kis kis kis, kamar wata tsohuwar karuwa, dan mayafin dake jikinta ma ba wani abun kwarai ba ne yadda kasan wata yar iskar budurwa haka ta fito, arzikinta daya abaya ce a jikinta ba Atamfa ko lace ba. Ta kusan minti talatin a gurin har ta fara gajiya ta fara takawa gafen titin tana tafiya sannan Ramlee ta kirata sai ta kwatanta mata inda take, tana sauke wayar wata Benz ta wuce gabanta sai kuma ya dawo baya ta faka daidai inda take tsaye. A hankali mai tukin motar ya sauke gilashin motar yana kallonta, suna hada ido sai ta sakar masa murmushi shi kam ya dade da yi ma fuskarsa ado da murmushin.
“Hajiya ke ce haka dai?”
Ta dauke kai tana fari da ido sannan ta sake kallonsa da kyau, shi din ne dai abokin Faruq da ta taba roka kudi ta WhatsApp a lokacin data saci numbersa a wayar Faruq.
“Ni ce dai ranka ya dade, ya akai ka gane ni?”
“Kyakkyawar mace irinki ai kowa ya gani zai tsaya, sai dai daga baya mutum zai tantance idan ya sanki ko akasin haka”
Ta yi murmushi.
“Ka dawo nan ne ko zuwa kai?”
“To gani nan dai, Ina zuwa haka? Ina abokin nawa ya barki a rana tana gasa ki”
“Abokin ka ai ya dade da yin tazara, duk kyau surar nan da kake gani ya zubar wata zai dauko”
“Subhanallahi, lallai da labari a bakin naki mai kyau, da zaki taimaka min da kin shigo motar nan”
“Wallahi kawata nake jira, zata zo nan ta dauke ni”
“Okay”
Ya dauko katinsa ya mika mata.
“Gashi a taimaka a kirani, duk dai na san ba a rasa number”
Ta yi murmushi bayan ta karba, sannan ta daga kai tana kallon Ramlee data faka a dayan gefen.
“Okay zan kira ka Inshallahu”
“Na gode kyakkyawa”
Ya fada yana kare mata kallon irin kallon nan na yan iska. Sannan ya rufe gilashin motar ya hau titi, ita kuma ta nufi gurin da Ramlee ta faka motar ta bude ta shiga.
“Waye wacan?”
“Wani abokin Faruq ne”
“Okay”
Sai da suka hau titi sannan Ramlee ta kalleta ta ce.
“Hope dai kin shirya?”
“A shirye nake, kawai dai ina gudun a samu matsala ne”
“Ba wata matsala, Dr KB kwararen likita ne, ba yau na saba aiki da shi ba, ki kwantar da hankalinki”
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin kamar kar ta aikata.
________________
Inshallahu a nan zamu dakata sai kuma bayan sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana ganin lokacin cikin koshin lafiya. Fatar Allah ya karba mana ibadar da zamu shiga ya yafe mana kurakuranmu.
Ina neman afuwarku. Sai mun hade a Book 2 bayan Sallah inshallahu. Happy Ramadam
Showing 132001 words to 132434 words out of 132434 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45