𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢t + 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. Asma'u Muhammad Auwal (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) ASMEETAH 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZa ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ ᵏᵒ ʷᵃˢᵘ ˡⁱᵗᵃᵗᵗᵃᶠᵃⁱ, ⁱʸᵃ ˡⁱᵗᵗᵃᶠⁱⁿ ᵐʸ ᵉⁿᵉᵐʸ ᵏᵃʷᵃⁱ ᶻᵃ'ᵃⁿᵃ ᵗᵘʳᵃʷᵃ... 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗻⃪𝗲⃪ (1) ꧁꧂ *(C.D.S)* Chief of Defence staff Chief Suraj Mahendra Marka shugaban sojoji na ƙasar U.S wanda a baya ya zauna anan ƙasar Nigeria dake garin Babban Birnin F.C.T Abuja, yana da mata ɗaya wato Agent Madam Parveen jami'ar C.I.D da ƴaƴansu uku! Babban Ɗansa shine Marshal. Mohandas Suraj Mahendra, Sai kuma Ɗansa na biyu shine Commander. Rakesh Suraj Mahendra, Sai kuma Autarsa Amreesha Suraj Mahendra, C.D.S Suraj ya rasa Ɗiyarsa Amreesha tin tana ƴar shekara biyu a duniya ta hanyar hatsarin mota da sukayi ita da mahaifiyarta Madam Parveen a hanyarsu ta dawowa daga garin Kaduna zuwa Abuja, wacce Madam Parveen ita take driving ɗinsu Anan suka samu babban hatsari anyi nasarar ceton rayuwar Madam Parveen amma saidai ita Amreesha yarinya ƴar shekara biyu ba'a sameta a cikin motar ba, an dudduba ko ina a wajen da sukayi hatsarin amma an gaza samun koda ƙyallenta ne balle gawarta, iyayenta sun shiga damuwa mai tsanani na rashin ɗiyarsu Amreesha, yanzu shekara goma sha takwas da faruwar wannan Al'amarin, shin Amreesha tana raye ne ko dai ta mutu? ALLAHU a'alamu.... Sai dai wannan family christal ne, gaba ɗayansu jami'ai ne hakan yasa suke da wani tambari na zanen catoon ɗin bindiga a gadon bayansu daga iyayen har ƴaƴan, kuma itama wacce aka rasa wato Amreesha tanada wannan tambarin, babban burin C.D.S Suraj shine idan Amreesha ta girma zata zamo jami'a ta musamman acikin sojoji amma kash lokaci guda ya rasata... Amreesha wasu masu farauta ne suka tsince ta acikin jeji a yashe, saida tayi wajen shekara guda a hannunsu tukun suka yanke shawarar kaita gidan marayu ko za'a samu iyayenta tinda su har yanzu sun kasa samun iyayenta, a wannan lokacin kuwa iyayen Amreesha har sun bar Nigeria sun koma ƙasar U.S gaba ɗayansu domin sun saddaƙar da cewa ɗiyarsu Amreesha ta mutu.... ꧁꧂ Chief of Army's staff Chief Muhammadu Zaiduddeen Bature. yana zaune a nan ƙasar Nigeria dake garin Abuja G.R.A. su uku iyayensu suka haifa daga shi sai ɗan uwansa Sarki Abubakar Zaiduddeen Bature, mai martaba sarkin ƙasar Jidda, sai ta ukun su Aunty Yolash tana aiki a ministry of education dake garin Bauchi.. Chief Muhammad Bature Matarsa ta farko itace Hajia Fateema wacce ALLAH yayi mata rasuwa tin shekarun baya sakamakon haihuwar ƴan biyunta wato the twins, MAJOR GENERAL RAZHDEEN (M.G.R) da kuma SURGEON DOCTOR ROSHAN (S.D.R).. daga baya Chief Muhammad Bature ya Auri Matarsa ta biyu Hajia Kilishi wacce yanzu take zaune dashi da yaranta Biyar duk Mata, ta farko itace Meenat sai ta biyu kuma Pinky sai Ruky da Ummy sai Autar ɗakinsu wato Tiny itace ƙaramar cikin su, Hajia Kilishi taso ta samu ɗa namiji amma ALLAH bai bata ba, tin akan ƴarta Tiny aka cire mata mahaifa sakamakon matsala da mahaifanta ya samu, tayi kukan rashin samun yaro namiji sannan tana baƙin cikin yanda Chief Muhammad yake nuna so da ƙauna wa ƴan biyunsa duk da ba'a waje ɗaya suke ba, M.G Razhdeen yana zaune a ƙasar U.S anan yake da aiki, gidajensa kuwa sun kai goma sha a ƙasar U.S babban amininsa kuwa shine Marshal Mohandas ɗan gidan C.D.S Suraj. shi kuma S.D Roshan yana zaune a ƙasar Egypt anan Babban hospital ɗinsa yake.... ꧁꧂ SARKIN JIDDAH Mai martaba sarki Abubakar Bature Matansa biyu Babbar matarsa itace Maimuna (Mamy) bata taɓa haihuwa ba kuma an tabbatar bazata iya ɗaukar ciki ba, hakan yasa mai martaba ya Auro ƴar Sarkin ƙasar Niger kyakykyawa mai suna Maryam (Innayo) cikin ikon ALLAH bayan shekara Innayo ta samu juna biyu, a haihuwa aka yi mata Operation aka ciro mata zankaɗeɗiyar ɗiyarta mace, Mai martaba yayi matuƙar farin ciki dajin wannan Albishir da akayi masa a yayinda ita kuma Hajia Mamy baƙin ciki kamar ya kasheta hakan yasa ta biya wa Doctor ɗin asibiti akan ya cirewa Innayo Mahaifa ba tareda kowa ya sani ba, hakan kuwa akayi sannan tasa aka sace jaririyar bayan ta rufewa jaririyar baki yanda bazata iya yin kuka ba ta hanyar tsafi data karɓo a gurin bokanta, ta biya maƙudan kuɗi akan aje a bisine jaririyar da ranta yanda baza'a ƙara jin labarin ta ba, Washe garin ɓatan jaririya ba ƙaramin girgiza kowa yayi ba banda Hajia Mamy da kuma Doctor sai wanda ya tafi da jaririya iya su kawai suka san sirrin, Mai martaba saida ya faɗi sumamme jin labarin ɓatarta, itama uwar ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, Mai martaba bayan ya farfaɗo baiyi ƙasa a gwiwa ba haka yasa aka yanka ƙaton rago ya raɗawa ɗiyarsa suna REEMAH inda ace namiji aka samu Yarima za'a sanya masa amma yanzu macece, Shi kuwa wanda ya sace Reemah bai bi maganar Hajia Mamy ba na cewar a bisine jaririyar lokaci guda imani ya shige shi haka ya fita da Reemah daga ƙasar Jidda a sirance kai tsaye Nigeria ya kawota, bai tsaya a ko ina ba sai a gidan marayu dake garin Abuja, yana miƙata ya gudu bai tsaya bada information nashi ba, lokaci guda aka rasa shi, kafin ya bayar da Reemah daman yayi mata zanen tambarin masarautarsu dake ƙasar Jidda da ƙunar wuta yanda bazai taɓa goguwa ba har abada akan cinyarta (Lap).... ꧁꧂ Aunty Yolash Ƙanwa agurin Chief Muhammad Bature da kuma Mai martaba sarkin JIDDAH. Abubakar Bature, Auntyn su M.G Razhdeen da S.D Roshan da sauran ƙannensu mata, ita wannan tinda take bata taɓa yin Aure ba, tasa Aikin Boko a gaba sai tarin dukiyar da take dasu, batada damuwar kowa a ranta! Gata da farin jinin mazajen Aure amma taƙi sam tana zaune anan Bauchi a fantamemen gidan kanta amma saidai ta zuba masu tsaro a gidanta, Aunty Yolash Smiling woman ga son temako da tausayi duk sati take fitar da zakkah sannan tasa a rabawa gidan marayu kayan Abinci da suturori da kuɗaɗe, mutane har so suke jumma'a tayi da sassafe kafin ta fito gurin aiki ƙofar gidanta yake cika da al'umma saboda ta saba raba zakkah da sadaka, kwanan nan ta rabawa gurgwaye kekuna maza da mata, Aunty Yolash kenam babu ruwanta ita kowa nata ne, kuma Insha ALLAH muna sa ran kwanan nan zata fito zaɓen Minister a garin Bauchi.... ꧁꧂ ꧁꧂ Babban gidan marayu dake garin Abuja a ciki akwai mutane da yawa wadanda suke kai kawo manya da 'kananu kowa yanata harkar gabansa kamar gidan prison duk suna sanye da kaya iri daya ajikinsu, kuma babu halin fita ko ina babban gate a tsare yake da wasu manya manyan masu tsaro, idan kunga marainiya ta fita daga cikin gidan nan to saidai an samu wasu masu kud'i ne sukazo za6ar yarinya da zasu dauka ko a matsayin er aikinsu, su dai basa d'aukar yara sai dai yan mata wad'anda zasu iya juran aiki.... Wata zankaɗeɗiyar budurwa ce wacce bazata wuce shekara 20 ba tana zaune akan wani ɗan dakali tana wasa da wani siririn sarƙa dake lanƙaye a wuyanta mai ɗauke da catoon ɗin Jesus Christ ajiki ta ɗan ƙasin sarƙar zanen Cross ne, Idonta akan sarƙar tanata jujjuya shi, kwatsam kunnuwanta suka jiyo mata wani ɗan hayaniya ta gefenta, ɗagowa tayi da manya manyan idanuwanta mai ɗauke da zara-zaran eyelashe! White eyes ɗinta ne suka sauƙa akan wata mata yanda take ta dukan wata matashiyar yarinya mai buzuzun gashi irin mai murɗi-murɗin nan har gadon bayanta, yarinyar kana ganinta kasan irin yaran buzayen nan ne ƴan ƙasar Niger kyawawa, Budurwar dake zaune ganin yanda aketa dukanta yasa ta tashi da gudu ta nufi wajen cikin sassanyar murya ta ce "Haba ke kuwa Aunty Salma mai tayi miki ne haka kike dukanta?..." A fusace wacce ake ƙira da Salma ta juyo tana kallonta a ƙasƙance ta ce "Ke Baiwar ALLAH ki kiyaye Ni wallahi, bana son shishshigi shin da kika taso rama mata dukan zakiyi ne?..." Baiwar ALLAH tayi murmushi sannan ta ce "Aunty Salma meyasa bakya tausayin Ƴar Amana ne? ki dubi halin da take ciki Kurmiya ce bata iya yin magana dan ALLAH ki rinƙa mata uzuri..." Salma ta ce "ke Baiwar Jesus domin bazan ce miki Baiwar ALLAH ba tinda baki haɗa hanya da musulunci ba Arniyar banza..." Lumshe ido Baiwar ALLAH tayi sai ga zafafan hawaye a hankali ta buɗe su da sassanyar muryarta ta ce "Aunty Salma ina ganin mutuncinki, na roƙe ki kar ki sake ƙirana da Arniya saboda ina sallah, ina Azumi, ina karatun Alkur'ani mai girma, ina nisanta kaina daga aikata saɓon ALLAH to meyasa zaki rinƙa ce mun Arniya?..." Kwashewa da dariya Salma tayi harda tafa hannayenta biyu sannan ta ce "a fuska musulunci a zuciya kuma kafurci, idan ke ba Arniya bace me zaisa ki rinƙa yawo da sarƙar Jesus a wuyanki? saboda kin raina wa mutane hankali koh?..." Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi tareda faɗin "Ba haka bane Aunty Salma! tin ina ƙarama nake ganin wannan sarƙar a wuyana, duk da ban tashi a gaban iyayena ba amma nasan a lokacin dana rabu dasu nayi wayo kuma wannan sarƙar daga wajensu ya fito saboda haka zan cigaba da adana wannan sarƙar har ALLAH ya bayyano mun da iyaye na....." Salma harararta tayi sannan ta ce "da dukkan alamu iyayenki Arna ne shiyasa suka sanya miki sarƙa mai ɗauke da Cross ɗin Jesus Christ mttssww....". taja dogon tsuka tare da barin wajen... Baiwar ALLAH sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana faman zubar da hawaye, ji tayi wacce take tsaye a gefenta ta rungume ta sosai itama tana zubar da ƙwallah, Baiwar ALLAH ɗagowa tayi tana kallon Ƴar Amana wacce ta rungumeta cikin tausayawa ta ambaci sunanta cikin sassanyar murya ta ce "Ƴar Amana kiyi haƙuri komai lokaci ne, mu cigaba da haƙuri ALLAH yana sane damu kuma Insha ALLAH zai kawo mana agaji, kowa ya tsane mu acikin gidan marayun nan Ni suna ɗaukata a mazannin Arniya alhalin ba haka bane, ke kuma saboda ALLAH ya yo ki Kurmiya shiyasa ake cin zalinki kiyi haƙuri kinji ko? ina tare dake duk tsanani duk wuya bazan rabu dake ba, ke Ƴar Amana tace..." Itama Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon Baiwar ALLAH babu bakin magana sai hawaye amma tana jin duk abunda ake faɗa... Baiwar ALLAH hannu tasa tana gyara sumar kan Ƴar Amana wanda ya tarwatse gashin yayi buzuzu duk ya nan naɗe, Ita kuma Baiwar ALLAH gashin ta tsantsi ne dashi har gadon baya baƙi ƙirin sai sheƙin da yake... suna tsaye suka ji wata mata tana cewa "ku kuma pah masu fararen fuskoki me kuke yi anan? anata ƙiran sallar mangarib ku wuce ku koma ɗakunan ku..." Baiwar ALLAH riƙe hannun Ƴar Amana tayi har sun fara tafiya matar ta ƙira sunan Baiwar ALLAH sannan ta ce "idan kunje kisa Ƴar Amana tayi sallah kar ki rinjayeta ta koma ƙabilan da ba nata ba ...." Baiwar ALLAH ɗaga kanta kawai tayi alamar toh saboda matar itama ɗaya ce daga cikin shuwagabannin gidan, Da hawaye a saman fuskar Baiwar ALLAH suka shige ɗakinsu, suna shiga kuma ta shige toilet tayo alwala sannan ta fito ta tura Ƴar Amana itama ta shiga domin ɗaurowa alwala, kafin ta fito kuwa Baiwar ALLAH ta shimfiɗa musu sallaya sannan ta cire wannan sarƙar dake wuyanta ta zura ƙaton hijab tana jiran fitowar Ƴar Amana, tana tsaye itama ta fito ta saka hijab ɗinta a tare suka yi sallah kamar yanda suka saba kullum, suna idarwa Baiwar ALLAH ta ɗauki Alkur'ani mai girma ta soma karantawa itama Ƴar Amana tana zaune a kan sallayar ta zubawa Baiwar ALLAH ido ba halin yin magana amma tana ɗaukar komai a ƙwaƙwalwarta, da haka har Baiwar ALLAH ta kammala sannan ta ɗauki wannan sarƙar natan ta sanya a wuyanta gudun kar ya ɓata, saboda tana tunanin ta sanadiyar wannan sarƙar zata samu iyayenta.... Knocking aka fara musu a ɗakin da hanzari Baiwar ALLAH tazo ta buɗe miƙa mata flask ɗin abinci akayi sannan aka wuce, Ɗakuna ne acikin gidan bana wasa ba, ko wane ɗaki mutum bibbiyu ne aciki, idan breakfast za'ayi kowa zuwa gurin babban dinning yake yi, anan ake hallaruwa kowa ya kama kujerar zamansa a jeru da doguwar table a gaban kowannen su yanda kowa zai ajiye plate ɗinsa asa masa abinci haka idan rana tayi, dadaddare ne sakamakon duhu ya fara shiga ba'a barin kowa ya fito daga cikin ɗakin shi hakan yasa ake zuwa kowa a bashi abincin darensa a ɗaki, Kullum a cikin wannan rayuwar ake.... Baiwar ALLAH tin tana shekara uku aka kawota saida tayi shekara biyu a gidan nan kafin aka kawo Ƴar Amana ita kuma tana jaririya, dalilin da yasa Baiwar ALLAH da Ƴar Amana suka shaƙu saboda tin lokacin da ƴar Amana take jaririya ake baiwa Baiwar ALLAH rainonta, lokacin babu wasu mutane sosai a gidan, da haka suka tashi shiyasa Ƴar Amana take kallon Baiwar ALLAH a mazannin ƴar uwarta ta jini saboda ita ta tashi ta gani tana kula da ita, wanka da wanki da komai har yanzu Baiwar ALLAH ita take mata, wanka ne kawai yanzu ta daina mata, amma hatta waran kwanciyarsu ma ɗayane tin suna yara basu rabu ba. Yanzu Baiwar ALLAH tanada shekara Ashirin 20 a duniya.. Ita kuma Ƴar Amana tana da shekara sha biyar 15 a duniya... Kuma duk acikin su babu wacce tasan sunanta, tin lokacin da aka kawo Baiwar ALLAH ta manta sunanta idan aka tambayeta sunanta sai dai tayi shuru hakan yasa duk wanda zai ƙirata sai dai yace Baiwar ALLAH da haka sunan ya bita kuma har yanzu bata iya tuna sunanta ba.... Ƴar Amana kuma wanda ya kawota aka tambaye shi sunanta yace musu Ƴar Amana sunanta kuma ya sanar musu cewa da haka za'ana ƙiranta har ta girma, shiyasa itama ta tashi babu suna sai dai Ƴar Amana.... Haka rayuwar ƴan mata biyun nan yake gudana acikin gidan marayu, kowa ya raina su ana musu kallon ƙasƙantattu wasu suna zargin cikin shegensu akayi aka zubar dasu, wasu kuma suna faɗin ƴaƴan ƴan gudun hijira ne, Basu san cewa Ɗaya daga cikinsu Ɗiyar shugaban sojojin ƙasar U.S bane (C.D.S).. Ɗaya kuma Ɗiyar Mai martaba Sarkin ƙasar JIDDAH bace kuma jikar mai martaba sarkin Niger, Ɗiyar ƙanin Chief of Army's staff na Nigeria.... BAIWAR ALLAH DA ƳAR AMANA STORY BY ASMEETAH ku cigaba da bibiyata a cikin littafi na mai suna *MY ENEMY...* Comments 🙏 And Sharing book, Ku saurari Chapter two zuwa Monday idan har na samu ƙarancin comment... Idan kuma na samu comments yanda nake so daga Saturday zan poster kuma, Bazaku ji Armashin chapter one ba har sai kun shugo chapter two anan labarin zai fara gobara🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢+ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ Asma'u Muhammad Auwal (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) ASMEETAH. 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ᵖˡᵉᵃˢᵉ ᵒⁿˡʸ ᶠᵉᵐᵃˡᵉˢ ᵃⁿᵈ ᵈᵒⁿ'ᵗ ᵃˡˡᵒʷ ᵗᵒ ˢᵉⁿᵈ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ⁱⁿᵗᵒ ᵐʸ ᵍʳᵒᵘᵖ🙏 ⁱᶠ ⁿᵒᵗ ⁱ ʷⁱˡˡ ʳᵉᵐᵒᵛᵉ ʸᵒᵘ, ᵃᵐ ʷᵃʳⁿⁱⁿᵍ ʸᵒᵘ .. ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (2) ꧁꧂ Ƙiran Asubar farko akan dodon kunnen Baiwar ALLAH wacce take zaune akan sallaya tana jan carbi a hankali tin ƙarfe biyu na dare bata koma bacci ba, kullum saita tashi tayi sallar dare... tashi tayi a hankali ta ɗosana mazaunenta a bakin gado tareda kai hannunta kan Ƴar Amana wacce take lulluɓe da mayafi, cikin sassanyar murya Baiwar ALLAH take ambatar sunanta "Ƴar Amana! Ƴar Amana!! ki tashi ana ƙiran sallah, kinji koh?.." ganin Ƴar Amana bata motsa ba yasa ta haura saman gadon gaba ɗaya ta ɗagota tareda yaye mata mayafin data rufu dashi, jin yanda jikinta ya ɗau zafi ga rawar sanyin da take yi yasa Baiwar ALLAH tsorita ta zazzaro ido waje tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un Ƴar Amana meya same ki? wayyo zazzaɓi ke samun ki bari na dubo miki magani...." a ruɗe Baiwar ALLAH ta sauƙo ta nufi waran da jerin kayansu suke nan ta fara fitar da kaya daga cikin jaka tana faɗin "ina tunanin akwai sauran magani, ALLAH yasa na samu wayyo ƴar uwata ba lafiya..." Ita kuwa Ƴar Amana tana kwance sai rawar sanyi take gaba ɗaya ta fita hayyacinta, Baiwar ALLAH tasowa tayi jiki ba ƙwari tana tsaye takai hannu ta riƙo kunkuminta tana sauƙe numfashi cike da tausayawa tace "Ƴar Amana ban samu maganin ba, gashi yanzu idan naje tambaya ba lallai mu samu ba saboda sau ɗaya ake bamu magani a wata idan ya ƙare kuma shikenam, amma ki kwantar da hankalinki zanje na gwada tambaya ..." tana kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita kai tsaye office ɗin shugaban su ta nufa, tana zuwa ta tsaya a gaban ƙofar office takai hannunta a hankali tana knocking, jin shuru yasa ta tura ƙofar ta shige ta kuma rufe ƙofar kar a ganta saboda doka ne wata ta shiga office ba tareda permission ba, anan duk wasu abubuwan da ake buƙata suke nan ta fara bincika ko ina tana neman akwatin maganinnuwa, har gari ya fara washewa daƙer ta samu akwatin ta buɗe a hanzarce ta ɗauki packet na paracetamol da maganin ciwon ciki da kuma maganin olcer domin gaba ɗaya daga ita har Ƴar Amana olcer na damunsu sakamakon rashin samun isasshen abinci, tana gama jidan magani ta juya zata bar ofishin kwatsam ta tarar da Ogansu yana tsaye ta bayanta wanda yanzu zuwansa, zaro ido Baiwar ALLAH ta soma yi tana haɗiyar yawu daƙer ga wani zufa da yake gangaro mata, buɗan baki tayi zatayi magana a wahalce mutumin ya ɗaga mata hannu alamar tayi shuru, yana mata wani irin kallo yace "Baiwar ALLAH kin shugo hannu, barewar dana daɗe ina farauta yau gashi ta faɗo tarko nah, Baiwar ALLAH! Baiwar ALLAH!! shin kin san hukuncin yin sata acikin Office?..." Baiwar ALLAH shuru tayi tana kallon ƙasi tana tunanin yanda zata kuɓuce a hannun wannan azzalumin mutumi, ya juma yana nemanta da lalata amma taƙi bashi haɗin kai, daman yana neman yanda zaiyi ya kamata da laifi yau kuma gashi ga ita... katse ta yayi daga dogon tunanin data faɗa tareda cewa "duk wacce aka kama tayi sata to hukuncin ta shine ayi mata bulala hamsin sannan ayi mata tsirara daga ita sai pant da bra a zagaya da ita cikin wannan makeken gida na marayu kowa da kowa ya ganta..." yana magana cikin izgilanci ya gyara tsayuwarsa sannan ya goya hannayensa a saman ƙirjinsa ya kuma cewa "toh ya kike gani! shin kin yadda ayi miki wannan tozarcin ne ko kuma dai zaki bani haɗin kai saina ƙyale ki..." Baiwar ALLAH ɗagowa tayi da rinanan idanuwanta waɗanda tasha kuka dasu ta haɗe hannayenta biyu ta ce "Yallaɓai dan girman ALLAH kayi haƙuri wallahi ba komai nazo ɗauka ba illa magani, Ƴar Amana tana can bata da lafiya ka temaka mun..." cikin rashin nuna damuwa ya ɗaga kafaɗunsa tareda cewa "i don't care about Damuwata shine ki bani lokacinki mu fake...." kafin ya rufe baki Baiwar ALLAH ta tafo da gudu ta durƙusa a gabansa tare da riƙe masa ƙafafu tana kuka ta ce "dan ALLAH Ƴallaɓai ka temaka mun, bana son abunda zai zubar mun da mutunci na, inaso na haɗu da iyayena cikin ƙoshin lafiya, inaso na rinƙa alfahari daku koda bama tare saboda tin ina ƙarama kuke riƙe dani, kun zamo mun tamkar iyaye nah, dan ALLAH Yallaɓai Ni ƴa ce a wajenka bai kamata wannan al'amarin ya afku ba..." Lumshe ido yayi yana sauƙar da numfashi a hankali game da cewa "wayyo daɗi cigaba da rungumar sawaye nahh.." yakai hannunsa ya cabko nata hannun ya ɗora saitin AK-47 ɗinsa yana hura iskar bakinsa, Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta fincike hannunta da ƙarfi tana ja da baya murya na harharɗewa ta ce "A'uzubillahi ALLAH Ubangiji ya toni asirinka yallaɓai...". ta tashi tabi hanyar fita zata gudu yayi saurin riƙota ya mannota saman ƙirjinsa yana zazzaro mata eyes tare da darara mata tsawa ya ce "Keee bari kiji a wannan lokacin ƙarya kike ki tsallake tarko nah, duk ƴan matan cikin wannan gidan babu wacce ban ɗanɗani kalar zumanta ba sai ke da kuma ƴar uwarki Ƴar Amana, don haka ba kowa kuka fi ba dole kuma saina kusance ku kota halin ƙaƙa...." Baiwar ALLAH jin ya ambaci sunan Ƴar Amana yasa ta dakata dayin kukan tana masa wani irin kallo na ƙasƙanci ta ce "Yallaɓai duk abunda zaka yi kar ka ƙara sako sunan Ƴar Amana acikin maganarka domin banga abunda ta tare maka ba, ita ɗin yarinya ce ƙarama du Da du bazata wuce shekara sha biyar ba a duniya, na zamo mata tamkar uwa don haka kayi komai akaina amma banda ita ..." Yallaɓai ganin ɓacin rai a fuskar Baiwar ALLAH yasa tayi masa ƙwarjini dai daita muryarsa yayi sannan ya ce "okay fine yanzu acikin biyu ki zaɓi ɗaya, shin zaki amince mun da buƙata ta in yaso duk abunda kike buƙata zaki samu a waje na ko nawa kike so ko kuma kin zaɓi a fitar dake bainar jama'a ayi miki bulala sannan a zagaya dake zigidir...." Ajiyar zuciya Baiwar ALLAH tayi tana zubda ƙwallah ta ce "ban taɓa jin labarin gidan marayu ana musu wannan mummunan abu ba sai a wannan gidan, Ni bazan bi hanyar da zan saɓawa Ubangiji na ba domin da kunyar lahira gwara ta duniya, na Amince ayi mun hukuncin da aka zaɓar mun, insha ALLAHU idan hukuma taji wannan ƙazamar labarin bazata barku ba domin kunci amanar da aka baku na riƙon ƴaƴan marayu...." kafin ta rufe baki Yallaɓai ya zage ya zabga mata mari yana huci ga baƙin cikin bata amince masa ba ga kuma ta tsaya masa a gaba sai gaya masa maganganu take... Baiwar ALLAH kama fuskarta tayi tareda fashewa da matsanancin kuka, cikin ɓacin rai Yallaɓai ya zaro wayarsa ya ƙira ma'aikatan gidan cikin lokaci ƙanƙani sai ga su sun shugo su biyar duk mata, ganin Baiwar ALLAH yasa suka ce "Baiwar ALLAH meya kawo ki cikin office da sassafe?..." Yallaɓai ya sanar musu cewa "kuje ku rubuta wannan yarinyar ɓarauniya ce kullum saita shugo cikin office ta saci kuɗin tallafin da ake kawowa marayu, yau nazo na kamata tana kokarin buɗe akwatin kuɗi, saboda haka baza mu ƙyaleta ba, ku fitar da ita waje ku tara duk mutanen da suke gidan za'a yanke mata hukunci...." duk maganganun da yake yi kuwa idonsa akan kyakykyawar fuskarta, ita kuwa kanta a sunkuye sai zubda hawaye take hannunta kuwa riƙe da maganin data ɗauka, Acikin ma'aikatan nan kuwa duk basu yadda da abunda Yallaɓai ya faɗa ba dake sun san halinsa mayen mata ne idan mace taƙi bashi haɗin kai haka yake mata wannan sharrin, kuma yana sawa a cirewa mace kayan jikinta ne acikin mutane domin yaga surar jikinta sai yake fakewa da hukunci... Duk gidan marayun nan babu maza iya zallar mata ne kuma babu mai fita daga gidan saboda kar akai ƙorafi akan yallaɓai duk abunda yakeyi a ɓoye yake yinsa, kuma shine shugaba mai kula da yaran marayu amma yake cin Amana... Ɗaya daga cikin matan ce ta riƙo hannun Baiwar ALLAH tareda jan ta suka nufi waje, kai tsaye harabar gidan aka fita da ita cikin sa'o'i aka ƙira duk yaran da suke gidan suka fito, lokaci guda har an hallaru a wajen ana son ganin hukuncin da za'a yiwa Baiwar ALLAH, domin har an sanar cewa tana satan dukiyarsu acikin Office, masu jin haushinta suna ji masu tausaya mata kuma har da hawayensu.., Ita kuwa Ƴar Amana tana can cikin ɗakinsu bata san meke faruwa ba, ganin har yanzu Baiwar ALLAH bata dawo ba yasa ta yunƙura daƙer ta tashi ta nufi toilet, taje ta ɗauro Alwala tazo ta tada sallah, a nutse tayi sallar ta sannan ta jero addu'o'inta acikin zuciya tana zubda ƙwallah, ganin har an ɗau awanni Baiwar ALLAH bata dawo ba yasa ta yunƙura ta fice daga cikin ɗakin, tafiya take bata ga kowa ba, dake a saman beni suke, saida ta miƙi dogon compound dake saman beni tukun ta fara taka matakala a hankali ta sauƙo ƙasin beni, anan ta fara ganin tarin mutane a cushe guri ɗaya, da gudu ta ƙarisa wajen ganin meke faruwa, abun da ya tada mata da hankali shine ganin Baiwar ALLAH a tsakiyar fili tayi kneel down ga kwantaccen sumar gashi a kwance saman gadon bayanta sai sheƙi yake, ga Kuma wata zankaɗeɗiyar dorina ajiye a gefenta, wata inyamurar mata ce Madam eniola itace mai yin bulala, tazo taza cire wa Baiwar ALLAH riga suka ji daga can bakin get an hura wutsur dake tsakaninsu da get akwai tazara mai nisan gaske, wannan wutsur ɗin da aka wura shine alamar tabbatar da anyi manya-manyan baƙi waɗanda suka kawo ziyara wa marayu, Yallaɓai yana tsaye takaici kamar zai hallaka shi saboda yaso ace yaga kyakykyawan surar jikin Baiwar ALLAH, domin ALLAH ya yi mata wani irin baiwa ta halitta komai nata a tsare yake, kyakykyawa ce ta asali kamar ba ƴar Nigeria ba, ga surar jiki mai kyau domin ita ba siririya ba sannan ita ba ƴar lukuta ba amma doguwar mace ce fara tass kamar jini zai fito daga jikinta... A fusace Yallaɓai ya ce "kashhh wayyo ALLAH banso anyi baƙi daga yanzu ba, ku ɗauke mun wannan yarinyar ku kaita can ɗakin duhu ku kulleta kuma kada wacce takai mata abinci da ruwan sha har sai tayi regretting...." Ƴar Amana ganin an ɗago da Baiwar ALLAH yasa ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka, itama Baiwar ALLAH juyowa tayi tana kuka ta rungumi Ƴar Amana, a ɓoye Baiwar ALLAH ta ware tafin hannun Ƴar Amana ta damƙa mata maganunnuwan sannan ta shafa sumar kanta tareda faɗin "ki kwantar da hankalinki komai mai wuce wa ne, nidai fata na ki kula mun da kanki, ganan magani kije kisha zaki samu sauƙi sosai...." Ƴar Amana duk taji abunda Baiwar ALLAH take gaya amma saidai ba halin mayar da martani sai kawai ɗaga mata kai data yi... Yallaɓai ne ya darara wani irin tsawa yana faɗin "ku janye mun wannan kurmiyar anan, kuma kowa ya kama aikin gabansa banason baƙin nan su fahimci akwai matsala...." Duk suka amsa da TOH... Baiwar ALLAH can ɗakin duhu aka nufa da ita wanda yake can nesa da bayan ɗaku na, Ƴar Amana dake ta sulalewa zata bi bayan su Baiwar ALLAH anata riƙeta gaba ɗaya ta fita hayyacinta, saida Yallaɓai yazo har gabanta yasa hannu ya zabgeta da wani irin gigitaccen mari har saida ta faɗi ƙasi ta kife, ɗagowa tayi hancinta har ya fashe sai ɗigo da jini yake tana ta kar kaɗa masa hannu alamar magiya akan yayi haƙuri ya ƙyale Baiwar ALLAH, ta kama ƙafarsa tana girgiza masa kayi, haka yasa ƙafa ya yi filli da ita gefe nan ma dungura, bakinta yanata kakkarwa kamar zatayi magana amma babu halin yi, a wannan dungurawar da tayi har tsintsiyar hannunta ya karye sakamakon faɗuwar da tayi akan hannun, amma babu wanda yasan hannun ya karye sai mutsil-mutsil take tayi tana ƙoƙarin tashi sai ga wasu zankaɗa-zankaɗan motoci baƙaƙe manya-manya sai sheƙi suke waran motoci guda biyar sun nufo hanyar da zai kawo su har cikin harabar gidan... wasu ɗirka-ɗirkan sojoji ne suka fara fito wa masu ƙwarjini wanda ko ido baza kaso ka haɗa dasu ba, saida sojojin nan suka gama fitowa duk suka jejjeru kowa da manya-manyan bindigunsu a hannu, ɗaya daga cikin sojojin ne ya buɗe murfin ɗaya daga cikin motocin bayan mintuna ƙalilan saiga ƙafar wanda aka buɗewa gwanin burgewa sai gashi ya fito gaba ɗaya mutumin yana sanye da wata danƙareriyar shadda sky blue da hula kalar shaddan, takalmin ma kalar kayan, yana sanye da wani ɗan siririn farin glass akan dara-daran idanuwansa, mutumin fari ne tass kyakykyawa dashi, dattijo yanada farin gemu amma akwai ɗaukar ido, fuskarsa kuwa yana ɗauke da kyakykyawan murmushi.... Wakilin gidan marayun wato Yallaɓai ganin Chief of Army's ne yau ya kawo ziyara yasa jikinsa ya ɗau kakkarwa, alamun rashin gaskiya ne suka bayyana mishi, yana tunani a ransa cewa "meyasa General zai zo amma ba notice, zuwan ba zata innalillahi, ALLAH yasa dai kar ya kama mu da laifi... " cikin gaggawa aka kawo wa General gurin zama da lema, haka kowa ya rinƙa zuwa yana gaishe su, saida kowa ya isar da saƙon gaisuwa tukun Chief of Army's General Muhammad Zaiduddeen Bature yakai idonsa kan yarinya dake zaune a ƙasin floor duk jini ya wanke mata fuska ta ƙura idonta akansa ko ƙibtawa bata yi, General miƙa mata hannu ya yi alamar tazo yanda yake, Ƴar Amana ƙoƙarin tashi ta soma yi jin hannunta a karye yasa ta koma ta zaune tana kuka, General kallon yanda Yallaɓai yake ya yi shi kuwa ganin kallon da akayi masa ne yasa shi cewa "Am amm Ammm yarinyar Kurmiya ce bata ji sannan bata gani amma akwai rigima..." General ya ce "bashi na tambayeka ba shin meya faru da ita?..." Muryar Yallaɓai ne ya soma kakkarwa yana faɗin "wallahi General a bishiya ta faɗo, taje wancan bishiyar mangoro ne saboda rigima ta hau ta faɗo, yanzun nan case ɗin da akeyi kenam kuka shugo..." Jinjina kai General ya yi sannan ya ce "duk ina kuke kallo har yarinya zata hau saman bishiya bazaku dakatar da ita ba? wannan sakaci ne da rashin kula da yara..." sunkuyar da kansa ƙasi yayi yace "sorry General lokacin babu kowa ata wajen..." Duk sauran mutanen gidan sun jinjina irin girman ƙaryar da Yallaɓai ya zabga lokaci guda... General ne ya tura wani soja ɗaya akan yaje ya dubo Ƴar Amana ko akwai ciwo a jikinta bayan fasuwar hanci da bakin... Sojan saida ya yi checking natan sosai kafin ya gano cewar harda karaya a hannu nan kuwa ya sanar wa General, General zare glass ɗin idonsa ya yi tareda faɗin "whatt! ta karye kuma? Oya kuyi hanzarin kaita hospital right now..." Ɗaya daga cikin ma'aikatan ce tazo ta ɗago da Ƴar Amana, idonta kuwa akan General tana ta masa magana da ɗayan hannunta mai lafiya tareda girgiza masa kai tana nuna hanyar da aka kai Baiwar ALLAH... Shi Yallaɓai ya fahimci abunda take gaya amma sai dai shi ɗin General bai fahimta ba amma shima idonsa akanta yana son gano wani abu acikin zancen zucin da take yi kuma tanata jujjuyar da hannu... Yallaɓai cikin gidan marayun gudun kar General ya fahimci abunda Ƴar Amana take son aikar da saƙon yasa ya yi saurin cewa "Ammm General yarinyar bata son allura ne shiyasa take ta karkaɗa maka hannu, kuma ga dole za'a ɗora mata hannu zata sha azaba..." "Okay" abunda General ya furta kenam, nan da nan yasa sojojinsa suka fara sauƙar da buhunan shinkafa da kayan abinci sannan yasa aka rabawa duk matan dake cikin gidan manya-manyan atampopi masu kyau da tsada da kuma kuɗaɗe haka yasa duk aka rarraba musu, ya bayar aka ajiye wa Ƴar Amana tatan wacce tin ɗazu har sun tafi hospital da ma'aikaciya ɗaya, saida aka gama rabo tass banda Baiwar ALLAH dake can acikin duhun ɗaki ba haske ko kaɗan sai tarin sauraye.... Suna kammalawa Chief of Army's General Muhammad Bature da sojojinsa suka tafi..... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (3) ꧁꧂ Bayan tafiyar su General sauƙe ajiyar zuciya Yallaɓai yayi sannan ya ce "Nagode wa ALLAH, na tsallake rijiya ta baya..." Ganin yanda matan wajen suka zuba masa ido yasa ya turɓune fuska tareda faɗin "me kuka tsaya gani munafukai kawai..." kafin kace mai duk suka watse a gurin, domin ba ƙaramin tsoronsa suke yi ba. Ƴar Amana tana hospital tareda ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan, sai kumbura take tayi cike da tsanar Yallaɓai domin a yanzu babu mutumin data fi tsana irinsa, kuma ta ɗaura ɗamarar yaƙansa domin cikin ranta ruruwa yake tsabar takaicin abunda Yallaɓai yayi musu ita da Baiwar ALLAH, Ga hannu an ɗaɗɗaura mata ƙarafuna ji take kamar daga asibitin nan ta gudu amma sai dai bazata iya guduwa tabar Baiwar ALLAH ba... Baiwar ALLAH kuwa tana cikin ɗakin duhu a zaune ta kifar da kanta saman gwiwowinta tayi kukan har ta gaji, ga sauraye sun isheta ga kuma wani irin murɗa da take ji tsabar yunwa, a yanzu babu tunanin da take yi illa halin da Ƴar Amana take ciki, ta ƙagu tasa ta a idonta domin ba ƙaramin tausayinta take ji ba, tana zaune har dare bata yunƙura ba sannan babu alamar motsin mutum, sai can misalin ƙarfe 12 na dare kowa da kowa yayi bacci saita fara jin motsin mutum a tsorace ta miƙe tsaye zuciyarta na bugun 3+3 tana tunanin har ta saddaƙar domin ta tabbatar da Yallaɓai ne, zai iya zuwa mata a kowani lokaci balle yaga ta fake gefe guda... ji tayi ansa key an buɗe ƙofar a hankali aka shugo, bata iya ganin ko waye ba saboda tsananin duhun ɗakin, saida aka kunna hasken torch sannan taga ashe Aunty Habiba ce wacce take kula dasu, murya na kakkarwa Baiwar ALLAH ta ce "Aunty Habiba kece 🥹..." Dasauri Aunty Habiba tasa hannu ta toshe mata baki alamar tayi shuru, a hankali ta soma cewa "Yallaɓai ya ce kada wanda yazo gurin da kike balle a kawo miki abinci ko ruwan sha, kuma ba'a san ranar fitar dake daga cikin wannan akurkin ba, nima a ɓoye nazo Ni domin na tabbatar Yallaɓai ya tafi gidansa zuwa anjuma zai iya dawowa ya bincike ki, yanzu abinda nakeso dake shine zan fitar dake a ɓoye ki gudu ki bar wannan gidan domin rayuwarki tana cikin hatsari Baiwar ALLAH..." Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "Aunty Habiba yanzu idan kika fitar dani shin baza kiyi laifi ba?..." Aunty Habiba ta ce "kar ki damu dani babu wanda zai san Ni na fitar dake..." Baiwar ALLAH taja dogon numfashi sannan ta ce "a gaskiya bazan iya tafiya nabar Ƴar Amana ba, ban san a wani hali zata kasance ba..." Aunty Habiba ta dafa kafaɗarta ta ce "Baiwar ALLAH kar ki damu zan kula da Ƴar Amana sannan itama zuwa wani ɗan lokaci zan fitar da ita..." Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "a'ah gaskiya ki bar Ni kawai, insha ALLAHU zuwa gaba ALLAH zai kawo mana mafita ta wani hanya, domin nasan idan na fita bansan ina zan nufa ba, rabon dana leƙa cikin gari tin zuwana wannan gidan ina ƴar yarinya ta, yanzu bansan ya kalar garin yake ba, zan iya fita na tarar da waɗanda zasu kashe Ni ko su sace Ni, zan cigaba da zama tareda ƴar uwata Ƴar Amana...." Aunty Habiba ta ce "shikenam Baiwar ALLAH duk yanda kika yanke Ni dai ina tare da ke, kuma bazan iya barinki da yunwa ba dole kullum zan rinƙa kawo miki abinci kuma kinsan yau da gobe sai ALLAH asiri na zai iya tonuwa shiyasa naso ki gudu, amma tinda kin ƙi bazan gajiya ba, ga wannan leda abinci ne a ciki idan kin ci saiki jefar da ledar ta cikin wancan ƙofar sannan ga pure water..." Baiwar ALLAH rungumar Aunty Habiba tayi tana kuka ta ce "Nagode sosai Aunty Habiba amma ina tsoron kar a kama ki, da kin barni hakan nan idan ALLAH yaso zan rayu zan cigaba da rayuwata..." Aunty Habiba tace "hakane amma bazan iya barinki da yunwa ba Baiwar ALLAH, yanzu dai zan tafi kar azo a ganni..." har Aunty Habiba ta juya zata tafi Baiwar ALLAH ta tsayar da ita tareda faɗin "Aunty Habiba banyi sallah ba, dan ALLAH ki temaka mun zanyi sallah..." Aunty Habiba ta ce "tashin hankali yanzu ya zanyi? Amma jira Ni ina zuwa..." Da sauri Aunty Habiba tabar wajen ba tareda ta rufe ƙofa ba, cikin ƴan mintuna sai gata ta dawo hannunta rinƙe da butar Alwala tana zuwa ta shiga cikin akurkin ta kunna light, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin babu Baiwar ALLAH ta fice, waige-waige ta soma yi tana faɗin "ina kuma taje? Na shiga uku...." ajiye butar hannunta tayi sannan ta nufi compound ɗin ɗakunan yaran dasauri zata hau upstairs gida na sama sai taji ana buɗe gate ɗin gidan Yallaɓai ya dawo da mota zai shugo, gaban Aunty Habiba ne yayi wani irin yanke wa addu'o'i kawai take jerowa domin tasan halin Yallaɓai bashida mutunci, da gudu ta ƙarasa hawa saman beni kai tsaye ɗakin da Baiwar ALLAH suke ta nufa domin zata iya cewa zata gano Ƴar Amana, tana buɗe ɗakinsu kuwa saiga Baiwar ALLAH tana rungume da Ƴar Amana sai kuka suke ta sha, Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi a ruɗe tana faɗin "yanzu Baiwar ALLAH abunda zakiyi mun kenam? so kike asirina ya tonu to Yallaɓai ya dawo kuma nasan zai iya zuwa yanda kike ya dubo ki..." Baiwar ALLAH a ruɗe take kallon Aunty Habiba ta ce "bazan iya wuni guda banga Ƴar Amana ba..." Aunty Habiba bazata iya jin abunda Baiwar ALLAH zata ce ba a gaggauce tasa hannu zata jawota su koma kwatsam Ƴar Amana ta riƙe Baiwar ALLAH sosai tana girgiza kai alamar babu yanda Baiwar ALLAH zata je... Aunty Habiba ta kalli Baiwar ALLAH sannan ta ce "ki sani cewa zaman ki a cikin ɗakin duhu shine zai ceceki daga tozarcin da za'ayi miki, yanzu kuwa idan har Yallaɓai ya ga kin fito toh kuwa zai iya ƙudurta abunda yayi niyar yi miki, saboda haka ki temaki kanki kizo mu koma kafin ya ankara dake..." Baiwar ALLAH jin abunda Aunty Habiba ta faɗa yasa ta fara janye jikinta daga na ƴar Amana tana ƙoƙarin zamewa ita kuwa Ƴar Amana ta ƙanƙameta sosai da hannu ɗaya taƙi sakinta, Baiwar ALLAH tana binta a hankali saboda kar ciwon hannunta ya fame amma ita Ƴar Amana fur taƙi sakinta daƙer Aunty Habiba tasa hannu suka fincike hannun ƴar Amana wanda ta riƙe, da gudu suka fita itama ƴar Amana tabi bayansu kafin ta iso bakin ƙofar Aunty Habiba taja ƙofar ta rufe ta kulle ta baya... a hankali suke bin jikin gini suna tafiya, da haka har suka sauƙa daga saman beni kafin su wuce dole sai sun bi ta gaban bakin ƙofar office ɗin Yallaɓai kuma gashi ƙofar a buɗe take haske ta ko ina, ƙafewa sukayi a gurin suka rasa yanda zasuyi, Aunty Habiba ce ta ɗan leƙa cikin office ɗin taga yanata bincika wasu takardu, ganin haka yasa ta kamo hannun Baiwar ALLAH suka wuce da gudu kafin ya ɗago, Daiden lokacin da Yallaɓai ya ɗago gani yayi kamar wurgawar mutum, tsaya kallon bakin ƙofar ya yi kafin daga bisani ya miƙe tareda nufan bakin ƙofar ya fice, waige-waige ya tsaya yi amma baiga alamun mutum ba ga haske ta ko ina, girgiza kai ya yi sannan ya koma ciki a tunaninsa mutanen ɓoye ne suke wasa saboda yanzu misalin ƙarfe 1 ne na dare, kuma babu wanda zai iya shugo gidan saboda security dake can bakin gate, kuma babu wanda zai iya fita sai ma'aikatan gidan... Suna isa wajen Aunty Habiba ta ce "toh ganan buta kiyi sauri kiyi alwala zan rufe ki ne..." Baiwar ALLAH ta ce "to Aunty Habiba..." haka ta samu tayi alwala sannan ta shige Aunty Habiba ta ce "ganan mayafina ki shimfiɗa kiyi sallah, na barki lafiya...". tana kaiwa ƙarshen tasa key ta rufe ƙofar sannan tayi tafiyar ta... Haka Baiwar ALLAH tayi zaman ƙunci da kaɗaici tayi sallolinta tareda addu'o'i sannan taci abincin da Aunty Habiba ta kawo mata a leda tasha ruwa, tana zaune bata rintsa ba saida aka ƙira sallar asuba sannan ta tashi tayi sallar asuba saboda ta riƙe alwalar da tayi.... Shi kuwa Yallaɓai har zuwa wayewar gari bai wani tuno da Baiwar ALLAH ba, shi har ya manta da tana can cikin ɗakin duhu domin shi ALLAH ya ɗora masa cutar mantau, cikin ƙanƙanin lokaci zai iya manta abu saidai a tuno masa, kuma saiya ga mutum tukun yake tunawa dashi, harkokin gabansa kawai yake... After one week Har zuwa wannan ranar Yallaɓai bai tuno da baiwar ALLAH ba, kuma babu wanda ya tuna masa ko ya labanta masa, itama tana can kullum hankalinta a tashe yake gaba ɗaya ta gaji da zaman ɗakin duhun nan ga sauro kamar bala'i duk jikinta tabon cizon sauraye ne ko iya bacci bata yi saboda kullum acikin fargaba take especially idan dare yayi, Kuma har zuwa yanzu Aunty Habiba takan kawo mata abinci da ruwan sha a ɓoye... Ƴar Amana karayar hannunta sai dai Masha ALLAH ta fara samun sauƙi, duk ta rarrame na rashin ganin Baiwar ALLAH amma sai dai ana kula da ita sosai akwai wacce take zuwa ɗakinsu tayi mata wanki da gyaran ɗaki sannan ta temaka mata wajen yin wanka, Ƴar Amana kullum tana ɗaki bata fita ko ina, abinci har ɗaki ake kawo mata, Aunty Khadija kenam ita take ɗawainiya da ita bayan tafiyar Baiwar ALLAH, amma sai dai Ƴar Amana damuwarta shine taga Baiwar ALLAH!.. Misalin ƙarfe 5 na yamma Ƴar Amana ta fito bayan ɗakuna wajen lambu tana tsugune kamar mai tunanin wani abu, dama jira take hannunta ya fara samun lafiya kafin ta fara ɗaukarwa Yallaɓai hukuncin ta, faɗan kurma baya taɓa shigewa akwai tarin mugunta tarin-tarin azuciyar Ƴar Amana, tana zaune ta ɗauki baƙar leda ta ɗaure tafin hannunta sannan ta fara ciran ƙarara tana sawa a leda, ta tashi ta bar wajen ba tareda kowa ya ganta ba, saida duhu ya fara gabato kafin a kunna Sola ta shiga office ɗin Yallaɓai cikin sa'a ta samu ya shiga toilet ɗinsa dake cikin office ga kayansa akan kujera yanda ya cire kafin ya shiga wanka, a gurguje ta fara zazzaga masa ƙarara a cikin kayansa riga da wando gaba ɗaya, zaiyi wanka anam saiya koma gidansa kafin yake chanza kayan sawa sai kuma ya ƙara dawowa haka yake wannan zirga-zirgar daga gidansa sai gidan marayu amma ba haka kawai yake yawan zaman gidan marayun ba saboda yana rage zafi sosai akan ƴan matan gidan, duk wacce yaso ya nema zai samu babu mai dakatar dashi... Ƴar Amana tana gamawa ta fice kai tsaye saman beni ta haura ta nufi ɗakinsu, Shi kuwa Yallaɓai fitowa yayi daga toilet yana ɗan raira waƙarsa tareda goge jikinsa da towel yana sanye da gajeren wando mai pant iya cinya, ɗaukar wayansa yayi ya danna ƙira a waya cikin ƙanƙanin lokaci ya fara magana "Hello Maman Haneef ki dafa mun abinci mai daɗi ganinan zuwa sannan ina buƙatar ferfesun kifi..." yana kaiwa nan ya katse ƙiran, ya ɗauki wandonsa ya zura sannan ya saka t-shirt ɗinsa mai roba-roba mai dogon hannu, Gashi daga rigar babu singlet, ɗaukar key ɗin motarsa yayi da wayarsa yana shirin fita sai ji yake kamar ana mintsinan shi sai mil-mil yake taji, hannu yakai yana sosawa kafin kace mai duk jikinsa ya ɗau ƙaiƙayi, nan ya fara rikicewa yana sossosa jikinsa da hannu bibbiyu, kafin wasu seconni cikin wandonsa shima yaɗau ƙaiƙayi, hura iskar bakinsa yayi da ƙarfin gaske tareda tamƙe AK-47 ɗinsa saboda wani irin ƙaiƙayi da ya fara masa, acikin yana jurewa har ya koma yana ihu yana sose-sose haka ya haɗe bayansa da jikin gini yana gogawa kafin kace mai hawaye har ya wanke masa fuska, Tinin hankalinsa ya fice daga jikinsa ya fice daga cikin officer ɗin da gudu yana kurma ihu, saida yazo tsakiyar filin gidan ya doku a ƙasi yana birgima tareda kurma ihu da ƙarfin gaske, Jin ihu yasa duk mutanen gidan suka fiffito da gudu gaba ɗaya sun tsorita, haka aka taru da ma'aikatan gidan gaba ɗaya babu wanda bai fito ba, manya da ƙananu, ga haske dadau-dadau ta ko ina kamar hasken rana, duk da duhu bai gama shiga ba ƙarfe 6 amma har an kunna hasken Sola a duk gidan, Yallaɓai haka yaketa birgima yana faɗin "wayyo ALLAH al'umma ta ku temake Ni ku sosa mun, wayyo ku sosa mun! ku sosa!! ku sosa mun!!!...." a gigice ya miƙe tsaye ya cire rigarsa ya jefar gefe guda, sannan ya zamar da wandon jeans ɗinsa ya zauna daga shi sai gajeren wandonsa, haka yake tsalle yana jumping abu ba kyan gani gashi baƙi ƙirin dashi, "Wayyo ku kawo mun ruwa, ku kawo mun ruwa jikina ƙaiƙayi..." Haka mutanen wajen nan suke dariya kamar cikinsu zai ƙulle, dake zallar mata ne a wajen sai sautin dariya ne yake tashi, hatta ma'aikatan matan saida suka ɗan dara, a yayin da wasu suka je ɗauko bokitan ruwa suka kakkawo masa wajen bokitain biyar, haka suke kwara masa ruwa a jikinsa yana sosawa amma abun kamar ƙaruwa yake a gigice ya danna uwar ihu yana faɗin "wayyyyyooo ku daina zuba mun ruwa zan mutu, ɗuwawu naaaa zai fice ku ƙira mun likitoci, asibiti akaini..." yana wani irin lanƙwasa kamar mai yin rawa yana tsalle ganin tsayuwar bazaiyu ba yasa ya ƙara kwanciya a ƙasi yana birgima da juye-juye da shanbe-shabe, hannunsa ɗaya yana sosa jikinsa ɗaya kuma yana riƙe da AK-47 ɗinsa gamm... Ƴar Amana kuwa tana saman beni tana kallon duk halinda ake ciki, ta haɗe rai babu alamar Annuri a fuskarta, duk abubuwan da yakeyi ko kaɗan bata ji tausayinsa ba sannan ko dariya bai bata ba saima ƙara jin haushinsa da take yi, Ga gashin kanta buzuzu duk ya rufe mata fuska sai wanda taɗan janye gefe yanda zatana kallon komai, Ganin batada lokacinsa yasa ta koma cikin ɗakinsu... Yallaɓai fa abu sai ƙaruwa yake, ɗan ƙaramin gajeren wandon mah haka yasa hannu ya janye gaba ɗaya ya zauna haka tsirara, ya miƙe tsaye yana jujjuyawa zigidir... Nan Ma'aikatan wajen suka fara koran yaran gidan, amma yaran furr sunƙi koruwa haka suka fara ele suna ihu tareda faɗin "wayyo Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir! Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir!! Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir!!!..." suna tafa hannayensu suna masa waƙa, Su kuwa manyan kowa rufe idonta tayi wasu suka jujjuya da gudu wasu kuma suka rufe fuskokinsu da hannayensu masu hankalin kenam, wasu ma'aikatan ne suka nufi bakin gate da gudu zasu je ƙiran security dake da nisa sosai zuwa bakin gate shiyasa duk abunda akeyi security basu sani ba... Shi kuwa Yallaɓai haka yake tsalle yana girgiza tareda faɗin "ku sosa! ku sosa!! ku sosa mun ku sosa!!..." Yaran kuwa suna faɗin "Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir...." Sai da security suka zo suka fara bulale yaran suna kora kowa cikin ɗakinsa, haka suka zurawa Yallaɓai doguwar jallabiya sannan aka sakashi a mota sai hospital, acikin motar ma haka yake wannan haukar gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa.... Aunty Habiba ganin haka yasa ta wuce gurin Baiwar ALLAH, tana zuwa ta buɗe mata dake key ɗin a wajenta yake, ta ce "Baiwar ALLAH fito yau kam babu kwanan wahala, kije ki kwanta acan ɗakinku..." Baiwar ALLAH cike da mamaki ta ce "Aunty Habiba lafiya kuwa? meya faru, kodai Yallaɓai ya fitar dani .." Aunty Habiba ta ce "Yallaɓai yayi tafiya kuma nasan zaiyi kwana biyu kafin ya dawo..." cike da farin ciki Baiwar ALLAH ta ce "yau zanga Ƴar Amana ALLAH sarki rabin raina ALLAH yasa tana lafiya..." Haka suka wuce suka bar wajen, Baiwar ALLAH da gudu ta haura saman beni kai tsaye ɗakinsu ta wuce tana zuwa ta tura ƙofar ta shige, Ƴar Amana tana zaune a saman gado ta naɗe sawayenta kamar mai cin tuwo kai a sunkuye gaba ɗaya gashin kanta ya rufe mata fuska... Baiwar ALLAH tana shugowa ta haura saman gado yanda Ƴar Amana take tasa hannu ta jajjanye mata sumar gashin sannan ta ɗago da haɓarta tareda faɗin "Ƴar Amana ga Baiwar ALLAH ki ta zo gare ki..." Ɗagowa Ƴar Amana tayi tana kallon Baiwar ALLAH nan danan hawaye ya soma gangaro mata a gigice ta rungumeta tana kuka, itama Baiwar ALLAH rungumarta tayi sosai tana kuka tana bubbugan bayan Ƴar Amana alamar rarrashi..... 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 𝘾𝙊𝙈𝙈𝙀𝙉𝙏 𝘼𝙉𝘿 𝙎𝙃𝘼𝙍𝙄𝙉𝙂... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (4) ꧁꧂ Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana tana kallonta cike da tausayawa tace "ƴar uwa ya na ganki kamar kina cikin matsala?..." Aunty Habiba dake tsaye ta zuba musu ido tareda yin murmushi ta ce "Baiwar ALLAH kenam kin dai san halin kayanki ita Ƴar Amana ai ba'a gane farin cikinta da kuma baƙin cikinta kullum acikin haɗe fuska take, Ni tinda nake daku ban taɓa ganin Ƴar Amana tayi murmushi ba balle naga haƙwaranta....." Ƴar Amana tana sunkuye da kanta ƙasi duk tana jin tattaunawar da suke yi akanta sai dai babu baki, Baiwar ALLAH tana shafa sumar kanta ta ce "ALLAH sarki ƴar uwa, ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe insha ALLAH...." ta ƙarasa maganar tareda ɗago kanta tana kallon Aunty Habiba cike da mamaki ta ce "Aunty Habiba kince Yallaɓai yayi tafiya shin ina yaje? amma naga Yallaɓai baya tafiya yayi kwana biyu baizo nan ba..." Aunty Habiba tayi murmushi sannan ta ce "baki san abunda ya faru da Yallaɓai bane shiyasa..." Nan Aunty Habiba ta kwashe komai ta gaya mata halinda Yallaɓai ya tsinci kansa. Baiwar ALLAH har saida tayi dariya itama ta ce "amma wacece tayi masa wannan aika-aika?..". Aunty Habiba ta ce "waye zai sani? Bayan anyi abu a ɓoye amma duk randa Yallaɓai ya gano ko wacece toh kuwa kashinta ya bushe, Allah dai ya rufa mata asiri, amma Ni naji daɗin hakan sosai saboda nima ba ƙaramin jin haushin Yallaɓai nake ba wallahi..." Baiwar ALLAH sunkuyar da kai ƙasi tayi tana maganar zuci "Babu wacce take da ƙwarin gwiwar zuwa tasa ƙarara acikin kayan Yallaɓai sai Ƴar Amana, domin ta daɗe tana ƙulle ƙullen yanda zata hukunta yallaɓai amma nake dakatar da ita, duk yanda akayi Ƴar Amana ce wayyo..." tana cikin wannan tunanin taji Aunty Habiba tana faɗin "kunga dare yayi na barku lafiya, amma Baiwar ALLAH kada fa ki fita waje saboda za'a iya kulla miki makirci ace kece kika fito kika sawa Yallaɓai ƙarara..." Baiwar ALLAH ɗaga mata kai kawai tayi ba tareda ta ce komai ba.. Bayan fitar Aunty Habiba dasauri Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon Ƴar Amana tareda faɗin "kece koh? nasan ke ce amma ki kiyayi ranar da asirinki zai tonu domin babu ruwa nah...." ta ƙarasa maganar tana ɗora kanta akan filo ta jawo mayafi ta rufe kanta gaba ɗaya, Ƴar Amana ganin yanda Baiwar ALLAH take mata magana cikin ɓacin rai yasa ta fusata ta ɗauki filon gefenta ta fara doka mata, a ruɗe Baiwar ALLAH ta yaye mayafin data rufu ta taso tana faɗin "ke kinada hankali kuwa? me kuma nayi miki?.." haka ƴar Amana take kwaɗa mata filo a duk yanda ta samu a jikinta, ganin bazata daina ba yasa itama baiwar ALLAH ta ɗauki filonta ta soma rausa mata itama haka kowa yake dukan kowa, ganin abun bazaiyu da filo ba yasa suka fara kaiwa juna duka da hannu bibbiyu, Ƴar Amana ce ta kafa bakinta a kan dantsen Baiwar ALLAH ta galla mata uban cizo, a firgice Baiwar ALLAH ta cafki sumar kan Ƴar Amana bata san lokacin datayi wulli da ita ba har saida ta faɗo daga saman gado, ƴar Amana kifa kanta tayi a ƙasi saboda tsananin buguwa da tayi akan hannunta mai ciwo, kuka take yi amma sai dai babu sautin kukan sakamakon sihirin da akayi mata tin tana jaririya, ko kuka zatayi sautin baya fitowa balle tayi ihu... Itama Baiwar ALLAH dafe dantsenta tayi har fatan gurin ya ɗan ɗaga gurin yayi jawur har da hawayenta tsabar zogin da gurin yake yi mata... Sun ɗau mintuna sosai a haka babu wacce ta kalli kowa har zuwa yanzu Ƴar Amana tana nan a ƙasi bata ɗago ba, Ganin shuru yasa Baiwar ALLAH leƙa ƙasi yanda Ƴar Amana take, a hankali ta sauƙo da ƙafafunta sannan ta zauna a ƙasi tareda jawo Ƴar Amana saman cinyarta tana rarrashinta cikin kulawa, cikin sassanyar murya Baiwar ALLAH take faɗin "Duk ke kika jawo amma ko kaɗan banaso nayi faɗa dake, bansan wani irin zuciya Allah yayi miki ba, Ƴar Amana dan ALLAH ki zamo mace mai haƙuri da juriya, ki rage wannan fushin nakin sannan ki rinƙa kaiwa zuciyarki nesa, baki san yanda rayuwa zata kasance damu ba, ke gashi yanda ALLAH ya yoki babu bakin magana amma na tabbatar da cewa kina jin duk abunda ake faɗa, kinje kin saka ƙarara a kayan Yallaɓai dakinyi haƙuri ma komai zai wuce...." kasa ƙarasa maganar tayi sai wasu zafafan hawaye yanda yake zubo mata, suna zaune a haka har bacci ɓarawo ya jidesu, Ƴar Amana tana kwance kan cinyar Baiwar ALLAH, ita kuma Baiwar ALLAH ta ɗora kanta a bakin gado da haka suke shan baccin su... Misalin ƙarfe 2 na dare Baiwar ALLAH ta farka daga baccin da ya ɗauketa daiden lokacin take tashi yin sallar dare, ganin babu ƴar Amana akan cinyarta yasa ta waiga bayanta ko tahau saman gado nan ma bata nan, tunani tayi ko ta shiga toilet ne, haka tayi ta zaman jiran fitowar ta amma shuru, hakan yasa ta miƙe tsaye taje bakin toilet ta fara knocking a hankali tana ambatar sunanta "Ƴar Amana! "Ƴar Amana!! "Ƴar Amana!!! me kike yi ne har yanzu a toilet?..." ganin ko motsi babu a cikin toilet yasa ta buɗe ƙofar toilet nan ma wayam ba kowa.... Ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske a ruɗe ta ce "TOH ina taje a wannan daren?...". ta ƙarasa maganar tana zazzaro manya manyan idanuwanta, da hanzarinta ta nufi bakin ƙofar fita tana zuwa ta buɗe ta fice a gaggauce, nan ta shiga neman ƴar Amana amma bata ganta ba, har ƙasin beni ta sauƙo tana lelleƙa ko ina amma babu alamunta, Baiwar ALLAH ba ƙaramin tsorita tayi ba na rashin ganin Ƴar Amana.... kai tsaye hanyar lambu ta nufa da gudu domin yawon Ƴar Amana baya wuce nan, tana yawan zuwa lambun cikin gidan wanda yake da rata sosai da filin harabar gidan, sai kayi tafiya sosai kafin ka iso lambu, wurine a tsabtace, ga bishiyoyin mango da kashu dasu Apple da sauran kayayyakin fruits, ga wasu flawowi agurin gwanin burgewa ba abunda zakaji a gurin sai kukan tsuntsaye, waɗannan kukan tsuntsayen ne suke jan hankalinta sosai kuma ita ƴar Amana ba ta cika son zama acikin mutane ba, tafi son ta fake ita kaɗai kuma ta kasance mai son kaɗa jita .. Baiwar ALLAH tana isa gurin lambun tsikar jikinta ya fara tashi wani irin tsoro ne yake ziyartar ta, dake akwai hasken Sola sosai a wajen bata wani damu sosai ba, kunnuwanta ne suka fara jiyo mata sautin kiɗan jita mai daɗin sauraro acikin flawowin wajen, murmushi tasau jin wannan sautin jita tasan Ƴar Amana ce, a hankali tasau ajiyar zuciya sannan ta ce "Alhamdulillah tinda na same ki..." tana cikin wannan maganar zuci taji a dafa kafaɗarta ta baya, da murmushi asaman fuskarta ta juya tana faɗin "Ƴar Amana meyasa kike son fitowa acikin daren nan kam.." bata iddasa maganar ba taga Ƴar Amana kai a sunkuye sumar gashin ta duk ya rufe mata fuska, hannu Baiwar ALLAH takai tana gyara mata sumar kan natan ai kuwa a slow ta ɗago da wasu rikitattun idanuwa mai ban tsoro da firgici, ƙwayar idanuwanta zallar fari ne babu ɗigon baƙi ko kaɗan, a tsorace Baiwar ALLAH tayi saurin kawar da hannunta daga kanta baki a buɗe ta gagara rufesu a firgice ta ce "Ƴar Amana ke ce?..." murya na kakkarwa take wannan tambayar, Aljanar dake gabanta buɗe baki tayi tana wani irin dariya kamar na yara, a firgice Baiwar ALLAH ta juya da gudu zata bar wajen, ita kanta bata san ina take yi ba ashe ƙara tusuwa cikin lambun take, anan ta samu jikin bishiya ta jingina bayanta tana sauƙe numfashi sama sama still ana kan kaɗan jita, ga wani irin sauti mai ratsa zuciya amma bata san a yanda ake wannan kiɗan ba amma tabbas acikin wannan lambun sautin yake fita, Baiwar ALLAH tana cikin wannan halin taji an shaƙo mata wuya ta bayan bishiya da ƙarfin gaske, ƙoƙarin ceton kanta take amma ta gagara ƙwace wa haka taketa mutsil-mutsil tana shanbe-shanbe domin ba ƙaramin shaƙa akayi mata ba, har numfashinta yana shirin ɗagewa, idanuwanta sun fiffito waje haka hawaye yake bin saman fuskar ta, ganin ta kusan sheƙawa kuma babu wata mafita yasa ta fara jero addu'o'i acikin ranta, kuma babban abunda ya jawo mata wannan shine ta shugo cikin lambu kai tsaye babu addu'a ta manta batayi ba tsabar ta rikice a neman Ƴar Amana, kuma ƙa'ida ne daga mangarib an dena shugowa cikin lambu saboda akwai tarin hatsarurruka aciki sai mai ƙarfin imani ne zai iya tsallake wa, Ƴar Amana ce kawai take iya shugowa cikin lambun nan a kowani lokaci kuma ta fita lafiya ƙalau ba tareda wata matsala ba, ta rigada ta zamo nasu sun zaɓeta a matsayin tasu... Baiwar ALLAH har idanuwanta sun fara lumshewa kawai taji an sakar mata wuya, lokaci guda ta faɗin ƙasi tana riƙe da wuyan, numfashi daƙer take iya fitar wa, ba ƙaramin jiki tasha ba, wannan sautin jitar ne yake dukan dodon kunnenta a hankali ta zaburo ta tashi zaune daƙer ganin bazata iya miƙewa tsaye ba yasa ta fara rarrafe a wajen tana jero addu'o'i, tana rarrafe tana nufan wajen da take jin sautin jita, tana cikin wannan halin har ta iso wajen, ganin Ƴar Amana tayi tana zaune a bakin bishiyan Banana tana ta kaɗa jitanta mai kyan gani da kuma sauti mai daɗi, Ƴar Amana ta iya kiɗan jita sosai, Baiwar ALLAH tunani ta fara yi kar taje kuma ba Ƴar Amana bace, haka take ƙarewa Ƴar Amana da kallo a ɓoye cikin flowers, Ƴar Amana kanta a sama tana kallon hasken farin wata, fuskarta ɗauke da murmushi wanda bata taɓa nuna murmushinta a kowa sai idan tana fake waje ɗaya nan ma kamar yanzu cikin dare da hasken farin wata, wannan yanayin yana sata nishaɗi sosai... Baiwar ALLAH haɗiyar yawu tayi gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta a cikin ranta ta ce "Allah dai yasa Ƴar Amana ce...". ta ƙarasa maganar tana rarrafawa a hankali sai gata a gaban Ƴar Amana hannu tasa ta riƙo hannayenta wanda take kaɗa jita dasu, a hankali Ƴar Amana ta sauƙo da fuskarta daga kallon sama da take yi, ta kafa idonta akan Baiwar ALLAH tana wani irin tunani a ranta ganin a halin da Baiwar ALLAH take ba'a cikin kwanciyar hankali ba... Baiwar ALLAH ta ce "Ƴar Amana meya kawo ki nan cikin dare, shin bakya tsoro ne? tashi mu tafi kinji..." Ƴar Amana zamar da hannunta tayi zata cigaba da kaɗa jita Baiwar ALLAH tayi saurin riƙo hannun tana girgiza mata kai ga hawaye shaɓe-shaɓe a saman fuskarta, Ƴar Amana ganin yanda Baiwar ALLAH take kuka yasa ta miƙe tsaye zasu tafi amma ba'a son ranta ba, kamar yanda mutane suke son sautin kiɗan jitar Ƴar Amana haka suma Aljanun shiyasa suke biye da ita saboda wannan sautin jitar ta, da haka suka bar cikin lambun Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana har suka isa harabar filin gidan, daga nan suka haura saman beni kai tsaye ɗakinsu suka nufa, Bayan shigarsu ɗaki Ƴar Amana saman gado ta haura ta zaune ga jitarta a gefe guda, ita kuma Baiwar ALLAH toilet ta nufa taje ta watsa ruwa a jikinta sannan ta ɗauro Alwala, tana fitowa tareda faɗin "ki tashi kema kiyi alwala kizo muyi sallah, tinda Allah yasa ba bacci kike ba..." Ba musu haka Ƴar Amana ta tashi itama ta shige toilet tayo alwala sannan ta fito itama ta sanya hijab ɗinta kamar yanda Baiwar ALLAH tayi, daidaita tsayuwarsu suka yi sannan suka fara sallah a nutsu... Bayan sun idar Addu'o'i suka yi na neman tsarin Ubangiji sannan ko wacce addu'arta baya wuce Allah ya bayyanar mata da iyayenta lafiya, bayan sun gama ne Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon Ƴar Amana cike da mamakinta na abunda ta gani yau a cikin lambu, ta ce "Ƴar Amana Ni meyasa kike yawan zuwa lambu ne cikin dare? Bayan kinsan akwai tarin Aljanu a cikinsa, idan kaɗa jitarki zakiyi why bazaki bari sai gari ya waye ba?..." Ƴar Amana itama zuba mata fararen idanuwanta tayi kamar wacce zata yi magana, Baiwar ALLAH ta kuma cewa "shin kinsan abunda ya faru dani a cikin lambun kuwa?..." still idon Ƴar Amana akanta ko ƙibtawa bata yi sai daga bisani ta motsa tareda zuwa gaban mirror ta jawo drower jikin mirror ta ɗauko wani littafi da biro sannan tazo ta zauna a bakin gado ta soma rubutu... Cike da mamaki Baiwar ALLAH take binta da kallo tana mamakin tayaya Ƴar Amana ta iya rubutu balle karatu? ita da ta nuna bata jin komai sannan bata taɓa shiga aji ba, tana cikin wannan tunanin taji an jefo mata littafi da biro tayi firgit ta dawo hayyacinta, bin littafin tayi da kallo daga baya ta ɗauka tana karantawa kamar haka ( Kada ki sake bina gidan lambu cikin dare...) zaro ido Baiwar ALLAH tayi cikin nuna farin ciki ta ce "Ƴar Amana daman kin iya rubutu? indai haka ne ai sai mu rinƙa yin chatting ta rubutu...". ɗagowa Baiwar ALLAH tayi taga har Ƴar Amana ta kwanta tareda rufe kanta acikin mayafi, girgiza kai kawai tayi sannan ta fuskanci gabar ta cigaba da addu'o'inta, ƙa'idanta shine idan tayi sallar dare bata komawa bacci har sai an ƙira sallar asuba... Bayan wata guda da misalin ƙarfe 10 na safe bayan an kammala breakfast kowa ya wuce ɗakinsa saiga wata mota ƙarama ƙirar jeep an buɗe mata gate ta tafo da gudun gaske, baiyi parking a ko ina ba sai a harabar gidan, ya fito yana sanye da 3quarter a jikinsa irin na ƴan kwallo da rigarsa mai hannun singlet, tsayawa yayi yana bin gidan da kallo lokaci guda yasa wusir a bakinsa ya hura da ƙarfin gaske yanda kowa na gidan zaiji daga gidan ƙasa har zuwa gida na sama, kafin kace mai saiga mutanen gidan sun fara fiffitowa da gudu, ganin yallaɓai ne ya dawo yasa duk suka shiga taitayinsu, haka kowa ya zo filin gidan suka tsatstsaya duk suka saka shi a tsakiya, Bin kowa yake da kallo fuska ba Annuri, can baya ya hango Ƴar Amana kai a sunkuye yana taku cikin salo yaje gabanta yasa hannu ya ɗago haɓarta suka haɗa ido huɗu, fuska ba walwala ya ce "ina ƴar uwarki take?..." Ƴar Amana shuru tayi bata bashi amsa ba ya darara mata tsawa yana kuma tambayarta amma Ƴar Amana ko girgiza batayi ba balle ta nuna cewa taji tsoron tsawar da ya yi mata... Wata daga cikin ma'aikatan ce ta ce "Yallaɓai ka manta ne ita ɗin Kurmiya ce bata jin abunda kake faɗa..." sai a yanzu ya tuno ashe Kurmiya ce, cikin mugunta ya damƙi sumar kanta sannan yazo da ita tsakiyar filin yana faɗin "ina zargin ɗaya ce daga cikinku wata ta sanya mun ƙarara acikin kayana, ko ke ko Baiwar ALLAH....." A gigice ya daka uwar tsawa yana faɗin "Ina Baiwar ALLAH ta fito nan..." still yana riƙe da sumar gashin Ƴar Amana wacce ita kuma tana ta kai kawo tana kokarin zamar da gashinta domin ba ƙaramin riƙo yayi mata ba, Aunty Habiba tana tsaye ta ce "Yallaɓai ai tin kafin ka tafi kasa a rufe ta a ɗakin duhu..." kafin ta ƙarasa maganar ya daka mata tsawa itama tareda cewa "ƙarya kuke munafukai, nasan kun daɗe da fito da ita shin tana inaaaa?..." Baiwar ALLAH tana laɓe tana ganinsu ganin yanda yake riƙe da sumar gashin Ƴar Amana yasa ta fito domin bazata iya juran ganin hakan ba, fitowa tayi ta nufo gurin da suke, matan wajen ne suka fara buɗa mata hanya ta wuce har tsakiyar mutanen ta tsaya tana kallon floor, Yallaɓai ganin Baiwar ALLAH yasa ya saki kan Ƴar Amana yazo har gabanta suna facing juna, wani irin kallo yake mata daga bisani ya ce "ke ce kika saka mun ƙarara acikin kayana?..." Baiwar ALLAH tace "lokacin da akayi haka ina can ɗakin duhu .." Yallaɓai ya kuma cewa "kenam wancan yarinyar ce?..." ya ƙarasa maganar yana nuna yanda Ƴar Amana take.. Nan ma Baiwar ALLAH ta ce "ba ita bace.." tayi maganar ba tareda ta ɗago ba Yace "taya kika san ba ita bace?.." Tace "saboda nasan bazata aikata ba ." tintsirewa da dariya yayi sannan ya ce "na tabbata duk marayun matan dake cikin gidan nan babu wacce zata iya mun wannan abun sai ku biyu ke da Ƴar Amana..." ɗagowa Baiwar ALLAH tayi tana kallonsa tace "saboda sun baka haɗin kai shiyasa? mu kuma saboda munyi Allah wadai da halinka shine ka ɗora mana tsanarka akan mu ?..." tana ƙarasa maganar ya zabgeta da mari yana huci yace "ke Ni zaki tsaya a gaba kina gaya mun maganganu? saboda kin raina Ni?..." wata ce daga cikin yaran gidan ta ce "Yallaɓai ai tinda muka ganka tsirara zancen raini ya ƙare..." duk suka kwashe da dariya, haushi kamar zai kashe Yallaɓai cikin tashin hankali ya darara musu tsawa tareda faɗin "duk ku sunkuya kuyita tsallen kwaɗo har yamma..." haka kuwa suka hau yin tsallen kwaɗo banda Baiwar ALLAH da Ƴar Amana da suke tsaye sai sauran ma'aikatan, Yallaɓai yana zazzaro ido waje yana fuskantar Baiwar ALLAH yace "ke kika saka mun ƙarara ko ƴar Amana?..." Shuru Baiwar ALLAH tayi bata bashi amsa ba, yana jinjina kai ya ce "okay don't worry Ƴar Amana yau saita gane kuranta..." ya juya zai nufi yanda Ƴar Amana take a tsaye ta ƙura masa ido Baiwar ALLAH tayi saurin cewa "Ni ce na saka maka ƙarara acikin kayanka, babu laifin Ƴar Amana..." Juyowa yayi yana mata kallon up and down ya juyo zuwa gare ta kafin ta ankara yasa mata ƙafa ya girbeta bata san lokacin data doku a ƙasi ba, kafin ta ɗago ya zabga mata mari har saida taga duhu tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fii musibati wa akhlif li khairan Minha, Allahumma inni kuntu mina zalimin..." haka yasa hannu ya ɗagota ya riƙo fuskarta da hannu bibbiyu ya gwara mata kansa a goshinta sannan ya hankaɗata gefe ta faɗi ƙasi tana mai jin hajijiya, Ƴar Amana ta kumbura sosai kamar zata fashe ganin yanda yaketa zaluntar Baiwar ALLAH haka ta tafo da gudu yana juyowa kafin ya ankara ta rungumo shi takai bakinta saitin AK-47 ɗinsa ta garzaya masa cizo na gaske, wani irin gigitaccen ihu yayi har saida mutanen wajen suka toshe kunnuwansu tsabar ƙarfin ƙarar, still Ƴar Amana bata ɗago da kanta ba ta sake kafa haƙwaranta ta garzaya masa kuma du, ihun da yake yi ne yasa security bakin gate suka jiyo sai gasu da gudun gaske, kafin su ƙaraso Ƴar Amana ta ɗago saida ta saita gurin ta kai masa canki da ƙafarta da iya ƙarfinta! zaro ido yayi waje a yayin da numfashinsa ya tsaya cakk sai luuuuu ya faɗi sumamme, Duk waɗanda suke wajen sun tsorita sosai ganin yallaɓai a kwance ba motsi, kuma har tayi wannan aikin babu wacce ta dakatar da ita, Baiwar ALLAH a ruɗe ta tashi tayo gurin Ƴar Amana ta rungumeta tana kuka tareda faɗin "mun shiga uku Ƴar Amana kin kashe shi har lahira, bamu da mafita daga gidan marayu sai gidan prison wayyo ALLAH nah, da rabon baza muga iyayen mu ba har abada...." ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, itama Ƴar Amana kuka take kanta akan kafaɗar Baiwar ALLAH.... Security suna zuwa basu tambayi meya faru dashi ba suka ɗauke shi domin yin temakon gaggawa saboda halinda yake ciki, ga jini har ya wanke masa wandonsa haka jinin yake bin ƙafafunsa.... Wayyo da wuya Yallaɓai fah ya rayu yanda naga abun nashin yana ƙwararar da jini🥺🤔🤔🤔 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (5) ꧁꧂ Innalillahi wa inna ilaihi raju'un Yallaɓai AK-47 ɗinsa ya daina aiki, amma anyi nasarar ceton rayuwarsa, sai dai yana jin jiki sosai jinya yake bana wasa ba, saida aka fitar dashi ƙasar waje kafin abun nashin ya daidaita amma babu ƙwari domin bazai iya yin amfanin komai akan matarsa ba, Matar kuma ta gaza yin haƙuri ta tattari ƴaƴanta Uku tayi tafiyarta domin a cewarta bazata iya rayuwar zaman Aure dashi ba, saboda zata cutu matuƙa haka ta dage har ya sake ta... Yallaɓai ya ɗauki tsanan duniya ya ɗorawa Ƴar Amana domin ita tayi sanadiyar lalacewar rayuwarsa, babu yanda zaiyi haka ya shigar da ƙara akan Ƴar Amana... 3 months ago Ƴan mata ne suke zazzaune akan kujerun roba wanda yake gidan marayu, ko wanne sun haɗa group ɗinsu sai shan shapta suke ta sha, kura ya mutu ai wasa, Yallaɓai baya nan sun samu ƴancin kansu babu hantara da takura, A yanzu misalin ƙarfe 4 na yamma Baiwar ALLAH da Ƴar Amana suna can ɓangaren Lambu, sun sa kayan fruits a gaba Baiwar ALLAH sai sha take a yayin da ita kuma Ƴar Amana take kaɗa sautin jitan ta mai daɗin saurare da hannu bibbiyu, suna zaune babu mai sauraron kowa acikinsu... Motoci ne waran su biyar na Police suka diddirƙo a filin gidan, ƴan matan gidan ne duk suka mimmiƙe suna ja da baya cike da tsoro da fargaba, kafin kace mai matan gidan duk sun taru ganin motocin Ƴan sanda ga kuma Yallaɓai, D.P.O ne yazo ya tsaya a gaban Ƴan matan tareda faɗin "ina sauran Ma'aikatan gidan?..." kafin ya rufe baki sai gasu sun tafo da gudu daman su biyar ne Aunty Habiba da Aunty khadija da Aunty Salma da sauran biyun, suna zuwa suka fara gaishe da D.P.O, daga bisani suka maida kallonsu kan Yallaɓai tareda faɗin "Yallaɓai ya jikin?.." kawar da kai yayi gefe ko sauraronsu baiyi ba, D.P.O yace "shin kunsan wannan?..." ya ƙarasa maganar yana nuna Yallaɓai, Duk suka amsa da "Ehh.." ya kuma cewa "shin ko zaku iya sanar mana abunda ya faru dashi?..." matan gidan ne suka fara kallo-kallo suna kallon junansu daga baya suka ce "Gaskiya bamu san abunda ya faru dashi ba, mudai munji labarin bashida lafiya..." D.P.O yace "bana son ƙarya fah? shin ina Baiwar ALLAH da Ƴar Amana?..." suka ce "suna Lambu..." ya sanar wa ɗaya daga ciki cewar taje ta ƙira su, nan danan aka tafi ƙiransu.. Yallaɓai kallon yaran yake cike da mamaki lokaci guda sun juya masa baya har suna goyon bayan ƙarya akan su tozarta shi, hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba dajin haka.... nan da wasu ɗan lokaci saiga Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sun taho, Ƴar Amana tana riƙe da ƴar jitar ta hankali kwance, Baiwar ALLAH ganin Yallaɓai yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske lokaci guda ta dafa ƙirjinta tareda faɗin "Na shiga uku abunda nake gudu zai tabbata..." D.P.O yace "yadai kika daskare a wajen kodai bakida gaskiya ne?..." girgiza kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ƙaraso yanda sauran matan suke tsaye, D.P.O ya ce "Yallaɓai Ibrahim shin wacece acikinsu tayi maka wannan aika aika domin wannan al'amarin ba ƙaramin abu bane, dole zamu ɗau hukunci akanta, sai tayi zaman cell bayan tasha duka ..." Baiwar ALLAH jin haka yasa idanuwanta suka cicciko da hawaye, Yallaɓai da yatsa ya nuna Ƴar Amana tareda faɗin "wannan yarinyar zamanta a gidan nan babban illah ce domin ba ƙaramar Mayya bace..." Baiwar ALLAH ta riƙe hannun Ƴar Amana tace "Dan ALLAH D.P.O kuyi haƙuri wannan yarinyar Kurmiya ce bata ji sannan bata magana kuma ku dubi shekarunta yarinya ce ƙarama ƴar shekara 15 zaman cell bai dace da ita ba..." Yallaɓai wani irin harara yake wurgawa Baiwar ALLAH domin ta fiye shishshigi a al'amarinsa, kuma sai tana abu kamar sahabiya .... D.P.O ya ƙurawa Baiwar ALLAH ido sannan yace "shin kinsan abunda ta aikata masa ne?..." Baiwar ALLAH tayi shuru tareda sunkuyar da kanta ƙasi, Aunty Habiba ta buɗu baki waran cewa "D.P.O bamu san abunda Ƴar Amana ta aikatawa Yallaɓai ba amma zamu so sanin abinda ta aikata..." ta juya bayanta tareda cewa "ko ba haka ba Ƴan uwa?..." ta ƙibƙibta musu ido.. Duk suka amsa da "Ehh bamu san komai ba, a sanar mana..." Yallaɓai a fusace ya maimaita gayan abinda Ƴar Amana ta aikata masa kuma ya sanar cewa a gabansu duk hakan ta faru... kafin ya rufe baki duk ƴan matan suka fara tintsirewa da dariya, wata daga cikin ƴan matan tace "daman yallaɓai akan wannan ake maganar? naga hari ka kaiwa Aljanar kuliya ita kuwa ya cabke maka tsuriya agaban mu akayi hakan, shine kake son yiwa ƴar Amana sharri? toh kaji tsoron Allah domin zaifi maka ka sanarwa kowa labarin kuliyan nan..." wata ma ta fito tazo gaban D.P.O tace "D.P.O shin taya za'ayi yarinyar da bata jin komai sannan bata iya yin magana ta iya yanke ƴaƴan gwailon Yallaɓai alhalin babu abinda yayi mata! indai ba fyaɗe yayi niyyar yi mata ba, toh mudai kuliya muka sani ba Ƴar Amana ba..." wata yarinya itama tace "shin Yallaɓai ayaban nakan ya daina aiki ne? toh idan kuna son kama kuliyar nan kuje cikin Lambu cikin dare, tafi fitowa acan, mudai ba ruwan mu..." Ɗaya daga ciki ta kuma cewa "rashin kula da tsuriya ne yasa haka, da kana tattalinsa da hakan bata faru ba, kuliyar tayi maganinka taga duk gidan nan babu namiji, kamata yayi a kawo mana shugaba mace wacce zata ji tausayin mu ehen ..." wata ce kuma du ta kuma cewa "wata ƙila fyaɗe zai yiwa kuliyar shiyasa ta cabke ƴaƴan masarrafa 🤣🤣🤣..." D.P.O ganin bazai iya sauraron maganganun ƴan matan nan ba yasa ya juya yana faɗin "shirmen banza kuzo mu tafi, Yallaɓai Ibrahim wannan maganar kawai a rufe shi anan domin waɗannan maganganun da suke faɗi zaisa a ɗaureka saboda zargi zai iya biyowa baya, waɗannan yaran shegen wayo gare su zasu iya sawa a kulle ka a prison domin naji suna maganar fyaɗe, mun Barka lafiya...." D.P.O da mutanensa gaba ɗaya kunya yabi ya ishesu haka suka ja motarsu suka tafi, shima Yallaɓai jikinsa ne yayi sanyi jin abunda D.P.O ya faɗa, haka yayi zuruuu yana wani irin tunani.... Bai ankara ba yaji ɗaya daga cikin ma'aikata ta miƙo masa takarda tareda faɗin "Yallaɓai ga wannan saƙo ne daga sama, an canza maka waran aiki zuwa gidan marayu na maza, mu kuma za'a kawo shugaba ta mace zuwa nan da wata ɗaya, yau ake buƙatar ka bar gidan nan Yallaɓai..." Hannu yasa ya karɓa cike da ɓacin rai, ya ɗago yana bin Ƴar Amana da kallo, shi kaɗai yasan irin muguntar da yake tsarawa a ransa, haka ya juya jiki ba ƙwari ya nufi hanyar gate, yana jin yanda yaran gidan suke tsokanansa da cewa "Yallaɓai mai gutsurarren tsuriya aje a cigaba da tsarkin ruwan zafi....." Baiwar ALLAH cike da farin ciki ta juyo tana faɗin "Nagode muku ƴan uwa, kun temake Ni sosai Allah ya bamu mafita..." suka ce "kar ku damu Baiwar ALLAH ai yanzu mun zama ɗaya, mun kuma haɗe kayuwan mu yanda babu mahalukin da ya isa ya cutar damu, mun ƙwaci ƴancin mu..." haka suke rungumar juna cike da farin ciki da haka kowa ya koma ɓangarensa, temako kuwa suna samu sosai daga waran al'umma, babu rashin kayan abinci komai akwai... Bayan Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sun koma ɗaki zama sukayi suna fuskantar juna Baiwar ALLAH ta ce "shikenam yanzu babu wani tashin hankali sannan babu fargaban komai, mu kwantar da hankalin mu nasara tana nan zuwa gare mu .." Ƴar Amana tana kallon cikin idon Baiwar ALLAH nan take tasau wani irin lalataccen murmushi wanda tinda take bata taɓa yin irinsa ba, Baiwar ALLAH bata taɓa sanin Ƴar Amana tanada wannan kyau ba sai yanzu da taga murmushin ta mai ɗauke zuciya, sannan bata taɓa sanin Ƴar Amana tanada dimple ba sai yau domin bata magana balle kaga lotsewarsu sannan bata dariya kuma bata murmushi, Baiwar ALLAH a ruɗe tace "wow beautiful girl my sister, da ace zaki kasance a haka cikin murmushi da kin wanke mun duk wani tabo dake cikin zuciyata..." ta ƙarasa maganar tana zubda ƙwallah, lokaci guda Ƴar Amana ta koma yanda take a baya babu alamun Annuri a fuskarta cike da tausayi ta kwantar da kanta saman cinyar Baiwar ALLAH..... Misalin ƙarfe goma na dare bayan kowa yaci yasha kowa ya nemi makwancinsa, suma Baiwar ALLAH sun kwanta asaman gadonsu kamar yanda suka saba, ita Baiwar ALLAH itace a bakin gado ita kuma Ƴar Amana a can baya take, amma saidai a yanzu Ƴar Amana tana zaune ne akan gado tana kaɗa jitan ta cikin salo da ƙwarewa a yayinda Baiwar ALLAH take kwance tana sauraron wannan sautin mai daɗin sauraro, da haka har bacci ya ɗauke Baiwar ALLAH, A wannan daren Ƴar Amana bata samu yin bacci ba har waran ƙarfe biyu na dare tana zaune tana ƙiɗan jita, ji tayi ana knocking ƙofar ɗakinsu a hankali waran sau uku, kallon fuskar Baiwar ALLAH tayi taga tanata shan baccin ta, ji tayi kamar ta tashe ta saboda lokacin sallar daren ta yayi amma ta gaza yin haka, a hankali ta sauƙa daga kan gado ta nufi bakin ƙofa zata duba ko waye ne, babu alamun tsoro a tattare da ita haka tasa hannu ta buɗe sakatar ƙofar ta buɗe, tana buɗewa kamar jira ake kwatsam taji an jawota waje da ƙarfin gaske, aka rufa mata wani farin ƙyalle akan fuskarta nan take ta sume a wajen, wani gabjejen mutum ne yasa hannu ya ɗauketa saman kafaɗarsa sannan yayi tafiyarsa da ita, haka yake sauƙa down stairs da sauri-sauri yana sauƙa yabi ta wani ɓoyayyen hanya ya ratsa, lokaci guda aka nemeshi aka rasa.... Can bayan awa guda da faruwar haka Baiwar ALLAH tana motsawa a hankali tana son tashi tayi sallah, ganin hasken ɗakin yayi mata yawa acikin ƙwayar idanuwanta yasa ta buɗesu gaba ɗaya dake basa kwana da haske a ɗaki, tashi tayi tana addu'o'i ta sauƙar da ƙafarta ƙasin gado kwatsam idanuwanta suka hango mata ƙofar ɗaki a buɗe wangam, a zabure ta zaro ido waje tareda faɗin "innalillahi ya za'ayi Ƴar Amana tabar mana ƙofa a buɗe kalan azo a sace mu.." ta ƙarasa maganar tareda miƙewa tsaye ta nufi bakin ƙofa tasa hannu ta rufe tareda sanya sakata, juyowar da zatayi taga babu Ƴar Amana akan gado sai iya jitar ta, maida idonta tayi kan ƙofar toilet taji dai babu motsin mutum a ciki, a ruɗe taje ta buɗe ƙofar toilet taga babu kowa a ciki, ta ɗaga kanta sama tana kallon agogon bangon ɗakin ƙarfe uku yanzu har da rabi, cike da fargaba ta kalli yanda jitarta yake, asaninta indai ƴar Amana zata fita to da jitarta take fita, a fili ta furta cewar "yanzu haka tana can waran Lambu, Ni kuwa ba zuwa zanyi ba wallahi, na horu ba Ni ba aljanu...." ta buɗe sakatar ɗakin yanda inta dawo zata shugo... haka ta shige cikin toilet tayo alwala sannan ta fito saida ta cire sarƙar Jesus Christ tukun ta sanya hijab ta tsaida sallah, har ta idar da sallar taga ƴar Amana shuru bata dawo ba, tanata addu'a har aka ƙira sallar asuba ta tashi tayi sallah, nan ma ƴar Amana shuru, taɗan kishingiɗa kafin kace mai bacci ya ɗauketa bata tashi farkawa ba sai ƙarfe goma na safe, nan ma anzo ana bubbuga ɗakin ne aka sanar cewa azo ayi breakfast, A firgice Baiwar ALLAH ta tashi tana murtsuka ido ta duba waran kwanciyar ƴar Amana bata ganta ba, anan hankalinta yayi matuƙar tashi, saita fara tunanin kodai ta dawo ta fita ne, sai kuma hankalinta ya kwanta, tana jan ƙafa ta shige toilet tayi brush sannan ta fito ta rufa mayafinta ta fice daga ɗakin... tana sauƙa ƙasin beni ta fara baza idanu ko zataga ƴar Amana amma ko mayafinta bata gani ba, ta dudduba ko ina babu ita, haka ta shiga tambayar mutanen wajen ko sun ganta amma amsa ɗaya ake bata cewar ba'a ganta ba, da gudu Baiwar ALLAH ta nufi can Lambu tana zuwa ta fara ƙwalla ƙiran sunan Ƴar Amana, duk cikin lambun nan babu inda bata duba ba amma ko alamunta babu, tin daga lokacin Baiwar ALLAH ta fara zubda hawaye tareda faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un...." A ranar wuni akayi ba'aga ƴar Amana ba, ko labarin ta babu, Baiwar ALLAH tasha kuka kamar ranta zai fita, fuskar nan tayi jawur tsabar kuka abunka da farar mace, idanuwanta sun kukkumbura sunyi jawur suma, ganin wuni guda ba'a ganta ba yasa aka shigar da bayanin ɓatan ƴar Amana can hukumar human right, zasu zo suyi bincike akan al'amarin, gashi yanzu har ana ƙiran sallar mangarib..... Human right basu tashi zuwa ba sai washe garin ɓatan ƴar Amana, a daren jiya Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka, abinci kuwa ko loma ɗaya batasa a bakinta ba balle ruwa, a ranar da masu bincike suka zo sun bincika ko ina, basu samu wata hujja ba, hatta security masu gadin gidan suma babu wata alamar data nuna cewa an shugo gidan ko kuma an fita, saida sukayi waran sati guda suna bincike kafin suka samo wata ɓoyayyar hanya acikin gidan ta bayan gidan, hanya ce wanda saika bi ta cikin ƙasa kafin ka fice a gidan, wato gidan ƙasa, abun ya bada mamaki a kowa na cikin gidan babu wanda yasan da wannan hanyar, haka sauran mutanen gidan suka fara tsorata... Bayan an gama bincike an gano hanyar an yanke cewar Ƴar Amana guduwa tayi bawai ɓata tayi ba ko saceta, abun ya bada kowa mamaki sosai, an faɗi hakane saboda a kawar da maganar ɓatan ta, waɗanda suke faɗin hakan sune shuwagabannin masu gidan marayun, mutane da yawa basu yadda da hakan ba, amma saidai babu yanda aka iya, haka maganar ta baza cikin gidan da hukumomi cewar ƴar Amana ta gudu daga gidan marayu.. Baiwar ALLAH jin maganganun da aketa yayatawa yasa ta ɗora hannu akanta ta fara ihu kamar ranta zai fita, kuka take sosai a filin gidan, har tana ƙoƙarin shiɗewa tana kuka tana faɗin "shikenam an ɓatar mun da Ƴar Amana, nasan Ƴar Amana bazata iya tafiya ta barni ba...." Sauran ƴan matan gidan ne suke rarrashinta suna bata haƙuri, Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta fita hayyacinta idanu sunyi zuru-zuru tsabar rikici da tashin hankali ta faɗi a wajen sumammiya.... Ƴar Amana tinda aka sato ta aka jefar da ita acikin wani ɗaki bata farfaɗo ba yau sati guda domin ba ƙaramin guba aka sheƙa mata a hanci ba, An ɗaɗɗaure hannayenta da ƙafafuwanta da igiya tana kwance saman wani wantalelen katifa, ɗakin ɗan ƙwaƙwas, amma sai dai ɗakin acikin jeji yake bayan gari, ga masu gadinta wasu zabga zabgan maza su biyar ko wannensu yana riƙe da ƙaton bindiga a gannunshi..... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (6) ꧁꧂ Bayan sati biyu da ɓatan Ƴar Amana! Har wannan lokacin Baiwar ALLAH bata samu ƙwanciyar hankali ba, kullum acikin kuka take ba ci ba sha gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta rarrame sai kurmin ƙashin wuya, idanu sun kukkumbura sunyi lufu-lufu abinka dame manyan eyes, fuska duk ya kokkoɗe dake farar mace ce kamar ba jini a jikinta tayi fari fatt, tana fama da jinya a jikinta amma babu wanda ya sani ita kaɗai tasan abinda take ji ajikinta, ga damuwar ƙazafin da akayiwa Ƴar Amana cewar ta gudu ne daga gidan marayu! A gidan marayu kuwa an kawo musu wata shugaba mace Madam Aliya, wannan lokacin sunyi dacen samun shugaba ta gari mai jin tausayi da son temakawa al'umma, Ƴan matan gidan sun samu sauyin yanayi sosai na jin daɗin rayuwa, yanzu wata guda da kawo Madam Aliya kowa yana harkokin rayuwarsa cikin farin ciki, babu tsaro na takurawa, maganar Ƴar Amana kuwa tin tinin an rufe shafinta ba'a maganar ta, tin daga lokacin da Ƴar Amana ta ɓata Baiwar ALLAH bata ƙara fitowa filin gidan ba, daga ɗaki sai ɗaki, iya Aunty Habiba ce kawai take zuwa mata, takan kawo mata flask na ruwan tea saboda iya ruwan tea kawai take iya sha, sannan Aunty Habiba tayi iya kokarinta akan akaita asibiti amma Baiwar ALLAH taƙi yadda kuma taƙi yadda ta haɗu da sabuwar shugabar da aka kawo musu saboda tasan ko bataso dole sai an kaita asibiti, taji labarin matar tanada kirki sosai, a haka take ƙunshe da rashin lafiyarta, hatta sallah a zaune take yinsa tsabar hajijiyan dake ɗinbar ta, ga yawan ciwon ƙirji da take fama dashi, Ƙarfe takwas bayan sallar isha'i Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya yanda ta idar da sallah tana jan carbi cikin nutsuwa taji an buɗe ƙofar ɗakinta tareda yin sallama, cikin sassanyar murya ta amsa ba tareda ta waiwaya ba saboda tasan Aunty Habiba ce, Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi ta nemi bakin gado dake gefen Baiwar ALLAH ta zauna tare da zabga uwar tagumi idonta akan Baiwar ALLAH, Baiwar ALLAH kallon Aunty Habiba tayi tare da sau murmushi tace "Aunty lafiya kuwa ki kayi tagumi?..." Aunty Habiba ta ce "dole nayi tagumi Baiwar ALLAH, kina yarinya dake amma kina so ki sanyawa kanki hawan jini, bakida lafiya kin ƙi sanarwa kowa kuma kin haneni na sanar shin meye dalilin yin haka ?..." Kasalalliyar murmushi Baiwar ALLAH tayi tana kallon guri guda kamar me yin tunanin wani abu, bayan ƴan mintuna da zurfafa tunaninta sannan ta buɗi baki tareda faɗin "ban san a wani hali take ciki ba, ita ɗin yarinya ce ƙarama kuma Kurmiya, ina tsoron kar wani abu ya cutar da ita, ban saniba ko tana cin abinci ko bata ci shin taya zan iya cin abinci kuma taya zan iya yin bacci alhalin ƴar uwata bata samu yinsu ba aciki...." kafin ta rufe baki kuka ya kuɓuto mata kamar daman jira take ayi magana tayi kuka, tsabar tausayi Aunty Habiba itama saida ta share hawaye ta sauƙo ƙasan sallaya tareda rungumo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta cikin kulawa... Aunty Habiba bata tashi barin ɗakin ba sai da ta tabbatar da cewar Baiwar ALLAH tayi bacci tukun itama ta tashi ta fice a ɗakin bayan ta kwantar da ita, Around 1:30AM cikin dare Baiwar ALLAH ta tashi da matsanancin ciwon ciki, wanda a wannan daren ta kasa tashi tayi sallar da ta saba yi koda yaushe, tana daga saman gado ba abunda take sai juyi haɗe da nishin azaba, tana cikin wannan halin bata san lokacin da ta faɗo daga kan gadon ba, ganin ba wani sarki sa ALLAH yasa ta nufi bakin ƙofa da rarrabe tana kuka game da faɗin "wayyo temako! zan mutu wayyo ciki na, dan ALLAH temako...." muryarta ba wani fitowa yake sosai ba Saboda tsantsar azaba daƙer take iya motsi da leɓɓenta, da haka tayi nasarar ficewa daga cikin ɗakin tana rarrabe ita kanta bata san ina ta nufa ba, ganin mutum tsaye a gabanta tsargagam ko motsi babu yasa ta dakata ta fara binsa da kallo tin daga ƙafarsa har zuwa ƙarshen kansa, sai dai abun mamaki yana sanye da baƙar hula a kansa da fuskarsa gaba ɗaya, a ruɗe ta juya zata koma daga inda ta fito mutumin yayi saurin cabko sumar kanta ya ɗagota sama yana ƙareta da kallo, ita kuwa ƙoƙarin ta shine taga ta zame masa tana so tayi ihu amma sai dai muryar ya shaƙe, a hankali ya furta "Baiwar ALLAH kwanakin ki sunzo ƙarshe, ki sani cewar Ƴar Amana tana hannu na, itama na kusan gama wa da ita, ku kukayi sanadiyar tarwatsa mun rayuwata, don haka saina kashe ku, zan fara ne daga kanki...." Baiwar ALLAH cikin firgici ido a zazzare daƙer ta iya cewa "wanene kai?..." kafin ta sake cewa wani abu ya haɗe kanta da jikin bango ya gwara nan danan jini kamar da bakin ƙwarya haka yake bleeding, yasa hannu ya toshe mata baki sannan ya kawo bakinsa saitin kunnenta yace "Ni sunana Ɓoyayyen mutum, ki shirya yin bankwana da duniya yanzu..." cikin zafin nama ya janyo ta saitin tagar beni sannan ya kifar da kanta ƙasin tagar yanda zatana kallon can ƙasin benin, Ita kuwa ba abinda take sai haki domin ba ƙaramin wahalar da ita yayi ba, ganin yanda ta zubawa ƙasin benin ido yasa ta fara jin hajijiya da jiri ga ido yanda ta zazzaro su tsabar tsoro da firgici game da tashin hankali, Dariya mutumin ya soma yi irin ta manya manyan mungwaye waɗanda suka shahara wajen yin mugunta, lokaci guda ya dakatar da yin dariyar yana huci yace "shin kinsan ina kike kallo? TOH mutuwarki kike kallo kuma yanzu zaki bita ku tafi...." kafin Baiwar ALLAH tayi wani motsi har ya ɗago da sawayenta ya dungurar da ita ƙasin beni mai tsayin gaske, kafin ta ƙarasa faɗawa ƙasi wani irin gigitaccen ihu tayi mai raunana kunnuwa wanda ba iya mutanen gidan Bama hatta masu gadi zasu jiyota...... A firgice ta yaye mayafin data rufe jikinta dashi tana kurma ihu kamar ranta zai fita, Da gudu wasu mata suka turo ƙofar ɗakin ta suna tambayarta cewar "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake haka kike ta ihu ko ina ana jiyo ki..." wata daga ciki ne itama tace "Baiwar ALLAH tinda muke dake bamu taɓa jin kinyi irin wannan ihun ba sai yau, shin me yake damunki haka?...." Ita dai Baiwar ALLAH haka take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya duk ta haɗa gumi kamar wacce ta watsa ruwa a jikinta, ga idanuwa yanda sukayi jawur sai jan numfashi take daƙer, abubuwan da suka faru da ita ne a cikin mafarki suke dawo mata ƙwaƙwalwarta, lokaci guda ta suma jin hajijiya da matsanancin ciwon kai, ganin batada ta cewa yasa ta fashe da kuka.... tsabar tsayin mafarkin da tayi bata san gari ya waye ba har ana neman wajen ƙarfe 8 gashi ko sallar asuba bata yi ba... Suna cikin tambayarta halinda take ciki saiga Madam ta shugo ɗakin ita da Aunty Habiba, tana shugowa taje ta samu bakin gadonta ta zauna cikin tausayawa takai hannu ta jawo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta tareda faɗin "kiyi haƙuri kinji koh! Habibah ta sanar mun duk halinda kike ciki, but don't worry I will find something else for you okay..." Madam ta kalli sauran matan da suke tsatstsaye a ɗakin tace musu "Please kuyi haƙuri ku fita kowa ta kama gabanta tana son hutawa..." hakan kuwa sukayi sai iya Aunty Habiba ce kawai ta tsaya, Madam ta kalli Aunty Habiba sannan tace "jikinta zafi sosai, Inaso zan kaita hospital yanzu, ki kula mun da Office ɗina duk wacce take buƙatar abu saiki bata Please...." Aunty Habiba ta amsa mata cikin girmamawa, Haka Madam ta tallafawa Baiwar ALLAH suka tashi tana janta a hankali har suka bar cikin ɗakin, a halin yanzu Baiwar ALLAH bata san a wata duniyar take ba domin ta rigada ta jikkata sosai, kana ganinta kasan babu jini a jikinta domin ba ƙaramin fari tayi ba har wani yellow ² tayi fuskar tayi fattt, da haka suka sauƙa down stairs, suna sauƙa kuwa tasa aka kawo mata motar ta har wajen da suka tsaya saboda majinyaciyar bazata iya zuwa har wajen parking ba domin ya yi mata nisa sosai, Lokaci guda Madam taji wuyan Baiwar ALLAH ya karye mata a saman kafaɗatar ta, a ruɗe ta kalleta ido a zazzare ganin bata motsi kwata-kwata, a tsorace Madam ta sakata cikin motar ta itama ta shiga ta buƙaci ɗaya daga cikin matan gidan ta shiga motar itama zata raka su, ai kuwa a ɗari Madam ta finciki motarta sai bakin gate...... MA SHA ALLAH SABODA RANAR FARKO NE YASA NA TURO MUKU PAGE ƊAN KAƊAN SBD WASU NASAN BASU DAWO A HUTUN SALLAH BA BUT NEXT DA YAWA ZANYI MUKU .... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (7) ꧁꧂ Ledar jini ne yake ɗiga ɗis! ɗis!! ɗiss!!! a yayin da ita kuma wacce take kwance a saman gadon hospital take bacci ido a lumshe gwanin burgewa, a hankali jinin yake shige mata hannun da aka ɗaura mata, haka take fitar da numfashi slowly, jin yanda sanyin A.C yake ratsa jikinta yasa ta ɗan soma mutsil-mutsil tana yatsina fuska still ido a lumshe, daƙer ta iya fara buɗe eyes ɗinta, a cikin tana ganin dishi-dishi har idon ya washe, haka take bin saman ceilling da kallo ko ƙibta idon bata yi, jin wani irin la'anannen ƙamshin turaren da yake bugan hancinta yasa ta ɗan juyar da kanta saitin yanda ƙamshin yake tashi, abinda ta fara gani shine zara-zaran yatsun hannu fari ƙall ga yatsun hannun sun sha zobina da warwaraye na gwal tana ɗauke da wata makekiyar waya wanda a ƙalla zai kai 2millions, ga wani danƙarariyar Abaya mai bala'in tsada wanda duk rigar a jere yake da duwatsu masu ƙalƙali da ɗaukar ido, a hankali take bin zazzafar ƙirar jikin matar dake zaune akan chair da kallo har zuwa kan kyakkyawar fuskar ta, ganin matar yasa ƙirjinta yayi wani irin bugawa a razane take ƙoƙarin tashi zaune ido a zazzare, a yayin da ita kuma matar hankalinta duk yana kan wayar hannunta sai daddannawa take alamun chatting take, tasha kitson Attach har gadon bayanta sai gyalen rigar da ta ɗora akanta... Daiden lokacin da Madam Aliya ta shugo cikin room ɗin hannunta riƙe da ledoji guda uku, ganin yanda Baiwar ALLAH take a razane idonta akan Madam Parveen yasa ta ƙaraso da sauri tana faɗin "Lafiya kuwa Baiwar ALLAH? kin tashi ne? ya jikin nakin?...." haka take jero mata tambayoyi tsabar yanda take jinta a ranta, domin tinda tayi ido huɗu da Baiwar ALLAH taji ta shiga ranta sosai da kuma tausayinta , tana ƙarasowa ta zauna a bakin gadon da Baiwar ALLAH take still idonta akan Madam Parveen, Madam Parveen jin shigowar Madam Aliya yasa ta ɗago da kanta tana binsu da kallo daga bisani ta tsayar da idonta akan Baiwar ALLAH yanda taga kallon da take mata kamar wacce ta santa... Madam Aliya tana riƙe da ɗayan hannun Baiwar ALLAH tace "Baiwar ALLAH shin kin santa ne kike kallon ta?...." A hankali ta soma girgiza kai alamar a'ah! Madam Aliya ta kuma cewa "ita ɗin Babbar Aminiyata ce, tare mukayi primary school to secondary, sunanta Madam Parveen, jami'ar C.I.D ce wato Agent Madam Parveen, Matar Chief of Defence staff General Suraj Mahendra Marka shugaban sojojin ƙasar Australia (U.S). Jiya ta shugo Nigeria domin gudanar da wasu ayyuka na kwana biyu daga nan ta koma can, ta kawo mun ziyara ne taji labarin ina nan hospital tare da ke shine tazo...." Tinda Madam Aliya ta fara kora jawabai Baiwar ALLAH ta sake baki tana kallonta tareda kasa kunne tana sauraron duk abinda take faɗi, bata ankara ba taji Madam Parveen ta dafa kafaɗarta tareda faɗin "what's ur name?..." Baiwar ALLAH girgiza kai kawai tayi domin ita kanta bata san sunanta ba... Madam Parveen ganin bata ba ta amsa ba yasa ta mata magana ta Hausa yanda zata gane, a tunaninta bata iya turanci ba ne, Ta kuma cewa "Dota Ya ya sunan ki?..." Madam Aliya ce ta kwashe da dariya jin har yanzu Madam Parveen bata ƙware a Hausa ba, wani irin harara Madam Parveen ta wurgawa Madam Aliya ganin dariyar da take yiwa Hausar ta, Ta ce "what are you laughing for?...." Girgiza kai kawai Madam Aliya tayi ba tareda ta ce komai ba sai ƙunsar dariya take... Madam Parveen sharar da Madam Aliya tayi ta juyo ta cigaba da tambayar Baiwar ALLAH cewar " wa ne ne ya sameki kike kwanta a hospital? typhoid or maleria? Ga babu jini a body naki sorry my Dota....." ɗaga mata kai kawai Baiwar ALLAH tayi domin bata san wani amsa ɗaya zata bata ba.... suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo da wasu nurses su biyu suna biye da shi, yazo duba lafiyarta sannan ya cire mata allurar jinin da aka ɗaura mata domin kaɗan ne ya rage, ya kalli Madam Parveen yace "ke ɗin Mamanta ne ko Auntyn ta?...." dasauri Madam Parveen ta girgiza kai tana faɗin "No no noo bani santa ba, I have a Daughter but I lost her since 20 years later.....". tana kaiwa ƙarshen maganar ta tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi sakamakon hawayen da yake shirin zubo mata.... Doctor ya girgiza kai sannan yace "sorry Madam I think you are her mother because naga kuna kama sosai ...." yana kaiwa nan yayi ficewarsa tare da nurses dake biye dashi! jin abinda Doctor ya gaya yasa Madam Parveen ta ɗago tana ƙarewa Baiwar ALLAH kallo tareda share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata, Ita kuwa Madam Aliya tinda Doctor yayi maganar nan take bin Madam Parveen da Baiwar ALLAH da kallo domin itama ta tabbatar da suna mungun kama sosai kamar wanda suka haɗa jini, bata lura da hakan ba sai yanzu, komai nasu iri ɗaya, har ta buɗe baki zata yi magana Madam Parveen ta katse ta da cewar " i known my Daughter she's already died since laters, Omg! inaso zan tafi...." ta kai hannu ta shafa sumar kan Baiwar ALLAH tana faɗin "take care Dota, Quick recovery okay .....". tana kaiwa nan ta tashi ta fice daga cikin room ɗin da sauri domin bata son shiga damuwa, saboda idan kana son ganin damuwar Madam Parveen shine ka kawo mata maganar Ɗiyarta Amreesha, nan danan zata rikice ta fara kuka ba ƙaƙƙautawa hakan yasa tayi saurin ficewa... Ganin haka yasa Madam Aliya itama tabi bayanta da sauri, suka fice a tare. Baiwar ALLAH jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, domin taji wani abu a jikinta amma har yanzu ta kasa kawo cewar tanada alaƙa da wannan matar Madam Parveen saboda ita ma ta fara tunanin cewar iyayenta mutuwa sukayi, nan ta shiga dogon tunani tana tambayar kanta "shin meyasa naji wani abu akan wannan matar? sannan meyasa ake cewa munyi kama alhalin bamu da wata alaƙa, amma kuma tace itama ƴarta ta ɓata tin shekarun baya, to me hakan yake nufi?....." haka zuciyarta take ta magana amma a zahirance girgiza kai ta rinƙa yi tana magana a fili cewar "a'a! a'a!! a'a!!! Bana son kalan dangi, idan iyayena suna a raye nasan wata rana zamu gana da juna amma idan har basa raye to na tabbatar haka zan cigaba da rayuwata cikin ƙasƙanci...." lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, ta zura hannunta a cikin rigarta ta ciro ƴar sarƙarta wanda yake ɗaure a wuyanta mai zanen Jesus Christ, tana murza sarƙar tana hawaye kanta na kallon ceilling, tana cikin wannan halin saiga Madam Aliya ta shugo tana ta surutu tin kafin ta shugo "Daman ai nasan bazata tsaya ta saurareni ba, ita idan aka kawo zancen Amreesh shikenam an rasa hankalinta, Allah dai ya bayyanar mana da ita idan kuma ta mutu Allah ya jiƙanta....." da haka ta zauna a bakin gado tana wannan surutun daga bisani tayi tagumi tareda sunkuyar da kanta ƙasi tana hura iskar bakinta, itama damuwarta ya isheta na rashin haihuwa tsawon shekara da shekaru amma haka take danne zuciyarta babu yanda ta iya.... Jin shishshitun kukan Baiwar ALLAH yasa ta ɗago da sauri tana faɗin "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake?...." Cikin kuka Baiwar ALLAH take faɗin "Mamanaaa! Abbanaaa!! Ina son ganinsu, Mommy and Daddy suna inaaaa? Kowa yana tareda iyayensa amma banda nii, wannan wata iriyar ƙaddara ce haka....." nan ta ƙara fashewa da kuka sosai mai cin rai, Daƙer Madam Aliya take rarrashinta cikin kulawa, tana bata haƙuri, Baiwar ALLAH ce ta rirriƙe hannayen Madam Aliya tana cewa "dan ALLAH ki temaka mun naga iyayena, dan ALLAH Aunty..." Ita kuwa Madam Aliya ta ƙafar da ƙwayar idonta akan sarƙar wuyan Baiwar ALLAH, cike da mamaki take bin baiwar Allah da kallo tareda sarƙar wuyan, tanaso tayi magana amma ta kasa lips ɗinta har rawa yake, domin tasan a yanda taga irin wannan sarƙar, Wannan sarƙar kaf Nigeria babu mai irinsa kuma Designer ɗin sarƙar a iya mutum ɗaya kawai akayi shi, Domin Madam Aliya bazata taɓa mantawa ba, ita da Madam Parveen suka je har ƙasar Maleshiya aka ƙero wannan sarƙar wa Amreesh, dake Madam Parveen su ɗin christal ne hakan yasa aka yi musu mai design ɗin zanen Jesus kuma ba ƙaramin kuɗi aka kashe wa sarƙan nan ba, Madam Aliya hannu na kakkarwa ta miƙar da hannunta saitin wuyan Baiwar ALLAH tana jujjuyar da sarƙar ata gefe da gefen sarƙar akwai yanda aka rubuta sunanta da ƙananun baƙi wato amreesh, A razane Madam Aliya tace "Amreesh...." tana bin fuskar Baiwar ALLAH da kallo sai a yanzu kamannun Amreesh lokacinda take ƙarama yake bayyanowa akan fuskar Baiwar ALLAH, A lokacin ba ƙaramin ruɗewa Madam Aliya tayi ba, muryarta har harɗewa yake gurin faɗin "Please juyo naga bayanki akwai abinda nake son gani...." Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take bin Madam Aliya da kallo kamar wata zautacciya, Haka Madam Aliya ta kwantar da Baiwar ALLAH kan cinyarta ta ɗage mata rigar jikinta saiga drowing photon bindiga ya bayyano, Madam Aliya bata san lokacin da ta fara washe baki ba tsabar farin ciki domin ta tabbata Baiwar ALLAH ɗiyar Madam Parveen ce, domin duk ƴaƴan Madam Parveen sunada wannan tambarin zanen bindiga a gadon bayansu, Yayun Amreesh su biyu Mohandas da Rakesh sai Amreesh hatta ita kanta Madam Parveen tanada wannan tambarin da Daddynsu shima, ba ƙaramin farin ciki Madam Aliya ta tsinci kanta a ciki ba, a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "bari nabi bayan Madam Parveen yau zatayi kwanan farin ciki...." tana kaiwa nan ta fice daga room ɗin da gudu... Ita dai Baiwar ALLAH sam bata fahimci komai ba sai sake baki datayi tana bin bakin ƙofa da kallo yanda Madam Aliya ta fice, abun ya ɗaure mata kai sosai..... Ita kuma Madam Aliya tana zuwa ta shige motarta a ɗari ta fice daga cikin hospital kai tsaye airport ta nufa domin Madam Parveen ta sanar da cewar ita komawa ƙasar U.S zatayi baza ta iya aikin da tazo yi ba saboda ɗiyarta Amreesha, kwata-kwata ta tsani nan ƙasar Nigeria..... Please help me and share dis book 🙏🏼🙏🏼🙏🏼 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (8) ꧁꧂ Madam Aliya hanyar airport ta nufa tana gudu tana ƙoƙarin ƙiran wayan Madam Parveen akan ta dakatar da ita daga tafiyar da zatayi, dan zai iya yuwa tana zuwa ta samu jirgin da zai tashi, ƙira akan ƙira amma Madam Parveen taƙi yi picking hakan yasa Madam Aliya ta ƙarawa motarta gudu.... Ita kuwa Baiwar ALLAH tana zaune abun duniya duk yabi ya isheta ga bala'in yunwar da take ji bata ci komai ba, idonta ne ya sauƙa akan ledojin da Madam Aliya ta shugo dasu, da sauri ta sauƙa akan gadon ta bubbuɗesu cikin sa'a ledar farko banƙararrun kaji ne a ciki sun sha eggs, sai leda na biyu soyayyun dankali ne da eggs sai shawarma ga lemukan gora da farro na ruwa, haka ta zauna ta fara tura su kamar wanda wani zai ƙwace, taci abinda zataci tabar sauran domin ba ƙaramin ƙoshi tayi ba, ta buɗe murfin gorar lemo tass saida ta shanye su, sannan ta miƙe ta nufi toilet tayi wanka tare da ɗauro Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah... ꧁꧂ ꧁꧂ ꧁꧂ Ɓangaren Ƴar Amana! tana zaune a bakin gado ta haɗe kai da gwiwa sai sumar gashinta da ya rufe mata kanta gaba ɗaya, tana jin buɗar ƙofar ɗakin tayi saurin ɗagowa domin ganin ko wanene ya shugo idonta duk yayi jawur tsabar kukan da take sha kullum, ganin wanda yake shugo mata kullum ne yasa ta ƙara fashewa da kuka saboda tasan bazai taɓa jin tausayinta ba balle yayi ƙoƙarin fitar da ita, mutumin koda yaushe fuskarsa a rufe take da baƙar hula, yauma kamar yanda ya saba haka ya shugo da wata ƴar leda wanda ba komai ne a ciki ba sai abinci jallof rice, yana zuwa gabanta ya wurga mata ledar abincin sai pure water da ya kuma jefa mata, da sauri ta rarumi ledar abincin ta buɗe a gaggauce ta wangame ɗan ƙaramin bakinta ta fara turawa ba ƙaƙƙautawa domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, abinci ne a rana sau ɗaya ake bata, idan aka bata yanzu sai kuma gobe shiyasa bata wasa waran cin abincin nan danan har ta lashe ta ɗauki ruwan shima ta gwangwaɗe, Shi kuwa Guest yana zaune ya kafa idonsa a kanta yana jiran ta kammala yayi mata abinda ya saba yi kullum domin bazai iya ganin Nama a gida ya barta ba dole zai ɗan rage zafi, tana kammalawa yasa hannu a cikin rigar sanyinsa ya ciro wata ƴar ƙaramar allura yana jujjuyata idonsa zuru-zuru acikin hular fuskar yana ƙareta da kallo, Ƴar Amana ganin allurar yasa ta fara ja da baya domin tasan allurar kullum sai yayi mata daga nan bata sanin abinda yake faruwa da ita saboda hankalinta fita yake daga jikinta sai bayan 24 hours take farfaɗowa, tana cikin karkaɗa masa kai da hannu bibbiyu tana roƙonsa domin babu bakin magana, bata san lokacin da ya yo sufa ya janyota jikinsa ya caka mata wannan allurar ba, daga nan bata ƙara motsi ba sai kanta da yake kan faffaɗar ƙirjinsa, yafi minti 30 yana kallon kyakykyawar fuskarta, sannan ya kwantar da ita kan gadon yasa hannu yana shafa sumar kanta da gefen fuskarta, yana jin wani abu sosai a ransa wanda shima kansa bai san dalilin hakan ba, yana mamakin kansa sosai abinda yayi niyar yi baya taɓa aikatawa, yana son kasancewa tare da yarinyar amma yana matuƙar jin tausayinta especially idan ya hasasho yawan shekarunta wanda bazata wuce 15yrs ba, sannan gata Kurmiya.. A razane ya miƙe daga kan gadon ya sauƙa kullum acikin haka yake bai taɓa aikata abinda yayi niyya ba saidai kawai yayi mata allurar, kuma daya kasance daman ba manemin mata bane, sam baya shiga harƙar mata wannan ma abinda yasa yake jin hakan a ransa saboda a fake suke kuma yarinyar tana matuƙar burge shi, bai taɓa jin wani abu akan wata yarinya ba sai akan Ƴar Amana, abun yana matuƙar ɗaure masa kai gata yarinya ce bata gama cika cikakkiyar mace ba, Wannan mutumin shi ake ƙira da GUEST mungu ne na asali akan abinda aka umarce shi, shima yana aiki ne a ƙarƙashin wani mai ƙarfin iko, baya taɓa bayyanar da fuskarsa kuma sannan baya shiga cikin gari sai cikin dare, ya kasance rayuwarsa a cikin daji ne da mutanensa manya-manyan ƴan daba masu kayan yaƙi, Itama ƴar Amana sashi akayi ya ɗaukota ya cigaba da riƙeta a gurinsa kafin a aiwatar da aiki akanta, shima kansa Guest bai san dalilin da yasa aka ce ya ɗaukota ba, sannan bai san mai za'a mata ba sai dai idan lokaci yayi a sanar masa idan har shine zaiyi aikin akanta, GUEST baya neman mata sannan baya shaye-shaye, idan kuwa aka bashi aiki akan kisa bayayi saidai shima yasa wani yayi, bashida tsoro sam sannan baya fargaban komai, baya aiwatar da abu da kansa saidai idan an bashi umarni..... ꧁꧂ ꧁꧂ Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya kusan awa uku sai faman addu'o'i take tana jiran shigowar Madam Aliya shuru-shuru har yanzu gashi ana shirin ƙiran sallar mangarib, tana zaune taji an turo ƙofar ɗaki, ɗagowar da zatayi taga Nurse tayi tunanin Madam Aliya ce domin ta gaji da zaman asibitin nan, Nurse tana shugowa tace "am kece wacce Madam Aliya ta kawo?..." Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga mata kai tareda faɗin "eh Ni ce..." Nurse taja dogon numfashi tare da girgiza kai tace "sorry for what am going to say...." Baiwar ALLAH idonta akan Nurse domin tana son jin abinda zata gaya ita har ranta so take taji Nurse tace an sallame su domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, Nurse tace "Doctor ya ce kada na sanar miki amma naga babu amfanin ɓoye miki tinda naga kinada tawakkali da sanin ƙaddara mai kyau ko akasin haka, kiyi haƙuri dan ALLAH, ALLAH yayiwa Madam Aliya Rasuwa sakamakon hatsarin mota akan hanyarta na zuwa airport....." Kafin Nurse ta ƙarasa maganar Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye da sauri ido a zazzare tana bin Nurse da kallo kamar wata zararriya, Nurse ta ƙarasa maganar ta da cewar "motarta ce ta shige cikin traller, yanzu haka tana nan mutuware zaki iya zuwa ki ganta...." tana zuwa ƙarshe ta juya ta fice tabar Baiwar ALLAH a sanƙare a wurin... Mutuwar Madam Aliya ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba, domin babu wanda bai santa ba saboda ba ƙaramar mata bace ta sanu sosai, anji mutuwarta sosai especially mijinta, Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Sai bayan isar Madam Parveen ƙasar U.S sannan ta biyo ƙiran wayan Madam Aliya ganin yawan miss call ɗin da tayi mata waran 30 missed call, abun ya bata tsoro sosai, kuma bawai taƙi ɗaukar ƙiranta bane wayar ce a silent, bayan ta ƙira jin muryar Namiji yasa ƙirjinta bugawa, a hankali ta furta cewar "where is madam Aliya?..." Mutumin yace "sorry Madam Parveen baki ganeni ba koh? Ni mijinta ne wayar tana hannuna sakamakon hatsarin motar da Hajia Aliya tayi, yanzu haka bata raye ta riga mu gidan gaskiya, har mun ɗaukota a mutuware tana gida za'a sallaceta...." duk wannan maganar ta turanci yayi mata, yana kaiwa ƙarshe ya katse ƙiran, Madam Parveen kamar a mafarki taji wannan maganganun, jin kanta tayi yana juyawa, a ruɗe ta fara girgiza kai tana faɗin "kai kai Kaiii i can't believe, Madam Aliya she never die, dis is a lie...." haka ta ƙara dialing number Madam Aliya tana ƙira amma ba'a picking daga ƙarshe akayi switch ɗin wayar, jin hakan yasa ta hau Social media a ruɗe domin ta ƙara tabbatarwa ai kuwa tana hawa abinda ta fara gani shine photon Madam Aliya ana sanar da labarin mutuwarta ta ko ina!... bata san lokacin data jefar da wayar gefe ba, haka ta ɗora hannu akai ta fara rausa ihu tana faɗin "Jesus! Jesus!! Jesus!!! Oh my God my Best friend...." ihu take kamar ta nitse ƙasi, ga bata samu kowa a gida ba balle a samu mai rarrashinta..... Baiwar ALLAH tinda taji labarin mutuwar Madam Aliya tasa ƙafa tabar hospital bata tsinci kanta a ko inaba sai akan titi, tafiya kawai take tana kuka ita kanta bata san ina zata je ba, rabonta data taka saman kwalta tin tana ƴar yarinya, tana tafiya har dare yayi mata a hanya, Ganin bata san ina zataje ba yasa ta samu guri a bakin wani ShopRite ta zauna, ta zuba uban tagumi hawaye yaƙi tsayuwa, tana cikin wannan halin saiga wasu maka-makan motoci kusan guda 15 a jere sun zo sun wuce, a razane ta miƙe tsaye tana ɗaga musu hannu tare da ɗaga murya tana faɗin "Dan ALLAH temako! temako!! temako!!!...." haka tabi bayan motocin da gudu saboda taga basuda niyyar tsayuwa kuma ba lalle su jiyota ba, tana cikin binsu da gudu taga sun sha wata kwana duk da tayi mungun gajiya amma haka ta daure itama tasha kwanan da sukabi tana haki numfashinta har ƙoƙarin ɗagewa yake tsabar gudun data sha, ita kanta tayi mamakin yanda ta iya bin motocin nan da gudu, tana shan kwanan da motocin suka bi ta fara ganin wani irin haske mai kashe ido sai walwali hasken yake yana bada haske kala-kala, ga wasu maka-makan gidaje wanda daƙer zaka iya ganin tsayin gidajen, unguwar yanda kasan a wani country yake, ko wane gida da kalar haskensa wannan yana bada hasken red wannan gidan hasken blue wannan green wannan white wannan purple wannan yellow kala-kala gasunan, babu alamar duhu a unguwar haske ta ko ina, wannan unguwar shi ake ƙira da Aljannar duniya, domin duk wanda ya shugo unguwar nan bazai so fita ba saboda tsaruwar da yayi, unguwa ne na manya-manyan masu kuɗi na gaske, gidajen ministoci ne da govrnoni, da Generori gasu nan dai, Baiwar ALLAH ta kasa tsayar da gudun sannan kanta na kallon sama sai kallace-kallacen gidaje da ta tsaya yi still bata dena gudun ba, ita har ta manta mai take bi da gudun, gaba ɗaya ta shagaltu, bata tashi ankara ba saida taji an girbe mata ƙafa da ƙarfi wanda saida tayi sama kafin ta doku a ƙasin floor wanda duk unguwar a zagaye yake da floor babu ƙasa ko ɗaya, Goshinta ne ya bugu da ƙasi bata san lokacin da ta sau ƙara mai ƙarfi ba, lokaci guda tayi shuru saida ta ɗau kusan minti 30 kanta a kife kafin ta soma motsawa a hankali tsabar buguwar da tayi hatta jikinta saida yaji, A hankali ta fara ɗago kanta ga goshi har ya fashe sai jinin da yake zuba, lumshe idonta ta fara yi saboda tsananin hasken da yake shirin kashe mata ido, ba hasken komai bane illa hasken unguwar da kuma layin gidan data biyo wanda layin gidan yake cike da manya-manyan security sojoji masu jajayen handkerchief a ɗaure saman goshinsu, Baiwar ALLAH ganin sawun takalmin sangamemen soja a gabanta yasa ta fara bin ƙafar da kallo tana binsa da kallo har saida ta ɗage kanta sama sosai kafin ta iya ganin fuskar mutumin yana ɗaure da jan ƙyalle akan goshi sai huci yake, mai ƙirar samudawa jikinsa sai zaƙami yake yana sanye da kakin sojoji, Ganin wannan soja yasa ta ƙara kifar da kanta alamar suma tayi........... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 9 to 10 ꧁꧂ a hankali take ƙoƙarin buɗe idonta daga doguwar sumar da ta tafi, jin tanata lilo ta kasa tsayuwa guri ɗaya yasa tayi hanzarin buɗe idonta a gaggauce domin taga a wani hali take, bata tsinci kanta ba sai a saman ƙarfen transformer ata Tsakiya an ɗaure mata ƙafafu kanta na kallon ƙasa sai lilo take kamar igiyar shanya, ganinta a haka yasa kanta ya fara juyewa saboda ganin ƙasa take kamar zata faɗo ga anyi sama da ita sosai nan danan ta fara jin hajijiya bata san lokacin data rausa uban ihu ba a kiɗime, wani soja ne a gurin yana tsaye zaman gadinta a yayin da sauran sojojin suke can bakin aikinsu na tsaron layin gidan General, dake transformer ata bayan layin yake can akaje aka ɗaure Baiwar ALLAH.... ihu take bana wasa ba shi kuwa yana tsaye ko kulata baiyi ba, sai wayar hannunsa irin wanda sojoji suke aiki dashi ya kara a wajen bakinsa yana magana ta turanci cewar "wannan yarinyar pah ta tashi, ya za'ayi da ita?...." amsa ɗaya aka bashi sannan ya katse ƙiran ya ɗaga kansa yana mata wani iri kallo da jajayen idanuwansa, shima kansa saida ya ɗaga kansa sosai kafin ya yake iya kallonta domin da igiya aka jata sama, zuwa yayi ya since igiyar da aka ɗaura a jikin transformer sai gata ta tafo zuuuuu tayo ƙasi, sauran kaɗan kanta ya doku da ƙasa sojan yayi saurin tarota sannan ya zaunar da ita domin ƙafafunta a ɗaure suke guri ɗaya, kwana tayi a saman transformer jikinta ba ƙaramin ciwo yake mata ba tare da hajijiya duk ta gama haɗa gumi tayi jirippp, Gani tayi sojan ya durƙusa a gabanta ya ƙafe mata jajayen idanuwansa yana riƙe da ƙarfen shocking a hannunsa ganin shocking yasa ta zazzaro manya-manyan idanuwanta waje tana karkaɗa masa kayi tareda haɗiyar wata nannauyar yawu wanda ya tsaya mata a maƙogaro, Shima ido ya zazzaro mata murya a dire yace "wacece ke?..." Cike da firgici murya a shaƙe cikin ƙinƙina ta soma cewa "wallahi wallahi Ni ba kowa bace, bansan kaina ba...". kuka mai ƙarfi ne ya yanko mata, A tsawace ya daka mata tsawa tare da faɗin "shut up! ur very stupid, I asking you who are you, and what are you planning?..." tana maƙale da murya tace "dan ALLAH kuyi haƙuri ku barni in tafi wallahi ban san ko inaba bansan kowa ba?...." bata ankara ba taji sauƙar zazzafar mari akan fuskarta har sai da lips ɗinta ya fashe, ga goshi a fashe yanda aka girbeta, buɗe baki tayi ta fara kuka ya ƙara ɗaukan hannu zai mareta tayi saurin yin shuru tareda ƙanƙame idanuwanta, cikin zafin nama irin na sojoji ya sauƙar da hannunsa ya fasa marinta ya miƙe tsaye yana faɗin "zakiyi bayani...." haka ya tafi ya barta a wajen ƙafa a ɗaure tareda hannaye, tasha kuka sosai kamar ranta zai fita kamar yanda ta kwana a wajen haka tin safe take nan har ana ƙiran mangarib yanzu, yunwa da ƙishi ba ƙaramin azabtar da ita suke ba, sai a lokacin wani daga cikin sojojin ya waiwayo ta wannan kam yafi wancan zafin rai domin yana zuwa ya sameta harta gyangyaɗa tana shan baccin azaba, cike da mugunta ya jona mata shocking dake hannunsa a saitin ƙirjinta, tana bacci bata san lokacin da ta zabura ta rausa uwar ƙara har sai da sojan ya toshe kunnensa, daga nan ta nemi hankalinta ta rasa ta sume a gurin, Su sunyi tunanin ko ƴar mafiya ce, ko kuma tazo da abun cutarwa domin ba kowa ne yake shugowa cikin unguwar nan ba sai masu arziƙi na gaske waɗanda suka sanu, hannu yasa ya fara bubbugata amma shuru ko motsi babu hakan yasa yaja uban tsuka yace "foolish girl, raguwar banza....." haka shima ya tashi yayi tafiyarsa, a waran Baiwar ALLAH ta kwana a sume saida gari ya kuma wayewa kafin Allah yasa ta farfaɗo da matsanancin ciwon kai, ga sanyin duniya ga yanda ƙwari suke hawa kanta wasu na cizonta, a kwana biyun nan har ta fita hayyacinta tayi baƙi, idanuwa sun shanshanye duk ta rame, tana cikin wannan yanayi na ƙunci idonta na kallon gefe guda kamar mai tunanin wani abu sai hawayen dake tsiyaya kamar pampo, bata san lokacin da wani daga cikin sojoji yazo ya tsuguna a gabanta ba ya ƙura mata ido, gyaran murya yayi mata ganin har zuwa yanzu bata san da mutum a gurin ba, a zabure ta waigo ta kalle shi, ganin soja ne yasa ta zaro ido waje tana shirin fashewa da kuka domin a yanzu bata ƙaunar ganin ko wani soja, ta tsani ganin kakin sojoji balle su kansu, Ganinsa yasa ta saddaƙar cewar shima da kalar muguntar da zaiyi mata, kula ya ajiye mata a gabanta da pure water yana faɗin "sorry ba cutar dake Zanyi ba, abinci na kawo miki...." yasa hannu ya buɗe kular abinci yana ƙoƙarin saka spoon zai bata a baki ganin hannayenta a ɗaure suke kuma ba'a bashi damar sinceta ba domin shima yaron su ne bashida wani iko akai, Babu yanda ta iya haka take buɗe baki daƙer yana bata domin yunwar da take ji yana shirin fin ƙarfinta kwana biyu batasa komai a cikinta ba ga azabar da ake gana mata, haka ta kammala cinye abincin tass ya bata ruwa tasha, tashi yayi zai tafi domin ya gama aikinsa tayi saurin dakatar dashi tare da cewar "dan ALLAH yaushe za'a since Ni? na gaji sosai Inaso na nemawa kaina mafita, bansan komai ba, bansan kowa ba, dan ALLAH ka temaka mun, tinda har ka ciyar dani da hannunka nasan akwai imani a tattare dakai dan ALLAH......" Dogon numfashi yaja sannan ya juyo ya kalleta cike da tausayawa ya dawo gabanta ya tsaya yace "kiyi haƙuri da zan iya temaka miki da zan temaka ko baki ce ba saboda nasan a halinda kike ciki, banida wani iko akai duk oganni nane amma kiyi haƙuri ki ɗan jira General ya dawo yau insha ALLAHU zai dawo daga ƙasar Egypt yaje wa Yaronsa Doctor Roshan visiting sannan yau yake Birthday jiya ya tafi amma yau yana kan hanyar dawowa, da zaran ya dawo za'a sanar masa halin da ake ciki, zai buƙaci ya ganki daga nan zai iya temaka miki domin mutum ne mai son mutane da temako amma sai idan kin sanar masa gaskiyar cewar ke wacece sannan daga ina kike, mai kika zo yi, waya turoki idan kika sanar masa gaskiya toh zai temaka miki, amma idan kika ɓoye masa gaskiya General yanada saurin kama mai laifi zakiyi bayani, saboda haka You better known what are you going to say...." yana kaiwa nan yayi tafiyarsa.... wani abu ta haɗiya kamar wanda ta haɗiyi dutsi tsabar takaici, lokaci guda ta fashe da kuka mai cin rai tare da faɗin "Yaa ALLAH ka dube Ni da idon rahama, ya Allah ka kawo mun sauƙi acikin lamura na, Yaa ALLAH kasa na cinye wannan jarabawar da nake ciki, ina cikin mawuyancin hali amma nasan ƙaddara ta ce tazo mun a haka, ya Allah kada kasa na wuce a haka, Yaa ALLAH ka fini sanin yanda ƴar uwata ƴar Amana take, Allah kada kasa ta kasance a irin halinda nake ciki domin ita ɗin bata san ciwon kanta ba har yanzu, Allah ka temake mu....." haka take kuka tana kaiwa Allah kukanta, tin daga safiya har zuwa yamma misalin ƙarfe 5 babu sojan da ya ƙara waiwayota sai yanzu, yana zuwa yasa hannu ya fincikota yasa ƙaramar wuƙa ya yanyanke mata igiyar da aka ɗaureta dashi, yana nan fuska ba Annuri wannan daga ganinsa babu wasa, Baiwar ALLAH kai a sunkuye domin bata ƙaunar haɗa ido dashi domin ta gane shi shine wanda ya shona mata shocking, yana gamawa ya miƙar da ita sannan yaja ta akan su tafi, bata ankara ba tajita a ƙasi sakamakon kumbura da ƙafarta yayi bazata iya tafiya ba a halin yanzu, ƙafar ba ƙaramin ciwo yake mata ba ga hannu ya ɗangale babu halin miƙar dashi tsabar tsamin da yayi shima ya kumbura sosai, ganin haka yasa sojan bai jira wata-wata ba ya ɗagata ya ɗorata saman kafaɗarsa ganin zata ɓata masa lokaci.... Saida sukayi tafiya mai nisa kafin taga sun iso layin wani ƙanƙararren gida wanda kana shigowa layin ka daina taka ƙasa sai floor, ga wasu zankaɗa-zankaɗan sojoji kusan su ashirin ko wanne yana riƙe da ƙatuwar bindiga ga jajayen ƙyalle a ɗaure saman goshinsu idanuwansu jajaye babu alamar wasa a fuskarsu, tana saman kafaɗarsa amma tana ƙare ko ina da kallo amma bata bari ta haɗa ido da soja ko ɗaya ba, gani tayi an buɗe musu wani makeken gate wanda ya tsaru mai tsayin gaske, ginin gidan gaba ɗaya a zagaye yake da tiles, suna shiga ciki wasu sojoji ta ƙara gani su biyar sun ƙame guri ɗaya ko motsi babu, ga jerukan motoci kala-kala ko wanne da design ɗinsa da kuma kamfaninsa sun kai guda ashirin domin duk ƴan gidan babu wanda bashida mota duk ba'a barinsu suyi driving saidai security yakaisu duk inda zasu je, ga wasu irin flowowi na alhurma masu kyan gaske, a cikin motocin ne ya zaɓi guda ɗaya ya saka Baiwar ALLAH a seat ɗin baya sannan shima ya shiga, domin babu yanda zaka iya shiga gidan ba tare da mota ba, saida suka ƙarayin tafiya mai nisa kuma du wasu security suka ƙara buɗe musu wani gate na biyu, suna shiga taga wani makeken swimming pool a tsakiyar filin gidan wanda a tsakiyar ruwan wani abu kamar flower ne yake bada feshin ruwa sai ruwan yayi sama kafin ya zubo a cikin S-pool amma sai dai wannan swimming pool ɗin bana wanka bane just anyi shi ne don ado domin flowers ne a ciki, saida suka zagaya wannan S-pool tukun zaka iya bi ta ɓangaren dama sannan zaka iya zagayawa ta ɓangaren hagun domin a tsakiya yake, ta order side wani makeken filin ball ne wanda yake can nesa dasu, nan ma suka sake miƙar hanya, ata gaba aka sake buɗe musu wani gate na uku kuma du, Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi ganin tafiya taƙi ƙarewa, saita fara tunanin kodai gidan masu satan mutane ne, nan danan gumi ya fara keto mata, wannan part kam basu yi wata tafiya mai nisa ba taga anyi parking a waran ajiye motar, cikin zafin nama yasa ƙafa ya ture murfin motar sannan ya zagayo ya ɗauketa saman kafaɗarsa, kai tsaye cikin compound suka nufa anan ne part uku ya kasu, part ɗin da yake ɓangaren dama suka nufa nan ne babban falon General wajen da yake ajiye manyan baƙinsa, part ɗin da yake tsakiya kuma babban part ne wanda ɗakunan kowa yake ciki idan ka shiga ciki yayi jirgi ya sauƙa a iya falon kawai tsabar girmansa, Baiwar ALLAH kallon gidan take a baibai domin tsarin gidan ya fara wuce misali, ganin kanta take kamar ba'a Nigeria take ba, ga wani irin sanyi mai daɗin gaske yanda yake ratsa sansanin jikinta, gidan ne ta ko wane ɓangare ansa A.C mai bada sanyin gaske, da cemerori ga flowowi masu bada nasu sanyi suma, tana cikin wannan yanayin bata san lokacin da aka direta ƙasi ba, saita para tangal-tangal zata faɗi ƙasi domin ji take kamar zata nitse ƙasi ne tsabar tudun carpet da laushisa, ko ciwon ƙafar ma ta daina jinsa tsabar yanayin jin daɗin data tsinci kanta a ciki, weather falon Chief of Army's mAh ya isheta jin daɗin rayuwa, ga wani irin ƙamshin da yake badawa, falon ta tsaya kallo gaba ɗaya ta rikice tsabar tsaruwar falon, kafin General ya fito daga cikin order room ɗin na falon domin nan ne bedroom ɗinsa idan yanason hutawa, Sojan yana mata magana akan ta zauna amma sam bata jin mai yake faɗi tsabar hankalinta yana kan tsaruwar falon, cike da takaici yasa ƙafa ya girbe mata ƙafafu sai yaraf ta faɗi a ƙasan carpet, a nan ne ta dawo cikin hayyacinta, faɗuwar da tayi a ƙasan carpet mai makon taji ciwo saima ƙara miƙewa da tayi ta baje tayi shame-shame tana lumshe ido a hankali, tama manta ina suka zo, sanyin falon ne da ƙamshinsa duk ya ruɗe ta, wani irin harara sojan ya wurga mata amma ko kallon yanda yake batayi ba, yana shirin yi mata mugunta yaso ya taka ruwan cikinta saiga General ya fito yana sanye da jallabiya fara har ƙasi, yana ganin Baiwar ALLAH a kwance bai wani damu ba saima murmushin da ya sake tare da zama yana gyaran murya, jin anyi gyaran murya yasa ta firgita ta tashi a zabure tana kallace-kallace, daƙer ta iya tsayar da idonta akan General ta ƙura masa ido kamar wanda ta sanshi, a cikin zuciyarta tana raya abubuwa da dama a cikin ranta take faɗin "wannan kamar na sanshi, wasu lokuta yana zuwa gidan marayu, tabbas shine domin daman soja ne...." General maida idonsa yayi kan sojan yace "Tall man ya akayi ne?..." Anan Tall man ya kwashe Abinda ya faru ya sanar masa amma bai sanar masa zaluncin da sukayi mata ba, ya ƙarasa maganar da cewa "daman mun riƙeta ne akan saika dawo tukun, duk hukuncin da ka yanke shi zamu aiwatar...." General ya jinjina kai ya maida idonsa kan Baiwar ALLAH....... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (11 to 12) ꧁꧂ Ƙura mata ido yayi kamar me tunanin wani abu, ita ko bata san yanayi ba sai kallace-kallacen da take, daga bisani ya ce "meye sunan ki?..." kamar daga sama taji Muryar ya ɗuro mata kan dodon kunne a firgice tace "amm Baiwar ALLAH..." cike da mamaki yace "ke ki gaya mun sunan ki saiki tsaya kina mun shirme, what do you means?..." kamar zatayi kuka ta kuma cewa "wallahi tallahi bansan sunana ba, haka na tashi naji ana ƙirana da Baiwar ALLAH..." Tallman dake tsaye ganin yarinyar tana shirin rainawa Ogansu hankali yasa yayi saurin kai mata ƙafa a saitin baki, ya yinƙuro Kenam General yayi saurin ɗaga masa hannu alamar ya dakata, cike da mamaki General yace "daga ina kike? sannan me kika zo yi nan area?..." Baiwar ALLAH kuka ta soma yi ta kwashe komai ta sanar masa, bata ɓoye masa komai ba, Jinjina kai General yayi sannan yace "Kenam kece yarinyar da Hajia Aliya ta bari a hospital?..." dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga masa kai cike da fargaba, Jinjina kai General yayi sannan yace "ina sane dake daman, kafin rasuwar Hajia Aliya ta bani duk wani information ki, ta ce kina cikin damuwa zaman gidan marayu bazaiyu ba domin akwana a tashi wata rana zaki wayi gari bakya doron duniya, hakan yasa na yanke shawarar idan an sallame ku a hospital saita kawo ki nan gidana ki cigaba da zama kafin Allah yasa a samu iyayenki, daga baya nake jin labarin mutuwar Aliya, naje har hospital domin duboki amma bakya nan kin tafi, Yanzu dai tinda Allah yasa kin kawo kanki yanda zaki zauna ki cigaba da rayuwarki cikin ƴanci Alhamdulillah...." Baiwar ALLAH farin ciki kamar bazata mutum ba, sai murmushi take ta zabgawa ganin a gidan da zata zauna, amma lokaci guda data tuno da Ƴar Amana sai taji kamar ta rausa ihu, babu yanda ta iya haka take danne zuciyarta domin bata son General ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita... General ne yace mata "tashi maza na kaiki ciki yanda mutanen gidan suke koh?..." Dasauri ta miƙe tana ɗingishi daƙer take jan ƙafar, General ganin haka yasa shi cewa "what! meya faru dake haka?..." Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "babu komai" idonta akan sojan dake tsaye yana jinsu, General idonsa yakai kan sojan cikin ɓacin rai yace "ku baku san mace bace? daga ganin mutum baku san dame yazo ba shin da Alkhairi ne ko da sharri baku sani ba, just kun fara ɗaukar hukunci akai, wani irin abu ne haka? ku kiyaye saurin ɗaukar hukunci banaso...." Sojan dake tsaye yana kallon gabansa ya ce "Yes Sir, Insha Allah zamu kiyaye..." daga baya General ya ɗaga masa hannu akan ya wuce, Bayan fitar sa itama Baiwar ALLAH fitowa tayi tare da shi General, kai tsaye compound dazai sadasu da cikin babban falon na gidan suka shige, General ganin yanda Baiwar ALLAH take ta kallace-kallace yasa ya riƙo hannunta suka ƙarisa shigewa, a cikin babban fallon suka tarar da kowa na gidan duk sun hallaru dake a yau Aunty Yolash dake Bauchi itama tazo ta abunda ya kawota shine ta'aziyyar Hajia Aliya, Hajiya Kilishi ce zaune itama da zankaɗa-zankaɗan ƴan matan gidan wato yaran Hajia Kilishi dake duk yaranta mata ne su biyar, Babbar cikinsu wato Minal tana kwance akan sofa 3 seater ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana sanye da gajeren jeans wanda ya tsaya mata a iya gwiwa sai faman daddanna wayar hannunta take mai ƙirar iphone 15 sai tauna ciwgum take tana ƙararass, asalin ƴar girman kai kenam ga iya ɗaukar fashion, bata hulɗa da ƙananun mutane sai manya-manyan ƴaƴan masu kuɗi kamar yanda take ƴar Babban mutum, ta tsani ganin talaka marar class a rayuwarta, yanzu tanada shekara 25 ta kammala Degree ɗinta a ƙasar England..... Sai waɗanda suka biyo bayanta wato Pinky and Ruky ƴan biyu ne duk mata Hajia Kilishi ta haifa, waɗannan yaran sune masifaffun gidan, banda wulaƙanta mutum ba abinda suka iya, ga gadara da isa da burga, Pinky and Ruky their are too stubbornness, yaran masu kuɗi kenam jiki duk madara, su biyu suna kwance suma akan 5 seater wannan ta ɗorawa wannan ƙafa wannan ma haka, sai faman danna wayoyin hannayensu suke maka-maka, yanzu suke da shekara 20 cif cif suna karatun Degree ne a ƙasar London..... Sai gambonsu wato Ummy dake zaune a 1 seater ta nannaɗe ƙafafuwa ta sanya farin glass akan dararan idanuwanta kana ganin glass ɗin kasan na medical ne mai tsadar gaske, dake tanada matsalar ido, tana riƙe da ƙaramin littafin Alkur'ani mai girma baki da motsi a hankali take karantawa acikin zuciyarta domin yayunta sun tsawatar mata akan cewa kada ta toshe musu kunne da karatunta, Ummy uwar masu gida Kenam, full name Maryam mai sunan mahaifiyarsu General da mai martaba sarkin ƙasar Jidda da kuma Aunty Yolash, Ummy batada matsala ko kaɗan Sarkin haƙuri, bata fiye yin magana ba, ta kammala Secondary school anan school of Nursing, ana son turata ƙasar waje akan taje ta cigaba, tace ita bata son zuwa ƙasar waje tafison tayi school anan Nigeria dalilin da yasa bata cigaba ba Kenam saboda mahaifiyarta Hajia Kilishi tace nan duniya duk ƴaƴanta babu wacce zata cigaba da school a nan Nigeria tace saidai yarinyar tabar karatun kwata-kwata indai a Nigeria zata yi, shiyasa Hajia Kilishi bata sa Ummy a ranta ba saboda ita kaɗai ce bata ɗauko halinta na rashin mutunci ba, yanzu Ummy uwar masu gida tanada shekara 17 a duniya amma sai halin dattawa...... Daga kan Ummy Hajia Kilishi ta dakatar da haihuwa domin a cewar ta yawan haihuwa yana lalata mace, bata son tara yara kamar ɓeraye a gida, waɗannan huɗun sun isheta Minal, da twins Pinky and Ruky sai Ummy, bayan nan ta ɗau shekaru bata sake haihuwa ba sai daga baya ta samu cikin Ƴar Tiny ba'a son ranta ba, bata san ya akayi ta samu cikin ba domin ba ƙaramin planning tayi ba, anan sun samu matsala sosai da General mijinta akan saita zubar da cikin, shi kuwa yace saidai ya sake ta, haka ta haƙura babu yanda ta iya harta haifi Ƴar Tiny, tasha wahala sosai Saida aka mata Operation, ganin mace ta ƙara haifa yasa tace a cire mata mahaifa saboda ta fidda rai akan samun yaro namiji gashi yara sun taru mata, tayi kuka sosai duk yaranta babu namiji... Ƴar Tiny yanzu shekarar ta 5, fitinanniyar yarinya ga rashin jin magana da yawan ɓarna, Ita kaɗai ce a tsakiyar falo tana zaune akan carpet sai wasa da ƴar tsanarta take tana mata kitso, Aunty Yolash itama tana zaune akan kujera 2 seater idonta akan wayar hannunta tana jiran shigowar General tanaso tayi masa sallama zata koma Bauchi, A yayinda ita kuma Hajia Kilishi take kan 3 seater itama tana press ɗin wayar ta tana tauna ciwgum, inta ɗago saita harari Aunty Yolash domin basa jituwa sosai akwai ƴar tsama a tsakaninsu, Ita Aunty Yolash a rayuwarta ta tsani mutum ya cika wulaƙanta ɗan Adam don yanada ƙarfin iko, shiyasa Aunty Yolash bata shiri da Hajia Kilishi domin halinta Kenam wulaƙanci da girman kai gashi harta koyawa yaranta banda Ummy wacce ta fita daban a cikinsu sai Tiny wacce ita yarinya ce ba'a san wata kala bace ita.... Suna cikin wannan halin saiga General ya shugo yana riƙe da hannun Baiwar ALLAH da sallama a bakinsa, Baiwar ALLAH gaba ɗaya tayi bususu da ita ga ƙafa ba takalmi ga tayi wani irin datti har farinta yaɗan disashe, Aunty Yolash ce da Ummy kawai suka ɗago tare da amsa masa sallama a yayinda ita kuma Hajia Kilishi da sauran yaran ko ɗagowa basuyi ba domin sun san da cewar Abbansu ne ba wai wani ba, Ƴar Tiny ce ta tashi tana faɗin "Abbah Oyoyo! Abba ina abinda nace a siyo mun, ina alƙawarinaaa...." Abbah yace "kiyi haƙuri Auta ki bari sai kowa yayi bacci da daddare zan baki kinji koh...." turo baki Tiny tayi ta ce "toh Abbah wacece wannan yarinyar..." ta ƙarasa maganar tana farfara ido, kama kuncinta yayi yana wasa da ita yace "Auntyn ki ce?..." Ƴar Tiny ƙara turo baki tayi tare da faɗin "cabb ɗin wannan mai dattin ce Aunty na?..." Hajia Kilishi dasauri ta ɗago domin tabbatar da abinda ƴar Tiny take faɗi, ai kuwa idonta ya sauƙa akan Baiwar ALLAH nan take ta miƙe tsaye tana harararta cike da takaici ta ce "wannan kuma aina ka samota General?..." ya ɗago yana kallonta yace "Baƙuwa kukayi kuma zata cigaba da zama ne acikin gidan nan...". A zabure Hajia tace "whattt!!!! Impossible I swear, ko wani jaki da dabba da alade sai a kawo mana gida? TOH yarana ma sun isheni bana buƙatar ko wani ƙazami ...." cike da takaici General Yake binta da kallo, ya girgiza kai sannan yakai idonsa kan Aunty Yolash wacce ta taso tazo gaban Baiwar ALLAH ta kamo hannunta tana faɗin "your welcome Baƙuwar mu ki shugo kinji koh...." Fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, ta zaunar da ita akan kujera, Baiwar ALLAH ganin kallon da Hajia Kilishi ke mata yasa tayi saurin zamewa ƙasin carpet tace "a'a Aunty a ƙasi ma ya isa...." Minal juyowa tayi tana wurga mata harara lokaci guda taja tsuka ta cigaba da press ɗin wayar hannu ta, Pinky da Ruky ƙusu ƙusu suke suna magana ciki ciki Pinky tace "zata ci durun uwarta ne tinda ta kawo kanta kurkukun azaba..." Ruky tace "barta Ni kaɗai ma na isheta saita ƙwammace gwara tayi zaman daji wallahi, ai ina Abbah ba mazaunin ƙasar nan bane to ai tazo da sauƙi...." haka suketa wannan mita a junansu.... General ne ya kalli Ummy uwar masu gida da murmushi akan fuskarsa domin aduk lokacin da ya kalli Ummy ko yana cikin ƙunci sai yaji sanyi a ransa, yana matuƙar ji da ita sosai ga mai sunan mahaifiyarsa ce Abar ƙaunarsa, Yace "Uwar masu gida ga Abokiya na kawo miki...." itama murmushi tayi ta taso daga zaunenda take tare da ajiye littafin Kur'ani tazo yanda Baiwar ALLAH take itama ta zauna a ƙasin carpet ta rungumeta tana faɗin "Abbah ai wannan tafi ƙarfin Abokiya sai dai Aunty...". ta kalli Baiwar ALLAH tace "Barkan ki Aunty nah...." Itama Baiwar ALLAH murmushi ta saki tana kallon Ummy ga glass ɗin yayi mata kyau sosai gata fara ce itama tass, Hajia Kilishi ta dararawa Ummy tsawa tace "taya ta zamo Auntynki dan ubanki munafukar banza...." tanayi tana kallon General domin in kanaso ka ƙuntata masa TOH ka zagi Ummy, anan zaku samu matsala, kafin ta ankara ya wurga mata wayar hannunsa zai kai mata mari Aunty Yolash tayi saurin riƙo shi tana faɗin "kayi haƙuri Yaya, ka ƙyaleta abinda take nema kenam, tinda bata kama girmanta ba kai kuma saika nuna mata ka fita sense ko dan saboda yaran gurin nan...." General yana Huci ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, Hajia Kilishi tana hararar Aunty Yolash tace "Ni ce banida hankali Kenam, ki tsaya a iya matsayinki na ƙanwar mijina karki nemi ki shiga mun gonata wallahi...." Aunty Yolash ta dubeta dakyau sannan tace "daman ke har gona ce dake? Mttssw....." General cikin ɓacin rai yake kallon Hajia Kilishi yatsarsa akan Baiwar ALLAH yace "akan wannan yarinyar zakiyi sanadiyar rasa igiyar Aurenki wallahi tallahi...." Dasauri Hajia Kilishi ta juyo tana kallonsa cike da mamaki. Minal dake kwance Saida ta miƙe zaune tana faɗin "whatttt!...." Pinky da Ruky kam sake baki sukayi jin abinda Abbansu ya gayawa Ammynsu... Minal tashi tayi taja dogon tsuka zata haura upstairs yanda ɗakinta yake, Abbah ya darara mata tsawa yana faɗin "your very stupid, Amina are you mad? ina magana shine zaki ja mun tsuka kibar mun gurin? Ko mahaifiyarki gata nan batada wannan ikon da ina cikin mata magana taja tsuka tace zata bar gurin, Amina ki kiyaye Ni i swear to God zan rufeki a gadurun kiyi kwana biyu muga girman kan nakin..." ya cigaba da cewa "wallahi tallahi duk yarinyar da naji labarin tana musgunawa yarinyar nan saina sa an rufe ta a barrack aita azabtar da ita kunji da rantse koh, ku bar ganin bana zama a Nigeria duk inajin labarin rashin mutuncin da kukeyi, kuna jamun magana a gari a matsayina na General Sojoji amma ƴaƴana babu tarbiyya tirr wallahi...." Pinky ce ta kalli Ruky a hankali tace "kuttt buro ubaaa akan wannan matsiyaciyar za'a rufe mu a gadurun?...." Abbah ne ya kalleta yaji duk abinda tace duk da a hankali tayi maganar, cikin ɓacin rai ya ƙira sunan Ƴar Tiny yace "Auta kije gaban Balkisu da Ruƙayyat duk ki mammare su..." Ai kuwa da gudun gaske ƴar Tiny taje gabansu da ƴar ƙaramar hannunta ta seta fuskar Pinky ta zabga mata mari sannan ta zabgawa Ruky mAh, ta dawo ta zauna tana dariya,.. Pinky da Ruky abun yayi musu ciwo sosai harda hawayensu, Abbah yace "wannan shi ake ƙirada ramuwar gayya, tsabar raini ina magana kuma kuna yi TOH mu cigaba...." Minal zama tayi kai a sunkuye sai zubda ƙwallah take a rayuwarta ta tsani ayi mata faɗa hakan yana ƙuntata mata rai sosai... Aunty Yolash tana rarrashin Abbah tace "kayi haƙuri Yaya, idan ka biyewa yarannan hawan jininka zai iya tashi, nayi waya da twins Razhdeen da Roshan next week suna kan hanya, ka kusan hutawa da hayaniya...." Hajia Kilishi ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa jin an ambaci sunan Twins zasu dawo, tana matuƙar jin shakkar su da tsoronsu uwa uba Major general Razhdeen wanda suke ƙiransa da sunan Uncle Deen... Sauran yaran ma sun girgiza sosai dajin dawowarsu Ko wacce jikinta ne ya soma kakkarwa, especially Minal Babbar cikinsu duk tasha jinin jikinta.... Banda Ummy wacce take farin cikin dawowarsu, Ƴar Tiny kuka ta soma yi tana faɗin "banaso su dawo, Uncle Deen dukana yake yiiii..." 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 13 to 14 Aunty Yolash gaban General ta tsaya cikin nuna damuwa tace "Yaya idan ba damuwa ka bani yarinyar na tafi da ita mana tinda mutanen gidan ba son zamanta a gidan suke ba, zata sha wahala ne a gurinsu.." General a fusace yace "dole zata zauna a cikin gidan nan, kuma naga wacce ta isa ta takura mata, gobe da sassafe zan hau jirgi zan tafi Maleshiya akwai meeting ɗin da zamu gudanar acan, zanyi two weeks wata ƙil su Roshan su rigani dawowa..." Aunty Yolash girgiza kai kawai tayi tare da faɗin "shikenam TOH, daman Nima yanzu nake son komawa Bauchi..." General yace "ok akwai saƙon da zan tura miki zaki gani kafin ki isa..." ya kuma cewa "Ita kuma yarinyar nan ku kaita ɗakin da zata zauna...." ya kalli Ummy yace "uwar masu gida ganan Auntynki nan zan baki kuɗi kuje ɗaya daga cikin security yakai ku super market kiyo mata siyayyan kayayyakin da zatayi amfani dasu..." Ummy tace "toh Abbah...." shi kuwa wuce wa yayi ya haura upstairs yanda ɗakin kwanansu yake, ita kuwa Ummy hannun Baiwar ALLAH ta riƙo suka miƙe tana cemata "tashi na kaiki ɗakinda zaki zauna koh..." ɗakinda yake ƙasin stairs ta shigar da ita, itama Aunty Yolash bin bayansu tayi, a yayinda Hajia Kilishi take binsu da harara ta kasa cewa ƙala, cikin takaici taja dogon tsuka itama ta haura upstairs can bedroom ɗinta, Itama Minal jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta wanda yake saman Upstairs, Kana shigowa cikin babban falon zaka tarar da gidan beni Three part, ta bangaren dama akwai beni mai hawa uku , kana kai ƙarshe zata tarar da layi gida biyu right and left, idan kabi layin right shine zai kaika har part ɗin Major general Razhdeen, da ɗan rasa kaɗan kafin ka isa part ɗinsa.... Layin left kuma shine zai kai ka har part ɗin Doctor Roshan shima kafin ka isa akwai ɗan tazara... Idan ka sauƙo falon kuma still akwai gidan beni ta bangaren hagun mai hawa biyu shi kuma, kana kai ƙarshen Benin zaka tarar da ɗakuna guda biyar a jere, ɗakunan ƴan matan gidan Kenam kowa da ɗakinsa, ɗaki na farko shine ɗakin Minal sai na biyu kuma ɗakin twins pinky and Ruky ɗakinsu ɗaya sai ɗakin Ummy ta gefensu sai kuma ɗakin Ƴar Tiny amma a waran mommynta take kwana ita sai ɗayan ɗakin da babu kowa a ciki, Kowa ɗakinsa da ɗan tazara dana ɗaya, Kana komowa falon kuma zaka ƙara tarar da gidan Beni ta tsakiyar right and left, nan ma hawan beni uku ne kana hawa zaka tarar da ɗakuna biyu, ɗakin Hajia Kilishi da kuma General, A ƙasin falon kuma a ƙasin benin su General wani wantamemen dining table ne sai ƙaton kitchen ata gefe guda da kuma store na kayan Abinci, A ƙasin benin ƴan matan gidan kuma ɗakuna uku ne a jere wato ɗakin baƙi idan sun zo, A ƙasin benin su Doctor Roshan nan ma ɗakuna uku ne a jere a ɗaya daga cikine aka ajiye Baiwar ALLAH, sai kuma ta kusa da ɗakinta ɗakin Aunty Yolash ce idan tazo hutu, Baiwar ALLAH tana zaune a bakin gadonta Ummy itama tana zaune ta gefenta tana riƙe da hannunta tace "Please Aunty Meye sunanki?..." Baiwar ALLAH kallonta tayi tare da sau murmushi tace Baiwar ALLAH...." Cike da mamaki Ummy take kallonta tace "ikon Allah sunanki kenam? Allah sarki, toh ki kwantar da hankalinki bazaki sha wahala acikin gidan nan ba Insha Allah, kar kiji fargaban Hajiyar mu just saidai tayi barazanar ta....." Haɗiyar yawu Baiwar ALLAH tayi tare da jinjina kai tana murmushi ba tareda ta ce komai ba, Aunty Yolash tana tsaye tana jinsu idonta akan Baiwar ALLAH ta ce "duk abinda akayi miki acikin gidan nan na wulaƙanci kiyi gaggawar sanar mun, za'a ɗau hukunci akai..." ta kalli Ummy sannan ta kuma cewa "Uwar masu gida idan kika ga anyiwa baiwar Allah abinda bai dace ba to ki sanar mun, Ni kuwa na sanarwa Abbanku kinji koh?....." Ummy jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha ALLAH Aunty..." daga nan Aunty Yolash tayi musu sallama tace "Ni zan koma Bauchi saina sake zuwa..." Ummy tace "TOH Aunty ko nazo na rakaki ne?..." Aunty Yolash tace tana murmushi ta ce "Ni da zan tafi a motar! ki kwantar da hankalinki ganan amanar Baiwar ALLAH an baki ita ki kula mana da ita, yanzu tashi ki nuna mata gurare acikin ɗakin da toilet kafin ku fita yin siyayyan kayayyaki...." Ummy tana murmushi itama tace "TOH Aunty..." daga nan Aunty Yolash ta tafi... Bayan Ummy ta nunnuna mata gurare har cikin toilet tacewa Baiwar ALLAH "ganan ɗakinki, yanzu dai tinda yamma ta gabato mu bari sai gobe da safe muje super market koh! saboda idan mun fita yanzu dare zai iya mana, kuma inada burin mu zazzagaya har gidan zoo da waran wasanni, mu ɗan je yawon shakatawa, yanzu dai bari naje na dubo miki kayan da zaki chanza acikin kayana sai kiyi wanka kafin na dawo kiji...." tana kaiwa nan tayi ficewarta. Baiwar ALLAH murmushi kawai take domin Ummy ba ƙaramin burgeta take ba, tashi tayi ta shige toilet kamar yanda Ummy ta umarceta, da shigar ta brush ta farayi sannan tayi wanka tare da ɗauro Alwala.. tana fitowa kuwa ta tarar da Ummy harta kawo mata kayan ta ajiye a saman gado, saidai tana kawowa tayi ficewarta, Murmushi Baiwar ALLAH ta ƙara saki sannan a fili tace "Allah Sarki a duniyan nan yanda kaga maƙiyanka haka zakaga masoyanka..." ɗaukar doguwar rigar tayi ta zura har ƙasi sannan ta ɗauki dogon hijab ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah, Misalin ƙarfe 8 na dare bayan kowa ya zazzauna a dinning za'a ci abinci, zama sukayi suna jiran fitowar Hajiyarsu domin bame fara cin abinci sai kowa ya hallara haka dokar yake, Ummy ganin mommy batada niyar fitowa yasa ta ɗauki ɗaya daga cikin kulolin abinci zata nufin ɗakin Baiwar ALLAH domin tasan yau ne farkon zuwanta gidan bazata iya cin abinci a cikin mutane ba , Jin murya kamar daga saman yasa Ummy tsorita da sauri ta ɗaga kanta sama ganin Mommynsu tayi tana tsaye a saman Upstairs tana kallon na ƙasan falon, Cikin ɗaga murya tace "ina zaki kai mun kular abincin?..." Ummy idonta akan Mommynsu ta ce "mommy a baƙuwar mu zan kai, ba lallai ne ta iya ci acikin mutane ba ....." Hajiya Kilishi kasa yin magana tayi ta zuba mata ido ganin yanda shishshigin Ummy yayi yawa, ji take kamar ta dirƙo daga saman stairs tazo ta rufata da duka, tana hararar ta tace "kinibibi, iyeyi, kisisina, rawar kai, da son gwaninta wallahi zaki ci ƙaniyarki ne a wajeni idan baki kikiyayeni ba, saboda ubanki yana goya miki baya shine zaki raina mutane ko? Ita ɗin baƙuwar dan ubanta tafi ƙarfin fitowa tazo ta karɓa saidai akai mata? kije kice ta fito inji Ni matar gidan, ba'a kawota don ta ci ta sha ta kwanta ba...." Ummy jiki ba ƙwari tazo ta ajiye kular sannan ta nufi ɗakin baiwar Allah! harta kusan isa Hajiya Kilishi ta tsayar da ita tare da faɗin "na fasa aikenki ma dawo ki zauna domin bana ƙaunar ki haɗa alaƙa da waccan yarinyar da batada asali...." ta kalli yanda ƴar Tiny take zaune sai faman tura abinci take domin ita bata jiran sai kowa ya hallarun Nan, Hajiya tace "Auta je ɗakin ƙazamar yarinyar nan da aka kawota ɗazu ki ƙira mun ita...." Ƴar Tiny da gudu ta nufi ɗakin tana cewa "TOH mommy...." ta ƙarasa maganar daiden lokacin da ta tura ƙofar ta shiga... Minal harara ta gallawa Ummy tana faɗin "munafukar Banza kawai, idan baki kama kanki ba sai nayi miki dukan tsiya wallahi mttssw...." Ummy tana jinta ko ɗagowa batayi ba balle ta kalleta sai ji tayi su twins suna faɗin "anya kuwa Ummy jinin gidan nan ne kuwa? naga ɗabi'unta gaba ɗaya babu kala...." A daidai lokacin da Hajiya Kilishi ta ja kujera ɗaya ta zauna itama fuska a haɗe domin bata farin cikin kawo baiwar Allah, hatta ƴan aiki basa zama mata a gida saidai suzo suyi aikinsu su tafi, bata ƙaunar ganin baren mutum a kusa da ita.... Ƴar Tiny tana zuwa ta tarar da baiwar ALLAH tana kwance saman katafaren gadonta sai shan bacci take bayan tayi Isha'i, Ƴar Tiny tana huro hanci tare da Turo baki ta kai hannu ta ɗauki wata ƴar ƙaramar allura akan mirror ta Cakawa Baiwar ALLAH a saitin ɗuwawunta, dan ma da hijab a jikinta, a zabure baiwar Allah ta tashi tana salati domin mintsinar ba ƙaramin ratsata tayi ba, har cikin ƙwaƙwalwata, Baiwar ALLAH tana kallon Ƴar Tiny kamar zatayi kuka tana sosa wajenda ta caka mata allurar, Ƴar Tiny tana farfara ido tace "ke ɗin meya kawo ki gidan mu, kuma har da saka kayan Aunty Ummy to ki cire mata kayan ta kar ki shafa mata datti...." Haka ƴar Tiny ta kai hannu tana jan rigar jikin baiwar Allah wai saita cire kayan Aunty Ummy, har da fashewa da kuka tana ja... Baiwar ALLAH gaba ɗaya hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa yanda zatayi da ƴar Tiny, Ita damuwarta kar ƴan gidan suce dukanta tayi....... *DAN ALLAH KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE ƊIN, KU ƊAN RAGE SANNAN KUYI MUN UZURI BANA SAMUN YI MUKU UPDATE DA WURI, AKWAI ƊAWAINIYA SOSAI A GABA NANE, AMMA INSHA ALLAHU GOBE INSHA ALLAHU ZAMU KOMA GIDA SABODA GOBE ZAMU KAMMALA EXAM, DA ZARAR NA KOMA KOMAI ZAI ZO DA SAUƘI, KUYI HAƘURI.....* 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 15 to 16 ꧁꧂ Jin ihun da ƴar Tiny take yasa twins suka shugo ɗakin da gudu suna faɗin "meya faru ne Auta?..." suka kalli yanda Baiwar ALLAH take a zaune suna jifanta da harara baki a haɗe wajen cewa "la'ananniya me kika mata?..." Baiwar ALLAH tana zubda ƙwallah tace "wallahi ba abinda nayi mata, ina kwance ta caka mun allura sannan ta fara ihu...." bata ƙarasa maganar ba taji Pinky ta darara mata tsawa tare da faɗin "yimun shuru Mayya kawai, karuwar waje toh bari kiji gidan nan bawai kin shigo shi don hutu bane sai zallar wahala, kisa a ranki cewar a matsayin ƴar aiki aka kawo ki yarinya...." ta ƙarasa maganar tare da jan hannun ƴar Tiny suka fice, itama Ruky harara ta watsa mata tare da jan dogon tsuka suka fice... Baiwar ALLAH fashewa tayi da matsanancin kuka tana cikin wannan halin taji an dafa kafaɗarta ana bubbugan bayanta cikin sassanyar murya Tace "kiyi haƙuri komai yayi farko zaiyi ƙarshe, ki tashi muje kici abinci...." Baiwar Allah ɗagowa tayi tana kallon Ummy da rinanan idanuwanta haka ta tashi jiki ba ƙwari sukayi falo, A dinning table Baiwar ALLAH ta zauna itama Ummy zama tayi a kusa da ita tana zuba mata abinci a plate, Baiwar ALLAH ɗaukar spoon tayi tana ɗibar abinci tana ci kamar wacce ta shekara bata ci komai ba, tsabar yunwa tura abincin kawai take har tana ƙoƙarin ƙwaruwa, dasauri Ummy ta ɗauki cup mai ruwan sanyi ta bata tasha, suna cikin wannan halin saiga Minal ta sauƙo daga stairs idonta akan Baiwar ALLAH wacce take ta tura abinci, cike da izzah tazo waran ta tsaya tana yamutsa fuska tace "Keee!..." Baiwar ALLAH ɗagowa tayi a hanzarce tana bin Minal da kallo, Minal harara ta watsa mata tare da faɗin "kar ki sake haɗa eyes dani, inba haka ba saina carkwane idon...". Dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi sannan ta cigaba da cewa "Meye matsayinki acikin gidan nan?..." Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi ba tare da tace komai ba, Tsawa Minal ta daka mata cewar "ba magana nake miki ba?..." tana kuka tace "Nima ban sani ba wallahi ...." Minal tace "okay zaki sani ai, bakida wani matsayi acikin gidan nan don haka kada na sake ganin kin ɗosana ɗuwawunki acikin ɗaya daga cikin kujerun dinning ko na falo, na haramta miki wannan umarni nane, saboda haka yanzu ki sauƙa ƙasi ki zauna mayyar abinci kawai....." Baiwar ALLAH tashi tayi daga kan chair ta zauna a ƙasi da plate ɗin abincinta a hannu, Juyawa Minal tayi zata tafi Ummy tayi saurin cewa "amma gaskiya Aunty Minal baku kyautawa, ki tambayi Abbah ya rigada ya bata matsayi a cikin gidan nan, itama ta zamo ƴar gidan....." bata ƙarasa maganar ba taji Minal ta darara mata tsawa "Shutt uppp! your very stupid idan baki shiga taitayinki ba wallahi i will teach you a lesson, naga kwana biyun nan tsutsar kanki na motsi, bari Abba ya tafi kiga aiki da cikawa...." taja dogon tsuka tare da wucewa fuuuu kamar zata ɗaga sama, hanyar waje tayi zata fice.... Ummy girgiza kai tayi tare da faɗin "ALLAH ya sawwaƙe ya kuma shirya mana zuri'a..." Ummy ta kalli Baiwar Allah sannan tace "ki cigaba da haƙuri wata rana sai labari, sannan duk abinda sukayi miki ki daina nuna damuwa ƙarara a fuskarki dama zuciyarki gaba ɗaya domin su haka suke so su rinƙa ganinki acikin damuwa, idan kina biye musu ciwo ne zai kamaki banda yawan kuka please...." Baiwar ALLAH ta jinjina kai sannan tace "Insha ALLAH Sister zanyi ƙoƙarin yin hakan...." da murmushi a fuskokinsu haka suka kammala kowa ya kama waran makwancinsa, Ummy ta haura upstairs ita kuma Baiwar ALLAH ta wuce ɗakinta, tana shiga ta nufi toilet ta watsa ruwa ajikinta tare da ɗauro Alwala sannan ta fito ta tsaida sallar isha'i.... ꧁𓇽꧂ 🇾 🇦 🇷➪🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 🧚🧚🧚🧚 tana kwance akan katifarta kamar yadda ta saba kullum, a wannan lokacin misalin ƙarfe 1 ne na dare, acikin bacci take jin ana ƙiran sunanta a hankali yasa ta buɗe idanuwanta gaba ɗaya tana ɗarɗar ga kuma daman a tsorace take tin ranar da ta laɓe a jikin ƙofa taji ana faɗin acikin satin nan za'a tura ta can ƙasar waje domin an rigada anyi cinikinta, da sheƙeta za'ayi daga baya kuma suka canza shawari, a ruɗe ta tashi zaune tana waige-waige ganin babu kowa sai hasken nepa da yake kashewa yana kunnuwa da kansa, Ƴar Amana fashewa tayi da kuka ganin babu wata mafita, wata siririyar murya taji anata tintsirewa da dariya ga hasken ɗakin ya ɗauke gaba ɗaya sai duhun daya biyo baya, tana cikin wannan halin taji an ɗagota sama tare da yin hajijiya da ita sai ɓatt ta ɓace gaba ɗaya, ana ɓacewa da ita sai hasken ɗakin ya bayyana, Ƴar Amana bata tashi tsintar kanta ba sai a bakin ruwa, wajen tsittt babu motsin kowa sai ƙarar ruwa wanda yake kai kawo ga kifaye yanda suke tashi sama suna tsunduma cikin ruwan, bata iya hango ƙarshen ruwan ba tsabar faɗi da tsayi ga kuma zurfi, ga wani irin sanyin da yake ratsata, ƙasar wajen laushi babu gudan dutsi ko ɗaya, tana ta faman waige-waige amma babu alamun mutum ko wani abu mai rai, gaba ɗaya a kiɗime take tana cikin wannan halin tada an ajiye wata ƙatuwar jita da red flower akai sannan taga an ajiye wata jar doguwar riga da takalmi ba tare da taga ko waye ba, idonta akai haka take matsowa gurin a hankali lips ɗinta na kakkarwa, domin ƴar Amana idonta idon ganin jita ko wani irine saita taɓa, tana zuwa wajen taga lokaci guda an sanya mata doguwar rigar da takalmi sannan anyi mata gyaran gashi, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba, kallon kanta take sosai ta cigaba da kallon gefe da gefenta ko zata ga wani amma babu motsin kowa, hannu na kakkarwa takai kan jitar tana daddannawa a hankali yana bada sautin kiɗa, acikin tanayi a hankali harta komo tana daddannawa da ƙarfi ga wani irin sauti mai daɗin gaske yanda yake tashi, haske ne ya fara bayyana a wajen mai farfatsin wuta kala-kala, lumshe idonta tayi a hankali tana wasa da yatsunta akan jitar.... 🇧 🇦 🇮 🇼 🇦 🇷➪🇦 🇱 🇱 🇦 🇭  Dake kwance saman katafaren gadonta jin sautin kiɗa yana dukan dodon kunnenta yasa tayi saurin buɗe eyes ɗinta domin tasan kalar sautin nan irin na ƴar Amana ce, dasauri ta sauƙa daga kan gadon taje jikin window ta buɗe tabulen window tare da zuge glass ɗin window, wani irin haske taga yana tashi sama mai kaloli kala-kala ga kuma yanda sautin yake tashi amma saidai ba murya, murmushi Baiwar ALLAH tayi tasan wannan Ƴar Amana ce domin iya kiɗa take badawa babu bakin magana, Lumshe ido Baiwar ALLAH tayi sannan ta fara bin yanayin kiɗan tana rera waƙar a hankali, da kaɗan kaɗan har sound ɗinta ya fara tashi da gaske tana bin sautin tana rera waƙar itama ido a lumshe tana daga cikin ɗaki a tsaye a gaban window.... Ƴar Amana itama tana ɓangarenta wanda bata san a yanda take ba haka take jiyowa muryar Baiwar ALLAH yana dukan dodon kunnenta yanda take bin sautin tana rerawa, a gaggauce Ƴar Amana ta buɗe idonta tana kallace-kallacen ko zata ganta amma sai dai iya haske kawai take gani yana ta farfatsi hakan ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa tana daddanna jitar tana bada sautin, itama Baiwar ALLAH tana can tana rera waƙar, haka kowa yake jiyo wa ɗan uwansa... Yana kwance akan lallausar gadonsa mai girman gaske yana lumshe da kyakykyawan idanuwansa ga kyakykyawar fuska kamar mai yin murmushi, a hankali yake shan baccinsa kamar a mafarki yake jiyo sauti mai daɗin gaske da kuma murya mai kashe zuciya suna dukan dodon kunnensa, ganin kamar ba'a cikin mafarki yake jiyowa ba yasa ya fara buɗe eyes ɗinsa a hankali yana lumshe su gwanin burgewa, jin har yanzu bai daina jin sautin da muryan da ake rera waƙar ba yasa ya ƙara miƙewa zaune yana waige-waige, tashi yayi a hankali yana taku har ya isa bakin ƙofar bedroom ɗinsa yana shirin buɗewa yaje falo ko plasman ne a kunne, har yakai hannu zai buɗe idonsa ya sauƙa akan window dake bai gama sauƙar da labulayen ba, wani irin haske yake gani ta waje yanata tashi mai farfatsin wuta kala-kala, cike da mamaki yaje jikin window yasa hannu ya ƙara buɗe labulen yana kallon wannan hasken, ga sautin kiɗa yanda yaketa tashi sannan zazzaƙar murya yana kan dukan dodon kunnensa, wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi a hankali yake lumshe idonsa, Sautin kiɗan da yake ji ba ƙaramin kashe masa jiki yayi ba, A hankali yake motsi da lips ɗinsa ido a lumshe ya ce "WHO is dis girl? me suke nema a gareni?...." still bai buɗe idonsa ba ya cigaba da cewa "ƴan mata biyu! ɗaya tana kaɗa jita, ɗaya tana rera waƙa, kullum saikun zo mun a mafarki yanzu kuma sautin kiɗa da kuma sautin Muryar ku sun fara bayyano mun a zahiri shin me kuke nema a gareni? shin ku ɗin aljanu ne ko mutane? ku bayyana mun kanku mana, ku daina azabtar da zuciyata haka, ku daina hanani bacci please, idan wani abu kuke buƙata ku bayyanar mun da kanku, Ku gaya mun me kuke so! me kuke so!! me kuke so!!! I said tell me what do you want from meeeee......" A tsawace ya ƙarasa maganar tare da bugan jikin glass ɗin window da ƙarfin gaske har sai da ya dagargaje glass ɗin, hannunsa yaji rauni sosai daiden lokacin da komai ya ɗauke cakk babu hasken nan sannan babu sautin kiɗa kuma babu Muryar waƙar, ya faɗa saman gadonsa yana caccakuɗa sumar kansa tare da yin ihu tsabar juyawar da kansa ke yi ga wani irin ciwonda yake yi haka yake ihu har sai da sojoji masu gadinsa suka jiyo ihunsa, da gudu suka turo ƙofar bedroom ɗinsa bayan sun wuce ƙaton falonsa, kamar yadda suka saba haka sukayo kansa suna faɗin "Ogah sorry, what's wrong sorry sorry..." Saida sukayi masa allurar da ake masa kullum kafin hankalinsa ya dawo jikinsa sai kuma ya wuce da yin bacci... Daman kullum hakane da ihu yake tashi daga bacci na fitar hayyaci domin ba'a cikin hankalinsa yake ba, sakamakon mafarkin ƴan mata biyu da yake yi kuma sun gagara bayyana masa fuskokinsu wannan karan kuma sai sautin muryar ɗaya da kuma sautin kiɗan ɗaya sun bayyano masa a zahiri, idan ya tashi a wannan halin akwai allurar da ake masa wanda shi yake dawo dashi hayyacinsa daga nan kuma saiya wuce dayin bacci, Har fargaban kwanciya bacci yake saboda wannan matsalar shiyasa yake so ya koma Nigeria ya samu Abbansu suyi magana akan lamarin ko za'a iya temaka masa, Bayan ya koma baccinsa Sojojin ne suka fice masa a ɗakin kowa ya koma kan aikinsa..... Baiwar ALLAH tana kammala waƙar daga nan haske ya ɗauke itama kanta ne ya fara juyawa ta rasa a wani duniya take, daƙer take ja da baya har ta faɗa saman gadonta tana dafe da goshinta nan danan bacci yayi awun gaba da ita..... Ƴar Amana tana dakatar da kiɗan hasken wajenta ya ɗauke itama dafa kanta tayi sakamakon juyawar da yakeyi nan danan ta faɗi a ƙasin wajen daga nan ta nemi hankalinta ta rasa...... Wannan al'amarin daya faru Aljanun Ƴar Amana ne masu wannan aikin, a iya mutum uku kawai suka bayyanar musu da wannan sirrin Daga ƴar Amana sai kuma BAIWAR ALLAH da kuma Major general Razhdeen, bayan su babu wanda zai iya jiyo sautin kiɗa da kuma muryar Baiwar ALLAH, waɗannan hasken sune masu aika saƙo, Sukan ɗauki sautin kiɗan Ƴar Amana su aikawa Baiwar Allah dake Nigeria sannan su ɗauki muryar Baiwar Allah su aikawa Ƴar Amana dake bakin Teku a ƙasar Misra, su kan ɗauki muryar da kuma sautin su aikawa Major general Razhdeen dake ƙasar Australia, Kasar Misrah nan Aljanun Ƴar Amana suka kaita bakin Teku.... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 17 to 18 ꧁꧂ Washe garin ranar Monday da safe Baiwar ALLAH tana kwance kan gadonta har zuwa wannan lokacin bata samu farfaɗowa ba, da ƙarfin gaske aka turo ƙofar ɗakin cikin zafin nama, Hajia Kilishi ce ta tsaya tana binta da kallo tare da taɓe baki tace "iyeee ƴar hutu, yarinya an samu guri dole a wataya uhmm hakane...." Dasauri ta nufi toilet taje ta ɗebo ruwa a bucket tana fitowa ta kwara ruwan nan gaba ɗaya akan Baiwar ALLAH dake kwance tana dafe da goshinta, a ruɗe ta farfaɗo tana jan numfashi sama-sama, gaba ɗaya a firgice take, daƙer ta iya saita hankalinta ta tsaida shanyayyun idanuwanta akan Hajia kamar wacce tayi shekaru tana jinya duk ta rame ta zamo kalar tausayi, bata ankara ba taji Hajia Kilishi ta zabga mata mari tare da faɗin "tashi dan ubanki, Ni zaki rinƙa yiwa irin wannan kallon? yau zan ga waye gatanki acikin gidan nan, General ya tafi yanzu kallo ya koma sama, dan haka ki biyo ni falo yanzun nan...." ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsuka ta fice.. ita kuwa Baiwar ALLAH tana zaune hannu akan fuska, wasu zafafan hawaye ne suka fara gangaro mata, da haka ta tashi ta nufi toilet tayo alwala sannan ta fito tayi sallar asuba domin yau ta makara sosai ƙarfe 7 yanzu haka, Bayan wasu mintuna ta kammala tare da jero addu'o'inta sannan ta miƙe zatayi hanyar fita da zureren hijab ɗinta saiga Minal ta shugo da bala'inta ganin Baiwar ALLAH yasa ta tsaya tana balbaleta da masifa "ke wato dan kin raina mutane tin ɗazu matar gidan tazo da kanta ta ƙiraki amma ki ƙi zuwa dan buro ubanki! saboda kin mayar mutane Mahaukata koh?....." Baiwar Allah kamar zata fashe da kuka tace "kuyi haƙuri Sallar Asuba nayi....." bata ƙarasa maganar ba taji Minal ta kamo kunnenta ta murɗa da ƙarfin gaske tana faɗin "sallo kinji koh, ƴar gidan akharami taho munafuka kawai...." taja kunnenta suka fice falo, ba ƙaramin murɗe mata kunne tayi ba da haka har suka ƙarasa cikin falon yanda sauran mutanen gidan suke suna isa Minal ta wurgar da ita ƙasin carpet, Ga Hajia Kilishi tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya sai hararar Baiwar ALLAH take, sai kuma ƴan mata biyu twins suma suna zaune a kujera ɗaya ko wacce idonta akan wayar hannunta, sai Minal wacce zamanta Kenam akan kujera idonta akan Baiwar ALLAH, Ummy ce kawai bata nan tana can ɗakinta bata farka ba ita da ƴar Tiny... Hajia tana kallon Baiwar ALLAH tace "na ƙira ki shine zaki ɓata mun lokaci koh ?...." Baiwar ALLAH ɗagowa tayi tace "Hajia Sallah.........". bata ƙarasa maganar ba taji an harba mata baki da ƙafa ɗagowa tayi da rinannun eyes ɗinta tana kallon Minal wacce ita tayi cankin, nan danan lips ɗinta ya fashe sai jini dake takalmi mai tudu ne a ƙafarta, su ko ina zasuje da takalmi a ƙafarsu, kwanciya ne kawai idan zasuyi suke cire takalmi... "Idan na sake jin anyi magana kema kin buɗe wannan ruɓaɓɓen bakin ki kema kinyi Uhmmm kin san sauran...." Hajiya Kilishi idonta akan Baiwar ALLAH tace "Meye sunanki?..." A hankali tace "Baiwar ALLAH...." cikin zafin rai Hajiya Kilishi tace "kowa ma ai bawan Allah ne dan ubanki..." Baiwar Allah tayi shuru kai a ƙasi, Hajia Kilishi ta cigaba da cewa "Inaso ki sani cewa wannan gidan bawai kin shigo shi saboda hutu bane, baccin safen nan dakatar dashi zakiyi saboda bakida ƴancin yin baccin safe sai masu gidan, wacce take zuwa yi mana aiki a gidan nan yau na sallame ta saboda bana tara ƴan aiki, guda ɗaya nake riƙewa, saboda haka ki ɗaura ɗamaran yin aikin daya dace acikin gidan nan, aiki na farko shine zaki tashi da asuba ki fara share-share da goge-goge su dinning table da kitchen, kujerun falo da plasman da frig gaba ɗaya zaki goggoge ba saina lissafo miki ba kema kinsan abinda ya dace, daga nan zaki haura upstairs kije kibi ɗakunan yarana duk ki gyaggyara musu ki wanke musu toilet gaba ɗaya, sannan ki sauƙo ki haura upstairs saman ɗakina ki shiga nan ma ki gyara mun sannan ki wanke toilet, ɗakin mijina kuma ban baki izinin shiga ba, Bayan kin kammala sai ki shiga kitchen kiyi mana girke-girken abun breakfast, kuma kece zaki rinƙa mana girki kullum daga safe har rana har na dare sannan ki tattara ki wanke kwanuka, Still idan kayan yarana sunyi datti zasu tattaro miki kije ki wanke musu tass ki goge musu, ƙarin ayyuka kuma sai matasan gidan sun dawo zakiyi bayani, Kinga can?......" ta nuna Upstairs part ɗin su Razhdeen ta kuma cewa "wancan part ɗin duk ɗakunan gidan nan baya su girma domin ko wani ɗakinsu akwai falo da kuma bedroom da toilet duk sai kin shishshiga kin gyara musu da zaran sun dawo sannan kina kammala girki ko wanne zaki kai mishi ɗakinsa ne saboda su basa cin abinci acikin mutane, kowa da dining ɗinsa acikin room ɗinsa, Ki shirya yarinya ba hutu kamar yanda kika tsara yi......." Hajia Kilishi tana iddasawa ta tashi tayi hanyar fita tare da faɗin "Ni zan wuce gurin aiki saina dawo, sannan ke kuma Minal banaso kina makara a wajen aikin ki, ki samu ki shirya ki tafi....." Minal tace "toh Mommy sai kin dawo..." itama tayi maganar tare da miƙewa tsaye zata haura upstairs idonta akan Baiwar ALLAH ta ce "Madam zaman mai kike yi? bazaki fara aikin bane?...." Baiwar ALLAH tashi tayi tana girgiza kai alamar a'ah... Dasauri ta miƙe ta fara karkaɗe kujerun falo tana goggogesu, Suma su Pinky ne suka tashi tare da faɗin "ga can tilin kayan wankin mu idan kin kammala aikin gida saiki hau wanki kuma....". suka ƙarasa tare da haura saman stairs. tinda Baiwar ALLAH ta fara aiki bata tsaya ba saida ta kammala share-share da goge-goge harda su kitchen da gyaran ɗakunan gidan gaba ɗaya dasu wankin toilet sannan ta shiga kitchen zata girka abun breakfast, tana cikin aikinta saiga Ummy ta shugo tana jinjina kai tace "kinsha aiki sosai Aunty Baiwar Allah, sannu da ƙoƙari...." juyowa tayi da murmushi asaman fuskarta tana kallon Ummy tace "ai Ni aiki baya ban wahala, yanda kasan wasan yara haka na ɗauki aikatau, ai motsa jiki ne, yawan kwanciya ma illah ne....." Ummy girgiza kai tayi sannan tace "Allah Sarki su kuwa suna ganin kamar horaki suke yi, so nake sai Abbah ya sauƙa daga jirgi idan ya huta saina ƙira shi na sanar masa duk abubuwan da suke faruwa..." Baiwar ALLAH riƙo hannun Ummy tayi sannan tace "please sister kimun wata alfarma...." Ummy dasauri ta jinjina kai tare da faɗin "Yes inajinki..." Baiwar ALLAH tace "dan girman Allah duk abinda akayi mun acikin gidan nan karki sanar wa Abbah, haka duk abinda za'ayi mun, wahala ne na rigada na saba tin ina yarinya saboda haka babu abinda zai sha mun kai akan duk aikinda za'a sanyani nayi, wannan shine Alfarmar da zakiyi mun, Banason Abbah ya rinƙa tayar da hankalinsa akaina naga kamar bashida lafiya, nidai indai zan samu ci da sha kuma idan dare yayi zanyi bacci Alhamdulillah, ki kwantar da hankalinki ki rinƙa kawar da kanki akan duk abubuwan da za'ayi mun...." Ummy idonta acikin na Baiwar ALLAH cike da tausayawa take kallon ta tace "gaskiya kinada kyakykyawar zuciya kamar yadda fuskarki take da kyau da ɗaukar hankali especially idan cikakken namiji yayi ido huɗu dake....." Baiwar ALLAH bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba jin abinda Ummy take faɗi tace "ke dai kinada abun ban dariya wallahi....." Murmushi Ummy tayi sannan ta ce "da zan rinƙa ganinki acikin yanayin farin cikin nan ai dana fi kowa farin ciki...." Itama Baiwar ALLAH murmushi take ga dimple yanda yake lotsawa gwanin burgewa Lokaci guda ta ɗan sau fuska tana motsi da lips ɗinta idonta akan Ummy tanaso tayi magana amma saita fasa, Ummy tace "ehen tell me, mai kike son cewa?...." Da fara'a akan fuskar Baiwar ALLAH tace "Ni daman bayan ku akwai sauran ƴan gidan waɗanda basa nan?...." Ummy tace "sosai ma suna nan tafe kwanan nan zaki gansu, jaruman gidan, su biyu ne amma tamkar mutane dubu suke, Razhdeen da Roshan su ɗin twins ne, iya su biyu ne kawai basa nan...." Baiwar ALLAH zaro ido tayi jin yanda Ummy take yabonsu ta jinjina kai sannan tace "nifah na ɗauka iya ku mata ne kawai babu yaro namiji, amma duk Hajia ce ta haife ku har su?....." Ummy sauƙe numfashi tayi sannan tace "Kinga Aunty Baiwar Allah Ni yanzu yunwa nake ji, bari na tayaki yin girkin saboda mu gama da wuri munayi muna hirar mu...." Baiwar Allah cikin nuna farin ciki tace "TOH shikenam...." Ummy ta ɗauki blander ta fara niƙa kayan miya domin ferfesun chicken zatayi ita kuma baiwar Allah zatayi wainar masa, Haka suka fara aikinsu gurin yayi tsit Sai can bayan wasu mintuna Baiwar ALLAH tayi gyaran murya sannan tace "Sis baki bani amsa ta ba...." Dariya Ummy tayi ganin yanda Baiwar ALLAH take son jin labarin su Razhdeen da Roshan, tace "yawwa kin tambayeni akan cewar Hajia ita ta haifesu koh?..." tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa "gaskiya ba Hajiya bace ta haifesu ba, suma mamansu daban Ni kaina bansan mamansu ba, kai ƙarewa ma a yanda naji su kansu twins ɗin basu san mamansu ba saboda a lokacin data haifesu a ranar Allah yayi mata rasuwa, bayan wasu shekaru kuma Abban mu ya Auro Hajiyar mu Kinga itama mommy bata san mamansu Uncle Deen ba....." Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta tace "Uncle Deen kuma du?...." Murmushi Ummy ta kuma yi tare da faɗin "Uhm Uncle Deen shine Razhdeen haka muke ƙiransa dashi domin shiɗin ya cancanci sunan baya ɗaukar kansa a matsayin Yaya sai dai Uba hakan yasa ake ƙiransa da Uncle Deen shi kuma ɗayan sarkin Smiling Yaya Roshan muke ce mai, shi wannan a matsayinsa ya zauna na Yaya Kenam...." Baiwar ALLAH jinjina kai tayi haka kawai sai murmushi take ta sauwa ta ce "amm kar kice na cikaki da surutu shin Yaya Roshan ɗin yanada yawan murmushi ne? Amma kuma zai iya kasan cewar kamar su ɗaya ko kamar yanda ake samun ƴan biyu masu kama ɗaya...." Ummy ta juyo tana kallonta da murmushi akan fuskarta tace "suna kama amma ba sosai ba, shi Razhdeen yafi Roshan haske sosai kamar balarabe haka yake dake mahaifiyarsu Balarabiya ce ƴar ƙasar Makkah, toh Razhdeen ita ya ɗauko a kyau da farin fata sannan yana tara suma sosai akansa yanda kasan gashin mace macen ma ƴar India domin sumar kansa har gadon bayansa ga laushi kamar Audiga, sannan yanada ƙirar jiki sosai domin yafi Roshan tsayi da faffaɗan jiki da komai yafi Roshan, kasancewarsa shi ɗin Soja ne yana yawan motsa jiki, Major general Razhdeen yanada matsayi sosai a ƙasar Australia....." ta dakatar da maganar tare da juyowa ta kalli Baiwar ALLAH taga duk ta haɗa gumi sai faman zazzaro ido take, Murmushi Ummy tayi sannan tace "jin yanayinsa kaɗai ya sanya ki cikin zulumi, TOH idan kika ganshi sai kinyi kamar zakiyi fitsari a jikinki saboda ganinsa yafin jin labarinsa firgitarwa, Shi ɗin baya ra'ayin mace ko kaɗan, ko kallon mace baya son yi balle wai soyayya? kaiiiiii ko a mafarki ban taɓa jin ance ganan budurwar Uncle Deen ba, ƴan mata da yawa suna mararinsa amma sai dai suna shakkar kusantarsa, Uncle Deen baya dariya sannan baya son yin magana, baya son zaman cikin mutane bayason hayaniya, sannan baya son raini............" Ummy bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tana faɗin "dan ALLAH Sister ya isa haka, banason jin labarinsa just ki bani labarin Yaya Roshan nasan shi ɗin zamu fi jituwa domin na tsani mutum mai girman kai da jiji dakai....." dariya Ummy tayi sannan tace "kodai kin tsunduma ne kema?...." buɗe baki Baiwar ALLAH tayi da sauri ta ce "wa Kenam?..." Ummy tace "shi Uncle Deen mana..." Zaro ido waje tayi tana girgiza kai tace "waaaa koda wasa, wane Ni, dan Allah rufa mun asiri ina zaman lafiyata kar kisa na fara jin sauƙar ice a gadon baya na, zan tsaya a iya matsayina na ƴar aikin gidan babu ruwana ..." Ummy jinjina kai tayi sannan tace "Allah sarki yanzu haka fuskar Yaya Roshan nake hasashowa da wannan kyakykyawar murmushinsa mai ƙayatarwa, shi ɗin na daban ne ga kyakykyawan zuciya ga asalin kyakykyawa ne shima na bugawa a jarida, fari ne shima tass amma bai kai Razhdeen ba, amma shi baya tara suma gaskiya yana yawan ɗora farin glass akan dara-daran idanuwansa masu kyan gaske......." Bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tace "kamar yadda kema kike ɗora glass akan dara-daran idanuwanki masu kyan gaske baaa...." ta ƙarasa tana gyara mata sakun glass ɗinta, Ummy tace "ai shi Yaya Roshan idanuwansa lafiya lau suke kawai dai yanayin aikinsa na Doctor ne yasa yake yawa saka glass, Ammm Roshan da Razhdeen sunada ɗan banbanci kaɗan saboda yanayin lips ɗin Razhdeen yaci jaaa sosai shi kuma Roshan lips ɗinsa maroon ne yanda kasan sweet lollipop, kuma gaskiya shima bashida kula ƴan mata amma akwai farin jininsu kam, shi Roshan abinda yasa ƴan mata suke tinkararsa saboda bai iya fushi ba kullum acikin Smiling yake, koda an ɓata masa rai bazai taɓa nuna cewar ransa ya ɓaci ba saidai kawai ya sharar domin baya riƙe mutum a ransa, shiyasa ba'a jin tsoronsa ga yawan wasa da dariya, abu ɗaya ne Yaya Roshan yafi tsana a duniyarsa shine wulaƙanci ya tsani yaga ana wulaƙanta mutum, kuma bashida ƙyanƙyami, ke Yaya Roshan pah yayi a rayuwa duk macen data samu Roshan wallahi tayi dacen samun masoyin gaskiya......" Sauƙe dogon numfashi Baiwar ALLAH tayi tana riƙe da saitin zuciyarta tace "Wayyo Allah har na ƙagu dana ganshi wallahi...." Ummy tace "Razhdeen ko Roshan?...." Baiwar Allah turɓune fuska tayi tana ɗan hararar Ummy tace "wani Razhdeen ana zaune ƙalau, nifah tinda kika fara lissafo mun kalar ɗabi'unsa naji sam jinin mu bai haɗu ba, Ni ina ɓangaren Yaya Roshan ehen...." Ummy tace "kar daiii...." Baiwar Allah juyowa ta kuma yi tana kallon Ummy tasan mai take nufi dasauri Baiwar ALLAH ta girgiza kai tare da faɗin "dan Allah Ummy ki daina faɗin haka Kinga jiya-jiya nazo gidan nan banaso a fara samun matsala dani akan wannan al'amarin, kinsan yanda nake a cikin gidan, wallahi koda wasa bawai inajin soyayyarsa bane kawai dai ɗabi'unsa sun burgeni ne ....." Ummy ta ja numfashi tare da dafa kafaɗarta tace "na fahimce ki Aunty Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki babu wata matsalar da zaki samu Insha Allah, Nima tsokananki nake....." Gaba ɗayansu murmushi suka sau, suna cikin wannan halin sai suka ji an turo ƙofar kitchen da ƙarfi, da sauri suka waiwaya suna kallon Minal wacce ta zuba musu ido sai faman harararsu take, Tace "Inaso zan fita aiki kin kasa kammala mana girki tsabar rashin mutunci...." Idonta akan Baiwar ALLAH sunkuyar da kai tayi ƙasi tace "kiyi haƙuri yanzu zan zo na shirya akan dinning na kammala....." taja dogon tsuka sannan ta maida idonta kan Ummy tace "ke kuma uban mai ya kawo ki kitchen? Sarkin shishshigin international, kinada matsalar ido amma kina zuwa waran gass? Let Mommy come back zakiyi bayani...." tana kaiwa nan tayi ficewarta, Baiwar Allah tace "Kinga Ummy ki samu ki fita ba'a barinki kina shugowa kitchen ki temake ni, Kinga laifina za'a gani...." Ummy tace "ai wallahi badan laifinki za'a ganiba babu Abunda zaisa nabar kitchen ɗin nan sai mun ƙarasa, kuma Abbah shima bayaso...." Baiwar Allah tace "Nima na kammala yanzu zan fito da kayan abincin...." Ummy ficewa tayi tana turo baki....... *KAIIII WANNAN PAGE ƊIN KAMM DUK HIRAR BAIWAR ALLAH DA UMMY SUN CIKA MANA GURI 😅😅😅....* 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 19 to 20 ꧁꧂ Bayan Baiwar ALLAH ta kammala shirya kayan breakfast akan dinning itama ɗaukan nata tayi ta wuce bedroom ɗinta, kujerar Minal yana fuskantar na Ummy, suma twins suna facing juna sai ƴar Tiny ata gefen Ummy ko wacce tana carkwane plate ɗinta da spoon babu mai kula kowa a cikinsu, har suka kammala, Minal ficewa tayi zata gurin aiki wato Banker anan take aikinta ita ce manager na bank, itama ƴar Tiny fita tayi da gudu tana sanye da kayan uniform hannunta riƙe da lunch bag akwai security da yake kaita school, twins kuma ɗakinsu suka nufa domin har yanzu hutunsu bai ƙare ba da zarar hutu ya ƙare zasu koma ƙasar London, ita kuma Ummy tsaya kwashe plate ɗin dake dining ta tsaya yi domin ta ragewa Baiwar ALLAH aiki, ita kuwa fur taƙi yin karatu tin daga sacondary ita in ba'a Nigeria ba baza tayi karatun ba amma tanason zama Doctor kamar Yayanta Roshan, tana shirin shiga kitchen da kuloli da plate a hannunta saiga Baiwar ALLAH itama ta fito da plate ɗin data ci abinci, fuska ɗauke da murmushi ta ce "ke dai Ummy bakya jin magana ko? yanzu idan Hajia ta shugo ta tarar dake fah?...." Ummy tace "to bari kiji kafin kizo ina taya ƴan aikin gidan nan aiki kuma babu yanda aka iya dani, don haka babu abinda zai fasaya, Uhmmm kina wasa da uwar masu gida Kenam...." Baiwar ALLAH girgiza kai tayi tana dariya ta ce "sannu uwar masu gida, dole a ganki a ƙyale..." Ummy ta ƙarasa da cewa "ƙwarai kuwa ko matar gidan ce tayi jayayya dani dole zata bar gidan...." Baiwar ALLAH zaro ido tayi waje ta toshe bakinta da hannu bibbiyu tare da faɗin "naaa shige su, wallahi rufa mun asiri..." ta shige cikin kitchen da sauri, itama Ummy dariya take ta shige kitchen, Suna shiga Ummy ta kalli Baiwar ALLAH da take shirin yin wanke-wanke tace "Aunty Baiwar ALLAH ki kawo nayi wanke-wanke sai kije ki shirya Kinsan zamu fita yin shopping koh? Abbah ya bani kuɗin da za'ayo miki siyayya..." Baiwar ALLAH tace "lala kedai jeki fara shirin ki kinga Ni ina gama wanke-wanke zan fara wanki...." zaro ido Ummy tayi rai a ɓace jin an ambaci wanki tasan kayan Yayunta ne tace "wankin kayan uban wa zakiyi acikin gidan nan?...." Baiwar ALLAH juyo wa tayi tana kallonta jin yanayin furucinta cike da mamaki ta ce "wankin kayan Uba nah....". sannan ta juyo ta cigaba da wanke-wanken ta, Ummy ganin ran Baiwar ALLAH ya ɓaci yasa tazo dab da ita ta dafa kafaɗarta tace "sorry Aunty Baiwar ALLAH Amma maganar gaskiya baza kiyi wanki acikin gidan nan ba, matsayinki ya wuce wannan kema saidai ki bada naki a wanke...." juyowa Baiwar ALLAH tayi tana fuskantar Ummy ta ce "please Ummy ki daina shiga shirgin nan, Ni duk abinda akace nayi zanyi iya ƙoƙarina naga nabi doka a zauna lafiya, Meye acikin wankin? duk ba motsa jiki bane? yawan hutu ma illah ne, koda na kasance mai ƴanci acikin gidan nan I swear to God bazanyi rayuwar irin wannan hutun ba ace komai baza kayi ba saidai ayi maka, bazan iya ba, Inaso ki kwantar da hankalinki ki nutsu, kema ba cewa kikayi kina son aiki ba? so ki barni nima nayi komai lokaci ne, kina ganin kamar cutana suke yi da suke sakayi aiki koh? to wallahi sona suke ba wai ƙiyayya bane, duk wanda zai sakaka kayi abu mai amfani to wallahi sonka yake, shin idan nayi Aure wazai mun? shin idan nayi Aure ban iya aikin gidan miji ba ko girke-girke yazanyi? nidai a gidan mijina bana buƙatar ƴar aiki sam bana so, shin baki san aikin nan da nakeyi lada nake samu agurin Ubangiji bane? TOH Inaso ki sani Ni ban iya rayuwar hutu ba, motsa jiki kawai na sani, kuma yanzu ne damar da nake dashi yanda zan koyi komai na ayyukan gida da makamancin su, please ƴar uwa banaso ki ƙara yin magana akan aiki domin rashin yin aikin cutuwa ne a gareni matuƙa....." Ummy tana zubda ƙwallah ta ce "Nima Insha ALLAH bazan zauna ba, dole tare zamuna aikin gida....." Baiwar ALLAH tace "ke kam babu halin yin aiki saboda......." bata ƙarasa ba taji Ummy ta katseta da cewa "wallahi babu wacce ta isa ta hanani ko ita wacece, kuma mata ta taɓani taga ikon ALLAH saidai suyi barazanar su amma babu wacce ta isa ta taɓa mun tsokar jikina...." tana kaiwa nan tayi ficewarta rai a ɓace kai tsaye upstairs ta haura yanda zai kaita ɗakinta, Baiwar ALLAH girgiza kai tayi a ranta tana jinjinawa Ummy sam bata jituwa da mahaifiyarta kamar ba ita ta haifeta ba...... Around 4 O'clock na yamma Baiwar ALLAH ta kammala duk wasu ayyukanta tayiwa su twins wanki sannan tayi girke-girke na abincin rana ta sake yin gyaran gidan sannan tayi wanka ta sanya kayan da Ummy ta ɗauko mata wata Abaya mai shegen kyau da duwatsu masu sheƙi da gyalensa ba ƙaramin kyau tayi ba dake kayan milk ne sun karɓeta sosai duk da ba wani kwalliya tayi ba, tana tsaye a jikin mirror tana ƙare kanta da kallo, jira take Ummy tazo ta ɗauketa su fita yowa shopping domin tana fargaban fita falo da kayan Ummy a jikinta, kaya ma masu tsadar gaske.... tana cikin wannan halin tajiyo muryar Ummy daga falo tana masifa tare da yin kuka, muryarta kawai kake ji daga ƙarshe ta fashe da kuka, a tsorace Baiwar ALLAH ta nufi falo da gudu zuciyarta na ɗarɗar gudun ganin abinda zata tarar, tana zuwa ta tarar da Ummy a durƙushe a ƙasin carpet sai rera kuka take kamar wacce aka mata duka, sai kuma Minal a zaune wacce bata juma da dawowa ba sai ƴan mata twins dake tsaye sunyi cirko cirko suna huci ko wacce ranta a ɓace, Minal ganin Baiwar ALLAH sanye da rigar Abayar Ummy sai kuwa ta miƙe tsaye a fusace ta ce "Keee! Uban wa yace ki saka rigar nan mai bala'in tsada? ....". Itama Ummy ta miƙe tsaye tana fuskantar Minal ta ce "kada ko wacce ta kuskura tayi mun maganar rigar nan saboda ba taku na ɗauko ba, riga ta ce inada ikon da zan yi kyauta da ita...." ta kalli Baiwar ALLAH sannan tace "Aunty Baiwar ALLAH kukan da nakeyi kukan baƙin cikin sace kuɗin da Abba ya bani ya ce muje nayi miki siyayyan kayayyaki ne, Million 3 haka ya bani cash amma yanzu naje ɗauka ban gani ba, kuma acikin su ne wata ta ɗauke ko kuma suka haɗa baki suka sace...." Pinky ta ce "ke Ummy dakata kar ki sake cewa an sace saboda mun fi ƙarfin three millions wallahi, a yanzu haka cikin account ɗina inada kuɗin da sukafi ƙarfin ten millions, kuɗin da kike magana akai kuma Mommy ce tace muje mu ɗauko mata su indai a wannan ƙazamar za'ayo siyayya.....". ta ƙarasa maganar tana nuna Baiwar ALLAH.... Ruky itama tsoma baki tayi tace "ƙwarai mommy ce take buƙatar kuɗin tace indai a wannan ƙwailar zakije yin shopping TOH gwara a ƙona kuɗaɗen domin ba ƙwalisa tazo yi cikin gidan ba...." Minal zama tayi tana kurɓar coffee domin idan ƙananun ƙwari sunayi ita bata shiga zancen sai sun gama tukun, Ummy kamar zata haɗiyi ranta tsabar takaici haka take binsu da harara, suna cikin wannan halin saiga Mommy ta shugo ita da Ƴar Tiny ta dawo daga school itama, zama tayi tareda jefa handbag ɗinta gefe tana sauƙe numfashi, ta ɗago tana bin yaran da kallo ɗaya bayan ɗaya cikin yamutsa fuska tace "wai meke faruwa ne?...." kafin su fara yin bayani saida suka mata sannu da dawowa gaba ɗayansu, itama Baiwar ALLAH durƙusawa tayi har ƙasi tace "sannu da dawowa Hajia....." Mommy ko kallon yanda take batayi ba, idonta akan Ummy wacce ita kaɗaice bata mata sannu da dawowa ba ga hawaye shaɓe-shaɓe a kan fuska, Hajiya Kilishi tace "ke! kinfi ƙarfin mun magana ne?...." Ummy tana kallon gefe tace "ai ba kullum nake a haka ba, kema Kinsan idan kika dawo Ni ce first ɗin yi miki magana, yanzu akwai matsala ne...." Hajia Kilishi ta rigada tasan halin ɗiyarta Ummy idan ta birkice babu kwanciyar hankali kuma daman gado tayi gadon mai sunanta uwar mahaifinta Hajiya Maryama asalin masifaffiyar mata ce ta asali, tana kallon Ummy tace "Meya faru?..." Ummy juyowa tayi itama tana kallon Mahaifiyar tatan tace "kuɗin da kika sa aka ɗauko a ɗakina zaki ban...." Hajia Kilishi tace "me zakiyi dasu?...." Ummy cike da mamaki ta ce "me zanyi da kuɗin kuma? Ina gidan masu kuɗi ace mai zanyi da kuɗi?..." Hajia Kilishi cikin ɓacin rai tace "ki kiyayi furucinki domin Kinsan a gaban wa kike a tsaye...." Ummy tana fari da eyes ɗinta ta ce "eh na sani mana, a gaban matar gidan nake matar ma ta biyu...." Hajia Kilishi ta miƙe tsaye tare da gyara tsayuwarta domin al'amarin Ummy yana shirin fin ƙarfinta jurewa kawai take ta ce "shin matar farko ce ta haifeki ko ta biyun?..." Ummy tana karkaɗa yatsu tare da farfara eyes ta ce "ehhh TOH kamar dai mata ta biyu ce ta haifeni amma ina tantama akai saboda sam bata ɗauko halayya irin na uwa ta gari ba, Ni kuma zanso uwata ta kasance cikin nagartattun iyaye kamar dai mata ta farko...." Hajia Kilishi hajijiya ne yake shirin ɗaukarta tana dafe da goshinta jin maganganun Ummy sun zurfafa, A fusace Minal ta miƙe tsaye tareda daka mata tsawa ta ce "ya isa haka Ummy, daman rashin tarbiyarki har yakai haka? mahaifiyarki kike gaya mata maganganu son ranki?....." Suma twins bakinsu a haɗe wajen cewa "kutmeleciii, jar uban nan, anya kuwa Mommy Ummy ƴarki ce kuwa?...." Ummy tana harararsu ta ce "ai Ni dana fi kowa farin ciki inna kasance ba'a tsatson hajia kilishi na fito ba, Kunga dallah ku mun shuru bada ku nake maganata ba, ko wacce taja bakinta tayi mun shuru, Ni yanzu ba wani dogon jawabi ba a ɗauko mun kuɗina a bani ...." Hajia Kilishi ganin inta biyewa Ummy zatayi sanadiyyar kamuwa da hawan jini domin babu haihuwar data sha wahala kamar haihuwar Ummy amma wai yanzu itace take tsaye a gabanta tana faɗa mata maganganu... Idon Hajia Kilishi ne yayi jawur cikin sassanyar murya ta ce "Ummy babu Abunda kika rasa a cikin gidan nan shin idan na baki kuɗin me zakiyi dasu?...." Ummy fuska a yatsine ta ce "temako..." Hajia ta ce "duk cikin unguwar nan wa kikaga yana buƙatar temako?...." Ummy ta ce "in babu acikin unguwa ai akwai acikin gari..." Hajia Kilishi a tsawace ta ce "bazan bada kuɗin ba, ai nasan a wannan yarinyar duk zaki kashe kuɗin, saboda bawai tazo gidan nan saboda ɗaukan fashion bane aiki tazo yi ....." Ummy a taƙaice ta ce "kika ce bazaki bada ba? Abbah ya bani kuɗi sannan ki karɓa kice bazaki bada ba?...." Hajia Kilishi ce tayo kan Ummy cikin zafin nama kamar zata rufata da duka ta ce "Ummy nace bazan bada kuɗin ba ki dake Ni, kinji ko dake Ni nace...." Ummy ja da baya tayi ganin jikinta dana mommynta yana shirin haɗuwa kamar masu dambe, Murmushi tayi sannan tace "bazan dake ki ba mommy amma ki sani zanyi miki abinda yafi duka zafi, let Abbah come back, u will see what am going to do, I swear to God I'll break the secret, Sirrin da kike ɓoyewa saina buɗa shi kowa ya sani, saina fasa ƙwai indai baki chanza wannan bad behavior naki ba, mummunan hali da kuma cin amanar wanda ya yadda dake, mommy wallahi tintinin na cireki a raina, bakya raina sam domin bana shiri da maciyi amana......" Bata ƙarasa maganar ba taji an zabgeta da mari har sau biyu akan fuskarta, ƙanƙame idon tayi tareda dafe fuskar da hannu biyu ta ko wani ɓangare, a hankali take ƙoƙarin buɗe idon ganin ko wacece mai ƙarfin zarrar da ta isa ta mareta, tanason ganin ko wacece shin mommy ce ko Minal ko kuma acikin twins ne, ganin Baiwar ALLAH tsaye a gabanta tana zubda ƙwallah alamun ita tayi marin, Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "haba Ummy! haba Ummy!! haba Ummy!!! ban taɓa tunanin zakiyi haka ba, ina kallonki mai hankali ashe gwara kowa ma dake, mahaifiyarki ce fa kike gaya mata maganganu son ranki, uwa uwace pah koda ta kasance mai tsinetsine ce akan bolaa......" Baiwar ALLAH bata ƙarasa maganar ba taji Ummy ta katseta da cewa "uwa uwace amma gwara mun uwar da take yawo tsirara akan titi ta fiye mun wannan uwar....." ta ƙarasa maganar tana nuna Hajia Kilishi da yatsa...... tana ƙarasa maganar tayi gudu ta haura saman Upstairs tayi ɗakinta da gudu tana kuka...... Hajiya Kilishi dokuwa tayi akan carpet ta ɗora hannu aka ta fara rausa ihu tana faɗin "na shiga uku na lalace ɗiyata ta tsane Ni, bansan me nayi Wa Ummy ba ta tsaneni, Ni na haifeta a cikina, na ɗauki tsawon wata tara ina ɗauke ta ita acikin cikina sannan Ni nasan irin azabar dana sha a haihuwarta, nazo na shayar da ita har tayi shekara biyu amma abinda Maryam zatayi mun Kenam?....." Minal ce ta durƙusa itama ta rungumi mommy tana rarrashinta, Pinky kam cewa tayi "ai Ni banyi mamakin jin hakan ba saboda tin ba yau ba nake cewa Ummy ba ƴar gidan nan bace, chanza mana asalin Ummyn mu akayi da wannan masifaffiyar yarinya...." Rukky tace "ehhh! ana ce mana marasa tarbiyya ga cikakkiyar marar tarbiyya nan ai...." Ƴar Tiny fashewa tayi da kuka itama ganin mommynsu tana kuka, Baiwar ALLAH bazata iya sauraron jin kukan Hajia Kilishi ba yasa itama ta haura upstairs ta wuce ɗakin Ummy, tana shiga ta tarar da ita tanata zuba kaya acikin wata ƙatuwar akwati, Baiwar ALLAH ƙarasa shugowa tayi ta zauna a bakin gado idonta akan Ummy tace "Ina zakije kuma?...." Daƙer Ummy take motsa lips ɗinta tace "ina kuwa zanje Ni da gidan ubana...." Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "kina ganin kin kyautawa kanki? Mahaifiyarki ta fashe da kuka saboda ke, shin ribar mai zaki samu idan kin ƙuntata mata?....." Ummy ko kallon Baiwar ALLAH batayi ba tace "TOH ina ruwana...." Baiwar ALLAH cike da takaici ta ce "Allah sarki wasu suna rayuwa ba tare da iyaye ba, suna so suga iyayensu amma babu hali, ki godewa Allah daya bar miki mahaifiyarki......" Kafin Baiwar ALLAH ta iddasa maganar ta Ummy ta katseta da cewa "Kinga Aunty Baiwar ALLAH da wannan uwar tawan gwara ace uwata daga haifata ta mutu wallahi tallahi, Uhmmmmm! kinaso kisan wani abu ne akan wannan mahaifiyata? bawai bana sonta bane ɗabi'unta da halayyar ta sam ba masu kyau bane, Duk da har yau babu wanda yasan abinda mahaifiyata take aikatawa amma ya zama dole na fasa ƙwai domin bazan iya juran ganin ana cin amanar mahaifina ba inaji ina gani a matsayina na uwar masu gida wacce akafi yadda da ita akan kowa... Uhmmmmm! Aunty Baiwar ALLAH Inaso kisan cewar mahaifiyata mazinaciya ce....." A razane Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye tana furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un....." Ummy ta cigaba da cewa "Yes! Ita tayi sanadiyar rabani da masoyina wanda nake matuƙar so da ƙauna kuma nake burin Aura, akwai wanda mahaifiyata take zuwa wajensa suna yawan haɗuwa a hotel, hotel ɗin kuma anan mahaifin saurayina yake aiki, wata rana saurayina yaje hotel gurin mahaifinsa dake basuda ƙarfi sosai sai kawai ya kalli mommy da wani ƙaton mutum mai ƙaton ciki sun karɓi key, dake ita mommy bata taɓa ganin saurayina ba saidai taji labarinsa, sai saurayina yake tambayar Babansa cewar mai wannan matar take zuwa yi anan sai mahaifinsa ya sanar masa cewar ai kusan kullum suna zuwa, saurayina baiyi ƙasa a gwiwa ba haka ya bibiyesu har ya samo ɗakinda suka shiga cikin rashin sa'a basu rufe ƙofa ba, a take ya zaro wayarsa ya fara musu video suna kwance a cikin mayafi ga kayansu a gefe guda, Daga baya ya ƙirani a waya yake cemun wai in rinƙa yiwa mahaifiyata nasiha da wa'azi domin ita yanzu ba ƙaramar yarinya bace, a lokacin na samu matsala sosai dashi saboda a tunanina ya raina mun mahaifiya ne sai daga baya ya Turo mun video ta WhatsApp, a lokacin ji nayi kamar na kashe kaina, tin daga wannan lokacin na fara bibiyan wayar mommy, nayi nasarar saka mata waya a recording sannan nayi tracking phone ɗinta , duk wayar da zatayi ina jinta sannan ina sakawa ana bibiyanta duk yanda zataje, tana zuwa wajen aiki amma daga wajen aiki take wucewa hotel shiyasa bata dawowa gida da wuce sai dare, idan aka tambayeta sai tace aiki ne yake riƙeta, Amma kuma bata zuwa wannan yawon idan Abban mu yana gida saboda tasan baya wasa idan lokacin dawowarta gida yayi zai fara sa ido har saita dawo ko acikin yaran ne ma, hakan yasa na tsani mommy kuma har zuwa yanzu ta kasa chanza hali, kuma yau bata je wajen aiki ba, wuni tayi a gidan mutuminta dake shima matarsa bata nan, kuma karki manta matar mutumin ƙawarta ce, inasa ana bibiyan mommy duk yanda taje sai an ƙirani an gaya mun, Jira nake Abbah ya dawo za'ayita ta ƙare......" Baiwar ALLAH ta girgiza tajin wannan labarin Sai furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un kawai take.. Can Baiwar ALLAH ta kamo hannun Ummy ta zaunar da ita ta rungumeta a hankali take faɗin "kiyi haƙuri Ummy abinda nake so dake kar ki bari kowa yasan da wannan maganar, ki samu hajia ki zauna da ita kuyi magana ta fahimta kiyi mata nasiha na tabbata zata bari, idan ma tasan kinsan a halinda take ciki zata bari kodan saboda ke...." Jin ummy bata kulata ba yasa ta ɗago da manyan idanuwanta tana kallon Ummy, taga Ummy ta kafa ido guri ɗaya, da sauri Baiwar ALLAH ta waiwaya tana kallon bakin ƙofa taga me Ummy take kalla sai kawai taga Hajia Kilishi tana tsaye ta jingina bayanta a jikin bango kanta a sama tana zubda ƙwallah ko magana babu, a zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye ido a zare tana kallon Hajia Kilishi.......... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 21 to 22 ꧁꧂ Hajia Kilishi zama tayi a bakin gado dab da Ummy, ta juyo tana kallon Baiwar ALLAH wacce ta miƙe a zabure tana tsaye kai a sunkuye taji Hajia tace mata "Inaso ki bamu guri zanyi magana da ɗiyata...." Ba musu taja sassanyar jikinta tayi hanyar fita har zata buɗe ƙofa taji Ummy tana cewa "jirani mu fita tare..." itama ta nufi bakin ƙofar! Hajia Kilishi miƙewa tayi tsaye cikin ƙunan rai ta ce "Ummy gurinki fah nazo..." Ummy ta juyo tana mata wani irin kallo ta ce "gurina kuma? au na ɗauka ziyara kika kawowa ɗakin ai, toh indai gurina kika zo ƙafata ƙafar Aunty Baiwar ALLAH, domin yanzu itace jinin jikina, in babu ita babu Ni sannan in babu Ni to kuwa babu ita saboda haka duk abinda zaki faɗa a gabanta zakiyi idan kuwa ba haka ba wallahi bazan saurareki ba....." ta ƙarasa maganar tana yamutsa fuska. Hajia Kilishi kamar ta haɗiyi ranta tsabar takaici daƙer ta iya motsa baki ta ce "toh shikenam naji duk ku zauna...." Ummy tace "okay yanzu naji batu..." ta ƙarasa maganar tareda ɗosana mazaunenta akan kujerar mirror tana fuskantar Hajia Kilishi, ita kuwa Baiwar ALLAH tsayawa tayi ta jingina bayanta a jikin bango tana kallon ceilling, tana mamakin Ummy ta yanda take da ƙwarin gwiwar gayawa mahaifiyarta maganganu son ranta, hakan sam baiyi mata daɗi ba, ga yanzu tace indai Baiwar ALLAH bata tsaya ba itama bazata saurareta ba hakan yasa Baiwar ALLAH tsayuwa amma badan haka ba ai uwa da ƴa suna buƙatar sirri especially halinda ake ciki yanzu... Hajia Kilishi gaba ɗaya duk ta haɗa zuffa domin a tsorace take taji duk maganganun Ummy akan ta, daƙer ta iya samun ƙarfin halin cewa "Ummy dan ALLAH kiyi haƙuri...." Ummy itama kallonta take cikin rashin fahimta tace "sorry for your self...". ta ƙarasa maganar tare da kawar da kanta gefe... Hajia Kilishi kallon Baiwar ALLAH tayi sannan ta jinjina kai ita bataso ace Baiwar ALLAH tasan da wannan sirrin ba amma dan babu yanda ta iya ne, gashi yanzu mutuncinta ya zube a idon Baiwar ALLAH, haka take ta wannan tunanin.... ta Kuma cewa "duk naji maganganunki wanda dalilin da yasa kika tsaneni Kenam amma Inaso ki sani cewar dolenki Ni ce mahaifiyarki, ko ki soni ko ki ƙini Ni na haifeki Ummy, amma akwai Right ɗin da ƴa zata zauna ta bawa mahaifiyarta shawarwari masu kyau da inganci, haka itama anaso uwa ta gari ta zaunar da ƴaƴanta tayi musu nasiha da shawarwari masu kyau, amma sai dai Ni ɗin ban kasance a irin tsarin iyaye masu yin haka ba, hakan yana matuƙar damuna sosai...." Dakatar da yin maganar tayi jin yanda Ummy take kwashewa da dariya harda kama ciki, ba hajia ba hatta Baiwar ALLAH abun ya bata mamaki da kuma haushi, saida Ummy ta daidaita nutsuwarta tukun ta kalli Hajia Kilishi ta ce "ehen! cigaba mana ya kika tsayar da tatsuniyar...." Baiwar ALLAH ce ta buɗi baki zata yi magana taga Hajia Kilishi ta ɗaga mata hannu alamar dakatarwa cikin fushi ta ce "ki dakata mun bada ke nake magana ba kada naji kin tsoma mun baki, duk abinda tayi taga daidai ne a gurinta shiyasa...." Sannan ta juyo kan Ummy ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce "Ummy dariyar me kike?...." Cike da mamaki Ummy take kallon Hajia sannan tace "naji kince ƴa ta zaunar da mahaifiyarta tayi mata nasiha da shawarwari shine na hasashoki yanzu fisabilillah Mommy kece zaki zauna ƴa tayi miki nasiha? nasihar mijinki ma yaushe kika ɗauka balle na ƴaƴa, Uhmmmmm yanzu da kika ga babu wani sarki sai Allah shine zaki zo ki cikani da zaƙin baki koh? saboda Kinga asirinki yana dab da tonuwa ...." Miƙewa Hajia tayi taje gaban Ummy tana hawaye sannan ta durƙusa da gwiwowinta a ƙasin carpet ta kamo hannun Ummy tana rirriƙe su, Ba Baiwar ALLAH ba hatta ita kanta Ummy saida jikinta yayi sanyi ganin mahaifiyarta acikin wannan halin kuma saboda ita, taji ba daɗi a ranta sosai, Hajiya Kilishi ce ta soma magana cikin sassanyar murya ta ce "Ummy ƴata kisani ko mai zaki mun bazan taɓa tsanarki ba balle na gujeki, ina sonki har cikin raina , Ummy dan ALLAH ki rufa mun asiri, wallahi tallahi matsala ce tasa nake aikata haka amma yanzu nayi nadamar aikata haka a rayuwata, ba wai don saboda kar mijina ya rabu dani bane a'a saboda Inaso na tsira da mutuncina ne, shin idan aka tambayeni meya rabani da mijina mezance? idan akace saboda yawon bin hotel ne yasa mijina ya rabu dani shin ya zan kasance? shima kansa Abban nakun zaiji kunya matuƙar ace yana matsayin Chief of Army's amma matarsa tana bin wani namiji awaje, hakan bazai yuba, dan ALLAH Ummy ki temake Ni duk da ance da kunyar lahira gwara ta duniya amma duk ina neman tsari daga jin kunyar lahira dana duniya, domin a duniya matsayina ya wuce wannan layin, sannan Inaso na jawa ƴaƴana mutunci a gurin al'umma, Ummy yanzu idan kika tona mun asiri yanzu zakiga an fara yaɗani a social media da television domin mijina ba ƙaramin mutum bane haka zalika nima kuma abun kunya ne a gareku....." bata ƙarasa maganar ba kuka ya kuɓuce mata ta kifa kanta akan cinyar Ummy.... Ummy itama kukan take ta zamo daga kan kujerar ta zauna a ƙasin carpet yanda Mommynta take, tana kallon Hajia ta ce "mommy gaya mun meyasa kika zaɓi wannan ƙazamar rayuwa wanda ko mu ƴaƴanki baza muyi haka ba ..." Hajia Kilishi ta ce "akwai dalilin da yasa na zaɓi wannan rayuwar...." Ummy cike da mamaki ta ce "shin ci kika rasa ne ko sha? ko kuma kuɗin kashewa?..." Hajia Kilishi cikin nuna damuwa ta ce "ko ɗaya ban rasa abubuwan da kika lissafo ba, amma saidai na rasa lafiyar jikina shine dalilin da yasa nake bin wani a waje..." Ummy idonta akan Hajia Kilishi ta ce "bangane mai kike nufi ba ..." Hajia Kilishi tana kuka tana riƙe da hannun Ummy tace "Ummy duk cikin ƴaƴana daga ke sai Tiny a ƙarantar shekaru kinada yayu amma kuma duk kin fisu hankali da tunani mai kyau, hakan yasa na zaɓi na gaya miki sirrin abinda ke damuna tinda kema naga kin damu dani shiyasa duk sanda zan fita kike sawa a bibiyeni abinda ko Minal bata taɓa yin ƙoƙarin hakan ba, Ummy bansan wani irin halitta ne dani ba na ƙarfin sha'awa, inada munguwar sha'awa wanda idan nayi kwana biyu zuwa uku ban samu namiji ba akwai matsala babba, yawan zuwa hospital da nakeyi akan wannan matsalar ne tinda Allah ya bani miji ba mazauni ba, mahaifinku sam bai damu da mace ba, hakan yasa idan ya tafi ƙasar waje baya dawowa da wuri sai yayi watanni har shekara bai dawo nan gida Nigeria ba, shin da haka zan rayu? idan cikina ya murɗa ji nake kamar zan bar duniya tsabar azaba har saina ga namiji a kusa dani , Amma duk da hakan ban taɓa barin wani namiji daban wanda ba mijina ba ya shigeni saidai na tsaya a iya Romance, da haka zanji sanyi a raina, Ban san ya zanyi ba wallahiiii......." Nan ta ƙara fashewa da matsanancin kuka mai cin rai... Ummy juyowa tayi tana kallon Baiwar ALLAH wacce itama tana tsaye ta zuba musu ido ba ƙaramin tausayawa Hajiya tayi ba, Ummy gaba ɗaya ta rasa mai zatace abun yana shirin fin ƙarfin ƙwaƙwalwarta, ganin babu abinda zata ce yasa ta kai hannu ta rungumo mahaifiyarta tana rarrashinta tare da faɗin "kiyi haƙuri Mommy wallahi inasonki wannan rayuwar da kika ɗauko ne banaso Amma tunda lalura ce tasa Insha ALLAH zan nemo miki mafita amma ba wanda kike ciki yanzu ba, shin Abbah yasan a halinda kike ciki na lalurar nan?....." Hajiya Kilishi ɗaga kai tayi alamar eh! murya na kakkarwa ta ce "ya sani tin kafin a haifeku amma sai dai yaƙi ɗaukar maganata da serious, wani sa'in idan nayi mishi maganar nan sai yace na dena takura masa, duk da shima yana iya ƙoƙarinsa niɗin ce dai Inaso infi ƙarfinsa amma abun nashin yayi yawa shekara guda bai kusanci matarsa ba duk yana can yawon tafiye tafiyen ƙasashen waje....." Ummy gyaran murya tayi sannan tace "mommy wata ƙil ke harija ce koh?...." Hajiya Kilishi tana kuka lokaci guda ta tintsire da dariya tana dukan Ummy a gaba cikin zolaya take faɗin "ke dan ubanki aina kika san akwai Harijai ?..." Ummy murmushi tayi sannan tace "mommy nifa inada burin zama Doctor kawai dai ƙasar waje ne bazan fita ba, dole Abbah ya rinƙa guduwa kullum baya zama saboda kina shirin ƙarar masa da ruwan jikinsa, mommy inaga Aunty Minal ma ke ta ɗauko domin itama tana cikin wannan halin amma saidai ita bata bin maza, akwai maganinda take sha ta samu sauƙi kafin wani lokaci kuma du, zanje na ɗauko miki kema kina sha zaki samu sauƙin abun sosai...." Hajiya Kilishi zaro ido tayi cike da mamaki ta ce "Kenam Minal tana fama da irin matsala ta? tabbas tana yawan ciwon ciki amma banyi tunanin akan haka bane, Minal tana buƙatar Aure amma saidai taƙi kawo tsayayye wanda za'a aura mata, ta nace a wancan Christal na ƙasar Australia shi kuma Abbanku bazai taɓa Aura mata shi ba...." Ummy ta ce "tana masifar son Mohandas ɗan gidan Chief of Defence staff na ƙasar Australia amma sai dai shi ba musulmi bane kuma iyayensa bazasu barshi ya musulunta ba haka itama baza'a barta ta Auri christal ba, but suna son junansu basa son rabuwa....." Hajiya Kilishi kamar zata ƙara fashewa da kuka jin Minal irin matsalar gare ta tayi matuƙar tausaya mata sosai cikin yanayin damuwa ta ce "TOH tace idan ba Mohandas ba bazata Auri kowa ba TOH ya zamuyi mata? Kedai Ummy kisan yanda zakiyi ki temaka mun dan ALLAH, bayan isha'i ina jiranki a room ɗina...." tana ƙarasawa ta miƙe tsaye ita har ta manta da Baiwar ALLAH tana cikin ɗakin sai yanzu tayi ido huɗu da ita, bata ce komai ba tayi ficewarta........ *GA WANNAN KUYI MANAGE ZUWA DARE ZAKU GA ANOTHER PAGE KUYI HAƘURI BANDA CHAJI NE A WAYA SHIYASA.....* 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 23 to 24 ꧁꧂ Hajiya Kilishi har ta fita ta ƙara dawowa ta ce "yawwa Ummy kuɗinki dana ɗau zan baki, har ma zan ƙara miki 2millions su zama 5 sai kuje kuyo siyayyar ko? Amma yanzu dare zai yi muku ku bari saida safe idan ta kammala ayyukan gidan...." ta ƙarasa maganar tana kallon Baiwar ALLAH sannan taja ƙofa ta rufe tayi tafiyarta, Baiwar ALLAH da sauri ta nufi yanda Ummy take cike da farin ciki tace "gashi na gaya miki komai a hankali ake bin abu, Kinga kuwa kinyi nasara akanta ta sanadiyar fahimtar juna yanzu kuma naga tayi sanyi sosai...." Ummy ta ce "uhmmm! Sai naga tayi wata guda bata wuce yawonta ba tukun na yadda da nadamar Mommy, a yanzu dai jikinta yayi sanyi akan batun nan amma indai akanki ne mommy bazata ja ki ajiki ba, ai mai hali da wuya ya canza amma ina roƙon ALLAH duk rashin mutuncinda zatayi da wulaƙanci ya tsaya a iya haka banda yawon zina, domin shine babban illar dake damu na a raina, zan temaka mata INSHA ALLAHU....." Baiwar ALLAH ta ce "Allah sarki! Allah yasa ta chanza har abada sannan Allah ya kawo mata ɗauki ya bata sauƙi....." Ummy ce ta amsa mata da Ameen! A yayinda ƙwayar idon Baiwar ALLAH suka sauƙa akan wani photo dake cikin akwatin Ummy dake buɗe bata zuge ba, Ummy jin Baiwar ALLAH tayi shuru ne yasa ta waiwayo tana kallonta, itama idonta takai kan photon da take kalla, murmushi Ummy tayi sannan ta kai hannu kan photon ta ɗauka tana kallo, Idonta akan photon ta ce "wannan shine......" Bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tayi hanzarin cewa "RAZHDEEN...." ta ƙira sunan a yayin da zuciyarta ke bugun uku² gumi ne yake keto mata a duk ilahirin jikinta, wani irin yawu ta haɗiya still idonta akan photon da Ummy take riƙe da shi, Murmushi Ummy ta kuma yi sannan ta ce "yanayinsa yayi zubi da sunansa, jarumin maza Kenam kallo ɗaya mace take masa ta razana, daga kallon photonsa gaba ɗaya kin fita hayyacinki shin ina da kin ganshi a zahiri?..." ta juyo tana kallon Baiwar ALLAH ta kuma cewa "yadai? shin kina jin wani abu akansa?..." Dasauri Baiwar ALLAH ta girgiza kai tareda faɗin "ko kaɗan wallahi, wannan ba mutum bane, kyansa yayi yawa sannan ga ƙirar jiki kamar basamude sannan ga sumar gashi har gadon baya kamar mace, ina! Ina!! Ina!!! Sam bana yinsa...." Zaro ido Ummy tayi ta ce "Uncle Deen ne ba mutum baaa?, gashi yana sanye da kayan Sojansa gwanin burgewa....." ta jinjina kai sannan ta ɗauko wani photo ta ce "wannan pah?...." sakin fuska Baiwar ALLAH tayi tare da sauƙe nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce "wannan shine Roshan koh?...." Ummy murmushi tayi tace "zubinsa yayi kama da sunansa Sarkin murmushi kenam...." Baiwar ALLAH ta ce "yanzu ma gashi da kyakykyawar murmushinsa, dimple a lotse ga farin glass akan darara eyes ɗinsa gwanin burgewa wannan shine jarumi nah....." Murmushi Ummy ta kuma yi tare da ajiye photunan acikin akwatinta ta ce "saima kin ganshi anan zaki zauce ganin kyakykyawar murmushinsa dake ƙayatar da kyakykyawan fuskarsa....." BAIWAR ALLAH ta ƙagu da taga wannan kyakykyawan mutumi mai kyakykyawan zuciya wato Roshan, a hankali ta furta "wow that's awesome, ma sha ALLAH 🥰....." 🇾 🇦 🇷  ➪ 🇦 🇲 🇦 🇳 🇦  Sai da tayi wata guda a wannan yankin bata motsa ko ina ba, ga jita a waran saidai ta kaɗa jitarta ta kwanta a ƙasin wajen mai laushin gaske har bacci ya ɗauke ta, da zaran ta farka kuma zata tarar da ƙayatattun girke-girke masu ɗaukar ido, kullum da kalar abincin da ake kawo mata ga nama baje-baje haka zata zauna ta take cikinta tam tasha lemuka kala-kala, har zuwa yanzu babu mutum ko ɗaya wanda ta gani, kayan sakawa kuwa sai dai taga an chanza mata kaya Kuma kullum acikin ƙamshi take, yanzu ma kamar yadda ta saba tana zaune da wata ƙaramar jita a hannunta tanata kaɗawa sauti mai daɗin gaske yana tashi, tana cikin wannan halin taga wani ƙaramin kifi ya fito bakin ruwa ya kasa komawa sai mutsil-mutsil yake, a hankali ta miƙe tsaye tana riƙe da jitarta a hannu ta nufi bakin ruwan wanda tinda aka kawota nan bata taɓa zuwa wajen ruwan ba balle tayi ƙoƙarin shiga sakamakon ganin kalar ruwan mai launin green ne sai ruwan yake bata tsoro, a wannan lokacin tazo dab da ruwan da niyar temakawa kifi tasa hannu ta ɗauki kifin a hankali ta zura hannunta acikin ruwan ta maida kifin ciki, wanin irin sanyi taji ruwan yayi mai ratsa jiki, jin daɗin ruwan yasa ta zura ƙafafunta ciki ta zauna a bakin ruwan tana murmushi, ta ɗauki jitar ta fara kaɗawa a hankali, gani tayi ƙafafunta sun fara komawa kalar ruwan wato green, yana bin duk ilahirin jikinta nan danan fatar jikinta ya koma launin green har fuskarta, Daga wannan lokacin bata tsinci kanta ba sai a bakin titin ƙwalta tana kwance ga jitarta a gefe tana riƙe dashi amma saidai ba'a cikin hayyacinta take ba, Bata tashi farfaɗowa ba sai tsakiyar dare sakamakon ruwan sama da aketa zabgawa domin ruwan ne ya farfaɗo da ita, tashinta ta fara waige-waige ko zataga wani a gefenta amma babu kowa ga yanda ruwan sama yake dukanta, ta koma asalin launin jikinta daman wannan ruwan shine zai kai mutum ainahin yanda yake da zarar ka shiga wannan ruwan, a yanzu dai Ƴar Amana ta tsira daga zaman can ta dawo Nigeria yanda take, yanzu kuma zata fara neman mafita akanta tinda a halin yanzu ba'a hannun kowa take ba, tana free..... Bayan Watanni Uku (Three months later) Wasu Manyan Jirage ne suka sauƙa a airport guda biyu, Ɗaya jirgin Australia (U.S) Ɗaya kuma jirgin ƙasar Egypt ne, Sai jerukan motoci guda ɗari manyan baƙaƙen motoci masu taya ta baya guda hamsin sai motoci masu kakin Soja suma sunada taya ta baya guda hamsin, Ga manya-manyan security masu manyan bindigu, security masu baƙaƙen kaya sune motocinsu baƙaƙe sai kuma motoci masu kakin Soja su kuma sojoji ne aciki, Wanda yake jirgin ƙasar Egypt ne ya fara fitowa, Innalillahi wa inna ilaihi raju'un 😳😳 wani kyakykyawan gabjejen saurayi ne fari tass yana sanye da fararen kaya suit ajikinsa, fuskar nan yana ɗauke da kyakykyawar murmushi, hannunsa ya miƙawa na gefensa wanda yake escort nashi ya miƙa masa wani ɗan siririn farin glass saida yasa farin handkerchief sannan ya goge ya ɗora glass ɗin akan dara-daran idanuwansa farare masu ɗaukar ido, haka yake bin security wajen da kallo da ko ina still da wannan murmushi akan fuskarsa, ga wasu ma'aikanta waɗanda suke jan akwatinansa zuwa motocin da aka tanadar musu, Wani ne daga cikin security sa masu baƙaƙen kaya yazo gabansa yana faɗin "your welcome Doctor, we should go......" Hannu ya ɗaga masa ba tare da yace komai ba, idonsa akan jirgin Australia yana jiran fitowar twins ɗinsa, kafin ya ɗage eyes ɗinsa sai ga wani sangamin mutumi ya sauƙo daga nashi jirgin, Innahu min Sulaimana wa Innahu Bismillahi Rahmani Rahiim, Alla ta'àlu alayya wa'àtuni muslimiinn........ RAZHDEEN yanda kasan ba jinsin mutane ba tsabar kyau da ƙirar sura mai kyau ga sumar gashi mai ɗaukar ido sai sheƙi yake tsabar baƙi shi kuwa kamar jini zai fito a jikinsa, Sojan hutu kenam, Duk farin Roshan da kyansa bai kamo ƙafar Razhdeen ba duk da shima Roshan ɗin Duniya ne, Fitowar Razhdeen tsayawa yayi yana lumshe Golding eyes ɗinsa, yana sanye da farar t-shirt a jikinsa ga rigar ta kama jikinsa sosai sai ƙirar ƙarfin jikinsa kake gani yana bayyanowa, wandon jikinsa kuma kakin Sojan U.S ne, takalminsa mai sawu ciki ne na sojoji shima mai kakin Soja, sumar gashinsa yasha gyara sosai zuwa sajen fuskarsa ba ƙaramin kyakykyawan mutum bane Razhdeen sai dai fuskar nan ba Annuri ko kaɗan, A hankali yake taka ƙasi kamar mai tambayar ƙasa nufan gurin Roshan yayi, Shima Roshan da murmushi a fuskarsa ya nufi yanda Razhdeen yake, suna haɗuwa suka rungumi junansu sosai kowa yana kewan ɗan uwansa, daga bisani suka rabe jikinsu Roshan kamar zai tashi sama tsabar farin cikin ganin ɗan uwansa twins ɗinsa tsawon shekara guda ba'a haɗu da juna ba, Cikin nuna farin ciki Roshan ya ce "I missed you my Man...." Shima Razhdeen duk da ba dariya yake yi ba sannan ba murmushi yake ba amma fuskarsa a sake yake alamun nuna farin ciki shima ya ce "I missed you too my twins...." suka sake rungumar juna a karo na biyu daga bisani suka rabe jikinsu suka jeru suna taku cikin ƙasaita da nuna mulki, duk da tsayin Razhdeen amma da kaɗan yafi Roshan tsayi domin shima Roshan gabjejen mutum ne ba laifi amma saidai Razhdeen yafi Roshan faɗin jiki da faɗaɗɗan ƙirji sosai.... Duk wanda ya gansu sun jerun nan suna taku sai ya yabesu domin ba ƙaramin burge mutanen wajen sukayi ba, Suna isa dab da wata kyakykyawar mota wanda sabo ne yau aka ɓarota saboda twins, a gaggauce Security yayi saurin buɗe musu murfin motar duk suka zauna a back seat iya su biyu sai wanda zai yi driving nasu, Sauran yawan motocin kuma duk ƴan rakiya ne, Motarsu ce ta fara yin gaba sai sauran motocin suka biyo bayansu a jere cikin slow ake bin motocin ba hayaniya ko jiniya, wannan taryar da akayi musu ko president iyakaci, duk yanda suka wuce sai an tsaya ganin motocin da yawansu kuma gasu a jere suke tafiya, sauran motocin kan hanya ne suka fara kakkauce musu, RAZHDEEN ganin suna kutsawa cikin gari yasa shi cewa "YOU...." security mai driving ne ya dakatar da tuƙin yana sauraron Razhdeen, kamar bazaiyi magana ba murya ciki-ciki wanda saika kasa kunne kafin ka jiyo shi kuma magana ɗaya yake yi baya maimaitawa ya ce "bana son wuce wa ta cikin gari, mu zagaya ta bayan gari...." Security ya ce "okay Sir...." ya karya kwana suka wuce ta wata hanya wanda zai zagaya dasu bayan gari, Roshan ne yayi murmushi yana jinjinawa Twins ɗinsa tareda maganar zuci "My Man Kenam har yanzu kana nan da wannan halin nakan...." Sauran motocin ne suma suka bi bayansu, tafiya suke sosai domin ba ƙaramin ƙarawa kansu nisa sukayi ba, inda ace ta cikin gari suka bi da yanzu sun isa gida, kaɗan ya hana su fita cikin gari su zagaya kafin su isa gida, Razhdeen yayi saurin dakatar da security tare da faɗin "wait...." dakatar da tuƙin akayi suma motocin bayan tsayawa sukayi, Roshan ne ya juyo yana kallon Razhdeen cike da mamaki ya ce "My Man! ya zaka dakatar damu acikin jeji?...." Razhdeen ƙwayar idonsa ya wurga cikin jejin yana bin jejin da kallo sakamakon jin sautin jita yana tashi kaɗan-kaɗan, irin sautin da yake ji acikin mafarkinsa, Juyowa yayi yana kallon Roshan cikin sassanyar murya ya ce "bakaji wani irin sauti mai daɗin gaske yana tashi ba?....." Girgiza kai Roshan yayi tare da faɗin "Nop i didn't hear any sound, na dai ji kukan tsuntsaye, please my man let us go home ina tsoron waran nan ......" Razhdeen buɗe murfin motar yayi tare da furta "Uhmm! har yanzu baka zama jarumi ba, zanje na dubo aina sautin nan yake tashi...." har zai kutsa cikin jejin Roshan yayi saurin riƙo shi yana girgiza masa kai ya ce "Please my man kazo mu wuce gida, babu abinda zaka gani acikin jejin nan sai abin cutarwa...." Suma sauran Sojojin ganin twins sun fito yasa duk suka fiffito da bindigu a hannayensu, Sai a yanzu kowa ya fara jin wannan sautin yana tashi da ƙarfin gaske, sautin ne yake dukan dodon kunnen Razhdeen, lumshe eyes ɗinsa yayi yana sauraron sautin mai kashe jiki exactly irin sautin da yake ji acikin mafarkinsa ne, Razhdeen yana shirin fizge hannunsa daga riƙon da Roshan yayi mishi zai shiga cikin jejin, Roshan ya kuma riƙe shi sosai yana faɗin "My Man Nima inajin sautin amma idan na barka ka shiga baka san me zaka tarar ba, wata ƙil Aljana ce take ruɗanka da wannan sautin, please kazo mu tafi don't worry komai zai zo maka cikin sauƙi....." Daƙer Roshan ya samu ya shawo kan Razhdeen da lallami suka shige motar, suma sauran Sojojin shigewa sukayi suka fara tafiya, Still idon Razhdeen a saitin yanda yake jiyo sautin yana tashi, daga bisani ya kwantar da kansa akan kujerar motar tare da lumshe kyakykyawan idanuwansa, sai bayan sun shiga cikin gari tukun ya daina jin sautin jitar..... Basu yi tafiya mai nisa ba suka sha kwanar da zai sadasu da ƙayataccen unguwarsu mai ɗaukar ido, suna shiga layin unguwar tin daga farkon layin har ƙarshenta sojoji ne a jere ko wanne yana riƙe da bindigarsa.... Gidan kuwa an tsara shi yayi mungun kyau ta ko ina filawowi ne a gidan, Idan aka zo kan babban falon gidan Wayyo Aljannar Duniya Kenam, musamman ƴan aiki aka ɗauko daga ƙasar waje domin su gyara gidan, da masu abinci girke-girke kala-kala kusan guda 15 ko wanne da kalar abinci acikin flask duk saboda dawowar twins, A yaran gidan kuwa duk babu mai wargi da walwala sai Ummy, itace mai nuna farin cikin dawowarsu, Hajiya Kilishi tana can upstairs cikin bedroom ɗinta domin tinda su Razhdeen suka dawo shikenam babu farin ciki daman ba ƙaunarsu take ba, Minal da ƴanmata twins Pinky da Ruky suna zazzaune akan kujerun falo sunci kwalliya sosai amma sai dai ba walwala, bawai basa farin cikin dawowarsu bane don saboda daga yanzu zasu Fara takura, bazasu samu ƴancin kansu kamar baya ba, Ummy kuma sai zarya take acikin falon tana jiran shugowarsu, jin an buɗe last gate wanda daga shi sai babban falo yasa Ummy razana cike da zumuɗi ta kwallawa Baiwar ALLAH ƙira wacce itama a kitchen take tana fargaban ganin twins domin jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, sai wani ɗarɗar take tana jin tsoro, jin ƙiran Ummy yasa ta razana tana sauƙe numfashi sama-sama ta ce "na shiga uku sun shugo...." Ummy ta ce "ganan Yaya Roshan kiyi saurin kawo Apple ɗin, farkon dawowa farkon cin Apple kar ki bari su wuce....." Baiwar ALLAH jin an ambaci Yaya Roshan yasa tayi saurin ɗaukar tray mai ɗauke da kayan fruits tayi cikin falo da sauri, Domin Hajia Kilishi ce ta sanarwa Baiwar ALLAH cewar suna shugowa ta kai musu kayan fruits da juice duk da bata sonsu amma hakan bai hanata sa a kyautata musu ba.... Baiwar ALLAH zuwa tayi ta tsaya a bakin ƙofa wanda suna shugowa zasu ɗauka, amma kuma a tsorace take sosai har jikinta ɓari yake, Ummy tana daga bayanta tana tsaye tanaso taga yanda Baiwar ALLAH zatayi idan tayi ido huɗu dasu, Su Minal kuma sunyi shuru duk sun sha ruwan jikinsu, kowa da abinda yake tunani a ransa na haɗuwa da Uncle Deen domin shine macijin mai sara.... Buɗe ƙofar falo akayi a yayin da security masu escorting suka tsatstsaya a bakin ƙofar falon shi kuwa gogan ya shige, Baiwar ALLAH ta tafo da sauri akan zata miƙawa Yaya Roshan ya ɗauki fruits acikin glass tray kawai idanuwanta suka sauƙa akan kyakykyawan fuskar Uncle Deen ga sumar gashi sun sauƙo har kafaɗa, sajen nan ya kwanto har zuwa gemu da waran gashin baki duk sun kwanta yayi luf sai ƙaramin baki wanda yaci red sosai kamar wanda ya shafa jan baki, fuska kuwa ba Annuri... Baiwar ALLAH ganinsa yasa ta ƙafe a wajen idonta kuwa akansa duk da ba'a cikin hayyacinta take ba, Wani irin kallo ya watsa mata ganin yanda ta fita hayyacinta lokaci guda Ko sauraron ta bai tsaya yi ba haka yabi yana taka matakalar Beninsu yanda zai kai shi part ɗinsa domin a gajiye yake yana buƙatar hutu baya son hayaniya.... Su Minal duk miƙewa sukayi tsaye suna mishi your welcome amma ko kulasu bai tsaya yi ba da haka ya wuce abinsa.... Ita kuwa Baiwar ALLAH baya tayi zata faɗi Ummy tayi saurin tarota, har ta sume a wajen, daƙer Ummy ta jata ta shige da ita bedroom ɗin ta wato ɗakin Baiwar ALLAH shine a ƙasin falo... Shima Roshan yana can yana ta gaggaisawa da mutane, Abbansu ma ya dawo shima yana waran taron manya-manyan mutane waɗanda sukazo ganin twins wato Razhdeen da Roshan, shidai Razhdeen ƙin tsayawa yayi domin baya son yawan hayaniya.... Ƴar Amana kuwa tana cikin jejin da su Razhdeen suka wuce domin ita take kaɗa jitarta..... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 25 to 26 ꧁꧂ Abba ne ya fara shigo wa cikin falon yana ɗauke da murmushi alamun yana cikin farin ciki sosai, ya zauna a ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon, kallo ɗaya yayi wa ƴan matan gidan yasan akwai matsala domin ko wacce babu Annuri a fuskarta especially Minal babbar cikinsu sai Pinky da Rukky dake zaune a two seater, yasau fuskarsa tareda faɗin "Meya sameku na ganku a haka ana cikin farin cikin dawowan ƴan uwanku?...." Minal ce ta fashe da kuka hannunta akan fuskar irin kukan sakalcin nan, Abbah ya ce "A'ahhhh sirikata ya haka kuma, gaya mun meya faru?...." a cikin kukan take faɗin "yanzu fisabilillah Abbah shin ya dace haka?...." Abbah ya ce "ehen go ahead inajinki...." ta cigaba da cewa "tsawon shekaru uku yanzu bamu gana da Uncle Deen da Yaya Roshan ba, munata zumuɗin ganinsu amma Uncle Deen saboda bai damu da mu ba muna mishi ur welcome but he didn't answer us why Abbah? wani irin laifi mukayi masa ne wanda bazai iya yafe mana ba, tin muna yara bamu tashi munga Uncle Deen cikin fara'a ba, kodai baya son kasancewar mu acikin gidan nan ne? Abbah gaya mun Ni saina bar masa gidan...." ta ƙarasa maganar tana kuka... Abbah gaba ɗaya jikinsa ne yayi sanyi 🥺 nan take yaja wata doguwar ajiyar zuciya yana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya ya ce "kuyi haƙuri bawai manufarsa haka bane, daman can Razhdeen haka halinsa yake tin yana yaro, kunga kuwa tin kafin a Auro mahaifiyarku kenam balle yayi tunanin za'a samo ku, ga misali ɗaya shin haka Roshan yake? kunga dai twins ne amma ko wanne da kalar halayyarsa, sauƙar Razhdeen daga cikin mota bai tsaya kula kowa ba haka ya wushe al'umma waɗanda suka taru saboda su yayi tafiyarsa, ko Ni nam Razhdeen bai tsaya saurarona ba balle ku, so saboda haka kuna masa uzuri inda sabo ai kun saba da halin Razhdeen saidai ku bada labarinsa a wasu, kuyi haƙuri Sirikata babu yanda zan yi da Razhdeen sai dai Addu'a......" Suna cikin wannan halin sai ga Roshan ya turo ƙofa da sallama a bakinsa yana ɗauke da Ƴar Tiny a kafaɗarsa, Pinky da Rukky ne suka tashi da sauri suka nufi yanda yake, shima da murmushi a saman fuskarta ya rungumosu jikinsa yana faɗin "wow my beautiful twins, ƴanmata an girma...." Dariya suka yi suna faɗin "your welcome Yaya Roshan, we really missed you...." Shima dariya yayi tare da faɗin "me too my beautiful twins...." Minal tana daga zauna akan kujera tace "your welcome My Bros...." Kallonta yayi tare da sauƙar da ƴar Tiny dake hannunsa yace "ke ɗin bazaki taso kimun oyoyo bane?..." Murmushi tayi sannan ta tashi tana zuwa yanda yake ta rungume shi tana dariya, shima dariya yake ya ce "well done Amaryar Marshall Mohandas...." Dasauri ta kifar da kanta saman ƙirjinsa a hankali take faɗin "please Yaya Roshan kar kasa Abbah ya fusata..." Shima raɗa yayi mata a kunne tare da faɗin "Kenam har yanzu ana kan chaƙwakiyar ne?..." ta ce "uhmmm Yaya Roshan Kenam kaima kasan inba Marshall ba bazan Auri kowa ba, sai dai a cigaba da drama...." Duk acikin raɗa suke maganar ba tare da kowa yaji abinda suke faɗi ba, ɗagowa tayi suna dariya, Abbah ya juyo yana kallonsu ya ce "Auu munafurcin mai ake yi ne nake jin ƙusƙus......" Ƴar Tiny ce ta nufi gurin Abbah da gudu tana faɗin "Abbah bayi na gaya maka Aunty Minal ce ta ce bajata Auyi kowa ba inba Yaya Matall Moandas ba...." ta ƙarasa maganar cikin tsatstsamar bakinta... A fusace Abbah ya kalli Minal cikin ɓacin rai! kafin kace me Minal tayi gudu ta haura upstairs kai tsaye ɗakinta ta nufa domin tasan Abbah yanzu zai fara tadawa kowa hankali akan batun nan..... Hajiya Kilishi ce itama ta sauƙo tana sanye da wata danƙareriyar less ɗinta mai bala'in tsada, tasha makeup ba ƙaramin kyau tayi ba, tayi fari fat da ita duk da tana ɗan haɗawa da bleaching, ta nemi kujera ɗaya itama ta zauna dab da Abbah idonta akan Roshan ta ce "ur welcome Son..." Shima yana ɗauke da murmushi ya ce "thank you Hajia, fatan na sameku lafiya..." kamar baza tayi magana ba can ta ce "we are all fine..." ya ce "Ok thank God...." Abbah ya ce "Amm Roshan kaje ka rage kayan jikinka kayi wanka sai kuzo ga kayan abincin da aka tanadar muku, gaba ɗaya zamu haɗu a dinning ne inka fito sai kayi wa Razhdeen magana...." ya ce "okay Dad..." Har ya fara haura saman stairs ɗinsu ya dawo yana baza eyes, Abbah ya ce "lafiya kuwa?...." yana ɗauke da ƙayataccen murmushi ya ce "where is my love?...." Abbah murmushi yayi domin duk gidan babu wanda bai san ita kaɗai yake ƙira da haka ba, shima Abbah cewa yayi "Nima sauran kaɗan na tambayeta ka rigani..." ya kalli Pinky ya kuma cewa "wai ina Uwar masu gida ne? ban ganta ba tinda na shugu...." Pinky ta ce "uhmm tana ɗakin Baiwar ALLAH..." Abbah ya ce "ha'a toh su fito falo mana, ita uwar masu gida tasan lover ɗinta ya dawo shine bazata zo yi masa oyoyo ba..." Rukky tayi saurin cewa "Abbah Baiwar ALLAH ganin Uncle Deen yasa ta sume shine Ummy ta tafi kaita ɗakinta...." Abbah kallon Hajia yayi yaga ko Annuri babu a fuskar nan ya ce "ikon ALLAH, ita kuma ganin Razhdeen ya sata suma, ba shakka indai Razhdeen ne kaɗan Kenam daga aikinsa....." Roshan ganin bai fahimci maganganunsu ba yasa ya haura upstairs tare da faɗin "saina sauƙo..." Bayan haurawarsa da mintuna talatin saiga Ummy ta fito tana tura lips cikin sakalci take jumping da sawayenta tace "Ni har yanzu My love bai shugo bane?....". Pinky tana zaune idonta akan Ummy tana harararta ta ce "ke dillah bama son hauka...." Ummy turo baki tayi ta ce "Ni bada ke nake ba kiyi mun shuru...." Rukky ta ce "tselan uwa sakalcin banza dan ma bake bace Autar yau da an shiga uku ...." Ummy tana nuna Rukky da yatsa tace "Kee nutsu ki kama kanki ai ba'a kanku nake ba...." Abbah ya katse su da cewa "Kinga uwar masu gida jeki masoyin nakin yana can ɗakinsa,.." ya kalli su Pinky ya ce "ku kuma babu ruwanku da ita..." Rukky tace "ai wallahi Abbah kai kake goya mata baya shiyasa ta raina mutane..." Abbah ya ce "ku kuka jawa kanku raini dai, yanzu da bakuyi mata shishshigi ba ai baza tayi ƙoƙarin gaya muku magana ba...." Pinky ta kalli Rukky sannan ta ce "zo mu koma ɗaki..." suka wuce suna turo baki, sai ya rage daga Abbah sai Hajia sai kuma ƴar Tiny wacce itama tashinta kenam wai zataje gurin Uncle Deen. Abbah ganin har zuwa yanzu Hajia bata saki fuskarta ba yasa ya matsa kusa da ita ya riƙo hannayenta yana murzasu a hankali idonsa akan fuskarta ya ce "ya akayi ne matar bindiga?..." Kallonsa tayi sannan ta ƙara kawar da fuska gefe ta ce "babu komai..." Yace "no kina cikin damuwa ne yakamata ki sanar mun koh? tinda na dawo yau sati guda amma babu walwala kodai nayi miki laifi ne?...." Girgiza kai kawai tayi alamar a'a tace "bana jin daɗin jikina ne..." "Meya same ki?" yayi maganar cikin sassanyar murya, kamar zata yi kuka ta ce "marata ciwo....." murmushi yayi domin yasan damuwarta ya kamo hannunta ya ɗago da ita yana faɗin "sorry my dear muje daga ciki ko kafin yaran su fiffito dinning...." tashi tayi itama tana murmushi suka haura upstairs yanda part ɗinsu yake .... A Ɓangaren Doctor Roshan yana kwance saman katafaren gadonsa wanda yasha gyara ɗakin sai fitar da ƙamshin turare yake, yana lumshe da ido kamar meyin bacci tsabar zunzurutun gajiya, Ummy ce ta turo ƙofa cike da zumuɗin ganin masoyinta kuma ɗan uwanta, shugowa falon tayi taga wayam babu kowa sai jerin tsararrun kujeru na alhurma ga plasman a manne a jikin bango sai showing indian Film ake, gefe guda kuma wani ɗan ƙaramin frig ne gwanin burgewa, sai kuma ƙaramin dinning table wanda iya mutum biyu kawai yake ɗauka, falon ya tsaru sosai, Murmushi Ummy tayi a fili tace "yanzu haka yana cikin bedroom ɗinsa..." tana zuwa dab da bakin ƙofar bedroom tasa hannu tana knocking a hankali gudun kar ta kutsa masa kai tsaye bata san a wani hali yake ba, Yana kwance yaji ana knocking ido a lumshe ya furta "Yes come in...." turo ƙofar tayi ta shugo tana ganinsa a kwance tayi gudu ta nufi yanda yake tayi tsalle ta faɗa masa jikinsa tana dariya.... shima dariyan yake ya ce "kai kai Kaiii my love wannan ai saiki karyani irin wannan tsalle haka...." Ta ɗago tare da faɗin "oyoyo my love wallahi nayi kewarka sosai, amma kai baka damu dani ba tinda har ka shugo baka nemeni ba......" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa jan kuncinta yayi yace "Ni na isa naƙi damuwa da uwar masu gida wane niii, kina raina sosai kamar yanda nake ranki tinda naga kullum saikin ƙira masoyinki Roshan a waya...." Dariya tayi ta ce "yawwa Yaya Roshan ina tsaraba taa..." Saida ya tashi zaune yana fuskantar ta ya ce "tsaraba kam sunanan lodi-lodi sai kin zaɓa kin darje kafin sauran su ɗauki nasu...." ta ce "wow shiyasa nake ji dakai Yaya Roshan ɗina saboda kaima kana ji dani ...." yana kallonta fuska ɗauke da murmushi ya ce "ya za'ayi bazan damu dake ba? kepah kinada darajoji da yawa a gurina...." zaro ido Ummy tayi tare da bugan ƙirjinsa tace "kaiiii Yaya Roshan toh lissafo mun...." Saida ya gyara zamansa tukun ya fara cewa "na farko ke mai sunan Hajiyar mu ce marigayiya wato mahaifiyar Abban mu wacce tin muna jarirai take riƙe damu, ita ta sakaltar damu, bata son ko cinyaka ta cije mu, duk abinda muke so zatayi ƙoƙarin yi mana, shiyasa muke matuƙar ji da kakar mu har Allah ya karɓi rayuwarta, Na biyu kuma again sunan my first lover gareki, Allah sarki Maryama ta mutumiyar kirki ga yawan fara'a, kyakykyawar hallita lokaci guda nayi rashinta, da yanzu na tabbata munada ƴaƴa amma mutuwa tayi mun yankan ƙauna, a waɗanda nafiso a raina daga mahaifiyata wacce ta rasu sanadiyar haihuwar mu sai kuma Kakar mu wacce tayi rainon mu har rai yayi halinsa sai kuma Abar ƙaunata Maryama wacce tayi hatsarin mota tabar duniya....." Ummy Turi baki tayi cikin shagwaɓa ta ce "Kenam Ni banda Ni acikin sahun masoyanka? daman nuna soyayyarka bai je zuciya baaa...." Yaya Roshan ya ce "ki fahimce Ni My love! inada waɗanda nake so da yawa, waɗannan wanda na lissafo su sune sukafi soyuwa a cikin zuciyata, in hakane ai ban lissafo da Abbah ba kuma Kinga ai bazance bana sonsa ba...." Ummy fuska a turɓune ta ce "toh wacece ta huɗu?..." tayi tambayar a shagwaɓe, ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce "My man! wato twins ɗina Razhdeen sai ta biyar kuma itace Uwar masu gida wato my love...." ya ƙarasa yana jan kuncinta ya cigaba da cewa "sai na shiga kuma Abbana, sai kuma sauran masoyana waɗanda suke sona nima nake son su....." Ummy tana jinjina kai ta ce "wato Ni ce ma ta biyar uhmmm hakane...." tintsirewa yayi da dariya yana jan lips ɗinta domin ba ƙaramin dariya ta bashi ba, Saida suka gama shan hirarsu sosai kafin ya tashi yana faɗin "uhmmm my love idan na biyeki sai mu kwana muna zance, yanzu dai bari na shiga wanka, naji Abba ya ce gaba ɗaya zamu haɗu a dinning kar su fara jiran mu...." Itama Ummy tashi tayi ta ce "TOH my love idan ka kammala muna jiranka a ƙasi...." Ɗaga mata hannu yayi tare da shigewa toilet..... Bayan fitar Ummy kai tsaye part ɗin Uncle Deen ta nufa tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofa tana knocking a hankali domin tasan halinsa muddin ta shiga bada izininsa ba saiya korota duk da baya yawan zama a falonsa sai dai idan wani aiki zai yi a computer yakan zo falo ya zauna akan sopa computer kuma tana kan ƙaramin glass table na tsakiyar falon, tana cikin knocking taji muryar ƴar Tiny tana faɗin "yeshhh coming..." Ummy acikin ranta tace "shegen iyeyi har wani yesh coming..." shugowa tayi da sallama a bakinta ta tarar da Uncle Deen yana zaune sai faman danna computer yake ita kuma ƴar Tiny tana gefensa da wani ƙaton Biscuit mai madara a hannunta, motsa baki kawai Uncle Deen yayi ba tare da anji mai ya ce ba, amma alamu ya nuna cewar amsa sallamar yayi, zuwa tayi ta zauna gefen ƴar Tiny tace "Uncle Deen your welcome...." a taƙaice ya ce "Ok" ba tare da ya ɗago ba, Ɗaga kafaɗa Ummy tayi alamar bata damu ba, domin kaɗan Kenam daga halayen Uncle Deen, inka san halin mutum saika sha maganin zama da shi.... Ummy kallon ƴar Tiny tayi sannan ta ce "Tiny ɗan sammun biscuit ɗin mana, Kinga babu kalar shi a Nigeria na daɗe banci ba...." Ƴar Tiny hararar Ummy tayi sannan ta ce "wayyayi tayyayi balan bayal ba, ki tambali Unkui Deen mana...." Ummy cikin ɓacin rai ta ce "shegiya mai tsatstsamar baki....." bata ƙarasa maganar ba taga Uncle Deen ya jefo mata wani irin kallo har sai da ta razana, ga yanayin juyowar nashin yasa sumar kansa wantsilowa zuwa fuskarsa sai dara-daran idanuwa kake gani ta cikin sumar gashin, Haka ƙirjinta yake bugun uku uku sai yanzu ta tuna ashe ba'a zagin Ƴar Tiny a gabansa saboda takwarar mahaifiyarsu ce wato FATIMA BINTU, sunan mahaifiyarsu Razhdeen da Roshan, shine aka sanyawa ƴar Tiny sunanta, Amma Razhdeen da Roshan basa ƙiranta da ƴar Tiny saidai Mama... Ummy tashi tayi suƙu-suƙu zatayi waje yayi saurin dakatar da ita tare da nuna mata wata ƴar jaka wanda cikinsa zallar biscuit ɗin ne, jiki ba ƙwari haka taje tasa hannu ta ɗauka tare da yin godiya, idonsa akan computer ya ce "tsarabar Mamana ne saboda haka a ita zakiyiwa godiya...." Ummy ta kalli ƴar Tiny tace "Nagode Tiny..." turo baki ƴar Tiny tayi sannan ta ce "a shaye zaki yi mun gojiyar? ki durkusha kashi kimun gojiyar....." wani irin yawu na baƙin ciki Ummy ta haɗiya cike da jin haushin ƴar Tiny ta durƙusa da gwiwowinta ta ce "Nagode sosai Ƴar Tiny...." ta miƙe idonta akan Uncle Deen wanda yasa hannu yana ture sumar kansa zuwa baya eyes ɗinsa akan computer ko kallonsu bai yi ba, Ummy taja ƙafa zata fice taji Uncle Deen yayi magana, Dasauri ta waiwayo tana kallonsa ta ce "na'am!..." Domin sam bata ji me ya ce ba, amma taji kamar yayi mata magana, murya ne kamar ba'a halitto shi ba bayason fitar da Muryar, Shi kuwa a ƙa'idarsa magana sau ɗaya yake yi baya maimaitawa, Jin yayi mata shuru ya cigaba da uzurinsa yasa ta kalli ƴar Tiny ko zata temaka ta maimaita mata abinda ya ce, Ƴar Tiny tana tura biscuit a ɗan ƙaramin bakinta ta ce "waiii Keee kuymiya ce? aka ce kije ki kiyawo An uwanki shu jo Nam...." Ɗaga kai Ummy tayi tare da faɗin "tam shikenam...." Dasauri tabar ɗakin domin ba ƙaramin ƙuluwa tayi da ƴar Tiny ba, A cikin ranta kuwa cewa tayi "wannan ƴar Tiny saina ci ubanki wallahi, ƴar Banza kawai tsatstsamar bakinki ma ya isheki...." Da wannan takaicin ta sauƙa falo tana sauƙa kuwa ta tarar da su gaba ɗaya suna zazzaune, tazo ta tsaya a kansu tare da faɗin "TOH Guys Big bros yana ƙira...." Minal ta ce "ke dallah in zakiyi magana ki buɗe baki mu sa'anninki ne..." Ummy ta ce "a'ahhh zakuyi bayani ne to Uncle Deen ne ya ce duk a ƙira masa ku...." Pinky Sarkin tsoro a razane ta miƙe tsaye tareda dafa ƙirji ta ce "Mun shiga uku me mukayi kuma daga dawowarsa?...." Rukky ta ce "ke kina magana a hankali Kinsan yanada kunne wallahi...." ta ƙarasa maganar tana riƙe da hannun Pinky wanda duk ɗinsu jikinsu ne yake ɓari kamar masu jin sanyi, Minal miƙewa tayi itama tana kallon Ummy ta ce "lafiya kuwa? kodai wani abu ne?...." Itama a tsorace take sai dai bata nuna tsoron natan a fili ba... Ummy ta ce "Uhmmm kuma dai kunsan ƙiran Uncle Deen ba lafiya bane, sannan kuna ɓatawa kanku lokaci ne, in har bakuje da wuri ba akwai matsala ga takaicin ƴar Tiny da zaku shaƙo...." Minal ta ce "kunga kuzo muje koma menene tinda ba kashe mu za'ayi ba ai da sauƙi..." Har sunyi gaba suka juyo sukaga Ummy ta nemi guri ta zauna Minal ta kuma cewa "haka kuma idan ƴar aike bata koma ba akwai matsala...." Ummy tsuka taja tare da miƙe wa tabi bayansu itama duk suka haura upstairs can ɓangaren Uncle Deen...... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 27 to 28 ꧁꧂ Jiki a sanyaye suka tura ƙofar ɗakin Uncle Deen da sallama a bakinsu, Minal ce ta gaba su kuma Pinky da Rukky suna daga baya² jiki sai ɓari yake, Ummy ce tayi ƙarfin halin cewa "Uncle Deen ga sunan ..." yana zaune a yanda yake ko motsawa baiyi ba still eyes ɗinsa akan computer sai faman danne-danne yake ko sauraronsu baiyi ba, Sai da suka ɗau tsawon mintuna 15 suna tsaye bai kulasu ba, sai ƴar Tiny ce ta ce "Ankui Deen gashunan sunata shaye tin ɗaju....." Daiden lokacin ya ɗago da kansa tare da rufe computer sa yana binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, ya miƙe tare da faɗin "kuyi mun kneel down a wajen tinda baku iya gaisuwa ba, today I will teach you how to respect someone...." duk zaro ido sukayi a tsorace, Minal ce ta ce "Uncle Deen shugowarka munyi maka magana baka kula mu ba...." kafin ta ƙarasa ya juyo a fusace yana mata wani irin kallo na ɓacin rai, ai tinin duk suka durƙusa kamar zasuyi kuka, Ummy itama ƙafarta ne yake kakkarwa ta ɗan sunkuya ita bata durƙusa ba sannan kuma ba'a miƙe take ba tana son jin abinda zai ce dangane da ita tinda tazo ta gaishe shi, har zai shige bedroom ɗinsa ya sake juyowa yana kallon Ummy ya ce "you leave my room...." Da hanzari Ummy ta fice a ranta take faɗin "Better...." sannan ya nuna Pinky da Rukky ya ce "two of you go and wear your trousers...." a tare suka haɗa baki waran cewa "akwai wandina a jikin mu...." suka ƙarasa murya na kakkarwa, ya ce "Ok stand your legs up...." Pinky da Rukky kallon juna suka shiga yi domin sun san abinda yake nufi, kafin su ankara suka ji ya darara musu tsawa tare da faɗin "ko baza kuyi bane?...." Dasauri suka ɗaga ƙafafuwansu saman jikin bango, hannayensu a dafe a ƙasi suna kallon ƙasin carpet, ga hawaye shaɓe-shaɓe.... ya kalli Minal wacce take durƙushe itama tana kallon gefe guda, tsananin takaici ne a ranta, tana tunanin wai har yaushe zata yi girman da za'a daina hukuntata.... tana cikin wannan tunanin taji ya ce "You rest your hands up..." Hakan kuwa tayi ta ɗaga hannayenta sama gwiwowinta a kife ƙasin carpet, yana gamawa dasu yayi shigewarsa ciki, Bayan mintuna talatin Abbah da Mommy ne suka sauƙo downstairs, Abbah ganin falon wayam yasa shi cewa "ha'a ina mutanen gidan? ina ce ai sun hallaru a dinning...." Mommy tana yatsina fuska ta ce "Uhmmm!..." iya abinda ta iya furtawa Kenam saboda tsananin izzah... duk zama sukayi a dinning saiga Ummy ta fito daga room ɗin Baiwar ALLAH, Abbah ya ce "Uwar masu gida ina kuka shiga ne haka, ina Dota ta farfaɗo ne?...." Ummy fuska a sake tana murmushi ta ce "Abbah ta samu farfaɗowa yanzu haka na barta tana sallah ne...." Daiden lokacin da Yaya Roshan ya sauƙo down yana sanye da farar jallabiya, shima nufan dinning yayi yana faɗin "gud Afternoon my parents...." Abbah shima amsa masa yayi da murmushi akan fuskarsa ya kuma cewa "sai yanzu duk kuka samu damar fitowa Kenam..." Roshan yana sosa ƙeya ya ce "Abbah bacci ne ya ɗauke Ni shiyasa...." Abbah ya ce "sai yanzu da yunwa ta tasheka kenam koh?...." Murmushi yayi sannan yakai idonsa kan Ummy wacce take tsaye, ya ce "yadai Ƴar gidan Soja bakya gajiya da tsayuwa ne?...." Abbah ya ce "ina sauran ne suzo mana..." Ummy ta ce "duk suna ɗakin Uncle Deen suna karɓan tsarabar hukunci..." Hajia Kilishi ta ɗago tana kallon Ummy cikin ɓacin rai ta ce "whattt? daga dawowarsa har ya fara azabtar mun da yara? wani irin abu ne haka, gaskiya bazai yuba ƴaƴana ba jakuna bane suma sunada ƴancin kansu acikin gidan nan tinda suma gidan ubansu ne ba agolanci aka kawo su ba....." Abbah sam baiji daɗin kalamanta ba amma saidai bai nuna hakan ba sai cewa yake "wait mana ki saurareni! ba maganar agolanci bane shin Razhdeen bashida iko idan yaran sunyi laifi ya hukunta su? meyasa kike nuna banbanci a tsakanin yaran nan ne kam? gani nake Razhdeen da Roshan da ƴaƴanki duk ɗaya suke babu ruwanki da shiga shirginsu, haka akeson uwa ta kasance...." Mommy ta ce "au memakon ka ɗau hukunci akai shine zaka goya masa baya? daman na daɗe da fahimtar bason yarana kake ba kamar yanda ka nuna kafi son mahaifiyarsu Razhdeen akaina ...." ta ƙarasa maganar tare da kawar da kanta gefe tana zubarda ƙwallah!!!! Abbah ganin ya fara fusata ne ya ce "Kinga ki tsayar da wannan kishin nakin a haka, ita wancan ta rigada ta bar mana duniyan nan da yake cike da ƙalƙal banza da wofi, sannan kafin na fara tarayya dake da ita na fara, in badan mutuwa ba da tayi mun yankan ƙauna aina zan ganki balle na Auro ki, Ni banida ra'ayin zama da mata biyu, kuma nayi niyar mutuwar matata BINTU cewar bazan ƙara Aure ba haka zan zauna, amma babu yanda na iya haka aka tilastani akan Aurenki bawai bana sonki ba, amma Inaso kiyi adalci shin Ni na ganki nace Inaso? babu wannan! haɗamu akayi ba tare da mun san juna ba har akayi Auren lokacin ma bana Nigeria... Saboda haka ki dena haɗa kanki da Fatima domin ko a halayya ne tayi miki nisa...." Roshan yana zaune ganin abun yana shirin wuce gona da iri yasa shi cewa "Please Abbah ya isa haka, babu daɗi irin haka..." ya kalli Ummy wacce itama tana tsaye tana jinsu duk da bataji daɗin kalaman Abbah ba amma tafi jin haushin Mommynta domin ita ta fara.. Roshan ya kalli Ummy ya ce "My love jeki ƙira yayun nakin mana...." Ummy ta dafa ƙirji tare da faɗin "waaaa! cab wallahi Yaya Roshan daƙer na tsiratar da kaina daga ɗakin Uncle Deen...." Murmushi yayi sannan yace "okay bari naje na dubo su...." kai tsaye upstairs ya haura sannan ya miƙi part ɗin Razhdeen, yana zuwa yasa hannu ya tura ƙofar ɗakin, ganin yanda su twins suke ƙafafu a sama jikinsu sai ɓari yake duk da sanyin A.C dake ɗakin amma gumi suke tsabar azaba gaba ɗaya sunyi lukus, idanuwansu har sunyi jawur tsabar kuka, hannu yasa ya tallafosu yana faɗin "ku tattaso maza..." haka suka tashi suna sakin numfashi, itama Minal tashi tayi tana kuka domin abun da cin rai, 25years take amma dizgata ake agaban ƙannenta... Roshan ya ce "kuyi haƙuri ku daina kukan nan..." Shi baima lura da Ƴar Tiny ba sai yanzu da ya ji maganar ta tana cewa "Yaya Yoshan wayace ka ceceshu, ajiyaishu fa aka bani, Ankui Deen ya ce duk wacce ta taci na gaya maca...." ta ƙarasa maganar tana turo baki.. Roshan ya ce "laifin mai sukayi?...." Ƴar Tiny ta ce "meyaca bacu jo shun gaiceci ba...." Roshan ya ce "TOH ki ce masa yayi haƙuri a wannan lokacin sai sun ƙara tukun...." Saiga Uncle Deen yana sanye da Black jallabiya ba ƙaramin kyau yayi ba sai farinsa ya ƙara fitowa ya fito yana faɗin "babu yanda zasuje su cigaba da karɓar hukuncinsu...." Roshan yaje har gabansa yana faɗin "haba my Man yau fa ka dawo, ka bari sai bayan kwana biyu saika fara bayyanar da dabi'unka mana ..." Uncle Deen yamutsa fuska yayi sannan ya ce "ɗabi'una ai a bayyane suke a ko ina, saboda haka ka bar mun su anam...." Roshan ya ce "Abbah yana can yana jiran mu gaba ɗaya, kayi haƙuri Please...." Saida yayi kamar bazaiyi magana ba can ya ce "Ok...." yana faɗan haka da gudun gaske Pinky da Rukky suka bar ɗakin sai kuma Minal tabi bayansu ita da Roshan a tare suka sauƙa, Duk zama sukayi, Abbah ya ce "ina yake shi ɗin?...." Roshan ya ce "yana sauƙowa...." Abbah baiji daɗin ganin yanda idanuwansu suka canza launin ja ba saboda kuka, amma sai dai yaja bakinsa yayi shuru ko tambayarsu baiyi ba cewar me sukayi ba, Amma yasan Razhdeen baya hukunci haka kawai sai da dalili, a ransa ya ce "yanzu haka basuje sun gaishe shi bane, kuma kamata yayi duk subi ɗakunansu suje su musu sannu da dawowa, a tarbiyance ba wai a gaisa sama-sama ba, kuma daman yaran sunada irin wannan ɗabi'ar na rashin gaisuwa...." suna zaune Saida suka jira Razhdeen ya fito hannunsa riƙe dana ƴar Tiny suka ƙaraso dinning, Abbah dariya yayi yana kallon ƴar Tiny ya ce "wato ke Auta dake ake shiri Kenam, ahhh lallai kin ciri tuta agurin Ankui Deen ɗinki 😅...." turo baki tayi ta ce "babu yuwanka da Ni Abbah, muyi faca...." zaro ido Abbah yayi waje ya ce "yau ɗin dani akayi faɗa? saboda kina tare da da Uncle Deen koh? ai zai tafi zakizo ki sameni daramm...." Kawar da kai gefe tayi tana harare-harare...... Uncle Deen ganin ana zaune ga kuloli ba wanda ya tashi balle ya zuzzuba yana hararar kulolin tare da shan kanwa ya ce "Meye amfanin zaman mu anam?...." Itama ƴar Tiny ta ari bakinsa da cewa "wai Ni ina wan can yalinyal ne tajo ta juba mana abincin mana, Ni wayyayi lunwa nace ji....." Ummy tana harararta ta ce "ke dallah rufe mana baki sa'arki ce ita?...." Ƴar Tiny zaro ido tayi tana nuna Ummy da ɗan ƙaramin yatsarta ta ce "ceee wayyayi tayyayi cema ciciyaye Ni...." wani irin dogon tsuka Uncle Deen yaja yana ƙoƙarin tashi, Roshan yayi saurin riƙo hannunsa tare da faɗin "wait My Man yanzu za'a zuzzuba...." ya kuma cewa "Ni wacece mai zuba abincin ne kam gashi Man ɗina ya gaggauta...." ya ƙarasa maganar yana binsu da kallo. Ummy ce ta ce "Aunty Baiwar ALLAH ce kuma tana fitowa yanzu...." Banda Abbah da Ummy duk cikinsu babu wanda baiji haushin Baiwar ALLAH ba jinkirin fitowar da tayi ga kowa najin yunwa.... Itama kuma Baiwar ALLAH tana ciki tsananin tsoro ne da fargaba ya hanata fitowa, sai tazo zata fito saita koma da gudu, yanzu ne na ƙarshe Saida tayi addu'a kafin ta jefo ƙafarta na dama waje tukun ta fara taku a hankali jiki duk ba ƙwari, kamar marar lafiya haka take ƙanƙame jikinta kanta a sunkuye sam bata ƙaunar ganin Uncle Deen.... da haka ta ƙaraso wajen da sallama a bakinta, Uncle Deen ko ɗagowa baiyi ba kai a sunkuye yana pressing phone ɗinsa, Roshan ne ya ɗago tare da amsa sallamar data yi, yayi ido huɗu da ita, gabansa ne yayi wani irin yanke wa kamar wanda yaga abun tsoro, a hankali ya furta "ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raju'un......" ba tare da kowa yaji shi ba, ya cigaba da cewa "godiya ta tabbata ga sarkin hallitun duniya, ALLAH na gode maka daka halitto wannan kyakykyawar halitta...." Duk waɗannan maganganun acikin ransa yake yinsa, yana cikin wannan sambatun yaji Hajia Kilishi ta darara mata tsawa tare da faɗin "Meye amfanin ki acikin gidan nan? Kenam mu zamu zo muna jiranki saboda isarki da gadara? wannan shine na ƙarshe na gaya miki...." Baiwar Allah kai a sunkuye ta ce "kiyi haƙuri Hajia bazan ƙara ba INSHA ALLAHU...." Abbah ya ce "kinga Dota zo ki zuzzuba abinci kema ki zauna ki ci koh...." A hankali ta furta "tam Abbah nagode...." kafin ta fara zuba abincin Saida taje gefen Razhdeen ta durƙusa ƙasi ta gaishe shi, hannu kawai ya ɗaga mata ba tare da ya furta komai ba, Sannan taje gefen Roshan wanda idonsa akanta ya gagara ɗagewa sai ji yayi ta gaishe shi, Amsawa yayi cikin kulawa ya ce "Barkanki da fitowa Gimbiya...." Duk ƴanmatan gidan zaro ido waje sukayi jin sunan da ya ƙirata dashi, kallo kallo suka shiga yi cike da mamaki.... Shi kuwa ko a jikinsa, Tashi tayi jiki a sanyaye ta buɗe kulolin ta fara zuzzuba wa kowa abinci a plate, ta kaiwa kowa nashi sannan itama ta zauna a gefen Ummy da ƴar Tiny.... A nutse kowa yake cin abincinsa gurin yayi tsittt, Roshan yana ci idonsa akan Baiwar ALLAH, Ummy ce kawai ta lura da haka tanayi tana kallon Yaya Roshan da kuma Baiwar ALLAH wacce itama take satar kallonsa idan ta haɗa ido dashi sai tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi, kuma du saita ƙara ɗagowa ta kalli Uncle Deen tana jinjina girman kai irin nasa, daƙer yake motsa bakinsa idan yakai abinci ciki..... ta kuma kai idonta kan Uncle Deen sai karaf suka haɗa eyes ɗagowarda zai yi, domin shi a tsarge yake idan ana yawan kallonsa jikinsa ne yake bashi, Dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana jan numfashi daƙer ga wanin irin gumin dake gangaro mata, Uncle Deen cigaba da uzurinsa yayi bai saurareta ba, Shi kuma Roshan yana cikin kallon Baiwar ALLAH idonsa ya sauƙa akan na Ummy wacce taketa ƙaresu da kallo, Murmushi ta sau masa tare da ƙibta masa ido ɗaya, Harararta yayi da gefen ido yana motsi da lips ɗinsa ya ce "sa'idawa manya...." Roshan ganin bazai iya yin shuru ba yasa shi cewa "Ni Abbah wacece wannan ban santa ba?...." kafin Abbah ya buɗe baki yayi magana har ƴar Tiny ta rigashi cewa "wannan ai el aicin gidan mu ce...." Cike da mamaki Roshan ya ce "ƴar aiki kuma? wannan ɗin? amma naga batayi kama da ƴar aiki ba....." Hajia Kilishi ce ta watso masa harara tare da faɗin "au daman ƴan aiki ɗin kamanninsu daban ne? TOH ƴar aikin ce ko zaka canza mata matsayi ne?...." Roshan shuru yayi baice komai ba, Uncle Deen yana yamutsa fuska gira a haɗe cool voice ya ce "ƴar aiki meya haɗata da zama acikin mu? hakane tsarin yake daman a rinƙa zaman cin abinci da ƴar aiki? ya kalli Baiwar ALLAH a tsawace ya ce "Keee! tashi kibar nan Right now I don't want to see your face....." Baiwar ALLAH jiki na ɓari a tsorace ta tashi zata bar wajen, Ran Abbah ne yayi mungun ɓaci ya ce "Dota nemi ware ki zauna...." Baiwar ALLAH idonta akan Uncle Deen ta ɗan ɗosana mazaunenta akan kujera ba tareda ta sake jikinta ba, Roshan cizan lips ɗinsa yayi ta ƙasi sam baiji daɗin abinda Uncle Deen yayi mata ba.. Abbah ne ya soma magana cikin ɓacin rai idonsa akan Ummy Ya ce "uwar masu gida meyasa duk abubuwanda suke faruwa acikin gidan nan bakya gaya mun?..." ya cigaba da cewa "lokacinda na tashi barin ƙasar nan menace miki akan yarinyar nan? Kenam bazaki iya cika mun alƙawarin da kika ɗaukar mun ba? Ko dana tashi tafiya nace miki ta zauna a matsayin ƴar aiki ne? dana kawota nace miki gata nan ƴar aiki na kawo muku? Gaya mun mana....? ya ƙarasa maganar a tsawace idonsa akan Ummy, Dasauri Ummy ta girgiza kai kanta a ƙasi sai faman zubar da hawaye take, ganin duk an ɗora mata laifi... ya cigaba da cewa "Nasan daga mahaifiyarki har Yayunki babu mai ƙaunarta shiyasa na damƙata a hannunki ashe baki ita bashida wani amfani, meyasa duk abinda sukayi mata bazaki ƙirani ki sanar mun ba kuma muna waya koda yaushe, TOH daga yau" yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya yana nunnuna musu yatsa ido a waje yanda yake zazzaro su ya ce "idan na sake ganin wani abu ya sake fitowa marar amfani wallahi duk ɗinku sainayi mungun saɓa muku, ba'a matsayin ƴar aiki na kawota ba, yanda kuke a matsayin ƴaƴana TOH haka itama take a wannan matsayin, kada na sake ji na gaya muku...." ya nuna Hajia Kilishi ya ce "musamman ke kece ummu ƙaba'isu mai haifar da duk wasu matsaltsalu toh ki dakata haka tin kafin mu shiga rana domin abun bazai miki daɗi ba......" Mommy idonta akan Abbah tana masa kallon takaici ido duk ya cicciko da ƙwallah ta tashi a fusace tabar dinning, kai tsaye upstairs ɗinta ta haura..... Ƴar Tiny gaba ɗaya ta kumbura jin abinda Abbah yace wai itama ƴarsa ce ta ce "co co co Abbah wacece uwacca acicin gidan nan?...." Abbah ya kalli ƴar Tiny ya ce "zan doke ki a waran nan idan baki rufe mun baki ba, kema harda ke koh? kina biye Uwarki da Yayunki kuna shirme zanyi maganinku ai...." Ƴar Tiny hannu ta ɗora akan fuska tana ƙinƙishin kuka.... Uncle Deen dalilinda yasa baya son cin abinci acikin mutane Kenam hayaniya, ya tsani yawan magana da hayaniya nan danan kansa zai fara ciwo..... Sai tsuka yake shi kaɗai, shima tashi yayi zai bar wajen Abbah yayi saurin dakatar dashi yana faɗin "zo nan ina zakaje kuma...." Uncle Deen kamar bazaiyi magana ya ce "am okay..." Abbah ya ce "ban yadda ba zoka zauna kaji ...." Ba yanda ya iya haka ya koma ya zauna..... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 29 to 30 ꧁꧂ Abbah ne ya kalli Uncle Deen sannan ya ce "ka ƙarasa cin abincinka bana son zama da yunwa..." Uncle Deen baice komai ba sai caccakar plate ɗin da yake da spoon, Waran yayi tsittt kamar ba mutane, sai bayan wasu mintuna da murmushi kwance saman fuskar Roshan idonsa akan Baiwar ALLAH ya ce "Abbah...." Abbah ya amsa masa cikin kulawa daiden lokacin da yakai one spoon inside his mouth... sauƙe numfashi Roshan ya yi tare da faɗin "nayi tsintuwar wata kyakykyawar Ɗawisuwa acikin gidan nan...." Ummy zaro ido tayi waje tana harararsa irin na gatsalin nan domin tasan me yake nufi.. Abbah ya ce "ha'a Ni daman baka san akwai Ɗawisai a gidan bane? ai sunada yawa akwai part ɗinsu na musamman....." Roshan ya ce "Uhmm! Abbah Kenam wannan Ɗawisuwar dana gani ta daban ce...." Abbah ya ce "ai duk ba abun tada hankali bane idan kanaso sai muje ka zaɓi wanda kakeso sai a yanka maka koh....." Murmushi Roshan ya yi sannan ya kuma cewa "wannan bata yankawa bace saidai na sata a gaba naita kallonta...." Abbah yace "au TOH ai duk yanda kake so hakan zakayi ai..." ya kalli Ummy sannan ya ce "Ni uwar masu gida Ɗawisai nan sauran guda nawa ne?...." Ummy tana kumshe dariyarta daƙer ta ce "Abbah sauran basu fi goma ba...." ya ce "duk ina sauran?...." Ta ce "Abbah duk an cinye mana..." "Toh sarakunan cin nama...." A cewar Abbah. Baiwar ALLAH ta lura da kallon da Roshan yake yi mata itama ɗagowa tayi ta sauƙe eyes ɗinta akan ƙayataccen murmushinsa mai ƙayatarwa..... itama bata san lokacin data sau tata murmushin ba, cikin jin kunya ta tashi a hankali zata bar wajen, Abbah ya ce "yadai Dota....?" ta ce "amm Abbah na ƙoshi ne.." ya ce "ok tam shikenam..." tana barin wajen itama Ummy ta tashi, da haka har sauran ƴan matan suma suka tattashi aka bar iya Abbah da Uncle Deen da kuma Roshan... Baiwar ALLAH tana shiga room ɗinta taje gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta fuska ɗauke da murmushi, tana cikin wannan halin sai ji tayi ance "Uhmmm daman Nasan za'ayi hakan..." Dasauri Baiwar ALLAH ta waiwayo bayanta tana bin Ummy da kallo daga bisani tasau ajiyar zuciya tareda faɗin "wallahi har kin tsoratar dani...." Da murmushi a fuskar Ummy ta ce "daman nasan buddin kuka ga juna sai kun kwarewa junanku...." Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta ta ce "kamar ya ban ganeba..." Ta ce "Yaya Roshan mana yanzu baki fahimci komai game dashi bane?..." Baiwar ALLAH fari tayi da eyes ɗinta sannan ta ce "kamar ya kenam..." Ummy matsowa itama tayi jikin mirror ta ce "tinda bakya zuwa Ghana bari nayi miki filla filla kamar ƴar nursery, Yaya Roshan alamunsa ya kware miki ne...." Zaro ido Baiwar ALLAH tayi cikin rashin fahimta ta ce "kwarewa kuma? Bangane ya kware mun ba, aina kuma yaushe? Kinga rufa mun asiri yaushe ma na ganshi balle ya kware mun?...." Ummy ta sauƙe numfashi tana bin Baiwar ALLAH da kallo daga bisani ta girgiza kai ta ce "okay tinda baki gane mai nake nufi ba bari na barki haka, zaki gane abinda nake nufi zuwa gaba, amma dan ALLAH kar in yazo gareki ki wulakanta mana shi domin shi ɗin yanada rarraunar zuciya....." tana kaiwa nan tayi ficewarta, Baiwar ALLAH bin bayanta tayi da kallo cikin rashin fahimtar abinda take nufi..... Abbah da twins Rosh da Razh har zuwa yanzu suna dinning alamun wani ɗan tattaunawa suke yi..... *BAYAN SATI ƊAYA DA DAWOWAR RAZH DA ROSH....* Roshan a ɗan waɗannan kwanakin yana bibiyan Baiwar ALLAH amma sai dai ya kasa tin karar ta, amma duk waranda take shima yana nan, hatta kitchen idan ta shiga ya rinƙa zirga-zirga zuwa kitchen yaje ya ɗauko cup ya fito kuma du ya sake komawa ya ɗauko spoon, still ya sake shiga zuwa ɗaukan wuƙa wai zai yanka Apple, haka zai rinƙa wannan zaryar har Baiwar ALLAH ta kammala da kitchen ɗin ta fito, abun har ya fara bata mamaki, itama Ummy tasa ido akansa sosai ganin Ɗan uwanta yana cutuwa sosai yasata zuwa har part ɗinsa, tana shiga ta same shi yana zaune a bakin gado kai a sunkuye ya rufe fuskar da hannayensa alamun yana cikin damuwa, Itama Ummy zama tayi dab dashi tana fuskantarsa cikin sassanyar murya ta ce "my love..." Ɗagowa yayi yana kallonta da shanyayyun eyes ɗinsa da bacci ya ƙaurace musu, Ta kuma cewa "kana cikin damuwa nasani amma meyasa bazaka nemi na temaka maka ba?...." Murmushi yayi idonsa akanta ya ce "bazaki iya temaka mun ba my love, Damuwata tafi ƙarfin tunaninki...." Murmushi tayi sannan ta ce "Damuwarka bazata wuce akan Baiwar ALLAH ba, meyasa kake tunanin bazan iya ba? tinda kai ka gaza Ni zan sameta na sanar mata halinda kake ciki akanta...." Roshan yayi saurin katseta da cewa "No no no please karki fara, ki barni zanyi mata magana da kaina...." Ummy ta ce "Uhmmm! yarinyar da kullum saita shugo ɗakinka ta gyara maka room ta wanke toilet ɗinka ta chanza maka bedsheet sannan ta feffeshe maka ɗaki da turare, idan tayi girki ita zata kawo maka har ɗaki ta ajiye maka akan dinning idan kana kusa ita zata zuba maka a plate duk idanuwanka akanta amma ka kasa sanar mata kana sonta, TOH idan baka sanar mata yanzu ba sai yaushe? Please My love ka cire tsoro da fargaba ka tinkareta kar kabar damarka ta kuɓuce, toh bari kaji akwai ranar da muka fita da ita wallahi saida tayi samari kusan goma kuma duk manya-manyan mutane babu talaka, shiyasa take fargaban fita outside, Idan ka tsaya kallon ruwa kwaɗo zai yi maka ƙafa ne, domin yanzu haka burin Abbah ya sama mata nagartacce miji ya Aura mata ne, yakamata ka fito kayi yaƙin ƙwatar soyayyarka kar ka tashi a tutar babu....." Roshan gaba ɗaya ya susuce idonsa akan Ummy ko ƙibtawa baya yi tsabar razana da yayi jin tanada manema, jinjina kai yayi sannan ya ce "hakan bazai taɓa yuwa ba, dole a yau zanyi mata magana...." suna cikin wannan halin sai suka ji sallama daga falo, Roshan murya na kakkarwa ya ce "come in...." Ummy tana ƙumshe dariya ta ce "Haba My love wallahi zaka bayar da maza kamar irinsu Uncle Deen...." kallonta yayi yana tura ƴar lips ɗinsa ya ce "Deen mutum ne daman...." Buɗe baki tayi tareda rufe bakin da hannu bibbiyu ta ce "wallahi babu ruwana..." ya juyo yana kallonta ya ce "duka na zai yi ne? ke ƙyale Ni fah yanzu tsoron soyayya nake yi tin lokacin da mutuwa ta riski Abar ƙaunaata...." kafin ya ƙarasa maganar saiga Baiwar ALLAH ta shugo da sallama a bakinta, duk suka amsa mata cikin fara'a Baiwar ALLAH ta ce "amm na kammala shirya kayan abincin a dinning...." idonsa cikin nata ya ce "okay sannunki da ƙoƙari gani nan fitowa amma kar ki tafi ki jirani...." sunkuyar da kanta tayi tana kallon ƙasi, tana murza yatsunta kamar zatayi kuka ba tare da ta furta komai ba... ya fahimci kamar tana cikin matsala ya ce "Are you okay?..." Girgiza kai tayi da sauri bata san lokacin da tayi ba tsabar tsoro.. Ya ce "toh meya faru ne?..." tayi shuru ta gagara cewa komai Sai Ummy ce ta tsoma musu baki tare da faɗin "Yaya Roshan kasan fa tana zuwa part ɗin Uncle Deen batason tayi dismiss ne akwai matsala kasan halin mutuminka...." Jinjina kai yayi sannan yace "okay idan kin gama dashi inason ganinki...." Dasauri ta furta "TOH...." ta juya.... tana fita ta sauƙa falo ta nufi kitchen nan ma taje ta jido kuloli a dinerset ta sake haurawa saman stairs kai tsaye part ɗin Uncle Deen ta nufa, ta ɗora tray akanta ta fara knocking a hankali kar taje bacci yake yi ta tashe shi ta tsokalo tsuriyar Dodo, ganin shuru ba'ayi magana ba yasa ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakinta, ganin falon wayam yasa ta nufi dinning ɗinsa taje ta jejjera masa kayan abincinsa, sannan ta nufi frig ta ɗauko kayan fruits da lemuka tazo ta yanyanka masa kayan fruits acikin glass plate mai ɗan faɗi, ta kammala shirya masa komai da komai abubuwan da zai buƙata kamar yanda tayiwa Roshan amma saidai kayan haɗin Uncle Deen yafi na Roshan domin Uncle Deen yanada tsauri sosai, Sai yace baya cin wannan, ya ce yana buƙatar wancan ya ce baya son wannan haka yake kullum shiyasa saita fara gamawa da Roshan kafin tazo kan na Razhdeen saboda a ɗakinsa tafi ɓata lokaci.... tana kammalawa ta nufi hanyar bedroom ɗinsa tana zuwa nan ma ta sake yin knocking, har saida tayi kusan sau biyar kafin ya amsa mata ya bata umarnin shugowa, Doka ne indai ta kawo abinci toh saita musu magana kafin ta fita saboda wani sa'in sukan wuni acikin bedroom basu leƙo falo ba balle su san an kawo abinci, ta turo ƙofar a hankali da sallama a bakinta, ganinsa yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske, dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana maida numfashi, shi kuwa yana tsaye a gaban mirror daga shi sai pant na maza ajikinsa babu riga sai tarin gargasa, alamun wanka zai shiga, ta cikin madubi ya kalleta sannan ya ce "tsayuwar me kike, ki shiga ki haɗa mun ruwan wanka...." ɗaga masa kai kawai tayi domin kusan kullum ita take haɗa masa, kamar yanda yace haka ta nufi toilet taje ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi-ɗumi saida tasa turaruka kusan kala goma acikin ruwan, tana shirin fitowa sai gashi ya kutso kai ciki, dasauri taja da baya tana jero addu'o'i acikin ranta, tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta ganin zugegen mutum a gabanta, du Da du tsayinta a iya saitin ƙirjinsa ta tsaya nan ma bata ƙarasa zuwa ƙirjin ba, wani irin haɗiyar yawu tayi har saida maƙogaronta ya riƙe, dasauri takai hannunta saitin wuyanta tana shafawa jin yanda yake mata ciwo, ratsa ta gefenta yayi ya nemi guri ya zauna, murya ciki-ciki ya ce "ki zauna ki gyara mun faratu na...." jiki na ɓari ta ce "toh...." haka ta jawo farin baho zuwa gabansa mai ɗauke da ruwa aciki, sannan ta ɗauki abun yankan farce ta durƙusa a gabansa, a hankali ya ɗago da ƙafarsa ya zura cikin ɗan ƙaramin bahon mai ruwan ɗumi, na wankan kuma na gefe guda, jikinta ne yake ɓari sosai haka hannunta ma da haka takai hannunta cikin ruwan bahon ta kamo ƙafar tana wankewa a ciki kafin a fara gyaran farcen, Akwai sabulun wanke ƙafa ata gefenta mai ruwa kamar shawer gel inta tatsi sabulun a hannunta saita zoza a ƙafar, ji take kamar bayan kifi take wanke wa tsabar laushin ƙafar, haka ƙafar yake zamewa ya fancala cikin ruwan, haka take kokuwar riƙe ƙafar da zarar ta ɗago da ƙafar saiya zame daga hannunta dake hannunta ma akwai laushi sosai shiyasa ta gagara riƙe ƙafarsa saida akayi haka kusan sau uku, Idonsa akan screen ɗin wayarsa da yaketa faman pressing ya ce "idan kika sake jefar mun da ƙafa saina canke ki...." Kamar zata yi kuka ta ce "ƙafar taƙi kamuwa, sulalewa take .." baice mata komai ba haka ya cigaba da uzurinsa... Daƙer ta samu ta cabke ƙafar ta ɗora akan cinyarta yanda bazai zame ba, ta ɗauki abun yankan farce ta fara gyara faratun a hankali gudun karta yanke shi domin abu mai sauƙi ne saboda tsananin laushin ƙafar saika bi a hankali... cikin nasara ta kammala gyara ƙafar dama, ta kamo na hagun nan ma daƙer ta samu ta wanke kafin ta ɗora ƙafar akan cinya ta fara yanke masa, tana cikin yanke na babbar yatsa bata ankara ba taga abun yankan ya yanke masa babbar yatsa, nan danan sai jini jajawur, a razane ta zaro manya-manyan idanuwanta waje kamar zasu faɗo, dasauri ta ɗaga kai tana kallonsa cike da mamaki taga ko motsi baiyi ba yanata pressing phone ɗinsa shi baima san an yanke shi bama, Baiwar ALLAH da sauri tasa rigarta tana goge jinin dake tsirtowa, nan danan gaban kayanta ya ɓaɓɓaci da jini ganin jinin yaƙi tsayuwa yasa ta fara daddanne masa yatsu tana matse jinin da rigar jikinta hawaye kuma haka yake gangaro mata, Shi kuwa jin yanda take ta danne masa ƙafa yasa shi kallon yanda take a hankali yake motsa lips ɗinsa ya ce "what is going wrong?..." Ga yanda taketa ɗigo masa ruwan hawaye akan ƙafar, motsa ƙafar yake a hankali yaga rigarta duk ya ɓaci da jini sai a lokacin ya ankara da gurin data yanke shi shati guda still jinin bai daina zuba ba, a hankali ya zura ƙafar cikin ruwan ɗumin tare da jan dogon tsuka eyes ɗinsa akanta ya ce "tashi ki ban guri ...." A gaggauce ta tashi gudu-gudu ta buɗe ƙofar toilet ta fice, kamar zata dungura ta nufi falo nan ma ta buɗe tayi ficewarta, cikin sa'a bata samu kowa a falo ba bayan da sauƙa down stairs haka tayi saurin wucewa room ɗinta, tana shiga ta fara sauƙe nannauyar numfashi, kafin itama ta nufi toilet, gaba ɗaya kayan jikinta ne ya ɓaci tana mamakin yanda Uncle Deen yake da jini haka a jikinsa..... 🇾 🇦 🇷  ➪ 🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 🧘🏻‍♀️🎻🎻🎺 a yawace yawacenta har ta fito cikin gari tana gararamba da ƴar jitar ta a lanƙaye a wuya, gurin mafaka ta samu wanda koda yaushe tana wajen kuma bata rasa na abincin da zataci ta hanyar kaɗa jitarta, Wani layin titi ne wanda mabarata suke zama a wajen, da zaran wani mai mota ko mai arziƙi yazo wuce wa su tattashi suna roƙonsu na Annabi, duk waɗanda suke wajen nakasassu ne daga makafi sai kurmaye sai kuma bebaye sai kutare babu mai cikakken lafiya a gurin, Sunan titin shine layin nakasassu road, a waran Ƴar Amana take tazo gurin ta sanadiyar wani mutumi temaka mata yayi ya kawota gurin domin ta samu abinda zata ci yau da kullum, idan sadaka za'a bayar nan za'aje idan ma wani tallafine nan layin za'aje, Yar Amana tana zaune da zaran taga wani mota yazo zata tashi da gudu taje kusada motar tana kaɗa jitar ta, tsaɓar tsananin daɗin sautin babu mai motar da zai zo ya wuce bai bata kuɗi ba, wani sa'in kuma ta sanadiyar ta ake bawa duk nakasassun gurin sadaka saboda daɗin sautin jitarta, da haka take rayuwarta inta tara kuɗi ta siyo abincinta taci da ƙoshi, idan taga wata bata samu kuɗinda zata sai abinci taci ta ƙoshi ba saita raba kuɗinta biyu ta bayar da sauran, Ƴar Amana bata taɓa samun kuɗi bata raba da wata ba acikin nakasassun, dake duk yawanci tsofaffi ne marasa ƙarfi....... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 31 to 32 ꧁꧂ Around 5 0'clock na yamma acikin ranar Juma'a! Uncle Deen ne ya sauƙo falo a yayinda ya tarar da Roshan zaune akan kujerar falo yana fuskantar dinning table, a yayinda ita kuma Baiwar ALLAH tanata faman goge dining da farin ƙyalle, Ji yayi an dafa kafaɗarsa ta baya dasauri ya waiwayo a zabure ganin Razhdeen yasa ya sauƙe nannauyar ajiyar zuciya tareda dafa ƙirjinsa ya ce "kaiii my Man har ka tsoratar dani...." Uncle Deen yana riƙe da wayar sa ya ce "what are you looking for?...." murmushi Roshan ya yi sannan ya ce "Ɗawisuwa...." ya ƙarasa maganar dai-dai lokacinda yakai eyes ɗinsa waran da Baiwar ALLAH take... Uncle Deen cikin rashin fahimtar abinda yake nufi yasa shi kallon plasman yaga ana showing namomin halittu kamar su kaji da talotalo har da su Ɗawisai, a tunaninsa kallo yake ya jinjina kai tare da faɗin "okay amma eyes ɗinka ba'a kan plasman suke ba...." jin Roshan yayi masa shuru kuma sai sakin murmushi yake ya tsayar da idonsa guri ɗaya, Razhdeen ne ya kalli waran da yake kalla, ganin Baiwar ALLAH tanata goge goge yasa shi ƙara kallon Roshan, ya lura kamar yarinyar yake kallo, girgiza kai Uncle Deen ya yi yana motsa lips ɗinsa a hankali ya ce "you are crazy...." ya yi juyawarsa zai fita domin akwai waranda yake son zuwa, buɗe get ɗin compound yayi ya tarar an kawo masa motar da zai shiga, ta ciki akwai wani soja wanda ya kasance shine mai driving ɗinsa, Uncle Deen fuska a ɗaure ya ce "yau Ni kaɗai nake son fita...." Sojan ne ya fito yana faɗin "okay Sir..." Bayan ya fito ya shiga yana murɗa key ɗin motar, a hankali ya fara jan motar har saida yaje bakin gate na biyun ƙarshe da haka ko wani gate akwai sojoji haka akaita buɗe masa ana sara masa tare da bashi gaisuwa har ya fice daga gidan gaba ɗaya, yana fita ya ɗau hanya a ɗari nan danan ya ɓace a layin unguwar ko bayan motar ba'a gani, akwai waran da Uncle Deen zai tafi hakan yasa ya buƙaci tafiyar shi kaɗai kuma babu wanda yasan inda zai je, tafiya yake mai nisan gaske har saida ya fara barin gari, a bakin titi ya tsayar da motarsa yana kallon cikin dajin da farkon zuwansa anan yake jin sautin da ya saba ji acikin mafarkinsa, ꧁𓇽꧂ Baiwar ALLAH tana kitchen tana yankan naman kaji manya-manyan irin kajin turawan nan, ji tayi anyi sallama cikin sassanyar murya batare da ta waiwayo ba ta amsa sallamar domin tasan Roshan ne, a wannan lokacin yazo ne da niyar yi mata magana saida yaje dab da ita ya tsaya idonsa akan kayan chickens, ya ce "bakya gajiya da aiki ne?..." girgiza kai tayi idonta akan abun yankanta ta ce "daman ana gajiya da aiki ne?..." kallonta ya yi fuska ɗauke da murmushi ya ce "of course indai mutum ba robot bane ba ..." ɗan murmushi ta saki sannan ta ce "toh waya sani ko robot ɗin ce...." ya ce "ahh indai robot ce ke zaki yi aikin da yafi haka ...." murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba, ya kuma cewa "kina buƙatar tayi ne?..." girgiza kai tayi ta ce "a'ah Nagode..." ya ce "gaskiya Ni kuma Inaso na tayaki ya za'ayi Kenam?..." ta juyo tana kallonsa da dara-daran idanuwanta ta ce "Babban mutum baya aiki...." ya ce "Uhmmm! haka kika ce amma Ni duk a ayyukan gida babu Abunda ban iyaba hatta girke - girke kala kala saidai na koya miki...." Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Okay yau kai zakayi mana ferfesun kajin nan, Ni kuma bari na ɗora rice...." bata ankara ba taji yana tapa hannayensa cikin nuna farin ciki yake faɗin "wow am so glad, dakyau haka nake so, daga yau Ni zan rinƙa taya ki aikin girke-girke....." Kallonsa tayi da murmushi kan fuskarta ta ce "Dakyau...." ta miƙo masa abun hura Gas ta ce "amshi ka hura wuta ga pot ɗin da zakayi using dashi sannan ga can kayan spices komai da komai....." karɓan abun ya yi yana jujjuya shi yasan abun amma kuma bai san ta yanda ake using dashi ba, gudun kar ya dizgar da kansa yasa yakai abun dab da Gas ɗin yana manna abun ajiki ko wuta zai kawo, jin ta tintsire da dariya yasa shi juyowa yana kallonta, shima murmushi yake saki ganin yanda Dariyar yake yi mata kyau, tinda ya dawo bai taɓa ganinta tayi dariya ba sai yau, a hankali ya furta " *WOW* beautiful girl..." ba tareda ta ji ba ...... Saida tayi dariyarta mai isarwa sannan ta karɓi abun hannunsa tana faɗin "kawo nan ka gani, a wannan ɓangaren ka samu 0 mark sauran na gaba...." ta murza yanda abun yake kamar torch light sai ga wuta yana burtsowa tasa hannu ta kunna Gas ɗin sannan ta kunna, ta kalle shi taga idonsa a kanta ko ƙibtawa bayayi ta katse shi da cewa "ehen ɗora pot ɗin...." yayi firgit kamar mai yin tunani yayi saurin ɗora pot a ruɗe yake faɗin "ina oil..." Murmushi tayi sannan ta ce "saika fara tafasa tumatur saboda tsamin jikinta...." ya ɗauki tumatur kamar yanda ta ce hakan yayi ya juye a cikin pot ɗin, yana kallon cikin tukunyar ya ce "ai ya tafasa a sauƙe?..." dariya tayi tana dafe da goshinta ta ɗago tana cewa "sai ruwan jikin tumatur ya tsotse tukun ka sauƙe saika soya oil ɗinka.... Ɗan turo lips ɗinsa yayi sannan ya ce "ai baki gaya mun haka ba .." zaro ido tayi tareda faɗin. "kai daka ce ka iyaaa?...." ɗan buɗe eyes ɗinsa ya yi yace "hakane fa na iya ashe ...." A wannan lokacin haka suka wuni a kitchen suna hira tare da yin Ayyukan su cikin farin cikin kasancewa da juna, Baiwar ALLAH ba ƙaramin nishaɗartuwa tayi ba kasancewarta da Roshan domin mutumin ya iya mu'amala da mutane kuma yanada saurin shiga rai da shaƙuwa, a wannan ɗan haɗuwarsu har sun shaƙu sosai kamar wanda sukayi shekara suna tare, suna cikin hirar su Roshan ya ce "Ni in tambayeki mana idan ba damuwa...." Baiwar ALLAH tana satar kallonsa ta ce "ina jinka...." ya ce "Meye asalin sunanki?...." Saida taji gabanta ya yanke lokaci guda ta sauya daga yanayin farin cikin da take, kai a sunkuye cikin sassanyar murya ta ce "Nima bansan sunana ba ...." Roshan yana cikin juya miyan kajin da yake yi yaji ta bashi wannan amsar kamar bata cikin farin ciki, jiki ba ƙwari ya cire ludarin miyan ya ajiye a gefe sannan ya ƙarasa yanda take tsaye tana zuba shinkafar data dafa a cikin kuloli, yana fuskantar ta yasa hannu ya tallafo haɓarta sannan ya juyo da ita saitinsa suna fuskantar juna kamar zaiyi kuka ya ce "sorry na ɓata miki rai koh? banso hakan ta faru ba, inda nasan tambayar sunanki zai jawo ɓacin rai da banyi gangancin yin haka ba, kiyi haƙuri *AMMATA NAH* ....." tasau murmushi haɗi da bugar ƙirjinsa ta ce "it's okay, ko a labarinka ban taɓa jin ka ɓatawa wani rai ba, saboda haka nima abu ne mai wuya naji ɓacin rai akan ka *YAYANAH*....." Da haka suka cigaba da hirarsu har suka kammala girkinsu tsab, ferfesun miyan kaji dai Roshan ne ya yi girkinsa ita kuma tayi sauran girke-girke domin ba girki ɗaya ake yi ba.... A wannan ranar tare suka jera kayan abinci akan dinning suka shirya komai tsab tsab... Ummy ce ta sauƙo daga upstairs tana murtsuka ido alamun daga bacci ta tashi bugu da ƙari kuma taga Yaya Roshan shi da Baiwar ALLAH suna shirya kayan abinci tare suna ƴar hirarsu mai armashi, Cike da mamaki ta ƙaraso wajen tare da faɗin "my love wai kaine yau da Aunty Baiwar ALLAH?...." yana ɗauke da murmushi ya ce "very surprised koh?....." Dasauri ta jinjina kai ta ce "yeah...." Itama Baiwar ALLAH murmushi tayi tare da faɗin "Meye abun mamaki toh?...." Ummy ta ce "Uhmmm! bazaki gane bane but there's something going on, yau Ranar farin cikinsa ne kasancewarsa dake, damar da yake nema tintini Kenam sai yau ya samu....." ta ƙarasa maganar tana kanne masa ido ɗaya ayayin da shi kuma ya sake baki yana binta da kallo, yanda ta dizgashi a gabanta, girgiza kai yayi sannan yace "toh Sarkin surutu anji...." Dariya tayi tare da kai idonta kan Baiwar ALLAH wacce tayi shuru tana sauraronsu Ummy ta ce "wayyo yau bacci nayi shiyasa banzo na tayaki aiki ba, sai yanzu na tashi ayi mun afuwa..." Roshan ya ce "da bakizo kin tayata ba ai Ni na tayata ga ferfesun chicken dana haɗa sai ƙamshi yake...." Ummy ɗan turo lips ɗinta tayi ta ce "yoo Yaya Roshan ai wani ne zai yabi girkinka ba kai da kanka ba, waima da gaske kai kayi mana ferfesu? cabbb zamu ci ciki...." Ɗan harararta yayi ya ce "bangane zaku ci ciki ba ..." Ummy ta kalli Baiwar ALLAH sannan ta kuma cewa "haba Aunty Baiwar ALLAH ya za'ayi ki bashi yin girki alhalin ba iyawa yayi ba, matan gidan ma yaushe suka iya girki balle shi yana namiji, ai gwara ki bashi markaɗen tumatur dasu tattasai da kuma wanke-wanke....." ta ƙarasa tana kanne masa ido cike da zolaya, shi kuwa yana tsaye ya goya hannayensa akan ƙirji ya zuba mata ido, gaba ɗaya ya rasa abun cewa! Ummy ganin haka yasa ta cewa "Wayyo na fara ganin fusata acikin ƙwayar eyes ɗinsa bari na fece..." ta ƙarasa maganar dai-dai lokacinda ta juya zata bar wajen, Baiwar ALLAH tayi saurin cemata "Kinga kafin ki fece ɗan shiga ki ƙirawo su kice an kammala girkin...." Ummy ta ce "okay don't worry 👌...." Roshan neman guri yayi ya zauna sannan ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Ammata yau a kusa dani zaki zauna saboda haka ga kujera zauna...." ya nuna mata kujerar gefensa, ba musu ta zauna tana jiran fitowar ƴan gidan kafin ta fara zuzzubawa, ai kuwa ba jumawa sai gasu sun fara fitowa ɗaya bayan ɗaya domin ba ƙaramin yunwa suke ji ba, Pinky da Rukky ne suka fara zuwa duk suka zazzauna tare da cewa "gud Afternoon Yaya Roshan...." ya amsa musu cikin kulawa, saiga Minal itama ta fito tana ɗaure da fuska daman ita koda yaushe a haka take kamar wanda ake aiko mata saƙon mutuwa, idan kanason ganin fararen haƙwaran Minal toh ka zauna kusa da ita a yayinda take waya da Marshall Mohandas, zama tayi tana motsi da lips ɗinta ciki ciki ta ce "well done Yaya Roshan...." Itama amsa mata yayi yana tsokananta da cewar "Amaryar Marshall ba son raini...." saiga Ummy itama ta sauƙo daga part ɗin su Abbah ta sanar musu cewar an kammala girki.... zuwa tayi ta zauna a gefen Roshan suka saka shi a tsakiya ita da Baiwar ALLAH, Pinky abun ya ɗaure mata kai cike da mamaki ta ce "Yaya Roshan naga kai kam kai maka abincinka ake can room ɗinka, meyasa yau ɗin kuma?...." murmushi yayi tare da gyara farin glass ɗin idonsa ya ce "yau ɗin tare zanyi lunch da Ammata nah...." zaro ido Pinky tayi ta ce "wacece kuma Ammatan ka?..." Rukky ce ta tsoma baki da cewar "mu mana, su waye Ammatan inba mu ba, tare zamu ci...." Girgiza kai yayi yana murmushi domin shi yasan abinda yake nufi..... Su Abbah ne suma suka sauƙo, duk zama sukayi dai-dai lokacin da Baiwar ALLAH ta miƙe tana ƙoƙarin zuzzubawa kowa, a wannan zaman Ƴar Tiny bata nan tana school, tinda safe idan ta tafi sai yamma take dawowa misalin ƙarfe 6 saboda harda islamiyya take haɗawa..... ꧁꧂ Uncle Deen wuni yayi a wannan dajin yana neman abun harinsa wato wacce take damunsa da sautin sarewa, acikin bacci har a ko ina, abun ya bashi mamaki jin har zuwa yanzu bai ji sautin na tashi ba kuma a waran kwanaki yaji... Haka ya gama kewaye dajin har ya gaji ya shiga motarsa zai koma gida, Hanyar daya bi yazo bata nan ya koma ba domin a 'ka'idarsa baya maimaita hanyar da ya bi, zagaye yayi yabi ta wani layi wanda tsakaninsa da gida akwai rata sosai, yana shiga wani road ya tarar da wasu mabarata suna zazzaune ganin mota yasa duk suka tashi da hanzarinsu suka kewaye motar suna bara da'a temake su dana Annabi, shi tinda yake bai ta6a biyowa ta wannan layin ba amma ya fuskanta duk masu neman temako ne, tsayar da motarsa yayi ya bud'e wani d'an boxe wanda yake cike da kud'ad'e ya ciro bob guda a 'kalla kud'in zasu yi million guda, ya bud'e murfin motar ya fito duk sun cika shi da hayaniya sai dai babu yanda ya iya dasu, a hikimance yake musu magana cewar "ko wacce ta koma waran zamanta zan zo yanda take ...." ba'a son ransa yake d'aga murya ba sai dai yazo wajen da dolensa ya bud'e murya yayi magana domin duk waran tsofaffine babu wacce batayi jika da shi ba, haka ya rin'ka lalla6asu har suka zazzauna ya fara bawa kowacce dubu hamsin hamsin domin sunada yawa sosai, saida ya bawa kowa yaje zai shiga motarsa yaji wata tsohuwa tana masa magana daga zaune domin gurguwa ce bazata iya tashi ba, juyawa yayi yaje har gurinda take zaune sannan ya dur'kusa yana kallonta, ta ce "daman akwai wata yarinya ce 'karama taje siyo mana abinci to itama kurmiya ce shine nace ko zan iya kar6a mata sadakar da kake bayarwa...." jinjina kai yayi sannan ya mi'ka mata sauran kud'in daya rage masa a hannu dubu d'ari cib, tsohuwar kar6a tayi tana masa godiya tareda shafar fuskarsa tana sanya masa albarka, da haka ya tashi ya shige motarsa nan danan ya yabar wajen a d'ari.... yana tafiya saiga Yar Amana ta dawo hannunta ri'ke da kwanuka guda biyu tata dana tsohuwar kusada ita wacce ta kar6a mata temakon.... Tsohuwar haka ta mi'ka mata kud'in nan ko d'aya bata zara ba a yanda suke, Yar Amana tana zaune ta kar6a cike da mamaki ita tinda take bata ta6a ri'ke kud'i mai yawan gaske kamar na yau ba, dasauri ta d'ago kai tana kallon tsohuwar alamun tana bu'katar bayani.. Tsohuwar ta ce "yau kam da sa'a muka fito, yanzun nan wani mutumi yazo ya raba mana kud'ad'e, shi ba mace ba sannan shi ba namiji ba domin yanada sumar gashi kamar mace amma yanayin jikinsa irin 'karfaffun mazan nan ne, to waya sani ko mata maza ne sai Allah...." Yar Amana kallon tsohuwar take domin tsab tana jin duk abunda take fad'i mayarwa ne bazata iya ba, takai idonta kan kud'in ita kanta bata san mezatayi da kud'in nan ba..... ꧁꧂ Duk suna zazzaune a dinning, kowannen da shinkafarsa da miyan chicken akan shinkafar da shi kansa chicken ɗin amma sai dai abinci ya gagara ciyuwa tsabar tsananin yawan gishirin dake cikin miyan ferfesun, kowa yayi gumm babu wanda ya ce ƙala, Hajia Kilishi kam dafa goshinta tayi ta sunkuyar da kanta ƙasi tsabar takaici ga gishirin yayi mata yawa a baki ko haɗiyar yawu ta kasa yi, Shima Abbah yana zaune tinda yayi loma ɗaya bai ƙara motsawa ba, ga abincin a cikin bakin ya kasa tofarwa sannan ya kasa motsi da bakin, Rukky kam fashewa tayi da kuka tana faɗin "Wayyo Allah nah yunwa nake ji amma abincin bazai ciyu ba..." Pinky daman yanda tasa abincin a baki haka ta tofar dashi a cikin abincinta sai faman kora ruwa take.... Minal kuma tashi tayi dasauri ta shige kitchen domin shine a kusa taje tana kwarara amai acikin sink na wanke-wanke, Ummy itama tana kaiwa loma ɗaya bata ƙarasa taunar abincin ba ta zubar acikin hannunta tana yatsina fuska tare da faɗin "Haba! haba!! haba!!! Daman ai nasan za'a rina....." Baiwar ALLAH itama tana zaune yanda ta kai lomar abincin bata ƙara motsa bakin ba, ita bata haɗiye ba sannan bata tofoshi waje ba abincin nanan acikin bakin kamar yanda Abbah yayi shima, Roshan shikam sam bai nuna wani reachen ba duk da shima daƙer ya haɗiye abincin daya kai bakinsa, daga nan saiya ɗebe miyar da naman kajin ya zuba a wani plate daban ya fara watsa iya zallar shinkafar a bakinsa yana faɗin "to ya za'ayi ai dai baza'a zauna da yunwa ba, ko wacce ta barbaɗa oil da maggi ta ci, Ni banga laifin abincin nan ba kawai dai ɗan tazarcen salt akayi....." Minal ce ta fito gadan-gadan da masifarta tazo tana nuna Baiwar ALLAH da yatsa tare da faɗin "ke wawiya ce, so kike ki kashe mu? Bayan ga wunin yunwa baki kammala mana girki da wuri ba hakan ma kizo ki zabga mana salt acikin girkin so kike mu hallaka koh? toh wallahi ahir ɗinki dan ubanki kuma ki tashi kije ki sake mana wani girkin...." bata ƙarasa maganar ba taji Abbah yana ɗaga mata hannu tare da cewa "Uh'ummm! Uh'ummm!! Uh'ummm!!!....." baki a ƙunshume yana ɗaga hannu, tashi yayi ya nufi upstairs yanda part ɗinsa yake, yana shiga ya nufi toilet yaje ya zubar da abincin bakinsa sannan ya ɗauki makilin da brush ya wanke bakin tukun ya sauƙo falon ... yazo yana faɗin "ya akayi abincin yau yayi gishiri?...." Ummy tana daga zauna ta ce "Abbah yau fah girkin manyan Maza muka ci, Yaya Roshan ne yayi mana ferfesu mai ban burgewa da ɗanɗano....." Abbah ya ce "Roshan kuma? meya iya da za'a bashi girki...." Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ya akayi Roshan yayi girki kuma Dota?...." Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "Abbah shine yace ya iya girki na bashi yayi...." Abbah ya ce "shi Roshan ɗin ne ya iya girkin?...." Roshan ɗagowa yayi yana kallon Abbah sannan ya ce "na iya mana Abbah, haba ya ake ɗauka na kamar ƙaramin yaro ne...." Abbah jinjina kai yayi ya ce "ahhhh ba shakka ka iya girki sosai..." Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ina sauran girkin da akayi ina fatan dai duk bashi yayi su ba?...." Baiwar ALLAH kamar zata yi kuka ta ce "wallahi Abbah duk shi ya zuzzuba gishiri acikin girke-girken da akayi, kamar yanda wannan yake haka waɗancan ma suke....." Abbah girgiza kai yayi sannan ya ce "lahaula kuce yau anyi wasten abinci acikin gidan nan, na tabbata ko karnukan gidan nan bazasu iya cin wannan girkin ba sai dai akai can Bola...." Abbah ya kalli sauran yaran ya ce "kunga ku tattaso duk muje restaurant...." Minal ta ce "ta sake girka mana wani...." Roshan yayi saurin katseta da cewa "saidai Ni zan sake girka muku domin ta gaji, muddin ita zata sake yin girki to kuwa saidai Ni zan yi ...." Abbah ya ce "batun sake girki duk bai taso ba domin ita ba boyi-boyi bace, Kuma daga yau ban yadda Yarinyar nan ta cigaba da ayyukan gidan nan ita kaɗai ba, duk zaku fiffito ku rinƙa tayata...." Minal ta ce "gaskiya Abbah aiki zai mun yawa, kasan da sassafe nake fita gurin aiki sai Azahar kuma, ga gajiyar aikin office sannan nazo na tarar da aikin gida? gaskiya a'a ganan su cima zaune su Pinky basa zuwa ko ina...." Ummy ta ce "Ni daman ina tayata aiki yawwa...." Pinky fuska a ɗaure ta ce "mu ai mun kusan komawa school London, don haka mu ba cima zaune bane...." Abbah ya ce "toh kafin ku koma London zaku na tayata aikin gida daga yau, ku tashi mu tafi restaurant...." Duk tashi sukayi har da ita kanta Hajia wacce taketa fushi bataso tayi magana Abbah ya dizgata acikin yaranta shiyasa tayi shuru.... Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ki taso mana kema..." Girgiza kai tayi sannan ta ce "a'a Abbah zanci shinkafar da oil da maggi, kuma Inaso kafin Uncle Deen ya dawo zan sake girka masa abinci...." Shima Roshan cewa yayi "Nima bazanje ba zan ƙarasa ci da oil da maggi sannan nayi wanka nayi bacci...." Abbah ya ce "toh kai kam waya gayyace ka duk bakai bane ka fallashe mu, rabon da muje restaurant har mun manta sai yau saboda kai....." yana kaiwa ƙarshe yaja yaran gidan zasu fice, Roshan ya ƙwalla ƙiran Ummy tare da faɗin "kema wato har dake za'a guje mun abinci koh?...." Ummy ta juyo tana riƙe da kunkumi ta ce "cabb wazai ci wannan girkin a kwana ana gudawa da zawayi....." Dariya Roshan yayi idonsa akan Baiwar ALLAH wacce ta zauna tayi shuru kamar mai tunanin wani abu, ga shinkafar bakinta yanda ta tofar itama a tafin hannunta........ 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 33 to 34 ꧁꧂ Roshan da Baiwar ALLAH su kaɗai aka bari a cikin gidan basu fita ko ina ba, suna zaune akan dinning babu wanda ya kula kowa, ita dai Baiwar Allah ta barbad'a maggi da oil tana ci hankali kwance dake ta saba ci irin wannan abincin a gidan marayu da ta zauna, shi kuma Roshan ya zuba mata eyes yana kallon yanayin yanda take taunar abincin kamar bazata ci ba, ga dimple yanda yaketa lotse wa sai ya 'kara fito da asalin kyanta sosai, ji yake kamar ya rungumeta tsabar tsananin so da 'kaunarta da ya shige cikin zuciyarsa lokaci guda, a hankali yake motsi da lips d'insa bai san lokacin da ya furta cewar "you're the Beautiful Queen of kingdom my part of mine, i love you so much with all my heart....." Dasauri Baiwar Allah ta waiwayo tana kallonsa cike da mamakin furucin da ya yi, lokaci guda ta tintsire da dariya tana tafa hannayenta tareda fad'in "woooo lallai Yayana wannan first lady takan ta zautar dakai da yawa, kana zaune amma kana tunaninta? to ni ba ita bace ni Ammatanka ce not your Queen ehen, ka farfad'o daga mafarkin zaunen da kake....." Kafin ya ce wani abu har ta mi'ke tsaye tana 'ko'karin tattare kulolin kan dinning, baice komai ba harta gama tattarawa ta shige kitchen, tashi yayi ya bi bayanta, yana shiga ya tsaya ta bayanta yana tunanin sanar mata cewar yana sonta, bata san ya shugo ba ta juya da sauri zata fice suka mannu da juna, a rud'e take fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." har tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota tareda mannata asaman 'kirjinsa, kwantar da kanta tayi kan kirjinsa tana maida numfashi domin ba 'karamin tsorita tayi ba, saida suka d'au tsawon mintuna biyar a haka kafin ta fara motsawa tana kokarin d'agowa, Roshan tintinin har ya fita hayyacinsa tsabar tsananin feeling dake kawo masa hari, a hankali take d'ago da kanta saitin fuskarsa nan suka had'a ido, babu wanda ya kawar da kansa haka suka cigaba da kallon juna, daga bisani ya fara matso da fuskarsa saitin nata numfashinsu na hargutsuwa, a hankali ya kai hannunsa ya tallafo ha6arta yana shirin had'e musu baki, itama Baiwar Allah ta shiga yanayin da tinda take bata ta6a shigarsa ba a hankali ta lumshe idonta domin ba 'karamin kashe mata jiki yayi ba da irin sallonsa wanda shi kad'ai yasan sirrin abunsa, cikin salo ya kamo lips d'inta ta 'kasi ya fara socking kamar wanda ya samu lollipop, ita kuwa 'yar uwa bata san lokacin da ta zagayo hannayenta ta bayansa ba, ta rungumeshi sosai kamar zata mayarshi cikinta, cikin salo da kwarewa yake fitar da ita daga hayyacinta ta hanyar lips socking, itama lokaci guda ta fara mayar masa da martani a hankali kamar babu rai a jikinta, suna cikin wannan halin suka ji an turo 'kofar kitchen, a rud'e Baiwar Allah ta kawar da kanta gefe tana 'kokarin kwacewa, shi kuwa ya ri'ke ta sosai ganin yanda take a rud'e bata cikin hayyacinta, fashewa tayi da matsanancin kuka tana girgiza kai had'in da cewa 'ni ka sake ni dan Allah, na shiga uku ka rufa mun asiri ka sake ni, banasoooo....." Jawo ta yayi ya rungumeta sosai a jikinsa yana bubbugar bayanta a hankali alamar rarrashi, Roshan ko waiwaya wa baiyi ba balle yaga wanda ya shugo sai ji yayi ance "Ya iyaha iyayya! Yaya Yochann me kuceyi haka? wa ce ce ka yunguma ?....." Ba tareda ya juyo ba ya ce "kinga Mamana jeki waje maza, barkwano ne ya shige mata ido shine nake hure mata, banaso tayi kuka a gabanki ne...." kafin ya 'karasa maganar ta katse shi da cewa "wayyayi tayyayi bay yadda ba, ai naga cocan bacinta kaceyi, kuma! kuma!! kuma!!! cena gaya wa Ankui Deen da Abba da Mommy....." tana kaiwa nan ta juya da gudu ko tsaya sauraronsa batayi ba, yanata 'kiran sunanta "kinga Mamana tsaya mana kiji...." harta fice abinta... Baiwar Allah ce ta fizgi kanta daga jikinsa tareda zabga masa mari akan kunci, tana kuka har idonta yayi jawur tana fad'in "wallahi ka cuce ni, ka zubar mun da mutuncina da kimata acikin gidan nan, yanzu idan Abbah yaji wannan batun ya zanyi da rayuwata, idan Hajiya ta ji shikenam kashina ya bushe......". bata 'karasa ba kuka yaci ranta, da'ker ta iya dakatarwa ta cigaba da cewa " kasa nayi abunda tinda nake a rayuwata ban ta6a aikatawa ba, ata sanadiyarka kasa mutuncina ya zube a idon yarinya 'karama...." Roshan idonsa a kanta yana ri'ke da kuncinsa ta 6angaren dama yanda ta mare shi, wani irin rad'ad'i yake ji a ransa na ganin hawayen Ammatansa, lips d'insa na kakkarwa da'ker ya iya furta "kinga Ammata bawai niyata na cutar dake bane, wallahi ina masifar son........." bai 'karasa iddasa maganarsa ba yaji ta hankad'a shi baya tareda furta "yi mun shuru...." tayi maganar cikin d'aga murya, bata tsaya sauraronsa ba tayi saurin ratsa ta gefensa ta fice daga kitchen, da gudun gaske ta wuce room d'inta tana kuka... Yar Tiny tana zaune a falo da uniform a jikinta sai faman tura Biscuit take a baki ganin Baiwar Allah ta wuce tana kuka yasa ta fara jinjina kai ta ce "Uhmmm! jaku cani ai, yau kam aciyinku ya conu don wayyayi tayyayi cena gaya wa cu Abba, in in ince Yaya Yocan yana cocan bakin ey aici jidan nan......" Roshan ne shima ya fito daga kitchen yana goge d'an guntun hawayenda suka gangaro masa, ganin sun had'a ido shi da Yar Tiny yasa ya sau mata murmushi yazo ya zauna kusa da ita yana fad'in "Mamana Biscuits ake ci ne?....." ta juyo tana kallonsa ta ce "ey Bicci nace ci ...." Ya ce "kuma baki cire uniform ba?..." kai kawai ta d'aga masa ba tareda ta ce komai ba, ya kuma cewa "Mamana kina sona?...." da sauri ta had'a masa kai alamar ey! ya jinjina kai sannan ya ce "toh idan kuwa kina sona da gaske banason kowa yaji wannan maganar, idan kuwa kika gaya wa mutum d'aya to kuwa zan sha poison na mutu, bazaki 'kara ganina ba har abada, kin dai san duk wanda ya mutu baya dawowa koh?...." Fashewa tayi da kuka ta rungumi Roshan tana fad'in "bana co ka mucu Yaya Yocan, wayyayi Tayyayi bajan jayawa kowa ba...." Ya d'ago da kanta yana fad'in "kin dai san kyan Alkawari cikawa koh?...." tana kuka ta ce "nayi maca aikawayi Yaya Yocan, bajan jayawa kowa ba......" Ya ce "shikenam Mamana daina kukan maza, inasonki Mamana...." itama ta ce "ina conka Yaya Yocan nima...." Ya ce "ok bari naje na kwanta nayi bacci koh...." kad'a masa kai kawai tayi ta cigaba da cin Biscuit d'inta..... Haurawa upstairs yayi yana tunanin Baiwar Allah, sam baiji dad'in abinda ya yi mata, zuciyarsa hargutsuwa take kamar zai fad'i tsabar hajijiyan da yake shirin d'ibarsa, daker ya samu damar 'karasa isa part d'insa, yana shiga falonsa kai tsaye bedroom ya wuce yana tangal-tangal ya fad'a saman katafaren gadonsa..... Itama Baiwar Allah tana kwance akan gadonta ba abunda take sai kuka, sai a yanzu take nadamar marin Roshan, cikin takaici take dukan kan gadon tana kuka mai cin rai, wani irin matsanancin ciwon kai ne yake damunta har idonta yana kokarin rufewa, ganin tana kokarin sumewa yasa ta tashi a hargitse ta nufi toilet, tana shiga ta kunna shower a kanta, ruwa mai sanyi ne yake ratsa duk ilahirin jikinta tin daga kan sumar kanta, ta kunna ruwan sanyi ne sakamakon zafin da jikinta ya d'au.... tin daga cikin toilet ta d'auro alwala ta fito, nufan wardrobe tayi ta zaro doguwar riga marar kauri mai hannun singlet ta zura sannan ta sanya hijab har 'kasi ta shimfid'a sallaya tareda tsaida sallah.... Around 8:00 O'clock mutanen gidan suka dawo, saida suka zagaya wuraren shakatawa kafin suka dawo gida, a falo suka tarar da Yar Tiny tana kwance saman doguwar kujera sai sharar bacci take ga Biscuit yanda ta dun'kule kamar wanda za'a kwace, Abbah ne ya ce "ha'a Auta mutanen rigima har akayi bacci....." Ummy kuma nufar d'akin Baiwar Allah tayi ba jumawa ta fito tana murmushi ta ce "itama Aunty Baiwar Allah bacci take akan sallayarta...." Mommy fuska a murtu'ke ta ce "shine ita tana can room d'inta tana shan bacci ta bar mun yarinya a falo ga sanyi A.C kalan mura ya kama ta...." Abbah ya ce "haba Khadija meye abun fad'a anan? itama bacci ne ya d'auketa kina ji....." Hajia Kilishi kamar zatayi kuka ta ce "ai daman baka ta6a goya mun baya ba, saboda ka gaji da zama dani...." tana kaiwa nan ta haura saman upstairs tana gunaguni... Abbah bai ce komai ba ya kalli Ummy ya ce "uwar masu gida d'auketa kije ki cire mata uniform saiki kwantar da ita...." Ummy ta ce "toh Abbah...." tasa hannu ta d'auki Yar Tiny suka haura upstairs dake tare suke kwana, ta juyo ta ce "Abbah saida safe don nima ba fitowa zan 'karayi ba...." Abbah da murmushi a fuskarsa ya ce "toh Uwar masu gida Allah ya tashe mu lafiya...." Minal kuwa tin shugowarsu ta haura abinda bata tsaya jin ta bakin kowa ba... Suma Pinky da Rukky sallama sukayi wa Abbah suka haura saman room dinsu.... Abbah zama yayi a falo shi kad'ai yana fuskantar plasma, so yake yaga dawowar Razhdeen domin an sanar masa cewa ya fita tin da rana kuma gashi yanzu har dare yayi bai dawo ba, sannan ya'ki yin picking calling ..... Misalin karfe 10:30 sai ga Razhdeen ya shigo falo, tarar da Abbah yayi yana zaune sai bacci yake sha, Da kamar zai wuce part d'insa har ya soma haura upstairs sai ya juyo yana kallon Abbansa, bazai iya barinsa a haka ba yaje ya zaune a gefen Abbah yana 'kiran sunansa cikin sassanyar murya "Dad! Daddy!! Daddd!!!....." A rud'e Abbah ya bud'e idonsa yana fad'in "ina kaje Razhdeen? banason yawon daren nan......" Uncle Deen kallon Abbah yake cike da mamaki, Na farko daga tashinsa a bacci yake wannan sumbatun, na biyu kuma shi ba wani karamin yaro bane da har za'a damu in bai dawo gida ba.... Abbah yasa hannu yana shafar fuskarsa yana hamma tareda yin hamdala, daga bisani ya juyo yana kallon Uncle Deen cikin nuna damuwa ya ce "Razhdeen ina kaje?...." Uncle Deen ya ce "Dad nifah am not a small child...." Abbah ya ce "yes i known that but you support to tell me anyway u want go...." Uncle Deen ganin yanda Abbah yake nuna damuwarsa akansa ya ce "okay i will take care don't worry...." ya karasa maganar tareda mi'kewa tsaye yana kokarin tafiya.... Shima Abbah tashi yayi ya haura part d'insa yana jan 'kafa da'ker tsabar tsananin baccin da yake ji...... Misalin karfe 1 saura Uncle Deen yana ta kai kawo a falonsa, yana tunanin yarinyar nan mai busa sarewa tambayoyine cike acikin zuciyarsa yana maganar zuci cewar "idan har yarinyar nan mutum ce nayi alkawari saina nemota, kuma saina kasheta domin ba karamin wahalar da kwakwkwalwata take ba, kullum ina shiga matsala saboda ita because of why? i will teach her a lesson, Idan kuma ba mutum bace!......." ya dakatar da maganar zucin da yake yi tareda hura iskar bakinsa....... Dai-dai lokacin da Baiwar Allah ta turo 'kofar d'akin da sallama a bakinta tana d'auke da tray na kuloli a hannunta.... Kallo d'aya yayi mata ya kawar da kansa gefe yana cin boom, ita kuwa wuce tayi ta nufi dinning taje tana jejjera masa kayan abinci, zuwa tayi tasa hannu zata buɗe ƙofa ta fita sakamakon daren da yayi har ƙarfe 1:00 yanzu, taji yayi mata magana tsayawa tayi tareda juyowa tana fuskantar sa amma saidai tana kallon ƙasin carpet ne domin bayaso a cika kallonsa, kamar bazaiyi magana ba daƙer ya ce "tinda meya hanaki kawo mun abinci?...." cikin sassanyar murya ta ce "kayi haƙuri bansan dawowarka bane ...." juyowa yayi yana kallonsa ya ce "tin ƙarfe 10 na dawo amma dubi clock 1 O'clock are you stupid? idan kika sake mun jinkirin kawo food ranki zai ɓaci...." Dasauri ta ɗaga masa kai tare da faɗin "insha ALLAHU baza'a ƙara ba...." "Better for you, saiki jira idan na kammala saiki tattara shirginki ki bar mun room...." a cewar Boss.... zuwa yayi ya zauna a dinning itama zuwa tayi ta fara zuzzuba masa, tana kammalawa taja ta tsaya tana jiran gamawarsa, Cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta zabura tare da zaro manya-manyan idanuwanta, da sauri takai ƙwayar idonta kan Uncle Deen taga yana shirin kai one spoon cikin bakinsa, a gaggauce tayi saurin riƙe masa hannu wanda itama kanta bata san tayi hakan ba, hannunta na riƙe sa hannunsa wanda yake riƙe da cokalin abinci, Dalilin yin hakan a lokacin da bacci ya ɗauketa akan sallaya bata tashi farfaɗowa ba sai yanzu, a gigice ta tashi saboda ta tuna bata kawo wa Uncle Deen abinci ba, tana fita falo kai tsaye kitchen ta nufa, tana shiga ta ɗauki kulolin abincinsa wanda ta ware masa gefe guda ta kai masa, Gaba ɗaya ta manta ashe abincin yayi gishirin da bazai ciyu ba, a niyarta daman ta sake masa girki ne sai kuma mantuwa ya biyo baya... jikinta ne ya hau ɓari ganin hannunta yana riƙe dana Uncle Deen, Wani irin kallo ya watsa matsa mata bata san lokacin da ta sake masa hannu taja da baya ba, nan danan hawaye har ya wanke mata fuska..... cikin ɓacin rai ya ce "wani irin shashanci ne haka? Are you a madness?...." Dasauri take girgiza masa kai! ya ce "okay ina kin mayar Ni abokin wasan ki koh? Kneel down for here...." zuwa tayi ta durƙusa a yanda ya nuna mata tana kuka, ta haɗa hannayenta sama tana kallonsa ta wutsiryar ido taga ta yanda zai fara cin abincin nan... hannu yakai kan spoon yana haɗa miya da shinkafa da nama akai ya ɗeba yakai saitin ɗan ƙaramin bakinsa wanda daƙer yake buɗe su, yana kai abincin cikin bakinsa tauna ɗaya biyu ya sandare guri ɗaya, haka ya tsayar da bakin ya dena motsa shi ƙwayar idonsa akan abincin dake cikin plate......... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 35 to 36 ꧁꧂ Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗanin da Baiwar ALLAH tayi gaba ɗaya ta susuce hannunta a sama ta ƙanƙame idanuwanta sosai saboda gudun halin da zata ga Uncle Deen, ta rigada ta saddaƙar yau kashinta ya bushe, haka jikinta yake ɓari kamar wacce take cikin ruwan ƙanƙara.... cikin yanayin rashin jin daɗin bakinsa haka ya burtso da abincin bakinsa cikin plate ɗin abincin yana yamutsa fuska, tinin har fuskar yayi jawur abunka da farin mutum, ba komai ne yasa haka ba illa tsananin ɓacin rai da ya shiga lokaci ƙanƙani, Ɗagowa yayi a fusace yana wurga mata wani irin la'anannen kallo wanda zaisa mutum sumewa wata ƙil tacan ya rasa rayuwarsa, Allah ya temake ta idanuwanta a rufe suke rub sam bata ƙaunar haɗa ido da shi, wani irin tsawa ya daka mata cikin fitar hayyaci, kamar daga sama taji sauƙar tsawar a firgice ta zaro da manya-manyan eyes ɗinta tare da ƙafesu guri ɗaya tsabar tsananin ruɗanin data shiga bata san lokacin da ta fara sakin fitsari a jikinta ba, haka jikin yake kakkarwa kamar mai farfaɗiya... Ganin halinda ta shiga cikin lokaci ƙanƙani yasa ya sassauta muryarsa idonsa akanta ya ce "wani irin dabbanci ne wannan? You want kill me?...." Baiwar ALLAH dai ido a ƙafe zuwa yanzu ta daina kakkarwar da take sai dai bata motsi kwata-kwata, already ya rigada ya fiskanci halin da take ciki bata cikin hayyacinta, tashi yayi yana jan ƙafa daƙer ya shige bedroom ɗinsa kai tsaye toilet ya shige, yana shiga ya ɗauki brush tare da matsar makilin yayi brush sosai, Saida ya tabbatar baya jin ɗanɗanon gishirin tukun ya wanke bakinsa ya fito, ya ƙara nufan falo still yanda ya barta anan ya dawo ya sameta a ƙafen bata motsa koda ɗan yatsarta ba ma.. Buɗe frig yayi ya ɗauki farror mai sanyi ya tako har yanda take a durƙushe already ya buɗe murfin robar ba tare da ya tsiyayi ruwan ba haka ya fara kwara mata ruwan da bakin robar a saitin fuskar ta, a razane ta motsa tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya haka take fitar da numfashi sama-sama daƙer, har eyes ɗinta sunyi jawur... Durƙusawa yayi a gabanta yana kallon cikin ƙwayar eyes ɗinta rai a ɓace ya soma faɗin "ba suma zakiyi ba ko mutuwa zakiyi yau sai kin ɗanɗani kuɗanki, sai kin girbi abinda kika shuka, saboda rainin wayo zaki kawo mun abinci mai gishiri?....." Fashewa tayi da kuka ta soma faɗin "wallahi ban sani ba...." kafin ta ƙarasa faɗin abinda zata ce yayi saurin daka mata tsawa tare da faɗin "shut up! your very stupid, I don't want to breath your smelling mouth, abinda nake so dake shine yanzu ki tashi kije ki cinye duk abincin nan....." Baiwar ALLAH tin tinin ta haɗiye kukanta, jin ya ce taje ta cinye abincin yasa ta ɗago a razane tana kallonsa.... zaro mata ido yayi yana faɗin "Now! Now my friend...." wani irin haɗiyar yawu tayi mai kama da fitar rai, jiki na ɓari ta tashi tana jan ƙafa ta nufi dinning tana kuka, ya ce "oyah seat down...." ya nuna mata kujerar dinning, tazo zata zauna anan ya lura da jiƙar kayanta da sauri ya dakatar da ita tare da faɗin "wait! don't seat here, Meya kawo wannan jiƙar a kayanki ?..." dasauri takai idonta kan kayan jikinta tanata faman dubawa eyes ɗinta ne suka sauƙa akan rigarta ta wajen mazaune ruwa sai faman ɗiga yake, a ruɗe ta ɗago tana kallonsa cike da tsoro da fargaba, shi kuwa ƙwayar idonsa ya wurgar saitin wajen da ta zauna before, yaga wajen duk jiƙar ruwa, juyowa yayi ya kalleta tare da faɗin "whattt! kina nufin kice fitsari kika mun a carpet? ....." jinjina kai ya soma yi domin yau ɗin nan ba ƙaramin ɓata masa rai Baiwar ALLAH take ba, idan ya ce zai ɗau hukuncin abubuwan da tayi masa zai iya raunanata ne, tsabar ya rasa abinda zai yi kuma ya rasa abun cewa Dogon tsuka yaja sannan ya ce "i hate You wallahi, because of you are an ingratitude fool, Now ki cire mun wannan ƙazantar da kika mun akan carpet ki fita mun dashi daga room, kije ki wanke sannan ki dawo ki gyara mun room, akwai new carpet in order part from outside ki ɗauko ki saka mun a room, zan shiga nayi bacci sauran kuma ki tashe Ni kiga ikon ALLAH....." yana kaiwa nan yayi shigewarsa cikin bedroom, yana shiga ya shige toilet domin yin wanka...." Baiwar ALLAH sauƙe numfashi tayi tana bin ƙofar bedroom ɗinsa da kallo cike da mamakin rashin imaninsa da tausayi, ɗago kai tayi ta kalli agogo taga ƙarfe 3 sauran mintuna, Ga idanuwanta yanda sukayi lufu-lufu suka kumbura lokaci guda ga wani irin baccin da take ji amma babu halin yi, Girgiza kai tayi sannan ta nufi tsakiyar filin falon tana ƙare ko ina da kallo, tana nazarin ta yanda zata fara ɗaga kujeru kafin ta samu damar cire carpet ɗin, babu yanda ta iya haka ta fara jan kujerun a hankali tana zamar da carpet, da iya ƙarfinta take janye sopas har tayi nasarar cire carpet ɗin gaba ɗaya, sai dai ɗaukar carpet ɗin ma wahala domin ba ƙaramin nauyi gare shi ba, irin mai gashi nan ne, daƙer take jan carpet har ta fice daga falon, nan ma sauƙa daga kan beni ma aiki ne babba, cikin ikon ALLAH ta fice da carpet ɗin waje can bakin fanfo waran wanki, sannan ta wuce yanda sabin carpets suke taje ta zaɓo masa carpet mai kyau kalar kujerunsa sannan ta koma part ɗin Uncle Deen, nan ma taje tasha wahalar shimfiɗa carpet ta jejjera kujerun a yanda suke a tsare, sai falon ya ƙara kyau sosai gwanin burgewa, tana gamawa da wannan ɓangaren ta koma waran dinning tana tura baki acikin zuciyar ta kuwa cewa tayi "wallahi bamai saka Ni naci wannan abincin...." tasa hannu ta ɗauki kulolin gaba ɗaya ta nufi hanyar waje dasu zata kai can kitchen.... Shi kuwa Uncle Deen bayan ya fito daga wanka iya jallabiyarsa ya zura sannan ya tsaida sallah daman already ya haɗo da alwalarsa, yayi sallolin lafulfuli sannan ya tashi ya cire rigar jikinsa ya zauna daga shi sai 3 quater da singlet a jikinsa saida ya feffeshe jikinsa da turare sannan yabi lafiyar gado, duk waɗannan aikace-aikacen da Baiwar ALLAH tayi bai sani ba domin shi tin tinin bacci yayi gaba da shi.... Baiwar ALLAH dawowa cikin room ɗin tayi ta goggoge dinning ɗin da ya ɓaci da maiƙon ferfesu.... Doctor ROSHAN yana kwance saman katafaren gadonsa yana fuskantar ceilling, yanda yaga rana haka yaga dare ya kasa yin bacci, tunanin Baiwar ALLAH ya hana shi sukuni, fuskarta kawai yake gani a saman ceilling, Ganin ya kasa yin bacci yasa shi miƙewa zaune yana dafe da goshinsa tsabar tsananin ciwo da yake masa, daƙer ya tashi yana jawuwa ya nufi toilet Ba jumawa ya fito da damshin ruwa a jikinsa alamun wanka yayi haɗi da alwala domin shimfiɗa sallaya yayi ya tsaida sallah bayan ya zura farar jallabiyarsa..... Baiwar ALLAH bayan ta kammala komai a ɗakin Uncle Deen ta dubi agogon ɗakin ƙarfe huɗu da rabi na asuba, jiki a sanyaye tasa hannu zata buɗe ƙofar falon ta wuce kafin ta ankara da hakan ta soma jin surutai acikin bedroom ɗin Uncle Deen, A tsorace ta waiwaya baya tayi tunanin da ita ake, ganin bata ga kowa ba kuma ga maganganun da ake yi kamar ba lafiya ba, da sauri ta nufi bedroom ɗinsa tasa hannu a hankali ta tura ƙofa ta shige, zuciyarta na dar-dar abun mamaki gani tayi Uncle Deen gashi nan a kwance ido a rufe amma yana wani irin surutai sai faman juye-juye yake gaba ɗaya ya haɗa gumi jikinsa yayi sharkaf duk da sanyin A.C dake ɗakin, "Why! Why!! Why!!! I don't like it, ki bayyana kanki please, aina zan same ki, idan har ke mutum ce I need to see you bana so ki rinƙa wahalar dani da wannan sautin naki, ki mun adalci, banaso! banaso!! banasooo!!!!, zan kashe ki i swear, I swear I'll kill you........" Haka yake haɗa zaƙami yana wannan surutan, hannunsa yakai saitin kansa ya riƙe sosai yana faɗin "Wayyo kaina, Wayyo kaina zai fashe ciwo ku temake Ni ....." Baiwar ALLAH ganin halinda yake ciki ba ƙaramin tausaya masa tayi ba, kuma duk acikin baccin yake waɗannan maganganun.. Ganin yana shirin zaucewa yasa ta nufi har yanda yake kwance da gudu, hannunta ne ya soma ɓari tana son temaka masa amma sai dai tana tsoro, idan ya fara wannan abun nashi Allura ake masa ya dawo normal, ita kuma a halin yanzu ta rasa mai zata masa, haka ta fara tunanin ko taje ta sanarwa Abbah ne ko Roshan, wani dabara ne ya faɗo mata da sauri ta shige toilet taje ta jiƙo towel da ruwan sanyi ta dawo a tsorace ta ɗan haura saman gadon da yake ta ɗora masa jiƙaƙƙen towel ɗin akan goshinsa, jikinsa ne yake kakkarwa sosai ga jikinsa yanda ya ɗau zafi jin sanyi yana ratsa shi yasa ya sau nannauyar ajiyar zuciya baisan lokacin da ya jawo Baiwar ALLAH saman faffaɗar ƙirjinsa ba tare da rungumarta sosai still jikinsa na kakkarwa kaɗan-kaɗan, a tunaninsa yarinyar da ta juya masa baya tana kiɗan jitarta ita ya runguma domin a wannan lokacin yayi nasarar riƙota sakamakon ruwan da aka saka masa, basa son ruwa kwata-kwata aljanun yarinyar da suke jefa shi cikin wannan halin a yayinda yake cikin baccinsa, wani irin sauƙe numfashi yayi cikin lokaci ƙanƙani hankalinsa ya kwanta daga nan ya wuce da ainahin baccin da yake, Baiwar ALLAH tsoro ne ƙarara a saman fuskar ta, ga yanda ya rungumeta ko kwakkwaran motsi ta kasa yi, haka jikinta yake ɓari itama saboda tsoro da fargaba ...... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 37 to 38 ꧁꧂ Baiwar Allah tana Saman ƙirjin Uncle Deen har aka fara ƙiran sallar asuban farko basu motsa ba, ta kasa motsawa sai zuciyarta dake bugun uku-uku, gaba ɗaya ta haɗa gumi sharkaf ji take kamar ta haɗiyi ranta tsabar tsoro da fargaban Uncle Deen da zaran ya tarar da ita a haka, Sam bata runtsa ba gaba ɗaya bacci ya ƙaurace mata, ƙiran sallah ne ya daki dodon kunnensa a hankali ya fara juyar da kansa Ido a lumshe, hannunsa ya ɗago daga kan Baiwar Allah ya ɗora kan goshinsa yana fitar da numfashi sama-sama, a hankali Baiwar Allah ta ɗago da kanta tana fuskantar sa, manyan idanuwanta ta sauƙar kan kyakykyawar fuskarsa a tsorace take kallonsa ganin yana mutsil-mutsil da eyes ɗinsa yana shirin buɗesu Wani irin juyi tayi bata san lokacin data faɗo daga saman gadon ba har saida ƙafarta ya gurmuɗe, buɗe baki tayi zatayi ihu jin zafin ciwon ƙafar dasauri tasa hannu a saitin bakinta ta rufe ruff tinin ta haɗiye kukan, tana zazzaro Ido... Shi kuwa jin nauyi a kansa ne yasa ya buɗe eyes ɗinsa gaba ɗaya yana kallo ceiling, jujjuyar da ƙwayar idanuwansa ya soma yi ko zaiga mutum domin yaji kamar motsin mutum a kansa amma baiga kowa ba, jin anata ƙiraye-ƙirayen sallah ne yasa ya tashi zaune yana dafe da goshinsa, ganin towel yayi ya faɗo daga saman kansa, cike da mamaki ya ɗauki towel da jiƙar ruwa a jiki yana jujjuya shi, Juye²juye ya fara yi amma Babu kowa, sakin dogon numfashi yayi tareda wurgar da towel ɗin gefe ya sauƙar da zura-zuran ƙafafunsa ƙasin carpet yana shirin tashi, Baiwar Allah tana kwance ƙasin carpet ta ƙarƙashin gadon amma sai dai bata ƙarisa shigewa ciki ba saboda gadon a matse yake da ƙasi babu yanda zatayi ta shige gaba ɗayanta, ganin sawayensa yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske kamar zai faso ya fito tsabar harbawar da ƙirjinta ke yi, miƙewa yayi ya nufi toilet domin ɗaurowa alwala yana shiga kuwa tayi saurin hautsunowa a ruɗe ta miƙe tana ɗingishi tayi saurin ficewa daga cikin bedroom daman already ƙofar a buɗe take, a gurguje ta samu nasarar fita daga falon ma, a hankali take taka Benin domin ba ƙaramin buguwa tayi a ƙafar ba, tana sauƙa public falo ta nufi kitchen kai tsaye, tana shiga ta ɗora hannayenta a saitin ƙirjinta tana fitar da numfashi daƙer, kunna ruwan fanfon sink tayi ta wanke fuskarta sannan ta tsiyayi ruwa a cup ta sha domin maƙogaronta ba ƙaramin bushewa ya yi ba, saida ta kammala hutawarta a cikin kitchen tukun ta fito falon tana takawa a hankali idonta ne suka sauƙa akan Roshan wanda yake ƙoƙarin sauƙowa downstairs shima idonsa akanta, tsayawa tayi tana tunanin marin da tayi masa Nan danan taji ba daɗi a ranta, tayi nadamar wulaƙancin da tayi masa tana maganar zuci idonta akansa, har ya ƙarasa sauƙowa baice mata komai ba shima kuma ya kasa ɗauke eyes ɗinsa akanta, suna cikin wannan halin basu san lokacin da Uncle Deen shima ya sauƙo falon ba, hannu yasa ya dafa kafaɗar Roshan tareda faɗin "my twins what's wrong with you?...." A firgice Roshan ya juyo yana kallonsa da smile akan fuskarsa ya ce "there's nothing my Man....." Uncle Deen idonsa yakai kan Baiwar Allah tareda faɗin "okay that's good...." Baiwar Allah Kai a sunkuye gudun karta haɗa Ido da Uncle Deen a gurguje ta nufi room ɗinta kafin ta ƙarasa taji muryar Abbah daga sama shima yana ƙoƙarin sauƙowa yana faɗin "lafiya kuwa Dota naga kina ɗingishi?...." Juyowa tayi tana ƙiƙƙina idonta akan Uncle Deen wanda idonsa akan agogon hannunsa yana ƙoƙarin saita shi ta ce "am am ammm Abbah dam daman buguwa nayi ne ....." Roshan idonsa akanta shima ya lura da yanayin tafiyarta amma sai dai ya fahimci akwai wani abu domin eyes ɗinta akan Uncle Deen suke, dasauri Roshan ya waiwaya yana kallon Uncle Deen yaga shi hankalinsa ba'a kanta yake bama, ya sake Kai idonsa kanta anan suka haɗa Ido, Abbah yace "toh kina lura maza kinji Koh...." Ɗaga Kai sama tayi ba tareda ta ce komai ba tayi saurin shigewa room ɗinta... Haka suma duk suka haɗa kayuwansu suka nufi hanyar fita zuwa masallaci daman kullum haka suke tare suke zuwa masallaci, duk suna sanye da jallabiya Roshan da Razhdeen fararen jallabiyoyi ne a jikinsu shi kuma Abbah yana sanye da baƙar jallabiya ga haske dadau-dadau ta ko ina kamar rana, Baiwar Allah zama tayi a bakin gadonta tana jin tada motarsu har suka tafi a lokacin itama ta tashi ta nufi toilet yowa alwala, tana mai jin takaicin Uncle Deen ba komai ne ya ɓata mata rai ba illah rashin yin sallar dare, ta saba kullum zata tashi tayi sallah daga ƙarfe ɗaya zuwa uku amma yau saboda Uncle Deen bata yi sallolin ba, da wannan takaicin tayo alwala sannan ta fito da ɗauki zureren hijab ɗinta ta zura sannan ta tsaida sallah..... Around 9:00 Baiwar Allah da Ummy suna kitchen suna fama haɗa breakfast sai kuma Pinky a gefe guda tana wanke-wanke tana jin yanda suke hirar su amma bata sa musu baki ba sai faman tsuka take ta jerawa, ita kuma Rukky tana falo sai gyare-gyare take da goge-goge, Bayan wasu ɗan mintuna duk suka hallaru a dinning iya mutum biyu ne Babu Roshan da Razhdeen daman su Kai musu ake can part ɗinsu, suna cikin yin breakfast minal ta tashi da hanzarinta ta zari handbag ɗinta domin sauri take zata fita gurin aiki, daga ita sai mommy itama ta kammala shirinta zata tafi office itama, Ƴar Tiny kuma daman bata tsayawa yin breakfast lunch ake haɗa mata kularta a saka mata acikin lunch bag ɗinta taita tafiya, ko wacce ta security da yake kaita gurin aiki, Shima Abbah tashi yayi cikin shirinsa na kakin soja zai tafi headquarters domin gudanar da wasu ayyuka, kafin ya fice ya juyo yana kallon Ummy ya ce "uwar masu gida ganan Dota ki rakata gurin Roshan ya duba mata ƙafarta...." Ummy ta amsa da "toh Abbah....." sai gurin ya rage daga Pinky sai Rukky da Ummy da kuma Baiwar Allah, suma Pinky da Rukky suna kammalawa suka tashi suna hararar Baiwar Allah suka bar wajen, su haushinsu Abbah yafi damuwa da Baiwar Allah akan su.... Itama Baiwar Allah tana gamawa ta fara tattara kulolin kan dinning zata Kai su kitchen Ummy ta tayata duk suka gyara wajen, suna kitchen Baiwar Allah ta kalli Ummy sannan ta ce "Sister Ummy Dan Allah ki temaka mun ki Kai breakfast ɗin Uncle Deen ni zan Kai na Yaya Roshan ..." Ummy ta ce "ok ba damuwa bari na miƙa masa...." ta ɗauki na Uncle Deen tayi gaba, Ita kuma ta fara shirya na Roshan kuma daman tanaso ta same shi ta bashi haƙuri akan laifin da tayi masa ... Ummy ce ta shiga room falon Uncle Deen da sallama a bakinta gani tayi falon wayam Babu kowa, zuwa tayi gurin dinning ta ɗora kayan abincin akai, idonta akan tsarin falon yanda ya zama, cike da mamaki take bin falon da kallon tana maganar zuci "yaushe Uncle ya chanza carpet ɗin falon? ....." tana cikin wannan tunanin taji ya ce "what's wrong?..." A zabure takai idonta kansa tareda faɗin "gud morning Uncle Deen....." ba tare da ya nuna wata damuwa ba ya ce "same to you Hajia ta...." Wani irin farin ciki Ummy tayi yau ta samu kansa daman bayan Ƴar Tiny sai Ummy waɗanda yake shiri dasu acikin yaran gidan, kuma daman sunan da yake ƙiranta dashi kenam Hajiya domin ita ɗin takwarar Hajiya Maryama ce kakarsu kenam.... idonsa akanta ganin yanda take ta sau murmushi ya ce "are you okay?...." Dasauri ta ɗaga masa Kai tana jinjina masa, ya ce "ok whare is her?...." Ummy cikin rashin fahimta ta ce "who?...." Ɗaure fuska yayi kamar bazaiyi magana ba bayan seconni ya ce "the Girl...." Ummy gudun karta hargitso shi yasa tayi saurin hasasho Baiwar Allah nan danan ta ce "ohhh ƙafarta ne yake mata ciwo shiyasa na kawo yau ɗin...." Goya hannayensa yayi Saman ƙirjinsa yana kallon dinning ya ce "ki ɗauki gaba ɗaya kayan abincin Nan ki koma dashi can yanda suka fita, sannan ki ce mata tazo ta right now...." yana kaiwa Nan ya nemi guri ya zauna akan kujerar falonsa yana pressing phone nashi .. Ummy zaro Ido tayi waje tana jinjinawa Uncle Deen tareda amsa masa cikin girmamawa ta ɗauki gaba ɗaya kayan abincin ta fice dasu, tazo zata sauƙa downstairs taci karo da Baiwar Allah tana ƙoƙarin haurowa zata miƙi ɗakin Roshan ita kuma tana tafe daƙer, Ganin Ummy yasa ta dakata cike da mamaki ta ce "ya naga kin dawo da kayan abincin?....." Ummy ta ce "wallahu a'alamu yace kije yana nemanki...." Baiwar Allah saida ƙirjinta ya buga ta zaro manya-manyan eyes ɗinta tareda faɗin "ni kuma?....." Ummy ta ce "Kinga baya son delay fah ki samu kije...." Baiwar Allah ta ce "shikenam ba komai, bani na hannunki ke kuma saiki karɓi na Yaya Roshan ki Kai masa...." Ummy ta ce "kar ki koma da kayan abincin ki ajiye anam idan ya ce yana buƙata saiki dawo ki ɗauka...." Baiwar Allah ta ce "toh shikenam...." ta ajiye kayan abincin kamar yanda Ummy tace sannan ta miƙi hanyar part ɗinsa, ita kuma Ummy ta nufi part ɗin Yaya Roshan, Baiwar Allah shiga tayi da sallama a bakinta ta tarar dashi yana zaune ko ɗagowa baiyi ba balle ya amsa sallamarta, Sunkuyar da kanta tayi ƙasi ta ce "gani...." Fuska a murtuƙe ya ce "baki iya gaisuwa bane?...." Murya a harharɗe ta ce "ina kwana...." Baice mata komai ba sai cewa yayi "meya hanaki kawo mun breakfast?...." kamar zatayi kuka ta ce. "ƙafata ke mun ciwo..." ya ce "meya sameta?...." "Buguwa nayi...." A cewarta. Ya ce "Oh God! Shi ya hana ki kawo mun breakfast?...." Baiwar Allah dasauri ta amsa masa tareda ɗaga masa Kai ganin ya tausaya mata, Ya ɗago da fararen eyes ɗinsa yana kallonta ya ce "nake ga tinda ƙafar ba yankewa tayi ba ai bazai hana ki kawo mun breakfast ba Koh?....." Baiwar Allah ɗagowa tayi tana kallonsa kamar zatayi kuka Babu bakin magana, ya kuma cewa "Koda ƙafarki yankewa tayi dole ki tokara da sanda ki kawo mun abinci, daga yau last warning kar na sake ganin ƙafar wata ta kawo mun abinci indai bake bace, idan kuwa ba haka ba daga ke har ita you will see what am going to do, Yanzu kije ki ɗauko mun abinci now! now!! Before I count 1 to 5...." Baiwar Allah juyawa tayi tana sharar hawaye ta fice, tana zuwa ta ɗauki kayan abincin a yanda ta ajiye a saman Benin, Ɗauka tayi ta nufi ɗakinsa tana Jan ƙafar da sauri kafin ya ambaci biyar a ƙirgensa, Da sallama a bakinta ta shige falon saida tazo tsakiyar falon ƙafarta ta sake gurmuɗewa ta faɗi gaba ɗaya kayan abincin suka watse, ga miyar Ogusi yasha tsala-tsalan naman kaji aciki duk miyar ya kife gaba ɗaya.... Baiwar Allah bata san lokacin da ta fara furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibatin wa akhlifli khairan Minha, Ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....." Saida ya bari ta gama addu'o'inta sannan ya ɗago yana kallonta fuska a hargutse, Ita kuma hannayenta biyu ta haɗe guri ɗaya ta ɗago dasu alamar roƙo, bakinta ne yake kakkarwa zatayi magana amma ta kasa furta komai sai kukan da take yi .... Ya ce "ki haɗiye mun kukan Nan, kin ci sa'a yau murnar ƙarin shekara ta kuma shekarar rasuwar mahaifiyata, bazan yi murna ba kuma bazanyi jimami ba, zan sassauta miki hukunci, abunda zakiyi shine kisa bakin ki duk ki shanye miyan da kika zubar akan carpet, sannan kizo ki mun mopping....." Kamar yanda ya ce a hanzarce ta kifar da kanta ƙasin carpet ta soma Shan miyan Nan kamar wata Akuya, tass saida ta shanye miyan Nan dake Allah ya temaketa iya miyar ce kawai ta zube sauran abubuwan duk akulle suke da marafansu, bayan ta kammala tashi tayi ta tattare kulolin ta fice dasu, Daga baya ta sake dawo da abun goge-goge da bucket mai ɗauke da ruwa a ciki tazo ta fara mopping duk da goggoge wuraren da ya ɓaci, Sannan ta sake fita da kayan aikin, Ba jumawa ta sake shugowa da wasu kulolin abinci daban kuma du a hankali take tafe ta ƙarasa gurin dinning ta jejjera masa kayan abincin.... Shi kuwa yanata uzurin gabansa ko kallon yanda take beyi ba, Bayan ta kammala daƙer ta daidaita tsayuwarta sannan ta ce "na kammala...." Tasowa yayi yana Jan ƙafa kamar mai tambayar ƙasi ya ƙarasa dinning ya zauna akan chair, itama zuwa tayi ta zuba masa a plate taje ta buɗe frig ɗinsa ta ɗauko cold water da su juice da milk ta kawo masa, kafin ya fara cikin abincin saida ya sata tazo tayi one spoon saboda gudun kar yayi irin na jiya, ta juya zata tafi ya dakatar da ita tareda faɗin "ina Zaki je?....." juyowa tayi tana kallonsa ta ce "zanje a duba mun ƙafata ...." Ya ce "ai baki gama karɓan hukuncinki ba, kiyi mun kneel down a tsakiyar falon Nan...." cike da takaici take kallonsa har taji ta tsane shi saboda muguntarsa, ba yanda ta iya haka ta durƙusa daƙer tayi kneeling... tsiyayar juice yayi a glass cup sannan ya kurɓa ya ajiye yana shirin Kai abinci bakinsa ya ce "rest your hand up...." Nan ma tayi yanda ya ce tana wurga masa harara ta gefen Ido ba tareda ya sani ba..... Suna cikin wannan halin suka ji sallama, Roshan ne ya shugo domin duba Ɗan uwansa ya tarar da Baiwar Allah durƙushe a ƙasi ta ɗaga hannaye sama ga hawaye yanda yayi sharkab akan fuskarta, jikinta ne yayi kakkarwa tsabar gajiyar da tayi ga ƙafarta yanda ta gurɗe yayi tsami sosai sai azabar ciwonda yake mata... Roshan idonsa akanta Wani abu ne kamar kibiya yaji ya soki saitin zuciyarsa, dasauri ya lumshe eyes ɗinsa tareda cije lips ɗinsa na ƙasi.... Uncle Deen yana kan dinning idonsa akan Roshan ya ce "are you okay...." Girgiza Kai Roshan yayi ya nufi yanda Baiwar Allah take yasa hannu ya ɗagota, kasa tsayuwa tayi sai luuu ta faɗa Saman ƙirjinsa tayi ƙasi zata faɗi ya yi saurin riƙota ya riƙeta sosai, yana jin yanda ta fashe da kuka ji yayi kamar shima ya yi kukan, Uncle Deen cike da mamaki yake binsu da kallo ya ce "Twins what happens?..." Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi ya kuma yi sannan ya ce "My heart so painning me...." "Why...." A cewar Uncle Deen.. "Because of this girl....". Roshan ya ƙarisa faɗa yana bin Baiwar Allah da kallo wacce ta narke masa a jiki.. Uncle Deen yamutsa fuska yayi sannan ya ce "I don't understand, what do you mean?...." Roshan ɗagowa yayi yana kallon Razhdeen kamar Wani ɗan maraya ya ce "she's my life ....." Cikin rashin fahimta Uncle Deen ya ce "Who?....." Roshan ya ce "This girl......" A zabure Uncle Deen ya miƙe tsaye daga zaune tareda faɗin "Whattttttt!!!! Are you a mad?....." Cikin ɓacin rai Roshan ya ce "am not a mad, nasan abunda nake yi, this girl she's my destiny and my life, so please I begging you don't try to hurt her again, because am going to marry her soon....." Uncle Deen cike da mamaki yake bin Roshan da kallo tinda suka taso Bai taɓa tsayawa a gabansa yana gaya masa maganganu ba sai yau, abun ya kulle masa Kai ....." Roshan ɗaukar Baiwar Allah yayi saman kafaɗarsa yana shirin fita da ita, Uncle Deen ya dakatar da shi tareda faɗin "kada ka kuskura ka fita da yarinyar Nan, umarni ba shawara ba....." Roshan cike da mamaki shima ya juyo yana faɗin "Umarni? wai Umarni kake bani? ....." Uncle Deen ya ƙaraso gabansa da cewa "Yes! bazaka fita da yarinyar Nan ba saboda inada right ɗin da zanyi Iko da ita sannan na hukuntata da zaran tamun laifi...." Roshan girgiza Kai kawai yayi ya juya zai fita cikin ɓacin rai Uncle Deen yasa hannu ya finciko Baiwar Allah daga Saman kafaɗarsa ya cillata kan kujerarsa 3 seater, A kiɗime Baiwar Allah tasau ƙara lokacin guda ta sume a wajen saboda irin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki... Roshan ganin yanda yayi wurgi da Baiwar Allah yasa ya zuciyo Bai san lokacin da yakai wa Uncle Deen naushi a saitin lips ɗinsa ba..... Razhdeen hannu yasa ya kama bakinsa idonsa akan Roshan cike da mamaki yake binsa da kallo, tin suna yara basu taɓa samun matsala har takai da duka ba, kuma Bai taɓa ganin Roshan yayi faɗa da kowa ba sai yau akan mace, abun ya sosa wa Uncle Deen rai yayi niyar yakai wa Roshan naushin da saita sume a waran amma lokaci guda zuciyarsa ta sauƙo saboda sonda yake yiwa ɗan uwan nashin bazai iya cutar dashi ba, Amma sai dai yayi niyar masa hukunci ɗaya shine bazai bashi Baiwar Allah ba tinda har ya gano itace rauninsa kuma har zai iya ɗaukar hannu ya naushe shi saboda ita, Kafin Roshan ya motsa ya nufi yanda Baiwar Allah take tinin Uncle Deen har yaje ya ɗauketa da hannu ɗaya ya wuce da ita bedroom ɗinsa sannan yasa key ta ciki ya kulle... Dasauri Roshan ya nufi bedroom ɗin tura ƙofar yayi yaga har ansa key, kamar zaiyi hauka haka ya ringa buga ƙofar da ƙarfin gaske........ 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 39 to 40 ꧁꧂ Tsararren masarauta mai cike da ƙayatattun kayan alatu wanda fadawa ne da kuyange suke ta faman zarya a cikin masarautar, Sarkin ƙasar Jidder wato mai martaba Abubakar Al-Saddiq yana zaune a katafaren kujerarsa na alhurma da wasu manyan mutane dattawa su biyar suma suna Zazzaune akan kujerun fadar, da duk kan alamu suna tattaunawa ne akan wani abu mai muhimmanci, wata matashiyar yarinya ce ta shugo da sallama a bakinta tana riƙe da tray a hannunta wanda aka jejjera kayan fruits aciki dasu lemuka sai wasu ƙananun glass cups waɗanda za'a tsiyayi juice a ciki, ajiye tray ɗin tayi akan table wanda yake tsakiyar falon fadar, saida ta gaggaishe su kafin ko wanne ta kai masa abun maƙulashe saitin gabansa, tana kammalawa ta miƙe zata koma ciki taji wani daga cikinsu ya ce "sannunki da ƙoƙari...." juyowa tayi ta kalle shi sannan ta ce "Nagode Baba...." haɗe rai mutumin yayi jin ta ƙirashi da Baba kuma har cikin zuciyarsa yarinyar ta burge shi, kafin ya ɗago kai ya kalleta har ta fice... Mai Martaba ne ya kalle shi sannan ya ce "lafiya kuwa Alhaji Ahmed? naga lokaci guda ka sauya...." Murmushi Alhaji Ahmed yayi sannan ya ce "Mai martaba shin wannan yarinyar ɗiyarka ce? Amma kuma naga kai tin ɗiyar daka haifa aka rasata baka sake haihuwa ba, shine abun yake bani mamaki kuma gata yarinyar batayi kama da Baiwa ba...." Dogon numfashi Mai martaba yaja tare da jinjina kansa ya ce "hakkun Alhaji Ahmed abinda ka faɗa gaskiya ne, ita wannan yarinyar Ƙanwar matata ce ta farko wato Hajia Mamy, tin yarinyar tana ƴar shekara biyar ta ɗaukota take riƙe da ita har zuwa girmanta, kun dai san Mamy bata taɓa haihuwa ba, ita kuma matata ta biyu A'isha itace ta haifa mun ɗiya mace wato Reemah wacce har ilah yau bamu sake jin labarin ta ba tin tana jaririya yau kimanin shekaru sha biyar ana shirin shiga ta sha shida....." wani daga cikinsu ne yayi magana wato Alhaji Hamza idonsa akan Mai martaba ya ce "Allah sarki shin tana raye ne ko ta mutu Allahu a'alamu, idan har tana raye Allah ka bayyanar mana da Reemah, idan kuma ta mutu Allah yasa mai ceto ce a ranar alƙiyama....." Duk suka amsa da Ameen... Alhaji Ahmed bayan yayi jimm kaɗan ɗagowa yayi tareda faɗin "Ni kuwa Mai martaba idan za'a bani dama inaso na fara neman yarinyar nan wallahi, ta burgeni sosai....." Duk sauran mutane huɗu da suka rage ne suka haɗe masa baki da cewar "yanzu kai Alhaji Ahmed ina zaka kai wannan yarinyar da shekarunka, matanka biyu, yara takwas ɗaya tana gidan mijinta harda jikanka....." Alhaji Ahmed cike da mamaki yake binsu da kallo ya ce "yanzu fisabilillah saboda Allah ya bani waɗannan sai akace karna ƙara Aure? namiji fah an bashi damar Auran mata huɗu...." Suka ce "ehh amma saika nemi dai-dai dakai ba yarinya ba, domin mun tabbata bazata yadda taje kan ta uku ba...." Cikin fusata Alhaji Ahmed ya ce "toh Ni yarinya nake son Aura...." Suka ce "toh Allah ya temaka ya bada Sa'a ...." Ya ce "Ameen..." Tareda fuskantar Mai martaba wanda ya tsaya yana sauraron su, Ya kuma cewa "mai martaba inason jin daga bakinka akan manufata, Ni nayi alƙawari indai za'a bani yarinyar toh zan tsara mata gidanta da ban ta wataya ita kaɗai babu wani takura....." Mai martaba ya ce "duk naji batunka Alhaji Ahmed, yanzu dai babu abinda zan iya cewa akan al'amarin nan domin bani zan zauna dakai ba, ita yarinyar da zata zauna dakai kaje ka fara tuntuɓar ta idan ta amince Ni bani da wata matsala....." Alhaji Ahmed jikinsa ne yayi sanyi domin yana ji ajikinsa za'a samu matsala daga wajen yarinyar tinda har ta ƙira shi da Baba! Murya a sanyaye ya ce "amma mai martaba nake ga idan har kai kayi mata magana zata fi ɗaukar mahimmanci maganar har ta amince mun, naga yarinyar tanada tarbiyya tana jin maganarka sosai....." Jinjina kai mai martaba yayi yana maganar zuci cewar "Uhmmm! Rashin sani yafi dare duhu, amma inda kasan halin Matata Mamy da kuma Ƙanwarta Ramlat da bakayi gaggawar furta cewar yarinyar tanada tarbiyya ba...." Jin Alhaji Ahmed ya katse shi da cewa "yadai mai martaba?...." yasa yayi firgit tareda faɗin "shikenam zan samu Ƴar uwarta Babbar Matata muyi magana da ita, idan har ita ta amince toh komai zai dai-daita kai dai kayi addu'a...." Alhaji Ahmed yayi masa godiya cikin girmamawa daga baya sukayi sallama da mai martaba duk suka tafi, ko wannen su da zugegiyar motarsa yake tafe babu talaka a cikinsu, asalin manya-manyan masu kuɗi ne, shima mai martaba barin cikin falon yayi ya shige cikin gidan...... Shiga cikin wani katafaren ƙaton falo yayi wanda ya tsaru sosai da kujeru, Part biyu ne acikin falon wanda saika hau saman beni kafin ka shige room ɗin matan gidan, kai tsaye part ɗin da yake ɓangaren dama mai martaba ya nufa, saida ya haura upstairs sannan ya shige room ɗin Hajia Mamy ya tarar da ita tana zaune a bakin gadonta sai faman danne-danne take a waya, tasha makeup sosai tana sanye da less a jikinta, Kana ganinta kasan tana shan hutu sosai tayi wani irin ƙiba, ta ko ina a cike yake babu rama, Baƙa ce amma tana da kyan ta, Sallama yayi mata kafin ya samu guri ya zauna dab da ita idonsa akanta, cikin fara'a ya ce "Uwar gida bakya laifi...." Juyowa tayi ta kalle shi tana yamutsa fuska ta ce "bana laifi kuma? Sai dai kaje ka yabe Amaryarka acan ɓangaren ta ...." Murmushi Mai martaba yayi sannan ya ce "ke matsala dake kenam ba halin kiyi wasa da mijinki..." Mamy tana ɗaga kafaɗu ta ce "taya zanyi wasa dakai wannan ai sai Amarya, Ni kuma kaga ba Amarya ba ce....." Dogon numfashi yaja tareda cewa "shikenam, yanzu dai ba wannan ba akwai maganar da nake so nayi dake akan Ramlat, Daman wani Aboki nane ya ganta ya ce yana so shine........" kafin ya ƙarasa maganar tayi saurin katse shi da cewa "meeeee? wa kenam?....." Ya ce "ha'a meye abun firgita kuma? Alhaji Ahmed ne ...," Miƙewa tayi tsaye tareda kama kunkumi ta ce "impossible wallahi, wannan dattijon zata Aura? hakan ma itace ta uku? wallahi mai martaba baka son mu da alkhairi haba dallah......" Kallonta yayi ya ce "toh yanzun ya kike so ayi?...." Saida ta wani juyar da idanuwanta tana gatsine ta ce "idan har kana son mu da alkhairi kuma kana sona da gaske inhar kanason haɗa jinsi dani toh ya zama dole ka Aurar mun da Ramlat a Razhdeen, Domin mun gama maganan nan cewa zaka ƙira Yayanka a waya ka sanar masa cewar ka bayar da Ramlat wa Ɗansa Razhdeen, idan kuma baka ɗauki Ramlat a matsayin ƴa ba shikenam....." Mai martaba gaba ɗaya ya rasa yanda zai yi akan wannan batun shi kuma fargaban ƙiran Yayansa yake akan maganar bayan haka yasan halin Razhdeen ba Amincewa zaiyi ba, Hura iskar bakinsa yayi sannan ya ce "Amma Mamy kin dai san halin Razhdeen, ba irin mutanen nan ne masu sauƙin kai ba! ba lallai ya yadda ba ina laifin kice Roshan amma Razhdeeeeen kaiiiiii ......" tinin harya haɗa gumi domin lamarin Razhdeen sai Allah amma Mamy ta kasa ganewa ita burinta ta haɗa Ramlat da Razhdeen, yana cikin nazari yaji ta fashe masa da kuka tana faɗin "saboda ban taɓa haihuwa ba shine komai na roƙa ba'a yarje mun, yanzu fisabilillah so nake na haɗa jinsi da ahalinku sakamakon bana haihuwa amma furr kaƙi yadda ......" Mai martaba ya ce "kina ji ba, bawai nine ban yadda ba sannan ba Yayana bane bai yadda ba shi kanshi Razhdeen ɗin ne bazai yadda ba....." A tsawace ta ce "toh baza ku saka shi dole ba? ku ba iyayensa bane? dole idan kuka tsayar masa zai amince....." Ya ce "Uhmmm! Mammy kenam Razhdeen ba yanda kike tunani bane shi, meyasa bazaki zaɓi Roshan ba sai Razhdeen wanda yafi ƙarfin ai masa dole, Ai yanzu Mace ma ba'a mata dole balle namiji....." Gaba ɗaya Mamy ta kasa fahimtar shi sai faman zuba masifa take, ganin bazai iya jurewa ba yasa ya tashi zai fice a room ɗin...... Duk tattaunawar da sukayi Ramlat tana tsaye a bakin ƙofa tana jinsu, jin mai martaba yana shirin fitowa yasa tayi saurin tura ƙofa zata shiga da sallama a bakinta dai-dai lokacin da zai fito shi kuma, Cikin ɓacin rai ya wuce yayi tafiyarsa, Ramlat ce ta ƙarisa gurin Mamy tana faɗin "wai ke Mammy meye damuwarki da dole saina Auri Uncle Deen? Na gaya miki Ni Yaya Roshan nake so, inasonsa sosai har cikin zuciyata....." Mammy ta ce "ke Dallah rufe mun baki, ai ke mahaukaciya ce shiyasa baki san rayuwa ba, Meye Roshan yake dashi?....." Ramlat ta ce "a'ahhhh ai kuwa Mamy bazaki ce Roshan ba kyakkyawa bane....." Mammy ta ce "Shashasha rufe mun baki, wani kyau kuma? Ai kuɗaɗe sune kyau, duk wanda yafi kuɗi toh shine kyakkyawa, Toh bari kiji na gaya miki Roshan ko kamo ƙafar Razhdeen baiyi ba a yawan kuɗaɗe, Ke kinsan adadin yawan motocin Razhdeen kuwa? kinsan adadin yawan gidajensa a nan Nigeria kuwa? kinsan adadin yawan gidajensa a ƙasar Australia kuwa? kinsan adadin yawan jirgayensa kuwa? kinsan adadin yawan gwalagwalen da yake dasu kuwa? kinsan adadin yawan dalolin da yake dasu kuwa? kinsan adadin yawan Nairorin da yake dasu kuwa? Bugu da ƙari ga kyau ga ƙiran sura mai kyau, wallahi kin more yarinya idan kika Auri Razhdeen, Shi Roshan bai kai Razhdeen dukiya ba, toh bari in taƙaice miki ko Ni Razhdeen yazo yace zai Aure Ni a halin yanzu toh wallahi da gudu zan kashe Aurena na Aure shi......" Zaro ido waje Ramlat tayi sannan ta ce "Mamy kina Auran Baffansa kuma kice zaki Aure shi? ai babu Aure a tsakanin ku tinda mai martaba kamar mahaifi yake a gurinsa ...." Mamy tana turɓune fuska ta ce "yooo ina ruwana da wani tsarin addini, Ni kuɗi kawai na sani, ke wawuya Arziƙi na bin mu da gudu ke kuma kina ƙoƙarin kaucewa, inaso ki Auri Razhdeen mu ci Arziƙi mubar Arziƙi, Mu tashi a cikin dukiya, mu ci dukiya, mu sha dukiya, mu kwanta a cikin dukiya, mu mutu acikin dukiya....." Jinjina kai Ramlat tayi ta ce "ai kuwa Mamy yanzu ma baza kice a cikin talauci kike ba, tinda a koda yaushe bakya rasa kuɗaɗe manya-manya....." Mamy ta ce "shuru dallah, bakya son mu cigaba ne?...." Ramlat ta ce "shikenam Mammy ya wuce...." Mamy ta ce "atoh ko naji dai....." Mai martaba bayan ya fita a ɗakin Mamy kai tsaye part ɗin A'ishansa ya wuce, yana shiga ya tarar da ita sai faman goge jeren kumbon ta take irin na sarakuna masu kyan gaske da sheƙi, Sallama yayi mata tareda faɗin "kaga manyan mata Ƴar gidan sarki, jikar sarki, matar sarki! Amarya kenam Maman Reematu....." Ɗagowa tayi da murmushi kan fuskarta ta ce "sannu da shugowa mai martaba, duk wannan yabon a Ni kaɗai?...." Ya ce "kin cancanci hakan ne shiyasa...." Ta ce "godiya nake mai martaba....." Jinjina kai yayi yana kallonta cike da ƙauna ya ce "kiyi haƙuri yau ranar ki ce amma na shiga ɓangaren Mamy akan wani batu...." Ta ce "Tabb lallai mai martaba yanzu akan hakan ne sai an bani haƙuri? babu komai wallahi ...." Yaja dogon numfashi tareda faɗin "Allah ya miki Albarka....." ta amsa cikin girmamawa ...... lokaci guda fuskarta ta sauya kamar zatayi kuka ta cigaba da goge kumbonta, riƙe hannunta mai martaba yayi tareda juyo da ita suna fuskantar juna ya ce "meya faru dake Sarauniya?...." ta ɗan sau murmushi ta ce "banaso na rinƙa ɓoye maka abu maganar gaskiya idan ana ambato mun sunan Reemah gaba ɗaya kaina juyawa yake, sai na rinƙa jin bugun zuciyata yana ƙaruwa, inaji a jikina cewa Ɗiyata Reemah tana nan a raye domin inajin motsinta acikin zuciyata, Bugu da ƙari ma tin daga kanta ban ƙara samun haihuwa ba, abun yana damu na a raina......" Shima mai martaba ya damu sosai ganinta acikin wannan halin ya ce "ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zai dai-daita, kamar yanda kike tunanin cewar Reemah tana raye insha Allahu zata bayyano, ki cigaba da addu'a kinji...." kai kawai ta ɗaga masa ...... ✍️✍️✍️ Roshan yayi iya ƙoƙarinsa ganin ƙofar bedroom ɗin Uncle Deen ya ɓallu amma babu alamu, yayi bugawar har ya gaji, yana hawaye haka yabar ɗakin kai tsaye falo ya sauƙa ya nemi kujera ɗaya ya zauna tareda dafe goshinsa da hannaye biyu yana zubar da hawaye, zuciyarsa ce take wani irin tafasa wanda tinda yake bai taɓa shiga yanayi irin na yau ba, Shi kuwa Uncle Deen kwantar da Baiwar Allah yayi kan gadonsa shima ya nemi kujera ya zauna ta gefen gadon, yana jin yanda Roshan yake buga ƙofar amma ko motsi baiyi ba, yana mamakin yanda Roshan zai iya ɗaukan hannu ya buge shi, yana ji a ransa cewa inda wani ne daban yayi mishi haka da za'a zo a ɗauki gawarsa ne..... suna wannan halin har suka wuni a haka zuwa yamma dai-dai lokacin dawowar sauran mutanen gidan daga gurin aiki, Roshan yana zaune a falo sallah ma a falo yayi shi, yana zaune kan sallayar Ummy data kawo masa, ita kuwa tana gefensa sai faman rarrashinsa take, ganin yanda idanuwansa sukayi jawur tsabar kuka yasa Ummy itama ta fashe da kuka, A ranar yau babu wanda ya shiga kitchen domin girka abinci, Pinky da Rukky daman suma tin kafin a fara wannan al'amarin suka fita zasu je ziyara old school ɗinsu, Hajiya Kilishi ce ta fara shugowa daman yanzu da wuri take dawowa gida, Ganin Roshan a tsakiyar falo akan sallaya yasa gabanta yankewa a tsorace ta ce "waye ya mutu a cikin yarana?....." Roshan kasa yin magana yayi sai Ummy ce ta ɗago tana kuka ta ce "ba mutuwa akayi ba, matsala suka samu shi da Uncle Deen....." Hajia Kilishi zaro Ido tayi cikin yanayin farin ciki yau kamar anyi mata bishara da gidan Aljanna, acikin ranta ta ce "wonderful, wannan kyakkyawan albishir haka....." harararsa tayi sannan ta ce "Allah ya sawwaƙe toh...." ba tareda ta tambayi dalili ba tayi wucewar ta dasauri ta haura upstairs...... Bayan wasu mintuna saiga Pinky da Rukky suma sun dawo suna ƴar hirarsu ganin abun mamaki yasa suka tsaya baki a wangane Pinky ta ce "Yaya Roshan lafiya kuwa, kuka fa kake yi? wannan wani irin mummunar rana ce haka?....." Rukky cike da mamaki ta ce "tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin fushi matuƙa a fuskar Yaya Roshan ba balle Kuka innalillahi wa inna'ilaihi raju'un......" Ummy tana jinsu bata kulasu ba kanta a ɗore kan kafaɗar Roshan, suma ƙarasowa sukayi gurinsa suka zazzauna suna fuskantar sa kafin kace mai suma sun fara hawaye, Suna cikin wannan halin saiga Ƴar Tiny ta dawo daga school tana goye da jakarta hannunta kuma yana riƙe da lunch bag ta shugo tana tsallenta, Ganinsu yasa ta nufi yanda suke da gudu ta faɗa saman cinyar Roshan tana faɗin "Yaya Yocan Oyoyo...." ɗagowar da zatayi taga fuskar Roshan yayi jawur tsabar kuka da ɓacin rai buɗe baki tayi tana kallonsa lokaci guda kuma ta fashe da kuka tana faɗin "Wayyo Ayyah nahhh Yaya Yocan yana kukaaaaa, Yaya Yocan meya came kaaaa ....." Ummy ce ta darara mata tsawa da cewa "ke Dallah rufe wa mutane baki, murya sai kace gyare ....." tashi tayi da gudu tana faɗin "bajanyi cuyu baaa kuma wayyayi tayyayi cena gaya wa mommy nahhh....." ta ƙarasa maganar tareda haurawa upstairs yanda part ɗin Hajia Kilishi yake, Itama Minal shugowa tayi ta same su a haka, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin Yaya Roshan acikin wannan halin, Ta tambaya akan meke faruwa Pinky ta ce "mu ma haka mukazo muka same su...." Ummy ta sani amma sai dai taƙi cewa komai bare shi kuwa bashi ma da bakin magana, zuciyarsa ce take ta faman harbawa da ƙarfin gaske, Turo ƙofa akayi da sallama a bakinsa ya shugo ganinsu a haka yasa Abbah firgicewa ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Allah yasa dai komai lafiya, amma da dukkan alamu ba lafiya ba....." Zama Abbah yayi akan kujera yana facing ɗin Roshan sai tambayarsa yake meke faruwa amma sam yaƙi cewa komai, Sai Ummy ce ta zayyanar masa da duk abubuwan da suka wakana dake a lokacin da abun ya faru tana bakin ƙofar Uncle Deen tana jin duk faɗan da sukayi....... Abbah ya ce "yanzun shi ɗin Razhdeen yana ciki shi da Dota?....." Ya tashi tareda haurawa saman upstairs ɗinsu kai tsaye part ɗin Uncle Deen ya nufa, Dasauri Roshan ya miƙe tareda bin bayan Abbah ko za'a dace, Minal jin akan Baiwar Allah ne duk wannan matsalar yasa taja dogon tsuka ta wuce part ɗinsu, Suma su Pinky cewa suke "yanzun akan Baiwar Allah muma mukayi kukan? tirrrrrr....." suma haura part ɗinsu sukayi domin abun bai dame su ba, Amma ta wani ɓangaren mamaki suke meya haɗa Roshan da Baiwar Allah kuma? meye alaƙar dake tsakaninsu har ta kai ga haka? waɗannan tambayoyin ne suke ta yawo akawunansu.... Abbah yana zuwa yasa hannu zai buɗe ƙofar falonsa yaji a ƙarƙame, Roshan cike da mamaki ya ce "wahatttt? nan ma ya kulle? me yake nufi da hakan? Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....." Ummy ta ce "Yaya Roshan ka kwantar da hankali Please banason ganin hawayen jarumin namiji ......" Abbah buga ƙofar ya shiga yi yana ƙiran sunansa: "Razhdeen! Razhdeen!! Razhdeen!!! kazo ka buɗe ƙofar nan tin kafin ranka ya ɓaci....." Haka shima Abbah yayi yayi har ya gaji amma Razhdeen bai zo ya buɗe ba, kuma yana kwance a doguwar kujerar falonsa ya miƙar da ƙafafu yana facing ceiling idanu a lumshe kamar mai yin Bacci amma sai dai ba Bacci yake ba, duk yana jin bugawar da ake ya sharar, ba ƙaramin ɓata masa rai Roshan yayi ba shiyasa gaba ɗaya zuciyarsa yake a hargutse...... Ita kuwa Baiwar Allah tana kwance a bedroom har zuwa wannan lokacin bata farfaɗo ba... Haka su Abbah suka haƙura suka koma falo har zuwa misalin ƙarfe 12 na dare, Abbah ba yanda baiyi da Roshan akan yaje ya kwanta a ɗakinsa amma yaƙi sai cewa yayi "Please Abbah zan zauna anan falo har zuwa Asuba nasan zai iya fitowa zuwa masallaci.... Abbah ya ce "shikenam Roshan mu zauna toh, domin bazan iya barinka anan ba cikin wannan halin, Ka kwantar da hankalinka kar kayi fushi da ɗan uwanka, kai ma dai kasan halinsa bai kamata ka biye masa ba...." Roshan kamar zaiyi kuka ya ce "toh Abbah ya zanyi? bazan iya juran ganin yana azabtar da ita ba, inasonta Abbah....." Jinjina kai Abbah yayi sannan ya ce "Uhmmm! Roshan kenam ai na sani daman, tin farkon dawowarku da yanda kake shishshige mata duk idanuwana akanku yake, duk wani motsin ku na sani, kayi haƙuri komai a hankali ake yinsa, duk abinda haƙuri bai baka ba toh rashinsa bazai baka ba ......" A haka suka kai har sallar asuba babu wanda ya rimtsa, a falo duk sukayi sallar asuba amma basuga fitowar Razhdeen ba, Shima Razhdeen acikin room ɗinsa yayi Sallah, yana zaune akan sallaya yaji motsin Baiwar Allah daga kan gadon sai faman juyi take, daƙer ta ɗan buɗe eyes ɗinta tana jero addu'o'i, Ganin yanda room ɗin yake chanza haske kala-kala yasa tayi saurin buɗe idanunta sosai domin tasan ɗakinta babu irin wannan fitillu haka daban daban, A razane ta tashi zaune tana faɗin "nashiga uku aina nake?...." Idonta ne suka sauƙa akan Uncle Deen wanda yake kan sallaya ko kallonta baiyi ba, A ruɗe ta ɗora hannu akai ta rausa wani irin uban ihu idanu kamar zasu faɗo.... Dasauri ya juyo yana kallonta cikin ɓacin rai, wani irin tsawa ya daka mata agigice ta haɗiye ihun tana jan numfashi da ƙarfi.... A ruɗe Abbah da Roshan suka miƙe tsaye daga kan sallaya jin ihun Baiwar Allah, Da gudun gaske Roshan ya nufi upstairs kai tsaye part ɗin Razhdeen ya nufa, shima Abbah bayansa ya biyo, jin har yanzu ba'a buɗe ƙofar ɗakin ba yasa Roshan fashewa da kuka yana faɗin "Shikenam Abbah ya kasheni ya gama da rayuwata, daman nasan babu yanda za'ayi su kwana ɗaki ɗaya bai mata wani abu ba, Abbah Razhdeen ya cuceni sannan ya cuceta na tsane shi Abbah, I hate him! I hate him!! I hate him!!! ......" Barin wajen yayi yana kuka ya nufi room ɗinsa shima, Abbah tsabar takaici bai iya cewa komai ba, sai hannu yasa ya dafa jikin bango Kai a sunkuye sai faman girgiza shi yake....... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 41 to 42 ꧁꧂ Kwance yake a falo kan 3 seater ya ɗora hannu akan goshinsa ido a lumshe kamar meyin Bacci, Ita kuma Baiwar Allah tana bedroom yanda ya baro ta sai faman rera kuka take akan sallaya yanda ta idar da sallar asuba bata tashi ba har zuwa yanzu misalin ƙarfe 9 na safe, Saida ta gama kukanta ta share tukun ta tashi ta nufi falo, a tunaninta Uncle Deen ya fita sai kuma ta tarar da shi akan sopa, ganinsa yasa gabanta yankewa, ta juma tana tsaye idonta akansa wanda ko motsi bayayi alamun yayi nisa a cikin baccinsa, Kallon bakin ƙofa tayi nan ta fara taku a hankali ta nufi bakin ƙofa zata fice, cikin rashin sa'a tana isa ta riski ansa key a ƙofar, cikin ɓacin rai haka ta juyo tana kallon Uncle Deen kamar zata rausa ihu, zamewa tayi ƙasi ta zauna a bakin ƙofar tareda kifar da kanta kan gwiwa ta cigaba da rera sabon kuka.... kamar a mafarki yake jin ƙinƙishin kuka a hankali yake mutsil-mutsil da eyes ɗinsa har ya iddasa buɗesu gaba ɗaya, kallon yanda take zaune yayi daga bisani yaja dogon tsuka saboda hakane yasa yabar mata can bedroom ɗin amma saboda nashi ta biyo shi nan ma, tashi yayi tareda miƙewa tsaye ya nufi waran frig ya buɗe sannan ya kalli yanda Baiwar Allah take a zaune fuska a haɗe ya ce "ke! tashi ki miƙo mun tray ɗin kan dinning can ...." Tayi kamar bata ji shi ba kai a kife, saida yayi mata wani gigitaccen tsawa tareda faɗin "Ba magana nake miki ba?...." A tsorace ta ɗago jiki na ɓari ta tashi ta nufi dinning ta ɗauko tray sannan ta kawo masa, Hannu yasa ya karɓa sannan ya fara jido kayan fruits yana jejjerawa akan tray ɗin tare da Cake 🍰 da juice, ya rufe frig sannan yaje ya ajiye akan dinning, ya kalli yanda take a tsaye Ya ce "ki zo Nam...." Juyowa tayi ta nufi dinning itama yasa hannu ya gyara zaman kujerar tareda faɗin "zauna ga kayan breakfast....." Girgiza Kai tayi tareda cewa "a'a na ƙoshi...." Cikin ɓacin rai yake kallonta ya ce "kin san idan na fara dukan ki acikin ɗakin nan bamai ƙwatarki Koh?....." Kamar zata fashe da kuka fuska ba annuri ta zauna tareda saka tray a gaba nan ta fara ɗaukan kayan fruits ɗaya bayan ɗaya tana ci, kuma daman da matsanancin yunwa ta tashi.... Shima zama yayi tareda kifar da kansa akan table ya zura dogin yatsunsa acikin sumar kansa yana caccakuɗa shi, alamun yana cikin damuwa over.... Baiwar Allah duk tana kallonsa amma sai dai ko a jikinta Ita dai tana cika cikinta ne.... Roshan gaba ɗaya ya rasa mai yake masa ciwo ajiki, abinda Razhdeen yayi masa sam baiji daɗin hakan ba, ya kasa zama guri ɗaya sai zarya yake acikin room ɗinsa, yana cikin wannan halin saiga Ummy ta shugo da sallama a bakinta tana riƙe da tray ɗin kayan breakfast, ajiye masa tayi a ƙasin bed ɗinsa domin a halin da yake ciki bazai iya zama a dinning ba, Ummy ce ta tsaya a gabansa tareda faɗin "Dan Allah Yaya Roshan ka daina shiga damuwa haka, tinda har ba saceta akayi ba tana nan acikin gidan ai zata fito ....." yana zubda ƙwallah ya ce "Uhmmm! Sau ɗaya naji ihunta ya daki dodon kunnena daga lokacin ban sake jin motsinta ba, Bansan me yayi mata ba...." Ummy cikin nuna damuwa ta ce "Yaya Roshan ka kwantar da hankalinka babu abinda ya faru, nasan Uncle Deen bazai taɓa aikata wani mummunan abu ba, inaso ka kyautata masa zato...." Idonsa akan Ummy ya ce "shikenam insha Allahu...." Ta ce "toh zauna muci abinci yau tare na sako mana saboda nasan idan kai ɗaya ne baza ci ba ....." Murmushi yayi sannan ya zauna, Ummy ta fara zuba musu a plate ɗaya tareda two spoon, tana jansa da hira suna ci cikin kulawa..... Abbah shima lamarin Razhdeen ya yi matuƙar bashi mamaki da kuma haushi, tinda yake da Razhdeen bai taɓa ɓata masa rai irin ta yau ba... ☾D☽☾A☽☾Y☽ - 5 ࿙R࿚࿙A࿚࿙Z࿚࿙H࿚࿙D࿚࿙E࿚࿙E࿚࿙N࿚🤦‍♀️🤦‍♀️🤦‍♀️ A kwana a tashi yau kwana biyar kenam Razhdeen bai buɗe ɗakinsa ba, Yana zaune a falo kan sopa sai danna computer sa yake hankali kwance, Baiwar Allah ce ta fito daga bedroom ɗinsa tana sanye da baƙar jallabiyarsa yanda tayi wanka ya bata akan ta sanya domin kayan jikinta sunyi datti, zuwa tayi ta durƙusa a gabansa kanta a ƙasi ta ce "Dan Allah Uncle kayi haƙuri nasan nayi maka laifi amma hukuncin nan daka ɗaukar mun yayi tsauri da yawa, na roƙe ka da girman Allah ka buɗe mun ƙofa nabar ɗakin nan, inason ganawa da Mutanen gidan, bansan me zasu yi tunani akan mu ba, kodan saboda Abbah ka temaka wannan ba ɗabi'ar ɗan musulmi bane mahaifinka na ganinka amma kana zaune da macen da ba muharraminka ba acikin ɗakin........." Bata ƙarasa maganar ba taji da daka mata tsawa da cewar "Enough! U are very stupid, saboda Kinga na sake miki kwana biyu shine zaki nemi ki raina Ni?....." Baiwar Allah tana hawaye ta ce "ba haka bane Uncle amma mutanen gidan zasu wani irin bahagon tunani akan mu yau kwana biyar muna ɗaki....." Ɗaga mata hannu yayi alamar ta dakata haka tareda yi mata wani irin kallon ƙasƙanci ya ce "wani irin tunani? akan mu? Uhmmm! Bari kiji yarinya Ni Razhdeen nafi ƙarfin nayi tarayya dake kowa ma yasan da haka saboda kinyi mun ƙanƙantar da bana ɗaukar ki a matsayin ƴa mace, Kada ki sake yin irin wannan tunanin na gaya miki....." Cikin ɓacin rai take kallonsa ta ce "koda banyi tunanin nan ba amma sauran mutanen zasu yi...." Ya ce "Wait! bana son sa'insa saboda Ni nafi ƙarfin tunaninki, ki tashi ki koma bedroom na bar miki can karna sake ganin ƙafarki a yanda nake...." idonta akansa tana huce ta miƙe tsaye ta ce "Wallahi Uncle babu yanda zanje Ni kuma yau kwanana na ƙarshe kenam a ɗakinka domin bazaiyu ka zubar mun da mutunci ba....." Ɗagowa yayi yana kallonta cike da mamaki daƙer ya iya furta "Ni kike gayawa maganganun nan?..." Kawar da kanta gefe tayi ko kula shi batayi ba, tsabar takaici bai ƙara ce mata komai ba haka ya cigaba da pressing ɗin computer, ganin ya cigaba da abinda yake yi yasa ta juya ta nufi bakin ƙafa tasa hannu tana bubbuga ƙofar da ƙarfin gaske tana magana da ƙarfi cewar "Dan Allah Azo a temake Ni, jama'a temakoooo....." waiwayawar da zata taga mutum sangangam a bayanta yana tsaye ya goya hannayensa kan ƙirjinsa idonsa akanta, Saida ƙirjinta ya buga ganin shi a haka, itama tsayawa tayi tana kallonsa idonta har ya cicciko da hawaye, hannunsa ya ware yana nuna mata hanya da cewar "zo ki wuce ciki....." sunkuyar da kanta tayi ƙasi tana ƙoƙarin share hawaye, Ya kuma cewa "magana nake miki..." still kanta a ƙasi ko ɗagowa batayi ba balle tasan da ita yake, bata ankara ba taji ya saɓata akan kafaɗarsa yayi cikin bedroom da ita, ƙoƙarin zamowa take tana tutture shi, a garin ajiye ta a kan gado ta harɗe musu ƙafafu a garin ƙwacewa, cikin rashin sa'a ya kifu a kanta duk suka doku akan gadon, ɗan ƙara tasau jin nauyinsa akanta, gagara tashi yayi sakamakon rasa ƙwarin jikinsa, gaba ɗaya ta kashe masa jiki, tinda ya kifar da kansa akan ƙirjinta bai ƙara motsawa ba, sumar kansa gaba ɗaya ya rufe mata fuska saida suka ɗau tsawon mintuna a haka kafin daga bisani ta ɗan fara motsawa tana ƙoƙarin ture shi, sai a lokacin shima ya ankara bai san lokacin da yayi saurin sauƙa daga kanta ba yana fitar da numfashi sama-sama, kansa ne yake wani irin sarawa tinin gumi har ya wanke masa duk ilahirin jikinsa, a gigice ya yi saurin faɗawa bathroom domin sam baya juran zafi duk da sanyin A.C dake ɗakin, shi kansa bai san dalilin shigarsa cikin wannan yanayin ba, domin bai taɓa shiga wannan yanayin ba sai yau, Ita kuma Baiwar Allah tana nan a yanda take ko motsawa batayi ba ta ƙanƙame idonta kunya ne ya lulluɓeta.... ࿙R࿚࿙O࿚࿙S࿚࿙H࿚࿙A࿚࿙N࿚. A hankali yake sauƙowa daga upstairs kamar zai kife, hannunsa yana ɗore akan saitin zuciyarsa, daƙer ya sauƙo falo wani irin hajijiya ne ya ɗebe shi yayi baya luuu zai faɗi dai-dai lokacin da Abbah ya sauƙo shima daga upstairs ɗinsa, da gudu Abbah yayo kansa yayi saurin riƙo shi tareda manna shi a jikinsa yana faɗin "Roshan! Roshan!! Roshan!!! kana lafiya kuwa?...." Shi kuwa Roshan ba abinda yake faɗin illah "Abbah zuciyata zata fashe Abbah, Abbah tafasa take zato fashe, ka temaka mun Abbah zan mutu, zan mutuuu......" ya ƙarasa maganar tareda fashewa da matsanancin kuka hannunsa akan ƙirji, shi kaɗai yasan halin da yake ciki, kafin Abbah ya ankara har ya fara Aman jini, ɗayan hannun yasa yana toshe bakinsa kar jinin ya fito amma inaa abun yaci tira hannu duk ya ɓaci da jini, shima Abbah gaba ɗaya ya ɓata masa kaya da jini, Gaba ɗaya Abbah ne ya fita hayyacinsa ganin halin da Roshan ke ciki, gaba ɗaya ya rasa ta yanda zai fara temaka masa shima Abbah kawai ya fashe da kuka, daƙer ya samu ya lalumi wayarsa a aljihu ya ciro yayi dialing call number security gidan, Ga mutanen gidan basa nan iya Ummy ce take room ɗinsu bata san wainar da ake toyawa ba, Sojoji ne suka shugo kusan su biyar kai tsaye nufan wajen da Abbah yake riƙe dashi sukayi, su biyu suka ɗauki Roshan Abbah yana biye dasu a baya, haka suka nufi hospital.... A ranar a hospital suka kwana Abba ne yake zaune agurin Roshan sai Sojojin da akazo dasu, A washe gari duk mutan gidan suma suka yo hospital har da uwar gayyar wato Hajia Kilishi.... Razhdeen kuwa duk halinda ake ciki bai sani ba, ga yayi switch up ɗin wayarsa balle a ƙira shi a sanar masa, yana zaune a falo kamar yanda ya saba yana dafe da goshinsa haka kawai yake jin gabansa yana yankewa wanda bai san dalilin hakan ba, Ƙirjinsa ne yake bugawa da ƙarfin gaske ga kansa yanda yake sarawa da duk kan alamun akwai mummunan abinda yake shirin faruwa dashi, yana cikin wannan halin yaji ƙarar ihun Baiwar Allah daga ciki, a ɗan ruɗe ya ɗago da kansa yana juyar da eyes ɗinsa waɗanda suka faffaɗa suka rame, hatta fuskarsa ma ta ɗan rame, sake jin ihun yayi a karo na biyu a hanzarce ya miƙe tsaye tareda nufan bedroom ganin bata ciki yasa yakai eyes ɗinsa bakin ƙofar bathroom, a karo na uku ya sake jin ihun ya daki dodon kunnensa, zuwa bakin ƙofar yayi yasa hannu zai buɗe, yaɗan dakata yana fargaban shiga gudun kar ya tarar da ita acikin wani hali amma jin nishinta da ƙarfi yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin ya shige, ganinta yayi a ƙasi tana kwance shame-shame tana riƙe da cikinta sai murtsukuku take tana juyi tareda fitar da nishi da ƙarfi-ƙarfi, Daga ita sai towel kawai a jikinta, haka yake binta da kallo cike da mamakin abinda ya sameta, idanuwansa ne suka sauƙa akan jinin da ya ɓata tiles ɗin toilet, jini ne yake bin ƙafarta yana gangarowa daga ƙasinta, zaro ido yayi yana Binta da kallo a ruɗe ya nufi kanta, hannu ɗaya yasa ya ɗagota ganin bazata iya tsayuwa ba yasa ya mannata ajikinsa, Zagayo da hannayenta tayi ta bayansa ta ƙanƙame shi sosai jikinta na kakkarwa tana kuka tareda faɗin "Cikina ciwo, marata ciwo dan Allah ka temaka mun zan mutu, bazan iya cigaba da rayuwa ba ciki nahhhh, Marataaaa....." nan itama ta fashe da kuka, gaba ɗaya ya rasa yanda zaiyi da ita, ga duk ta ɓata towel ɗin da jini dake farin towel ne, wani dabara ne ya faɗo masa nan ya yi mata ɗaukar luɗa ya zaunar da ita acikin farin baho na wanka yasa hannu ya zamar mata da towel jikinta idonsa a lumshe domin baya ƙaunar ganin tsaraicin mutum, da sauri ya waiwaya bayansa bayan ya kunna mata ruwan fanfo mai ɗumi-ɗumi, juyawa yayi ya fice daga cikin toilet ɗin ya nufi wardrobe ya ciro new towel baƙi sannan ya koma cikin bathroom idonsa a lumshe, da haka ya gyarata ya temaka mata tayi wanka sannan ya ɗagota tareda ɗaura mata towel ya ɗagota ya saɓata kan kafaɗarsa yayi bedroom da ita, duk wannan ɗawainiyar a makance yayi mata ko sau ɗaya bai yadda ya buɗe eyes ɗinsa ya kalleta ba, Itama kallonsa take duk da wahalar da take sha amma bai hanata yin mamakin ƙarfin hali irin na Razhdeen ba, Bayan ya fita da ita zaunar da ita yayi akan kujerar bedroom wanda yake beside bed, A hankali ya buɗe idonsa sai kyawawan eyes ɗinsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar Baiwar Allah wanda itama kallonsa take, nan suka fara kallon juna, sun ɗau tsawon minti biyar a haka daga bisani ya fara motsa lips ɗinsa a hankali ya ce "Are you okay?...." ɗaga masa kai tayi ba tareda tace komai ba, Ya ce "ok! kina period ne?...." ɗaga masa kai ta kuma yi... Ya kuma cewa "daman haka kike idan zakiyi period?....." Dasauri ta ɗaga masa kai alamun ey...." Jinjina kai yayi sannan ya ce "akwai maganin ciwon cikin da zan baki kisha yanzu insha Allahu bazaki ƙara shan wahala ba dazaran zakiyi period....." Kallonsa kawai take ba tareda ta ce komai ba, Ya tashi a hankali ya nufi drawer mirror ya buɗe gida na tsakiya ya ɗauko wani magani ƙananu acikin ƙwalinsa, buɗe guda biyu yayi sannan ya ɗauki gorar faro yazo gabanta ya durƙusa sannan ya miƙa mata maganin, Hannu tasa ta karɓa sannan ta jefa a baki ta kafa gorar ruwan tasha.... tashi yayi yana faɗin "wait for me...." ya nufi falo kai tsaye bakin ƙofa ya nufa yasa key ya buɗe ya fice, domin yasan babu kowa a gidan, yana jin fitar su da motar amma baiyi tunanin wata matsala bane........ 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 43 to 44 ꧁꧂ A hankali yake sauƙa down stairs ganin babban falo wayam ba kowa yasa kai tsaye ya miƙi room ɗin Baiwar Allah, (Ohh Ni kuwa na ce daman Razhdeen yasan ɗakin Baiwar Allah 🤔🤔🤔) Shiga yayi ya nufi wardrobe ɗinta ya fara dube-duben abinda yazo nema, cikin sa'a kuwa yana buɗe wardrobe ɗin ƙasa ya tarar da jerin pants da ledojin pad, ya ɗauki pant guda uku da ledar pad guda ɗaya domin bazai iya tsaya farkewa ba, yana ɗauka ya yi saurin ficewa ya nufi upstairs zai koma part ɗinsa gudun kar a kama shi domin yana mungun fargaban haɗuwa da Abbah, Bayan ya koma room ɗinsa key yasa a ƙofar ya koma bedroom ya tarar da Baiwar Allah a yanda ya barta tana zaune ta kwantar da kanta a jikin sopa, Ganinsa yasa ta ɗan ɗago da kanta tana kallonsa fuska a jagalgale tsabar wahalar ciwon cikin da take fama da shi, lokaci guda ta zamo kamar abun tausayi, zama yayi a gefenta tareda miƙa mata pant sannan ya buɗe ledar pad ya ciro mata guda ɗaya ya miƙa mata tareda faɗin "ki shiga bathroom kisa...." yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka a shagwaɓe ta ce "a halin yanzu bazan iya amfana da komai ba, bazan iya yin wani aiki ba marata ta riƙe sosai bazan iya miƙewa tsaye ba balle na iya tafiya...." Dogon numfashi yaja eyes ɗinsa akanta ɗan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi tareda faɗin "toh yanzu ya kike so ayi? idan kika zauna a haka zaki ɓata jikinki ne, ki daure ki tashi kisa...." Girgiza Kai tayi tana zubar da ƙwallah, ya ce "Kinga maganin ne yake aiki da zaran kinci abinci kin kwanta kinyi bacci shikenam zaki daina jin ciwon...." wani irin murɗa taji ita kanta bata san lokacin data zabura ta kamo hannunsa ta riƙe sosai ba, jikinta har wani kakkarwa yake tana riƙe da hannayensa duk biyun idonta a ƙanƙame, haƙwaranta har dukan juna suke tsabar kakkarwar da suke kamar mai jin zunzurutun sanyi, ita kaɗai tasan tsananin azabar da take ji, addu'o'i kawai take jerawa, Shima kansa ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, a hankali ya zamar da hannayensa sannan ya kwantar da ita a jikin kujerar, ya ɗauki pant ɗin ya saka pad a ciki, yana gama haɗawa yakai pant ɗin saitin sawayenta ya ɗago dasu tareda zura sawayen acikin pant ɗin, ƙirjinsa ne yake bugun uku-uku da ƙarfin gaske hannunsa na kakkarwa haka yake jan pant ɗin sama har yazo saitin kyawawan manyan cinyoyinta masu laushin masifa gasu farare tass har wani ɗaukan ido suke, saitin zuciyarsa ne yake wani irin bugu Rass! Rass!! Rass!!! a yayin da yayi ido huɗu da cinyoyinta masu ɗaukar hankali, wani irin haɗiyar yawu yayi gaba ɗaya jikinsa ya tsimu sai kakkarwa yake, a hankali yake ɗago da kansa har yakai eyes ɗinsa saitin fuskarta ga yanda take fitar da numfashi a hankali ɗumin numfashin yana dukan fuskarsa, eyes ɗinta a lumshe kamar wanda bacci ya ɗauke ta, hannunta a saitin mararta duk biyun, maida kallonsa yayi saitin cinyoyinta yana fargaban ƙarasar da hannunsa can ciki, babu yanda ya iya da haka ya ƙarasa sanya mata pant ɗin mai ɗauke da pad, kansa na kallon gefe gaba ɗaya ya rikice har idanunsa sun kaɗa sunyi ja, jawo ta yayi saman faffaɗan ƙirjinsa sannan yayi mata ɗaukar luɗa ya miƙe tsaye tareda nufar waran katafaren ƙaton gadonsa da ita, yana zuwa ya kwantar da ita daga ita sai towel a jikinta, tashi yayi ya nufi mirror ya ɗauko turare mai bala'in ƙamshi yazo ya feffeshe duk ilahirin jikinta dashi domin baya ƙaunar zama haka ba turare, uwa uba yaga a halin da take ciki dole ta kasance cikin ƙamshi indai tana tare da shi domin Razhdeen ma'abocin son turare ne shi da Roshan jirginsu ɗaya ne.... Bayan gama feffesheta da turare ya janyo blanket ya rufe ta dashi, shima bathroom ya faɗa domin yin wanka..... 🄷🄾🅂🄿🅸🅃🄰🄻 Roshan ne kwance an sanya masa oxygen yana lumshe da ido alamun ya samu yin Bacci, fuskar tayi fiyau ba ƙaramin ramewa yayi ba ga yayi wani irin fari fatt da shi, Abbah yana zaune a bakin gadon da yake sai kuma sauran kuma suna zazzaune a kujerun ɗakin, babu wanda aka bari a gida, Doctor ne yake tsaye yana kora jawabi a Abbah cewar "dole idan ana son kwanciyar hankalinsa ayi masa abinda yake so, akwai abinda ya dame shi a ransa wanda ya gagara cire shi har takai ga taɓa lafiyar zuciyarsa, amma shin ciwonsa ya taɓa tashi kuwa? kodai yanzu ne farkon tashinsa?...." Dogon numfashi Abbah ya sauƙe tareda jinjina kai muryarsa har ta ɗan disashe shima ya ce "haƙiƙannin gaskiya wannan ciwon nashin yanzu tashinsa na biyar kenam, lokacin da yake yaro ƙarami sau uku yana tashi toh amma da aka fitar shi can ƙasar waje akayi masa aiki bai ƙara tashi ba sai kwanakin baya kusan shekara uku lokacin da budurwarsa ƴar classmate ɗinsa ta samu hatsari ta rasu, a lokacin ya jijjiga matuƙa tsabar tsananin son da yake mata, naje na nema masa Auran yarinyar har an bashi ita Allah ya shiga tsakaninsu, ciwonsa ya tashi sosai nan ma saida muka fita dashi ƙasar Ethiopia tukun rayuwarsa ta dai-daita, an kafa mana sharuɗa da dama akan Roshan muddin muna son rayuwarsa, shiyasa bana son abinda zai taɓa shi, bana ƙaunar ɓacin ransa domin muddin idan Ran Roshan ya ɓaci toh abu ne mai tsananin gaske saboda shi mutum ne mai kawaici da rashin sa abu a ransa, bashi da abokin faɗa sannan baya fushi akan abu saidai idan abun yakai maƙura, toh idan har ɓacin ran nasan yakai maƙura toh akwai matsala......." Abbah yana kai ƙarshen maganarsa ya sunkuyar da kansa ƙasi yana zubda ƙwallah domin ko kaɗan baya son ciwon Roshan... Doctor ne yake rarrashinsa game da faɗin "kayi haƙuri Chief kaima yanada kyau ka rage shiga damuwa saboda hawan jininka....." Abbah a zabure ya ɗago yana kallon Doctor ya ce "na ƙwammace gwara ciwo na yaita tashi akan na yaron nan wallahi...." Doctor ya ce "it's okay! But meye musabbabin faruwar hakan? Sannan tin jiya da aka kawo Roshan banga ɗayan ɗan nakan ba wato Razhdeen shin kodai ya koma U.S ne?....." Abbah kamar zai haɗiyi ransa tsabar takaici ya ce "bani da Ɗa mai sunan Razhdeen, Roshan kawai nake Da...." Doctor cike da mamaki yake bin Abbah da kallo, Hajia Kilishi itama dasauri ta ɗago tana kallonsa, Itama Minal dake zaune buɗe baki tayi tana kallon Abbah a yayinda take riƙe da phone ɗinta, Pinky da Rukky kuwa kallon juna suka shiga yi ko wacce fuskarta a hargutse, Ummy cike da mamaki ta ce "Abbahhh......" Ɗaga mata hannu Abbah yayi tareda faɗin "kada ko waccen ku ta kuskura tayi mun magana indai akan Razhdeen ne, baya daga cikin jerukan ƴaƴana, na fidda shi ba Ni ba shi daga yau....." Doctor cike da mamaki ya ce "Subhanallahi amma me yayi zafi haka Chief?...." Abbah ya ce "haka kawai na yanke hukuncin nan domin bazan taɓa haifan yaron da zai saka mun ciwon kai ba ko ya bijirewa maganata ba impossible, haka kuma duk wacce zata bijirewa maganata toh wallahi zan cire hannuna ne akanta sai dai ku nemi wani uban, koda zan zauna babu yaro ko ɗaya ......" ya ƙarashi maganar yana nuna su da yatsa, Hajia Kilishi ganin ya sako ƴaƴanta aciki yasa ranta ya ɓaci sosai ta ce "amma ko wani irin laifi suka yi maka bai kamata kayi musu wannan hukuncin ba, faɗan da kake yi ma babu daɗin ji....." Abbah ya ce "dole abi dokata indai anason zaman lafiya kuma kema harda ke ban ware kowa ba, zan iya baki takardar sallamarki indai baki canza ɗabi'unki ba....." Zaro ido tayi tana kallonsa cike da mamaki acikin ranta kuwa cewa tayi "anya kuwa ba shaye-shaye Chief yayi ba?...." Abbah kallon Doctor ya yi sannan ya ce "yaushe za'a iya sallamar mu?...." Doctor ya ce "gobe da safe insha Allahu domin a daren yau akwai allurar da zamu yi mishi, kuma gaskiya Yakamata indai anason kwanciyar hankalinsa toh a faranta masa, abinda yake nema a bashi insha Allahu za'a dace......" Abbah ya ce "toh shikenam ba damuwa...." Daga nan Doctor yayi ficewarsa, Itama Hajia Kilishi tashi tayi tana kallon yaranta ɗaya bayan ɗaya ta ce "ku tashi mu koma gida...." Minal tashi tayi ta nufi bakin ƙofa zata fice duk sauran ma tashi sukayi banda Ummy dake zaune ta ce "Ni zan zauna da Yaya Roshan....." Abbah ya ce "ki tashi ki bisu zan cigaba da zama dashi....." Ummy jiki ba ƙwari haka ta tashi tana jan ƙafa daƙer ga hawaye yanda yake go slow akan fuskarta, Abbah ganin halin da Ummy take ciki yasa ya ƙira sunanta cikin sassanyar murya ya ce "uwar masu gida....." waiwayowa tayi tana kallonsa cikin damuwa, ya kuma cewa "dawo ki zauna...." sakin fuskarta tayi tareda ɗan sau murmushi ta koma ta zauna, Hajia Kilishi fuska a haɗe ta fice, Sojoji biyar ne sukayi escort ɗinsu zuwa gida, Motar ɗaya nasu, ɗaya kuma sauran sojoji ne aciki daman motar biyu ne a yayinda aka bar wasu sojojin a hospital..... suna isa gida babu wanda ya iya shiga kitchen domin girka abinda zasu ci, Ɗaya daga cikin sojoji suka aika yaje restaurant ya siyo musu abinci, A ranar su Abbah a hospital suka kuma kwana, yau kwanansu uku a hospital.... Razhdeen bayan ya idar da sallar Asuba, miƙewa yayi ya nufi falo yanda yake kwana akan doguwar kujera sakamakon wani irin sarawa da kansa ke yi, buɗe frig yayi ya ɗauki maganin ciwon kai ya ɓare tareda since murfin gorar faro ya kafa a baki saida ya shanye ruwan nan tass yana sauƙe numfashi sama-sama, ya wurgar da gorar gefe sannan ya nufi 3 seater ya kwanta ba tareda ya cire jallabiyar jikinsa ba, yana riƙe da goshinsa nan danan wani irin dogon bacci yayi awun gaba da shi, can ya fara jin ƙinƙishin kuka, yana ji amma bai kula ba a tunaninsa mafarki yake, ganin da gaske yake jin kukan yasa ya fara yunƙurin buɗe eyes ɗinsa waɗanda bacci basu gama isarsu ba, a hankali yakai idonsa saitin yanda yake jin kukan, eyes ɗinsa ne suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar Baiwar Allah sai sharar kuka take tana durƙushe a gabansa, A hanzarce ya tashi zaune idonsa akanta daƙer ya iya motsa lips ɗinsa ya ce "lafiya kuwa....." Cikin kuka take faɗin "yau satina guda a cikin ɗakinka ka ƙi barina na fita, ya kake so nayi da rayuwata? Ni idan baka son zamana a gidan nan ne zan tafi nabar gidan, amma zaman kaɗaici ya isheni haka, bansan me kake nufi da hakan ba....." Nan ta ƙara fashewa da matsanancin kuka mai cin rai, Lumshe eyes ɗinsa yayi sosai ya juma bai buɗe su ba daga bisani ya buɗe a hankali domin ba ƙaramin ciwo kansa ke yi ba, Ganin bazai iya juran jin kukanta ba ga ciwon kai yasa shi cewa "ok tashi na fitar dake don't worry....." dasauri ta miƙe tsaye cikin nuna farin ciki, shima tashi yayi yasa hannunsa a aljihu ya ciro key ɗin ɗakin, har sun nufi bakin ƙofa suka ji an fara bugan ƙofa da ƙarfin gaske, Muryar Abbah suka ji yana faɗin "Razhdeen kayi ƙoƙarin buɗe ƙofar nan tin kafin nasa a ɓalle ƙofar kuma wallahi baza kaji daɗin abinda zanyi maka ba, kafin nan da mintuna uku ka fito da yarinyar nan, idan kuma nima so kake ka kashe Ni kamar yanda kayi sanadiyar mutuwar ɗan uwanka Roshan shikenam kayi ta zama da ita....." Abbah ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka yabar wajen kai tsaye falo ya nufa..... Razhdeen a kiɗime ya zaro da dara-daran idanuwansa waɗanda lokaci guda suka kaɗa launin ja, bai san lokacin da yayi baya ya doku akan kujerar falon ba, wani irin gumi ne yake tsirto masa, sumar kansa gaba ɗaya ya harhargutse ya baje tsabar tashin hankali da ya shiga lokaci guda, Baiwar Allah kuwa hannu tasa ta toshe bakinta sai faman zazzaro ido take nan danan hawaye har ya wanke mata fuska, tanaso ta fitar da kukanta amma sai taji muryarta ya dishe gaba ɗaya, ƙoƙarin shiɗewa tayi taji ya riƙo hannunta da ƙarfi jikinsa har wani zaƙami yake ya jata suka nufi bakin ƙofar ɗakin, key yasa ya buɗe yana janta suka fice, A hanzarce ya sauƙo downstairs tare da Baiwar Allah, Ganin mutanen gidan yayi gaba ɗaya suna zazzaune ko wacce da hawaye akan fuskarta, idonsa yakai kan Aunty Yolash wacce ta samu zuwa daga Bauchi jin rasuwar Roshan domin tin da asuba ta kamo hanya, shi kuwa Roshan ya rasu ne tin cikin dare misalin ƙarfe 2, yanzu haka ƙarfe 9 ne na safe, ana jiran isowar su Sarkin Ƙasar Jidder da iyalansa zuwa ƙafe 10 ko 11 ayi jana'izar sa domin mutuwarsa har ta bazu ko ina, iya Razhdeen ne bai sani ba shida yake cikin ɗaki, Bayan ya gama kallesu gaba ɗaya sannan idanuwansa suka sauƙa akan Gawar Roshan dake kan makara an gama lulluɓe shi da likkafani jana'izarsa kawai ake jira ayi.... Razhdeen ganin Roshan yasa yayi baya zai faɗi tsabar wani irin hajijiyar da ya ɗebe shi, dasauri yasa hannu ya riƙe jikin bango yana fitar da numfashi sama-sama, Baiwar Allah da gudu ta ratsa ta gefen Razhdeen ta nufi wajen da su Ummy suke a zaune a ƙasin carpet, Ummy rungumar Baiwar Allah tayi tana kuka tareda faɗin "Yaya Roshan ya rasu, Aunty Baiwar Allah Yaya Roshan ɗin mu ya tafi ya bar mu, kin ganshi nan kwance ki ce ya tashi dan Allah kar ya tafi ya bar mu......." ta ƙarasa tareda fashewa da matsanancin kuka, itama baiwar Allah kukan take tana rarrashinta, Abbah ne ya sauƙo daga upstairs yana riƙe da Bindiga a hannunsa gadan-gadan ya nufi tsakiyar falon ya tsaya yana fuskantar Razhdeen ya ɗago da bindigar ya saita shi yana kuka...... Razhdeen tsayawa yayi yana kallon Abbah shima hawaye yaƙi tsayuwa masa, Dasauri Aunty Yolash ta miƙe tsaye tareda faɗin "Yaya me kake shirin aikatawa?...." Duk sauran Yaran suma miƙewa suka yi suna zazzaro ido waje hatta Hajia Kilishi itama ta tsorita da ganin abinda Abbah yake shirin yi.. Abbah yana kuka Ya ce "Razhdeen ka cuceni wallahi, kayi sanadiyar mutuwar ɗan uwanka mafi soyuwa acikin zuciyata, ka bijirewa maganata, ka toshe kunnuwanka a yayin da nake rarrashinka game da lallaminka akan ka buɗe ƙofar ɗakin ka, kasa yarinya a ciki ka kulle baka tunanin halin da zata shiga ga Ɗan uwanka har ya kwanta a gadon asibiti sakamakon ciwon zuciyarsa har takai ga ya rasa rayuwarsa, alhalin kasan ciwonsa zai iya tashi a kowani lokuta, yanzu shikenam kayi farin ciki ko? kaji daɗi Roshan ya mutu yabar maka duniya, daman so kake ka kashe shi ta hanyar ƙuntata kuma gashi ya mutu, falillahil hamdu nasan kayi farin ciki a yayinda Ni kuma baƙin ciki nima zai kashe Ni....." Girgiza Kai Razhdeen yake yana kuka sam baya jin daɗin kalaman Abbah, Abbah ya cigaba da cewa "bazan juri ganinka a doron duniya ba, kaima zaka je wajen da ɗan uwanka ya tafi, na ƙwammace gwara na bisineku ku biyu nasan zanji sanyi a raina, Banaso na cigaba da kallonka a matsayin maƙiyi nah gwara kawai ka mutu kaima...." ya ƙarasa maganar tareda kunna kunamar bindigar Ummy ce ta zo yanda Abbah yake ta durƙusa tareda kama ƙafarsa tana kuka tana roƙonsa akan kar yayi kisan kai, "Abbah dan Allah kayi haƙuri kar ka raba mu da Uncle Deen, mun rasa Yaya Roshan bamaso mu rasa Uncle Deen ka temaka mana ...." Suma sauran durƙusawa sukayi suna roƙan Abbah akan ya ƙyale shi, Razhdeen yana kuka ya ce "Daddy nah indai mutuwata ce zatasa kayi farin ciki dan Allah ka harbe Ni a saitin Nan....." ya ƙarasa maganar yana nuna saitin zuciyarsa da hannunsa, ya cigaba da cewa "ciwon zuciya ne ya kashe mun twins ɗina asanadiya ta don haka nima ka harbe Ni a saitin zuciyata domin ɗaukan fansar ɗan uwana......" Shima fashewa yayi da kuka yana kallon Abbah, Abbah shima kukan yake, Aunty Yolash ce ta nufo gurin da Abbah yake zata fizge bindigar kar tsautsayi tasa ya harbe shi, a tunaninta barazana Abbah yake masa, ai kuwa kafin ta ƙarasa Abbah ya yi saurin harba bindigar, bullet bai sauƙa a ko ina ba sai a saitin ƙirjin Uncle Deen...... A duk yaran gidan Babu wacce batayi ihu ba, Ummy kam ƙafewa tayi a wajen idonta akan Uncle Deen wanda yakai ƙasi, Aunty Yolash itama zaro ido tayi tareda ƙamewa a wajen baki a buɗe, Hajia Kilishi itama hannayenta tasa ta toshe bakinta da su tareda zaro ido waje, Baiwar Allah kam batasa lokacin da ta yanki jiki ta faɗi sumammiya ba..... Durƙusawa Abbah yayi tareda fashewa da matsanancin kuka ga bindiga a hannunsa, Sojoji ne suka shugo falo da gudun gaske jin harbin bindiga...... A Razane Razhdeen ya farfaɗo daga doguwar baccin da ya ɗauke shi ya tashi zaune yana haki da ƙarfi-ƙarfi gaba ɗaya ya kiɗime game da haɗa gumi yayi sharkafff, Addu'o'i ya fara jerowa yana waige-waige yaga ashe MAFARKI YAYI...... Idonsa yakai kan Baiwar Allah wacce take zaune a dinning table da farantin Cake a gabanta domin ta tashi da matsanancin yunwa, tayi wankanta ta sanya doguwar baƙar jallabiyan sa, tayi kyau sosai sai haskenta ya ƙara bayyanowa ta ɗaure sumar kanta da rawani mai ɗigon ɓaki da fari..... Itama juyowa tayi tana kallonsa ganin halinda yake ciki, itama tasan yayi mummunan mafarki ne ganin a yanda ya tashi a firgice... Uncle Deen numfashi yake fitarwa sama-sama yakai idonsa kan Agogon ɗakin yaga yanzu ƙarfe 10 na safe ne, ba shiri ya tashi ya nufi yanda Baiwar Allah take a zaune ya kamo hannunta ya ɗagota tareda jan ta suka nufi bakin ƙofa, Ita dai kallonsa take ta gagara cewa komai, Key yasa ya buɗe suka fice yana jan hannunta... Suna sauƙa downstairs suka tarar da Abbah yana zaune dab da Roshan yana rarrashinsa akan ya kwantar da hankalinsa, Ga sauran Yaran gidan suma suna zazzaune akan kujeru, Roshan na ganinsu yayi saurin miƙewa tsaye idonsa akan su, Shima Abbah ɗagowa yayi yana kallon Razhdeen cikin ɓacin rai........ WAYYO YAU DAI NASAN NA HARHARZUƘA ZUCIYOYIN MASU KARATU 😁😁😁😁 MUSAMMAN AUNTY KHADIJA KAR ZUCIYARKI TA BUGA MAFARKI NE, YARONKI ROSHAN YANA NAN ....... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 45 to 46 ꧁꧂ "Daddy......" Dakata Razhdeen, Abbah ne yayi maganar tareda ɗaga masa hannu ya miƙe tsaye yana fuskantar sa ya ce "babu abinda zaka gaya mun Razhdeen, ka ƙuntata mun matuƙa....." Razhdeen sunkuyar da kansa yayi ƙasi a yayin da ita kuma Baiwar Allah ta ratsa ta gefensa ta ƙarasa sauƙowa falon, Roshan ne ya nufi inda take kafin ta ƙaraso yasa hannu ya rungumota yana sauƙar da ajiyar zuciya alamun farin ciki, Jin hayaniyar Abbah yasa gaba ɗaya ƴan matan gidan suka sassauƙo falo, Ita kuma matar gidan a saman upstairs ta tsaya tana kallonsu, Abbah ya cigaba da cewa "tinda har bazaka ji maganata ba to zama dakai bashi da wani amfani, Saboda daga yanzu ka kama hanya ka fita mun a gidana, kaje duk yanda zaka je amma babu ruwa na, duk abinda ya sameka babu hannuna, Bazan tsine maka ba amma kaje na dena ganinka a gaba na balle na ƙunshi baƙin cikin ka......" Dasauri Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah ga hawaye yanda yake gangaro masa, lips ɗinsa na kakkarwa daƙer ya iya cewa "Please Dad......" Abbah ne ya ƙara katse shi da cewa "am not your Dad, please stay away from me, zansa a duba mun yarinyar idan har wani abu ya sameta toh wallahi zanyi maganinka domin saina shigarka kotu an yanke maka hukunci....." Abbah ya juyo yana kallon Baiwar ALLAH ya ce "Daughter gaya mun shin ya miki wani abu? kamar dai fyaɗe...." Dasauri Baiwar ALLAH take girgiza Kai alamar a'a, tana zubda ƙwallah sam bata ji daɗin hukuncin abinda Abbah ya yanke wa Uncle Deen ba, Abbah ya ce "Kinga kar kiji tsoronsa ina tare dake ki gaya mun gaskiya, kar kimun ƙarya....." Baiwar Allah fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi Abbah babu abinda ya mun....." Abbah ya ce "okay shikenam..." ya juyo yana kallon Razhdeen ya ce "Allah ya temake ka, now leave my house....." ya ƙarasa maganar yana nuna masa bakin ƙofa, Roshan ne ya matso dab da Abbah kamar zaiyi kuka ya ce "please Daddy kar ka kore shi, wannan hukuncin yayi tsauri, dan Allah ka ƙyale shi we need him...." Abbah fuska a murtuƙe ya ce Da Roshan "babu ruwanka...." Abbah ya kuma cewa "Razhdeen in har baka bar mun gida kafin na ƙirga ɗaya zuwa biyar ba wallahi zan tsine maka Albarka yanzun nan....." Zaro ido Roshan yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, shi tinda yake bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar Abbah irin ta yau ba, murya na kakkarwa Roshan ya ce "Daddy......" Abbah yayi saurin katse shi da cewa "I said shut up......" Shi kuwa Razhdeen tin tinin har ya haura upstairs ya nufi part ɗinsa kafin ɗan wasu mintuna har ya dawo hannunsa riƙe da troley, eyes ɗinsa har sunyi jawur, haka ya sauƙo yayi hanyar waje, Roshan ne ya tsayar dashi da cewa "My Man please...." Razhdeen juyowa yayi yana kallon Roshan yaɗan sau murmushi a hankali ya furta "Am so sorry my twins, please forgive me....." Jinjina kai Roshan yayi tareda faɗin "na yafe maka My Man, please stay safe...." Ɗaga masa kai Razhdeen yayi tareda juyawa yayi tafiyarsa.... Roshan kuka ne yake shirin kuɓuto masa tinin yayi saurin haurawa upstairs ya nufi part ɗinsa, Shima Abbah yana huci ya nufi upstairs ɗinsa, anan ya tarar da Hajia Kilishi tana tsaye tana kallonsu, ba tareda yace mata komai ba yayi wucewarsa cikin bedroom.... Murmushi tasau tareda bin bayansa itama ta shige ciki.. Baiwar Allah tana sai zubda ƙwallah take gaba ɗaya ta rasa mai yake mata daɗi a duniyar nan, bata ankara ba taji Pinky ta zunguri goshinta tareda faɗin "ai duk ke kika jawo hakan, munafukar banza kinsa an kori Yaro a gidan ubansa ke kuma da babu dangin iya kina Nam abinki ....." Rukky ta ce "muma mu shafa wa kanmu ruwan sanyi domin nasan wata rana muma zata sa a kore mu daga gidan uban mu, daman haka take da buri a ranta, ta zama ƴar gaban goshin Abbah......" Pinky ta ce "waima na kasa fahimtar komai shin daman akwai soyayya a tsakanin Yaya Roshan da wannan ƙazamar yarinya?...." ta ƙarasa maganar tana kallon Rukky Rukky ta ce "tambaya kike ko neman sani? ke tinda baki fahimci haka ba, ai saboda ita Yaya Roshan ya ƙwanta jinya, Kuma idan hasashe na yazo dai-dai shima Uncle Deen kamar sonta yake....." Pinky ta zaro ido tareda faɗin "Whattttttt? Kema dai kinsan Uncle Deen yafi ƙarfin wannan kucakar yarinyar....." Rukky ta ce "idan ba haka ba mezaisa ya rufe kansu a ɗaki daga shi sai ita, nifah ina tunanin wani abu ya shiga tsakaninsu, domin ba yanda za'ayi ace Mace da namiji sun keɓe sheɗan bai shiga tsakani ba kuma tsawon sati guda,......" Pinky ta ce "bana tunanin haka domin Uncle Deen bazai taɓa aikata hakan ba...." Rukky ta ce "kenam shi ɗin dutsi ne?...." Pinky ta kuma cewa "bana tunanin abinda kike konkonto akai zai iya zamo gaskiya domin kinfi kowa sanin waye Uncle, Sannan in har Yaya Roshan shima sonta yake to kuwa za'a kwashi ƴan kallo domin bazamu taɓa yadda a shugo da wannan ƙazamar cikin jinsin mu ba, bamu san asalinta ba wata ƙil mayya ce tazo ta ciccinye mu ɗaya bayan ɗaya, Kai bazama mu yadda a Aureta ba wallahi....." Rukky ta ce "taya zaki iya dakatar da wannan al'amarin bayan ke ƙanwa ce ba uwa ba sannan ba Yayar miji ba...." Pinky tana zunɓuro baki ta ce "ai wallahi ko ta hanyar malamai zan dakatar, Saboda na tsani yarinyar nan...." ta ƙarasa maganar tareda jan dogon tsuka tayi wucewarta, Itama Rukky kallon Baiwar ALLAH tayi wacce tin da take tsaye tana sauraron su itama ta ce "banza kwartuwar banza, karuwar wofi, kariya mai bin mazaje....." ta ƙarasa tana harararta itama tayi wucewarta duk suka haura upstairs.... Da gudu Baiwar Allah ta wuce room ɗinta tana kuka... Duk halin da ake ciki Ummy bata nan taje school ɗinsu karɓo result..... Razhdeen bayan fitarsa Motarsa ya shiga a fusace yayi tafiyarsa, Sojojin dake escort ɗinsa any way suna tambayarsa akan cewar zasu yi rakiya ne amma ko kulasu baiyi ba haka suka haƙura suka barshi ya yi tafiyarsa, Kai tsaye ɗaya daga cikin jerukan gidajensa ya nufa wanda saika bi ta layin mabarata road kafin ka ɗau hanyar gidan, Gudu yake da motarsa amma hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, maganganun Abbah ne suke masa yawo a ƙwaƙwalwarsa, yana cikin wannan halin sauran kaɗan ya buge wata kuturwar dattijuwa tana shirin tsallaka kwalta tana riƙe da ƴar robarta, Da ƙarfin gaske ya danna burki saida mutanen wajen suka tsorita sun ɗauka yayi kaɗa ne, dake wajen zallar mata ne nakasassu, Goshinsa ne yayi matuƙar buguwa a jikin sitiyarin motar, Saida ya ɗau mintuna biyar a haka bai ɗago da kansa ba, still yana nan a wannan halin, yana jin yanda mabaratan suka kewaye motarsa suna faɗin "a temaka mana dana Annabi...." Dake motar mai baƙin glass ne basa iya gano wanda yake ciki, zuciyarsa ce take magana "hakan na nufin yazo waran da yazo ranar har yayi rabon kuɗaɗe...." Jin hayaniyar mabaratar ya ƙara jefa shi cikin wani hali, domin shi sam baya juran jin hayaniya, jin ƙarar sautin sarewa yasa ya yi saurin ɗagowa sai faman sake nannauyar numfashi yake, jin har yanzu bai daina ji ba yasa ya shiga waige-waige ganin jerukan mabarata yasa bai iya ganin wacce take kaɗa jitar ba, a tunaninsa mafarki yake, sautin da yake ji a cikin baccinsa ne yake ƙara hura masa ƙwaƙwalwa, a hanzarce ya buɗe murfin motarsa tareda sauƙar da ɗayan ƙafarsa ta dama, a hankali ya ƙarasa sauƙar da ɗayan ma, yana jin yanda suke shashshafa shi duk a neman temakon amma haka yake sa hannu yana tutture su gefe tareda ratsawa ta tsakiyarsu yanaso ya bi yanda yake jin sautin, Ita kuwa wacce take kaɗan jitar tana can zaune bayan wata ƙatuwar bishiyar dake kusa da bakin hanya tana ta kaɗa jitar ta, domin ita koda wasa bata taɓa zuwa yanda mutum yake neman temako saidai a kawo mata har yanda take zaune, a hankali yake nufan inda take, murɗi-murɗin zirin gashin ta kawai yake gani dake ta juya bayanta, Haka mutane wajen suma suke bin bayansa saida yazo dab da ita sannan ya tsaya tareda ɗaga musu hannu alamar su dakata, Ita kuwa Ƴar Amana bata san da mutum a bayanta ba, haka ta cigaba da kaɗa jitar ta hankali kwance ga ƙatuwar jakarta a gabanta na kuɗaɗe yanda ake bata sadaka, zagayowa yayi ta gabanta yana binta da kallo, cike da mamaki ya durƙusa a gabanta a yayinda ita kuma take lumshe da idanuwanta, jiki na ɓari yakai hannunsa kan haɓarta ya ɗago da fuskarta suka fuskantar juna, jin an ɗago da fuskarta yasa tayi saurin buɗe idonta tana ƙare shi da kallo, Still idanuwansa yakai kan sumar kanta wanda shi zai bada shaidar wacce yake nema ne, wacce yake yawan ganinta a cikin mafarkinsa, babu abinda ya chanza a duk suffarta, sai dai abinda ya ƙara bashi mamaki kuma yaga yarinya ce, Da hannunsa yake murza sumar gashin ta wanda ya kasance laushi futus ga wani irin murɗi-murɗi kamar wanda aka tsoma a ruwan zafi, Ita dai kallonsa take ba tareda tasan ko shi waye ba, Sai dai abinda ya bata mamaki shine sumar kansa kamar mace har kafaɗa dasauri takai hannu tana shafar sumar kansa da murmushi akan fuskarta, Bata san lokacin data ajiye jitar hannunta ba....... *KUYI HAƘURI KUYI MANAGE DA WANNAN ZUWA GOBE DA SAFE DAN ALLAH.....* 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 ✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️ 𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢ 𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪. 𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚) 𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇 𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅 👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈 𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈 ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ, ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ.. 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃: 1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ. 3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃. 4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼. 𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 47 to 48 ꧁꧂ A wannan lokacin yana shirin zaucewa domin gaɓa ɗaya tunaninsa baya jikinsa, kallon Ƴar Amana yake kamar wanda ya yi gamo, ƙwayar idanuwansa ya wurgar kan jitar dake ajiye a gefe guda still ya sake ɗagowa yana binta da kallo, jikinsa har wani zaƙami yake daƙer ya iya buɗan baki ya ce "ke ce? why are you disturb my heart?...." Cikin rashin fahimta Ƴar Amana take binsa da kallo ba tareda tasan ko shi waye ba, ganin yanda ya zuba mata na mujiya yasa ta gama tsorita, hannu takai kan jitar ta tayi saurin rarimo shi a zabure ta miƙe tsaye da gudu tabar waran, kai tsaye gurin tsohuwar da take kula da ita taje ta zauna kusa da ita tareda maƙala hannunta acikin na tsohuwar, miƙe wa yayi shima idonsa agun yanda take zaune can bakin titi, yana mamakin yanda ya ganta acikin mabarata sam bata dace da mai neman TEMAKO ba, yanayin jikinta ya nuna alamun ita ƴar gidan manyan mutane ne, tin daga kan launin fatar jikinta mai launin madara zuwa kan sumar gashinta fesfes mai laushin gaske haɗi da ƙamshi, Azo kan kayan jikinta irin na ƴaƴan masu kuɗi doguwar riga fari tas irin party gown, ƙafar ta babu alamun datti ko kaushi, ƙafa ne kamar na jarirai tsantsi da kuma laushi! tana sanye da white toes, abunda ya ƙara bashi mamaki shine baiga wata nakasa a jikinta ba "To meya zaunar da ita acikin nakasassu marasa gata?...." abinda ya furta a cikin ransa kenam, a hankali yake taku kamar mai tambayar ƙasa ya nufi yanda motarsa yake ya buɗe front seat ta gefen drive ya ɗauko wata baƙar leda mai ɗauke da maƙudan kuɗaɗe, sannan ya dawo saida ya zaɓo wata daga cikinsu mai ɗan lafiya ya bata rabin kuɗin wanda shi kansa bai san adadin yawan kuɗaɗen ba amma a ƙalla zasu yi karo uku wato 3 millions, abinda ya rage a hannunsa kuma basu fi 1 million ba, nufan yanda Ƴar Amana take yayi, Ganinsa yasa ta ƙanƙame tsohuwa domin a halin yanzu tsoronsa ne a bayyane saman fuskarta, yana zuwa ya durƙusa tareda miƙa mata sauran kuɗin hannunsa, ƙin karɓa tayi sai faman girgiza masa kai take, tsohuwar ce take faman rarrashinta game da faɗin "kar ki damu Allah ne ya turo mana wanda zai rinƙa temaka mana, kuɗin da yake bamu sun isa muyi shekara muna morar su, idan baki manta ba akwai wata rana dana ce miki wani yazo ya raba mana kuɗaɗe mai yawan gaske to ai wannan shine, ba mai cutarwa bane ki kwantar da hankalinki....." jin abinda tsohuwa ta faɗa ne yasa ta dawo hayyacinta, kallon kuɗin hannunsa tayi sannan tasa hannu ta karɓe tareda rungumar kuɗin akan ƙirjinta tana bin sumar kansa da kallo, ta gagara tantancewa shin namiji ne ko mace, amma ta lura da damtsen hannunsa da kuma ƙirar jikinsa haɗe da faffaɗar ƙirjinsa irin na ƙarfafan mazan nan waɗanda ake nunowa a film ɗin India, har zuwa yanzu jira yake tayi masa magana koda godiya ne kamar yanda sauran mabaratan suke ta zabga masa godiya da fatan alkhairi, Ƴar Amana sai dai ido kawai, wani irin kallo take masa kamar mai harara, ba komai bane illah hararar domin a rayuwarta ta tsani yawan kallo, shi kuwa ya kasa ɗauke eyes ɗinsa akanta, Ganin irin hararar da take wurga masa ne yasa ya dawo hayyacinsa, a ɗan zabure ya miƙe domin bayaso ya yi abinda zaisa a gano shi, kai tsaye motarsa ya nufa ya buɗe drive seat ya shige yana kallonta ta cikin Black glass ɗinsa wanda na waje bazai iya ganin na cikin motar ba, a haka yaja motar ya yi tafiyarsa zuciyarsa cike da tambayoyi game da nazarurruka, lokaci guda yaji ransa yayi sanyi duk wata damuwa ta yaye masa, yana driving shi kansa bai san lokacin da yake sakin wata rikitacciyar murmushi ba, maganar zuci ya fara yi "ina ji a jikina wannan ce yarinyar da nake nema, domin babu abinda ya chanza daga launin ta, duk da ban taɓa ganin fuskarta ba but I known she is my dreamer, but she's too young, yarinya ce ƙarama how comes zata iya kaɗa jita haka? can't believe....." ya ƙarasa maganar zuci haɗi da girgiza Kai, yana mamakin al'amarin, Da wannan tunanin ya isa yanda zaije..... Ƴar Amana jujjuya kuɗin hannunta take tana tunanin ina zata kai waɗannan maƙudan kuɗaɗen... Tsohuwar ce ta kalleta sannan ta ce "me kike tunani ne ƴata?...." Ƴar Amana nuna mata kuɗin hannunta tayi tana girgiza Kai alamar bata san yanda zatayi dasu ba, Dariya tsohuwar tayi har saida jajayen haƙwaranta suka fito ta ce "ƴata kenam waɗannan kuɗaɗen ai kashe su abu ne mai sauƙin gaske a wurin ki, yanzu mu kuɗin da aka bamu sai suyi shekara basu ƙare ba amma ke a yau zaki ƙarar dasu......" Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon tsohuwar sam bata fahimci mai take nufi ba amma taji duk abinda ta ce.... Tsohuwa ta cigaba da cewa "a siyan sutura kaɗai zaki kashe fin rabin kuɗin nan, uwa uba Azo kan takalma da turarukan gashi Shiyasa kullum sumar kan ki baya rabuwa da ƙamshi, amma baki damu da siyan kayan abinci ba kuma baki damu da yin kwalliya ba ke kullum kin ƙare a siyan kayayyaki....." Kau da kai Ƴar Amana tayi jin abinda tsohuwar take faɗi, Ƴar Amana sam bata son zama da ƙazanta kullum acikin gyaran jiki take gata yarinya ƙarama amma ta tsani ƙazanta, ma'abociyar son tsabta ce da kuma son ƙamshi, da zaran ta samu kuɗi masu dama zata wuce super market ne, idan taje bata magana a kowa zata ɗauki basket ta kutsa ciki, ita da kanta zata zazzaɓo abubuwan da take buƙata sannan tazo su lissafa yawan kuɗaɗen kayayyakin su, haka zata ciro kuɗi ta miƙa musu idan akwai canji su bata, amma yawan kuɗin da take kashewa sun kai kimanin dubu ɗari biyar ko fin haka.... shiyasa tsohuwa take faɗin "kashe kuɗi a gurin ƴar Amana babu wuya....." Daren yau ko sau ɗaya Uncle Deen bai rimtsa ba, fuskar Ƴar Amana ce take masa gizo shi har yanzu bai yadda cewar mutum bace, ganin yawan tunanin bazai kai shi ba yasa ya tashi ya nufi bathroom ya ɗauro alwala sannan ya fito tare da zura jallabiyarsa ya ɗoru akan sallaya a nutsi ya tsaida sallar darensa, 𝕭⃤𝖆⃤𝖎⃤𝖜⃤𝖆⃤𝖗⃤ 𝖆⃤ 𝕬⃤𝖑⃤𝖑⃤𝖆⃤𝖍⃤ Baiwar Allah tana cikin mawuyancin hali domin itama a cikin daren nan bata rimtsa ba, wani irin zazzaɓi take fama dashi mai rikitarwa ga tunanin Uncle Deen, wani irin zafi take ji acikin zuciyarta game da raɗaɗin tafiyarsa, duk wulaƙancin da ake mata acikin gidan saboda tafiyarsa sam bata damu ba, damuwarta ɗaya shine Uncle Deen ya tsaya mata a rai, a halin yanzu ji take tamkar a cikin kabari take, shaƙuwar da tayi da Razhdeen ya wuce misali, gani take inta buɗe idonta zata ganshi a gefenta, ko kaɗan bata taɓa jin tsanarsa acikin zuciyarta ba, tana matuƙar jin wani abu akansa, tana kwance ta fashe da matsanancin kuka haɗe da maganar zuci "Uncle Deen ka dawo gare Ni dan Allah, meyasa zaka tafi ka barni cikin wannan mawuyancin hali, bazan iya samun nutsuwa ba tare da kai a kusa dani ba, meyasa? meyasa saida na gama sakaka acikin zuciyata lokaci guda zaka tafi ka barniiii......" kuka take bana wasa ba, jikinta har wani ɓari yake, haka ta kwana da wannan ciwon raɗaɗin son kasancewa da Uncle Deen, Daƙer ta iya tashi ta nufi bathroom domin ɗaurowa Alwala anata ƙiraye-ƙirayen sallar asuba, yanda taga rana haka taga dare.... Misalin ƙarfe 10 na dare Abbah yana zaune a falo ya tara duk mutanen gidan, Hajia Kilishi itama tana zaune akan sopa ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana son jin dalilin da Abbah ya tara su gaba ɗaya, Shima Roshan yana zaune a one seater yana sanye da blue jeans da blue t-shirt wanda ya kama jikinsa sosai kai kace saboda shi aka ƙero rigar sannan ya ƙara ɗora sweater a saman rigar mai launin Black and blue, Sauran yaran gidan kuwa suna ƙasin carpet iya Baiwar ALLAH ce bata gurin, Abbah ne ya kalli ƴar Tiny ya ce "Auta je ki ƙira Auntynki....." Ƴar Tiny ƙura masa ido tayi haɗi da cewa "naga gashu nan jajjaune..." "Aunty Daughter zaki ƙira a room ɗinta...." a cewar Abbah. tsayawa tayi tana turo baki ta ce "ita ɗim Aunty na ne?...." wani irin tsawa Abbah ya daka mata saida ta gigita bata san lokacin da ta nufi ɗakin Baiwar ALLAH ba tana kuka, suma duk waran ba wanda bai tsorita ba, Roshan ne ya kalli Abbah sannan ya ce "Please Abbah cold down...." kafin wasu ɗan mintuna saiga Baiwar ALLAH ta fito sanye da zureren hijab alamun tin sallar asuba bata cire ba, zuwa tayi ta durƙusa ta gaishe da Abbah, ya amsa mata cikin kulawa sannan takai idonta kan Hajia Kilishi itama ta gaishe ta, kawar da kanta tayi gefe ba tare da ta amsa mata ba domin zuwa yanzu ba ƙaramin tsanar Baiwar Allah tayi ba, saboda ita duk yaran gidan basa jin daɗin zaman gidan, koda yaushe suna cikin antara.... Baiwar Allah ganin Hajia bata kulata ba yasa ta kalli Roshan taga ita yake kallo shima ta gaishe shi, cikin murmushi ya amsa mata, Abbah ya kalli yaran gidan fuska a haɗe ya ce "ku ɗin bazaku gaisheta ba ne?....." duk suka ɗago suna kallon Abbah cike da mamaki, Banda Ummy cikin sakin fuska ta ce "gud morning Aunty Daughter...." ta ƙarasa tana dariya itama Baiwar ALLAH murmusawa tayi, Roshan ne ya ce "wato kema kin bi bakin Abbah Koh?...." yayi maganar idonsa akan Ummy.. Pinky ce take kallon Abbah cikin takaici ta ce "Abbah mu fa mun girmeta, ita ya dace ta gaishe mu...." Itama Rukky ta ce "gaskiya yanzu fa we are almost 23 years ita kuma nasan bazata wuce 20 or 21 ba....." Minal dai ko ɗagowa batayi ba tanata pressing phone ɗinta, Abbah ya kalli Minal ya ce "kepah Amina kema bijire mun zaki yi ne?...." Cike da mamaki Minal ta ɗago tana kallon Abbah ta ce "au wai har da Ni?...." Abbah ya ce "kina shakku ne?...." ta juya tana kallon Baiwar ALLAH tareda faɗin "gaskiya ba'a mun adalci ba indai akasa na gaishe da wannan yarinyar....." Abbah ya ce "adalcin kenam tinda yanzu itace sama daku...." Hajia Kilishi a fusace ta ce "how comes zata zamo sama dasu? kawai dai kanason zamar mun da yara Agolai waɗanda basu da ƴanci...." Abbah ya ce "Zata zamo matar Yayansu Kinga kuwa dole su darajata su mutuntata...." Kallon juna Ƴanmatan gidan suka shiga yi abu yazo muku kamar almara, Hajia Kilishi cikin rashin fahimta tana jifar Baiwar ALLAH da wani irin mummunan kallo ta ce "ban fahimta ba...." Baiwar Allah kanta a sunkuye ita kanta bata san ina Abbah ya dosa ba, Abbah ya ce "ƙwarai da gaske na yanke shawarar Aurawa Roshan Daughter, Roshan ya sanar mun cewar yana sonta zai Aure ta bayan na bashi labarin ta, haƙiƙannin gaskiya naji daɗin haka sosai domin inaso na sauƙe nauyin dake kaina tabar hannuna ta koma hannun mijinta Roshan, Amma hakan bashi zaisa na daina lura da al'amuranta ba dole zansa ido akan yanayin zamantakewar ta da mijinta da kuma ku masu nuna ƙiyayyarku akanta tinda ba wani guri za'a Kaita ba, a cikin gidan zasu zauna amma part ɗinta daban, Ni nayi Na'am da Auren nan....." a firgice Rukky ta kalli Pinky haɗi da cewa "daman na gaya miki......" Pinky kamar zata haɗiyi ranta ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, amma za'a yi babban buro uba a gidan nan....." sunyi maganarsu acikin raɗa ba tare da anji su ba Minal cike da mamaki take bin Baiwar ALLAH da kallo fuska a murtuƙe ta ce "taya zamu zauna da wacce bamu san asalinta ba?...." Abbah ya ce "ta yanda kuke zaune da ita yanzu...." Roshan ganin yanda suke ta hararar Baiwar ALLAH yasa yaɗan motsa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ya ce "kunga ku dakata haka! na farko baku zaku Aura mun ita ba sannan baku zaku zauna mun da ita ba yakamata ku fuskanci yanda rayuwa take, kuma ku samo mazajen Aure kuyi Auren ku....." kafin ya ƙarasa Hajia Kilishi ta ɗaga masa hannu tare da miƙewa tsaye tana fuskantar sa ta ce "ka dakata haka Roshan, wannan cin mutunci da cin fuska ya isheni haka! kenam kana musu gorin Aure ne ko meye? Wawan yaro wanda baka san inda yake maka ciwo ba, In banda ƙaddara meya haɗaka da wannan yarinyar da ba'a san asalin ta ba, wata ƙil ƴar cikin shege ce aka jefar da ita ta tashi a gidan marayu, kaine wanda za'a ce ka fuskanci rayuwa yanda take kaje ka nemo ƴar asali bawai ƴar tsintuwa ba......" Abbah ne shima ya miƙe tare da zabga mata mari a gefen fuskarta, saida ta faɗa kan kujera tana riƙe da fuskarta, Duk acikin yaran babu wanda bai zabura ba, ko wacce zuciyarta na bugun 3³, Baiwar Allah ta kasa ɗago da kanta domin yanayin da take ciki yana shirin fin ƙarfin tunaninta, kuka take ba ƙaƙƙautawa, bata san meyasa wannan al'amarin yake shirin afkuwa ba, Abbah cikin zafin rai ya ce "idan kika sake faɗin mummunan kalma akan yarinyar nan wallahi zanyi miki abunda bakiyi zato ba...." Hajia Kilishi ganin bazata iya juran kalar wannan wulaƙanci ba a gaban iyalanta yasa ta tashi a fusace cikin zafin rai take nunawa Abbah yatsa tare da faɗin "Na faɗa ita ɗin ƴar cikin shege ce marar asali kayi duk abinda zakayi, tinda har wulaƙancinka yakai ka rinƙa dukana a gaban ƴaƴana to meya rage yanzu, kuma wallahi tallahi bazan taɓa bari ayi Auren nan ba saidai In wata amma banda wannan ƴar jagaliya, Kuma koda mahaifiyarsa tana raye bazata taɓa barin ya Auri wannan marar asali ba, saboda bani na haifeshi ba shine zaka nuna mun ban isa dashi ba, toh sai ayi Auren mu gani ai....." Murmushin takaici Abbah yayi ya ce "ki cigaba da nuna mun yatsa wata rana zan ɓalla ƴar yatsar ne, Kuma da kike cewa baza'ayi Auren ba basai kina gidan daki dakatar ba......" Hajia Kilishi cike da mamaki ta ce "oh kana nufin korata zakayi?...." Abbah ya ce "ehh! kije ki na sakeki saki biyu...." A zabure Roshan ya miƙe tsaye yana faɗin "Abbah meye kake shirin aikatawa?...." Abbah juyowa yayi yana kallon Roshan ya ce "bawai nake shirin aikatawa ba, na ma aikata an gama ka nemi guri ka zauna...." Roshan ba yanda ya iya haka ya nemi guri ya zauna domin baya ƙaunar kaucewa maganar Abbah, Minal da Pinky da Rukky da kuma Ummy duk miƙewa sukayi tsaye domin hukuncin da Abbah ya yanke akan Mommy yayi tsauri, Minal tana kuka ta ce "Abbah yanzu ɓacin ranka har zaisa ka sallami Mahaifiyar mu muna raye?....." Pinky da Rukky babu bakin magana sai kuka, Ummy ce taje gaban Mommy ta tsaya tana kuka ta ce "Mommy kinsan fa ke babbar mai laifi ce agurin Abbah har ma agurin Ubangijinki meyasa bazaki kiyaye ba, Meyasa bazaki bi umarnin mijinki har ki nemi yafiyarsa akan laifin da kika aikata masa ba?....." Bata ƙarasa maganar ba taji Mommy ta hankaɗata baya har saida ta faɗi ƙasin carpet tana faɗin "Maryam ki kiyayeni tin kafin na illata ki, ke wata iriyar jakar yarinya ce marar kishin mahaifiyarta, a gaban ki Mahaifinki ya mare Ni amma baki ji zafin hakan ba, a gaban ki Mahaifinki ya sake Ni bakiji zafin haka ba, anya kuwa ke jinina ne?......" kafin ta ankara Abbah ya ƙara zabga mata mari ata ɗayan gefen fuskarta again yana huci ya ce "daki taɓa uwar masu gida gwara kin rama marin da nayi miki, domin idan ina ganinta tamkar ina kallon mahaifiyata ce, duk duniyan nan babu mai ƙiran sunan Ummy kai tsaye da asalin sunanta sai ke saboda bakya respect ɗin mahaifiyata......" Minal da gudu tayo kan Mommy ta riƙeta tana kuka, Hajia Kilishi cike da raɗaɗin baƙin ciki ta ɗago itama takai hannu ta zabgawa Abbah mari, Ummy tsabar firgita bata san lokacin data ɗago daga kwance ba sai faman zazzaro ido take waje, suma sauran yaran ido kawai suka firfito waje cike da mamaki, A ruɗe Roshan ya miƙe tare da nufan yanda Hajia Kilishi take cikin zafin nama ya ɗauki hannu zai mareta yaji an riƙe masa hannu ta baya, A firgice ya juyo yaga waye ya dakatar da shi idonsa ne suka sauƙa akan Baiwar Allah tana kuka ta ce "dan Allah ku dakata haka, bazan iya juran ganin wannan mummunan ta'agazan ba ...." Hajia Kilishi tana bin Roshan da wani irin wawan kallo ta ce "ai na rantse da Allah inka sake hannunka ya taɓa jikina da sunan mari saina yi maka abinda bakayi zato ba, dana nuna maka cewa Ni Hajia Kilishi nafi ƙarfin wulaƙanci......" Abbah jiki na zaƙami yana riƙe da fuska tsantsar mamaki ne ya hanashi sauƙar da hannunsa daga kan fuskar, murya na kakkarwa ya ce "nayi danasanin Aurenki kuma uwa uba dana haɗa zuriya dake tirrr, nayi nadama matuƙa da ban samarwa ƴaƴana uwa ta gari ba, nayi alhinin rashin matata Fatima mutumiyar arziƙi ko musu bata taɓa mun ba, Allah sarki mutuwa tayi mun yankan ƙauna, yanzu ki fita mun a gida tin kafin na hallaka ki, yarana kuwa ko dake ko ba ke zasu rayu tinda duk cikinsu babu ƙaramin yaro sai Auta, akwai jariran da ana haifansu suka rasa mahaifiyarsu kuma sun rayu kamar dai su twins Roshan da Razhdeen......" Hajia Kilishi murmushin takaici tayi sannan ta ce "Da kyau! Ban damu ba dan ka koreni daga gidanka, ƙarewa ka kori ɗan daka haifa a cikinka ma balle Ni da kawoni akayi kuma zan tafi....." Abbah cikin tsawa ya ce "to kije mana tsayuwar me kike? daman abinda kike nema kenam kije ki cigaba da yawon iskancinki, Uwar masu gida tana ɓoye mun abubuwa akanki bata san na rigata sani ba, hotel ɗin da kike zuwa na sani, gidan Alhaji Shehu da kike zuwa kuna yawon barikinku na sani, ce miki akayi aikin sojan da nake yi a banza nake yinsa? ko kuma tafiye-tafiye ƙasar wajen da nake zuwa duk shashanci ne bana lura da iyalai na? duk wani motsinki na sani, akwai waɗanda suke samun ido akan iyalaina gaba ɗaya ko ina nan ko bana nan, ki je ki bana buƙatarki yanzu......." Abbah ya ƙarasa maganar tare da fashewa da matsanancin kuka a yayinda ita kuma Hajia Kilishi gaba ɗaya jikinta ne yayi sanyi jin an tona asirinta a gaban yaranta, sannan shi kansa Abbah ya sani bawai iya Ummy bace....." Itama fashewa tayi da kuka cikin jin kunya ta haura upstairs, ba jumawa ta sauƙo da akwatinta a hannu ta nufi bakin ƙofar fita, Abbah zama yayi akan sopa yana huci ya tsayar da idonsa guri guda kamar mai tunanin wani abu, ya ce "kuma idan kuna buƙatar bin mahaifiyarku ku bita ban hanaku ba, Idan kuna son kasancewa tare da ita ku bi bayanta amma inaso ku sani cewa daga yau kar ku ƙara ganina a matsayin mahaifinku muddin ku ka bita, Ni inaso rayuwarku ta inganta ne....." Durƙusawa Minal tayi a ƙasin carpet ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, babban takaicinta halin da Mommy ta jefa kanta aciki na yawon hotel, Suma su Pinky zama sukayi suna kuka, Ƴar Tiny kuwa daman tin fitowar Baiwar ALLAH bata fito ba kwanciyarta tayi akan gado har bacci ya ɗauketa, Abbah ya ce "duk ku zauna ku fuskance Ni..." ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter kiyi haƙuri da abinda kika gani da kuma kika ji, tambaya ɗaya zan miki yanzu inhar kin Amince, shin kina son Roshan zaki Aure shi?...." Baiwar Allah tana kuka ta ce "Abbah taya zan Auri Yaya Roshan bayan Ni kaina bansan asalina ba shin wacece Ni?...." Abbah ya ce "duk wannan maganar ki barshi inhar kin ɗauke Ni a matsayin mahaifi toh ki dena sawa a ranki cewar bakida kowa, Ni na zamo miki kowa uwa da uba duk....." Baiwar Allah ta jinjina kai tare da faɗin "shikenam Abbah duk yanda ka yanke dai-dai ne, Ni bani da zaɓi...." Abbah ya ce "ba komai Daughter Allah ya miki Albarka....." ta amsa da Ameen.... ya kuma cewa "insha Allahu zuwa next week za'ayi taron ɗaurin Aurenku....." Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗago tana kallon Abbah ta ce "Abbah dasauri haka?...." Murmushi yayi sannan ya ce "toh me za'a jira Daughter, nafi son ayi abu a wuce gurin...." Kallon Roshan tayi da rinannun idanuwanta, a yayinda shi kuma yake fama sake mata murmushi, Sunkuyar da kanta tayi ƙasi tana sabinta kukanta sakamakon tuna Uncle Deen da tayi, a yanzu shine a ranta saboda tsananin shaƙuwar da tayi dashi, tin daga lokacin da ya mata wanka ta fara ƙaunarsa da irin kulawar da ya bata tana ciwon cikin nan, Gaba ɗaya sai taji kamar ta sanar wa Abbah cewa Uncle Deen take so, amma sai dai abune mai wahalar gaske ta furta hakan...... Abbah ne ya juyo da kallonsa kan Pinky da Rukky sannan ya ce "ku kuma bayan biki da kwana biyu zaku koma ƙasar London ku cigaba da karatunku, hutunku ya ƙare, Nima zan koma Ethiopia sai bayan shekara ɗaya na dawo" ya kalli Minal ya ce "zan bar miki Amanar gidan nan a hannunki saboda kece babba, Uwar masu gida da kuma Auta zasu kasance a ƙarƙashinki yanzu kece mahaifiyarsu, Duk abinda kuke buƙata ku tuntuɓi Roshan, kuma zai rinƙa zuwa yana duba ku...." Minal tana sauƙe numfashi ta ce "insha Allahu Abbah..." Ya kalli Ummy sannan ya ce "uwar masu gida tinda bakya son barin Nigeria na sama miki school of nursing zakina zuwa da dawowa, akwai security da zai rinƙa kai ki kullum sannan ya ɗauko ki....." Itama ta amsa da "toh Abbah...." ta kuma cewa "Amma Abbah Yaya Roshan bazai koma gurin Aikinsa bane?...." Abbah ya ce "akwai wani aikin da zai gudanar anan Nigeria sai yayi two years kafin ya koma Egypt shi da matar sa....." Ummy tana hawaye ta ce "what about Uncle Deen? Dan ALLAH ka dawo dashi cikin Ahali muna buƙatar sa....." Ajiyar zuciya Abbah ya ja kafin ya cigaba da cewa "ina sane dashi bazan taɓa barinsa ba ai, nasan a yanda yake domin nasa anbi mun bayansa, inaso yaje can ya huta ne kuma ku huta da fargabansa...." Cikin farin ciki Ummy ta ce "toh ina yake?...." Abbah ya ce "yana gidansa na can ƙwarimpa...." Abbah ya kuma cewa "yanzu dai ku tashi kuje kuyi mun lissafe-lissafen abubuwan da ake buƙata na biki, sannan Roshan ka ɗauki Daughter da uwar masu gida kuje su zaɓo kayan furnitures, da kayan lefe da duk abubuwan da ake so, Sannan gobe inaso kaje ƙasar Jidder ka gano Uncle ɗin ku domin tinda kuka dawo baku je ba, idan zaka tafi kabi ka ɗauki Ɗan uwanka Razhdeen ku tafi tare....." Abbah yana kaiwa nan ya haura upstairs, suma kowa tashi yayi ya koma muhallinsa iya Baiwar ALLAH da Roshan kawai aka bari a falon.... ✓✓✓✓✓ Uncle Deen yana kwance saman katafaren gadonsa ya ɗora hannu akan goshi ido a lumshe kamar meyin Bacci, tsananin yunwa ne yake damunsa ga shi kaɗai ne a gidan balle yasa a nemo masa abinda zai ci, sannan bai taɓa shiga kitchen ba balle ya iya cooking, ga wani irin kasala da yake ji balle ya tashi yaje restaurant tako ina ba sauƙi, yana cikin wannan halin yaji wayarsa tana ringing, a hankali yakai hannu ya rarumo wayar dake saman chest ɗinsa, ido a lumshe yakai wayar saitin kunnensa ba tareda yaga sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar ba, "ℎ𝑒𝑙𝑙𝑜 𝑚𝑦 𝑂𝑔𝑎ℎ! a𝑚 o𝑛 𝑚𝑦 wa𝑦t𝑜 𝑁𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖𝑎..." "𝐴𝑟𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑠𝑢𝑟𝑒?..." a cewar Uncle Deen, domin ya rigada ya dauki murya.. ta 6angaren Marshall kuma cewa yayi "𝑌𝑎𝑛𝑧𝑢 ℎak𝑎 in𝑎 airpor𝑡 𝑛𝑎 𝑠𝑎𝑢𝑘𝑎 𝑎 𝑁𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖a, daman na 𝑔𝑎𝑦𝑎 maka zuwan bazata zanyi maka...." Uncle Deen kara narkewa yayi akan gadonsa domin baya jin zai iya tashi balle yaje airport ya ce "look! you know 𝑤ℎ𝑎𝑡? kazo gidana na nan 𝑘𝑤𝑎𝑟𝑖𝑚𝑝𝑎 am here, but are you together with escorts?...." Marshall ya amsa masa cike da mamakin yanda yake jin muryar Abokinsa kamar 'Dan maye ya ce "na bana tare 𝑑𝑎 kowa but are you 𝑜𝑘𝑎𝑦? naji muryarka kamar baka da lafiya, and meyasa baka gida 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢𝑛?....." Uncle Deen jin bazai iya amsa masa wadannan tambayoyinsa yasa shi cewa "𝑃𝑙𝑒𝑎𝑠𝑒 𝑐𝑎𝑟𝑟𝑦 𝑦𝑜𝑢𝑟 𝑠𝑒𝑙𝑓 𝑎𝑛𝑑 𝑐𝑜𝑚𝑒 𝑡𝑜 𝑚𝑦 ℎ𝑜𝑢𝑠𝑒 𝑟𝑖𝑔ℎ 𝑛𝑜𝑤, 𝑎𝑚 𝑛𝑜𝑡 𝑓𝑒𝑒𝑙𝑖𝑛𝑔 𝑏𝑒𝑡𝑡𝑒𝑟...." yana kaiwa ƙarshen maganarsa yayi ƙitt ya yanke ƙiran tare da jan dogon numfashi...... 𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪. 𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔 Daga Alƙalamin Asma'u Muhammad Auwal Giade 𝘼𝙎𝙈𝙀𝙀𝙏𝘼𝙃✍️ 𝙁𝙄𝙉𝘼𝙇 𝙊𝙁 𝙏𝙃𝙀 𝙁𝙄𝙍𝙎𝙏 𝙎𝙏𝙀𝙋✅ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙀𝘾𝙊𝙉𝘿 𝙎𝙏𝙀𝙋 𝙄𝙎 𝘾𝙊𝙈𝙄𝙉𝙂 𝙎𝙊𝙊𝙉✍️ 𝙩𝙝𝙚 𝙚𝙣𝙙 𝙤𝙛 𝙨𝙩𝙚𝙥 𝙤𝙣𝙚 49 𝙩𝙤 50 Knock! Knock!! Knock!!! jin yanda ake ta ƙonƙosa ƙofa yasa ya ɗan buɗe shanyayyun eyes ɗinsa waɗanda bacci yake shirin yaƙarsu, ɗan tsuka yaja a hankali yakai hannunsa saitin goshinsa jin gaba ɗaya jikinsa a mace bashi da wani sukuni a tattare dashi, kasa tashi yayi ya shantake da haka jin an daina bugun ƙofar, can wasu ɗan seconni yaji an fara danna ƙararrawar ƙofar, a ɗan ruɗe ya tashi zaune yana faɗin "oh my god..." shi gaba ɗaya ya manta da yayi baƙo haka ya miƙe daga shi sai three quarter sai kuma singlet yana jan ƙafa da ƙer ya yi falo, a hankali yake taka matakalar beni jin har zuwa yanzu baccin bai bar idonsa ba sai faman hamma yake ga wata iriyar la'anannen yunwan da yake ji da haka ya isa bakin ƙofa, hannu yasa ya buɗe ganin Marshall Mohandas yasa shi ware fararen eyes ɗinsa, shi sam ya manta da cewar Marshall ya ƙira shi akan cewar yazo, Marshall ƙarasa shugowa yayi idonsa akan Major sai faman harararsa yake, da haka ya shige cikin falon yana jan akwatinsa, murmusawa Uncle Deen ya yi tare da rufe ƙofar shima ya yo ciki, tin kafin ya nemi kujera ya zauna Marshall ya ce "wato ka shanya kayanka a waje sai yanzu kaga damar buɗewa?...." Deen ko kulashi baiyi ba ya iddasa zama akan two seater tareda kwantar da bayansa ajikin kujerar kansa na kallon sama, Marshall cikin yanayin damuwa yake bin Deen da kallo cikin cold voice ya ce. "Major what is wrong with you?...." Ɗagowa Deen yayi yana binsa da kallo ya ce "meya faru?..." Marshall ya ce "naga gaba ɗaya yanayinka is not better, akwai damuwa a tattare dakai domin duk wanda ya ganka yasan kana cikin problems, so what's going wrong please tell me...." Uncle Deen girgiza Kai ya yi sannan ya ce "meye zakayi idan na gaya maka?..." Marshall murmushi ya yi game da hura iskar bakinsa ya ce "I'll going to find you a solution...." Uncle Deen idonsa akan Marshall ya ce "Really?..." Marshall ya amsa masa da "yeah...." Girgiza Kai Uncle Deen ya yi can na wasu ɗan lokuta ya ce "okay! don't worry..." Marshall cikin yanayin damuwa ya ce "kodai akan mafarkin yarinyar nan ne?...." Ɗan buɗe eyes ɗinsa ya yi dasauri yakai ƙwayar idanuwansa kan Marshall, lokaci guda yaji kamar wanda aka jona masa shocking a jiki, Ƴar Amana ce ta faɗo masa a rai lokaci guda kuma yaji wani sanyi a ransa wanda bai san lokacin da ya ɗan sau wata ɓoyayyar murmushi ba, Marshall jin ya kasa bashi amsa yasa shi maimaitawa ya ce "ita ce Koh?..." Girgiza Kai Uncle Deen ya yi tare da faɗin "I already find her...." A zabure Marshall ya ce "Whattttttt!!!! wai da gaske kake Major? but how comes?...." Uncle Deen tsaya kallon Marshall ya yi ganin yanda ya firgita jin ya ce ya samo ta, "Wait! duk wannan ruɗin na meye?..." a hanzarce Marshall ya yo kan Uncle Deen ya zauna dab dashi fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "na tayaka farin ciki Major domin wannan yarinyar ba ƙaramin wahalar dakai take ba, ina murna ne saboda matsalarka tazo ƙarshe, You know Babban Malami ya sanar mana cewa ciwon mafarkinka bazai warke ba har sai kayi ido huɗu da yarinyar, kaga kuwa daga yanzu wannan mummunar mafarkin ka daina shi har abada, Amma taya ka sameta?..." Uncle Deen jin Marshall ya cika shi da surutu yasa shi cewa "oh my god Marshall! I don't know how can I explain for you, please leave me alone...." Marshall a hanzarce ya riƙo hannun Uncle Deen yana faɗin "i want to see dis useless girl da take wahalar mana dakai..." A firgice Uncle Deen ya juyo yana kallonsa fuska a ɗaure ba alamar wasa ya ce "WHO is the useless girl?...." Ganin yanda yanayinsa ya sauya lokaci guda yasa Marshall cewa "it's okay am just jocking, yanzu dai tashi ka rakani gurinta in batayi Sa'a ba na harbe mata kai...." a fusace Deen ya juyo tare da watsa masa wani irin kallo, cikin zolaya Marshal yake cewa "am sorry sorry am just playing, please tashi muje naga ƴar baiwar yarinya mai fitowa a cikin mafarkin jarumin jaruman sojoji...." hannu Uncle Deen ya ɗora akan goshinsa yana bubbugawa a hankali tsabar tsananin ciwon da yake masa ga Marshall kuma yana damunsa da surutu, a hankali ya furta cewa "I'll not go anyway, am hungry and am not feeling well once...." sauƙe numfashi Marshall ya yi tare da faɗin "okay! daman tinda naji kace baka gida nasan akwai matsala domin indai kana Nigeria baka son yin nesa da Daddy, saboda haka yasa nabi ta restaurant nayo mana shopping kayan abinci dasu fruit...." ya ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye ya nufi yanda wata ƴar jaka take yasa hannu ya buɗe ya ciro wata leda mai ɗauke da take away ya ciro guda biyu da spoon a jiki, sannan ya ɗauko wata leda mai kayan fruits da juice, yazo ya jawo ɗan ƙaramin glass table dake tsakiyar falo zuwa gaban Deen ya ɗoɗɗora kayan ciye-ciye akai, bayan ya kammala shirya komai enough a hankali ya fara feeding ɗin Deen yana sashi cin abincin daƙer saboda a rayuwarsa ya tsani cin abincin restaurant, a nutse suka kammala cin abincin su daga baya Uncle Deen ya taya Marshal ɗaukar jakarsa bayan ya ji kansa garau ya kaishi wani tsararren bedroom dake saman upstairs, Dake falo biyu ne a cikin ɗaki ɗaya sai bedroom huɗu ko wanne yana saman upstairs, two bedrooms suna upstair a falon farko sai another two bedrooms a falo na biyu, Marshall ya sauƙa ne a falon farko saida ya zaɓi bedroom ɗaya acikin biyu dake upstairs, Shi kuma Uncle Deen a falo na biyu yake shima yana ɗaya daga cikin bedrooms a saman upstairs, Bayan Uncle Deen yakai Marshall bedroom ɗinsa shima sauƙowa yayi ya nufi falonsa kai tsaye upstairs ya haura ya nufi bedroom ɗinsa, Bathroom ya shige domin yin Bathing.... Shima Marshall kafin ya shige Bathroom yayi wanka saida ya ƙira wayar Minal bugu ɗaya aka ɗauka, murya ciki-ciki ya ce "hello Beb na sauƙa a Nigeria...." daga ɓangaren Minal kamar bazata mutu ba tsabar farin ciki tana kwance saman katafaren ƙaton gadonta tana sanye da doguwar rigar bacci marar kauri mai hannun breziyya ta ce "honey yanzu haka kana ina?...." ya ce "ina tare da Major a gidansa na Ƙwarimpa...." A ɗan ruɗe ta ce "me! Uncle Deen kuma...." Ya ce "wait kar ki damu kinsan dai Major bashi da case akan mu, daman Daddy ne baya son tarayyar mu amma kamata yayi naje na sameki a can gida...." Cikin nuna farin ciki ta ce "okay zan zo na sameka....." tana kaiwa nan tayi saurin katse wayar sakamakon jin motsin mutum yana nufo room ɗinta.... shima a ɓangarensa sauƙe dogon numfashi yayi tare da manna wayar a ƙirjinsa yana sakin ƙayataccen murmushi, daga bisani ya jefar da wayar saman bed ya shige Bathroom yana ɗaure da towel a kunkuminsa, Mohandas inba gaya maka akayi ba bazaka taɓa cewa Christal ne ba saboda zubinsa da kalar ɗabi'unsa irina musulmai ga kyautatawa.... Around 3:30PM Minal ce cikin shirinta taɗau wanka kamar zataje party, tana sanye da shadda less tasha ɗinkin doguwar riga har ƙasi, style ɗin ɗinki gaba ɗaya zigzar wuta ne daga sama har ƙasa, tasha takalmi mai tsini blue kalar shadda less ɗinta sai sarƙa da ɗan kunne blue colour, da gyale shima blue colour, handbag shima blue, kwalliyar fuskarta kuwa kamar wanda aka tsara mata daga ƙasar waje hatta eyelashes ma blue, lips ɗinta ne kawai ya kasance red a yayinda girarta da kwallin ido da kuma eyeliner suka kasance Black colour, sauƙowa falo tayi tana ƙamshin turare ta tarar da Pinky da Rukky da kuma Ummy da Ƴar Tiny suna kallo, Ƴar Tiny ce ta ɗago tana kallonta ta ce "Aunty ina jaki je?..." Harara Minal ta watsa mata ba tare da tayi magana wa kowa ba ta nufi hanyar ƙofar fita daga falon bata ankara ba taji muryar Abbah yana faɗin "ina zaki je ?...." Dasauri ta waiwayo tana kallonsa a yayin da ya ƙarasa sauƙowa daga upstairs yana fuskantar ta tare da goya hannayensa ta gaban ƙirjinsa, Ƙiƙƙina ta fara masa tana kai ƙwayar eyes ɗinta kan sauran yaran gidan, A tsawace Abbah ya ce "ki buɗe baki kiyi mun magana...." a tsorace ta ce "Abbah bikin ƙawata zanje kuma Ni ce babbar ƙawa...." fuska a haɗe Abbah ya ce "idan zaki fita kinfi ƙarfin sanarwa cewar zaki je wani guri?...." kai ta sunkuyar ƙasi tana wasa da yatsun hannunta, Sai ji tayi ya ƙara cewa "wato Mohandas ya ƙira ki cewar yazo Nigeria Koh? shine zaki je ku haɗu, toh bari kiji duk wayonku a tafin hannuna kuke, tin sauƙar Mohandas a airport na sani domin akwai ma'aikata na da yawa acan, sannan yana shiga gidan Razhdeen security gidan suka ƙira ni suna sanar mun, na gaya miki bana son soyayyarki da Christal, bawai bana sonsa bane kawai addininsa ne banaso ki fita harkarsa na gaya miki, saboda ku muka yanke zumunci tsakanina da mahaifinsa, mahaifinsa baya son sa dake nima kuma haka amma kun ƙi rabuwa, Amma zanyi maganinki zan nemo miki wani ne na Aura masa ke, kuma kada na kuskura naga ƙafarki a waje....." Minal gaba ɗaya jin kanta take kamar ta sheƙe kanta gaba ɗaya hawaye duk ya wanke mata fuska cikin kuka take faɗin "Abbah wallahi inasonsa...." A fusace Abbah ya ce "kisa ya musulunta indai har kina sonsa in ba haka ba bake ba shi...." Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai ta nufi upstairs da gudun gaske tana kuka ta haura kai tsaye room ɗinta ta nufa.... Shima Mohandas yana zaune a falo yasha kuptarsa maroon colour yasha kyau sosai ga sajen nan ya zaunu sai faman pressing phone ɗinsa yake yana jiran isowar abar ƙaunarsa, yana cikin zaman kaɗaici saiga Deen ya fito yana sanye da baƙar jallabiyansa wanda ya tsaya masa a iya gwiwa dake jallabiyan da dogon wandonsa, Gaban rigar yasha aikin wuta ga kayan yabi shape ɗin jikinsa gaba ɗaya, kayan ba ƙaramin masa kyau suka yi ba gasun kama jikinsa matuƙa sai kayan suka ƙara bayyanar da ƙirar ƙarfin jikinsa, Sumar kan nan ya yi masa kyakkyawar gyara gashi a kwance lupp har ƙasin kafaɗa sai sheƙi yake yana fitar da wani irin ƙamshi na daban ga ya haɗu da ƙamshin turaren jikinsa gaba ɗaya gidan ne ya turniƙe da ƙamshi, yana riƙe da key ɗin motarsa ya tsaya yana kallon hanyar fita a hankali yake motsa lips ɗinsa ya ce "Are you finish?..." Mohandas tin daga kan takalminsa har zuwa kan sumar kansa yake bi da kallo sakin baki yayi gaba ɗaya Deen ya burge shi duk da kullum acikin burge shi yake amma na yanzun wanka ya ɗau sama da yawa, Uncle Deen ganin Marshall sai ƙare shi yake da kallo yasa shi haɗa rai fuska ba annuri ya ce "bana son kallo fa, nace ka kammala?...." Murmushi Marshall ya yi sannan ya ce "kai ɗin ne Major sai a slow, amma ina zamu je?...." juyowa Deen ya yi yana kallonsa ya ce "ina kace na rakaka?...." Marshall ya ce "Ohoooo na tuno, wai waran dreamer takan? toh ai nima happiness ɗita tana nan zuwa don haka na fasa fita....." Uncle Deen kallonsa yake cikin takaici domin shima yana muradin ƙara ganin yarinyar, kafin Uncle Deen ya motsa baki yayi magana yaji wayar Marshall tana ringing hakan yasa ya haɗiye abinda zai furta, Murmushi Marshall ya saki tare da faɗin "gata ta ƙira wata ƙil tana bakin gate ta iso...." Ɗaga ƙiran yayi yaga video call ta ƙira, ganin ta a zaune tsakiyar gado sai kuka take yasa shi tsorita a ruɗe ya ce "meya faru dake Beb?...." tana kuka ta ce "kayi haƙuri honey Abbah ya dakatar dani...." cikin rashin jin daɗi Marshall ya ce "taya Abbah yasa nazo ƙasar?...." cikin kuka take faɗin "An ƙira Abbah an sanar masa zuwanka, kasan Abbah yanada mutane daga airport har gidan da Uncle Deen yake...." A hankali ya furta "Oh my God! yanzu ya zanyi na haɗu dake? ga can gidanku akwai tsaro na musamman balle nace idan Abbah ya fita aiki nazo, ya zanyi?...." ya ƙarasa maganar ciki ciki kamar wanda zaiyi kuka, Uncle Deen ganin zancen su yaƙi ƙarewa yasa shi cewa "Hmmm! na tafi if you finish your madness u can follow me ....." yayi maganar tareda nufan bakin ƙofa zai fice, Shima Marshall ganin bazai iya juran ganin kukan Minal ba yasa shi cewa "please my wife stop dis cry I don't wanted, ina zuwa zan ƙira ki daga baya...." yana sauƙe ƙiran ya ɗora wayan saitin zuciyarsa yana sauƙe numfashi daƙer, cike yake da damuwa amma sai dai babu mafita, miƙewa yayi yana jan ƙafa daƙer yayi waje shima, a cikin mota ya tarar da Deen yana zaune a driver seat, buɗewa yayi ta gefensa ya shige lokaci guda damuwa ta bayyano ƙarara akan fuskarsa, Ganin haka yasa Uncle Deen kawar da kai gefe yana shirin karya kwana zai nufi hanyar gate, A wannan lokacin har sukayi nisa babu wanda yayi wa kowa magana, shi Uncle Deen bai iya rarrashi ba balle ya bashi haƙuri akan damuwar da yake ciki, shi kuwa Marshall baƙin cikinsa shine ba lallai har ya tafi yaga Minal ɗinsa ba tinda har Abbah yasan yana ƙasar, zuwa aiki ma zai iya dakatar da Minal har sai ya bar Nigeria, Uncle Deen tinda suka fara tafiya ko sau ɗaya bai juyo ya kalli yanayin da Marshall yake ciki ba, Da haka har suka isa yankin mabarata, Dasauri Uncle Deen ya danna burki a dai-dai wurin cike da mamaki yake bin wajen da kallon ganin gurin ya hargutse da kiɗe-kiɗe, ga yanda mabaratan nan suka zagaye tsakiyar ƙwalta sai gurin yayi circle duk suna zazzaune sai faman bubbuga ƙwanikansu suke a kan ƙwalta suna rera waƙa, Ita kuma Ƴar Amana tana tsakiyar su sai ɗirkar rawa take tana juyi, babu hanyar wucewa duk wani mai mota ko napep ko mashin yazo wucewa ta bangaren dama sai dai ya juya baya amma duk sun tushe hanyar wucewa suna zazzaune wasu tsofaffi ne wasu kuma madaidaita, Ƴar Amana ce kawai ta kasance mai ƙaramar shekaru a cikinsu, haka zalika duk wanda yazo wuce wa ta bangaren hagun shima sai dai su juya kamar yanda su Uncle Deen suka fito suma inda ace shigewa suka zo yi sai dai su kowa baya domin bazasu bada hanya ba, already gomnati ta mallaka musu yankin da gidajensu a ata gefe guda, Uncle Deen idonsa ne suka sauƙa akan Ƴar Amana wacce take ta shan rawa, su kuma sauran suna zaune suna bada sautin kiɗa tare da rera wakokin gargajiya domin na zamani duk cikinsu babu wacce ta iya, A hanzarce Marshall ya juyo yana kallon Deen tare da faɗin "Nan ɗin mai akeyi ne haka?" cike da mamaki yake bin Ƴar Amana da kallo ganin irin rawar da take, a hankali yake motsi da lips ɗinsa ya ce "Nan ne wajen da kace na rakoka...." Marshall ya ce "amma waje kamar waran ƴan gala?..." juyowa Uncle Deen ya yi yana kallonsa ya ce "kana ganin tsofaffin mata kace waran ƴar Gala?..." Ɗaga kafaɗu Marshall ya yi tare da faɗin "naga kamar masu neman temako ne, amma shine zasu tare hanya subar yarinya ƙarama tana musu rawar ƴan China...." murmusawa Uncle Deen ya yi tare da faɗin "su baka ga aikin da suke yi bane?...." "Of course naga su suke ƙarfafa mata gwiwa suna tayata kiɗa, But ina Dreamer ɗinka? Hope ba'a nan take ba...." ƙayataccen murmushi ya saki a karo na biyu ya ɗago da yatsarsa yana nuna wajen da mutanen suke eyes ɗinsa akan Ƴar Amana ya ce "ita ce yarinyar...." Dasauri Marshall ya juyo yana kallon Uncle Deen ya ce "Whattttttt! kar dai kace ita ce yarinyar mai rawan?....." kafin Uncle Deen ya juyo ya bashi amsa har Marshall ya yi saurin buɗe murfin mota ya fice, kai tsaye waran su ya nufa, yana zuwa ya fara ɗaga musu hannayensa biyu sama tare da dakatar dasu da cewa "ku dakata! Ku dakata!! Ku dakata haka....." kafin kace mai gurin yayi tsit idanuwansu akansa, sai wata tsohuwa ce tayi ƙarfin halin cewa "meye damuwarka damu? nan yankin mu ne sai muyi abinda muke so...." wata daga ciki itama ta ce "idan wucewa zakayi yau mallakarka sai dai ka juya baya ai ba nan ne kaɗai hanyar wucewa ba...." Marshall yasau ajiyar zuciya tareda faɗin "kunga kuyi haƙuri, ba wai dakatar daku zanyi ba nima ɗan uwanku ne mai son kiɗe-kiɗe amma yanzu dai ku ɗan ara mun yarinyar ku zanyi magana da ita....." wata daga cikinsu ne ta buɗe baki zatayi maganar cewa kurmiya ce! Ƴar Amana tayi saurin ɗaga mata hannu akan tayi shuru karta sanar masa, domin duk abinda zai ce zata ji shi mayarwa ne bazata iya ba, A hankali take taku cikin ƙasaita ta nufi yanda yake ta tsaya dab dashi tana fuskantarsa tare da goya hannayenta ta gaban ƙirjinta, Marshall haɗiyar yawu yayi wanda bai san ya yi shi ba, gaba ɗaya yarinyar ce ta fara bashi tsoro ganin irin ƙarfin halin da take da shi, still ya tuno da cewa ita ce take wahalar da Major acikin mafarki gaba ɗaya sai yaji wani irin gumi ya yanko masa, tin daga kan ƙafarta ya fara binta da kallo ganin tana sanye da farin takalmi toes, sai wani gajeren wando wanda ya tsaya mata a iya gwiwarta da rigar Best wanda bai ƙarisa rufe cibiyarta ba daga nan eyes ɗinsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar ta wanda yake a ɗaure babu wani annuri a tattare da ita, ga wasu murɗaɗɗun gashi wanda ya baje mata har gadon baya, yana gama ƙareta da kallo ya juya da gudun gaske ya nufi yanda motarsu take, a cikin motar ya tarar da Uncle Deen zaune yana kallon duk abinda yake faruwa, ba tareda ya shiga cikin motar ba ya zura kansa ta cikin glass yana haki yake cewa "Major haƙiƙannin gaskiya na yarda cewa wannan yarinyar itace take fito maka acikin mafarki domin zubinta irin na Aljanu ne sak, Amma sai dai yarinya ce ƙarama domin ko Nono bata fara ba, bari na koma gurinta yau zanyi magana da Aljana....." haka ya juya ya koma yanda ya baro ta, Shi dai Uncle Deen yana jinsa amma ya kasa cewa komai saboda Marshall yana shirin bashi dariyar da rabonsa daya yi tin yana yaro ƙarami.... Marshall tsayawa yayi shima yana fuskantar ta saida yayi gyaran murya kafin ya soma magana kamar haka "Am da farko dai sunana Marshall Mohandas daga ƙasar U.S, ke ina son jin sunanki....." Ƴar Amana gyara tsayuwarta tayi idonta akansa, ta ɗago da hannunta ɗaya tana yiwa mutanenta alamar su gaya masa, Gaba ɗayansu a tare suka buɗe baki waren faɗin "ƳA DAGA ALLAH...." ɗan zaro eyes ɗinsa ya yi cike da mamaki ya ce "kenam daga sama ta faɗo?...." baki a haɗe wajen cewa "kana tantama ne?...." Dasauri yake girgiza musu Kai alamar "a'ah..." sunkuyar dakai yayi ƙasi yana maganar zuci "Tabb Jesus Christ! ban taɓa ganin Aljana ba eyes to eyes ba sai yau...." bai ankara ba yaji ta ɗago hannu sama ta riƙo haɓarsa sai faman juyar masa da idanu take, cikin rashin fahimta yake binta da kallo jikinsa har ɓari yake jin Aljana ta taɓa shi, wata tsohuwa ce ta ce "tana maka alamu ne daka zo kuyi rawa...." zaro ido waje ya yi tare da faɗin "Rawa kuma? okay tam ku jirani ina zuwa....." Juyawa yayi ya nufi motarsu, yana isa ya kuma tsayawa a jikin motar yana fuskantar Uncle Deen ta glass ya ce "wallahi Major tsoronta nake ji kuma tace muyi rawa...." murmusawa Uncle Deen ya yi sannan ya ce "kar ka damu mutum ce kamar kowa, kaje kayi abinda ta saka...." Marshall ya ce "okay tam kunna mana waƙa...." Ba musu Uncle Deen yasa hannu ya kunna Audio domin yana son faranta mata so yake yaga murmushinta ko sau ɗaya ne.... Kafin Marshall ya isa wajen har Ƴar Amana ta fara cashewa da rawa jin sautin ƙida mai daɗi, shima Marshall jujjuyawa ya fara yi yana rawa, kafin kace mai sauran mabaratan ma duk sun mimmiƙe suma suka fara jujjuyawa da masu ƙarfin jiki da marasa ƙarfin jikin duk rawan suke, Gurage suma haka suke rawa a zaune, Kutare suma salon rawansu daban yake har da makafi, a wannan lokacin kowa ya kasance cikin farin ciki da annashuwa, Ƴar Amana ganin yanda tsofaffi suke cashewa yasata kwashewa da dariya ba tare da sautin ya fito ba, wannan dariyar da tayi akan idon Uncle Deen tayi shi, Dariyar ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba shima yana zaune ta cikin motarsa bai san lokacin da ya sake wata ƙayatacciyar murmushi ba, babu wanda yasan da mutum acikin motar domin Black glass gare ta, Marshall shima lokaci guda ya tsinci kansa cikin farin ciki duk wata damuwa babu ita, wasa-wasa shima ya zage sai girgizawa yake yana tintsirewa da dariya, saida sukayi rawarsu mai isarwa sannan yaje ya ɗebo tilin maƙudan kuɗaɗe yazo ya rarraba musu, ya tafi yana ɗaga musu hannu cikin nuna farin ciki, suma sunyi matuƙar farin cikin kasancewa da shi, Da haka Uncle Deen yaja mota suka tafi cikin kewar rashin ganin Dreamer sa..... 𝙄𝙉𝙏𝙀𝙍𝙑𝘼𝙇 Da yamma liss misalin ƙarfe 5 Baiwar ALLAH tana zaune a ɓangaren swimming pool wanda ya kasance a bakin ruwan akwai jerukan kujeru na alhurma masu ƙayatarwa da tables, hakan na nufin waran shakatawa kenam, tana zaune akan kujera ita kaɗai tasa ruwa a gaba wanda ya kasance launin blue gare shi, tayi tagumi da duk kan alamu doguwar tunani ta faɗa, fuskarta ya nuna tsananin damuwa ƙarara ita kaɗai tasan matsalar dake damunta, tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafaɗarta, a zabure ta miƙe tsaye tare da juyowa tana son ganin wanda yake bayanta, Ganin Roshan yasa ta kawar da kanta gefe tana faɗin "taya kasan ina nam?...." dogon numfashi ya sauƙe tareda faɗin "Ummy ce ta sanar mun cewa taga kinyo nan, wai me yake faruwa ne naga kamar bakida lafiya...." "Lafiya ta ƙalau...." a takaice tayi maganar fuskar ta na kallon gefe, Murya ciki-ciki ya ce "Ammata me yasa kike gudu na? bakya son haɗuwa dani! Abbah ya ce na ɗauke ku ke da Ummy kuje ku zaɓi kayan furnitures amma ke sam kin ƙi zuwa sai da iya Ummy na tafi, me yake faruwa?...." Hawaye ne yake shirin zubo mata tayi saurin sunkuyar dakai saboda kar ya gane a taƙaice ta ce "babu komai, bani da lafiya ne ..." A ruɗe ya ce "Subhanallahi Ammata bakida lafiya shine baki sanar mun ba? meye amfanin aikin likitanci na indai bazan iya kula dake ta hanyar bada magani ba..." ya jawo ta jikinsa yana faɗin "gaya mun me yake damunki? bana son ganinki cikin damuwa...." lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka daman jira take a taɓota tayi kukan da ya tsaya mata a rai, a firgice ya zaro handkerchief ɗinsa daga aljihu yana ƙoƙarin goge mata hawayen fuskarta, shima kamar zai fashe da kuka yake faɗin "Ki daina mun asarar hawayenki mai matuƙar tsada, dan ALLAH Ammata nah, ina jin zafin haka a raina....." Sam bata son Auren nan amma gaba ɗaya kamar wanda aka ɗaure mata baki ta kasa sanar masa, Soyayyar Uncle Deen zai hallakata, ta kamu da matsanancin sonsa bana wasa ba, inta tuno cewa bashi zata Aura ba sai taji kamar ta hallaka kanta, cikin takaici da baƙin ciki bata san lokacin data ɗago daga rungumar da yayi mata ba, tasa hannu da iya ƙarfinta ta ture shi baya daman yana dab da ruwa, ƙafarsa ta zame sakamakon tsantsin tiles dake wajen ya yi baya ya tsunduma cikin ruwan swimming pool, Da sauri ta nufi hanyar fita daga part ɗin tana kuka, har ta fara hawa saman beni zata fita ta waiwayo bayanta jin ko motsinsa bata ji acikin ruwan, Gaba ɗayansa ya nutse ciki sai saman ruwan da ya shafe, A tsorace ta juya da gudun gaske ta nufi bakin ruwan tana ƙiran sunansa "Ya Roshan! Ya Roshan!! Dan ALLAH ka fito kar ka mutu a ciki, na shiga uku na, banaso nayi sanadiyar mutuwarka dan ALLAH Ya Roshan, wayyo Allah nahhh...." Ganin babu wata mafita yasa itama ta faɗa cikin ruwan, dake bata iya ruwa ba haka ta rinƙa facal-facal a cikin ruwan, tana nutsewa tana ɗagowa da haka itama ta nitse numfashi yana shirin ɗagewa, Lokaci guda saiga Roshan ya ɗago saman ruwan yana riƙe da kunkumin Baiwar ALLAH, tana fitar da numfashi sama-sama har ta sume akan faffaɗar ƙirjinsa, Ɗarata yayi saman kafaɗar sa yake yana taka matakalar da zai fidda shi daga cikin ruwan, Kwantar da ita yayi a ƙasin tiles duk jikinsu a jiƙe jirip, a hankali ya haɗe hannayensa biyu ya ɗora kan ƙirjinta yana dannawa a hankali daga bisani kuma yakai fuskarsa saitin nata yareda ɗora ɗan lips ɗinsa kan nata yana hura mata iskar bakinsa, cikin lokaci ƙanƙani numfashin ta ya dawo a hargitse, tari ta fara yi tana amar da ruwan da tasha, daga baya ta buɗe lumshashshun idanuwanta kamar maijin bacci, yana kwance ta gefenta eyes ɗinsa akanta itama shi take kallo haka suka shiga kallon juna ba tare da wani ya ƙibta a cikinsu ba, A zabure suka dawo hayyacinsu jin magana kamar daga sama ance "iyyyeee soyayya haka...." Ummy ce tayi maganar tare da juyawa da gudu tabar wajen, Suma tashi sukayi, kafin ya ankara harta bar wajen da gudu itama, tsayawa yayi yana kallon ta har ta ƙule masa, shima jiki a jiƙe yake shirin barin part ɗin.... Da Daddare misalin ƙarfe 9 bayan an gama dinning, Roshan ne zaune akan sopa 3 seater hannunsa riƙe da ledar Maganinnuwa har da Allurai, yayi tagumi alamar dogon nazari yake, Ummy ce ta sauƙo daga upstairs da tarar da shi a cikin wannan halin, a hanzarce ta nufi wajensa tana ambaton sunansa "Yaya Roshan!.." shuru bai ɗago ba ta ƙara maimaita ƙiran sunansa har sau kusan biyar saida ta bubbugi kafaɗarsa tukun yayi firgitt ya ɗago yana kallon Ummy, Zama tayi a kusa da shi ta zuba masa eyes cike da mamaki take faɗin "Ango kuma a cikin damuwa? Yaya Roshan me yake damunka alhalin kana shirin mallakar farin cikinka, kamata yayi a ganka cikin farin ciki...." Ɗan tsuka yaja acan cikin harshensa yana dafa goshinsa ya ce "bansan me yake damun Ammata ba, gaba ɗaya guduna take bata son kasancewa tare da Ni, duk hanyar da zai haɗamu bata ƙaunar biyo wajen bansan me yasa ba...." Sauƙe numfashi Ummy tayi tana hararar Roshan ta ce "Ɗazu ba ku na gani a swimming pool ba?...." Girgiza Kai yayi cikin nuna damuwa ya ce "Ni na bita wannan wajen sannan da hannunta ta tura Ni cikin ruwa tana kuka zata bar wajen, bansan meya dawo da ita a wannan lokacin ba itama ta faɗa ruwan, Nifa na fahimci kamar ba sona take ba....." Zaro ido waje Ummy tayi tare da faɗin. "koda wasa kar kayi tunanin nan, domin Aunty Baiwar ALLAH tin kafin ku dawo take muradin son ganinka, idan taga hotonka har wani irin murmushi take saki na farin ciki, Zai iya yuwa yanzun kunyarka take ji saboda an kusan ɗaura muku Aure, daman indai Amarya tanada kunya toh har ayi Auren bata son haɗa Ido da Angonta....." kallonta yayi ya ce "wai da gaske kike?...." cikin fara'a ta ce "sosai ma...." Sai yanzu yaji zuciyarsa tayi wasarrr, murmushi ya saki tare da faɗin "Ma sha ALLAH! indai rashin ganina shi zaisa tayi farin ciki to Ni kuwa nayi Alƙawari har a ɗaura Aure bazan ƙara barin mu haɗu ba, tinda Amaryata kunya gare ta...." Itama Ummy murmushi ta saki tare da kai hannunta kan ledar hannunsa tana faɗin "meye wannan?..." Ɗan harararta yayi tareda faɗin "to Sarkin kwaɗayi pharmacy ne na ɗauko a medicine room zan bawa Matata ta ce mun tana jin zazzaɓi, Kuma na bubbuga ƙofar ɗakinta taƙi buɗe mun...." Ummy ta ce "ai nasan bazata buɗe ba indai tasan kaine, kawo nakai mata...." Ya ce "Ok please kiyi ƙoƙarin ganin tasha maganin sannan kiyi mata Allurai tinda kema Doctar ce...." Murmushi tasau tare da cewa "Insha ALLAH...." ya miƙe tare da nufan upstairs dazai kaishi part ɗinsa, har yayi nisa ya juyo ya ce yana faɗin "gobe bazaku tashi ku ganni ba saboda da sassafe zamu tafi ƙasar Jidder Ni da twins, na baki Amanar Matata....." Ta ce "to Allah ya kiyaye hanya My Sweet Bros...." ta nufi room ɗin Baiwar ALLAH shi kuma ya wuce part ɗinsa, Ummy a hankali taje tana knocking door tareda ambatar sunanta "Aunty Daughter! Aunty Daughter ki buɗe ƙofa Ni ce pah......" Kafin ta ƙara furta wani abu har tazo ta buɗe mata, murmushi Ummy tayi tana faɗin "wato a Yayana ne baza'a buɗe ba koh?..." Baiwar Allah ta koma ciki tare da ɗosana mazaunanta a bakin gado, Itama Ummy zama tayi dab da ita tana kallon ta cike da mamakin ganin yanda ta rame tayi fari sol kamar ba jini a jikinta, Baiwar Allah kallon front ɗinta take ko annuri babu a fuska, Ummy ta ce "am daman magani akace na kawo miki, sannan zanyi miki allura..." Baiwar Allah kallon Ummy tayi ta ce "waya ce miki bani da lafiya?...." Ummy ta ce "labarin zuciya a tambayi fuska, gashi jikinki ya nuna cewar bakida lafiya..." ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi frig ta ɗauki ruwan jarkan ta koma side ɗin Baiwar Allah ta zauna, buɗe ledar tayi ta curo Maganinnuwan gaba ɗaya tana ɓarewa tareda ƙoƙarin bata, Girgiza Kai Baiwar ALLAH tayi ta ce "Ni lafiyata ƙalau bazan sha ba....." Ummy cikin ɓacin rai ta ce "wallahi sai kin sha ko kuma naje na haɗaki da Abbah domin shi yace na kawo miki...." Jin haka yasa ta karɓa ta watsasu a baki tare da kafa bakin jarkan ta korasu da ruwa, Bayan ta kammala shan su gaba ɗaya, miƙa hannunta tayi Ummy tayi mata Allurai, tashi Ummy tayi tace "saida safen ki...." tabar ɗakin domin ta fahimci kwana biyun nan Baiwar ALLAH bata son yiwa kowa magana, Itama tashi tayi taje ta rufe ƙofar ɗakinta sannan ta shige bathroom tayi wanka, tazo tayi shigar sleeping dress ta ƙwanta zuciyarta cike da tsananin kewar Uncle Deen da son kasancewa tare da shi sannan tana muradin ganinsa..... Asubar farko Yaya Roshan ya kammala haɗa jakarsa wanda zai tafi da ita domin zai iya kasancewa suyi kwana uku kafin su dawo, ya kammala shirinsa tsab ya fice daga part ɗinsa zasu je masallaci, a falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa, a tare suka fice.... Shima a ɓangaren Uncle Deen bayan ya dawo daga masallaci zama yayi akan ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon farko, zaro wayarsa yayi yana ƙoƙarin kunna shi domin wayar a kashe ta kwana, yana cikin wannan yanayin saiga Marshall ya sauƙo daga upstairs yana sanye da sleeping dress mai botula ta front ɗin gaba, rigar ta sauƙa masa har gwiwa sai gajeren wandon dake ciki, yana hamma ya ƙarasa sauƙowa falo domin ba ƙaramin yunwa ya tashi da shi ba, zama yayi beside Uncle Deen yana faɗin "am hungry too...." Uncle Deen ba tareda ya kalle shi ba ya ce "go and inter kitchen...." Marshall ya ce "okay kasan dai ina yin girki ko? let me go and find us food...." ya ƙarasa maganar tare da miƙar hanyar kitchen.. Ba jumawa Uncle Deen ya soma jin knocking, a hankali ya furta "WHO?..." ta waje yaji ance "your twins ..." jin muryar Roshan yasa shi miƙewa ya nufi bakin ƙofa, yana buɗewa saiga Roshan ya kutso kai tare da rungumar Uncle Deen cike da nuna farin ciki, Shima Uncle Deen yayi farin cikin zuwan Roshan, A tare suka ƙarasa shiga ciki tare da zama guda ɗaya suna kewar juna, saiga Marshall shima ya fito daga kitchen yana faɗin "wa nake gani kamar S.D (surgeon doctor)...." miƙewa Roshan yayi suka rungumi juna yana tambayarsa yaushe yazo... Marshall ya ce "wallahi jiya isowata, am glad to see you..." shima Roshan cikin nuna farin ciki ya ce "me too..." suka zauna gaba ɗaya cike da kewar juna, suna cikin tattaunawarsu sai suka ji an buɗe ƙofar falo, dasauri suka waiwaya ganin Minal yasa Marshall saurin miƙewa tsaye, cike da mamaki Uncle Deen yake binta da kallo, ƙarasowa tayi ta zauna akan kujera tana gaishe su, Uncle Deen ne yayi maganar cewa "meya kawo ki da sassafen nan?..." Roshan yayi saurin taran yawunsa ya ce "sawa tayi nayiwa Abbah ƙaryar da ita zamu tafi ƙasar Jidder, ita kuma ta tsara cewa zata zauna anan gidan ita da Marshall har mu dawo, kuma nima inaga gwara su fahimci juna akan tsarin yanda zasu gudanar da soyayyar su, Su samawa kansu mafita...." Uncle Deen juyawa yayi yana kallon Marshall sannan ya juya eyes ɗinsa kan Minal tare da faɗin "tayaya iyayen Mohandas zasu barshi ya musulunta and then how comes Minal zata koma christal?....." Marshall gaba ɗaya ya rasa yanda zai ɓullo wa al'amarin, Roshan ne ya ce "duk abinda ya kamata na sanar yanzu na riga da na faɗawa Minal, ita kuma zata sanar wa Marshall idan ya amince toh Ma sha ALLAH! Ni kuma zanyi ƙoƙarin fahimtar da Abbah, idan kuma bai amince ba ya rage nasu, shawara mai kyau dai na bada bayan wannan shawaran bani da ta cewa....." Uncle Deen cikin rashin fahimta yake bin Roshan da kallo ya ce "wani irin shawara ne haka?...." Roshan ya ce "gaskiya zai mun nauyin furtawa a gaban Marshall saboda bansan wani irin kallo zai mun ba...." ya ƙarasa maganar idonsa akan Marshall! Minal ce ta buɗi baki ta ce "Yaya Roshan ya sanar mun cewa nace wa Marshall idan har ya aminta kuma yana son Aura na toh ya musulunta a ɓoye ba tareda iyayensa sun sani ba, shi kuma zaiyi ƙoƙarin fahimtar da Abbah....." A ruɗe Marshall ya ɗago yana kallon Minal, cikin ƙanƙanin lokaci damuwa ya bayyana ƙarara akan fuskarsa, Uncle Deen ya ce "Whattttttt? kunsan abinda kuke shirin aikatawa kuwa?...." kafin ya ƙarasa maganar yaji Marshall ya ce "wannan shine mafita, daman na daɗe ina tunanin haka, inhar zaku bani goyon baya Ni kuwa zan musulunta duk da nasan duk randa mahaifina ya gano dole zai kashe Ni ......" Roshan ya ce "Insha ALLAH babu abinda zai faru dakai, muna tare dakai har abada...." Minal farin ciki kamar bazata mutu ba, Uncle Deen kuwa cewa yayi "ba dani za'ayi wannan cin amanar ba...." Roshan ya riƙo hannun Uncle Deen ya ce "please my Man Kai ɗan hannun daman mahaifin Marshall ne, zaka san yanda zakayi ka fahimtar da shi sannan mahaifiyarsa tamkar ɗa ta ɗauke ka itama zaka fahimtar da ita....." Uncle Deen yana pressing phone ɗinsa ya ce "Hmmmmm!!!...." bayan haka bai ƙara cewa komai ba, Roshan ya ce "ok yanzu dai ba lokaci domin Muna so zamu je ƙasar Jidder Ni da My Man, kai kuma Marshall ka zauna da Minal anan har mu dawo, amma please kar ku fita ko ina domin akwai mutanen Abbah, Ban taɓa masa ƙarya ba amma yau nayi masa saboda soyayyarku, ina tausayin masoya sosai....." Gaba ɗayansu murmushi sukayi domin sun san Roshan Romeo ne daman, Banda Uncle Deen wanda ya tsayar da eyes ɗinsa akan Roshan jin ya furta dashi za'aje Jidder, Roshan shima kallonsa yayi ya ce "Any problems?...." Uncle Deen miƙewa yayi tare da faɗin "I'll no go anyway..." ya ƙarasa maganar tare da miƙar another falonsa wanda zai kaishi har bedroom ɗinsa, Roshan ya ce "please my Man Abbah ne yace muje...." "I tell you bazan je ba...." ya yi maganar bayan ya shige falo na biyu... Roshan ya ce "okay let me go domin lokaci yanata ƙurewa...." Marshall ya ce "Ni S.D me yake faruwa da Major ne naga ya baro can gidan..." Roshan ya ce "oh bai gaya maka ba?...." Marshall ya ce "ka dai san halin mutumin bazai tsaya bani wani dogon labari ba...." Roshan ya ce "Okay...." Nan Roshan ya kwashe komai ya sanar wa Marshall, Marshall Sam baiji daɗin abinda ya faru tsakanin Abbah da Major ba... Shi dai Roshan tashi yayi ya fice, yana fita shima Marshall ya miƙe tare da nufan part ɗin Uncle Deen har bedroom ya samo shi yana kwance, Zama Marshall ya yi a bakin gadonsa yana faɗin "seriously Major baka kyauta ba, Umarni Abbah ya bada cewa ku tafi ƙasar Jidder tare amma ka ƙara bijirewa, idan yaji bazaiji daɗi ba, please kayi haƙuri ka tashi ka shirya kabi bayan Roshan, idan har kanason farantawa mahaifinka...." Marshall ba ƙaramin nasiha da shawarwari ya bawa Uncle Deen ba, jikin Uncle Deen ne yayi sanyi ya tashi sannan ya shige bathroom ya yi wanka, ya fito ya shirya tsab sannan ya fice, A falo ya wuce Marshall da Minal yayi ficewarsa, yana fita kuwa yasa sojansa akan ya kaishi airport.... ya sanarwa Sojan akan su bi ta layin mabarata domin yana buƙatar sanya Ƴar Amana a idonsa, hakan kuwa akayi cikin sa'a kuwa idonsa ya sauƙa akanta tana zaune a bakin titi kusa da tsohuwa da jitarta a hannu tanata kaɗawa cikin zazzaƙar sauti mai ratsa zuciya..... Saida motar ta ɗan zarce kafin ta tsaya sannan saiga Uncle Deen ya zaro ƙafarsa waje ya fito cikin ƙasaita ya nufi yanda take, bata lura da shi ba sai sauƙar mutum ta gani a gabanta, dasauri ta ɗago da kanta sama tana kallonsa, Shima durƙusawa ya yi idonsa akanta, saida ya gama ƙareta da kallo sannan ya fitar da wasu kuɗaɗe a aljuhunsa ya ɗora Mata akan cinya dai-dai lokacin wata ƴar ƙaramar jakarsa ta faɗo wanda bai lura da ita ba, tashi ya yi yabar wajen ya nufi motarsa, yana shiga kuwa suka tafi, cike da mamaki Ƴar Amana take binsa motarsu da kallo ta rasa gane shin waye wannan wanda yake shirin kutsa mata rayuwa, sai a lokacin ta lura da jakar daya jefar a wajen, wannan jakar yanada muhimmanci matuƙa domin aciki har da I.D card ɗinsa na soja da national I.D card dana ƙarin matsayinsa na Major General... A zabure ta ɗauki jakar tare da miƙewa da gudun gaske take bin motar wanda basu gama yin nisa ba, babu murya balle ta kwalla musu ƙira, bata gajiya ba haka take bin motar da gudu tana ɗaga musu hannu, Domin in har yaje airport ba tare da ticket ɗinsa ba akwai matsala dole sai sun juyo kuma duk suna cikin jakar, Motar ba wani gudu yake ba amma har zuwa yanzu basu lura da cewa ana bin bayansu ba, Ƴar Amana ganin bazasu tsaya ba yasa ta ɗauki wata ƙatuwar dutsi ta ƙarawa gudunta mai har saida ta kusan iddasu tukun ta wurga wannan dutsen cikin sa'a kuwa ta sauƙa akan glass ɗin motar ta baya, Burki suka danna jin bugun abu ta bayan motarsu, Security wanda yake driving ne ya buɗe ya fice domin ganowa abinda ke faruwa, ganin Yarinya ce ta kwaɗo musu dutsi yasa shi fusata ya ɗauki hannu zai zabgeta da mari Uncle Deen ya yi saurin riƙo hannunsa, sojan juyawa yayi yana kallon ogan nasan gani yayi Uncle Deen ya girgiza masa kai tare da sauƙar da hannunsa ƙasi, Idonsa yakai kan Ƴar Amana yaga ta rufe fuskarta da hannayensa biyu tana kaɗa musu hannu alamar suyi haƙuri, Uncle Deen gani yayi jakarsa a hannunta da sauri yakai hannu yana rarumar aljihunsa yaga jakarsa ce ya jefar, Karɓar jakar ya yi tare da rungumota jikinsa domin ta temakashi a karo na farko, sai kuma yaji yarinyar ta ƙara shiga ransa, Ƴar Amana zamewa tayi daga jikinsa ta rufa da gudun gaske ta juya baya, tsaya kallon bayanta yayi daga bisani shima ya koma cikin motar suka tafi... suna isa airport jirgin yana shirin tashi, ganin Major yasa akayi saurin dakatar da jirgin kafin ya tashi, Uncle Deen ne ya nufi yanda jirgin yake bayan ya kammala register yayi komai, yana shiga ya tarar da Roshan seat ɗin da yake zaune shi kaɗai anan ya samo shi suka zauna tare, Roshan kawar da kai gefe yayi yana sakin murmushi........!!!! *TOH MASOYA NAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN KASHI NA ƊAYA SAI MUN SAKE HAƊUWA A ZANGO NA BIYU.....* *DAN ALLAH KUYI HAƘURI AKAN JINKIRIN DA NAYI MUKU WALLAHI BANI DA LAFIYA NE KU MUN UZURI....* *INSHA ALLAHU NAN BADA JUMAWA BA ZAKU SAKE GANIN UPDATE NA STEP TWO,* *YANZU DAI ALLAH YA BANI IKON KAMMALA STEP ONE....*