanallahi,me yasa kazauna da yunwa irin haka,kai meyasa baka jin magana ne"mummy ta faɗi cike da damuwa.

"mummy muna cikin mutanene"yafaɗi a marairaice.

"bari insa akawo ma abinci yanzu katabbatar kuma kaci"tana kaiwa nan ta kashe wayar.

Kitchen ta nufa,cikin saa ko tasamu zahra da surayya suna girka abinda zasu ci,indomie ce suke dafawa amma kowa da raayinsa,na zahra da manja da busasshen kifi,na surayya kuma mangyaɗa ne domin soya indomie tayi da kwai.

Suna ganin mummy,duka suka rusuna suna gaisheta,murmushi tayi ta amsa sannan tace tana kallon girkin na zahra"yauwa zahra maza ki juye abincin in ya ƙarasa kije ki kaiwa,yayanku yunwa yakeji ki hanzarta kinji,nasan baze iya cinyewa ba,kema ba ci ne dake ba duka ze isheku."amsawa zahra tayi da cewa "to mummy bari in kai masan"tana kaiwa nan ta juya ta fice daga kitchen ɗin taje ta ɗauko hijabinta,ta ɗora kan doguwar rigar baccin dake jikinta,ta dawo kitchen ɗin ta juye abincin a plate me kyau tasa cokali,sannan ta kifa wani plate ɗin asama,ta fito ta nufi sashin nashi.

Da sallamarta ta tura ƙofar ɗakin,zaune yake yanzu yana waya da jameel yana sake masa bangajiya,shigowarta tasa ya kashe wayar ya maida hankali kanta.a sanyaye ta zo gabanshi da abincin,tsugunawa tayi gab da ƙafarsa,tace"barka da dare,ga abinci inji mummy"ta faɗi tana miƙa masa abincin.

Amsar abincin yayi ya ajiye a gefensa, sannan yace "bani ruwa a fridge"batare daya kalleta ba.
Miƙewa tayi da hanzari taje ta ɗauko ruwan,ta dawo ta tsuguna ta miƙa masa.

Amsa yayi sannan yace"miƙo min ɗayan wayata akan gado seki tafi"miƙewa tayi da hanzari ta nufi cikin bedroom ɗin nasa.

Zahra iyayen tsabta,tana shiga tasamu komai na ɗakin a hargitse,hatta kayan daya cire zube suke kan gadon be ɗauke ba.

Hijab ɗin jikinta ta cire ta rataye akan ƙofa,sannan ta shiga aykin da baa sata ba wato gyaran ɗakin nasa.

Komai seda ta tabbatar ta ajiye shi a mazuninsa,ta ɗauko wani zanin gadon ta sauya masa ta gyara tsarin ajiye fulullukan,sannan ta isa kan mudubi ta fara gyara kan mudubin shima,dan komai ya hargitsa shi.

Hammad wanda tun ɗazu yagama cinye abincin da mummy tace baze cinyeba,zaune yake zaman jiran ta kawo mashi wayar amma yajita shuru kamar an shuka dusa.
Miƙewa yayi ya nufi cikin ɗakin dan yaga ko me ya hanata dawowa falon.

Mamakine ya kamashi ganin ɗakin nasa agyare tsab ga wani niimtaccen ƙamshi, dake tashi,,ita kuma hakimar tana gaban mudubi tana gyara turarukansa.


A hankali ya taka yazo bayanta ya tsaya hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,kallonta yake ta mudubi,gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuska sabida duƙawar da tayi.

Bayan ta kammala,ta juyo da sauri zata bar gurin,ayko se tsintar kanta tayi a ƙirjin Hammad,ƙoƙarin faɗuwa take,da sauri yasa hannu ɗaya ya tarota ta dawo ƙirjin nashi.

Sunkuyar da kai tayi kunyar duniya tabi ta isheta,se sosa bayan kunne takeyi.

"ina wayar tawa?"ya tambaya a ƙasetance.

Ganin beda niyyar sakinta ne yasa ta fara miƙa hannu bayansa,tanaso ta ɗauko wayar akan gadon da ta ajiye.

Hannunta be kai ba,hakanne yasa ta yunƙura da ƙarfi domin ta ɗauko masa,ayko baya Sukayi su duka da ita suka faɗa kan gadon hammad a ƙasa ita kuma asamansa ɗare ɗare.

A kunyace ta ɗago ido tana gyara gashin kanta,ta saci kallonshi,shima ita yake kallo,a hankali ta zame ajikinshi ta sauka da sauri tayi falon dan ta ɗauki abincin daya rage taje taci itama.dan yunwa takeji.


Muje zuwa



Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*

*15*


Da asuba,da kanshi ya tasheta yabata jallabiyarsa tasa tayi rolling da rawaninsa tayi sallah,sannan ta koma bacci bayan ta cire masa rigar tasa,

Bata farka ba se tara na safe,tuni hammad yayi wankansa ya kimtsa,jin motsin da yayine yasa yazo ya sameta a zaune ta farka,rigarta take ƙoƙarin sawa amma zafin da gun ƴunar jiya ke mata yasa ta kasa sawa sabida rigar bata kai jallabiyar daya bata faɗi ba.

Da sauri ya ƙaraso gurinta,ɗago ido tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kai,

Zama yayi kusa da ita har jikinsu na gogar juna,waigowa tayi asanyaye ta kalleshi shima ita yake kallo,hannu yasa ya zagayota dashi ya kamo rigar yasa mata,sunkuyar da kai tayi ta runtse ido sabida zafin da taji,a hankali yace"sorry,"gyaɗa kai tayi sannan ta miƙe,ta fice daga ɗakin,yabi bayanta da kallo,yana haɗiye wani miyau.

Se da ta fice ne kuma kunyar ta faɗo mata,to tacewa mummy agurin wa ta kwana,kasa ƙarasawa cikin falon tayi ta tsaya tana wasi-wasi.

Hammad ne ya fito zashi gaida iyayen nasa,anan yaci karo da ita tsaye tana tunani,ƙarasowa yayi inda take,yace"ke lafiyarki ƙalau kuwa,tsayuwar me kikeyi anan?"
A raunane ta ɗago idonta ta dibeshi tana hawaye tace"kunya nakeji suji na kwana agurinka"

Murmushi yayi sannan yace "sabida kin kwana da kwarto ko?"

Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin "Allah ya tsaremin miji da zama kwarto,ni mijina ba kwarto bane,aniyarka ta bika"sam ita ta mance ma matsayinsa agunta take wannan batun.

Be kulata ba hannu yasa yaja hannunta suka nufi falon,itako tirjewa take tana kuka tana "wallahi bazaa ganmu atare ba,nide kasakeni ka tafi kai kaɗai"a haka suka shigo falon,inda mutanen gidan ke zaune a dinning suna karyawa,ɓurarin da zahra kewa Hammad ɗinne ya dawo da hankalinsu kansu,
Shiko Hammad be saketa ba seda suka shigo falon,ay tana ganinta gaban su mummy,da sauri ta ɓoye abayanshi,duk yadda Hammad ya kauce itama da gudu zata koma gurin,sosai abun yaba su daddy dariya,a hankali daddy yace "rakata ɗaki mana muhammad,ka tsaida ita anan"

Murmushi yayi sannan yaja hannunta zuwa ɗakin nasu se ɓoyewa take agefensa.

Seda ya kaita sannan ya dawo gun mahaifan nasa,tsugunawa yayi ya gaishesu sannan yaja kujera ya zauna,

"Angama shirya komai na gidan da zaku zauna,anjima mummynka zasu kaita gidan,ka kwantar da hankalinka"daddy ya faɗi yana murmushi.

Sosai kunya ta kama Hammad,ya sosa ƙeya yana murmushi yace"daddy ay ko anan ɗinma zamu iya zama"

"kuci gaba da mana rashin kunya a cikin gida ko?"daddy ya buƙata.

Shuru Muhammad yayi dan se yanzu yagano ma manufar daddyn.

Haka yayi break fast duk a tsarge,yana gamawa ya miƙe ya bar falon.

Shiryawa yayi ya fice zuwa gun amininsa Jameel,kasancewar yana hutu be koma bakin aykiba.

Surayya ce tasamu zahra a ɗaki tayi wanka ta kimtsa cikin wata atamfa ja da milk me golden tayi kyau matuƙa.
Tana shiga ta fara mata tsiya,"kaga amaryar yaya,me bin angonta ɗaki"duka zahra takai mata tana faɗin"zanko haɗaki dashi,bari muhaɗu"

"ayya yarinya kwantar da hankalinki yau zaa kaiki gidanshi seku dena satar hanya"ta ƙarasa maganar tana tuntsira dariya,

Zahra de ba baka se kunne,seda su mummy sika bar falon sannan taje tayi breakfast ɗinta.

Da magriba su mummy da ƙawayenta guda biyu suka kai zahra gidan auranta daya gaji da haɗuwa,se kuka take wurjanjan ita bazata zauna ba,

Surayya aka baro agurinta azuwan in Hammad yazo yasa direba yakawota gida.

Hammad ko suna can shida jameel yana ƙara kwantar mai da hankali,akan auran nasa da zahra,tare da bashi tabbacin insha Allahu zasi ga ƴarfillonsa,

Sai da ishai daddy ya kirashi awaya ya shaida masa tun ɗazu ankai masa matarsa gida.

Jameel ne yasa shi yayi wanka ya kimtsa awata sabuwar shadda ta jameel ɗin,sannan,suka fito domin yamasa rakiya,kaji da madara suka siya sannan suka ƙaraso gidan.
Jameel besan me yasa ba amma lokaci zuwa lokaci gabansa na yawan faɗuwa,a haka suka ƙaraso gidan.

Muje zuwa


Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYIMIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*ayi haƙuri ina tare da mara lafiya ne,shiyasa,*


*14*


Tana isa falon plate ɗin abincin ta ɗauko ta buɗe ga mamakinta ba komai aciki se ƙayoyin kifin.
Tsayawa tayi riƙe da plate ɗin hawaye na biyo kumatunta,a haka ya ƙaraso falon.

Be kulata ba yaje ya zauna,yafi minti goma azaune be waiwayi inda take ba,seda ga ƙarshe ya waigo,ga mamakinsa kuka take riƙe da plate ɗin daya gama cin abinci tana jujjuyawa a hannunta.

"me ya faru kike kuka?"ya tambaya.
Cikin kukan tace"wannan abincin dan kaina na dafa mummy tace in kawo maka tasan zaka rage bazaka cinyeba,nima se inci amma kuma gashi ka cinyen ni ban ciba ga dare yayi,tsoron shiga kitchen zanji
Showing 6001 words to 9000 words out of 28223 words