da fad'in “shawara mai k'yau, lallai kanason d'ankan nan, ka tambayi abokanka, Wanda bazai mik'a wuyanba saiya fad'a yanzun nan”.
“karka ta6a mana yara please, duk zamu mik'a wuya”.
Galadima ya tuntsire da dariyar da wanima zai iya rantsewa bai ta6a ganin yayiba, yace, OK, good dattijan k'asa, saina jiku acan”.
🤣🤣ana shagali a Nigeria yau kam🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀ amma Nigeria novel ba tamuba😜.
Su Alhaji balala dai kam sun mik'a wuya, da Kansu suka kai Kansu police station mafi kusa, daga can suma d'aukesu zuwa inda IG yace.
Galadima yay hamdala ga ubangiji dukda bawai komai yagama kammaluwa bane, amma lallai an d'akko hanya.
Ya bada Umarnin tashi suyi sallar La'asar, kafin a dawo a cigaba da gashi😜.
....................................★
Bayan sun idar da salla C.P ya kira Galadima, suka shaida masa su Alhaji Bana suna hannunsu yanzu haka.
Galadima dake tsaye yace, “Alhmdllh, zuwa safiyar gobe kuma sai a kai case d'inmu Court, Dan inason komai yafarune cikin gaggawa ya k'are, bana son jan jiki a aiki”.
C.P ya kalli IG Dan jiran amsa.
Kai IG ya jinjina masa alamar za'ayi hakan.
C.P ya shaidama Galadima amsar IG.
Galadima yace, shikenan, shi yatashi daga aiki, saikuma safiyar gobe.
C.P zaiyi magana I.G ya dakatar dashi alamar ya barsa kawai.
Ta6e baki Galadima yayi yana yanke wayar, ya maida kallonsa gasu Muftahu da duk suna maidashi television, gira d'aya ya d'age musu, sukuma sukai masa jinjina👍🏻.
Kauda idonsa yayi ya maida ga yaran, yace, “yaya akwai mai buk'atar wanka ko barci?”.
Gaba d'aya suka amsa da duk suna buk'ata.
Kallon Ameer da Saleem yayi yabada Umarni da ido.
..............................★
'D'aya bayan d'aya suka dinga kaisu suna wanka, duk Wanda yagama sai abashi lemo, batare daya San miye acikiba saiya shanye, daga sha ko mintuna 3 basa k'arawa suke 6ingirewa barci🤣.
🤣🤣ho Galadiman mu kasan takan tsiya, Zuma kenan, ga zak'i ga harbi🤸🏻♀, kaga Na Munaya baban triplets, bada kanka a sare kaje gida kacema su mama Fulani an k'illesa👌🏻😜😂.
Da akazo kan Harun k'in tankawa yayi, Dan haka Galadima yace su barshi kawai, amma harsu Malam Saminu da Alhaji Darma su Farhat duk sunma Kansu gyad'ar dogo sunje sun mik'e zasu huta.
Nuren ya kalli Galadima cike da tausayi yace, “Brother kaima kad'anje ka huta mana”.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, yajawo lap-top gabansa yana girgizama Nuren kai alamar a'a.................✍🏻
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu_*😭👏🏻
[8/3, 5:00 PM] Ana Musleem: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻1⃣8⃣
.................Yauma dai kotun ba'a cewa komai, wad'anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk'arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai.
Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d'inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k'yau matuk'a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak'iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock's Nuren ya lek'o yana fad'in “Brother ka hanzartafa mun makara”.
“umhum” kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk'usa gabansa yana kama k'afar daya sakama sock's d'in ya saka masa takalmi.
Baki Galadima ya tsa6e yana cewa, “kaifa shegen gaggawane dakai wlhy, ni bansan INA kuka kwaso halinnanba, haka Momma da Aunty Mimi suke, komai kunfison mutum yanayi kamar wani mazari”.
Nuren ya sanya dariya yana saka masa d'aya takalmin, yace, “to sokake muke Abu kamar marasa laka a jiki? Munaya dai kam tana fama...”
Hararsa yayi, hakanne ya hana Nuren k'arasawa, Galadima daya wani tsaresa da ido yace, “Tana fama da k'aniyarka”.
Nuren ya mik'e yana fad'in “oho maka dai, mu ka fito su sarkin mota tuni sukazo”.
Mik'ewa yay ya d'auki turarensa Na kullum a bag d'in daya had'o kaya ya fesa, k'amshin ya gauraye ko ina, waya d'aya ya zura a aljihu ya fito.
Su Ahakam duk shagala sukayi da kallonsa, a ransu suna matuk'ar yaba tsarinsa, komai nasa abin birgewane, kamar yanda ya saba haka yabasu hannu da kansa sukayi musabaha dukda suna nok'ewa alamar jin kunya da girmamawa a gareshi, shikam babu ruwansa, inhar bakasan halinsa bane dolene tashin farko ka jefeshi da kalmar girman kai.
Su Farhat ma suka gaisheshi cikin risinawa, wani miskilin murmushi yamusu yana d'aga musu hannu kawai, ya kalli Saleem tare da masa nuni yabama kowa kayansa.
Saleem ya amsa da cewar “ok boss”.
Bag d'in da wayoyinsu ke ciki ya d'akko, amma sai sukace sukam ya barsu, Dan inhar ba'a yanke hukunci ba zasu dawo su cigaba da zama dasu, Dan zama da Galadima akwai dad'i, kuma ko an yanke hukuncima masarauta zasu bishi.
Shi dariyama abin ya bashi, hakanne yasakashi bubbuga kafad'ar Yassar dake kusa dashi yana sakin murmushin da har hakwaransa ke bayyana, ya wucesu yana sauka daga benen cikin takunsa Na birgewa.
Suma duk binsa sukayi a baya, komai nasa Saleem ya tattaroshi, dan bazai sake dawowa gidanba koda ba'a yanke hukunci ba kuwa.
Harun dai anyi laushi matuk'a, dan maganarma yanzu ba iyayin mai k'arfi yakeba, saboda saiya gadama yakecin abinci, babu kuma mai sakashi dole yaci.
Cikar k'ofar gidan tabama Galadima mamaki matuk'a, yakuma d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya ba, musamman yanda duk aka zubo masa ido, a Bayama an kallesa balle yanzu da yayi abun kallon, y'an sanda da dogaransa da suka zo d'aukarsa tun d'azun sai k'ok'arin hana y'an jarida dakeson zuwa ga Galadima sukeyi, amma suna k'ok'arin kutsowa.
Tsaye Galadima yayi ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, saida yaga shigarsu Rahma mota dasu alhaji darma sannan yanufi inda sarkin mota ya bud'e masa, y'an jaridar daketa masa tambaya ko kallo basu isheshiba ya shige mota abinsa, yayinda Muftahu ya zauna gefensa, Nuren Na a gaba.
Mortar y'an sanda Na a gabansu da Bayansu, a haka akayi tafiyar.
Sauran y'an sandan da aka bari suka shiga gidan domin d'akko gawar Ahmad, amma sun bincika lungu da sak'o babuma alamar an cutar da wani, sai harbi guda d'aya daya shiga jikin bango, (shima Wanda Galadima yayine sanda ya tsoratasu da cewar ya kashe Ahmad), basu samu komaiba dazai nuna Galadima d'an ta'addane, sai suka fito suna kulle gidan, amma basu tafiba harsai kotu tabada damar hakan.
............................★
Sun Isa Court d'in, inda Galadima da Nuren da Muftahu ne kawai suka Shiga, yaran dasu Alhaji Darma an kaisu wani d'akine kusada wajen.
Takun takalman Galadima dake tafiya cikin tsantsar izza da nuna jinin mulki ya saka dukkan jama'ar kotun zuba masa idanu, shikam ya had'e fuska tamkar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta dabaya d'aga k'afar zubar ruwa, kallon kowa bayayi, gashi ya toshe idanu da Google eyeglasses d'insa da babu mai kallon kwayar idonsa.
A kujerar farko irin wadda su Alhaji Mamman ke zaune shima aka nuna masa shida Nuren da Muftahu.
Wani zama yayi dake tabbatarma da mak'iya shid'infa sarakine, gaba da baya kuma.
Hakan ya k'ona zuciyar su Alhaji balala matuk'a, amma babu yanda zasuyi.
Zaman Galadima babu jimawa saiga alk'ali ya fito, kowa ya mik'e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna.
Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk'ali idanu, yagama dube-duben ta kardun gabansa sannan ya d'ago ido yana kallon jama'a, yace, “Yau shari'ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk'atar Wanda yay k'ara, da wad'anda ake k'ara a gaban kotu”.
A hargitse su alhaji Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud'ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za'ayiba.
Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d'in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan ya mik'e.
Dole suma duk suka mik'e inda aka buk'aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad'anma.
Alk'ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k'ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak'a kai tsaye?”.
Murmushi galadima yayi, ya cire eyeglasses d'in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y'an cikinsa da tunaninsa, hakanne yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta.
Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad'an cije lips, cikin k'asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari'a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k'addarar ciwo ta kwantar tsawon wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wannan kuma sanadin shine Na d'auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d'aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhammad Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k'are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had'iye hawayen.
Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad'anda suka k'ullaceshi da farko.
Galadima ya cigaba da fad'in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana'a mai wahala kad'ance banyitaba a k'asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk'usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k'aunarsa da nakeyi, duk da banida burin yin aiki a k'ark'ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had'aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad'e ina bulayin Neman hanyar bincike akan abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d'ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a nemamin aiki k'ark'ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad'annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k'yaleni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y'an ta'adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k'ark'ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a lokacin nagama bautar k'asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok'i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6a shari'a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d'insu, tun hawan Computers d'in danai a tashin farko Na gane da had'in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula da Computers d'in sunada buk'atar k'arin ilimi ma gaba d'aya. Cikin sauk'i Na d'akko bayanan da aka d'auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d'auki abinda nayi matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok'on kasancewa a cikinsu amma nak'i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan yaje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk'i, hakama Baffi ya fad'amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d'aya sai nima naji yakamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko file Na binciken case d'in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d'in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y'an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d'in gefe kawai. Tun a file d'in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaji Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk'uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsananta bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had'in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLAH yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d'an dakatama gaba d'aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai.
Saida Na d'auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk'uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi had'arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d'in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k'ut sannan d'an uwansa, Dan haka yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad'amin akan miya faru dashi kafin had'arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k'arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k'are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Dan nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k'arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d'aya itada y'ay'anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d'aukarsu suma. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d'iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-kaffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d'akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fuskarsa da handkerchief. Yaciga da fad'in,
“Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d'akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had'amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d'akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a shekara d'aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al'amurana, kuma inhar Nazo k'asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak'iyana Na auri wadda sukaso sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y'ay'ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had'a kai wajen Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari'a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink'urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k'addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k'urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak'ar case d'in mahaifina dashi, hakan kuma tafaru bisa sanadin matata, data dinga zak'ulomin wasu masu alak'a da mahaifinta kuma Na jikinsu tanderu, irinsu Mamman k'afur, Alhaji Halluru, saikuma daga baya ga SD, wato Alhaji shehu Darma, Wanda shine aka saka yake bibiyar Alhaji Auwal Fharuk yana masa barazana, satar yarana da akayi a ranar sunansu ta kawo bayyanar aminina d'an uwana cikin case
Showing 291001 words to 294000 words out of 308791 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98 Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103