Bayan tafiyar ku ya zo nema mini transfer, shinefa wannan matar ta tisa shi a gaba ta dinga yi mana sharri…Amman kar ki damu, duk fushin da Yaya zai yi dani na san 2 weeks d’innan yana cika ya huce, kuma zai saurareni, daga nan zan zo in sha Allah..
Yau sauran 5 days ai kwanankin su k’are.”
Ya fad’a sounding so relieved.

“Kafin nan an d’aura mini aure”
Ya ji Maryam d’in ta fad’a..

Ba abinci ko ruwa yake sha ba amma wata muguwar kwarewar da yayi sai da ta d’auke shi kusan minti uku yana tari tukunna ya dawo dai dai.
Cikin tsananin tashin hankali yace “kiyi mini wasa akan komai Maryam amma banda wannan!! me hakan yake nufi???”
Yayi mata tambayar da kakkausar murya…

Duk abinda ya faru daga dawowarta zuwa yanzu babu abunda Maryam ta b’oye mishi.
Ga mamakinta bai ce mata komai ba, kawai taji ya ajjiye wayar.

Ta kai kusan minti d’aya da kan wayar a hannunta, tukunna ta share hawayenta ta ajjiye ta juyo da nufin komawa d’aki suka yi ido biyu da Shuwa.

Gabanta ne yayi mugun fad’uwa, cikin rawar jiki da na murya mai cike da in ina
ta k’arasa inda Shuwan take ta hau kame kame “Da da ddmn kawai nn ccemishi bai kky…”
Wani wawan marin da Shuwa ta kwasheta da shi ne yasa ta kasa k’arasawa, bata dawo dai dai ba ta k’ara mata wani wanda yasa har sai da ta kai k’asa tana shirin tashi ta rufeta da duka…..
Sai da Shuwa tayi mata lilis!! kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba, dan har sai da takai bata iya kuka tsabar azaba, tukunnan ta kyaleta tana mai cewa
“Tunda na lura kin daina fahimtar yaren magana
watak’il ki fahimci wannan!.
Gani kike yi yanzu kinfi k’arfin kowa ko? To ni da ke mu zuba mu gani.”

Tana gama fad’in haka ta wuce ta isa wajen landline d’in, ta gwada yafi sau nawa amman dai ko ba’a d’auka bane ko kuma bai tafi ba.

A haka tazo ta wuce ta tsallake ta, ta tafi ta barta a kwance a falon tana kukan wahala..
Ganin ba zata iya taimakawa kanta bane yasa kawai ta hak’ura, a wajen baccin wahala ya kwasheta.

Kamar a mafarki taji ana tab’a fuskarta ana haskawa da tochila, bud’e idanuwanta taci gaba da yi, bata ganin komai sai hasken fitilar…sama sama take jin muryar Ya Usman yana cewa “Abba ba sai ka kira Likitanba, ta farfad’o.
Da sauri Madu ya k’araso yana tamabayarta “mai ya faru? Mai ya sameta?”
Bata ida bashi amsa ba Shuwa wadda ke shigowa yanzu tace
“Ni da itane.”
Da mamaki ya mik’e ya juya yana mata kallon tuhuma kafin yace “ke da ita? ban ganeba.”

“Dukanta nayi”
ta fad’a tana k’ok’arin wucewa.

Da sauri yace “mai yasa??dakata mana!! Ina zakije ana magana! Mai ta yi miki?”
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin hanata wucewa.

Da mamaki Shuwa take kallon shi dan bai tab’a yi mata haka ba. Kallon Maryam d’in tayi da take k’ok’arin zama, sannan
tace “Kamata nayi ta kira wanchan Yaron na makarantarsu, tana cewa za a yi mata auren dole…
shiyasa na zane ta! tunda kunnenta ya daina jin magana watak’il idan aka tab’a lafiyarta zata fi fahimta tun……”

Madu bai bari ta k’arasa ba ya rufeta da fad’a, shi kanshi ya manta rabon da yayi mata fad’a hakan suna a su kad’ai ma, ballantana a gaban Yara.

Sai da yayi mata tatas tareda kwakkwaran kashedin kar ta sake dukar masa Y’a, tukunna ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace! Shi a ganinshi yanzu Maryam ai ta wuce mari ma ballantana irin wannan dukan, kuma abun haushin ta tsallaketa ta barta ko bi ta kanta ma bata yiba, idan ma mutuwa zatayi bata damuba kenan.!
Sai da yaje masallaci ya zauna shi d’aya, daga baya yayita karatun Qur’ani tukunna ya d’an samu zuciyarshi tayi sanyi.

Shi kanshi ya san idan akwai abu mafi soyuwa a rayuwar sa to Maryam ce, bayajin akwai uban da yake son Y’arshi a duniyar nan kamar yadda yake son Maryam, shi yasa idan ya tuna ranar Jumaar nan zai aura mata wanda bata so sai yaji gabanshi yana ta fad’uwa, amman bashi da yadda zai yi ne shiyasa, hakan it’s the right thing to do.

Ita kuwa Shuwa da kyar ta fita daga shock d’in data shiga na fad’an da Madu ya rufeta da shi, aikuwa akan Maryam itama ta zazzage nata fad’an, kafin ta juya tayi d’akinta.

Maryam mamakin yadda Shuwa ta juya mata baya lokaci d’aya take yi, ita kam zata yi k’ok’arin yin yak’i da zuciyarta ta rabu da Abba dan taga abun nasu yana shirin tab’a har zaman lafiyan iyayenta.

Muryar Ya Usman ce ta katse mata tunani, da sauri ta d’ago ta kalleshi…a hankali yake ce mata “Ya jikin?”
“Da sauk’i” tace dashi, tana k’ok’arin kawar da kanta daga kallonshi, dan bata son ganin fuskarshi! Gani take yi shine ummulabaisin haddasa mata duk wata fitinar da take ciki a yanzu.

Sake fuskantar ta yayi ya d’an tsugunna a gabanta sannan yace “Inane yake yi miki ciwo?”

Chan k’asa a hankali murya ciki ciki tace “Babu ko ina.”
Ta fad’i hakan tana turo baki tana k’ok’arin tattaro ragowar k’arfinta domin ta samu ta mik’e.
“Mai kike buk’ata??”
Ya sake tambayarta.
“Ba komai.”
Tace dashi a d’an hassale sannan ta mik’e da sauri dan so take ta bar wajen.

Mik’ewa shima yayi, sannan yace
“Maryam!”.
Tsayawa kawai tayi ba tare da ta amsa ko ta kalleshi ba, dan zuwa yanzu ta fara tunanin anya su Ya Usman basu had’a jini da mayu ba kuwa?….

Maganarshi ce ta katse mata tunani “Ba kya sona ko?”
Yayi mata tambayar yana isowa dab da ita.
Shiru tayi bata ce komai ba.
A hankali ya fara magana....
“Maryam ko baki fad’a ba na san bakya sona a yanzu!
Amman inaso ki san wani abu guda d’aya! ‘Ko da ace bana sonki, auran had’i za ayi mana, kika yi wannan tawayen, kika nunawa duniya bakya sona kika zab’i wani a kai na to tabbas ko sama da k’asa zata had’e wallahi sai na aureki!!
Ballantana kuma Ina sonki!
A yanzu bani da burin da ya wuce In aureki saboda abu uku:
‘Soyayyata a gareki

‘In nuna miki kuskuren ki

‘sannan inaso ki gano soyayya ta da take a cikin zuciyarki wadda wanchan Yaron yake k’ok’arin binnewa…

Dan haka shawarata a gareki itace ki daina d’aga hankalinki kina k’ok’arin hana abunda ba zai tab’a hanuwa ba’.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita.


Maryam bata samu daman tafiya d’akin da tayi niyya ba, hakan ta koma ta zauna a wajen taci gaba da kuka, har sai da Bilkisu ta zo tayita lallashinta tukunna ta mik’e ta isa d’aki tayi ta jero nafilfilinta..
Dan sai a lokacin ma ta lura ashe dare yayi.

Washegari da safe taga anata shirye shirye, zuwa k’arfe d’aya motocin y’an Maiduguri suka fara sauk’a, sai a lokacin ta tabbatar tabbas aurenta za ayi, kuma tayi alk’awari idan son Abba zai kasheta ba zata sake kiranshi a waya ba, dukda ta karb’i uzurin shi da ya gaya mata, kuma ta yadda ba son Yarinyar yake yi ba amman mai yasa zai kashe mata waya? kuma bai ma fad’a mata magana mai dad’i ba da zata d’an kwantar mata da hankali…..
Tana wannan tunanin wata cousin d’inta ta shigo ta, suna ganin juna suka hau murna, dan ba laifi suna shiri sosai da Maryam d’in.
Bayan sun d’an gaisa tace “turota aka yi ta kirata”
Tayi sauri ta je kafin fushin Inna ya k’aru….
Tunda Maryam taji an ambaci inna gabanta ya hau fad’uwa!
Haka ta zari gyalenta ta fita jiki ba kwari, cousin d’in tata na biye da ita.
Tun kafin ta k’araso Kakar tasu ta fara surfa mata fad’a, da yaren Shuwa da Hausa duk had’awa take yi, dan kaf Shuwa ta labarta mata halin da ake ciki…….tana yi sister’s d’in Shuwa suna tayata, ahaka dai suka yi mata tattass sai kuma aka koma nasiha ana cewa “ta bi zab’in da iyayenta suka yi mata, ta kyale wanchan Yaron waye waye….”
Ita dai Maryam tayi shiru tanata kad’a kai kamar k’adangaruwa, sai da suka gama tukunna suka hau yi mata gyaran jiki, bayan nan akace taje tayi wanka anjima akwai kaulu. Nan suka shirya kayayyakin Al’ada da su tabarma wai zasu kai gidan ango, Shuwa kam sai ce musu take yi “ai da sun bari, dan babu wani shirin aure da akayi, babu ma fa tambaya ba komai kawai dai Madu yace jumaar nan zai aurar da ita ga koma waye shi kuma Baban Usman yace ga Usman nan, to maybe sai a masallacin gobe za ai komai a lokaci d’aya kuma a d’aura auren”
Amma su dai basu biye taba sai da suka kai kayan tukunna hankalinsu ya kwanta, a cewarsu ai wannan dolene dan ma babu lokaci ne da duk wata al’ada sai sunyi…..

Gyaran jikin da aka yiwa Maryam na iya wuni d’aya yayi masifar karb’arta, tayi kyau sosai!!
Tana zaune gaban mirror tana shafa mai fitowarta kenan daga wanka, cousin d’inta ta d’azu ta sake shigowa tace mata
“Wai Shuwa tace tayi sauri taje parlourn Madu yana nemanta yanzu yanada bak’i.”
A gurguje ta shirya ta saka doguwar riga y’ar kanti ta zumbula uban hijabi kalar blue black, ta fita da niyyar idan ta dawo sai tayi shirin Kaulun.

Kowa ya kalleta sai ya k’ara, ana ta yaba kyawun da tayi haka tazo ta wuce su ita dai bata cewa ‘k’ala’ sai dai murmushi.
Tunda aka ce mata Madu yana kiranta haka nan gabanta yake fad’uwa, tana k’arasowa bakin k’ofar falon taji fad’uwar da gabanta yake yi ya tsananta!! Da kyar ta iya saisaita kanta tayi knocking, ta ciki taji muryar Baba Bashir yana cewa “ta shigo”
Hannu tasa ta murza handle d’in k’ofar sannan ta tura had’e da tura kai ta shiga, kanta a k’asa.
Haka nan ta kasa d’agowa sakamokon yadda zuciyar ta ke bugawa sosai sosai, sai da ta samu waje ta zauna tukunna ta d’ago kanta da niyyar gaishesu......

BULAMA ✍️







So da Buri
Free Book
14


idanunta suka sark’e a cikin na Abba wanda ya kafeta da ido ko alamar kyaftawa bayayi.....

Mutumin dake zauna a gefen sa mai tsananin kama da shi ne taji yana cewa “Ma sha Allah, mun sameki lafiya??”

Cikin d’an jin kunya ta sunkuyar da kanta sannan tace “ina wuni.”

Yana murmushi ya amsa mata,
Ita kuma ta juya ta gaida Madu da Baba Bashir, sannan ta gaida Abba wanda ya kasa daina kallonta, ko kunya ta kasa hanashi kallonta a gaban iyayenta.

Da kyar ya iya cewa “Lafiya”
Wanda ba ma kowa ne ya ji ba sai ita d’in da take kallon fuskarsa.

Madu ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana “Maryama wannan shine Yayan Abba”
Yayi maganar yana nuna wannan mutumin da yake zaune a gefen Abba.
Jinjina kai Maryam tayi sannan ta sake gaidashi kanta a k’asa
Murmushi shima yayi ya sake amsawa dan a gaskiya Maryam ta burge shi, yanayin nutsuwa da hankalinta sun burgeshi.

Madu ne ya cigaba da cewa “Lokacin da muka dawo daga hajji mun baku labarin wani bawan Allah da ya taimakemu aka tseratar da Usman ko?”
Jinjina kai ta kuma yi.
Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin yace
“To gashi nan a zaune”
yayi maganar yana sake nuna mata Yayan Abba, da sauri ta d’ago ta sake kallonshi wanda shi kuma a yanzu Abba yake kallo har yana d’an tab’ashi da alama nuni yake yi masa da ‘kallon ya isa haka’.

Modu ne ya d’aura da cewa
“Sunanshi, Alhaji Yahaya Umar Farouk mai turare, d’azun nan aka yi sallama ana son ganina, abun mamaki ina fita sai na ganshi, mutumin da muke nema ruwa a jallo sai gashi yau har gida.
Daman ni tun ranar da naga Abba a makarantar ku naso tambayarshi saboda tsananin kama da naga sunayi, amman kasancewar yadda abubuwa suka kasance a ranar ya sanya ban samu dama ba.”

Alhaji Yahaya ne yayi gyaran murya sannan yace
“Ina mai baku hak’uri, da kuma rok’on mu manta da wanchan zancen har Abada!
Saboda hakan ba abune mai maana ba especially idan muka yi duba da yanayin hankali da tarbiyyar Yaran.
Laifin su d’aya da suka yi shine da suka tsaya kula juna a makaranta, kowa yasan hakan sab’a doka ne, wanda hakan ne ya sanya ma maganar ta samu gurbi.

Ban san waye ya had’a kuma ya fad’i wannan labarin ba amman tabbas na san k’arya ne…. Mu uku mahaifin mu ya haifa a duniyar nan, bani da d’an uwa mafi kusanci dani kamar Abba, shiyasa ko a lokacin da nayi aure ma tare muka tare a chan part d’ina dashi kuma har yau a gidana yake…. na san abinda Abba zai yi na san wanda ba zai yi ba, dukda ance ba a shedar mutum amma ni kam zan shedi Abba a duk inda yake.

Na hanashi fita ne tun dawowarshi ba dan komaiba sai dan saboda ita Yarinyar,
saboda na san ko wanne Uba idan aka fad’i irin wannan maganar akan y’arsa dole zai d’au zafi ba kad’an ba, so shiyasa na hanashi zuwa nace masa ya d’an bari abubuwa su lafa tukunna sai mu zo, dan already daman na saka a raina zamu zo neman aurenta, dan a duk fad’in duniyar nan bata da mijin da yafi dacewa ta aura kamar Abba.

Sannan Abba ya tabbatar mini da soyayyar ta a cikin zuciyarshi, nutsuwa da hankalinta duk ya gamsu dasu sai a lokacin ne ma yake fad’a mini ashe lokacin da yayi rashin lafiya har na taho ban samu munyi sallamaba wai duk a ta dalilin ya nemi gidan nan ne bai samu ba.

Kuma ya fahimtar dani Yarinyar da aka zab’a mishi a gida sam baya sonta, ko ya aureta ba zasu zauna lafiya ba, shiyasa naga ya dace muje mu samu Mahaifin mu muyi mishi bayani yadda zai fahimta tukunnan muzo nan
To amman kuma jiya sai ya zo mini a hargitse wai jibi za a d’aurawa Maryam aure!! Da na koreshi nace ‘ya jira har sai lokacin da na d’iba mishi yaga maryam d’in yayi tukunna zamuzo’ dan ni a tunanina kawai fad’a yakeyi ba wani aure, dan naga ya k’agu ya ganta d’in
A take ya sume min, da kyar ya farfad’o yau da safe, bayan Likita ya tabbatar mana jinin shi ne ya hau saboda damuwar da take neman yi mishi illa, shiyasa a take na saka shi yayi wanka ya d’an ci abinci ko mai d’akina ma ban samu damar gayawa ba muka taho..

A labarin Maryam, ta gayawa Abba cewa ka ce ranar Jumaah zaka aurar da ita, so a iya yadda na fahimta watak’il baka riga kun tsaida mijin ba,ko?
Saboda haka
gamu nan mun zo neman aurenta ban sani ba ko za a amince a bamu…
…….Very short ya d’an basu biography d’in familyn ‘Mai turare’.”
Dayake sanannen family ne, nan suka ce “ai suna jin ma sunan familyn..”

Baba Bashir ne yace “Alhaaji munji abinda yake tafe da kai, amman kafin komai da farko muna so mu fara yi maka godiya!! Mun gode sosai da taimakon da kayi kwanakin baya, Allah ya saka da alkhairi.
Sannan magana ta biyu,
ni dai kamar uba nake a wajen Maryam dan haka na bawa Abba ita halak malak!! Idan Allah ya kaimu gobe Jummah indai a shirye kuke za’a d’aura aure, sai dai In wani mugun hali muka ji a kansa (dan za muyi bincike kamar yadda ake yi In sha Allah) amman bayaga haka gobe iwar haka bi’izinillahi ta’ala an d’aura musu aure.”

Da sauri Madu ya kalle shi, kafin yace “Bashir maganar Usman fa, ya zamu yi?”.
Murmushi Baba Bashir yayi sannan yace “kar muso kanmu anan mana, Usman fa shi kad’ai yake son Maryam ita bata sonshi, wannan Yaron kuma”
yayi magana yana nuna Abba
sannan yace “yana sonta itama shi takeso.
Sannan abu na biyu, wannan bawan Allah” ya nuna Yayan Abba sannan yace
“Tun ranar da ya taimaki Usman muke son sake ganinshi dan mu gode mishi, yau gashi Allah ya kawoshi yana neman abu a wajenmu! Mai zamu tsaya jira???? Ka tuna shine fa silar fitar da Usman a wanchan had’arin wanda ba dan an gano gaskiya ba, da watak‘ila babu Usman a doron k’asa yanzu.

Kuma dani da kai duk na san auren nan nasu sai yafi kwantar mana da hankali, saboda abubuwa da dama..”

Shiruuu! Madu yayi…..tabbas duk abinda Baba Bashir ya fad’a babu k’arya a ciki, dan haka shima ya yanke shawarar ya bi bayan Baba Bashir d’in a take!
Juyowa yayi ya fuskanci Maryam sannan yace
“Maryama kina sonshi ko?”
Dariya Baba Bashir da Yayan Abba suka yi sannan Baba Bashir yace
“Kaima dai neman magana kake yi.”

Murmushi yayi kafin yace
“kawai ina son inji ta bakinta ne, ta fad’a a gaban kowa.”
Sannan ya sake maimaita mata tambayar……cikin jin nauyi a hankali ta d’aga kanta alamar ‘eh’.
“Alhamdulillah” shine abinda Madu yace, sannan shima ya tabbatarwa Abba ya bashi Maryam…
Yace “Ba sai ya wani had’a lefe ba sadaki kawai suke buk’ata su zo da shi gobe.”

Yayan Abban ne yace
“Maganar b’oye b’oye babu ita a tsakaninmu kuma ni mutum ne daman straight forward….

A gaskiya! Ba lalle mahaifinmu ya yarda da d’aurin auren a gobe ba, duba da yadda ya riga yayi wa Abban mata kuma a yau zamu gaya mishi d’aurin auren, na san za a d’an kai ruwa rana, watak’ila yace sai nan da sati biyu dan zai d’anyi gayyata…
Amman wannan duk ba matsala baceba, za azo a goben ko iya mu uku ne in sha Allah zamu d’aura auren, dan na lura Madu yana so ayi auren a gobe, inyaso daga baya sai a sake sabon aure mai taro idan mahaifinmu ya tsayar da rana…..”
A hakan kuwa aka bar maganar.
Murna a wajen Abba ba’a magana, dan ko kunya bayaji, haka nan ya zage ya dinga jero godiya ga su Madu, har sai da Baba Bashir ya fara tsokanarshi……:

Sallamar Maryam suka yi ta tafi su kuma suka ci gaba da hirar su cikin mutunta juna kafin daga baya suka yiwa juna sallama suka tafi akan gobe za’a had’u a masallaci in sha Allah…..
Da kyar Alhaji Yahaya ya lallashi Abba ya hak’ura
ya bishi suka tafi saboda da shi
Showing 42001 words to 45000 words out of 124886 words