🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒 GARWASHI🍒🍒 Page 1 Hadiza Bara'u gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Ubangiji Allah kayi musu Rahama kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH don girman shaffakin manzon Allah kasa ADDU AR da sukayi garemu karbabbiya ce Har kullum Ina godewa masoyan Rubutun Gidan iko bani da Bakin godewa sai dai nace Ubangiji yafi Ni yabawa son so nake muku Yan uwa Allah ya hada mu a ALJANNAH🥰 Godiya ga Ubangiji da ya yarda har na sake dawowa da wata firar Mai take GARWASHI Allah yadda kake taimako na a ko yaushe ka ci gaba da taimako na har karshen numfashi nayi ta yin nasara a komai na Fara lafiya na Gama lafiya 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ........"Kaddara sunanta guda Daya ne Amma ma anarta da harsunan ta sunfi gaban a kidaya bare a iyakance. A yadda na fahimci kaddara da Kuma sunanta sai na kalli Duniya da abinda ke cikinta duk a matsayin kaddara. Idan nace kaddara to Ina nufin kaddara. Sai dai yadda Ni na fahimci kaddara akaran kaina ba Haka sauran mutane suke kallon kaddarar ba. Domin ko mun samu banbanci kwarai da gaske. A gareni kaddara itace komai ya samu bawa kaddara ne Dadi da wuya. Samu da Rashi Rayuwa da mutuwa ita kanta DUNIYA da abinda ke cikin ta kaddara ne . Zuwan bawa Duniya ma kaddara ne Amma sai na fahimci mutane Abu guda Daya Tak suke Kira sa kaddara shine wani Abu da ya samesu marar Dadi shine kawai kaddara ban sani ba Ni fahimtar da nayiwa kaddarar ko don ya kasance gaba Daya Rayuwa ta kaddarorin ne sukayi Mata zobe ne yasa na fahimceta Haka? Koko nawa zaton ne dai Haka ? Oho. A wannan labarin ma da Zan baku ma babu komai a cikin sa sai tarin kaddarorin da suka faru akaina da iyayena da ma Yan uwana kwara biyu da muka Rayu a wannan kuntatacciyar Duniyar marar tagogin da zasu bamu iskan da zamu Shaka bare mugane Yan cin dake cikin Duniya Wanda har na kirawa kanmu GARWASHI domin ko gara zama a cikin GARWASHIN WUTA da irin kaddarar da kaddarar ta Miko Mana dolen mu kuma muka Mika hannu muka karba har ma muka bita da godiya duk da babu murmushi yayin godiyar sai ma tarin HAWAYE Mai radadi a garemu musamman ma Ni yarinya Fatima Zahra da duka duka shekaruna Sha biyar ne kacal Amma kaddara Bata tausayawa kuruciya ta ba kamar yadda bata tausayawa mahaifiyata ba Akan Rashin dangi da Yan uwa tayi aikin ta Akan mu😭 Ku shirya ku Kuma gyara Zama kuji yadda kaddara tayi sukuwa ta kumayi zamiya Akan mu Wanda karfin imani ne ya Hana mu hadiyar zuciya mu kauce daga cikin Duniya da Rayuwa........... *** *** **** **** **** GARWASHI Karfe 12:09 am ta buga Mana muna tsakiyar filin jirgin marigayi malam Umar Musa yar Adua a garin katsina motar da mahaifiya ta ke ja kirar marcendy ce 3400 muka SHIGA filin jirgin Wanda yayi daidai da Jin Rigugin jirgin AZAMAN Yana Shirin sauka Alamar dai ba wani dogon jira zamuyi ba Daddyn zai iso nayi murmushi Mai sauti yayin da ammi ta tayani wurin fadin "Munzo a daidai ga abin Sona Nan Zuwa Ta fada itama tana Kara fadada murmushin ta Wanda yayi daidai da parking din motar da tayi a daidai parking space da sauri na balle murfin motar na fito ina daga kaina sama Ina kallon jirgin da Yake shawagin sauka kasa cikin wani salo Wanda ya dauki hankali na Na daga tafin hannun na Ina Kare Ranar dake kashe min ido don na kalli jirgin da Wai buwar da yakeyi idan zai sauka da kyau har ma in bawa Yan uwana labarin da nagani Ammi tana Raba Mana kallo Ni da jirgin da ya dauko abin sonta cikin murna da farin ciki har zuwa lokacin da jirgin ya Soma saukowa kasa Yana tsillawa aguje kamar ba sauka zaiyi ba kafin ya zuro tayoyin shi da nagan su ya mitsimitsi kafin ya diresu a kasa fankokin shi na wulwulawa inda kuma wata mota Mai dauke tsani wato kwarangar da matafiyan zasu tako zuwa kasa Na finciki hannun Ammi Wai ta taho itama da sauri ta biyo Ni inda Kuma Naga kamar bata sauri don Haka na saki hannun ta na sheka aguje da nufin idan Daddyn ya fito in fada jikin shi na Rungume shi nayi mishi oyoyo shi Kuma ya sureni yayi sama Dani Yana cillawa sama. don gaskiya Ina son Daddy na fiye da ammi don shi Kam biye min Yake Kuma duk abinda nake so shima shi Yake so yayi wasa Dani yayi dariya in fada mishi damuwa ta yayi min magani akasin ammi da ta Fi bawa Yan uwa na maza kulawa musamman Yaya Abdullahi da kanena sulaiman muhimmanci fiye Dani Ni Kuma Daddy yafi bani muhimmanci abinda ban sani ba shine kaddarar farko kenan da Zan Soma dandan Akan harshena da idanuna da Kuma zuciya ta Akan Daddy na Mai bani kulawa Muna tsaye muna jiran a bude kofar jirgin don inyi ido Hudu da Daddy na koma in fada jikin shi muji dumin ya da mahaifi da nafi kowa muradin hakan Kofar jirgin ta bude inda na Fara ganin aminin Daddyn ya Fara fitowa fuskar shi Babu sassauci kafin wani mutum ya biyo bayan shi sai Kuma wasu fuskoki da ban San su ba ban taba ganin su ba suka fito suka dauke da wani Abu Mai kamar gadon tura marasa lafiya wani Abu Wanda aka nade cikin farin yanki kwance Akan gadon kamar gawa........ Gabana naji yayi wata irin sarawa har naji kaina na neman daukar ciwo na juyo Ina kallon Amma wadda ta taho aguje tana bude fuskar Wanda ke kwance Akan gadon Nan fuskar was Zan gani? Daddy na ne babu Alamar motsi ko numfashi a tare dashi Kafin na tambayi aminin Daddyn wato Alh Mustafa abinda ke faruwa Akan Daddy na sai Jin kukan mahaifiyata ammi naji cikin wata murya da ban zaci Tata bace........... Littafin GARWASHI na kudine ga me son Jin cikakken labarin zai biya dari uku ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin GARWASHI daban yake da sauran labaran gidan iko kasance da shi don Jin yadda kaddara tayi Aikin ta Akan wadan Nan bayin Allah💃🏿 Kar ku Bari abar ku baya Gidan iko shine sunanan ke cewa saduwar ALHERI🥰 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 3//4 Hadiza Bara'u gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Godiya ga Ubangiji madaukakin sarki Mai iko Kan komai da kowa da yake aminta har komai ya zamo cikin falalar shi ta kasance kun fayakun Allah ka saka mu a cikin kun fayakun Dinka Duniya da lahira Gaisshe da haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria tare da girmamawa 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ..........Kukan da Naga Ammi nayi ne ya fahimtar Dani wani Al amari Mai girma ya faru ko Kuma Yana Shirin faruwa Wanda ban shirya ji ko gani ba bare daukar shi a zuciya ta. Har ga Allah ban kawo mutuwa Akan Daddy ba abinda kawai Rai na ya bani bashi da lafiya tuna hakan da nayi ma ya kara jefani a cikin Rudani da tashin hankali don ban bawa Daddy mutuwa a wannan lokacin ba sai yayi min Aure har Ya'ya na sai ya dauka Amma fa a yadda na tsara kenan ban San nayi daban da tsari na da tsarin Ubangiji ba. Wannan kaddarar itace ta zamo masomi ko nace mafari duk da Akwai wata dadaddiyar kaddarar da na baro muku ita a baya Akan Daddyn da ammi wadda itama zakuji sanadin kaddarar da ta hadasu Wanda haduwar ce kuma ta sake bada wata kalar kaddarar duk shi Ubangiji babu Ruwan shi idan zaiyi Abu ba don aso ko aki ba a mutu ko ayi Rayuwa shiyasa ma akace alkalamin kaddara zanen shi baya gogewa to hakan take Akan mu shiyasa muke ta biya kaddarar mu da Bakin mu muna kuka ko muna dariya...... Kukan da Ammi ke Rerawa cikin fita hayyaci da kalaman dake nuna mutum yaji dukan da mutuwa ke barwa Wanda tayiwa ta adi wato sambatun radadi na Soma jiyo abinda take fadawa Daddy...... "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un yau Ni Ina Zan saka kaina faruk me yasa kayi min Haka? Ina Alkawarin da kayi min na zaka zamo min Uwa Kuma Uba? Ga wa ka barni bayan kasan bani da kowa sai Allah sai Kuma Kai ba don na Rasa Ahali da dangi da Yan Uwa ba? Don Allah ka tashi Kar kace min ka tafi ka barni da yaran ka da Basu da gata sai Kai. Don Allah Umar ka tashi ka ci gaba da kasance wa farin ciki na kamar yadda kayi min alkawari kafi kowa sanin bani kowa sai Kai Yan uwan ka zasu samu damar keta Ni . Iyayena zasu kasheni in suka tabbatar babu Kai a Duniya kayi min Rai kayi min gata Kar a tarwatsa min farin ciki don Allah ka tashi faruk kace min baka mutu ba kana Raye Yadda take jijjiga gawar mijin nata ne ya sake fahimtar Dani lallai munzo gabar da wasu mutanen suke so muzo don su wulakanta mu musamman Ammi da Yan uwan Daddy basu kaunar ta don kawai ta kasance ahalul kitabi kafin Auren Daddyn shikenan suka Dora Mata kahon zuka sai gashi yanzu Daddyn da ya zamo Mata garkuwa yau Babu shi duk da ban San komai Akan abinda zuciyar ammi ta kunsa ba Zan iya cewa zafi biyu takeji a yanzu Zafin Rasa mijin da yayi Mata gata da Kuma zullumin abinda zai biyo bayan mutuwar mijin nata daga bangaren Yan uwan shi Tunda na tsinci kalmar mutuwar Daddyn a harshen ammi nake Taya ta kukan Rashi ko nace nake Taya ta tausayawa kanmu don nice nayi Rashi tayani kawai takeyi Mun cika filin jirgin da kukan mu Ni da Amma kafin aminin Daddyn wato Alh Mustafa ya katse ammi da wata tsawa Yana zare Mata idanu abinda yayi matukar Bata mamaki don ta hango wani Abu Mai Kama da tsanar ta fal idon shi abinda Bai taba nuna Mata a lokacin Rayuwar mijin ta ba akasin zolaya da kambama ta wurin iya kula da abokin shi....... "Ke da Allah saurara Mana Haka Nan tsiyar tubabbu kenan ko zasuyi shekarun Annabi huhu a cikin musulunci sai sun nuna maka asalin su da jinin jikin su mu a addinin mu na musulunci kukan mutuwa haramun ne kar ki sake daga Mana murya anan ja daga baya ki Kuma matso da mota mu saka shi mu wuce gida dubi da Allah yadda Kika Tara Mana mutane sai kace akanki aka Soma Rasa miji Ni da ammi muka bishi da jajayen idanun mu cikin wani madaukakin mamaki kafin jiki a sanyaye ammi ta Mika mishi key din tana fadin Bata da nutsuwar iya tuki don Haka sai ya amsa ya matso da motar aka sako gawar mahaifina muka shigo mota ya tuko shi da wannan mutum da bamu San ko waye ba muka nufo gida muna sake sabunta kukan mu A falo aka shimfide gawar Daddy inda Alh Mustafa ya cewa ammi ta buga waya can kauyen su Daddy ta sanar dasu Jiki na kyarma tare da bugun zuciya ta Soma neman layin yayar mahaifina wato Yaya Badura cikin sa a Kuma ta sameta Amma sai da tayi Ringing sau biyar kafin Yaya Badura ta daga tana fadin "Waye? Ammi taji wani sabon kuka ya kwace Mata tace "Yaya Badura nice Aminatu........ "Na Gane muryar ai meye Kuma kike min shaken hanci (kuka)? Ammi ta Kara saka kuka tana fadin "Faruk ne Yaya Badura don Allah kuzo kuce mishi ya tashi Kar ya tafi ya barni bani da gata sai Allah sai Kuma shi......... "Ke aniyar ki ta biki yar arnan dawa fatan da kike mishi kenan ya tafi ya bar Miki dukiya ko? To ki kwana da Shirin ciwon Kai idan ya samu ummaru na Rantse Miki sai kin bar Duniyar Nan bakar kaddara kawai. Kukan ammi ya Kara tsanani saboda Jin masifar da Badura ke Mata ita Kam Tata ta sameta Badura tana sabe da wayar a kunnen ta tana sauraren kukan Ammi Bata kashe ba sai da ta tsinto muryar Alh Mustafa Yana waya Yana fadin Alh faruk ne Allah yayiwa Rasuwa sai kawai Badura ta kwantsama uban ihu inda mutanen gidan suka taru kanta tana fadin matar ummaru ce ta kirata tana kuka Kuma taji ana fadar ummaru ne Allah yayiwa Rasuwa. Kan kace me ? Sai gasu kwai da kwarkwata sun ciko mota mazan su da Matan su Yara da manya sunyi dirar mikiya agidan Abu ga jahilcin kauye sai gidan ya amsa sunan shi wato gidan makoki don kewaye gawar sukayi suna ta gurzar kuka har da masu tashin aljanu wato Yaya Badura Wai ta Rasa Dan uwa me kaunar ta da daukar takalifin ta Ahaka aka shirya Daddy akayi mishi sutura aka yi nufin sada shi da makwancin sa har aka bukaci ammi tazo tayi mishi sallamar bankwana. Ta kuma taho idonta na zubar HAWAYE ta sunkuya tana mishi ADDU AR samun kyakkyawan makwanci da samun Rabon Duniya da tana Kuma fatan can tafiye mishi wannan kuntatacciyar Duniyar marar mutane masu Adalci Adalcin da suke kasa yiwa kawunan su bare suyiwa wani..... Kawai sai ji tayi an finciko ta an cillo waje Ta dago idonta tana Kuma Jin zafin hannunta da ya bugu da Bakin kofar ta kalli yagana sai bude manyan hantunan ta takeyi Wai afusace take "Uban me Kika sani acikin musulunci da musulmai da har kike wani mimi mi da Baki ADDU A kike son nuna Mana kin iya ne? Ai Baku gada ba bare kiyi abin kuzo mugani tuban Taki ta muzuru tuban ganin abin Duniya? Da Allah fice anan Kar kisa ayi mishi azaba akan tsayuwar ki Akan shi kayan kazanta dake iyalan oduduwa da fafaroma Jin abinda ya kumbo na yagana ke fada tana tada murya yasa na kamo ammi dake HAWAYE muka fito yagana na Rako mu da wani matsiyacin tsaki Sallamar bankwana da banyi da mahaifina ba sai dai na Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa don lokacin da Naga an fito da mankarar dake dauke da gawar shi ban sake sanin abinda yayi kantafi da Rai na da nutsuwa ta ba sai dai farkowa nayi naganni a Kan cinyar ammi tana shafawa fuskata Ruwa na kumayi nasarar ganin fuskar ta da ta kumbure saboda kuka Kuma har yanzu idaniyar ta Bata kafe da zubar Ruwan HAWAYE ba............. Wannan labarin na kudine ga Mai son cikakken labarin zai biya 300 ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin GARWASHI daban yake da sauran littatafan gidan iko Kar ku Bari abaku labari Gidan iko sunan ke muku fatan ALHERI🥰💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 5//6 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Har kullum godiya ga Ubangiji ta zamo Dole Akan yadda ya sauwake Al amura masu yawa agareni Allah ka Kara dubun dubatar salati ga shugaban halitta Wanda nake fatoh shiga cikin ceton shu Ranar alkiyama Masoyan Rubutun Gidan iko babu yadda Za ayi na manta ku kun Kai har kun wuce a gareni ba don na iya ba kuke yabawa tare da ADDU AR fatan ALHERI gareni har da iyayena ko nayi nufin aje alkalamin don bawa kwanya da zuciya hutu sai naji fatan ALHERIN ku nake bukata sai na girgije na Soma sabon typing🥰 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ..........Zaman makokin mahaifina shima wata makaranta ce guda da za a dauki Darasi Kuma irin Darasin Nan da Duniya ce kadai Kan koyar da irin shi Amma ba Wai mutane irin dangin mahaifina ba Zaman makokin ya kasu Kashi biyu NE a cikin gida yayin da akeyin guda Daya a waje wurin mazan... Ko dayake can din ma biyu NE akeyi inda dangin mahaifina suka kafa majalisar su ta Yan uwa Kuma dangi yayin da Alh Mustafa ma shi da jama ar da suka San shi da marigayin mahaifina da mu amalar su suna kammale wurin Alh Mustafa inda Kuma su kawu madu da kawu gide suke tasu majalisar ta Yan uwan Daddyn in sunzo wurin su suke sauka kamar yadda a Nan ma cikin gida zaman ya kasu Kashi biyu . Su Yaya Badura da yagana suna falon Daddyn inda yagana ce tazo ta ce da ammi ta Bata key din dakin Dan uwan ta Bata Kuma ja ba ta Bata sai dai da Yake Kan nasu babu komai sai handama da babakere babu Arabi ba Boko sai hadama da son Azurta Kai yasa basu waye da komai na maraya ba kasancewar ko acan garin nasu na Maiduguri kauye ne sosai shiyasa ma da yagana ta karbi makullin ta kasa bude uwar dakin Daddyn sai suka tare a falon yayin da ammi ke falon dakin ta Kuma makotan tane Wanda suke gaisuwar mutunci tare da ita musamman mama da suke ga gida ga gida Kuma ta mayar da ammi yarta saboda ko shawara da ita ammi keyi shiyasa take tare da ita Kuma mutanen unguwa ma duk da kasancewar unguwar ta G R A ce irin Rayuwar kowa tashi ta fissheshi ake ba Ruwan kowa da kowa yasa dai daiku sukan gaisa ayi barka ko gaisuwa inda can Kuma wurin su Badura duk Wanda zaizo daga Maiduguri Kai tsaye wurin su yake yada zango Ranar farko ta mutuwar Badura da yagana ne a cikin kichen suna faman dorawa da saukewa na abinci Wanda yagana ta karbo Dan makullin store Wanda ke shake da kayan abinci suka SHIGA sabgar gaban su na gurkawa da Rabawa Amma ko cokali guda ammi Bata gani da idon ta ba bare ayi Mata karar miko Mata ita da jama ar da suke zaune sai fa mama ce ta saka yarta ta dafo wake da shinkafa aka kawo Nan ammi da sulaiman don ni dai Kam ban zaci ko da dimuwa Ruwa ya ratsa makoshi na ba bare abunci Wanda su yagana ke faman hadidiya Sai bayan Isha I ne kawu madu da kawu gide suka nado tabarmin suka shigo ciki inda kawu gide ya Soma bude fridge din dake kicin yayi Arba da Naman kaji da na shanu ya kuwa kwalawa yagana Kira ta karaso inda ya Rufe ta da masifa Wai ga nama cike da na ura Amma tayi musu abinci babu nama? Ta ke ya Bata umurnin yi mishi farfesun Naman saniya a take Kuma yagana ta hau aikin dahuwar Naman Haka kawu gide yayi ta zaga gidan Kuma duk abinda ya gani sai ya bude ko Kuma ya nemi sani har yagana ta gama hada farfesun yace yaga fridge a kofar falon ammi taje ta duba in lemu ne ta kwaso musu Haka suka baje tamkar wadan da suka Zo dinner ba mutuwa ba Ammi dai tana kallon su inda mama ta kula da take taken Yan Daddy din dama ta San komai sai ta bawa ammi shawarar Kar ta sake tace zata tanka musu duk irin abinda kuwa zasuyi Kar tace musu ko uffan tunda dai Ya'yan ta uku ne Kuma babu Yan uba bare a nemi tada Mata hankali da wani Rabon GADO in aka Gama sadaka dai dolen su su tafi su barta da Ya'yan ta ammi kuwa ta amsa da to Kowa ya watse saboda Dare aka barmu yamu yamu inda ammi tayi nufin budewa su kawu gide bos kwata don su kwanta Amma sai lamarin ya juye tamkar bakar magana ta fada musu yagana da Badura suka ce Ina wuta su jefa ta duk suma kawu madu da giden ba mutunci ne dasu ba Wai su da gidan Dan uwan su har sai ta nuna musu iko? To ba kwartanci sukazo ba don su ko Matan Duniya sun Kare sai ita to zasu hakura da mata bare tayi tunanin zasu iya duban ta a mace bare wani Abu da dan uwan su Yake ganin ta burgeshi shima kahuwa tasa shi Auren ta da ya biye tasu to da ya barta ta Rayu da irin jinsin ta iyalan oduduwa da fafaroma cewar yagana kenan wadda ta zarta su kiyayyar ammi Tun daga Ranar ammi Bata Kuma SHIGA hurumin su kawu da Yaya Badura ba iyakar dasu gaisuwa shima ba amsawa suke ba in ma sun amsa to zaka samu idon wani ne a wurin shima sai sun bita d kallon wulakanci Sai da akayi kwana bakwai kafin Alh Mustafa ya Tara mu mu duka Ni da ammi da sulaiman yayin da Yaya Abdullahi yake can Egypt Yana karatu Kuma har yanzu Bai San abinda ke faruwa ba don ammi tace cikin jarabawa yake ba zata sanar dashi ba Kuma mama ma haka tace Kar a fada mishi don Haka Babu shi a cikin taron da aminin Daddyn yayi Mana wato Alh Mustafa da Kuma kawu madu da giden da Badura da yagana "Dama na Tara ku ne don na sanar daku wani Abu da Baku sani ba in Kuma saukewa Umar wani nauyi dake kanshi saboda babu wani nauyi Akan mamaci me hadari irin bashi ba Kuma bashin komai ne Akan shi sai bashi da nake binshi na kudi har million goma Sha biyar don Haka idan an nutsu sai a biyani kudina don Kar su SHIGA cikin gadon Yara ! Ni da kaina da Yan kananun shekaru na nasan mahaifina shike bin Alh Mustafa kudi na Wanda ya ambata wato million Sha biyar Amma a yau da kasa ta shafe ji da ganin Daddyn sai gashi Yana fadin shi ke bin Daddyn alhalin shike taimakar shi a ko yaushe Kuma ko ina..... Ban Kai karshen tunani na ba naji ammi ta dauki kabbara tana fadin . "Ko ka manta ne Alh Mustafa sake tunawa kamar dai shine yake binka wannan kudin ai ka manta a gabana akayi hakan ? Fadin Haka da ammi tayi Ina wuta ya jefa ta .... "Kina nufin sharri nayi mishi kenan bana binshi zanzo nace Ina binshi? Kina Ina lokacin da na biyashi wancan kudin da kike neman kala min sharri?.......... Kawu gide ya Soma bawa Alh Mustafa hakuri Yana kwantar da Kai da Rarrashi. "Rabu da ita Alh waye Bai San tsakanin ku da ummaru ba ? Dole ne ma duk abinda ke tsakanin ku sai ta sani? Ko Ni ai nasan da wannan bashin don ya fada min Ni nayi zaton ma sun Kai million ashirin Ammi tayi murmushin Alh Mustafa na fadin ai ya bashi million biyar ne shiyasa suka koma Sha biyar....... Kar ka damu Mustafa ai yanzu ma za ayi ta takare don duk wani Abu da Yake mallakin unmaru ne yanzu zata fiddo shi ta bamu a fitar maka da kudin ka saura kuwa a mu wuce dasu mu ajewa Yara ya Rage nata ta bar yaran hannun mu Ruwan ta ne Kuma ta komawa arnan iyayen ta dasu duk Daya Wai anyiwa tuwo barin Mai Amma dukiya Kam yau zamu karbe komai ku tafi da ita Haka ammi ta kwaso kaf wasu kaddarori da tasan mallakin marigayi ne ta zube Agaban su Abu Daya take Jin ba zata yarda ba shine su karbe Mata Ya'ya Amma dukiya bakuwa ce Kuma Arzikin Ya'yan ta ba GADO kawai Yake ba Yana can a tsakar Allah Gaba Daya suka dauki hayaniya Wai ba iyakar abinda ummaru ya mallaka ba kenan ta boye wasu abubuwan Kuma sai ta fiddo su. Ammi ta Rantse Bakin Ranta Amma Basu yarda ba hatta sarkokin zinariyar ta sai da yagana ta kwaso Haka suka shiga kasafin son zuciya aka Fara sallamar Alh Mustafa da kaddarorin da yayiwa siyen son Rai a matsayin kudin shi yayi musu sallama ya wuce ya barsu da kasafi Abin mamaki da nuna tsantsar jahilci shine yadda sukayi kason na maza biyu mace Daya Amma babu tumunin takaba ga ammi sai uwa da Uba da suka Dade da Rasuwa Amma su an fitar musu da nasu kason duk da suna kasa🤔 Wai tumunin takaba sangarta mace ne Banda Alfarmar da akayi mata a cida ita a cida Ya'yan ta ga Kuma gadon su sai Kuma anyi wats bita da Killin Bata wani Abu alhalin ga Wanda sukayi silar zuwan shi Duniya ko sun faku ai akwai magadan su Ammi dai Bata CE musu ko uffan ba suka Gama kasafin su sukayi haramar tafiya gida inda suka jide abincin dake store suka Kuma kwashe suturun marigayin da duk wani Abu dake cikin dakin shi sai da suka jide shi kaf hatta kujeru da gadon dake dakin shi da TV sai da su Badura suka kwashe komai kafin suka fice zuwa gida inda Kuma Ni da ammi mutuwar ta da wo Mana sabuwa mukayi ta kuka lallai Wanda Bai hadu da Rashi irin namu ba lallai Bai San bakin cikin dake dukan zukata ba musamman dangi irin namu marasa tausayin Kai da tausayawa wani. Tun daga wannan Rana muka Soma karbar kaddarori mabanbanta Wanda karfin imani ne kurum ya Hana mu hadiyar zuciya. Tun daga wannan Rana na Soma mafarkin ido nayi bankwana da duk wata daula da Jin Dadi da na Budi ido acikin ta nayi bankwana da burin fita waje karatu kamar yadda Dan uwana Yaya Abdullahi yayi. Nayi bankwana da gayu irin na Yar gata nayi bankwana da cima irin wadda uba me so da kauna yakewa Ya'yan shi tattali natyi bankwana da suturu na kawa da yayi Wanda mafi yawan mutane suke Fara gani ajikina. Nayi bankwana da ...da...da ... Bankwana da abubuwa masu yawa na Kuma sauya daga wata Fatima Zahra ta da can a wani Dan TAKAITACCEN zamani da tarihin sa bashi da tsayi zuwa wata Rayuwa ta da ban wadda ta fahimtar Dani kasuwar da kaddarori sukayi a Duniya. Ba don na Isa hakurin ba ba Kuma don na iya ba sai don tilas na iya jurewa Amma idan abubuwa suka isheni sai na Rufe kaina a daki nayi kuka na ma ishi na share HAWAYE kafin nace "Ashe dai mutuwa itace Mai tona Asiri? Watan Daddyn mu biyu da Rasuwa Yaya Abdullahi ya samu hutu ya Kuma taho ba tare da ya sanar damu zuwan shi ba don duk lokacin da sukayi waya da ammi yakan yawaita tambayar ta Wai Ina Daddy ne baya kiranshi Kuma layin shi baya tafiya Amma ammi Bata bashi amsa sai dai ta shashantar da tambayar tashi shi kuma ya taho ba tare da ya sanar ba sai ganin shi mukayi kamar daga sama ganin shi ya sake dawo min da mutuwar sabuwa don nasan a yau abinda ammi take boye mishi zai fito fili fitowar da zamu sake jajantawa kanmu mu Kuma tausayawa kanmu.......... Littafin GARWASHI na kudine ga Mai son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN akan wannan layin 08035191669 Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari a Baku labari gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI🥰 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 7//8 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Littatafan Gidan iko Jan kunne Wuka a makoshi Zan fasa kwai Sai A lahira Mugun kulli Matar sarki Dukkan su zaku iya samun su a kasuwa saboda published ne Dole na gaishe da masoyan Rubutun Gidan iko musamman masu ADDU A da fatan ALHERI Ubangiji ya fini yabawa Sai haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria a ko yaushe Kuma ko Ina ALHERI 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 .........Jikin ammi yayi matukar sanyi ganin Yaya Abdullahi ba sanarwa . Ni kuwa kuka na ne ya bayyana mishi wani Abu ya faru ko Kuma zai faru. Ina durkushe Agaban shi Ina faman Rera kuka na kasa dago Kai na dubeshi kamar yadda ya kasa Rarrashi na ya kuma kasa tambaya ta ba asin kukana. Ammi ta zuba Mana ido tana Raba Mana kallo itama ta kasa tsayar da nata HAWAYE Sulaiman ne yake fasawa Yaya Abdullahi Rasuwar Daddyn Kan shi tsaye Kuma ya fadin hakan saboda kuruciya Kuma shi tunda yayi kuka lokacin da za a fitar da gawar Daddy Bai Kuma sai dai ya kalle mu munayi Ni da Amma har wani lokacin nake tambayar kaina juriya ce ga sulaiman koko kuruciya? Sai na Gane jaruman Duniya sune Wanda basa taba Barin damuwa ta kassara musu farin ciki ta hanyar nuna komai ba komai bane . Sune Kuma Basu yarda damuwa ta kawo musu cikas ko tazgaro ba don suna ganin abinda ya faru ya faru babu Kuma me iya dawo da bara ta dawo bana in ba Allah ba sai su murje komai ya Zama ba komai ba su fuskanci abinda ke gaban su manta da wani tabo da kaddara ta kawo musu in ma kaga sun tuna to sun waiga baya ne don hango wani abun ba wancan ba sai yayi clation da shi Duk juriyar da nasan Yaya Abdullahi da ita da jarumta irin ta maza Amma kukan da yakeyi Ni kaina sai da na tausaya mishi domin ko kalaman da Yake fada ne Dole su saka Mai imani zubar HAWAYE mussamman da na tuna burin mahaifin mu Bai wuce ya inganta Rayuwar mu da ilimin da zamu zamo abin alfahari ba mu Kuma zamo ya fita hakkin mu da kowane irin gata da gatantawa "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Yake ta maimaitawa Yana fadin "Shikenan Rayuwa ta juya Mana baya burina na son karatu ya Rushe duk yadda nake son karatun Nan Dole Zan barshi "Shikenan SHIGA UKU ta samemu ammi Ina tausayin kaina Ina tausaya Miki. Maganganun da Yake fada ne ya tabbatar min da lallai baya cikin hayyacin shi domin ko sambatu yake tayi Kuma Ni da ammi an kasa samun Wanda zai Mika mishi wata kalmar da ta danganci hakuri ko Rarrashi Duk juriyar sulaiman sai da ya Rungume Yaya Abdullahi Yana Taya shi kuka Koko tausayin shi ne ya Kama shi oho Bai tsinke ba sai da yaji abinda Alh Mustafa da Yan uwan mahaifin mu sukayi na karbe duk kaddarorin Daddyn. Ya kasa tankawa ammi akan wannan Rashin mutuncin kamar yadda ya kasa tsayar da hawayen shi. Tun daga wannan Rana sai Rayuwa tayi Mana wani irin sauyi me yawa sauyin da yazo da kaddarori kala kala domin ko Yaya Abdullahi Bai samu zarafin komawa Egypt ba Domin ko kudin da ake biya mishi ba kadan bane Dole ma karatun ya tsaya ya dawo gida ya zauna muke Rungume da hannuwa in da muka tsira da gidan da muke ciki da Kuma motocin da Daddy Yake Hawa har guda uku sai ta ammi guda Daya don haka ammi ta taramu nida Yaya Abdullahi take fada Mana cewa zata siyar da Tata motar ta nemi wani kasuwanci ta Rika yi saboda mu samu na cin abinci inda Kuma yaya Abdullahi ya kawo shawarar a siyar da duka motocin sai a siyi babbar mota wadda zata Rika yin sufuri ana bamu kudin muna yin lalurar mu. Ammi tace A a Kar a siyar da na Daddyn Wai hakkin mune Kar suzo su shige a banza Amma Tata ko ta shige a wurin hidimta Mana batajin komai Akasin ace gadon da mahaifin mu ya bar Mana ya salwance bamu Mori komai ba don ta San cewa abinda su kawu madu suka karbe da sunan Adana Mana sun dai fada ne kawai Amma ba adanawar zasuyi ba Abdullahi ya tambayi Ammi har da kudin Daddyn na account din banki duk sun kwace? Tace har fa abincin dake store Basu Bari ba sun Jude Kai sururun shi ma da komai na dakin shi Basu Bari ba sun kwashe Wanda Bai bar wannan ba yaushe zai iya Rike Amanar maraya? Ni dai Nagode wa Allah na Kuma godewa uban ku da yayi silar kawo Ni cikin hasken musulunci ba Kuma Zan butulcewa Ubangiji ba don wasu daga cikin bayin shi suna goranta min Ni din tuba nayi . Na yarda na Kuma Amince da musulunci shine karbabben addini wurin Allah na Kuma gode da ya Azurta Ni da samun ku a cikin musulunci sai dai Yan uwan uban ku da suke zagina da aibata Ni Akan tuba na Kuma ko su zanyi musu uzurin jahilci don aganina irin karbar da Dan uwan su yayi min irin ta ya kamata ace sunyi min kasancewar shi musulmi Dan uwan musulmi ne sai suka nuna min har abada shi Wanda ba musulmi ba in ya shigo cikin musulmi bashi da muhalli sai gori sai kyara da hantara. To babu komai in ma sunce ba zasu karbe ku a matsayin Ya'yan Dan uwan su ba Ni ina son ku tunda Kuma na hakura da Yan uwana da iyayena da gatana na baiwa komai da kowa baya Suma Zan iya Barin su tunda nayi Ruko da igiyar Ubangiji nasan ba zata tsinke ba sai mu Riki Allah Ni da ku nasan ya ishemu a ko ina Kuma ko yaushe Mun Sha kuka da Jin wannan magana ta ammi Domin ko Bata taba fada Mana wani Abu da ya girgiza zukatan mu kwatankwacin irin wannan ba inda Kuma muka hakikance lalli Wanda yayi Rashi irin namu shine ya San dacin da ke akwai cikin Duniya Kuma Wanda Bai Rasa Uwa ko Uba ba hakika Bai San wani bakin ciki Mai yawa ba Rayuwa tayi Mana sauyi hatta da irin cimar da muka Saba da ita ta sauya sabulun wanka ma ya sauya daga porrin zuwa Dan gida Nigeria. Makwanci ya sauya sutura ta sauya a komai mun samu sauyi kamar yadda sauyin Rashin Daddyn ya same mu Haka sauyin komai ya nuna kanshi a garemu Tuni aka siyar da motar ammi aka siyi karamar motar gwalp wadda kuma ta Rasa Wanda zata dankawa Amanar ta don ba kowa ta sani ba inda ta tuntubi mama ko za a cigita Wanda zai karba yayi Mata sufuri ita Kuma mama tace zatayiwa mijin ta magana ya samo Mai Amana. Yaya Abdullahi yacewa ammi shi zai Rika Jan motar Yana zuwa Kano kaduna da sauran Yan garuruwan da ke kusa Wanda zai iya Amma Ammi tace Bata yarda ba don ba sabawa yayi ba Kuma ma Bata yarda ba wahala ce tukin mota . Duk nacin da yayi ya Kuma nuna Mata duk Wanda za a samo ba zai Kai ya shi ba Amma Ammi tace Bata yarda ba gara ta bude mishi shago ta zuba mishi Yan kayan treda ya zauna anan seet room din Daddy Wanda kofar shi ke kofar gidan Haka Kuma akayi Yan sauran kudin da ta Rage na ragowar kudin motar ta su ta zubawa Yaya Abdullahi kayan treda Kuma cikin ikon Allah Asirin mu ya Rufu a ciki muke samun na hidimar gida har ma ayi Mana hidimar karatun mu Ni da sulaiman dake makarantar kayalwa dake kofar durbi Ni Kuma Ina makarantar scondry ta government college Yar kutungu Muna ta Rayuwa a Haka cikin ikon Ubangiji da kallon komai Akan idanun mu da zukatan mu da Kuma godewa Allah a ko yaushe Kuma kowane irin hali da Kuma Mika hannu mu karbi ko wace irin kaddara kaddarar ta Miko Mana zamu karba mu Kuma godewa Allah tare da neman sauki acikin kaddarar da kaddara ta Miko Mana Wata hudu da kwana goma da Rasuwar Daddyn mu ta fita takaba inda lissafin hakan da Kuma kwanakin mahaifina a kasa Bai taba kubce min ba a kullum dai nayi alkawarin Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa wadda na tabbatar ita kadai ce gatan da zanyi mishi shigen Wanda yayi min Na dawo makaranta kenan na Tara's da ammi tayi wanka tayi Yar kwalliyar ta kadaran kadahan cikin wata atamfa me saukin farashi wadda mama ce ta siya Mata ita ta kumayi lalle abinda ta Dade batayi ba tunda Daddyn mu ya kwanta Dama tayi sallama da ko Mai Mai kamshi bare lalle sai dai Kuma duk da wannan Yar kwalliya da tayi maimakon Naga tana murna sai na Tara's tana kuka abinda ba sai an fada min ba tuno Daddy ne yasa ta kuka Ta tusa aya da gyadar da ta soya zata Rabawa makota Amma sai Kuma take inda ta karya zuciya ta Nima sai na soke kaina cikin cinyoyi na Ina tuno Daddy da Kuma kalubalen da Rashin sa ya bar Mana wanda shi Allah baya barin wani don wani yaji Dadi. Lallai da Ubangiji na barin wani don wani yaji Dadi to da lallai muna daga cikin wadan da ba zasu taba zubar da HAWAYE don bakin ciki ba sai dai kukan Dadi irin na Ya'yan gata Domin kuwa na tabbatar Daddy zaiyi iyakar kokarin shi don ganin bamuyi kuka don Bakin ciki ba sai dai kukan Dadi Haka Ammi ta bawa zuciyar ta hakuri Nima na bawa tawa muka share hawayen mu ta kulla ayar da gyadar ta bani na Rabawa makota gida gida har wasun su sukan Aiko Mata da Yan kudi Wai sadaka ce wasu Kuma abinci danye sai gashi ta samu kudi masu yawa da abinci .washe gari sai ga Yan uwan Daddy su kawu gide da yagana da kawu madu sun diro gidan suna zare idanu Alamar dai Rashin mutunci ne ya kawo su............. Labarin GARWASHI na kudine ga Mai son cikakken labarin zai biya 300 ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Salon labarin daban yake da sauran Kar ku sake ayi Babu ku bare abaku labari Gidan iko ne sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 9//10 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Har kullum Godiyar ta tuke ga Ubangiji Mai ikon kowa da komai da Yake nufar bayi da abinda Yake so su zamo ko su kasance aciki ne ya nufeni da alkalami Wanda Ni kaina ban San yadda akayi hakan ba salati da Aminci ga shugaban halitta S A W Allah ka Kara wasila da fadila agareshi da Ahalin gidan sa da masu biye dasu da kyautatawa ADDU OIN fatan ALHERI ga mahaifina da mahaifiya ta fatan Rahama fatan Dacewa fatan samun babban Rabo a Nan Duniya da can lahira 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ...........Na zube Agaban su kawu gide da kawu madu da Kuma ya kumbo yagana Ina gaishe su yayin da ammi ke kokarin shimfida musu tabarma tare da kawo musu Ruwan sanyi ta Kuma ce na kirawo Yaya Abdullahi yazo ya gaishe da su kawu madu Duk wannan abin da ammi ke musu cikin kallon banza suke binta Haka Kuma Babu Wanda ya amsa gaisuwar ta bare ya kalli Ruwan da ta aje musu Muka shigo Ni da Yaya Abdullahi ya zube Yana gaishe su suka amsa mishi cikin sakin fuska da Fara a har suna mishi gaisuwar Daddyn abinda ya bani mamaki sosai ko da Yake shi Yaya Abdullahi yayi sa a su kawu gide suna son shi kamar ba Dan ammi bane da suke saukewa kwandon tijara Kuma bayan Haka ma sunfi tsana ta fiye da sulaiman Wanda Bai tako sa ar da Yaya Abdullahi ya tako ba Yaya Abdullahi Yana sunkuye Agaban su kawu madu Wanda ke fadin abinda ya kawo su Wai kaf dukiyar da mahaifin mu Yake ciki Yake juyawa gadon da iyayen su suka mutu suka bar musu ce shi Kuma saboda shine Mai nasibin siye da siyarwa sai Yaya Badura tace abar mishi ita ya juya tunda abin duk na gida ne in yaso idan ta yadu tayi harshe sai a fidda kowa to akan hakan ake sai Kuma ga Ajali ya Riske shi ya mutu da nauyin dukiyar su don Haka suka Zo don a sake lissafi da dai sunyi hakuri sun barwa marayu to Amma daga baya da suka tuna da gidan Nan da Kuma motocin marigayin shine suka Zo karbar hakkin su dama su shi Abdullahin ne suke so suyi magana dashi saboda shine namiji Kuma Dan su don ta ammi ba ta isa suyi wannan maganar da ita ba. Mu duka mukayi Duff tamkar babu kowa a wurin Yaya Abdullahi ne ya dubi Ammi yake cewa "Ammi kinji abinda sukace....... "Ubanwa yace ka sako Mana ita? Cewar kawu gide "Harkar Wanda suka shafi musulmi ne ba harkar Yan lahadi ba kaima abinda yasa muka sako ka don Dole za a kiraka jinin mu Kuma ba Wai shawarar ka muke nema ba Kar kace zaka wani daga Mana hanci Umarni ne ba shawara ba Bari kaji abinda muka Zo dashi Ya dubi kawu madu Yana fidin "Munzo ne mu debe ku mu wuce daku can maiduguri ita Kuma wacan kayan banzan mu sallame ta ta komawa kafuran iyayen ta dama mu bama maraba da shigowar ta cikin Ahalin mu sunan ku dai uban ku ya gama Bata muku shi tunda ya gama jinin ku da ahalul kitabi mu kuwa yaya zamuyi da ku tunda mahaifa ta hado mu dashi muma sai dai mu kalli Allah kawai Amma in Banda zumuncin Allah yaushe irin haka zata faru har ka kalli Ahalin mutum ? Gabana naji yayi wata faduwa Jin abinda kawu gide yake fada ba Wai komawar mu kauyen ne takaici na ba a a tadda Yake aibata uwata wadda ta zabi shigowa cikin su don an kwadaitar da ita hasken musulunci Amma su da suke musumai sune suke tozartata tamkar dai ace Ridda tayi daga musulunci ta koma inda ta fito wato addinin ta na kirista Agaskiya idan dai har zai zamo mutanen dake amsa sunan musulunci irin dangin mahaifina ne to na tabbatar da duk Wanda ya shigo cikin musulunci da gudun shi zai fice ya bar addinin duk yadda yake son shi kuwa saboda Rashin nagartar wadan da ke amsa sunan musulunci har ma yayi zaton abinda yaji ko ya gani Akan musuluncin ba Haka bane yaudara ce Ammi da tunda taji abinda suka fada ta Fara kuka da iyakacin karfin ta don ta San Bata da karfin fada dasu Kuma in har aka Raba ta damu to ta gama SHIGA UKU don Haka ta dire duka gwiyawun ta akasa tana kuka ta hade hannuwan ta wuri Daya Alamar Roko akan kar su Rabata da Yayanta ita ta yarda in ma gidan ke Basu so su ganta ciki zata tashi Kuma zata bar musu Amma don Allah Kar su Raba ta Ya'yan ta Kukan da ammi keyi yayi masifar kada hantar cikina har naji koma me za ayi ba Zan taba barin a Raba mu da ammi ba don da iyakar gaskiyar ta take kuka tana Rokon su fuskar ta ta baci da Ruwan HAWAYE sai ahi take musu da Roko Amma babu Wanda ya kulata sai ma harara da suke jifarta da ita tamkar idanun su zasu zubo kasa........ "Mun fa gama magana babu wani tsari da Zaki kawo Mana baccin da muke tsoron bar Miki Ya'yan don kar ki mayar dasu kafurai ai da har su zamu bar Miki ki koma can Legos ki mayar dasu kafurai duk matsalar kuce ba tamu ba. Cewar yagana Yaya Abdullahi yayi magana cikin wani sanyi Wanda ke nuna cikin firgici yake firgicin da na tabbatar na ganin Ammi a wannan halin ne "Kuyi hakuri kawu da dai Ni kukace na dawo Maiduguri ne to da zanyi alfahari da hakan Amma Zahra da sulaiman idan aka maida su can gaskiya inajin Ni kaina banyiwa kaina Adalci ba Kuma ma na lura Ammi Bata son Rabuwa da su don Allah ku bar maganar Raba ta dasu .......... "Kai fita idona na Rufe kaji in ka kuskure na Rufe idona kana ciki akwai matsala mun Gama magana ba shawarar ku muke jira ba....... "Wai shima Nan haka da shi ya iya iya shege? Cewar kawu gide da ya tari nunmfashin madu..... "To ai matsalar gwamutsa jini kenan ka dai gani sai kace wasu tsararrakin shi muna magana yana mayarwa bafa kunya garesu ba musamman waccan me idanun uwa anyi barin kwai a titi kawu gide ya fada Yana Nuna ni...... "To yaushe zasuyi kunya dama uwar su Bata wanye da banbance Haram da halak ba? Bata wanye da tsarki da kafurci ba? Cewar yagana Haka suka ci gaba da cin mutuncin mu da cin fuska tas suka yage fuskokin mu kafin suka bukaci mu tashi mu gado kayan mu mu wuce Maiduguri inda Kuma tashin hankalin ammi ya karu tayi ta kuka me sauti tana Kara Rokon su da suyiwa Allah da ANNABI su bar Mata mu Amma kamar ba Allah take Rokon su ba inda Kuma yaya Abdullahi ya Gane ba irin su kawu gide akeyiwa kawaici ba don Haka ya fada musu gaskiya ba zamu bisu Maiduguri ba tunda Ammi Bata so...... "Kai kace me? Kawu gide ya fada Yana zaro kwala kwalan idanun shi Ya kuwa sake maimaita mishi abinda ya fada na ba zamu bisu Maiduguri ba........ "Karya kakeyi Wallahi uban ka ma Bai Isa na yanke hukunci ya Musa min ba bare Kai kayan banzan da Bai Kai na wofi ba ko Kuna so ko Baku so gaku can kunje Maiduguri ubanku ma da can yake tutiya da alfahari. Ya fizgo hannun sulaiman dake kankame da ammi kafin Jin ana Shirin Raba su nima Kuma yagana ta finciko hannuna ta Rike Alamar dai da gaske suke Shirin tafiya damu....... "A a ku sake su ai daukar duka hutawa tunda Haka suka shirya su da Uwar su ai bayan tiyar akwai wata cacar tunda ba zasu biyo mu ba ai mu bar su dama don kar a zagemu ne ace saboda kasa ta Rufe idon unmaru ne muka yada su kasan mutane ba iya musu ake ba yanzu ne zakaji ana ga zance ga magana sai dai Yaya zasuyi damu akan dukiyar gadon mu dake hannun sa? Ya fada Yana kallon Ammi Cikin shesshekar kuka Ammi tace "Ku kasa dukiyar yaran Nan sake hannunku uku ku dauki Daya sauran biyun sai ku Adana musu...... "Yo har nawa ne abinda muka karba da kike fadin mu dau kaso Daya mu aje saura? To dukiyar dake hannun mu Bata Kai Daya bisa goman abinda muke bin ummaru ba shekara nawa Yana juyata ?..... "Kawu kuje ku Rike ta duka mun bar muku a matsayin dukiyar ku. Cewar Yaya Abdullahi. Yagana ta watso mishi wani shegen kallo tana fadin "Ko gidan Nan aka hada Mana dashi ba a biya mu ba don Haka asan dai yadda Za ayi don ni ban yarda iyakar dukiyar da ummaru ya Tara ce matar can ta kawo ba...... "Gida ma ai ya zamo wajibi mu karbeshi mu saka shi kasuwa in yaso sauran cikon mun yafe tunda abin duk na gida ne Kuma Dan Uwa ne. Wannan magana ta kawu gide itace ta kawo karshen jayayyar akan gidan da muke ciki sun kwace shi a matsayin kudin da suke bin mahaifin mu Wanda ko Ni na San Babu wasu kudin su a hannun shi. Mutumin da ya kasance cin ka da Shan ka duka shine in ma jari sukayi kukan ya karye shine Mai tada shi Amma yau saboda kawai mutuwa Mai tonon Asiri sunga babu shi shine har suke fadar Wai gadon su Yana hannun shi bayan sun karbe komai namu na Kuma mahaifin mu Dan gidan da muke ciki ma yau shi ya tsone musu Ido har suna fadin shima nasu ne Anya kuwa idan dai har haka zumunci ya koma ba Dole asha wuyar Rayuwa ba🤔? Ban zaci Rashin mutuncin nasu ya Kai inda ya Kai ba sai da Naga kawu gide yayi tsaye akan Yaya Abdullahi Wai ya bashi takardun gidan Ammi Kuma tace ya dauko su suna Nan dakin Daddyn cikin akwatin takardun shi Dole kuwa Yaya Abdullahi ya dauko su ya mikawa kawu gide suka fice suna fadin tunda mun zabi Uwar mu akan su to mu sani da Uba ake Ado Riga ko a kasuwa sai a siyo Kuma duk Dan da yarasa Rigar Uba yayi asara Kuma har abada a tsirara yake yawo Kuma tunda muka kisu to Kar mu sake mu nemesu mu Riki dangin uwar mu in yaso mu dauwama a cikin musulunci ko mu koma kafurai duk Daya Wai anyiwa tuwo barin Mai Kuma sun bamu notice na kwana talatin mu nemi wurin Zama don zasu saka gidan kasuwa su siyar da Haka suka fice suna aibata ammi da Dan uwan su dake kwance kushewa Wai shi ya ja musu ya jajubo musu Ahalin oduduwa da fafaroma Ban taba tsintar kaina cikin tashin hankali ba tun bayan Rasuwar Daddy sai a yau da na Gane gidan Zama ma zai gagare mu bare abin kaiwa abakin salati sai Kuma na Gane shi bawa Yana zuwa Duniya ne kawai don ya karbi kaddarorin sa kyawawa ko Akasin hakan kamar dai mu da muke tsaka da karbar namu kaddarorin masu saka idaniya zubar HAWAYE.................. Labarin GARWASHI na kudine ga me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 11//12 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Tsokaci Akan masu siyen labaran mu su Kuma fiddoshi waje suna yadawa to ku sani kudin da kuka biya ba na copyright bane bare kuce kun siya Kuna da damar yada shi yadda kuke so kudin karatu kuka biya idan son yadawa kike to kicewa marubuciyar copyright zata siyar Miki kigani idan cinikin ku zai tsaya a 300 ko 500 don Allah mu Rika kiyaye hakkin juna Kyautar wa ga Anty fauza Yar Amana ba Zan taba mantaki ba Koda lokaci yazo da Zan aje alkalami don kinyi min Amanar da Zan Dade Ina tuna ki Allah yakara sutura 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ..........Gaba Daya naji Duniya da Rayuwa sun fice min Arai. Banda ALLAHU Babu Mai tsara hakan . Na tuno Ammi da labarin da ta bani na yadda ta hadu Daddyn mu har zuwa auren su Wanda ya Tara kaddarori masu yawa inda Daddyn mu yayi Mata gata yayi mata sutura ya kawota cikin Ahalin shi Wanda basuyi Mata maraba ba Amma yace tayi hakuri shi din zai zame Mata uwa Kuma Uba har da dangi. Kuma hakan ya kasance har ma fiye sai gashi tana tsaka da bukatar shi Ubangijin da yayi Mata baiwa da samun shi ya Kuma yi Mata wata baiwar ta Rasa shi in ba Allah ba wa ya Isa yayi hakan? Na dago kaina na kalli Yaya Abdullahi dake Rike da hannuwan ammi Yana goge Mata HAWAYE Yana kuma Bata hakuri ita Kuma sai Albarka take ta saka mishi Akan abinda yayi na tuburewa da kin bin su kawu gide. Shima Kuma hakuri Yake ta Bata Yana son kwantar Mata da hankali "Kiyi hakuri Ammi kaddarar mu ce Haka da yardar Ubangiji ba zamu taba tozarta ba don Allah kiyi hakuri Akan batun gidan Nan zamu tashi mu bar musu duk yadda aka Dade a gidan Duniya wata Rana za a tako gidan lahira "Wannan Haka yake Kar ka damu Abdullahi tunda na Rasa mahaifin ku nayi hakuri babu abinda ba Zan iya Rasawa na jure ba fatana Ubangiji ya SHIGA lamarin ku ko da bana Raye Kuma kada Ubangiji ya sa nayi nadamar kasancewa cikin musulmi da musulunci . Tunda na yarda Allah Daya ne ai nagama yin Dace . A ko Ina Kuma ko yaushe Banda abinda Rikewa face Allah iyayena ma na barsu na zabi Allah na Kuma tabbatar ba zai wulakanta Ni ba Kuma kuyi hakuri da duk irin Rayuwar da kuka samu kanku aciki Allah shine Mai zanawa bawa kaddara idan aka zano maka ita baka isa ka goge ta ba Allah ya kaimu Nan da wata gudan in Sha Allah zamu samu wani matsugunnin Haka na SHIGA zaga gidan mu Ina Rayawa a zuciya ta Wai Nan da kwana talatin zamu tashi mu barshi tuni HAWAYE na suka kafe Akan in na tuno yadda Rayuwa ta ta faro da yanzu da irin juyin da tayi min sai dai nace "ALLAH na gode maka Allah ka Kara min imani kasa Kuma na cinye dukkan kaddarori na ba tare da na Rasa imani na ba Na Gama zagaye gidan kafin na koma Kan motocin Daddyn Suma Ina shafasu zuciya ta na tuno min abubuwa masu yawa akan mahaifina da irin tanadin da yayi Mana a Rayuwa Ashe kana taka NE Ubangiji Yana tashi tashin Kuma itace tabbatacciya. Na tuno irin motar da na taba nunawa Daddyn nace Ina son ya siya min ita ya Kuma ce inayin candy zai gwangwanje Ni da ita Ashe kafin nayi candyn kaddarori sun zagaye Rayuwa ta Naci gaba da shafa motocin Daddyn inaji a Raina tamkar jikin shi ne nake shafawa sai Kuma zuciya ta take kissima min kudin motar Nan tashi wadda ya siyo daga karshe wato homa Jeep Sai kawai naji zuciya ta na fada min to me zai Hana mu siyar da homar mu fanshi gidan mu da ake bamu notice? Ban tunkari ammi da maganar ba sai na fita wurin Yaya Abdullahi a shagon tredar shi Yana zaune inda na ga kayan shagon sunyi kasa sosai saboda Akan su kadai muka dogara acikin su ne mukeyin komai Ashe ko Dole suyi kasa Dama gashi naji Ammi na fadin sufa dama kayan treda ba wata Riba gare su ba Na dubi Yaya Abdullahi inda na gano Ramar shi wadda ban taba kula da yayi ta ba. Da na tsura mishi ido ma Sai na ga ba Ramar kadai yayi ba har Baki fatar shi tayi sai naji tausayin shi ya kamani musamman da na tuno inda Yake karatu wato Egypt sai Naga lallai Dole zafin Nigeria ma yasa shi Baki "Yaya ne Zahra me kike so? Halan cakulat din Zaki kwashe min? Nayi murmushi Wanda ya taho da hawayen tausayin shi matukar yaga dayan mu cikin damuwa to yafi mu SHIGA damuwa don Haka nace "Dama Yaya Abdullahi wani tunani nayi me zai Hana a siyar da wannan sabuwar Jeep din ta Daddy sai inga kamar ta Isa ta fansar Mana gidan mu hannun su kawu gide Koko Yaya kake gani?..... "Kin ko yi tunani Mai kyau Zahra ya akayi ma bamuyi wannan tunanin Ni da Ammi ba? Muje ma yanzu in fada mata shawarar ki don itace ma mafita Ammi da taji abinda Yaya Abdullahi ya sanar da ita sai tace "Shiyasa ba a Raina tunanin yaro kowa da irin balagar da Ubangiji yayi mishi wani azancin magana wani Kuma ta hangen nesa kunyi tunani Bari nayiwa mama magana sai ayiwa abban su Nana magana ya samo Mana me siye Haka kuwa akayi motar Bata dauki lokaci ba aka siyar da ita kasancewar sabuwa ce ajiki Kuma sabuwar yayi sai gashi kudin ta sun iso kudi masu auki kuwa inda Yaya Abdullahi yace duka ma asiyar dasu ko wani kasuwancin sai ayi da kudin su. Haka kuwa akayi sai dai su din basuyi Darajar ta farko ba Domin kuwa Basu kaita Daraja ba inda Kuma har yanzu ba a samu Wanda zai karbi motar Ammi ba inda abban su Nana yace Yana tsoron mutane ne saboda ba bu Allah a ransu shi Kuma Yana tsoron ya kawo Wanda zai zalunci bayin Allah Amma yace Ammi ta Kara hakuri in Sha Allah za a samo Wanda zai karba Kwanakin da su kawu gide suka diba na kwana talatin ya na cika kuwa sai gasu wannan karon daga shi sai kawu madu suka Zo "Yaya kun tattare kayan ku dai ko Abdullahi? Fadar kawu madu Yaya Abdullahi yace Eh kawu Amma akwai wani hanzari ba gudu ba Ina son ku Kira dillali yayiwa gidan Nan kudi muji idan zamu iya biya sai mu biya..... Kawu gide yace ai shi din aikin shi kenan yiwa Kaya kudi don duk dabbobin garin su shike musu kudi wannan gidan ma zai iya mishi kudi.... Yaya Abdullahi yayi murmushi Yana fadin kawu ai dillalin dabbobi daban da na gidaje....... "Au me kake nufi kenan? Kana nufin ba Zan iya mishi kudi ba kenan? Yanzu in ubanka ne Zaka karyata shi irin Haka? Da sauri Yaya Abdullahi ya bashi hakuri Yana fadin ba Haka bane Ya Sha mur Yana micincina idanu ya dubi gidan Yana fadin Banda an kashe gidan da kazanta ai har million Tara zai iya kaiwa inda Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da yasa hadamar tasu ba Mai yawa bace Amma Kuma da ya nemi su rage sai suka ce in yayi musu a million Tara din su biya in kuwa Bai musu ba to su nema gaba don yanzu zasu Rufe gidan....... "Yayi kawu mun gode muje banki a Ciro kudin Haka suka tafi da kawu gide aka Ciro kudin aka damka wa kawu madu inda Yaya Abdullahi yace su bashi takardun gidan da suka amsa. Kawu madu ya Kara gyara Rikon da yayiwa kudin Yana fadin "Ai Kai da uwar ka Baku da wayo tunda kukayi nufin yaudarar mu dama sai da nace akwai kudin marigayi a cikin banki abinda ta kawo Dan debowa kawai tayi ta boye sauran to wadan Nan kudin idan dai har ummaru zai dawo Duniya to zasu dawo gareku idan har son gidan Nan kukeyi sai kun Kuma kawo wata million taran kafin ku zauna acikin wannan gidan su Kuma wadan Nan kudin mun Rage ne daga cikin kason gadon mu don Haka idan Kuna da muradi kwa iya fiddo wasu kudin shima kafin Nan da Rana irin ta yau sati guda Daya Tak muka Baku idan da kudi ku zauni gida idan Kuma babu to na Rantse maka da kabarin uwa ta kayan ku ma waje Zan auna muku su kaji na Gaya maka Ya dubi kawu gide Yana fadin "Muje gide. Da Haka suka fice Rungume da tarin kudin har million Tara Ammi ta sauke tagumin ta da doguwar ajiyar zuciya babu Mai motsin kirki bare magana inda Kuma yaya Abdullahi yace karar su zai Kai Amma Ammi tace Kar ya Fara ya dai Ida kwaso sauran kudin ya basu inda Ni Kuma nace Mata da dai mu Kuma Basu kudin suyi tafiyar su dasu gara mu siyi wani gidan tunda ta Hana ayi karar su don wannan damar da suka samu ce tasa suke tsula iskancin su Sai dai duk da saka cigiyar da akayi na gidan da zamu siya da akayi kafin cikar wa adin da su kawu gide suka bamu yazo shiru ba a samu ba har zuwa Ranar da su kawu suka dawo don Jin inda aka kwana don Basu ma jira jin wani bayani ba inda kawu madu ya Soma fito da kayan mu Yana watso su kwar gida duk wani Abu da ya tarbi gabanshi surowa kawai Yake Yana watso su waje Ammi tacewa Yaya Abdullahi ya kwaso sauran kudin dake bankin ya bawa su kawu madu shi Kuma yace Yana tsoron ya dauko sauran kudin ya Basu suyi Mana yadda sukayi a farko Amma ganin sai watsi suke Mana da Kaya yasa yaje ya fito da kudin Amma yace sai sun bashi takardun gidan kafin ya Mika musu kudin..... Kawu gide ya Miko mishi takardun a cikin jakar da suke tun farko kafin Yaya Abdullahi ya Mika musu kudin suka fashe da Dariya a lokaci Daya kafin kawu madu yace "Ai tunda kukace yaudara ce aikin ku mu da kune in Baku fiddo Mana hakkin mu ta Arziki ba ai zaku fito dashi ta tsiya Wai Kai Dan Boko ba zaka bada kudi ba sai an baka takardu to ga takardu Nan Amma fa na bogi ne na asalin suna hannun mu idan kazo zaka iya biyan wata million taran na maido maka su don Haka ku fito zamu datse gidan mu............... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ko don littafin GARWASHI daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan Ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 13//14 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Allah kayi musu Rahama ka yafe musu kayi musu dukkan wata Alfarma da kakewa muminan bayinka Ba zan taba mantawa da wadan Nan mutanen ba Anty Jamila Yusha u Anty Rahane sani Dan Kani Anty Amina brn kebbi Antyn Yola Allah ya Kara sutura Sai haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ............Yaya Abdullahi ne yaga da gaske suke Shirin izo keyar mu waje su Rufe gidan gashi Kuma babu inda zamu Kai kayan da sukayi Mana watsi dasu kofar gida bare inda zamu saka hakarkarin mu mu kwanta Ya zube Agaban kawu gide yana Rokon shi Alfarma..... "Kawu kaifa uban mu ne don Allah Kar ku tozarta mu bamu da inda zamu koma kuji tausayin mu sau biyu fa Kuna karbe Mana kudi don Allah Kar ku Rufe Mana gida..... "Ai tunda kukace ku Yan iska ne Kai da Uwar ka ai kun gamu manyan Yan iska tunda babu Arziki a cikin lamarin ku babu yadda bamuyi da ita ta fiddo Mana hakkin mu ba Taki Kuma Kai da muke ganin namu ne ka goyawa kafurar Uwar ka baya ko gidan ubanwa kuka samo wadan Nan kudin Haka in ba satar su Uwar ka tayi ba? To ko zaku shekara kuna kawo wasu kudin da sunan fansar wannan gidan to muma zamu shekara karbe muku kudi tunda abin naku yazo da Raini da yaudara wannan gidan dai ko kwai kuka NASA cikin shi sai kun barshi in ma Ruhin ku ke ciki sai dai ku marawa ubanku baya Ya Soma hado Kan get din Yana kokarin Rufewa Dole muka ido kwaso kayan mu Yaya Abdullahi Kuma ya karbi key din motar Ammi dake parking space ya fito da ita muna kallo ya bugawa kofar manyan kwaduna sukayi gaba suka barmu muna tattare kayan mu da sukayi watsi dasu. Dole gidan mama muka shigar da kayan mu acikin shagon gidan muma Nan mukayi mazauni don can cikin gidan dakin mama ne da na Mai gidan ta sai na Ya'yan su don Haka abban Nana yace idan zamu iya Zama a cikin shagon to mu koma kafin ya cigita Mana gida Na dubi shagon Wanda kofar shi take cikin soron Kuma akwai wadda ke fita waje inda beraye ke gadar su son Ransu yau anan Allah yayi ikon shi Akan mu da komawa Rayuwa lallai bawa Bai Gama sauyawa ba sai Ranar da ya komawa Ubangiji Muka koma Rayuwar cikin shago mu duka muka gwamutsu a wuri Daya har da Yaya Abdullahi Wanda yaso ya bar Mana Nan ya koma kwana waje duk da kasancewar yanayin damuna da ake ciki Amma Ammi tace Bata San zancen ba tunda wurin Yana da girma Dole suke wuri Daya shi da sulaiman Ni Kuma Ni da Ammi Mama tayi ta fada da taji dalilin wannan wulakancin da su kawu sukayi Mana na karbe Mana kudi har sau biyu Kuma sukayi mana watsi da kayan mu...... "Haba Amina wannan ai Ragon azanci kikayi da Kika Bari aka sake Basu wasi kudin mutumin da Bai iya son dan uwan shi ba yaushe kike tunanin zai tausayawa Ahalin sa? Kuma ai maganar Abdullahi ai itace gaskiya da kin bari yayi karar su ai shi alkalin ba irin su Yake ba yanzu irin haka ke da Dadi saboda Allah? In ma da gaske suna da hakkin ai ba zasu karbe muku kudi har sau biyu ba ai in mutum ya Gane kana shakkar shi to shi Kuma lokacin ne zai bude kofofin tozarta ka me akeyi da muguyen dangi irin wadan Nan? Ammi sai hakuri take Bata tana kuka don gani takeyi ta batawa mama Rai don da gaske mama ta fusata ba kadan Amma Dole mama tayi hakuri tace "Naji babu Dadi ne Amina da ace a gabana hakan ta faru wallahi ba Zan kyale su ba don zanyi wankan tsarki ne in siyi fadan Nan in yaso Ni dasu mu gurfana gaban kuliya manta sabo haba me akeyi da dangi irin wadan Nan ai gara a Raba gari kowa ya tsaya matsayin shi tunda Wanda ya hada ya Raba ko shi din ma ai ba dadin su yaji ba Amina kema kinfi kowa sanin hakan Rayuwar mu ta koma a gidan mama inda Yaya Abdullahi ke bude shagon shi na tsohon gidan mu muna samun na hidimar yau da kullum duk da kayan shagon sunyi kasa kwarai mun cinye sai Dan abinda ba za a Rasa ba Akace zari dai Daya Bata barin Dame domin ko sannu ahankali kayan shago suka Kare kaf mun cinye su tas har ta Kai abinda za a Kai baka sai Mama ta tallafa Mana inda duk muka fita a kamannin mu na asali muka koma wasu Yan Allah ya Baku mu samu😭 Hakika mama ta taka Rawar gani Akan mu da Rayuwar mu domin ko tsayin zaman mu a gidan ta tayi Mana hidima da dawainiya ita da mijin ta Wanda shima ba karfi ne dashi ba . Idan ammi na kuka tana godewa mama akan karamcin da take Mata sai Mama tace ai Nima kinyi min karamci Amina shi kuwa Dan halak baya manta halacci Ni meye bakiyi min ba lokacin da muka SHIGA namu halin kwatankwacin irin wannan? Sai na Gane akwai hikima cikin wata Karin magana da malam bahaushe yayi da yace ka yada ALHERI ka tsince shi a gaba domin ko ban mance ba lokacin da Ammi keyin girki ta aikawa mama sau uku a Rana lokacin da Abban Nana yayi tafiya neman kudi komai ammi bawa mama takeyi ko ta nema ko Bata nema ba hatta da omo da Sabulu aika Mata takeyi sai gashi yau da ace ammi irin Rayuwar Nan tayi irin ta kaza me ci ta goge Baki ko muguwar makotaka tayi Ashe da bamu San inda zamu jefa Kan mu ba Muna cikin wannan halin tsaka Mai wuyar ne Kuma aka samu gidan haya Amma a can kofar marusa sai dai kudin da zamu Fara biya ma babu su sai mamace ta biya Mana muka kwaso muka dawo kofar marusa muka baro makotan kirki irin mama muka dawo wata unguwa me cike da kwatoci da gidajen laka Mai Rufin kwano ko silin Babu kasa Kuma babu tiles Sai daben sumunti. Daki biyu ne a gidan inda mukayi masauki a Daya Ni da Ammi da sulaiman muka barwa Yaya Abdullahi Daya sai dai Kuma inda take a kasa take dabo shine babu abinda zamu juya na Sana a Wanda Dole sai da shi ko da Rayuwa zata tafi yadda ake so saboda bukatun yau da kullum Dole muka Rungume hannuwa inda Kuma mama da Abban Nana sukayi Mana karamcin nasu suka biyo mu da shinkafa da garin masara da garin Dan wake Ni da kaina naji araina da ace abban Nana ne danginmu akasin su kawu gide da zumunci Bai zamo zumuncin zamani ba Kuma da ba a zagi Yan uwa da dangi ba Haka muka Mike da kaddarar da Ubangiji ya zano zata same mu . Gidan da muke ciki na wata masifaffiyar tsohuwa ne marar hakuri kamar zawo wadda Allah yayiwa Arzikin gidaje da shaguna Wanda ta bayar ake haya ake biyan ta kudin hayar Wanda Kuma ya kuskure Bai biya ba zai jita tamkar yaji a ido ko Kuma in yanayin damuna ne baka biya ba tasa a kware maka kwanon Rufin dolen ka ka biya ko ka Kara gaba Kuma baka Fara SHIGA muhallin ta sai ka biyata kudin da kukayi na wata ukune ko shekara Na dawo Daya makaranta inda na shigo sabuwar unguwar mu inda nake wuce mutane suna min Rakiya da ido na Kuma San Rashin sani NE ya kawo hakan ko da Yake nasan a yadda nake ko da Rayuwa tayi Mana sauyi me yawa na Rashin abubuwa masu yawa Amma Kuma hakan Bai sa na Rasa abubuwa uku ba wato kwarjini da tsabta da Kuma kyawu ba wannan Kam Koda na Rasa komai ban Rasa su ba don Haka sai na wuce Abu na bana kulawa Kuma dama Ni din ba me son wasa ko shirme bace bare sharholiyar Yan mata masu irin shekaru na komai nawa cikin nutsuwa da kame Kai ko cikin kawaye ban Faye SHIGA ba kawaye na ma biyu NE a makaranta Suma ba nice na SHIGA jikin su ba sune suka shigo Wai Ina burgesu sai muke kadaran kadahan don ban saki jiki dasu sosai ba Na shigo gida na iske ammi a tsakar gida tana girki tsakar Rana don babu kichen a gidan sai tsakar gida take girki inda na iske ammi na sakun Dan wake abinda na tsana a Rayuwa ta don duk Ranar da Kai Dan wake a cikina Koda kwara daya ne sai nayi ta zagawa bandaki cikina baya son sa Amma sanin da nayi ammi ta San bana son shi yanzu ne da na furta zata ce zata sama min wani abun Dole na maye kiyayyar Dan waken da soyayya bayan nayi Mata sannu da gida da Kuma aiki "Yauwa Zahra ta kiyi hakuri kici Dan waken Nan sai ki Sha Yar kanwa gata Nan ba zai Bata Miki ciki ba naso na sama Miki ko garin kwaki ne Amma abin ya gagara..... Zuciya ta naji ta karye saboda tausayin ammi na dubeta sai zufa take a tsakiyar Rana inda wahala ta sauko Mata da wani irin tsufa tamkar ba itace Yar gayun Nan da Daddy ke kambamawa a fagen kyau. Haka muka ci Dan waken Nan Amma Kuma kamar hadin Baki mu duka ukun muka kware da Rudewar ciki muna ta zagaya bandaki Ni da Yaya Abdullahi da sulaiman ammi ta Rude ta fito ta siyo Mana magani flajin kafin muka samu afuwa Zaman Shirun da Rashin abinyi yasa Yaya Abdullahi yanemi shawarar ammi Akan ta barshi ya dauki motar ta ya Soma sufurin ko don kudin hayar da ke kusanto mu Dole ammi ta yarda Yaya Abdullahi ya Soma sufuri zuwa Kano ko funtua duk inda dai ya samu fasinja a Haka muka samu Rufin Asiri Mai yawa Ashe wannan Jan motar na Yaya Abdullahi shima wata kaddarar ce ke Shirin sauka Akan mu kaddarar da zata girgiza mu fiye da kaddarorin da suka Riske mu a Baya............. Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Wannan labarin na GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 15//16 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga Yan kungiyar kainuwa writes associated Gaba Daya kaf Ranka takaf ban cire ko guda ba Allah ya Kara daukaka Sadaukarwa ta biyu ga dukkan musulmin da Ubangiji ya jarabta da kuncin Rayuwa Allah ka fidda bayin ka daga kunci da talauci ka maye da gurbin Arziki Ban manta masoya ba har Abada kuwa ba Zan manta Babu abinda yafi a furta maka ana kaunar ka musamman Irina da ban Kai ba ban Kuma iya ba 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ........... Wannan wahalar da Yaya Abdullahi ya samu kanshi a Rana tsaka ta Jan mota da sufuri tayi matukar tafiyar da kumarin jikin sa Ya Kara dafewar fata ya Kuma Kara Rama Akan wadda ya samu Kai acikin ta Amma da Yake jarumi ne sai ya nuna min bafa komai bane wannan duk na lokaci ne Kuma zai wuce da yardar Ubangiji shi lamarin Rayuwa guda biyu NE ko dai ya wuce ya barka ko Kuma Kai ka wuce ka barshi Haka ya fada min a lokacin da nake kokawa halin da Naga ya SHIGA na wani sauyin saboda sanin da nayi mishi na Bai taba SHIGA wani hali na Rayuwa irin wannan ba bare nayi tunanin sabo Amma Kuma Dole na gamsu da bayanin da yayi min don a sanin da nayi mishi Yana fatan ganin ya fita hakkin mu Akan komai Kar dai muce muna son kaza to kuwa zaiyi kokarin sama Mana abinda muke so inda Kuma na Gane a kokarin Yaya Abdullahi so Yake a Dole sai ya maye Mana gurbin Daddy da muka Rasa Nima sai naji zanso hakan Amma Kuma gaskiyar magana nafi son naga Yaya Abdullahi shima a huce Amma ba cikin wannan wahalar ba to Amma ya muka iya tunda haka alkalamin kaddarar mu ya zano Mana? Na dawo makaranta kenan na iso kofar gidan mu inda na hango motar Yaya Abdullahi a kofar gida inda na SHIGA tunanin yau kuwa ya dawo da wuri na SHIGA gidan da karsashi na inda na samu Ammi ta zabgo tagumi cikin damuwa sai naji hantar cikina ta kada "Anmi lafiya dai ko ? Na fada murya ta na Rawa don naji ajikina ba lafiyar da na tambaya ba...... "Lafiya Lau Zahra Abdullahi ne dama ya dawo babu lafiya Kuma gashi babu kudi a hannu na bare na Kira likita Amma tashi kije gidan maman Nana ki aro min ko dubu Biyu ne dama gareshi nake saka Ran samun kudin idan ya dawo to jiki da jini yau lafiyar Taki...... Kafin ma Ammi ta gama zancen ta na wuce kuryar dakin Yaya Abdullahi Wanda na samu Yana ta kelaya uban Amai tsanwa Shar Alamar kumallo ne babu komai a cikin sa Na matsa kusa dashi Ina mishi sannu kafin na Kama shi na jingina shi jikin filo na fito da sauri na dauko kokon da na Rage da safe na kuza mishi Ruwa ya Zama farau farau na dawo na bashi ya dan Kora ya koma ya kwanta na kwashe Aman kafin na fice zuwa gidan mama na fada Mata sakon ammi ta kuwa bani kudin har ma ta zubo abinci Mai yawa a kula tace na kawowa Yaya Abdullahi Kuma nace tana duba shi kuma zata Zo duba jikin nashi Na kawo wa ammi kudin da sauri Kuma tace na Kama Mata Abdullahi mu Kai shi Asibiti Na kamo shi muka fito ammi ta bude motar muka SHIGA kasancewar ta iya mota yasa Kai tsaye muka nufi Asibiti aka duba yaya Abdullahi akayi mishi gwaji sakamakon na malairia ne da da Kuma Rashin Samun hutu sai Kuma ulcer dake neman Kama shi don Haka aka shawarce mu da bashi cikakkiyar kulawa da Kuma samun hutu kafin aka Rubuto magunguna muka dawo gida Dole Yaya Abdullahi ya zauna a gida ba don ya samu hutu ko kullawar da likitan ke magana akai ba sai don ya samu afuwar jiki ya koma bakin aiki a ganin shi talaka irin shi wane hutu zai nema Wanda sai ya fita ya samo ake bukatun Rayuwa. Zuwa wannan lokacin duka duka shekarun shi fa ashirin da biyu NE don dai Jin Dadi da kuma jikin girman yasa ya Zama wani babba Amma yanzu da Rayuwa tayi sauyi duk wannan jikin nashi ya zube ya koma Dan kadan don shekara bakwai ne tazarar dake tsakanin mu Ni da kaina na Gane Yaya Abdullahi Yana bukatar hutu don Haka sai zaman jinyar shi ya Kara budo Mana wasu shafukan a cikin littafin da Yake Rubuce da tarin kaddarorin mu inda Yake Shan magani Amma sauki sai ga Ubangiji da Kuma godiyar Nan dai a gareshi Muna cikin jimamin jinyar Yaya Abdullahi sai ga haj ladi matar da muke haya a gidan ta ta doko Mana sallama har ga Allah mun manta da cikar wa adin kudin ta saboda jinyar Yaya Abdullahi "Masu gidan suna Jin sallama ko kuwa duk cikin Rainin da ake shirin kawo min ne anaji na Ina kwada sallama ake yi min banza? Ammi ta amsa Mata da bamuji bane hajiya sannu da Zuwa shigo ciki...... "A a ba sai kin sakani a daki ba don ba dogon turanci ne ya kawo ba kudina na biyo karba bani kawai na wuce in har Babu Raini a cikin lamarin naku "Kiyi hakuri hajiya Wallahi babu Raini a tsakanin mu yaron wajena ne babu lafiya kingan shi Nan kwance dama shine me biyan kudin don Allah hajiya ki Kara hakuri Zan kawo Miki kudin ki har gida da Ubangiji ya yaye wannan ciwon ne ya kawo hakan... "Ke Yar Nan Kar kice Zaki kawo min kalaman karya ki fake da karsana ki harbi guzuma "Don anji nayo sallama ne ake nadewa a gado ace ba a lafiya? In dai lafiya ce waye Mai lafiya a yanzu? Nima ba ita gareni ba Amma nake mazewa nayi harkokina Ni da har hauhawar jini ma gareni Amma ban nade a gado ba sai wannan katon ne akwance Wai baya lafiya? To ki kiyaye Ni don bani da Dadi ko da gishiri Zan Baki watan gaba ki kawo min kudina don ba Zan lamunci a zaune min gida akasa biyana haya ba yo yaushe ma ake haka ? Nan gaba kuwa ai mutum zai iya cewa gidan nashi ne to a fita idona na Rufe don in na Rufe da mutum a ciki ba zai fito ba yayi ta Zama kenan Da haka ta fice daga gidan tana zuba Ruwan tijara Ammi ta dafe kanta tana SHIGA wani zuzzurfan tunani Haka na fice zuwa makaranta zuciya ta a kuntace ban iya dorar da duk wani darasi da akayi a makaranta ba saboda zuciya ta tana wurin daban Akasin gangar jikina dake cikin ajin amma zuciyar Bata cikin ajin Haka na dawo inda na iske motar Ammi dake kofar gidan mu an Mata pentin taxi Amma sai ban dauka wani Abu ba azatona ma ba motar ta bace na SHIGA gida na iske Yaya Abdullahi Yana ta amai inda ammi ke fada min magungunan shi ne suka Kare babu Kuma kudin siyen wasu shiyasa ciwon ya koma sabo Dal Dole aka SHIGA kame kame Washe gari naji Ammi na cewa sulaiman Kar yaje makaranta ya tsaya ya kula Mata da gida da Kuma Yaya Abdullahi. Ban tambaye ta inda zataje ba NASA Kai na fice zuwa makaranta inda yauma ban kula da kalolin darussan da aka koyar damu ba saboda tunanin Rayuwa har aka tashi na taho Ina zancen zuci har na kawo bakin titi Zan tsallake Ina hanga dama na da hagu na don kiyaye ban fada wa abin hawan da ke son wucewa ba inda Kuma na hango wata taxi tayi parking a gabana Ina dubawa sai Naga Ammi a mazaunin direba sai wasu Mata dake baya da Kuma wata mace a gaba Gabana yayi masifar faduwa inda najiyo Ammi na fadin "Shigo muje Zahra har an taso? Na bude bayan inda ke da wurin zaman mutum Daya na zauna na Rufe motar Ammi taja motar muka wuce Ina cike da tarin tambayoyi shin ammi mota ta koma ja ne? Ko kuwa wadan Nan matan Ina zata kaisu? Matan Nan na cikin mota suka katse min tunani ta hanyar fadin "Ai Ni Wallahi baiwar Allah kin burgeni don wannan Rayuwar babu nakasasshe sai kasasshe Haka Kuma Babu maraya sai Rago tunda har Ubangiji ya Azurta ki da motar nan Taki ce ta kanki da ki tsaya bawa mutanen wannan zamanin marasa Amana suna cutar ki gara ki tuka abinki tunda ma Allah yasa kin iya don Ni Wallahi zaburar Dani kikayi don Zan cire tsoro Nima na koyi motar Nan don tsaro ba don tsoro ba . Dayar matar dake gaba ta karbe maganar da cewa "Ai in Gaya Miki Aisha Mata na ganin tasku a Duniya Kar ma ace Allah yayiwa mijinki Rasuwa wayyo Allah na taba SHIGA wannan siradin na Rantse Miki da Allah aduk yawan yan uwan mijina aka Rasa samun zakaran da zai tallafa min da kwayar hatsi ke sai a shekara ma ban saka dayan su idons ba ga Yara har biyar baccin Sana a ta ai da Asiri ya tonu shiyasa yanzu da Naga baiwar Allah Nan tana Jan mota sai tausayin ta ya kamani don nasan akwai wani Al amari da ya sata hakan Ammi tayi murmushi daidai da ta kawo su bakin babbar kasuwar central market ta gyara parking suka fito suna Miko Mata kudin ta suna Kuma binta da ADDU A ta fatan ALHERI ga Kuma kiyayewar Ubangiji ta karba tana godiya ban San lokacin da HAWAYE ya balle min ba na kife kaina a cinya ta Ina kuka inda najiyo Ammi na min magana cikin sanyin murya .............. Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 17//18 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga daukacin ZURIAR dake Rike zumunci tsakanin su da Allah ba don abinda suka hango ba ko Wanda zasu samu don yanzu zumunci ya zamo jari hujja Gaisuwar girmama ga Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ............Muryar Ammi najiyo akaina cikin wata murya da na Gama fahimtar cikin Hali tayi maganar "Kiyi hakuri Zahra komai Kika ga ya faru ga bawa Rubutacce ne bawa Kuma Bai Isa ya sauya shi ba. In ba Allah ba wa ya Isa yayi hakan? Nasan kinajin zafina Akan wannan hanyar da na dauko wadda nake ganin itace mafita Domin ko ya zame min Dole na tashi na Kare mutuncin ku tunda Dani a cikin Wanda sukayi sanadin zuwan ku Duniya Ashe ko ya Zama Dole na SHIGA na fita don ganin ba kuyi kukan Rasa wani Abu ba . Ba Zan sake Barin Abdullahi ya komawa aikin Nan Mai wahala ba nice ya kamata nayi tukin mota Amma ba fita garuruwa ba iyakata Nan cikin gari kawai na Kuma yi Miki alkawarin Kare mutunci na da naku in Sha Allah duk Runtsi duk wuya inaji ajikina Zahra akwai lokacin da komai zai zamo tarihi kamar ba ayi ba don Haka Daina kuka kinji ? ADDU A nake Rokon kiyi min Allah ya tsare Ni sharrin karfe da Kuma sharrin mutum da aljan "Ammi ba haushin ki nakeji ba illa tausayin ki Ammi ban taba ganin mace na tukin taxi ba shiyasa nake tausaya Miki Kar kema wahala tayi Miki yawa irin wadda ta riski Yaya Abdullahi..... "Babu komai Zahra Allah ya Rufa min Asiri don na lura Ubangiji ya saka min nasibi don kusan Dubu biyar na samu bayan na fidda Dubu biyun Mai da na siya kinga sai mu biya haj ladi kudin ta abinda na samo gobe Kuma sai mu siyo abinci mu aje in Sha Allah wahalar mu ma tazo karshe Haka kuwa Ammi ta zage fita Aikin tuki Kuma tana samo kudi sosai inda na Gane shi Ubangiji da ka tashi da nufin kana son ya taimake ka to zai kuwa taimake ka sai dai Kuma Yaya Abdullahi dake kwance Bai San hakan ba Kuma ammi tace Kar mu sanar dashi don da yaji ba zai yarda ba Kuma gashi ba lafiya gareshi ba Tuni aka biya haj ladi kudin hayarta muka zauna lafiya har ma Ammi ta samu kudin da ta siyawa Yaya Abdullahi magani ta Kuma siya Mana kayan abinci Wanda Rayuwa ta koya Mana cin dangogin su Wanda bamu waye su ba amma dole muka Saba tun muna ci cikin mu na baci muyi ta zawayi har muka Saba daga wannan sabon sauyin zuwa Wanda Muka sani muka Kuma Saba Jikin Yaya Abdullahi yayi sauki har ya Soma tambayar kanshi yawan fitar da ammi takeyi Amma dai Bai tambaye ta ba Bai Kuma tambayi kowa ba inda a yau ya fito waje Yana zaune Yana kallon yadda mutane ke ta Kai kawon su kawai sai yaga Ammi ta shawo kwana cikin motar da aka mayar taxi Kuma ga Alama kamar garin take zaga wa Ya taso ya karaso daidai da tafito Rike da ledar da ta siyo Dan Raba Mana dangin makulashe ya karbi ledar suka shigo ciki Yana mata sannu da Zuwa ita Kuma tana murnar ganin ya Soma fitowa waje Alamar sauki ya samu "Iska kake Sha ne Abdullahi? Masha Allah Allah ya Kara lafiya kaji ? Ya amsa da Ameen Ammi Amma ya Naga motar Nan anyi Mata fentin taxi? Ya fada Yana kallon Ammi wadda ta shiryawa tambayar tashi "Sai dai kuyi hakuri Abdullahi Amma ai ya Zama Dole na Mike tsaye don na ga Baku yi kukan Rashi ba in kun Rasa Uba jajirtacce to tabbas Baku Rasa jajirtacciyar mahaifiya ba don Haka Kai ma inaga makaranta ya kamata ka koma don yadda na samu sa ar Nan abubuwa suna tafiyar min yadda ya Dace kaima na yanke shawarar ka koma karatu kawai....... Ya Soma kada kanshi Alamar A a ba zai iya Barin ta da wannan dawainiyar ba. ...... "Ammi nine fa Ubangiji ya baku don kuyi alfahari da haihuwa ta . Nine Wanda Ubangiji ya kawo muku don na dauki takalifin ku keda Daddyn mu da Kuma kanne na to tunda Ubangiji Bai yarda Daddyn yaga Haka ba sai ke don me Zan Bari kiyi ta wahala Haka ? Don Haka don Allah don Annabi kiyi hakuri da fitar Nan nine Zan fita na Nemo muku duk abinda kuke so tunda na samu lafiya dama sai da wani ya fada min ulcer ce ke neman kamani da na fada mishi abinda nakeji shi Kuma yace akwai maganin Hausa da zai bani Zan Rabu da ita Yana a funtua ne in naje Zan neme shi ya bani shikenan Ammi don Allah don Annabi kar kice A a idan Kika ce a a kamar Baki yarda Zan zamo Miko abin alfahari ba.... Ammi bata yarda ba daga farko don cewa tayi bashi da lafiya ya Bari ya Kara samun sauki tukuna shi Kuma ya CE baya son yaga tana fitan ne don Haka ta hakura da fita shi Kuma ya zauna zaman shanye maganin shi kafin ya koma bakin aiki Sati guda Daya Tak ya koma aiki inda Ni da kaina naji gaskiya bana son aikin Nan na Yaya Abdullahi hankali na ya Fi kwanciya Akan na ammi ban San Dalili ba ko da Yake dalilin ba zai wuce na kaddara ba wadda Ubangiji ke darsawa wasu Jin wani Abu da zasu yarda dashi ko Akasin hakan Wanda matukar suka bibiyi abin Nan da Basu yarda dashi ba sannu a hankali sai su Tara's da kaddara acikin shi kaddara kuma me ciwo a zuciya Aikin Yaya Abdullahi ya Dore don yanzu har wata Yar kiba ya somayi bayan ya karbo maganin ulcer ya Kuma yi amfani dashi har ya warke daga cutar ulcer harkokin shi suka tafi daidai komai namu ya tafi daidai kamar dai irin Rayuwar da ta samemu a tsakar Rana guda Daya Tak A dangin mahaifina kuwa shiru babu Wanda ya neme mu bare yaji ya muke Rayuwa ya muka Fadi ya muka tashi ko da Yake naso na yaudari kaina idan nace so nake Wai wani yazo da sunan duba mu ai ko a mafarki naga hakan Zan karyata suna wurin su muna namu sai ma Nana CE ke fada min wai Yan uwan Daddy sunzo Kan maganar gidan mu har ma sun saida shi Wanda ya siye shi ma yace Rushe shi zaiyi ya sake sabon Gini Kasancewar makarantar mu daya da nana ta gidan mama kusan ma itace kawata ta kusa kusa don a tare ake kaimu makaranta a wani lokaci can da ya Jima da shafewar tarihin shi Wannan magana ta Nana ta kadani ba kadan ba don da nadawo gida ma sai da na sanarwa ammi abinda nanar ta fada min "To ya za ayi Zahra in ma Basu saida shi yanzu ba zasu saida shi Nan gaba Allah ya Baku mafiyin abinda kuka Rasa Ina Rokon Allah yayi muku gata fiye da Wanda mahaifin ku yayi nufin yi muku na amsa da Ameen ya Rabbil Alamin Da na kebe ma sai naji Ina son yin dogon nazari Akan shin Wai mu kadai ne muka kuskuro shigowa Duniya da Rashin Dacewa Akan Yan uwan Daddy ko ko Ammi da Ubangiji yayiwa nasibin shigowa hasken musulunci? Yan uwa da dangi dai ta bangare biyu ake alfaharin samun su wato Uwa da Uba shi Daddy nashi Basu da kirki suna kin Ammi ne don kawai ta kasance ahalul kitabi suke kinta to su Kuma dangin Ammi fa? Su Kuma meye matsalar su damu da suka yada mu basa son mu Basu rabar mu ? Da na nutsa sai Nagano yadda Ammi ta sanar Dani shigarta cikin musulunci ya bar baya da kura Wanda har nemanta suka Rakayi don su kasheta Allah ya kareta Daddy ya dauke ta suka bar kasar Baki Daya shine fa ta tsira daga harin da ake kawo Mata Amma Kuma sai Naga indai Haka akayi Rabuwar to Babu dalilin da zasu neme mu don a fahimta ta ma yadda su kawu gide suka tsani Ammi saboda ta fito daga wata kabila da yare akasin nasu suke kinta to su Yan uwan Ammi na tabbatar da sunfi su kawu gide kinmu tunda su neman Ammi suke ma su kasheta Akasin su kawu gide da basu nemi kisan ba don Haka kuwa Ashe yaudarar Kaine ince zasu tallafe mu don Haka sai Naga Bari na koma baya na hasko muku madubin kaddarar da ta haske Akan Ammi da Daddyn mu Wanda haduwar su CE sanadin kaddarar mu har Kuma zuwa yau din Nan da muke tsaka da garari a cikin Duniya don Haka ku biyo Ni kuji haduwar mahaifina da mahaifiya ta da irin kaddarar da ta taka Rawar da har suka Zo Kan gabar Aure da haihuwar mu muka Kuma shigo Duniya cikin wani mashahurin gata Amma dare Daya Ubangiji ya sauya komai duk dai acikin waccan kaddarar da take Rubutacciya Kamar yadda Ammi ta sanar Dani sunanta Justina............ Labarin GARWASHI na kudi ne ga duk me bukatar jin cikakken labarin zai biya dari uku 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 19//20 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Tukwici ne gareku Nafisa Rabi u Umar Mrs Abdul Rukayya GAWATA Hadiza D Auta Wasila ummu Aisha Bilkisu h muhd Haj Jamila Dan fajo Rabi atu Bashar Abdullahi Fedyn bash Nagode muku kwarai Gaisuwar girmama wa ga haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Yan Uwa na maza da Mata Ahalin gidan Alh Bara'u Sani majema Ubangiji ya Kara daukaka 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ............Justina shine sunana Yar gidan wani mashahurin me kudi Mai suna maazi Nkem . Ma azi Nkem hamshakin Mai kudi ne Wanda ya Tara dukiya Mai dumbun yawa saboda shaharar shi ta fuskar kasuwanci komai saidawa yake in nace komai to Ina nufin komai Domin ko Maazi Nkem har gidan giya gareshi bama guda Daya ba don Haka komai da Ruwan ka ne don mu a Al adar mu Dole ne ma mutum yayi kudi na kecw Raini don Babu abin kunya agaremu irin mutum ya Rayu cikin talauci Kuma ya mutu cikin talauci har Diyan jikoki sai an gorantawa ace Basu da k'ashin arziki don haka NE maza ke zagewa su nemi kudi ba sai lallai ta hanyar Sana a ba ta kowace fuska dai kayi kudi don ka kaucewa talauci Akasin wasu dake fita bakin Rai bakin fama su sata ko suyi kisa su kwashe koma su bi Dare su fasa gidaje ko shaguna Akasin Maazi Nkem Wanda shi Sana a ce ta Tara mishi kudin shi kowace iri ce kuwa zaiyi ya samu kudi inda ya Auro mamata madam Amaka ita Kuma ma aikaciyar Yar Boko ce don har Aiki ta Fara Amma ganin Maazi Nkem da kudin shi shi ya hanata Aikin Kuma ta yarda ta hanu. Rayuwar gidan mu abin burgewa ce don mu uku iyayen mu suka haifa maza biyu mace Daya Kuma dukkan mazan biyu yayu nane nice karama Kuma mace Daya don Haka fasalta yadda Zan kasance a tsakanin iyayena Idan nace sunaji da Ni naso Bata yawun bakina ne kawai ba garesu iyayena ba Baga Yan Uwa na ba guda biyu Sony da Emmanuel wadan da suke tsare da wasu bangarori na dukiyar Maazi Nkem Wani Abu Kuma da ke burge mutane akaina shine Ni din tamkar ba jikin Amaka da Maazi Nkem na fito ba don ko kusa banyo kalar kowa ba tamkar ma ba Yar Nigeria ba nafi Kama da black American sai dai Ni farace tas irin farin Maazi Nkem Amma bayan wannan komai nawa daban ne kuma na musamman ba irin na Yan Matan garin mu ba. Manyan idanu da dogon hanci me idanu irin na yankan kifi lumsassu gashin kaina har kafada bakina Dan karami Wanda a gefe Kuma Ramin kyau ne (dumple ) da nayi murmushi sai ya loba Kirjina daidai Ni da shafaffen ciki da budadden kuturi daga kasa ta ko Ina nayi daban da Matan yankin mu don za a Tara dari sai sa a mukai uku hatta d yatsun hannuna daban suke Kuma abin kallo ne wurin mutane mussamman maza sai Kuma akayi sa a bana son kallo da na kula ana kallo na yanzu ne zan fashe da kuka Kar ma ace tare nake da Amaka ko Maazi Nkem Wanda Yake alfaharin sakani gaba nayi mishi Rakiya duk inda zaije kuwa Akasin yasa ka babban Dan shi gaba suje wato Sony sai nice yake sakawa gaba muje Duk wani Abu da Zan nema a gidan mu Zan sameshi wurin Maazi Nkem ko Amaka ko su Sony da Emmanuel kowa Yana min abinda nake so hatta makaranta ta kudi aka sakamu a komai sai an kure adaka ake Mana Sai dai Kuma a gefe guda iyayena sun tsani nayi mu Amala da bahaushe Kai ba Ni kadai ba ko su Sony aka gani da aboki bahaushe yanzu zakaji bakin Amaka don tafi Maazi Nkem kin hausawa da ma addinin da sukeyi wato musulunci don Amaka ko siyayya batayi wurin musulmi bisa Dole su Sony suka hakura da abokai musulmi sukeyi da Yan jinsin su Wanda yaren da addinin Yake Daya Sai dai Kuma Ni a wurina abin ba Haka yake ba don na Fi son nayi kawance da hausawa Kuma Ina masifar son mu zauna fira da su muna Labari don nagane su din suna da wayewa sosai kuma basa nuna min kyama Akasin wasun mu dake nuna kyama ga hausawa irin dai Amaka Ni Kuma sai ya zamo kawaye na kaf hausawa ne Kuma musulmai Ina Kuma Jin dadin taraiyar mu da su don babu kyashi bare mugunta a tare dasu sai nake Jin dadin kasancewa dasu har bana son ayi hutu don kar mu Rabu harma nakan ziyarci wasun su a gidajen su Amma fa Ni ban taba gayyatar wata zuwa gidan mu ba don nasan yadda nake zuwa gidajen su iyayen su na faram faram Dani su idan sukazo gidan mu kunya kawai zasu Sha don nasan ba karamin aikin Amaka bane ta Rako su da bulala Na kasance me lalurar aljanu Wanda ban mance mafarin cutar tawa ba wata kirsimeti ce munje gida can jihar imo kasancewar su Amaka duk Yan jihar imo ne ana ta bukukuwan crismeti mun nutsa daji Ni da kawaye na kasance wa ta me son korayen tsiro na SHIGA Ina ta tsinko duk kalar koren tsiron da yayi min sai Kuma na hango wani wuri fetal babu komai a wurin tamkar an share ko haki guda Daya Babu abin ya bani mamaki ganin daji ne babu kowa Amma Wai wurin kamar an share tas tas sai kawai naje na zauna a wurin yayin da su coma suke can saman bishiyar kwakwa zasu Ciro Mana Ni Kuma Ina Zama a wurin Nan sai naji wani Abu Yana hau min Kai tamkar Yana tilasta Ni Rufe idanu inda Kuma naji coma na kwala min Kira Wai na tashi daga inda na zauna baban ta yace Kar su sake su taka ko da kafa ne bare su zauna . Sama sama najiyo ta ban Kara sanin abinda ke faruwa Dani ba sai dai farkowa nayi na ganni Akanyar Amaka suna ta Rusa ihu Nima sai na Soma Rusa ihu inda aka kwasheni zuwa gidan Mai magani akayi ta banka min sauyoyi magani da hayaki Haka muka dawo gida ba tare da tunanin cewa akwai wats sauran matsala Akan wannan ciwon ba don magani daban akayi ciwo daban. Sai ya zamo ba a Rufe kwanan wata ba tare da ciwon Nan ya tashi ba Kuma Haka akayi tayin magani daban ciwo daban har waje dai an kaini Amma babu wani sauyi sai bankar maganin bature nakeyi da neman sauki Akan ciwon tashin aljanu Wata Rana a makaranta kawata sumayya Ahmed yabo ke fada min da ciwon nawa ya tashi a makaranta cewa ciwona fa ba na Asibiti bane warakar shi tana cikin Alkur ani don dai bamu sani bane Sai naji kwarai na gamsu da maganar sumayya Ahmed don inda ciwon na Asibiti ne ai har waje an fidda Ni Amma dai ana Nan jiya iyau Da na komo gida nake fadawa Amaka cewa ciwona ba na Asibiti bane sai tayi maza ta tareni tana fadin.... "To na Ina ne? Na fada Mata yadda sumayya Ahmed ta fada min wai warkewar tana cikin Alkur ani ai kuwa ban Rufe bakina na Amaka ta gaura min Mari tana Sababi............... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan labarin na daban ne Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 21//22 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa gareku Anty Aisha Bara'u Anty Maryam Bara'u Anty Zabbau Bara'u Anty Binta Bara'u Fatan ALHERI ga Uwa ta haj Sa adatu lawal Ade Allah ya Kara sutura da lafiya Kyautar wa ga iyalan haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria mazan su da Matan su Allah ya daga lamarin ku 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ............."Ba Zaki Rabu da masu sallah ba ko? Bance Miki Kar ki kuma Zama kusa dasu ba? Ta fada tana zaro min idanu inda nake turo Baki gaba Ashe bansani ba na Kara bawa Amaka haushi sai kawai naji ta zaune Ni akaina da manyan kuturanta Wai naji nauyin ta akaina Ta kuwa zaune Ni Tana fadin "Ai tunda dai na Raba ki da mutanen Nan mayaaudara masu tallatawa mutane Addinin su ko Bai nema ba matukar Baki Rabu da mu Amala dasu ba to Zan saka wuka in yanke kine matukar na karajin kinyi magana da masu salla Sai da ta gaji don kanta kafin ta daga Ni Amma ko kadan banji Ina son in Rabu da kawaye na ba sai dai duk yadda Amaka zatayi sai dai tayi Haka na ci gaba da Rayuwa cikin ukubar matsalar jinnu sai dai duk Ranar da ciwon ya motsa sai dai mu tare a Asibiti mu Kashi kudi mu dawo A lokacin da na Gama karatu Maazi Nkem ya siya min mota me tsada na Soma SHIGA gari a kuma wannan lokacin ne na some tsanar zuwa coci inda Amaka ke Mika kokon barar ta ga malaman cocin Akan ciwona inda ake ta min ADDU A yayin da Maazi Nkem Yake bada kyautar kudi da Kaya ana kawowa coci yayin da Ni Kuma naji kwata kwata bana son zuwa cocin a duk Ranar lahadi Amaka Kan tusa Ni gaba muje wani lokacin ma a mota ta muke zuwa inda Kuma na Soma kalula da karyar ciwona tun Amaka Bata farga ba har dai ta gane son zuwa ne banayi ta Kuma ce ban Isa ba bisa Dole take tasani gaba muje Amma da mun Isa sai na fakaici idon ta sulale na bar cocin na koma gida A cikin wannan lokacin ne Kuma na samu adimition din jama ar Legos a matakin farko inda Kuma muka sake hadewa da kawaye na na baya wato sumayya Ahmed yabo da fauziyya Yar Amana muka sake kullewa fiye da Baya Zuwa wannan lokacin na farajin Ina Sha awar irin kayan da suke sakawa musamman hijabi da dogayen Raguna amma na San ko giyar wake Nasha ban Isa na Kai su gida ba bare Amaka ta gani bare na kaisu jikina Na dubi sumayya bayan mun fito daga lacca nake duban ta cikin Sha awar shigar ta ta atamfa da katon hijabi harma da Nikabi "Wai sumayya kin taba fada min ciwona bana Asibiti bane na Alkur ani ne ko? Tace Eh haka ne Justina hakan NE kawai zakuyi ki Rabu da ciwon ki don aljanu ne fa suke shigar mutum Kuma sunfi shigar Mata mafi yawan lokuta Matan dake yawan Zama babu Dan kwali ko Babu suturar kirki Suma Wai Sha awar Matan suke ku Kuma ba zaku iya saka irin kayan mu ba Nace "To Ni yanzu yaya zanyi da Alkur ani in warke ne sakawa ake a Ruwa koko yawo Zan Rika yi dashi? Sumayya tayi Dariya tana fadin "A a karanta Miki za ayi sai kiga kin samu sauki Amma fa sai Allah ya yarda kinsan komai Allah ne ke yin shi Nayi shiru don nasan Amaka ba zata yarda da hakan ba Dole nayi shiru Amma a Raina Ina tunanin Yaya za ayi ayi min karatu? Haka na kasance Ina ta fama da ciwo in ya tashi Nasha maganin bature in Kuma lahadi tayi na sulale Amaka tayi ta Sababi tana fadin ba zanje ayi min ADDU A ba to Allah yasa asake wata lahadin bakije ba kiga abinda zai faru Ban damu ba Ni fatana kawai na samu Wanda zaiyi min karatun Nan don kullum abin ci gaba yake akasin da nake kwanciya ciwo yanzu bugeni ake na Fadi tamkar matacciya magani kuwa babu Wanda ba a Nemo min ba Amma babu wani ci gaba Mun Isa jihar imo inda ake bikin Yar sarkin imo wanda ya kasance sarkin garin mu Kuma Wanda Maazi Nkem Yake matukar girmamawa tamkar ya duka ya bi ta kanshi ya wuce . Wannan girmamawa da Maazi Nkem yakewa sarki yasa suke matukar mutunci Wanda Nima na samu SHIGA a gidan nashi harma na zamo kawar onye wato Amarya don Haka da bikin ya tashi Maazi Nkem ya kwashemu har Amaka muka tafi halartar bikin gidan sarauta a jihar imo Kai tsaye fadar sarki muka Fara Isa mukayi gaisuwa inda sarki ya dafa kaina Yana yabawa kyauwuna Yana Kuma yi min ADDU A cikin yabawa da nuna kauna Aka Soma gudanar da shagalin biki irin na gidan sarauta inda Amaka ke can wurin matar sarki suna ta gudanar da nasu shagalin Nima Ina cikin su onye amarya wadda na ji Wai Dan sarkin aber ne zata Aura Duk wasu Kaya na shagalin bikin an tanade su an Kuma Rabawa mahalar ta bikin Wanda Nima na samu kasona na wata Riga doguwa Mai hannun shime wadda aka Dan Rufe kirjin ta da wani less me shara shara Kuma aka tsuke kasan ta ta yadda ta bayyana kuturin Wanda ya sakata Wurin da za ayi taron katon filine Wanda ya ke a cikin gidan sarautar inda Kuma aka hada wasu manyan manyan itace aka hada wuta tana ci ganga ganga . Shi dai wannan taron sunan shi agare amarya ce za a bawa namijin tantabara shi Kuma Angon abashi macen tantabara su fito fili inda wutar Nan take ci idan Amarya ta taba sanin wani namijn kafin Angon nata to tantabarin hannunta zai mutu idan kuwa Bata taba sani kowa ba to na tantabarar hannun Angon nata zata mutu.............. Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan Labari daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 23//24 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Allah kayi musu Rahama kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH madaukakiya da dukkan musulmin duniya Yabawa ga masoyan Rubutun Gidan iko musamman masu comment sannun ku da kokari son so 🥰 Tukwici ne ga Anty Amina maman muhmd da Anty A'smau maman maama 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 .............Muna tsaye a filin Ina hagun onye dake Rike da tantabarar ta yayin bici ke ke damanta yayin da shima Ango Peter yake tare da abokanshi yarima Gibson Yayan Amarya Wanda ya zuba min ido Yana kallo na abinda na tsana kenan Hatta Ahalin gidan sarkin sun fito filin don su ga yadda Wannan taro zai Kare Amma fa fuskar Uwar Amaryar cikin tsoro da zullumi don in har ya kasance yarta ta taba sanin wani namijn to karshen abin kunya ne a garesu Kuma abin kunya ga sarki da Ahalin gidan sa ace Yar gidan shi ta lalace kafin Aure don Haka kowa ke cikin taraddadi domin ko in har aka samu akasi shima Angon ba zai taba Auren ta ba don Haka acikin filin ma ba iyayen Amaryar ne kawai ba har da Ahalin gidan su Ango Peter kowa zuciya na bugawa musamman uwar amarya A gefe na kuwa bana tare da komai sai nishadi don bikin ya kayatar Dani Kuma wannan Al ada tana burgeni ko Babu komai dai zai zaburar da Yan Mata kame kansu ko don irin wannan Rana da suke gudun fallasa ban sani ba ko don Ina tare da kewaye hausawa ne masu nuna min watsewar da ake a Jami a da Kuma na cikin gida yasa wannan Al adar ta burgeni? Ko ko dai don bana Ra ayin watsewar ne ? Oho Amma Kuma da yawa daga cikin yaren namu suna tur da Allah wadai da wannan tonon Asiri don da dayawa daga cikin Yan Matan dake Rasa budurcin nasu su Samarin ne ke batasu da Romon bakan su zasu Aure su wasu Kuma Yan uwan su NE na jiki ke karbe musu budurcin da ko mu muke girmama matar da takawo wa mijinta shi a gidan shi batayi saken da ta Rasa shi tun a waje ba Kuma shi wannan tonon Asirin ba Wai sai a irin gidan sarauta ake you shi ba ko a gidajen talakawa suna alfahari da shi don suna ganin hanyace da ake wanke zukata daga zargi Ango zai karbi matar shi babu zargin ta zaga yawo ko wani ya Rigashi samun budurcin da suke wa kulafuci. Suma Kuma iyayen ta zasu San Basu bawa yarsu tarbiyar banzaba kowa dai zai Gane Babu cuta a cikin Auren su bare zargi. Sai dai Kuma a gefe guda akwai wata Al ada da akeyi ga Ya'yan gidan sarauta musamman namijin da ke jiran gado wato yarima shi Kam idan zaiyi Aure Koda kuwa Yar gidan talaka ce zai aura sai anyi wata banzar Al ada wadda nake tsinewa a Raina don ba karamin haushi take bani ba har nake ganin in da nice matar da yariman zai Aura ba Zan taba yarda ba sai dai komai zai faru ya faru Wannan Al ada kuwa da na Kira banza kuwa itace ba za a taba daura Auren su da matar da Yake so ba sai sunyi gwaji Wai shi Dan sarki ba zai Auri mace ba sai wadda aka tabbatar da zata haihu don Dole ne yadda aka haife shi shima ya Haifa Kuma kamar yadda zai gaji mulkin gidan su shima sai ya bar Wanda zai gajeshi shiyasa ma ake ganin Dole ne ma ya haihu Kuma ba zai taba Auren matar da Bai sani ba ko ba zata haihu ba shiyasa ma suka bullo da Al adar ba za a taba daura Auren su ba sai an kawo yarinyar da zai aura din Koda kuwa tana wata kasa ne sai an kawowa yariman ita ya kwanta da ita tsayin wata uku zata yi a dakin shi tamkar matar shi idan tayi ciki a cikin wannan lokacin na watanni uku to shikenan sai maganar Auren su ta Mike a Dora sanwar Aure ya danganta da yadda suka tsara bikin wata ta haihu a dakin yariman wata Kuma sai ta Tara Yara fiye da biyu ko uku kafin ayi shagalin bikin wasu ma har haihuwa biyar suna yi kafin Auren. Idan kuwa mace tayi wata uku a dakin yariman Bata samu ciki ba to sai akara Mata wata uku wata shida kenan idan tayi wata shida babu ciki to wannan ba zata haihu ba Kuma duk yadda suke son juna Dole zasu hakura ya Nemo wata Ni kuwa sai nake ganin kamar ba ayi hikima ba wurin yin wannan banzar Al ada shiyasa ma naji na tsaneta ba kadan ba Ashe ban sani ba kaddara ta zano Dani a cikin wadan da wannan lamarin zai sako ciki ba Muna tsaye a wurin wutar da na Gama tabbatar sai da aka Gama tsafeta don in ba tsafi ba ta Yaya daga kawai mace ta Rasa budurci don an Bata wata tantabara ta Rike ta Zo gaban wuta ba saka tantabarar akayi a wuta ba sai Kawai tantabarar ta mutu? Dole ne akwai tsafi da sihiri acikin Lamarin Wata tsohuwa me amsa sunan kakar onye ta wurin Uwa ta fito hannun ta da wata yizga ta Soma zagaye su onye amarya da Ango Peter dake gaban wuta tana kada yizgar hannunta me kama da jelar doki sai da ta kewaye su sau ba adadi kafin Suma suka Soma zagaye wutar dake ci harshen ta na kokarin lasosu inda Allah ya fidda onye kunya Bata taba sanin wani namijn ba sai Peter inda tantabarin hannunta ya mace aka Kuma cilla shi sama Amma ya dawo kasa a matsayin matacce amma ita tantabarar hannun Peter da aka cillata sama sai ta tashi sama firrr abinta sai wuri ya kaure da tafin murna da sowa inda Ango Peter ya daga Amarya onye sama Yana juyi da ita inda Uwar Amarya tafi kowa murna da Jin dadin fita kunya da ace an samu matsala to da har gidan sarkin Sai sun fice sun barshi amma yanzu har kyauta sai iyayen Ango da shi kanshi sarkin Sai sun Mata kyauta kuwa ta girma da kasaita Wai ta iya tarbiya Ango Peter Yana Rike da onye Yana juyi da ita a sama kafin ya sauke ta aka saki kidan Duma inda Kuma fili ya kaure da Rawa sai dai wani abun mamaki Ango Peter Yana dire Amaryar shi onye sai kawai naji anyi sama Dani ana juyi Dani inda naji wani tsoro ya kamani inda na Soma laluben wanda yayi min wannan Aikin idona ya fada Akan yarima Gibson Yayan onye wato yarima me jiran gado sai Kuma fili ya Kuma daukar tafi da sowa me tsanani abinda yayi matukar bata min Rai ya Kuma yi matukar faranta Ran Amaka da Maazi Nkem Kan kace me? Sai ga sarki da kanshi da matar shi mamar su yarima Gibson har ma da su Maazi Nkem da Amaka har ma da mutanen Arziki sun Rufu Akan mu suna zaba Mana Ruwan nairori yarima Gibson Yana sabe Dani ana zuba Mana kudi wuri na Kara ksurewa da sowa da tabi Aguje Naga wasu mata dake hidimtawa a gidan sarautar sun karaso a gareni dauke da wasu murjanai na garari suna daura min a hannu da wuyana har da kafafuna Abunda ya Kara bani haushi Wai duk na meye wannan abun da suke min ? Kuma meye dalilin wannan dagawar da yarima Gibson yayi min alhalin Amarya ce kawai akewa hakan kamar yadda Peter yayiwa onye?.......... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan Labari daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI😂 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 25//26 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga yan uwana Yaya shamsu Bara'u Yaya murtala Bara'u Yaya Sulaiman Bara'u Yaya isma il Bara'u Yaya Yusuf Bara'u Yaya Ibrahim Bara'u Fatan ALHERI har kullum gareku masoyan Rubutun Gidan iko kune gidan iko Baki Daya tunda kuke yinta 🥰 Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ...........Gibson ya zuba min ido tamkar yaga wata bakuwar halittar da ta bayyana a gareshi yanzu wadda Bai taba gani ba. Abinda ya bakan ta min Rai don bana son wani namiji ya tabani bare shi Gibson irin daukar da yayi min har hucin nunmfashin sa najiyo Akan fuska ta Nima na zuba mishi nawa manyan idanun muka SHIGA kallon kallo inda na SHIGA fasalta suffar yarima Gibson kyakkyawan mutum Wanda shima ya fita daban a cikin Ahalin gidan su duk kuwa da kyauwu irin na Ya'yan sarkin to yarima Gibson ya zarta su don shima kamar ba Dan Nigeria ba fari ne tas har yellow yellow yakeyi ga cikakkiyar suffa ta maza da Bakin gashin Kai da kwantaccen saje da manyan idanu da gashin idanu masu kyau Kai karshen magana dai irin namijin Nan ajin farko A yadda onye ta taba sanar Dani Ya'yan sarakunan da suka so yarima Gibson basa kirguwa Amma shi yace duk basuyi mishi ba Wai har wata Yar sarki da ta so shi ya kita mutuwa tayi saboda tsananin son da take mishi Kuma kasancewar ta ya daya tilo a wurin ubanta da ta mutu ubanta yace tunda yarima yayi mishi sanadin Yar shi zai ga abinda zai faru don ba zai taba yarda son shi ya kashe mishi yarshi ba saboda kiyayyar da Yake Mata to shima zaiga abinda zai faru. Babu Wanda ya dauka furucin wannan sarki zai Zama matsala sai da yarima Gibson ya samu wadda Yake masifar so wata yarinya ce itama Yar gidan sarauta wadda suka so juna kamar su hadiye kansu Amma da akazo Kan gwajin da sukeyi na sai matar yarima tayi ciki ko zata shigo gidan shi da sunan matar Aure sai aka samu matsala domin ko sai da ta shafe watanni shida babu ciki babu Alamar shi inda a kace babu maganar Aure Dole Kuma a Rabu Amma soyayyar da sukeyi wa juna ta Hana su yarda da wannan daddadiyar Al ada tasu inda kuma Suma iyayen suka CE Dole ne a Rabu kowa yaje ya samu Wanda zai haihu dashi Son da Gibson yajeyiwa budurwar shi yasa ya kwanta ciwo Mai tsanani Wanda ya haifar mishi gagarumin ciwon zuciya Wanda kadan ya Rage ya kwanta Dama wato mutuwa Abinda ya dauke hankalin yarima Gibson daga Kan duk wata mace da zai kalla da sunan burgewa ko yaji zuciyar shi ta amsa Akan ta har ma ya Daina tuna zaiyi Aure Nan gaba sai gashi kwatsam kallo Daya yayi min ya manta da ajiyar da yayiwa mata wadda ake watsarwa a maliya Azahirin gaskiya yarima Gibson bashi da wata makusa ta kowane fuska gashi dai kyakkyawa ajin farko gashi jinin sarauta gashi Kuma Mai tarin dukiya me Kuma yayi saura? A fuskar wasu kenan wasun ma kuwa irin su Amaka da Maazi Nkem Wanda suke cikin farin ciki da murna yau su kuwa wace irin sa a ce dasu da har suka haifo Yar da zata taka gidan sarki da sunan matar yarima Gibson? Inda Kuma muka samu sabanin Ra Kenan don Ni ko ga farcen yatsana banji yarima Gibson ba bare ya burgeni a ido har yayi nasarar SHIGA zuciya ta inji Ina son shi ko kusa Haka Kuma ko Alama Ni ba Zan taba yarda ayi min wannan banzar Al adar da suke tutiya ba badon ba Zan iya yarda ayi min ba tunda Ni dai ko hannu na wani namiji Bai taba Rikewa ba sai dai don kawai bana Jin son yarima Gibson a Raina ba Kuma Zan so shi ko da kuwa mutanen garin Legos da imo zasu Kare Na fincike daga Rukon da Gibson yayi min Ina Shirin barin wurin ne naji wasu Mata da na lura suna suka daura min murjanai din Nan ne suka dauko Ni Dan das suka nufi cikin gidan sarautar Dani inda naji haushin su ya Kara kamani Ina Shirin balbale su da masifa ne Naga sun shige dakin matar sarkin wato uwar su Gibson da onye har tsakiyar dakin ta Wanda ya gaji da kayatuwa da kayan kawa da ado irin na sarauta Kan kace ? Suka shigo fito da wasu Kaya na daban suna Shirin saka min inda na Gane sun Raina min wayo tunda har suke Shirin kwabe min Riga gani zaune Na Mike a fusace Ina zuba masifa suna bani hakuri suna sunkuyar da kawuna kamar wasu munafukai sai ga Mah wato matar sarkin itace ta sani nayi shiru ta Kuma nunawa Matan Nan kofar fita da hannunta suka kuwa fice suna sauri ita Kuma ta Soma saka min kayan Wanda ta Kare da Rataya min wasu murjanai a wuyana da Kuma Dora min wasu a kewayen gashina Sai ga su Amaka sun shigo wadda ke ta murna da Jin Dadi Ni Kuma na Rasa Gane duk ana me ake min wannan tarairaya? Haka biki ya Kare Amma ba tare da Ni ba don an hanani SHIGA cikin yan Mata Wai na fita a layin su Ban tsinke da wannan lamarin ba sai da muka tashi tahowa inda aka lodo kayan akwatuna na garari da kasaita aka hado mu dasu tare da dukiya Mai yawa Wai kyauta tace daga yarima Gibson Kuma Yana Nan Zuwa mu gana ko ince mu fahimci juna Duk wannan Abu da Yake faruwa ban San komai akai ba sai da muka Zo gida naji labarin da Amaka ke fadawa Yan uwana su Sony da Emmanuel Wai Ni din na shigo Duniya a sa a inda yarima Gibson ya ganni ya Kuma zabeni a matsayin matar Auren shi Su Sony ma murna suke son suna ganin Ni Kam bayi Dace tunda Zan haifo princess in Kuma Zama matar 🤴 Dukan da wannan magana ta Amaka tayi min har ciwon Kai naji Yana sauko min ta Ina Ni Zan iya yarda da wannan abubuwan da na Dade da tsana na bikin Auren Yan yaren mu? Kuma ma Ni babu wani Gibson a Raina bare kaunar shi Sai kawai na kudirewa Raina da zuciya ta Koda za ayi me ? Ba Zan taba Auren wani Gibson ba ni ai ba Yar sarki bace su kuwa basa Aure sai Ya'yan sarakuna to yaje ya Nemo wata Yar sarkin amma ba Ni ba don kuwa banayi bana kamar inayi............... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin Nan daban yake da sauran Kar ku sake ayi Babu ku Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 27//28 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Iitattafan Gidan iko Jan kunne Wuka a makoshi Zan fasa kwai Sai A lahira Mugun kulli Matar sarki Dukkan su published ne Amma an dawo da Zan fasa kwai da sai A lahira online Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Wanda har abada bani da kamar su Allah kayi musu Rahama da gafara kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH Uwa ta ta kaina haj Habiba Abubakar magaji Yar Adua Allah ya Kara lafiya da nisan kwana Mai Albarka 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ...........Ina zaune cikin tafasar zuciya da Bakin cikin wannan Al amari Wanda su Amaka da Maazi Nkem ke ta fama yaya ta maganar musamman Amaka da take ta faman Kiran waya tana fadin a Taya ta murna Wai zanyi Aure a gidan igwai wato gidan sarauta ko da ya ke ba Amaka kawai ba hatta Maazi Nkem ma sanar da mutane Yake Aure na a gidan igwai din inda Ni Kuma nake ta ganin wautar su Nasha mamaki da aka bude akwatunan da yarima Gibson ya Rako Ni dasu domin kuwa kayane irin na gidan sarauta tare Kuma da tarin murjanai da kayan Ado Amaka sai kakabin kayan takeyi tana murna ita da Maazi Nkem Da Ranar zuwa coci kuwa tayi Amaka ba ta boyewa fastor komai ba har ta nemi a yi mata addu a yarta ta SHIGA gidan igwai da kafar dama in da Kuma fastor ya tambayi Amaka sun dai sanar da igwai matsala ta ta aljanu ko? Tace A a ba su fada ba yace to su fada musu don Kar suce an cuce su idan Gibson Yana Sona a Haka ko acan sai suyi min magana tunda lalura ce Da Amaka ta dawo Bata boyewa Maazi Nkem yadda sukayi da fastor ba inda su duka cikin su ya duri Ruwa don suna ganin idan Gibson yaji ba zai Auri me cutar aljanu ba sai kawai sukayi mursisi suka ki fada Ni kuwa tunda na kudurtawa Raina da zuciya ta ba zan Auri Gibson ba to Haka nake nufi banayi bana kamar inayi sai na shiryawa zaman jiran inji wata magana da ta danganci batun Auren mu da Gibson don in fashe fashewar da komai zai tarwatse Zuwa wannan lokacin na Gama yarda matsalar ciwo na tana saga Alkur ani kamar yadda sumayya ta fada min sai kawai na SHIGA laluben ta Yaya hakan zata faru? Sai kawai na Soma da Rufe tsiraici na tunda ta fada min harda shigar tsiraici ke jawowa mutum aljanu Dama Ina da less less da atamfofin ma kawai dai nafi son shigar kana Nan kayan NE irin su English wear da sauran su don Haka sai na Fara da saka less da atamfa Ina Kuma sirkawa da kana Nan Wata Rana na dawo daga makaranta Ina tafe a mota ta sai na kunna Redion motar abinda ban Faye yi ba ko da kuwa Zan kunna din to CD ne Zan saka naji cred debit ko 2 pac ko dangogin su amma a yau sai na latso cenal din FM inda Kuma najiyo ana Rera Kira a cikin wata murya Mai dadin sauraro sai dai ba muryar ce ta ja hankali na ba irin abinda naji Yana ratsa zuciya ta wato karatun kanshi naji Ina so Gaba Daya na bawa karatun Nan hankali na da nutsuwa ta har na karaso gida Ina muradin karatun Nan Kuma bana son ya Kare don Haka da na Zo parking space din gidan mu ban fito ba sai nayi zamana A motar Ina sauraron karatun Ina Kuma Jin wani Abu na keta zuciya ta Yana SHIGA har Yana sauko min da wata nutsuwa ta musamman wadda ban San abinda ya kawo min ita ba ko da Yake ba zance ban San abinda ya kawo min ita ba tunda Bai wuce wannan karatun ba Sai da awa Daya ta cika kafin aka janye karatun Wanda banso ba Dole na hakura na Kuma kashe Redion na fito na SHIGA gida na samu Amaka tana fadin Ina na tsaya yau ban dawo Kan lokaci ba? Nace Mata a makaranta ne aka tsaida mu wani gwaji Washe gari da ma sai da na kunna Redion ko zanji karatun Nan amma sai na Tara's suna want program Wanda yasani Jan tsaki na kashe Redion Bayan mun fito ne nake tambayar fauziyya ko tana da karatu a wayar ta ta tura min? Ta tambaye Ni wane irin karatu nake so? Nace Mata na Alkur ani nake so. Ta Jima tana kallo na kafin tace min Ina dashi amma me zakayi dashi? Na fada Mata jiya ne naji shi a mota Kuma yayi min Dadi shine nake so don nayi ji duk lokacin da nake so Sai ta shiga yi min bayani akan Alkur ani da maganin da yakeyi Wai har maganin kunci da Bakin ciki yakeyi Kuma shi din maganin kowace irin cuta ce Kuma waraka ne Ba Zan karyata hakan ba don Ni da kaina naji ajikina don Haka sai na ce mata kwarai na yarda da hakan don Nima naji hakan. Nafisat Rabi u Umar itama duk muna tare a wurin Kuma taji duk abinda muke magana akai sai tace Amma kuwa Justina iyayen ki ba zasu damu ba idan sukaji kina Jin karatun Alkur ani? A garin mu fa gombe akwai wata yarinya da iyayen ta suka kashe ta don kawai tace tana son hijabi tana kuma Sha awar yadda ake sallah sai kawai suka kashe ta Wai gara ta mutu da dai tace salla tana burgeta kenan zata iya shiga wata Rana. Nabi nafisa da kallo don Ni nasan nafi waccan yarinyar da aka kashe hadari don Amaka ko taraiya da masu salla Bata son nayi bare Kuma addinin su ya burgeni ai idan akwai abinda yafi kisa to sai Amaka tayi min shi Amma sai nayi maza na cewa nafisat Babu matsala Hikimar da nayi itace hearphon nake sakawa a kunne na in saurari Kira ata yadda nake so babu Wanda yasan me nakeji Abin mamakin da na kula dashi Ni da kaina shine yawan mafarkai da nakeyi Wai gani Ina kallon mutane suna salla wani lokacin ma Zan ganni a cikin sahun salla anayi tare Dani Kuma Wai wani gari ne da ba Legos ba don mafi yawan mutanen da muke sallar tare dasu farare ne tas masu dogon gashi Matan su Sanya da hijabi da Nikabi mazan kuwa sanye da fararen doguwar Riga sun Kuma yafa wani farin mayafi ko ja ko Baki kowa dai da kalar dake kanshi Idan na farka sai inji Ina begen wannan wuri da na ganni in Kuma ji muradin inyi salla amma Kuma Ina tsoron Amaka ta ganni Dole nayi shiru Kwana biyu Ina sauraren karatun Nan Ran Nan sai tsautsayi ya samu waya ta ta lalace gashi Kuma muna cikin strike wato yajin aiki bare fauziyya ta sake tura min karatun Alkur ani Dole na wuce kasuwa na siyo CD masu yawa na kawo mota na zube idan fita ta Kama Ni na saurara idan kuwa babu kowa a gidan sai na dawo mota na kunna na saurara Tsautsayi Wai in ya wuni baya kwana Ranar Nan Yaya na Sony ya dawo gida babu kowa ya iskeni na kure volume cikin Kira a ta malamin da har na hardace sunan shi wato sudais na kasa kunnuwa Ina saurare har ban San lokacin da Sony ya shigo ba sai da Naga inuwar mutum akaina na farga dashi a tsaye ya zubo min idanu Yana Huci tamkar zai hadiye mu Ni da motar tawa inda Kuma na San kashina ya bushe don gashi can ma ya kwarmatawa Amaka da Maazi Nkem kafin Nan ma nasan shima ba kyale Ni zaiyi ba sai naji a jikina............ Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran Gidan iko shine sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 29//30 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga haj Lubabatu Ali Mai chanji marubuciyar Amaryar zamani akan Rashin mahaifin ta Alh Ali Mai chanji marnar gangare Allah yayi mishi Rahama yasa kwanciyar shi hutawa tare da namu iyayen duka dama dukkan musulmin duniya Fatan ALHERI ga mahaifiyata haj Rabi atu Abubakar magaji Yar Adua Allah ya Kara nisan kwana Mai Albarka Kayatar wa gareku masoyan littafin GARWASHI hakika kun cancanci yabawa Gidan iko na godiya Allah ya Kara daukaka 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ...........Da sauri na Danna stop na kashe Gaba na na balli balli ganin mazuran da Sony ke min Kafin ma na fito daga motar sai ji nayi ya shakoni ya finciko daga motar Yana kwada min wani Mari da faskeken hannun shi me kama da faranti "Wato dama abinda Amaka ke Fadi akan ki gaskiya ne har kin Soma kawo Mana su cikin gida? Ganin da gaske Yake zai jibge Ni ya barni da ciwon jiki don bashi da kirki wurin duka shiyasa ma Amaka ke bashi go ahead din ya jibgeni in nayi laifi akasin Emmanuel Wanda baya da zafi akan komai kuma ko laifi nayi akace ya jibge Ni afuwa ma shi Yake nema min akasin wannan marar kirkin Sony don Haka nayi nufin kwacewa in gudu Amma sai na Gane Bai Rike Ni don ya saki ba ya Rike Ni ne don ya Nadi banza don Haka nasoma kicin kicin kwacewa shi Kuma ya Soma kwada min Marika Yana masifa inda nayi RAM da hannun shi na Galla mishi uban cizo Wanda ya tilas ta shi sakina na kuwa auna aguje na fada daki na maido sakata Ina kuka Inajin shi Yana zuba Ruwan tijara Wai su zamu kunyata duk kokarin su Amaka da Maazi Nkem da suke Rike da addinin mu sau da kafa sai nice shegiyar da Zan nuna musu addinin nasu ba na gaskiya bane? To yau sai ya karya min kafa guda Inajin shi nayi shiru don nasan sai su Amaka sunfi shi shafawa akan Lamarin Ni kuwa gani da wata irin zuciya wadda duk abinda take so to son shi kawai takeyi . In nace so to Ina nufin so Haka Kuma duk abinda take ki kinshi take da gaske in nace ki to ina nufin ki shiyasa naji Arai na su daiyi su Gama Amma babu Mai canja min Ra ayi na ai wuya Bata kisa sai kwana ya Kare Sony Yana zaune falo Yana fada madam Amaka da Maazi Nkem suka shigo suka same shi Yana tijara maazi Nkem ya tambaye shi abinda Yake wa fada ya Kuma kwashe abinda ya sameni inaji Amaka ta daki kirji tana fadin Kai me kake cewa my son? Ya sake maimaita mata abinda ya ji ya Kuma gani sai kawai Amaka ta kwasa aguje ta Soma dukan kyauren dakin tana fadin na bude ko ta karya kyauren ta shigo wato banji maganar da ta fada min ba ta Kar na sake nayi kawance da hausawa shine ma don na Raina ta na shigo mata gida da Yan wake waken masu salla na kunna Mata ? Wato na Raina ta ko? To na fito Naga yadda zatayi Dani Da dai ta gane ba Zan bude ba sai ta juyo Kan Sony ta Rufe shi da duka tamkar shine yayi Mata laifin Wai don me ya barni Bai yi min laga laga ba? Ya nuna Mata cizon da na Galla mishi Wanda yake digar jini Shi kuwa Maazi Nkem ya gama mutuwa daga zaune ba Kuma komai yake takaici ba sai don in igwai yaji halin da nake ciki Dole ne su fasa Aure na su Kuma sun kwashi Rayukan su sun Dora Akan Aure na gidan igwai Duk Ina Jin su nayi bakam don nasan bude dakin daidai Yake da tarbar damusar dake Jin yunwa Amma Kuma ga mamaki na sai naji ana sako makulli za a bude sai Kuma na tuna Ashe fa akwai safaya na makullan don Haka sai nayi maza na fada ban daki na Rufe inda Nan ma ban tsira ba Amaka ta cakumo Ni ta fito Dani sai Huci takeyi inda Kuma na Gane Kashi na ya gama bushewa Shake Ni Amaka tayi da duka karfin ta tana fadin "Gara dai na kashe ki da kija min abin kunya ace yata ta koma salla Ni kuwa wace Riba naci ? Saboda kin Raina Ni na hanaki gaisa wa da su shine kike shigo min gida da Yan wake waken su kina kunnawa to fada min addinin da Kika zaba? Fada min nace ! Ta fada da Amon murya Ni Kuma naji Shaka sosai don na yarda na Amince Amaka kasheni din zatayi don bata shakeni don na Rayu ba A a sai dai don ta Mikani lahira Wai ko zata huta da Bakin cikin da nake Shirin jawo Mata Maazi Nkem ne ya dakawa Amaka tsawa Yana fadin "Zaki kashe min yarinya ne ko Yaya? Da sauri Amaka ta sakeni inda Emmanuel ya kamo Ni ya taso Ni Yana min sannu Maazi Nkem ya Rufe Amaka da masifa Akan kokarin kisan da take Shirin yi Maazi Nkem ya kamo hannu na ya wuce Dani dakin shi Yana maido kyauren dakin ya Rufe kafin ya fuskance Ni "Gaya min abinda kike nufi shin Zaki bar addinin mu ne na iyaye da kakanni Koko Yaya? Sanin da nayi mishi shima ba son hausawa da musulunci Yake ba sai na kadaa kaina Alamar A a karatun ne dai yake burgeni sai kawai naji shima Maazi ya Rufe Ni da duka Amma na makale ajikin shi Ina fadin kuskure ne ba Zan sake ba kafin ya saurara min Yana Huci A Ranar Hana Ni abinci sukayi Kuma sukace idan suka sake ganina da hausa man ko waye to Zan fadawa Yan garin mu Kasset din CD CD dina kuwa duka Amaka ta kwaso su ta saka guduma ta dandake su Redion cikin motar ma sai da ta saka Sony ya cire ta Wai taga gidan uban da Zan Kuma sauraran karatun Allah cikin ikon shi aka janye strike muka koma makaranta na samu su fauziyya da sumayya na cewa fauziyya ta tura min karatun Nan ta kuwa tura min masu yawa naci gaba da Jin abuna ta cikin hearphon inda Kuma naci gaba da mafarkai Akan wannan kayataccen wurin muna salla wani lokacin ma har littafi nake ganina na bude Ina karatu inda Kuma wata da mukeyin sallar a tare tace na Daina saka kayan da nake sakawa Allah baya son irin Haka in Rika saka irin nasu wato doguwar Riga in Kuma Rika Rufe jikina don Yana da matukar Daraja in son samu ne ma in Rika Rufe fuska ta Nikabi Abinda ya bani mamaki bayan na farka daga wannan mafarki shine matar da taba Ni wannan shawarar ba fa da hausa tayi maganar ba ba Kuma da yaren mu na Igbo ba da wani harshe Mai matukar Dadi Kuma maganar sai ya zamo tamkar irin karatun da nake saurara kalar maganar Tata Amma Kuma Wai na fahimci abinda take nufi sai kuma na yanke shawarar siyo kayan Nan da matar Nan ta shawarce Ni Amma Kuma sai zuciya ta tambaye Ni to ta Ina Zan Soma saka kayan Nan? Ba dai Nan gidan da sony da Amaka suke ba? Ashe kuwa da sauran kallo Ana Haka NE auren Sony ya taso muka SHIGA sabgar bikin shi da Amaryar shi sisiliya wadda ta Jima tana dakon son shi Na SHIGA kasuwa don na siyowa Amaka Ashoke Wanda zata Rabawa kawayen ta tunda tuni dama aka tanadi less din Ashoke ne babu don Haka na nufi kasuwa cikin mota ta inda tun kafin na Kai na Soma Jin kaina Yana juyawa Alamar dai ciwona zai tashi kenan don gaskiya tunda na Soma sauraren karatun Alkur ani ya Dade Bai tashi ba don Haka a yau sai naji Alamar zai tashi kamar na koma gida na fadawa Amaka ba Zan iya zuwa ba Amma Kuma sai Naga ai na kusa cimma kasuwar kawai na karasa in yaso in na suyo Mata Ashoken in baro motar na hawo ta haya don na tabbatar ba Zan iya tuko ta na nadawo ba in yaso ko Emmanuel ne yazo ya daukar min Haka kuwa na karasa kasuwar cikin shigar kana nanun Kaya da dogon takalmi high hill sai dogon gashi na da ya Sha gyara sai kyalli yake har ya sauko Kan kafada ta Na fito daga motar Ina karajin kaina Yana juyawa . Abinda kawai na sani na Kuma Rike shine na San lokacin da na maida kyauren motar na Rufe daga Haka ban Kuma sanin abinda ya faru kaina ba anan aka makenk na Fadi kasa a tsakiyar kasuwa. Kuma wannan lamarin shine mabudin bude kofar kaddarar da ta hado Ni da mahaifin ku Umar faruk har zuwa lokacin da kaddara tayi Aikin ta ta kaddaro kaddarar da faifan kaddarar ya bude har zuwa inda ake a yau a Kuma yanzu................. Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿🥰 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 31//32 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga Ahalin gidan ma aiki da duk masu kaunar shi da gaskiya suka Kuma bisu da kyautatawa Tukwici ne ga Hadiza ta maman Aliyu da hafsat da Zainab sani maman jinio da Zahra Fatan ALHERI ga Maryam Bara'u Mero Allah ya gyara min ke 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 .. .......Ina kwance shame shame a tsakiyar kasuwa inda aljanu na suka buge Ni na Kuma Fadi babu Alamar motsi ko numfashi Amma abin mamaki babu Wanda yabi ta kaina bare ya kawo min dauki koda ta mayar Dani inuwa ne Amma kowa sai ya wuce Ni abin shi Amma Kuma ga faruk abin ba Haka Yake ba don Akan idon shi hakan ta faru ya Kuma jira yaga Ni ko wani daga cikin yarena ko zai tallafa min Amma kowa sai dai ya kalleni ya wuce don Haka ya karaso a kaina ya Kuma fahimci matsalar tawa ta bugun iska ce don Haka sai ya Soma tofe Ni da ADDU OI cikin ikon Mai sama kuwa sai naji tamkar ana zuba min Ruwan sanyi Wanda ya farkar Dani daga wannan wahalar. Na bude idona Ina kallon shi inda naji Yana karanto wani karatu Wanda na taba Jin irin shi a Bakin Mai karatun Nan wato sudais. Ga mamaki na Sai naji tamkar ana zare min wani Abu marar Dadi ajikina ana kuma mayar min da wani sasaanyan Abu Mai sanyi har zuciya ta "Sannu yayi min cikin sanyin murya na amsa da yauwa Ina kallon shi da irin kulawar da ya bani alhalin shi din ba yarena da addinin na Daya dashi ba Akasin su Wanda na fito a yare da addinin na dasu din Basu kula ba sai Wanda Amaka Bata son nayi mu Amala dasu to Ni kuwa saboda Allah ya za ayi na mance da hausawa ko na Daina kulasu alhalin su din suna min karamci tamkar dai a cikin su nake? Ya dauko min key din mota ta da na watsar a can gefe ga Kuma Yar jakar post dina da kudina suke ciki itama na watsar sai shine ya tattaro min su ya bani Yana fadin Zan iya tuka motar ? Na ce mishi ba Zan iya ba ya Kuma tambaya ta me Zan siya? Na fada mishi na Kuma nuna mishi shagon da Zan SHIGA idan na koma gida Zan turo Yaya na ya daukar min motar. Ya Miko min key dina da jakata na karba Ina mishi godiya da irin taimakon da yayi min yace babu komai Wai yiwa Kaine Na SHIGA shagon da Zan siyi Ashoken Ashe Wai shine Mai shagon na siya na biyashi inda yayi min sauki ya Kuma fada min gaskiya Akan Wanda na Fara zaba cewa quality din su ba na sosai ba inda ya nuna min Mai kyau na Kuma siya muka Rabu Ina Mai farin cikin haduwa ta da shi da Kuma irin taimakon da ya bani ba tare da ya duba koni wacece ba ya taimake Ni babu kyama babu duba addini R Tun daga wannan Rana sai nayi sabo da Umar faruk sabo kuwa Mai yawa har ta Kai duk abinda Zan siya to wurin shi Zan siye shi kuma na lura Yana da sani sosai ta fuskar addini sai na Kara kusantar shi don na Soma fada mishi abinda nakeji Akan addinin su shi Kuma Yana fada min ita Rabauta in Allah ya Rabautar da bawa ko a ki ko aso sai yayi .Kuma a yadda ya fahimci lamarina mahaifa na basa so Kuma su iyaye biyayya ake musu a duk abinda sukayi umarni . Haka yayi ta bani shawarwari Akan nayiwa iyayena biyayya Bai taba fada min na bijire ba sai naji ya Kara burgeni lamarin shi Kuma ya tsaya min Arai na kasa mantawa dashi Musayar lambar waya da mukayi dashi wani lokacin nakanji kamar na kirashi Amma Kuma sai naji Yana min kwarjini tsoro Kuma ya kamani ince to in na kirashi in ce mishi me? Duk yadda naso na yakice shi na kasa Domin kuwa sai mafarkin shi nakeyi Wai muna salla a tare dashi a kayataccen wurin Nan Ban Ankara ba naji zuciya ta taja Ni na afka a soyayyar Umar faruk Wanda na kwana biyu ban je shagon shi ba don Ina tsoron yace baya Sona tunda Ni din ba jinsin sa bane kuma ba yaren shi bane me yuwa ma yafi Amaka tsanar mu Amma Kuma nasan daga gareshi dai ba Zan samu hakan ba sai dai ko ta bangaren iyayen shi don na tabbata yadda Amaka Bata Sona da hausawa Haka shima Umar din Koda shi ya Soni to iyayen shi ba zasu Soni ba kasancewar Ni din ba yaren shi bace tuna hakan da nayi sai ya jefa Ni a cikin Rudani Ban boyewa kawayena ba na makaranta sai da na fada musu abinda Yake damuna Akan Umar faruk inda sumayya tayi ta min dariya tann fadin "Kai Justina kin SHIGA hannu gaskiya Amma Kuma lamarin naku da mamaki don yazo ne akarkace don in har naki iyayen sun yarda da Auren musulmi to shi nashi ba zasu yarda ba Amma kiyi ta ADDU A in da ALHERI Allah ya tabbatar ya Kuma kawo hanya Mai sauki ta tabbatuwar lamarin Ita kuwa nafisat Rabi u cewa tayi da ace dai na musulunta ne abin zaizo da sauki Amma Kuma Yaya nake ganin iyaye na zasu karbi musulunci na? Sai Kuma na hango Ranar da za ace wa Amaka gani na musulunta bana ko shakka bindigar Maazi Nkem zata dauko ta harbeni don ita da kanta take fadin zata kasheni ne in dai nace Zan biyewa hausawa bare Kuma ace na SHIGA musuluncin da ta gama tsana a Duniya. Ban boyewa nafisat yadda Amaka ke tsanar musulmi ba ita Kuma tace gaskiya Akwai matsala. Na SHIGA damuwa ba kadan ba inda duk suka Gane na Gama kamuwa da soyayyar Umar faruk inda Kuma waya ta tayi Kara na duba sai nayi Arba da sunan Umar faruk Yana yawo Akan screen din waya ta na yi saurin nunawa nafisat nace Mata gashi Nan ma Yana kira tace dauki Kar ta tsinke shima dai ga Alama ya kamu sai dai kafin na daga har Kiran ya tsinke Amma ba a Jima ba wani Kiran ya sake shigowa na daga Ina mishi sallama ya Kuma amsa Yana fadin Ranki yadade Justina shikenan kin barni ina ta jaje har gidan Redion BBC? Nayi murmushi nace ai kuwa baka Zo gidan mu ba da baka Kai Cigiya ba..... "To ai ban San gidan naku ba tunda Baki fada min ba don Kar na kawo Miki ziyara...... "Idan kuwa zaka Zo me zai Hana na baka address? "To abani address din sai nazo tunda ke kin min yaji. Murna ta cikani na Kuma tura mishi address din ya Kuma fada min Ranar da zai Zo zai kirani Kawaye na sun bani shawarwari Akan kame kaina da Kuma kiyaye abinda zaisa Umar faruk ya janye jikin shi akainan don yadda sukaji muryar shi da kalaman shi kamar Babu yaudara Ni Kuma sai na fada musu sanadin haduwar mu dashi da irin taimakon da ya bani inda su duka sukace zasu so ganin shi don ya burgesu da Haka dai muka Rabu na dawo gida Ina ta dokin Ranar da Umar zai kirani yace min gashi Nan Zuwa don ban San irin tarbar da zanyi mishi ba Kwana biyar da yin hakan sai ga Kiran nashi ya shigo waya ta na dauka Ina gaishe shi Ina Kuma tambayar shi Allah ya sa dai yau zai Zo? Ya Kuma tabbatar min da kwarai kuwa yau zaizo da misalin karfe biyar na yamma nace to Ina jiran zuwan shi Karfe biyar kuwa na bugawa sai ga manyan motocin gidan igwai yarima Gibson ya karaso kawo min ziyarar ba zata a zatona bakona ne Umar faruk don Haka na fito tarbar shi cikin murna Amma Ina zuwa sai Naga Akasin hakan wato yarima Gibson cikin SHIGA ta nuna shi din jinin sarauta ne saboda kurewa da cinyewa ta fannin kyau da gayu inda Kuma naji kamar na fasa ihu ko in Fadi kasa In ta Rusa kuka ....... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰💃🏿😂 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 33//34 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Godiyar har kullum ga Ubangiji Wanda ya yarje min komai cikin sauki da fuwacewa salati da Aminci da taslimi ga Annabi MUHD S A W da Ahalin gidan sa madaukaka da duk Wanda yabisu da kyautatawa Tukwici ne ga Hafsat Bara'u ba Duhu Allah ya bada ilimi me Amfani Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ..........Duk murmushin da yarima Gibson ke jifata dashi na Jin Dadin ganina hakan Bai sa naji nayi farin cikin ganin shi ba sai ma wani turiri da naji zuciya ta nayi don Ina ganin zai kawo min cikas akan zuwan Umar Ina tsaye Ina kallon yadda ake faman tattare mishi Riga da shimfida mishi dogon kafet din da zai taka shi kuma Yana ta jifa na da murmushi Ya karaso Yana me Rungume Ni Yana fada min wasu kalamai Wanda Rashin sa ar da ya tako Bai taba burgeni ba bare naji son a zuciya ta bare Kuma kalaman shi suyi min Dadi. Ya saka tafin hannun shi cikin nawa hannun ya Runtse Yana ci gaba da rada min kalaman kauna a kanne na Yana Kara Rungume Ni tsam a jikin shi yayin da tsanar shi ke Kara zagaye jikina da zuciya ta na Soma zare hannu na daga nashi hannun Ina Shirin zare jikina naji Amaka ta iso tanawa Gibson barka da zuwa tamkar zata mayar da shi cikin ta ta sake haifar shi inda Kuma naji waya ta ta dauki tsuwwa na duba na kuma ga Umar faruk ne na daga da sauri inda Yake fada min ya karaso Gaba na yayi masifar faduwa don lamarin ya Zo min da Zaki da madaci da ace Amaka Bata karaso ba to da na sulale na fice zuwa wurin Umar faruk Kuma yadda na kula tana ta bare baren murnar zuwan Gibson idan nace Zan fita komai zai iya faruwa Kuma banajin Zan iya Barin Umar a waje na shanya shi don zuwan wani Gibson da bana kallon shi a wata tsiya sai Wanda ya nemi katse min kwanciyar hankali da shiga Rayuwa ta ta karfi da yaji Na daga wayar Umar Ina mishi sannu da Zuwa na Kuma tambaye shi ya karaso? Yace min gashi a kusa da gidan mu nace gani Nan Zuwa Amaka ta kwada min harara Wai ban sauki Gibson ba na barshi a tsaye . Na SHIGA laluben yadda za ayi na sulale na fita wurin Umar ba tare da Amaka ta nemi kunya Tani a gaban Gibson ba sai Kuma na Gane in ba tarairayar Gibson nayi ba to kuwa ba Zan samu na fita ba don Haka sai nayi nufin karrama shi Na sauke shi a falon saukar Bakin Maazi Nkem na Kuma kawo mishi abin tarba dangin Ruwa da nau ikan namo mi da abinci irin na girma da kasaitacce irin barasake Gibson Amaka kuwa sai barin jiki take tana fito min da Kaya na garari Wai inyi kwalliya don har da murjanai ta fito min dasu Wai nayiwa yarima Gibson kwalliya Nayi hikimar cewa Amaka Zan karbo abu wurin grace wata yarinya ce Nan makociyar mu inda Amaka tace nayi maza na dawo nayi wanka Kar ya tsaya jirana Aguje na fita na hango Umar a bangon gidan su grace Yana tsaye cikin fararen Kaya Wanda suka Kara fito da kwarjinin shi naji kamar na Rungume shi don tsabar kyan da yayi min a ido Bakine kalar fatar jikin shi ba Kuma Baki sosai ba irin kalar Nan da ake cewa cokulat kala shi ba Baki ba shi Kuma ba fari ba wankan tarwada. Dogo ne sosai Kuma Mai murdadden jiki Yana da fadi a kirji da Kuma dogon wuya sai idanun shi matsakaita da tattausar suna irin ta labarawan Maiduguri wato shuwa sai sajen fuskar shi da hancin shi mikakke dodar a Kan dakalin fuskar shi sai Kuma wani annuri a goshin sa Mai Kama da an diga mishi bakin Abu a tsakiyar goshi Na karasa gareshi Ina murmushi nayi mishi barka da zuwa shima yayi min murmushi Yana kallon tsakiyar idanu na kunya ta kamani na sunnar da kaina kasa. "Shikenan Kuma sai na Rabu da jinki Justina? Na tsinto maganar tashi Akan kaina "Kayi hakuri ban San zaka nemi Ni bane Na fada inajin kallon Nan nashi har jinin jikina. "Gani to na neme ki Kuma Zan gaida mama da Baba..... Rudewar da nayi har shi ya fahimci hakan don Haka sai nace mu SHIGA gidan su grace zanyi wanka yanzu Kuma na kawo mishi Ruwa Muka SHIGA gidan su grace na sauke shi a parking space na karbo fararen kujeru wurin maman Grace na Kuma fada Mata na sauki bako na a parking space tace ok Na fito na aje Mana kujerun na Kuma ce mishi ya bani minti goma Zan dawo Na fice zuwa gida na fada wanka na fito na saka kayan da Amaka ta fito min dasu ita da kanta ta SHIGA tsara min kwalliya kasancewar ta kwararriya a fannin make up don har kanti ta bude inda ake tsantsara kwalliyar kanti. Ta daura min murjanai ta Kuma fesheni da turare kala kala na nufi inda Gibson Yake Amma Kuma zuciya ta tana wurin Umar Wanda nayi fatan ace wurin shi na wuce Kai tsaye Amma Kuma ban Isa ba koda kuwa na Sha giyar wake Fadawan dake gadi a kofar inda Gibson Yake suka sunkuyar da kawunan su Wai don kar su kalleni na wuce su Ina Jan tsaki Araina Na shigo na same shi Yana kishingide irin kwanciyar jinin sarauta Amma Yana ganin na shigo ya taso ya tarbeni Yana bani hot kiss abinda ya ke bakan ta min Rai shi Kuma Yana ganin ta Haka NE zai nuna min yadda yake jina a zuciyar shi Muka tsurawa juna ido muna kallon juna a tsakiyar ido kafin ya zaunar Dani dab dashi na Kuma kula da bai taba komai ba don Haka na Soma service din shi da nau ikan abin da aka Tara mishi Kuma ya dan taba kadan daga cikin abinda na zuba mishi Yana ci kuwa yana kallo na "Ina fatan dai ke kikayi girkin Nan? Ya fada Yana Ruko tsintsiyar hannu na na kada mishi Kai Alamar bani nayi ba sai ya mayar da Naman da yakai Baki Yana gutsura kamar Dan yaro Ya yagi tissue paper Yana goge hannun shi da Bakin shi ya Dan kurbi lemun Dana zuba mishi a tanbulan sai kawai Naga ya kwanta Akan cinyoyi na Yana Riko hannun na Yana matsawa Yana Kuma kallon idona Yana fada min nayi mishi girki kafin ya tafi don yaji irin dandanon hannuna Wai ta dandanon girkin mace ake ita din wacece a cikin Mata Maganar tashi ta bani haushi ba kadan don Haka na tambaye shi yaushe ne zai tafi? Yace 4:00 na yamma na dubi agogo Kuma 2:51 ne don Haka nace to ya jirani na SHIGA kichen yanzu nayi mishi girki don har coice din shi na tambaya don nasan na Gama samun damar da nake ta neman samu ta zuwa wurin Umar Na fito nacewa Amaka yace girki na Yake so nayi mishi Amaka tace to na SHIGA kichen Mana nayi mishi me shegen dadin da zai manta da kunnen shi Na SHIGA kichen Ina hada slinder na kuma Dora tukunya da sauri Kuma na fice zuwa wurin Umar Wanda nayi dabarar fito mishi da Ruwa da lemu har da nama Muna ta fira Yana fada min shi Yana so ne yayi min silar da Zan Rabu da ciwona na bugun aljanu don abin Yana Ranshi idan ya tuno da yadda abin ke samu na. Ban boye mishi ba na sanar dashi yadda nake son karatun Alkur ani da Kuma mafarkan da nake yawan yi Wai Ina salla har na Fara tunanin yadda Za ayi na taka tsanin da Zan zamo Ina yin sallar Nan shi Kuma Yana Kara fada min girman iyaye da hakkin su na ayi musu biyayya hakan ya Kara jefa Ni cikin Rudani don na Rasa ta Ina Zan Fara? Mun Dade muna fira har bamu San lokaci yaja ba sai da Rutu Mai aikin gidan mu tazo take fada min wai sanwar da na Dora ta kone har ta so haifar da gobara don Haka na biyo Rutu muka taho inda na iske Amaka ta cika ta batse kadan ya Rage ta fashe muna shigowa ta wurgo min wata matsiyaciyar harara tamkar idanun ta zasu zubo kasa................. Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 35//36 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga Anty Jamila Yusha u ma aikaciyar Rema sokoto Anty j Allah yakara daukaka na gode kwarai da kaunar Rubutu na Allah ya shirya ZURIA Fatan ALHERI ga mahaifiyata haj Rabi atu Abubakar magaji Yar Adua Allah yayi Miki sutura cikin suturar da yayiwa ma aiki S A W🥰🥰🥰🥰🥰 Yabawa ga haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria har muddin Rayuwa da numfashi Allah yasa har gidan ALJANNAH 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 "Wane irin wulakanci ne kike Shirin yi Mana? Cewar Amaka da tayi furucin a fusace. Dama kin shirya kunya ta mu ne a cikin Ahalin igwai? Yaron Nan ya Sanya ki Aiki kin Kama kin fice har ya Soma gajiya Wai me kikeyi ne agidan su Grace din? Na tura Baki gaba Alamar Raina ya baci da tijarar da Amaka ke min saboda wancen shashashan wato Gibson Jin ban Bata amsa ba yasa ta tubi Rutu tana tambayar ta Wai me nakeyi agidan su Grace din? Rutu ta bude Baki Wai zata fadawa Amaka abinda ta Tara's inayi wato fira da Umar Amma hararar da na watsa mata ne yasa tayi gum da Bakin ta ta SHIGA kame kame Ni Kuma nayi cikin kichen Ina duba ta adin da girkin nawa ya jawo Amaka sai masifa take min kamar zata Rufe Ni da duka Ni Kuma duk Raina ya baci saboda firar da Umar yake min tafi komai muhimmanci a gareni gashi kuma Amaka ta Rabo Ni daga gun sa ita a Dole sai na tarairayi Dan gidan igwai.... Muna a Haka Amaka na fadin sai na sake Dora mishi wani sabon girkin sai ga Gibson ya fito da niyar tafiya don har biyar ta kusa bugawa Amaka ta Soma fadin zai tafi Bai jira sun gaisa da Maazi Nkem ba Kuma baici abincin ba? Yace yayi maraice ai zai dawo gaishe da Maazi Nkem din girki na kuwa ai gajen hakuri ne yayi tunda Zan Zo zaman dakin shi kafin bikin Auren mu ai zaici Ya Riko hannun na muka bishi wurin da motocin shi suke Yana Rungume Dani a gefen kafadar shi Yana Rada min wai nayi mishi Rowa ta girki na Wanda yaso ya dandana yaji zakin hannu na Wanda inda yaji zakin hannun nawa to da kwana yayi Amma yanzu zaije ya fadawa igwai Yana son nazo nayi mishi Zaman daki sai yaji girkin nawa... Nayi maza na hade fuska don nasan abinda Yake nufi da zaman dakin da zanje nayi mishi wato dai inje in samo ciki Wanda zai tabbatar da Auren mu kamar yadda Al adar take abinda kuma nakejin ba zai taba yuwa ba Kuma zai yuwu ba don Haka nace mishi "Ba Zan Zo yi maka zaman daki ba karma kace Haka in dai girki ne zanyo shi na sako maka mota akawo maka shi har gida....... Ya katse Ni Yana murmushi "Ai ba girkin kawai nake so daga gareki ba my love ganin da nayi Miki a yanzu ya nuna min kuskuren da nayi Ina da kamar ki Amma ace na barki kina nesa Dani sai dai nayi ta ganin ki a cikin bacci na da mafarki na? Ki saurari aike na cikin satin Nan Zaki iso min zaman dakina ya Miko min wata jakar fata me zanen Ado irin na tambarin sarautar su yace igwai ne ya ce akawo min kafin ya Kuma Miko min wata ita Kuma jakar Leda ce ta wani kamfani ita Kuma mamar shi ce tace ya kawo min shi kuma hannu na ya Kama ya saka min wani tsadadden zobe na zinariya Mai Daraja wadda itama ajikin zoben tambarin sarautar tasu ne amma anyi wa zoben harafi guda biyu na farkon sunan mu wato j & g don Haka ya fada min shi Kuma ga tashi kyautar Nan ya Kuma sumbaci yatsun nawa bayan ya gama saka min zoben Fadawan dake biye dashi a baya suka kwashi kayan nawa suka Rike Wai su Kai min gida Har na juya Zan koma gida don hankali na Yana wurin Umar bayan nace mishi yayi min godiya wurin mama da Kuma igwai akan abinda suka bani sai kawai naji ya Ruko min hannuwa Yana min kallon tsakiyar idanu Wai Haka Zan barshi Ni ba Zan bashi abinda zai Rika tunawa Dani ba? Na bishi da manyan idanu na don ban San abinda Yake nufi ba sai kawai naji ya jawo Ni cikin motar Yana hada tsinin hancin shi da nawa inda na Gane abinda yake nufi Wanda Kuma banajin zai sameshi don ba Zan iya yi mishi yadda zai gamsar dashi ba tunda banayin shi Amma ko hakan da na Raya a zuciya ta ya juyo Koko Alamar hakan ya gani shiyasa Bai Bata lokacin jira na ba ? Oho sai kawai na tsinto bakina a cikin nashi na Kuma kasa kwacewa sai da ya sakeni Don ya so hakan. Na fito motar Ina Jin wani Abu Yana min yawo a jiki saboda irin hakan bata taba faruwa Dani ba a son Raina ko Akasin hakan irin na yau don Haka wannan Rayuwar bakuwa ce a gareni Wannan shine bankwanan da mukayi da yarima Gibson ya tafi Yana min wani kallo Wanda nakejin don ya cuceni ne ya hada bakin shi da nawa yake min shi Na kawowa Amaka kayan da ya bani da zoben shi da kyautar igwai da kuma ta mah wato uwar yarima Gibson Amaka ta Rafsa guda Mai tsananin karfi tana Rawa Wai anyi min kyauta sai Kuma ta SHIGA budewa tana gani inda Ni Kuma na sulale zuwa wurin Umar Wanda na hango shi ya fito daga gidan su Grace Yana tsaye jikin bangon gidan Ina karasowa ya Soma fadin wannan Kuma waye Haka yazo wurin ki Justina? Gaba na ya Fadi Jin Ashe yaga duk abinda ya faru tsakani na da Gibson sai ban boye mishi ba na sanar dashi shine Wai mijin da iyaye na suka zaba min.... Ya dube Ni Yana Fadin Ashe Ni Kuma igiyar Ruwa na Kama kenan Justina tunda har anyi Miki miji? Nima na dube shi nace "Kana Sona ne kenan? Yace kwarai kuwa sai dai nasan Babu ta yadda Za ayi na sameki tunda har iyayen ki sunyi Miki miji Kuma ko da basuyi Miki miji ba ba lallai ne su bani Auren ki duk da tazarar dake tsakanin mu Amma nayi nufin na fahimtar dasu idan suka ki bani Auren ki saboda tazarar mu to Kuma gashi ma Ashe an bada ke ga Dan gidan sarauta Kinga kuwa abinda ba zai taba yuwa ne ba su tada wannan alkawarin..... Nayi saurin tarar shi Ina fada mishi nifa dama ba Wai son Gibson nake ba Ni shi kadai nake so don nayi alkawarin ba Zan taba Auren Wanda muke addini Daya dashi ba sai Mai salla Zan Aura ko da banyi salla ba ina son anayin salla a gabana Kuma ma Ni gaskiya Al adun da akeyi ne wurin Auren mu ba suyi min ba da ya nemi ba asi na Kuma fada mishi ya Jima Yana kallo na kafin yace zamuyi magana yanzu na SHIGA gida tunda yayi maraice zamuyi waya. Na Raka shi har Baki hanya inda Kuma muka gamu da Maazi Nkem ya karyo kwana ya Kuma ganmu Ni da Umar sai dai da sauri nayo baya umar Kuma ya tafi abinshi Kayan da Maazi Nkem ya Tara's Amaka ta baje tana ta kambama su su suka dauki hankalin shi inda Amaka ta sanar dashi zuwan yarima Gibson Wanda ya kawo min wannan kayan sai ya Kira wayar igwai yayi godiya ya Kuma ce wa sarkin bashi gari ne sai yanzu ya dawo ya samu sako in yarima Gibson ya dawo ayi mishi sannu Ban san yadda suka Kare ba Maazi Nkem da Amaka da kayan Gibson Washe gari da naje makaranta nake fadawa nafisat da fauziyya yadda mukayi da Umar Wanda yazo takanas don ya fada min Yana Sona amma Kuma Yana tsoron iyayena mussamman da na fada mishi an bawa yarima Gibson Aurena lokaci kawai ake jira fauziyya tace gaskiya Justina Lamarin ku fa yazo da Rudani ke ba Kya son yarima Gibson su Kuma iyayen ki shi suke so Umar kike so Umar kuwa Babu ta yadda Za ayi iyayen ki su bashi Auren ki yaya zakuyi kenan? Nima abinda nake tunani kenan a Rai na Ina son nayiwa iyayena biyayya Amma Kuma gaskiya bana son Auren Gibson sai Umar Wanda Kuma na tabbatar iyayena ba zasu taba yarda da Auren mu ba Koda kuwa shi shi kadai yayi saura a Duniya Yaya zamu Kare kenan? Dukkan su sun bani shawarwari Akan nayiwa iyayena biyayya kuma na Roki Allah ya zaba min ALHERI Na dawo gida jikina a sanyaye inda na makala hearphon a kunne na Ina sauraron karatun Alkur ani Wanda na ji nutsuwa tana sauko min har ma bacci ya kwashe Ni kuma cikin Rashin sa a wayar hearphon din ta zare daga jikin wayar Wanda Ni na zare ta saboda matsewar da nayiwa wayar garin bacci ai kuwa Kira ar ta fito tar ta cikin bututun sauti na wayar Amaka dake zaune kusa Dani ta dubeni ta Kuma dubi wayar dake ta amayar da sauti cikin fusata Amaka ta fincike wayar ta kwantara ta da kasa ta watse Ni Kuma ta sharara min Mari Wanda na farka a gigice Ina zare idanu "Wato Ashe Baki Daina sauraren wake waken Nan ba ko? Nace Mata karatu ne fa ba wake wake ba.... Ta Kuma kwada min Mari kafin ta shakeni tana fadin Wallahi kasheni zatayi ba Zan jawo Mata abin kunya ba tunda dai na zabi dabi ar masu salla nace ita ta burgeni to gara kawai ta kasheni ta huta don Bata da idon duban Yan uwan ta da suka Rayu cikin addinin su Kuma Wai ace Ni Yar da ta Haifa na ce addinin ta ba na gaskiya bane gara ace ita din ta kasheni da dai nayi Mata wannan wulakancin Ai kuwa da gaske Amaka take don tun Ina iya shaida abinda ke faruwa har naji numfashi na Yana kokarin daukewa daga gabgar jikina zuwa wata Duniyar Wanda ban santa ba Ban San ya akayi ba sai naji Emmanuel Yana kwata ta daga hannun Amaka Wanda tace dawa Allah ya hada ta ba dashi ba? Sai ta Rufe shi da duka Wai shike Goya min baya don Haka gara ta kashemu Ni dashi sony kadai ya isheta Rayuwa tunda shi ai me son addinin nata ne. Emmanuel dai dayake namiji ne ya kwaci kanshi hannun Amaka ya Kuma fice ya bar gidan inda Maazi Nkem ma ya dawo yaji labarin abinda na aikata bindigar shi ya kafa min a goshi Yana fadin zai kasheni wallahi da dai ace musulunci nake kwaikwayo . Da kyar baban Grace ya Basu magana suka hakura Amma fa Nasha jibga wurin Sony sai da yayi min laga laga kafin ya barci jiki duk jini da cuwuka Amma wani abun mamaki da na kwanta bacci sai gani dai wurin Nan Ina salla har ana Miko min kyautar littafin da naga mafi yawan su suna budewa suna rero Kira a irin wadda nake so da saurare abinda Kuma yasakani kudurewa lallai sai nayi sallar Nan Kuma sai nayi karatun Nan da nake yawan saurare sai kawai na diro daga Kan gadon nayi wanka da Ruwan zafi na gasa jikina ko Mai ban saka wa cikina ba na fice daga gidan................... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunana ke cewa saduwar ALHERI💃🏿 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 37//38 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ne ga duk inda masoyan ANNABI MUHD S A W suke afadin Duniya Allah ya karawa ANNABI Daraja da wasila da fadeela Sadaukarwa ga iyalan marigayi Alh Ali Mai chanji marnar gangare Allah Ubangiji yayi mishi Rahama yasa kwanciyar shi hutawa dashi da dukkan musulmin duniya Fatan ALHERI gareku masoyan Rubutun Gidan sannun ku da kokari littafin GARWASHI na jinjina muku🥰 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ..........Kai tsaye gidan su fauziyya na nufa da dai wurin Umar nayi nufin zuwa sai nayi wani tunani sai kawai na nufi gidan su fauziyya Duk yan gidan su sun sanni muna Kuma girmama juna don Haka da na SHIGA sai da muka gaisa da kowa kafin fauziyya ta kaini wurin maman su na gaida ita cikin sakin fuska ta amsa min na kuwa ji dadin yadda suke karbata babu nuna kyama bare suyi min daukar hanci irin Wanda Amaka kewa hausawa da musulmi Amma su Babu Ruwan su Basu Kuma tallata min addinin su ba kamar yadda Amaka ke zargin Wai hausawa ne ke neman jana na SHIGA jikin su shiyasa take Hana Ni mu Amala dasu "Daga Ina kike haka Justina cikin uwar Ranar Nan? Na dubi fauziyya Ina Fadin. "Don Allah fauziyya wata Alfarma nake nema Kuma ya zamo sirri a tsakanin mu don bana son kowa yaji maganar nan Kuma ke nasan Zaki Rufa min Asiri ko ba Haka ba? Fauziyya Yar Amana tace kwarai kuwa Justina ai tsakanin mu Babu tonon Asiri ai mun wuce wannan wurin ki Kara sakawa Ranki mu fa musulmi muna da Amana fiye da zaton ki don Haka fada min abinda kike so nayi Miki Alfarma ko mamana ba zataji abinda Kika yarda Dani Kika fada min ba Zan tayaki boye sirrin ki daga Ni sai ke Sai Allah. Na Kuma gode da Kika zabeni a matsayin wadda Zaki fadawa sirrin ki. "Na ce na gode fauziyya don Allah salla nake so na Fara Amma ban San ya zanyi ba Kuma bana son iyayena su San na Fara salla shine Naga ke kadai kike fada min yadda addinin ku yake Kuma na Faye mafarkai Akan Ina salla da karatun Nan da nake yawan saurare shine kawai na yanke shawarar in Fara salla don naji zuciya ta tafi aminta da salla fiye da abinda mukeyi a cikin addinin mu ko Babu komai addinin ku ya koyar daku Adalci ya koyar daku yiwa Wanda ma ba addinin Yake ba Adalci Kuma ya koyar daku saka kaya masu mutunci ya Kuma koyar daku ibada wadda zuciya ke nutsuwa idan anyita don Haka fauziyya na San iyayena ba zasu so na bar addinin su ba Amma Ni gaskiya nafi son musulunci fiye da addinin da na gada don da shine gaskiya da ban Faye mafarki dashi ba tunda ku ai ba kwa mafarki da namu addinin ko kunayi? Na tambayi fauziyya ta Kuma kada min Kai Alamar A a basayi nace to kin gani ? Fauziyya tayi kabbara tana fadin "ALLAHU Akbar kabeeran Kai Amma nayi Miki murna Justina sai dai Kuma Ina tsoron abinda zai biyo baya idan mahaifan ki suka fuskanci kin bar addinin su don gaskiya bana son ki samu matsala da iyayen ki......... "Fauziyya na shiryawa komai Koda kuwa zasu kasheni ne kamar yadda suke fada banajin zanyi nadama da mutuwa ta ke dai taimakeni ki fada min yadda zanyi ki Kuma Rike min sirrina Kar ki fadawa kowa Fauziyya Yar Amana ta lakana min kalmar shahada tana karanta min Ina maimaitawa ta Kuma karanta min kadaitakar Ubangiji da tsarkake shi da matsayin sa shi Daya Tak bashi da abokanshi taraiya da Kuma shaidawa shi kadai Yake Haka Kuma Annabi MUHD S A W bawan ne Kuma manzon sa Duk na biya Kuma naji zuciya ta ta yarda da abinda na biya din inda Kuma fauziyya ta fada min sai nayi wanka na SHIGA musulunci da kuma yadda ake wanka idan period tazo da Kuma wankan tsarki na zahiri da Kuma na mafarki duk ta koya min yayin da ta Soma sanar Dani salla da bangarori da ke gareta irin abinda Yake Dole da Wanda akayi sauki da Wanda akayi sassauci wato farali sunna mustahabbi duka dai inda tace sannu a hankali zata ke sanar Dani Kuma in fadawa Umar shima zai taimaka min ta wata fuskar don Haka Ina gidan su fauziyya akayi sallar zuhur muka tashi fauziyya ta fada min niyar daga cikin zuciya ta Zan kudura ta ta Kuma ce na kalli yadda zatayi Alwala duk abinda Naga tayi Nima nayi. Haka kuwa akayi muka yi salla ta Kuma fada min sai na Rage saka kayan da zasu Rika fidda min part din jikina wato masu bayyana tsiraici Haka na dawo gida zuciya ta tamkar anyi Mata wanki babu komai nakeji Sai farin ciki da wani irin iska Mai sanyi Yana kada Ni sai najini tamkar bani ba don har nauyi sai naji na Rage na koma wata Yar shafal Aduk lokacin da Zan duba Inga ya Kai Wanda fauziyya tace min nake salloli sau biyar azuhur da la asar magaruba da Isha I Sai subahi kowane ta fada min lokacin su duk da tace lokacin Yana sauyawa musamman idan yanayi ya sauya irin zafi zuwa sanyi ko damuna Amma tace idan ma yanayin ya sauya zata sanar Dani Aduk lokacin da zanga lokacin sallar yayi Zan SHIGA dakina na Rufe na fada toilet nayi Alwala na zaro katon hijabi na Wanda nasiyo don salla na zurma nayi salla ta wadda duk lokacin da Zan gamata sai naji wani Dadi da farin ciki kafin na zauna Ina tunani sai Kuma in boye hijabi na kafin na bude dakin in fito Ina makale da hearphon a kunne na Ina sauraren karatun Alkur ani Mai girma Kuma Alkur anil Kareem Haka Yar Amana ta fada min sunan shi wato Mai girma Nayi Shirin SHIGA kasuwa inda Zan fanshi Alkur ani don Ina son na Fara koyon karatun sa don Haka nayiwa Amaka bankwana na SHIGA kasuwa sai da kyar na samo shi don Haka kai tsaye na nufi wurin Umar don shigar da na fito da ita daga gida ba itace na shigo kasuwa da ita ba hijabi na Yana jakata Ina fitowa na zurma kayana don Haka Umar ma da ya ganni cikin hijabin sai da mamaki ya Kama shi ya zuba min ido Yana kallo na cikin kaunar da bata boyu ba yana ta murmushi Ni kuwa kunya ta kamani ganin irin kallon da Yake bina dashi. Ya kasa tankawa sai dai kallo na yake Bai Kuma fita daga mamakin da Yake ciki ba na Kara kashe shi da wani mamakin inda na fiddo Alkur ani daga cikin hijabina nace mishi nazo ne ya koya min karatun Alkur ani. ALLHU Akbar kabeeran Ni Kuma nayi maza nace Asshhadu An Lailaha illallahu wa Asshhadu Annan Muhammaur rasulullahi S A W Umar Bai boye farin cikin da yayi ba da Kuma Jin abinda na furta Amma Kuma sai ya tambaye Ni ta Yaya hakan ta faru? Na Gaya mishi duk yadda akayi da Kuma yadda mukayi da fauziyya har zuwa abubuwan da ta fada min Akan salloli da dukkan abinda ya shafi musulunci Ni Kuma nace Zan siyo Alkur ani nazo ka Fara koya min Kuma kaima Zan Roki Alfarmar ka Rufa min Asiri Kar ka fadawa kowa Shima yayi min alkawarin Rike min sirrina Kuma yayi min alkawarin Zama min Dan uwa Kuma zai Dora Ni akan dukkan abinda ya shige min Duhu fiye da Wanda fauziyya tayi min tun daga wannan Rana ya Soma da koya min Alkur ani tun daga basmala zuwa fatiha da kula uzai Wanda tuni Yar Amana ta koya min su Kuma na iya tun da dasu nake salla Kuma yace Yana son ganin fauziyya Yar Amana don itace macen da ba zai taba mantawa da ita ba Wai don ta Kara taro mishi masoyiya . Na Rufe fuskata Ina Fadin yanzu ne kake Sona ko kuwa tun tuni? Yayi murmushi yace ai tun daga Ranar da na Fara ganinki kin Fadi na kamu da kaunar ki don a Ranar banyi bacci ba ke nayi ta gani sai dai Ina zullumin yadda Al amarin mu zai kasance sai gashi Allah da ikon shi kin zamo yadda nake Kinga kuwa ai Dole na godewa Allah na Kuma yabawa Yar Amana. Kunya ta hanani Zama na taso Ina Fadin Ni dai Zan tafi gida ya taso ya biyo Ni Wai yayi min Rakiya har bakin motata ya kawo Ni ya Kuma bude min Yana fadin Wai Baki ma fada min sunan da Kika canja ba ko ita Yar Amana Bata fada miki komai Baki ya canja na yanzu? Nace ta fada min kawai dai ban San sunan da Zan amsa bane..... "Ai na zaba Miki shi tun tuni tin kafin yau din Nan sunan ki Aminatu idan Kuma munyi Aure sai na kiraki da abin Sona kunya ta kamani inda naji lallai sunan Aminatu ya burgeni sosai na Kuma yarda sunana kenan nayi mishi godiya nace Nima zabin nashi yayi min da haka mukayi sallama Yana Kara fada min lallai gobe goben Nan na kawo mishi Yar Amana yayi Mata tukwici nace mishi Zan kawo ta kuwa. Naja motata na nufi gida Ina karasowa na hango motocin Nan da sukazo tare da yarima Gibson inda naji gaba na ya Fadi ban tsinke ba sai da na SHIGA gida bayan na cire hijabina na boye a mota na SHIGA gida na samu Amaka ta hado min akwatina Wai dama yanzu take nufin kirana don yarima Gibson ya Aiko a daukeni don naje nayi mishi Zaman dakin da Zan dawo da ciki Wanda suke fatan a zaman wata uku kadai na samo shi ba sai nayi zaman wata shida ba don Auren namu kusa kusa za ayi shi ba lokaci za a ja ba.............. . Labarin GARWASHI na kudine ga duk Mai bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰💃🏿😂 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒 Page 39//40 Hadiza Bara'u Gidan iko Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne Sadaukarwa ga dukkan musulmin duniya wanda suka yarda da kaddara suka Kuma yarda Babu Mai yi face Allah suka Kuma dogara ga Ubangiji Allah ya kabamu mafita Fatan ALHERI ga mahaifina dake kwance kushewa Allah kasaka Rahamar ka Akan sa da dukkan musulmin duniya Kuma muminai maza da Mata Kyautar wa ga Anty Aisha Bara'u Allah ya Baki lafiya yasa kaffara 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ...........Nayi turus Ina kallon Amaka da ta jido min akwatuna tamkar wadda zata bar garin gashi Kuma a yanzu babu abinda nake bukata irin sarari don na Rabi Umar na Kuma Kara sanin yadda Zan bautawa Ubangiji sai gashi Wai Amaka na fada min wai Zan tafi wani gari inda Zan kwaso zunubi Wanda Wai Zan tare a dakin wani Kato tamkar matar Auren shi ba Kuma Zan dawo ba sai da cikin shege Wanda su Kuma wannan cikin shine abin alfaharin su "Kizo Mana kiyi wanka Kika tsaya Raba Mana kallo ko ko me kike nufi ne naga bakya murna da zuwa zaman dakin yarima Gibson? Amaka ta katse Ni da fadin Haka Amma nayi shiru ban tanka Mata ba "Wai bakiji abinda nake fada bane kike min shiru? Na fa kula da take taken ki Akan yaron Nan Dan gidan igwai Banga kina Rawar jiki akan shi ba halan Baki da labarin har Mata ke mutuwa saboda son shi? "Wahala ce Bata ishi wadda ta mutu Akan shi Ni a idona Banga abin Rawar jiki Akan shi ba.... Ban Rufe bakina ba naji Mari Amaka ta kwado min "Ai dama tuni nagane abinda kike nufi akan yaron Nan to Kuma kinyi karya Wallahi sai kin Aure shi Koda Zaki mutu sakaran banza marar tunani Baki San Rabo bane Aure a gidan igwai? Yar iska ki haifo Mana princess ba alfahari bane? Tashi maza kiyi wanka na kaiki in Kuma Roki ayi Miki ADDU A ki SHIGA da sa a kina zuwa ki samo ciki ko haihuwa ba Zan Bari kiyi a gaba na ba za ayi bikin ku ki haihu a can don su tabbar da ke din irin haihuwa ce Haka nayi wanka Ina kuka na shirya aka loda Mana Kaya a mota inda Amaka ta Kira Maazi Nkem take sanar dashi Aiken da akayo daga gidan igwai na akai Ni inyi wa yarima Gibson zaman daki inda shima Maazi Nkem din ya cika da murna da farin ciki Wai zanjewa yarima Gibson zaman daki don Haka ya yi min ADDU AR inje cikin sa a Kuma Wai don baya kusa da har dashi cikin Wanda zasuyi min Rakiya don Haka da Amaka kawai muka tafi wadda ta Kira kawayen ta biyu madam go slow da Kuma maman Bose sukayi min Rakiya suna ta Kara kambama dacen da nayi na Sa ar da na tako har na dauki hankalin yarima Gibson da irin daular da Zan SHIGA sai suka SHIGA yi min fatan Ina SHIGA in samu ciki yadda Zan Kara martaba a agidan igwai Haka muke tafe suna ta santin gidan sarautar suna Kuma Kara bawa Amaka shawara Wai ta nema min maganin makiya da mahassada saboda Matan da suke son Auren yarima Gibson yace baya son su to suna iya Hana mu zaman lafiya Ina sauraren su da firarrakin su Wanda suka cika min kunne da tsabar haushi da takaici . Haka muka muka Isa jihar imo kasancewar motocin masu lafiya ne Kuma gudu suke tamkar jirgi shiyasa bamu Jima sosai ba muka Isa gidan igwai inda muka iske masu tarba sunyi dandanzon suna jiran karasowar mu inda Amaka da kawayen ta suka Soma Kara gyara min Ado na Wanda yasha murjanai Wanda sune karshen adon na gidan sarautar Suma kuma Kara fesheni da turaruka kala kala suna yafa min mayafina Wanda na janye daga kaina Ahalin gidan igwai suka suka tarbe mu zuwa dakin mah inda aka sauke mu da nau ikan abinci irin namu da ma Wanda ba namun ba irin na turawa. Har falon hutawar igwai aka kaini na gaishe shi Yana Rike da hannu na Yana saka min Albarka Yana Kuma fatan na zamo farin cikin Gibson Wanda ya zamo shi kadai ne da namiji a wurin igwai sauran Yan uwan shi Mata ne shiyasa soyayyar shi daban take wurin igwai A sashen mah muka kwana sai da su Amaka Zasu tafi ne suka Mika Ni dakin yarima Gibson dama Haka Al adar take uwar yarinya ce ke Kai yarta dakin da zatayi zaman ita da kawayen ta ko Yan uwan ta don Haka da muka shigo garin Amaka ta sanarwa kanwar ta ta karaso aka Rakani dakin na Gibson Wanda Amaka taja kunne na sosai akan karbar Gibson ko don nayi saurin yin ciki don na samu zarafin mamayar Ahalin gidan igwai yadda Za ayi hanzarin biki don ba Zan haihu a gida ba sai a gidan yarima Gibson "Allah yasa kiyi wani Abu da zai Sosa Mana Rai kiga yadda zanyi Miki wallahi don na kula sai na taba lafiyar jikin ki ko zamu daidai ta don kema nan Haka dake kin iya iskanci to Allah yasa ayi wata banji kinyi ciki ba kiga yadda nake a zahiri don Rashin mutunci Zan kera Miki har sai kinyi nadamar sani na Amaka tana Rike da kunne na take min wannan kashedin kafin tayi min wani shegen Rankwashi me tsananin zafi Suma kawayen ta madam go slow da mama Bose har ma da mama Ester kanwar Amaka duk shawarar saurin yin ciki suka bani Wai kuruciya ke damu na shiyasa ban San girman da ya sameni ba Da Haka igwai ya hado su Amaka da shatarar Arziki suka taho inda Kuma aka SHIGA yanka min talo talo na tarbar yarima Gibson zuwa dakina tamkar dai ace yau din itace Ranar tarewa ta Ina zaune Ina kallon yadda zamu Kare Ni da yarima Gibson Akan wannan banzar Al adar wadda ko da ban samu tsarkin musulunci ba ba Zan yarda da ita ba saboda Rashin sa ar da yarima Gibson ya tako ta Rashin son shi da nake bare Kuma yanzu da nagane abunda su Amaka suke farin cikin ya faru tsakanin mu ai Zina ce ita kuma Zina laifi ce Dan da Kuma aka haifa ta hanyar Zina shine shege da na nutsu sai nagane da yawan Ya'yan da yaren mu suke Haifa shegu ne Ni Kuma na kudure ba Zan taba haifar shege ba Da sauri na Mike don ganin lokacin sallar magaruba ya yi inda na fada toilet din dakin da aka aje Ni da sunan shine dakin Gibson Wanda ya gaji da haduwa da kawar Rayuwa na SHIGA na dauro Alwala na Kuma bude kayana na jawo hijabi na zurma na tada salla Ina cikin sallar ne naji an shigo Amma duk da Haka ban katse salla ta ba don na daura damarar nunawa kowa irin addinin da na zaba amutu ko ayi Rai................... Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669 Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunana ke cewa saduwar ALHERI💃🏿🥰