Da confidence dinta take takowa zuwa cikin gidan nasu. Kamar ko yaushe bata damu d kallon me kallo ba......bata damu da hasashen me hasashe ba......hakanan bata damu da zunden me zunde ba,ta keta a hankali har ta isa qofar dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna makaranta a irinsa.

Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon.

Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?.

"Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta.

Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a kunne huda.

"Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?.

"Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 87


Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya.

Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar

"Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu bare ta bari ya bace mata

"Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen.

"Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar dimuwa da gigita.

"Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu.

Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta

"Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare.

"Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin.

"Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan dakin gaban hudan ta zauna jabar.

"Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa.

"Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu.

"Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma yayimin alqawarin bani kulawa kaman yadda iyaye ke bawa 'ya'yansu......banyi wani abu da ba daidai ba fa,kema kin tsara rayuwarki ne daidai yadda kikeso......kina kuma abinda kk ga dama a sanda kikeso.....ni ko nadra ko haneefa akwai wanda ya taba tsaidaki ko ya hanaki?,ni mene ma nayi?,abinda ban taba wuce layin bayan gidanmu ba?,ban taba zuwa hotel ko joint joint ba.....ba'a taba ganina da wani d'a namiji a cikin mota mun kebe b.......".

Sake saukar wani lafiyayyen marin da yafi na dazu shi ya daukewa huda dukkan wata kalma da zata ci gaba da fita a bakinta. Marin da wannan karon ya jawo digar jini daga hancin hudan,muryar sabreen din kuma dake shaking tace

"Huda?.....kinyi hauka ne?,eh idan ma haukar kikayi kisan wadanne kalamai zaki gayamin.......nice sabreen da na baki tazarar shekara kusan biyar cikin rayuwarki.....nice sabreen da na sadaukar da walwalata farincikina da martabata saboda kuji dadi!....nice sabreen dana hana muku kuka......nice sabreen dana hana muku jin yunwa da wulaqanta.....nice sabreen dana zame muku garkuwa......nice sabreen dana maye muku gurbin uwa da uba wanda kece ta farko daya cancanci ta zama shaida akan hakan......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu na shaawa ko burgewa a jikinki da d'a namiji zai gani ya burgeshi......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu da zaki amfana mini face zallar qauna da 'yan uwantaka fa fisabilillahi......wanne sauran kulawa kike buqata da ban baki ba?,wacce sauran qauna ce da tafi wannan girma da fadi?......soyayya huda?.....kin san wanne abune da yafi tarwatsa rayuwar diya mace?,kinsan wanne abu ne yafi zama girman nadama cikin rayuwar 'ya mace?,kinsan mene ne mabudin nadama......wahala da azabtuwa da zuwa da qaddarar da bata sauyuwa cikin rayuwar mace?......ba komai bana face SOYAYYA kuskure na gaba da rayuwar kaso casa'in dake afkawa shine AURE......namiji!.....bashi da imani......bashi kuma da tausayi.....namiji BUTULU ne dake iya bijirewa halasci komai girmansa.......namiji halittar data fi kowacce halitta son kanta cikin duniya.....halittar da babu imani cikin ruhinta ta fannin azabtar da ruhin diya mace.......samun salamar rayuwaki ki rayu ke daya.....baki saka kanki cikin sabga ko sha'anin kowanne d'a namiji ba......wannan wani karatu ne da rayuwa tayimin bayan gushewar abba da ummina.....mutum na farko da ya fara qoqarin bata rayuwata shine ALHAJI LAWAN......" Da wani irin kallo huda ta dubi sabreen,saidai ta kasa furta komai

"Eh....alhj lawan maqoci kuma aboki ga mahaifinmu,......tun daga wannan rana na fara karatun waye namiji?,daki bayan daki kinsan komai kafin na fara sakaya wasu al'amuran daga idanunki saboda samun damar saituwar tunaninku.....huda!......dago kanki ki kalleni da kyau!" Ta furta da gasken gaske,abinda ya sabbabawa hudan duban nata da idanunta da suka hada hawaye masu yawan gaske

"Ba suna kirana karuwa ba?,ba cewa suke ina yawon ta zubar ba?,ba cewa sukeyi nayi cikin shege yafi sau a qirga ba?,ina bin maza?,ina sata?,ba haka suke bada shaida ba?......to na barsu da Allah na kuma barsu da ranar da zasu tsaya gaban Allah su baida shaida akan hakan......ni aminatu ahmad na rantse miki da girman Allah ban taba bawa kowanne d'a namiji kaina ba.....ban taba sanin d'a namiji ba ban taba kwanciya da kowa ba,idan kuma na taba....."

"Aah yaa sabreen" Huda da kuka ya kecewa ta fada da hanzari tana dora hannunta saman bakinta yayin da dukka hannayenta ke rawa.

Wani qauna da tausayi na 'yan uwantaka ke tsirgawa kowannensu. Daga ita har huda din hawaye ne da kuka ya ballewa kowannensu har zuwa wani lokaci

"Me yasa kika boyemin wani abu daya shafi rayuwarki huda.....bayan hudubata kullum a kanku itace.....komai girman matsala ko qanqantarta.....kome girman abu da qanqantarsa da kukaga alamun zai afka cikin rayuwarku.... Alkhairi ne a idanunku ko sharri ban yarda a boyemin ba?.....kinsan wayeshi?". Kai kawai huda ke kadawa ragowar hawayen idanunta suna sauka tana jin wani abu maras dadi cikin qirjinta

"Sunansa na asali shine naseer bawai bassam ba......yayi amfani da sunan bassam ne saboda sunan dana bashi nawa shine basma a madadin sabreen......dila ne na qwayoyi da cocaine da dukkan wani nau'in kayan maye,yana dillancinsu da safararsu zuwa qasashe masu yawa ta wannan qazantacciyar hanyar ya tara duk wata dukiya da yake qafafa da ita. Ya qware ainun wajen ta'ammali da mata duk kalar wadda ranshi yayi mishi.....yarinya ko babba musulma ko Christian,koda kuwa ba harkarki bane idan wani abu a kanki ya darsu zai sanya a dauko masa yarinya yayi mata fyade......a irin haka muka hadu,kuma na zama sanadiyyar daya buga gagarumar asarar da har yau ya kasa murmureta bayan kuma ba haka ya tsara ba......yayi zaton ya samu irin matan barikin da zai kashema kudi ya gama da tenure dinsu ya sallamesu........tashi d'aya na bace masa bat......yana da balain naci da bibiyar da nayi imani ita ta bashi daman gano ni wace da inda nake......yayi nufin yin ramuwar gayya ne a kanki huda....saidai kuma naci alwashin sai nayi silar qarar da ragowar rayuwarsa a gidan maza tunda har bai daddara ba ya dawo cikin hurumina.......yaso kuma taba killataccen gold din da hannu vai isa yakai gareshi ba".

Ta sani ta kuma dade da sani zantukan adda sabreen kamar rubutu ne saman dutse.......bata qarya komai runtsi komai wahala,don haka maganganunta akan waye bassam naseer sukayi matuqar tsoratata. Jikinta ya sake daukan rawa.....wannan shine dalilin da ko yaushe yake qoqarin yadda zai shirya haduwarsu tana rushewa?.

"Ki rabu dashi don Allah adda.....kada ki sake jefa kanki cikin hadari.....". Bata saurareta ba ta jefa mata wayartata zuciyarta na mata wani irin ciwo da kuma son daukar fansa

"Bakin alqalami ya riga ya bushe......kirashi ki jaddada masa zaku hadu da yammacin litinin,saidai kice kina tsoron kada a gane kin fita a gida.....kuna da event a wani guri dab da wajen acan kikeso ku hadun" Tayi maganar tana qoqarin yago paper cikin wani memo dake saman bedside din hudan tana rubuta mata sunan wajen.

*_LITININ DIN DA MUTANE DA YAWA SUKA CIWA BURINTA.....LITININ DIN DA ZATA ZANA QADDARORI CIKIJ RAYUWAR WASU,WASU QADDARORIN KUMA DA SUKE ZAMA MABUDIN QOFOFI MASU TARIN YAWA GA RAYUWAR WASU.....MABUDIN FARA GWAGWARMAYA DA TIRKA TIRKAR DA ZATA JA MANA RAGAMA HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN.....ZAMU GANI WAYE LITININ DIN ZATA ZAMEWA FARAR RANA KO AKASIN HAKAN?_*

_KUCI GABA DA BIBIYAR 'YAN MUTAN HUGUMA_🥰🥰🥰






Showing 162001 words to 163771 words out of 163771 words