kirki bata ci. Abu na ganin Maryo ta janyota da sauri ta ce. "Abu ina kika shiga muna ta nemanki tun ɗazu" Kamar an buɗe famfo haka Maryo ta faɗa jikin Abu ta fashe da wani irin kuka, Inna Habi da sauri ta ɗago ta kalleta sannan ta kauda kanta gefe ɗaya tana rumtse idonta. Wasu bayi da ke cen gefe ne suka juyo suna kallon Maryo, dukda basusan abin da yake damun Maryo ba amma da jin irin kukan da take yi ka san daga cikin zuciyarta kukan yake fitowa. Abu bubbuga bayanta ta fara yi cikin tausayin ƴar uwarta ta ta ce. "Me yake faruwa Maryo?" Maryo hawayen ne ya kuma zubo mata da sauri ta kama hannun Abu ta kai saitin ƙirjinta. Abu zaro ido tayi jin yadda zuciyar Maryo ke bugawa da ƙarfi cikin sauri. Kafin Abu tayi magana ta ce."Duk bugun numfashi yana sauka da dakom soyayyarsa Abu mutuwa zanyi ba zan iya rayuwa babu shi ba, shi ya koya mini zallar soyayyarsa yanzu kuma ya juya mini baya. Ina ji a jikina kamar ba shi bane kamar ba zuciyarsa bace idan har zuciyarsa ce a jikinsa babu yadda za'ayi baiji abin da nake ji a zuciyata ba, Abu ki taimaka min bansan sanda na fara sonsa ba ban san yaushe na dulmiya cikin tekun ƙaunarsa ba, abu ɗaya na sani wallahi ina sansa ina ƙaunarsa amma ya juya mini baya Abu kin ga" Maryo ta janyo hannun Abu ta ɗora akan ɗan yatsan da zoben hannunta yake kai ta ci gaba da cewa."Har nuna miki na yi a ranar da muka haɗu da ke da hannunsa ya bani, tun kafin wannan ranar kowa yasanni da shi amma me yasa lokaci ɗaya yi mini haka. Abin da ban taɓa tsammani bane amma yau ya mareni a gaban mahaifina Abu ki duba irun hallacin da mahaifina ya yi masa, bansan laifin da nayi masa amma duk laifin da nayi ban cancanci irin wannan hukuncin..." bata ƙarasa magana ba Abu ta sa hannu ta toshe mata baki saboda yadda mutane suka fara taruwa a bakin ƙofar suna leƙensu, rumgume ta Abu tayi a saitin kunnenta ta ce mata. "Kiyi shiru Maryo mutane suna kallonmu kinasan a dinga yi da mu a cikin gidan nan kenan?" Sororo Maryo ta yi tana kallon Abu cikin sanyin murya ta ce. "Shikenan Abu na bar maganarsa kenan?" Abu da gyaɗa mata kai.
Abu ta fara girgiza kai ta ce. "Bakiji yadda zuciyata take yi mini ba Abu, ba zan iya ba..." bata ƙarasa magana ba wani irin tari ya sarƙe ta nan take ta fara wani irin kakari sai ga wani irin aman jini na fita daga bakinta nan take numfashinta ya fara ɗaukewa ta yanke jiki ta faɗi a gurin.
Lokacin da aka kaishi masauki kwanciya ya yi akan katifa ringingine idanunsa sun ciko da ƙwallah yana tuna soyayyarsa da Shukra.
Zaune take a wani ɗan madaidaicin ɗaki ta ga ya shigo hannunsa ɗauke da wata babbar leda, turo baki gaba tayi ta ce. "Ya Maleek wallahi tun ɗazu nake jiranka har na fara jin tsoro" hancinta ya lakace yana kwaikwaiyar muryarta yace. "Tsoron me bayan kinsan ba daɗewa zan yi ba" Juya masa baya tayi alamun tayi fushi tana ajiye ɗinkin hular da take yi, ta bayanta ya rumgumota ta faɗo jikinsa yace. "Tuba nake amma kinsan dai nima ba da san raina na daɗe ba" Kafin ta yi magana ya fara buɗe ledar da ya shigo da ita sannan ya ɗauko Ƴar tsala ya sa mata a bakin yace. "Na cika alƙawari dai tunda ga ƴar tsalanki" ci ta fara yi harda lumshe ido tana haɗiyewa kamar wacce ta haɗiyi maɗaci ta fara kakarin amai, da sauri ya janyo mata rigarsa dake rataye yasa a gabanta nan ta hau amai har sai da ta amayar da duk abin da ta ci" cikin tausayawa ya fara mata sannu ta langaɓar da kai ta ce. "Ya Maleek anya ba mutuwa zan yi ba?" ta faɗa hawaye na zuba daga idonta. Ya sa hannu ya goge mata yace. "Shukura ki daina faɗin haka, laulayi ne kawai. Kina tunanin idan kika mutu zan iya rayuwa ne" Murmushi tayi ta ce. "Ba sai ka kula da abin da zan haifa ba"
Tashi ya yi zaune yana goge hawayen da ke zuba a idonsa, a hankali ya furta. "Shukra me yasa me yasa zaki yi mini haka" kamar wanda aka mintsina haka ya zabura ya miƙe zaune ya ciro wayarsa lambar Mahaifinsa ya kira har sai da ta tsinke ba'a ɗauka ba, kira ya ƙarayi sannan ya ji murya mahaifin nasa a tsakiyar kansa sakamakon dogon tunanin da ya shiga.
"Maleek ya akayi?" Maleek ya shafa kai yace. "Ranka ya daɗe barka da hutawa" Mahaifin nasa ya amsa sannan yace. "Allah ya taimakeka naga Shukra a gidan Kawu" da mamaki Mahaifin nasa yace. "Wace shukuran?" Maleek yace. "Shukra dai tawa" ajiyar zuciya Mahaifinsa ya yi sannan yace. "Maleek Allah har yanzu baza ka sawa zuciyarka salama ba, ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo" Maleek kamar zai yi kuka yace. "Wallahi da gaske nake yi na ganta da idona" Muryarsa ce ta fara rawa ya ci gaba da cewa. "Amma ko kaɗan bata nuna ma ta sanni ba Mai martaba" Mahaifin nasa yace. "Maleek ba tun yau ba fa na ce maka ka dage da addu'a domin na lura mutuwar yarinyar nan yana san taɓa maka ƙwaƙwalwa, Shukra yau shekararsu nawa da mutuwa ina jin ta kusa biyu idan ba mantawa nayi ba, saboda irin haka nace maka dama ka fitar da wata matar ka yi aure amma fir kaƙi" Maleek ya taƙarƙare ya fara zabga rantsuwa.
"Na rantse da girman Allah ita na gani Ranka shi daɗe, kasan bazan maka wasa ba a cikin fadar Kawu fa na ganta ta fita tana hawaye da alama ma kamar shari'a yake musu, ni dama na daɗe da ji a jikina Shukra tana nan da ranta bata mutu ba tunda har gobe ba'a tsinci gawarsu ba." Mahaifinsa yace. "Dama ya za'ayi aga gawarsu bayan wuta ta cinye su ƙurmus, wallahi Maleek ina tsoron kar yarinyar nan ta fara yi maka fatalwa" Maleek yace. "A fadar Kawu fa na ganta ka yarda dani wallahi ka turo wani daga nan yazo ya ganta idan ƙarya nake." Ganin ya dage yasa Mahaifinsa yace. "To shikenan zan yi nazari akai" suna yin sallama ya kira Mahaifiyarsa ya sanar da ita halin da ake ciki itama ba ƙaramin kaɗuwa tayi da jin zancensa ba, bayan ta gama sauraronsa ta ce. "Maleek ka tabbatar da abin da ka faɗa gaskiya ne kuwa kar na kira Yaya naji akasin haka" cike da ƙarfin gwiwa yace. "Wallahi da gaske nake Umma" har lokacin mamaki take ta ce. "To amma wannan lamari akwai ɗaure kai to Ina Hassan da Hussanin ko baka gansu ba? Kuma ita me tace maka?" Maleek yace. "Bangansu ba Umma, kuma ba wata doguwar magana mukayi da ita ba, bige ni tayi gar ta miƙo mini kayan tana bani haƙuri" Umma tayi jim ta ce. "Anya Maleek wannan lamarin naka akwai ƙamshin gaskiya, ace Shukra ta ganka amma ta kasa nuna farincikinta a fili? Amma babu damuwa zan kira Yaya zan ji daga bakinsa." Maleek ya sauke a jiyar zuciya yace. "To Umma" daga haka suka yi sallama da ita, tashi ya yi ya dinga kaiwa da kawowa lokaci-lokaci yana naushin iska. Gabaɗaya kansa ya kulle banda faɗuwar gaba babu abin da yake ji.
Saif na shiga sashen Mahaifiyarsa ya kusa karo da Baiwa Bintu dukda alokacin ba ƙwarin jikinta taji ba haka ta rissuna cikin girmamawa ta ce. "Tuna nake ranka ya daɗe" Gyaɗa mata kai ya yi yana binta da kallon tausayi har ya shiga ɗakin yana jin matsanancin tausayinta, zama ya yi ya gaishe da Mahaifiyarsa sannan yace. "Ammi wannan ba baiwar nan bace ni bansan sunanta ba" Fulani Zaliha ta ce. "Bintu ba ita ce wallahi baka jinyar da yarinyar nan ta sha ba kamar bazatayi rai ba, bayan na asibitin da akayi na hausa ma fa haka ake ta fama kasan jikar uwar bayi ce baka ga tashi faɗin da ta dinga yi ba, ciwo kamar mayu kamar kuma iska gashi nan dai" Saif yace. "Amma me ya kawo ta nan ba Baiwar Umman Salman bace.?" Fulani Zaliha ta gutsiri tufa ta ci gaba da cewa. "Eh a baya baiwarta ce amma gaskiya har yanzu bata koma mata ba tunda jikin nata har yanzu da saura, yanzu ma langa ta kawo mun wacce Uwar bayi ta tafi da tuwo rannan" Shiru Saif ya yi yana ƙara jin tausayin Bintu a ransa lokaci ɗaya yaji ta kwanta masa a zuciya a hankali ya furta. "Allah ya bata lafiya" Fulani Zaliha ta amsa da Ameen sannan ta ce. "Dama tun ɗazu na ji ka shiru ance min anga fitarka Saif banasan ka dinga nisa da gida fa" Saif yace. "Ammi dama naje gaida me martaba ne" ɗan tsuke fuska ta yi sannan ta ce. "Hakan ya yi kyau amma ka dinga lura" Saif yace. "In sha Allah! Ammi naga wani baƙo yazo amma naga yana yanayin kama da ni naji Mai martaba yana kiransa da Maleek" Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce. "Ɗan uwanka ne ai" sai kuma yanayin fuskarta ta sauya cikin damuwa ta ci gaba da cewa.
"Dan dai baka sansu ba, amma ɗan wajen Addanku ne Adda Zainabu me tsokanarka idan tazo" Murmushi ya yi yace. "Kai amma me yasa bansan shi ba" Fulani Zaliha ta ce. "Ai kasan shi sojan ruwa ne basu cika zama ba idan yazo kuma a ya daɗe ya kwana ɗaya" Saif ya jinjina kai yace. "Ai ta daɗe ma bata zo ba" ta ce. "Ai kuwa dai" daga haka suka ci gaba da hira Saif yana san sanar da ita yadda sukayi da Maryo a fadar Sarki Aminullah amma yana kokwanto, daga ƙasan zuciyarsa kuma yana jin kamar bai kyauta ba amma lokaci ɗaya sai yaji haushinta ya kamashi dan a duniya yanzu babu wacce yake jin haushi kamarta.
Tsaye suke a bakin tsibirin Fulani Maryama ta kalli Jakadiya ta ce. "Jakadiya wannan karan bafa zuwa na bane ni kaɗai, zuwan mu ne domin nemarwa kanmu mafita" Jakadiya sai raba idanu take ta ce. "Eh haka ne amma wallahi nikam lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro" Fulani Maryama ta yi mata wani kallo tana shirin magana akayi musu iso zuwa cikin kogon dutsen Boka Marduska. Kamar ko yaushe yanzu haka ma yana zaune a gaban wuta daga shi sai wata rigar fata me baza da wandon fata. Kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai ya ci gaba da sha'anin gabansu kamar ma bai gansu ba, kallan juna sukayi tsakanin Fulani Maryama da Jakadiya saboda tun da suke zuwa Marduska bai taɓa yu musu irin haka ba. Fulani Maryama ce tayi ƙarfin halin fara magana.
"Barka da aiki sarkin bokayen duniya Marduska me dogom zamani" Marduska ya kalleta bai tanka mata ba ya ci gaba da watsa wasu ƙasusuwa a cikin wutar sannan ya ɗago yace. "Maryama meke tafe da ke?" a nan ta fahimci Marduska fushi yake da ita saboda kana zuwa gurinsa kafin ma ka buɗe baki zai sanar da kai abin da yake tafe da kai. Ta russunar da kai ta ce. "Muna neman yafiya da alama munyi gagarumin laifi" Marduska yace. "Nasan akan Ɗanki Salman kika zo da Rayzuta" Jakadiya tare da Fulani Maryama kamar ƙadangaru suka gyaɗa kai lokaci ɗaya. Bushewa ya yi da wata mahaukaciyar dariya sannan ya kallesu yace. "Wuya ko da magani ba daɗi. Maryama dubi yadda kuka yi zumu-zumu kamar an jiƙa kasa a ruwa. To maganar gaskiya Maryama gidan ku na cikin wani irin yanayi ni da kike gani na wannan ƙurar tafi ƙarfi na dan bazan iya dakatar da ita ba. Shuɗaɗɗun ruhika haɗe da rayayyun ruhika ne suka gogawa a tsakani kinga kuwa ni meye nawa a ciki, maganar da Saif ya gaya miki tabbas haka ne domin Ɗanki sam baida imani irin zuciyar ubansa gareshi, wallahi kika nemi ki bashi matsala yana iya aikaki ƙiyama sannan matsawar kika bari aka ɗaura masa aure da Rayzuta to na tabbata mai ƙwatar kansa a gidan nan sai mai yawancin kwana. Ke in taƙaice miki labari wallahi gidan zasu tada gabaɗaya dan ko Sarki Aminullah banajin zai tsira da numfashi, domin tsoguwar gaba ce kuma kema kina da hannu a cikin wannan shuɗaɗɗiyar gabar." Fulani Maryama ta zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce. "Marduska me ye nawa a ciki?" Murmushi ya yi bai tanka mata ba yace. "Kafin zuwan wannan ranar nima bansan da haka ba har sai da Zulik ya bayyana, duba nan" ya ƙarasa faɗa yana nuna mata wata ƙwarya kusan lokaci ɗaya suka leƙa ita da Jakadiya, Fulani Maryama ce zaune a gaban wata sarauniya tana motsa baki da alama magana take yi mata, kafin ta gama fahimta suka ga ya ɗauke. A razane Fulani Maryama ta ce. "Marduska yaushe haka ta faru? A iya sanina bantaɓa zama baiwar wata ka duba fa ka gani kowa yasan ni ƴar Sarki ce gaba da baya kuma Sarki nake aure" Marduska yace. "Wannan amsar tambayar taki tana gurin Zulik wato Salma ki bishi a sannu shi zai warware miki komai ko shi ko Rayzuta, amma karkiyi fatan Rayzuta ta waiwayoki domin sam bazai yi miki kyau ba." ya nuna Jakadiya yace. "Ke kuma ina jiye miki ranar da Saif ɗan wajen Zaliha zai juyo gareki tabbas a lokacin me ƙwatarki sai Allah, dan sai ya ƙasƙantar da ke a cikin gidan sannan kuma ya yi miki kisan wulaƙanci domin Furzaan cike yake da baƙin cikinki" Jakadiya ta ce, "Waye kuma Furzaan ni ƴasu" Marduska yace. "Ɗan wajen Zaliha ne sannan ita kanta Rayzuta bata kyaleki ba ko dan abin da kika yiwa Sarki Aminullah domin Mahaifinta ne" A zabure Fulani Maryama ta miƙe tsaye ta ce. "Me kake faɗa? Yarinyar ce ƴar gidan Takawa?"
Daga cen Masaraurar Adamawa wata mata na gani Aƙalla zata yi shekara Arba'in da biyar, safa da marwa take ta yi a cikin ɗakinta cikin tashin hankali. Wayarta ta ɗauka ta doka kira babu jimawa aka ɗauka ko amsa sallamar ba'ayi ba ta ce. "Ka san wanne mummunan labari na samu yanzu? Wai Maleek ya je Masarautar Kano gidan Wan Mahaifiyarsa ya kira Mai martaba wai ya ga Shukra a cen" daga cen ɓangaren yace. "Fulani me kike faɗa ne wai? Yarinyar da muka bankawa wuta ita ce ta aka gani a masarautar Kano?" Matar da ya kira da Fulani ta ce. "Wallahi da gaske nake fa yanzu haka Sarki ya tashi Mutum biyu daga nan sun tafi cen yanzu ina muka kama idan yarinyar nan ta bayyana? Kasan asirinmu ya gama tonuwa dai.Ni kam har bansan ya zanyi ba wallahi" Mutumin yace. "Lallai tsugunne bata ƙare mana ba, Amma kuwa dole musan abin yi matsawar Shukra ta dawo gidan nan hatta zaman duniyar ma sai ya gagaremu."
INA MUKU FATAN ALHERI🥰
BA WANI PAGE DAN WALLAHI WUTARMU TA LALACE TUN KWANAKI KUYI HAKURI DA ERRORS
KU HAƊE A COMMENTS🤾🏻♀️🤣
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[09/11/2021, 18:13] Ameera Adam🌚: 24...
Marduska ya kalli Fulani Maryama da yadda take ta tada jijiyoyin wuya, wani tsohon ƙoƙon kan ƙwarangwal ya ɗauko ya kantami wani kore-koren ruwa ya sha sannan yace. "Maryama meye naki na ta da jijiyoyin wuya bayan duk ƙafafar da kike yi Salman fa ba ɗan masarauta bane" Fulani Maryama ta kalli Jakadiya da tayi ƙuri tana raba ido kamar shege a rabon gado, wani yawu ta haɗiya me ɗaci ta ce. "Marduska duk ba wannan ba. So nake na ji ta ya akayi yarinyar ta haɗa jini da Takawa? Ni ce uwar gidan Sarki Aminullah kuma duk a kan idanuwa aka haife ƴaƴan sa guda ashirin da bakwai biyu sun rasu, ko a mafarki ban taɓa jin ance wata daga cikin ƴaƴansa ta ɓace ba, kuma Sarki Aminullah ƙwarƙwararsa ɗaya ƴaƴanta biyu duka mata ta ina suka haɗa dangantaka?" Marduska ya kafeta da ido yana kallo sannan yace. "A inda ba ƙasa anan ake gardamar kokawa. Duba mini nan" ya janyo wani ɗan ƙoƙo da bai fi tafin hannuwan kakkauran mutum ba ya nuna mata, daga cikin ruwan ƙoƙon Maryo ce ta bayyanawa cikin shiga ta alfarma daga cen kan karagar mulkin rangaɗaɗau fuskar Sarki Aminullah ta bayyana ɗauke da murmushi, Maryo ce ke motsa baki bayan wani lokaci ta miƙe ta rungume shi sannan ya sumbaceta a goshi ta fice daga fadar, fitarta babu wuya sai ga mace mai siffar Fulani Maryama ta ƙaraso ta durƙusa gaban Sarki Aminullah tana gaishe shi cikin girmamawa. Boka Marduska yasa hannu ya shafe saman ƙoƙon su Jakadiya suka daina kallon, kamar haɗin baki suka sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya.
Jakadiya ta ce. "Marduska ni bansan ta ina zan fara ba saboda al'amuran duk masu sarƙaƙiya ne? Ka fayyace mana abin da yake ɓoye" Marduska yace. "Bani da hurumin fayyace muku abubuwan da ba hurumina bane, ina ta ƙoƙarin inbaku haske dai ta yadda zaku fahimci al'amuran. Amma muddin nayi katsalandan ina iya fuskanta barazana daga waɗannan ɓangarorin guda uku. Karku manta da gaya muku shuɗaɗɗu da rayayyun ruhina ne suke gwabzawa kuma dukkanninsu zaƙaƙurai ne kowanne ka nemi ka yiwa shisshigi to tabbas zaka iya zama shuɗaɗɗe." Lokacin da Marduska ya dire da zancensa ya kallesu a zatonsa zasu kuma jefa masa tambaya amma sai yaji shiru da alama sun miƙa masa lamuransu. Ya gyara zama ya ci gaba da cewa. "Zan
Showing 27001 words to 30000 words out of 57328 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10 Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20