[8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 *D'INGISHIN KWAD'O.* *By* *Surayya Dahiru Gwaram* *(Mrs M.I.Nashe)* *Marubuciyar* *HALIN YAU* SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* *SADAUKARWA GA* *Gabadaya labarin sadaukarwa na ga Hajiya Bilkisu Garba* *(Barr B.I.Garba)* *Kalmar na gode da alherin ki gare ni ta yi kadan matuka da gaske* *Amma ina miki fatan Ubangiji ya iya miki da iyawarsa, ya kare Ki daga dukkan sharrin zamani, ya shirya miki zuria akan tsarin shari'a ya rayasu cikin imani ya kula da su fiye da kulawarki* *Surayya ta gode, ta sake gode wa Ubangiji ya taya ni godiya* *Allah ya dauwamar da zaman lafiya da bunkasar arziki a gidan auren ki* *Barr Allah ya so ki, ya sanya soyayyarki a zukatan salihan bayinsa*. *Dukkan littafin Dingishin kwado nakine, ban samu damar yi miki takwara ba Amma alkalamina ya yi miki.* *Jarumar labarin takwararki ce duk da labarin ba shi da alaqa da rayuwarki ta kowacce fuska*. *Madallah da Barista Bilkisu Garba*. *Yabo* *Ina Godiya tare da yabawa ga iyalan Alhaji Muhammad Tukur Gwaram* *Malama Amina Sani Gwaram* *Cheif Town planner Sani Muhammad Tukur* *Hon Salisu Tukur Janko(wakilin gwamna)* *D.S.E Dahiru Muhammad Tukur.* *Wrt Halima Muhammad Tukur* *Dr Abubakar Muhammad Tukur* *Dr Yusuf Muhammad Tukur* *Aliyu Muhammad Tukur* *Usman Muhammad Tukur* *Fatima Muhammad Tukur* *Umar Muhammad Tukur* *Amir Muhammad Tukur*. *Allah ya so ku ya rufa muku asiri duniya da lahira ya kore hargitsin rayuwa a tsakaninmu*. *Allah ya jiqan iyayenmu*. *Fatan alheri ga kannenna guda biyu* *Aliyu Dahiru Ibrahim(Abba)* *Zainab Dahiru Ibrahim (Husna)* *Allah ya so ku da ku da dukkan zuri'arku* *Allah ya jiqan iyayenmu*. *Godiya ga shugaban lafazi* *Mal Sadik Abubakar* *Na gode sosai Allah ya saka da alheri*. *Gaisuwar fatan alheri ga iyayen d'akina* *Haj Khadija Abdullahi Gwaram* *Haj Halima Dalha Shehu* *Haj Rabi Sani madakin Gini* *Haj Salaha Abubakar Zaria* *Haj Hafsat Sodangi* *Haj Zainab Abdul Wahab* *Haj Hadiza Bawa Sodangi* *Haj Jamila Habibu Yakasai* *Haj Ummukulsum Muhd Kumo* *Haj Hadiza Fari* *Haj Aisha Abdu Gusau* *Haj Fatima Ali* *Haj Fatima Bugaje* *Gaisuwar Sada zumunci ga aminaina* *Haj Hauwa Sa'id Yidi Gombe* *Haj Maryam Sani Abdullahi(Malaysianfabrics)* *Haj Naja'atu Harazimi* *Haj Ni'ima Bala Rabi'u* *Haj Anty Nana Musa* *Haj Bilkisu Mainaira* *Umm Muhd collection* *Haj Fatima Bakin kasuwa* *Haj Barira Btj fashion* *Haj Aisha Muhammad Umar (Mami)*. *Gaisuwar ta'aziya ga* *Hafsat Abubakar Elnafati* *Adda UMMi Allah ya jiqan Hajiya ya saka aljanna makoma* *Jinjina* *Jinjina ga marubuciyar zamani Jamila Umar Janafty* *Ba dan ke ba da littafin Dingishin kwado bai kammala ba yanzu, Surayya Dee ta gode, tare da fatan alheri mai yawa a dukkan rayuwarki* *Goro* *littafina har kullum goro ne ga y'aruwata kanwata* *Aisha Muhammad Lame* *Mafi girman nasarar da rubutu ya janyo mini haduwa da ke na kan gaba Aisha!* *A duk sadda na kalli yadda kika daukaka lamarina kika amince mini, kika gasgata ni, sai na ji kwalla na ta kwarara* *Ke ce kadai jini bai hadamu ba nake jin inama jini ya ratsamu, amma na yi imanin amincin da aka gina shi domin Allah sakamonsa aljanna* *Madallah da Aisha Lame* *Mai kayan y'an gayu na oriflame da dukkan nau'in mayuakan gyara fata.* *Lafazi writer's* *Bismillahir Rahamanin Rahim*. 1 *Shimfi'da* *Karfe d'aya da rabi na talatainin dare a garin Katsina. Ruwa ake tafkawa tamkar da bakin kwarya. Garin ya yi sanyi. Baka jin komai sai zubar ruwan sama babu kakkautawa. Jefi jefi hasken walkiya na haska sararin samaniya. A daidai wannan lokacin da galibin mutane suke kwance suna barci cikin salama da nutsuwar zuciya a dalilin yadda garin ya dauki sanyi mai dad'i. Ni kuwa kwance nake gefen gadona hawaye d'aya na bin d'aya. Zuciyata ta kai makurar wajen nauyi akan al'amarin mijina. Na tashi na yi zaune na k'ara hasken fitilar gefen gadona(dim light). Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske. Ga shi nan dogo sambal. Fari tas kuma kyakkwan gaske. Duk inda ake neman namiji mai cikar halitta ya kai. Mijine na nunawa sa'a. Irin mijin da duk macen da ta ganshi sai ta ce wow. Domin hatta yanayin jikinsa tamkar ya zaba. Ba siriri ba ne, ba shi kuma da jiki. Komai na halittarsa tamkar da kansa ya yi. Mafi yawa k'awayena suna mini kallon na tafka sa'a. Idan kuwa muka yi hoto aka ga ni. An dinga fad'in kallon wannan mijin na ki kad'ai ya isa ya wanke miki zuciya. Hawayen idona ya sake yawaita a dalilin yadda tausayin kaina ya kama ni. Ni da kaina nasan kyawunsa ne abin da na gina aurena a kai. Cikin jerin abubuwa guda hudu da Annabi ya ce a duba a yayin aure. Annabi addinin mutum ya horemu mu fara dubawa. Ni kuwa sai na fara duba kyau, kyau ma iya na siffa na bi, ban nazarci na zuciya ba. Na shafe shekaru ina kuka sosai. Kukan kaico, kukan nadama. Amma a yau kukan ya BANBANTA da na baya. Domin kukan da nake yi a yanzu na kewa ne, na tsantsar bukatar a kad'aice da ni ne. Yanayin zafi da damina yana matukar sanya y'aya' mata a cikin sha'awa mai yawa, yayin da maza tasu sha'awar tafi tsananta da sanyi. Na tsananta tunanin watanni da na kwashe a rataye. To a rataye mana, domin a baki ne nake matar aure. Yau watanni takwas kenan wani abu na auratayya bai gitta a tsakaninmu ba. A shekarun baya idan wani ya fad'a mini zamu shiga irin wannan yanayin ni da Baban Amrah zan musanta ne, na kuma ga beken mutum tare da jefa shi sahun y'an adawarmu. Sai gashi yau da gobe ta kawo mu wani irin bigire da muke rayuwa cikin wani mawuyacin hali kamar ba soyayya ce ta hada mu ba. Tamkar ba mune muka so juna ba. Na sani, shima ya sani a ka'idar shari'a mace ta kan yi hak'urin rashin namiji ne na watanni hudu matukar ba aure ne bata da shi ba. Amma a wannan zamanin da muke ciki mazaje na rataye matayensu na tsawon shekaru basu take su ba. Ba kuma sa jin d'ar ko tsoron had'arin da suke jefa mataye a ciki. Ni da kaina a yau tsoron Ubangiji ne zai sa na hadiye abin da nake ji a gangar jikina. Ba dan nasan hukuncin wacce ta yi zina da aurenta ba, da tuni na afka mata, tunda mazan wajen suna ganin k'uruciyata sabanin nawa mijin kallon na yi masa tsufa yake yi mini. Mata da yawa sun halaka a dalilin wannan matsalar. Maza sun yi sanadin jefa matan aure a cikin masifar zina da aurensu. Musulunci ya kange mace daga kowacce irin mu'amala da namijin da ba muharraminta ba. Mijinta kad'ai aka lamunce ta yi huld'a da shi kaitsaye. Hatta muharraminta ma akwai geji a mu'amala. To amma mazan yau loakcin yin hira da matansu ma basu da shi. Zai yini a wajen neman kud'insa. Idan ya dawo gida kuwa wayarsa ce abar hirarsa. Mace zata yiwa namiji magana, zai amsa mata hankalinsa na kan wayar hannunsa. Mace zata yi girki, ta yi kwalliya, ba za'a mata kallon rahama ba, har a gane irin kyaun da ta yi, bare a yabe ta ta ji dad'i. Ni kam tuni na cirewa kaina wannan damuwar. Na daina yin kwalliya saboda shi, na daina yin girki don ya yaba. Ina yinsu ne don iyalina. Ina yinsu dan kaina. Tuni na fita daga wannan matsalar tunda na gane bazan samu yadda nake so ba, sai na hak'ura nake yin dukkan abin da ya zame mini wajibi a matsayin ibada. Ibada kuwa yinta kake yi çike da juriya da addu'ar a karba. Abin da na kasa cirewa a raina daya ne, al'amarin shimfi'da. Juriyata ta tasamma karewa, hakan kuma na da nasaba da kasancewar jinine a jikina ba mai ba. Sannan halitta ce ban isa na zare sha'awa a tare da ni ba. Na mika hannu na zaro tissue din da take ajiye a gefen gadon. Na hau gogewa. Na dinga ambato Hasbunallahu wa ni'imal wakil a fili, na jima har na fara samun nutsuwa a tare da ni. Na jima ina tunanin na yi abin da zuciya take azalzalata ko kuwa na cigaba da jarumtar da nake yi. Cikin k'arfin hali da na zuciya na matsa kusa da shi, na kwanta na rungume shi ainun. Na sanya hannu na fara shafar sumarsa a hankali cikin nutsuwa da son na kunna shi. Tsawon lokaci ina ta shafarsa a wurare daban daban amma bawan Allah ya yi funfurufus tamkar da bulo alhalin na tabbatar idonsa biyu. Murya na rawa na ce "Baban Amrah shekaranjiya fa da bakinka ka ce sai yau". Murya babu amo ya ce "To na sake d'agawa sai jibi idan na ji dad'in jikina, gabadaya ba ni da lafiya ba moruwa zan yi ba". Yana rufe baki wani irin mololon abu ya tokare mini ya ninka nauyin da kirjina ya yi. Na kasa kukan. Na kuma kasa kwanciya. Fiye da shudewar awa guda ina zaune cikin kaduwar wulakancin da yake tata mini tamkar wacce aka bashi ni akan dole. Wai duk mata ne idan sun haihu, zama ya fara nisa sosai suke fuskantar wulakanci da tozarcin namiji ko kuwa ni ce kawai? Jiya na cika shekaru talatin da biyar da haihuwa. Amrah da itace babbar diyata tana da shekaru goma sha hudu. Sai k'aninta Faruk mai shekaru sha 12, sai kuma k'aramarsu Farha mai shekaru biyar. Shekaru biyu kenan da sake tsanantar lamarin. Na kuma hakkake ba zai daina ba, domin kullum da kalar wanda zai yi mini. Har ta kai jallin fargaba nake mu zauna inuwa d'aya da shi. Duk yadda na debe kunya na sake nemansa, amma ga abin da ya sake fad'a mini tamkar wancan karon. Wanne irin zalunci ne haka da k'etare iyakokin shari'a? Ganin zan yi asara biyu. Sai kawai na mike na doro alwallah na hau nafila ina tsananta addu'ar a kare ni daga afkawa b'arna. Ina kan sallaya aka yi kiran assalatu. Sai lokacin ya yi mik'a ya tashi ya zauna. Ni kuwa na mike na sake tada sallah dan yin raatainin fijir. Da k'yar ya yunkura ya shige bayi. Ya fito ya yi nafila sannan yasa ya kai ya fice uffan bai ce mini ba. Da na ji masallaci sun tada sallah sai nima na mike na yi tawa sallar cikin kankan da kai. Na riga na saba da zama kan sallaya har rana ta keto. Sannan na mayar da nafila sai kuma na fita kicin na saka ido akan y'an aiki. Dankalin turawa na bawa Alti mai aikin abinci umarnin ferewa da soyawa. Yayin da na hau hidimar dama kunu tsamiya. Amma da lemon tsami zan yi. Ita kuwa Alawiyya tana hidimar gyara falo da goge shi, tare da taimkawa Farha a shiryawa. Kafin bakwai na safe mun kammala komai an shirya abincin kan dining. Dukkan yaranmu sun shirya cikin uniform. Amrah ce makarantar ta daban yayin da Faruk da farha suke makaranta daya. Cikin walwala muke karyawar tamkar bamu da damuwa. Tare muka fita, shi ya wuce da Amrah yayin da ni na wuce da Faruk da Farha makarantarsu tunda Farha ma a pri 1 take yayin da Faruk yake a sakandire.(Js2) Har bakin gate din makarantar na kai su, suka fita suna fad'in "Thank you Mahmah! A dawo lafiya". Na amsa ameen my dearies a yi karatu lafiya ". Cikin nutsuwa nake tukin har na isa cikin jami'ar Umaru Musa Y'ar addu'a(Umyu). Na adana motar a inda aka tanada. Na fito cikin nutsuwa na nufi ofishina da yake a tsangayar kimiyya da fasaha. K'ananun ma'aikatu sai gaisuwa suke miko mini cikin girmamawa, ina amsa musu cikin sakin fuska tare da mututantawa. Da Bismillahi na zauna akan kujera. Na ajiye jakar hannuna, da na siya a Egypt wajen *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* tare da fito da wayata. Na kalli agogon da yake daure a hannuna na ga saura mintina goma sha biyar na fara bada darasi. Na fito da ruwan faro daga fridge. Ba wani sanyi tabbacin yanzu aka saka da aka yi sharar office din. Na dauki abubuwan da zan bukata na fita zuwa hall din da zan bada darasin pharmacology. Duk inda na gitta dalibai maza da mata idanuwansu na kaina. Ni kuwa ina ta maimata addu'ar "Waallahu yas'muka minan nasi. Domin kaucewa kaifin idanuwansu. Sau tari akan kunne zan ji yaran matan suna fad'in "wannan mata ta had'u, ta morewa rayuwar duniya, komai ta hada, asali, kyau, ilimi, kudi, miji mai kyau, kyawawan y'aya' ga lafiya. Ita kam mun rasa menene gibinta a rayuwar nan da ake cewa mutum tara yake bai cika goma ba. Ni kuwa murmushi kawai nake yi domin dukkan abin da suka lissafa hakane. Sai dai tawayar da na ke fama da ita, itace mafi munin tawayar da za'a jarrabi mace irina da shi. Hatta wasu cikin danginaa irin wannan kallon suke mini duk da kuwa kafatalin mazan sisters dina sun fi nawa mijin kudi amma kowa kallon the most peaceful marriage ake yiwa aurena Amma deep inside ni nasan abin da nake fuskanta. Ni kad'ai nasan gashin k'umar da mijina yake yi mini. Mafi yawa kuma haka mata irina suke fuskantar kalubale daban daban. Amma na riga na yi imani komai yana tafiya ne bisa ikon Allah. Ba komai kake so kake samu ba, mutum kuwa bai samun yadda yake so matukar a cikin wannan duniyar ne da babu cikakken jin dad'i a cikinta. Cikin nutsuwa na isa d'akin da zan gabatar da darasin. Na yi musu cikin gogewa da saukakken kuma gangariyar turanci. Cikin abin da yake debe mini kewa har da koyarwa da nake yi. Yana cikin abin da yake samar mini da nutsuwa na manta damuwowin da nake kwana na yini a cikinsu. Yau har yamma ina cikin makaranta dan haka na biya na dauko yara tunda suma sai after biyar suke tashi a ciki suke islamiya. Tun kafin na yi horn maigadi y a bude mini katafaren gate din gidan namu. Kafin na kammala tsayar da motar ya fito yana danne danne wayar da ya zame masa ka'ida da dabi'a. Yadda yaran suke masa hugging suna fad'in "We are back Dady, sannu da gida". Suka shige da gudu, nima haka ya karaso ya rungume ni tare da karbar jakar hannuna yana fad'in "Welcome dear". Na amsa da murmushi da ce wa "Thank you! Tare muka shiga cikin katafaren falon. Kaitsaye dakina muka nufa. Ya shiga taya ni cire tufafin jikina. Abin wuya ya cire mini. Ya zuge zif din doguwar rigar atamfar da take jikina. Wanda dinkin ya yi matukar zauna mini tamkar y'ar shekaru talatin. Na yi saura daga ni sai bra da pant da siket. A maimakon ya tsikari kirjina kamar yadda aladarsa take sai kawai ya koma gefen gadon ya kishingide tare da mayar da hankalinsa kan wayar da ta sake zame mini tashin hankali a rayuwar aurena. Na sake yin jarumtar mazewa na shiga wanka. Har na fito na shirya bai ankara ba, don kuwa ya riga da ya yi nisa a sabon shafin da ya bude. Duk yadda na so na cigaba da jarumtar cigaba da kawar da kai akan lamarin wayarsa abin ya ci tura. Dan haka na fara tunanin lokacin da zan shammace shi na dauka. Tabbas sai idan yana barci cikin dare. Domin yana cikin jerin mutane masu nauyin barci. Haka duk tsananin rudani da tashin hankali baya hana shi barci. Ba jimawa suka fice zuwa masallaci shi da Faruk. Gabadayanmu da yara muna falo, maimakon ace muna hira cikin farin ciki da walwala. Amma kowa da wayarsa a hannu yana nausawa cikin yanar gizo. Ogan nafi zaton chart yake yi da wacce take birkita shi. Ni kuwa ina cikin group din mu na old girls muna tattauna yadda taron reunion din da zamu yi zai kasance. Amrah kuwa bincike take yi tana aikin gida akan wani darasi da aka yi musu a makaranta aka kuma basu aikin gida a kai. Yayin da Faruk yake yin game. Farha kuwa hankalinta na kan tafkekiyar allon talabijin din tana kallon katoon. Na ajiye tawa wayar ina nazarinmu gabadaya. Jikina ya yi sanyi yadda waya take lashe mana dukkan lokutanmu. A shekarun baya a lokacin da yaranmu suke kananu sosai waya bata shiga jikinmu irin haka ba. Amma a yanzu mafi yawan mutanan wannan karnin sun fi girmama sha'anin waya fiye da komai. Na saki ajiyar zuciya na ce "Daddy, Amrah, Faruk, Farha dinner is ready". Na mik'e na nufi dining din. D'ayan bayan d'aya suka biyo ni har muka hallara. Kowa da kansa ya yi serving kansa as usual. Mun ringa mun saba da rashin magana idan ana cin abinci dan haka ba a jin komai sai karo tsakanin tangaran da tsokali. Mun kammala aka fara kiran Isha. Dan haka muka hau haramar yin sallah, yayin da Daddy da Faruk suka sake ficewa zuwa masallaci kamar yadda suka saba. ** Dare ya yi nisa. Na mirgina na tab'a shi na tabbatar ya yi nisa. Sai kawai na lallaba na zaro wayarsa da take karkashin filonsa. Jikina na bari na fice zuwa falo bayan na mayar da tawa wayar gurbin da na zare tasa. Na zauna a bakin kujera, na fara kokarin cire password din, na rubuta sunana da babban bak'i *BILKISU* amma bata bude mini ba. Na sake rubuta *Bili* nan ma bata bude ba. Kaina ya kulle yaushe ya canja? Na tambayi kaina a rude. Na yi jim ina nazarin me zan saka ta bude mini domin ina jin tsoron kada na cike adadin da zata ki buduwa gabadaya. Da zullimi na rubuta *B Funtua* nan ma bai bude ba. Cikin sa'a na sake rubuta *Faruku Sm* sai ta budu. *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* *Egyptian abayas* *Egyptian nighties*. *Bags and jewelries* *Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria* *Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*. # +201121544627 # +2349162662750 Zuciyata ta buga da sauri. Na lalubo manhajar Whatsapp dinsa nan ma na tarar ya sanya masa tsaro. Na sake rubuta wanda ta bude mini waya. Sai bai bude ba. Na rasa yadda zan yi. Kawai sai na rubuta lambar wayarsa. Ai kuwa ya bude. Ban kunna data ba. Dan haka na fara duba last contact din da ya yi magana da su a wannan daren kafin ya kwanta. Suna d'aya ne ya ja hankalina kuma shine na karshe da ya yi magana da shi . Na maimaita sunan a hankali *Hawwah*. Zuciyata ta sake tsananta bugu. Na bude na fara bibiyar hirarsu. Babu wani abu na assha, amma maganganun da suke tattaunawa suna alamta cewa sun dade a tare. Sun kuma fad'a cikin matsananciyar soyayya a tsakaninsu. Sannan na fahimci gabadaya kudadensa a kanta suke karewa ni kuma ya bar ni da hidimar rik'e masa gida da shi kansa. Mafi kankantar kudin da yake tura mata da na shiga text messages din da banki suke yi masa dubu ashirin ne. Na fahimci tun yanzu shi yake yi mata komai na rayuwa. Maganganun ta suka fahimtar da ni yarinya ce k'arama wacce da kad'an ta girmi Amrah. Wata magana da ta ja hankalina da na ga ta ce masa yau na ga matarka bata da kuzari. Ya bata amsa da fad'in bansan me ya same ta a tsukun nan ba. Ita ba yarinya ba, ba zata fad'i damuwarta ba, sai ana bin kanta. Sai kace yarinya sa'arku. Irin wannan rarrashin an yi mata itama, yanzu kuwa naku ne yara da za'a lallaba ku, a tarairaye ku. Ta turo nasa imoji na dariya da na nuna soyayya. Gumi ya dinga yanko mini. Ashe ma dalibata ce? Wanne irin tozarci bawan Allan nan ya shiryo mini ne? Anya kuwa na cancanci haka daga wajensa? Hawaye ya kwace mini. Zuciyata ta yi nauyi, na fara tunanin wai da me na tsira ne a cikin wannan auren? Sadaukarwar da na yi masa me ce ce ribata? Anya kuwa zan iya zaman kishi da wata macen a karkashin ikon Baban Amrah? A fili na furta ba zan iya ba, shima kuwa ba zai iya ba. Tabbas cikin biyu dole d'aya ta kasance. Ko dai idan ya gama daukin amarya ya dawo mini, ko kuma ni ya sallama ni ya cigaba da more kuruciyarta. Amma na sani, shima ya sani ba zai iya gamsar da mace biyu ba a tsarin halittarsa. Sannan nauyin aljihunsa ba zai rik'e masa gida biyu ba. Hakanan ba shi da jarumtar da zai yi adalci a tsakaninmu. Dole akwai wacce zata janye shi a tsakani. Na rasa yadda zan yi da azababben kishin da ya tokare ni. Na tuna duk fafutukar aikin da nake yi ban ajiye komai nawa ba. Tunda rik'e gidan ni ce. Ban tab'a raba aljihuna da nasa ba. Komai tare muke yi, asalima sai da aka kai jallin da baya yin komai a harkar hidimar gida. Ban tab'a gajiya ko nuna kasawa ba. A yanzu da nake ganin zan samu sassauci da HALACCI ashe shi idonsa na kan yara k'ananu kusan sa'annin y'ar cikinsa. "Da me na tsira ke nan ni Bilkisu?" Na furta cikin rawar murya irin ta kuka sosai. *Pay via* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*. *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* *08032773332* *09069067488* *Surayya Dee* ✍️ [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *DINGISHIN KWADO* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS.M.I.NASHE)* 2 *Lafazi writer's* *Wannan littafin na kudine pay 1k via 2384876855 Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# #09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram ga wadanda suka biya kudi n karatu*. *Na gode muku Allah ya saka da alheri.* *Contact me 08032773332* *what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. Na kifa kaina a hannun kujerar na yi kuka tamkar hawayen idanuwana zasu kare. Ina layi na tashi na mayar masa da wayarsa na dauki wayata. Duk yadda na so na yi nafila na kaiwa Ubangiji damuwata kasawa na yi. Ba abin da zuciyata take yi irin tafarfasa, tamkar na ciro ta na wanke komai ko na huta da tsananin da nake ciki. Da k'yar na dinga ambato ya Hayyu ya Kayyum bi rahamatika astagisu. Na jima kafin na fara samun sassauci. A raina na fahimci manufar shari'a da ta yi togaciyar tsananta bincike kan abin da ake boye maka ko wanda baka san da shi ba. A da zato nake yi wanda ban gasgata ba. A yanzu kuwa na bankadowa kaina damuwa da kunci. Domin zan rayu ne cikin zullimi da zargi. Na saki gauron numfashi. A fili na furta k'arin aure ba laifi ba ne a wajen namiji mai ra'ayin k'arawa. Sannan Ubangiji da bibbiyu ya ce su fara domin yasan ya haliccesu da son mataye da yawa. Ba kuma zan bijire wa ayar Ubangiji ba ne ta hanyar kin amince wa da k'arin aurensa ba. Zan bijire ne don na tserar da shi tashi da shanyayyen bangare daya ranar alkiyama. Domin yadda na shaida Annabi manzon Allah ne haka na shaida k'arin aure bana maza irinsa ba ne. Ba zai iya adalci ba tabbas. Har aka k'ira assalatu ban iya tsinana komai ba, sai kuka da sake saken zuciya. Har ya fito ina zaune ko yunkurin tashi ban yi ba. Ya k'araso kusa da ni murya babu amo ya ce "Ashe kina nan?" Bai jira amsawata ba ya fara tafiya yana fad'in sai na dawo. Na bi bayansa da kallo ba tare da na iya fad'in uffan ba. Da k'yar na tokara na tashi, na dauro alwallah. Ba k'aramin jarumta na yi ba, kafin na samu hankalina ya daidaita na yi sallar cikin nutsuwa ba. Gabadaya fuskata ta aune, na yi fiyau da ni. A yadda nake jina ko ina da darasin da zan bayar da safe ba zan iya halatar makaranta ba. Sai kuma ya kasance sai karfe 4-6 nake da darasi. Dan haka ina layi na nufi dakina na kwanta, sabon kuka ya k'wace mini tamkar dai ba kwana na yi ina yi ba. Da k'yar na yi k'ok'ari hadiye kukan saboda sanin da na yi a ko wanne lokaci yarana na iya shigowa idan basu ganni a kicin ina hidima kamar yadda na saba ba. Na ja duvet na lullebe jikina. Ilai kuwa sai ga Amrah ta shigo. Da kulawa sosai ta ce *Mahmah* ba kya jin dad'i ne yau?" Murya ta babu amo na ce "Kwana na yi da ciwon kai da zazzabi. Na sha magani yanzu shine na kwanta ko zan samu na rintsa." "Ayyah sorry Mahmah! Allah ya baki lafiya". A hankali na ce "Ameen. Ki je kicin ki tayasu ku shirya komai, ki kula da Farha". "To Mahmah". Ta amsa a nutse ta fice ba tare da ta ja k'ofar ba. Ko minti daya ba'a yi ba, suka dawo dukkansu har Faruk. Suka gaishe ni sannan suka mini sannu. *Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?* *Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa* *Malaysianfabricsng* 07020695644. Amrah ta kadasu suka fice bayan ta rufe k'ofar dakin. Na sani ta kawo sune dan kada barci ya sure ni su tashe ni. Bai shigo ba sai bakwai da mintina daidai lokacin da muke fara karyawa. Da kulawa ya ce "A kwance kike, ba ki da lafiya ne?" Na kasa amsawa domin ji na yi gabad'aya haushinsa ya turnike ni har wuya. Ya zauna a bakin gadon. Ya tab'a jikina ya ji da zafi, ya ce "Zazzabi ne a jikin ki, amma kin kwanta. Ki tashi ki shirya na ajiye ki a asibiti idan kin kammala sai ki dawo gida ki kwanta." Na girgiza kai na ce na sha magani yanzu, barci zan yi, nasan zai sauka in sha Allah ". Ya mik'e ya ce "Allah ya kara lafiya sai na dawo " Ya saka kai ya fita, ya karya sannan ya fita da yara gabad'ayansu. Hawaye ya sake silalo mini, ba dan komai ba sai na takaicin yadda na dauki dukkan so da yarda na damkawa Baban Amrah. A haukana na dauka a yanzu ne zan ci moriyar hak'uri da sadaukarwa da na yi. Ashe wanccan tunanin nawa ne ni kad'ai. Domin a yanzu ko bai bude baki ya ce mini ba na burge shi, na yi masa tsufa ba, ayyukansa da yadda yake mu'amalantata ya fahimtar da ni. Na goge hawaye na kalli fanka yadda take wulwulawa da k'arfi. Na saki ajiyar zuciya. Ina sake gane haka alamuran duniyar nan suke jujjuyawa tamkar fitar kibau a jikin mashi. Na rufe ido ina tariyo abubuwan da suka yi ta faruwa a tsakaninmu da ya kamata na fahimci al'amarin da yake ransa, amma saboda na riga na bashi total submission sai nake dada nausawa tare da zama bagidajiya a kansa. Dirin wayata ya ankarar da ni, ana kirana, domin na saka ta a vibration ne. A kasalance na dauka ganin sunan aminiyata kuma y'ar uwata ya sanya na dauka babu b'ata lokaci. Karon farko da na dauki wayarta ba tare da na yi tsaki ba. A sanyaye na ce "Maman Abdul ya family?" Ta amsa da ce wa "A kwance kike ne?" A hankali na ce "Eh bana jin dad'i ne fever da ciwon kai suka taso ni a gaba." Ta bude murya ta ce "Kuma sun taso ki a gaba, sai kika nade a gado, kika kasa gane kamata ya yi ace kina gaban likita, dan a duba ki a d'ora ki kan magani?" Na saki ajiyar zuciya na ce "Maman Abdul na sha magani idan bai sauka ba zuwa anjima zan je na ga Dr din". Ta ja tsaki ta ce "Nan da mintina kad'an zan zo na raka ki, tunda shi ya fice ya barki a kwance." Na kasa bata amsa domin ba k'aramin aikinta ba ne ta hau zagina tunda tana cikin jerin mutane masu hangulalliyar zuciya. Kazalika bata sassauci akan lamarina da Baban Amrah. Ilai kuwa sai ji na yi ta yi tsaki ta katse wayar. Na ajiye wayar na yunkura na zauna da k'yar a dalilin yadda nake jin rashin k'arfin jikina na tsananta. A hankali na muskuta na sauka na doshi bayi. Na sakarwa kaina shower. Domin na tabbatar sanyin ruwan zai rage mini dumin da jikina ya had'a. Na kammala saka undies na zura doguwar rigar batik ta Malaysian Fabrics. Babu nauyi haka dinkin ma plane ne. Na daura dankwalin. Na feshe rigar da tauraren kaya tunda na fesa na jiki kafin na saka kayan. Na shafawa lebena wet lips. Na fito da mayafin da ya dace da atamfar. Hakanan takalmi da jakar kalar mayafin ne. Na makala barima wacce a cikin jakar na dauko. Na dauki wayata na fita falo. Na tarar ko ina a gyare. Na leka kicin na tarar da su biyun suna fere doya. Daga k'ofar baya. Suka hau gaishe ni da yi mini sannu da jiki. Na amsa musu da ce wa na ji sauki. Na kalli Alawiyya na ce "Ki je ki gyara dakin". Na dubi Alti wacce ta fita a haife na ce "asibiti zan je. Ki kula da gidan, kada kuma ku je ko ina". Da ladabi ta ce "Mahmah a dawo lafiya, Allah ya kara sauki". Na amsa da "ameen na gode " Har na fara tafiya ta biyo ni ta ce "Mahmah ki dan sha kunu mana. Na dama ya yi kyau." Na murmusa mata na ce "To zubo mini Alti". Da murna da rawar jiki ta tafi dauko mug din da nake sha da shi. Ta dauraye sannan ta goge da wankakken kicin towel. Ta ciko shi taf. Ta tsugunna ta ba ni, na karba na ce "Na gode sosai Alti". Ina kurban kunun Maman Abdul ta shigo, sanye cikin gown din wani fitinannen material da ya yi matuk'ar yi mata kyau ainun wacce order ce da ba'a samu a koina sai a *Malaysianfabricsng* 07020695644. Bata zauna ba ta ce "Ta so Malama". Na kalle ta na ce "Rigimaatu zauna ki sha kunun gyada". "Na karya already idan mun dawo zan sha." "To ba ni mintina biyar na kammala Sha". Bata ce komai ba, ta zauna tabbacin zata jira ni din. A hanzarce na shanye. Na ajiye cup din na mike muka tafi. Su Alawiyya suka biyomu suna mana fatan dawowa lafiya. Muka gaisa da Baba mai gadi a mutunce muka bude k'ofar k'aramin get muka fita tunda bata shigo da motar ciki ba. Muna tafe tana tukin ta cikin nutsuwa, ni kuma na yi zurfi a tunanin halin da nake ciki. Ina son na fad'a mata abin da na ga ni a wayar mijina. Ina jin tsoron tention din da zata kara mini. Na riga da na sani ko yanzu aurena ya mutu murna zata yi watak'ila ta had'a da k'warya k'waryar walima. Ba kuma zata yi hakan dan murnar aurena ya mutu na rasa wata daukakar duniya ba. Zata yi ne domin tana ganin zan samu y'ancin zuciyata. da kuma farinciki. Har muka isa bamu yi maganar da zarta uku ba. Ba b'ata lokaci muka ga Dr ta rubuta mini magunguna ta kuma gargade ni na k'aranta damuwa domin jinina ya hau sai dai ba sosai ba. Ni kuwa nasan rashin barcin da ban yi ba, da kuma tsananin da na kwana a ciki ya isa ya sababa mini komai. A hanyar komawarmu ta sassauta fishinta ta ce "Ba zan gaji da fad'a miki ce wa aure is not all about do or die ba ne. Allah da kansa ya yi maganar idan kun fahimci kun kai lokacin da ba kwa burge juna, ko ba kwa son juna ya fad'i yadda al'amarin zai tafi cikin ihisani da kyautatawa. Amma gabad'aya hausawa bama amafanin da wannan nafsin! Sai mu yi ta zama irin wanda babu lada a cikinsa sai zunubi ma. To zunubi mana tunda duk zuciya babu dad'i an koma ana zaman y'aya', ba zaman Allah da Annabi ba. Duk abin da za'a yi ba dan Allah ba, ba zai yi albarka ba. Y'aya' nawa ne uwayensu suka fad'i suka mutu a wannan duniyar? Sun mutu ne ko sun kasa rayuwa? Bare kuma da ranki da lafiyarki. A lokacin da mijin da ya k'arar miki da kuruciyarki ya gundura da ke, a lokacin kuma Ubangiji zai turo miki wanda shi kuma a hakan yake son ki, yake kaunarki. Bilkisu kin yi hakuri, kin biyayya, kin yi sadaukarwa, kin yi adalci, kin yi komai. Amma fad'a mini what do you have in return?" Na fara kuka sosai. Ta gangara gefe ta ce "Bude baki ki mini magana Bilki. Kin sani bazan yad'a sirrinki ba, na damu da ke tamkar ko ma fiye da kaina. Kalle ni, ni ce ta ki BBM ". Hawaye na zuba murya na rawa na kalle ta na ce "Baban Amrah ne, soyayya yake yi da k'ananun yan mata wadanda basu bawa Amra shekaru biyu ba! Kuka mai nauyin gaske ya kece mini. Amma ita bata ka'du ba. Sai ma ce wa ta yi "soyayyar da yake yi da y'an mata ya kamata ki saka a ranki, ko kuwa kamata ya yi ki gane irin kuskuren da kika rayu a kai, ki yi d'amarar gyarawa? Bilki ba fa zan rufe ki ba, domin ni da ke bamu hadu dan munafunci ba. Dan haka bazan yaudare ki ba, tamkar yadda bazan yaudari kaina ba. A halin yanzu mijinki zai bukaci yarinya k'arama. Domin shi a yanzu yake kan ganiyarsa. Kinsan kuma na tab'a fad'a miki da jimawa har muka samu sabani akan hakan. Ni yanzu ba soyayyar da yake ba ne cikas ba. Yadda kike ragaita a hannunsa ne tashin hankalina. Bilki kina da zafafa soyayya. Anya kina yawan tuna hadisin Annabi da ya ce mu takaita soyayya da k'iyayya domin komai na iya juyawa. Ma'ana masoyi kan rikide ya koma makiyi. Haka nan makiyi kan rikide ya koma masoyi. Menene something precious a tare da Baban Amrah da kika zama haka ne?" Na kalle ta ina son na fahimce ta da kyau. So take na kashe aurena ko kuwa? Duk abin da nake yi ina da damar da zan yi ne. Allah ya yassare mini. Na yi k'asa da kaina domin na hakkake ba ingiza mai kantu zata yi mini akan halin da nake ciki ba. Tun fil-azal take adawa da yadda nake gudanar da rayuwar aurena. Ta rayu tana kaicon yadda komai ya cukurkude mini. Na nisa na ce "Ba yadda kike zato ba ne. Kin ringa kin sani ban dauki abin duniya da muhimmanci ba. Dan haka duk abin da nake yi a gidana ban tab'a jin kaicon yinsa ba. Na fi son soyayya fiye da kudi. Na fi son a ririta ni, fiye da a ajiye mini komai babu kulawa. Na fi bukatar kulawar miji sama da na tara abubuwan kyalekyale." Ta numfasa ta ce "Yanzu fad'a mini kin samu yadda kike so din ne? Kusan asara biyu kika yi Bilki. Ke baki yi tattali kin mori karatunki da aikinki da kike yi babu hutu ba. Sannan kuma baki samu yadda kike so a wajen mijin da kika d'ora dukkan fatanki a kansa ba. Tun farko na fad'a miki kada ki bada k'ofar da zaku yi joint pocket. Amma kika k'i." Cikin kuka na ce "Yanzu "Maman Abdul ina da kudi sai na bar mijina yana ragaita? Ina da hali sai na bari mu zauna da yunwa! Ina da dama sai na bari mu zauna a gidan haya, ko kuwa na zuba ido a dinga ganin y'aya'na kamar almajirai saboda rashin sutura da kyakkwar makaranta?" Idonta ya ciko da k'walla. Ta yi dabarar daukesu ta ce "Ba ina nufin haka ba. So nake ki gane ba kowa ne yasan alheri ba. Yanzu fad'a mini da kika yi hakan kin samu abin da kike so? Har yau baki samu ba. Ni da na bar mijina da hidimar gidansa na fiki samun kulawa, na fiki nutsuwa, na kuma fiki gamsuwa da kokarin miji. Ban tab'a yarda na yi abin da nasan ba hakkina ba ne. Na yarda zan yiwa kaina irin suturar da ta dace da ni ko da shi ba zai mini ba. Zan siyawa y'aya'na suturar da nake son ganinsu a ciki, mussaman idan zan je taro da su. Haka nan idan ta tura ta kai bango zan shiga cikin tallafin karatunsu domin idan na ginasu kaina na yiwa sabida na yi amanna y'aya' mallaki uwa ne. Ko ina nake a duniya zasu nemi ne ba kuma zasu canja ni da wata ba. Sai kuwa magani idan ba ni da lafiya ko su. Sai kuma na tabbatar miji ba shi da sukunin yin wannan hidimar. Idan kika cire wadannan ba abin da zan yarda na daukewa miji, komin kashin abin da yake da shi sai ya kawo ya bamu tunda shari'a ma bata dauke masa ba." Ta nisa ta cigaba da ce wa "Mafi yawa fa mazan yau da zarar suka ga kana tausaya musu kana sana'a kana hidima a gidan wai maimakon su karfafa ka, su yaba maka, sai su dinga sakar maka ragamar rik'e gidan a hankali. Kafin a ankara sai su bar maka kaso takwas na rik'e gidan gabadaya. Ranar da baka yi ba kuwa sai ya zama ka yi zunubin da zasu juya maka baya ko ma su sallame ka. Kuma akan idonka zasu yi aure su dinga yiwa d'ayar matar hidima da dukkan iyawarsu. Da zaka yi magana sai a taru ace kishi kake yi, da ai baka yi k'orafin ya barka da wahala ba sai yanzu. Shi kuwa gogan ko d'ar ba zai ji ba zai ce "Ai ita yarinya ce, yaro kuwa bai san babu ba, ke ma lokacin da kike kamarta ai ba abin da bai miki ba. Dole ki hak'ura idan kina son zama da shi, rikicewarki kuwa na iya sawa ya sallama ki ya cigaba da zama da matarsa ba tare da tunanin kun tara yara ba." Na kalle ta na ce "Na gane na kuma san gaskiya kike fad'a mini wacce babu son kai a cikinta." Ta ruk'o hannuna ta ce "Ki fara nazarin yadda za ki gyara kuskurenki. A yanzu yana da halin da zai rik'e gidansa Bilkisu. Dan haka ki zame ki bar shi ya dauki nauyin da Allah da kansa ya wajaba masa. Idan ba shi da hanyar samun kudi ta yaya zai fara tunanin k'arin aure, ko kuwa itama ke zai aurowa ki cigaba da rik'e masa ita?" Na kalle ta a matukar kidime na ce "Sai ka ce na zama sauna Basma?" Da rauni ta ce "Ai kuwa shasha ma ya mayar da ke ba sauna ba Maman Amrah! Muka yi shiru a dalilin na kasa magana, gabadaya kaina ya kulle. Ina ta tunanin fad'i tashin da na dinga yi a baya amma gabadaya ban ga ribar hakan ba. Na fesar da ajiyar zuciya na ce "Zan gyara abin da zan iya gyarawa Basma. Amma ba duka ba. Domin kinsan idan ina son abu to ina sonsa ne da dukkan zuciyata. Ba abin da zan mallaka da zan yi masa iyaka da shi. Allahu yana kallona yana kuma kallon zuciyata. Idan abin da nake yi saboda shi ne to da sannu zai kawo mini mafita, na yi imani zan ga alheri ko da kuwa ba nan duniya ba ne. Abu d'aya na kudire idan har ya yi aure a wannan halin da muke ciki to tabbas shine tikatin sakina. Domin hakan da zan yi shine cikakkiyar soyayya tunda zan tsallakar da shi fad'awa halaka ne. Baban Amrah ba zai iya ba, na yi imani ba zai iya ba. Zan yi kokarin na danne komai domin ina son shi, ina son na rayu da shi, ina tausayinsa da y'aya'nsa. Amma idan har ya zabi wata saboda ni, to zan kauce na bashi waje domin ba zan hana shi abin da Allah ya ba shi dama ba. Da ace shi din jarumi ne, na tabbatar zai iya rik'e mata biyu cikin mutunci da adalci, da zan danne komai na jagoranci k'arin aurensa na bashi dukkan gudunmawar da ta dace tunda ga kan kudi har zuwa samar masa da kwanciyar hankali. Son da nake masa ba zai ba ni kuzarin da zan hana shi morewa rayuwarsa ba. To akasin da aka samu shi ba jarumin ba ne ta ko wacce fuska. Ni kuma bazan yarda na yi hakurin da babu lada sai cutarwa a cikinsa gabad'aya ba." Wata irin salama da annuri ya sauka a dukkan jiki da fuskar Basma. Ta ce "Na ji dad'i Bilkisu! Na gode miki, na kuma fahimce ki a yau k'warai da gaske. Zan fara yi miki addu'ar Allah ya mayar da shi irin yadda muke son ganinsa, daga yau na daina fatan ki bar shi, zan kuma tsaya miki har ki tsallake dukkan kalubalen da kike fuskanta a rayuwarki". Hawaye ya tsinke mini da rawar murya na ce "Na ji dad'i da kika fahimci sonsa kaddara ta ne ba wai ni ce na makale akan dole ba. Babu abu mai azabtarwa irin so. Mussaman son da ake yinsa babu dalili. Domin idan duniya zata hadu ana son fahimtar da kai had'arin da kake ciki ba zaka gane ba. Illah sake nausawa jeji tare da k'ullatar mutane da kuma ƙalubalantarsu. *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* *Egyptian abayas* *Egyptian nighties*. *Bags and jewelries* *Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria* *Tuntube ta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*. # +201121544627 #+2349162662750. Surayya Halin yau ✍️ [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2347020695644 3 *MalaysianFabrics* *Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.* *Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.* *7020695644.* A hankali ta yiwa motar ki ta hau titin da zai kaimu gidana da yake cikin Shagari lowcost. Zuciyata ta buga ganin motarsa a harabar gidan tabbacin ya dawo. Bamu tarar da shi a falo ba. Muka zauna Alawiyya ta kawo mata kunun. Ta sha, sannan ta mike tana gyara mayafin ta. Ta dauki jakarta ta kalle ni ina shirin tashi dan yi mata rakiya. Ta ce "Wallahi na yafe miki. Zauna ki huta, tunda kin sha magani ki kwanta ki yi barci idan kika tashi In sha Allah you will be better" Na ce "Zan kokarta." Ta tafi tana fad'in"Sai mun yi waya, ki sha magani, ki kuma kwanta ki huta sosai. Fiye da shudewar sa'a ina zaune a falon ni kad'ai. Gyangyadi ya fara cafka ta. Na tabbatar a cikin magungunan akwai wanda zai saka ni barci. Baya ga hakan ma na ci bashin barci jiya. Da k'yar na yunkura na yi dakina, ina yaki da sashen zuciyata da take son na je na gano halin da yake ciki. Amma na daure na kwanta. Na fara barci na ji muryarsa tamkar a mafarki. Na bude idona da suka canja launi saboda barci da kuma rashin isasshiyar lafiya. Fuskarsa babu fara'a ya ce "Tunda Basma ta zo ai yau kuma sai abin da na ga ni a gidan nan. " Murya babu amo na ce "Babu kyau zato fa". A hanzarce ya ce "menene zato a cikin maganata? Na ce zan kai ki asibiti kin k'i, saboda kin raina k'ok'arina! Amma da yake tana da tasiri ta shigo har gidana ta dauke ki, ta kai ki asibiti ta dawo da ke bayan ta gama yi miki hudubobin da na yi amanna na hure kunne ne. Kinsan ina gidan, amma ki kasa zuwa ki ga halin da nake ciki, ko ki tambayi ba'asin dawowar da na yi, sai kika yi kwanciyar ki saboda kin riga kin fara gina katangar karfe a tsakaninmu! Ya fad'a cikin bacin rai da ya bayyana a fuskarsa da gangar jikinsa gabad'aya. Na zuba masa ido, na kasa ce wa komai. Domin ya riga da ya bari na fara fahimtar ainihin kalarsa. Ba abin da yake buguna irin idan na tuna yadda ya kaikace yake fad'awa yarinya k'ankanuwa maganata. Wai ni ba yarinya ba ce bare ya lallaba ni. Sa'a d'aya da na yi dai duk tsufana ya kere mini. Na murmusa kad'an na dauke idanuwana akan kyakkwar fuskarsa da ta fara bak'ancewa a idanuwana. Na kuma yi amanna kishin da yake yagalgala ni ya janyo na ga bakinsa. Na kuma gamsu ba za'a dauki lokaci mai yawa ba zuciyata zata yafe masa, ta cigaba da ganin farinsa. Ganin na yi shiru kuma ina kallonsa sai ya fahimci akwai al'amarin da yake zuciyata mai nauyi. Ya matso ya zauna murya babu sukuni ya ce "Maman Amrah wannan kallon na ki, ina buk'atar fashin baki" Na dauke idanuwana, na lumshe su ba tare da na ce kanzil ba. Ya numfasa ya ce "Fad'a mini matsalar ki, ban gamsu da kallon da kike bina da shi. Haka nan ban gamsu da yadda kike mu'amalanta ta ba." Na sake yin shiru. Don bansan abin da zance masa ba. Domin duk yadda na tunzura bazan iya bude baki na yi masa gatsali ba. To na ce masa me ma? Tunda ni na binciko kuttu da kaina. Da na cigaba da dauke idanuwana daga kan wayarsa da ban ga abin da ya gigita ni ba. Ya yi k'wafa ya ce "Basma ba zata ga alheri ba in sha Allah." Har cikin zuciyata na ji rashin dad'in kalamansa. A sanyaye na ce "Basma na cikin jerin masoyana, tana cikin wadanda suka damu da damuwa ta. Ban zaci zaka iya mata mugun fata haka ba." Ya mik'e a kausashe ya ce "Yadda kika gamsu masoyiyar ki ce haka na tabbatar makiyata ce. Kuma ni Wallahi ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli ya ci riba." Ya fice cikin sauri tare da bugo k'ofar da k'arfi tabbacin ya yi fishi sosai. Na sauke nannauyen numfashi. Na furta "Subhanallah! A bayyane. Zuciyata ta sake nauyi wato ko mun rabu ba shi da kaico. Na fara gasgata da gaske yanzu babu soyayyata a tare da shi tunda har ya yi irin wannan furucin tare da rantsuwa. Ina kwance lamo ba abin da nake yi sai tunanin rayuwarmu. Tunanin k'alubalen da na ratsa. Hawaye ya silalo mini a dalilin mahaifina da ya fad'o mini. Badakalar da ke faruwa a cikin zumuncin zamani na matukar tsorata ni. Na sha jin labaran damalmalewar zumunci daban daban amma ban tab'a cin karo da irin na gidanmu ba Ban tab'a ganin rashin kunya da mutunci irin wanda na ga ni a zuriarmu ba. Idan na tuna abin da ahalinmu suka yi sai na ji kunya da tashin hankali na rufe ni irin mai saukar da zazzabi da kasala. Hakan na cikin dalilin da ya sanya bana kaunar aurena ya samu tasgado domin bana fatan na koma gidanmu da zumar zama mai tsayi. Don kuwa ina cikin jerin mutanan da aka jarraba da rashin dacen uwa. Mahaifiyata wata irin uwace mai wuyar sha'ani. Mai yada bacin rai a tsakaninmu, mai yayata kuskuren da jama'a suka yi mata. Shiyasa gabad'aya mu y'aya'nta bamu da kwarjini ko farinjini a cikin dangi. Munanan dab'iun da ta cusawa mana ya sanya ake yawan rikici da mu. Domin duk wadda ta fad'a mana ya mata kaza zamu kullece shi tare da k'ulla adawa da shi, ba tare da tunani ko shakkar komai ba. Hawaye ya silalo mini, domin ni da kaina na tabbatar muna shan zagi a idon duniya. Duk da ni kad'aice ban bi ra'ayin mahaifiyata da yan'uwana ba, amma hakan ba zai hana na shiga sahun y'aya'nta ba. Na muskuta ina jin makakin bacin rai har cikin zuciyata don kuwa ina cikin matan da basa son tuna da d'insu. Domin ni gabadaya bacin rai da kuttu yafi yawa a kafatalin rayuwata. Tun daga rayuwar gidanmu har zuwa rayuwar aurena. Amma dalilai masu yawa suka sanya na yi nufin yin bitarsu tiryan tiryan dan na lura bayar da labarin nawa na iya zama izna hadi da hannunka mai sanda ga mutanen yau, mussaman mata da sune iyayen al'umma. Ina kuma fatan duk wacce ta ji labarina zata yi duba na tsanaki ta laluba wacce irin dabia take aikatawa, shin kina cikin mutane masu manta tarin alkairai, akan kuskure guda daya tak? Ku biyo ni sannu a hankali, ta yadda zaku fahimci inda na dosa domin kuwa mai tsananin aiki da lura ne zai fahimci Dingishin K'WADO. Sunana Bilkisu Isa Funtua. Ni y'ar asalin k'aramar hukumar Funtua ce ta jihar Katsina. Ina matukar son garina, ina alfahari da kasancewata y'ar asalin Funtua. Shiyasa a duk sadda na samu sukuni na kan yi bita tare da nazarin garin namu. Dan haka kafin na kutsa cikin labarin nawa sai na fara fayyace yadda garin namu yake. K'aramar hukumar Funtua Tana daya daga cikin manyan Kananan Hukumomin Najeriya da aka samar tun bayan gyaran tsarin kananan hukumomi da akayi a shekarar 1976. Ita ce kuma hedikwatar mazabar Katsina ta Kudu, wadda ta kunshi kananan hukumomi har guda goma sha daya (11) wadanda suka hada da: Bakori, Danja, Dandume, Faskari, Sabuwa, Kankara, Malumfashi, Kafur, Musawa, Matazu da kuma ita kanta Funtua. Tana da girman murabba'i 448 km² da yawan jama'a (225,571 a bisa ƙidayar 2006) sannan kuma mutum 570,110 bisa ga ƙiyasin 2016. Shugaban shine shugaban karamar hukuma a hukumance. Mazauna karamar hukumar hausa Fulani ne akasarinsu, sana’o’insu kasuwanci, noma da kiwon dabbobi ne. Funtua tana da yanayi mai kyau yayin da take kan latitude da longitude 11°32′N da 7°19′E bi da bi. Garin yana da matsakaicin zafin jiki na 320C da zafi na 44% Funtua tana cikin iyakar kudancin jihar Katsina. Shi ne birni na biyu mafi girma a jihar bayan Katsina. Tana iyaka da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a kudu, Bakori daga gabas, Danja a kudu maso gabas, Faskari a arewa maso yamma da Dandume a yamma. Har ila yau garin namu bashi da matsalar ababen more rayuwa irinsu ruwa da wutar lantarki. Funtua tana da tashar watsa lantarki ta kasa mai karfin 132KV na National Grid da ke zuwa daga Mando tasha ta Zariya daga nan ta wuce Gusau ta tsaya a Talata Mafara. Yana da kyau a lura cewa tashar watsa wutar lantarki mai karfin 132kv/33kv da ke Funtua tana gudanar da ayyukan kananan hukumomi 9 daga cikin kananan hukumomi 11 da suka kunshi Gundumar Sanata Funtua. Yayin da rashin wutar lantarki ya zama ruwan dare gama gari a fadin kasar. Funtua ba ta da irin wannan matsalar saboda garin na samun wutar lantarki na tsawon sa'o'i 12-20 a kullum. Don haka duk mai sha'awar zuba jari zai iya zuwa ya saka hannun jari. Dangane da Samar da Ruwa; An albarkaci Funtua da madatsun ruwa guda 2, wato; Mairuwa da Gwagwaye da suke hidima da birnin da wasu sassa na majalisar Faskari da yankin Bakori. Har ila yau, akwai gonar Songhai da ake amfani da ita don horarwa da noman wasu kayayyakin gona. Haka nan Funtua ta haifi manyan mutane da suka yi shura a fannoni daban daban a jihar Katsina da k'asa gabad'aya. Bayan haka garina ne ya samar da tsohuwar marubuciya *Haj Bilkisu S Funtua.* Allah ya kara lafiya uwar marubuta da makaranta. Wannan kenan. Gidanmu na cikin unguwar low-cost wacce shiya ce ta tsofaffin y'an boko, kuma masu kumbar susa.. Katafaren gida ne da ya amsa sunan mahdi ka ture sabida k'arfin ginin. Hakanan gida ne iya ganinka domin kafin ka kai k'arshen katangar da ta kewaye gidan ma aiki ne babba. Gidan na dauke da sassa daban daban har guda biyar. Sai dai tsakanin ko wanne sashe tafiya ce mikakkiya. Ma'ana akwai tazara mai yawa ta yadda ba za'a iya yin komai tare ba. Shashen farko na Alhaji Musa ne wanda kowa a zuriarmu ke kiransa da Baba babba. Sai shashen tsakiya na mahaifiyarsu ne kafin ta rasu. Daga baya sai ya koma wajen ajiye amfanin gona domin iyayenmu manoma ne na fad'a a jarida. Sai sashen Alha Isa wanda muke kiransa da Baba k'arami. Shine kuma mahaifina. Akwai sashin ma'aikatan gidan da kuma sashe guda na baki da samarin gidan. Su biyu kacal iyayensu suka haifa sai dai mahaifinsu Malam Muhammadu d'an babban gida ne a Funtua asali yana da alak'a da gidan sarautar garin, suna da zuria mai yawa, domin y'aya'n babansu sun kai talatin, sai dai shi ya rasu tun suna k'ananu ainun. Don haka ba wani zumunci suke yi sosai ba a dalilin kishi ya rufe idonsu, sannan mijin ya rasu kowa saita ja gefe da ya'yanta. Mahaifiyarsu kakarmu kenan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu. Mahaifiyarsu kakarmu ke nan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu. Dan haka bata yi aure ba sai da suka girma suka zama samari duk da akwai tazarar shekaru biyar tsakanin Baba babba da Baba k'arami. A lokacin da suka girma kuma ta yi aure ta wuce shekarun haihuwa. Sun taso cikin wata irin soyayya da ririta junanmu don kuwa mahaifiyarsu ta yi matukar cusa soyayya da tausayi a tsakaninsu. Bayan haka kuma sun samu Ilimin addini da na boko. Baba Babba tsohon ma'aikacin gwamnati ne, haka tsohon d'an majalisar dokokin jihar katsina ne tun a jamhuriya ta biyu. Sannan mashahurin manomi ne dan kuwa sai an sako shi a cikin sahun manoma a k'asa gabad'aya ba wai jihar Katsina kawai ba. Baba Babba gabjejen attajiri ne da Ubangiji kad'ai yasan yawan arzikin da ya bashi. Dan na yi imani shi da kansa bai san adadin dukiyarsa ba. Ni bansan hekta nawa yake nomawa a shekara ba balle na hakaito. Idan na ce manomi ina nufin kololuwar manomi ne da yake noman da gaske. Dan kuwa makudan milyoyin kudi yake narkawa a gonaki. Idan kaka'a ta yi kuwa shima ba k'aramin dukiya yake cika dakuna da manyan shaguna ba. Baba k'arami kuwa likitan dabbobi ne. Shima da nasa arzikin tunda yana kasuwancin siyar da lafiyayyun dabbobi, tunda ga kan awakai, tumakai, dokuna, shanaye da rakuma. Shiyasa gidan gonar Baba Babba cike take da lafiyayyun dokuna, rakuma da kuma raguna harma da shanaye da tsuntsaye daban daban. Danginsu dawisu da tatalo, jimina, geese, agwagi, da sauransu. Gidan gonar duk fad'in Funtua da kewaye babu ta biyunta. Domin cike take ainun da dukiyar dabbobi, hatta kaji ana zuba sama da dubu ashirin na k'wai da na ci, kajin Hausa ma birjik ne iya ganinka. Tattabarun da suke ciki kuwa baza su kayyadu ba. Gidan gonar Ladi farms ta yi bunkasar da har Madara ake sarrafawa a cikinta domin shanayen waje masu bada Madara zallah ma yawansu ya kai kurewa. Kifaye kuwa ba'a magana. Baba k'arami ke kula da ita a dalilin shi din kwararren likitan dabbobi ne. Samun kulawa da kiwo na mussaman da suke samu ya sanya dabbobin suke ta bunkasa suna haihuwa akai akai. Idan ana lissafin manyan gidajen gona a Nigeria ba wai a Funtua ko arewacin Nigeria ba sai an sako gonar Ladi farms ta Baba babba. Gidanmu da muke ciki na Funtua tare suka yi ta siyan filayen suka kuma gina abunsu. Kowa zuba kudi yake yi, dan haka mallakinsu ne su biyu. Bayan haka suna da kadarori daban daban da suka yi tarayya a kai. Misali gadonsu basu raba ba. Sannan akwai wasu kadarori da suke siya tare. Amma a zahirin gaskiya Baba babba ya fi mahaifinmu dukiya nesa ba kusa ba. Duk da namu mahaifin ma attajiri ne na gaske. Ina wannan bayanin ne dan ku fahimci labarin da kyau. Iyayenmu biyu hamshakan alhazai ne, sai dai dole wani ya fi wani. Dukkan iyayenmu maza matayensu guda daya ne. Haka kuma Ubangiji ya azurtasu da haihuwa sosai. Ya'yan Baba babba guda shida ne. Wacce matarsa Hajiya Saratu ta haifa masa, muna kiranta da Momi. Ukun farko maza ne Yaya Abubakar, amma Asad ake kiransa, Yaya Umar Faruku, Yaya Usman. Sai Yaya Salaha. Daga kanta an jima sosia kafin a haifi Yaya Munira. Sai Abida da take auta, kuma ita kad'ai na girma duk da dai ba wani fiko ne mai yawa ba, tare aka yi goyonmu. Sunan mahaifiyata Haj Habiba, muna kiranta da Mami. Mu bakwai ta haifemu. Yaya Sulaiman, Yaya Hamida, sai ni Bilkisu, Ansar, Anisa sai autarmu Saddiqa. Idan aka had'amu da y'aya'n Baba babba mun zama sha biyar ke nan. Kusan kowa na da abokin haihuwarsa. Yaya Sulaiman da Yaya Usman. Yaya Hamida da Yaya Salaha. Daga nan sai abin ya juya. Gabad'aya mun taso ne bisa jagorancin Baba babba. Domin baba k'arami idan ya tafi Katsina ranar litinin sai alhamis da yamma yake dawowa. Idan ya dawo din ma mafi yawa yafi zama a Ladi farms sai dare ake samunsa. Gabad'aya mun fi shakuwa da Baba babba, akan mahaifinmu tunda yafi shi haba haba da yara, sannan shi muke ga ni kullum yaumin. Amma kuma Ya Munira tafi shakuwa da baba k'arami, matuk'ar yana gari to duk inda zaka gan shi tare da Munira a gaban motarsa ta shiga ransa ainun fiye da mu ya'yan cikinsa. Iyayenmu mata suna zaune lafiya duk da babu abin da suka had'a. Misali ko wacce bangarenta daban sannan akwai tazara mai yawa. Sai dai dukkan ahalin gidan k'wai da kwarkwata da hadiman gidan ana cin abinci ne daga tukunya guda. Domin akwia sashe guda da na y'an aiki maza masu kula da gyara harabr gidan da shuke shuken gidan, da mata masu girki da gyara cikin gidajen. Kawai umarni ake basu. Mu kuwa yaran gidan kowa na da yancin ya zauna a sashin da yake so ko dai na Baba babba ko sashen Baba k'arami. Idan an fahimce ni bamu taso mun ga banbanci ko wani rikici a tsakanin iyayenmu maza ko mata ba. Shiyasa soyayya ce mai yawa a tsakaninmu gabadaya. Bamu zama yan mata ba aka yi auren Yaya Salaha da Yaya Zainab da Kuma Yaya Hamida fiko mai yawa suka yi mana, amma da yake sai da suka yi digiri a fannoni daban daban mun data kafin a aurar da su. Amma dai ko sakandire bamu shiga ba, kawai muna ita tuna sadda aka yi auren ne. Mun taso mu uku Yaya munira da ni da kuma Abida. *Assalamualaikum barkanmu da lokaci ya hak'uri da ni?* *Ina gabatar muku da wannan labarin nawa, tare da fatan zaku karbe shi da kyau, zan yi matukar farinciki idan har kun bibiye shi cikin nutsuwa*. *Ina kuma bada hak'uri ta yadda bana iya tsallake rubuta labarin da yake d'amfare da zumunci wala na jini ko na abota ko kuma na surukunta.* *Wannan karon labarin harshe biyu gare shi don haka zaku ga ya kasu biyu* *Haka nan labaran Surayya basa nufin habaici ko shagube ga wani ko wata. Dan haka idan an ci karo da abin da ya yi dai dai da rayuwarki, ko ta waninki ba da niyya bane. Akasi ne kawai*. *Fatana dai a yi karatun cikin nutsuwa har a fahimci darasin cikin labarin.* *Surayya Dee* ✍️ [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2347020695644 4 *Contact me 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. Ni da Yaya Munira mun taso cikin wata irin soyayya da shakuwa. Da wahalar gaske mu yi fad'a sabanin da babu jituwa ko kad'an tsakanin ta da Abida. Koda yake ita Abida da ta kasance k'aramarmu tana da wani irin hali murdadde, bata kaunar ka tab'a mata abinta ko kad'an, hakanan ta yi matukar kyamar ka kwanta mata a gadonta. Duk da dama gado uku ne a cikin dakunanmu na kowanne sashe. Bayan haka kuma tana cikin mata masu high taste bata amfani da kowanne irin garabitin abu, sai zababbe. Y'ar kwalliya ce ta sosai tun tana k'arama. A zahiri mun fita kyau, amma da yake tafi mu gayu sai ta fimu daukar ido. Kusan kullum sai ta sani kuka domin ni tun tasowa ta haka nake sanyi kalau mai matukar raunin zuciya. Yaya Munira ke k'watata a hannunta sanadin da ya ta'azzara rashin shirinsu ke nan. Amma kuma bata yarda a ci zalina a makaranta. Nan da nan Abida zata yi makarbiya ta mayar da fad'an kanta ko da kuwa bata yi mini magana. Kazalika basa shiri da Yaya Sulaiman kwata kwata basa jituwa, a cewarta shi din mai nuna son kai ne da tak'ama, a gabanta yake nunawa nice k'anwarsa alhalin yana ganin yadda Yaya Farouk yake mini alkunya fiye da ita. Shi kuma ya ce ra'ayinta da iyayyinta ne basu yi masa ba, yarinya ta yi ta juya mutane, matuk'ar yana gidan to kuwa sai an musu shari'a don sai ya yi mata abin da zata harzuk'a sai da Baba k'arami karami ya yi masa wuta wuta sannan ya daina fitinarta, don kuwa gaban Baba karami ta kai maganar tana rusa ihun ya mata iyaka da shi ko ta kira masa yan civil defence. Ba k'aramin dariya Baban ya yi ba, karshe ya wanke Sulaiman ya ce "ka fitinar mini Abida fa Sulaiman. Maimakon ka jata jikin ka, har ku k'ulla alheri sai ka dinga yi mata sheganta to ina ruwanka da bak'inta? Ina ce dakin Allah ma bak'ine ashe kuwa bak'i ba muni ba ne ba kuma tawaya ba ce! Ya ce "Na daina Baba amma lallai ka ja kunne ta akan gatsinen da take mini tare da harara ko da ban mata magana ba, sannan duk ranar da ta sake kwashe mini takalma idan na ajiye a bakin k'ofa, komai na yi mata ita ta ja". Baba ya gintse dariyarsa ya ce "Kin ji ko Abida ki daina, shima ba zai kara bata miki ba". Ta ce "Shike nan yanzu dai ka sake jaddada masa ka yi mana iyaka babu ni, babu shi har gaban abada". Baba ya kwashe da dariya ya ce "A a ba haka za'a yi ba, ba dhi ba tsokanar ki bare ya saka ki kuka, kema ba ke ba masa rashin kunya, wannan kam na shata muku layi. Duk wanda ya tsokani wani kuwa to la shakka da ni yake fad'an! Daga haka ya sallame su. Shike nan aka samu saukin rikicinsu. Ni mamakin Yaya Sulaiman nake yi idan ya sako Abida a gaba da wulak'anci don magana ma da kyar yake yin ta baya son hayaniya ko kad'an, yayin da Abida take y'ar kwarfniya ta gaske watakila wannan banbancin ya sake hab'aka yar tsamarsu. Muna kammala firamare aka kaimu Makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori(F G.C Bakori). A lokacin Yaya Munira na aji uku(J.S.3) na k'aramar sakandire a Makarantar. Tare ake yi mana komai. Kayanmu a hade suke, amma Abida bata yarda muci abinci tare. Sai dai kwanonta daban. A shekarar kuma babban wanmu Yaya Asad ya yi aure, ya wuce da amaryarsa Asaba da yake d'an sanda ne mai mukamin ASP a lokacin. Sannu a hankali rayuwa take shudewar har muka sami shiga aji uku. Yaya Munira tana aji biyar. Ta fara zama budurwa sosai. Tsayinmu d'aya da ita saboda ni din doguwa ce sosai. Amma siririya sai da ina da kugu sosai. Haka nan farare ne mu tamkar tsada sabanin Abida da take bak'a. Duk gayunta da farar fatarmu basu rudeta ta yi sha'awar sauya launin fatarta ba. Ko mai zata siya sai ta duba ingredient matukar ta ga sinadarin hydroquinone to kuwa zata ajiye shi. Tsayina da sanyin halina ya sanya dalibai suka lankaya mini Bilki sola. Matukar ka ce Bilki sola a lokacin da muke FGC Bakori kowa ya san ni. Ba ni da k'awaye, daga ta botsara Abida sai kuwa Basma Bello Maska. Kawai Ubangiji ne ya k'ulla abotarmu, don tafi dacewa da Abida, masifaffiya ce ta gaske itama. Kawarmu ce gabad'aya tunda ajinmu d'aya haka dakin kwananmu guda. Amma kawancen yafi k'arfi da ni. Da wahala mu yi fad'a sabanin ita da Abida kullum sai sun yi, wani zubin sai su yi sati basu yi magana ba domin dukkansu masu ra'ayin rukau ne, masu ji da kansu ne. Sannu a hankali Yaya Munira ta kammala ta barmu, ta yi sa'a a shekarar ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahamadu Bello ta Zaria. Kafin mu gama FGC mun zama cikakkun yan mata. Da Basma da Abida matsakaicin tsayi ne da su. Sabanin ni da nake doguwa sosai. Na keresu, a wanccan lokacin har kunyar tsayina nake ji, domin bana jin za'a samu wacce ta fini tsayi a makarantar sai dai mu yi taya. Daga sama ba ni da kiba ko kad'an, amma ina da fad'i ta kasana. Gabad'aya kirar jikina ya fi dacewa da kwalbar coca cola. Doguwar fuska gareni mai dauke da siririn dogon hanci tamkar biro. Hakanan bakina d'an tsut mai dauke da jajayen lebuna, da k'ananun hak'ora jerarru farare kal tamkar kankara. Gashin kaina baki mai sulbi har gaban goshina. Sannan a cike take ga kuma tsayi. Kallo d'aya tak zaka fahimci ni din kyakkwar mace ce lamba d'aya sabanin Basma da Abida da suke da boyayyen kyau, irin sai an kallesu da kyau kafin a fahimci kyaunsu. Mun dawo hutun zango na biyu muka yi sa'a Baba babba ya sahale mana muka tafi katsina hutu gidan Yaya Salaha wacce ma'aikaciya ce a ma'aikatar ruwa ta jihar Katsina. Bana manta ranar da muka fara haduwa. Yammacin wata juma'a bayan Yaya Salaha ta dawo daga aiki, ta aike mu, mu karbo mata sak'o a gidan iyayen mijinta a k'ofar bai. Direban mijinta ya kaimu. A k'ofar muka tarar da samari guda biyu. Tun daga nesa muke hangensu da yake fuskar gidan muke nufa. Su kuma a zaune suke kan tebirin da yake girke a k'ofar gidan. Mun fito zamu shiga gidan, idona ya fad'a cikin na dogon saurayi fari tas. Sumarsa ta tabbatar mini yana da alak'a da mutanan Habasha ko Bafulatanin usul. Faduwar da gabana ya yi, a kallon farko ya sanya ni cikin rud'u. K'afafuwana suka hau sark'ewa, da k'yar na daure na bi Abida a baya muka wuce. Zuciyata na cigaba da dokawa da tsananin gaske. Bamu wani jima ba muka fito. Muka sake tarar da su , mun gota su kad'an, kafin mu shiga mota, suka taso da azama. Wanda yafi tsayin ne ma'ana wanda na kadu da kallonsa ya yi jarumtar ce wa "Sannunku y'an mata". Zuciyata ta sake tsinkewa domin sai na ji tamkar wanda hausar tasa ma ta dabance. Ya zuba mini ido, yana son mini kallon tsanaki, gangar jikina ta taya zuciyata rawa. Na kasa amsa masa sannun da ya yi mana. Abida cikin ko d'ar ta ce "Sannunku dai Rijalu! Dariya ta k'wacewa d'ayan mai duhun fata da kuma matsakaicin tsayi. Cikin dariya ya ce "Bari na matso kusa da ke da alamu ke na dad'e ina jira". Ta rausayar da kai ta ce "A a kada ka matso, domin kuwa shekaruna sha shida, karatu zan yi, kuma na likitanci ka ga ina buk'atar nutsuwa mai yawa akan karatuna". Ya sake fadada murmushi ya ce "Nima dalibin ilimi ne, hutu na zo, ina karatun Islamic law a k'asar Sudan. Sunana Lawal ". Ta ya mutsa fuska ta ce "Idan daga Allah ne zai sake had'amu kamar yadda muka had'u yanzu babu tsammani." Ta shige mota. Yayin da na bi bayanta tamkar kazar da k'wai ya fashewa a ciki. Domin gabadaya saurayin nan ya yi matukar tafiya da zuciyata a kallon farko. Ya biyo ni yana ce wa "Saka mini lambar wayarki, mu dinga gaisawa". Murya babu amo na ce "Bama rik'e waya sai mun kammala makaranta." Ya ce "Sunana Sahal Sulaiman Mashi. Ya ciro takarda a aljihunsa ya rubuta S.S.Mashi tare da lambar wayarsa ya jefo akan cinyata tunda nice a setin da yake. Ya sanyaya murya ya ce ga lambata nan ki k'ira dan Allah da manzonsa." Kafin na ce komai direban ya ja motar mun tafi. Muna nisa da unguwar ina sake jin zakuwa da son cigaba da tattaunawa da shi. Shine saurayin da ya tab'a tunkarata kai tsaye, ba wanda zasu rubuto wasika ba. Shine kuma namijin da zuciyata ta fara bugawa a dalilin sonsa. Domin kallo d'aya na gane shi din matukar kyakkwa ne, sannan dogo ne na gaske. Bayan haka na gan shi cikin kwalliya ta burgewa. Na dauki takardar ina kallon lambobin da ya rubuta su a jere cikin wani irin salo. Ga mamakina sai na ji hatta rubutunsa ya shiga raina ko tantama bana yi yana cikin dalibai masu baiwar sarrafa rubutu babu shakka. Na shagala k'warai da gaske da kallon lambobin. Ba zato kawai Abida ta fizge, bata tsaya wata wata ba ta cukuikuiye ta yaga ta wullar ta window. Na zuba mata ido zuciyata na sake tsananta bugawa. Idona ya ciko da k'walla. Na kasa bude baki na ce mata uffan. Maimakon itama ta kama bakinta sai kawai ta ja tsaki mai tsayi tare da ce wa "Nasan kina iya buga masa waya domin na k'are miki nazari na ga ya shiga ranki. Ni kuwa ban miki sha'awarsa ba, domin idan namiji ya cika kyau had'ari ne babba a wajen mace bare ke solobiyo". Har muka isa gida bakina a dinke ruf, na shige daki na kwanta sai kawai na fashe da kuka ina yinsa k'asa kasa amma na bacin rai ainun. A haka Yaya Salaha da Abida suka tarar da ni, duk k'ok'arina na hadiyen kukan sai da Yaya ta fahimci kuka nake yi sosai. Ta rikice ta dinga tambayar ba'asun kukan, na kasa cewa komai. Abida ta ja tsaki ta ce "Wani tsalelen saurayine ya bata lambarsa akan ta nemi shi, shine ni kuma na yaga takardar kin ji sanadin kukan da take yi. Yaya Salaha ta yi jim domin bata tab'a zaton yadda nake very silent har zan fad'a tarkon soyayya tashi guda haka ba. Mussaman da ni ko karance karance bana yi. Abida ce kullum cikin fakar idonta take tana debo littafan Hausa a dakinta tana raba dare wajen karatun. Ta numfasa ta ce "Share hawayenki, Bilkisu, rabu da Abida.". Abida ta yi maza ta ce "Idan an k'addara mijinki ne zaku sake haduwa, amma ni ban miki sha'awarsa ba zubin majununai ne da shi". Yaya Salaha ta d'auki salati tana ce wa "Oh ni y'asu ke Abida wacce irin yarinya ce tun baki tafasa ba zaki kone? Har kinsan kalolin mazaje? Har kina iya banbance na gari da kuma majununi?" Ta yi dariya ta ce "Allah kuwa Yaya ina ganinsa na ji bai mini ba, da ace d'ayan da ya nuna yana sona ne yake sonta da ba zan yaga takardar ba, domin ya yi, kyaunsa kad'an ne, sannan mai wararren kai ne, haka nan bak'i ne. Amma Sallau yake ko wa? Fari ne tamkar tsada, ga kuma alamun izza tare da shi. Sam sam zuciyar Bilki bata dace da wannan ba, domin artabun da zata yi da y'an mata ba kad'an ba ne". Mamakin Abida ya sake daskarar da Yaya a tsaye. Ta ce "Ke mai ya hana ki so wanda ya nuna yana son na ki tunda kin tabbatar shi ba munafiki ne ba?" Ta yi dariya ta ce "Ban shirya aure kusa ba, dan haka bazan bada k'ofar da za'a zo gidanmu da sunan ana sona ba, hakanan ba zan yi gangancin fara soyayya a yanzu ba.". Yaya Salaha ta gwale ta da fad'in " To uwar iya. Idan ke baki shirya aure yanzu ba, kada ki sake toshewa Bilki hanyar samun samari. Ina ce bana zaku kammala sakandire, idan ta samu tsayyaye wanda ya shirya ita aurenta zata yi ba zata zauna ta tsufa da sunan karatu ba. Allah bar shi sai ta cigaba da karatunta a dakinta." Ta ce "To shike nan ba zan sake ba, ta kallo ni ta ce "Sorry Bilki solar soyayya". Yaya Salaha ta ce "Allah ya shirye ki kawai Abida." Ta matso kusa da gadon da nake kwance ta ce "Yi hak'uri kin ji Bilkisu. Tashi ki yi alwallah an fara kiran sallah. Sai kuma kunya ta rufe ni haka siddan. Na kasa koda motsi, yayin da ta juya ta tafi a dalilin ringin din da wayarta ke yi daga falo. Abida ta saki gauron numfashi ta ce "Bilhillazi shiyasa jinimu bai jitu ba, yanzu yadda kike sokokuwar nan ashe abin da yake zuciyarki azim ne, ke ce da kuka akan wanda yau d'aya tak kika d'ora idonki a kansa?" A sanyaye na ce "Kin ga Abida bana shiga shirginki irin haka, kin fitinane gaskiya, ina ce kin yaga takardar kin jefar? Na ro'ke ki, ki shafa mini lafiya pls and pls". Bata kula ni ba, ta dauko littafin HAMIDA na Maryam Kabir Mashi ta hau dubawa sai kuma ta kallo ni ta ce "Sai na ga kamar S.S Mashi ya rubuta ko?" Ban kulata ba na mike na shige bayi domin na sani idan ba wuri na bata ba, tana iya sake sa ni sabon kuka. Ilai kuwa da na fito daga bayi ta bini da ido ta ce "Da kika share ni kanki kika yiwa asara. Niyya na yi a turo mini lambar Anty Maryam Mashi tunda marubuciya ce na sayi shafi d'aya a cikin littafinta na gaba da zai fito kasuwa a yi miki cikiyar S.S Mashi. Nasan da wuri za'a samo shi tunda garinsu d'aya. Watak'ila ma wata cikin danginsu ta ga cikiyar tunda mata mun raja'a a karatun littafi". Na ja dogon tsaki na tada salla na kyale ta. Ita kuwa ta fashe da dariya mai hade da ihu ainun tare da ce wa ",Oh ashe sola macijin sari ka nok'e ce, ana miki kallon salaha nutsatssiya ashe abin da yake ranki kabiran ne. Bilhillazi gwara ni sau milyan da nake fito da zahirina a fili. Haba ai kina cutata Wallahi. Ana ta miki kallon hankali, ni kuma ana mini kallon buzu buzu saboda kawai ban iya nunkufurci irin na ki ba. Komai na ki kunbiya kunbiya, ni ban da gayunki da tsananin son turarenki ban ga me kike yi mai kyau ba ". Har na idar da sallah bata daina zungure zunguren magana ba, har da fad'in tafi kowa shan wahalar rayuwa a gidanmu tunda ni da muka taso tare zuciyata mai fad'i ce, ana mini kallon tausayin ta matsa mini ashe ingiza mai kantu nake yi mata a wajen jama'a, na barta tana ta bankaura tare da harigido, yau Allah ya bayyana mata gaskiyar lamari. Tsananin tisa ni a gaba da Abida ta yi akan maganar S.S. Mashi ya sanya na ware na daina tunaninsa akan dole. Har zuciyarta kuma na fahimci bai yi mata ba da gaske. Bamu koma Funtua ba sai ana saura kwanaki biyar hutunmu ya k'are. Muna sauka a mota da Baba babba muka fara yin tozali. Sanye yake cikin farar jallabiya fara kal haka hular kansa ma fara ce irin ta larabawa. Idonsa sanye da farin gilashi. A tsaye yake cak, duk da ya tsufa amma yana nan da k'arfinsa garau dan kuwa da mai ra'ayin aure ne sai ya auro yarinya k'ankanuwa tunda da kudinsa. Ban ankara ba na ga Abida ta fetsa ta isa gare shi. Shi kuwa ya mik'a mata dukkan hannunwasa yana fad'in lale da Abida k'anwar Bilkisu." Ta kame baki ta ce "Ai Baba na zo maka da sabuwar jarida mai dad'i nawa zaka siye ta?" Ya murmusa ya ce "Na siye ta da d'awisu" Daidai lokacin na kariso na tsugunna ina gaishe shi, ya miko mini hannunsa guda na rik'e nima. "Cikin kanzagi ta ce "To Bilki dai ta yi kasuwa ta samo wani irin mutum da kiris ya rage ya shiga sahun zabiya ta makance a kansa, gara tun wuri ka sani babu ajandar karatu a wajen ta." Tana rufe baki ta falfala a guje ta yi cikin gida. Yayin da na yi k'asa da kaina ina jin kunya da nauyi suna mini kawanya. Ya sassauta murya ya ce "Mai gadon zinare da gaske kanwar ki take yi ko kuwa shegantakarta ce?" Murya babu amo na ce "Yaya Salaha ce ta aike mu gidan inlaws dinta, sai suka tare mu a k'ofar gidan, d'aya ya ce ni, d'ayan kuma ya ce ita." Ya murmusa ya ce "Ashe har da ita ma ta yi kasuwar?" Na sake sunkuyar da kaina kasa ban amsa ba. Ya ce "To sai kuka yi ya ya?" A hankali na ce "Ita ta ce ba zasu shirya ba domin karatu zata yi mai yawa. Ni dai ban yi magana ba, amma ya ce na ba shi lambar wayata, na ce ba ni da waya, shine ya rubuta mini tasa." Ya numfasa ya ce"idan kin nutsu ki kawo mini lambar ". Murya babu amo na ce "Abida ta yaga tun a ranar". Da azama ya ce "Saboda me?" "Ta ce siffar munafiki ne da shi, sannan tunda fari ne bai yi ba". Dariya ta sosia ta kama Baba ya ce "Allah ka shirya Abida." Ya ce "Ki yi hak'uri, idan daga Allah ne zai kawo dalilin da zai sake had'aku. Sannan duk wanda ya nuna yana sonku lallai lallai ku turo shi gidanku ya nemi izinin magana da ku. Tashi ki shiga, ki fad'a mata kuma bata ci kyautar d'awisu ba". Na yi murmushi na ce "To ni kuma da na fad'i gaskiyar magana fa Baba?" Ya ce "Kin ci kyautar talo talo sai ki soya ki tafi da abinki makaranta." Da murna na ke yin godiya. Sannan na isa cikin gidan. Bangarensu Abida na fara isa, abin farinciki na tarar da Yaya Munira ta zo hutun mid semester. Da gudu na rungume ta ina jin farinciki har cikin zuciyata. Na sake ta muka zauna muna gaisawa sosai. Abida ta fito daga bayi tana fad'in Yaya Munira na siyarwa Baba jaridata ta yau, amma me za ki ba ni na fesa miki?" Cikin sace iska Yaya Munira ta ce "Rik'e abar ki dan kuwa ba ni da abin bayarwa." Domin al'adar Abida matukar ta baka labari sai ka biyata, shiyasa tafi kowa y'an canji ko abin dad'i. Yayyenmu maza Abida guntsi fesa suke ce mata, kuma ko a kwalarta, haka nan idan ta fad'a maka abin da baka sani ba, baka biya ba, to ta ringa yi maka bak'in naci ke nan, ko ta dauke wani abu naka mai muhimmanci, shiyasa Yaya Munira bata yarda ta sayi jaridarta, dan kuwa k'arshe sai dai Momi ta biya ko Baba ya biyata da kaza ko tattabaru. Shiyasa ita kad'ai ce mai dakin kiwo a gidanmu. Daga can bayan gidajenmu aka yi mata dakunan kiwon tattabaru da na dabbobi. Wato Abida kes ce babba. Kowa kuma ya sani ta shiga ran Baba babba ainun, duk da yana iyakacin k'ok'arinsa wajen dannewa baya ware ta ya fifita ta. Amma matukar ta murde akan ta siyarwa wane ko wance jarida ba'a biyata ba, to fa dole Baba ya bata auren tattabaru, ko kuma ta tubure sai tunkiya shiyasa ta had'a nata garken. Ban da haka ko labarin littafi bata yinsa a banza siya ake yi. Ta kan ce ba zai yiwu ta zauna ta bata lokaci ta yi karatu ba, sannan ace ta bada labari a bagas ba. Ba ta yi arahar hakan ba kuma zata zama haka ba. ✍️ [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 5 *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* *Egyptian abayas* *Egyptian nighties*. *Bags and jewelries* *Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria* *Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*. # +201121544627 # +2349162662750 Yini guda muna ta namu kasafin a dakinmu, sai da muka sallaaci la'asar sannan muka dunguma sashenmu suka gaida Mami muka cigaba da yin shiriritarmu. Sai da magariba suka tafi. Yaya Munira tana ta jaddada mini na taho mu kwana tare sai gobe mu zo nan mu kwana. Bayan sun tafi Mami ta zuba mini ido cikin takaici ta ce "Sokokuwar banza sai yanzu kika ga damar zuwa mini? Tun azahar kuka dawo amma kika kasa zuwa sai dazun nan! Munira tun safe ta zo gidan bata zo ta gaishe ni ba. Abida kam ai ko motar bata gama tsayawa ba ta yi wajen uwarta, amma ke da yake baki bani muhimmanci a duniyar ki ba, ai kin bisu kin tayasu adana uwarsu. Ke kam kin yi asarar hali gabadaya, sunan Saratu kika fi dacewa ki amsa ba mai gadon zinare ba." A tausashe na furta "Ki yi hak'uri Mami". Tsaki kawai ta yi, ta shige dakinta. A wannan ranar a sashenmu na kwana domin fargaba nake yi na ce zan tafi wajensu Yaya Munira. Da daddare Yaya Sulaiman da su Ansar hadi da autarmu duk muna falo tare da Mami sai fad'a mana rikicin da take yi da yan'uwanta, tare da ankarar da mu y'an uwanta sun wareta ne dan mijinta ya zarta nasu. Sannan dangin Babanmu kuwa suna fifita Momi a kanta dan suna ganin Baba babba ne don 1. Alhalin arzikin tare da mijinta ne. Ni dai ban tofa ba, ina safare ina jin babu dad'i, domin kaf dinmu bamu son yan'uwanta a dalilin yawan laifinsu da take furzarwa a gabanmu babu sassauci. Sannan dangin Babanmu ma a hagunce muke kallonsu muna ganin sun fi son Momi da y'aya'nta. Ansar da yafi kowa bin ra'ayinta ya ce "Rabu da y'an kusun uwa Mami! Shiyasa gabad'aya bana musu gaisuwar arziki daga dangin na ki har na su Baban, gabad'ayansu na washe su, me zan yi da wanda zai musgunawa uwata?" Ta muskuta tana jin dad'in yadda yake taya ta son komai tamkar dai mace. Ta numfasa ta ce "Da wayonka ka taso ka ga yadda nake tiritiri da y'an uwana menene bana d'ora maka ka kai musu, duk zanin da na cire idan zan bayar su zan bawa amma tsabar hassada basa yarda su fad'i alherina, komai zan basu a raine ne, kowacce ta zuba mini ido, ina auren mai wadata alhalin asirin ciki sai hanji. Komai d'an-uwa ya yi babakere a kai, me za'a yi da kasafin gidan nan ne?" Suka had'a baki wajen fad'in "Ai Baba k'arami ne ya sarayar da y'ancinsa gabad'aya fa ya koma tamkar yaron Baba babba ne ba wai d'anuwa ba. Kuma abin kaicon dukiyar tasu ce gabad'aya, watak'ila ma ta Baba k'aramin ta fi rinjaye, ya kasa tsayawa waje d'aya, yau na Katsina gobe na Funtua. Idan ya zo garin ma idan kana son ka samu hankalinsa ainun sai dai ka bishi Ladi farms yana can yana k'arar da lokacinsa cikin dabbobi". Na saki gauron numfashi tare da kame bakina duk kuwa ina da kalamai fal a zuciyata. Nan da nan Mami ta hauro ta dinga surfa mini sababi tana furzar da kalamai masu ciwo. "Shashar banza mai za'a yi da zuciya irin ta ki. Munafukar wofi, to duk iyashege irin na ki, ni ce dai kanki ya dawa, domin ni din da ba kya so, ni ce na kawo ki duniyar." Murya babu amo na ce "Ta ya ya zan k'i ne Mami? Na roke ki yi hak'uri." Gabadaya suka yi mini ca suna kaico da ni, a lokacin kuma na fara fahimtar dukkan y'anuwana suna matukar jin zafina a dalilin nafi shaƙuwa da yaran Baba Babba a kansu, duk da basu tab'a tunkarata kai tsaye ba. Amma maganganun da suke amayarwa tare da yi mini kaico ya sanya na fahimci dukkansu masu wahalallen ra'ayine, basa raina abin yin sarhutu. Hatta su Ansar da suke kannena sai da suka saka baki wajen caccakata. Babban abin da yake ba ni mamaki idan an had'u basa nuna adawarsu da iyalin Baba babba, hatta Mami idan suna tare da momi da yaranta sai ka rantse babu komai a ranta na gilli saboda tsananin yadda ta iya hadiye komai. Idan na zauna ni kad'ai ina nazartar yadda al'amarin yake gudana sai kaina ya yi mini nauyi ainun. Tare da hasashen ko Momi da yaranta ma suna adawa da yadda Baba babba yake wahala da mu babu banbanci da iyalinsa? Wannan tunanin na matukar caja mini kai, domin ni a lokacin ban yi zaton za'a iya mua'amala da fuska biyu ba. Kullum kwanan duniya wannan tunanin na dabiar ahalina ya haifar mini wani irin tunani dangane da mutane, a hakan na samo sha'awar son nakaltar halayyar danadam. Sai dai ban samu damar hakan ba, a dalilin zuciyata a sake take. Sai nake yiwa mutane hukunci da yadda nake. Bana zargi, bana munanan zato. Da naga tunanin halayyar momi da yan'uwana zai gigita ni, sai kawai na daina matsawa kaina, bana tunawa sai idan ina gabanta, sa'a d'aya ma bata nunawa a waje ,sai imu imu. Sai dai kuma hakan ya janyo kulli da yawa a zukantanmu. Misali mafi yawa muna yiwa kowa kallon munafukanmu ne. Ma'ana a bazance muke kallon danginsu Baba, tare da zargin sunfi son su Abida. Haka dangin mami. Tsakanina da Allah ni bana wannan akidar haka ma Yaya Sulaiman yana da sassauci, to amma Shi wani irin mutum ne da Magana ma bai cika yi ba matukar bata shafe shi ba, dan haka Duk abubuwma da Mami take fada ko take yi, a dunkule zai ce "Yi hakuri, Ki cire komai a ranki,, Allah ya Baki Ni, ba abin da ba Zan yi miki ba na jin dadi". Ga shi a wajenta ba ni da kwarjini ko kad'an. Haka nan yan'uwana basa yarda su yi maganar sirri matukar ina wajen, sun riga sun yi amanna nafi son Momi akan Mami na kuma fi kaunarsu Yaya Munira akansu, wanda ba haka ba ne duk yadda nake son y'aya'n Baba babba dai bai kai y'aya'n da mahaifiyata ta haifa ba, hakanan ba zai yiwu na so uwar wasu sama da tawa uwar ko hauka take yi kuwa. Haka dai na lallaba kwanakin hutunmu suka k'are. Ranar da zamu koma makaranta an kammala shiri tsab har mun shiga mota mun zauna, sharrin karfe juyin duniya mota ta tashi amma ta ki. A lokacin motocin gidan hudu ne, ta Baba babba d'aya, ta Baba k'arami d'aya sai guda biyu ta amfanin gida. D'aya ta amfanin gidan ta yi faci, wacce kuma aka shirya a kaimu a ciki ta k'i tashi.nBaba babba da yake tsaye ya ce "Sai a nemo bakanike dan kuwa ta'azziya zan je Maska." Abida ta ce "Gaskiya Baba motarka ce baka son bamu, tunda motar nan ta iso kake kaffa kaffa da ita. A lokacin mota kirar 190 ta hamshakan Alhazai ce. Ya ce "Da ace yayanku na gari da sai na bashi motata ya kaiku domin na gamsu da tukinsa. Amma babu yadda za'a yi Faruku ya ja mini mota". Yaya Faruku ya bata fuska ya ce "Baba kana bada ni a gaban Abida, domin Bilkisu a nutse take." *MalaysianFabrics* *Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.* *Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.* *7020695644.* Abida ta yi caraf ta ce "Yaya Faruku na rantse maka nafi Bilki hankali, green snake ce ita. Da kasan abin da ke zuciyarta da ka fasa yin amaryar da ita." Na galla mata harara na ce "Yo ni ma tuni na fasa yin da shi, tunda ya riga da ya yi aure har ya haihu ai ya zama cus". Baba ya yi dariya ya ce "Ai kuwa dai Mai gado tunda bai jira ki ba, ba zai same ki ba". Cikin barkwanci Yaya Faruku ya kalle ni ya ce "Kada ki bari su ruguza ginina a zuciyarki? Ba kin ce ko matana uku ke ce ta hudu ba?" A zabure na ce "Da ne Wallahi! Ai garama Yaya Usman da kai, tunda dawowa kawai na yi na ga ka yi aurenka! Ko a fuska baka tab'a nuna kana da wata budurwar ba". Baba babba ya fashe da dariyar da bai cika yinta ba. Abida kuwa har wani juyi take yi, tana fad'in "Yau an ji kanku da Yaya Faruku" Domin mutumina ne na gaske. A zahiri kuma yake nunawa yafi sona akan Abida. Kafin ya bata abu d'aya ya bani sau biyar. Idan kuwa tare ya siyo mana sai na zaba sannan zai bata wanda na bari, ko kuma ni ya tambayi ra'ayina kafin ya siyo abu, ita kuwa baya tambayarta. Hakan da yake yi yana dadawa Baba babba da Momi zuciya. Tunda haka siddan Yaya Asad ya tisa ni a gaba ina k'arama a dalilin ba ni da gashi. Ina kuma shan majina sannan shiru shiruna ya yi masa yawa. Matukar yana falon momi bana iya ko da wucewa ne. An yi anyi ya daina mini muzurai da razana ni, amma fir ya ki, shiyasa na taso da matsanancin tsoronsa. Bama shiri ko kadan Kamar dai yadda Yaya Sulaiman ya tisa Abida a gaba Duk da Shi ba cin zalinta yake yi ba, kushe ya yake tare da gwasaleta. Sadda muke firamare shine yake kaimu makaranta a mota idan ya zo hutu daga makarantar horar da y'an sanda ta Wudil. Matukar Baba babba ya ga na bace masa a gidan to Yaya Asad na gari. Wata rana na shiga wajensu, banbsan dodon ya zo ba, sai ganinsa na yi gurfane gaban Baban yana sanye da kakin yansanda wanda a lokacin bai fi wata da fara aikin ba. Ina ganinsa na juya zan zura a guje. Yaya Faruku ya yi maza ya ruko ni ya ce "Ke ba abin da zai yi miki." Yayin da shi kuma ya galla mini harara tare da ce wa "Nutsu ki zauna ko na d'ora miki duniya a kanki ". Ai kuwa jikina ya hau tsuma domin kakinsa yasa na sake tsorata da shi, hakanan ni da Abida muna matukar tsoron ya d'ora mana duniya. Wani abu ne da shi mulmulalle mai tsananin nauyi da yake dagawa na motsa jiki, idan ya so mana mugunta sai ya ce sai mun yi kama kama mun matsar da shi gefe wanda bama iyawa ko motsa shi, a haka zamu yi ta yi har sai mun gaji sannan zai ce mu bari. Baba ya kalle shi ya ce "Ba dan ka yi mata tsufa ba da na baka aurenta na ga yadda zaka yi, ka takura sarauniyar shaiba da yawa Asad." Yaya Faruku ya yi fit ya ce "Haba Baba a gabana zaka bawa tsoho auren amaryata, ai Bilkisu tawa ce". Yaya Asad ya ce "ina da shekaru ashirin da bakwai kana da ashirin da biyar menene banbancin namu da zaka jingina mini tsufa? Ni mai zan yi da wannan y'ar tastitsiyar yarinyar da har yau da ta ke cika shekaru goma bata bar cin tasono ba". Sanin da na yi ya hana ni cin tasono ya sanya ina rawar murya na ce "Wallahi ban ci ba, ko rannan da Abida ta ga nasa hannuna a hanci na kai baki ba tasono ba ne, amma ta ce sai ta fad'a maka ". Gabadaya suka saka dariya ban da ni da nake ta zufar fargaba. Domin wahalar gaske yake ba ni wajen cewa sai na d'ora duniya a kaina. Baba babba ya ce "Ke rabu da shi kin ji. Daga shi har Faruku duk sun yi miki tsufa". Da sauri na ce "A a Baba Yaya Faruku ne" Suka sake yin dariya, yayin da Yaya Faruku ya yi ihun murna tamkar ba a gaban Baba yake ba. Da alfahari ya ce "ai tuni mun saito ta da Bilki komin tsufana ita ce amaryata". Na numfasa daga hakaito kuruciyata da ban yi nufin budewa gabad'aya ba, na kalli yadda Abida take murnar gwale Yaya Faruku da na yi, tunda har yau da muka zama y'anmata yafi jana a jikinsa fiye da ita, ko gidansa muka je yafi haba haba da ni, lamarin da yasa matarsa ta washe ni ainun tun ban fahimci inda ta dosa ba har na gane, shiyasa da na yi wayo sai na daina zuwa, domin muddin muka je hutu to fa ba shi ba zama lafiya a gidansa har sai mun bar gidan. A garin Funtua yake zaune, shine kuma yake kula da shige da ficen kudi na Ladi farms, tunda Yaya Asad ya yi nisa yana Kebbi shekaru biyu kenan ya bar Asaba. A lokacin kuma yaransa biyu duk mata. Yayin da Yaya Faruku yake da yaro namiji. Na tausashe murya na ce "Har gobe ni ce amaryar Yaya Faruku" Da yake shi mai haba haba ne yafi dukkan mazan gidanmu wayayyen kai, domin idan ya shiga cikin mata sai ka rantse shima mace ne, idan biki ake yi a gidanmu kuwa cikin su Yaya Salaha yake shiga a yi rawa da shi yana musu liki, gabadaya rayuwar Yaya Faruku abin sha'awa ce, baya da damuwa, ba shi da tsanani ga shi dan gaye na sosai kuma fari irin wanda nake so. Amma Yaya Asad ga bak'i, ga shi mummuna, duk da dai Abida ta ce nice nake ganin muninsa tunda na rufe zuciyata a kansa, ni kuwa bana yarda da maganarta duk da ban tab'a tsayawa na masa kallo sau biyu ba, amma nasan dogo ne mai murdadden jiki tunda ma'abocin motsa jiki ne ainun tun tasowarsa. Tabbas sifarsa ta dace da jami'in tsaro. Ya yi tafi ya ce "Ni nasan duk yadda ake kushe ni nasan sarauniyar shaiba tawace". Baba ya sake murmusawa, yayin da Abida ta yi gum alamun bata da tace wa. Tamkar jifa sai gani muka yi mai gadi na bude tangamemen get din gidan. Moto kirar pegoeat ta shigo, sai kuma wata irin ta y'ansanda mai dauke da logon y'ansandan k'asa reshen jihar Kebbi. Motocin na tsayawa wani ya yi saurin fitowa ya bude k'ofar Yaya Asad ya fito da alamu shine jagorar tafiyar gabad'aya. Yana fitowa suka fito da azama. Shi kuwa ya durfafi Baba babba kai tsaye. Yana zuwa gabansa ya cire hular kansa ya kame tare da sarawa Baban wanda hakan shine kololuwar gaisuwar girma a gidan jami'an tsaro. Haka tawagar y'an sanda har su takwas suka yi layi suka yi Baba kwatankwacin yadda ogansu ya yi. Shaukin gaisuwar ta debi ni, karon farko na ji sha'awa aikin damara ta shige ni. Domin an yi ittikafin babu inda ake girmama wanda ya wuce ka mukami irin a aikin d'amara. Abida sarkin kankanba ta yi maza ta matsa jikin baba tana ce wa "Baba pls na shiga rigar nima a mini wannan gaisuwar dan girman Allah." Baba ya bibbigi bayanta tare da ce wa "Ho Abida! Su kuwa da suka koma gefe sai suka sake matsowa suka jeru, suka cire hulunan suka yi mata tata gaisuwar tamkar ita ce momi. Dad'i ya kamata ta dinga dariya tana fad'in thank you so much ". Yaya Faruku ya matso gabana ya yi mini yadda ya ga sun yi, ya ce "Bilkina duk da ni farar hulane karbi tawa gaisuwar." Na yi murmushi tare da ce wa "Na karba da godiya Yaya Faruku". Ba zato kawai Yaya Asad ya yi mini yadda ya yiwa Baba babba. Kaina ya fasu na kasa boye kaduwar da na shiga a dalilin yadda ya girmama ni. Ba tare da bata lokaci ba yaransa ma suka ƙame mini. Karon farko da Yaya Asad ya kambaba ni. Murya ba amo na ce "Na gode sosai Yaya! Takaici ya shake Abida. Ta ce "Bilhillazi Bilki kin shiga uku, ni dai kam bansan me yasa aka had'amu sa'anni ba, haka kawai sai gana mini azaba kike yi. Ni sai da na roka aka k'ame mini, amma ke baki roka ba, har shugaban bataliyar ma ya rusuna miki, ga Yaya Faruku farar hula, haba haba gaskiya kina k'warata! Gabadaya wajen aka dauki dariya domin kowa yasan zata mayar da gaisuwar da aka mata wani abin alfahari ne. Sai gashi nima an mini fiye da tata. Daidai lokacin Yaya Sulaiman ya shigo harabar gidan a lokacin kuma yana ta shirin tafiya k'asar Germany dan yin karatun likitanci. Duk da basa shiri ko kadan ya ce "Abida yau d'aya bari na miki alherin da kike ta fadin ba ni da shi". Ta galla masa harara tare da ce wa "Ba an mana iyaka ni da kai ba? Na rantse sai na fadawa Baba k'arami". Ya k'ame mata tare da sara mata ya ce A yafi Malam Sule Abidan Baba". Ta wani dauke kai ta ce "Na karbi tubanka, ban sani ba ko ba zaka dawo ka tarar da ni ba, ko kuma kai ba zaka dawo ba". Jikin kowa ya yi sanyi amma Yaya Sulaiman ya ce "Yauwa Abida Allah ya yafe mu gabadaya ba sauran fada in sha Allah a tsakaninmu. Sannan in sha Allah zamu tsufa kafin mu mutu". Daga haka ya koma wajen Yaya Asad da jama'arsa yana marabtarsu. Wannan karamcin da Yaya Asad ya yi mini ya sanya na saci kallonsa na k'are masa kallo. Tabbas ba shi da muni ko kad'an, sannan kuma ba zai shiga sahun masu kyawun fuska ba, mussaman idan da su Yaya Faruku, da kuma saurayin da na kasa mancewa da shi S.S.Mashi. Amma kuma duk ya keresu haiba da ginannen jiki. Abida ta ce "To ga shi Allah ya kawo Yaya Asad sai ka bashi motar ya kai mu Baba". Yaya Faruku ma ya ce "Ai kuwa dai, ga shi". Nan da nan Baba ya canja fuska ya ce daga zuwansa ko ciki bai je ya gaisa da iyayensa ba, bare su sha ruwa sai ya hau kai ku makaranta?" Abida da take son a kaimu a motar dan darajarta ta k'ara d'aguwa ta mairairaice ta ce "Ina Funtua ina Bakori Baba babba? Balle a wajen jami'in tsaro irin Yaya Asad ba sai ya arce da k'afafunsa ba ma, bare a mota". Gabadaya y'ansandan suka sake yin k'asa da kansu suna dariya tare da fad'in "drama girl". *Contact me 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* 06 *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Dan Allah Ki zo mi saka order din ciccibin garari ko kazar sababi Ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*. Yaya Asad ya ce "Ni ne zan kai ku? Shekara da shekaru wa yake kai ku?" Ni dai da ba wani sakewa da shi na yi ba, ban ce kanzil ba. Yaya Faruku ya ce "Baba ne ya ce "Ba zai ba ni motarsa na tuka ba, wacce kuma aka yi nufin kaisu a ciki ta k'i tashi. Shine ya ce kai kad'ai zai iya bawa motarsa. Sai kuma Allah ya kawo ka babu zato ba sai ka kai su ba ". Nan da nan ya ce hakkun ya aki Umar. To marabci wadannan da na zo da su." Cikin girmamawa ya karbi mukkullin mota a hannun Baba babba. Shi da Yaya Faruku suka kwashe kayanmu suka dawo da shi motar da za'a yi tafiyar da ita bayan ya dakatar da tawagarsa da suka yi nufin kwashewa tare da ce wa "Wannan hidimar ta mahaifina ne dan haka ni yafi cancantar na yi da kaina". Ni na shiga gaban motar a dalilin yadda nasan Abida owners coner ne wajen zamanta tana matukar son ta zauna a wannan gefen ana janta, ita kuma ta hakimce bayan ta sanya glass ta hau duba mujallar Tambari ta ado da kwalliya ko littafin Hausa. Ni mamakin yadda take daukar ta d'aya nake yi. Domin yana wahalar gaske ka ga Abida ta yi karatun da ya shafi na boko, matukar zaka ganta a nutse tana karatun cikin nutsuwa to kuwa littafan Hausa ne ko mujallar ado da kwalliya ko kuma na girke girke. Amma karatun boko a gajarce take yinsa. Daga k'arshe sai na gano tana cikin jerin dalibai da ake kira student with high I.Q. Tana da tsanin hazakar da ta kerewa dukkan y'aya' matan gidanmu. A maza kuwa da Yaya Asad da Ansar k'anina zasu fafata. Ni kam average ce, ba ni da hazaka sai naci, nacin ma na dole ne, domin hidima iri d'aya ake yi mana, amma kullum ta kawo sakamako mafi daraja wato 1st position, ni kuma na dinga kawo babu yabo, babu fallasa. Kishin haka ya saka nake nacin karatu tare da bita har na samu nake kawo sakamako mai kyau domin bana wuce tsakanin 5-9. A duk sadda zamu tafi a hanya sosai muke hira da Yaya Faruku ya yi ta zolayarmu tare da sakamu dariya ta hanyayoyi da dama har ya ribacemu mu manta fargabar komawa makaranta. Amma a wannan tafiyar tsit kake ji hatta Abida da ba wani shayinsa take ji ba, baka jin bakinta, a karshe ma sai ta ciro da littafin Tsuntsu duka Tsuntsune na marigayi Malam Abubakar Imam ta hau nazarinsa, domin ta ce ba karatu take yi kawai a littafin ba, har da nazarin yadda zata samu azanci. Mun fara nisa amma gabadaya a takure nake zaune. Wani irin abu ya mamaye ni na rashin sabo da zullumi, na dinga jin tamkar na ce ya dakata na koma baya. Na dinga mutsu mutsun rashin sukuni. Ya kalle ni ta madubi ya ce "Ina fatan yadda kika zama tsaleliyar budurwa no more cin tasono". Na yi k'asa da kaina cikin jin kunya k'warai da gaske. Abida ta yi gajeriyar dariya ta ce "Ta daina cinsa amma kasan farce take ci duk girman nan nata ". Ya ce ",Wonderful! From Shan majina, to cin tasono, to cin farce, sannu mai sabbin update". Abida ta fashe da dariyar iyashege tare da ce wa "Bak'in ciki kamar na sume idan muna tafe tana fama cusa yatsu a baki, gabad'aya sola ya danne zahirin sunanta. Ya murmusa ya ce "Wai ke autar Momi waye babba a tsakaninku ne? Na ga fa kin rainata da yawa". Ta ce "Ai ita ce gabad'aya wata iri ce, ba wadanda yasan wacece Bilki sai Allah sai ni". Ya share Abida ya juyo gare ni tare da ce wa "To ki bude kunnen ki da kyau. Ba hadisi ba ne, amma maganar masu Ilimin rayuwa da hikima ne, ta yadda idan suka yi magana ko hasashe sau tari yana zama wajabat. Cin farce mafi yawa ance yana dauwamar da mai yinsa cikin kunci da talauci. Kina son daga gidan arziki ki fad'a na talauci ne?" Na girgiza kai da sauri. Ya ce "To ki daina cire farce da baki." Da hanzari na ce "Tom". Abida ta ce "Allah yasa dan ya riga ya zame mata addiction". Yaya Asad ya ce "Zata daina mana Abida". Yadda ya yi maganar sai na ga kamar ba azababben nan da yake kidima ni ba. Na saci kallonsa na ga still yana nan a mai siffar k'arfi, bai yarda ya tara teb'a ba. Ko a yanzu yafi matarsa kuruciya, haka nan sai ka dauka bai yi aure ba, duk da shekarar da muke shiga sakandire ya yi auren ga shi yanzu idan mun dawo mun kammala. Ya waiwayo ya ce "Wai ke kallon me kike ta bina da shine haka? Tun dazu nake jin kallon ki a jikina, kada ki bari fa na juya na d'ora miki duniya". Abida ta kyalkyale da dariya mai yawa. Yayin da na yi muk'us a dalilin babu sakewa a tsakaninmu. Sai da ta yi dariyar da ta ishe ta sannan ta ce"Kasan kullum idan muka je sashen samari bata yarda ta wuce ta kusa da duniyar, kuma bata gajiya da fad'in duniyar Yaya Asad bana son ki". Shima ya yi dariya amma ba mai yawa ba sannan ya guntse fuska ya ce "Oh ba kya son duniyata? To ki tabbatar idan ba ki daina cire farce da baki ba, kina tare da ita. Kun cike jamb ne?" Murya babu amo na ce"Eh". "Wanne course kika cike?" A hankali na ce "Computer science " Ya ce"da kyau". Ya mayar da hankali kan tukinsa ba tare da ya sake fad'in komai ba. Abida ta ce "Yanzu kai ma babban Yaya haka zaka mini? Ai dai ni ce y'ar dakinka, amma ka tambaye ta akan karatunta ni baka tambaye ni ba, alhalin haka Yaya Faruku yake nuna mana banbanci, na yi ta cika bakin dan nawa yayan ya yi nisa ne, shine daga zuwanka zata k'wace mini kai?" Ya bugi sitiyari bayan ya yi murmushi mai sauti ya ce "Wa zai shiga tsakaninmu, ai nasan ke guru ce, na kuma dad'e da sanin burinki, ki zama likita, ashe kuwa ba sai na tambaye ki ba, ita kuma na tambaya ne dan ta d'an saki jiki da ni, ba ki ga yadda ta takure ba ne?" Ta numfasa ta ce "Na fahimta yanzu, amma da na ji haushi domin na kai kololuwar gajiya da yadda ake k'unsa mini takaici akan Bilki, da yadda ake yabon ta fini nutsuwa." Ya yi dariya tare da ce wa "Autar Momi ke ma ki zama marar hayaniya irin ta mana, kinsan nutsuwa a wajen mace adone na mussaman da yake kawata ta fiye da adon da ake yiwa fuska". Ta yi fit ta ce "A a Yaya bar ni na dinga k'watar kaina a wajen jama'a ita ma shiru shirun nata na nunkufurci ne, ni tunda muka je Katsina ta nemi rikicewa akan wani solalayi mai zubin makirai na tsorata da ita na fahimci ta wuce tunanina." Da mamaki ya ce "Maigado wannan kike nufi?" Da kazangi ta ce "Bilkin da take gefenka dai." Ya numfasa ya rasa abin fad'i. Can ya sake numfasawa ya ce "Wonder shall never end! To kuma ta fasa da Faruku ne?" Abida ta ce "Ai tunda ya yi aure ta ce "Ta fasa fas dama kuruciya ce". Ya kallo ni kad'an ya mayar da fuskarsa a kallon gabansa. Ya ce "Maigado wai kin fasa da Faruku da gaske?" Da yake ni ban iya karya ba, ko zagaye zagaye ba. Sai kawai na daga kai tabbacin eh. Ya ce "Ikon Allah ban yi zaton akwai lokacin da zaki ce soyayyar da kika wanzu kina yi masa zata zama ta kuruciya ce ba. Lallai yau na sake fahimtar al'amarin mata da kuma kuruciya babban al'amari ne da ba zaka ganesu ta dad'in rai ba." Abida ta sake ce wa "Kasan tun akan auren da Yaya Faruku ya yi na karaya da lamarin Bilki. Domin ranar da muka dawo ta samu labarin ya yi aure kukan da ta yi ba kad'an ba ne. Sannan sai wanccan term din fa ta yarda suka shirya take kula shi. Gabadaya boye masa take yi. Shima sai da sharadin ita ba budurwasa ba ce" Yaya Asad ya saki gauron numfashi ya ce "Allah ya kyauta. Amma dai ki dage da karatu, kar ki yarda ki jefa kanki a cikin had'arin soyayya. Idan kika yi Ilimi maza da yawa zasu so ki kala kala. Sai ki ga har da manyan mutane masu rik'e da mukamai daban daban ko manyan Alhazai y'an kasuwa". Abida ta sake ce wa "God forbid auren d'an kasuwa, basu iya komai ba sai ra'ayin ruk'au, da dunkufe cigaban mace". Cikin kaduwa ya ce "Autar Momi gaskiya kin kerewa tunanina, wato saboda kun girma ba'a gabana ba ya sanya giggiwar ki ta yi yawa ko? Ki tabbatar a gidana zaki yi karatun ki na jami'a, na ga alama sai na sake sanya ido akan ki k'warai da gaske." Yana rufe baki ta yi maza ta ce "Haba Yaya ai idan sallar daren da nake yi akan Baba ta karbu ai abroad zan wuce na yi karatuna. Sola zaka dauka ka saka mata ido tun bata daukowa kanta mijin kara da kiyashi ba". Kan dole ya yi shiru yana mamakin yadda k'ananun yara suka girma tashi guda. Ya numfasa yana tuna shekarar haihuwarsu ya kammala karamar sakandire. Har suka k'arasa garin Bakori bai bar mamakin wayewar da ya gani tare da Abida ba. Haka nan shiru shirun Bilki da yake ganin ya yi mata yawa tun tana k'arama ya fahimci ya bita har kan girmanta da alamun rashin wayo a tare da ita, amma kuma ya fahimci tana cikin mata masu tsananta soyayya masu tsananin kishi. Wanda hakan alamun mace na cikin kalubalen fad'awar gararin rayuwa. Domin abubuwane guda biyu da mace ba zata iya tsallakewa ba. Na farko soyayya ta zama mahadi ne na rayuwar kowanne bil-adama har ma da wasu halittun irinsu jinnu da dabbobi. Sannan kuma kishi shima wani gini ne da ba zai yiwu mace ta rushe shi daga jikinta ba. Shi a yanzu da yake da shekaru shida da aure matarsa bata huta da saka masa ido ba, bata hutar da zuciyarta zullumin kada ya so wata ko ya kula wata macen ba. Duk da babu wata k'ofar da ta ga ni na ce wa yana soyayya da wata macen. Shi a karan kansa ya k'yamaci polygamy domin yana kallon artabun da ake yi a tsakanin yan'uwan da suka fito daga mabanbanta iyaye mata. Mahaifi kuwa kullum a cikin zargin yafi karkata a wani bangare yake, mafi yawa iyaye mazan da suke da mabanbanta iyalai sun fi saurin tsufa da gajiyawa sabida tsananin zullumi da fargabar yadda ahalinsu suke a wargaje. Bayan hakan y'aya'n kullum a cikin artabu suke da matan uban, haka matan uba a cikin dauki ba dad'i ake da su akan y'aya'n da ba nasu ba. Wadannan dalilan ya sanya ya k'i polygamy ya k'udire mace guda ta ishe shi rayuwa kamar yadda ya taso ya ga iyayensa maza da mata guda guda. Shiyasa zumunci da soyayyar gidansu ta sha banban da ta kowanne ahali. Amma matarsa bata gane hakan ba, kullum cikin tsanantawa kanta take, har fad'i take yi, jikinta na fad'a mata kamar watarana zai samo yarinya sa'ar Aysha d'iyarta ta farko ya aura. Da haka gara ya yi yanzu ba sai ta tsufa ya dauko mata yarinyar da zata zo ta rainata ta hanata sakat a gidanta, saboda tak'amar tana gamsar da miji da kuruciyarta ba. A duk sadda take irin wadannan kalaman dariya yake yi tare da ce wa "K'arin aure ai zuwa yake yi, idan an k'addara mini zan k'ara da kaina ne zan fad'a miki. Ki daina tayar da hankalinki akan abin da yake gaibu ne". Amma a k'asan ransa baya da ko sha'awar ya k'ara din, amma bai san me yasa tsayin Bilki ya yi masa ba, yadda take a tsaye cak, mai fadadden k'ugu zata dace da matar jarumin d'ansanda irinsa. Sai dai kuma yana ganin yarinyace k'ankanuwa da bai kamata ya bijiro da wannan maganar a tsakaninsu ba, mussaman da yake ganin Faruku yafi shi cancantar ya yi amarya da ita. Daidai lokacin ya isa cikin harabar babbar makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori. Ya tayamu sauke kayanmu, ya damkawa kowacce sabbin y'an d'ari biyu guda goma, dubu biyu d'aya ke nan, wanda a wanccan lokacin dubu biyu kudi ne mai auki. Ya mana nasihar mu kame daga k'awayen banza, mu kuma dage mu fito da result mai kyau ta yadda zamu samu gurbin shiga makarantar gaba. Muka yi masa godiya, ya ja motar ya tafi. Yana fita, motar gidansu Basma ta shigo. Muka rungume juna da ihun murna. Tare muka biya leburori suka kwashe mana kayanmu zuwa hostel. Daren ranar bana mantawa da shi domin da k'yar barci ya sure ni. Ba komai ya hana ni sukuni ba, illah yadda na ga mutanen gidanmu sun gasgata soyayya muke yi ta gaske da Yaya Faruku. A farkon kam lokacin da ba ni da wayo ina sonsa, da na shiga sakandire na gane soyayya tabbas ina jin sonsa har raina duk da shi zolayarsa ba zata bari a gane gaskiyar alqiblarsa ba. Haka dai muke tafiya a shine saurayina, domin duk sadda zan hakaito saurayina a duniya to Yaya Faruku ke zuwa mini, komai da komai nasa yana burge ni. Amma daga lokacin da ya yi aure na ji a duniya na tsani ko kallonsa na yi. A yanzu da nake yin hankali sai na fahimci ba sonsa nake yi da aure ba, kawai shakuwa ce, da kuma yadda yake girmama lamarina, shiyasa zuciyata ta bashi wani babban matsayi da ya zarce kowa a gidanmu har yan'uwana da muke ciki guda kuwa. Amma tsakanina da Allah an jarrabe ni da ƙin auren zumunci. Ba dan komai ba ni dai a tsarina ne bana so, ban ga kuma wadda zan iya aura ba cikin ƴaƴan Baba Babba. Ko Yaya Usman da na ga take taken cewa zai yi yana sona tunda Faruku ya yi aure, nan da nan na canja masa fuska ko gaishe shi na daina yi, dan kada ma ya samu fuskar tunkarata ko bayyana maganar. Da ya fahimci bana ra'ayinsa ko kadan sai ya haƙura cikin salin alin. Baki da baki Baba ƙarami ya nuna mini yana son ya bawa Yaya Usman aurena da zarar na kammala sakandire, bayan auren na cigaba da karatuna a dakina. Ban ji nauyi ko shakku ba na ce "Baba bana sonsa, na ro'ke ka kada ka furta wannan kudirin naka wani ya ji". A sanyaye ya ce "Ba zan miki auren dole ba, Allah ya had'aku da abokan arzikinku daga ke har shi. Na rufe magana tunda dama shi bai fad'a mini ba, amma nasan tabbas yana sonki, duk da yana iyakacin k'ok'arinsa wajen dannewa tunda bai ga fuska a wajen ki ba." Na bata rai na ce "Na rufe k'ofar da zai furta, Yaya Faruku kad'ai zan iya karba, shima kuwa tunda ya yi aure magana ta k'are da ikon Allah ba zan yi auren zumunci ba. Ina jin tsoron kada zumuntarku mai k'arfi ta shiga tasgado". Ya yi dariya sosai ya ce "Bilkisu babu yadda za'a yi akan d'ana na bata da d'an-uwana. Kin san kuwa yadda muke son juna da Baba babba? Mu kad'ai mahaifiyarmu ta haifa, kuma bamu tab'a rayuwa ba waje d'aya ba, ban da aikin da nake zuwa Katsina na yi kwanaki bamu tab'a rabuwa ba, domin ko makarantar kwana tare muka yi a Barewa duk da ya zarta ni aji sosai. Har yau ban haifi d'an da zai shiga tsakaninmu ba, tunda dai ba kya so, to na bar maganar domin Annabi ya ce "Kada mu aurar da ku sai kuna so, sannan yayunki da aka aurar babu wacce muka yiwa tilas, ke ma kuwa ba za'a yi miki ba. Na kama baki a zuciyata kuwa na ce me ma zaisa na yi tunanin zai iya ce wa yana sona don na fasa yi da Yaya Faruku? Me zan yi da mutumin da ya ba ni shekaru kusan sha shida. Da kaina na yiwa kaina dariyar hasashena. *Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.* *Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa* *08163761797* ✍️ [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://wa.me/c/2347020695644 07 *Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?* *Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa* *Malaysianfabricsng* 07020695644. Kwanaki k'alilan na manta komai na durfafi karatuna. Bana biye wa rashin karatun Abida domin na riga da na san ba kwanyarmu d'aya ba. Kwanci tashi muka dawo gida rubuta jamb. Kwanaki biyu muka yi, muka sake juyawa dan rubuta jarabawar karshe. Ranar 9 ga watan 9 muka kammala jarabawar karshe wanda ta zama ranar murna da doki hadi kuma da zullumin rabuwa da junanmu. Ni da Basma sai kuka muke yi, Abida kuwa sai hidimarta take yi wanda Babu alamun kuka ko wata damuwa mai yawa. Da ta gaji da ganin kukanmu sai kawai ta ce "To ku koma s.s.1 mana." Basma ta zabura ta ce "To mu koma tare y'ar sarkin BAK'AR TA'ADAR cabawa mutane magana." A banzance Abida ta ce "To na gaji da kukan munanfincinku. Haba da munsan junanmu? Allah ya had'amu, dukkanmu kuma munsan adadin zaman da zamu yi mu koma inda muka fito. Da lokacin ya yi muna da ranmu da lafiyarmu mai ya kamata mu yi?" Ba wacce ta tanka mata. Ta numfasa ta ce "Sai mu yi fatan duk inda rayuwa zata kaimu mu kasance cikin aminci, ya kuma bamu sa'ar samun sakamako mai kyau. Mu da muka yi sa'a ma daga jaha d'aya muke, duk runtsi zamu dinga haduwa." Jikinmu ya yi sanyi domin bamu yi zaton Abida zata sauko ta yi magana cikin kwanciyar hankali haka ba. Basma aka fara zuwa d'auka. Har jikin motar na bita tamkar ba zamu rabu ba. Da k'yar muka bari direban ya ja suka tafi. Abida tana daga kan akwatin kayanta ta ce "Ni fa Bilki na gaji da wannan kusancin naku da Basma. Ban son na ga mutane sun cika dagewa k'awance irin haka. Wallahi da bamu yi kandi ba sai na saka an bibiyeku haba wannan makalewar da kuke yiwa juna ta yi yawa " Duk yadda na ji haushin kalamanta haka na daure na guntse baki ban tanka mata ba. Domin na sani nice a ruwa, saboda ta fini harshen zaro magana. Ilai kuwa ta kaikace ta ce "Da ni ce ke, murna zan yi, zan bar wajen da ake ce mini sola. Ke gabad'aya wata iri ce Bilki, har rasa ajin da zan saki ki nake yi." Na sake matsewa ban ce komai ba. Ita kuma ta kasa hak'uri ta sake fad'in "Wannan shiru shirun naki da kuttu yake sola." Ko motsi mai k'arfi na ƙi yi, balle na biye ta. Kan dole itama ta kame bakinta domin tasan ba kulata zan yi ba. Tsawon lokaci muna zaune jugum jugum sai na ji ta ce "Wato Bilki kina da hak'uri, kina da gudun mu yi faɗa. Albarkacin baƙin cikin da nake ta nausa miki idan na haihu zan ba ki abin da na haifa dan ki ta tunawa da ƙuruciyarmu da yadda nake miki sababi amma ki jure, kina sona na shaida, nima kuma ina sonki fiye da Yaya Munira da Yaya Faruƙu ". Hawaye ya zubo mini na ce "Na gode sosai Abida, idan kuma Allah yasa kika ba ni ɗin wani a duniya ba zai ji ba ni na haifa a bakina ba, ba zan taɓa nuna banbanci da wadanda na haifa ba." Ta matso kusa da ni tana share mini hawayen da yaƙi tsayawa ba tare da na shirya faruwar hakan ba. Da ƙyar na yi jarumtar shanyen kukan na ƙaƙalo murmushi na ce "Amma so nake ki soni fiye da Yaya Asad". Ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Ban iya ƙarya ba, ban iya yaudara ba, ban so wani cikin yan'uwana sama da shi ba. Dan haka ki yi haƙuri kawai Bilki". Na dara kaɗan na ce "Na yi hak'uri Abidan Baba". Ba jimawa Yaya Faruku ya zo, shi ya zuba kayan a but bayan mun je ya karbo mana pass din tafiya. Na kasa sakewa na nuna masa farincikina na kammala sakandire, bare na bashi labarin abubuwan da suka faru. Gabaɗaya alhinin rabuwa da class mate ya taɓa ni. Sannan Abida ta yi matuƙar sanyaya mini zuciyata da gangar jikina gabadaya. Haka nan sai nake ganin tamkar akwai wata ƙaddara da take ɗamfare a tsakaninmu. Tunanina ya tsananta, da na ga lallai ba fahimtar komai zan yi ba,sai kawai na hau yin istigifari. Kan dole Yaya Faruku ya haƙura da rashin kuzarina, haka Abidan ma bata da karsashi kamar yadda ya santa da guntsi fesa. Da tuni ta ishe shi ya sayi jaridarta. Shi kuma da hanzari yake siya domin yasan mafi yawa labaran jaridarta nawa ne. Baba ƙarami muka tarar a harabar gidan yana dakon isowarmu a dalilin Baba babba ya je Lagos taron da gwamnatin tarayya ta shiryawa masu samar da Madara a ƙasa. Ya karbemu da murna. Muka tsugunna a gabansa muna gaishe shi domin shi din ba shi da haba haba irin baba Babba. Ya amsa cikin sakin fuska tare da yi mana fatan alheri a cikin kammala karatun da muka yi. Ya kuma ce "Yanzu ne zaku fara gwagwamarya da rayuwa, na roki kada ƙalubalen rashin samun abin da ake so ya sanya ku canja kyawawan ɗab'iunku, sannan duk inda rayuwa zata kai ku to ku zama wakilan addini musulunci da Hausa Fulani na gari abin koyi". Murya babu amo muka ce "In Sha Allah Baba! Kaitsaye sashenmu muka dosa domin kuwa mun riga mun san Baba babba baya tab'a yarda ya yi tafiyar da yasan zai wuce kwana biyu ba tare da rakiyar Momi ba. Gabadaya Baba babba bature ne. Ma'ana a bayyane yake nuna soyayya ga ahalinsa. Baya yarda da al'adun bahaushe akan sha'anin aurensa. Duk inda zashi momi na gefensa. Amma Baba k'arami kuwa shine asalin d'an gargajiya gabadaya irin wannan rayuwar bata dame shi ba. Ga shi har digirin digir gir ya yi. ** A wannan shekarar muka samu gurbin karatu. Dukkanmu a A.B.U Zaria. Abida ta samu nasarar samun MBBS din ma'ana burinta na zama likata zai tabbata. Yayin da ni na samu Nutrition and dietetics. A wanccan lokacin ban so kwas din ba, domin ba shine zabina ba, amma na hak'ura tare da fatan ya zame mini alheri, tunda ba zai yiwu na ce zan sake neman wani kwas ba. Basma ma ta samu nasarar shiga jami'ar sai dai ita jami'ar Bayero ta samu, inda zata karanci lab science. Baba k'arami tare da Baba Babba suka kaimu har cikin makaranta, bayan nasiha da jan kunne iri iri. Ba abin da ya tsaya mini irin yadda Baba k'arami ya fito da al'amarin da yake ciwa iyayen yau tuwo a kwarya. Da kakkauran murya ya ce "Tunda kuka iso duniya bamu huta da hidimarku ta kowanne bigire ba, har zuwa yau dinnan bamu huta da dawainiyarku ba, ba kuma mu tab'a gazawa ba. Bayan hidimar da muke yi muku da aljihunmu da k'arfinmu haka nan bamu tab'a gajiyawa wajen yi muku addu'ar shirya da samun nasarar rayuwa ba. A yau da zamu kai ku jami'a wajen ka zo na zo, wajen da babu kwaba. Abun da zamu fad'a muku d'aya ne tal. Ubangiji ne wakilinmu akan tarbiyar da muka wanzu muna yi muku, idan kun taimaki kanku kun k'are mana mutunci kun kare naku, to kun tsallake kalubalen rayuwa mai yawa, idan kuwa kun ha'incemu kun watsar da tarbiyar da muka d'oraku a kai, kun jefa rayuwarku cikin garari da tashin hankali hadi da bak'in ciki marar yankewa. Ubangiji kuma zai mana sakayya. Ku kiyaye, ku kiyaye, kada ku kusancin zina bare ta baku sha'awa ku afka mata, masifarta yawa ne da ita, naso take yi. Kun isa aure duk wacce ta had'u da namijin da ya yi mata, ya nuna zai aure ta ta turo mana shi, zamu aurar da ita babu jinkiri." Gabaɗaya mun yi laƙwas kunya ta dabaibaye mu domin Baba ƙarami cire kunya ya yi sosai ya ding faɗin "Mun san sha'awa halitta ce, kuma kun kai shekarun da zaku buƙaci namiji amma kuma bata gurbatacciyar hanya ba, kada ku yi sanadin da zamu kunyata mu mutu da baƙin ciki dan Allah." Nasihar ta yi matukar ratsamu, gabaɗaya kuka muke yi, har Abida da ta fini taurin zuciya. Sun jima tare da mu a makarantar tare da Yaya Munira da a lokacin ta shiga ajin ƙarshe inda take karantar (Law) shari'a kevnan. Haka suka barmu cikin jan kunne da nasiha iri iri. Ba bangarenmu ɗakunan kwananmu ɗaya da yaya Munira ba. Amma muna haduwa akai akai, yayin da muke ɗaki ɗaya da Abida haka abincinmu a haɗe tamkar muna F.G.C Bakori. Sannu a hankali muke karatun har muka cinye shekarar farko. Yaya Munira ta kammala cikin nasara. Mun yi kewar rashinta a kusa da mu, domin sosai take yi mana alheri da saka ido a kanmu. Cikin sa'a a wannan shekarar jamiar zata yi bikin yaye dubban ɗalibai(convacation). Sosai muke ɗoki da murnar yaya Munira na cikin waɗanɗa suka yi sa'a baza su yi dogon zama kafin a yi bikin ba. Kusan kowa ahalin gidanmu ya halarci bikin inka dauke Yaya Asad da bai samu sukunin zuwa ba. Domin bai ɗaɗe da komawa jihar Anambara ba, tare da ƙarin girma. Amma hatta dukkan yayunmu mata da suke da aure sun zo. Kwalliya muka yi ni da Abida sosai tamkar mune graduate ɗin. Hakanan mune mu ke kai komon hidima da ahalinmu a wajen. Su Baba sai farinciki suke yi, suna mana addu'a muma Allah yasa su ga namu bikin gamawar. Gabaɗaya aka amsa da "Ameen". Ɗiyar Yaya Zainab Anisa ta ce zata yi fitsari. Sanin da na yi Abida bata yarda ta yiwa yara tsarki ya sanya na ruƙo hannunta na yi can gefe inda babu jama'a da ita, bayan na dauki ledar pure watee guda ɗaya. Na ɗago daga sunkuyen mayar mata da pant idanuwana suka sarƙe a cikin na tsalelen saurayin da nake kwana nake tashi da tunaninsa. Sanye yake cikin graduation gown wanda hakan ya tabbatar mini shima ɗalibi ne a makarantar. Da murmushi ya ce "Duk yadda aka yi ke ce alherin da nake ta roƙa babu gajiyawa." Bugun zuciyata ya tsananta domin ban taɓa zaton zamu sake haɗuwa ba. Ya tausasa harshe ya ce "Fara faɗa mini sunanki dana garinki. Dan kada ki sake ɓace mini". Na yi ƙasa da kaina harshena ya yi mini nauyin da ban yi zaton zai yi a wannan saɗarar ba. Ya kalli Anisa ya ce "ya sunan antinki?" Ta ce "Anti Bilkisu." Ya murmusa ya kalle ni ya ce "sunan ya dace da zubin hallitar da ubangiji ya yi miki, tabbas ke ɗin sarauniyar mata ce, kuma sarauniyar zuciyar Sahal." Na kasa tanka masa, na kuma kasa tafiya na bar shi. Kamar jifa Abida ta iso, na zuba mata ido ina kallon yadda take masa wani iron kallo. Jikina ya hau ɓarin kada ta mini sanadin tsiya domin har zuciyarta na shaida bata ƙaunarsa tun hadɗuwarmu ta farko. A sanyaye ta nuna shi da yatsa ta ce "S.S.Mashi again? Da walwala ya ce "Tabbacin haɗuwarmu haɗin Allah ce. " Ta rausayar da kai ta ce "Ubangiji ya yi zaɓin alheri." Da karsashi ya ce "Ameen ƙanwar rijalu". Dukkanmu muka yi dariya domin mun gane tsokanarta ya yi da nufin raha. "Ya mayar da hankalinsa kanta ya ce baki tambayi naki masoyin ba?" Taɓe baki ya yi tare da faɗin "Na mance ma yadda yake, ban sake tuna shi ba sai yanzu daka yi maganarsa." Ya rausayar da kai ya ce "Da kin san yadda Musawa ya rikice a kanki da kin ji kunyar wai kin manta da shi". Kaitsaye ta ce "Ina abin jin kunya tunda ba dama zan ba shi ba! A sanyaye ya kalle ni ya ce "ina fatan dai Bilkisu zata ba ni dama." Ban amsa masa ba, ya juya ga ABIDA ya ce "ki taimake ni kada ki hana a ba ni dama". Ta maƙe kafada tare da ce wa "Matuƙar tana sonka ai fatan alheri ne nawa, abu da ba ni zan tayata ɗaukar jidalin ba" A matuƙar sanyaye ya ce "Wanne irin jidali kuma?" Ba fargabar komai ta ce "Tiritiri da matsalolin da ake shiga a dalilin auren namiji mai bayyananen kyau mai k'arancin shekaru. Mamaki ya sanya ya kasa magana. Da ƙyar ya ce "da alamu idanuwanki sun haska miki ni a baibai". Yana rufe baki ta ce "Ina da yaƙinin shekarar da shugaban ƙasa Wasola ya sauƙa daga mulki ka iso duniyar." Ya kaɗu da furucinta domin kuwa hasashenta gaskiya ne, tabbas a wannan shekarar aka haife shi a ƙarshen shekarar ma. Ganin ya yi turus ta ce "Ni nasan ba zaka wuce warin yaya Munira ba" Ya haɗiye bacin ransa ya ce "Amma ina ganin ke zan baki shekaru shida zuwa bakwai." Ta ƙyalkyale da dariya ta ce"Ka girme ni tabbas amma da shekaru uku da watanni, ita kuwa Bilki babu watanin ma". Daga haka kuma ta silale ta yi tafiyarta. Takaicinta ya shaƙe shi a dalilin ya gano bata maraba da soyayyarsa da ƴar'uwarta shiyasa ta shigo da wannan rainin hankalin. Ni kuwa gabaɗaya na kasa magana domin ina tsoron jidalin Abida idan mun koma hostel. Amma gabaɗaya na ji babu daɗi yadda take yi masa iyashege mai cin rai. Gefe guda ina cikin zullumin kada ta kore mini shi, ni kam ko na girme masa ina sonsa a haka bare sarkin kankanba ta ce ya ba ni shekaru uku. A matuƙar sanyaye ya ce "Dan Allah saka mini lambarki" Tare da miƙo mini wayar hannunsa. Na karba na sanya masa. Na fara tafiya ya biyo ni yana faɗin "Yayanki ne ya kammala ko Yayarki?" Cikin nutsuwa na ce Yayata ce" "Wanne course ta karanta?" Ya tambaya a gajarce. "Law". Da matuƙar mamaki ya ce "Ya sunanta?" "Munirah Musa Funtua". Na furta cike da alfahari, domin sunanta ya yi fice a department din art and social secience gabaɗaya. Da mamaki yake girgiza kansa yana faɗin "Munee sister ɗinki ce?" Na ɗaga masa kai tabbacin eh. Ya ce "Munee gifted ce ƙwarai da gaske." Kafin na amsa masa sai gata, sanye cikin irin rigarsa. Ta ce S. Mashi kai kaɗai a nan?" Tare nake da Bilkisu ƙanwarki, nifa na ga mata Munee". Ta yi dariya tare da ce wa "Idan tana sonka ai shike nan". "Idan bata sona ba zaki taya ni kamfen ba Munirah?" Kai tsaye ta ce "Ni da ba ni zan zauna mata ba, kaga bai kamata kuma na tirsasa mata ba". Ya ce "Hakane". Tare da sakin ajiyar zuciya. Tare da yaya Munira suka shige cikin taron da alamu wani abu zasu yi. Yayin da ni da Anisa muka koma cikin ahalinmu. Sai yamma lis suka ɗauki hanyar komawa gida Funtua. Yayin da Abida ta kaikaice take faɗin yau zuciyar sola sai Allah ta ga masoyinta. Ban yarda na buɗe baki na tanka mata ba. Amma matuƙar zamu zauna daga ni sai ita, zata kaikaice ta ce "Bilki yanzu sai ki amince da yaron nan? Na rantse miki fa da kad'an zai girmi yaya Munirah. Ya miki yaro da yawa, ga shi sololayi zubin makirai, kin ga Bilki ina raba ki da kisan mummuƙen namiji". Ranar da ta fara faɗa mini wannan maganar na yi dariya ƙwarai da aniya domin yadda ta yi maganar tamkar wacce tasan kuttun ya'ya maza. Shi yasa a kullum ina tuna Abida sama da sau goma a rana. Domin komai ta faɗa mini a hankali nake ganinsu a cikin rayuwata, suna tabbata. Na numfasa na fashe da kuka ainun, sosai na yi kuka. Kukan da na tabbatar ba zan daina yinsa ba ila yau mil ƙiyamati sannan na cigaba da hakaito rayuwarmu tamkar a majigi. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 08 *Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *07036662633* *Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253* Cikin sanɗa da hila S.Mashi ya shiga jikina. Domin wata irin kalar soyayya yake gwada mini mai tsayawa a rai yana kirana sama da sau biyar a , kullum kuma sai ya zo ya ganni, al'amarin da nake mamakinsa, ina yawan tambayar kaina shi bai tafi gida ba ne ko kuwa? Ashe a Zaria yake zaune gidan Baffansa wan mahaifinsa wanda prof ne a jami'ar. Haka nan a cikin quarter's din makarantar suke zaune. Sanadina ya sanya bai tattara ya tafi gida Katsina ba tunda ya kammala Asalin su Sahal ƴan asalin ƙaramar hukumar Mashi ne. Mafi yawa zuri'arsu ƴan boko ne wayayyu, sun kuma watsu a sassan arewacin ƙasar. Wasu na Kano, wasu na Kaduna, wasunsu na Katsina da Zaria, wasu kuwa na Abuja da cikin Mashi. Sannan mafi rinjaye su farare ne ƙal masu zubin sadaka yalla, domin duk fadin Mashi da kewaye idan ka ce gidan jajaye yaro da babba yasan gidan ake nufi.. An tabbatar asalin tushensu na Agadaz ta ƙasar Nijr. Kakannnsu daga can suka fito, kowa kuma yasan alaƙar mutanen jihar Katsina da Nijer. Mahaifinsa na cikin waɗanda suke zaune a Katsina. Tun Abida na kushe da nuna adawarta akan S.Mashi har ta haƙura ta zuba minu ido a dalilin watarana da ta ganmu tare a Libry muna hira. Ta kasa kawaicin ɗauke kai ta iso gabanmu ta ce "Wai ko yaushe kuna tare kenan? Ya zo da safe, ya zo da rana, ya zo da yamma, yanzunma da daddaren sai kun haɗu? Amma ai kinsan ba'a barinmu hirar dare a gida ko?" Na kasa ce mata komai domin gaskiyar magana ta faɗa mini. Ta numfsa ta ce "Sahalu ta kasa faɗa maka dokokin da aka sanya mana kafin a barmu mu zo makarantar nan. Dan haka zan faɗa maka domin ni ɗin jakadiyar iyayenmu ce. Tsakanina da Allah kana ɗagawa Bilki hankali. A yanzu ne ta shiga aji biyu. Tunda ka shigo rayuwarmu gabaɗaya ka ɗauke mata hankali daga karatun da ta baro gida dominsa, alhalin kai ka kammala naka tare da Yayarmu da muke makwabtaka da ita wajen haihuwa. Kada ka kuma zuwa wajenta a ranakun litinin zuwa juma'a, sannan haramun ne zuwanka a irin wannan lokacin. Bayan haka mu dokace ta dole sai mutum ya bayyana gaban dattijaanmu ya gabatar da kansa tare da neman izinin magana da ƴarsu". Cikin takaicin yadda take nacin jingina masa fikon da ya yi mana bai kai ya kawo ba, ya ce "Na ji Abida a kuma cikin satin nan zan je Funtua na nemo iznin, na gode da tunatarwa". Daga haka ya miƙe ya tafi babu sallama. Ta zauna kusa da ni bayan ta ja ƙaramin tsaki. Tunda ta zauna ba abin da take yi sai yaɓa mini baƙaƙen kalmomi. A matuƙar tunzure take faɗin kin faɗo da yawa. "Ina rantse miki Bilki da wannan sololayin gara miki auren Yaya Faruku mai mata da yara, gara miki yaya Asad duk da yadda ya baki tazarar shekaru masu nauyi. Yaya Usman ya yi ta nuna miki soyayyar da babu algus kina tankwabewa sai kuma ki buge a auren wannan abin? Wai ko dai kina da raunin fahimtar abu mafi kwanciyar hankali da dacewa ne? Ki ture waɗannan da suke cikinmu guda ni da su, wataƙila zuciyarki ta kisima miki ina da son kai, me yasa kika ƙi bawa tarin masoyanki dama sai Sahalu da idan ya kai shekarun ganiyarsa zai ga tsufanki?" Daidai wannan gabar ma sai da na kasa riƙe hawayena. Hakikanin gaskiya Abida ta soni ta yi dukkan iyawarta ta yakice mini shi a rayuwata amma ina? Domin ya iya shirya zakakkun kalmomi, ya iya ririta zuciyar mace, bugu da ƙari kyakkyawan ne na gaske, irin wanda nake so. Jin na yi shiru ta tunzura ainun ta ce "kyawunsa ne yake rudarki, amma da ace kin kula da kyau da kin gane ba shi da kyau, domin dukkan kyawunsa irin wanda yafi zama abun burgewa ne idan mace ke da shi. Fari dogo, mai kyawun fuska. Sai dai a lankwashe yake tunda bashi da siffofin karfafan maza, na rantse miki ba zai iya yin gwagwarmayar rayuwa ba, ina jiye miki gararin rayuwa! Ni fa ko ina da rai ba zan baki kafada ki yi kukan kuttun Sahalu ba. Domin na faɗa miki tun tafiya bata yi nisa ba, amma dan jaraba kin kasa fahimtar manufata. Haka kawai na fara mata kuka ina faɗin "Ki yiwa Allah ba dan ni ba ki daina jingina masa yarinta akan idonsa, baya so, baya jin daɗin al'amarin. Dan Allah Abida kada ki sake kore mini shi ". Na ƙarasa cikin kuka na sosai. Tsawon lokaci ina mata kuka yayin da ita kuma ta kasa ko da kwakkaran motsi. Can ta numfasa ta ce "Wato duk abubuwan da na faɗa ke ko saurarensu baki yi ba, balle na saka ran zaki fahimce ni?" Ta fesar da iskar baki tare da ce wa "Well! Idan Allah ya ya yarda ba zan kuma jingina masa ƙuryciya akan idonsa ba, amma ki sani har duniya ta naɗe a idona yaro ne ƙanƙani da bai fi ki aike shi a matsayin ƙanin mijinki ba. Amma tunda bansan gaibu ba, bansan dalilin da yasa aka jefa miki sonsa ko na ce kika jefawa zuciyar ki ba, na ajiye makamaina, amma ki sani babu ke babu kawo mini matsalolinsa, ke bama za ki ga fuskar tunkarata da kalubalen Sahalu ba. Domin Allah ne shaidar yadda nake jinki a zuciyata da kuma yadda nake guje miki artabu anan gaba. Babu damuwa na daina adawa da soyayyarki da shi tunda kina cikin jerin mutane masu son mutum a kallon farko ba tare da nazari ko tsinkayen halayyarsu ba. Fatan alheri amma ki sani matuƙar kuka cigaba da hirar dare zan bugawa Baba babba waya na faɗa masa kin yi bara'a da kyawawan turbobin da suka ɗora ahalinsu a kai. Sannan tabbas idan mun koma zan siyar musu jarida mafi tsada domin kuwa zan fayyace musu gaskiya da gaskiya cewar aure kike so dan haka su aurar da ke, sai ki kammala karatun a dakinki domin ni ba zaki dinga sanya ni cikin zullumi da fargaba ba, alhalin karatuna na matuƙar buƙatar nutsuwa." Na yi shiru tare da goge hawayena domin na yi matuƙar samun nutsuwar zata daina gwanya masa, sannan ban ji damuwa ba dan ta ce zata faɗa a mini aure. Ta yi ƙwafa tare da ce wa "Kina da kayan kuttu sola! Daga haka ta buɗe tafkeken littafin gabanta wanda modern Biology ne ta hau bita cikin nutsuwa. Yayin da ni kuma na bude littafin()sai dai bana fahimtar komai. Gabaɗaya nutsuwa ta yi mini tutsu, ba dan komai ba sai dan Ubangiji ya sanya albarka a harshe Abida a gaban iyayenmu, idan ta yi shaidar abu gabaɗaya suna raja'a domin ita ɗin bata iya ƙarya ba, a tsaye take tamkar nonon maza akan komai, idan ta ce zata yi abu ko zata faɗa to tana nufin har zuciyarta hakane. Bayan haka na hango da gaske take da ta ce tana cikin zullumi akan yadda na daukaki Sahal. Gabaɗaya rauni ya kamata a dalilin kukan da na yi mata. Tunda ga wannan rana Abida bata sake tisa ni gaba tana kushe Sahal ba, sai dai kuma bata ba ni ƙofar da zamu dinga maganarsa ba, nima kuma ganin yadda ta kame daga yawan takura ni, sai na warware na daina takura kaina na rungumi karatu domin dama faragabar kada ta kore mini shi ta hanyar yi masa isgili ne yake kiɗima ni. Amma a yanzu na wartsake tunda na sani ita ɗin bata faɗar magana da zummar waƙe. Nutsuwar da na shiga da kuma takaita zuwan Sahal sai ya samar mana da daidaito a tsakaninmu. Ta daina musguna mini, ni kuma na mayar da hankali wajen karatuna. A haka muka zana jarabawar zangon ƙarshe. Muka tafi hutu gida, wanda dogon hutu ne na watanni kusan uku. A ranar da muka isa gida Abida bata bari mun kwana ba ta zayyanewa Baba babba halin da nake ciki, a kuma gabana da muka je gaishe shi. Ya nunfasa ya ce "Alamun al'amarin daga Allah ne tunda wanccan karon kin toshe hanyar da zasu haɗu amma cikin ikon Allah sai ya sake haɗasu. Dan haka ki taya ƴar-uwarki da addu'a kawai, sau tari muna ƙin abu sai abu ya zamo alheri, abinda muka raja'a akansa kuma sai ya shayar da mu mamaki." Wata irin salama ta shige ni, domin na yi zaton Baba zai ce sai mun kammala karatu ko kuma na zaba aure ko karatu. Cikin taushi ya cigaba da ce wa "Ai ya turo ƙanin mahaifinsa ya nema masa iznin magana da ita, mun kuma amince. Tare muka yi Barewa College da iyayensa. Ni ajinmu ɗaya da wan baban nasa, mahaifinsa kuwa ajinsu ɗaya da Baba ƙarami. Mutanen kirki ne zuri'arsu basu da aibun da za'a guji haɗa iri dasu. Namiji ai baya kaɗan Abidan Baba. Ta ya Bilkisu son abin da take so." Kunya ta kama ni, na yi ƙasa da kaina ina jin farin ciki na ratsa ni. A sanyaye Abida ta ce "Shike nan Allah ya tabbatar da alheri." "Ameen ameen Abida! Ke ma Allah ya fito miki da naki mijin duk sai na haɗa na aurar da ku rana ɗaya". Da azama ta ce "Na roke ka Baba ka bar maganar nan haka. Bilki ta samu miji, ta kuma amince a yi mata aure. Ni kuma ban samu ba, ko na samu ma sai na kammala karatuna, dan Allah kada maganar nan ta yi tasiri a zuciyarka, ita dai da ta ga zata iya to a yi mata auren ta, Allah ya bata sa'a". A sanyaye ya ce "Ameen". Daga haka ya sallame mu. Duk wanda ya zo gidan sai ta bashi labarin halin da ake ciki. Yaya Faruku kuwa da ta bashi labarin ya zuba mini ido ya ce "Da gaske dai kin fasa yi da ni ko Bilki? Anya alkawari ya ce haka?" Na yi murmushi tare da sunkuyar da kaina ƙasa. Yaya Munirah kuwa addu'ar fatan alheri ta yi ta kame bakinta daga tofa komai. Amma kuma bata armasa al'amarin duk da ta san Sahal sosai tunda shima law din ya karanta. Satinmu biyu da yin hutu yaya Asad ya turo da direba ya kwashemu zuwa Anambara dukkanmu uku. A wannan lokacin matarsa na da tsohon ciki. Mace mai kirki da haba haba da mutane. A wannan lokacin haihuwarta hudu duk mata zata yi ta biyar sai ta daya ta raayi bara. *Na ce Duk masu son oriflame products kowanne iri ku tuntubi Aisha Lame zaku samuna sassuakan Farashin da ya Dara na saura rahusa*. *07036662633* Yaransu kyawawa kana ganinsu ka ga jinin gidanmu. Ni da yaya Munirah muke yin komai na hidimar gidan domin mun lura sassafe yake tashi ya hau hidimar shirya yaran nasu tare da rage mata ayyukan gidan, domin iyayen ƴar aikinsu basu yarda ta biyosu kudu ba. Shiyasa yake taya ta aiyukkan da cikinta ya yi nauyi. Ganin haka ya sanya muka daina komawa barcin safe muna gama azkar zamu fice mu hau hidimar gyaran gidan da abun da zai ci tare da yara. Sai sun tafi sai ku koma mu kwanta idan mun tashi sai muyi abin da zamu ci. Ba ƙaramin daɗin zuwanmu suka yi ba. Duk da yadda Abida bata sanya kanta a hidimar da muke yi ba, daga matar gidan har maigidan tattalinta suke yi tamkar ƙanwar momi ce. Na riga da na gane yadda Baba babba ke son Abida haka yaya Asad ma aka jarrabe shi da sonta. Shiyasa idan tana gabansa take baje dukkan wants ɗinta shi kuma yana yi mata yadda take so. Bansan me yasa har muka yi kwanaki bata fesa musu na sake haɗuwa da Sahalu ba ta bakin nata. A wannan zaman na ɗan fara sakewa da yaya Asad har ina iya zama tare da shi mu yi hira gabaɗayanmu. Wani dare muna zaune a falo ni da Abida muna kallon wani Nigerian fim (The wold apart). Jaruma Ini Edo ta yi matuƙar ba ni tausayin yadda ta faɗa tarkon son ɗan sarki. Domin nasan zafin soyayya. Tausayin da na shiga na yadda iyayen yaro suke ƙyamar haɗa iri da talakawa makaskanta. Tuni barci Mai nauyi ya yi awon gaba da Abida, yayin da yaya Munirah da matar gidan sun jima da shigewa dakunan barci tare da yara. Ni kaɗaice idona biyu. Daidai lokacin kuma na ji alamun dawowar maigidan. Ya shigo sanye da kakinsa da suke matukar yi masa kyau. Yana nan cak a tsaye tamkar saurayi. Ga shi sun fara tara yara. Duk da dai babu tazara a tsakanin yaran nasu. A zamana na fahimci shi ɗin mai son ƴaƴane bai ɗauki ɗabiar yin tazara ba, har ita matar ko dan lokacin duniyar bata waye irin yanzu ba ne, ko dan rayuwar cike take da aminci da sauƙin rayuwa? A kasalance ya shigo jikinsa babu kuzari ya zube a kan kujerar da take maƙwabtaka da wacce Abida take kai. A hankali na ce "Sannu da dawowa yaya". Ya amsa da faɗin "sannu Sarauniyar shaibah. Kallo kuke yi ne har barci ya sure wannan?" Kaina na ƙasa na ce "eh. Ya taya ni mayar da hankali kan allon talabijin din. Murya babu amo na ce "Na yi maka abinci?" Da mamaki ya ce "A wannan daren zaki iya yin girki?" A sanyaye na ce "Ai akwai komai da za'a buƙata indai zaka ci, sai na dafa maka". Ya ce "idan baki takura ba, dafa yunwa nake ji sosai". Na miƙe da hanzari, na nufi kicin ina tunanin mai kuma zan dafa ne? Wanne iyayyin ne ya jani yi masa tayin girki? Ina ma na bar shi ya ɗauko cake ɗin da ya saba ci da shayi ya ci abinsa. Na fi mintina goma ina tsaye a jikin freezer ina nazarin me zan yi masa mai sauƙin sarrafuwa kuma wanda ba zai dame shi ba tunda kwanciya zai yi. Take na yanke shawarar na yi masa jollof din patateo. Sai da na kammala yanka albasa na yi jajjaga tattasai da attaruhu sannan na ɗora na tsayar da ruwan sanwa ƙadan tunda dankalin turawa baya karban ruwa da yawa sannan na fara feraye dankalin. Na buɗe firij na ga ragowar papper fish ɗin da muka ci da rana. Na fito da wanda nasan zai cinye na zuba a girkin. Na rufe, na koma gefe, gabaɗaya ƙamshi ya cika kicin ɗin na tabbatar har gidan gabaɗaya ya karaɗe. Rabon da na ga sinadaran girki masu ƙamshi irin wadanccan sai a shekarun nan bayan ma haihuwar Farha. Spice ɗin Amreesh spice's Kano duniya ne, domin suna saka armashin girki, suna mayar da ƙamshin gida ya zama na alfarma, haka nan ko baka jin yunwa ƙamshin zaɓaɓɓun spices na sanya ka ci abinci ba tare da ka farga ba. Tabbas spices ɗin Amreesh ba shi da na biyu a wajena da wajen duk wanda ya taɓa tu'amalli da su. Ku nemi naku kai tsaye ta wannan lambar..09093510131 Tana aika ko ina a ƙasar nan. Ga mutanen jiharmu ta Kano da Katsina kuwa kakarku ta yanke sa'a domin takuce, ku hanzarta tuntubarta. Dinner bowls ɗin da na san ana zuba masa abinci na dauko na zuba a ciki. Na shirya komai hatta coffee ɗin da yake sha duk dare sai da na shirya, hakan kuma bai hana na saka masa ruwa da lemo masu sanyi ba. Na kinkima na nufi falon. yana hango ni ya zabura ya miƙe tare da faɗin "standstill! Ta ya ya zaki kinkimo wannan tray haka ba ki san illar da daukar abu mai nauyi yake yi muku ba?". Ya ƙaraso ya karɓe. Maimakon ya dire a dainin tunda shine kusa da kicin sai kawai ya wuce cikin falon da alamu so yake yana ci muna hira, domin ni dai ban taɓa ganin ya ci abinci ba akan dainin ba, tunda muka zo. Hakan kuma bai mini daɗi ba domin takura zan yi, so nake kuma na dawo da kallon baya domin an wuce ni da yawa, tunda CD plate ne a lokacin. Muka zauna ya fara cin abincin cikin nutsuwa. Ya kalli yadda na mayar da hankalina kan kallon. Ya ce "To zo mu ci mana yayar Abida". Na yi murmushi tare da ce wa "Alhamdulillah tuni muka ci abinci bana tare da yunwa". Ya ce "Jiya Abida ta siyar mini da jaridarta da maƙudan kudaɗe. Zuciyata ta harba, na tabbatar labarin jaridar ya shafe ni ko da kuwa ba gabaɗaya ba. *A lame skin & Beauty Zaki samu dukkan nau'in kayan oriflame da dukkan mayukan da suke gyara fata **07036662633* Ya cigaba da cin abincin ba tare da ya fasa labarin ba. Ni kuma na cigaba da kallon da ba fahimtar komai nake yi ba, tunda ya zauna. Jira nake ya kammala na kwashe kwanukan na tashi Abida mu yi ɗaki na kalla gobe idan Allah ya kai mu. Sai da ya kammala ya yi gyatsa tare da hamdala. Ya ce "Sarauniyar shaibah ashe kin iya girki mai ɗanɗano na musamman?" Bansan ya aka yi ba dariya ta ƙwace mini na ce "Kasan me yasa ka ji daɗinsa?" Ya girgiza kai da azama ya ce "Faɗa mini sirrin, nasan dai Madam ma ba baya ba wajen shirya girki, amma dai ke da nasan ba shiga kicin kuke yi ba, na yi mamakin yadda kika yi shirya shi cikin nutsuwa, kuma cikin ƙanƙanin lokaci." Da dariya sosai na ce "Sai dai ka yi hakuri domin ka ci majina haɗi da tasonon Bilki. Hakan ne ya sanya ya maka daɗi da yawa. Ya maƙe kafada tare da miƙo mini tafin hannunsa na dama ya ce "Fato mini, ki ga idan ban lashe ba, bare wanda ya ɓace a cikin abinci wuta kuma ta ƙone dukkan bacteriya ɗin da zai yi illa." Na yi ƙasa da kaina domin wani irin kallo yake yi mini da na kasa gasgatawa. Zuciyata ta harba da tsananin gaske domin gaskiyar magana Sahal kawai ke mini irin wannan kallon, domin ko yaya Faruku ban taɓa ganin ya yi hakan ba, duk da na tabbatar yana sona bilhakki, kawai bansan me ya hana shi zama serious ba. Hakan da ya yi kuma shine yafi domin ba zan taɓa yarda na auri mai mata ba, bare matarsa azababbiya ta ɗauki karan tsana ta ɗora mini haka siddan matsalakan Kunya ta rufar mini, jikina ya yi sanyi sosai domin har cikin zuciyata kallon ya taɓa ni ƙwarai da gaske. Ya haifar mini da wasiwasi da sanyin jiki. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA*. *9* *Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633* *Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253* Ya numfasa bayan ya janye hannunsa. Ya ce "Ashe kun sake hadewa da yaron da autar momi ta ce ƙiris ya rage ya shiga sahun zabiya". Na kasa amsawa domin nasan babu labarin da yafi wannan tashe a cikin jaridar Abida. Murya babu amo ya ce "Wai har iyayensu sun zo wajen baba babba?". Na ɗaga masa kai dan ya gane tabbas zancen da ya ji a wajenta gaskiyar lamari ne. Murya babu amo ya ce "Anya baki yi rushing ba kuwa Maigado? Kina kallon kan ki a madubi kuwa? Ke fa gaba ɗaya ba'a miki zubin da ƙananun maza zasu same ki ba. Kin fi dacewa da zaratan maza musamman na jami'an tsaro". Na kiɗeme ainun domin na kasa gane shima son nawa yake yi ne ko kuwa? Ni kuwa me zan yi da shi? Ban so yaya Usman ba a matsayin saurayi, sai shi? A ture ma yaya Faruku bai zama serious da maganarmu ba, amma kaf ya'yan baba babba shi kaɗai zan iya yin haƙuri na karbe shi a matsayin mijin aure ba dan komai ba sai dan tarin alherinsa da sadaukarwarsa, sannan ina jin zuciyata tana bugawa akansa. Ban da shi kuwa ban ga wanda zan iya yiwa alkunya ba a cikinsu, domin na tsani auren zumunci har zuciyata. Bare yaya Asad kwata kwata bai mini a matsayin mijin aure ba. Ya mini baƙi da yawa, ba shi da kyawu irin wanda nake so, sannan ƙarfinsa ya yi mini yawa, a lokacin sai nake ganin kuskure kaɗan zan yi masa ya targaɗa ni. Bare kuma ga matarsa da ta fini ilimi da gogewar rayuwa dan kuwa da kaɗan ya girme mata shekarar da suka yi aure ta kammala digirinta na farko a jami'ar Maiduguri. Yayin da shi kuma a lokacin shekararsa ɗaya da kammalawa. *Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.* *Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa* *08163761797* Da suka yi aure ta yi digirinta na biyu a Ɗanfodiyo University Sokoto a lokacin yana aiki a Kebbi. Dan haka ya ajiyeta a Sokoto yake jele tsakanin Kebbi da Sokoto. Yanzu kuma ƴaƴansu uku tana shirin dire masa na hudu. Waya kai ni cusa kaina a tsakaninsu ta riga da ta fini wayewa da dabara, shi ɗin ma kamar a hannunta yake. Ganin na kiɗima ainun da furucinsa, watakila kuma ya hango ban taɓa tunanin zai iya ƙulla wata alaƙa ta daban da ni ba, sai ya yi maza ya ce "Wani abokinane matarsa ta rasu watanni uku shine ya ganki ya ce yana son ki, mutumin kirki ne yaransu huɗu suma". Yana rufe baki na ce "Abokinka fa! Tabdi gaskiya he is too big for me. Ka bashi haƙuri kawai! Na faɗa bayan na tsuke fuskata ainun . A tausashe ya ce "Ai na bashi haƙuri tunda na samu labarin kin bada damar da aka je gaisuwa wajen baba babba ai magana ta ƙare". Jin haka na ɗan saki fuska kaɗan. Sai kuma ya ce "Amma shi kuma ya ce "Tunda ba ƙudin aure aka kai ba, ba kuma auren aka ɗaura miki ba, zai jarraba sa'arsa domin kin shiga zuciyarsa kin yi kane kane". Yana rufe baki na ce "Wallahi ka ba shi haƙuri dan kuwa ba zan yarda na saurarere shi ba, tsoho da shi zai ce yana sona?" Jikinsa ya yi sanyi ya ce "Shi ke nan zan ba shi haƙuri tunda na gane da gaske ba zai ci albarkacina ba. Dama gani na yi mutumin kirki ne, kuma zai yi miki adalci. Wasa ma nake yi miki matarsa da ranta kawai tana Kano tana karatu ne, shi kuma so yake ya samu wacce zata zauna da shi a Kaduna." Na ce "Ya bincika a wani wajen ka ga nima ai karatu nake yi a Zaria. Ko kuma ga Abida nan ko zasu shirya". Da sauri ya ce "Ya ga Abidan amma bai nuna ita ba, dama kuma mai irin yanayinki yake so marar hatsaniya, wacce zata ɗauke kai game da sha'anin yara da matarsa." Na yi kamar na ce "To ba zai samu ba indai sai ni, amma kwarjininsa ya sanya na kame bakina. Amma raina ya ɓaci akan me ba zai ba shi Abida ba sai ni zai liƙawa sa'ansa mai ya'ya da kuma matar da bata iya sarrafuwa. Domin da ya isa da ita ai da ta bar karatun ta zauna da shi, ko ta yi karatun a Kad poly. Ya miƙe tare da sakin ajiyar zuciya ya ce "Na gode Maigado, na gode da girki, yanzu me kike so na baki dan ki san na yaba da karamcinki?" Na yi murmushi na ce "I need nothing, amma na roƙeka?" Da sauri ya ce"Ina jin ki?" "Ka daina ce mini Maigado. Su Baba kaɗai ke faɗa mini, yanzu tunda ka fara faɗa mini Abida da sauran jama'a sun ɗauka". Ya murmusa ya ce "Ina takaicin sanar miki kin roƙi abun da bazan iya yi miki ba. Domin ina matuƙa jin dad'i idan na ce miki sarauniyar shaibah ko Maigado. Kinsan kuwa duk Bilki ai mai gadon zinari ce." Na tsuke fuskata na ce "Ni kam bana so, yanzun nan mutanen gidanmu zasu riƙe su bar Bilkin". "To ki dinga rubuta sunan duk wanda ya ƙira ki da Maigado idan na zo ki faɗa mini, zan yi miki maganinsa ko waye." Na ce "Ba zaka daina ba ke nan yaya Asad?" Kai tsaye ya ce "Ina jin daɗin sunan ne, sannan kuma ban iya yaudara ba, tunda bazan iya dainawa ba". Ya fita waje ya dauko bandir ɗin 500 a motarsa ya ajiye mini akan cinyata, ya ce ki ajiye idan kin koma gida ki siyi abin da kike so, na gode sosai sarauniyar shaibah" Ya wuce wajensa ba tare da ya sake ce wa uffan ba. Na kashe kayan kallon na hau tashin Abida. Abin mamaki ban wani sha wahalar tashinta ba. Mamakin da na yi ita ɗin mai nauyin barci ce, hakanan mai wahalar tashi ce a barci. Kwanaki biyu Anty Maryam ta haihu still dai mace. Hidima sosai maigidan ya yi, cikin farin ciki. Gaba-daya Aysha babbar ɗiyarsu shekarunta takwas, amma an mata ƙanne hudu, shiyasa a jere suke fikon ƙadan kaɗan ne a tsakaninsu. Khadija a ce ta biyu, sai Saudat ta rasu bayan an haifi Hafsat, sai kuma Hafsat da ita aka yaye akan dole. Duk inda na yi Hafcy nan take yi, hatta da mamanta ta tafi asibiti haihuwa a wajena ta kwana. Ba kuma ta yi mini rikici ba duk kuwa da yadda take da maƙon uwa. Kwana da yini kawai ta yi, aka sallamosu bayan an tantance lafiyarta da ta jinjira. Kusan ni ke hidimar gidan, yaya Munirah tana taya ni da shara ne da moping, amma girki da kula da yaran duk ni nake yi, wani zubin ta kan yi wanke wanke. Abida kuwa kullum a naɗe take wai bata da lafiya, sai dai kuma jinyar bata hanata cin abinci da wanka da kuma nazari a mujalloli da littafai daban daban. Ganin hakan da masu gidan suka yi ya sanya suka raɗawa ɗiyarsu Bilkisu. Ranar da ya faɗa mana sunan diyar kenan Abida wiwi ta rushe masa da kuka hannuwa a ka, tana ce wa "Yaya Asad haka zaka yi mini, lillahi wa Rusulihi ai kowa yasan ba shiri kake yi da ita ba. Ni ce taka ita kuma ta yaya Faruku sai kuma ka tashi kasa sunanta alhalin ni yafi cancanta ka saka. Wanne iri kunyata ni ka yi haka?" Da rarrashi ya ce "Kwantar da hankalinki autar momi! Ba matar Usman an ce ta kusa haihuwa ba, to ki ji a ranki matuƙar mace ta haifa to sunanta Maryam-Abida." Ta sassauta kukan ta ce "Ni dai na fi so kai ka yi mini". Ya ce "zan yi miki matukar ina raye. Sannan zan saka miki ma a gidan Usman a kusa, sai dai idan ba mace aka haifa ba. Ta sassauta kukan, duk da so ta yi a canjawa yariyar ta amsa Abida. Yayin da Yaya Munirah ta saki gauron numfashi ta ce "Allah ya bani haƙuri! Ya yi gajeriyar dariya tare da faɗin "Ke ai yayarsu ce Munee". A kuɗin da ya bani na ƙirgi dubu ashirin na bashi na ce ya siyo ragon suna, sauran ya yi hidimar sunan Bilkisu. A lokacin ragon dubu goma na bada labari ne. Ya karba da murmushi ya ce "Lallai kin iya karrama takwara sarauniyar shaibah! Na sake ɗaukan dubu biyar na kaiwa Anti Maryam na ce idan ta fita ta siyowa little Bily ɗankunnen gold. Murna da godiyar da ta yi ya sanya na gane ta iya mu'amala da mutane. Na sani tafi ƙarfin abin, sannan na tabbatar ɗan kunnen gold za'a siyo a sanya mata, tunda dukkan ya'yan uku ko wacce zagayayyen ɗan kunnen gold ne a kunneta. Da matuƙar murna ta ce"Ai kuwa gobe zan fita da kudin nan zan siyo mata Bilki". Tana mini godiya, nima, ina yi mata godiyar, domin na tabbatar da bata yarda ba, ba zai soma saka ma sunan nawa ba. Cikin dare Abida ta tashe ni. Ta zuba mini ido ta ce "Bilkisu a ina kika samu kudaden da kike ta wadaƙa da su haka ne? Nima na zuba mata nawa idanuwan na ce "satowa na yi Abida" Na bata amsa a kufule domin na gaji da abubuwan da take yi mini, tunda aka ce sunana aka sawa jinjira. Bayan haka kuma, na fara ƙosawa da yadda take yawan haiƙe mini tamkar dai itace gaba da ni. Ta jijjga kai ta ce "Na rantse zaki san kin mini gatse. Ai na riga na gane shima sonki yake yi, duk hirar da kuka yi rannan da daddare idona biyu bakam na yi, duk ɓare ɓaren da kika yi na girki, da yadda ya kaikaice yake faɗin abokinsa na sonki duk na ji, kin sani, nima na sani ba wanda ya aiko shi, kansa yake ƙwanƙwasawa ƙofa. Na rantse gari na wayewa zaku ga tsiya sai na tsarawa matarsa komai na ga yadda za'a yi ta cigaba da yarda da ke, shima kuma na ga ƙarshen juya mini baya. Muna komawa gida kuwa zan siyarwa Baba ƙarami da yaya Faruku wannan labarin domin shine shafin farko kuma mafi tsada a jaridata." Jikina ya yi sanyi sosai. A raunane na ce "Kada ki yi mini haka Abida! Kin ga haka matar yaya Faruku ta tsane ni, ki taimake ni, mu bar garin nan lafiya, ina kuma roƙon ki kada ki saka baba ƙarami a maganar nan kinsan dai yarda zai yi, alhalin kuma na turawa baba babba wanda nake so." Ta ja tsaki mai tsananin gaske ta yi kwanciyarta bayan ta juya mini baya. Hakan da ta yi mini tabbacin ne na ba zata sake yin magana ba, domin haka ka'idarta take matuƙar ta kwanta ta juya baya to ta gama. Kan dole na kwanta nima. Amma na shafe awanni barci bai sure ni ba. Washegari na dinga yi mata shisshigi da azarbabin ta kula ni, ita kuma tana yauki gami da cin magani tare da muzuran yau ƙwai zai fashe. Idan ta ce zata fasa ƙwai din nan sai na ji cikina ya yamutse. Kai Abida ta mini iyashege iyaka. Ban da rashin wayona ai da na barta ta fasa ƙwan tunda dai da ɗan uwanta zai tashi, kuma ma ai bata da garantin son nawa yake yi. Amma gabaɗaya ta kiɗima ni. Ta firgita ni, ganin na matsu ta huce ya sanya ta ce sai dai na sayi gatsen da na yi mata. Jiki na rawa na zaro dubu biyu na ajiye a gabanta. Ta dauka tana juya su. Tsawon lokaci ina dakon mai zata ce, sai da gama ja mini rai sannan ta ce "saura wata dubun dan ba zai yiwu na sarayar da wannan labarin cin amanar a dubu biyu ba. Ki dinga soyayya da mijinta a cikin gidanta ita kuma ta dauki dukkan yarda ta zuba miki. Komai Bilki, Bilki dai, gara na taimake ta na faɗa mata yadda kuke son nukurkusa ta da baƙin ciki." Ban ce komai ba, na sake zaro dari biyar biyu na ajiye mata. Ta haɗesu waje guda ta buɗe tsakiyar Mujallarta ta zubasu. A tsume ta ce "Shike nan ba zan faɗa mata ba. Amma ki tabbatar idan kika janye biyayyar da kike yi mini zan faɗa ne kawai, ki cigaba da kawo mini abincina d'aki." Dad'i ya ratsa ni na ce "To Abida ƙanwar Bilki na gode! Daidai lokacin yaya Munirah ta fito daga banɗaki da yake cikin ɗakin. Ta ja tsaki ta ce "Bilki ki rabu ita da mana sai wahalar da ke take ta yi, komai zata yi, ki barta ta yi ɗin ai dai ba za'a kashe ki ba, sai gana miki azaba take yi ke kuma kina ta bin kanta." Da azama na ce "a a yaya Munirah ai mun ma saito ta." Yayin da Abida ta ja tsaki ta ce "To ta zuga ki kwabarki ta yi ruwa.". Bojuwa herbs* *Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?* *Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?* *Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?* *Muna dafa ciccibin da yake ciki da mace, yake kyautata matuncin mace komin tsufanta* *Kazalika muna sayar da saiwowin dahuwar idan ke kike so ki dafa da kanki* *Muna dafa kazar sababi gangariya,mai saukar da niima da kuma hade mace* *Akwia kuma saiwowin dahuwar idan zaki dafa da kanki*. *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida maijego* *Bazawara package* *Man ayun Chad da Marwa Wanda Babu algus, zumar silki kola* *Hakkkn daka emergency na mussaman* *Tightening set* *Kudai ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin aminci da rahusa, bana siyar da abin da bashi da inganci* *A Dade ana yi sai gaskiya* *08032773332 what'sapp only* ✍️ [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 10 *Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* *Egyptian abayas* *Egyptian nighties*. *Bags and jewelries* *Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria* *Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*. # +201121544627 # +2349162662750 Ni dai na kame bakina dan nasan tana iya cewa ta fasa siyar mini da rikicin. Dan haka kaffa kaffa na dinga yi da ita har muka fara shirin barin garin. Ranar da zamu tafi Hafcy kuka har da bubburwar zata bini. Su Khadijah ma duk sun yi lamo domin mun saba da su matuƙa gaya, direbansa ne ya tukomu a motarsa. Muka dawo gida lafiya dauke da tsaraba da kayayyaki masu yawa. Murnar da iyayenmu suka yi da hidimar da yaya Asad ya yi damu ba kaɗan ba ce. Kwanaki biyu Baba Babba a cikin murna da kuzari yake yi. Motsi kaɗan zai ce "In sha Allah ko bama raye Abubakar zai jagoranci kula da dukkan alhalinmu . Barin idan Abida na rattaɓa masa irin kuttu da ta shaƙa a gidansa a dalilin fifita ni da yake a kansa. Sai ya sassauta murya ya ce "Hakan na sake alamtar da ni halin girma ne da shi, sannan zai cigaba da zama babba a tsakaninku muddin rai, ai itace ƙanwarsa ta tashin ƙiyama, kema yi maza ki ƙwace Sulaiman". Ta kyaɓe baki haɗi da buɗe ƙofofin hancinta ta ce"Hmm Baba ke nan! Akwai something behind his caring to her! Definetly akwai wani abu a mind ɗinsa abun ya yi yawa. Bayan haka ni Yaya Sulaiman ina ruwana da shi bare yanzu da baya k'asar." Jikina ya ɗauki tsuma tare da hirji. Domin na tabbatar baba babba zai so ace wani cikin ƴaƴansa ya auri wata a cikinmu dan sake cure zuri'a ta zama dunkullaliya. Sai dai ni kam ba qdai a kaina ba. Shiyasa na toshe dukkan ƙofar da za'a mini auren zumunci. Tunda har yaya Faruku bai furta so ko wani yin motsi mai ƙarfi akan akan soyayyata da shi ba, ai kuwa sai dai a yi a bar ni, babu wanda zan so, in ba shi ba a cikinsu. A kai a kai Sahal yake zuwa zance. Duk ranar da zai zo bana cikin sukuni, girki kwalliya duk na musamman ne. Abida kuwa bata sake cewa komai akan lamarinsa ba. Da gaske ta runtse idanuwanta daga lamarinmu. Sai dai akai akai take yi mini habaicin na ƙi ƴan-uwana ko karar zumunci ban iya ba. Ranar da ƴan kirkin suke kusa ta leƙa su gaisa, ranar da take a botsare ko tunkararta bana yi. Yaya Munirah dai duk sadda ya zo sai ta je sun zanta akan shirye shiryensu na tafiya call to bar a jihar Kano. Wata ranar juma'a da yamma muna tare da Sahal na ci kwalliya ta burge wa. Sai jifan juna muke yi da wani irin murmushi da yake fitowa daga ƙasan zuciya. Ina samun nutsuwar zuciya idan ina tare da shi. Ina jin farin ciki mai daɗin gaske. Domin tunda ga ƙasa zuciyar nake jin farin ciki da zumudi. Muna haka yaya Faruku ya shigo harabar gidan. Kai tsaye ya iso inda muke ya mikawa Sahal hannu suka gaisa. Cikin barkwanci ya ce "Dama na matsu na ganka na ga mai ka taka ne daga zuwanka ka rushe gwamnatina a wajen Bilkisu tashi guda?". Kunya ta kama shi ya ce "Yayanmu ba rushe ka na yi ba, girma ka ci ka matsa mini kaɗan". Yaya Faruku ya faɗaɗa murmushinsa ya ce " Tunda kasan ba ƙarfina kafi ba shike nan, na zama surukinka, ka riƙe mini ita amana domin ita ɗin mai haƙuri ce kuma mai nutsuwa ce." Cikin kunya Sahal ya ce "Da ikon Allah zan rike ta da kyautatawa". Daga haka ya kalle ni, Ni kuma cikin nauyi na ce "Yaya Faruku barka da yini." Ya amsa yana faɗin ai na ɗauka kin zama kurma". Ya wuce cikin gida. Ya numfasa ya ce "Yaya Faruku mutumin kirki ne Bilkisu". Na ce "Sosai fa" Muka cigaba da hira cikin shauki domin ban ƙi mu tabbata muna hira cikin wannan yanayin mai dadi da walwala ba. A wannan dogon hutun mun sake shaƙuwa domin tsallaken kwana ɗaya kacal yake yi. Wani zubin ma kullum ne sai ya zo ko tsoron titi ba ya yi. Ranar wata Laraba da ba na mantawa da yammaci lis muna hirarmu a inda muka saba zama wato harabar gate dinmu daga gefe, domin mu a gidanmu ba'a yarda da hirar falo. Sai dai a filin Allah ƙarkashin bishiyoyi da furannai. Ba zato yaya Asad ya bayyana shi kaɗai babu ƴan rakiya daga dukkan alamu a jirgi ya iso Kaduna. Sai kuma ya iso Funtua tunda haka yake yi matukar zai zo ganin gida. Ya hango ni, ya dunfaromu cikin saurinsa domin shi mutum ne mai hanzari ga shi ƙarfaffa na gaske. Zuciyata ta buga, bansan me ya sanya nake matuƙar nutsuwa idan na ganshi ba, hakanan a duk sadda idanuwana suka hango shi ko da ban ji kalaman bakinsa ba sai zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na kan rasa wannan kasafi sai dai na fi tunanin tsoronsa da ya gina a zuciyata tun ina mitsitsiyata. Duk da a yanzu kirki yake yi mini tare da tarairayata fiye da ƴar ɗakinsa sarkin rikici Abida. Yana isowa na mike tsaye murya a dashe na ce "Baban Bilkisu sannu da zuwa. Ya su Nana da Anti?" Maimakon ya amsa da baki sai ya cire hularsa tare da ƙamewa ya kuma sara mini tamkar dai yadda ya taɓa yi mana ni da Baba babba shekarun baya. Daɗi ya ratsa ni har zuciyata domin gaisuwa ce mai ƙololuwar daraja bare kuma ace mai ɗamara ne ya yiwa farar hula irina da ba ni da wani muƙamin komai sai dan girmamawa kawai. Murmushi ya subuce mini, na ce "Baban Bilkisu na gode da karamcinka". Ya taya ni murmushi fararen haƙoransa suka haska baƙar fuskarsa. Ya ce "So nake Bilki ta manta batun duniyar yaya Asad ta yi ta ganinsa a cikin mutanen da suke sonta tare da kambaba dukkan lamarinta." Na ƙayalkyale da dariya na ce "Ai tunda ka mini takwara na yafe maka, na manta komai na gane na sha gaban Abida. Amma fa ni gaskiya har gobe yaya Faruku ne best" Ya yi waiwaye ya ce "Idan autar momi ta ji wannan maganar ai kin kunyata ni Maigado". Na sake yin dariya na ce "Ai gaskiya na furta". Daidai lokacin Sahla ya gaishe shi cikin nutsuwa domin ya lura ma tamkar bai lura da shi ba, ko kuma mun manta da shi gaba-daya. Ya amsa gaisuwar babu yabo babu fallasa sai dai ko kadan babu raha ko karramawa. Ya wuce cikin gida ya barmu. Hirar da bata yiwu ba ke nan. Domin mintina biyar ya ƙara ya mike tare da faɗin "Zan wuce ina son na isa Zaria da wuri. Baba ya ce zan raka shi dubiya bayan maghriba". Ban kawo komai a raina ba na ce "To" Muka yi sallama ya tafi a sanyaye. Na shiga falon Momi na tarar da shi tare da su Baba suna taya shi rarrashin Abida domin tunda ta gaishe shi bata sake kula shi ba, duk yadda take tatsarsa a dalilin bai mata takwara ba, sai ni ya yiwa, bai sa ta huce da shi ba har lokacin. Na zauna na ce "Wato Allah ya so ni da ba zamu yi kishi ba Abida." Ta galla mini harara tare da ce wa "Yo ai ke tsare mini gaban da kika yi ko kishiya sai haka. Kowa Bilkisu, kowa Maigado, duk wanda suke jama'atane a da kin kwace mini su a yanzu. Abin kaicon kuma naki mutanen kin riƙe su gam tsabar haɗama." Gaba-daya aka kwashe da dariya, yayin da ta gintse tata dariyar da take neman ƙwace mata. Baba ya ce "Abida ƙanwar Bilki kina sanya ni nishadi, idan kuna makaranta sai na ta jina tamkar wanda ya rasa wani abu. Domin kullum kuna ɗebe mini kewa na yi ta tuno da ƙuruciyarku." Yaya Asad ya ce "Yaran nan kun samu duniya, Allah yasa lahirarku ta zarce hakan." Wannan karon Abida ce ta yi dariya tare da ce wa "Kai Yaya! Ya murmusa ya ce "To me zan ce? Gaba-daya kun tattare soyayyar ya'yan fari da ya'yan karshe ku kaɗai. Fatan Allah yasa kuna ibada tuƙuru yadda lahirarku ma zata yi muku daɗi fiye da nan" Ya nisa ya ce "Wai ina Muni ban ji ɗuriyarta ba". Baba ya ce "jiya ta je Katsina yayarsu bata jin daɗi shine ta je ta ɗan kula mata da yara kafin tafiyarsu Kano ta taso". A ladabce ya ce "Allah ya bata lafiya, amma mun yi waya bata faɗa mini bata da lafiya ba". Baba ya ce "ka manta zurfin cikinta ne? Kasan kuma ce wa zata yi, kana nesa ba zata tayar maka da hankali ba tunda ba kashirban take ba '". Bamu tashi ba sai da aka fara kiran sallar magarib. Ni da Abida muka yi sashinmu dan bawa baba babba damar ganawa da baban Bilkisu sosai. Tunda ya mini takwara na koma ce kishi hakan a gabansa ko ba'a gabansa ba. Na kuma fahimci yana son sunan domin da karsaahi haɗi da kazangi yake amsawa. Daren ranar shiru Sahal bai ƙira ni ba, tunda tara da rabi ta yi na shiga tunanin ko lafiya domin da zarar tara ta yi idan muka fara waya muna kaiwa goman dare ko fiye da haka tamkar da akan iska muke magana ba kuɗi ba. Da goma ta yi sai na kasa haƙuri na buga masa, amma har ta katse bai ɗauka ba, kuma bai katse dan ya biyo baya ba. Ban shiga mamaki ba sai da aka shafe mintina talatin bai bugo ya gabatar da uzzirin baya kusa ko yana tare da iyayensa ba. Gabadaya na daburce, na sake ƙira a karo na uku sai na ji an kashe wayar ma bakiɗaya. Da yake fashin sallah nake yi, sai na takure a kan gado gaba daya na rasa jin daɗin zuciyata. Yayin da tuni Abida ta yi barcinta cikin nutsuwa. Idan akwai abin da yake burge ni da Abida to rashin sanyawa kai damuwar duniya ne. Samsam bata yarda ta yi sabo da abin da zai dame ta. Kusan kullum sai ta ce mini soyayya lalura ce kabiran. Kafin ta yi barci ma da ta lura da yanayina sai da ta ja tsaki ta ce "Ya miki sabo da kalaman da kaso saba'in cikin ɗari na daɗin baki ne ba na gaskiya ba. Da zarar an haɗaku zaman aure hirar mintina goma ma sai an wayi gari ba zai iya ware wa cikin lokacinsa ya yi da ke ba, a yanzu kuma ya yi miki sabo da doguwar hirar da idan baki ji daga gare shi ba zaki kidime ki kasa sukuni. Me za'a yi da soyayya irin taki ne Bilki?" Da nasan gaskiya ta faɗa sai na kasa amsa mata domin ba ni da bakin yi mata musu ko raddi dan idan ta kaikaice ta fara cashe mini sai ta sanya ni kuka na gaske. Sannan zata juya ta yi kwanciyarta, cikin nutsuwa zan ga tana sauke numfashi tabbacin barci mai cike da nutsuwa take yi. Da ƙyar na yi barci ina ta saƙesaƙe ko jinya ce ta kwantar da shi tunda a kullum sai ya ce mini ba zai iya barci bai ji muryata ba. Shiyasa ma baya ƙirana sai ya yi sallar Isha domin da zarar mun gama waya barci yake yi muryatace abu na ƙarshe da yake ji a ko wanne dare. Ina idar da sallar asuba na sake ƙiran layinsa amma shiru kake ji a kashe take. Na shiga damuwa duk yadda nake son komawa barci ranar ban samu sukunin komawa ba. Sai da muka karya muka yi sashen Momi hannuna ɗauke da ledar alawa da biskit masu tsada cikin wanda Sahal yake kawo mini na ɗiba na zuba a leda da yawa da mufin na bawa baban Bilkisu ya kaiwa Hafcy. Muka tarar shi kadai yana karyawa kuma ya yi haramar komawa. Muka gaishe shi ya amsa tare da faɗin "Na shiga gaida Mami da Baba ƙarami baku tashi ba". Abida ce ta amsa da ce wa "ki ce ban tashi ba kawai, amma ita bakam ta yi bata cikin hayyacinta saurayinta ya yi mata fushi tun daren jiya ta rasa walwala da kuzari ". Ga mamakina sai na ga ya ɓata rai, bacin ran da ya bayyana har a fuskarsa. Da farko tamkar zai share sai kuma ya kasa hadiyewa ya ce "Har haka kika bari ya mamaye ki ne Bilki? Ni ba dan kar na zama babban kwabo ba da sai na ce miki kin fishi ƙarfi da karsashi, gabadaya fa siffar mata gare shi wannan yaron, dan dai kina sonsa ne, autar momi ta yi gaskiya zubin makirai ne da shi, kin kasa ganewa, bansan me yasa ba zaki gane gaskiyar lamari ba, yanzu saboda Allah Maigado menene aibun auren mai mata ne?" Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Amma saboda yadda Abida ta kasa ta tsare tana kallonmu nasan ba iya kallon kawai take yi ba, har da nazari. Domin kamewa ta yi tana kallonmu cikin tsananin nutsuwa. Dan haka cikin rawar murya haɗi da kuka na ce "To shine ya tunkare ni da sunan soyayya ban da shi babu wani, sannan mai matar ai bai zo ba, bare ace na jingina masa aibu." Bansan ya aka yi ba Abida ta yi fit ta ce "Sau dubu nawa zasu zo? Yaya Faruku fa?" Takaicinta ya shake ni, na rushe da kuka sosai na ce "Da yaushe ya taba tare ni da sunan soyayya ta gaskiya ba ta wasa ba?" Kafin ta amsa mini Baban Bilkisu ya ce "Kin fita gaskiya. Faruku bai zo da gaske ba, amma akwai wadanda suke son ki da gaske kina tankwabarwa, abokin nan nawa da gaske yake yi, bayan shi akwai wani da zaki amince ya tabbatar mini ko yaushe a shirye yake domin kin yi masa irin sosai ɗin nan". Abida ta numfasa ta ce "oh Yaya Asad! Ya yi biris da ita domin sosai ya ɗaure fuska dan haka dole ta kame bakinta ta tsuke. Ya numfasa ya ce " share hawaye ki ki daina kuka kin ji, ba wacce aka yiwa auren dole a gidan nan, matukar ina raye kema ba za'a yi miki ba, ina miki fatan alheri tsakaninki da yaron". Daga haka ya mike ya zura hannu a aljihunsa ya ciro ƙudi ya damƙawa Abida ya ce "ke da ita, ku sayi abin da kuke so idan zaku koma makaranta." A sanyaye ta yi masa godiya. Ni kuwa na kasa yin godiyar. Ya ce "To mu je ku raka ni mu yi sallama da su Baba." Na miƙe na zare abin hannuna wanda na stones ne, na sake zaro ribbon din kaina na jefa a ledar alawaer na ce "ga shi ka kaiwa Hafcy, ka faɗa mata I realy miss her silly questions." Ya murmusa ya ce "Kullum sai ta yi hirarki, kullum sai ta ce "Anty Maigado zata. Ga shi Maigado ba mai fahimta ba ce". Zuciyar tawa ta sake karaya,.nauyi mai yawa ya kama ni. Na saci kallon Abida na ga itama kallona take da dukkan nutsuwarta. Haka muka bi bayansa ba tare da mun iya tofawa ba. Ya yi sallama da kowa, iyayenmu suka bishi da sanya albarka tare da nema masa tsarewar Ubangiji akan dukkan lamarinsa. Har waje muka bishi ni da Abida. Bana manta kallon da ya kafe ni da shi, amma bai ce ƙala ba, illah faɗin "ku kula da kanku Allah ya sake haɗamu da alheri." Abida ta rike hannunsa ta ce"Ka kula da kanka yaya! Su Baba na buƙatarka, matarka da ƴaƴanka na buƙatarka, muma muna sonka, kada ka saka damuwa mai yawa akan lamarin wanda baya bukatarka ko ba shi da asara idan ka haɗu da jinya ". Ya zuba mata ido irin sosai tare da ruƙo dukkan hannuwanta murya cike da rauni ya ce "Zan kiyaye autar momi! Sai dai bana son ki zama mai son kai, ko tursasawa ga rayuwar wani ta hanyar kyara da ƙaranta mu'amala. Kina da hazaƙa, kina da saurin fahimtar al'amurra. Na roki kada ki yi ƙullaci ko kushe wanda Maigado take so " Ta amsa da ce wa "To" a takaice. Jikina ya sake sanyi sosai domin na gaskata sona yake yi. Sai dai tabbas bai yi mini ba, duk yadda yake a tsaye kuma ƙarfaffa. Amma bana son auren zumunci, bana son auren mai mata bana son baƙin namiji. Ya shiga motar da ta zo daukarsa suka tafi. Abida ta yi gaba ta bar ni da sanyin jiki. Da ƙyar na ja ƙafafuwana na bi bayanta. Shariyar Abida da rashin samun wayar Sahal suka yi mini rubdugu. Yini guda ina ɗaki sai juyi nake yi na rasa sukuni a jika da zuciyata. Da na idar da sallar la'asar na dauki wayar na sake ƙiran layinsa a karo na barkatai. Cikin sa'a ta shiga, gaba-daya na ji wani irin salama ta shige ni. Sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba. Na sauke ina sake gaskata lallai akwai matsala. Sai dai tunanina bai haƙaito mini menene dalilin faruwar haka ba. Ina ta kokawa da zuciyata akan kada na sake ƙiransa. Ba zato sautin da na sanya masa na real love by massari ta hau tashi. Kamar zan share amma na kasa sharewar. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 11 Deenah cakes and more -Kano 09038055790 IG @Deenah cakes and more Snacks such as : Birthday cakes Cupcakes Samosa Springrolls Meatpie Frozen snacks Event snacks *Lafazi writer's* Jiki na bari na amsa kiran. Ba wani karkasashi ya ce "Na ga tarin missed call dinki, hidima ta sha kaina ban samu sukunin kiranki back ba". Na yi sororo da waya a hannuna. Domin a yadda na dauka babu hudimar da zata hana ya nemi ji daga gare ni, mussaman wayar dare da ta zame mana kaida. Tsawon lokacin ban samu sukunin lalubar kalma ko guda ba. Ya numfasa ya zarce da ce wa "Bilki so nake ki bani dama na turo a tsayar da maganar aure a tsakaninmu. Don so nake yi, na takaitawa kaina zullumi da fargabar rasa ki". Gabana ya takarkara ya fadi. Aure kuma? Ban ci karfin karatuna ba, duk yadda nake son Sahal ban hakaito na yi aure a lokacin ba, domin dukkan sisters dinmu ba a aurar da su ba sai da suka kammala digiri. Ga Yaya Munira ma bata yi a aure ba sai ni?" Da rawar murya na ce "Aure yanzu?' Ga mamakina sai kawai ya katse wayar gabadaya. Ba tare da ya ce uffan ba. Na rike wayar ina kallonta tamkar wacce zata fahimtar da ni dalilin sauyin da nake ga ni a tare da Sahal. Gabadaya na sake rikicewa, na kasa gane mai yake yi mini dadi a duniyata. Kwanakin biyun da suka biyo baya masu tsauri ne domin gabadaya Sahal ya yi watsi da ni. Na kasa tattauna halin da nake cikin da kowa. Abida ce abokiyar hirar, sai dai ban isa na tunkareta da maganarsa ba. To ban fada mata matsalata da shi ba kullum a cikin yi mini habaci da shaguben son da nake yi masa ya zarce wanda yake yi mini take. Bare yanzu da take mini fushi akan ban so brothers dinta ba. To ina kuma ga na bude baki na tabbtar mata damuwar da nake kwana na yini a cikinta Sahal ne sababinta. Cikin rashin karsashi nake hada kayana na komawa makaranta tunda a sati mai zuwa hutunmu zai kare. Kwanaki biyu ke nan da nutsuwa ta yi mini tutsu sosai a dalilin kullum lamarina da Sahal na sake cakalkalewa. Na gama tunanina nasan ban yi masa komai ba. Haka kuma nasan bamu samu sabanin ra'ayi ba. Haka siddan matsalakan ya dauki zazzafan fushi da ni, dan kawai yasan zuciyata ta shaku da shi, ta kuma kambaba sha'aninsa. *Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633* Ranar talata da daddare bayan Abida ta yi barci. Na lallaba na kira wayarsa domin na kai matukar gajiya wajen takura da yanayin da ya jefamu. Bugu biyu ya dauka murya babu amo ya yi sallama. Na amsa sai kuma na yi shiru. Na kasa ce wa kanzil. Murya a dashen ya ce "Me ya hana ki barci Bili?" Maimakon na amsa sai na jefa masa tambaya na ce "Ni kam mai yake faruwa ne. Tun zuwan da ka yi last gabadaya ka canja mini, na gama iya nazarina ban hango inda muka samu sabani ko na bata maka ba. Amma ina ta ganin changes masu yawa a tare da kai. Tun ina yi maka uzzirin ko yanayin rayuwa ne har na fahimci kawai dan ka ga na damu da kai ne shiyasa zaka yi amfani da hakan wajen gigita nutsuwata! Na kammala maganata cikin yanayin damuwa ainun. Ya numfasa ya kaurara murya ya ce *Bilkisu".* Na kasa amsawa domin ban saba jin ya kama cikakken sunana ba, yafi ce wa Bilki ko Bily. Ya zarce da fadin "Gaskiyar maganar ban ji dadin wulakanta ni da yayanku ya yi a gidanku ba! Gabana ya takarkara ya tsinke. Na kasa hakaito wanne a cikin yayan nawa yake batu a kansa? Ban kai ga ganowa ba ya ce " Bilki tuni na fahimci mafi yawa y'anuwanki basu sona tare da ke. Na gama tunanina ban samu gamshasshen dalilin da zai sa su washe ni irin haka ba. Amma daga ranar da muka yi ido hudu da Asad Funtua na gane shi suke marawa baya, haka nan muzanta ni da ya yi a gabanki ya tabbatar mini da ce wa sonki yake yi, an kuma shirya yaudarata ne shi ya sanya aka karbi iyayena da hannu bibbiyu." Raina ya baci sosai. Da rawar murya na ce "Wa ya shirya yaudarar naka ni ko iyayena Sahal?" Jin na harzuka da yawa sai ya yi maza ya sassauta ya ce "Ai idan muna magana a tsakaninmu iya ni da ke ta shafa, babu maganar iyayenmu a ciki don kuwa ba abokan wasanmu bane. Ke kike mini wasa da hankali. Domin yadda kika manta da ni daga isowar yayanki wajen da muke zaune ya tabbatar mini da cewar kema kina sonsa, kinsan kuwa duk yadda iyayenku zasu so ni ba kamar dansu ba ko?" Na sauke nannauyar ajiyar zuciya na ce "Ba a mini dole akan lamarinka ba, da yawuna ka turo aka tambayar maka izinin neman aurena, menene zai tayar maka hankali akan Yaya Asad?" Da azama ya ce "Soyayyarki da na ga ni cikin idanuwansa da gangar jikinsa ce ta dame ni". A tausashe na ce "Indai ba a nawa idanuwan ka ga soyayyarsa ba, ban ga abin damuwa ba, domin kuwa na riga na zabe ka". Maimakon ya ji dadin kalamaina ya gasgata ni, ya huce. Sai ya numfasa ya ce "Indai nine zabinki to zan turo a yi maganar aurenmu idan ba haka ba, to kuwa sai dai idan hakan ya zama lisisin korata. Ni ba zan iya jure zullumin da nake ciki akan wannan tafkeken dansandan ba". Na murmusa na ce "Me yasa ka karaya haka? Me yasa ka rasa jarumtar gwarazan maza?" Murya babu amo ya ce "saboda Baba babba ne ubansa. Kin sani, na sa ni kuma still baba babban ne mai bada aurenki, idan kuwa haka ne ko ban ce komai kin san ína da hujjoji da zasu karya dukkan confidence dina." Na numfasa na ce "Dukkan sisters dina da aka aurar sai da suka kammala jamia, ni fa yanzu ne na gama shekarar farko ma, ka yarda kai ne zabina". Ina rufe baki ya ce " Allah ya bamu alheri! Cikin fishi ya furta hakan, sannan ya katse kiran. Na daure ban kira shi ba . Kwanaki biyu Muna cikin takaddama. Kan dole na hakura na bi ra'ayinsa na amince mu yi auren tunda shine samun masalaaha a tsakaninmu. Domin gabadaya ya fittitke akan ko dai mu yi auren ko kuma na ya yi gaba ba zai yarda na cigaba da yaudararsa ba. Bamu koma makaranta ba sai da ya turo aka yi maganar aure tare da kawo dukkan abubuwan da ake yi ja al'ada. A sanya aure watanni hudu masu zuwa wanda ya yi daidai da kammala zangon farko na aji biyu. Mahaifana duka biyu basu wani so lamarin ba, domin kowa da dalilin da ya hana shi zumudi. Baba karami so ya yi ace a cikin yayan Baba babba ne zai aure ni, yayin da mami take kuncin ga Munira nan da kammala digiri ba a yi mata aure ba sai ni dan bakar mugunta irin ta Baba babba. Ni dai na kame bakina ban ce mata komai ba, amma nasan koma menene nice da alhakin komai tunda sai da baba babban ya tambaye ni, na amince Sannan ya basu damar zuwa da maganar aure. Ansar na zugata, yayin da Yaya Sulaiman ya ce "Mami huce ki daina damuwa dan ta riga Munira da Abida aure ai ba wani abin bane. Kowa da yadda aka tsara masa rayuwarsa, kawai yi hakuri ki bita da addu'ar dacewa". A lokacin ya zo hutu. Kan dole ta hakura amma ba dan ta so ba. Murna da zumudi da Sahal ke cikinsu ba zai yiwu na iya hakaitosu ba. Domin gabadaya ya ninka kulawar da yake yi mini, yayin da ni kuma na takura gabadaya na kasa samun nutsuwa a zuciyata. Haka siddan nake jin tamkar na yiwa kaina garaje. Na rasa da wa zan tattauna, na rasa wa zan tunkara ko na samu na fita daga takura da na samu kaina a ciki. Ana jibi zamu koma makaranta. Da hantsi na ji ana ta kiciniya a harabar gidanmu. Da yake dakinmu na sashen baba babba muna ganin harabar ta taga. Da yake bana iya barci a dalilin nauyin da zuciyata ta yi mini a kwanakin nan. Ya sanya na sauka daga gadona na isa jikin tagar na yaye labulen kadan dan kada haske ya isa ga fuskar Abida ta tashi ta rufar mini da bala'i. Tunda aka saka ranar aurena ta sake botsare mini fiye da kwanakin baya. Ba gaba take yi da ni ba, a a kawai ta sake kamewa daga shiga dukkan shirgina, yana wahalar gaske ta yi mini magana a karan kanta, amma idan na yi mata zata amsa ko da a takaice ne. Haka nan shekaranjiya bayan an kawo kudin aurena. Ta kalle ni jikinta a sanayaye ta ce "Ina miki fatan alheri a cikin hukuncin da kika yankewa kanki. Ina miki fatan kada ki yi kuka a hannun Sahalu" Daga haka ta bude littafin Jiki magayi ta hau bitarsa da haka Har barci ya sure ta. Na saki ajiyar zuciya mai nauyi ina cigaba da leken yadda ake ta daura tampol tare da shimfida tabarmai . Tsawon lokaci ina tsaye ina kallo tare da cankecanken me za'a yi haka a gidan na hidima bamu sani ba? Na tabbatar da mutuwa ce ba zan ga ana yin aikin cikin walwala da nutsuwa ba. Nan da nan aka kammala shimfida aka shiga ajiye kulolin abinci kalakala tare da lemounan kwalba na maltina da su coke. Na sake shiga mamaki, sai na yi tamkar na tashi Abida sai na fasa domin tashinta a barci bata dauke shi da sauki ba. Yana cikin zunubin da idan aka yi mata sai an biya ta da wani abu, ko ku yi ta buga dabi. Kafin ka ce kwabo kuma sai shigowa ake yi ana ta zama, na gane wasu da yawa abokan Yaya Faruk ne. Yayin da ban gane wasu da yawa ba. Ina tsaye ina kallon ikon Allah kawai sai na ga Yaya Faruk ya shigo ya zauna cikin alhini, sai mika masa hannu ake yi ana yi masa jaje tare da fatan Allah yasa hakanne alheri. Kaina ya sake kullewa, a fili na furta "Menene yake faruwa ne?" Gabadaya wajen sai hada hada suke suna cin abinci ana ta hira yayin da Yaya Faruk ya tagumi cikin takurarren yanayi. Can Kuma na ji ya hau fadin "Ba fa hira da nishadi na kiraku mu yi ba. Na gayyatoku ne ku taya ni alhinin rasa sarauniyar shaiba". Suka dauki hayaniya kowa na fadin "Rashin rabo ya sanya bai fahimci Dingishin kwado da wuri ba. Ni kuwa gabadaya na ji jiwa na katantawa da ni, kaina ya kulle dakin ya shiga juya mini tamkar an mayar da kasan ya koma sama. Hawaye ya balle mini. Wani irin abu ya sake tokare mini a kirjina. Hakan ya saka damuwar da nake ciki ta rubanya tsananta. Bansan ya aka yi ba na ware baki na fashe da matsanancin kuka, hawaye da majina suka dinga sintiri a fuskata. A kidime Abida ta tashi ta zauna a tsakiyar gadonta. Murya a dashe kuma a firgice ta ce "Me ya faru, mutuwa aka rafkane Bilki? Hayaniya nake ji sosai". Ta duro a gigice dan taga abin da yake wanzuwa har ya sani kuka sosai. Bata ga komai ba, illah Yaya Faruk da jamaarsa suna ta cin abinci da alamu walima ake yi duk da shi din bata ganshi da kuzari ba. Ta saki labulen yayin da ni kuma na yi kasa na zauna dabas a kasan tayal ina cigaba da kokawa ainun. Ta yi shiru amma gabadaya jikinta ya saki. Ta zauna kusa da ni a tausashe tamkar ba Abida ba ta ce "Na hada ki da darajar ma'aiki ki fada mini me ya sanya ki kuka irin haka? Ta ruko hannuna na dama ta dora a saitin inda zuciyarta take. Wani irin bugu take yi fiye da kima. Ta zuba mini idanuwanta da barci da firgici suka jirgitasu. Na yi kasa da kaina ina gunjin kuka. Ta rike hannuna sosai tabbacin hakuri take ba ni duk da bata furta hakan da baki ba. Da rawar murya na ce "Yaya Faruk ne Abida! Na furta hakan cikin rushewa da kuka fiye da wanda nake yi. Ta zabura ta fita ko mayafi bata saka kan doguwar rigar barcinta cotton ba. Da Yaya Sulaiman ta yi kicibis. Ya shigo diban ruwan da lemo a fridge din momi. A matukar razane ta ce "Me yake faruwa ne a gidan nan Yaya Sulaiman? Ina Yaya Faruku?" Ya amsa da ce wa "Ga shi can ana masa jajjabin an kasa shi a soyayyarsa da Bilki! Tausayinsa ya tsirgawa Abida ta sani yana son Bilki, ta kuma sani tunda ya gane Yaya Asad shima an jarrabe shi akan sonta shiyasa ya shiriritar da maganar tun kafin su fahimci Yaya Asad na sonta shi ya fahimci hakan. Gabadaya dukkansu uku tausayinsu take ji, amma a yau na Yaya Faruk yafi tsananta. Bilki kuwa haushin yadda ta rufe ido ta kasa zaben mutum guda a cikin yayyen nasu ya dakushe tausayinta. Ta koma ta zauna a bakin gado tana hurar da iskar damuwa. Kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce "Bilkisu ki rufe mini baki, tun ban miki sanadin da zaki yi kuka fiye da hakan ba. Wanne irin kasafi ne haka? Menene zaki yi kuka akan Yaya Faruk alhalin ba dole aka yi miki kika zabi waninsa kika bar shi ba. Ko makaho ya zauna da ke da Faruku sai ya gane yana tsananin sonki, amma kika runtse idanuwanki kika bar shi. Yanzu kuma ki ce zaki yi kuka dan yana bayyanawa duniya alhinin asarar rashinki da ya yi! A matukar kufule take wannan maganar. Tashin hankali ya yi mini kawanya. Zullumi da fargaba suka saka na yi zurzuru cikin lokaci kalilan. Na rarrafa na isa gaban gadon da take zaune na durkushe gabanta na ruko dukkan hannuwanta biyu, murya na rawa na ce "Abida ki yi mini adalci, ki ji tausayina ko iya na yau ne a rayuwata. Na rasa gane me nake ciki, kaina na shirin fashewa, zuciyata na shirin tarwatsewa Wallahi ina jina cikin bala'in da ya yi mini dauri tamkar huhun goro! Ta sassauta amma bata furta komai ba. Na ce "Ki yi alkalanci na gaskiya Abida kin sani ina sonki, kin sani da ke nake son na yi sharing damuwata anan duniya dan Allah kada ki rufe mini wannan damar a wannan tsukun da nake ciki na cankacakare" Ta cigaba da yi mini zuru hakan da na gani na alamta mini hankalinta na kaina tare da abin da zan furta. Hawaye na zuba na ce "Abida tsakaninki da Allah Yaya Faruk ya taba tsayawa kai da fata akan yana sona, so na gaske?" Ban jira amsarta ba na ce "Na sani kun fi kusa da shi a kaina, amma ban zaci zaki yi mini irin wannan son kan ba Abida. Ya kike so na yi? So kike na ce wa baba babba Yaya Faruk nake so ya aura masa ni alhalin shi da yake namiji bai yi hakan ba? Bayan matarsa yana da halin ya auro uku ba ni kawai ba amma tsananin tsoronta, ya hana shi kuzari akan sha'anina. Amma ke da kika fahimce ni, irin fahimtar da babu wanda ya yi mini irinta sai kuma ki hau gaba da ni akan lamarin da bani da laifi a cikinsa ko kankani! Akan me zaki rufe mini kofofin tattauna halin da nake ciki Abida? Akan me zaki yi mini irin wannan alkalancin akan lamarina da ya Faruk?" Na fada ina rushewa da matsanancin kuka domin tsakanina da Allah gabadaya na daburce na kidime ban san ina son yaya Faruk over ba sai a ranar. Ta sassauta kwarai da gaske ta busar da iskar damuwa ta ce "Yaya Faruk mutum ne mai matukar karamci da sadaukarwa, yana sonki, yana da burin ya aure ki, so yake ki kammala sakandire sai ya bayyana ta yadda ba zaku dade kuna dating ba zaku yi aure. Kwatsam sai aka jarrabi yayansa da sonki, irin son da ya kasa boyuwa a kirjinsa da gangar jikinsa. Hakan da Yaya Faruk ya fahimta ya sanya ya zabi ya bar lamarinki a zuciyarsa gudun kada shaidan ya kawo musu yamutsi! Amma ke gabadaya kin tattara kin rufe kofar da Yaya Asad zai same ki, kin ga ai dole Yaya Faruk ya shimfida tabarmai a yi masa jajen asarar da suka taffka ta biyu babu " Na kasa cewa komai sai kukan da na cigaba da yinsa ainun. Murya ba amo Abida ta sake cewa "Dole na ji babu dadi akan sha'aninki mana. Na yarda Yaya Faruk bai zo ya nuna kansa da gaske ba. Yaya Usman fa? Yaya Asad fa? Wanne irin hannunka mai sandane bai yi miki ba? Har mai suna ya yi miki alhalin bai sanya sunana ba, kinsan kuwa na fiki cancantar ya mini cibina ba dan cikinmu guda ba sai dan tun filazal ni ce tasa ke ta Yaya Faruk ." Na zuba mata ido hawaye na cigaba da tsere akan fuskata. Yayin da ta numfasa ta ce "Dan haka ki rufe mini baki da wannan kukan domin dai ke kika yiwa kanki zabin da kike ganin kin gamsu da shi. Ba kuma zai yiwu ki hana zuciyata taya y'anuwana yanuwana bakin cikin asarar rasa ki da suka yi ba, hakanan ba zaki iya cire mini takaicin yadda kika zabi zumuncinmu ya yi rauni ba. Dan kuwa da wani cikinsu kika aura zan yi mu'amala mai k'arfi da gidanki fiye da ace bare kike aure". [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://www.instagram.com/deenah_cakes_and_more?igsh=c2lnZjk5Z3pjYjNw&utm_source=qr *Deenah cakes and more -Kano* *09038055790* *IG @Deenah cakes and more* *Snacks such as* *Birthday cakes* *Cupcakes *Samosa* *Springrolls* Meatpie *Frozen snacks* *Event snacks* *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 12 Na sake ruko hannunta na ce "Saboda hakan sai na rasa hakkin da nake da shi na zumunci? Shike nan har kawancenmu ma sai ya shiga tasgado Abida? Yanzu ba zaki sake a gidana ba dan ban auri siblings din ki ba? Ashe haka kike da son kai mai yawa ban sani ba?" Ta girgiza kai ta ce "Bilkisu kada ki juya mini manufata, kin sani sarai da abin da muke fata ya tabbata a tsakaninki da wani cikinsu, yadda gidanki zai zama dandali a wajena ko ban biki mun tare ba, to kuwa zan mayar da gidan ne wajen zuwana da hutawata domin dukkanku nawa ne sabanin idan ke ce tawa zan dinga yin kaffa kaffa domim ko iyayenmu ma ba zasu yarda na yi ta yi miki jele mai yawa ba." Da rawar murya na ce "Kira Yaya Faruk na fada masa ina sonsa ya je wajen baba babba sai a mayarwa da Sahal kayansa a dawo da auren kansa". Ta zuba mini ido ta ce "Ai hakan ba mai yiyuwa ba ne. Ban ji a jikina Yaya Faruk mijinki bane har abada kuwa. Dama Yaya Asad kika ce. Dan kuwa Yana sonki fiye da Yaya Faruk. Nima kuma ina taya shi sonki, ina matukar son a ce ya yi amarya da ke. Da bakinsa ya ce mini da ace ubangiji zai kaddara ki zama matarsa da ya tabbatar dukkan niimomi sun tabbata a gare shi. Idan har zai zauna ya fada mini hakan ni da nake kanwarsa na tabbatar son da yake yi miki mai girma ne." Na yi kasa da kaina na kasa furta kalma ko guda domin ni kam ban taba jin sonsa ba, asalima haushinsa ne ya sake cushe mini makoshi ta yadda ya zama sanadin da yaya Faruk ya shatawa soyayyata layi. A matukar raunane na ce "Ni dai sai idan Yaya Faruk ne! Na fada zuciyata a kuntace domin har cikin kasan zuciyata nake jin sonsa. Ta ce "ai maganarki ta yi k'arfin da ba za'a canja da wani ba. Baba babba ne ya karbi komai yanzu kuma sai ya koma ya fadawa iyayen Sahal ya fasa bashi aurenki haka siddan babu dalilinsa na yin haka. Sannan kuma a ji ya daura aurenki da wani cikin yayansa. Anya ko duniya bata yi zundensa ba, mu da kanmu ai dole mu kalubalance shi da zama dattijon kawai". A matukar raunane na ce "To ki dawo da amincin da yake tsakaninmu Abida. Ki daina share ni. Ki daina mini fishi Ubangiji ne shaidar ina cikin takurarren yanayi a dalilin auren da zan yi da kuma fishinki! Ta numfasa ta ce"Na huce maigado. Amma kin sani tun filazal jinina bai hadu da yaron nan ba, nima zan roke ki. Ki yiwa Allah ki yi mini adalci kada ki saka ni mu'amala da shi, kada ku samu sabani ki fada mini domin zan sake tsanarsa ba kuma zan ba ki shawara mai dadi ba a kansa. Idan kuwa hakane to kawai mu yi zumuncinmu da harkarmu a tsakaninmu amma kada na shiga cikin aurenki na roke ki, da sunan Ubangiji ki yi mini wannan alfarmar dan so nake aurenki ya yi k'arko ya kuma yi albarka". Da kuka sosai na ce "Ba zan fada miki ba, ba zan saka ki ba tunda na gane ba kya son shiga din. Amma ki sani wannan matakin zai iya zama nakasu a zuciyata, domin kinsan yadda na saba sharing damuwata da ke. " Ta numfasa ta ce "Ina fatan matsalolin da zaki shiga a gidan aurenki su zama kadan ne kuma masu sauki sosai." Har aka yi sallar azahar muna tare cikin wani irin yanayi mun yi jigum jigum kowa na ta sake saken zuci, ba kuma mu sanyawa cikinmu komai ba. Taron Yaya Faruk kuma sai lokacin ya tashi bayan sun yi jam'in sallah. Kowa ya kama gabansa suna ta yi masa tsiyar ya zama ragon namiji tunda ya bari wani ya shigo har cikin gudansu ya ci shi da yaki. Can muka jiyo shi daga falon momi yana dokawa Abida kira. Bansan ya aka yi ta kasa amsawa ba domin da gaske jikinta ya yi sanyi irin tubus din nan. Ba a jima ba muka ji ana kwankwasa kofar ɗakinmu. Murya a dashe ta ce "Bismillah. Ya turo kofar ya lek'o, da kansa kadan har ya fara hargagin tana jin yadda yake kiranta amma ta yi mukus alhalin ta ji shi. Ganinmu tare a zaune ga alamun kuka nake yi sosai ya sanya ya shigo d'akin gabad'aya ba tare da ya shirya ba. A matukar gigice ya ce "Me ya samu sarauniyar shaiba ko dai zuciyarki na taya ni alhinin da tawa zuciyar ke ciki na gagarumar asarar rashinki ?". Yana rufe baki na sake fashewa da kuka mai sauti tamkar dai ba shafe lokaci mai tsayi na yi ina kukan ba. Ya sake rikice wa ainun domin tunda nake da Yaya Faruk a hankalina wannan ranar ne karon farko da ya kai hannunsa jikina. Dukkan hannuwansa ya saka ya ruko nawa hannun dake cikin na Abida. Ya kasa cewa komai domin idanuwansa sun kada sun yi ja matuka da gaske. Ni da shi muka tsurawa juna ido, tuni nawa idanuwan suke zubar da hawaye yayin da nasa suka cika da kwalla taf. Soyayyata baro baro a idanuwansa da gangar jikinsa gabadaya. Domin ya yi laushi da alamun rashin kuzarin da yake zuciyarsa ya shafi gangar jikinsa gabadaya. Duk yadda yake da hayaniya da kwarafniya sai da kawo kudin aurena ya yi masa bugun da ya yi matukar kasarra shi ya zama irin yanayina na rashin hayaniya da shiru shiru. Murya na rawa na ce "Me yasa haka Yaya Faruk? Me yasa ka mini haka? Jamila ta fini tasiri da kyallin goshi a zuciyarka da idanuwanka ko?" Idanuwansa na cikin nawa ya shiga girgiza kai murya ba amo ya ce "Ina ko kusa, ba haka bane Bilkina. Kawai ba a kaddara mini cikin littafin kaddarata cewar ke matata ce ba. Amma Allah da ya haliccemu ya sani na soki, ina kan sonki. Ba kuma zan daina sonki ba sarauniyar shaiba muddin ina zukar numfashi". Daga haka ya kasa jarumtar sake cewa uffan illah rungeme ni da ya yi tsamtsam. Gabadaya jikina ya hau tsuma na kasa kwacewa domin na lura gabadaya ya manta cewar ni din ba Abida ba ce da idan ya rungeme ta irin haka shaidan ba zai kawo musu caffa ba dan kuwa muharramarsa alhalin ni kuwa so da begen juna ne a tsakaninmu. Da kyar na yi jarumtar zamewa na koma gefe ina kuka sosai, abin mamaki sai na ga shima hawaye na zubar masa haka ma Abida. Na sake kaduwa domin Abida tana da matukar taurin rai abin da zai sa zuciyarta ta karaya to kuwa lallai babba ne. Bai ce komai ya juya ya bar dakin, da alamu ma gidan ya bari gabadaya. Daga ni har Abida mun koma wasu iri tamkar wadda aka yi mana mutuwar kwatsam. Na kuma gane a yanzu tana tausayina, ta kuma daina jin haushina domin ta daina kyarata kullum a tausashe take yi mini magana. Har muka koma makaranta bamu wani wartsake gabadaya ba. Sahal da kansa ya gane ina cikin takurarren yanayi. Domin gabadaya bana mararain amsa masa waya kamar yadda nake yi a lokutan baya. Har zangon karatunmu ya fara nisa, sannan na warware na cigaba da sauraran Sahal cikin dadin rai. Domin shima na gamsu yana sona gabadaya ya rasa sukuni a dalilin sauyin da yake ga ni a tare da ni, kullum yana zarya tsakanin Zaria da Kano. Sannu a hankali muka kammala wannan zangon cikin nasara. Muka koma gida muka tarar an kammala komai na siyayyar aurena wanda Yaya Asad ne ya siya kayan daki tunda ga kan gado da setin kujera na alfarma. Hatta su firij da talabijin. Ya ce lokaci ya yi da su Baba zasu fara hutawa da hidimarmu, su fara shan yayan itace da suka shuka bayan dogon kulawa da suka yi da wannan dashen. Gidan maza sun kawo lefe da ya amsa sunan lefe domin kuwa ba karamin dukiya aka zuba ba. Ba yadda za'a yi ka ce angon bai fara aiki ko kuma ba sana'a mai k'arfi a hannunsa ba. A bakin Ansari na ji sati uku masu zuwa ne aure. Na riga kuma na sani Zaria zan zauna domin Baban Zaria ya bashi wani karamin gida a cikin Hanwa ya zauna dan kada karatuna ya samu tasgado. Duk yadda nake son Sahal amma na kasa jin doki da farincikin auren. Da zarar na ga giftawar Yaya Faruk da yadda ya zama sukuku sai na ji komai ya fita a kaina. Mahaifiyata kuwa takanas ta samo mini maganin sanyi daga Kano. Itama hanyarsa aka yi mata domin daga Chad ake kawo saiwowin. Kwanaki biyu kacal da fara shan maganin na fara jin marata sakayau. A farko ban mayar da hankalina wajen shan ba, amma jin na samu sauyi a jikina nan da nan ya sanya na mayar da hankali nake sha, mussaman yadda nake jin matsalolin da sanyi ke jefa mace a ciki. Hadakar bandakin makaranta kadai ya isa ya sanya infection yi mana katutu. Haka wani hakkin daka mai kyau kullum sai ta tsare ni na sha a cikin yogurt ko Madara. Tun a lokacin na gasgata kayan Bojuwa Herbs masu asalin kyau ne ga rahusa. 08032773332 tuntubi wannan layin don samun naki kayan gyaran na mutanen Chad. Saiwowin dahuwar kaza ta siya ta hada ta dafa mana tare da ita. Na dinga tunanin wai har yanzu mami suna yin harkar nan ne? Abida da Basma Maska ne kadai suka yi mini kawance, duk da Basma a kano take karatunta na jamia hakan bai sa kawancenmu ya yi rauni ba. Tare da mahaifiyarta da kanwarta suka zo. Da yamma suka koma, suka barta sai washagari zata tafi. Ranar 15/7 aka daura aurena da Sahal Sulaiman Mashi a babban masallacin juma'a na Funtua. Yaya Asad da dukkan iyalinsa sun zo daga Enugu. Anty Rukayya kuwa matarsa Dispenser, oven da microwave ta kawo ban da kayan souvenirs masu uban yawa dan kuwa har da farantan tangaran da kofina mai dauke da sunana da na ango. Courtesy Mr& Mrs Asad Funtua family. Sosai bikinmu ya yi armashi. Matar Yaya Faruk kuwa tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha dan tsananin murnar da take ciki. Lafiya lau aka yi hidimar bikina cikin walwala da nutsuwa. Ban sake gane Abida tana sona tamkar yadda nake sonta ba sai ranar da za'a kai ni dakin aurena. Tun safiyar ranar take kuka, sai da tayarwa da dukkan wanda suke gidan hankali domin gaskiyar magana ba wanda ake so a gidanmu irin Abida. Duk yadda take a baude da kuma tsautsaren ra'ayi tana da wani iri jini mai tasiri. Kowa sonta yake yi tare da kaffa kaffa da ita, ba iyayenmu ba, ba kuma a tsakaninmu ba. Da akace na fito za'a tafi ta rike ni gam nima kuma na riketa na ki tashi. Yaya Faruk da ya ga zamu batawa su baba babba lokaci tunda zuwa zasu yi su juyo sai ya shigo dakin namu. Ya saka hannu ya janye ta ya sakata a jikinsa yana fadin "Ai ba rabuwa kuka yi ba autar momi. Ina ce nan da sati hudu ma hutun zai kare ki koma Zaria ku hadu ku cigaba da rayuwa tare?" Bata ce masa komai ba. Ta cire zoben hannunta wanda na gold ne ta kamo yatsana na hannun dama ta sanya mini. Ta ce forget me not Bilkina. Sannan duk ranar da na haihu to kawai ki kaddara kin sake haihuwa dan na san kafin nan, kin haifo mini nawa, hakurin da kika yi da ni a tsawon rayuwarmu ba zai tafi a banza ba, zan miki alherin da zaki tabbata kina sona. Fatan alheri mai yawa! Sai kuma kuka ya sake kwace mata. Ina kuka sosai Yaya Faruk ya fita da ni. Domin bayan ii rabuwata da gida ba karamin raunana zuciyata ta yi da soyayyata da na gani a tare da Abida ba. A motar baba babba C.R.V. muka tafi. Yaya Faruk ne mai tuki sai Baba babba da baba karami. Duk yadda su baba suka so Yaya Asad ya shigo a tafi da shi tunda ya riga ya dauki girma yana hurar da su dawainiya ya sanya suma suke jagorantar da shi akan sha'aninmu. Kansa a kasa ya ce "Allah ya kaiku lafiya Baba. Ga Faruku nan duk daya ne. Ya leko ya ce "Ki zama mai hakuri, ki sake ninka hakurinki. All the best maigado! Daga haka ya matsa gefe. Cikin nutsuwa Yaya Faruk ya ja motar muka tafi. Gidan Baba. Zaria aka kai ni. Baba babba ya rike hannuna ya damkawa wan mahaifin Sahal kuma waliyinsa amanata. Shi kuwa ya saka hannu ya rike hannuna gamgam. Yana fadin "na karbi amaana in sha Allah y'arku tana amintaccen hannu." Tarba ta karrmawa ya yi mana, iyalinsa kuma suka baibauemu da abinci da na sha, duk ni kaina kasa yake kuma a kunshe cikin mayafi . Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a gidan Baban Zaria. Zuciyata sai tsallen bad'ake take yi, yanzu shike nan na bar gidanmu gabadaya sai dai na je da bakunta? Iyayena da kansu suka dauko ni suka kawo ni wani gidan da nufin na zama cikin ahalinsu muddin rai. A raina na dinga jin lallai al'amarin aure ba karami bane a addini da rayuwa ba. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* *Lafazi writer's* 13 Message Amreesh spices & more on WhatsApp. https://wa.me/message/Y7KSRJ7PDQSCC1 *Fatan alheri ga* *Haj Dr Safiya Saulawa* *Haj Zahra Shehu*. Sai da aka yi sallar isha sannan Baban zaria da matarsa da ake kira da Mama suka kai ni gidana da babu nisa tsakaninmu da su. Unguwar kusa ne kwarai da jamiaar. A gidan muka tarar da shi tare da amininsa Lawal. Addua sosai Baba ya yi mana tare da jaddawa Sahal girman hakkina da yake kansa. Haka nima ya ta nanata mini na kulla abota da hakuri da kuma juriya, sanna na gane biyayyar da aka kallafa mini na yi masa umarnine daga Ubangiji. Dan haka duk abin da zan yi masa na hidima na yi min Allah dan kuwa shi ya shirya tsarin aure da kansa. Mama ta shigar da ni cikin dakina ta zaunar da ni akan gadona tana ta yi mini fatan Ubangiji yasa na zama tsohuwar gidan. Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a sabon gidana da zan fara sabuwar rayuwa a cikinsa. Jin ana kiran sallar magahariba ya sanya suka tafi, su Sahal suka rakasu wajen mota suna ta godiya da ban gajiya gasu Baba, sai da motarsu ta bace musu. Basu shigo ciki ba suka wuce masallaci dan sauke farali. Bayan an idar suka shigo da ledoji da alamu sun siya tun dazu a mota suka barsu. A guggurje ya yi barkwancinsa tare da ajiye mini bandir din yan 200 wai kudin siyen baki. Ya yi mini sallama ya wuce, dan hanyar Katsina zai kama a daren nan. Da kazangi ya dawo ya zauna daf da ni ya rungume ni yana shakar kamshina. Gabadaya na takura, bansan meyasa ban ji tsumin da na ji a lokacin da Yaya Faruk ya rungume ni ba a yanzu. Tabbas jikina ya shiga bakon yanayi da bai saba ba, ban sani ba ko tsananin alhinin rabuwa da ahalina tare da fargabar yadda zan shiga cikin sabon ahali ne oho. Cikin nutsuwa ya ware mayafin da na lulluba da shi. Ya mikar da ni ya ce "Zo mu je falo mu ci abinci. " Tsire ne mai kyau sai yogurt da kuma ruwan roba masu sanyi. Duk yadda nake jin yunwa ban iya cin naman ba, sai yogurt din na sha, shima ba wani mai yawa ba. Bai wani sake ba, sai da ya dawo daga sallar isha. Ya sake janmu sallar nafila ya yi mana adduar zaman lafiya da albarkar rayuwaa. Da rawar Jiki ya mannu da ni ya ce "Yau ranace ta mussaman a tarihin rayuwarmu gabadaya. Ina fatan Ubangiji ya sanya albarka a dukkan zaman da zamu yi." Murya babu amo na ce ",ameen". Duk yadda nake jin bakunta ta kewaye ni sai da ya hilace ni ya dangana ni da lafiyayyen gadonmu da ya sha shimfida ta alfarma. Cikin gaggawa yake yin komai, gabadaya ya dinga sarrafa ni, ya jima yana shafata tare da kissing dina. Bai samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar ya isa inda ya dade yana fatan ya isa. Bai wani jima ainun ba. Yayin da ni ban wani gane komai ba sai radadi. Na kalle shi yana ta numfarfashi, daga haka barci ya yi awon gaba da shi. Na jima ina ta sake saken zuci ban kuma isa na hakaito mai nake sake sake a akansa ba. Na duba wayata na ga shadayan dare. Na mike na shiga bayi dan yin wanka. Domin Mami ta ce mini kada na bari na dinga barci da janaba in ba dole ko lalura ba. Na gasa kaina sannan na yi wanka. Har na kammala na shirya bai motsa ba. Na lallaba na kwanta a gefensa. A haka nima barci ya yi awon gaba da ni. Bamu makara sallar asuba ba, sai dai da muka koma din sai wajen goma muka farka a dalilin dukkanmu mun tara gajiya, na fito daga wanka ina shiryawa cikin nutsuwa, shi kuma yana daga kwance yana kallona cikin murmushi. Daidai lokacin kuma ya fita ya karbo abin karin kumallo da aka aiko mana daga gidansu. Funkaso ne da kunun gyada. An zuba cikin kyawawan kwanuka. Kaitsaye dakin ya shigo da kwandon. Ya zuba mini ido ina sanye cikin guda daga cikin kyawawan material din Malaysia, mai kalar siminti da yarfin kwanduwar kwai. *Contact umm Nihla for all your *Malaysian fabrics. *Malaysian Batik and more* *All are unique and classy* *Available wholesale and retail* ....... Ya ce "Billy kin kara kyau sosai Na murmusa cikin kunya na ce "Na gode ". Ya wuce bayi yana ce wa "bari nima na yi wanka kada tazarar da kika yi mini a kyau ya sake tsananta." Na murmusa ba tare da na ce kanzil ba. Bai wani jima ba,¹0 pop-up ya fito daure da tawul na yi maza na dauke kaina. Bai ce komai ba ya fice zuwa daya dakin da yake a matsayin nasa. Na hanzarta canja zanin gadon da duk ya baci da jinin budurci na canja wani. Na shiga bandaki na kama duk inda ya baci na wanke, na yarfe sannan na ninke na baza shi akan kyauren bandakin. Ya shigo sanye cikin yadi mai taushi shudi kalar sararin Subhana(sky blue). Sosai ya yi kyau zuciyata ta doka da tsananin gaske, take raunin da soyayyarsa ta yi a dalilin Yaya Faruk ya kau, mai kyaune irin wanda nake so duk da dai siriri ne irin sosai din nan, na tabbatar sirintarsa tana karawa tsayinsa kaimi. Sabuwar soyayyarsa ta sake yun mmkuro mini tana sake bin dukkan sassan jikina tana mamaya da k'arfin gaske. Idona ya kada kwallar shauki ta cikasu taf. Da hanzari ya iso inda nake. Ya ce "sannu da aikin lada Bily. Allah ya yi miki albarka! Mu je mu karya yunwa nake ji sosai." Gabadayanmu kamshi muke yi. A plate daya ya zuba mana abincin. Ya turo mini kofin shayi gabana tare da ce wa "zuba sugar da su madara yadda zasu yi miki". Ban ce komai ba, domin kaina a kasa yake, kunya da bakunta ke dawainiya da ni gabadaya. Cikin nutsuwa da walwala muka karya duk da ni kunya ta yi mini dabaibayi. Bai fita ba sai da aka yi sallar azahar. Ya yi tafi masallaci ya ce zai shige gida ya gaidasu Baba. Na idar da tawa sallar. Na dauko wayata da take kashe tun daren jiya. Na kunna, na jinkirta ta daidiata. Mami na fara kira, ta amsa da walwalar da take alamta mini ta yi kewata sosai. Har na ji dadin yadda ta mu'amalance ni. Ta dinga fadin nasan kina da hakuri da shanye damuwa, ki yi kokarin ninka hakurinki Bilki, hakurin nan dai shine aure, shine ma rayuwa gabadaya. Murya babu amo na ce "To Mami na gode Allah ya kara miki lafiya da hakuri. Ta amsa da fadin "ameen, amma ai ni bana hakurin da zan cutu, a sha'anin aure ne kawai nake dukkan hakuri domin zawarci bashi da dadi Bilkisu! Ko a gaban uwarka da ubanka zaka yi shi kuwa bare ni marainiya ce, tun ba'a aurar da ni ba na rasa uwarta, mahaifina kuwa ban yi haihuwar fari ba na rasa shi. Ga shi ni din an jarrabe da wata irin nannauyar jarabawa.mai matukar nauyi. Y'anuwana suna cikin magautana." Na nisa na ce "Mami sunnar rayuwace ai, ba ke kadai bace kike da k'alubale da y'anuwanki ba, mutane da yawa ne, kawai ke dan kina yawan furzarwar ne, ba kya iya barin al'amarinsu a ranki ko dan a samu saukin gaba da b'acin rai. Manyan bayin Allah sun fuskanci kiyayya a wajen danginsu, haka Annabawan Allah. Idan kuma Allah ya rufa maka asiri Mami ba wani mahalukin da zai tona maka. Sai dai ya tonawa kansa. Na numfasa na ce "Allah ya jiqan magabatanki, Allah ya saukaka miki dukkan kasafinki Mami ". Ta amsa da"ameen ameen a sanyaye." Karon farko da na yi mata jirwayen hakuri akan shaaninta da danginta bai zame mini sanadin bacin rai ba. Na kashe wayar na kira su baba daya bayan daya. Su kam dukkansu albarka da addua suke yi mini. Suna sake jaddada mini basa jin dar a kaina ba zan kunyatasu ba. Abida na kira daga karshe, muka sha hira, tana ta tsokana tana cewa "Na ajiye mata kazar amarci a fridge tunda satin sama zata dawo makaranta. Cikin nutsuwa da tattali muke rayuwarmu. Babu damuwar komai, sai dai ni duk yadda Ake fadin ango na gajiyar da amarya ta hanyar kusantarta a kai kai da sunan doki ban ga hakan ba. Don kuwa ina amarya ma ba wani sosai ba, sai mu debi kwanaki bai yi ba, illah iyaka idan zamu kwanta zai rungume ni mu yi barcinmu. Hakanan da rana yana dan rungamata da sumba idan zai fita ko idan ya dawo shima ba wai dole ba. Tuni muka koma makaranta. Abida ga dawo tana hostel, duk yadda na so ta dawo mu zauna a gidana ki ta yi tare da gabatar mini da hujjar ba zata taba munafuntar iyayenmu ba . Don kuwa ba zasu yadda ta dawo ta tare mini a gida ba. Dan haka ba zata yi kuma a boye ba. Ko weekend Ina son ta dinga yi mini amma yar ra'ayin rukau din bata gamsu ba. Asalima sau biyu tak ta zo mini gidan. Duk da na shafe watanni da auren. Zuwa lokacin kuma na riga na gane Sahal na cikin jerin maza da basu damu da harkar auratayya sosai ba. Sai dai kuma yana kokarin ya ga ya gamsar da ni idan har an hadun. Watanni biyar da aure ya samu aiki da Nigerian airways na lokacin. Sun dauke shi cikin jerin lauyoyin da zasu yiwa kanfanin aiki. Dan haka ya wadata ni da komai na more rayuwa tun daga kan abinci har tufafi duk da yana ganin na lefe da yawa ban waiwaiyesu ba. Duk satin duniya zai bar Kano ya taho Zaria. Ranar jumaa da yamma zai zo sai ya yi sammako ya tafi litinin da asuba. Duk wannan jelen da yake yi, sau daya tak zai neme ni, ma'ana idan ya zo jumaar nan aka hadu to fa sai wata jumaar. A kasan raina ina son ace had'uwar tafi hakan yawa ko da sau biyu ne sai dai kunya da nauyi sun hana ni magantuwa ko nuna wata alamar ina bukatarsa sama da yadda yake. Mamakin da nake yi, idan har yana gida to kuwaa kusa da ni daf yake zama koma nace a jikin juna, haka idan ina kicin ina aiki to yana gefe yana taya ni tare kuma da kai hannunsa duk inda yake son tabawa baya damuwa ko ya zama sanadin da zai ja ni dakin, yayin da ni kuma nake tsintar kaina na jike jagab. Sadda muka kammala aji biyu zamu shiga na uku muka koma Kano da zama, baban Zaria ya yi cukun cukun da na koma jamiar Bayero na shiga aji ukun na cigaba da karatuna a can. Na yi kewar Abida sosai. Duk ba wani zuwa gidana take yi ba. Amma kullum sai na yi mana girki na tafi mana da shi makaranta. Ban wani sha wahala a B.U.K ba saboda Basma Maska anan take, k'awancenmu ya sake zama sabo mai cike da aminci da nutsuwa. A lokacin kuma ina a dauke da ciki na watanni biyar. Ban nemi komai na rasa ba, komai daidai gwargwadon iyawarsa yana yi mini. Haka na yi goyon ciki, cikin kulawa da tarairaiya don kuwa duk abin da nuna sha'awarsa ya dinga siyowa har sai ya gundure ni. Cikin marka markan ruwa irin na watan Augusta na haifo kyakkyawar yarinya mai kama da Babanta sak. Murna kamar me domin ina son abu maikyau a rayuwata. Daga shi har danginsa sun nuna mana gata da kulawa domin kaya har rasa inda zan ajiye su na yi. Haka nawa dangin suka dinga zarya tsakanin Funtua zuwa Kano. An kawo mini yayar Mami da suke 'yay'an mata zar wacce jininsu ya jitu. Zata zauna da ni idan an yi suna sai mu koma Funtua tare tunda na yi sa'a cikin hutu haihuwar ta zo. Ya dade da fada mini idan mace na haifa to sunan maman Zaria(Hajiya Rabi) zai saka domin kuwa ta yi masa alakairai daban daban da ba kowacce mace zata yiwa d'an k'anin mijinta haka ba. Dan haka tuni an yiwa yarinya huduba da Rabi'a Na lank'aya mata Amrah wanda Abida ce ta zabo inkiyar. Ranar da ta zo ganin baby ta kula da yadda nake yawan kallon jinjirar ga shi ko ya ya ta yi kuka zan mika hannu na karbe ta. Tana ganin inna ta shiga bayi ta ce "Wato Maigado kina da zurfafa soyayya. Soyayyar Babanta ce ta shafe ta kike kasa kawaici, ko kuwa kina cikin iyaye masu tsananta soyayyar 'ya'yansu ta yadda basa iya boyewa a gaban kowa?" Na yi k'asa da kaina domin kuwa na sani Abida ta na fahimtata tamkar yadda ta fahimci kanta. Ta numfasa ta ce "ki sassauta, ki danne, na sani dole ki so ta, amma dinga yin kawaici a gaban manya, sannan fa ki sani wannan ba taki ba ce tawa ce, domin dai ni ce zan haifo miki ta ki" Na murmusa na ce "Abida to yaushe za ki mayar da ni uwa tunda har yanzu k'in ki kula kowa bare ki yi aure na saka ran zaki haifo mini tawa". Ta murmusa ta ce "lokaci ne ai Bilkisu! Idan Allah ya kawo lokacin sai ki ga an yi ko da ban so ba". Na tabe baki tabbacin ban gamsu ba. Dan dai ban isa yin musu da ta mai yawa bane yanzun nan zata murde mini. Tunda na yi aure bata yarda ta kwana a gidana ba sai sanadin haihuwar. Daga Zaria ta taho kai tsaye har aka yi suna tana nan. Bayan suna da kwanaki uku ya kaimu Funtua da kansa tare da uban kayayyakinmu. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 14 Duk yadda Abida bata son yara, haka duk yadda bata bada fuskar da iyayen yara zasu hada ta da hidimarsu bare ta yi musu raino. Amma ta zage da dukkan k'arfinta tana rainon Amrah. Bata son goyo a rayuwarta. Amma kullum Amrah a bayanta take yini bata ko gajiya, kowa tu'ajjibi yake yi, ita kuwa fadi take yi, tunda ita aka haifawa dole ta yi rainonta dan ta ji kanta idan ta tsufa, ko kuma ta yi mata addu'a idan mutuwa ta sure ta. Ranar da ta fada hakan jikin kowa ya yi sanyi, aka dinga fadin haba autar momi ai ba zaki mutu ba, sai kin haifawa Bilkisu tata diyar da kika bata tun shekarun baya. Ta murmusa ba ta ce komai ba. Na yi matukar jin dadin zaman jego a gidanmu domin bana aikin komai tsananin na yi wanka na bawa baby nono sai ko barci. Komai yi mini Ake yi tun daga kan iyayenmu har kan yayyen da kaina. Amrah ta sha gata sosai. Yaya Faruk kullum ya shigo sai ya saka Abida ta kunto masa ita ba zai bata ba, sai zai tafi ,kaya sosai ya kawo mana ni da ita. Matarsa da k'arfin guiwarta ta zo ganinmu har da turmin zanin goyo. Haka iyalin Yaya Asad duk da basu zo ba amma kayan azriki mai yawa ya iso mana daga garesu. An hakura an bar komai kamar yadda kaddara ta zabawa kowa rayuwarsa. Zarya ta sami Sahal domin duk sati sai ya zo ganinmu. Yaya Hamida babban galon din sanyi ta yi mini order tare da sauran kayan gyara na maijego ko ma na ce maijego package din gabadaya ta yi mini daga Bojuwa Herbals(08032773332) Kazar sababi ce sai na koma Kano zasu aiko mini. Ni da kaina nasan na hade na matse tamkar ban haihu ba. Satinmu hudu muka tattara muka koma Kano, saboda hutun makaranta ya kare, ba dan haka ba sai na yi watanni biyu, tunda shi uban gayyar ba mai tsananine sosai ba. A gugguje nake hakaito muku rayuwarmu ta baya iya wanda zan tuna da wanda yake da mahimmaci shi kawaii zan hakaito dan ku fahimci halin da na shiga ku yi mini alkalanci na gaskiya, dan haka ba zan hakaito wuraren da Basu da muhimmanci ko darasi ba. Ranar da muka koma ya tisa ni da rawar jiki, ya dinga bare bare har sai da muka kebe sannan na samu saukin bibiyar da yake yi mini. Na zuba masa ido yana gefe yana barcin da ya zame masa ka'ida, matukar ya samu nutsuwa da ni to kuwa idan ya fara barci sai asuba sannan zai tashi ya yi wanka ya tafi masallaci. Nazarinsa nake yi, na gamsu dari bisa dari baya mu'amala da matan banza. Domin shi gabadaya harkar bata zame masa irin do or die din nan ba. Yana iya sati ko sama da hakan bai yi ba, sai dai idan ya so kuma ba zai taba samun sukuni ba idan ba yi din ya yi ba. Tsura masa idon da na yi kawai tunani nake yi, yadda bai taba hakaito cewar nima zan iya bukatarsa a wasu lokutan da shi na shi da bukatar. A wanccan lokacin da nake cikin shekarun kuruciya ba zan taba iya kada billena na nemi shi ko nuna masa ina da bukata ba, mussaman bisa al'ada an tafiyar da mu mijine yake da hakki akan wannan al'amarin. Kullum karatun da ake yi mana bita shine duk sadda miji ya bukace ki, to ki bar komai ki amshe shi if not ki fada cikin Allah da ma'aiki sannan ki kwana cikin tsinuwar mala'iku. A fili na ce "To wai ita mace laifine idan ta bukaci mijinta ko kuma shi miji ba shi da wani laifi idan har sai yana da bukata za'a hadu, ko da ita mace tana da bukata? Idona ya ciko da kwalla domin a kasar Hausa ba karamin abin kunya ba ne ka fito da maganar da shafi wannan lamarin bare har ka yi korafi. Yanzun nan za'a yi maka mummunan zaton ka saba ma'amala da wasu mazan ne shiyasa ka raina kokarin mijinka daga yin aure shekara daya tak. Na tuna sadda nake da watanni biyar da aure da na yiwa yaya Hamida korafi akan shaanin ban fahimce shi ba, ba karamin kunyata na yi ba. A hakan na ba haka siddan na yi mata korafi ba. Maganin sanyi da na mata take ta aiko mini, na gamsu da kyaun kayan Bojuwa Herbals tunda tabbas daga Chad suke kawo wasu saiwowin. Mussaman na sanyi da na dahuwar kazar sababi. Akai Akai Yaya hamida take yin order duk sadda zata siya Kuma tare take siya mana, sai a kawo mini gidana ni sai na tura mata nata Kaduna tunda a can take aure. A duk sadda na ci kazar sababi din nan yini nake yi cikin wani hali, idan kuma shi bashi da bukata sai dai na gama tsiyayata ni kadai. Sa'a daya ma sanyi flusher da yake da tasiri nan da nan mai ciki bata sha. 08032773332 order ur sanyi flusher and kazar sababi now. Dana gaji ranar da ta ce za'a kawo mini na ce mata "Yaya Hamida ni kam Kar a kawo mini, domin gaskiya ni ban wani gane kan abin ba, sannan ba kullum ne ake yi ba." Salati ta dinga yi tana fadin "Bilkisu ashe baki da hakuri? Har yaushe aka yi auren da za'a ji wannan maganar a bakinki? To gyara ba dan mijinki ya gamsu zaki yi ba? Duk macen da zai taba nan gaba sai ya gane ke ta dabance. Ni din nan sai da na yi haihuwa uku sannan na gane kan lamarin ban kuma fasa gyara kaina ba.! Na yi sakato ina sauraren yadda take kunfar baki. Kunya ta kama ni. Haka na ajiye wayar ban iya cewa komai ba. Hakan da ta yi mini ya sake sakawa na kame bakina ban sake bude maganar ba. Kan dole na tashi na yo wanka, na gyarawa Amrah kwanciya sannan na kwanta don nasan ba zata farka ba sai asuba. Tare da shi muke rainonta, Indai yana gida yana bata lokaci wajen rike mini ita. Haka nan siye siye kayan ci da na wasa tun ba'a zo lokacin bukatarsu ba ya yara mata su masu yawa. Haka nima suturar da yake yi mini tamkar an yi masa gorin yana yi mini kwangensu, komai fa ban nema na rasa ba. Shi dai inda mace tafi bukatane hankalinsa baya kai ainun. Don kuwa tunda na haihu sai ya zama dalilin da rungume ni da yake yi idan zamu yi barci ya daina. A bisa hujjar ba za'a bar yarinya a gefe ita kadai ba. Yarinyar ta shiga ransa ainun ga shi tana girma kammaninsa na sake bayyana a tare da ita. Bayan haka kullum cikin tsabta yake ganinta da kwalliya, ko da fara tumbidi bana gajiya da gyarata don gudun kada a ji karnin nono tare da ita. Sosai muke zaune lafiya bani da matsalar danginsa ko rashin wani abu. Idan ya kaini makaranta ko idan ya samu sararin dauko ni da yawa mata kallon so da birgewa suke binsa da shi. Domin kwarai da gaske mai kyau ne, duk da siririne sosai. A hakan har Amrah ta shekara tana kuma tafiya. Bani da kawa sai Basma kusan a Kano ma bansan kowa ba sai ita. Shiyasa muka kulle muke aminci tamkar jinine ya hadamu. Mun kammala karatunmu na fara bautar kasa a cikin Kano bayan an yi cuku cuku an maido ni domin da jihar Bayelsa aka tura ni. Amma ban je can ba a dalilin an mini marriage certificate. Da taimakon baban Zaria aka bar ni a Kano. Basma ce aka tura ta jihar jigawa. Satinmu biyu da fitowa daga camp aka bikinta, sosai muka yi hidima ni da Abida, min halarci bikin har Katsina inda aka kaita muka je kai Amarya. Lafiya lau muke rayuwa har zuwa lokacin da muka shafe shekarun biyu har da watanni ba zance ga babbar matsala a aurena ba. Na farko Sahal ba shi da takura, ma'ana baya mini kullen nan, shi dai kafin na fita ma sanar masa, ko daga makaranta ne na so wucewa wani wuri ba shi da matsala da hakan matukar zan kira shi na Sanar masa. Haka nan akai akai zai kwashemu mu je restaurant mu yi dinner mu dan zaga malls ya mana siyayya. Bana rasa kudi a hannuna don baya mini shamaki da kudinsa. Kawai inda matsalar take sha'awarsa akan mace ne ta yi mini kadan. Dan muna nisa abin na sake yawa, a farkon zamanmu baya wuce sati bai nemi ni ba, amma a yanzu sai mu kwashe kwanaki goma har a d'ora. Idan aka dauke wannan matsalar bansan matsala a aurena ba. Wasu dararen haka zan yi ta hawaye marar sauti, har barci ya sure ni. Ba Wanda nake son na tattauna wannan matsalar sai Abida aman babu dama dan kuwa ta rufe dukkan amincin da zai sa na kai mata korafin aurena. A lokacin kuma tuni Yaya Munira ta yi aure amma ba'a kasar take ba, tana Paris, tana ta zurfafa iliminta na lauyanci. Yayin da Abida na daf da kammala karatun likitanci. Har kuma lokacin bata bada kofar da zata yi saurayi bare a yi mata maganar aure. Kwanci tashi asarar mai rai Amrah ta yi watanni goma sha bakwai a lokacin kuma mamanta Abida ta zo daga Zaria ta dauketa suka tafi Funtua zata yayata. Tun watanni biyu na so yayeta domin komai ci take yi sannan kuma ta jima tana yawo ma'ana ta jima da yin kafafuwa, ga ta doguwa tamkar Babanta. Abida ce ta ki amincewa bisa hujjar Indai itace uwarta, itace zata yaye ta to sai ta samu dogon hutu. Sosai Amrah ta saba da ita. Dan haka bata yi mata kuka ko rikicin yaye ba. Sannu a hankali rayuwa take tafiya. Ban jima da gama makaranta ba na fara sana'ar kayan fulawa(snacks) tare da abincin yara. Kamar na fada muku na karanci nutrition and dietetics. Muna yawan zuwa kauyuka da asibitoci muna wayarwa jama'a hankali akan abin da ya kamata su dinga bawa yaransu da su kansu saboda lalurar tamowa tana yawaita a kan yaran karkara. Bincike kuma ya nuna na rashin isesshen (). Dan haka sai nake yawan rubuce rubuce cikin harshen Hausa da na Ingilishi a kasar sadarwa ya Facebook a lokacin ita kadaice kafar sadarwa da zaka dinga yada manufofinka. Dan haka na tara mabiya sosai, cikin hikima sai nake tallata hajata na bakery da nake yi. Cikin kankani lokaci na samu karbuwa domin a Kano kusan duk manyan bukukuwan da za'a yi ni nake aikin kayan snack da drinks da za'a sha a bukukuwan. Sosai Ubangiji ya sanya mini albarka. A hakan Kuma Sahal bai taba kin yi mini hidima dan yana ganin ina samun kudi ba. A shekarar da Abida ta kammala karatunta ta zama likita ta fito a matsayin physician. Na haifi namiji. Domin walimar da su baba suka shirya mata na je da tsohon ciki, na dawo Kano da kwanaki uku na haifo yaro lafiyayye fari tas. Sai dai wannan kama yake yi da ahalina, ma'ana dangina ya kwaso. Cikin kyautatawa Baban Amrah ya bani dama na zabi sunan da za'a sakawa yaro. Kaitsaye na ce masa "Yaya Faruk nake so na yiwa takwara". Ba ja in ja, take ya yiwa yaro huduba da sunan Umar Faruk. Tare da fatan ya samu albarkar da yake cikin sunan, ya kuma gaji kirki da fara faran din mai sunan nasa. Na fahimci har zuciyar Sahal na ganin k'imar Yaya Faruk yayin da ko ambaton Yaya Asad ba ya son a yi a gabansa balle a je ga jallin yin hirarsa. Cikin nutsuwa nake jegon yaya Faruk domin har mun lankaya masa inkiyar, amma da Yaya Faruk ya zo ganinsa ya bada umarnin a kira shi da Faruk dinsa indai shi aka yiwa mai suna to a kira shi da sunansa kamar yadda shari'a tafi so. Shike nan ake ce masa Faruk yayin da ni sai na hada da Yaya Faruk ko ma na ce yayana kawai. Wannan karon umma da zo mini zaman jego sati uku kawai ta yi mini ta tafi nisa hujjar mijinta ba ya jin dadi, abokiyar zamanta. Dan haka saddiqa autar Mami da a lokacin tana aji hudu na sakandire sai aka turo mini ita tunda basu jima da yin hutu ba. Amrah kuwa dama tana Funtua wajen Mamanta duk da Abidan Mami ta barwa ita domin tana yin Housemanship a generall hospital Katsina. Ban jima da yin arbain ba aka yi auren Anisa kanwata da take bin Ansar. Hatta baba babba bai so aka yi auren Anisa ita kadai ba, ya so ne a hadasu da Abida amma ta kafe akan ita bata sami miji ba. Dan dan haka ayi auren Anisa tunda ita ta samu miji. Akan dole aka yi bikin Anisa Wanda a lokacin tana shekarar karshe a nursing school ta Kaduna. An rasa gane inda Abida ta saka gaba akan aure. Gabadaya ta ki daukarsa da muhimmanci, ta ki bawa kowa fuskar da zai tunkare ta. Wani malaminsu a nan jamiar Ahamadu Bello ba irin nacin da bai yi mata ba. Sadda zata zo Kano da na haifi Yaya, zata kwana daya, sai ta dauki Amrah su wuce Funtua, yana jin ta zo Kano ya biyo ta daga Zarian, falonmu aka sauke shi. Aka kai masa samosa da meat pie tare da lemo da ruwa. Bai wani jima ba ya tafi. Na kuma tabbatar sallamarsa ta yi, ta hanyar gabatar masa da tana da uzzirin da zata yi a lokacin. Cikin kwantar da murya na ce "Autar momi wannan kam ya yi ba shi da kyau sosai, sannan cikakken jikine da shi, ga shi d'an boko ne irinki." Fuska ba walwala ta ce ",Ko kusa da yi bai yi ba, Bilkisu. Kinsan har yanzu bai tunkare ni kaitsaye ba sai dai hannunka mai sanda tare da gifts din da bazasu rude ni ba. Mafi muni ma rainon yaransu zan yi masa. Matarsa ce ta rasu 7months ago. Ta bar masa yara biyu duk maza. Shine yake neman wacce zai aura ya mai mata lalurar yaransa idan kuma ka ce ba zaka yi ba society ma ba zai maka adalci ba, idan kuma ka karba yaran kana musu hidima su yi ta azabtar da kai, kuma ubansu ma ba yaba maka zai yi ba.! Ta muskuta ta ce "Kin ga na yi kama da wacce za'a aura dan ta yi rainon yara? Ko kin ga na matsu da yin auren ne bare har a yi madadi da ni?" Da azama na ce "Ina kuwa maman Amrah! Saboda yadda ta daure fuska ainun nasan idan na kawo mata misalin da yake nufin ba lallai al'amarin ya zo a yadda ta fahimce shi ba, ta janye sassaucin da ta yi mini har take yi mini bayanin da zan gamsu da ra'ayinta cikin lumana. Kuma Gaskiyar magana shakkarta nake yi har yanzu da muka girma. Abida no nonsense ce sannan bata taba karban abin da bai yi mata ba, kunya ko kawaici basa tasiri a inda zata cutu. Ta sake ce wa",An dame ni da ina korar samari. Na auren ne bai zo ba, ai ni bana son wannan wahallaliyar soyayyar Maigado. Sannan duk da namijin da ba zai iya tunkarata kaitsaye da nufin yana sona ba, to kuwa ba zan taba sauraronsa ba domin ba shi da confidence ni kuwa jarumi nake so na gaske." Na numfasa na ce "Allah ka turo jarumin nan da wuri." Bata motsa ba, bare kuma ta amsa. Na tsura mata ido na ce ,"Amma kinsan dai na matsu ki haifo mini tawa yar ko Abida?" Ta murmusa ta ce "Aure ai ba shine tabbacin idan an yi za'a haihu nan da nan ba. Ke dai ki yi fatan Ubangiji ya kawo masu albarka, ba ga Yaya Faruk nan a hannunki ba, ai shi naki ne". Na rike hannunta murya na rawa na ce "A a ba haka muka yi ba autar momi. Kada ki canja magana". Ta yi murmushin da take yi idan zata yi maganar da take nufi har zuciyarta. Ta ce "Bana magana biyu kin sa ni. Sai dai dole ki jira lokaci. Aure, haihuwa da mutuwa duk saurin mai sauri sai ya jira lokacinsu, idan kuma lokacin ya yi zasu zo ne tamkar habo ko da baka shirya ba. Kika sa ni ma ko ni ba ni da rabon auren a nan duniyar! ✍️ [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://chat.whatsapp.com/KK6YX9u8tej7fpnQUEtvGS?mode=ac_t *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 15 *Contact me 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. *Littafi na d'aya ya kammala* *Masu son cigaban labarin ku biya kudin karatu a kai ku paida group zamu fara kashi na biyu gobe litinin idan Ubangiji ya so*. *Idan mun fara kuma babu fashi daga ranakun litinin Har juma'a za'a dinga samun update* *Babu posting a ranakun asabar da lahadi*. *Ina mik'a Godiya ga wadanda suka siya littafin nan mussaman wadanda suka fara biya tun kafin na fara sakin shafukan kyauta.* *Na gode sosai Allah ya bar kauna, ya saka muku da alheri*. *A madadin Ummiel foods* *Ina tallata muku kulikuli tamkar kilishi* *Ba ordinary kulikuli bane.* *Classic kulikuli da ba'a yaro mai k'iwa, ina wadanda aka Hana iyayensu cun nama kuna suke fama da kwadayin?* *Maza ku garzaya ku siya musu wannan kulikulin da Idan ana cinsa tamkar kilishi ne*. *An yi Shi cikin tsabta da ta samu nasarar tantanceqa data Nafdac*. *Ana siyan daya ana bada sari*. *Akwai a Abuja* *Akwai a Kano* *Akwia a Lagos* *Sannan nation wide delivery ne*. *Ana samunsa a wasu daga branches din Rufaida Drinks na cikin birnin Kano*. *Don saka order a tuntubi Ummiel foods a 08036355535*. "Gabadaya sai nake ganin tamkar kwanakina sun kusa karewa, kawai Baba babba nake ji, if not Indai zan gama lafiya, ai ba ni da wani zullumi domin mutuwa tilas ne komin dadewar da zaka yi a doron kasa kuwa". Hawaye ya kece mini, na kasa furta kalma ko guda Bata yi yunkurin hana ni ba, sai dana daina dan kaina sannan ta numfasa ta kaurara murya ta ce "this will be the last time da zan zo gidanki, ki tisa ni gaba kina mini kuka akan aure Maigado. Zan yi aure idan an kaddara mini, zan mutu idan wa'adina ya yi! Abubuwane da duka ba zan tsallake su ba. Abin da nake so ku fahimta daya ne. Na yarda sallah wajibi ce, haka nan na yarda azumin Ramadan wajibine, na kuma yarda zakka dole ce idan kana da arziki. Bayan wadannan na yi imani da manzanni, na yi imani da littafin da Ubangiji ya saukar, na kuma yi imani da mala'iku na kuma hakkkake Ubangiji daya ne shine kuma Ubangiji komai da kowa.! Ta yi shiru tana sake kafe ni da ido yayin da na kasa ce wa uffan. Ta zarce da ce wa "Amma kin sani, kamar yadda na sani aure ba dole bane, akwai ma wadanda auren yake zama haramun a kansu. Na san kaina, na tabbatar zan iya tsare kaina, dan haka ba zan je na yi gaggawar yin aure da wanda ban nutsu da shi ba. Dan kawai kawayena da kannena sun yi aure ba. Shekaruna ashirin da hudu kacal, a ajinmu nice mafi karancin shekaru, ni da kika ganni ma ina kammala Housemanship din nan ba wai aiki zan tsaya yi ba, zan koma ne na yi specialized a gynecologist. Ko shekaru talatin na haura ba zai zame mini abin aibu ko na kaico ba, matukar ina cikin kamewa. Idan Allah ya turo wanda ya cancanta sai a yi da shi. Amma ba zan yiwa kaina gaggawa ba. Ku dai da kuka yi auren, ina yi muku fatan alheri." Na rike hannunta murya babu amo na ce "Allah ya kawo wanda zaki nutsu da shi da gaggawa Abida". Ta murmusa ta ce "Ameen Maigado. Ke kam dama ai kina cikin sahun matan da suka tsananta a son aure. Ga shi kuma kin yi gam da katar kina zaune lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk yarintarsa da nake gani ashe dattijone a zuci". Na kyalkale da dariya domin kuwa yadda ta yi maganar tana kyaba baki tabbacin har lokacin kallon yaron da bai kai ya aure ni ba take yiwa Baban Amrah. Da dariyar na ce "Ina son na ce miki sau tari tunaninmu ba ya zama gaskiya. Sai ki ga wanda aka zatawa kyakkyawan zato ya kunyata mutane. Wanda aka munana masa zato ya bada mamaki ta hanyar sauke nauyi daidai da tsarin shari'a." Ta sake murmusawa wanda yake matukar kara mata kwarjini ta ce "Hakane Maigado. Allah ya taimakemu gabadaya." Daga haka ta bude jakar hannunta ta fito da glass ta sanya ta sake ciro littafin Tsuntsu duka tsuntsu ne ta hau karatu. Hakan kuma alamune ta gama maganar ta kuma sallame ni. Back to story Hawaye ya goce mini, domin a yau kewar Abida nake yi sosai ina jin tamkar na yi Tsuntsu na ganni a gabanta duk da ta shata mini layi akan ba zata ji damuwata akan lamarin Sahal ba. A yau kam ba wanda nake so na fadawa tozarta ni da ya yi a wajen yarinya kankanuwa irin Abida ko da kuwa zata gwasale ni, ko da ba zan ji kalma mai dadi ba. Kuka na sosai ya kwace mini, na rasa inda zan tsoma raina a fili nake fadin wayyo Mami, wayyo Abida wayyo Yaya Sulaiman wayyo Baba babba. Ni kam Bilki ina ganin jarabawar rayuwa Allah ka taimake ni ka sassauta mini, Ubangiji ka yafewa mahaifiyata." Ban san kuka nake yi mai sauti sosai ba, sai da Na ji hannun alti a jikina tare rufe mini baki. Da matukar damuwa ta ce "Mahmah sake dauraewa mana, na sani kina cikin yanayin da zaki yi kuka kwarai da gaske. Amma sake sanya jarumta a cikin kasafinki. Duk abin da kike tunanin kin rasa, indai ba imani da lafiya kika rasa to barka, da sannu komai zai dawo miki. Ubangiji baya kunyata mai jin kan bayinsa. Idan tunanin wargajewar gidanku ce ta taso miki, kalle ni mana Hajiya. Duk duniya ba ni da Wanda zan nuna na ce jinina ne ta fuskar nasaba. Kin sani, kin Kuma tabbatar ni yar tsintuwa ce ban san kowa nawa ba, amma a hakan nake rayuwa cikin k'arfin zuciya da karban kaddara. Idan kuma kuttun mijine ya mintsine ki, ki sake kallona mana, kin san dai a yanayin da na shiga ba aikin k'arfi da sana'ar da ban yi yana karbe kudin ba. Komai ni ce a auren nan. Haihuwa uku bai taba siya mini ko da tsumman goyo ba. Hakan bai ishe shi ba, ya saka kafa ya gudu ya bar ni da su. Tsananin babu ya sanya ciwon yunwa ya kashe su daya bayan daya. Hakan kuma bai saka na fadi na mutu ba tunda da sauran kwanana a gaba. Shin yanzu bai wuce mini ba?" Ta tambaya cikin karyewar murya tunda kuka take yi irin na sharbe. Na rike hannunta sosai murya na rawa na ce ",Ina son na ga Abida, ina son na ganni gaban Baba babba. Ina son na fadawa Yaya Faruk halin da nake ciki. Ina son na ga Yaya Hamida a gidan nan" Kuka ya sake kwace mini mai gunji sosai. Ta ce "ki yi waya da Faruku. Baba babba kuwa kina iya zuwa idan kin nutsu. Ganin Abida ne sai dai ki yi hakuri domin nasan irin ganin da kike son ki yi mata, domin har yanzu lokacin da zaki ganta, irin ganin da kike so bai yi ba tukun. Yaya Hamida kuwa duk tsawon lokaci zaki ganta a inda kike matukar Ubangiji ya sanya tasiri a cikin jini . Ki yi hakuri, sake hakuri, Allah yana tare da masu hakuri." Hawaye jage jage a idona na ce "Na gode sosai Alti. Ina matukar jin dadin zamanki tare da ni. Kina debe mini kewar Abida da Yaya Munira " Ta goge kwallar idonta ta ce "Ni ce da godiya, Ubangiji ya jibanci lamuranki." Murya babu amo na ce"Ameen ". Da ta ga na nutsu kadan sai ta yi amafani da fikon da ta yi mini ta ce "Tashi ki watsa ruwa, ki yi sallar azahar, kin ga har uku na shirin yi". Ban musa ba, ban kuma amsa ba, na mike na durfafi bayi dan yin abin da ta ce din. Wankan na yi, sannan na doro alwallah. Na idar da salla kenan ta shigo mini da plate dauke da faten dankalin turawa da ya ji alaiyahu da bushassen kifi. Na karba tare da godiya. Ta ce "Ki ci mahmah sai ki fito falo, zaman ke kadai na haddasa miki tunaninka masu kassara kwakwalwa." Na ce "To Alti, zan fito". Ta fita tana fadin "Bari na je na yi sallah, ke kam kin hada da laasar." Ta ja kofar ta rufe. Sannu a hankali nake cin abincin duk yadda bana jin dadin jikina da zuciyata haka na tura shi dan dai na sanarwa Alti nutsuwa. Domin idan ta ganni a irin wannan yanayin gabadaya rasa walwala take yi, ta damu da ni matuka gaya. Tana matukar kwantar mini da hankali, na aminta da ita irin sosai din nan. Na cinye na bude ruwan robar da ta ajiye mini na sha. Na yi gyara na furta "Alhamdulillah! A fili. Na yi shiru zuciyata sai sake sake take yi. Mafi girman abin da take sakawa kuwa shine me yasa Baban Amrah baya tausayina, baya nuna damuwa da lamarina tamkar yadda Alti take yi ne?" Kaina ya kulle na kasa hasaso dalilansa na yin hakan. Daidai da Amrah idan ta ganni cikin rashin sukuni ko firgici ta iya harhada kalmomin da zata yi mini magana da su dan na samu sassauci, amma shi kam sai ya yi tamkar bai game ba, ko kuma ta hau fadan na cika makala abu a raina tamkar dai ni kadai ce mai damuwa. Amma na fara gasgata Basma da ta ce na daina burge shi ne. Na sake tuna Abida da ta taba ce mini ya yi miki yaro Bilki! Lokaci zai zo da zai daina ganin komai a tare da ke domin a lokacin kin masa tsufa sa'annin yayan cikinku zai dinga hari. Ba kuma zaki iya yin komai ba a lokacin domin ya riga da ya gigita miki kuruciyarki. Cikin jarumta na danne hawayen da yake neman sake ballewa. Murya na rawa na furta "Ki bani dama mana Abida." Gabadaya zuciyata ta yi mini nauyi ainun. Kishi da kewar ahalina suka taru suka sababa mini irin al'amari a zuciyata mai matukar nauyi na gaske. Gabadaya na rasa inda zan tsoma raina na ji sassaucin halin da nake ciki. Wayata ta yi haske, na mika hannu na ga sako ne daga banki suke sanar da ni an cire dubu sittin da takwas ta hanyar amfani da katin (A.T.M) Mamaki mai tsananin gaske ya rufe ni domin yau ba'afi kwanaki uku ba ya cire kudade masu nauyi. Na sake dubawa na ga super market ne suka cire kudin. Na shanye mamakina watakila kayan amfanin gida ya siyo ko kuma dan kayan kwalam zai siyo mini tunda ya sani idan na shiga irin wannan yanayi bana iya cin abinci mai nauyi. Na yi sukuri ina tuno sadda Basma ta fahimci ATM dina na account din da albashina ke shiga na hannunsa. Hakan kuma baya hana wani lokacin ya karbi A.T.M din business account dina. Cikin fishi ta ce "Ba fa zaki kubuta daga abin da kike tsoro daga gare shi ba. Duk sadaukarwarki gare shi ba zai sanya shi ya zalunci kansa ko ya tauyewa zuciyarsa abin da take so ba. Ina jiye miki ranar da zaki fahimci ainihin karatun da nake miki bita a kansa. Ina fatan ki fahimta da wuri ba sai lokacin da komai ya k'ure ba". Na numfasa duk da ina cikin fishi amma a kasan raina still ga ni nake yi, menene aibu idan mace ta taimaki miji, ta kuma rufa masa asiri, menene jin dadin arziki idan har iyalinka basu wadata ba? *Muna siyar da gold daidai da Farashin kasuwa* *Muna siyan Wanda yake da receipt daidai da Farashin kasuwa*. *Ina matan da suke son siyan gold amma Basu san kansa ba, suke gudun a cucesu?* *To kakarmu ta yanke sakandon kuwa zamu siyo muku Babu cuta babu cutarwa daidai da Farashin kasuwa, abin jin dad'i Allah ne wakilinku*. *Ku tuntube ni a wannan lambar wandada suka shirya siya da gaske* *08032773332* Na kalli agogo na ga biyar tana shirin yi, daidai lokacin kuma su Farha zasu tashi a islmiyya ita da Yaya. Gabadaya na zama weak Dan haka haka na kwalawa Alawiyya kira. Ta shigo a hanzarce ta tsuguna. Na ce "Dauko mini jakar hannuna, ta mike da azama ta dauko akan madubi. Na zuge na cire yan dari biyar biyu na ce "Ki je ki taho da su Farha ba zan iya tuki ba". Ta karba tana ce wa "To mahma sannu Allah ya sauwake." Bata jima da fita ba, Amrah ta shigo bakinta dauke da sallama, tana sanye cikin uniform, ga jakar makaranta a kafadarta, tabbacin yanzu ta shigo. Da kulawa ta gurfana a gabana ta saka hannu tana taba jikina. "Sannu mamah na ji babu fever". Ta fada cike da kulawa. Na murmusa kadan duk da idanuwana sun yi kozai kozai na ce "Da sauki sosai Amrah. Ina Dady?" Ta ce "ya ce na taho aiki ya rike shi" Na ce "Tom ki je ki samu wani abu ki ci, nasan kun yi sallah". Ta mike ta ce "Bari na fara yin wanka." Na bita da ido ina sake shaidar tsananin kamannin da take yi da Sahal. Hatta tsayinsa duk ta kwaso, tana aji hudu a sakandire yanzu. Na yunkura na mike cikin k'arfin zuciya na fara zagaya dakina ina ta kokawa da sashin zuciyata da yake kalubalantar Babanta akan da Hawwa ya fita ya kashe mata kudin da suke nawa ne. Kudin da ba'a b'agas nake samunsa ba, sai na shafe kwanaki ashirin da biyar ina sammakon barin gidana duk sanyi, duk zafi ko damina, haka nan yini nake ina fama da alli da biro hadi da marking bayan bata lokaci wajen yin nazari tare da bitar yadda zan dinga koyarwa cikin hikima ta yadda dalibaina zasu fahimci darasin da kyau. Ba dan komai ba sai dan na tabbatar albashina halal ne. Sai ga shi duk wannan fadi tashin ina yi ne, wata tana ci a b'agas cikin dabara da hila. "Tirkashi." Kalmar ta subuce mini ba tare da na shirya hakan ta faru ba. Na cigaba da zagayen amma sai na tsinci kaina da ambaton "Rabbi inni lima anzalta ilaihi mini khairun fakeer! Yi nake yi a fili tare da nufin na samu saukin matsalolin da suka dabaibaye zuciyata da tunanina. Da yake alkawari ne na Ubangiji idan ka nemi taimakonsa cikin yarda da gasgata shine mai yi, zaka ga taimakonsa kuwa ta inda baka yi zato ba. Sannu a hankali na ji saukin zuciyata dan haka sai na fita zuwa falo dan kada na cigaba da zama tunani da bakinciki su kassara ni. Ina zama kuwa su Yaya Faruk suka shigo. Farha da bata yarda ta girma ba, ta taho ta fada mini na d'agota na tsinci kaina da kallonta, irin kallon nan mai tsananin gaske. Gabadaya kammanin Yaya Sulaiman ne akan fuskarta, wadanda basu san shi ba, sai suce da ni take kama tunda babu shakka ni da shi kamarmu har ta b'aci. Ta yi murmushin da irinsa Abida take yi ta ce "Mamah na fada miki bana son Alawiyya ta zo daukarmu! Na jata jikina na ce "Ai ba ni da lafiya ne Farha" Nan da nan ta ce "Oh sorry mahmah ya Jiki?" Na amsa mata da ce wa " sauki." Na ce "Maza je ki Yaya Amra ta watsa miki ruwa kafin ta fito tana dakinku." Da sauri kuwa ta dauki jakarta ta yi daki nsu, sai lokacin na mayar da hankalina kan Faruk da yake tsaye na ce "Kaima ka je ka watsa ruwa ka kuma tabbatar ka fito kayan nan ka bazasu a baya. Idan ka dawo daga masallaci anjima ka hada da na Farha ka wanke muku, kasan Yaya Amra ta ce ta daina yi Maka wanki tunda ka mata rashin kunya." Ya wuce yana kunkunin ta daina yi din mana. Tunda a washing machine ne Ai ya iya shima. Har muka kammala dinner babu shi babu duriyarsa. Bai dawo ba sai karfe tara na dare. A falo ya tarar da ni ya yi matukar kaduwa domin bai yi zaton zai ganni a falo ba. Yara suka yi masa barka da dawowa san nan suka tafi suka kwanta domin mun riga mun sabar musu 9 suke kwnaciya duk dare. Ya zauna daf da ni. Turarensa ya cika mini hanci. Cikin nutsuwa ya ce "Ya jikinki?" Murya babu amo na ce "Na warke" Na tsananta kallonsa ganin haka ya shigo hannu rabbana. Hawaye ya cika mini kwarmin idona. Tabbas a wajen yarinyar nan ya shantake ya yi dare bayan ya gama kashe mata kudaden da yake mallakina ne, ni kuma ya bar ni ko oho duk da ya bar ni a yanayin na rashin lafiya da sukuni sosai. *Alhamdulillah!* *Mu je ga book 2.*. *Book2&3 na kudine wanda za'a kammala cikin kwanakin k'alilan a Telegram da arewa.* *Kunsan dai marubuciyar bata jan rai wannan karon ma ba zata ja muk rai ba.* *Ku biya 1k ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*. *Menene matsalar da ta tarwatsa ahalin su Bilkisu duk da irin k'arfaffen. zumuncin da suke gudanarwa?* *Wacce irin rayuwa da sadaukarwaka ta yi da mijinta ne?* *Dukkan karatun da kuka yi , bamu kutsa cikin danbarwa da rikitarikitan da suke cikin labarin ba* *Sharar fage kawai muka yi*. *Ku gyara zama zaku sha karatu cikin nutsuwa babu jan rai in sha Allah* *Za ku yi nishadi, takaici, mamaki tare da alajabi cikin wannan labarin* *Ku biyo Bilki sannu a hankali har zuwa lokacin da zata cigaba da hakaito mana labarinta yadda zare da abawa zasu warware mana*. ✍️✍️