rk ****ZURFIN CIKI :-2**** ta dafa kafadata tana cewa kayi haquri mubarak na sani kana son nabeelah sannan itama tana sonka,sai dai kuma kayi kuskuren rashin bayyana soyayyarka gareta a sanda ta bukaci hakan,nayi kokarin dai- daita tsakaninku amma naji tsoron kada mutane suyi tunanin na aurar da nabeelah ga d'ana ba bisa son ranta ba sai dai bisa dole kasancewar ta girma a hannuna.......haka kuma yanzu bazan saka kaina cikin wannan matsalar taku ba amma zan goya muku baya bisa dukkan shawarar da kuka yanke,idan kuna nemana ku sameni a fallow*** na kalli nabeelah idona cike da hawaye na fara magana kamar haka'nabeelah ina sonki,kuma ina kaunarki, sai dai na kasance cikin irin mutane da sukan boye sirrin zuciyarsu,kiyi haquri ki gafarceni,nasan nayi miki laifi...nagode ki tashi ki tafi allah ya bada zaman lafia sannan allah yasa shine mafi alkhairi gareki........na miqe zan fita daga motar,ta kamo hannuna ta zaunar dani tana magana hade da wani kuka mai tsuma zuciya gami da sa tausayi kamar haka'yamubarak da farko na yarda kana sona amma yanzu na gane cewar soyayyar batayi tasiri a zuciyarka ba tunda har ka yarda zaka haqura dani kan wani ya aura,lallai na yarda baka kishina baka tausayina irin zaman da zanyi tare da wani namiji wanda ba kaiba,ka sani cewar zuciya ba zata aminci rabuwa da kaiba,jikina na haramtashi ga dukkan wani d'a namiji idan ba kaiba dan haka na qudiri niyyar mallakarka ka ta wane hali,yamubarak kayi kokari ka soni kamar yanda nake sonka,yamubarak kada ka bani kunya'*** na share hawayen dake zuba kan kuncinta,na kama hannayenta na kwantar da ita bisa kirjina,nabeela h ki amince da soyayyata gareki kada ki zargeni da komi sai alkhairi,nabeelah ina sonki kuma nine mijinki da yardar allah,da sauri ta tashi daga kan kirjina ta dafa kafaduna tana kallon fuskata,ta sumbaci goshina sannan ta rungumeni kan kirjinta tana cewa hakika farincikina ya karu,burina ya cika sannan alheri ya tabbata gareni.....amma *menene mafita? *da wane zance zamu tunkari abba? *sannan kuma lokaci yana da karanci garemu.... Na kalli nabeelah dake kan kirjina nace zaifi sauki muje wurin kawu aminu mu shaida masa halinda muke ciki...ni nasan me zan fada masa kuma zai yarda. *kai tsaye na tuka motar zuwa gidan kawu na tarar ya gama cin abinci yana gindin bishiya yana hutawa..bayan mun gaisa ya cigaba da magana kamar haka'lallai daga ganinku akwai matsala dan naga alamun damuwa gareku, shin ko baki son auren ne? Ya tambaya' na fara da cewa gaskiya kawu ita nabeelah ba wanda take son za'a bata ba,kawu yace wannan zancen banza ne dama shi yasa suke boye min to wallahi wannan maganar babu ita,ku tashi mu tafi gidan.... Na tuka mota har kofar gidan muka shiga shi kuwa kawu tun daga kofar gida yake ta fada..yana shiga su mama suka fito suna gaisuwa amma ko amsawa bayyiba ya cigaba da cewar'maganar auren nabeelah babu na soketa yanzu zata fada mana wanda take so kuma goben zan daura mata aure dashi...nabeelah ta kada baki tace'ya mubarak nake so' kawu yayi dariya yace au to ai shikenan ta kwana gidan sauki kuda dan iskanci abin na gidane ma kuke bata lokaci,to ai ni yanxu xan daura auren idan yaso kuje chan kuyi ta bikinku,sannan baba ya shigo yaji meke faruwa amma ba yanda zaiyi da kawu dan yasan halins doe qura ya zama waliyina shi kuma waliyin yamubarak aka daura auren*** take yamubarak ya daukeni muka tafi gidan kunshi daga nan ya kaini nayi kitso muka wuce gidan aunty nafeesat nayi wanka na saka rigar atamfa kaina ba dankwali na fito gareshi,wow nabeelah amma kinyi kyau,ya kamo hannu daga inda yake zaune gefen gadon,ya sumbaceni har saida numfashina ya dauke,ya kwantar dani kan gadon ya fara cire kayan dake.......hakika ban taba sanin haka yamubarak ya iya soyayyaba sai yau,lallai da tuni nayi asar miji,haka muka kasance cikin nuna kaunar juna har zuwaN CIKI book 2 part 1 ZURFIN CIKI book 2 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:05 Abba kwance kan gado,dare yayi nisa amma shi ya kasa bacci sam.saboda matsalar da yake ciki yanzun. domin kuwa matar shi in yaga bazai iya ba sai ya sawwake mata,amma maganar auran ummi koda Alhaji bai goya mishi ba bazai iya guje mata ba. "yanzun menene mafita?"ya tambayi kansa,wata zuciyar ta ce, "kayi shiru tamkar baka ga wannan takarda ba,tunda ba wanda yasan ka gani." a fili ya ce,"haka ne." ya ci gaba da tunanin kila ma yanxun ya janye kudirinshi,tunda yaga ummin bata da kan gado. don yaga rubutun yayi shi ne tun ranar da aka haifi ummi,ko kuma ranar sunanta. tunda gashi har da sunan ummi a jiki.mafita kenan yayi shiru.wata zuciyar ta ce,"in ko kayi haka kayiwa Alhaji da ummanka adalci? koda yar su ba yar adam ba ce bai kamata ka gujeta ba.ko don albarkacin son da suka nuna maka. shin da ummi ta kasance mai jin magana da nutsuwa,kuma mai tsananin kyau zaka gujeta? Kada kayi zaton Alhaji yayi kudurin aura maka yarsa ne don yasan zata zama mara ji,kayi nazari. haka Abba yayi ta tunani har asubah tayi,amma hukuncin da ya yanke shine yayi shiru. sai dai ya janye batun rabuwa da matar shi,don yasan yana sakinta zai zama mijin ummi,kai batun nan hadiye ma cikinshi shine mafi dacewa. dunkuna masu kyau yayi wa matarshi saboda cin suna.haka yayi wa dan siyayya daidai karfinshi,ya kawo ma umma. Taji dadi sosai nan ahj ya iske su, shima ya shiga dakin umman ya xauna ya ce a dauko masa abinci nan xai ci yau.ya dubi abba, babana nayi sautun raguna xuwa qauye nace xa a siyo nmanya.abba ya ce biyu?umma tace hakan yayi.abba ai tuwan girma miyarsa nama, aja rago daya xiqal a shiga wannan gida da shi? abba yace,me xai hana tunda ban musu qaryar arxiki ba sun san mu talakawa ne.ahj yace xancanka dutse bacna,amma maganar ummanka ita xa a bi, sannan xa a sai buhun shinkafa da cefane a kai musu.ana gobe suna abba da abokansa suka dira gidan da ragunan da kayan mai jego da na yaro sannan ga kayan abinci. sun samu anty a gidan,ta musu tarbar mutunci.da yake abba xana waya da ita,ya fada mata komai ta sani.hjy zainu da taji kukan raguna ta fito,anty tace dan Allah momy kada ki musu magana,kin ga shi da abokansa ne.da qar ta samu ta turata sashin ahj,shi kuma murna yayi yace aje a daure su.zainu tace ahj menene na numa farin ciki sai kace ba ma cin nama?can ba xa a ka kada ba dan kawai shagalin sunan, sannan tace harda shinkafa suka kawo sai kace muna yunwa? nana take ya hade rai tare da cewa,zainu kada dai ki ce min kin sa an dawo da yarinyar nan gidan ne dan ki kashe mata aure?tace haba dai. ya ce to hir dinki dan bansan in kuma jin irin xantukan nan yayi ma matarsa daidai arxikinsa. mu kuma mu ma yarmu da jikanmu gwargwadan arxikinmu,in ya fito daga gun mai jegon ki turo min shi,sbd mu ji in da xa a yi sa sunan.tace ina xa ayi in ba nan ba?ya dube ta an taba haka?ki dai turo minshi.ta taba baki sannan ta wuce.lkcn da ta leqa dakin abba da abokansa suna xaune,abba yana ta fama da danne dannen waya,domin tun da suka shiga ya qi ko kallan inda bishira take bare danta.tace bishira ki eada musu in sun fito ahj na san magana da su.ta wuce ba tare da jiran jin amsa ba,ko amsa gaisuwan da abokan abba suke mata bata yiba.bishira ta kalli abba wanda tana hankalce da shariyan da yayi mata,tace kaji abin da momy tace?sai lkcn ya dubeta me tace? yayi maganar ne cikin tsare gida.dadynmu yana san ganin ku. bai amsa ba,sai kurun ya tura mata jakar kayanta,ki duba,ta xaxxage dinkuna ne na gani na fada masu kyau,duk da xannuwan ba masu tsada ba ne kala uku atamfa daya shaea daya sai kuma leshi.sai ko kayan yaron.ta dube shh an riga an sai mana kayan fitar sunanmu.ahmad ya dube ta wannan din baki so? tace ni bance ba.abba yace ku tashi muje.tace ina san magana da kai.ya ce kiyi maganarki.muktar yace kuxo mu fita ta dauki yaran tare da miqa mashi ta ce ina lura da kai rabon da ka dauke shi tun randa aka haifeshi,alhalin mu kuma yana nan yana hana mu baccin dare.kai kana can kana baccin ka.ta fadi haka ne cikin sanyin murya.ya amshi dan tare da cewa ai gara ya hanaku bacci tunda kunqi ku kaishi gurin babanshi.ya tsura ma yaran ido,wata qaunan dan ce take shigarsa.ta matso jikinshi.abba ya kalli furkarta,ita ma kallansa take,ta ce yanxu ko dan murmushin ka bana gani.yace,in da kina san gani da baki dawo ghda ba.yaci gaba da cewa na sha mamakinki bishira,da har xa ki yarda ki dawo gidanku ba da ixinina ba. kuma tun kafin ki haihu sai da na fada miki ba za ki zo gida ba.Ta ce To Abba mony ce ta ce sai an zo. Ya ce shi kenan ku zauna. ya mike mata yaron ta amshe shi ta kwantar ta kama mishi hannu. Abba wane suna ka sa masa? ya ce Sunan Alhj babba. Da sauri ta saki Hannushi . Sunan 'yan da? ya kalle ta Na zaci zaki ce suna mara ma'ana,tund da ne da sauki. ya fice. Haushin hali irin na Bishira ya ke ji.dn son shi yasan tana matukar sonshi,amma bata son yin biyayya ga abn d yake so. Ya samu su Mktr sannan suka shiga gurin Alhj ya tambaye su in d za a sa sunan,Abba ya ce a masallaci kusa d gidn babnshi ne za a yi addu a. Amma tuni an sa wa yaro suna Sulaiman.sunan babana. Alhj ya ce Madalla Allah ya raya mana shi, ba sai mun zo ba dn yanayin sanyi ne. Nan dai Abba d abokansa suka tafi suna yabn Alhjn. An ci sunan shima Abba shi d abokansa sun yi walima da Azahar. matar abokinshi Bala ita ce suka bai wa girkin ta yi masu. Mai jego taci gaba d wnk. Abba kan leka su lkc zuwa lkc,kusan dk lkcn d yaje ba su cika rabuwa d dadi ba sbd mgnr d hjy zainu kn datsa mishi. Umma shi ma bata yi fushi ba tana leka su dk d rashin sakar mata fuska d mai jegon tare d mahaifiyar keyi. Ummi tana tafe tana 'yan tsince-tsincenta,kmr yadda ta saba,sai ko taga sim,take ta yarda dk wani abu d t samu t dauki Sim din. Gefen zaninta t samu ta kulle,sannan ta tafi,cikin jakr mkrntrta t saka.wata rana ta dauki wayar umma ta shige daki,ta bude wayar ta cire sim din ta saka wanda ta tsinto a cikin zani ta soke wayar ta fito soro.Jikin dakin yaya Abba a bakin kofar ta dauki lamar Abba da ya rbt sbd masu zuwa nemanshi tana kira taji wayr tana ringing. Ta kashe tana ta dry,hk tayi ta yi wa Abba Flashing dg nan tayi gidn du Amina kawarta,tana ba wa Amina lbrn abn d ta ke wa Abba. Ta ce Amina nsn yanzun hk yana cn yana jin haushi,shi yasa ki ka ga ina murna.Ta ce in ya gane fa?Ummi ta ce Ai tsintar sim din nayi,Umma kuwa ba za ta san na dauki wayarta ba,domin yaya Abba da Alhjnmu kawai suke kiranta. Amina ta ce Yadda za a yi ki kira shi ne in ya dauka sai ki make murya ki canza suna. Ummi ta ce Tab,dn in ci duka. Amina ta ce Dalla cn gane ki zai yi? suka kira ya daga ummi ta sirantr d muryarta tana fadin "Hello! Abba ya ce Ke wace ce ki ke kiran layina? Ta ce Sunana '"Suhaila. ya ce Menene ki ke kirana?Ina ma ki ka samu lambata? Ta ce Gani nayi ni ma a cikin wayr. Tsaki yaja Sannan ya kashe.Suka dinga tsuntsira dry. Amina ta ce Sake kiranshi ki ce ma ke a kaduna ki ke. Ummi ta ce Kai yin waya akwai dadi ni ina son buga waya. Ta sake kira cikin Zafin rai ya ce Ke lfy??kin dame ni fa!Ummi ta ce To tsaya mana kaji ina son mu gaisa ne ni ina kaduna ne. Ya ce To na gode. Sai ma ya kashe wayar gaba daya suka yi ta kira a kashe. Tun daga ranar Ummi ta samu in umma tana aiki ko tana bacci sai ta sace wayar ta cire sim tasa nata ta kira Abba. Tun yana kyararta hr ya daina ya koma rokon ta daina kiranshi,dk a banza. Daga baya sai Abba ya soma sauraronta, ranar kuma ta kira shi ne misalin dayan dare,ranar taki zuwa dakin Tsohuwa ta kwanta a dakin umma. umma kuma dama dakin Alhj take kwana. A dai-dai lkcn ya kwanta kadaici ya dame shi,ga garin yanayin sanyi. wayar ta katse tunaninshi d yake yi na matarshi zuwa yanzu ya haddace lambar Suhaila. Ya daga ya ce "Hello ya ce Ke wai me ya hana ki bacci?Ta ce Ni ba sunana ke ba,Ni sunana Suhaila,kai fada min sunanka. Ya ce Abba Ta danne dryr d taso kwace mata ta ce Abba ba suna bane,Fada mn sunanka n gsky. Ya ce "Idris Yadda ya fadi sunan sai da ta dage kwarai sannan ta maida dryrta. Ya katseta d cewa Ina ku ke a kaduna?tayi dim,dn dai bata san ko ina ba a garin kaduna ba,ba ta ma ta6a zuwa ba. Take ta tuno Amina sun ta6a zuwa unguwar Sarki,dn hk ta ce "Unguwar Sarki. Ya ce, wai shekaranki nawa? Ta ce Sha takwas. Ta sheka masa karya.Ya ce Amma shi ne a ka ba kiwaya? ta ce ta ka san wanene Babana? Ya ce A"a ta ce, To shi ne mai bawa Gwamna shawara a jihar kaduna. Abba ya ce Lallai, ki ce in nazo kawo miki ziyara ba zan samun ganinki ba? Ta ce za ka ganni mana. Ya ce To zan zo. Ta ce To, Ya ce,Amma fa ina d mata ta haihu ne ta tafi wankan gida. . Ummi ta ce Lallai to sai da safe. Ya ce, Wa ke zuba miki kudi ne cikin waya?Ta ce Babana mana. ita sai lkcn ne ma ta tuna cewa ana saka kudi tunda ta ke kira bai taba kin zuwa ba,aranta ta ce kila wannan ba a sa kudi. Sunyi Sallama babu dadewa,wayar ta sake daukar tsuwwa. Ga zaton Ummi Abba ne sai da ta daga sannan taji muryar wani. Ya ce Da wa nake waya? ta ce wa ka ke nema?Ya ce Me wayr. ta ce Ummata ce kuma tayi bacci. Ya ce Yallabai nake nema. Ta ce Ban san wani yallabai ba,kada ka dame ni Ta kashe wayar tare da jan tsaki. Sannan ta cire layin ta maida na umma Wasa- wasa cikin kwanakin Abba ya soma damuwa da lamarin Suhaila kaduna, lokuta da dama ya kan kira layinta amma sai ya ji shi a kashe. Sam ba ya samunta sai lkcn d ta kira shi,ko da ya yi mata korafin hk,sai ta ce "Eh ita ce ke kashe layin sbd ana damunta. Sun yi jarabawar (J. S. C.E.)sakamako suke jira. dn hk yanzu tana gida ko yaushe tsokana kuwa bata fasa ba. Kullum ita d Amina cikin shirya yadda za su yi wa Abba waya suke, kudin cikin layin ya kare,Abba shi ke tura kati yanzun. Duk lkcn d Abba yazo gidansu d ya ga ummi ya hade rannan yana muzurai,ita km sai ta yi ta sheka dry,dmn tana tuno yadda yake kwantat d murya a waya. Wata rana hr duka ya yi mata sbd dryr d ta dinga yi daga sallamrshi a gdn. Tsohuwa kam ranar yini tayi fada,wai ita za ta bar gidan.Cin kashin d ake yi wa ummi ya yi yawa. A ce rashin 'yancin yakai ko dry ba a son tayi. Da kyar umma ta sha kanta t hkr. Wannan ta kaicin dukn yasa ummi tace ita kam sa tasa shi wahala. dn hk ranar gdn su Amina taje. suka shirya yadda in ta kira shi zata ce yaxo Kd ta ganshi, ummi ta ce mugu dama in yaje ya 6ace in huta. Hakn kuwa ta fada mishi, a ranar d suna waya. Ta ce '"Idris.dn Allah yaushe za ka zo ne? Ya ce Tun yaushe Suhaila nake cewa zan zo amma kin ki,to yanzun yaushe zanzo? ta ce kazo Juma'a ya ce A"a zan dai zo Asabar,Juma'a rabin rana ce. Ta ce,To sai kazo.Nan d kwana 4 kenan?ya ce Insha Allah,sannan ina son ki toro min da adireshin dn gdnk,sannan ranar d zan zo ki bar wayarki a kunne. Ta ce To." Ranar Asabar misalin goma na safe Abba ya shigo cikin sabbin kaya,ya yi matukar kyau tamkar sabon Ango. Umma ta ce za ka je gurin su Maigida ne?Ya ce A"a umma koda yake zan bi ta can.Kd zan je. Umma ta rike baki "Kd,? Me a ke yi?ya ce sai na dawo za ki ji.Ummi d ke wanke-wanke ta kwashe da dry. Umma ta dirma mata dundu tare d cewa,Ke wai ciwon dry ne y kama ki?Abba ya dubeta cike da tsana. Ummi ba za ki shiga hnklnki da ni ba?ta sunkuyar da kai tare d maida dryrta ciki. Sannan ta ce Yaya Abba dn Allah ka siyo min biredi,wlh biredin Kd dadi ne da shi. Lkcn d Amina suka dawo ta sammin. Ya galla mata harara,tare d fadin an ce miki nima bakauye ne irinki?In ma ki ka sake min mgn sai na gabje ki. . Ya kalli Umma Kada ki ce ma Alhj nayi tafiya amma in na dawo zan fada masa. ta ce ,To" Allah ya tsare. Abba ya fita. Ummi tana gama wanke- wanke ta shige daki dn yin gyaran gado. Umma na shiga kicin itama ta fito falo ta ciri wayr a caji taje ta saka sim. Take kuwa kiranshi ya shigo, ta daga ta matse murya kamar yadda ta saba, ka taso ne? ya ce Ina mota mun kusa tasowa. Ki turo mn adireshin. Ta ce Ba fa wahala,d kun sauka tasha sai ka ce a kawo ka unguwar sarki gidn mai ba Gwamna shawara. Ya ce Suhaila ma su ba Gwamna shawara d yawa Ta ce Um to ai a nan unguwar Sarki shi daya ne. Ya ce Ya sunan layin?ta ra sa me zata ce,gabnta y shiga faduwa.Ta samu kanta da cewa, Abuja Ya ce Abuja kuma Suhaila?ko dai Abuja road? Ta ce Eh gida mai lamba 6. ya ce To zan ci gaba da kiran layin. ummi ta ce To," Ta zauna tana sauke numfashi. Tab da ya dogata d ta bani,Sannan ta saka dry murna take yau yaya Abba zai sha wahala. Jefi-jefi ya kan kira ya ce sun zo gari,dk lkcn d ya kira in ta ji ringing sai tayi bayi da gudu, har Tsohuwa da suke zaune tare ta ce, ke takwara gudawa ki ke ko atini ne? Ta yamutsa fuska, sannan ta ce Bacin ciki ne. Tsohuwa ta ce, To taso uwarki ta baki magani. Ummi ta ce ya yi min sauki ma. Can kuma masu kiran layin suka kara kira. Ummi tayi kofar gida ta daga wayar a ka ce ke ina ki ka samu wannan wayar? Ta ce Oho 'yan rainin wayau kada ku sake kirana. Ta kashe wayar ta koma gida. Lokacin da Abba ya ce sun shiga KD har ma sun kusa sauka, sai ta cire layin ta ci gaba da harkokin gabanta ta manta ma da labarin wani yaya Abba. KADUNA Abba suna sauka a tashar kawo, ya sauka ya shiga raba ido yana kallon garin kaduna. Yau ce rana ta 2 d ya ta6a zuwa KD, daman sun zo daurin auran wani abokin su bara waccan. Ya kalli wani dan aca6a sannan ya yafito shi da hannu. Ya iso yana cewa Ina za ka? ya ce Unguwar Sarki. Dan aca6a ya ce Wane layi? Abba ya ce Abuja Road. Ya dubi Abba Rigasa kenan, unguwar Sarki babu layi mai wannan sunan. Abba ya ce, Ina zuwa, bari dai in kirata. Koda ya kira layin Ummi sai ya ji shi a kashe, yana ta kira a kashe. Ya dubi dan aca6a ya ce, Kasan gidn Mai ba Gwamna shawara? Dan aca6a ya ce, Hau dai muje sai mu tambaya. Abba ya hau mashin yana mai ci gaba da nemn layin Suhaila. Sun zagaye unguwar Sarki layi-layi suna tambayar masu gadi da 'yan dai-daikun mutanen da ke giftawa kasancewar unguwa ce ta manyan mutane, daga karshe dan aca6a yaba Abba shawar ya tafi gida kawai. Don haka sun gama zagayen unguwar Sarki har da makotanta, amma ba su samu ba. Gida daya ne aka ce musu da akwai Suhaila, amma yarinya ce ta goye. Kusan karfe 3 sannan suka koma tasha,ya biya dan aca6a, sannan yaje ya yi sallah. Zuciyarsa cike da takaici sai yanzu yake Sallah. gashi ya kasa samun layin Suhaila. kila ma tana sane ta kashe wayr dn kawai ta tazarta shi. Ya tuna d zagin d wani mu2m ya masa lkcn d suka tambaye shi ko ya san ina ne gidan mai ba wa Gwamna shawara? Mutuminya ce,mai ba Gwamna shawara a kan me? Ma su ba da shawara suna da yawa, ya sunan layin da ka zo? ya sunan mai gidan? kama ina lambarsu? Abba ya ce, Lambr kadai gare ni,km taki shiga.Mutumn ya ce,"Amma kai soko ne,gashi kmar wayayye.Ya ja tsaki ya wuce. Shi kanshi sai yanzu yaga wautarshi. ko me ya kawo shi gurin yarniyar?Shida dai ba za ya ce sonta ya keba,km ba ya ce ba sonta yake ba. Wani ma ya zaci dn kudi ubanta yazo,shi kam in ya koma shiru zai yi ko abokanshi zai ce musu bai gane ba kawai,dn yabi ya fada musu lbrn Suhaila,sun km san d batun zuwanshi gurinta sarai,km yasan hlinsu za su maida abn na tsokanarshi. Cikin matukar takaici suke tafe cikin motar kaduna zuwa kani,sun zo kwanar Dangora tsautsayi ya akfa musu. in da tayar motarsu guda ta fashe. . Nan take motar ta bar hannunta ta mulmula da su suna ta salati,nan aka kwashe su xuwa asibiti.wasu sun mutu take,wasu sun yi dogon suma.masu waya ta cikin wayarsu aka yi ta kiran yan uwansu,shi ma abba a cikin wayarsa aka kira lambar ummanshi da alhj da sauran su aka shaida musu cewa mai wannan layin sun samu hadari,kuma an kawo su asibitin mlm aminu kano yanxu.iyakan rudewa su umma sun rude,tsohuwa kam take cikinta ya kada ta soma xagawa bandaki tana kuka tana face majina.ummi bata gidan tana can gidan su amina suna ta hira suna cin dariya ,tace bari in je in qara sa layin in ya kira sai ince wayata chaji ne sai yanxu nayi.sadaf sadaf ta shige daki,kan kujera taga wayar,ta dauka ta saka sim din ta cire wancan. tana kunnawa sakuna suka soma shigowa. kafin ta bude ta duba sai ta jiyo muryar tsohuwa cikin kuka tana cewa wannan yaro ashe ajalh ne ya kira shi,ko me xashi yi kaduna?ni ban sani ba.ummi ta fito da sauri tana cewa,tsohuwa me ya faru?tace ba kina can gun yawanki na tsiya ba.Mai sunan mlm da ya tafi kd sun tafka hadari, yanxun haka suna asibitin mlm. ana xatan shi ma ya mutu.ummi ta saki ihu,sam bata san ta damu da dan uwan ta abba ba sai yau,ko tana kukan ita ce sila?oho.kafin kice haka,lbr ya watsu a unguwa abba ya mutu.cikin kuka ummi ta tambayi tsohuwa ina ummata? tace tare suka nufi asibitin da ummarku.taqi yarda ta jira su.ummi tana jiyo ihun kukan umman bashir ta xaga gidan.gidan ya rincabe da kuka,ummi fa hankalinta ya qara tashi.matarsa ta iso da kuka da yan uwanta a motoci.yayyantamaza suka nufa asibitin.can kusan qarfe takwas su alhj suka shigo.alhj ya ba mutane haquri,ya ce bai mutu ba dogm suma yayi.kuma Allah yayi taimako ba karaya.likitocin sunce xast duba shi xuwa gobe su gani.nan ko jama'a suka dinga fadin alhamdulillah.ummi ma tadan ji dadi a ranta,sanna fa kowa ya tafi dama wasu sunce xa stje yin sallah su dawo.saida suka koma sannan suka taho da umma,ummi cikin kuka tace umma da gaske bai mutu ba, umma tace eh bai mutu ba,muyi magana dashi. . Umma tace in sha Allah gobennan xai dawo gida. ummi tace to,umma tace kinga wayata? gaban ummi ya fadi ta tashi da sauri ta shiga neman waya,taci sa'ar ganin wayar,sai dai bata san inda ta saka sim din ba sai wanda ta tsinto ne a ciki.ummi dai tayi shiru ta miqa ma umma waya. kusan qarfe goma sha daya wayar abba da umma ta taho da ita ta soma qara,umma ta dauka.alhj ne ya ce ina wayarki ina ta kira ana cemin a kashe?una tace, a ku6e take gata ma a hannuna.yace to inata kira.tace qila faduwan da tayi daxu ne ta samu matsala.yace to dama zance ne ki dafa masa ruwan xafi a xuba a flask dan uwan matansa xai kawo mu yanxun a mota xai amsa ya kai.ta ce to alhj wayn xai kwana gunsa?yace bashir na nan kuma matarsa anyi anyi ta qi tafiya shi yasa na haqura xan dawo dan ba na xauna gun su ba ko? umma tace amma yaya jikin nashi?ya ce da sauqi yanxu ma yana son shan tea ne.tace to xan hada harda wayar tasa inya so ma dunga kiran shi kafin gari ya waye.ya ce yauwa ki bada.Alhamdulillah abba jiki ba matsala. Don hk a ka sallamo shi zuwa gd.kai tsaye gdn su umma a ka wuce d shi. A salin dakinsa a ka gyara a cikin kwana nan 3 ya yi ras sannan ya koma shago. Bishira kuwa lkcn mahaifinta ya ce maza ta koma dakinta,tunda ga abn d ya samu mijinta.Sun dawo hr da tafkeken injin Janareto wai yaron ba ya son duhu. Sannan ga kayan kallo d saraunsu.TabbasAbba ya ji dadin dawowar iyalanshi,dn dama yana cike d bukatarsu. Ranar yini suka yi gyaran gd ita da 'yan uwanta,sai byn magrib sannan ya shigo d tsarabobi.madara tatacciya da kaji. Ya dauki dansa cikin jin dadi yana kallonta cike da so da kauna,Nayi missing din ku da yawa.URFIN CIKI book 2 part 3 ZURFIN CIKI book 2 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:08 Ai bama shiri. shi ne fa ya kawo ni mkrntr kwana dn kawai baya son ganina. Suka yi ta mamaki. Can jimawa ya dawo, sun fito rakiyar 'yan uwansu Safiyya da na Khadija, suka ganshi tsaye yana danne- dannen waya. Ya taho ya gaida iyayensu duka,sannan suka koma gefe d ummi, ya ce Ni ma zan tafi. Ta ce, Ya Abba ko fa gaisawa ba mu yi ba. Ta karkatar da kai,Cikin raunin murya tamkar mai shawagaba,ta ci ga ba da cewa Ya Abba su Umma ba wanda ya ce a gaishe ni? Sai hawaye suka soma zuba. Hankicinshi da ke hannunta tasa tana sharar kwalla.Abba yana da matukar tausayin mace. Don haka duk da tsanar da ya yi wa Ummi sai da ya tausaya mata.Ya tausasa Murya. Sun ce in gaishe ki sosai, za ki ga gyada mai gishiri, Tsohuwa ta ce a ba ki.Umma ta miki miya, ta kuma daka miki yaji. Ta ce Na gode, Alhj me yasai min?ya ce kayan tea ne da lemun kwali. Ta ce Na gode. Tana ci gaba da share hawaye. Ya mike Zan tafi. yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi ya mika mata, ta ce A'a ya Abba ka bar kudinka. Ya ce Ba ni ne na baki ba,Alhj Karami ne ya ce in ba ki. Ta sa hannu 2 ta amsa tare d godiya.Sun raka shi kusa da Gate ita da su khadija,sai kuka Ummi ke yi. Bayan sun dawo dakinsu ne ta zauna tana duba kayan da ya lissafo mata,duk ta gani. Sai kuma saitin sabulun wanka da manshi da turaransa da hodarsa duk na (Aloe vera.) Shi kuma bai fada mata ko daga wa ba,ko ba komai ta dai yi murna sobada tana da 'yan kuraje a fuska,tasan kuma za su mutu. Sai kuma audagar mata,tayi dan murmushi. . Tunda Umma taji sallamar Abba ya shigo dakin ta bar komai tazo ta zauna tana son jin lbrn Ummi. Abba ya fahimci Haka,dn haka sai ya boye mata cewa, Ummi na kuka hr yanzun. Ya nuna mata ai Ummi ta kwantar da Hankalinta,km tayi hnkl dn ya bincika ya ji ana ta yabonta. Umma taji dadi Sosai,Sai da ya fara zuwa gurin Ummu,sannan ya je gida.Ya samu Bishira tana zaune tana aikin nata,wato Kallo. Tun da ta dawo daga wankan gida tazo da janareto da kayan kallo,shi kenan ta sanu abn yi.Kullum tana gabn (TV)da ta shi da safe in ta kokarta shi ne ta dafa ruwan tea ko wanka ba za ta yi wa dan ba,sai lkcn d man injin ya kare. Ya nufi gurin injin ya kashe,dif din da ta ji komai ya tsaya shi ne yasa ta zabura ta mike tana fadin Ba dai har man nan ya kare ba? Ta fito da niyar dubawa.Abba ta gani tsaye gabn injin yana bn tsakar gidan da kallo cikin takaici. Ta ce Baban Walid kashe min injin kayi??Ya ce Eh na kashe dn Allah dubi gidanki?kalli wanke-wanke kuda na bi dubi tulin wankin kayan Fitsarin yaronki. Dubi kicin dinki,kuma ko da bn shiga dakinki da wannan falon da ki ke kallo ba.na tabbata da wanda ki ka dauke ko tsinkw a cikin sa.Kila ma ba ki yi Sallah ba. Ta ce Dan karashe ne fa ya rage min in gama kallon in zo in yi aikin.Haushi ya sake kana shi,Sai kurum ya shige daki. Tsakuwar da ya dora kafa a kai tasa tsigar jikinshi tashi,sam ya tsani ya shiga daki ya dora kafa kan datti. Ya dawo yasa takalmanshi ya shiga da su,Walid yana kwance tun kayan da ya bar shi da su da safe sune a jikinshi yana ta bacci cikin fitsarin da ya shafka wanda ba wata leda da zata hana katifar ta jike. Ko wankan safe ma ba a mishi ba kenan.A fili ya ce,",Inna lillahi wa'inna ilaihinr raji'un. ya juya ya nufi shagi. Ita kam sai ta kunna injinta ta karasa kallonta, sannanta tashi ta dora girki.sai lkcn ta ma Walid wanka. Ta dan dauraye kwanukan da za su ci abnci,wai ta gaji sauran wanke-wanken sai gobe. Fati ta shigo,Bishira ta ce Yauwa Fatima naji dadin zuwanki.shuga dakina ki gyara min gado,ki dan yo min shara. Fati ta ce To. Ta shiga ita ma duk shegiyar darin ce gurin kuiyar aikin,dn haka ta dan birbira ta fito ta ce ta gama. Bishira ta ce Yauwa dan dauraye min kaya can na Walid. Nan ma tasan sama ta shanya. Bishira ta ce Yauwa ta ga abnci nan kici.sai ki dauki na Ummarku ki kai mata. Har Fati ta kai waje,Bishira ta kwala mata kira. ta ce,Zo ki tafi da wannan galan din na man fetir kije shagon Babn Walid kice ya taho mana da shi,dn man ya kare. Koda Fati ta same shi da galan ta fada mishi sako ya ce Ba zan siya ba,Maida mata galan din. Ta tafi,Shi kuma ya ci gaba da mita a zcyrshi. Yana fadin Na daina sayan man tunda ba za a bari sai dare a kunnan ba.Gidan Ummanshi yaje,ba ta nan ma taje barkar Haihuwa. Ko dakin Tsohuwa bai shiga ba,ya zauna nan falonta.Ya za kula ya zuba abncinshi ya ci.sannan ya dan huta sai ya fita zuwa gidan su Ahmad. Cam ya samu wasu daga cikin abokanshi suka shiga hira. Ranar dai Abba bai je gida ba sai misalin sha daya ko daya shiga bai nemi matar gidan ba,ya dibi ruwa ya yi wanka sannan ya shiga dakin. Ya lalibo makunnan wuta ya kunna,dn Nefa sun kawo wuta. Tana kwance irn banzan kwanciyarta da ta iya,dakin sai tashin wani irin wari yake kamar na ruma,kamar na fitsari ko na datti.Ya kalli ko'ina kullin kaya ne na wanki ne,na gaga ne ciki da guri.Ranshi ya baci,Ya kuma dubanta ga wata kiba da ta tafka. Tun da ta haihu ta zama rusheshiya,gashi bata son kama jikinta.Tsaki yaja,sannan ya dauki fiko ya fita. kan doguwar kujera ya jefa filo,ya kwanta a gajiye.Amma me?sai ya ji dora gadon bayansa acikin lema.Da sauri ya mike ya kunna wuta.Duk fitsarin yaron ne a kan kujerun dakin,dn haka sai ya nufi dakin da takw aje tarkace ya kunna wuta,shi ma dai duk shirgi. . Ya share Ya shimfida ta barma ya kwanta,a ranar ya dauri aniyar maida dakin ya zama nashi din-din-dn. Don haka washegari yasa a ka zo a kayi masa fenti,ya siyo kati fa ya yar da zanin gado,dk wani abu nashi sai da ya kwashe su. Kafin wata guda ya maida dakinshi cikakken daki,ya zuba dk wani abu da yake bukata. kafin ya fita kullum sai ya gyara dakinsa fes. ita kuma sam bata zuwa dakin,sai dai in yana da lalura yaje can ya sauke ya dawo. kazantarta kam ta kai in da ta kai,tunda hr kayan kashi tana zube su a cikin daki. Ya gaji yaje ya samu Anty ya fada mata,hr gidan Anty tazo ta zazzageta,ta tasata suka gyara gidan, amma ko a jikinta.Washegari ta ci gaba da in da ta tsaya. Sam babu wanda zai ganta ya ce haihuwarta daya. ¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤ UMMI yau ba wanda ya kaita murna,domin yau dai an basu hutu..Sai dai tunaninta zata ko iya kai kanta gida? Sunyi ban kwana bata da kudin mota, dan duk tayi taba su safiya kudin gurinta, amma ta ce yau ko da qafa ne xata gida.sun fito wajan mkrt wata maryam tana cema,ki tsaya mota xato da xata kaimu cikin kn.ummi tace baxan jira ba.sai ga abba kamar daga sama,tsoro ya kamata karya ce ta xauna gidan abokin sa da yace.hanka linta ya tashi cikin in ina ta gaida shi ya amsa.ya shiga mkrtn jim kadan ya dawo.hakan ta sha alwashin yau ko da shiya saita je gida.shi kam ma ya manta yai mata wannan maganan ma.ya sabi akwatinta suka je suka shiga mota. abba mamakin natsuwan ummi yake yi, ko da yake baxai ce ta natsu ba, qila lafawa tayi.tundaga soro ta saki jakanta da bokin tayi ciki da gudu,cikin kuka tana kiran ummanta.umma ta share do min tsohuwa tana cikin gida,kada tace tayi rashin kara,sai tsohuwa ne ta tashi da sauri tana fadin oyoyo takwara.suka qungume juna tace to menene kuma na kuka?umma ta fito nan fa ummi taje ta rungume ta.sai umma ta doje tace bubi shirme,sakar ni ni.tsohuwa tace haba suwaiba yarinya tana dokin, . Tsohuwa tace haba suwaiba yarinya tana dokin ganinki amma ki gwasale ta? abba ya ce daman nasan ba natsuwan da yarinyan nan tayi,har ina yabonta.dubi yanda ta xubarda kayan a soro.to xaki debo su.tsohuwa tace bari ni in debo mata tunda kai baka da tausayi.laile umma taga canji,do min ummi dai tunda ta dawo ko qofar gida bata fita ba,sai ko in an aike ta.sannan yanxu ba gudu da tsalle tsalle bare tsokana.ga aiki har girki ita kema umma komai.alhj yana shan shayi da safe,ummi ta yi sallama ta shiga. can gefen su umma ta xauna,sannan ta gaida alhj ta gaida umma wanda ta saka alhj agaba tana masa fira.wannan qa'idan umma ne bata barin mijinta shi kadai,in har yana gida.alhj yace suwaiba kinga ummina ko?laile abba yayi namijin qoqari. yarinya ta natsu.umma tace Allah ya amsa addu'an mu ka duba tsayuwan daran da muka dunga yi bayan tafiyan ta kan cewa Allah ya kintsa mana ita.alhj yace hakane,ummi dai na jinsu tana murmushi.can tace alhj anjima xanje gidan inna saratu in gaishe ta. qanwan sahura ce da ke aure a kabuga.ya ce to ummi, xanba umman ki kudin mota ko? ummi ta ce,to na gode.ta miqe ta fita ta bar mahaifanta cikin farin ciki jin dadin natsuwarta, suna godiya ga Allah mai shirya bayinsa.lkcn da ta shirya dan xuwa kabuga.sai umma tace ki kwana dan bana san ta fiyan yamma,kabuga da nisa.tace to sannan ta dauki kayanta kala guda, sannan ta fito.har xata wuce sai ta shiga gidan alhj qarami,sahura na ganinta ta hade rai,daman daqar take amsa gaisuwan ummi tunda ta dawo.ummi ta gaisheta a ciki ta amsa,sam ummi bata damu ba,tace umma ina fati?ta yatsine baki tace tana gidan abba,tace to inta xo ki ce mata naje kabuga sai gobe xan dawo.umman bashir tayi tsaki,tare da cewa ni yar aiken ki ne?ita dai ta wuce.tun dawowan ummi suke shiri da fati kamar me,ko yaushe suna tare suna fira.ummi tana mata labarin mkrtn su.ita kuma fati tana bata lbrn saurayin da tayi fahad,da irin son da take masa.ummi tace tab,ni ko xanyi saurayi nafi san irin ya abba...... . fati ta dubeta da al'ajabi kina nufin ya abba kike so?ummi ta xabura tana fadin tir, ko a mafarki Allah ya kyauta.ina nufin mai irin hirarsa da tsafta.fati ta qyalqyale da dariya tare da cewa ai na xaci shi kike cewa,inko ya ji kici duka ummi ta ce,ai ni ba ma da shi nake ba tab,shi da yayi auran so?kusan ko yaushe yanayin hiran tasu kenan.ummi tana tafe wadansu samari suka yi ta binta, sun shawo kanta ta tsaya da kyar,kuma har ta masu kwatancen gidansu. kwanaki uku bayan haka tana ki shingide kan kujeran dakin umma,misalin takwas saura ma dare.krtn wani littafi take yi na hausa da fati ta ara mata,sam ita bata taba krnt irin littafin ba,amma fati ta ce mata ta karanta da dadi sunan littafin NAGA TA KAINA na (sodangi).kasance wan wannan ne karo na farko da ta taba krnt lbrn soyayya,sai abin ya birgeta.amma nata ganin gwarxon sojan nan xai fi dacewa a ce abba ne, jefi jefi takan kalli abba da ke xaune kan kujera kusa da umma suna wani xance da bata jiyo su. 'Amma tasan ko me suke tattaunawa mai mahimmanci ne a gare su.sallamar wani yaro ne ya katse su,umma da abba suka amsa mishi a lkc gudu.yace wai ana kiran ummi a waje inji wadansu.da sauri abba ya kalla yaron,sam ba xai ce me yasa xance yaran ya fadar masa da gaba ba.sai ya lumshe ido sannan ya kalli ummi wadda kunya ta rufe kasancewar yau ce rana ta farko da aka soma yin sallama da ita.umma wadda kullum fatanta ummi ta samu miji,sai tayi murmushi,sannanta ce da yaron kace tana xuwa.abba ya dube ta da sauri, umma kin san ko su waye?ta ce, a'a.yace ya kamata a san ko su wanene dan kin san bata da kan gado,kowa ma sai ta jajibo kuma ma duk nawa ummin take da har xata soma tsayawa da samari?umma tace,to abba ai gara ta kama dahir, tana qare sakan dire ba sai ayi mata aure ba?yace gaskiya umma gara ta dan taba krt,dan yanxu xamani ne na krt.umma tace,tayi acan a dakinta.ta dubi ummi tasgi kije.ummi ta miqe ta fita.abba ya miqe shi ma,umma bari dai in gani ma su kamun kai ne? umma tace to.., . Sun gama gaisawa kenan sai ga abba ya fito.ganinsu tsaye da ummi sai ya tsinci kanshi cikin wani bacin rai.ya isa gun ya musu sallama, suka amsa, sannan suka gaisa.yace daga ina kuke? suka dube shi dayan ya ce lfy dai ko? ummi tayi karaf ta ce yayana ne.anan suka sake gaida abba.bai amsa ba, sai ma cewa yayi na tambeye ku kai ma kana tambayana,wai lfy? suka ce,kayi haquri,nan suka gabatar da sunansu.mai san ummi shine nazir, abokinsa kuma sagir. sun 3a masa cewa dukkansu daga kabuga suke.yace krt kuke ko kasuwanci? sagir yace,eh krt muke,amma muna taba kasuwanci a shagon mahaifinsa da ke kwari.abba ya dan yi jim,sannan yace to kai ka shirya aure ne?nazir yace eh to, nasan dai kafin a tashi yi mata aure na shirya.abba ya ce, to ita kam krt xata yi, kuma c ma buqatan ta hada krt da soyayya. ya dubi ummi da fatan xaki sallame su.ya juya gida.sagir ya ce, wannan wanki ne da gaske? ummi tace qwarai kuwa. nazir ya ce to yanxu ya kenan? kin ji abin da ya ce.ummi yayi shiru tana tunani, ita fa basu kwanta mata rai, tun randa ta hadu dasu,sam basu iya saka kaya kalar yadda ya abba ke sawa ba.dan haka sai tace, ina ganin xai fi mu haqura kada yaxo ni yayi ta mun fada.nazir ya ce yanxun haka xaki ce? ummi tace, um,sai da safenku.kada ku ja min duka.sagir cikin jin haushi ya ce,ki xama mangofak qarewan krt.sannan in kin gama wan naki ya aure ki. ita dai ta shige gida.kusa da soro ta iske umma da ya abba ta yo masa rakiya, tana kuma ba shi aaki kan cewa yayi ta haquri,tace ina fada maka ko yaushe ba fa fushi ko fada ne xai saka matarka a hanya ba.lallashi da nashiha,ka dunga koya mata giqki daka nutsu ka koya mata ba gashi ka ce ta iya daidai gwargwado ba?abba yace,hum lamarin yarinyan nan yayi nisa fa umma,wankan jikinta ni xan koya mata? sallah fa daga nake da ita.amma abin yaci tura.antynta sau nawa tana xuwa tai mata fada duk a cnxa,mkrtn ma ta qi xuwa.ni kuma da ce ruwanta.umma cikin al'ajabi tace, sallah! sallai ma bata san yi abba?abba yace umma baxan mata sharri ba... Ta ce Tabdi,to kuwa ba kuwa kazantarta ta wuce jiki hr d zcy. wannan ita ce kazanta mafi muni. Don haka dole ne ka zage damtse don ganin ta kama sallah,to menene marabar arne d Muslmi in ba Sallah ba?Abba ya ce Umma na mata nasiha na gaji. Ta ce To kasa ta a mkrntr Islamiyya,kila ta ji tsoran Allah in tana jin Wa'azi. Sannan ka dainga siyo mata kasasuwan wa'azi.Abba ya ce Umma kaset nawa na kawo mata bata sakawa,Kullum sai indiya da Hausa fim,in naki sayan man fetur in tana da kudi ta saya. In kuma ba a ta da shi sai ta dauki ittafin Hausa ta dukufa.umma ta ce Allah ya kyauta,kaje kayi ta hkr tare da addu'a. Ya kalli Ummi,sannan ya ce ma umma,kada ta sake fita gurin wadanan kananan yaran,sannan ya fita. A daki umma take tambayar Ummi daga ina suke? Ta ce um,Umma kyale su ni sam ma ba su min ba. Umma ta ce to Allah dai ya miki za6i nagari. Abba yana kwance a dakinsa ya yi lamo cikin bargo,ya kasa amsa ma kanshi tarin tambayoyin da ke yawo cikin kanshi. Haka tambayoyi suke zuwa masa daya-bayan-daya ,me yasa ya damu da lamarin Ummi??me yasa da a ka yi sallama da ita ya samu kanshi cikin wani tashin Hankali? Me ya sa ranar da zai je mata ziyara ya za6i ya sai mata kayan kwalliya? A fili ya ce,don tana kanwata.Zuciyarshi ta ki amincewa da haka. Me yake shirin faruwa da ni ne? ya fada a fili. Ya yi juyi zuwa rigingine,sannan ya dauki filo ya manna a kirjinshi, ya ci gaba da magana shi daya. Bana zaton cewa Son Ummi nake yi.don lkcn da na yi tsananin Son Bishira bn ta6a samun kaina cikin wannan yanayin ba. Kai Allah ya tsare ni da Son ummi,wannan mahaukaciyar yarinyar..........bugun kofarshi da a ke yi ne ya katse shi. Murayar Bishira ce ta na cewa Babn Walid!Babn Walid!! Ya bude kofar da sauri,ta ce Walid ne ke ta amai. Ya fita ya dauki yaron daga hannunta yana fadin Me zai hana shi amai,in ba a ci sa'a ba har zawo sai ya yi,Saboda kazantarki.Sam ba ki lura da me zai wawuro ya tura bakinsa. Ta ce Yau fa bai ci komai ba,tun da safe yake wannan aman.Ya ce shi ne ba ki sanar da ni ba?Ya cire masa kayan jikinsa wadanda ya ji suna ta doka karni.. . Ya isa igiyar shanya ya ciri wasu yasa masa,sannan ya fita dashi.Wani babban kyamis ya tafi da shi,mai kyamis din likita ne,sai dai ba na yara ba ne,amma kowa yazo sai ya duba shi.Nan dai ya masa bayani ya ba su magunguna. Sha biyu dai dai ya dawo,tana zaune tana kallo ya ce "A'uzubillahi,wai ke kallon nan masifa ya zamarmiki ne?to ki sani na kusan fita da kayan kallon nan. Ta ce,Tab,ka kaisu ina? dadinta dai dafa gidan ubana a ka kawo su. Ya ce ta za su koma gidan uban naki. Ta dafe kirji "Zagina ka ke yi?ya dora mata dan a jiki "An zage ki,ke din banza,kazama!yazube mata maganguna ya fita. Ya jima zaune a kofar gidanshi dafe da kai,yana tunanin shin wai shi kadai ne bai yi sa'ar mata ba,ko kuwa duk maza ne.Ya tuna abokanshi 2 da suka yi aure. Muktar d Jamilu,sam ba su da wannan matsalar,duk lkcn da yaje gidansu tsaf matansu,ga mutunci da mutanta mutane. Shi kuma a cikin abokanshi babu mai zuwa gidan sbd bata gainin kowa da gashi. 'Yan uwanshi sai wanda ta za6a sannan zata yi hulda da su. 'Yan garinsu kuwa can ¤ZAMFARA¤In suka zo kiri- kiri take nuna musu kyama ga rowa,sam bata hulda da matan abokanshi. Ya numfasa zai bi shawarar Umma ya gani, amma gaskiya Bishira ba matar zama ba ce. Tun da ya dawo sallarAsubahi dakinta ya shiga tana ta shirga bacci. Walid kuma ya yi faca-faca cikin kashi ya tausasa zuciyarshi ya ce "Bishira! . Bishira!!Ya dan duki kafarta,sannan ta tashi. Ya ce Ki tashi ki gyara masa jiki kiyi sallah.Ta ce,Tab, me ya yi?ya ce, "kashi ya yi.kurum sai ya ji ta ce Tab,wannan akwai dan iskan yaro.Yanzun dan ubanka kashi ka min? Sam bai san lkcn da ya watsa mata mari a baki ba,cikin murya mai karfi ya ce "kada ki kuskura ki sake ce ma dana dan iska!kar ki sake zagar min yaro kada ki yi wa dana baki.Ba zan dauki wannan ba. . Ta mike daga kan gadon tana kuka Ni ka daka? wlh sai na rama. Kasancewar lebe baya raina duka,sai jini.Nan da nan sai kumburi. Ta cakumo shi,wlh sai na rama.Ya hankadata kan gado ya bar gidan.cikin zcyrshi yana fadin ,"Wannan fitina da me tayi kama? Ita kam ruwa ta dafa sannan ta wa yaron wanka, cukuikuiye zanin gadon ta saka shi cikin baho,sannan tayi kwaskwarima ta sabi danta baki suntum ta nufi gida tana kuka. Mahaifinta bai nan yana Abuja,Hjy Zainu ta kalle ta bayan ta gama kero karyarta. Wai don yaro ya yi kashi ta ce yaron bai kyauta ba shine ya hau ta da duka da zagi. Hjy Zainu ta ce Amma wannan da muciya ya dake ki ko?ta ce, Da hannu ne,nushina fa ya dinga yi. Hjy Zainu ta ce Ai kin gani ba yadda ba a yi ba ki tsaya kiyi karatunki kin ki,kin kafe sai kin aure shi,wannan matsiyacin? Dama talaka yana da wannan tsiyar.Yanzun za ki zauna mu jiraZuwan Alhj,ba za ki koma ba.Ya dai baki takardarki in yaso ki koma mkrnt.Su kuma su dauki dan nasu. Bishira dai tayi shiru,zcyrta tana jinjina rabuwa da Abba d kuma danata. Abba kam gidansu ya nufa.Ummi ya soma cin karo da ita tana sanye da doguwar rigar bacci,ta dora rigar sanyu ta sakar ulu, a kai tana wanke baki da busushi. Ta dube shi,mmkn ganinshi tayi a wannan lkcn.Sai da ta dauraye baki sannan ta ce masa sannu da zuwa,ya amsa a hnkl bai san mai yasa ya kasa dauke idanunshi daga kanta ba,hr ta gama alwala tayi addu a ta mike. Ta dube shi da niyar yin magana,amma sai ta fasa don tana tsoron kada ya daka mata tsawa. Ta daga labulan dakin Umma zata shiga. Ya ce, "Ke!' ta waiwayo cikin hada rai,domin ta tsani kiranta da yake da ke!Ya ce Ummana fa?ta kalli dakin Alhj Ba ta fito ba,,Ta shige ta zura hijabi ta tada Sallah. Ya shiga dakin ya zauna,yana kallonta tana Sallah zcyrshi tana nazarin Rayuwar Ummarshi. Tun tasowarshi ya ke ganin kulawa da kyautatawa da take yiwa Alhj Babba ga biyya, sam bata wasa da dk wani abu nashi daga lkcn da ya shigo gida ta gama sauraron kowa sai lkcn da ya fita. Bai ta6a jin sunyi sa'in-sa ba bare ta daga murya sama da tasa.Shin sauran matan ba su fahimci irin wannan ladabi ba ne?Ummi tana addu'a zcyrta cike da tunanin shi kuma ya Abba me ya kawo shi da wannan sassafen? Muryar Umma suka ji daga waje tana cewa,"Ummi in kin idae ki fito ki share gidannan,ki wanke bayi,Ummi ta ce To''. Sam Umma ba ta san Abba ya shigo ba,dmn da ta ba Ummi umurni sai ta sake komawa dakin mijinta, Ummi ta wanke bayi kansu,sannan ta share ko ina na gidan, ta kunna risho ta dora ruwan karyawa, sannan ta shiga firar doya. Gyangyadi yake daga zaunw, Muryar Ummanshi ce ta farkar da shi tana cewa, "A'aha! ya bude ido cike da bacci.ZURFIN CIKI book 2 part 4 ZURFIN CIKI book 2 part 4 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:10 "A'aha! ya bude ido cike da bacci. Ya kalle ta tare da yin mika,ta ce "Lafiya"? Ya ce,Umma lfyr kenan.Ta zauna da sauri Me ya faru Kuma? Yayi dan tsaki,umma na gaji da auran nan ina ga wannan karan xan yar da qwallon mangwaro in huta ta quda. umma ta ce abba! abba!! me yasa baka da haquri? ban xace ka haka ba abba,ina ce jiyannan ka min alqawarin kawo qarshen duk wata matsala tsakaninka da matanka?shin ban fada maka hanyoyin da xaka bi ka xauna da matarka lfy ba?ya kamo hannun ta,umma ba na san bata ranki, ban san yadda xanyi da halin yarinyan nan ba ne. jiya fa ina kwance taxo tace min yarona amai naje kai shi kyamis,ina dawowa na samu ta xauna tana kallon,ina mata magana ta hayayyaqo min da asuba na tashe ta sallah,wai dan yayi kashi shine ta hau xagin yaron nan,wai dan iska. ni ko na bige mata baki har da cukume ni da dambe fa.umma tace kaine harda duka abba? dukan mace?ta xuba tagumi tana kallon shi,ya ce umma xaginshi fa tayi,kuma kin san dai ba kyau uwa ta dinga xagin danta.dan ba haka kikai min tarbiyya ba.kalli rashin ji irin na ummi, amma ban taba jin kin ce mata yar iska ba.tace to ba sai ka xaunar da ita cikin tsanaki ba?? . Yayi shiru a xuciyarshi fadi yake umma ba xata fahinta ba.tace, tashi kaje ka bata haquri, ka lallasheta.matafa sai haquri,kasan da qashin haqarqari aka yi su,dole ka ganta a karka ce.saidai nasiha da lallashi,da xaran ka ce kan dole xaka miqar da ita,sai ta karye.nan dai ta yi ta ma abba fada, har sai da shi kanshi yaga cewa eh,yayi saurin fushi.dan haka ya miqe ya nufi gida da nufin bata baki.sai dai kuma kash! lkcn da yaxo tuni tana gidansu.ya dawo ya sanar da umma, tace to dole sai alhj yaji kenan.ta shiga gun alhj yana shirin fita. yace yau dai suwaiba akwai abin da ya dauke miki hankali daga kaina ko? tace, me kagani? yace tunda kika fita ban kuma jin duriyarki ba, hatta karin kumallo yau uwata ce ta kawo min.ko taya ni shafa mai yau ban samu ba, tace uhum, abba ne in gaya maka na gani hankalinshi a duk tashe, matsala ce suka samu da matarshi,wai ta yi yaji.alhj yace,yaji? umma tace eh wai a ce kamar abba bai san yadda xai yi haquri da mace ba, alhj yace ina abban?ta ce yana daki yana karya wa. Ya ce kira min shi.abba ya xauna ya xayyane ma alhj komai duk abubuwan da ke faruwa wanda take masa,hatta batun sallah da bata san yi duk ya fadia.alhj yayi shiru,can ya ce in ko haka ne ba qaramin haquri kake yi ba, amma kaje xamu je gidan.abba ya ce, ni dama xa a baita can dana huta.alhj yace ba xa ayi haka ba haquri dai xa ka ci gaba da yi.xuwan su alhj biyu gidan amma ba suyi dace ba ance musu mahaifinta baya nan. antynta kuwa ta kira shi a waya ya ce yana nan xuwa gidanta.da dare suka je da ahmad sun same ta ita da mijnta,anty ta tare su cikin fara'a aka kawo musu kayan shaye shaye.nan dai abba ya fada mata komai.ya qara da cewa ban sani ba ko dan ni talaka ne shi yasa bishira bata ji maganata? anty tace dame ka gaxa mata? iskancintane kawai, wai bishira har da rashin sallah,xa ko taci qaniyarta gun alhj.mijin anty yace,tabdi lalle kana haquri nan dai suka ci gaba da hira har mijin antyn yayi mishi alqawarin cewa ya kawo takardunshi.MD din gidan rediyon tarayya na jihar kd, amininshi ne. Amininshi ne tun da abn da ya karanta kenan za a sama mishi aiki.Abba ya yi ta godiya. Bai san da wane baki zai gode ma mijin anty ba,tun daga nemna auran Bishira yake taimakoshi, darajar su shi da Anty da Alhjn su Bishiran yake hkr da halayanta. Ya zo ya sanar da su Umman,Sun yi murna hr Alhj ya ce dole ne in in masa godiya. Umma ta ce To Abba ka gani fa,ta dailin matarka gashi zaka samu aiki,ka yi ta hkr fa. Abba ya ce Umma ba fa ta dalilinta ba,in Allah ya rubuto zan samu ta hanyarshi sai ki gani,ko ban santa ba Allah ya kawo sila.Ta ce To yanzun dai ita ce Silar,Allah yasa albarka.Sai dai ba zan ji dadin tafiyarka garin Kd ka barni nan ba. Ya ce Umma ko ni tunda ya ce kd ke kurum ni ke tunan.Umma tayi Murmushi,Allah ya maka za6i na alkairi,dk in da za ka je.Amin Ummata. Mahaifin Bishira ya dawo kuma Alhj ya tasa Abba sun je in da aka kirata gata ga shi ga kuma iyayensu. Abba ya jero duk laifunkanta bai rage ko daya ba. Sannan ya ce,shi ma yana son ta fadi tsakani ga Allah me yake mata wanda ba ta So?Nan fa a ka ce ta fadan, sai ta shiga Kame-kame, Wai in ya shigo gida sai ya yi ta fadace-fadace sannan ba ya zama a gida sai tayi bacci,km ga abnci ta dafa amma sai ya amso na Ummarshi ya c. Alhjnta ya daka mata tsawa."Yi min shiru,yaushe ki ka bar musulunci? Ba kya sallah ko?sannan ki bude baki kina zagar masa da a gabansa?Ya bige miki baki kin kwaso kin taho gida,to a miki uban me?ya dubi Abba "Idiris me yasa ma ka mata duka ba?Ai ke babu abn da ya dace da ke irin duka. Maza ki kakkabe mayafinki ki koma gidanki,bana son in sake ganinki da sunan yaji a gidana, . Zan wulakanta ki. Kuma game da batun sallah dk lkcn da bata yi ba ka dakar min ita ni na saka,batun tsafta kuwa kada tayi,ka nemi mata ka aura ka barta da tsiyarta. kai dk lkcn da ka samu matar ma zan biya maka sadakinta ko 'yar wanene.Sai a lkcn Alhjn Su Abba ya yi magana. Hakuri za ka yi ranka ya dade,Allah ya saka da Alkairi bisa karamcin da a ka yi mana,kuma insha Allah ba za su sake ba. Abba ma ya yi godiya,sannan suka masa sallama.Ita ko Bishira mayafi ta dauko tana kuka suka tafi. Hjy Zainu ranta ya 6aci,taso a kashe auran don dama bata son Abba sam,kafin zuwan iyayen Abba da shi kansa Abban ta fadawa mijinta karairayi,kamu ransa ya 6aci. Ya kuma daukar wa kansa alkawari in ya bincika ya tarar haka ne dukanta da zaginta yake ba tare da ta masa laifin komai ba?sai yasa an raba auran. Amma da yaji batun Abba gata a gurin bata musu ba,sai ranshi ya baci da ita, har dai batun sallar nan.dn haka ya bincike yana da kyau ayi shi,kada ka yanke hukunci da maganar gefe daya,wannan shi ne adalci. Bayan sun dawo Abba ya rakata gida ya zo gurin Alhj da ya ce ya dawo yana jiranshi. Alhaji ya masa fada cewa dk in da tara tayi to ya kansace a gida. Sannan fadan da ta ce yana yi in ya shiga shi ma ya daina,haka ya dinga zama yana cin abncin.Abba ya ce to.Umma ma da ya shiga suyi Sallama nan dai ta kara masa fada tare da nuna mishi hanyoyin da zai bi ta ce kuma cikin satin nan yayo mata rijistar Islamiya tunda da ita a kusa. Ya shiga ya same ta zaune bakin gado tana ta fushi,ya zo ya zauna kusa da ita.Yasa hannunshi ya kamo nata,sannan ya kira sunanta bata amsa ba bata kalle shi ba ya ci gaba da mgn. Kin san dai ina sonki ko??ta dube shi Da ba kafin a zuga ka.Ya ce wa zai zuga ni? ta ce Wa kuwa in ba Ummar taka ba. Ya yi tsam ya ji haushin maganarta sosai,amma sai ya danne kada ki zargi Ummata tana sonki kin ki fahimta ne kawai.amma mu bar zancan kiyi hkr akan abubuwa da nike miki. ki yafe min nima na yafe miki. . Ya jawota zuwa jikinshi,hr gobe ina sonki sosai.Ranta ya yi sanyi don mata na son wannan kalma daga mazajensu. Ya kira sunanta ta dube shi cikin ido suke kallon juna,ya ce kin ya fe min?ta daga gira,kina sona hr yanzun?Ta kara mannewa a jikinshi "Ina sonka sosai ma.Ranar dakin shi suka kwana,kuma ranar ce rana ta farko da suka soma kwana a dakin nasa. Washe gari tunda ya dawo Masallaci ya soma akin share gida,lungu-lungu ya gama ya wanke bayi kan su sannan ya yako ta da kyar ta tashi ya ce tayi sallah ta yiwa yaro wanka. Tayi Sallar,wankan ta kuke wai akwai sanyu,sai ranar ta daga. Ya ce,To t dafa musu ruwan zafi su karya.Shi kuma ya fitar da wankinshi yana yi ya gama ya ce ta fito da duk wankinsu ita da yaron.Tsawaya ya yi yana kallon tilin kayan,amma gudun kada suyi rigima sai ya yi shiru ya ci gaba da wanki. . Ya cire kayan yaron da zannuwanta hr ma zanin gado wadanda yaron ya yi kashi ta aje su suka bushe,,wasu kayan hr da tsutsotsi. Ya kira ta ya ce "To kalli kayanki hr da tsutsotsi,wanna n ya dac fisabilillah?samo leda ki kwashe su,ba zan iya wanke su ba,in kuma za ki wanke to. Nan ta samo bako ta kwashe takai gurin bola,ya ce Bishira tsafta cikin addini ce,Annabi (S.A.W)ya ce Babu mai shiga Aljanna sai mai tsafta. Don Allah ki dinga kula,ke kanki za ki ji dadi in har ki ka tsaftace ko'ina na gidanki.Ta tura baki ta wuce. Ranar haka ya yini wanki kayan yaron dk sun dafe kaya masu tsada da kyau irin wadanda a ka sai masa daga gidan iyayenta,ranar dai ko shago bai je ba. Cikin satin dai babu laifi suna ta shiri,kuma tana daurewa tana yin tsaftar jikinta,haka nan yasa ta wanke kai tayo kitso. sai dai ita gani take dk an takura mata,amma tana jin dadin yadda ya sakar mata fuska kamar farkonauresu. Mitar da take masa kullum ya daina dadewa a waje,ita don Allah ya zauna a gida suyi hira. Ranar dai saiya gwada zama tun da ya dawo sallar Isha'i ya shigo gida. Tana zaune ba riga ya ce,Wai Bishira kayan kwalliyarki sun kara ne? ta ce,Me ka gani?ya ce,Rabon da in ga kwalli a idonki tun kina amarya bare dan jan baki. . Taja dan tsaki "kwalliyar me zan yi sai kace wata budurwa?Da dai nayi.Ya ce kin ji wani shirme kuma,ban da ke ai matar aure me miji a hannu ita ce da yin kwalliya. Ta ce, To ko ma nayi ba zama ka ke ba.Ya ce "To yau dai gani na zauna,kuma ina son a sheka min kwalliya. Ta dube shi Gsky sanyi ba zan iya yin wanka yanzun ba.Shiru ya yi yana kallonta,can sai ta zame ta kwanta,sai kuma bacci. Ya yi murmushi.Dubi matar da ta ce wai ba na zama a gida. to yau na zauna amma kalli yadda ta bingire tana shirgar bacci. Ya mike ya fice.cikin takaici korafin banza kenan take yi tunda ba ta san yadda za ta yi fira da mijin ta ba. haka dai abba yayi ta hakuri don baxai yiwu ya ce shi kadai zai dauke mata duk aikin gidanta ba. sai dai yayi wanda zai iya,amma duk wanda ya shigo gidan shi ko ba a fada ba yasan matar gidan kazama ce ta bugawa a jarida. ummi tana zaune gaban umma,fuska shabe- shabe da hawaye.ta rikewa ummar hannu."kinji don Allah umma kice wa ya Abba ya dawo dani garin nan.wallahi bana son makarantar kwana,ni dai bazan koma ba."umma ta ce "haba ummi xuwa yanzu ya ci ace kin saba da makarantar" ta ce,"umma bazan saba da rashinku ba....."karaf a kunnen Abba. ya ce,"to sai ko ki shirya sabawa,don wata rana ma aure zaki yi." umma ta ce sosai kuwa. tsohuwa dake zaune a kofarta,tana jinsu ta sako baki da cewa,"ku dai lallasheta,karatun nan fa da ake ta matsanta mata bana ganin manzo bane." Abba ya ce mata,"in ji wa? kin ji ki,to ana neman aljanna da karatun boko kuma ana neman wuta." ta ce,"kai ni raba ni da shegiyar karya tunda bata so a barta." Abba ya dubi ummi,"kada ma kiyi za ton maganar tsohuwa za tayi wani tasiri,gara ma ki shirya komai gobe da wuri zamu wuce." ta dube shi,"don Allah ya abba." ya mike ki shirya da yamma zanzo muje (sahad store). ya dubi umma na tafi. . Ta ce,"abba bamu ko gaisa ba,ya mutan gidan?" ya ce,"suna lafiya,sauri nake in karasa wasu dinkuna,saboda gobe bana nan jibi litinin zanje interview da gidan radiyo da talabijin na (c.t.v) ta ce,"a'a ka samu anan din ne?" ya ce,"eh bana fada miki ba da aka tura takarduna can sai suka ce gurin da zasu saka ni akwai wani wanda suke jin dadin aikinshi a gurin? don haka zasu turo ni kano,suna ganin ana bukatar irina.to shine mijin anty ya fada min to yanzu sun kirani ranar litinin zasu min (interview).ummi dai na jinsu bata ba kukanta ba.abba na ficewa umma ta ce tashi kije kiyo kitso ummina,kin ji? dakyar taje ta dawo.umma tana yankan kubewa wayarta ta shiga ruri,ta dauka Abba ne.ya gaisheta ta amsa,ya ce ummana ummi fa ta shirya? umma takai duba cikin daki inda ta hango unmi nade kan kujera tunda ta fito wanka. Tace can cikin kujera,wai sanyi take ji.yace sanyin lfy kuma? ta shirya ta sameshi gida,umma tace to gatanan xuwa sukayi sallama.umma tace ke ummi fito man in kin gama shirin.ummi tace umma nifa sanyi nake ji,ina ganin xaxxabi ne xai kamani.tace to ku biya ta kyamis kusai magani.tsohuwa tace ke yi kwanci yanki, dole ne fitan? umma ta miqe tana cewa, yanxu in ban je ba da yaxo xai fara min masifan shi ne. ta shirya ta fuce rai a bace.a nutse ta ke tafiya har daf da qofan gidan ya abba. sallama taji anyi mata.wani matashi ne suka gaisa, ya tambaye ta nanne gidansu? tace a,a lafiya?ba tare da bata lkc ba ya fara xayyane mata manu fanta,santa yake kuma da aure,tace kaga mlm sai anjima.ta shige gidan abba shiko ya kafe yaqi tafiya.da sallama ta shiga gidan,qaran inji baisa aji sallaman ba,dan haka ta jingina da rijiya tana kallan tsakar gidan.mamakin daya yadda mace daya a gidan ta kasa gyara gidan.sai kace gidan namiji, namijin ma qaxami. . abba ne ya fita wanka sanye da jallabiya fara.ya aje bokitin ya dube ta. yace ki siga ciki mana, ai tana falo.tayi sallama,bishiratana xaune da baso tana kalan tv, ganin umma ta daga labule sai ta hada rai tare da cewa lfy? ummi tace ina wuni. bishira tace lau, nace lfy? ta fada hadi da xare ido. ummi tace ya abba ne ya ce na xauna anan na jira shi. tace baxa a xo nan adame ni ba, ehe dan kallo nakeyi. ummi ta ja tsaki tare da sakin labulan, ta koma ta jin gina da rijiya.bishira ta fito.ke sarkin rashin kunya wa kike ma tsaki? ummi ko kallanta batayi ba.sannan tace baki isa kixo min har gidana ba,kice xakimin rashin kunyan da kika saba.abba ya jiyo hargowanta ya fito, yana qoqarin saka t- shirt baqa akan faran singiletin shi,wandan jeans ne mai laushi blue.yace,menene? tace, wannan mara kunyan yarinyan nanne xata sameni har dakina tamin tsaki.oa dubi ummi dake kallan qasa tamkar bata san me akeyi ba. yace ke ummi, ta dube shi da sauri,xan bata maki rai kinsan bana san raini ko? tace nifa ya abba banfa yi mata komai ba kawai fa.ya daga mata hannu,yace banasan ji. yace na fada maki dai bana san raini. takaicin duniya ya isheta,ta sunkuyad da kai cikin qunan rai.wanna shine gaba kura baya damisa.bishiqa kam sai ci gaba da mita take, shiko abba tuni ya koma dakinsa da qarasa shiri. ya fito fes, sam baxaka ce mijin bishira bane.qamshin turaransa ya karade gidan ya daga labule.ni na fita. tace sai ina? xan kai ummi ta sai duk abinda xata nema dan gobe xata koma mkrt. ta tabe baki. ya dubi ummi wadda ke cika tana batsewa,sannan ga sanyi alamun xaxxabi yana damunta.yace muje ko? ta dube shi sannan ta bishi.a qofar gida ya iske wannan saurayin,yace lfy, ko kana jiran wanine? saurayin ya ce wata yarin....sai ya hango ummi,dan haka ya katse batun da cewa yauwa gatanan. . abba ya kalleta ke uwar rore rore wannan ke yake jira ko? ummi tace oho mashi, bina yake tayi.abba ya ce, kayi haquri dan samari,ba aure xa a mata ba, krt takeyi. yace nima din bawai ina nufin yanxu bane.ya ce na fahince ka.to ka bari sai nan gaba,ina nufin in auran yayi sai kaxo ko???? Ya dubeta ranshi bace,ke kuma wuce muje.suka bar shi nan tsaye yana kallansu.yaga kishi qarara a idon abba.yace wannan ba wanta bane shima santa yake.ya raya aransa shima yayi gaba abin shi.shi kam abba suna tafe yana yi mata fada,wai tabi ta sakar ma maxa fuska kowane gaja sai ya xo yace yana santa.maimakon ta tsaya tayi krtnt,xamani na ilimi,ita dai ta qi kula shi,har yanxu takaicinta abin da matarshi ta mata,kuma ya nuna ya goyi bayanta.wayarshi tayi ringing,ya kalli ummi muje shago na mashin din nacan.sannan ya daga wayar,ita tana tafe ne amma sam bata jin dadi.da yake tafiyanta yanxu tamkar tana jin tausayin qasa take yinta,sabanin da da sai dai tayi gudu,shi da ke tafe yana waya ya riga ta isa.gefe ta tsaya ya shiga shago bayan ya gama amsa wayar.ahmad abokinsa yaxo xai shiga shagon ya ganta tsaye.tace ina yini ya ahmad? yace lfy lau yar daru.daman haka ya kan ce mata.ya shiga shagon yana waiwayanta,abbana barma yan shagon sallahu wasu kayan da xa a xo dauka,ahmad ya shigo. suka tafa,sannan suka gaisa.ahmad yace naxo ne in fada maka anjima xamu shiga gidan su hafsa dan gaida iyayenta,sai dai kuma ganin ummi ya sani jin wani abu.anya ba xan dawo gida da neman aurena ba?a rude abba ya ce wace ummi kenan? ahmad ya ce qawarka mana.abba ya ce dan Allah saki xancen nan kada ma ta jiyo ta raina mu,me ka gani naso a gun ummi? dan Allah kada ka cta min rai. . ahmad yace, allah in xai yiwu, nutsuwan ta birge ni .abba ya ce to ba da ni xa aci amanar hafsa ba.ummi kuwa dan Allah ka bar xancenta.yaea ahmad yaga abba ya sha mur ya tsare gida,dole ya saki batun.suka yi sallama ya tafi,abba na cewa sai yaxo da dare.yasa yaron shagon ya goge mashi mashin din sannan ya tada,ya kalli ummi fuskarshi daure xo ki hau.itama tata fuskar a daure take.tahau suka tafi,iskar dake kadata tasa xaxxabin dake san kamata ta qaru.ya kafe mashin dhn ya kalleta,muje mana.ta bishi suka shiga cikin sahad store din.tsaye tayi tana kallanshi yana diba kaya.da alama na iyalanshi yake diba,dan taga ya soma da pampas. Hannuwanta harde a qirjinta tana kallan shi,kome nashi yana birgeta.ya waiwayo ya dubeta, tsayuwarme kike yi a nan da ba xaki dauki abinda ya kawo kiba? ta rasa me xata dauka,sai kurun ta dauki makilin ta riqe a hannu,ya gama diban abin da yake so,sannan ya aje gaban masu amsar kudi.ya dubeta,bakya buqatar komai kenan? ta nuna mishi makilin din hannunta,tana murxa shi.ya harareta baxa ki dauki komai ba,kina da kayan tea dasu complex? tace a,a.y2e to ki tsaya kada ki dauka.ya soma dibo mata saitin sabulan nan daya taba sai mata na aloe vera,dan yaga duk kananan qurajen sun mutu.sannan ya hada mata da audugar mata guda biyu.ya kai table.lkcn ta dauki madara da milo ta kawo.yace wawiya,dalla matsa ki bani gu.yaje ya qara tsinto mata ,sanna akayi musu total ya biya.suka fita.kafin sukai gida haqoranta sun s6a haduwa,gashi tana ta takurewa,yace lfy,wani irim xama kika yi haka?tace,sanyinake ji.tana magana muryarta na makyarkyata.wani dan asibiti ya nufa da ita nan kusa da unguwansu aka dubata. Wurin allura,nan fa a ka soma daga.Ta ce,ita kam bata san allura.Abba ya daka mata tsawa da cewa,Allurar ce abn tsoro?Na gane sam ba ki son ki koma mkrnt,a gobe ne kuma sai kin koma duk abnki. Ta ce, Naji zan koma amma yanzun kam dn Allah Ya Abba kada amin allura.Nurse dai sai kallonsu take yi tana dariya. kwai Ummi sai ta soma hawaye ita fa har ga Allah bata son allura.Nurse ta ce,To ka rike ta mana ko ba Amarya ba ce?Naga shagwabar tayi yawa. Abba ya ce,Me? cikin tsawa ya yi maganar,hr sai da Nurse din ta tsorata,ya ce kanwata ce fa,kin ga wannan kucakar tayi kama tayi kama da Amare? Nan take Ummi taji ta muzanta,sannan km ta tsorata da irin tsawar da ya yi,ba ta san lkcn da ta shige a ka yi mata allurar ba. Ta fito tana sharar kwalla suka koma gida. Sai dai tana hada kayanta a Jaka,Sannan ta ga wadannan sabulun da kuma audugar,kenan shi ne dama ya sai mata wancan?ko me yasa ya sai mata kuma hr da augugar mata? . wata zuciyar ta ce,kila dn yaga Umma bata san kan abubuwan zamani ba sosai.A fili ta ce,kai umma tasan audugar mana. Haka dai ta ci gaba da tufka tana warwarewa,hr ta gama shirya kayanta. Yau kuma a bayan Tsohuwa ta za6i kwanciya,da dn komai ba sai dn suyi hirar yaushe gamo. Sai dai Maimakon hira sai ta tsunduma a tunani,ta bar Tsohuwa tana ta zance ita daya. Fitarsu da Ya Abba ta tsaya mata a rai,ita tayi ta tunowa tana murmushi.Sai dai bata Son tuna lkcn da ya yi wa Nurse din nan tsawa dn ta ce ko ba amarya ba ce kom me yasa zai mata Tsawa? ita kam kalamn Nurse din nan sun birgeta,shi kuma daga ganin yadda ya yi tsawar nan kalamn ba su masa dadi ba.......... wai takwara bacci ki ka yi ne?Muryar Tsohuwa ta katseta,ta ce,Idona biyu Tsohuwa.Ta ce, Tunanin me ki ke yi ne haka?Ummi ta ce "Um" ina tuna gobe yanzun ina can.Tsohuwa taja tsaki,Ai mai sunan Malam ya san takan mugunta. UMMI dai ta ce "Um.Tsohuwa kuwa sai yi take da mai sunan Malam.Tun Ummi naji tana "Um", hr zcyrta ta soma tsanar kalaman Tsohuwa. Sai dai bata da damar ta katse Tsohuwa tunda dn ita take yi,bata da mafita da ta wuce ta bar dakin,don haka ta suri butar Tsohuwa,wai zata je kewaye(bandaki). Shi ma Abban da ke kwance a tsakar dakinshi kan kafet ya tada kai da katifarshi,ban da tunanin fitarsu ta dazun ba abn da ya keyi. Sai dai damuwarshi daya,me yasa samari da dama suke kawowa Ummi hari?Me yasa ya ke jin zafin haka?Zuciyarshita amsa da cewa,ka so ko ka ki kana Son UMMI."a fili ya furta "Haba dai so,Allah ya tsare ni." Tun misalin tara Ummi ta gama shirinta tsaf,cikin kayan mkrnt mai ruwan hoda,mai gida-gida.Da kuka ta bar gidan yau ma. Haka nan kuka take hr suka isa mkrnt,ta samu Khadija hr tazo,dn haka tare suka kwashe kaya.Kafin Abba ya tafi sai da ya yi mata fada kwantankwacn wnda Umma tayi mata.Waton ta kula d kanta,kuma tayi abn da ya kawo ta,waton krt.Sannan ba ya son tayi kawance d yaketa shari'a.irin wanda wasu watsatstsun yaran ke yi.(Allah ya shiryesu). Sannan ya jadadda mata batun ibada,sannan ya kawo kudi ya bata,ta ce Umma fa ta riga ta bani. Ya ce,"Ki kara."ZURFIN CIKI book 2 part 5 ZURFIN CIKI book 2 part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:12 Umma fa ta riga ta bani. Ya ce,"Ki kara." Rayuwarta a mkrnta wannan karon ba laifi,sai dai fa hr yanzun ta tunu da gida sai tayi kuka. Su Safiyya suna mmkn yadda Habiba take da matsanancin nacin gida. ******** Abba ya shigo gidanshi dauke da ledajin kayan miya,da sauri ya dire su kofar kicin ya nufi Bishira da ke kofar bandaki tana shara amai. Ya kama ta,"lafiya?Me ki ka ce? Sai da ta gama aman sannan ya karasa da ita ta wanke baki da fuska a cikin bayin. Ya ce,Ba ki d lfy ne?Ta soma Hawaye, Ka gani ko Babn Walid,kila fa ciki ne da ni.Tun wancan Satin ya kamata in ga al'aldata amma shiru. Ya ce, To menene na kuka? Yi shiru,Allah ya inganta.Ta harare shi Dana fa bai shekara ba.Ya ce,To dole ne sai danki ya shekara sannan Allah zai baki wata kyautar? Ta soma kuka,Ni dai zan je a ciremin ne. ya hade fuska,Ban yarda da haka ba. Ganin ta tada hnklnta tana cewa "Dama Hjyrsu ta ce mata tabi a hankalu ta ki ji gashi nan yanzun tana da wani ciki. Ya ce To kada ki damu kin ji? Zamu je asibtin dn a tabbatar da cikin kafin a san abnyi. Da za suje asibiti shi ne ya dage sai da tayi wanka,dn d farko kaca-kaca ta dauko mayafi, ya ce sai tayi wanka ta canza tufafi. Gwajin farko ya tabbata tana da ciki,nan ta shiga kuka. shi kanshi ya damu domin bai so ciki yanzun ba.A son ranahi sai an yaye yaron kafin wani cikin. Amma ba shi da ra'ayin zubarwa,nashi ganin kyautar Allah ce,dn haka ya amsa ya kuma gode. Ya lallashe ta da cewa,ta yi hkr su amshi kyautar Allah dn haka wani na nema da kudi bai samu ba. likita ya ce,Kada ta damu,taci gaba da bai wa danta abnci tana hada mishi da nonon,a hnkli zata yaye shi bana farat daya ba. Bayan ya kaita gida ya kuma lallashenta,saiya nufi gurin Umma. Bayan sun gaisa,ta tambayi iyalanshi ya ce "Daga asibiti ma muke da Bishira." Umma ta dube shi da sauri,Waye ba lfy? ya ce, Ita ce.Sai kuka ma take yi wai dn an ce tana da ciki. Umma ta ce, Ikon Allah, to Allah ya inganta.Sai dai kuma kada Walid ya sha ciki. Abba ya ce,likiya ma ya yi mata bayanin yadda za ta yi masa,hr ta janye shi daga nono cikin hikima.Umma ta ce, Da za ta yarda ma an kawo mana shi nan. ya ce,Ai dama nan zan kawo shi da zarar an yaye shi Umma. Sam bai fada ma Bishira nufinshi na baiwa Umma Walid ba,dn yasan ba zata ta6a laminta ba.Sai dai itama tasan dole hakan zai yi. Don haka ta garzaya gurin Umman Bashir ta shaida mata cewa sunje asibiti,dk ta fada mata komai,sannan ta ce ita danta take tunani kada ya dauka ya kawo wa Ummarshi ita ma a mallake mata yaro. Umman Bashir Ta ce Wannan a zaune take,sai dai in ko ba a kai shi ba.Amma ki bari daga kin kula ya daina damuwa da nonon ki janye shi,zan zo in taho da shi wurina. Bishira taji dadi tare da cewa, Hakan dai yafi. Sabuwar kazanta ta samu,Bishira dk abn bi bangon daki an tofe da yawu.Rashin wanka sabo,kai abn nata sai addu'a. Ibada kuwa ba a mgn,domin dai tuni ta aje Sallah a gefe,Azumi dai tana yi amma in ta sha bata ramawa.Allah ya shirye wanda ya 6ata. Abba ya dai yanzun tuni ya yafe abincin gidansa,matsawar ba shi da kanshi ya girka ba,don kuwa dama can shi mutum ne mai kyankyani. In zata fita takan wanke kafafunta ta dauki kaya ta saka,sai ka rantse tayi wanka.Amma da zata matso kusa da kai,nan za ka ji kauri na tashu da karni da kuma wari. Dole ya hkr da laluranshi ta aure a gurinta,domin in yaje shimfidarta ba zata ki ba,amma wari da zarni suna hana shi yin komai cikin nutsuwa. In kuma dakinshi ya kirata ko bata kwana ciki ba har gari ya waye yana jin warin jikinta a shimfidarshi don haka lokuta da yawa yake hakura da ita. *********** . Ummi tana kwance kan gadonta,yayin da Khadija da Safiyya suke zaune bakin gadon Safiyyan wadda ke kallon Ummi. Hirar masoyinta take basu,Safiyya bata ko gajiya da zancensshi. Khadija ta ce,ita ma da zata taho har kuka nata Saurayin ya yi. Sai lkcn Ummi ta dube su,"kuka Khadija?Khadijata ce,"Riris Kuwa. Ummi ta ce, Hu'um ba namijin shi yasa nike da za6i a kan irin mijin da zan aura. Safiyya ta ce,"ke banza,dk cikin so ne. Ummi ta ce Ban damu da sai namiji yaso ni ba,in dai ya tara abubuwan da nake so ga namiji to zan yi amfani da kasantuwata 'ya mace in koya mishi Sona. Khadija ta tashi ta dawo kusa da Ummi,Kin san me ki ke fada?Koda yake sanar damu yadda ki ke son mijinki ya kasance? Ummi ta ce "Na farko mai son Addini,Mai Ilimi duka 2,mai hakuru ,sannan yana da saurin fushi,mai kuzari da kwarjini. Ma"abocin tsafta da tsantseni,wandadk tufafin da yasa sai sun kar6e shi,mai biyayya ga iyayensa,sannanmai kula da gidansa,baki mai tsare gida,ga yawan Ibada, Safiyya da khadija suka kwashe d dry,Khadija ta ce, Ina za ki samu dk mai wadannan lissafin da ki ka yi??? Safiyya ta ce, Kuma fa bata gama lissafin ba ke ba ki ji ana cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba? Ummi ta ce,Akwai shi,Ya Abbanmu haka Halayansa suke. Yanzu ma da ni ke lissafin shi na ke kallo a idona.Khadija ta ce,To ba dan uwanki ba ne da shi kenan kin samu a gida.Ummi ta ce,Wuu fitina Road,wannan ya mugun tsanata, ina son dai me irin halayarshi ds dabi'unsa.Khadija ta ce,Har da kamaninsa? Ummi ta ce,sosai ma. Saitaga sun sa dry.Safiyya ta ce, Malma shi ki ke so,kuma dk yanda a ka yi ba shakikin ki ba ne,da aure a tsananinku. Umma tayi Shiru tana kallonsu,Khadija ta ce,Habiba kenan,wai har saurin fushinshi tana so. Ummi ta 6ata rai tare da cewa,Tunda kun kasa fahimtata shi kenan.Ya zan yi in ce ina son Ya Abba yana da matarsa? SAfiyya ta ce,ke dai in da aure Tsakaninku kada ki tsaya "ZURFIN CIKI, kizo a karshe kina da kin sani. Ummi ta ce,A bar zancen. 32... Sai dai kuma a daran ranar ta tsinduma duniyar tunani.Tabbas zuciyarta da shisshiga take,tunda ta rasa wanda zata so sai Ya Abba. Wanda ya yi mata muguwar tsana.Afili ta ce,Duk kauce-kauce da kewaye-kewaye ba za su kai ni ba,Ya Abba nake so. Hawaye Suka soma sintiri daga idanunta. Wannan lkcn ziyarar da yazo Abba da Umma d Tsohuwa da Alhj Karami dk suka zo. Dadi ya kashe Ummi,ta rasa jikin wanda zata fara fadawa don dadi. Alhj karami ta soma kamkamewa sannan Umma,Tsohuwa kam ai tana manne jikinta hr suka zo tafiya.Shi ko Ya Abba yanzun kunyarshi take ji,dn haka tunda suka gaisa mgn bata kara hada su ba. Sai dai jife-jife suna satar kallon juna,in sun hada ido sai ya dan daure fuska.Safiyya da khadija sun gaisa da su sannan sun yaba da yadda a ke ji da Ummi. Da za su tafi kuwa Ummi kuka Tsohuwa kuka,sai da Abba ya ce ba za a sake zuwa da su ba,Sannan Ummi tayi shiru.Sun tafi sun barta d kewarsu,Kamar yadda suma suka tafi suna kewarta. ********** . Bishira da kanta ta dauki Walid ta kai ma Umman Bashir,domin ta san zai kai ma Ummanshi ne. Abba ya rufe ta da fada lkcn d y tambayi dan ta ce ta yaye shi ta kai ma Umman Bashir. Ya ce To je ki dauko mn yarona,dn ba can nayi niyyar kai shi ba,Ta rike kugu,kaje mana da kanka,tunda ba ka son zamn danka hannun mahaifiyarka to ni ba zan yi saken da Mahaifiyarka tayi ba a ka raba ta da danta ina fata ka fahimci karatuna? Kallo kurum ya bita da shi,sannan yaja tsaki tare da cewa,Dube ki kmr wata Bauna,jiki sai tsami yake. Ta ce,Eh dk abn da zaka ce kace. Ya juya ya fita rai 6ace. Umma ya Samu ya fada mata, ta ce, To menene na bata rai Abba? Can din da nan ba dk daya ba ne? ai ba za su cutar da shi ba. Ya ce, ki fahimce ni Umma,ba ina nufin zai cutu ba ne,amma can da yara kanana,nan kuma babu. Sannan......... ...... Sai kuma ya yi shiru tare d cewa,Shi kenan. Umma ta ce,Yauwa bana son kana daga murya kan abn da bai kai ya kawo ba. Allah ya raya mana shi ya kuma sauketa lfy. Abba Ya ce Ameen. Gidan (T.V)sun kira Abba sun masa (intervier)da kusan wata 2,dmn ya cire ran samun akin, ko da yaje suka ce sun dauke shi aiki. Abn d yasa suka yi jinkiri daukarshi,suna canza tsarukan aikin ne sannan sun sake tantance ma'aikatansu. Litinin Abba ya soma zuwa aiki kmr yadda a ka bukata,dakin watsa labarai a ka kai Abba. Sam bai samu matsala ba,dk d shi na mai yawan surutu ba ne,amma a cikin sati 1 ya goge da aikin,km an yaba da yadda yake watso labarai. Yana yi da Hausa minti sha biyar da turanci minti sha biyar,ana sakawa karfe 7 na yamma. Abba ya kama aiki cikin sa'a nan da nam sai farin jini cikin abn d bai fi wata ba ya nemi izinin a bashi fili koda mint 15 ne don gabatar da wani fili da ya yi masu don matasa. filin yana kiran shugabannin matasa na unguwanni suna hira da su akan halin da matasa suke ciki na shaye- shaye da sace-sace da kuma rashin sana'a. Da turanci a ke shirin,sannan a kan baiwa sauran matasa na gida su bugo waya su fadi nasu ra'ayin,game da abin da ya kawo hakan,da kuma hanyoyin da za a bi don magance su. Haka nan ya kan samu lkc ya shiga cikin matasan musamman ma su shaye-shayen da marasa sana'a dn jin ra"ayoyinsu,da dalilan fadawarsu cikin harkar. Kafin wani lkc filin ya yi suna kuma kullum yakan tallata filin kan cewa ya kamata Gwamnati ta dauki nauyi filin don yana taimakawa mata wurin inganta rayuwar matasa. Cikin ikon Allah sai gashi Gwamnati ta yaba da filin,ta dauki nauyin shirin kuma an sa shi hr fannin Radiyo. Lallai Abba ya shigo da kafar dama,Sannan hukumar gidan Radiyo tayi Matukar farin ciki da zuwan Idris Aminu Idris,wannan Ma'aikata. Sannan sai Abba ya zama wani sabon tauraro wurin Al'umma,dk in da a ka ganshi ya zama abn kallo. Matsalar shi daya gidanshi,in ka ganshi a waje Sam ba za a kayi tsammanin haka zaka samu gidanshi ba,Dattin ya karu,musamman da ya kasance yanzun ba shi da lkcn kanshi ballatana ya yi sammakon share gidan. Wankinshi mai kaiwa yake yi,haka nan nasu ya ce ta dinga kaiwa makota gidan wanki. Amma kafin ta hada ta kai aiki ne ita dai tayi kallo ko a shiga makota hira. Sam Abba ko adreshin Zai bada ya gwammace ya bada na gidansu Ummanshi dn ba ya so aje gidanshi ************* . Kwanci tashi Ummi suna ta fana da jarabawa zuwa (SS2) cikin ikon Allah suka gama. ranar da aka yi musu hutu kamar ta sani bata tsaya jiran Abba ba,Ta nufo gida. Shi kuwa lkcn suna kici-kicin kai Bishira asibiti zata haihu,amma yana sane da cewa yay Ummi zata dawo kuma hnklinshi na can. Motar wani Salis Abokin aikinsa ya aro ya kai su asibitin ita d Ummanashi. Bayan ya ba d dk wani abu da suke bukata ya ce Umma za shi dauko ummi. Umma ta ce,Ka barta tukunna in matarka ta sauka lfy gobe sai kaje tunda tana mkrnt ne. Ya yi-ya yi Umma ta ki,dole ya hkr. sai bayan la'asar sannan ta haihu,Nurse ce ta zo tayi musu albishiri an samu 'ya mace. Bayan an kintsa uwar,sannan a ka kaita dakin hutu,su kuma a ka kawo musu 'yar.Nurse din da ta kawo 'yar ta ce d Umma ke ce Mamanta? Umma ta ce,'Eh."Nursr din ta ce "kazantar yarinyar tayi yawa,kafin ta haihu sai da likita ya korata ta yi wanka,muka yi mata aski ko'ina jinkinta datti. Gsky Mama mijinta yana kokari,yanzun kuje ku dafa ruwan dumi ku kawo mata tayi wanka. Abba ya yi tsaki ya ce, kin ji ko Umma,Allah ya kara.Umma ta ce,Yanzun kaje gida ka dauki babban filas dina ka shiga wurin Umman Bashir ka ce Mata ta dafo ruwan Zafi,daga nan ma sa ji haihuwar. Yana shiga gidan tun daga zaure ya jiyo Muryar Tsohuwa tana cewa,Naji shiru-shiru kin ga dai hr yanzu. Yana saka kafa a tsakar gidan muryar Ummi ta daki dodon kunnanshi.in da ta ce,Kila kuma ta haihu yanzun. jinin jikinshi ya tsinke dn jin Muryae. Ya nufi dakin.Tana zaune tana shan rake. Ya dubeta, ita ma shi take kallo dn tunda ta diro ba wanda take muradin Gani irin shi,cikin sanyi murya ya ce,Ummi ke da wa ki ka taho? Ta sunkuyar da kai,Ni da wasu 'yan mkrntrmu ne muka dawo. Ya ce '"Good,tashi ki dafa ruwan zafi ki zuba a babban flask. ya dubi Tsohuwa da take ta tambayarshi ko mai dakin nashi ta sauka? Ya ce, Eh ta haifi 'ya mace. Tsohuwa cikin takaici ta ce,Sai yanzu kaga damar bani amsa?Dan walakanci kawai? Kai mai sunan Malam ka gyara halinka. Abba ya ce,Yi hkr Tsohuwa dk na gaji ne,Nan kuma ina yi wa Ummi mgn. Ta ce kana mata fadan ka dai. Ya ce,Tsohuwa wai ni hr yanzun ba zan wanku a wurink ba game da Ummi? ta ce, Ina fa zaka wanku?Har abada mai sunan Malam kai ba me kaunar takwara bane. . Yace to naji a bar maganar yanzu dai kishiyarki ta haihu.an samu ya mace.tace Allah ya raya mana. Yana jingine da bango yana kallon ummi tana ta shige da ficen daura ruwan zafi.komai cikin tsafta da natsuwa take yi. Sai da tasa ruwan zafi ta wanke flask din kasancewar anjima ba'ayi amfani dashi ba.ta tafasa ruwan tazo ta bashi,ya ciro wayarshi ya mika mata. "sa min a caji naga nepa sun kawo wuta" ummi ta jona waya sannan ta ci gaba da girkin dare don tasan Alhaji bai cika son wani abu da dare ba sabanin tuwo. Ta gama wanka sannan tayi sallar magariba tana kwance gadon tsohuwa tana tunanin abba. Tsohuwa nata lazimi in tayi magariba bata tashi sai tayi isha sannan taci abinci.ummi ta tuna wayar da yaya abba ya bata ajiya. Da sauri ta tashi tare da cewa "ke tsohuwar nan anzo tayaki hira kin share mutane" ta mike ta nufi daki ta dauko wayar ta kunna HEHE KIN MANTA YAYA ABBA KENAN?" Sakwanni ne sukai ta go slown shigowa sannan sai kira tashin farko data daga wayar muryar mace taji, ta ce "dawa nake magana" wadda ta kira ta ce "ina mai wayar?" ummi tace "dq matarshi kike magana,ke din wacece?" waccac n ta ce "in yazo ki tambayeshi? yasan me lambar." nan da nan sai ummi ta samu kanta yana juyawa,tayi tsakita kashe.ta shiga duba sakonnin da yawansu na mata ne masu sonshi,daidaikune na maza masu nuna yabawar aikinsa.hankalin ummi ya tashi ganin yadda mata suke farautar abinda take tsananin so.ta kashe wayar cike da nadamar kunnata Hankalin Ummi ta samu kanta yana juyawa,tayi tsaki ta kashe.Ta shiga duba sakonnin da yawansu na mata ne ma su sonshi,dai-daiku ne na maza ma su nuna yabawar aikinsu. Hankalin Ummi ya tashi,ganin yadda mata suke farauta abnda take tsananin So. Ta kashe wayar cike fa nadamar kunnata. Sintiri ta dinga yi a tsakar dakin,Sallamarshi ce ta, katse ta.Ta amsa ciki,sannan ta zauna ba tare da ta kalle shi ba. Ya ce,Bani wayata da abinci 'yan asibiti. Ta mike ta dauko masa abncin,sannan ta bashi wayar.sai dai tana yin komai ne fuskarta daure. Ya ce,Lafiya na ganki wani iri?ta dago ido ta kalle shi,ta sake tsuke fuska. lfy lau.Ya ce,shi kenan na tafi Sam bata tanka ba. Yana fita ta mike a kujera,so takeyi a lkcn ta samu makanta mafita,shin ko dai ta tare shi ne ta fada masa? wata zuciyar ta ce,In ko ya dinga kwallo da ke sai kin rasa mai cetonki. Ta tashi tare da cewa,Bari kawai in fada ma Tsohuwa.Zuciyarta ta sake rayawa.Tsohuwa fa ba zata yarda ba, domin kullum tana bada shaidar tsanar da Ya Abba ya mata,ta koma ta zauna. Sai ta samu kanta da fashewa d kuka,tana fadin wannan wace irin fitina ce ta same ni?me yasa zcyt ke son tozarta ni? Me yasa zata so wanda ya tsane ta?Ta mike ta shige uwar daka. Gado ta hau tana son ta lallashi zcyrta,dn ta daina son Ya Abba. Shi kuma yana tafe a mashin zcyrshi na mitar bata gaji da ganin Ummi ba,yadda take ta kai kawo ya ke gani a idonshi. Lkcn da ya kai musu abnci me jego ta gyare,dama ta zubar d jini ne shi yasa suka ki sallamarta,sukace sai da Safe. Ya samu kannanta sun zo da wata 'yar Babnsu.Sun gaisa an yi 'yar hira sannan suka ta fi lkcn ya dauki 'yar ya yi mata kallon sosai. Ya dubi Umma kin san yarinyar nan da wa take min kama?Ta ce,A'a. Bishira ta tsare shi da ido,ya ce lkcn d Ummi na karamarta sak wannan. Umma ta ce,Kana nufun d Ummi take kama?ya ce,"Eh,Bishira ba kunya ta ce,Allah ya kyauta ni 'yata bata kama da wata can wai ummi. Umma tayi saurin cewa,Dama zolayarki yake ba suyi kama ba.Shi kuma ya kalleta.Ko ki so ko kada ki so yarinyar nan sak take kama d Ummi. Ya mika ma Umma ita,yana ci gaba da fadin Maman Walid kina bani mmki,kina zaton zan ki raba 'ya'yanku d Ummi? Ya girgiza kai"Sun hadu hr abada ,domin in kin tsaga jikin 'ya'yanki dole za ki ga jinin Ummi. to ya ya ma ki ke tsammanin zan so wanda ba ya son Ummi? Ta ce, "Oho! Ni ba ka sona kenan?To in da na gode ma Allah dk dyniya ta san cewa Ummi bata kaunarka.dk da kana wanta.Ba ita ba ce silar kariyarka?ko an kashe ka ma bata da asara. Umma ta ce,'Abba jeka ban son in kuma jin bakinka in na isa. / ZURFIN CIKI book 2 part 7 ZURFIN CIKI book 2 part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:16 Ta samu an saka ranar auren fati da saurayinta Fahat,nan fa Alhj ya ce dama ke ni ke jira uwata ki dawo. A masu sonki ki fito da daya a hada auranku da 'yar uwarki Fati. Hankalin Ummi ya yi matukar tashi,ranar kasacin abnci tayi. Da suka zauna da Umma a daran ta ce Umma baki fada ma Alhj bani da tsayayyen saurayi ba?Umma ta kalleta,ba shi yasa na ce Kitsada ba,amma ba kya son fita. Duk kin bi kin kori masu sonki Abba na daure miki gindi,kin san dai Alhj ba yarda zai yi ki wani ci gaba ba,gara ma kin yi kokarin fidda miji kafin lkcn da ya dibar miki,in ki ba haka ba ya daki da mai rabo. Ummi tasa kuka ranar,kwana tayi tunani hr ta yanke shawarar zata fada ma Alhj Ya Abba take so. Da safen taje hr dakin Alhjn ta gaishe shi,ya ce uwata naga kamar bakinki da magana ko?Ta dube shi "Eh,a'a ba komai.Ta mike,dakin Tsohuwa ta shiga ta haye gado ta soma kuka. Tsohuwa ta dubeta a rude,Takwara ke da waye,? Nasan ba zai wuce me sunan Malam ba,dn shi ne kadai ke hana ki sukuni. A ran Ummi ta ce,shi ne kam,amma ba irin wanda ki ka sani ba. Amma a fili sai ta ce,Tsohuwa Alhj ne wai in fito da miji,kuma abn da ke damuna ni ba wanda na ke so. Tsohuwa ta ce, "Au, shi ne abn kuka?To bari kiji bana ba zan goyi bayabki ba,dn da ubanki ya ji ta tawa da yanzyn kina da diya 2 in da rabo. Amma mai sunan Malam ya ce za ki ci gaba da krt,yamzun ko tun da Allah ya kawu mu angama wannan kaddararriyar mkrnt ba sai aure ba? Ga Bunta nan hr an yi baiko, to rana guda za a yi shi in muna cikin masu rai. FUU Ummi ta fice,ta shiga dakin Umma tana tunanin wa zata fada ma matsalarta?kamar an tsikareta ta dauki mayafi zata fice. Umma ta ce, "Zo nan, ina za ki? ta ce "Wurin Fati. Tana shiga Bashir zai fito . Ya ce Yauwa Ummi ina son magana da ke. Ta dawo baya ya fita kofar gida ita ma ta fito,suka tsaya ya ce "Ummi gaskiya dama ba wani abu ba ne, ni dai na tsinci kaina da sonki. Ummi ta dafe kirji da sauri."Sona?" ya ce kwarai kuwa, dn haka za ya ki ka gani?ta dube shi,sam babu wata alama da ke nuna cewa dan uwan Ya Abba ne. Ta girgiza kai "kayi hakuri kawai Ya Bashir,wlhy zuciyata ta jima da kamuwa da son waninka." ya ce, Me ki ke nufi?Kin fi son bare da ni jininku? Ummi ta ce,"Ni dai na fada maka." Ya ce, "To kin fada min,ni kuma zan fada wa su Alhj." Gabanta ya fadi. Shi kuma ya yi tafiyarsa, . Sabon tashin hankali kenan. Sai damuwa ta lunku,bata ta6a marmarin zamn mkrntr kwana ba sai ranar. Ta rasa me zata yi taji dadi,gida ta koma cike da nadamar fitowa,ta zauna a falon Umma ta soma kuka. Umman tana dakin mijinta ya yi karin kummali. Sai da ya fita sannan Umma ta maido hankalnta ga lamuran gidan, kan kujera ta samu Ummi ta nata rera kuka. Umma ta ce "Ke Ummi lafiyanki? Abun ya soma zama iya shege,daga cewa ki fito da miji sai ki tsira kuka? To ina ganin kwadantaki zamu yi muci. Ummi ta ce, "Ni fa ba kukan da nike yi ba kenan,ni fa Ya Bashir ne fa. Umma ta ce Bashir me,? kiranki aka yi? Gara daya da ke ki. ta ce ba fa dukana ya yi ba wai cewa yai wai fa yana sona. Tab,Allah ya tsare ni. Umma dn Allah bana sonshi,gaban Umma jikinta a mace ta ce "Tabdi,ai ko in Alhj ya ji wannan zancan ta zauna. Ummi ta sake firgicewa, cikin kuka ta ce Da na shiga 3 Umma, ya ya zan yi ne don Allah?Umma ta ce,"Mafita daya ce ki fidda wani kafin zancan yaje wurin Alhj. Yinin ranar Ummi ta rasa mafita Addu'arta daya,Allah ya turo mata ko ma waye a daran yau ta ce ya turo iyayenshi. Wayar Umma tana hannunta,ta rubuta text ta goge yafi sau 20 da niyyar ta tura ma Ya Abba cewa tana sonshi,amma da ta tuno da irin dukan da zai zo gidan ya yi mata in ya karanta sai ta share. Ita dai ta san shi kadai take so. Tayi Sallar Istihara kusan sau 3,amma hr yau zcyrta na nan makale da son Ya Abba. Don bayan Isha'i kuwa a ka aiki kiranta, ai tare da dan aike suka fita. Wani saurayi ne wai shi Sahabi,dan unguwar ne Kuma sana'ar aca6a yake yi. Na dai manta. Suka gaisa ya gabatar da kanshi sannan ya fada mata dalilin zuwanshi ba tare da wani nazari ba,ta ce ta amnice. suka yi sallama ta dawo gida,umma ta tambaye ta wanene?Ta fada mata,sai dai Umma bata gane shi ba. Can jimawa Bashir ya aiko Kamal kaninsa wai Ummi tazo,ta ce kaje ka ce masa ba zan zo ba,ya sake aiko shi cewa in bata zo ba shi zai shigo. Umma ta ce mata tashi kije. Ummi hr d kuka ta fita,dn a rayuwarta ta tsani Bashir,sbd yanda ya raina Umma. Kuma ba ya ganin kowa da gashi sannan tana ganin in hr ta auri Bashir zai mata tsakani da auren Abba. Tana zuwa ta same shi zaune a dakalin kaofar gida,ta isa gurishin. Ya Bashir kiran me ka ke min? Ya ce,kin sani kema. Ta ce Ya Bashir dn girmn Allah ka bar ni ba,Usaina gidan kurma ce buduwarka ba? Ya ce Da ba, ya ci gaba da cewa,Ummi ina sonki so na hakika nayi mamakin yadda lkc daya zcyta ta kamu da sonki,to wai dn Allah ni me yasa ba ki sona? ta ce Ya Bashir ina da wanda nake so tun farko..........kamar daga sama suka ji muryar Abba yana cewa,Kai Bashir me ka ke fada? ya ce sonta nake. Abba sai da wayarshi da ke hannunshi ta kwace ta fadi don figici,bai bi takan wayar ba ya isa gabn Bashir ya ce, In ka kuma furta kalmar so ga Ummi sai na maka matsiyacin duka,ke kuma hr da fitowa kin zo tadi ko? kafin tayi magana ya ce,Bace min daga nan. Bashir ya ce,Amma ai ba laifi ba ne don nace ina sonta? Abba ya bige mishi baki tare da cewa In ji wa ya ce maka ba laifi ba ne?Bashir ya ce,An haramta aure tsakaninmu ne? Abba ya cakumo wuyan rigarsa Ni ne nan na haramta haka,kuma kar in kara jin wannan mgnr. Bashir ya fige ya nufi gida yana fadin cewa Yau zan samu Alhj da mgnr. Ina ruwanaka da zaka ce ka haramta min sonta? . Abba jikinshi hr 6ari yake dn tashin hankali, yasan in mgnr taje teburin Alhj to ta kullu yanda yake mishi mgnr hada auran Ummi da Fat. Har ya saka kafa a zauran gidan su Umma,sai kuma ya fasa ya dawo ya nufi gidan su Bashir din,yana saka kafa a zauren gidn Alhj Krm na fitowa. Don haka sai yaja baya,Alhj ya fito ya ce,A'a Abba ne? Abba ya ce "Eh ni ne. Ya gaida Mahaifin nasa,sannan Alhj ya tambaye shi cewa Babn naka yana gida? Gaban Abba ya yi mummunan faduwa,ko dai Bashir ya fada wa mahaifinsu ne? Alhjn ya ce ko ba ka ji ba?Abba ya ce "Eh a'a ban riga na shiga gidan ba. Alhjn ya ce To bari in ganshi. Nan jikin Abba ya jike da zufa. Da azama ya shiga gidan. Mahaifiyarsu tana alwala ya ce Umma ina Bashir? ta dube shi Lafiya ba ko sallama? ya ce Nayi ba ki ji ba ne? ta amsa sannan ta ce lfy ka ke nemanshi? ya ce lfy lau. ta ce Yana daki,shima na ganshi ya shigo a fusace. Abba ya nufi dakin. Bashir na zaune kan katifar idonshi na kasa yana girgiza kafarshi ta dama,Abba ya shiga ya ce,Bashir nazo ne in sake gargadinka a kan Ummi,sai dai naga hr kayi kuskuren fada ma Alhj krm ko,? Bashir ya mike ya daga sauti Ban fada mishi ba,amma ina da niyya. Ina sonta babu wanda kuma ya isa ya hana ni sonta. Abba ya kashe masa fuska da mari. Sai suka ji muryar Mahaifiyar tana cewa, Kara mishi Abba,ka cika dana. Ta shigo dakin hr gabn Bashir ta ce, Ni za ka tozarta? kayi kuskure. Ai da in ga ranar aurenka da Ummi gara naga gawarka kwance yafi min sauki. Abba da Bashir suka dubeta a rude. Ta ci gaba da cewa Bashir kai ma kasan ba zai ta6a sa6uwa ba ne in hada jini da Suwaiba,kafi kowa sanin kin da nike mata,zan iya daukar ranta ba don tsoron hukuma ba. Kuma hr dny ta nade ba zan ta6a kaunarta ba,kai ko fatan alheri ba zan ta6a mata ba. Ta kalli Abba, Baka ta6a faranta min rai ba irin yau,dama nasan cewa dole wata rana ka bayyana dana in dai kai jinina ne,na gode Allah da yasa ka zama mai kishina Kuma ka wanke dukkan laifukan da ka min a baya da ka nusar da ni Bashir na shirin jefa rayuwata a cikin garari,da ba ka mishi mgn ba yaushe zan san yana shirin jefa ni cikin bala'i. . Abn da Umma bata sani ba shi ne,tuni Abba ya yi mutuwar tsaye,hnklshi ya ninka na Bashir tashi,dn haka Bashir ya riga shi fita daga dakin. Da kyar Abba ya dago ido ya kalli Umma,ta ce Daina damun kanka shi ma din ko ba don Allah ba zai dawo hanya,duku-dukayau sati guda fa kenan da naje kauye na saida 'yar Akuyata guda daya sannan na bada kaji 2 ga Bokan kuka sbd a min akin da Ummi ba zata samu miji ba. Sai kuma a ce ko satin bai rufe ba dana na cikina ya zo ya ce yana sonta? Da sauri Abba ya dafa kirji Umma Boka! Boka ki ka ce Umma? Inna lillahi wa'inna ilaihin raji'un,Umma kin san cewa zuwa gurin Boka shirka ne ga Allah? kin san duk wanda ya mutu a shirka Allah ya yi alkawarin kona shi a wuta?Umma kina cikin hadari............ta kaste shi. Kai Abba!Ni ce nake cikin hadari?Ni ce Allah zai kona a wuta? ya ce, umma bana nufin haka, ina fada miki ne ki kiyaye da zuwa gurin Bokaye makaryata,macuta 6arayin Imanin Jama'a. Na ranste miki da girmn Allah umma Bokaye 'yan wuta ne,matsawar ba su tuba ba. Ta ce, Kai ni rufe min baki,da za ka ce karya ne sau nawa suna min asirn kuma yana ci. Ba gashi nan da ya min na kada Ummi ta riga Fati samun miji baga Fatin ta riga samun ba? ummi kuma ba ta d masoya. Abba ya ce, Umma kin ga karya ko? wa ya fada miki Ummi bata d masoya? ta ce, To me yasa ba wanda ya tsaya? Ya ce, Ni dai Umma ki bar zancan nan a wurina, Bashie zai bar Ummi ko yana so ko baya so,dn haka na hada ki d girmn Allah kada ki koma gidan mishieikin Bokan nan. Ta ce, Ba zan koma ba in hr zaka raba Bashir da alakakai din yarnyar nan. Ya ce Na miki Alkawari. ta ce, Shikenan. Ya fice jiki babu karfi.URFIN CIKI book 2 part 8 ZURFIN CIKI book 2 part 8 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:18 Kasa shiga gidan su Umma ya yi,haka nan ya manta sam da batun motar da yazo da ita a kofar gidan Umma. Ko Bishira bata san cewa ya shigo gidan ba,tana can jarabar kallonta na tsiya,ya rufe gidan ya nufi dakinshi. Ranar mu2m 5 bacci sai dai 6arawo,Umman Bashir kwana tayi saka da mugun zare. Umman Abban ma juyi kurum take yi hr Alhj ya gaji ya ce,Yau dai sai juyi ki ke yi. ta ce Na kasa bacci Alhj. Ya ce, Tashi to kiyo alwala kizo ki kama sallah,in kina da damuwa ne sai ki fada ma Allah. Umma bata tsaya ba,ta tashi. shi ko Abba wani matsanancin ciwon kai ne ya hana shi sallah. Ya dai yi nasarar yin alwala da ya shiga daki sai jiri. Dole ya kwanta rigingine tare da dafe kanshi da hannuwa guda 2,sunan Allah yake ta kira dan neman dauki. Ita ko Ummi dirshan ta zauna tana kuka,hr sai da hawayenta suka kafe,idanunta suka shiga zafi,kanta ya soma sarawa gefe daya. Ita ma ringingine ta kwanta tare da lumshe ido,Istigfari kurum take yi tare da hailala,shi ko Bashir mafarkai ne suka hana shi bacci,dk mafarkan na Ummi ne. Da safe da matsannancin zazzabi ya farka,dn haka bai iya zuwa Masallaci ba,da kyar ya yi alwala.yana idar da sallah ya kundundune cikin bargo. Matsanancin ciwon kan da Ummi ta tashi dashi ya firgita 'yan gidan,Musamman Umma wadda ta same ta kwance a tsakar daki da safe. Ganin fuskarta a kumbure ya tsorata Umma,hr sai da ta kira Alhj.Nan fa Alhj ya dauko wayarshi ya shiga kiran Abba,kan cewa yazo ya kaita asibiti. Sai dai tayi ringing ya kai sau 10 amma ba a daga ba. Alhj ya ce Ina yaron nan ya shiga ne?kuma ga motarshu a kofar gidan nan,na ganta da asubahi da na fita Masallaci. Umma ta ce,Tao Allah yasa dai lfy. Har karfe 8 Alhj na neman layin Abba shiru ba a dauka ba,ga Ummi rike da kai tana ta salati Umma ta ce,Alhj ko Bashir za ka sa ya duba shi? Alhj ya koma daki ya dauki hula ya nufi gidan Abba. Gidan a kulle ya same shi,dn haka ya dinga bugawa.Abba na jiyowa amma ba zai iya tashi ba,haka dk ringing din da wayarshi ke yi yana ji ya kasa tashi ne. cikin bacci Bishira taji bugun gida ya yi yawa,ta tashi ta bude. Da Alhj suka yi ido 2,ya ce lfy ba ku tashi ba? Ta ce Mun tashi. ya ce Ina maigidan naki? ta ce Ina ga ya fita,bari in duba. Ta juya ta nufi ciki. Alhj ya cika da mmk,ya za a ce wai mace bata san fitar mijinta ba? Anya wannan matar tasan darajan mijin? Tunaninshi ya katse lkcn da ta dawo tana cewa Alhj yana kwance ba shi da lfy. Alhj ya bita yana cewa Ba shi da lfy,amma ke ba ki sani ba?Wanna wane irin zama ku ke yi ace kina matarsa amma ba ki san cewa ya tashi ba lfy ba? Bishira ta ce To ai shi ne bai kira ni ya fada min ba. Alhj ya ce, Allah ya kyauta. ya nufi dakin. Abba na kwance ya kundundune cikin bargo sai rawar sanyi yake yi. Alhj ya yi Sallama ya shiga dakin ya rusuna ya daga daidai fuskarshi ya janye bargon ya ce, Abbana ba ka ji dadi ba? Abba ya bude ido,idanunshi jajir,ya ce Abba kaina ne tamkar zai 6alle. Sai zazza6i tun daren jiya. Alhj ya ce,Ikon Allah Yau kuma abn da na wayi gari da shi kenan? Ummi ma na can kwance da ciwon kan,to tashi. Shi yasa nake ta kiranka don ka kaita asibiti amma da ka daga ba. Yanzu tashi in za ka iya ka kira Ahmada abokinka sai ya kai ku asibitin. Abba ya ce To Wayar Ahmada din a kashe don haka sai Alhj ya ce "Af, na tuno da Bashir,kintsa bari in je muzo naga mator can kofar gidanmu ko?Abba ya lulubo makullin motar yaba Alhj., Zani kawai Umma ta daura ma Ummi,sai ta zura mata hijabi,suka shiga bayan mota su 3 da Umma da Alhj,sukaje gidan Abba suka dauko shi. Bishira taso zuwa amma suka ce ba wuri ta bar shi kawai. Asibitin kudi ne kuma likita guda ne ya duba su. Ummi dai hawan jini ne don ita a ka fara dubawa. Gado likitan ya bata,sannan Abba ya shiga shima likitan ya ce jininsa ya hau,amma ba kamar nata ba. Nan ya roki likitan cewa kada ya fada ma iyayensu abnda ke damunsa,ya rubuta mishi magunguna kawai. Likitan ya ce Ba komai. Amma me ya ke damunku kai da sister dinka ciwonku iri daya kuma ya kama ku a lkc daya? Abba ya ce Ba komai lalura ce kawai a ka kaddara ta same su lkc daya.Da Abba ya fito sai ya ce ma su Alhj Zazza6i ne. sai dai shi kanshi ya ji mmkn ciwonsu iri daya. Yana jingine da bango a dakin da a ka ba Ummi gado,yayin da Bashir ya tsaya a gabn gadon Umma tana zaune a kan kujera. Alhj krm d Bbba suka shigo tare da Likitan ya kalli Abba Yarona kana bukatar bacci ga. Abba ya ce To yanzun zan tafi gida. Ya iso kan Ummi wadda a ka daura ma ruwa,ya ce ku barta ta huta bata bukatar hayaniya,don haka ku rage daga cikin dakin. Alhji ya ce, To mun gode. Suka tafi suka bar Umma. A mota Alhj ya ce da Abba,ka fada a wurin ainkan? ya ce, Eh abokin aikina ya kira ni kuma na fada masa. Alhj ya ce,To shi kenan,yanzun sai muje can gidanmu zaka fi hutawa... .Yanayin aikinku ne ba ka samun bacci ko? eh kurum Abba ya ce,amma shi yasan tunanin Ummi ne ya ke hana shi bacci da matsalolin da yake hangowa. Yinin ranar yasha bacci,sai kusan 4 ya tashi ya yi Sallah,ya ji dadin jikinshi. Bishira tana gidan Umman Bashir wai ita da tazo jinyar miji,tana bata lbrn wai Abba bai fada mata ba shi da lfy ba,ya kira Alhj yazo yana ta min surutai wai mijina ya fita ban sani ba,meye- meye? Umman Bashir ta ce, Da Allah kyale su,don wani sabon iskanci ma wai Bashi ne ke son Ummi. Bishira ta mike zumbur tare da cewa, Bashir fa ki ka ce Umma? Hu'um,lallai da wani abu. Bashi da ya tsani Ummi shi ne zai ce yana sonta? Umma ta ce, Sannu 'yar albarja,ashe kin fahimta,? Tabbas nasan ke za ki fahimta,to in gaya miki Bashir ko yau da safe fa sai da muka yi ta dashi. Dubi yadda Bashir ke min biyayya amma yau ina fada yana fada. wai hr da ce min shi bai ga wani mugun halin Suwaiba da nike fada ba,tana min alkairi amma ni kullum ina binta da sharri. Kai dai jin wannan zancan ka san ba yin Bashir ba ne,don haka na ce masa ba komai nasan ba yin ka ba ne. Bishira ta ce,Tabdi,Umma sai kin tashi tsaye. Ta ce ke dai bari ai ina cikin wani hali shi kanshi miji naki sai na nema masa taimako. Don wannan ciwon nashi ban yarda shi ba, kuma lkcn daya. Fati ta shigo gidan da sallama,ta shiga dakinsu ta canza kaya. Umma ta ce,sai ina? ta ce Ya Abba ne ya ce in zo in canza kaya zamu je asibiti wurin Ummi. Bishira ta mike ya farka ne? Ta ce Eh hr ya yi wanka da sallah Umma ta ce Bari in same shi bai gama jin sauki ba zai tafi wurin wata can kema banza mara kishi kin taho jiki Na 6ari,Fati ta ce,Umma don Allah ki daina irin wannan abubuwan,wlh Umman su Ummi bata yin haka Bishira ta fita tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3 Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta ce, Ni a wa zan shiga maka ga . Bishira ta fita tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3 Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta ce, Ni a wa zan shiga maka gaba a baka ku taru kai da matarka ku halakata?Duk da Abba yana jin jikinshi gim, sai da ya dar dara,sannan ya ce, Sai ka ce ma su yankan kai? Tsohuwa kuma da za ki ce na cika zcy yanzun ba ga mata nan ina da ita ba tana kawo miki karan ina dukanta ne? Tsohuwa ta ce Tabdi,ni yaushe ma wannan guzumar matar taka zata zo guna da sunan kawo min kara? Ban da ma haka ni bani shi da mara kunya. Ya ce, sai Ummi ko? koda yake ita ai takwararki ce shi yasa lkcn da tayi tata rashin kunya ta zama 'yar lelanki. Tsohuwa ta ce ai wannan ba kuciya ba ce? Yanzun ko kai ba ka fi ta hankali ba.Abba da fati suka sa dry. suna isa dakin suka samu Umma suna waya da Alhj,Ummi kowa hr lkcn bacci take yi. Abba ya jingina da bango yayin da Tsohuwa da Fati suka je suka tsaya a gabn gadon. Sunyi Sallama da Alhj shi ma ya kira ne ya ji ko Ummi ta farka. Ta ce masa ba ta farka ba,kuma Likitan ya ce an fi son tayi baccin. Nan suka gaisa tare da tambayar mai jiki,Abba kallon Ummi yake,yau daya duk ta fyade kmr ta yi sati,sonta da tsananin kaunarta ne suka sake mamaye ko'ina na jikinshi. Ya kalli Umma wadda ke tambayar nashi jikin, ya ce da sauki. Sannan ya kalli Ummi tare da cewa Umma wai dame Ummi ta fara? Umma ta ce kamar ya ya? Ya ce mmkn ciwon Ummi nake,wai hawan jini?Dama can bata da lfy ne? Tsohuwa ta amshe da cewa, ko kai ai kasa mata hawan jini,irin tsanar da ka mata Mai sunan Malam ai ta isa. Abba ya ce Don Allah Tsohuwa ki daina mgnr nan. Ya dubi Umma yana me kara maimaita tambayarshi. Ta ce ko kusa ai kasan Ummi bata cika laulayi ba ma,lalura ce dai yanzun bata ga babba ba ta ga yaro,amma mafari daga yi mata zancen aure shi kenan take ta kuka. Abba ya ce to don Allah Umma ku barta da zancen nan,ina krtn take so tayi kayanta,don gudun hawan jinin nan kada yakw tashi akai-akai. Tsohuwa ta ce Don kawai kada jinita ya hau sai a zura mata ido kada tayi aure?ai ko lallai sai dai kada jininta ya sauka. in ya hau,aure ya haifeta dole tayi shi,in a kasarmu ce ta Zamfara wane ita. . Abba ya ce Muje in kai ki gidan Tsohuwa. Ta ce ban tafiya, sai naga dama Umma da fati suna ta musu dry. Nan dai Abba ya fita yaje wurin likitan ya amshi takardn maganin,dn da farko bai rubuta ba magaungunan ba. Kwanan Ummi 3 a asibiti a ka sallem ta. Abba ya kwashe su zuwa gida. Saurayinta Sahabi zuwanshi 2, kuma sun je da mahaifiyarshi. sai lkcn ne ma ta mishi kallon tsaff,sam ita ba sonshi take yi ba,sai dai gara shi da Bashir. Kuma ta lura Bashir din da gaske yake yi. Domin kullum zai zo safe da yamma,haka nan yakan dan tsaya hr yafi Abba wanda ke zuwa sau daya hr tana cewa ina ma yadda Bashir ke nuna tausayinshi a gare ta Abba ne. An shuri sati 2 da sallamo ta kuma ta warke sarai,sai dai fa hr yanzun Alhj yana nan kan bakanshi,ganin Bashir na son takura mata sai ta daina fita. Abba ya kira Basshir shagonshi wani yammaci,ya sake fada masa ya rabu da Ummi sai dai yau da lallashi yazo masa,. Ya ce Bashir ka ga mahaifiyarmu bata sonka da ummi,dn haka ka hkr ka nemi wata,na maka alwashin kashe ko nawa ne dn yin hakan zai faranta ran Umma. Bashir ya yi 'yar dry,sannan ya mike tsaye Ya Abba kenan! kana tsammanin ni wawa ne?nasan ba don Umma ka ke fafutukar in bar Ummi ba kana yi ne don kana sonta. Gaban Abba ya fadi,cikin saurin baki Abba ya ce,In ji wa ya fada maka? Allah ya kiyaye. kai ka san Ummi kanwa na dauke ta. Bashir ya kakki cikin idon Abba,sannan ya ce,"Haba Malam,fadan da ka ke da kalaman da ka ke furtawa suna nuna kishinka ne karara. Dubi cikin idanunka,kishinUmmi ka ke yi. don haka sai ka hkr ka bar min ita,domin ka san ba wanda zai fi girgiza Umma tsakanina da kai irin ka. Ya nuna Abba da yatsa, Za tafi bakin ciki ka zama mijin Ummi fiye da ni. Abba ya daga hannu ya falla mishi mari Bashir ya dafe wurin sannan ya kalli sau 'yan shagon wadanda marin ya janyo hankalinsu. Don farko ba su san abn da a ke tattaunawa ba.Bashir ya ce, ka mare ni? Abba ya ce, Zan kara maka,ko za ka rama ne? Bashir ya ce, Ba zan rama ba,amma zan fada ma su Alhj yau dinnan ina son Ummi. ya fita fuu. Abba ya zauna ya rike kai yana huci. shi kam Bashir ya kudurci niyyar fada wa iyayensu yau dinnan. Abba ya kira wayar Umma ta daga suka gaisa lkcn karfe 6 na yamma ya ce, Ummi fa? ta ce Gata can kwance. Ya ce Ba dai jikin ba? ta ce A" aikin karance-karancenta take. Ya ce, Ba ni ita Umma. Umma ta kwala ma Ummi kira,ta mika mata wayar tare da cewa "Yanyanki ne ke son magana da ke. Yau ce rana ta farko da suka yi waya a matsayin shi na Abba,ita kuma Ummi, in an debe lkcn da suka yi waya a matsayin shi na Abba ita kuma Suhailat. Tayi sallama cikin sanyi murya can kasan makoshinta ya amsa tare da runtse ido sakamakon tsigar jikinshi da ta tashi. Ya ce "Ummi ta ce Na'am yaya. Ya ce "Kina son Bashir? ta raunana murya. Yaya am sorry to say bana son shin gsky. Ya ce To yau kam zai sanar da su Alhj cewa yana sonki,in kina san kida wanda ki ke so to ki gabatar da shi kafin shi ya rigaki. Takaici ya kama ta, kamar ta ce, Ni kai na ke so.......ya ce kina jina? ta ce,To Ya ce, kin san in su Alhj suka ji ba ki da mafita,Ummi ta ce To ni fa bani da wanda nake so shi ne ban san yadda zan yi ba. Ya ce, shi kenan matsalarki ce., ya kashe wayar. Ummi tayi shiru tana tunanin mafita,ko dai ta hkr ne ta aure Bashir din? kai a'a to kuma gashi wanda take so ya ce matsalarta ce. Can dai ta yanke yadda zata yi,don haka ta kosa Alhj ya dawo. Tun kafin suje wurin cin abnci ta same su a dakinshi su da Umma,ya yii wanka yana kokarin fita sallar magriba. Ta ce Alhj dama wanda ya ke zuwa gurina ne ya ce in fada muku iyayenshi za su zo. Dadi ya kashe Alhj ya ce To to dan nan unguwar ne? ta ce Eh ya ce To madallah dama wannan yaron na sabon titi din nan Suwaiba wanda kwanaki nake fada miki nasan ubansa a kasuwarmu ya ke? Ta ce Naji wanda ya soma zuwa wurin Ummi? ya ce Shifa, Uban danai masa zancen naga dansa wurin 'yata sai cewa ya yi auran gida za su yi masa,ko ni na so hadin nan sai dai Allah bai so ba. Ya kalli Ummi Yaushe za su zo? ta ce Ya dai ce in tambaya ne. Alhj ya ce To Allah ya kawo su. Da dare Sahabi yazo ta ce Sahabi an ce in maka mgn ka turo ya ce Alhamdulillah, dama ina son in miki mgn sai ina tsoron kada ki ce ya yi wuri don haka gabe zan turo. Bashir yazo ya zauna gabn Alhj suna cin abnci ya gaishe su. Suka amsa ya yi shiru yana tunanin ta ina zai fara? Alhj Babba ya ce ya ya Bashir akwai wata matsala ne?Ya ce Am dama ina son in ce ni dai ina son Ummi ne. Ummi kuma?Alhj karami?Ya ce Eh Alhj Babba ya ce Ta amma ya aka yi kayi nauyin baki hr a ka ba wani dama? Bashir ya ce Alhj Wanene? Alhj karami ya ce Sai ka san shi? koda ba a tambaya ba, ba zan ba da goyon baya a baka Ummii ba, tashi ka bamu wuri. Abba ya ce, Bashir je ka ci gaba da addu'a Allah yasa Ummi ta zam rabinka,zan so haka dn na jima ina son zumuncin nan. Iyayen Sahabi sun zo kuma an basu hr ma an tsaida ranar daya fa ta Fati. Tun daga ranar Ummi kullum cikin kuka take wanda iyayenta suka kasa gane nufinta. Bashir bai daina cin alwashin sai ya auri Ummi ba, dn haka kullum cikin aiken kiranta yake. Ban da haka ma ya maida hnkl kan sana'arshi tunda ubansa ya mishi gorin wa zai ba shi mata ya ki tsayawa sana'a nashi ganin in ya rike sana'a r za a ba shi. Abba kuwa ya ji ya yi ma gidan wai don ya goge Ummi a ranshi. Anya "ZURFIN CIKIN nan zai kai su? . Sai mu hadu a littafi na Uku don jin yadda za a kare. ZURFIN CIKI book 3 part 1 ZURFIN CIKI book 3 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:21 Na Halima Abdullahi K/Mashi 1... Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je gaisheta." Ahankali yake tukin, kira'ar Ahmed Suleiman ce ke tashi wadda ya yi murya biyu cikin sanyin murya. Wayarshi d ake gefe ta soma ruri. Ya kali fuskar wayar, Hajiya Nina ce, don haka ya ci gaba da tukinshi, kusan kira na bakwai sannan ya daga. Ta ce, "Lokacinka ne za ka iya yin duk yanda kaso, amma kafin kazo hannuna wacce shawara ka yanke?" ya ce, "Ta me?" Ta ce, "Au, ka manta kenan? To ba damuwa za ka zo yau ne ko sai an dauko ka?" 2.... 'Yar dariya ta kufce masa, "Ki sa a dauko ni sai ka ce wani karamin yaro? In kin ci gaba da bibiyata za kiyi nadamar hakan." Ta ce, "Ko kuma kai kayi ba, na baka awa goma ka kawo kanka in ko ka 'ki, hum! Za a kawo ka." Abba yaja tsaki "Yanda ki ke zatona na wuce haka". Ta ce, "Idris Aminu Idris raina ya biya da kai, kuma dole sai na cimma hakan, jarumtarka din nan ta sake bige ni, kasan dalilin da yasa na ce nan da awa goma? In ka lissafa zai baka bakwai na yamma. Daidai lokacin da ake watso mana labarai ina kwadayin ina tare da kai, lokaci guda kuma ina kallonka cikin TV kana feso turanci, kasan ina son muryarka ga shi ka gwanance da iya tsara turanci, sai ka ce yarenka. Kada in cika ka da surutu sai mun hadu anjiman". Ta kashe wayarta. Abba yayi kokari ya tsaida motar shi a gefen titi a hankali ya furta "Allahumma ajir ni fi musibati..." ya kifa kansa a jikin sitiyarin motar, yana tunanin wai shin ba za ta sauya masa a halin da yake ciki ba? Wata zuciyar ta ce in tasan kana cikin wani halin ko? A haka ya isa gurin aikinsa, tunda suka shiga dakin daukar labarai, abokanshi suka gane yana cikin wani hali duk da bai kasance mai yawan magana ba, amma yau ba kamar kullum ba. Salis ne ya kasa hakuri, don haka bayan an gama daukar labarai da kyar sun je su yi sallar Azahar suna zaune wata Bafulatana da ke kawo musu fura ta kawo. 3..... Dama shi Abba bai cika shan fura da rana ba, yafi shanta da dare, don haka siyan kurum yake yi. Bayan yaje gida sai yasha, amma ranar ya ce mata ta bar shi kawai, ta jiya ma tana nan bai sha ba. Da ta tafi Salis ya dube shi, "Idris ba ka da lafiya ne?" Ya ce, "A'a me ka gani?" Ya ce "Ba yanda ka saba ba, duk kwanakin nan na lura kana cikin damuwa". Abba ya dube shi amma ai kasan nayi rashin lafiya ko? Salis ya ce dakata Idris kada kaga kamar na matsa maka sai na ji cikinka, ko kusa ba haka ba ne. Ni mutum ne mai saurin karantar duk dan Adam din dana zauna kusa da shi na awa daya bare kai da na zauna da kai tsawon lokaci, muna kuma ci gaba da zama. Idris na fahimci kana da matukar 'ZURFIN CIKI' dalili kenan da yasa ban ta6a damuwa da in tambaye ka matsalarka ba. Sannan dalilin 'ZURFIN CIKIN' da naga kana da shi ne yasa har kwanakin baya na kawo maka matsalata da iyalina. Alhamdulillahi ka bani shawara kuma nayi amfani da ita, kuma naga ci gaba, matsalolina sun ragu". Abba yayi dan murmushi. "Wai kana nufin saboda ina da 'ZURFIN CIKI' ne kaga ya dace ka sanar da ni sirrinka?" Salis ya ce "Kusan haka ne, don me Zurfin Ciki ya iya hadiye magana, sai dai a ganina zurfin ciki wataran zai iya fadawa halaka, ko wata gagarumar matsala". Abba ya dube shi, "Wace irin halaka? Salis ya ce, "Me zurfin ciki sai ciwon zuciya ya kama shi yana muku-muku da matsalarshi, wani ma har ya mutu da ita ba wanda ya sani. Amma in abu na cinka ka samu wanda ka yarda da shi mai amana ka fada masa zaka ji dan dadi". Abba ya ce, "To kai tunda baka da zurfin ciki, kenan bai dace ka ji matsalar ba?" 4....Salis ya tuntsire da dariya, "Ta nan ka 6ullo? Ai dama ka sani ba ina son yabon kaina ba ne, a'a duk surutuna nasan abinda nake fadi". Abba ya ce, "Salis na gode da kulawarka, matsalata ko ka ji ta nasan shawarar da za ka bani bata wuce ka ce in yi hakuri ba, ni kuma ba wannan ni ke son ji ba. Salis ba komai nake yiwa 'ZURFIN CIKI' ba, yawanci in ina da matsala nakan tunkari Ummata ne kuma ta warware min komai. Saboda na taso da wannan koyin da ta min, yanda na shaku da ita ko su Alhajina ba mu shaku haka ba". Salis ya ce, "To me ya hana ka fada mata wannan karon?" Abba ya ce, "Ba zan iya ba, sai dai in za ka samo min mafita ban da hakuri, to in fada maka". Salis ya ce "In sha Allah ba za arasa mafita ba". Nan Abba ya bai wa Salis labarinshi da Ummi tun farko har zuwa yau. Salis ya numfasa, sannan ya ce "Kaga illar 'ZURFIN CIKI' ko? Ummin ma taka ce amma kana nema ka rasata, ai ba mafitar da ta wuce ka samu Ummarka ko Alhajinka ka fada musu muradinka". Abba ya ce, "Tabbas haka ce mafita, sai dai idan na aikata haka abu biyu za su faru, na farko na zubar da mutuncin Alhajina, domin babu girma, sun ba da 'ya ba tare da wani dalili ba ya ce ya fasa. Sannan haramun ne neman aure cikin aure". Salis ya ce, "Haka ne, to hakurin kawai zaka yi". Abba ya ce "Ai mun yi ban da bada hakuri ko?" Salis ya saki dariya, sannan ya ce "To kayi addu'a". Abba ya mike tare da fadin "Ka tayani da addu'a". Daga nan ya shiga dakin, Filin Don Matasa na Hausa, don likkafar shirin tayi gaba yanzu har na Hausa yana gabatarwa. Kullum sake kar6uwa shirin yake a gurin Jama'a. 5......UMMI Tana kwance kan doguwar kujera, yau kwana hudu kenan bata saka Abba a idonta ba. Tamkar Umma ta san abinda ke ranta, sai ta tsinkayi Umma na cewa "Yau kwana uku ne ko hudu rabon Abba da gidan nan, sai dai ya kira mu a waya. Alhaji dai ya ce, yana zuwa gunsa kasuwa". Ummi ta ce, "Nima yanzun nake tunanin haka". Ta miko ma Ummi wayarta da ke gefenta. "Lalubo min shi in ji". Da ta soma /ringing/ sai ta mika mata. Ya dauka suka gaisa ta ce "Abba ko dai na maka laifi ne?" Ya ce, "Umma me a ka yi?" Ta ce, "Tsaf, ka dauke min kafa, wanda kullum komai saurinka sai ka biyo". Ya ce, "Ina nan zuwa Ummata, kina raina duk inda nabi, harkoki ne suka taru suka sa ni gaba". Ta ce, "Ni kuma sai na ke ganin kamar don ba mu dauki shawararka ba ne ta game da karatun Ummi shi yasa ka". Ya ce, "Umma ba haka ba ne, zan shigo da zarar na dawo". Ta ce. "To". Sam shi batun shi yayi ba, sai dai baya son yazo ya ga Ummi domin da ya ganta yake neman kwanciyar hankalinsa ya rasa na tsawon lokaci. Amma yanzun kalmar Salis ta karshe daya fafa masa da za su rabu a gurin aiki ita yake tunawa. Dafa shi ya yi tare da cewa "Miste Man shawara ta karshe, ka nunawa kanwarka kana sonta a fili". Ya ce "Tab, wannan shi ne me wahalar ai, furtawa Ummi kalmar so. Zubar da kai kenan". Ga shi ba sonsa take ba, duk yanda mace ke girmamaka da zaran ka ce kana sonta shi kenan ka zube a idonta. Musamman in kai ke sonta ita ba ta sonka, wata ma har da rashin kunya zata tsula maka, a fili ya ce, "Ina, ai ba zan ta6a gigin bari ta san ina sonta ba". Daga kasan zuciyarshi yaji an ce za ko ka sarata. Sai da ya yi sallar Isha'i sannan ya yi wanka ya saka kananan kaya, ya fito da nufin gidan su Ummarshi. Bishira ta bishi da kallo, daga ganin fita zai yi ta fito da saurinta tana cewa "Baban Walid! Baban Walid!!." Ya tsaya, ta dube shi "Ina za ka?" Ya ce "Gidan su Umma". Ta ce, "Ba wani gidansu Umma, kai dai kurum tadi za ka je". 6.... Dariya ta su6uce masa, sai da ya dara sannan ya ce "To in ma tadin zan je ya za ki yi dani?". Ta ce, "Tab!, ai na rantse maka kayi kadan. Kullum kuma ina 'kara fada maka kai mijin mace daya ne rak!" Ya ce, "In ji ki ko?" ta ce, "Eh." Ya ture ta gefe tare da cewa "Da sauki tunda ba fadin Allah ba ne". Yayi ficewarsa ya barta nan tana ta masifarta. Kan dakalin kofar gidan, Ummi ce zaune da Sahabi suna hira, duk da cewa Sahabin shi kadai ke ta surutanshi Ummi na can duniyar tunanin abinda zuciyarta ke so. Tun daga nesa ta shaki kamshin turaransa, zaraf ta mike tsaye. So take ta kalli fuskarshi amma ya dauke kanshi daga gare su. Haka nan ya share sannun da zuwan da ta ke mishi tare da shigewa cikin gida abinsa. Sahabi ya ce, "Ya Abba na nan kuwa kwana biyu na rabu da ganinshi?" Ta dauke kai sannan ta ce "Zan tafi gida". Ya ce, "Haba Ummi, zuwana fa kenan?" Ta dube shi. Ji take tamkar ta sheka mishi mari, ta ce "To kaina ciwo yake yi, sannan kuma ga Ya Abba yazo baya son ina dadewa a waje". Ya ce, "To shi kenan sai gobe?" Ta ce, "Don Allah kada kazo gobe, ka bari sai jibi". Ya ce "Za ki azabtar da ni, ba zan iya kwana biyu ban gan ki ba." Maimaikon taji dadin kalmar, sai taji takaici ya mamayeta. A ranta ta ce,, "Tunda ga gyatumarka ba". Ya ce, "In zo goben don Allah?" Cikin muryar tausayi yake maganar, ta ce "To shi kenan". Ta soma tafiya, ya dan tako ya biyo ta tare da cewa "Sahibata mu kwana lafiya" A kagare ta ce "Uhum". Ta samu Abba suna hira da Umma, ta tura mishi kular birabisko tana lallashinshi ya ci, tayi sallama Umma ce ta amsa. Ta shiga idanunta kan Abba, ta zauna a kujerar da ke fuskantarshi. Umma ta ce "Har Sahabin ya tafi?" Ummi ta ce "Eh". Ta tsura ma Abba ido tare da cewa, "Ina kwana Ya Abba?" Umma ta ce "Wane irin kwana kuma Ummi da wannan daren?" Ta ce, "Au, zan ce ina yini?" Ya amsa tare da kallonta, "Lafiya". Ya mayar da dubanshi ga Umma. "Umma Matar Ahmad fa ta haihu". Ta ce, "Eh, ba jiya ka fada min ba a waya? Me ta samu ne?" Ya ce, "Mace ta haifa, gashi ta sha wuya". Umma ta ce, "Allah Sarki, to Allah ya raya mata, zan je in dubota in mata barka gobe". Ya ce, "Allah ya kai mu, ai Ahmad yayi dacen mata ba kamar ni ba. A da Umma bana tunanin sake aure, amma yanzun ina ganin dole sai nayi mata biyu". Umma ta ce, "To ba dai yanzun ba duk nawa ka ke kuma yaushe kayi wancan?" Ya ce, "Umma ke dai ki min addu'a, ban samu irin macen data dace da ni ba". Ta ce, "Ina maka addu'a, Allah ya shirya maka matarka." Abba ya ce, "Ko ta shiryu sai nayi aure insha Allahu". Ta ce, "Abba ni ko gani nake ba ka san wadda za ka aure din ba itama da nata kalar halin zata zo, sai su taru su ruda ka". Ya kalli Ummi wadda ya lura da kallon da ta tsare shi da shi kamar tana son jin abin da yake fada ne. Ya maida idanunshi kan Umma. "Na yarda da tarbiyar wannan yarinyar da nake son aure yanzun, duk da yarinyar bata sona tana girmamani". Umma ta ce, "Har ka samu kenan, 'yar gidan waye? Ummi kuwa tuni makoshinta ya bushe, ta zaro idanu tana son ji wa kuma Abba ke so? 7:....Ya kalli Ummi ganin yadda ta zaro ido ya ce "Ke ni ke fadama wa ki ka zaro ido ki ka tsare ni da su?" A hankali ta lumshe idanu sannan ta maida kanta kan hannun kujera, ya fuskanci Umma "Ba 'yar unguwar nan ba ce", matsalar da yarinyar bata sona". Umma ta ce, "To ka bar ta mana ka samu mai sonka? Yo in haka ne ma ka ce gara matar taka ta gida, don ita tana sonka". Yayi shiru zuwa can ya ce "Umma in dai zan sameta zan aureta a haka". Umma ta ce, "Kayi addu'a, ina ko mamakin mene ne ta gani na 'ki a tare dakai Abba?" Ya ce cikin 'yar dariya "Umma ai ba dole ba ne sai ka birgke kowa". Ummi ta mike jiri na dan dibanta ta shige ciki. Zance ya dada watsewa, ta furta bayan ta fada kan gado, ni ina son shi shi kuma ashe yana can ya zarme da son wata. Ranar ta raba dare tana kuka daga karshe ta soma ba kanta shawarar ta samu Abba ta ce a fili dama shisshigi ne irin na zuciyata Ya Abba ba irina yake so ba. Shi kuwa zuciyarshi ta soma zargin wani abu a kan Ummi, irin yanda ya ga tayi kamar hankalinta ya tashi da batunsa. In ko haka ne zai fi kowa murna, wata zuciyar ta ce ka sani ko tsabar jin gulma ne yasa ta kafa maka ido duk da haka yasha alwashin bibiyarta. Sun taso daga sallar Juma'a shi da su Ahmad gidan budurwar Tukur suka dosa, wayar Salis ta katse shi. Wani aiki ne ya taso dole ya koma gurin aiki. Ya sauke su a unguwar shi kuma ya nufi gurin aikinshi. Karfe biyar ya baro gurin aikin da nufin yada zango gidan Ummanshi. 8.... Yasan yau juma'a duk yanda aka yi zai samu abinci na musamman, don al'adarta ce girkinta na juma'a daban ne, tana girmama ranar da abincin da ta san mijinta zai yi farin ciki da shi. Haka nan ta kan yi kwaliyyar musamman, shi yasa yake kara kwadayin aura Ummi, ya san zata dauki wannan tarbiyyar. Matasa guda uku a tsaye gefen titi cikin fara'a da murna suka tsaida shi, ya saba kusan kullum sai irin haka ta faru. Matasa kan tsaida shi suna ma su nuna jin dadi da ganinshi, a gaisa su wuce. Wasu kuma su amshi lambarshi har da ma su son adireshinsa, yanzun ma sai ya tsaya zai fito, tsum! Yaga sun bude motar sun shigo. Biyu baya daya gaba, ya ba su hannu suka gaisa su duka. Na gaban ya ce. "Mai matasa ai muna jin dadin taimakon da ka ke mana. Ya kamata a baka Sardaunan Matasa". Daya daga baya ya ce "Sarkin Matasa gaba daya zamu ba shi, don yana kokarin gurin binciko matsalolin matasa". Abba ya yi murmushi tare da cewa, "Na Gode". Dayan da bai yi magana ba sai ya ce "Amma mai Matasa ka san da wannan matsalar?" Abba ya waiwaya da nufin jin karin bayani, sai ko ya fesa mishi wata farar hoda a fuska. Take nan atishawa da tari suka tirnike shi. Ya soma mutsuka idanunshi bakinshi na furta "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Kafin 'yar sakwanni kanshi yayi din, kuma ya fita daga hayyacinsa. Suka tuka motar suka tashi dashi. * Farkawa ya yi tamkar wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude ido tangaran a kan silin, irin na masu hali. Kwan lantarki irin na kasaitattun gidaje ya daki hancinshi. Nan take ya shiga tunanin me ya kawo shi nan? ba 6ata lokaci ya tuna duk abinda ya faru, da sauri ya tashi zaune yana fadin "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Ya ci gaba da kallon dakin, cikin tangameme ne yana dauke da tafkeken gado da sauran saitin shi. Sai kafet din tsakar daki da kayan kallo, ga kuma kofofi guda biyu. Ya tambayi kanshi da cewa me ya kawo ni nan? me matasan suke nema a gurina?" Take muryar Hajiya Nina ta fado masa, inda take cewa "Za ka zo yau din ne ko sai an dauko ka?" ya girgiza kai tare da cewa, Lallai wannan makirar matar ce tasa aka mi shi haka". 9... Nan take ya soma karanta addu'ar neman tsari. Daya daga cikin kofofin ta bude, ya kure idonsa gurin da kallo, matar ta shigo sanye cikin doguwar riga baka mai ma6allai a gaba. Fara ce kyakkyawa, shekarunta suna tsakanin Talatin da takwas zuwa arba'in da biyar, domin kyawun nata sun 6oye shekarunta, ta baza gashi a kafada. Tsura mata ido yayi yana son tuna inda ya ta6a ganinta, domin tabbas yasan fuskar. Muryarta ce ta katse shi,"Dama nasan zuwa yanzun ka farko, kuma ka gama nazarin yanda aka yi kazo nan. Kila ma tunda kana da kamannin ma su basira ka hararo wadda tasa a ka dauko ka". Ya ce, "Kwarai kuwa". Lokacin ne ya tuno inda ya santa, wato Hajiya Zabba'u ce matar shaharraran Attajirin nan Alhaji Uzairu wadda a ke nuno ta a TV da Jaridu tana taimakon talakawa da Marayu. Wadda ake labarin tsoron Allahnta da gudun duniyarta, wadda ta gina Masallatai da Makarantun Addini ma su dama. Ya girgiza kai cikin matukar mamaki, ta ce "Ka gane ni kenan?" Ya ce (Cikin karfin hali) "Lallai mutum mugun ice. Wannan shi ne Allah a baki shaidan a zuci". Ta ce "Kai ne na biyu da ka furta wannan kalmar, sai dai bana fata ka zama na biyu da ya bakunci inda na farkon ya tafi. 10.... Ta tako a hankali ta dunfaro shi, ya matsa baya cikin zuciyarshi yana korar shaidan, 'yar dariya tayi. "Nutsu Idris ko ince Abba. Ba fyade zan maka ba". Ya dubeta da sauri, "Eh haka nace, in na son hakan zan maka, amma ba hakanne burina ba". Ta zauna bakin gadon, "Ka zo mu daidaita, in kana tsoron ciwo zan baka makari, sai dai ina so ka sani bana dauke da wata cuta". Ya ce, "Karya ki ke, kina dauke da mummunar cuta". Ta ce "In ka tashi daga dan jarida ne, ka koma Likita zan baka dama ka gwada ni". "Ya ce ba ki bukatar gwaji don ga ciwonki nan a fili ciwon zuciya". Ta ce, "Sam ba ni da ciwon a zuciyata, to in ma ina da shi me zai dameka tunda ba dauka za ka yi ba". Ya sake ja da baya ya ce, "Zuciyarki ta kamu da ciwon zina. Ta yi duhu dumdum! har bata iya ganin gaskiya...". "Ta daga mishi hannu, "Dakata min, ban tambayeka labarin wa'azi ba, domin in shi nake son ji ina da kaset-kaset kala-kala zan saka na ji". Ta mike zuwa wata durowa ta bude, dauri uku ta dauko ta aje gaban madubi na 'yan dari biyar-biyar sababbi dal! Ta ce, "Wannan za ka sha mai ne sannan kasa kati, kuma in ka kwantar da hankalinka zan canja maka mota, zaka je Makka. 11.... Sannan idan naga kana bin umarnina zaka yi suna a aikin jarida fiye da duk wani dan jarida da ka sani a kasar nan. Kai zaka taka duk wani matsayi da dan jarida ke takawa". ta sake nufoshi da tausasa murya. "In kabi yanda nace ba kai ba sake kwana a talauci..." Ya katseta da fadin, "In naki fa?" Ta hade rai tare da zuba mishi ido, "Shima kallonta yake, sai a lokacin ya ga tsufanta ya bayyana. Ta juya mishi baya tana 'yar tafiya, sannan ta ce "Am sorry to say". Ta juya ta dube shi "Za ka mutu". Gabanshi ya fadi, amma sai ya yi karfin hali ya ce "In na mutu sai me? Dama can mutuwa zan yi ko ba ki kashe ni ba. Kuma ni na san ba zan wuce iyakar ajalina ba, murnata daya zaki sauke min nauyin zunubaina". Ta matso kusa da shi "Ka san matasa nawa ke shiga malamai kawai don su yi hulda da ni? In ka dade muna hulda shi ne muyi wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon shekara daya don yana da hankali". A zuciyar Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu ban auri Ummi ba. Sannan ba Allah a ranta bare taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima". Ya ce, "Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda da ke? Sannan daman duniya tasan ki kina haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai sanni ba duk daya. Sudai burinsu kudin". 12...... Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar ba". Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka nadama irin wadda waninka ya ta6a yi. In kana da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka Ishara". Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba, domin alamar yana son ji kenan. Da a ce zan fadi sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta yaba. Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba. Sai dai nuna masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda musu zakka ba. Da jin haka sai ya taho, nan dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke so ba. Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba, shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure ne ya ce zai gudu. Don gidan nan duk masu tsaro ne har da ma layin gaba daya. Da sauri za a kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka kwana ciki. Domin duk a hannunmu suke, amma Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya min shame-shame zai mutu don yunwa. Ba arziki na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa shi a daki. Nasa Malamina ya karasa min shi, sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya kare a nan. To dama iyalanshi suna ta nemanshi an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu a cikin garin nan da ma wajen shi". CIKI book 3 part 3 ZURFIN CIKI book 3 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24 Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare, Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi ne ya fara baki abinci a baki. 20..... Watanki hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu, Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana. Lah, goyo? In ji Ummi. Umma ta ce, "Goyo sosai kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku yanzun sai in ta mamaki. Don tun ba ki fita a tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata hudu ba, ki ka tantance muryarshi. Haka nan sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya. Abba yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki Ummi. In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to sai da wayo da dabara. Ke har an kai lokacin da kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki wakar da yake miki. Ummin Abba da Alhaji, Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break dinsa zai debo miki tsaraba. Umma na bada tarihi Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in baki nono". Wata sabuwar kauna da so Ummi taji ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido, ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce "Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne, kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji". Ummi ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba? Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama, suka amsa. Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya faru da kai? Nan ya warware musu komai, suka yi ta al'jabi. Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka mata suka maida aure ba a bakin komai ba?" Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka, don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba to can gabanta hadu da mai tona ta. Su Alhaji suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda". Abba ya ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba". Suka ce Amin. 21... Ranar su Alhaji a tsakar gida suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin da aka bata. Ashe har yanzu Ya Abba na sonta, Allah ya sa haka har yanzun. Sai kusan sha daya Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida. Abba ya ji dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta ce, "Ka gaida 'yan gidan". Ya ce "Za su ji, har ya kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a kara sace shi fa, duk suka sa dariya". Abba ya dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur kuwa? Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar galan na fita". Alhaji ya ce, "Na shigo da mai dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi 'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a Allah zai kare ni. Yau kam Ummi ta dade bata ga daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau. Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce, "Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk lokacin da na ganka sai gabana ya fadi, musamman in kazo min da jarida". Yayi 'yar dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan sako ne. Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama, hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi? Ta soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har ta gama. Kafa kurum take karkadawa tana tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba. Amma duk da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta danna kira. 22.... Jim kadan aka daga ta ce, "Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba lau ba, kana ji? Ina yaron da nake baka labari dan jarida? Ya ce, Naji. Ta ci gaba, Yaron nan kaga yanda ya yayata ni a duniya? Sai na koya mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma ki ka ce sunanshi? Ta ce Idris, ya ce To zan kira ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai na gama bincikena duka. Ta ce an gama. Sintiri tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine. Ta daga da cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne? Ta ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai miki? Ta ce, Hum! Ke dai bari Aminiyata, yanzun nan na gama karantawa a jarida ban ma san hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba. Attine ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku mana. Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na kira Teacher ya ce in saurare shi". Attine ta ce, "Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba". Hajiya Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin maganar tsundum! Don haka dole in yi taka tsan- tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta bakin Teacher". 23.... Shikam Malamin duk lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka. Ya ce, Hajiya? Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta batun yaron nan ki watsar domin yanda naga al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari ba. Haka nan allura zata tono garma game da damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a gurin maigidanki. Tsaki taja don maigidana Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon neman kudi. Sam baya biya mini bukatata ba dole in nema ba? Yarana biyu cal a duniya duk sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani, don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min jinin matsiyaci. Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki yaron yana da kariyar da take kare shi daga Ubangiji. Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne, tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba za su iya tunkararshi ba... Dakata Malam, ta katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma muka ci nasara a kanshi? Ya ce kila shi Malamin kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko wannan da sauran shan ruwansa. Ta ce, "Kai ne sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar Malam". Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja sannan ta kashe wayar. Har gari ya waye ba ta daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya ba. Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken ga wasu Malaman. Sai dai guri uku zancan iri daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun. Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana da makaminsu? Daga karshe ta ce na bar shi mara rabo". Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da shi in nemi wani. Kai jama'a sai kace aikin Allah menene amfanin zinar ma da har ake shiga Bokaye dominta? Allah ka tsare mana Imaninmu, amin. 12 24.... Ummi tana zaune zata wanke 'yan kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata nishadi. Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso dan Yayana. Ta tsoma sikyat dinta da fant da 'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya. A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi. Ya ce, "Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba". Ya ce, "Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa suka gaisa. Ya dawo kofar Umma yana tabayarta. Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku ta juri wulakanci. Waccan haihuwar da Zilai kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan sunan, amma yau ta koma. Abba ya ce, "Ummata tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba kwarjini". Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min farce". Ta hango kayan Ummi na daura ta ce, "Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki, ace 'yammata suna saka rigar mama? Kunya ta cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25.... Abba ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya ne? Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar kujerarta ta zauna. Tir da wannan wayewar taku ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta ba? Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa goma ba ma ta sa ran mama ba. Abba dariya ta ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya kayan ta matse ta aje. Abba ya ce, "Yanzun Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas kurum ce fa, bata ma cika ba. Ta ce "Mu lokacin sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta. Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa 'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in huta gorinki. Abba ya matso, "Ummi don Allah in tambaye ki mana? Ta tsaya da yanke 'kunbar tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin? Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce, Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji mai sunan Malam da zancen wofi. Ya ce, "Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma dai bari in tafi abina. Ummi ina Azimi yau, zan zo in yi buda baki anjima. Ta ce, "To." Tsohuwa ta ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana la'ke a nan? Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta? Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba ne, na 'yan uwantaka ne? Kai ko dai ta fito ta ce Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa take ba. Kusan wata daya kenan rabon da ya samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi ya samu cikakkiyar biyan bukata ba. In ta zo dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga take mishi (Mtsw! Allah rabamu da kazaman Mata). Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya kare shi da fadawa sharrin zina. 26.... Bai zaginta ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi. Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan ruwa. Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah. Ta ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah. Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata. Sallamarshi ta jiyo suna gaisawa da su Umma, ta fito ya bita da kallo, kin yi kyau kanwata, Umma ta ce yau za ku hoton ne? Ta ce kila, Abba ya ce shi yasa ki ka yi kwalliya haka? Ba ta ce komai ba sai dai ranta bai so ma maganar da Umman tayi ba. Suna hira da Umma ta shirya misi abinci ta koma kan kujera ta dauki littafi lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. 13 Suna hira da Umma ta shirya mishi abinci ta koma kan kujera ta dauki littafi, lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. Shi ma haka ya ce wai ni littafin nan da ku ke nacin karatunshi dame kuke karuwa? Umma ta ce, Ai fa gara ka tambaye ta, don ban ga abinda ta ba muhimmanci ba irin wannan littafin. Ummi ta cem ina karuwa sosai Umma suna koya mana tarbiyya yyanda zamu tafi da rayuwarmu cikin tsarin Addini da al'adarmu. Abba ya ce amma basa koya tsafta da biyayya, Ummi ta ce suna yi sosai ma, ya ce Umma ni naga jarabar karatu irin na Bishira amma kullum mugayen halayenta bayyana suke yi. Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce, "To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27..... Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da aikin yi? Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don shiryawa su Alhaji Abinci. Ummi kam sun bar ta cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin yaran nan saura wata nawa? Ta ce, "Wata ko kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida, ban ga kana motsi ba? Alhaji bikin nan zai mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun kaya?" Ta ce, "Ni da cewa nayi ga Abba sai yaje ko kuje ku za6a musu kaya masu kyau a siya, kada a ba kafintoci in ba a yi sa'a ba har lokacin yayi ba a gama ba". Ya ce, "To zan sa shi ya tafi da su kawai su za6a". Ta ce, "Sai kayan girki na dai sayi tukwane da risho, sai kuloli". Ya ce, "Duk da haka uwata zan sa ta za6i wasu kayan." Umma tayi dariya tare da cewa, "Allah ya kara budi, nan dai suka yi ta lissafin kudi. Da safe Alhaji ya kira Abba a waya ya sanar da shi cewa ya dauki su Ummi suje su za6i irin kayan da suke so, duk da cewa zancan ya doki zuciyarshi amma ya ce "To." insha Allah zamu je, suka yi sallama. Sam baya son ya ji batun auran su Ummi, baya son rasata, kuma yana ji a jikinshi cewa zai same ta. ** ** 28.....Yammacin ranar Asabar La'asar lis garin yayi dan sanyi Abba ya nufi gidansu don daukan su Ummi zuwa kasuwa. Jikinshi sanye da farin yadi mai shara-shara, har ana iya hango fara kar din singiletin da ke ciki ta manne a jikinshi. Kamshin turarenshi ya cika dakin Umma wanda ba shiga yayi ba daga bakin kofa suka gaisa. Ya ce, "Ummi su fito don Ummi ce ke shiryawa tuni Fati ta fito, ya matsa kofar Tsohuwa suka gaisa, sannan ya ce "Umma sai mun dawo. Ya nufi waje yana fadin su Ummi su mishi sauri. Sun fito za su duru a baya Abba ya ce Ummi ta dawo nan gaba, ta zauna ranta dagule don ita bata bukatar wani za6i tunda ba wanda take so zata aura ba. Haka nan ta fuskanci Abba yau yana cikin wani irin yanayi, kila daga gida aka 6ato masa rai, nata tunanin kenan. Shi kam takaicin zuwa za6on kayan ke damunsa, ya kalli wayarsa da ke ruri ya daga, Salis ya ce kana ina ne? Ya ce ina nan unguwarmu zan kai kannena ne za su za6i kayan daki. Ya ce, "Ta ina zaku bi? Abba ya ce kai kana ina ne? Ya ce ina nan kusa da asibitin Malam, bari in jira ka a jikin gidan man nan, Abba ya ce "To." Salis ya kalli yarinyar da Abba ya ce Ummi koma baya ya ce, "'Yammata sannunku, suka gaishe shi ya yi murmushi ke ce Ummi?" Ta ce, "Eh, ya ce ya su Umma?" Ta ce lafiya lau, ya maida dubansi ga Abba wanda ke tuki cikin nutsuwa ya ce, "Idris akan batun yarinyar nan ne don Allah ka daure muje gidansu yau". Gaban Ummi ya fadi. Abba ya ce, "Don Allah Salis ka bar batun yarinyar nan, kai dai kasan halin da nake ciki game da wata". Salis ya ce, "Me yasa ka amsa kana sonta, kuma har kana daga waya duk lokacin da ta kira ka?" Abba ya ce, "Shike nan za mu je da yamma tunda wancan na rasa madafa". Salis ya ce kuma fa da hakan zai fi maka. Ummi gashin jikinta duk ya mike, suna fitar da zufa lumshi ido tayi luf a kan kujera ta kwantar da kai, Salis ya waiwaya ya dubeta, yaya dai? Ta yi dan yake, "Ba komai." . 29.... Sun je gurin kujeru da gadaje, Fati tayi ta ruwan ido yayin da Ummi ta koma ta jingina a kujerar da ta zauna. Abba ya dube ta. "Ke wanne ki ka za6a? Ita ta ce wancan farin". Ummi ta yatsina fuska, "Nifa bani da za6i, duk wanda ku ka ga yayi". Salis ya ce, " Idris yarinyar nan ina zaton tana sonka, naga tunda muka yi maganar zuwa gurin wata ta canza yanayi. Abba ya ce, "Kyaleta ba wani ya dubeta ba, ke Ummi tashi ki za6a mu ji farashinsu, sauri muke. Ta ce, "Ya Abba cikina ke ciwo, ka za6ar min don Allah". Ya ce, "Salis ita ma a bata farin kawai ko? Salis ya ce, "A daukar mata mai ruwan madaran, mai shagon ya ce sun fi tsada, Abba ya ce ka daukar mata su. Sun koma gefen kujeru nan fa Abba ya ce dole sai ta za6a, nan ma wanda ta za6a a ka ce sun fi na Fati tsada, suka ji farashinsu su sannan ya ba da wani abu suka tafi. Ya sauke su a gida, Fati sai ba Umma labari take yayinda Ummi ta shiga kuka, Umma ta ce ke kuma lafiya ki ke kuka? Ummi ta ce "Umma ni bana son in yi auren nan, bana son in bar gida. Fati ta ce, "Shi yasa naga tun a gurin shagon kina ta 6acin rai? Umma ta ce, "Shirmen banza da wofi, sai ki tayi. Ta fice, Fati ta ce Ummi ke kin cika son damuwa. Menene na damuwa? Kila ma kina nan unguwar.ovels / ZURFIN CIKI book 3 part 5 ZURFIN CIKI book 3 part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:29 ummi sannu da zuwanku, nan sukayi masa gaisuwa yace ummi kaisu ciki. 36.. Zainab tace a ranta wato ma ummi yafara gani, a fallon su umma suke don nan ta fara kai su, tace umma wanan ce zainab, wannan kuma matar abokinshi salis, umma tayi masu sannu da zuwa sanna tace ummi ta kaisu dakin bishira, sun shiga sun yi mata gaisuwa, bishira tace ke ko gaisuwa baki zo min ba koda yake bai dame ki ba, ummi tace nima ana ta zuwa min gaisuwan ne a gd, duk yan dakin suka kalli ummi, sahura tace ke asuwa? Bishira tace ita a mahaifiyar shi, ummi tace zainab kuzo muje, tun daga lkcn zainab tasa a ranta akwai matsala a wanan familyn din, basu jima ba suka yi sallama, inda ummi ta rakasu daga can itama ta wice gd, suna shiga soro shima ya shigo yace badai tafiya zakuyi ba? Ya kalli ummi sun sha ruwa ma kuwa?ummi wadda dama idanunta na kanshi ta amsa mishi da idanu. Yace yama akayi kuka gane gdn zainab tace yaya salis ne yakawo mu, ya kalli matar salis yace madam mun gode fa,tace bakomai Allah ya jianshi, sam ummi batasan lokacin da furucin ya fito mata ba, sai dai taji tace ya abba duk ka rame baka cin abinci ko? Shi kanshi yayi mamaki don haka ya ya tsura mata ido, sai taji kunya ta rufee ta saita kau da kanta daga kanshi,don kada su zargeta. Kayi hkr naji wani malami yace duk wanda yaranshi kananan uku suka rasu to zasu ceceshi ranar gobe. Kaga ynz kafara da daya,matar salis tace ai koma dayane indai kayi hkr kayi tawakkali,ummi ta kalle shi tace to kaji ma,yace ummi nifa tuni na dangana,ta sake tausasa murya to meyasa baka cin abinci? Ya tausasa murya wadda dama take a dusashe yace ummi inaci,tace ya abba baka fa yin karya,yace to yau zanzo inci a gabanki, ya kalli matar salis wadda ke murmushi, in naci a gabanta saita yarda ko? Tace tabbas! 37..Zainab wadda takaici ya cikata tace da matar salis anty nifa natafi, abba ya dubeta zainabu nagode ki gaida su mama sai nazo,batare da ta tsaya ba tace to, ummi ta musu sallama itama ta tafi gd. Zainab ta dubi matar Salis bayan tafiyar Ummi, ta ce, "Duk da son da na ke ma Idris din nan ba zan aure shi ba". Matar Salis ta ce dalili? Zainab ta ce, "Bana zaton ko matarshi ta gida da ya aura ya aje yana sonta irin yanda yake son Umiin nan". Abin nasu yayi yawa. Dubi yanda ya manta da ni, ta ita kawai yake yi. Matar Salis ta ce, kin ji ki da wani shirme, ita da zata yi aure?" Zainab ta ce, "Abinda ke tausar zuciyata ke nan in na tuna cewa zata yi aure, amma kai naga ji ba zan iya ba, haka suka tafi tana ta bai wa yarta labarin yanda Abba ke ji da Ummi. Kamar yadda Abba ya ce zai zo cin abinci da dare yazo, Ummi ta saka shi gaba wai sai ya cinye wake da alayyaho da kifin da ta dafa masa. Da kyar ya cinye plate din farko ya ce "Ummi na koshi kin ji? Ta daure fuska tana kallonshi, shi ma ita yake kallo yana dan murmushi. Ya ce, "Ina ma a ce tun da da haka muka yi sabo, Ummin cikin kwanakin nan kin lura cewa muna shiri". Ta harare shi, "Kana zaton na manta da irin dukan da ka yi ta min ne? Shi ma ya harare ta tare da kwaikwayon muryarta. "Kina tsammanin zan manta da irin tsokanar fadanki ne? Ko zan manta da Suhailar Kaduna...?" Kafin ya rufe baki tuni ta yi uwar daka da gudu, shi kam dariya yayi ta yi yana cewa ki zo mana Ummi, kin fitowa tayi har sai da ya bar gidan. Duk lokacin da suka kasance tare kowannan su yana mantawa yana da wata matsala. Saura kwana uku daurin auransu, lokacin dangi sun soma zuwa, musamman 'yan Zamfara. Ummi da Abba hankalinsu ya kai kololuwa gurin tashi. Ranar ya ziyarci Zainab wai ko zai samu 'yar nutsuwa. Bayan sun gaisa ta sake mishi gaisuwa, shi kuma ya mata bangajiya, dama tun da aka yi rasuwar bai zo ba. Ya ce "Zainab ina ganin da an gama hayaniyar bikin Ummi zan turo". Tayi shiru bata yanke ma kanta shawarar matsawar ya cikata da zancan Ummi yau kam za su yi ta ta kare. Jin tayi shiru ya ce kina jina Ummi... ta katse shi da sauri, "Ba Ummi nake ba Sorry Zainabu. Ya ci gaba bakina ne ya saba da kiran Ummi, da yake daga ni sai ita ne a gidan. Yanzun haka auran nan da zata yi ina cikin tsananin kewarta...Zainab ta ce ina Idris? Don Allah ni na hakura ka je ka auri Ummi, Abba ya dubeta cikin tsananin mamaki. 38.. Me ki ke fada? Me Salis ya sanar da ke? Ta ce Idris duk wanda ya san so, minti biyar in ya zauna da ku zai san kuna tsananin son junanku kuma ni na tambayi Salis cikinku daya? Ya ce min A'a tun daga nan nasan cewa ku masoya ne, ta nufi hanyar gida, da sauri ya sha gabanta. Zainabu kada muyi haka da ke, wallahi auranki zan yi. Ta ce, "Eh ai na san aurena zaka yi, amma ba sona ka ke ba, don Allah ban hanya sonka in zai yi ajalina ba zan aure ka ba, ya kauce ta wuce, ya bita da kallo har ta shige. Jiki ba karfi yake tuka motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don haka ya nufi dakin. 21. Jiki ba karfi yake tuka motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don haka ya nufi dakin. Bishira na zaune ta zuba tagumi tunanin danta take, ga Abba sam baya sakar mata fuska, ya ce "Lafiya Mamina take kuka?" Ya shiga ya dauketa Bishira ta ce, "Rigima cee kawai, ya nufi kan madubi inda ya hangi pampers ya dauki guda daya ya nufi dakinshi da ita. Bishira ta biyo shi itama ta zauna a gefen katifa kusa da shi, cikin sanyin murya ta ce, "Abban Walid don Allah kayi hakuri, ya ce me a ka yi? Ta ce, "Gani nayi kana ta fushi, ya ce ni bana fushi wannan kadan kenan ki ka gani daga cikin sakacinki, na tabbata kin fini jin bakin cikin mutuwar yaron nan. Musamman da ki ka zama sanadi, amma don batun yawo ni na daina miki fada, kiyi tayi illa dai zan nemo wadda zata dinga lurar min da gida. Ta ce me ka ke nufi? Ya ce aure zan yi". Ta doki kirji tare da fadin, "Aure?" ya ce, "Eh". Ta soma kuka haba Baban Walid, wane laifi na maka da zaka yanke min irin wannan mummunan hukuncin? Ya ce, "Don Allah fita, ta ce sai ka fada min dalilin yin auranka, ba za ka bar ni in ji da rashin dana ba ko? ta mike an zugo ka an ce kayi aure, to bisimilla. Ta fita ta zari mayafi tayi gidan Umman Bashir. Abba ya rungume 'yarshi ya yi laf a kan katifa shawara ya yanke zai tura magabanshi gidan su Zainabu ba tare da ya sake bi ta kan Zainabun ba. * Umma ta leko dakin Tsohuwa, Ummi kin san na ce miki kizo ki kwashe kayanki daga dakina ki adana su ko? Kin san dai yau duk na nesa za su iso, ki cire wadanda za ki bada. Tsohuwa ta ce, "Suwaiba yarinyar nan ina kallonta jiya bata runtsa ba, sannan da Asubahi a zaune tayi sallah. Umma ta shiga dakin warwas take a kan gado, Umma ta tasheta zaune Ummi ciwon kai ta keya ga jiri da ta ke gani daga zaune. 39.. Umma ta ce taso ki dan watsa ruwa ki karya, mikewar da zata yi sai ta sulale a kasa sumammiya, nan suka dau salati, Toshuwa kam kuka ta saka. Alhaji ya fito wanka kenan ya ji Umma na salati, don haka dakki ya shiga ya dauko waya ya kira Abba lokacin yana kokarin shiga wanka. Alhaji ya kira shi, jin cewa Ummi ba lafiya zari mukullin mota ya fito. Sai da suka kai asibiti sannan ya lura da silifas ya fito da jallabiyarshi ta wanka, Lkitan ma bai zo ba lambarshi suka amsa Abba ya kira shi. Ya duba Ummi sosai da kyar suka samu numfashinta ya dawo, sun daura mata ruwa sannan aka kaita wani daki. Likitan ya ce su zo ofishinsa, Ya kalli Alhaji ya ce, "Gaskiyar magana yarinyar nan tana bukatar kulawarku, ciwonta baya son sakaci. Jininta ya hau ya wuce matakin da zata iya samun mutuwar 6arin jiki. Su Alhaji suka dauki salati,, ya ci gaba da cewa yanzun dai addu'a zamu ci gaba da yi. Allah yasa in ta farfado kada wata matsala ta biyo baya. Sannan ya basu takardar magunguna". Alhaji ne ya amsa don Abba fita yayi ya koma dakin da Ummi ke kwance. Idanu ya zub amata, sam bai san cewa kuka yake ba, sai da Alhaji ya shigo ya dafa shi tare da cewa, "Haba Abba ba girmanka ba ne kuka. Addu'a za ka yi Allah ya bata lafiya". Ya share hawaye. Alhaji don Allah kada ka sanar da Umma abinda Likitan ya ce, Alhajin ya ce ai dama ba zan fada mata ba. Bari in je sai tazo ga takardar maganin inta zo sai ka siyo, ya ciro kudi ya mika ma Abba, Abba ya ce a'a da kudi a jikina. Alhaji ya ce ka amsa ka kashe kudi cikin kwanakin nan ina sane da duk lokacin da na ce kazo ka siyo wani abu sai kawai in gan ka da shi ban da kayan dakin da ka siya musu, Abba ya ce ai ina da shi ne. Bayan fitar Alhaji Abba yaja kujera ya zauna ya zabga tagumi tare da tsura ma Ummi ido, a zuciyarshi fadi yake ALLAH ka tashi yarinyar nan lafiya, Allah kasa kar ko ina na jikinta ya nakasa. Alhaji ya fada wa Umma an ba Ummi gado, don haka ta shirya su wuce. Abba ya tashi ya nufi ofishin Likitan, bayan ya kwankwasa Lokitan ya ba shi izinin shiga, ya same shi yana rubuce-rubuce. Ba tare da ya dago kai ba ya ce, "Zauna sai da ya kai aya rubutunshi sannan ya dago kai ya kalli Abba "Ba dai mai jikin ba ce ko?" Abba ya ce, "a'a ina son ne nima agwada nawa jinin, Likitan ya ce kana jin jikinka ba dadi ne?" Abba ya ce, "Eh da har yasa a dauko fayal din Abba kuma ya tasa ya dauki abin gwaji. Bayan ya gama ya zaunar, ya tsare Abba da ido wai kun yi gadon ciwon nan ne? Abba ya ce, "A'a, Likitan ya ce, "Jininka ya hau, sai dai ba sosai ba. Kila don kai namiji ne kana kokarin kauce ma abubuwa. Zan rubuta maka magani na sati daya, kuma ka dinga kokarin yin bacci a kalla na wa shida kada ka dinga yawan tunani. Kaga kanwar nan taka, sai sa'ar gaske zata tashi lafiya. Ku dai cigaba da addu'a, zata yi bacci na tsawon awa tara ko goma. Ina son daidai lokacin da zata farka ya kasance ta soma dora ido a kan wanda suke shiri ko wanda ta fi so a cikin mahaifanta ko danginta, Abba ya ce "To." Lokacin da ya koma dakin su Umma sun zo har da tsohuwa, nan Abba yake fada musu abinda Likitan ya ce game da farkawa in tayi. Koda bude bakin tsohuwa sai cewa ta yi ai ko dai ba a bar mai sunan Malam ba, tunda an ce wanda suke shiri, don in taga mai sunan Malam karasawa zata yi. * 22. Duk da ana cikin wani hali sai da su Alhaji suka murmusa. Abba kam daure fuska yayi yana kallon Tsohuwa, Umma ta ce, "Ai da ne Tsohuwa. Yanzun shiri suke tunda ta daina rashin jinta". Likitan ya shigo ya sake musu bayani kamar yadda ya yi ma Abba, sannan ya ce su bata guri kada zantukansu ya farkar da ita a samu matsala. Suka fito, Umma ta ce da Abba ya tafi gurin aikinsa, su Alhaji ma suka fita tare da Abba. Fati ta je gidansu Sahabi dan uwansa yana kankarar rake a kofar gida, inda yake saidawa ta tambayi Sahabi. Yaron ya ce mata ya ffita, ta ce To in yazo kaa ce masa Ummi tana asibiti ba lafiya, an bata gado. Karfe uku ya iso asibitin hankali a tashe, sun gaisa da Umma ta raka shi dakin, hankalinshi ya tashi da ganin Amaryarshi kwance a gadon. Abba kam yana gurin aikinshi amma hankalinshi na Asibiti, su Alhaji ma duk nan suka nufo, Abba sai da yayi magriba sannan ya shigo asibitin. Jikinshi babu karfi, bai matsa sai yaga farkawar Ummi ba ne saboda yasan da gaske ba shi ne ya dace idanunta su soma arba da shi ba, ya samu su Umma da su Alhaji. Sahabi da abokansa duk suna gurin, ya gaida su tare da tambayar ko ta farka? Umma ta ce har yanzun dai shiru. Ya nufi cikin gurin Likitan suka gaisa, ya ce Likita har yanzu ba ta farka ba. Suka jera zuwa dakin, Likiran yana cewa cikin wannan dan takin zata farka, In sha Allahu. Sun shiga takin tana dan motsi suka nufi gadon Abba ya ce Ummi. Likitan ya daga mishi hannu alamar yayi shiru ita kam daidai lokacin mafarkin Abba take wai suna tafiya ya rike mata hannu sai ga Sahabi. Yana zuwa ya kama hannunta tana tirjrewa, sai janta yake zai fita da ita, Abba yana tsaye yana kallonsu. Ita kuma sai kiran "Ya Abba! Ya Abba!! Take yi. Likitan ya kara kunne gurin bakinta ya dagowa yayi ya dube shi. "Waye Yaya Abba?" Abba ya ce ni ne. Liitan ya ce, matsa kusa, ya kama hannunta. Ummi. A hankali ta bude ido. Ya Abba! Ya abba, zan sha ruwa, ya ce to ya kalli likitan za ta sha ruwa, Likitan ya ce, "A'a bari ta dan kara warwarewa tukunna. Likitan ya kama kafafunta ya dan matsa, sannu ko. Ta kalle shi, kin ji zafi? Bata yi magana ba ya dauki allira ya 6are ya dan soka mata a tafin kafa ta ja kafafunta alamun taji zafi. Ta yunkura zata tashi, Ya abba zan tashi, ya tayar da ita zaune. "Likitan ya ce Alhamdulillah, Abba ya kalli likitan, ba matsala kenan? Ya ce, Ina zaton haka insha Allah, Abba ya ce "Alhamdulillahi, ya jinginata da jikinshi, sannu Ummina. 41.... Alhaji ya shigo yana cewa, "Ina Abba ne?" ya ganta zaune a'a ta farka ne? ya kama hannunta sannu uwata. Ta kalle shi. "Ina Ummata?" ya ce, "Bari in kira miki ita". Yaje ya sanar da su, sun shigo da murna. Sahabi ya iso gaban gadon. "Sannu Ummi". Ta kalle shi sai ta kwantar da kanta a kafadar Abba, "Ya Abba ina son in wanke bakina". Ya ce, "To bari in siyo miki Maclean din". Ta ce, "A'a kada kaje". Ya gyara zama "To shi kenan." Umma ta ce, "Me ta ke so?" Abba ya ce "Baki zata wanke". Umma ta ce "Ai nazo mata da maclean da burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki ce". Nurse ta kawo wani dan kwano na silba Ummi ta wanke baki da taimakon Abba. Likitan ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata magani. Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura tayi yawa. Kai shi fa wannan Yaya Abban bai masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko gaida shi yayi d kyar yake amsawa. Shi fa tun ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da Abba ba ya ji ya tsane shi. Umma ta ce, "Abba an kira Isha'i. Sahabi kaje kai ma ka huta yaran nan tun tuni ya ke nan". Abba ya kalle shi, "Ya kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan ya dan rusuna "Sannu Ummi". Ta ce, "Yauwa" "Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da safe. Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin wani abu yanzun ba". Umma ta ce, "Abba". Ya kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari. Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma sai da safe". Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar taka". Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba halinka ba ne kada in kuma gani". Ya ce "To Umma". 23. Su Alhaji sun yanke shawarar daga auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata. Gidan su Sahabi sun ji haushi musamman Innarshi, sun kashe dan abinda suka tattala don bikin amma gashi an daga, su kam da an daura auren in ta murmure sai a yi bikin. Sahabi ya shigo gidan ranshi a 6ace, ya kalli Mahaifiyarshi, "Inna wai sun ki a dauram?" Ta ce, "Sun ki, dama ai gaddamar dan yau ce. Ban da shegiyar gaddama ga 'ya can da a ka baka a daura ka gaddame, to yanzun ina ranar abin da aka mana? Gida duk dangi sun cika amma wai a daga biki, mu kuma karamin karfi ne da mu, bare mu ce nan da sati biyu zamu sake kashe kudi". Sahabi ya tuna abinda Abba ya masa a asibiti, shi ne dalilin da bai sake zuwa asibitin ba, yaja tsaki. "Kin san Allah Inna ni kaina sai yanzun nake jin haushin kaina da na ki amincewa da Badariyya. Mu zuba musu idanu in za su sake kawo mana cikas sai kawai in koma gurin Badariyya." Inna ta ce, "In da tun jiya kamin zancan nan da tuni yau ba a fasa daura auranka ba an ma da Badariyya". Ya ce, "Kiyi hakuri Inna mu ga nufin su". * 42... An sha shagalin bikin Fati kuma an kaita gidanta. Ummi jiki Alhamdulillah, Abba kullum in zai je aiki sai ya biya. Haka nan in ya dawo gida wanka kawai zai yi ya tafi, wataran sai goma ko sha daya. Abokanshi suna ta zuba duba Ummi, ita kanta da lokacin zuwanshi ya karato ta dinga kallon agogo ke nan tana kallon kofa. A zaman asibitin nan Umma ta gama karantar su tsaf., matukar son juna suke yi, sai dai taji takaicin da sai yanzun sonsu ga juna ya bayyana. Lokacin da ya kasance an riga an bada Ummi ga wani sai dai ta ci gaba da addu'a Allah yayi za6i na alkairi. Bashir yayi murna da fasa auran Ummi, dama a fasa gaba daya. Yana fitowa dakinshi ya ji Ummarsu tana cewa, "Kin san Allah Tasalla, uwar yaron nan da zai auri Ummi zata ga bakin ciki, don mallake mata da za su yi. Tana ji tana gani sai yanda suka yi da shi. Kuma ba yanda zata yi sai Allah ya isa". Tasalla ta ce "Ban da halin mutanan yanzun ba da sai na fada mata ba. Kin san makotanmu ne ta baya, gashi su ba karfi ba. Sahabin ne fa ke rike da gidan, kin san shine Babban a gidan". Sahura ta ce, "Don Allah Tasalla ki taimaka ki fada musu, don ko in har aka yi auran nan in suna cin abinci sau uku ne a rana, to za su koma dau daya". Tasalla ta ce "Ai ko zanje". Tana fita Bashir ya dawo kusa da Ummarsu ya ce, "Umma dama da kanki ki ka je, saboda za su fi yarda tunda sun ga ke kina da danganta da gidan". Ta ce, "To in Babanku ya ji fa?" Ya ce "Umma ai in kin fada musu ai kwa6ar su za ki yi, sannan kada kije a kan lokaci, kije ana gobe daurin auren". Ta ce, "Saboda me?" Ya ce, "Saboda su Alhaji Babban suji haushin rashin fada musu da wuri". Ta ce, "Haka za a yi, kuma in an fasa Malamai zan shiga don a hanata auran ma kwata-kwata". Ya ce, "Kada kije wurin Malamai yanzun tukun". Ta ce. "Ai dama sai an natsa". * Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je gaisheta." Ya ja tsaki tare da cewa, ballahaza wadda bata san mutuncin mijin auranta ba". Ya yakice labulen ya wuce yana jiyo ta tana cewa, "Ba dai za ni ba ko me za ka ce". Ranshi a 6ace ya isa asibitin, Ummi na zaune kan gado ta kosa Abbanta yazo, ko karyawa ta kasa yi, yana sallama suka hada ido. Nan ta ke ya ji ya manta da duk wani bakin ciki da ya taho da shi, ya isa bakin gadon fuskarshi dauke da murmushi. Itama murmushin take yi, ya ce. "Ummi ya ya jikin?" Ta ce "da sauki". Ya Abba kayi kyau sai ka ce Manajan Banki". Umma ta saka dariya, shi ma ya yi 'yar dariya, "To ko bankin zan koma?" Ta ce, "A'a kafi kyau da dan jaridanka Ya Abba, balle in kana turancinn nan a labarai". Ya lakuci kumatunta "Ko kwanwata?" Ya juya ya gaida Umma, Umma ta ce "Ka zo katafi gurin aikinka fa". Ya ce, "Umma sai sha daya yau zanje gurin aiki". Ta ce, "Ni na ma kosa a sallame mu". Abba ya ce "Ai kila a sallame ku yau. Likitan ya shigo ne?" Suka ce "A'a. Suna cikin karyawa Likita ya shigo ya same su, ya kuma kafa mata dokokin daina tunani, daina shiga duk wani abu da zai sa ta cikin damuwa. Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 6 ZURFIN CIKI book 3 part 6 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:31 Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin ranta. 26. 43... ABBA Ya kwaso su ya maida su gida, cikin satin Ummi ta murmure. Sahabi na zuwa sai dai da sun gaisa yake tafiya. Mahaifiyyarshi ma tazo, amma Bishira da Sahura ko le'ke, Bashir ma yana ta sintirin zuwa. Ganin haka Alhaji ya ci gaba da shirin biki, mutan kauye dai dama an ce kada su dawo, Ummi dai bata maida hankali ga komai ba. Ta ce ma Umma zata je gidan Fati, Umma ta ce To sai ki je gurin Sahura ta kwatanta miki. Abba ya same su suna zancen, don haka ya ce ta shirya zai kaita ya ajiyeta in ya tashi aiki sai yaje ya daukota. Yanda ta samu Fati da Angonta ana ta ji da juna abin ya tsokanota, sai dai ta kasa ganin dacewar soyayyar da Sahabi. Da mijin Fati ya fita Ummi ta ce, "Oh, Fati cikin kwana takwas dubi yanda ki ka yi kyau". Fati ta ce, "Amma ban rame ba?" Ummi ta ce "Eh to, kin dan rairaye". Fati ta ce, "Kai ai dole, gaskiya ina koduwa, wallahi ba ya barina in huta". Ummi ta ce, "Da me?" Fati ta ce, "Dallacan ki gane mana". Ummi ta ce, "Wai da me? Allah ban gane ba". Fati ta ce, "Ai ke sokuwa ce, gurin kwanciya mana. Ummarmu ta samu ta dirka min kayan sha na mata, gashi nan nazo ina ta shan wuya". Ummi ta zaro ido, "Da wahala ne?" Fati ta ce, "Tab, ai kin kusa kema za ki ji". Tsoro ya cika Ummi. Ta ce, "Zan ce ma Umma ni dai kada ta bani wannan kayan matan". Fati ta yi ta dariya tare da cewa, "Ke yanzun sai ki iya wa Ummanku wannan zance?" Ummi ta ce, "Sosai ma". Fati ta ce, "Ko ba ki sha ba yarinya sai kin sha zafi, ana kawo ni ko dan kwana daya bai raga min ba". Ummi dai ido ya raina fata. Koda Abba ya zo daukarta duk ta damu. ** ** 44..... Tasalla ta samu uwar Sahabi ta fada mata cewa, in dole ne sai danta ya auri Ummi, to ta amso mishi karya tambaya. Don kuwa wata rana sai ta taso ta ganshi ko da a hanya ne ta rasa samun hakan. Inna ta tsure ta ce, sai a fasa babu dole, ita dama tuni abin ya sire mata. Ana gobe daurin aure gidan su Ummi suna ta shiri Ummi na ta kuka, wannan karon ba Umma ba har Alhaji da Tsohuwa sun kule da wannan iskancin da Ummi ke yi. Alhaji ya ce "Ki sani uwata, wannan karon ko kin tsokalo ciwon nan naki auren nan dole ne babu fashi. Idan yaso jinin naki ya tashi ya ta6o sama ba zan kuma daga auran nan ba". Lokacin da Alhaji ke wannan fadan Abba yana gidan yana zaune dakin Umma yayin da Ummi ke gefanshi tana rusa kuka. Umma ta shigo ya ce "Umma don Allah ki lallashi Alhaji a dan daga bikin nan mana". Abba bai ta6a ganin ranar da Umma tayi mishi irin wannan kallon da ta masa yanzu ba tun tasowarshi. Sannan bata ta6a daka masa irin wannan tsawar ba ta ce "Kai! Abba shiga taitayinka, me yasa yanzun ka canza, ko kai ba za ka hukunta Ummi ba da irin wannan yaro da hankalin da take mana? Don gidansu kanta a ka soma aure? To wannan karon ba za a daga bikin ba, in yaso ta mutu, ke ko mutuwa ki ka yi gawarki can gidan mijinki za a je a miki sutura". Tsohuwa ma daga can tana yo nata fadan tare da dauko tarihe-tarihen da tana cewa, "Lokacinsu kaza-kaza". Abba ya sake kallon Ummi, matsanancin kukan da take yi yana daga mishi hankali, ya mike tare da kama hannunta, "Zo muje". Ya bude mazaunin direba ya ce ta shiga, shi ma ya koma ya shiga motar ya tasheta, tafiya kawai suke ba tare da ya san in da suka dosa ba. Kukan Ummi na tsikararshi, sun yi tafiya mai nisa sannan ya tsaya a hankali cikin wata irin murya, ya ce "Ummi ki fada min gaskiya kina son Sahabi?" Ta dago ta dube shi, "Ni bana son shi". "To me yasa ki ka fito da shi?" cikin dasasshiyar murya ta ce, "Ba ni da yanda zan yi ne, saboda in ban za6i Sahabi ba za a bani Bashir". Ya ce, "To ke yanzun fada min wa ki ke so?" Gabanshi ya shiga faduwa don tsoron kada kunnenshi ya ji mishi ta ce wani ba shi ba. Ta kuro shi da ido tamkar ta ce kai, amma sai take ganin in ta fada mishi haka dan shirin da suka soma yanzun zai wargaje, kila ma sai ya hada mata da duka. Wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatunta, daidai lokacin da yake cewa "Ko dan digo ki ka ji son ko waye a ranki kada ki rufe min". 45... Ta girgiza kai "Ba na son kowa Ya Abba". Cikin wani irin yanayi ya dubeta, "Shi kenan, sai ki je ki hakura da Sahabin a sannun kin so shi". Cikin kuka ta ce, "Ya Abba Allah ni bana son shi, kai to ka hada ni da ko waye mana". Ranshi 6ace ya dubeta cikin tsawa ya ce, "Ki rufa min baki tunda ba ki ta6a son kowa ba ki zauna da wanda ki ka za6i zama da shi. In da kina son wani ne to da sai in cije in tunkari su Alhaji, tunda kuwa babu sai in ce musu me?" Ya fada mota, ya koma kofar gidan. Koda ya tsaya tafi minti uku sannan ta fito, yana kallonta maimakon ya wuce gida sai kawai ya nufi gidan Maman Iman makociyarsu da suke shiri da ita. Shima kanshi na kan sitiyarin motar har ttsawon shudewar wasu dakiku, sannan ya nufi gida. 27. Misalin karfe tara Umman Bashir ta rangada sallama a tsakar gidan, Innar su Sahabi ta amsa tare da fadin "Shigo". Sahura ta shiga tana tambayar "Ba kowa dai ko?" Inna ta ce "Shigo mu kadai ne". Bayan sun gaisa ta ce "Ba ki sanni ba ko?" Inna ta ce, "Eh." Sahura ta ce, "To ni dai tsakani ga Allah zuwa nayi in ba ki shawara bisa ga yarinyar da danki zai aura. Tsakani ga Allah yarinyar ba ta da mutunci, sannan iyayenta za su mallake miki da, don ni kaina ya faru da ni". Sahura don makirci ta soma rishin kuka. "Dana maigidana ya ba su riko, ina sheda miki wannan zance 'yar uwa yanzun tsakanina da shi sai ido, sun makkale shi komai shi yake musu, ni ko da nayi wahalar ciki da nakuda sai na tashi a banza. To da yake an ce ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, shi ne nazo in sanar da ke. Amma in kin ji haushi kiyi hakuri". Ta yunkura zata mike. 46... Inna ta ce, "Zauna 'yar uwa, na gode. Nima fa tuni auran nan ya fice min a rai, dama da naga shi Sahabin ya dage ne sai kuma suka aiko gobe azo za a daura aure sai na hakura". Kafiin Sahura tayi magana sai Sahabi ya doka sallama, Inna ta ce "Yauwa zo nan". Ya nufo ta "Zauna kaji ma kunnenka". Ya rage tsawo, Inna ta ce "Baiwar Allah ya ki ka ce?" Nan Sahura ta soma zuga sharri, ta kara da cewa "Yaro ina ga ma za ka san dan nawa da suke riko Abba a ke ce masa". Cikin saurin baki ya ce, "Na san shi". Ta ce, "To dana ne da asiri suka amshe min shi, sai dai Allah ya isa". Ya tuna irin halayen da Abban ke nuna mishi. Yaa jinjina kai, sannan ya dubi mahaifiyarshi "Inna to da Kawu yayo binciken halayan iyayenta ai ana ta yabon halinsu". Inna ta ce, "Kin ji shi ko? To bari kaji, kwanaki ma Tasalla da ke bayan layin nan tazo ta fadan irin wannan matsalar ban kama ba ne don na asanta da shegiyar karya. To kuwa an yi biyu ba zan bari ai na uku ba, don haka a daran ta tabbatar ma da danta an fasa gobe ya wuce gurin Badariyya a daura, su kuma in sun ji shiru sa ba wani can". Cike da murna Sahura ta koma gida. * Maman Iman tayi lallashin duniya amma Ummi ta ki yin shiru, ga zazza6i tamkar wuta a jikinta. Sai kusan sha dayan dare sannan Maman Iman ta rako ta gida, lokacin Umma tana ta neman layin Abba a kashe. Ta ce, "A'a sun dawo ne yanzun ni ke neman Abba in ji suna ina ne?" Maman Iman ta ce, "Tun dazu tana gidanmu zazza6i da ya rufe Ummin, na bata magani ta 'ki sha". 47... Umma ta ce "Rabu da ita kar Allah yasa tasha, aure dai gobe babu fashim dubi irin yanda a ka sa gidan su yaron nan wancan karon suka kashe kudi gurin yin girki da sauransu ba a yi bikin nan ba. Yanzun a kuma dagawa daga lokacin da muka samu?" Maman Iman ta ce, "Ai ba zai yiwu ba, sai dai a bi ta da lallashi". Umma ta ce, "Mun daina lallashinta tunda ko mun lallasheta aikin banza ne". Maman Iman ta ce, "To Allah ya kaimu gobem bari in shiga gida sai mun shigo aiki da safe". Umma ta ce, "To sai da safe". Ummi tana shiga dakin Umma taga baki kwakkwance, ta ce a ranta "Mayu, don kalata sai da wasu suka dada zuwa". Tana fushi da tsohuwa amma duk da haka dakin ta nufa, ta kwanta a bayanta don ita tuni tayi bacci. Nishin kukanta ya farkar da Tsohuwar, kala bata ce mata ba, sai sauka tayi ta shimfida a kasa ta kwanta, sannan ta ce "Aniyarki ta biki Takwara". Wannan dare gurin Ummi da Abba wani dare ne mai cike da bakin ciki da tashin hankali, ko Sarkin sata bacci ranar bai samu galaba gare su ba. Dukkan su a kan kunnansu aka kira sallar farko, Abba ya mike cikin rangaji, jin jikinshi yake yi tamkar iska ta dauke shi saboda rashin karfi. Ruwa ya diba ya watsa, wanka sannan yayo alwala don yin nafila, addu'a yake Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi a gare shi. Da ya dawo Masallaci kwanciya yayi amma baccin ya ki bai fita ba sai kusan takwas. Koda yaga Bishira zaune a tsakar gida tana karatun littafin sam bai ji haushin rashin zuwanta gidan su Umma ba. Nashi ganin duk wanda yaje tamkar yana murna ne da rasa Umminshi da yayi, ita kuwa da gadara ta fito don ya ji haushi, bata je ba yana son sanin halin da Ummi take ciki amma ba ya ra'ayin zuwa gidan su Umma. Shagonshi ya bude ya shiga ya dan zauna har zuwa tara, yana kallon lokacin da Jama'a suka yi ta dafifin shiga layinsu don halartar daurin auran. Kurum sai ya samu kansa da tare dan Aca6a ya hau ba tare da ya shaida masa inda za su ba. Koda dan Aca6an ya tambaye shi ce masa ya yi mu je. 48.... Ita ko Ummi ranar zaune tayi sallah ta koma ta kwanta, duk kaikawon ai da 'yan shewe-shewen da jama'a dangi da makota tana jin su. Sai dai makoshinta ya bushe ga zufa da ta rufeta, duk da yanayin ba na zafi ba ne. Karfe goma daidai shi ne lokacin daurin auran, layin ya dinke da jama'a, Alhaji ranshi a dame don bai ga Abba ba. Ya kalli Alhaji Karami, "Ina Abba ne?" Alhaji Karami ya ce, "Abokan aikinshi ga su can sun zo ba a ganshi ba son daukan daurin auran". Alhaji ya ce, "Su dauka mana nasan yana nan tafe". Har sha daya ana ta jiran 'yan gidan Ango shiru, su Alhaji suka tashi dan aike gidan don a ce ana jiran wakilan ango. Amma sai a ka dawo musu da sako wai sun fasa, kalmar da ta rikita Alhaji ta tashi hankalinsa. Ga jama'a an tara, Alhaji Karami ya ce wadannan akwai kananan mutane." Daidai lokacin da muryar wani Maroki ta ratso dodon kunnuwansu da cewa, "Alhaji ku hanzarta Jama'a sun gaji da jira". Alhaji ya dubi Alhaji Karami, "Aminu a daura da Bashir". Alhaji Karami yayi shiru, can ya ce "A daura da Abba". Alhaji Babba ya ce, "Ina zuwa". Ya fito daga dakin Abba na da inda suke yin shawarar, ya ratsa mutane ya ce a yi masa magana da Suwaiba. Umma ta fito daga kicin ta same shi a dakinsa yana tsaye yana kai-kawo ta ce lafia? Ya ce Gidan ango ne shiru, an bisu sun ce sun fasa. To shi ne na ce me zai hana a daura da da Bashir? 49... Umma ta ce a daura da Abba. Ya ce, "Haka ma Aminu ya ce. To ni ban ga Abban ba ma, amma bari muje Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi". Take a nan a ka daura auren, Habiba da Idris Alhaji Babba ya kirgo sadaki ya mika. Alhaji Karami Waliyinta ya amsa, mutane na ta al'ajabin yanda lamarin ya sauya. Umman Bashir kuwa Bashir din ne ya shiga gidan hankali a tashe yana fada mata cewa da Abba a ka daura. Nan ko ta hau bala'i da zage- zage. Ummi ko tunda ta jiyo guda na alamta mata an daura aure, sai ta birkice ta shiga kowa da numfashinta. Fati da ke kusa da ita tana lallaminta ita ce ta kwala ihu, ba shiri aka yi asibiti da Amarya. Fati ta shiga gidansu da kuka, nan ta taras Ummansu tana bala'i sai lokacin ta ji da Abba a ka daura. Ta ce da Ummar su to menen ba shi ke nan ba? Umma ta hau zaginta tare da cewa, kar ki ga kin yi aure sai in miki shegen duka, Fati dai ta fice ta bar gidan. Sam Umma bata ji dar da ciwon Ummi ba, wannan karon don haka ma bata bi su Asibiti ba, da kanwarta Saratu a ka tafi. Likitan yayi ta fada lokacin da yake yi mata allurai, a kuma bata gado Umma ci gaba tayi da kula da bakinta. Yayin da zuciyarta take fara kar, ta sani kuma tayi Imani Allah ba ya tozarta addu'ar bawansa, matsawar bawan yayi hakuri tare da dogewa. Haka nan in baka samu biyan bukatarka nan duniya ba lallai gobe kiyama zaka tarar da abinka. Ta jima tana rokon Allah yasa 'ya'yan nata biyu su zam miji da mata su haifa mata jikoki masu albarka. Suma su Alhaji suna ta sallamar baki sai dai yanzun ba wanda ya damu ya gani irin Abba. Fatanshi Allah yasa Abban yayi farin ciki da wannan hukunci da suka yanke. Salis kuwa burinshi ya zama shi ne mutum na farko da zai wa Abba wannan albishir sai dai ya kira layin Abba sama da sau hamsim bai daga ba. Abinda bai sani ba shi Abba ma gida ya bar wayar, haka suka gama dauke-daukensu yayi hira da Jama'a da kuma iyayen Ango da Amarya don jin ta bakinsu a kan yanda auren ya juye zuwa na zumunci. Haka nan suka tafi ya samu abin sawa a Taskar labarai, burinshi yanzu shi ne ya je ya nemo angon. 28 50.....Abba kam kofar dan Agundi ya yada zango gidan su Mansir abokinsu, shi ne kurum cikin abokan Abba da bai yi aure ba. Yana isa kofar gidan Mansur na fitowa za shi daurin auren, wani dan layinsu a Gwammaja suka gaisa. Abba ya ce "Bari in dan kwanta a dakinka". Mansur cikin mamaki ya ce, Lafiya? Abba ya ce lafiya lau. Yana kwance dakin Mansur idanunshi suna kallon agogo, zuciyarshi tana raya yanzun abar sonshi ta zama matar Sahabi. Sai dai bai san dalilin da bugawar agogon karfe sha daya daidai tazo gwame da bugawar zuciyarshi ba. Zuciyarshi ta fada mishi cewa wannan alamu ne na an kammala daurin auren. Wasu hawaye ne suka biyo ta gefen idanunshi suna sauka a kan filon. Yini zur yana dakin in lokacin sallah yayi sai ya fito kofar dakin yayi alwala har duhun Magriba ya gabato. Ya fito tare da kulle dakin, don Mansur bai dawo ba, kuma dama ya ce ba zai dawo da wuri ba. Gidan nashi ba kowa lokacin da ya shiga, kai tsaye dakinshi ya wuce, ban da idanunshi da suka kai kan wayarshi ya manta ma yana mallakinta. Ya kai hannu ya dauka, bai ji mamakin yawan missed calls din da ya gani ba, kiran Salis ya sake shigowa. A kasale ya daga, muryar Salis ta ratsa dodon kunnanshi, fadi yake yana maimaitawa Ango- Ango. Abba cikin sanyin murya ya ce "Salis ya haramta a gare ka ka zolaye ni a halin da nake ciki. Sanin kanka kai kadai ne kasan yanayin da nake ciki". Salis cikin zumudi ya ce, "Kana nufin ba ka sani ba?" Abba ya ce, "Me?" Salis ya ce "To bani goron albishir in sanar da kai". Abba ya ce, "Don Allah Salis kada ka min karya". Salis ya ce, "Ina rantsuwa da wanda ya yi mu Ummi matarka ce, da kai a ka daura. Ina ka shige lokacin da al'amarin ya canza salo?" Abba ya mike zumbur. "Ka fa rantse Salis!" cikin dariya Salis ya ce, "Wai har yanzun ba ka sani ba? To ka aje min goron albishir dina". Abba yasa hannunshi a baki ya gatsa, zafin da ya ji ne ya tabbatar da mishi da ba mafarki yake ba. 51... Ai sai ya katse wayar ya zube yayi sujjada ya fita tsakar gida yana furta "Alhamdulillah." Ruwa yaja ya watsa ma jikinshim sannan ya yi alwala. Sabuwar shadda ya saka kalar kunkumadi, ya fesa turare sama da kala hudu. Hula da takalmin bakake, ya nufi Masallaci, daga can za shi gidan su Umma don jin karin bayani. Bayan sun idar da Sallah, mutane suka yi ta masa murna, nan ya hadu da su Alhaji kawai yau sai ya samu kansa da kunyar Alhajin. Alhaji ya ce, "Ubana ina ka shige duk yau?" Ya rasa me zai ce, sai in-ina "Am...na kwanta ne bana jin dadi". Alhaji yayi 'yar dariya, "Kai dai ka ce kana taya kanwarka fushi don mun ce ba zamu daga aure ba, to ba mu daga ba amma Allah cikin ikonsa ya sauya lamarin". Abba tamkar bai san komai ba, ya ce "Alhaji me kuma ya faru?" Alhaji Karami ya karaso gurin su yana cewa, "Kai Abba ina ka shige ne?" Abba ya dube shi "Nan dan Agundi na shiga". Alhaji ya ce, "Oho, shi yasa aka yi ta nemanka. To ka ji kuma yadda lamari ya sauya ko?" Alhaji Babba ya amsa tare da cewa, "Shi ne nake massa bayani, wato Abba iyayen yaron nan Sahabi muka yi ta jiransu su zo gurin daurin aure, wai ashe su sun fasa. Amma ba su shaida mana ba har bin su fa nasa aka yi, gashi mun tara jama'a kawai sai Aminu da Ummanka suka ce a daura da kai, da ni na ce a daura da Bashir". Dadi ya lullu6e Abba irin wanda bai ta6a ji ba, Alhaji ya ci gaba da cewa, kayi hakuri mun kara maka nauyi ba tare da mun ji ra'ayinka ba". Abba cikin matukar murna ya ce, "Haba, ai ko ba 'yar uwata ba ku ka daura min aure da ita zan aminta bare jinina. Nagode". Sun ji mamakin yanda Abba yayi murna, duk da sun san biyayya irin tashi ba zai 'ki ba, tare suka rankaya gidan su Umman, so kurum yake yaga Ummi. Ba mutane sosai, don haka har ciki ya kutsa, sai dai suna hada ido da Umma sai ya ji nauyinta, ta fada da fara'a. "Ina ka shige Abba?" Yayi dan murmushi, ta ci gaba "Sai kuma ka ji yanda abu ya kasance?" Ya ce, "Na ji Umma, Allah yasa haka shi ne alkairi". Ta ce, "Amin, Insha Allahu". Tamkar ya tambayi ina Ummin, amma ya kasa. Umma ta ce "A baka abinci ko?" sai lokacin ya tuna da batun abinci, amma baya gabanshi, ya ce "Na koshi Umma". Ta ce, "To ga na 'yan asibiti can in kayi isha'i". Da sauri ya ce "Wa ke asibiti kuma?" Ta ce, "Ummi ce, ko 'yan daurin auran ba su watse ba don ka ji yarintar nan ta hau farin suma don haushi ko leka su ban yi ba. Tana can it da Saratu sai Tsohuwa da ta matsa yanzun Alhaji Karami ya kai ta". Jikin Abba ya yi sanyi, kenan tsabar rashin sonshi ne ya saka Ummi suma? Ya ce Umma bani abincin asibitin. Sai da yaje gidanshi ya dauko dan mukullin motar, a zuciyarshi yana tambayar kanshi ina kuma Bishira tayi ne? Zai bude motar kenan muryar Bashir ta dakar da shi, "Kaci nasarar samun furen zuciyata, amma ka sani ka kulla abota da rashin zaman lafiya a novels / ZURFIN CIKI book 3 part 7 ZURFIN CIKI book 3 part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:33 kulla abota da rashin zaman lafiya a gidanka". * 52..A fusace abba ya dubeshi"xansa yan sanda su rufe min kai inhar zaka cigaba da kiran matata da furen zuciyarka,rashin zaman lfy kake cewa? An dade ba'ayi yaki abgdn ba kullum,bashir yace oho dai ni zanta zuga umma abba yaja tsaki tareda shigewa motarshi. Bashir yashiga gdnsu inda su ummanshi dasu bishirabke zaune jugum jugum tamkar masu zaman makoki,bishira tabi bashir da kallo lkcn dayace ga ya abba ya can a waje yashiga mota ya kure wanka,kila ma asibiti zaije ana fada maku yanaso kuna wani tilasta shi akayi,bishira cikin dasahhshiyar murya tace aiko da bala'i don ko bazan yarda ba,umman bashir tace sha kutuminki bishira,barni dasu zan maganinsu, bishira tafita fuu,amma saidai. Kafin ta isa gurin motar tuni ya, Cilla yabar mata hayaki. Da innna saratu kanwar umma ya soma cin karo a asibitun suka gaisa,tace ashe kuma haka abu ya zama? Yace eh"nima dana dawo dazu nasamu lbrin,tace Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,abba yace ameen inna,ya mai jikin? Tace dasauki,yace bacci take? Tace a'a ta farka tun kusan karfe uku,koda fatima ta fada mata yanda abubuwa zuka zama,tayita yan koke kokenta,gaban abba yafadi****tabbas ummi ba son shi take ba inba hka ba meye na kuka? Ya kalli inna bari in karasa,tace to kaje tshuwa na ciki,a ranshi yace jaraba road,yasan dai ko yane sai tshuwa tayi mishi surutu,yana tura kofar tareda salama suka hada ido da ummi,sun kure juna da kallo,kowanne nason ya fahimci ya dan uwansa yadauki abin"tshuwa ta katse su dacewa to zakin fama sai ynz kaga daman zuwa? Ya dubeta eh" ai eh ace? To me kikeso ince,tace to madalla ai na dade da sanin halinka,kuma da ace iyayenku sunyi shawara dani lallai da baza suyi wanna hadin ba Domin na tabbata kai zaka karasa takwara don baka kaunarta, haushi ya cika abba abba yana kallon tsohuwa yana tuna amsar data dace da ita, ummi kuwa tsura mishi ido tayi tana son jin me zaice,yace kamar kin sani,tace ahaf shiyasa tausan yar nan kebani tausayi, ta soma matsar ido,yace nima yakamata. ki tausayamin tnda cusa min ita akayi,ummi takoma ta kwanta lakwas tareda hakikancewabl kalaman abba sako ne zuwa gareta,matar cushe kuma bata daraja,to inaso kasan wani abu guda,duk randa naji wani abu daidai da wulakanci, toba kaiba har iyayenka saisun san naje makura. 52..Dazun nake gaya masu basun hada kai sun kulla auren nan ba,duk randa suka kuskura sukazo min da batun warwareshi saina basu mamaki,abba ya tabe baki tareda kallon ummi wadda takasa jurewa tashiga rera kuka,ya isa gaban gadon,"jikin ne ummi? Tayi shuru,kinci abinci? Nan ma ta share,sai kurum ya nufi wurin likitan zuciyarshi na kuna bako shakka kukan kin shi ummi keyi,sun zo da likita ya shiga yimata fadan kukan da takeyi,a cewar likitan kukan illa ne ga lafiyarta,tshuwa ta kalli likita dan nan dole ta koka a dauke ka ahadaka da wanda baya kaunarka"abba cikin takaici yace subhanallla! Don Allah tshuwa kibarni inji da abinda ke gabana,tace ina ruwana da abinda ke gabanka,likita yayi dariya yace mama yakamata ki koma gd haka,abba yace bari inkaita indawo,tace ban binka da can dani kazo? Abba yace nahuta,likita yayi dariya,da kyar suka lallaba tshuwa ta tafi da inna saratu,abba yaja kujera ya zauna gaban gadon,bayan fitan likita Idanu ya zuba ma ummi,godiya yake ma Allah a zucin shi daya amsa addu'ar shi yabashi abar sonshi,itako kai ta dukar a ynz takasa tantance kukan farin ciki take ko takaicin kalaman ya abbanta? Wani. Dan zare dake jikin hijabinta take wasa dashi,a zuciyarta kuma tambayoyi ne da fuska data jefa masa su,ya katse ta kinci abinci? Ta daga kai alamun eh" yace to yakamata ki dangana da kukan haka kisani ni kaina da ina nan bazan bari su alhji su daura maki aure da wanda bakiso ba. 53..Da sauri ta kalleshi,yace. amma inkin yi hkr zansame su zamu san yadda zamuyi,ta lumshe ido a zuciya tace tab! Ai rabamu sai mutuwa,zan juri duk wani ki dazan gani daga gareka,ya katsxeta kina zance a zuci fadi abnd kikeson cewa,tayi tagumi tareda kallonshi,ya abba yakanfi dacewa sa dan sanda ne ba dan jarida ba,sbd yanada saurin nazartar mutum,to amma meyasa yakasa gane tana son shi? Yayi murmushi,zanso inji abnda kikeb saqawa azuciyarki ko kinn samo mafita ne? 29. Zancan mafitar nan tana bata haushi, don haka saita canza zancen da cewa, tambaya zan maka guda biyu, ya dan yi shiru. Nazari yake, wace irin tambaya zata masa? Kila zata tambaye shi ne ko zai amince ya sahale mata auranshi, ya dubeta amsa daya zan ba ki in kin yarda, ta ce To dama zance ne ya ka ji lokacin da labarin sauyawar lamari ya zo gareka? Ya kura ta da ido, ya tambayi kansa a zuciya, me yasa take son ji@ yayi dan yake, yi tambayarki ta gaba, ta tsura mishi ido. Yanzun yaya za ka yi da maganar Zainab? Ya yi 'yar dariya, wacce amsa ki ke so a ciki? da sauri ta ce ba ni wannan amsar. Ya ce, "Kiin manta ni mijin mace hudu ne? Ta zaro ido kamar ya ya? Ya yi kokarin danne dariyarsa, sakamakon yanda ya ga ta zarana. Ya ce, "Ina nufin bayan Zainab har da wata, Ummi ta hade rai sannan ta zame ta kwanta cike da dana sanin tambayar. Abba ya yi mamakin kishin Ummi gare shi, ita da ba sonshi take ba? Ko da yake an ce mace ko bata son namiji in dai mijinta ne ta tsani ta ganshi da wata. Duk da haka ya ji dadin yanda ta nuna kishinta a kanshi, da ya tuna da Bishira ya ce tab, wata fitinar tana can tana jirana yau. Sam Ummi bata kara magana ba, shi kam Abba waya ma yake tayi Inna Saratu ta dawo, don haka ya mike ya kalli Ummi. Zan tafi ba tare da ta dago ba ta ce, sai anjima. Ya tafi yana waiwayonta bayan ya wa Inna Sallama. Kin shiga gidanshi ya yi sai kusan sha biyu a nufinshi lokacin Bishira tayi bacci, sannan yaje ya sai mata wayar da layi don yasan tana son waya. Kudinshi kenan ma ya kwashe ya sai mata, bai yi wani motsin kirki ba don kada ta farka, ya bude dakinshi ya shiga ya fito yana jan ruwan wanka kenan ta fito daure da zani a kirji. Jikinta ko dan kwali babu, gaban Abba ya fadi ta ce, "Munafukin Allah, annamimi dama ashe abinda kuke shiryawa kenan? To ka sani dole kasa ke ni don ba zan iya zama da Ummi ba, Allah ya kiyaye in hada miji da wannan 'yar yarinyar, tunda kai baka ga ai baya ba". Ya sassauta murya, "Haba Bishira, wannan abin fa Allah ya kaddaro za a yi haka, matar murtum kabarinsa. Ta ce, "To wannan ajalinka ce tunda wancan ya ki shi ne kai a ka cusa maka. Ya bar jan ruwan ya kama hannunta suka nufi dakinta, tana ta masifa. Ya ce, kibar maganar yanzu dare ne duk makota suna ji za su yi, kuma banga bain da zai sa ki daga hankalinki ba. Kin san dai ina sonki ko? Ta yi shiru tana kallonshi, ya ce ina zuwa. Yaje dakinshi wayar ya dauko mata, ga wayarki. Ta ce, "Eh don ka toshe min baki k? to bana so, ita wa ya san abinda ka sai mata? Ya ce, ya ki ke wannan maganar? Ban sai komai ba ko lefe ma tukunna. Ta mike tare da jefa mishi kwalin wayar, Ga tsiyarka nan matsiyaci, dole ka saka min da haka, tuni a ka gaya min tsiyar talaka na tafe. Haushi ya kama Abba ya dauki wayarshi ya tafi ya maida yazo ya dau ruwanshi yayi wanka, yana jiyo kukanta da duk zage-zagen da take yi. Shi kam katifarshi ya fada tare da rungume fito yana tunanin ranar da Ummi zata maye gurbin filon. 30. Har an tada sallah a Masallaci lokacin da ya farka, ya jima bai yi irin wannan baccin ba, da hanzari ya fito ya nufi ban daki don alwala. Abin mamaki Bishira ce zaune kan kujera a kofar dakinta, matar da sai ta kai takwas bata farka ba, amma yau bala'in kishi ya hanata bacci. Ta ce, "Eh na fito a ba ni takardata na gama zama da kai, ko in da take bai kalla ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi, ya nufi Masallaci yana jinta tana ina nan ina jira ba zan zauna ba. Haba, gaskiya naji na tsani yarinyar ashe mijina zata aura, tsaki ya yi ya bude gidan ya fice. Har gari ya soma haske yana cikin masallacin, tunanin zuwa gidan yake, daga karshe dai ya fita da niyyar zuwa gidan Ummarshi. Wata zuciyar ta tambaye shi da cewa, tsoron ta ka ke ji ne? Kar ka zama soko dai a gidanka. A fili ya furta cewa, tunda na bita ta lalama ta ki, bari in koma mata ta zafin, ida din me? Sai ya sauya hanya zuwa gida rai 6ace, fuska daure ya shiga gidan, tana ta kai-kawo a tsakar gida. Ta dumfaroshi sai ka ce sabon kamun hauka, daga ganinshi ta dinfaroshi. "Ka ban takardata ba ni ba zama da kai, tafiya zan yi". Ya harareta "Sai da takarda za ki tafi? Lallai ba ki ji tafiyar ba. To ba zan bada takarda ba, don ki sani, sai dai in kotu za ki kai can Alkali ya baki". Ta nufo shi da zummar shako masa kwala, ya ce Kina ta6a ni sai na zane ki, in yaso ki tafi da hujja". Ganin yanda Abba ya bude mata wuta sai taja baya, Ka isa ka zane ni, ai da ka san ka dake ni, don ko sai ka sha dauri. Ya nufi dakinshi, wanka ya fito yayi sannan ya yi shirin tafiya aiki, amma har lokacin tana nan, ga 'yarta ta tashi daga bacci sai kuka take yi. Ta dauke ta ta goya, ta shiga dakinta can kuma ta sauke 'yar tasa kaya ta fito ta dauraye fuska da kafa ta goya 'yar tasa kaya ta fito taja kofar tana fadin." "Tafiya zan yi". Ta fito ta same shi yana goge gilashin motarsa na gaba. Ta ce, Tafiya zan yi sai an kar6ar min hakkina". Murmushi ya saki, sannan ya kalleta, ta ina za ki bi in rage miki hanya? Ta dawo ta duki motar, Ba zan shiga wannan gwanganin motar ba, kai ne bakon mota. Kafi kowa sanin daga gidan da na fito, ko motar zuwa cefanen gidanmu tafi wannan tsarri. Ya ce. "Gurinki ko? Ni ai bani da wadda ta fita tunda bata gidan naku nike hawa ba. Sannan kuma tunda ba za ki zo in rage miki hanya ba shi kenan sai naga sammaci. Ya shiga motar ya tasheta yayi gaba, ba tare da ya saurari abinda take cewa ba. Ta isa gidansu cikin tashin hankali, Hajiya Zainu ta saurare ta tsaf, sannan ta ce "Kin dai ga abinda a ke fada miki, kina ganin ba zai faru ba ke so ya rufe miki ido, to yanzu an zo gurin. Bishira ta ce, "Ai na gane komai yanzun, Momy nayi nadama. Ta ce, "To zan tsaya miki matsalata Babanku, yana nan a gari na kuma san za su zo iyayen Abba. Amma wannan karon shi kanshi Babankun zan iya ja da shi, Bishira taji dadi sosai, don kuwa duk son da ta ke wa Abba yanzun kishi yasa ya koma 'ki. Gidansu Umma yaje a gurguje suka gaisa, ya kwashe su da Alhaji da Alhaji Karami zuwa asibiti, a motar nema ya ke fada musu cewa Bishira ta tafi gidansu Umma ta ce a kan me Abba, me ka mata? Ya ce, "Ban mata komai ba, ya fada musu duk yanda aka yi. Alhaji Karami ya ce, Sahura ke zugata, itama ai kwana tayi bala'in. Don haka kada kaje bikonta, Alhaji Babba ya ce, "Ba za a yi haka ba, da dare kazo muje, Abba ya ce To. Sun isa asibitin tana wanka, sun gaisa da Inna Saratu ta fada musu tana wanka, sannan likitan ya sallame su amma sai sha biyu za su tafi gida, lokacin an karasa mata allura. Abba can baya ya tsaya kusa da kofar shigowa ya jingina da bango idanunshi suna fuskantar kofar bayin, matuka ya kosa yaga Ummi. Sanye da hijabi da zani daurin kirji ta fito, da Abba suka soma hada ido, bai ta6a kallon Ummi da sha'awa ba sai yau. Kamshin turaren Abba ya ratsa ko'ina a dakin, ta zare idanunta daga nashi, ta kalli Ummanta sannunku Umma. Suka ce Yauwa. Ta gaida su sannan ta zauna bakin gado tare da sunkuyar da kai, Alhaji Karami ya ce, "Uwata jiki kuma ya yi sauki ko? Kanta na kasa ta ce, Eh, ta kasa dago kanta, gani take Abba ya cika dakin. Abban ya ce, "To ni zan tafi don lokacin aikina ya kusa, Alhaji zamu je ne in sauke ku? Suka ce To, Umma ta ce In an yi mata Allurar anjima ma nemo mai Taxi. Alhaji ya ce, To shi ke nan. Umma ta dubi Ummi ba za ki gaida Yayan naki ba? Ta saci kallon Abban tare da cewa, Au, ban ganshi ba. Ina yini? Ya ce, Umma me yasa za ki rokar min gaisuwarta? Inna Saratu ta ce, Kai Ummi da iya shege take, ina kallonta shi ta fara kare ma kallo sannan ta kalli kowa amma wai bata ganshi ba. Su Alhaji dai 'yar dariya suka yi sannan suka fita, Abba ya bi su tare da yi wa su Umma sallama. * 31. Bayan fitarsu, Umma ta dubi Ummi fuska daure, ina fatan baki nuna damarar nuna kiyayya ga Abba ba ne? Ummi ta sunkuyar da kai, a ranta ta ce, "Kin ji Umma da wani zance, ai ina zaton nafi Mahaifiyarshi sonshi ma bare ku. "Amma a fili sai ta ce, To Umma shi ma fa Ya Abban bai ce yana sona ba, Umma ta ce Saratu ji ta da wani shirme. Ina ce ita ce zata janyo ra'ayinshi gareta? Inna Saratu ta ce, Kwarai kuwa, ta hanyar ladabi, biyayya da girmamashi, musamman shi da ke da matsalar mata. Ummi ta ce, Kuma ina tsoron masifar matarsa ba dai guri daya zamu zauna ba ko? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa? Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai kama? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa? Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai kama? Kada ma in ji kin kuma zan nan, Ummi dai tayi shiru. Da dare Alhaji ya tasa Abba zuwa gidan su Bishira, zuwan su ne ma Alhajin yasan 'yarshi tayo yaji, cikin 6acin rai ya kira wayar Hajiya Zainu ya ce su zo ita da Bishira. Ba tare da ya jira amsarta ba ya aje wayar, ba tare da yasan abinda ya faru ba ya shiga ba su hakuri. Hajiya Zainau taje dakin su Bishira ta kira, suka nufi sashen Alhajin tana mitar cewa munafukai sun zo kenan, ai za'ayi ta bari muje mu ji. Suna shiga Alhajin ya kalli Bishira, "Me ki ka zo min ki yi a gida? Ta ce, Daddy cin amanata ya yi, aure fa ya yi da yarinyar da suka tsane ni. Alhajin ya daukin da ke gabanshi na plastik ya jefe ta da shi, auren shi ne cin amana don uwaki? Hajiya Zainu ta ce, "A'a Alhaji, zan cen gaskiya a duba hakkinta itama, ya ya za a dau 'yar da bata kaunarta, iyayenta basa kaunarta a ba shi. Sannan ta yi magana ya hauta da zagin iyaye? Ya ce, "Ke yi min shiru ban tambaye ki ba". Ya kalli Abba, Ya abin ya faru? Ban ji ta bakinka ba? Nan dai Abba ya fadi komai har ta taho, daidai da cewa tazo ya rage mata haya da abin da ta ce duka. Alhajin ya yi tsaki ya dubi Alhaji Babba, irin wannan ai ba a biyo su, tayi ta tafiya sai dai nima in ba zata koma gidanta ba, to ba gidana ba. Ya zura hannu cikin aljihu ya ciro rafar 'yan dari bibbiyu, Ga shi Abba, dama nayi maka alkawarin baka sadaki duk lokacin da ka nemo aure. 57..... Abba ya ce, "A'a ka bar su ai an riga an yi. Mahaifin Bishira ya ce, "Ni nayi alkawari. Suka yi godiya. Ya kalli Bishira, Ko ki bi mijinki, ko ki bar gidana. Hajiya Zainu ji take tamkar ta shake Abba. Ta ce, "Haba Alhaji, gaskiya ban yarda da wannann hukuncin..." Ya katse ta da cewa, Ke! Da Allah fita anan. Su Abba suna shiga mota Bishira na fitowa da kukanta, dole ta zo ta shiga motar. Alhaji Babba ke ta bata baki har suka kai gida, shi kam Abba da suke sauke Alhaji ya yi nasu gidan, suna shiga ta soma zantuka. Ba za ka ta6a samun kwanciyar hankali ba a gidan nan har abada, ba dai ka matsa an dawo da ni ba? Abba ya yi murmushin mugunta, ai ni wannan yajin naki naji dadinsa, gashi har na samu gudunmawa, kin ga sai naje kasuwa in soma darzo wa Amarya zannuwan lefe. Ya nufi dakinshi ya barta nan tsaye tana zage- zage, lefen banza, in ma uban lefe ne kai da ita sai na koya musu hankali. Kusan goman dare Ummi tana kan doguwar kujera, addu'a take yi Allah yasa Abba yazo ta ganshi kafin tayi bacci. Can kasan zuciyarta kuma kishi ne don tasan sun je gidansu Bishira ne biko ganin Alhaji ya shigo shi daya sai ta debe tsammani da zuwanshi. A ranta take raya cewa yanzun haka suna can suna cin soyayyarsu, kamshin turaren shi ne ke mata gizo a hanci. Amma sai kunnuwanta suka tsinkayi sallamarshi, a hankali tamkar ba ya son a san ya shigo. Umma tana ciki? Tambayar da ya yi kenan ba tare da ya jira ta amsa sallamar ba, ta tashi zaune da sauri a'a tana gurin Alhaji. Ya shigo ya zauna ta ce, "Sannu da zuwa". Ya amsa yana kalonta, ta sunkuyar da kai, gabanta ke wata irin faduwa. Shi kam ji yake tamkar ya manne ta a jikinshi, sai dai yana jin nauyin hakan tunda ba suyi wannan sabon da ba rin haka zata faru tsakaninsu ba. Dakin yayi shiru, ita tana wasa da yatsunta shi kuma yana kallonta, can ya ce "Ummi". Ta dube shi "Yaushe za ki tare? Ta ce, Nima ban sani ba, sai yanda su Umma suka ce. Ya dauko kwalin wayar da ya sai ma Bishira ta jefe shi da shi ya ciro wayar ya hadata da batir din bayan ya 6are sim din ya saka. Ummi dai tana ta kallonshi, ya manna chajar a jiki, ya mika ma Ummi jona min can, ya nuna mata soke din da ke bayanta. Ta amsa cike da sha'awar wayar duk da bata nuna hakan ba sannan ba ta ce kala ba. Ya ci gaba da cewa, "Karfe nawa a ke kashe inji? Ta ce, har yanzu ba a canza daga yanda ka ke kashewa ba. Ya ce, "Sha daya zuwa sha biyu? Ta ce, "Eh, ya ce in har zuwa wannan lokacin ba kiyi bacci ba to ki cire in an kashe, ki kunna ko da yake in dai ke ce ba sai na ce ki kunna ba. Ta dago ido ta kalle shi, ya ce, Eh kunnawa za ki yi ko za ki musa ne? Don kin fi ni ma sanin kan waya. Ta ce, Wayar Umma kadai na iya kunnawa, sai taka. Ya ce, Oho, cikin dan murmushi, na za ci ba za ki fadi tawa ba in tuna miki lokacin da kika kunna tawa. Haka nan don tsabar iya sarrafa wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin Kaduna. * 58....Haka nan don tsabar iya sarrafa wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin Kaduna. Ta zuba fuskarta cikin tafukan hannayenta, sam bata son Ya Abba yana tada wannan zancen, Umma ta shigo da sallama tana cewa, Yuwa Ummi, ina ki ka sa min 'yar kwalbar turaren nan? Ummi ta dago fuska, "Cikin jakarki ta rataye. Umma ta dubi Abba, "A'a ha, yaushe ka shigo? Ya ce Ban jima sosai ba. Ta zauna ya gaisheta, sannan ta ce masa dama Alhaji yanzu yake ce min zaman me Ummi ke yi a gidan nan? Ya zaci tun daga asibitin zata wuce dakinta, Ummi ta turo baki. Umma Alhaji ya gaji da ni sosai, suka kalle ta, Umma ta ce, Ji wani shirme, me ya yi na gajiya? Ta ce To dubi fa daga cewa an fasa aurena sai da ya matsa ya daura min aure. Sannann kuma yanzun wai ya zaci daga asibiti zan tare? Abba ya ce, Ai yana daki yi hanzari ki same shi don shi ya san amsarki ba Ummata ba. Umma ta ce, "Wallahi daga nan suka share Ummi. Ta kalli Abba ta ce, "To kawai yanda za a yi gobe ka kwashe kayanka daga dakinka sai a kai na Ummi din kawai. In yaso zuwa yamma ko Saratu da sauran makota sai su rakota. Abba ya kalli Umma, ni da so nayi a dan yi kwaskwarima a gidan kafin sannan na dan samu na sai ma Ummin Zannuwa. Umma ta ce, "Zancen wofi, yanzun tsirara take yawo? Kawai in kana da fenti a hannu a goga a kawo ta haka, in babu ma dai goben nan zata tare don ba zan amince ran mijina ya 6aci ba. Abba ya yi murmushi, to shi kenan Umma da safe kafin na fita zan nemo masu aiki ina da fenti da siminti sai ayi 'yar kwaskwarima shi ke nan. Dama ga kudi nan da Mahaifin Bishira ya bani, wai dama ya yi min alkawarin biya min sadaki. . 59... Umma ta ce, "Yanzun Alhaji ya gama bani labari, Mahaifin yarinyar nan mutumin kwarai ne, don Allah Abba ka rike yarinyar nan ko don darajar mahaifinta. Ummi ta ta6a baki, kishi ya motsa. Abba ya ce "In sha Allahu Umma nima abinda nike dubawa kenan, ni ke hakuri da ita. Ta ci gaba da cewa, Sannan kada kaga Ummi yar uwarka ce ka ce zaka fifitata, sam ba zan yarda da haka ba. Kayi adalci a tsakaninsu ka dinga addu'a Allah ya hada maka kansu. Ya ce, "In Allah ya yarda Umma zan kula. Ta ce, "To maza ka tashi ka tafi gurin iyalinka. Sam bai ma dace ka fito ba, kamata ya yi a ce ka zauna gida ka kara ba matarka baki, ya cee To Umma. Ta mike tana cewa, tashi maza. Ya mike yana kallon Ummi, yayin da ita kuma ta juya fuskarta cike da 6acin rai. Ya ce, Ummi ki fa kunna in an kashe injin? Sam ba ta tanka ba don haushi, sai da ya tafi sannan Umma ta dubi Ummi. Ki tashi ki kwanta don gobe ki tashi da wuri, kiyi duk shirin da ya dace saboda babu daga kafa a tarewarki gobe. Ki ta fasha-fishenki ba zamu kuma yarda da kalace-kalacen ciwonki ba, ta tafi abinta. A zaton Umma, Ummi tana fushin ba zata tare ba ne, ita ko haushinta korar mata miji da Umma tayi ya tafi gurin kishiyarta. Koda ta kulle kofar ba ta shiga uwar dakin ba, nan kan doguwar kujeta ta mike abinta. Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya. Abba ko kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai tsafta.I novels / ZURFIN CIKI book 3 part 8 ZURFIN CIKI book 3 part 8 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:37 Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya. Abba ko kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai tsafta. 60...Sai dai yana shiga gidan ya iske mahaifiyarshi da matar tashi suna ta zage- zage. Ya nufi gurinsu, Sahura ta ce, Sai yanzun suka barka ka taho? Ya ce, "Umma dama ban dade da zuwa ba". Ta ce, "Ina ta aiken kazo ina nemanka shi ne ka 'ki zuwa saboda ka maida ni 'yar iska ko? Ya ce, A'a Umma ba a fada min ba. Sannan aiki ne yasha kaina... Ta ce, "Rufe min baki, ai baka daga kafa da zuwa gun Suwaiba. To saurare ni da kyau ka ji, nazo ne in fada maka cewa ka rubuta saki ka ba wannan 'yar iskar yarinyar. Ya ce, Kiyi hakuri Umma, ki bari sai a hankali. Bishira ta ce, Umma yana sonta fa, jin ku kawai nake. Maganar Bashir gaskiya ce da ya ce da shi a ka shirya hakan. Umman Bashir ta ce, "Dama Abba kaima son Ummi ka ke yi? Ya ce, Umma ba zan ki Ummi ba, in kun yi la'akari da kaunar da iyayenta suke nuna min. Amman wallahi ban san komai game da auranmu ba, ta ce kana nufin kan dole a ka daura muku aure ba don kana sonta ba? Abba ya yi dan jim, ta ce kai nake sauraro, don ta tafi sai ya ce kusan haka dinne, itama kuma ba sona take ba. Umma ta ce, Ina ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai suna so. Ni dai bukatata yanzun kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka. 33. 61... Umma ta ce, "Ina ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai suna so. Ni dai bukatata yanzu kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka". Ya dan yi shiru yana tunanin wannan irin lamari a zuciyarshi ya ce, bari kawai in lalla6ata, zan yi yanda ki ka ce sai dai kuma in su Alhaji suka sa kawo ta ni ba zan iya ja da su ba. Sannann ke kanki bana so a ce ke ki ka sa ni in ma Ummi rashin mutunci, amma ki bar ni da ita in har ta yarda ta tare a nan gidan. Bishira ta ce, "Tab, ba ko zata tare a nan gidan ba". Umma ta ce "A'a ki bari in sun matsa ta tare a nan din ta tare, gara suna kusa muna kallon irin zaman da za su yi. Can gefe ba sai su rinjaye shi ba". Bishira ta ce, "Umma na tsani shegiyar yarinyar nan ne, bana son in ganta ko cikin mafarkina, bare a zahiri". Sahura ta ce, "Bishira na ce ki nutsu ki bar komai a hannuna, in ma zan hada da Bokaye ne ba Malamai ba in sha Allahu sai kin dara a gidan nan. Ta ce, "To Umma, Sahura ta ce, Yauwa ke dai ki zuba ido, Abba dai yana tsaye yana kallonsu. Sai lokacin yayi magana, Umma dare fa yayi, ta ce to muga ledar hannunka, ya mika mata. Ta buda ta gani, "A'a kaza? To ku zuba min nawa". Ya mika wa Bishira, Ki dibarwa Umma. Ya nufi dakinsa yana jin sallamarta tana fadin ta wuce, ya fito ya ce "To Umma sai da safe, ya rufe gidan ya koma dakinsa. Da ya shigo gidan ne da niyyar lallashin Bishira, amma yanda abubuwan suka zama sai ya ji ba ma ya son ganin Bishiran. Zantukan Bishiran da na Mahaifiyarshi sun saka shi cikin tunani, lamo ya kwanta a kan katifa yana ta harsaso irin zaman da za a yi a gidan. Anya kuwa ba zai kama wa Ummi haya ba? Cak! Hasken wutar dakin ya dauke tare da tsayawar Injin. A fili ya futa, Mai ya kare kenan, sai da ya yi shirin bacci ya kwanta tare da manne filo a kirjinshi, sannan ya dauko wayarshi ya kira layin da ya hada cikin sabuwar wayar da ya ba Ummi. 62.. Gabanta ne ya fadi, lokacin da taga lambar Ya Abba suna rawa a fuskar wayar, ta haddace lambobinshi tun shekarun baya. A fili ta ce, kenan ma ya hada wayar ba yau ya soma hada ta ba, ta sake yin lamo a kan gado tare da janyo filo ta manna a kirjinta. Ta daga wayar lokacin tana daf da tsinkikewa, can cikin makoshinta tayi sallama. Ya amsa, tsigar jikinsa a tashe sakamon jin muryarta tana ratsa jikinshi, ya ce "Ummi, ta ce Na'am Ya Abba. Ya ce, "Kina son ki tare goben? Ta lumshe ido, ba ni da za6i Ya Abba, duk yanda ku ka ce. Dadi ya cika zuciyarshi. To shi kenan ki tare goben, zan yi parking tun Asubahi sai in sa mai fenti yayi kafin in tafi aiki. Ta ce, "Ba an ce in mutum ya yi aure ana ba shi hutu ba? Ya yi 'yar dariya, "To ni ba ki ga yanda auren nawwa yazo daga sama ba? Amma duk da haka in na nemi hutun za a bani, ta ce kayi aikin kama kawai ba sai ka nemi hutu ba.. Ya katseta, "Don ba a sona shi yasa ba a damu na amshi hutu ba? Ta ce, "Ba nufina kenan ba, naga kana matukar son aikinka ne". Ya yi dan murmushi "Kin dai wayance kawai, to yanzun haka zaki tare babu ko dan kunshi bare gyaran kai irin na Amare? Koda yake ba aure so ba ne. Cikin muryar shagwa6a ta ce, "Ya Abba ka daina, ya ce me zan daina? Kana cewa bana sona, ai kai ma ba ka sona... Ya dan yi shiru, yanda ta ke shagwa6ar ne ta tsuma shi. Ya ce, ok, to goben sai kije ki gyaranki ko? ta ce, "Umma ba za ta bari in fita ba, amma me yin fulawa za ta iya ta mini". Ya ce, "To ina ne a ke gyaran gashin? Ta ce, "Cikin gari ne, ya ce kin san gurin? Ta ce, "Eh, amma ban ta6a yi ba, ya ce to ki bari zan shigo gidan kafin na tafi aiki zan ce Umma ta bar ki, ta ce "To." Suka dan yi shiru. Can ya katse shirun da cewa, "Me ki ke tunani?" "Yaushe?" "Yanzun." Ta dan musukuta, "Ina tunanin yanda abubuwan za su kasance gobe. Yanda har za'a yi fenti, sannan a jire kuma in tare duk a gobe". Ya ce "Duk mai sauki ne, ni kuma kin san tunanin da nake yi yanzun? Ta ce, "A'a, ya ce gobe kamar yanzun muna tare... da sauri ta katse wayar, me Ya Abba ke son fada? Ta kashe wayar sannan ta kudundune. Ita ma yanzun ya jona mata wannan tunanin, a fili ta furta gobe kamar yanzun me ya ke faruwa? Shi kuwa sai ya ji haushin kansa sakamakon furucin da ya yi har ta yanke wayar, wani gefen kuma sai ya ga kila don bata sonshi ne shi yasa har ta ji haushin furucin nashi. Kila ma yanzun tana can tana kuka in ta tuna gobe tana gidansa, dare ya tsala amma ya kasa bacci, don haka sai ya mike yayo alwala. Sallah ya shiga don kara nuna godiyarsa ga Allah da ya bashi Ummi tare da rokon Allah ya kimsa mata sonshi, daga karshe ya roki hadin kan matansa. 34 63..Yana wanka da safe ya jiyo muryar mum dinsa harta zo gdn, a zuciyarshi yace innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yana fitowa tace wurinka nazo, Bashir yazo ya fada min cewa yau za'a kawo fitsararriyar yarinyar nan ko? Abba cikin damuwa yace umma nima bansani ba, tace munafiki kasani, bari kaji ko an kawota ko magana bance ta hadaku da ita ba, kai in ma kaje girin munafukan iyayen nan nata su ka ce yau zata tare kace saika shirya. Bishira tace umma bazan yarda ta tare ba, bai sai min komai ba, ya kalli Bishira to itama na sai mata wani abun ne? Sahura tace to ina ruwan wani da baka sai mata ba? Abba yace toni bani da kudi ma, Bishira tace to kudin jiya da babana ya baka fa? Umma tace fito dasu, yace umma dama fa kudin sadaki ne ya biya min, kuma naba alhji karami waliyyinta sai dai ki je gun shi ki amsa, tace don kasan bazan tunkareshi bane shi yasa to tana binka bashi, zaka chanza mata kayan daki, ka sai mata zannuwa sannan ka bata jari, yace umma banyi alkawari ba, in dai na samu kudi kuma ta kwantar da hankalinta to xan mata, ya nufi daki yabar su nan sunata zantukan su. Lkcn daya shiga gdn su umman shi, ummi tana linke kaya tana sakawa cikin jaka, yana daga bakin kofa ta dago ta amsa sallamar shi ta kalle shi, ya kalli kayan sam zuciyarshi bata mishi dadi, ya nufi wurin umma don yana son neman alfarma abar ummi zuwa dan wasu kwanaki don yana so ya dan gyara gidan, rashin galihun zai yi yawa, ba lefe kuma gida ba gyara? Yayi sallama suka amsa, bayan ya gaishe su, ya dukar da kai yace alhji dama nazo ne neman alfarma, suka ce alfarman me? Yace inaso ne kudan bar ummi zuwa nan da sati daya, sannan na gyara gdn, kuma nayi mata sabbin dinki, alhji yace ba kana da fentin ba? Kaje kasa a goga, sai ka biyo ta kasuwarmu ka amshi zannuwa, abba yayi shuru umma tace koda wani abu bayan nan? Yace a'a, umma tace to an daga maka zuwa gobe, yace to umma da alhji nagode, ya mike ya zai fita, yace am umma ummi tace zata je gyaran gashi, suka yi dariya su kace ai wannan ikon kane, yace to na tafi alhji sainazo kasuwar, ummi ta jera masa kayan karin kumallo koda ya leka dakin sai tace ya abba ka shigo ga break, yace ummi zanyi latti, tace to da yunwa zaka tafi? Yace akwai shayi a can, tace come on ya abba zoka karya, ya kalli agogo minti biyar gareni, ta dau copi ta tsiyayo kunu ta mika masa, ya fara kurbar kunun, ta zubo kosai a plate tarike a hannunta dauka kaci, ji take tamkar ta bashi a baki, tsohuwa ta dago labulen dakin, tace zura masa a baki za kiyi? Ummi tace kada ya kware tsohuwa, an hana yin magana in ana cin abinci, toshuwa tace tafi can da cusa kai ba kwarjini, abba ya dire kofi tareda mikewa yace ummi saina dawo, ki bari da dare zan kai ki gyaran gashi, yasa hannu a aljihu ya zaro yan dari binbiyu guda biyar ya bata, tayi godiya ya ciro dari yaba tshuwa yace yar sa ido kema kiyi kotso da wannan, ta rike baki tana fadin wannan yara da munafunci suke, ya fita yana murmushi ummi tace a dawo lfy, ya sake waiwayo wa ya kalli ummi, suka saki murmushi, 35. 64.... Tsohuwa da ke bin su da ido ta ce, "Kai ban yarda da ku ba Takwara, dama can ke da me sunan Malam soyayya ku ke? ---- Umma da ta tsinci zancen bayan fitowarta daga dakin Alhaji, ta ce "Ya a ka yi?" Ta ce, "Suwaiba ina ga yarannan tuni kallonmu kawai suke. Sai wannan salo suke wa juna, sannan ga Takwara ciwon barin gida shiru, ina ga dama ciwon nan na mai sunan Malam ne." Umma ta saki dariya tare da cewa "Allah yasa haka ne. Ummi kam cikin daki ta kule zuciyarta zallah dadi. Misalin karfe biyu Umma ta dan kishingide baya, ta idar da sallah, tsuwar wayar da da Abba ya ba Ummi ajiya ce ta farkar da ita. Ta ce, Ummi me ke tsuwa a dakin nan? Wannan dai ba wayata ba ce. Ummi da ke tsakar gida ana mata zanan fulawa ta ce, Lah, Umma Ya Abba ne ya bani ajiya. Kila ma shi ne ya kirata, ta dubi wadda ta yi mata zanen fulawar ta ce Sabira don Allah shiga ki dauko min a kan gado. 2missed call ta gani, ta ce kash! Sai gashi ya sake kira, kafin ta daga sai da ta leka dakin tsohuwa ta hango ta kwance a gadonta. Dama a kofar dakin Tsohuwar take ta biyo inuwa ta daga wayar tare da sallama, ya amsa cikin dokin jin muryarta. Ina ki ka shiga ne? Ta amsa a can cikin makoshinta, ana min fulawa a tsakar gida wayar kuma tana daki. Ya ce, Ok ana miki zanen fulawar ne? Ta ce an ma ganin har ya fara bushewa ya saki murmushi tamkar yana gabanta. Ana yi miki me kyau? Ta ce, Eh yayi kyau sosai, ya ce Good, zan dawo kamar karfe uku saboda zan kwashe kaya za a yi fenti a daki, so kin ga ba zan samu kai ki gurin gyaran gashin da wuri ba. 65... Don haka sai mu bar shi zuwa dare ko? Ta ce, "To Ya Abba, ehm za a dafa maka wani abu ne? Dadi ya lullu6e shi amma saboda burinshi na kimanta Bishira a idonta sai ya a'ah. Na hutar da ke zan ci na Antynki Bishira, maganar ta soki ran Ummi har ta kasa magana, ya fahimci hakan don haka sai ya kawo zancen da cewa sai nazo. Ta tura baki tare da cewa uhm, tana kashe wayar ta shiga kunkunan cewa in yaso kaci abinci gidansu bana ta ba. Tsohuwa da ke sauraronta ta sheka dariya tare da cewa, ba dai ke kin ce me sunan Malam ba? Sai ma kin je gidanshi yarinya ban miki baki ba amma za ki raina kanki. Ummi ta cafke cikin jin haushi ta ce, wai to Tsohuwa da za ki ce na ce Ya Abba cewa nayi ina sonshi? Kuma da su Alhaji suka jona ni da shi da naki har da ke za a dinga cewa ban yi biyayya ba. Tsohuwa ta ce, Raba ni da gulmarki, kina sonshi ai ni ba yarinyar goye ba ce, kina waya kina kashe murya, san nan ciwoce- ciwancanki duk sun lafa. Sai wannnan rawar kai ki ke, to ki sani me sunan Malam dai ya aure ki ne don dole, matar cushe kuwa ba daraja take ba. Ummi ta ce, "To nima dai ai ba sonshi ni ke ba, ni dai tsohuwa don Allah ki daina samin ido. Ta mike, Na ma bar miki kofarki. Ta nufi kofar dakin Alhaji tana kunkunai. 36. 66... Sai dai duk da haka kalaman tsohuwa sun tsaya a ranta, matar cushe bata daraja, Ya Abba kan dole ya aureta, lallai zancen tsohuwa abin dubawa ne. Abba ya shigo gidan uku da doriya, tare yake da yara guda biyu, dayan zai mishi dan face-face, dayan kuma zai masa fenti. Sune suka taya shi kwasar kaya, bai samu Bishira a gidan ba, kila tana gidan Ummanshi, ko makota. Sun kama aikinsu shi kuma ya shiga kicin don ya dan dafa abinda zai ci. Bishira gidan Anty ta tafi kuka take wiwi wai ita fa ba za ta iya zaman gidan nan ba, ta ce "Aunty Farida tunda kuna shiri da Baban Walid ki ce masaya sawake min". Anty Farida ta tsura ma kanwarta ido, tausayin Bishiran ya cikata. Tabbas kishiya bata da dadi koda mahaukaciya ce bare mai hankali. Sai dai ita bata da ikon da zata hana ayi kishiyar koda kuwa mijinta ne ke son yi, don sunna ce ta mai tsira da Aminci. Bishira ta katse mata tunani da cewa, dubi fa Anty hatta Dady yanzu yafi son Baban Walid fiye da ni. A gabana ya dauki kudi yaba baban Walid, a halinni kara na kai a kar6ar min 'yancina, kuma Momy zata yi magana ya hanata cikin tozartawa. Hakan da Daddy yayi ba zubar min da kima yayi ba, har da ita Momy? Yaushe Baban Walid zai sake ganin darajarta? Anty Farida ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Bishira Dady bai zubar miki da mutunci ba, illa kara tarairayo miki mutunci da yayi daga ke har Momy. Kuma ni ba zan ce mijinki ya sake ki ba, haka nan ba zan ga laifinshi ba, domin aure sunna ce ta Manzon Allah (S.A.W), sam ba zan yi fushi da wanda ya raya Sunna ba, koda mijina ne. Kiyi hakuri kanwata koda bani da kishiya nasan akwai zafi, amma kema kina da laifi, dube ki fa. Yanzu Bishira wa zai gan ki ya amince ke kanwata ce ta hudu? Zato za a yi ke yayata ce, kin saki kin yi ragwaf, nonuwa har ciki haihuwa biyu jal, dubi yanda tsabar datti yasa fuskarki da dokin wuyanki zuwa bayanki duk kyasbi ya miki riga. Da kin zauna kusa da mutum wari ki ke tashi, hakora sun miki yalo, kai mijinki fa ya yi kokarin ba kowane zai dauki hakan ba. Duk ba ki kalli laifinki ba sai don ya kara aure yanzun? Ina ce kwanaki garin shegen gantalinki ne ki ka bar danki a gida ya fada rijiya ya mutu? To hatta Abban Nasir ce min ya yi da shi ne ba zai yarda ba, saboda haka ki dawo hankalinki ki zubar da kazantar nan ki kama Ibadarki. Bishira ba kya jin kunya a ce ba kya sallah? Kuma a tare da haka kina da wannan kazantar ki ke kaurace ma shimfidar mijinki. Kwanan baya ya kira ni a waya ya sanar da nicewa kin ce min ina wari, don haka ni kuma na ceya tafi gurin mai tsafta mai kamshi. Shima fa Anty magana yake dankara min don ba kisan halinshi ba ne. Anty ta ce, "Bishira kina cikin hadari, ga kin sallah sannan ga kauracewa miji ki kwana Mala'iku suna tsine miki. To daidaita sahunki, ga mijinki dan kwallisan dan Jarida mai farin jini, ki kalli yanda in yana gabatar da shirinsa yanda 'yammata kan kira su ce suna son lambarsa. Amma ke kina sakaci da shi, ki dubi yanda wata mata ta kawo masa hari kwanaki da a ce ya yarda ke ba za ki san kina da kishiyar waje ba. Ki shiga taitayinki zan dai miki taimako daya in kinamince za ki natsu. 67.... Bishira ta ce, Anty taimakon me? Ta ce, "Zan samu Momy su taimaka su canza miki kayan daki, sannan Dady ya ba mu kujerar Makka ni da ke da Aisha. To sai ya ce tunda ke kin ki kwantar da hankalinki ki kwantar da na mijinki to ya fasa naki, mu harmun yi passport. Bishira ta zaro ido, da gaske Anty? Anty ta ce, Allah da gaske. To yanzun shi ne ni ke son in ce muje mu ba shi hakuri kila ya amince. Bishira ta ce, Tashi muje Anty don Allah, Anty ta ce kin tambayo zuwa can ne? Bishira ta ta6a baki, nifa ko nan din ban wani tambaya ba, wallahi gidan ne bakikkirin nake ganinshi. Anty ta ce, "Ki dinga addu'a, kishi yayi miki yawa. Sannan ki daina fita ba tare da izinin mijinki ba, duk in da ki ka je har ki dawo Mala'iku suna tsine miki. Don haka yanzun tashi ki tafi gidanki, ni zan samu Hajiya da Dady yau din nan kuma in sha Allah za amiki gyaran dakin, sannan tafiyar za ta kasance tare da ke. Bishira ta ce, Na gode Anty, amma don Allah ki barni na dan huta a nan gidan duhunsa nake gani, don ba ki ji yanda ni ke ji ba ne Anty ko da dana Walid ya rasu ban ji kunci irin wannan ba. Ta sake rushewa da sabon kuka wiwi, Anty kallonta kawai take ta ma rasa me zata ce. Wayarta ta ciro daga chaji ta shiga kiran layin Abba, lokacin ya kira kananan kannanshi su Kamal suna ta fito da kayan dakin Bishira saboda ayi fenti har an gama nashi dakin. Wayarshi da ya ajiye a kan windown dakinshi ta shiga ruri, ya duba, Anty ce. Ya daga tare da sallama, ta amsa ya gaida ta cikin girmamawa da mutuntuwa, ta amsa da fara'a sannan ta ce, "Abba ga Bishira nan tazo tana kuka, kuma ta ce min ba ka san ta fito ba". Ya ce, "Eh haka ne, ta ce don Allah in baka wani abu ina son ganinka. Ya ce To zan zo Anty, amma yanzu ina aiki ne kayan dakin ta muke fita da shi za a yi mata fenti ne, ta ce To ko da dare ne haka, ya ce to zan zo. * 68.... Ummi tana ta zuba ido ganin Abba amma shiru har a ka yi Magriba tayi wanka tayi sallah. Tana zaune har Isha'i tayi daga Masallaci shima ya nufo gidan su Ummi, lokacin Ummi tana bakin gado tana 'yan shafe- shafenta.Ta juyo Abba suna gaisawa da su Umma, ta shirya cikin leshi mai ruwan lemun tsami, da dan mayafinta fari haka takalminta. Ta fito tana zaune kan kujera, ta ce "Sannu da zuwa. Za ka ci abinci?" ya ce, "Da sauri haka ba muko gaisa ba?" Ta zauna ina yini? Ya ce, lafiya lau. To na kawo abinci? Ya ce, daga gida fa nake, ina da kuma mata. Ummi ta ta6a baki, oh, haka ne ashe kana da mata, gani nayi da matar taka ka ke zuwa cin abincin daga nan ta lafe a kujera tare da hada rai. Ya mike muje ko? itama ta mike, ya kalle ta da wannan mayafin za ki? Ta ce, eh, ya ce a'a dauko hijabi ba zan lamunci yafa wannan dan mayafin ba. Ta kalle shi kamar ta ce ai matarka tana yafa irin shi sai kuma tayi shiru ta nufi uwar daki don dauko hijabi. Shi kuma ya nufi waje, ta yi wa su Umma sallama sannan ta fito. Yana tsaye jikin mota ya ce, ina wayar nan? Ta ce, "Gata nan a hannuna ya yi dan murmushi yace mayyar waya dama nasan sai kin dauko har yanzun cikin haushin maganar shi ta dazun take yi. Don haka bata kula shi ba, ya shiga motar ya bude mata gefen kusa da direba ta zauna cikin fushi. Lura ya yi da hakan, don haka sai ya ce ba ni tamata ta ce so nake in loda mata kudi. Ya guntse baki don kada yayi dariya, ganin yanda tamiko mishi wayar cikin hanzari gata Allah yasa bacewa nayi a bani ba. Ta juyar da kai tana kallon titi, shima bai sake cewa kala ba har suka shiga cikin gari. Ya dube ta, wane shagon zamu? Ta ce, duk wanda kaje, ni sanin wani saloon nayi? Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar Maiduguri.Shamsy belloRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 9 ZURFIN CIKI book 3 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:40 nayi? Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar Maiduguri. 69.... Abba ya ce mata ga Amaryata a gyara mata kai duk da ba wai gashi ne da ita ba ya yi kyau sosai ko nawa ne zan biya. Mai shagon tayi 'yar dariya, zan mata yanda ka keso ya dubi Ummi wadda ta samu kujera ta zauna fuska daure. Ya ce, "Kanwata zan tafi nayi aski nima, daga nan sai na dauki matata daga unguwa na kaita gida, sannan ta san in har ta bude baki to kuka ne zai kwace mata, don haka sai ta yi shiru. Ya fita yana 'yar dariya, mai shagon Yagana saloon ta ce, "Kai kanwata kun dace fa, kuma da alamayana sonki sosai.Ta kalli mai shagon hawayen da take makalewasuka zubo, ta ce "Anty ina so a nan, dubi fa abinda yake min.Komai sai ya ce min matarsa, matarsa, ko inaruwana da matarsa? Yagana ta ce, "Yana da matane? Sam bai yi kama da mai mata ba.Ummi ta ta6a baki ta ce, "Yana da mata da yakeso ni bana sonshi, baya sona, iyayenmu ne sukahada mu.Yagana ta ce, in ma ke ba kya sonshi shi kam yanadauke da tsantsar sonki a idanunshi n fuskancihakan. Ummi ta ce, "Anya kuwa? Bana zaton yanasona ne, in kin ce yabi iyayenmu ne zan fi yardadon shi din mai biyayya ne.Yagana ta tura mata kujera, zauna in soma miki,sai da ta fara gyara mata kai sannan ta ce, "In mamijinki ba ya sonki to kuwa ba za a yi wuyarshawo kai ba.Ummi tayi murmushi tare da kallon fuskarta tamadubin da suke fuskanta, ki ke gani Anty? Ta cesosai kuwa, ki tarairaye shi da kyau, kin san shinamiji dai dan shauki ne da son nishadi. (((KWARAI KUWWA!!!)))Ga kuma son tarairaya kamar jaririn yaro, ummi tace, "To zan yi hakan in har yin hakan zai sa ya soni.Yagana ta ce, "Zai so ki, zan so kiyi gyaran jiki dafata, Umi ta ce, kamar ya ya? Yagana ta ce, kayanmata zuwa gyaran fata, wanda za ki sha don 'karinni'ima. Ummi tayi shiru, don bata son irin wannanzantukan.Ta ce, "Kin yi shiru, Ummi ta ce Ummana ta ce bata son in sha komai, tunda ni budurwa ce, in je wamijina da ainihin halittata.In yaso daga baya sanin saboda 'yan garinmu sunzo da shi daga Zamfara. Yagana ta ce, Hakan mayana da kyau, domin Amare da yawa suna shanwahala sosai kasancewar ba su saba ba.Sannan mazajen ba su bambance ainihin yandamatan suke. Ummi cikin gundira ta ce, Gara ma nagyara fatar.Yagana ta ce, "Wancan ma za ki neme shi, ko nangaba Ummi ta ta6a baki, ni dai fada min na gayarnfatar.Ta ce, "Ina sai dawa in kina so zan baki kije gida kihada kiyi zan hada ma angon lissafi da shi Ummita ce, ba ni sai da suka gama a ka gyara matagashi fes, sannan ta dauko kayan ta shiga lissafamata kamar haka:-1. Man Zaitun2. Lalle3. Kurkur4. Madara ta ruwaZa ki hada su guri daya ki kwa6a, sannan ki shafejikinki da su kafin shiga wanka, in ya bushe idan zaki shiga wankan sai ki murje shi tas, dukwadannan 'yan kurajen na fuskarki za su mutu,jikinki ya yi laushi da sheki.Ga kuma wani.1. Sabulun Ghana2. Dettol3. Zogale4. Farar AlbasaZa ki hada Sabulun Ghanada da Dettol da garinzogale, da farar albasa, ki hada su ki kir6a kimurmule shima a jikin za ki ringa shafawa.Da fuska kafin ki shiga wanka, zan bar ki da biyunin sun amshe ki ma sun ishe ki. Yanzun ko inwanke miki kafa? 39. 70.... Ummita ce, "Ina tsoron kada yazo kuma kudin shi ba su kai ba, Yagana tayi 'yar dariya, kina tausayinsa ne? Ki daina tausayin mijinki shi ne zai amfana da gyaran da duk za ki yi. Ummi ta ce, "To wanke mini".Ta hada kayan wankin kafa ta ce yarana ke yi amma zan miki da kaina. Sai kuma taga zanen fulawa. Ta ce, "Au, an riga an yi zanen fulawa ma ba dama ayi, Ummi ta ce, Ohi ni na manta ma, to ki fada min yanda zan dinga gyara kafar, ta ce To bari in ba ki mai sauki ma. 1. Man kwaka 2. Man shanu 3. Man Zaitun Ki samu man kwakwa da man shanu da man zaitun ki hada man kwakwa da man shanu guri daya, ki shafa da dare da safe. Ki dan gasa kafar sannan ki wanke ki shafa man zaitun, za ki ga yanda kafafunki za su yi tamkar ta jariri. Ko ki yi na ruwan ko kumba, lalle ki hada su guri daya ki shafa a kafafunki da dare. Da safe ki wanke ki shafa man ridi, wadan nan kurum in kin rike su za ki ba wani labari, Ummi tace zan kiyaye in sha Allah. Shi kuma Abba yana fitowa daga shagon aski kai tsaye gidan Anty ya nufa, ya samu Bishira Anty ta matsa mata tayi wanka ta bata kaya ta saka. Ta kira mai kitso tazo tayi mata ta sata ta shafa turaruka. Tunda Abba ya shigo yake kallon Bishira, sun gaisa da Anty, sannan ta ce dama dai na ce kazo ne don Bishira ta baka hakuri. Sannan in maka tuni da yin adalci a tsakanin matanka, kuma na yi wa Bishira fada sosai. Ta dubi Bishira, ki ba shi hakuri, Bishira ta hada rai tare da turo baki, ta kalle shi cike da tsananin jin haushin shi. Kayi hakuri ya ce ba komai dama ni ban yi fushi dake ba, a zuciyarta ta ce, ba ka isa in baka hakuriba, albarkacin ina son zuwa Makka ne da kuma canjin kayan dakin. Ya yi wa Anty godiya ta ce ma Bishira gobe da wuri kiyi parking din duk kayan ki a waje da mun zo sai mu shirya miki. Bishira ta ce, Allah dai yasa su yarda, Anty ta ce,"Za mu su yarda in Allah ya yarda. Ta dauko wasu kayan sawa da sabbin kuloli ta ce ma Bishiran je kisa a motarku. Abba ya ce, "Kawo in kai, Anty na gode sai anjima, ta ce To Abba ayi ta hakuri". Ya ce, Ba komai, Insha Allahu. Suka biyo shi a baya tana kara jawa Bishira kunne kan cewa in har ta kuskura ta ji wata magana ta 6ullo ta rashin mutunci sai ta fasa tsaya mata a kan maganar aikin Hajji ko Dady ya amince sai tasa ya janye. 71.... Sun shigo mata Muhibba tana baya tana 'yanwutsil-wutsil dinta tamkar kurame, haka suke tafiyar. Ta zaci su nufi gida sai taga sun nufi cikin gari. Bata tambaye shi ina za su ba, har suka isa inda yayi parking ya dubeta, Madam ina zuwa, hum kawai ta ce. Ya bude baya ya dauko Muhibba ya sa6a a kafada ya nufi shagon saloon din. Daidai lokacin sun kammala komai, Ummi ta zari hijabinta da niyyar rufe kanta, Yagana ta ce a'a kanwata bari ya gani don ya biya ni 'yan kudina. Abba bai zaci Ummi tana da gashi ba, domin dai acikin Hausawa 'yan Arewa za a iya saka Ummi acikin ma su gashi. Yayi laya-laya a dokin wuyanta baki sidik. Yayi murmushi, lallai kin gyara da kyau. Nawa ne kudinki? Ta fada ya ciro ya bata, sannan Ummi tazari hijabinta. Mamaki take, Gida ya koma ya dauko Muhibba? Yamiko mata ita, Ga 'yarki. Ta amsheta. Yagana tace, yarinyar tana kama da ku. Abba ya ce, "Ai 'yarmu ce, suka yi mata sallama suka fito. Ummi da Bishira a tare gabansu ya fadi lokacin da suka ga juna. Bishira ta kauda kai yayin da Ummi taja baya daga mazaunin kusa da direban da ta nufa, ya bude mata baya ta zauna tana rike da yarinyar. Ya tada motar suka dauki hanyar tafiya kowanne zuciyarshi da abinda take karantowa. Ummi tunaninta Abba ya je ya zo da matarshi ne don yanuna mata shi fa matarshi yake so. Ita ko Bishira nata ganin wulakanci ne na karshe da ya dauko ta yazo da ita gurin wannan karamar yarinyar. Shi ko Abba addu'a ce a zuciyarshi Allah ya hada masa kan matansa, sai kuma ya soma tunanin ina zai soma zuwa? Nashi ganin in ya kai Bishira gida ya sauke ya tafi kai Ummi bai mata adalci ba. Amma ya kula Ummi tana fushi kuma yaso ya lallasheta, yana cikin wannan tunanin ya tuna dawayar nan. Ya kalli wayar a gefanshi. Dan murmushi yayi da ya tuna lokacin da ta dangwarar masa da wayar don ya ce ta matarsa ce. Yanayin yanda Ummin ke nuna kishinta yana birge shi, koda bata sonshi tana kishinshi sannan bata masa raini ko rashin kunya. Kofar wani gidan saida gasassun kaji da ire-iren kayan kwalam ya tsaya. Ya kalli Bishira Madam mu shiga ko? Ta ce, "A'a ni fa ba zan fita ba, ya ce To bari in dawo, ya nufi ciki. 72.. Ta waiwayo ta dubi Ummi, ta ce "Ba ni 'yata fitsararriya. Ummi ta mika mata tare da cewa nima ai ba cewa nayi a bani ba, ta ce "Kar dai ki min rashin kunyaki bar ganin an jona ki da mijina ki zata za ki hada sahu da ni. Ummi ta ce, "Sai dai kada a kuma in dai batun hada sahu ne, kuma ban damu don mijinki ba bai sona ba, tunda ni ina sonshi. Bishira cikin daga murya ta ce, oho? Dama sonshiki ke yi? Yanzun na gane da nufi aka yi. To ki sani kin sai ma kanki masifa da bala'i. Ummita ce, "Kin ga bala'inki can, daga nan batakara magana ba ta bar Bishira na ta masifa. Tundaki ka za6i ki auri mijina zan shayar da ke ruwan dana sani. Sai kin gwammace zama a kurkuku fiye da gidan mijina, daidai lokacin Abba ya dawo da ledoji guda biyu. Bishira bata yi shiru ba sai zagin Ummi take yi,"'Yar iska, 'yar daba... tsawa Abba ya daka ma Bishira, tare da cewa ba ki ji kunya ba da ki ke zaginta amma bata kula ki ba? "Ta ce, "To ka ji abin da ta ce min ne? Tsaki yaja tare da daukar wayar da ta aje yasa a ledar Ummi, sannan ya tada motar. Kofar gidan su Umma ya tsaya, Ummi wadda dama ta kosa tazo gida, ta bude motar ta fada gida cike da takaici. Ya kashe motar sannan ya dauki ledarta ya kalli Bishira, Ina zuwa. Kala bata ce ba. Illa baki da ta cije, kirjinta na yin wata irin suya. Ban da tana tsoron Anty kada ta fasa zuwa gurin Dadynsu da tuni ta shago Ummi ta nadi 'yan kayanta. Dakin Umma ta shige, Ummar tana shirin fitowa Ummi na shiga, ta ce kun dawo? Ummin ta hadiye 6acin ranta."Eh, mun dawo Abba a ya shiga gaida Umma sannan ya mika ma Ummi ledar, gashi kin manta Ummi ta amsa tare da cewa, an gode. Umma ta ce, "Me ku ka siyo in ce dai ka sai ma Bishira? Ya ce, "Eh na sai mata, kaza ce fa Umma ba wani abu ba". Ta ce, "To shi ke nan maza ka koma gurin su, yace "To. Tana fita ya kalli Ummi akwai waya a cikin zan kira ki, kuma bana bukatar ki kashe min waya. Ummi ta ciro wayar da sauri, ta dibe shi ba wayar matarka ba ce? Ya ce, "Eh tata ce, ta mika mishi cike da kunan rai, ga abinku ka kira ni da layin Umma. Ya ce, "Ke ce za ki cigaba da rike ma mata tawayarta, ba tare da ya jira jin me za ta ce ba yana murmushi, Ummi ta kasa gane cewa ita ce matarta shi. Ko kallon kazar bata yi ba illa dai tayi duk wasu abubuwan da ta saba yi kafin ta kwanta, sannan ta kunna wayar tana tsammanin kira. 73..... Shi ko Abba koda yazo Bishira tana ta mitar don tsohon wulakanci an zo da ita an shanya ta, bai ce mata kala ba illa dai motar da ya tada suka nufi gida. Gidan duk kaya saboda bai maida ba da a ka gama fentin, ya dauki tsintsiya ya share dakin, sannan ya shimfida katifa ya fito inda take zaune bakin Rijiya. Muhibba tayi bacci tana rungume a jikinta, ya ce kawo ta, ta mike a fusace ta nufi dakin ba tare data bashi 'yar ba. Ya bi bayanta, so kurum yake ya lallasheta ba wai don tsoronta ba sai don tausayinta, yasan mata kan kishi za su iya yin 'yar karamar hauka. Wasu ma sai sun yi babbar kuma bai dace ana nuna kishinsa ba, shi kuma yana nuna ko 'in kula a gare ta, gefen katifar ya zauna ya lalubo hannunta ya rike cikin nashi."Bishira!" ya ambaci sunanta cikin sanyin murya, bata amsa ba kuma bata dube shi ba, ya ci gabada cewa, "Bishira ban ga abin damuwa ba. Ko damata uku a ka daura min aure da su bare daya, inkin yi la'akari da irin son da nake miki ke kin san Bishira ba kiyayya ta hada mu ba. Kina manta wannan ne? Ta dago ta dube shi ta dan soma saukowa, yayi murmushi har yau ban daina sonki ba, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta turo baki sai kace 'yar yarinya. To ai na sha jin a ana cewa so daya ne tak, ya cehaka ne, ta ce "To tsakanin ni da Ummi wa ke keyi wa? Da sauri ya ce ke, ta ce Allah?Ya sake tausasa murya, haba Bishira ya ki ke wannan zancen kema kin sani, kuma don Allah na roki ki in muna tare ki daina min zancen Ummi, ke kadai ce za6i na. Bishira taji dadin wannan kalamai, don haka sukaci namansu suka kwanta, ya bukace ta a nan masai da ta ce kaje gurin Ummin mana. Ya ce, "Na ce in muna tare bana son kina min zancenta. Sai dai in kina son ci gaba da horon daki ke min ne. Haba Bishira, ko tausayina bakya yi?An fi wata uku kina haramta min halas dina. Kullum sai dai ina azumi sai ka ce gwauro? Yajawota jikinshi, ya rungume da kyar dai ya samu yadan rage matsala, sai dai ita ma ya lura tayi missing dinsa. Suna kwance har kusan sha daya saura tuni ita tayi bacci, shi kam daman so yake tayi bacci yakira Ummi. Ya mike yaje yayo wanka sannan ya nufi dakinshi. Yaja katifarshi ya kai dakin, sannan ya kwanta akai, ya kira Ummi lokacin bacci ya soma figarta. Ringing din ne ya farkar da ita, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga, kafin ta amsa sallamarshi sai da tayi wata doguwar hamma.Ya ce, "Ke baccin ki ma ki ke alhalin na ce zan kira ko? Ta ce, "Amma ka san bacci ba ya jira in ya zo,ni kuma ba zan iya yiwa bacci gardama ba". Ya ceto sarkin iya zance, yayi nufin zolayar ta. Yanzun dai na soma tunanin kin soma sona, gabanta ya fafi, sam bata son ya gano hakan yanzu. Tafi son sai lokacin da shima ya soma sonta. Ya katse mata tunani, hasashe na haka ne? Ta ce, ko kusa, mene hujjarka da fadin haka? Ya gyara kwanciya. Na farko naga ana ta kishina, sannan tun da a kadaura aure da ni sai ciwo ya kame kansa, kuma nalura kina ta zumdin tarewa a gidana.Ya saki 'yar dariya, yasan ya cika mata ciki da takaici, shiru tayi nazari take wacce amsa zata bashi, ko dai wayar zata kashe? Tamkar ya shiga zuciyarta, sai ya ce.... 41 Tamkar ya shiga zuciyarta sai ya ce, "Koda wasakada a kashe waya. Ranta ya sake 6aci, ta ce Ya Abba ka tafka kuskure da kayi zaton ina sonka,sam ni bana wani kishinka. In don ka ce wayar matarka ce na ce ka rike abinka, sanin kanka ne ba ma shiri da matarka, kuma duk abinda ka ce nata ne dole na guje shidon ba zan dauki wulakanci ba. Batun ciwo kuma daka ce tunda aka daura mana aure ka neme shi ka rasa dama bani na dora makaina ba, kaima ina naka hawan jinin ya tafi? Sannann kuma wane zumudi na nuna na tarewa a gidanka, Ya Abba ka sani yanda a ka tilasta maka aurena, to ni ma fa dole tasa na hakura. Amma ka rike a ranka bana wani sonka bani kamarina ina sonka, kalaman nata na karshe sun burgeshi har sun sa shi yin da ya sanin tsokale zancen. Sai kuma ya canza salo da cewa, haka dai ki ka ce amma ina da ja mu dai bar zancen, shin dazun kafin ki soma wannan tunanin me ki ke yi? Ta danyi shiru tana tambayar kanta. Dama mutumin nan haka ya ke? Oh yanzun dabara zai min sai ya gano ko ina sonshi dole, to kuwa bazai ji ba, ya katse ta da cewa ban san ki da karya ba. Ta ce, ina tunanin irin ukubar da zan sha a gidanka ne ta wulakancin da zaka min, ya yi shiru zuciyarshi tana cewa yarinyar nan ba ta san irinson da ka ke mata ba ai ta ma dauke ka mugu kenan. A fili sai ya ce, "Kuma fa kin yi tunani, Allah yabaki ikon daukar ukubar da zaki sha tare kuma dajure wulakancin da na tanadar miki goben Ummi. "Ya fadi, wai dama da gaske wulakancin zai mata. Gyara kwanciya kawai tayi bata kara cewa komai ba, kuma bata da nufin cewa wani abu, yasa taji haushi sosai, don haka sai ya tausasa muryarshi. "Ummi kina ji na?" Uhm" Kurum ta ce, don ya gane tana jin shi. Alkawari ta dauka ba zata sake cewakala ba, tunda ya hanata kashe wayar. "Ba ni da nufin miki..." Sai layin ya yanke daga gefanshi, ta ce, "Gara ma haka". Tana kokarin kashe wayar gaba daya kiranshi ya sake shigowa. Tsaki taja kafin ta daga, kuma a ciki ta amsa sallamarshi, sannan cikin murya mai kamar zata rushe da kuka ta ce "Ya Abba ni fa bacci nake son in yi". Ya ce, "Sam ba wani bacci da za ki iya yoa sai tunani". Ta ce "To na ji, ina son yin tunanin please".Ya ce, "Tunanin me za ki yi". Cikin gundira ta ce,"Dole in yi tunanin yanda zan kare kaina daga wulakancinka, don bana tsammanin zan dauka" .Ya ce, "Wasa nake miki fa." Ta ce, "Uhum, ban amince da cewa wasa ka ke min ba, don na tabbata mu ba abokan wasa ba ne".Ya ce, "To shi ke nan bari in bar ki kiyi tunanin, amma tunanin yanda za ki faranta min za ki yi". Muryar Bishira ce ta katse shi. "Oho! Ai tun da na farka ban ganka ba na san ana nan ana cin amanata". Ya kashe wayar da sauri, duk da dai Ummi ta riga ta jiyo muryar Bishiran. Sai dai bata fahimci me Bishirar take cewa ba, ringingine tayi tare da dora filo a kirjinta, tunani take yi wane irin zama za su yi? Koda bata da amsa ta kudurce har abada ba za ta dauki wulakanci ba, a shi ko a matar shi. Sai dai alkawari ta dauka ba za ta musu raini ba, matsawar ba su suka 6ullo da hakan ba. * ************************************** Shi ko Abba rigima suka dinga yi da Bishira cikin tsohon daren wai ya cuce ta ya kwanta da ita yazo yana hira da wata banza. Kila ma ya saba kwanciya da Ummin ne yau bai samu dama ba, Abba ya ce kin so kanki in ki ka yimin wannan zaton, don ban ta6a nemanki ba, kafinki shigo gidana, ko na ta6a?"Ta ce, "Don ka san dai ni ba fuska". Da ya gaji da iya korata ya rufe kofar ya koma can dakin. 40. 74... Washegarin ranar, ga mamakin Ummi tun misalin karfe goma jama'asuka cika gidansu, a ka dora abinci. Can kuma saiga yaran shagon Abba da dinkunan zannuwan daAlhaji Babba ya sai mata.Ranar Abba bai shigo gidan ba a waya ya kiraUmma suka yi magana, zuwa karfe uku angama yiwa Ummi jeren dakin da yake yana da girma yacinye komai tsaf.Fitar 'yan jere babu jimawa sai ga Anty Farida dakannasu motar tana da kaya tana biye da su, gadoda kujeru a ka canzo mata.Suka jera mata sannan suka lodawa motar na dasuka dauki hanya suka koma, Abba kam yana gurinaiki amma zuciyarshi tana gida.Fatanshi Allah yasa yana zuwa ya tarar an kaimishi Umminshi, kawayen Bishira da makotansu'yan jam'iyyarta duk sun shigo gidan sun hadu saizugata suke yi tare da nuna mata koda wasa kadata sakar ma Ummi fuska, kuma in ta mata takamata ta duki 'yan kayanta.Suna gidan a ka kawo Ummi, 'yan kawo Amaeyakam suna jiyo habaici da zagin da su Bishira ke yi,don haka suka ce kada a kai musu yarinyar.Inna Saratu da Inna Harira suka ce ai kuwa sai ankaita.Ba ko kunya Bishira ta zabga musu harara lokacinda suka fada mata cewa ga kanwarta sun kawomata, don Allah su zauna lafiya tare da Aminci.In yarinyar tayi ba daidai ba ta sata a hanya... takatse su cikin tsawa da mikewa tsaye. "Don Allahku fice min daga daki amanar kishiya? Har wai muzauna da aminci ku ke cewa?Tayi 'yar dariyar yake "Kun yi kuskure, ai batacanza daga sunan ta na kishiya ba, kuma kowa yasan kishiya abokiyar gaba ce."Inna Saratu ta ce, "Baiwar Allah jahilan mata sunesuke yin irin wannan tunanin, amma ga masu ilimisuna koyi da gidan mai tsira da Aminci (S.A.W)ne".Bishira ta ce, "To kawai dai ki ce min jahila ki huta,bari ku ji ba za n ba ku a 6oye ba, zama ne za muyi shi na rashin mutunci, na kowa ya iya allonshi. Don ina kishin mijina, kuma zan nuna". Tirkashi! Lallai akwai daru kenan. To masu karatu ku biyo ni cikin littafi na 4, kumana karshe domin jin yadda za ta kasance atsakanin Bishira da Ummi da kuma Oga kwata-kwata wato