*💔-BAKAR WASIKA-💔* _Mai Farin rubutu_ From the writer of RAI BIYU HAFSATU MANGA ZAGON KASA ZABIN RAI KHADIJATU GOBENA ZAKI FULANI ©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠ SADAUKARWA. Na Sadaukar da littafin nan ga Hajiya Habiba da iyalanta. GAISUWA Ga Mutanen Kirki, Rahma Kabir, da Mrs J Moon. GABATARWA. BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Idan aka ce Bakar Wasika Mai Farin Rubutu. Ana nufin wani dunkulelen sako mai wuyar fassara, kamar mutum mai nagarta sai wani mummunnan kaddara ta fada masa. Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Tafida, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal, Kabir da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA. Labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk kuwa da na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? Labarin BAKAR WASIKA kirkiraren labari ne kamar sauran labaraina, kun san dai ban saba baku kunya ba ko?😉 Wannan ma zai zo muku fiye da yadda kuke tsammaninsa inshallahu. Sai dai ba free ba ne na kudi ne, but ina da free pages daga 1-10 ga masu son jin dandanon labarin kamin biya. Kamar yadda kuka sani bana editing labari so ku yi hakuri da duk abun da zaku gani. P. O. V Na nufin Point Of View.                       بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ Page -1⃣ Matashiyar yarinya ce yar shekara goma sha-bakwai dauke da farantin giɗa tana tsaye jikin window makaranta tana leken daliban da ake yi wa darasi. Yadda ta maida hankali tana sauraren darasin da ake wa dabiban sai ka rantse da Allah har da ita a cikin daliban. Ilmin zamani na daya daga cikin abubuwan da suke matukar burge Aminatu kuma shi ne kadai abun da ta rasa a yanzu, wanda ta riga ta maye gurbinsa da talla a halin yanzu, a izuwa yanzu ta tabbatar bata da muhalli a ilmin zamani, sai dai shi ilmin yana da muhallin a zuciyarta. "Ba ni gidar goma" Wata dalibar ta fada da kamar rada gudun kar malamin da yake musu darasin ya ji ta, a munafunci ta jefowa Aminatu wata tsohuwar naira goma, sannan ta maida hankalinta gurin Malamin. Aminatu ta duka kasa ta sauke farantin dake hannunta sannan ta dauki naira goma din ta daga hijabinta ta saka naira goma din cikin hular dake kanta ta gyara hijabinta sannan ta dauki giɗar ta mika mata, yarinyar ta karba da sauri ta boye. A lokacin ne malamin ya hango Aminatu tana kallon allon da yake koya musu darasin, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake arba da yara na shigowa makarantar talla, wani lokacin har cikin ajijuwa suke zagayawa idan sun ga babu malamai a ciki. Sai dai tsayawa a nasu ana daukar darasin karatu babu kamar Aminatu domin ko daliban makaranta basa nuna mata natsuwa da maida hankali sai dai su nuna mata iya rubutu da kuma fahimtar darasin yadda ya kamata domin su a kullum suna aji ne, ita kuma sai idan talla ta biyo da ita. "Mtcheesss idan ba makarantun kauye ba ina ake wannan abun? Ace makaranta a bude har masu talla suna shigowa, ko wane aji babu ganbu (Kaure) balle har ma ace an zagaye mana makarantar" Malamin ya fada cike da jin zafin yadda aka wofintar da abun da ya shafi ilmin boko a yanki. Aminatu na jin haka sai ta duke kasa gabanta na faduwa, daman can yarinya ce mai gujewa fitina da tsoron bacin ran mutane. Dukuduku tai ta fice daga gurin cikin sanda ta koma can bakin kofar makarantar inda suke zama ita da sauran masu talla suna jiran a tashi yan makaranta fito siye siye. Rayuwar Aminatu rayuwa ce da ta ginu da ilimin addinin da kuma talla, domin bayan noma da mahaifinta yake yi wanda shi ne mafi akasarin mutanen garin galadi suke yi, babu wani abu da aka doraga da shi a gidansu kamar tallar da take, da rana zata kai giɗa makarantar boko, dare kuma ayi mata tuwo, da safe kuma ta fita tallar koko, hakan yasa rabin rayuwarta ta kare a talla. Sai dai ko kadan bata da matsalar rayuwa ta ko'ina domin ita kadai ce mace da mahaifiyarta ta haifa bayan zaratan maza bakwai. Rayuwarta kusan haka rabin rayuwar yan matan garin take ba kowa ya ke damuwa da karatun boko kamar yadda suke damuwa da talla ba, domin talla tana ba su komai cikin har da kayan dakin da ake yi ma yan mata. Garin Galadi wani yanki ne dake cikin karamar hukumar mulki ta shimkafi, gari ne mai cike da albarka manoma, kusan idan ka ambashi shimkafi kowa ya san gari ne na manoma garin mai cike da albarka da kuma mutanen kwarai. Karamar hukumar Shinkafi tana cikin jihar Zamfara, shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Hedikwatar karamar hukumar tana cikin garin Shinkafi kuma karamar hukumar na da iyaka da karamar hukumar Zurmi Maradun da wasu sassan jihar Sokoto da jamhuriyar Nijar. Garuruwa da kauyukan da suka kunshi karamar hukumar Shinkafi sun hada da Miyasa, Shinkafi, Bwane, Tunga, Fidani, Tubali, da Faru. An kiyasta yawan al’ummar karamar hukumar Shinkafi ya kai 177,811 mazauna yankin da ‘yan kabilar Hausa da Fulani suka mamaye. Yaren Hausa dai ana magana ne da shi a karamar hukumar, addini Musulunci shi ne addininsu. Karamar hukumar Shinkafi tana da fadin kasa kilomita murabba'i 674 kuma tana da matsakaicin zafin na digiri 34. Karamar hukumar tana da kogin Tafin Kaiwa da ke ratsa cikin yankinta yayin da matsakaicin saurin iska a yankin ya kai kilomita 11/h. Noma wani babban aiki ne na tattalin arziki da al’ummar karamar hukumar Shinkafi ke aiwatarwa. Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da al'ummar karamar hukumar Shinkafi suka gudanar sun hada da farauta, kasuwanci, kiwon dabbobi, da ayyukan fata. *** *** *** Tana zaune a gurin har aka tashi yan makarantar masu siyen gid'ar suka siya, wanda tai saura sai ta dauki farantin ta dora akai ta nufi gida tare da kawar tafiyarta Rumaisa, suna tafe tana kirga kudin gidarta har suka kawo mararabar hanya (Hanyar da ta kasu hudu) a nan sukai sallama kowa ce ta nufi gidansu. Da sallama ta shiga gidan kamar yadda ta saba. "Wa'alaikissalam yar Inna yar Albarka" Inna ta fada tana juyowa ta kalleta fuskarta dauke da murmushi. Sanusi ya wara ido ya zubar da ruwan daya wanke tufafinsa. "Mu da ba yan Inna ba a nuna mana bolar mu" Aminatu ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba, tai saurin aje farantin dake kanta ta mikawa Inna kudin hannunta sannan ta karbi dawon (Fura) da Inna take da inna take kirbi (Daka) ta cigaba da yi tana fada mata ko nawa aka samu yau. "Aminatu Auta, himma dai yar Audu" Sanusi ya sake fada da fuskar zolaya, daman can indai yana gida ya fi kowa zolayarta kamar wata abokiyar wasarshi. "Na ji dai ai ina aiki dai ni ba kamar sauran auta ba ne, kai da baka iya noma fa sai sana'ar tireda" Ta masa gwalo. Sai Inna ta saka dariya. "Fada masa dai yar auta gogar aiki, shi baya iya aikin karfi irin na maza sai sana'ar zama" Aminatu ta wani yi warrr da ido tana jin kirarin da Inna tai mata har cikin ranta, ganin hakan yasa Sanusi sake tsokanarta. "Eyee su igeee anji dadi, Igengen..." Take ta turo baki gaba. "Inna kin ga yana ce min Ige ko?" "To maza nawa aka haifa kamin a haife ki? Kin zama Ige ai" Aminatu ta kalli Inna da kwababbiyar fuskarta kamar zata fashe da kuka. "Inna kina jinsa ko?" "Dan Allah Sanusi ka gama ka fita ka bar mana gidanmu, ya zaka takurawa Auta" Inna ta fada. Sai Aminatu ta gyada kai "Atooo" Dariya yai ya debi ruwa a babbar buta ya zagaya bandakin da ya kasance na kasa kuma iya tsawon habar mutum, (shoulder) domin idan ka mike tsaye gaba daya, za a iya hangoka. Kamin ya gama wanka Aminatu ta gama kirba dawon har ta kwashe ta zuba wani, Auta ce amman ba kamar sauran ba, domin bata da ƙwiyar aiki, ita dai bar ta da shagwaba da yawan kuka idan an taba ba. "Baka ma wanku ba tsami kake yi" Ta fada tana yatsina fuska kamar gaske. Dariya yai ya shiga karamin dakin dake kusa da na Inna ya shirya cikin wata karamar shadda ta marasa karfi da ta gama shan jiki ya saka hullarsa taɓani ka ji Hadisi, sannan ya fito yana ta kwanbo da talkaminsa na roba. "Wallahi ba kai kyau ba" Cewar Aminatu tana dariya, sai Inna ta taya ta. "Lallai kam kyau ai sai Auta hanci har baka (Baki) sai dai a gwada mata haske shi ma kadan" "Inna Wallahi ki daina biyewa wannan yarinyar, idan ma ta samu miji irina ta more..." Har Aminatu ta bude baki tai magana sai kuma tai shiru ta maida dubanta gurin yayanta Amadu, wanda take tsoro kamar mutuwarta domin idan yana a cikin gidan bata da sukuni ko wani motsin kirki bata yi. Na tsantsiyar yarinya ce, sai dai shigowar Amadu ya saka ta kara natsuwa ta yi tsit a gurin kamar babu ita. Amadu irin mazan nan ne da basa wasa da yara balle kuma ita da take kanwarsa ta biyar. Wani tsohon babur dinsa Honda ya turo ya karaso inda suke, Inna na nashe dawon a tukunya, Aminatu kuma na zaune gaban turmin idonta kasa. Inna ta daga kai ta kalleshi yana kokarin jingine babur din ta ce. “Ka dawo?” “Eh ya gidan?” “Lafiya Kalau, ya kasuwa” Ya dan yi jimm cike da damuwa sannan ya sauke ajiyar zuciya. “Kasuwa da godiya Inna, amman abubuwan kasar nan sai hamdala, komai kara masa kudi ake, idan baka da wani babban jari yanzu sai kasuwancin ma ya gagareka” “To ya za'ayi kasar ce ta zama abun da ta zama, Allah ya ba mu azzaluman shugaban ni, ba su da tausayi kansu kawai suka sani” Cewar Sanisu yana nufo inda suke, Sai Amadu ya amsa masa. “Wallahi ga rayuwar mutane an maida ta kamar ta dabba, kai har kara ma dabba a yanzu, kuma sun kasa daukar mataki basa ma son ana ji, Nigeria kam ban san yaushe zata gyaru ba” “Allah ya kyauta, ni dai na wuce shago” Sanusi ya sake fada, sai Inna ta bishi da addu'a. “To Allah ya tsare ya bada sa'a” Har ya fice Aminatu bata dago kanta ba, ko da wasa bata son ta hada ido da Amadu, ba ganinsa kadai ba ko muryarsa ta ji sai ta ji gabanta ya fadi. “Inna Ina Lami kike neshen dawo da kanki? (Saka fura a tukunya)” Amadu ya tambaya. “Kai ma ai kasan bata nan, da tana nan ai ba zata bar ni nai wannan aikin ba, ta je ganin dan Kuidu (Kaciya)” Ya shaf kansa. “Na manta ta fada min, abubuwan ne sun yi yawa Wallahi” Ya fada yana nufar bangaren da Iyalinsa suke. Domin irin katon gidan nan ne na kauye mai fili wanda yaya suke dibar bangare suna kafa na su iyalin, bayan shi da yake da mata daya, Musa mai mata biyu ma a gidan yake zaune, sai dai shi ya fitar da kofar gidansa ta can baya sai an zagaya za a iya shiga, Iro da Sanusi ma da ke shirin aure a cikin gidan suka gina gurin da za su aje matansu. TALBA POV. Yana zaune a dining din har Momy da Baaba suka gama hada abun karyawa. A hankali ya dago yana kallon yadda Baaba take jera kulolin, hannunsa suke da wayarsa. A hankali ya lumshe idonsa ya bude, cike da kasaita ya motsa bakinsa, yana maida dubansa gurin Momy wanda taja kujera ta zauna. “Baaba a fadawa yaran nan su fito su karya” Matar da aka kira da Baaba ta dan risinawa Momy cike da ladabi. “To ranki ya dade” Ya nufi upstairs da sauri, da ido Talba ta bita kamin ya maida dubansa gurin KB da ya fito a daya daga cikin kokafin da suke can dayan bangaren falon. “Momy ina kwana” KB ya fada yana kokarin jan dayar kujera ya zauna, sai Momy ta amsa masa ba yabo ba fallasa, sannan ya mikawa Talba hannu suka gaisa, ya shiga hadawa kansa tea. A tare Amal da Leila suka sauko downstairs din, kai tsaye suka nufu dinning area, Amal da far'arta kamar kullum, Leila kam sai wani sham kamshi take musamman da ta hango Talba a zaune a dinning din. Amal ce ta riga isa ta zauna tana fadin. “Ya Talba Morning” Ya kai dubansa gareta yana sakar mata murmushi as respond, irin murmushin nan da be saba zama a fuskarsa ba. Bayan ta gaishe shi ta gaishe da KB. “Ya KB Morning” “Morning Amal” Ya amsa yana kai plantain a bakinsa. Leila na zaunawa Talba ya mike tsaye cike da izza, sai duk suka kalleshi. “Ah ah ba karyawa za kai ba?” Momy ta tambaya. “Zan yi breakfast a waje” Ya amsa kamar an amsa dole, already yayi nisa da dinning din. Sai da ya fice daga falon gaba daya sannan Momy ta kalli Leila. “Kun sake yin fada ne?” Leila ta kalleta cike da damuwa. “Momy miyasa kullum ni ce mai laifi?” Momy ta zare mata ido. “Yes tun da ya dawo sallah asuba yake zaune a nan, idan har babu komai to babu abun da zai saka ya zauna tun 6:30 har 9:30 dan kawai kin zauna kuma ya tashi ya ce ya zai karya a waje, zan kaiwa Daddynku abinci yanzu, ki same ni daki anjima” Momy na fadar hakan ta mike tsaye ta dauki wasu tsadaddun kuloli ta nufi kofar da zata sadata da bangaren Daddy. “Ni ma ba zan karya ba” Amal ta fada tana turo baki alamar ranta ya bace sai harara take watsawa Leila kamar ba yayarta ba, sannan ta mike tsaye ta fice daga gurin ta nufi upstairs. “Munafuka, ai daman tun da Yayanki be ci ba ba zaki ci ba Mtschesss” Cewar Leila tana binta da harara. KB ya bi Amal da kallo har ta shiga dakinta sannan ya kalli Leila. “Da gaske fada kuka yi kenan?” “Ai dole mu sake fada kuma mu yi ta fada, na gaji da halin Talba, na gaji, shi ba dan sarauta ba, ko yan sarauta ba su abun da yake, ba baiwarsa ba ce ni, and i hate nonsense” Mikewa tai tsaye a fusace har tana jefa da empty cup din dake gabanta, a take ya fadi kasa ya fashe, kamar zata tashi sama haka ta nufi upstairs. KB ya wara ido. “To ni ina ruwana, can ta matse muku, a takaice dai ni kadai zan karya a yau... Fine” Ya sake bude wata kular ya shiga zubawa kansa ferfesu. FARUQ POV. Ya aje kofin garin dake hannunsa yana kallon dansa. “Ka koshi ko?” Sultan ya daga masa kai yana murmushi kamar yadda shi ma yake masa murmushin. Faruq ya dauke shi ya dora saman kafafuwanta sannan ya kalli Mahaifiyarsa cike da damuwa. “Mama bari mu tafi kar dare yai mana” “Kara ka tafi da wuri kam tun da a kafa zaka je” Ya mike tsaye. “To sai da safe ayi ta mana addu'a dai” “Addu'a ai dole ce Faruq, Allah ya tsare, Sultan sai da safe ko?” “Sai da safe Mama” Sultan din ya fada da muryarsa da be gama kwarewa da iya magana ba. Daukarsa Faruq yai ya fice daga gidan, a kafa ya taka tun daga unguwar dallatu har Gadar Baga, ganin Sultan ya fara bachi sai ya dora shi a kafada Faruq, yana tafe gabansa na faduwa har ya iso gidansa. Sai da ya saka hannunsa aljihu ya lalaba garin kwakin dake cikin aljihun wandonsa da sugar ya tabbatar suna nan sannan ya kwankwasa kofar gidan. Yayi kusan rabin awa a tsaye sannan Rafi'a ta bude masa. Ganin babu komai a hamnunsa yasa ta ja tsaki. “Mtcheesss” Be ce mata komai ba ya saka kafarsa ya shigo cikin madaidacin gidan na zaman mutum daya, sannan ya maida kofar gidan ya rufe. Da sallama ya shiga cikin falon amman ta ki amsa masa sai latsar wayarta take kamar bata san da shigowarsa ba. Be damu ba domin in da sabo ya saba da halin matarsa. Dakinsu ya shiga ya kwantar da Sultan sannan ya dawo falo ya zauna kusa da ita, kana ya ciro garin da ba zai wuce gwangwani daya da rabi ba da surga ya mika mata. “Ga dan abun da muka samu” Daga shi har garin kallon uku saura kwata ta watsa masa. “Gari fa nake gani Faruq?” “Shi ne” Ya amsa mata kamar wani yaronta. “So kake jinina ya tsotse ne? Kara min jinin ma ya gagara? Haba Faruq, na wuni ban ci komai ba kuma yanzu ka shigo min da gari?” Ta masa maganar kamar zata fashe da kuka, ya sauke ajiyar zuciya a hankali. “Haba Rafi'a tun da kika ga na shigo miki da gari ai kin san ban samu komai ba ne, shagon na mu sabuwar unguwa ce ba a samun ciniki sosai, tun da na fita har babu wanda ya zo aski, wannan garin ma sai da na biya ta gida Mama ta siyo min aka jikawa Sultan ya sha sauran ne na kawo miki, Wallahi ni tun karin safe da na yi ban sake cin komai ba, kara ke na bar miki gwangwani biyu na wake...” Be marasa ta mike tsaye tana masa ihu. “Kai ka so Faruq kai kaso zama da talauci, sa'aninka suna can sun gina manyan gidaje wasu na da manyan motoci, su ci mai kyau su saka mai kyau, amman kai dube ka? Suturar kwarai ma ta gagareka, ni kaina da nake matarka ina kunyar a tararda ni a gidan nan, gida duk ya lalace, da an yi magana kace komai zai wuce sai yaushe zai wuce? Shekara biyar fa da aurenmu Faruq, ka dube ni ka gani tsabar kyau Baturiya ake ce min fa! Amman na kare a aurenka, auren kaddara auren cin garin kwaki, dan sunan mai dadi ma baka iya kirana da shi ba, Rafi'a Rafi'a, Fee'ah Fee'ah haka ake kirana ba Rafi'a ba” Ta nufi dakinta a fusace, shi kuma ya lumshe idonsa yana jin zafin maganar da ta fada masa. Yana zaune a falon har 11pm na dare sannan ya tashi ya rufe kofar falon ya kashe wutar ya shiga dakin ya shiga bathroom yai fitsari ya wanke kafafunwasa da fuskarsa sannan ya dawo dakin ya kwanta bayanta, can kuma ya tashi zaune yai ma dansa addu'a sannan ya kashe wutar dakin, ya dawo bakin gadon inda ya saba kwanciya yai tasa addu'ar, ya ciro wayarsa ya aje a gefensa ya kwanta, a hankali ya kai hannunsa ya fara shafata sai ta buge masa hannun ta tashi zaune. “Miye haka? Ka dawo min da garin dan jinina ya tsotse, kuma yanzu ka zo min na maka me? Da safe kuma dan ka ya dame ni da kayan fitsari tun da an gagara sai masa pampas, ga wannan tsinannen cikin wahala da yake jini, haba duk ni kadai? Wai kai baka da imani ne?” “Rafi'a wai miyasa bakinki ba shi da linzami ne?” Ya fada a fusace yana kokarin danne fushinsa. “Shi bakin nawa ai haila yake, kai kudi ka gani idan zan maka duk wannan, su masu kudi ka ga matansu na musu haka ne? Saboda sun ba su komai gurin kwanciya ma dakin yara daban ake amman kai ka hade ni daki daya da yaronka, anjima kace min na taso muje falo ko? To ba zan je ba” Sauka yai daga saman gadon gaba daya ya fice daga dakin, be tsaya a falo ba tsakar gidan ya fita gaba daya ya zauna saman turmi ya daga kansa sama. “Kun faya kun sai kai Allah” Ya fada yana kallon yadda taurari suka kawata samaniya. Rafi'a na jin ya fitarsa tai azamar dauko wayarta touching, ta dauki keypad dinsa ta shiga contact list tana neman wata number. MD Saleh a dai dai gurin ta tsaya ta bude sunan ta kwashe numbers din sannan ta maida wayar ta aje, sai tai saving number da Maryam Dahiru Sokoto, kana ta saka wayarta a silent ta kwanta. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -2️⃣ “Akwai abubuwa da yawa da rayuwa bata iya tafiya sai da su, a ciki akwai numfashi ci da sha, da kuma soyayya. Bana jin zan iya rayuwa idan babu kai a kusa ni, zan iya rasa ci da sha kuma na rayu da soyayyarka” Ta nade wasikar da ta gama rubutawa da hausar azami, tana murmushi sannan ta mike tsaye ta maida biron da littafin cikin jakarta ta islamiya ta rataya a jikin kusar dake gurin sannan ta saka hijabinta ta fito. “Inna an gama?” “Auta tun dazun na gama, kin yi sallah dai ko?” Ta saka wasikar a cikin jikinta tana murmushi. “Inna ke ma kin san bana wasa da sallah fa” “Haka ne, Auta Allah ya miki albarka” Inna ta fada Baba da ke zaune saman tarbarma yana sauraren redio ya amsa da Ameen yana murmushi. Sanusi ma dake aikin auna tuwon dawo a bakinsa ya so ma zolayarta kamar yadda ya saba. “Ku na fasa mata kai da wannan kafafuwan nata kamar itace” Aiko kamar jira take sai ta fara kukan shagwaba, musamman ganin duka gatanta suna nan Inna da Baba. “Baba kana jinsa ko?” Baba yayi dariya tare da kai hannunsa ya kashe redio dake gefensa, ya tofar da goron bakinsa. Yai mata alama da ta zo da hannu, kamar jira take sai ta karaso inda yake tana ta turo baki ita ala dole an taba ta. “Auta Mamana, ki daina biyewa Sanusi, shi da yake ragon maza, ke da kike Jaruma, ki daina nuna musu rauninki, kin ga shi kin ga Rilwanu ki daina bari suna saka ki kuka, da an miki aure sai kun yi ta marmarinki” Ta rufe ido da sauri cike da tsantsan kunyar irin ta ya mace bahaushiya. Hakan da tai sai ya kara saka Baba murmushi. “Allah ya miki albarka ya nuna mana lokacin Autata” Kasa amsawa tai da ameen domin Aminatu irin yan matan nan ne masu kunya da kawarda ido ga wasu abubuwan. Sai kawai ta mike tsaye har lokacin bata janye hannunta daga fuskarta. “Wai kunya take, kunya kike kika yarda kina fita zance” Sanusi ya fada yana dariya, a cikin hasken farin watan Aminatu ta watsa masa harara. Ta nufi inda kwallar tuwonta take ta nada ganwo ta dauka ta dora a kai sannan ta mika dayan hannunta ta dauki miyar dake cikin bokitin roba. “Ni na tafi gurin sana'a ta” Ta fada tana kara murda masa baki, Inna dai bata ce komai ba bayan murmushin da tai. Har ta kai bakin kofar fita daga gidan sai Baba ya kirata. “Mamana” Ta juyo. “Na'am Babana” “Allah ya miki albarka” Sai ta amsa tana kallon gefen Sanusi. “Ameen, yan bakinciki sai dai su mutu” Ba Inna da Baba da Sanusi kadai ba, har Rilwanu da Iro da suka shigo yanzu sai da suka saka dariya, domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, inda Aminatu ta yi habaici ko shagube to ba zai wuce Sanisu ko Rilwanu ba take yi ma. “Mai tuwo a bani na hansin” Ko kallon Rilwanu ba tai ba ta saka kai ta fice tana cinno baki gaba kamar zai zazzago ya zubo kasa. Kusa da Baba suka zauna ko wane ya aje bindigar maharba da manyan wukaken dake hannunsu. Kana ganinsu ka ga zaratan jarumai, tun daga kirarsu har yanayin shigarsu da muryarsu. Domin suna daya daga cikin manyan yan saka na yanki, abu ne mai wahala ka ga gidan da ke da maza uku ko hudu baka samu yan sakai a gidan ba balle kuma gidansu Aminatu da suke da maza bakwai. Ba wuka ba ko bindiga bata huda mahaifinsu balle kuma su da suke shiga dajijikan kauyen neman barayi da kansu. Tana yin nesa da gida kadan sai murmushi ya wanke mata fuska, a cikin abubuwan da tafi kaunar a rayuwarta akwai yan'uwanta, musamman Rilwanu Sanusi da Musa, domin sun fi sauran sake mata, da kuma kyautata. Gashi basa yarda ko da wasa wani ya nuna mata yatsa a waje balle har a taba ta. A natse take tafiya, tana ta mikawa mutanen data sani kuma suka santa gaisuwa cikin girmamawa, musamman abokan mahaifinta, sai da ta kusa dandali sannan ta rage saurin tafiyarta da alama akwai wanda take jira ko take son hangowa, can kuma ta ja ta tsaya ta juyo tana kallon hanyar data fito sai ta hango masoyinta tafe da saurinsa cikin shigar kananan kaya, murmushi ne ya cika fuskarta, sai ta sauke idonta kasa domin bata jin kunyarta zata barta tai ta kallonsa har ya karaso inda take. Sai da yai wani gyaran murya ya waiga ya ga babu mai ganinsu sannan ya ce. “Auta” “Na'am barka da dare” “Yau ina fitilarta?” Sai da yai maganar ta tuna da zancen wata fitila, sam ta manta bata zo da ita ba, sai a yanzu ta suna ta bar fitilar a dakin Inna bayan ta gama rubuta wasikar. “Wallahi na manta ta” Ta fada tana dukawa ta aje bokitin miyar dake hannunta, sannan ta saka hannu a cikin zanenta ta dauko wasikar ta mika masa, ya karba da dayan hannunsa dayan hannun kuma ya mika mata tasa wasikar. “Na je gida na karbo miki?” Ta zaro ido. “Kai Baba yana nan fa, ni ban saba aikin maza a gidanmu ba” Yayi yar dariya yana kokarin magana suka ji muryar Sanusi. “Auta...” Ba karamin tsoro Aminatu ta ji ba, domin bata saba tsayuwa da maza har a ganta ba, duk kuwa da kasancewar ta kai munzalin da zata iya yin hakan, amman kunya da tsoron yayyunta ya hana ta yin haka, duk inda ta san idan ta tsaya da wani za a gani ayi mata magana ko fada bata yarda ta tsaya a gurin. Maniru ne ya soma wayancewa ya mikawa Sanusi hannu suka gaisa, Sanusi ya amsa yana musu dariya. “Ka ce na zama yaya daga yanzu” Maniru yayi dariya Aminatu kuma ta duka da sauri ta dauki bokitin miyarta daman tuwon yana saman kanta. “Ga fitilar in ji Inna” Ya mika mata yar karamar touch light din dake hannunsa, sai ta karba da sauri ta juya ta cigaba da tafiya cike da tsananin kunya gabanta sai faduwa yake. Sai da tai nisa sannan Sanusi ya kalli Maniru ya ce. “Maniru idan kana son Aminatu ai gidansu ya kamata ka ta fi ba wai ka rika tare ta a hanya ba, amman irin wannan ai ba lallai ne kowa yai maka fahimta mai kyau ba” “Wallahi Sanusi ina son zuwa, ita take hana ni, sai tace tana jin kunya kuma yayyunta za su iya mata fada” Sanusi yayi dariya. “Shirmen ta ne, ba a aure mu za mu yi, idan ka shirya kawai ka min magana zan sanar da Baba sai a komai cikin mutunci” “Maa Shaa Allah, na gode sosai daman ni abun da nake nema kenan domin na gaji da zageye zageyen nan Wallahi” “Inshallahu zan yi magana da Baba, duk yadda ake ciki zaka ji” Sai da Maniru ya sake mika masa hannu suka gaisa sannan ya wuce yana ta jindadi abun nema ya samu. Aminatu na daya daga cikin irin yan matan nan da suke da farin jinin siyarda sana'a musamman a dandali duk kuwa da kasancewar ba wani kula samari take ba, amman abu ne mai wahala ta je da tuwo ta dawo da shi sai ta saida kaf wani lokacin ma har ta karbi na wasu ta siyar musu, saboda tsabtarta da kuma dadin miyar Inna. Har ta gama sai da tuwon ta nade komai nata a guri daya Wasikar da Maniru ya bata tana cikin jikinta, a dayan bangaren kuma tana ta tunanin yadda zata shiga gida, domin ta san abu ne mai wahala ace Yayanta Sanusi be fada cewar ya ganta da Maniru ba, ba fada kadai ba wata kila har doka sai ta sha a gurin Yayanta Amadu. Da gangan ta ki yarda ta je gida da wuri duk kuwa da kasancewar ta siyar da tuwonta a cikin lokaci, sai ta zauna a gurin tana ta kallon mutane fuska ba yabo ba fallasa, ba zaka iya karantar damuwarta ba, sai dai hakan kuma be isa ka fadi cewar tana cikin farinciki ba. Har kusan 11 na dare bata tafi gida ba tana zaune a gurin sai ta fakaici idon mutane sai ta matse yan kwalla da suke cika mata ido, sai kuma ta dan turo baki, sai kallon mutanen dandalin take sai ka rasa wa take turowa bakin. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta mike tsaye ta dauki robar ta dora a kai tai ma abokan sana'arta sallama, ta fara tafiya kamar bata son zuwa, ta san inda bata je ba sai an aiko nemanta kamar yadda ake idan ta dade bata dawo ba, dan haka bata da wata mafita data wuce ta koma gida. TALBA POV. Yana shakimce cikin mota har Ali ya iso gurin motar ya bude front seat ya shiga ya zauna yana kallon abokin nasa “Lafiya dai?” Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke sai huci yake, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya shiru ya maida dubansa wani gurin. Ali na ganin hakan yai dan murmushi. “Leila ta tabo ka kenan?” Talba ya kalleshi da idanuwan dake nuna bacin ransa karara kamar yadda fuskarsa ma ta kasa boye bacin ransa. “Wai yarinyar nan ni zata wulakanta?” Magana yake kamar wuta na fita a bakinsa. Ali ya masa kallon natsuwa. “In I'm not mistaken ka sake mata maganar auren kenan?” Shirun da Talba yai ne ya tabbatarwa da Ali eh ce amsar tambayar. “Amman ta wace siga kai mata maganar?” Talba ya watsa masa wani banzan kallo. “Kamar wani karamin yaro zaka tambaye ni wace Siga nai mata maganar?” “No baka gane ba ne Talba, su fa mata yan lalabawa ne, kai kuma sai kace komai da karfi da isa zaka yi ba haka ake ba” Talba ya watsa masa wani kallo. “Okay kamar ba baka san ni ba kenan? So kake na je na same ta ina lallashinta ta aure ni?” “No kai baka gane ba, Talba wannan lokacin ya wuce da zaka dinga tirsasa mace ta yi maka abu any how, na san Leila tana sonka amman kai din ne wani iri” “Kai Ali duk fa mace da zan aura alfarma zan mata, ba dai ita ta min ba, ina da kudi ina da kyau ina da ilmi ina da addinin da har a kasar waje za a iya bani aure balle a nigeria a nigeria ma a gidanmu” “Ka ga matsalar ka ba, wani irin alfarma tun da har kuna son junanku? Kar fa ka manta Talba Leila a waje tai karatu kuma wayayyiyar mace ce mai son burgewa, Talba dan kalaman nan na soyayya baka san kai mata ba, dan morning text din baka tura mata, balle har ka kirata ku yi fira, ko ka dauke ta ku fita, mata suna son wannan” “Ba zan yi ba, ina namiji zan wani zan wani rika lallaba mace, idan ma zan mata sai an yi aure, amman ba a yanzu ba ai sai ta raina ni, besides muna gida daya zan rika mata haka?” “To miye a ciki, ai an san aurenta zaka yi tun da an muku baiko, kai komai sai kace na zafi zaka yi, idan ka sake mata ba shi yake nufin ka bata umarni ta ki bi ba, dan Allah ka kirata yanzu ka bata hakuri” Kamar wanda aka cewa cire ranka ka bata haka Talba yai ma Ali wani irin kallo na mamaki da tsoro a lokaci daya. “Ni Mu'azzam Auwal Shimkafi zan kira mace na ce dan Allah ki yi hakuri? Macen da ba uwata ba? Malam dan Allah fitar min a mota” “Talba mata fa sai da haka, kuma ka canja hali dan Allah” “Ita ma ai bata iya kalaman soyayya ba, bata san ta kira ni ta gaishe ni ba ko ta turon sakon soyayya, kai ni bana jin ma akwai ranar da Leila ta taba kallona tace kana da kyau simple word bata taba fada min ba, sai ni zan fada mata? Ba yi wannan macen da zan zauna ina bude mata sirrin zuciyata ba har ina rarrashinta” “Wannan ji da kan babu inda zai kaika Talba, idan ka sake mata ka nuna mata kauna dole ita ma zata sauko fa” “Malam na ce ka fitar min a mota...!” Yanayin yadda yai maganar ya isa ya sanar masa ba da wasa yake ba, kuma ya san halin abokinsa idan ransa ya bace baya jin rarrashin sai dai hakan ba zai hana anjima ya kira shi yace yana son wani abu ba ko kuma su gadu a guri kaza. Salun alum ya bude motar ya fita yana murmushi da mamakin irin halin Talba. “Ina fada maka matsalata kana wani kokarin ba ni laifi, an fada maka mata haka ake musu ne!” Magana yake da kansa yana tukin cikin bacin rai, domin be san inda zai je ba a yanzu kasancewar yau weekend kuma gashi safiya ce be ma karya ba. @12:44pm Leila na zaune tool din mirror Momy tana zana mata abun da ya faru. “Kawai sakonsa na gani a wayata wai na fito waje yana son magana da ni, Momy babu ko irin shaukin nan Wai Ke fito waje ina son magana da ke, haka dai na daure na fita, na same shi a balcony ya kusan 30 be ce min komai ba, sannan wai ki yi fixing date na auren mu, Imaging babu ko dan shauki sai wani ji da kai” “Ke kuma kika ce masa me?” Momy ta tambaya tana harararta. “Na ce nasa ba zan yi ba, ni ban tashi aure yanzu ba” “Ki ba shi hakuri” Ta kalli Momy kamar tai magana sai dai ganin babu wasa a fuskar Momy yasa ta mike tsaye ba tare da tace komai ba ta fice daga dakin cike da bacin rai. Dakinta ta shiga ta dauki key din motarta da jakarta da wayarta, ta fito babu mayafi ta sauko kasa kamar zata tashi sama, daman ta saba fita babu mayafi abu ne mai wahala ka ganta da mayafi a jiki komai kankantarsa. Tana fitowa ta nufi gurin da motarta take ta bude ta shiga tai yi warming dinta sannan ta danna horn da karfi mai gadin na ganin hakan yai saurin bude mata gate. Kamar wata mai gasar tsere haka ta fito daga cikin gidan da mugun gudu ta hau titi tana jin kamar ta fasa ihu. Sai da tai nisa sannan ta dauki wayarta ta kira Adam. “Besty kana ina?” “Ina gida ya akai? Kamar kina cikin damuwa” “Ina ciki besty mun yi fada da Talba?” “Mtssss wai me ke damun Talba ne?” “Ina na sani, ban san abun da yake takama da shi ba, indai kudi ne ni ma ina da su, ilmin ina da shi kyau ba za a min gori ba, amman sai wani nuna isa da ji da kai” “Wallahi kam yan kalaman soyayya ma ace ba zaka iya yi ma mace ba, idan an yi auren ya kenan?” “Shine abun da nake magana a kai, ni kuma sai na nuna masa ina da tsada ni ba kamar sauran mata ba ne, dole na ja masa aji, yadda yake jin ba zai iya min kalaman soyayya ba ko ya dauke ni mu fita ko ba ni hakuri haka ni ma ba zan taba yi masa ba” “Hakan shi ne daidai, kara ya san darajarki a dole ya sauko idan yana sonki” “Shine ai, shi kawai abunda ya dauki mace ya mata umarni ta bi ya juyata yadda yake so, ni kuma sai na nuna masa na fi karfin haka Wallahi” “Yanzu dai kwantar da hankalinki ki samu ruwa ki sha, ki fita waje ki sha iska zan zo na dauke ki mu fita” “Har na ma fito gida amman bari na koma” “Okay but ki yi murmushi pls” Ta yi murmushin mai sauti kamar yadda ya bukata, sannan ta aje wayar, ta juya ta koma inda ta fito. Kamar yadda ta fito haka ta koma gidan da gudunta ba da damuwa da titi ko sauran motoci burinta dai ta aikawatar da abun da take so. Horn biyu tai kamin tai na uku Mai gadin ya bude mata gate ta shiga cikin gidan da mugun gudu ta faka motar a inda ranta ya so ta fito ta nufi kofar falon, door bell ta danna da karfi kamar zata balla shi sannan taja ta tsaya tana tsaki, shiru ba a bude ba har sai da ta sake danna door bell din sau biyu ta hada da knocking. Sannan Baaba ta bude mata. “Wallahi tallahi kika sake barina a tsaye a waje ina knocking, abincin ki ya kare a gidan nan Baaba” “Wanke wanke nake yi Leila shiyasa” “Na dai fada miki” Ta fada cikin tsawa, ba dan Baaba ta yi saurin kaucewa ba da Leila tureta zata yi ta wuce. Baaba ta maida kofar ta rufe sannan ta juyo cikin falon cikin rashin jindadi zata koma Kitchen din sai ta ji muryar Momy dake tsaye stairs. “Baaba a rika kula mun dauke ku aiki ne kawai saboda mu huta, a daina batawa yarana rai” Baaba ta daga kai ta kalli Momy sannan ta daga mata kai cikin da ladabi. “To Hajiya Inshallahu za a kiyaye” Sannan ta sadda kanta kasa ta nufi kitchen din cikin rashin kuzari. FARUQ POV. Kallonta ya tsaya yi da dayan biyu kamin ya amsa gaisuwar da tai masa, domin ba kasafai take gaishe shi da safe ba sai idan tana son wani abun ko kuma ta lura aljihunsa da dan nauyi. “Lafiya Kalau an tashi lafiya?” “Alhamdulillah, sai yunwa da nake ta ji tun jiya” “Toh Allah ya buda mana kofafin samu” “Amin...” Ta amsa tana kallon Sultan dake motsawa alamar zai farka daga bachin da yake. “Na ce wai ba zaka kira abokin nan naka ba, ka roki shi dan wani abu?” Ya girgiza mata alamar aa. “Ba zan dauna kullum ina bin abokai ina rokonsu ba, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abun da zai ci ba, kuma ni ma na yi karatun idan mu kai hakuri komai zai wuce” “Matsalar kenan Faruk girman kai, kana da girman kai, yanzu haka zamu zauna mu wuni da yunwa gashi idan ka fita baka dawowa sai dare? Ga ni da ciki ga Sultan?” Yayi shiru yana jin yadda kansa yake sara masa saboda maganganun da Baturiya ta fara masa. “Shiyasa na ce zubar da cikin nan zan yi na huta, kai ma ka huta domin na san ko ragon suna da wahala a samu a yanka masa wannan bakin talaucin da muke fama da shi” Ta fada cikin kukanta na munafurci. Sai ya kalleta a raunane. “Zubar da ciki ba zai kawo mana Mafita ba Rafi'a miyasa ba ki da tunani ne wai?” “To ni dai gaskiya yunwa nake ji, tun jiya fa ban ci komai ba, kuma anjima na nan ga Sultan ma” Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya mike tsaye ya fice daga dakin cike da damuwa. Binsa tai da harara. “Ni dai Wallahi na gaji da wannan bakar rayuwa, Allah kadai ya san yadda masu kudi suke ji, su kwanta a mai kyau a ci abun da ake so, ni ko na kare a nan duk kyau na” Ta fada tana mikewa tsaye tare da bin bayansa, sai da ta tabbatar ya fita sannan ta dawo ta dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta kamo number da tai saving jiya. Maryam Dahiru Sokoto ta aika mata kira, ringing tai har ta tsinke ba a daga ba ta sake kira nan ma ba a daga ba. “Ka ji yan gayu sai ayi ta kira basa dagawa...” Whatsapp dinta ta bude ta shiga gurin numbers ta kamo number wanda ke dauki da hoton wani matashin da ba zai wuce sa'an mijinta hakimce cikin mota. Sai da ta gama kallon hoton sannan ta shiga aika masa sako. ‘Assalamu Alaikum, ranka ya dade fatar an tashi lafiya, ya aiki ya Madam da yara. Ranka ya dade sunana Fee'ah matar Faruq abokinka, na kira baka daga ba shiyasa na yanke shawarar turo maka sako. Wallahi muna ciki matsala, yau kusan kwana nan mu hudu ba mu girka komai ba, shi ma idan ya fita haka yake dawowa saboda shagon da aka bude sabon gurin ne cikin wata sabuwar unguwa ba kowa yake ta aski ba, yanzu haka Sultan kuka yake, ni kaina dauriya kawai nai saboda da na, Dan Allah ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka, na duba na ga a cikin abokan Faruk babu mai tausayinsa da son taimaka masa irinka, na so Faruq yai maka magana da kansa amman yace nauyi yake ji, yanzu haka be san na dauki number ka ba, domin idan ya sani ina ciki matsala. Ka huta lafiya Allah kara rufa asiri’ A rarrabe ta tura sakon har tana gadawa da emoji din rokon da kuka. Sannan ta duba last seen dinsa tun jiya da dare, tana jin motsin turo kofar gidan tai saurin aje wayar ta kwanta kasa. Faruq ne ya shigo dakin rike da bakar leda har biyu a hannunsa. Ya aje mata dayar a gabanta ganin hakan yasa ta tashi zaune tana kallon 200 dari biyun da ya mika mata. “Ina ka samo?” “Ke dai ka bar” “Dan girman Allah Faruq ka daina mana cin bashi kana kara mana kanskanci a unguwa kamar kan mu farau talauci” “Ba bashi na ci ba wayata na bashi jingina” Bata ce komai ba ta karbi dari biyu kana ta bude ledar tana duba taliya da makaroni dake ciki sai maggi da mangyada. “To wannan ledar fa?” “Mama zan kaiwa” Yana fadar hakan ya juya ya kalli dansa dake sharar bachi sannan ya fice ba dan ranta ya so ba. “Mu ba mu wadatu ba amman sai dauka ka kaiwa wasu, mtchhhh” Ta karasa tana jan tsaki. “Kuma Wallahi sai na zubar da cikin nan haka kawai zan zauna ga talauci ga wahala da kurciyata da kyauna” Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki ledar taliyar ta fito waje domin sarrafawa. Kallo daya zaka masa ka karanci damuwarsa abubuwan duniya sun taru sun masa turr kamar ya zagi arziki kamar komai yake juye masa, gashi yayi degree amman aiki ya gagara duk inda yai applying shiru ba wani motsi. Da tunani kala kala mai achaba ya sauke shi unguwar Dallatu wato gidan mahaifiyarsa, sai ta ciro naira dari a mika masa sannan ya ratsa cikin gidanje har ya isa kofar gidan ya tura ya shiga da sallamarsa. Kanensu biyu mata da suke tsakar gidan suka amsa masa suna masa sannu da zuwa, bayan ya amsa musu ya nufi dakin Mahaifiyarsa ba karamin faduwa gabansa yai ba ganinta a kwance domin ba al'adarta bace yawan kwanciya musamman a irin wannan lokacin. “Mama lafiya dai? Ko jikin ne?” “Da sauki ai Alhamdulillah” Ta amsa masa tana murmushin karfin hali. “Wani irin da sauki ga ki kwance? Kai Innalillahi Wa'inna illahirraji'un” Jin furuncinsa yasa ta yunkura ta tashi zaune tana kallonsa. “Ina Sultan?” Kasa amsawa yai sai kallon mahaifiyarsa yake, yana jin kamar ace yana arzikin da zai iya kaita Asibiti, domin ba yau ciwon ya fara ba. “Mama ko dai maganar auren Aisha da akai ne jiya ya tada miki hankali? Idan ma fasa aurenta zai yi ai ba wani abu ba ne zata samu wani” “Har aure nawa za'ayi ta fashi ne Faruq? Haka zamu ta zama ana fashin aure saboda talauci? Kuma yaran nan sai girma suke, sai gulma ake mana a unguwa” Ta tambaya idonta tab da hawaye, Faruq yayi saurin kawarda nasa idon yana sauke ajiyar zuciya, domin kukan mahaifiyarsa na daga cikin abun da ya fi tsana a rayuwarsa. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. https://www.wattpad.com/story/283871769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZCqcO2wXIv6pkkxIr3do4ng1%2BTHhzoVPTPFtpfDcb1ftHOVsldMflpG2lAwd5aYtrehJ12WEeerjWSVNDZunKAH9QpxhI0A%2BzJsYI6RrshbTOZsoLUXljeZDCPaDNtKr *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -3️⃣ Shigowar Daddy ne yasa Momy ta cire farin gilashin idonta tana murmushi. “Ranka ya dade an fito?” Kusa da Amal ya zauna yana murmushi. “Allah ya yarda” Ya fada yana karewa katon falon kallo ganin Momy ce kawai sai Khadija da kuma Kabir, abun da ba kasafai yake gani ba, ya saba every weekend yana zuwa falon Momy ya zauna tare da ita da kuma yaransa, kowa ya fadi bukatarsa ayi hira a bawa juna shawara, ayi nishadi. Sometimes kuma shi zai kira su a bangarensa a tare a can. “Daddy barka da wuni” “Yauwa, Son” Ya amsawa yana yi ma kowa kallon tsanaki, ciki har da yar autarsa Amal da ta wani hade rai. “Hajiya ya ga falon ku kadai? Ina sauran yarana suke?” Momy ta kalli Kabir dake kallonta sannan ta kalli Amal kamin tace komai Kabir ya tari numfashinta. “Daddy yaranka biyu fushi suke da juna, kasan Angry Birds ne” Daddy ya kalli Momy. “Since when?” Kabir zai sake magana Daddy ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, wanda hakan ke nuna kai tsaye Momy yake son ta amsa masa tambayarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya. “Ni ma dazun nan na sani...” A tsanake ta labarta masa abun da ya faru ciki har da fadan da tai ma Leila. “Amman baki fada min ba? Taya zaki bar Mu'az ya fita ba tare da yayi breakfast ba? And baki dama ki san a wane hali yake ba?” Momy ta lumshe ido ta bude tana murmushi. “Wani lokacin kana maida Talba kamar wani karamin yaro, ya san yadda zai kula da kansa Alhaji” “Ko da Mu'az zai shekara dari matukar ina raye to shi yaro ne a gurina, a shirya mana abincin rana tare” “An gama ranka ya dade” Ya mike tsaye sai Amal ta kalleshi. “Daddy ni ma fa kaga ina fushin nan amman baka ce komai ba” Sai a lokacin Daddy ya tuna da tana gefensa sai ya kalleta yana murmushi. “Amal sorry wata taba ki?” Ta nuna Kabir sai Kabir yai saurin daga hannayensa sama ya mike tsaye. “Na ma bar muku falon” Kamin Daddy yace komai ya nufi kofar fita daga falon da saurinsa yana murmushi. “Mu yi masa uzuri amman yau kawai next idan ya sake tsokanarki zamu raba gari da shi” Daddy ya fada yana kallon kyakkyawar yarsa. Sai ta sakar masa murmushi. “Toh Daddy” “Good” Cewar Daddy yana ciro wayarsa ya kira Talba, ringing daya yai picking kamar daman can kiran yake jira. “Hello Daddy” “Mu'az kana Ina?” Ya kalli katon office din da yake ciki kamar mai son tantance inda yake. “Office Daddy” “Me kake a office? Yau Weekend?” “I don't know...Getting some fresh air” “Baka fada min kana da damuwa ba, mu da kai ba abokai ba ne? Ba ma boyewa juna abu?” Wani irin kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya mike tsaye daga inda yake zaune ya nufi windows. “Daddy ba irin wannan ba you know dan crisis ne kadan” Daddy ya tabe baki yana juya fuska kamar  Talba na gabansa. “Uhm.. Ka dawo gida yanzu zamu yi lunch tare” “Okay Daddy Allah kara maka lafiya, i love you” Daddy yayi murmushi ba tare da yace komai ba ya sauke wayar, sannan ya nufi wata kofa a dayan bangaren falon wanda zata sadashi da bangarensa. “Ita Leila ba ya bace kenan? Da ba zaka kirata ka tambayi inda take ba?” Daf da zai wuce Momy ta yi wannan maganar sai ya juyo ya kalleta, sannan ya dauke kai ya bude kofar ya fice. Sai da ya rufe kofar sannan Momy ta tabe baki ta kai hannunta ta dauki wayarta ta kira Leila, sai da wayar ta kusa yankewa sannan Leila ta daga. “Leila kina ina?” “Gidansu Madina” Ta amsa murya can ciki. “Ki dawo da wuri, and make sure kin ci abinci” “To Momy” Momy ta sauke wayar sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen. Misalin 2:30pm Talba ya daka motarsa harabar Daddy, ya fito ya nufi bangarensa kai tsaye hannayensa duka biyu zube a alhaji, tafiya yake kamar wanda baya son shiga bangaren, haka yake idan yana fushi be cika son ya rabi mutane ba ko kuma mutane su rabe shi, a tunaninsa tare da kowa zasu ci abinci, domin Daddy ya saba zuwa bangaren Momy ya zauna a ci abinci rana tare ko na dare wani lokacin har da na safe, sai dai yana yin haka ne kawai ranar kun Assabar da Lahadi. Domin ranar weekend ba ya fita ko'ina sai idan fitar mai dalili ce kamar daurin aure ko wani abun, wannan al'adar ba shi kadai ba har yaransa sun saba da ita, every weekend zaka samu kowa a gida sai mai dalilin fita yake fita. Ya samu kusan dakika 40 zuwa 50 sannan ya danna door bell din kofar falon Daddy, babu bata lokaci Amal ta bude masa kofar. “Ya Talba” “Lil Sis... Waye da waye a ciki?” “Just me and Daddy” Ya sakar mata murmushi sannan ta shiga cikin falon, tun da ya hango dinning din babu komai a kai ya tabbatar daga shi sai Daddy za su ci abincin. Kai tsaye ya wuce karamin Falon Daddy inda ya saba zama. Yana shiga ya samu Daddy zaune saman kujera yana amsa waya, sai ya zauna a inda aka jera manyan kuloli ya dauki plate biyu ya zubawa Daddy shimkafa, ya zubawa kansa a dayan plate din sannan ya bude miyar dake ta kamshin naman kaji ya zuba ma kansa kadan domin ba ya son miya tai yawa a abinci ya zubawa Daddy ta jera kofuna biyu ta zuba musu lemu ya hada komai sannan ya dauki na Daddy ya dora masa a dan karamin center table dake gefen kujera da Daddy yake kai. Sannan ya koma ya dauko na shi ya dawo kusa da Daddy ya zauna a kasa, ya soma cin abinsa yana kallon katuwar plasma dake karamin falon, Bayan Daddy ya gama wayarsa ya kalli Talba. “Na lura har yanzu baka san ka girma ba Mu'az, ya kamata ka koyi hakuri da iya danne fushi, idan ina kiranka na damu da inda kake, wata rana bana nan, domin akwai rayuwa akwai mutuwa, na san kana kokarin ganin ka kawarda damuwa a zuciyar wasu musamman yan'uwanka, amman kai baka san yadda zaka yi ka cire kanka a damuwa ba, sai dai ka karawa kanka” Talba ya dakatar da cin abinci da yake yana sauraren Daddy ba tare da ya kalleshi ba. “Ka daina fushi da abinci idan ranka ya bace, And su mata ba a fushi da su, lallabasu ake, idan ka san wahalar da na sha kamin ya auri Amina sai ka ji ka tsani matar nan, amman haka na daure dan marayan Allah da ni har Allah ya ba ni ita” Talba ya kalli Daddy yana murmushi mai sauki. “Haba Daddy” Daddy ya kalleshi yana dariya. “I'm telling you my friend” Daddy ya kai hannunss ya fara cin abinci. “So haka zaka yi hakuri kai ta lallabata, mata soyayya suke so da kulawa, no matter how rich they are, anya ma kana kiranta da safe ka ji ya ta tashi? Like hello Baby how was your night?” Talba ya saka dariya sosai har yana kwantawa jikin kujerar dake bayansa. Daddy ma Murmushi yai. “Yes... Gida daya muke da Hajiya kuma a guri daya muke kwana amman kana gani kullum sai na gaishe, ni ban san abun da yake damun ku yaran yanzu ba, mu a da kunya da rashin wayewar addini ya saka iyayenmu da mu kanmu ba su yi wasu abubuwan na more rayuwar aure ba, amman ku a yanzu ga ilmin addini da na zamani a arha ga wayewa amman kuke ta zaman matsalar zamantakewar aure, ban san miye matsalar matasan yanzu ba” “So that's mean nine mai laifi kenan?” “Kai ne mana, taya zaka samu mace kai tsaye da irin wannan maganar, bana jin yadda kake zaunawa kai hira da ni kana yi da ita ma, kawai kai gaka boss, gaskiya you're not romantic at all” Daddy ya karasa yana wani yatsina fuska, wannan karon dariya sosai Talba yai har muryarsa tana fita kamar ba shi ba, dariyarsa ce ta saka Daddy murmushi mai sauti. “Trust idan baka canja ba, za a iya kasa ka” Ya daga kafadunsa alamar be damu ba. “Then ai zan samu wata da gudu ma” “Hakan na nufin ba wani son Leila kake ba, because idan kana son ta you won't said that” Ya dan yi shiru kamar mai nazari. “No i love her Daddy kawai dai ina sonta, but i won't tolerate nonsense” Daddy yayi Murmushi yana dafa kafardarsa. “Idan so ya zurfafa a zuciyarka, baka san lokacin da za ayi maka nonsense ba kuma ka dauka, a lokacin zaka zama wani stupid, fool, za a fada maka baka ga tana maka kaza ba, kace ka ji amman kana sonta ba zaka taba ganin laifin abun da take maka ba, mark my words” Talba yayi murmushi irin murmushin nan dake nuna ban yarda ba, ranar ma ba zata zo ba. “Yanzu ka gama cin abinci kaje ka samu Leila duk inda take ka dauko ta ka dawo da ita gida, kuma ka bata hakuri” “No no no Daddy kasan ni bana ba wanda yake kasa da ni hakuri” “Ba sai kace mata sorry abun da nai ban kyauta ba, no ka mata abun da zata ji farinciki sai ta manta da komai simple” Ya dan yi jimm yana jin kamar an dora masa katon aiki. ‘Maybe i can try’ Ya fada a ransa a fili kuma sai ya amsawa Daddy da. “Okay Daddy, for the sake of you” Daddy yayi murmushi yana jinjina lamarin dansa. FARUQ POV. A gidan Mahaifiyarsa yai wanka sannan ya fito ya nufi gurin abokinsa, dake unguwar. He got lucky yana gida, yana sallama masa ya fito, bayan sun gaisa Faruq ya gabatar masa da abunda ke tafe da shi. “Shamsu, na zo neman wata alfarma ne a gurinka” “Allah yasa zan iya Faruq” Faruq ya busar da iskar bakinsa. “Wallahi ina cikin matsaloli ba ma daya ba, kasan matsalar kasar nan, mutum zai yi karatu amman aiki shiru, ga dan shagon da na kama sabuwar unguwa ce ba mutane sosai” “Wallahi kasar ce har ka rasa yadda zaka misalta ta, abubuwan sai a hankali, idan baka yi karatu ba abun ya dame ka idan kuma ka yi aikin ya gagara” “Shine nake son na fara koyon irin sana'arku, duk da ba iyawa nai ba amman dai idan nayi tare zan iya da yarda Allah” Shamsu ya masa wani kallo na mamaki, a tunaninsa zai ranci kudi ne a hannunsa, sai ya ji yana masa maganar sana'arsu, ba Shamsu kadai ba kusan duk wanda ya ji mutum mai degree zai yi sana'ar gini zai yi mamaki, domin muna a zamanin da masu degree da kuma mutane suke ganin ba ko wane irin aiki ne ya dace da su ba, wani abun ana ganinsa kamar kaskanci ne, ace kana da degree kuma kai yi shi. “Faruq zaka iya sana'ar gini kuwa? Kai da kai karatu? Kuma jikinka be saba da aikin wahala ba” “Shamsu kenan, wanda ya tashi a area kamar wannan kuma dan talaka zai ce be saba da aikin wahala ba? Ya kake magana kamar ba san gidan da na fito ba?” “To abun ne da mamaki Faruq naga kai ka yi karatu ka ni ban yi karatun ba” “Ka aje komai a gefe ka duba bukatata idan zai yiyu” “Inshallahu, sai dai ka san aikin mu tasowa yake ba wai kullum ba ne sai idan ta samu, inshallahu da mun samu zan kiraka a waya tun da ina da number ka” “To na gode sosai sai na jika” Ya mika masa hannu sukai musabaha, Shamsu ya koma cikin gidansa cike da mamaki, Faruq kuma ya nufi titi cike da damuwa. FEE'AH POV. “Gaskiya kina da kyau sosai” “Thanks” Shine reply din da tai ma mutumen da facebook bayan ta tura masa hotunanta masu kyau, kamar yadda ya bukata. “A ina kike da zama a Gusau?” Wannan karon tashi tai zaune tana tunanin irin karyar da zata masa, domin bata fada masa cewar tana da aure ba, duk kuwa da kasancewar bata dora hotonta a profile picture ba, sai hoton sunan Allah data saka as her profile picture dinta. “Gida dari” Ta bashi amsa. “Na san gurin idan na shigo zamfara inshallahu zan neme ki mu gaisa” “To Allah ya nuna mana” Ta bashi amsa tana murmushi, kamin ta sake shiga profile dinsa ta duba komai nasa, ciki har da gurin da yake aiki da kuma hotunansa, kana ganinsa ka ga wani hamshakin mai kudi mai connection da yan siyasa, domin yadda ake masa fadanci a profile ma ya isa ya sanar da hakan. Murmushi ta sake yi sannan ta dawo inbox din ta duba tambayar da yai mata ta biyu. “Are you on whatsapp?” “Yeah” Ta bashi amsa da sauri tare da rubuta masa number wayarta ta tura masa. “Okay Thank You so much Baturiya” Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana jin sunan har cikin ranta. Sannan ta fita facebook din ta shiga whatsapp, few massage ta samu ciki har da reply din da MD Saleh yai mata, shi ta fara budewa da sauri jikinta har rawa yake kamin ta gama karantawa. “Subhanallahi, Allah ya wadata, turo account number dinki” Mikewa tai tsaye ta daka wani uban tsalle ta dire tsabar murna da jindadi sannan ta tura masa account din tana masa godiya. “Alhamdulillah” Ta furta sannan ta shiga group chat dinsu na makaranta, ta fita ta leka na matan aure ta fita ta shiga na novels nan ma bata dade ba ta fita ta bude chat din Ramlee. “Kawata kin yi ciniki, wani ya ga Hotonki a wayata ya matsa na nemo masa ke” Tana gama karanta sakon kawarta Ramlee ta zaro ido tare da sakin baki a lokaci daya, domin ta san sana'ar kawarta, tana da connection da manyan masu kudi tana hada su da mata kyakkyawa kuma masu siga kamar yadda ita ma take hulda da su, sai dai duk iskanci Baturiya bata taba aikata alfasha ba, za dai hadu da mutum har su gaisa ko kuma ta yi masa nata wayon ta waya ta samu yan canji, amman bata san tai mu'alama da maza ba, bayan Faruq babu wanda ya taba saninta a ya mace. “Gaskiya aa Ramlee ni dai ina jin tsoro ba zan iya ba, amman idan kin san irin wanda zan yi ma wayo ne na ci kudinsa ba sai mun hadu ba, ba matsala” Ta mayar mata da amsa duk da kasancewar Ramlee tana Offline a lokacin, sannan ta kashe datan ta aje wayar ta mike tsaye ta fito waje. “Sultan zo nan yau zamu ci kaza” Ta fada tana zaunawa jikin kofar falon tana mikawa danta hannu fuskarta cike da murmushi kamar yadda zuciyarta take fal da farinciki saboda kudin da za a turo mata, Sultan din ya rugo da gudunsa yana murna. “Abba zai siyo mana ne” Ta shiga kabe masa riga tana fadin. “Ba nace ka daina cewa Abba ba? Ka rika cewa Daddy, yayan talakawa ne suke cewa Baba ko Abba, yaran masu kudi kuma su ce Daddy ka ji?” “To Daddy ne zai siyo mana?” “Aa adashen zan kwasa yau sai na siyo mana, amman karka fadawa Daddy ka kaji? Har da lemun kwalba zan siyo mana” Sultan din ya shiga murna yana jindadi yau za su ci kaji, rabon da su ci nama har ya manta. AMINATU POV. A bakin kofar shiga gidansu ta hadu da Sanusi tsaye yana latsar karamar wayarsa. “Ya Sanusi” Ya kalleta sai kuma yai dariya. “Igee ai sai ki fada mana cewar kin fara fita zance, mu shirya yi miki aure” Ta cinno baki gaba. “Ni dai dan Allah ka daina, Allah yasa ba ka fadawa Inna ba ko Baba” “Ban fada ba, amman dai zan fada masa, Baba ma baya nan” “Ina yaje?” “Gwaggo ta Makka aka aiko bata da lafiya sosai, shi ne suka je tare da Junaidu a babur” “Yanzu?” “No tun dazun” “Allah ya bata lafiya shi kuma ya dawo da ita lafiya” “Inna tace naje na dubo ki, idan kin shiga ki ce ni na zo da ke” “Wallahi ba zan fada ba” Ta fada tana nufar cikin gidan. “Ni kuma zan fada mata cewar kin yi saurayi” “To na bari” Ta yi saurin fada har tana dawowa baya, sai ya saka dariya ya biyo bayan kanwarsa suka shiga cikin gidan tare. Kamar Kullum inna na zaune tsakar gidan tana jiran dawowarta, domin bata bachi sai ta saka yarta a ido. “Oyoyo Auta yar albarka, an siyar ko?” Aminatu ta aje kwallon tuwon da bokitin miyar da plates din roba a gaban ina tana sauke gajiya. “Eh Inna wai Baba ya tafi gurin Gwaggo?” “Eh an aiko bata da lafiya, aka ce mai rabon ganawa da ita ya zo” “Allah ya bata lafiya” Ta fada cike da damuwa, sannan ta ciro kudin cinikin ta mikawa Inna, sai da Inna ta kirga kudi ta ga sun cika sannan ta cire wadanda ta saba bata tana sakawa a asusu ta mika mata. “Ga na ki” “Na gode” Ta fada bayan ta karba tana kallon Sanusi zuciyarta sai raya mata take zai fadawa Inna maganar, sai har sukai yar hira da zasu yi suka gama bata ci ya dauko zance ba, hakan yasa ta ji dadi sosai. Bata bude wasikar da Maniru ya bata, da fitilar da take zuwa talla ta haska wasikar da ya rubuto mata da hausar ajami, tana karantawa sai murmushi take tana jindadin yadda ya jera mata kalaman soyayya da kwantar da hankali. Bayan ta gama karantawa ta rumgume wasikar a kirjinta, can kuma ta tashi ta saka a cikin littafanta na Islamiya kamar yadda ta saba, sannan ta gyara gurin kwanciyarta ta kwanta. Inna kam bata kwanta ba sai da ta gama komai ta kintsa komai kamar yadda ta saba sannan ta kwanta tare da rage fitilar kwai dake dakin, hasken ya rago sai dai bata kashe gaba daya ba saboda Aminatu na tsoron duhu sosai, bata bachi babu fitila a kusa da ita. Misalin 12am gidan yayi tsit domin kowa ya nemi gurin kwanciya ciki har da yan awaki da tumakin da ake kiwo, can cikin bachi Inna ta soma jiyo hayaniya, tare da karar babura hakan yasa ta ta tashi zaune tana sauraren jikinta na bata ba lafiya ba, domin kowa ya san matsalar kasar a yanzu, balle kuma su da suke kauye. Aminatu kam sharar bachinta kawai take bata ma san ana yi ba, jin ihu da kuma fadar Innalillahi a makota yasa Inna ta nufi inda Aminatu take ta shiga tashinta. “Auta Auta” Ta fada murya can kasa kasa, a hankali Aminatu ta bude ido ganin Inna yasa ta tashi zaune. “Inna...” “Shiiiii” Inna ta mata alama da tai shiru. Wanda hakan yai daidai da banko kofar gidan ta kwano a shigo, ga wata uwar fitila mai shegen haske da suke ta hasken gidan da ita. “Innalillahi Wa'inna illahirraji'un” Inna ta furta gabanta na bugawa da mugun karfi, Aminatu ta mike tsaye da sauri kamar wanda ta rude, Inna ta shiga duba dakin tana jin kamar ace akwai wata hanya da zata bi ta fita, a rikice ta nufi gadonta. “Shiga nan Auta shiga shiga” Da sauri Aminatu ta nufi karkashin gadon na karfe ta shige, zuciyarta na wani irin zillo kamar zata fito, Inna ta nufi kofa domin duba sauran yayanta sai dai kamin ta isa kofar suka shuri kofar da mugun karfi ta cire suka shigo cikin dakin kamar an aikosu. Baya baya Inna tai tana fadin. “Innalillahi Wa'inna illahirraji'u” “Rufe mana baki dan ubanki” Yanayin yadda yai maganar da karayar halshe kadai ya isa ya sanar da cewar gayu ne suka hauro garin a yau, wato bandits abun da ba a taba ba, domin duk wani hargitsi da ake fama da shi sai dai su ji a makotan kauyukan ko kuma a hanya abun ya rutsa da yan garin, amman ba a taba shigowa cikin garin ba. Ba Inna kadai ba har Aminatu dake karkashin gado sai da ta saka hannayenta ta rufe bakinta. Ta ko'ina jikin Inna rawa yake, ganin manyan makaman da ke hannunsu. “Ina mijikin yake?” Kasa magana tai bakinta sai rawa yake kamar jikinta ga wani gumi dake karyo mata. “Wato ke ce uwar yaran ga yan iska ko?” Nan ma Inna kasa cewa komai tai sai ambaton Allah take a zuciyarta, hannayenta duka biyu rike da bakinta. “Innalillahi” Inna ta jiyo muryar yayanta a tsakar gidan, wani irin abu ne ya ziyarci zuciyarta sai ta ji kamar ace akwai abun da zata iya yi ta ceci yaranta. Dun dun dun ta ji tashin bindiga kamin ta tantance komai ta ji muryar Sanusi yana kuka. “Wayyo Allah na, la'ilaha illahu, Innalillahi” A lokacin ne hawaye ya cika idonta, irin hawayen da kowace uwa take yi idan ta kasa taimakon yayanta. “Wayyo” Ta jiyo ihun matar Amadu, bata san da inda kuzari ya zo mata ba har ta iya tambayarsu kamar ta rikice. “Me muka muku?” “Tambaya ma kike? Ba kun aje yan sakai a gidanku ba, wai masu yaya ko? To yau sai mun kashe su sai mun muku wulakanci” Inna ta hade hannayenta biyu tana kuka tana rokonsu. “Ku dubu girman Allah ku yi hakuri, ku kashe ni kar ku kashe yarana dan Allah...” Bata gama rokon ba, wani ya karaso kusa da ita ta fisgi rigar jikinta. “Cire wannan rigar ai har ke da kike uwarsu ba zamu bari ba” Sai a lokacin Inna ta kara firgicewa, ta fara bin fuskokinsu da kallo tana ganin komai kamar a mafarki. “Cire cire” Sai ta rika jin kamar ba hausa suke mata ba, gaba daya ta rasa gane abun da suke nufi, bata fahimci manufarsu ba har sai da suka barge rigar dake jikinta suka kama zanen shi na suka fisge suka jefar da shi can gefe, suka mata tsirara a gabansu. Aminatu dake karkashin gado ta yi saurin kara rufe bakinta wasu irin zafafa hawaye na sauko mata, saurin rumtse ido rai hango mahaifiyarta tsirara a kwance yaron da be wuce sa'ar danta na biyar ba ya fara keta mata haddi!! Ba mutum daya yai ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, haka suka jera su goma sha daya suka yi mata yadda suke so, sannan suka fita suka barta kwance kamar tsumma. Abun ka da uwa suna fita ta yi karfin halin rarafawa ta isa inda zanenta yake da idanuwan da take jin kamar kukanta ya kare a yau. Ta dauki zanen da hannunta amman yadda zata sarrafashi ta daura ta suturta jikinta ne ta manta sakamon jin ihun Sanusi, cikin rashin kuzari zuci da na jiki ta isa jikin kofar tana kallon yadda yan bidigar majiya karfi, suka danne Rilwanu a kasa, dayansu ya kunna babur dinsa ya hau ta kan wuyansa ya tsaya. “La'ilaha Illahu” Inna ta fada da wata irin muryar da bata taba sanin tana da ita ba, tana mika musu hannu. Ba su kulata balle su fasa abun da suke, ba su saukar da babur din a wuyansa ba sai da suka tabbatar ransa ya rabu da gangar jikinsa, daman haka suke ma irin su Rilwanu masu aikin sa-kai domin kare rayuwarsu da kuma ta al'ummarsu, idan suka halbeka da bingida suka ga bata tashi ba, sai su gwada adda, idan ita ma ba tai ba sai su saka dutse ko babur. Bayan sun kashe Rilwanu suka fashe rumbun hantsen dake gidan suka saka Iro a ciki suka kunna masa wuta, tare da hatsin. Wani irin ihu yake yana neman ceto amman babu wanda zai iya kawo masa dauki. “Kaico Kaico kaico” Inna ta fada tana kallon yadda danta ke ci da wuta, ga kuma wani a kwance, wani irin shiga da fita numfashinta ya rika yi da karfi, tana jin wani abu na mata yawo a ciki, gaba daya sai ta nemi dan sauran kuzarin nata ta rasa, a bakin kofar ta fadi kwance yawu da majina suna zubo mata a lokaci daya, cikin karfin hali ta dan dago kanta ta juyo ta kalli Inna Aminatu take boye, sannan ta juya tana kallon yadda suka dauko katon dutse suka daga sama suka saki a akan Amadu da yake da wasu barayin suka danne a kasa ko motsi baya iya yi, kamar yadda sukai ma Amadu haka wadancan barayin da suka zagaya gidan Musa suka masa, domin duk wanda ya san yayan Mai Damma ya san wuka ko bindiga bata hudasu, ya sha kuma ba bawa yaransa, ba dan komai ba sai dan kariyar irin wannan ranar, sai dai ayau shan be amfana musu komai ba, ba su kadai ba har da sauran mazan gari da bindiga bata fasawa, sukan kashe su da babur ko dutse, balle kuma Rilwanu da Iro da sukai kwarin suna a garin saboda aikin sa-kai da suke. Sanusi kam sai yai kamar ya mutum ganin nasa mai sauki ne, domin da babur sauka hau kafarsa dan kawai su gana masa azaba, baya ambatar komai sai Allah, ba a gidan Mai Damma kadai ba, a garin gaba daya haka suka ci suka shude babu wanda ya kawo agaji, suka ci karensu babu babbaka yadda ransu ya so sannan suka bar garin bayan su kwashi abinci da mata cikin har da matan Musa da matar Amadu. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai. Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. I just published "04" of my story "BAKAR WASIKA". https://www.wattpad.com/1188003519?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=gvBvvJY%2Brh7%2BfdxLjDxcLbTx9rDGdNBA0sMHgr3XMPr%2FqwZ4sIWJ88oZCr4nOa%2BILP0eBQ%2FKRLIQm73M62araHO6%2BoJXjoYprLv7YGhRYyguc1ysae3vRDycS1qvuqiM *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -4️⃣ “So yanzu ka yarda zaka bata hakuri kenan” Talba ta girgiza kai. “Kai no never ni fa ba zan taba ba wanda yake kasa da ni hakuri ba” Ali ya kalleshi. “Amman ka ce Daddy yace laifinka ne, kuma kaje ka bata hakuri” Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa ya sauke numfashi a hankali. “Yeah ba wai yana nufin na ce tai hakuri ba, ni yanzu so nake ka kirata ka bata hakuri kuma ka dauke ta ku je yawo ta wayance Shikenan komai ya wuce, amman karka ce ni na ce ka bata hakuri fa” Ali ya rausayar da kai yana kallon abokin nasa cike da mamaki. “Miye a ciki dan kace tai hakuri? Ko kuma ka dauke ta kuje yawo, faduwa kai?” Sai Talba ya amsa masa kai tsaye. “Yes, taya zaka bawa mace hakuri macen ma wanda take kasa da kai, ni me fa Ali” “To wai idan kuka yi aure kuka samu matsala, kuma kai kake da laifi...” Kamin Ali ya karasa Talba ya tari numfashinsa. “Sai ta ba ni hakuri” Ta fada da iyakancin gaskiyarta, domin har ga Allah be ga dalilin da zai saka shi bawa wanda ke kasa da shi hakuri ba, kuma mace sai dai shi a ba shi. Ali yayi murmushi. “Yanzu dai for the sake of Daddy zaka yi” “For the sake of him na zo har ina rokonka da kai, idan ba haka ba babu abun da zai saka na roke ka ma” “Look Talba I'm not her boyfriend, ban san kalaman da zan mata ba, kuma ba ni nai mata laifin nan ba” Talba ya mike, ganin hakan yasa Ali ma ya mike tsaye. “Fine, amman tare za mu je, kana driving ina baya” Talba be ce masa uffan ba ya nufi kofar fita, wanda hakan ya tabbatarwa Ali cewar ya yarda kenan. Sai da Ali ya shiga yai sallama da Samira sannan ya fito ya samu Talba a cikin motarsa. A hankali Talba yake tukin har suka fita daga cikin gidan suka hau titi. “Kirata ka tambaye ta tana ina” Ali ya masa wani kallo. “Kiran ma? Talba wai kai zaka bata hakuri ko ni? Just ka kirata ka tambayi tana ina ma you can't?” Ko kallon gefen Ali Talba be yi ba balle ya tanka masa. “Fine” Ali ya fada sannan ya zaro wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number Amal, domin baya son batawa kansa lokaci tambayar Talba number ta zai iya ce masa baya da ita ma. Ringing biyu ta dauka. “Hello” “Hello Lil Sis ya kike?” Ta yi murmushi jin ya kiranta da sunan da Talba yake kiranta. “Na'am Ya Ali ina lafiya” “Good number Leila nake so” “Okay zan turo maka yanzu” “Thank You” Ya aje wayar yana kallon abokinsa tare da mamakin halinsa. In few minutes Amal ta turo masa number, a take ya kira Leila, abun ka da mai jin kai sai da wayar ta yi ringing ta katse bata daga ba, har sai da ya sake kira, wannan karon ma sai da ta kusan yankewa sannan ta daga kuma tai shiru tana sauraren mai kiran, daman can haka take babu yadda za'ayi ka kirata kuma ka yi expecting ita zata fara maka magana, sai da Ali ya saka wayar a speaker sannan ya fara magana. “Kanwata Leila kina lafiya?” Jin muryar Ali yasa ta dan sake domin ta san waye shi. “Ali ya weekend?” “Alhamdulillah kina ina?” “Ina gida dari gidansu Madina” “Okay gani nan zuwa” Be jira abun da zata ce ba, ya aje wayar ya kalli Talba. “Idan munje ta fito kai zan bata hakuri sannan na baku guri ku yi magana” Talba ya masa wani kallo irin really! *** *** *** Leila ta aje wayar tana tabe baki. “Waye?” Madina ta tambaya tana gyara kwanciyarta. “Ali wai gashi nan zuwa?” “To ko ya san abun da ya faru tsakaninku ne?” “Maybe ai Talba baya boye masa komai” “Kin gani na fada ya damu fa” “Ya damu amman be kira ni ya bani hakuri ko ya aiko min da sako ba? Ni I don't think Talba yana so Madina” “Yana son ki mana Leila” Madina ta fada sannan ta sauka saman gadon ta kama hannun Leila. “Zo nan let me show you something” Gaban madaubin dakin ta nufa da ita ta tsayar da ita gaban madubin. “Kalli kanki da kyau Leila ki fada min abun da kika rasa” Leila ta kurawa kanta ido a madabin tana kallon irin baiwar da Allah yai mata ta kyau daidai gwargwadon. “Kyau?” Madina ta tambaya sai Leila ta girgiza kai. “Kudi? Lafiya? Kima, gata ko kuma me?” “Ba ko daya” Leila ta amsa. “Kina da kyau da babu namijin da zaki yi tayin kanki ya ce miki aa ko waye shi kuwa, mahaifinki na da arziki da zai iya siya miki rai idan ana saidawa Leila, kina da kima, ga gata ta ko'ina, kuma duk wannan tarin baiwar da take tare da ke sai zuciyarki ta raya miki Talba baya son ki?” Leila ta juyo tana kallon Madina “Za ki iya fada min dalilin da ya saka yake min haka?” Madina ta yi murmushi ta koma saman gadon ta zauna. “Saboda Talba, na daya daga cikin irin mazajen nan masu matukar tsada da wahalar samu, kin ga duk wannan abubuwan da kike da su, Talba na da damar da zai iya cewa ba ya son ki idan har baya son ki, kuma ta zauna, domin kin san mutun ne da baya boye abu a ransa idan be masa ba, kuma babu wanda ya isa ya cilastashi, idan har baya son ki kai tsaye zai fada, amman be amsa cewar baya son ki ba ya amince” Leila ta dan yi sama da ido. “Haka ne but...” Madina ta tari numfashinta. “But Talba yana da matukar tsada Leila, Talba wani irin murdadden mutum ne mai wahala sha'ani, yadda kike takama da kyau yana da kyau, yana da dukiya, yana da duk wani abu da ake so a jikin namiji, yana da arzikin da yake jin zai iya tankwara komai yadda yake so, yana ganin tun da yana da komai dole a bi shi” “Shi ne matsalarsa ai” Leila ta fada tana zaunawa kusa da kawarta. “Yeah ya kasa yarda cewar akwai abun da kudi basa siye, a nan ne kawai yai kuskure” Leila ta yi murmushi. “Ni kuma zan gyara masa wannan kuskuren, sai na nuna masa banbanci da sauran mata, dole ne ya san cewar ina da kima da daraja, kuma dole ya koyi yadda zai yi rayuwa da ni, all those four years of dating, ni nake bashi hakuri ko da ni ce da gaskiya, ina binsa kamar wani sarki da baiwa, all those years ni nake masa text how are you, so so so this, idan ya bar kasar nan ni zan kira shi na tambayi lafiyarsa, ko na masa sako, amman ko da rana daya Talba be taba daga waya ya tambayi ya nake ba! Idan na yi kwaliya be taba ce min kyau ba, be taba replied sakona ba, be san yai min kyauta irin ta masoya ba, balle har ya dauke ni muje yawo, ba zan taba yarda na aure shi a haka ba, now it's my turn, dole ne ya canja” Ta karasa yana yawo da idonta a dakin. Madina ta kama hannunta. “No Leila mutane irin Talba suna da wahalar sha'ani, kuma suna da shaukin kai ga wanda ya iya zama da su, kar garin gyara ki ballo wata barnar, idan kin bashi hakuri a inda kike da gaskiya ai ba laifi ba ne” “No dole ne ya gyara, yana son soyayya amman be san yadda zai nuna ta ba? Be san yadda zai biya ta ba? Ban taba kiran sunansa a gaban idonsa ba sai na sakaya, amman shi be taba gwada kirana da suna mai dadi ba” Ta karasa tana murmushi. “I'm such a fool” Ta kai dubanta gurin wayarta da ta soma ringing. Hannu ta kai ta dauki wayar sannan tai picking. “Hello?” “Kanwata ga mu harabar gidan” “Okay” Ya mike tsaye ba tare da tunanin komai ba ta nufi kofar fita. “Talba ne?” “Ali dai Uhm Talba zai zo nan?” Ta fada tana mere baki sannan ta fice, hango Motar Talba harabar gidan ba karamin mamaki ya bata ba, domin ko a mafarki bata taba saka ran zai zo ba, kuma bata zaton Ali ya aro motarsa ne. Tun kamin ta sauko entrance din ta canja tafiya, kamar wata hawainiya haka ta rika takawa kamar bata son karasawa kusa da motar. Da gangan tai haka domin ta san a cikin abubuwan da Talba ya tsaya akwai jira, ko bata masa lokaci for nothing, mutum ne da yake daukar lokacinsa da muhimmanci sosai, dakika daya ko biyu idan ka kara, zai iya rushe ko miye a tsakaninku, hakan yasa yana girmama lokacin wani da ra'ayinsa. Kamin ta iso Talba ya cika har ya kusan fashewa, ba karamin jihadi yai ba na bawa zuciyarsa hakuri har ta iso. Ali dake front seat ne ya sauke gilashin motar yana murmushi, Talba kam ko inda take be kallo ba sai taba wayarsa yake kamar his life depends on it. Kallo daya Leila tai masa ta dauke kai tana amsa gaisuwar da Ali yake mika mata. “Lafiya Kalau” Ta amsa tana kokarin juyawa. Sai Ali ya bude motar ya fita. “Ina zaki je?” “Ciki zan koma, baka fada min tare da wani zaka zo ba” Kallon mamaki Ali yai mata, ganin ta yi abun da bata saba ba. Wani irin tafasa zuciyar Talba take kadan ya rage ta kone, bude motar yai ya fito a fusace ya zagayo inda take tsaye. “Na zo nan ne, saboda Daddy ya saka ni, ba dan ra'ayina ba, na fi karfin daukar wulakancin mace ko wace iri ce, na fi karfi na bawa na kasa da ni hakuri wannan ranar ba zata taba zuwa ba...” Ali ya rasa inda zai saka kansa, sai kawai ya koma cikin mota ya zauna, shi da ya zo sasanci sai kuma a sake yin fada a gabansa. Talba na gama fada mata haka ya juyo ya dawo cikin motar yadda ya rufe ganbun motar kadai ya isa ya sanar da bacin ransa. Kamar wanda akai wa gorin tuki haka yai ribas ya rika danna horn, Mai gadin ya bude masa gate da sauri, ya firgi motar kamar wanda ya shirya bakuntar lahira. “Wannan wace irin soyayya ce Talba me ke damunka, wai anya kana son Leila kuwa?” Da mugun karfi Talba ya taka burki, he got lucky babu motoci da yawa a titin. “Fitar min a mota” Ya fada ba tare da ya kalli Ali ba. Ba sabon abu bane gurin Ali ya saba nasa haka idan ransa ya bace ko suka samu tsabani, sai dai baya hana anjima ya neme shi. “Kana da matsala Wallahi kana da matsala, wannan mugun fushin ban san inda zai kaika ba” Ali ya fada cikin bacin rai. “Ka san bana son ana min ihu” “Mtsssss” “And i hate tsaki” “Ba zan fita daga motar ba” Ali ya fada yana gyara zama. A take Talba ya bude motar ya fita ya barta kunne, ganin hakan yasa Ali yai saurin fita ya zagaya driver side ya cigaba da tukin yana mamakin rayuwar Talba. Gefen Titi Talba ya dawo ya tsaya, a ganinsa kaskanci ne ya shiga napep balle kuma ya hau babur zuwa gida, not just that even tsayin da yake a gafen titi ba girmansa ba ne, wayarsa ya ciro ya kira direban gidansu. “Ka zo ka dauke ni zan turo maka location ta whatsapp yanzu” Shine kawai abun da ya fada ya kashe wayar ya kunna datarsa ya shiga whatsapp dinsa ya tura masa location din, sannan ya maida wayar aljihu yana kallon titi, har lokacin zuciyarsa zafi take masa saboda Leila ta kira shi da wani, how on earth zata kira shi da wani? After like 15 min direban ya iso, da kalle kalle har ya hango inda yake ya faka masa motar, Talba ya bude ya shiga ba tare da yace masa komai ba, shi ma direban be yi kokarin yi masa magana ba domin ya san Talba baya son yawan gaisuwa da kuma kallo, idan kuma kana son bata masa rai to ka cika shi da surutu. Suna isa gida ya bude motar ya fita ya nufi bangarensu, wato shi da Kabir sai dai kowa side dinsa dabam, kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya jefar da wayarsa kan gado ya cire rigarsa da agogo ya shiga bathroom, sannan ya ciri jean din dake jikinsa ya kunna shower ya tara jikinsa yana kallon kansa a katon madubin dake facing dinsa a bathroom din, kamin ya dukar da kansa yana kallon zanen sunansa da tattoo dake kirjinsa wanda babu wanda ya san da shi sai shi kadai, can kuma ya dago ya lumshe ido. AMINATU POV. Kusan ko wane gida dake garin an taba, wasu an kashe wasu an kwashe duka da dabobi, wasu an tafi da yayansu da mata, wasu kuma anyi ma matan fyade, sai dai ba kamar gidansu Aminatu ba, domin wulakancin da akai wa mahaifiyarta ya wuce na kowa mutum goma shadaya a lokacin daya, kuma aka kashe yayyayunta hudu, aka kona rumbun hatsinsu, aka raunata wasu, aka kora dabobinsu. Ba gidan kadai ba garin gaba daya tsit yai duk kuwa da kasancewar barayin sun yi iya barnar da zasu yi sun tafi, amman tsoro ya hana kowa fitowa, sai kuke kuke kake ji a gidanje, sai dai gidansu Aminatu ya fita dabam da baka jin kukan kowa, har asuba Aminatu na boye karkashin gado, mahaifiyarta kuma tana zaune a bakin kofar idonta a bude amman bata iya komai kamar an zare mata lakka a jiki haka take ji, Sanusi kuma na tsakar gidan a sume. Kamar macijiya haka Aminatu ta fito karkashin gado, ta janyo zanen gadon dake kan gadon karfe dan bono na Inna ta nufi Inna dake kwance tsirara tana kawar da idonta tana kuka har ta karasa kusa da ita ta kulluba mata zanen. Sannan ta juya ta koma inda fitilar kwai take ta dauka ta kara haskenta, ta taka kamar mai koyon tafiya ta fito waje. Wani rawa jikinta ya fara yi hango rumbun abincinsu na ci da wuta, sai kuma ta juya a hankali ta sauke idonta kasa ta kalli gawar Iro, da ta Amadu, ga kuma Sanusi shi ma dake kwance, kafa na zubar da jini, gaba daya ilahirin jikinta ne ya fara rawa kamar yadda bakinta ma yake yi. “Ya... Ya... Ya.. Ya..” So take ta kira sunan daya daga cikinsu amman ta kasa, hawaye sai aikinsu suke a fuskarta. Ta saki fitilar numfashi na fitar mata da karfi, wani kuma na shiga da sauri. Juyowa tai ta kalli Inna dake kwance bakin kofar har lokacin idonta na zubar da hawaye, sai wulakancin da akaiwa mahaifiyarta ya fado mata a rai, komai ya zame mata sabo. “Me muka musu?” Ta tambayi kanta tana wani irin kuka na fitar hankali, sai kuma ta ruga da dugu gurin yayanta Sanusi ta taba shi. Sai kuma ta juya ta kalli yayanta Amadu dake kwance kai a fashe, take ta girgiza kai. “Ba da gaske ba ne aa, wannan be faru ba, yan'uwana ba su mutu ba, ba ayi ma mahaifiyata fyade ba, wadandan nan mutanen ba su zo ba, komai be faru ba” Ta tashi da sauri ta ruga da gudu daki ta koma gurin kwanciyarta ta kwanta taja abun rufa ta lullube ta kame guri daya ta runtse ido, da gaske so take ta farka daga bachin, so take komai ya zama mafarki. Sai a lokacin Inna ta samu kuzarin motsawa ta fashe da kuka. “Allah ka isar mana ga bayinka Allah....” Ta fada tana kara fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ta taba zuciya. Jin kalamanta ne yasa Aminatu ta saka hannayenta ta toshe kunnuwanta ta kara runtse ido ta kwara wani irin ihu da muryar da bata taba sanin tana da ita ba. “Aaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa” Ba makotansu kadai ba, har gidan dake tsakaminsu dashi gida biyar ne sai da suka ji ihun Aminatu. >>>>>>>>>> Anya Leila zata kai labari kuwa na cewar sai ta koyawa Talba darasi? Nikan nace Ali yana hakuri da wannan aboki nasa mai wuyar sha'ani da jin Kai😕😠😡 Allah sarki Aminatu, ko da yake mahaifiyarta ce abar tausayi. 😭😭😭 ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai. Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. https://www.wattpad.com/story/283871769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZCqcO2wXIv6pkkxIr3do4ng1%2BTHhzoVPTPFtpfDcb1ftHOVsldMflpG2lAwd5aYtrehJ12WEeerjWSVNDZunKAH9QpxhI0A%2BzJsYI6RrshbTOZsoLUXljeZDCPaDNtKr *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -5️⃣ Sai after sallah isha'i ya fito harabar gidan ya zauna a inda aka jera kujerun zama domin hutawa, kusa da garden, sai kamshin turare yake kamar sabon ango, fuskarsa cike da annuri, sai dai babu walwala ko kadan a tare da shi. A hankali ya hade yawun bakinsa ya daga kansa sama yana kallon taurarin dake samaniya, kamin ya juyo yana kallon Amal dake sanye da kayan bachi tana nufo inda yake. “Ya Talba” Ya dan sakar mata murmushi kadan. “Lil Sis ya kike?” Ta zauna a kusa dake kusa da tashi tana amsawa. “Lafiya kalau” Sai kuma ta yi shuru tana kallonsa. “Kina bukatar wani abu ne?” Ta girgiza kai ta soma wasa da yatsun hannunta. “Talk to me Lil Sis fada min damuwarki” Ya fada yana kallon yanayinta dake nuna akwai damuwa a tare da ita. “Yaya ka sake yin fada da Ya Leila ne?” Fada suka yi? Ya zai fada mata? Abun da suka yi fada ne ko aa, shi be ma tabbatar ba, all what he know is ta kira shi wani shi kuma ya fada mata magana, sincerely speaking ma ya manta me yace mata. “Yeah Maybe” Ya fada yana dan tabe baki. “Miya faru?” “Ta dawo gida tana ta kuka tun dazun, yanzu kuma kuma Daddy ya shigo yai ma Momy fada ita ma kuka take?” “Why?” “I don't know, kawai dai na ji Daddy yana cewa babu wanda ya isa ya wulakanta masa d'a, kuma wai ya zaba maka Leila ne saboda kar kaje neman auren wata a wani gidan ace ba za a baka ba saboda yadda kake behaving, amman a gidansa yana da iko da Leila” Talba ya cika ma bakinsa iska ya busar. “Ina Momy?” “Tana dakinta...” Amal ta karasa tana kallon Kabir daya doso inda suke zaune ta kofar gaba, kana ganinsa ka san a fusace yake. “Look Talba, ba zaka Leila kuka saboda bakin halinka and now ka saka Momy kuka ba okay? I won't tolerate this, dole ne sai ka auri Leila ne? Idan ba ka canja hali ba ba zaka taba aure ba a rayuwarka” Daga inda yake zaune ya dago yana yi ma Kabir wani banzan kallo. “Ka sani ba a amin tsawa ba a nuna ni da yatsa” “To sannu ubana, sannu Sarkin Arewa, girman kai zai kashe Mtssssssssss” Kabir ya karasa yana jan wani dogon tsaki. Amal ta yi saurin kama hannun Talba. “Ya taso mu bar mishi gurin gaba daya” Uffan Talba be sake cewa ba ya bi Amal dake rike da hannunsa, har sai da suka shigo cikin falon sannan ya saki hannunta. “Je dakinki zan yi magana da Daddy” “To amman karka ce masa ni na maka gulmar” Yayi murmushi ya juya zuwa bangaren Daddy. Daman can duk wata gulmar gidan gurin Amal ake jinta. Cikin natsuwa da kamala ya shiga bangaren Daddy, yai sallama Daddy ya amsa masa tare da kai hannu ya dauki remote ya kashe plasma dake kunne. Talba ya zauna kasa kusa da kafafuwan Daddy. “Daddy yau na kawo maka karar kanka” Daddy yayi murmushi. “Na taba Momy ko?” “Eh Daddy ka san bana son hawayen Momy” “To ai laifinta ne, taya Leila zata yi laifi na yi mata fada kuma tace zata shigar mata” “Amman Daddy Momy tana kare Leila ne kamar yadda kake min, kuma tun da har Momy ta shigar mata na yarda ni ne ba ni da gaskiya, domin Momy kullum tana side dina ne” Ya sauke ajiyar zuciya. “I will try my best na ga na zama Romantic, zan zama yadda Leila take so indai hakan zai faranta ran kowa, yanzu abu daya nake so Daddy ka je ka bawa Momy hakuri?” Daddy ya nuna shi da yatsa. “Hey i talk to your mom na mata fada, kuma ita ya kamata ta ba ni hakuri saboda rai na ya bace” “Amman Daddy ai kai kayi mata laifi” “Really? Kasan da wannan amman idan kai ma Leila laifi sai ka sa bata hakuri” Talba yayi murmushi. “Daddy wacan yana da banbanci da wannan, ita Leila ai yarinya ce, wannan kuma ba zaka iya da yayanta ba, yaranta ba za su yarda kai mata haka ba” “Leila ma wata rana uwar wasu ce, kuma yaranta ba za su dauki abun da kake mata ba, kamar yadda a yanzu kake jin rashin dadi, and tell me, you take your Mom side” Talba ya sake yin murmushi. “No Daddy kullum ai ina side dinka, amman dai ina son Momy ta daina bacin rai please” “Shikenan zan kirata ta zo nan na bata hakuri” “No Daddy ka tafi dakinta mana, zata fi daukar abun da muhimmanci Please” Daddy ya masa kallon mamaki. “So that's mean kasan yadda ake lallaba mace, duk abun da kake yi da gangan kake yi kenan?” Talba ya mike tsaye yana dariya kamar ba shi ba, Daddy ma murmushi yai mai sauti yana binsa da kallo cike da kauna irin ta Uba da D'a. Bangaren Momy ya dawo, kai tsaye ya nufo dakin Leila, be tsaya knocking ba ya tura kawai ya shiga, sai ya same ta zauna gaban mirror tana duba fuskarka. Tsaye yai cak kamar an dasa shi, ta ina zai fara? Me zai ce mata? Sorry? Shi da kansa? Yace mata sorry? After ta kira shi wani? Taya ma zai ce mata haka? For the sake of Daddy, wata zuciyar ta raya masa, but duk da haka be jin zai iya ce mata sorry. “Idan wani abu ya faru a tsakaninmu, ki bar shi a tsakaninmu ba zai wani ya ji ba” Ya fada sannan ya juya, sai kuma ya juyo. “And if you need something, lemme know” Yana fadar hakan ya juya ya fice ba tare da ya rufe mata kofar ba. Tabe baki tai ta mike tsaye ta isa gurin kofar ta rufe ta juyo ta dawo gaban madubin ta zauna. Har ga Allah tana son Talba, kuma ta san yana sonta amman abun da yake mata is yayi yawa, girman kansa da jin kansa yayi yawa, that's why dazun ta fadawa Daddy cewar bata shirya aurensa a yanzu ba sai nan gaba, Momy kuma ta goya mata baya ganin kullum ita ake kwaruwa, but this time around Momy ta goyi bayanta. Jin wayarta ta yi kara alamar sako yasa ta mike tsaye ta isa gurin da wayar take ta dauka ta duba sakon. “Good Night” Shine rubuce da number Talba, ba shiri ta zauna tana mamaki. Da gaske shi ne ya turo mata sakon ko wani dai? Dan murmushi. “Duk sai na rama abun da kai min, it's my turn” Ta fada tana jin wani irin dadi, juya ido tai. “Ya kamata ya san ina da tsada” Ta fada sannan ta kwanta saman gadon. *** *** *** Kamar jiya Saturday, yau kuma Sunday, kowa yana zaune a teburin cin abinci ban da Daddy da zai karya bangarensa da kuma Leila da take dakinta. “Ina Leila?” Talba ya tambaya yana kallon Amal. “Tace zai ba zata fito ba” “Why?” “Just” “Hada nata breakfast din na kai mata dakinta” Ba Momy da Kabir ba, ko Amal har Baaba mai aikinsu sai da ta kalleshi. “Kamar dai ba kai Talba” Kabir ya fada, sai Talba yayi murmushi kadan. “Sounds funny, right?” “No sounds new” Momy ta yi murmushi. “Ban fada muku ba? Wata rana Talba zai canja” Ya mike tsaye ya shiga hada ma Leila nata abun karyawa. “I didn't change, ina yi ne for the sake of you and Daddy” “So na dan ra'ayin kanka kake ba, kenan baka farinciki da abun da kake, doesn't make sense” Kabir ya fada yana tabe baki. Talba dai be sake ce masa komai ba har ya cirewa Leila komai ya dauka ya nufi upstairs. Amal ta mike da sauri ta bi bayansa ta rigashi karasawa gurin kofar ta bude masa saboda hannayensa duka biyu suna dauke da abu ne. Yana shiga Amal ya janyo kofar ta rufe, har gefen gadonta ya aje mata komai sannan ya dago ya kalleta. “Good Morning” Ya sake gaisheta duk da kasancewar ya aika mata da sakon gaisuwa da safe kuma bata masa reply ba, which is pain her. Bata amsa masa ba sai kallonsa take. “Ga breakfast dinki, idan kina bukatar wani abu ki fada min” Yana fadar hakan ya juya, sai da ya kusa isa kofa sannan ta ce. “Anjima zaka kai ni shopping” “Idan kin shirya ki kirani” Ya fada ba tare da juyo ba, sannan ya fice ya ja mata kofar. Yana saukowa downstairs be koma dinning din ba sai ya nufi kofar fita, yana fitowa ya tsaya bakin kofar falon ya kira Ali. Kamin Ali yai picking Kabir ya fito ya tsaya daidai inda yake tsaye. “Kasan mi ye Talba?” Talba ya kalleshi yana kokarin yanke kiran Ali da yake. “Kai dan'uwana ne, ba zan so ka cutu ba, kamar yadda ba zan so Leila ta samu matsala, ni shawarar da zan baka karka auri macen da baka so, domin zaku yi ta samun matsala ne kawai, ji abun da kake yi a yanzu saboda Momy da Daddy kake yi ba wai dan ka faranta ranta ba, kuma ba dan kana so ba, hakan kuma zai haifar da kiyayya da tsana a tsakaninku” Talba ta saka wayar aljihu yana kallon Kabir. “Ina sonta Kabir...” “No, maybe dai kana sonta saboda baka san miye so ba, ko kuma kana sonta saboda baka son ka bawa Daddy kunya, ko kuma kana sonta saboda kana son ka yi aure, amman na san wata rana zuciyarka zata so wata wata kila Leila ce ko wata dabam, a lokacin da zata maka laifi kuma na bata hakuri Wallahi baka ko sani ba, wanda zaka so faranta mata a karan kanka, idan tana cikin damuwa kai ta kokarin ganin ka cireta, idan tana kuka karika jin hawayenta kamar mutuwarka ne, duk wannan shan kunun da kake yi ita zaka sake mata ka rika neman tai maka murmushi kana mata dariya, idan zuciyarka ta fara wannan son, duk son da biyayyar da kake yi ma Daddy ko Momy idan suka muzantata sai ka ji ba dadi kamar kai aka yi ma, daga lokacin ne rayuwarka zata fara canjawa...” “Noo Kabir, you know i don't believe in love, so wannan daren ba zai taba zuwa ba balle har na kwanta na yi wannan kalar mafarkin, ku ne da kuke karance karance da kallo fina finai kuke dauka irin wannan soyayya gaskiya ce, even if gaskiya ce ma ni bana cikin irin wadannanhawayen mazan...” Yana fadar hakan ya fara sauka entrance din. Kabir ya bishi da kallo yana murmushi. AMINATU POV. Sai da haske ya fara bayyana sannan mutane suka leko gidan, duk da kasancewar kowa yana fama da nasa jimamin. Duk wanda ya shigo ya tararda gawar su Amadu sai ya zubar da hawaye, daman can kowa ya saka ran sai ayi musu ta'asar da tafi ta kowa saboda suna da yan sa-kai har biyu da da barayin yankin suke matukar tsoronsu, domin basa yi ma barayi da sauki musamman idan sun hadu da su a wani gurin. Da taimakon yan tsirarun garin da suka rage aka dauko zage aka rufe gawarsu, Sanusi kuma aka dauke shi kan babur zuwa babbar asibitin shimkafi, a lokacin ne Inna ta fahimci har da Musa aka kashe, kuma aka tafi da matansa biyu bayan matar matar Amadu, cikin yaranta da suka tsira Aminatu ce kawai ita ma dan ba su ganta ba ne, sai kuma Isa da ya tafi kai Baba gurin ganin Gwaggonsu, sai kuma Bashiru dake kasuwancinsa a birni tare da iyalansa. Karfe bakwai da yan mintuna Baba ya iso cikin gidan, domin labarin abun da ya faru ya same shi a can garin da yake gurin kanwarsa, yana shigowa cikin gidan ya kasa rike kansa, tsayi ma ya kasa duk da kasancewarsa namiji sai gashi ya zube kasa yana kuka da idonsa, Inna kam zaune kawai take tana kallon komai, hawayen sun dauke mata. Da dai daya Baba ya fara bin gawar yayansa har hudu yana dubawa, Isah ma kuka yake sosai, ya ga Amadu da ka fashewa kai, sai kuma Rilwanu, da aka takewa wuya da babur, haka Musa na da dutse aka fashe masa kai. Iro kam gawarsa bata wuce ta karamin jariri ba domin gawarsa ta kone kurmus daker aka samu aka hada dan abun da yai saura gudu daya aka lullube da zanen Inna. Baba ta fadi zaune ya fashe da wani irin kuka yana dora hannu saman kai. “Allah ka hana zalinci, Allah ka sani mutanen nan ba mu musu komai ba, Allah ka isar mana” Baba ya fada cikin wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya, sai kuma ya juyo ya kalli dansa Isah da shi ma kukan yake ya ce. “Isah ka gani an kashe an yan'uwanka...” Daga inda Inna take zaune ta amsa. “An kashe su Malam, d'a hudu, ni na haifi yarana kuma a gaban idona aka kashesu, yaran da ba su wuce sa'an yayana ba suka keta min haddi har su goma sha daya, a gaban yata, suka kone muna abinci, suka kora mana dabbobi, saboda kawai zalinci, titin kwarai ba mu da shi a garin nan, ba mu damu da cigaban zamani ba, taki ma sai an ga dama a bamu, duk wani cigaba ko aikin taimako ba mu san shi ba, da hakkinmu muke tara komai, yanzu kuma zaman lafiya da farinciki ya gagaremu...” Inna na gama fadar hakan ta mike tsaye da sauri jin kamar numfashinta zai fita, ta dora hannunta a kirji tana kuka tana neman agajin Allah. “Innalillahi, shikenan sun raba ni da murmushi sun raba ni da dariya, kuma sun keta rigar mutunci na” Safa da marwa ta fara yi cikin gidan hannunta akai tana kuka tana jijjiga. Duk abun da ake a kunnen Aminatu, domin bachin da take son ya dauke ta ta sake farkawa a rayuwar zahiri be dauke ta ba, har lokacin kuma jikinta be daina rawa ba, kamar yadda kunnuwanta ba su daina jin karar binga, haka idanuwanta ba su kawar mata da ganin da tai ana yi ma mahaifiyarta fyade ba. “Ina Auta? Ko sun tafi da ita?” Baba ya tambaya yana kuka sosai, sai wata matar dake tsaye kusa da Inna tana kokarin bata hakuri ta ce. “Aa tana daki” Duk wanda ya ji ko ya ga ba aje da Aminatu ba ya san da cewar ba su ganta ba ne, yadda suka kwashi matan garin suka tafi da su babu abun da zai hana su zuwa da Aminatu. Baba ya tashi da sauri ya shiga dakin, sai ya same ta a inda ta saba kwanciya tana lullube, ba jikinta kadai ba, har hakoranta kana jin kara yadda suke haduwa da juna tsabar yadda jikinta yake rawa. Baba ya kai hannu ya janye mayafin sai ta tashi da sauri idonta a kumbure ta kalleshi. “Baba...Baba... Baba... Baba” Baba ya sake fashewa da kuka. “Baba wasu mutane ne suka zo.. Ba mu musu komai ba Wallahi, ba mu musu komai ba... Sun... Sun... Sun... ” Ta kasa fada sai ta fashe da wani irin kuka ganin cewar da gaske ne komai ya faru ba mafarki ba. Ba ko wace gawa ta samu sallah da sutura yadda ya kamata, saboda yawan gawarwakin, ashe ma samun sutura da masu yi ma gawa sallah da kuma binne ta kamar yadda addini musulunci ya tabadar wani abu ne da ba kowa yake samu ba, domin wasu da tufafin jikinsu ake saka su a cikin ramen, wani ramen kuma sai a hada mutum hudu guri daya. Bayan an binne gawarwarkinsu ne, Bashiru ya iso, hankali tashe, yana shigowa shi ma ya fara nasa kukan, na rashin yan'uwa. Aminatu kam tana can gefe daya zaune ta ki yarda ta zauna cikin mutane ko kallon mutane bata so, kuma ta ki cin komai. Sai da ta ji Baba yana maganar zai tafi asibitin gurin Sanusi sannan ta mike tsaye da sauri. “Baba dan Allah ka tafi da ni” Ta fada cikin kuka, wani irin tsoro take ji ganin take kamar sake dawowa zasu yi, gaba daya a firgice take, a dayan bangaren kuma tana son ganin halin da dan'uwanta yake ciki. “Aa Auta ki zauna a nan, asibi ce fa” Ta yi saurin rike rigarsa ta fashe da wani irin kuka. “Dan Allah Baba ka tafi da ni, ka taimaka min dan Allah Baba ka tafi da ni” Idon Baba ya sake cika da kwalla. “To saka talkaminki mu tafi” Ta saka talkamin dake kusa da ita, bata tsaya neman nata ba, haka suka fito cikin gidan tana rike da rigar Baba, Baba ya nuna mata wani babur. “Ki hau Babur din Buba, ni zan hau na Isah” Sai ta girgiza masa kai tana kuka ta rumgume shi. “Aa Baba Baba dan Allah karka sake yin nisa da ni” Gani take kamar idan yana nan babu abun da zai faru, gaba daya ta rasa gane kan komai, kwakwalwarta ba zata iya dauka ba. A dole babur daya suka hau ita da Baba, dan motsi kadan sai ta ji kamar zuciyarta zata fado tsabar tsoro, har suka isa idon a rufe yake domin ganin take idan ta bude ido mutanen zata gani. Ko da suka isa sun tararda asibitin a cike, domin a kauyensu ko a gidansu kadai akai ta'asar ba, an kawo mutane da yawa, wasu sai ihu suke wasu kuma suna zaune suna jiran a gama da wasu a duba su. Baba da Aminatu waje suka tsaya Isah ya shiga ciki, ganin ya dade yasa Baba ya shigo cikin emergency tare da Aminatu, gaba daya ta kara firgicewa ganin yadda wasu ke zubar da jini. Kamin su karasa inda suke zaton dakin da Sanusi yake ne, Isah ya fito yana kuka. “Lafiya?” “Baba babu Sanusi, Sanusi ya tafi sai dai idan mun isko shi, Allah ya jikanka Sanusi...” Ya fada yana kuka, sai ga gawarsa an fito da ita. Aminatu bata san lokacin data saki rigar Baba ba ta ruga da gudu gurin gawarsa, duk ita duk tsoron gawa da take yau ta manta da wannan. “Wayyo Allah na shiga uku, Ya Sanusi” Sai kuma ta juyo da gudu gurin Baba dake kuka ta rike shi. “Baba kai yi wani abu dan Allah Ya Sanusi ya tashi” Baba ya girgiza mata kai yana wasu irin hawaye masu zafi. “Ba ni da rayuwa Aminatu, sai hakuri” Sai ta sulale kasa ta fashe da kuka. “Wayyo na rasa Yaya mai sani dariya, yayana mai tsokanata, Yayana mai so na” Baba ya duka kamar zai mata magana sai dai shi ma bashi da zuciyar yin haka a yanzu, sai ya kara fashewa da kuka. “Allah ya Isar mana Allah ka isar mana” Isah ya fada yana kuka, duk wani mai sauran imani da tausayi sai da idonsa ya cika da hawaye saboda tausayi. Zunbur tai ta tashi tsaye. “Baba ku duba kila be mutu ba...” Rugawa tai zata tafi gurin gawar sai Isah ya riketa, wani irin tsalle tai tana son ta kwaci kanta daga rikon da yai mata amman ta kasa, ta fisgi kanta ta fisga ta sake fisga ta sai fashe da tana jin kamar ace yau akwai abun da zata iya yi ta dawo da rayuwar Sanusi. >>>>>> If you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, and send the evidence to 08036126660, zan yi adding dinki paid group In-sha-Allah. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai. Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -6️⃣ Bakincikin mutuwa, da damuwar rasa rai, wani irin bakinciki ne da yake ma kansa muhalli a zuciyar bawa, baki yayi kadan ya bayyana yadda zuciyata take ji, haka zuciya ma ba zata iya daukar abun ita kadai ba har sai da taimakon idanuwa da gangan jiki. Taya Aminatu zata fadawa kowa yadda take ji? Taya zata rasa yayyu biyar maza kuma ta kasa kuka? Taya za a maida garinsu da gidansu kamar kufai kuma ta kasa kuka? Taya za a keta haddi mahaifiyarta a gaban idonta kuma ta kasa kuka? A tsakanin rasa yan'uwanta da kone musu abinci da keta haddin mahaifiyarta bata san wani yafi wani zafi ba. Anya zata iya dauka? “Duk ni kadai?” Ta furta wasu hawaye mazu zafi na sauko mata, kana ganin yanayinta da kuma jin kalaminta kasan bata cikin hayyacinta, ruwan hawayen dake mata zuba har ya canja launin fatar idonta, ya kumbura mata ido, kwayar idon kuma ta mata ja sosai. “Auta dan Allah ki yi hakuri, haba kowa ba yana da tabon mutane nan a garin nan” Anty Aina'u matar Bashiru ta fada tana kai hannu ta dafa ta. Aminatu ta kalleta kamar tace mata shiga zuciyata ki gani, sai kuma ta dauke kai ta hadeye yawu. Har aka yi gaisuwar kwana uku aka watse Amintu bata daina kuka ba, kukan da ta sha ko Inna bata yi ba, domin Inna ta bar komai a zuciyarta ne, idan ta yunkurin kukan ma baya zuwa mata, sai dai bata iya komai ko bandaki zata zagaya sai an rikata. Idan kuma ta zauna ta sanda kai kasa bata iya dagowa sai an rika kan nata an dago da ita. Kana ganinta ka san kukan zuci take wanda ya fi na ido illa. Washe garin Ranar da aka watse Aminatu na tsakar gida tana wanke wanken kayan abincinsu, sai kawai ta fashe da kuka, rayuwarsu take tunawa kwana hudu zuwa biyar da ya wuce, a da idan tai wanke wanke kowa zubawa ake, amman yanzu daga ita sai Isah da Inna da Baba kawai suke ci, ba kamar da ba. Tunawa da tai da maganganun da mutane suke mata cewar ta yi hakuri ko dan ta karfafawa mahaifiyarta guiwa yasa tai saurin share hawayen. Ta cigaba da wanke wanke bayan ta gama ta dauki kayan ta kai a inda suka saba ajewa ta aje. Sannan ta fara sharar gidan, tana yi tana ta ganin inda aka aje gawarwakin yan'uwanta, ta kasa daina ganin abun a idonta. Bayan ta gama sharar ta dauko tabarma ta shimfida daga bakin kofar sannan ta shiga ciki ta riko Inna dake kwance. “Inna muje waje ki sha iska” Daman zaman dakin ya fara isarta, sai ta yunkura, Aminatu ta taimaka mata ta mike tsaye tana takawa a hankali har suka fito, Aninatu ta zaunar da ita a hankali, sannan ta koma ciki ta dauko filo ta jingina mata a jikin ginin na kasa, ta jinginata. Take Inna ta sauke wata irin sanyayyiyar ajiyar. “Allah ya miki albarka” “Amin” Aminatu ta amsa hawaye na sauko mata ganin yadda rayuwata ta sauya mata ita da mahaifiyarta a lokaci daya. Inna ta sakar mata murmushi sannan ta soke kai kasa. Madafa Aminatu ta nufa ta kunna wuta ta dora tukunya ta zuba ruwa. Sannan ta koma ta auko shimkafar da yayanta Bashiru ya siyo musu ta fara tsinta. “Ji dan Allah ko tsintar shimfar bata iya ba...” Ta lumshe ido da sauri tunawa da yayanta Sunasi da tai, yana yawan tsokanarta komai take sai yace bata iya ba. A hankali ta daga kai tana kallon ginin da yai domin yana daf da aure shi da Isah. Duk yadda ta so ta tana kanta hawaye sai ta kasa, hannunta ta saka ta share hawayen tana jin kamar wani nauyi a zuciyarta. “Ashe haka ake ji idan aka rasa rai” Ta furta a hankali tana kokarin tsayar da kukanta, sai kuma tai murmushi da yafi kuka ciwo. “Mutuwa bakin takobi mai raba uwa da daya, ta raba yan'uwa ta raba mata da miji, kin maida mana gida kamar kufai” Ta damki shimkafar a hannunta wasu hawayen na sauko mata kamar ba gobe, a dole ta aje gyaran shimfara saboda hawaye ya hana ta ga komai. “Auta...” Ta juyo da sauri jin kamar muryar Inna ta kirata, sai dai ganin kanta a noce ya tabbarta mata ba kiranta tai ba, muryar dai ce take jin kamar ta Inna. A take ta fashe da kuka ta bar gaban murhun ta mike tsaye wanda hakan yai sanadiyar barewar shimkafar da ke jikinta ta nufo inda ta gudu ta fada jikinta tana kuka. Sai Inna tai saurin lumshe idonta da sauri tana jin kukan Aminatu har cikin ranta, tana son tace mata yi hakuri amman bakinta ya mata nauyin da take jin kamar maganarta ta kare a duniya, sai kawai ta daga hannunta ta dora a jikin Amimatu tana shafata alamar rarrashi. “Miyasa wani zai ji bakinciki da farinciki mu? A kauye muke zaune amman muna jindadi rayuwarmu, miyasa za su ruguza farincikinmu? Na kasa saba da rashin Yaya Sanusi Inna, Inna yanzu waye zai sake tsokanata? Yaya Amadu mai min fada baya nan, yaya musu mai bamu abinci baya nan, sun kashe Yaya Rilwanu da Yaya Iro...” Inna ta bude idonta ta saka hannu ta kama fuskar Aminatu. “Zan tafi na barki Aminatu, yar Autana, ina son ki saba da hakuri, akwai kalubale a gaba, mace da ta tashi a cikin gata da soyayyar uwa da uba da yan'uwa irin ki, duniya ta sauya mata lokaci daya? Dole zata ji ba dadi kuma zata fuskanci kalubale, amman zan fada miki wani abu, ina son ki rike ki rika maimaitawa, a duk lokacin da kika tsinci kanki a damuwa ko kika ga wani abun tashin hankali bakinki ya saba da furta Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, ri rike wannan kin ji” Aminatu ta kalli Mahaifiyarta hawaye na sauko mata. “Inna idan kika mutu kuma zai ki yi tsammani ni zan rayu? Wannan wace irin magana ce?” “Zaki rayu Autarta, dan na mutu ba shi yake nufi ki mutu ba, Allah be raya wani dan wani, kuma be kashe wani dan wani, da ya bar yayana dan ni, ko kuma ya bar su dan ke, yadda ya so haka yake” “Inna maganar da kika fada min yanzu, ta fi min ciwo fiye da rasa rayuwar yan'uwana, kada Allah ya nuna min ranar da zaki tafi ki bar ni, sai dai ni na tafi na barki” Ta fada cikin kuka sannan ta rumgumeta. Inna ta sake runtse ido tana jin wani kololon bakinciki yana mata yawo a zuciya. Suna haka Baba ya shigo rike da yar ledarsa ta dawo (Fura) ganinsa yasa Aminatu ta tsagaita kukanta ta daga jikin Inna tana fyace hancinta. “Kukan dai ne be kare ba” Ya fada yana zaunawa kusa da Inna kana ya aje mata ledar furar. “Ga fura Auta ta dama miki na san ba iya cin wani abua kike ba” Kallon furar kawai tai ta dauke ido. “Baba sannu da zuwa” Aminatu ta fada da muryarta ta kuka, wai Baba yai mata murmushi irin na su na manya domin shi kansa juriya kawai yake irin ta maza amman ya ji zafin mutuwar yayansa, da kuma keta haddi matarsa. Hannu biyu Aminatu ta saka ta dauki ledar furar ta nufi gurin da suke aje ruwa ta dauko kwanon ruwa ta zuba furar ta fara damawa da nono. Daga Inna har Baba kallonta suke, ta ba su baya amman hakan be hana ta jin abunda suke tattaunawa. “Ko ya rayuwa zata kasancewa Aminatu idan bana raye?” Baba ya kalleshi da sauri jikinsa yayi mugun sanyi, Aminatu kuma ta juyo ta kalli Inna hawaye na bin fuskarta. “Rayuwa zata kasance mai wahala Inna, zan zama marar gata marar yanci, dan farinciki da yai saura a rayuwata zai tafi ya bar ni, iskar da zan shaka ma sai na yi kamar na mutu sannan na same ta, Baba dan Allah ka yi mata magana ta daina irin wannan maganar” Ta karasa tana duban mahaifinta, Baba ya kasa cewa komai domin jikinsa yayi sanyi sosai idonsa har sun cika da hawaye, Inna ta kalleshi tana murmushi ita ma hawayen ne a idonta. “Yayanka sun fika jarumta Malam” “Wannan ba maganar Jarumta bace, magana ce marar dadi, kuma da na san abun da zaki fada kenan da ban shigo gidan nan yanzu ba” Ya karasa yana kai hannunsa aljihu ya ciro wayarsa dake ringing. Ya kara wayar a kunne tare da sallama sai dansa Bashiru ya amsa ta dayan bangaren... BATURIYA POV. Tana tsugune gaban murhu tana suyar naman kajin suka ji an kwankwasa gida. Ta kalli danta shi ma ya kalleta. “Ko Abba ne?” A take ta daka masa tsawa. “Ban ce ka daina cewa Abbah ba?” Sultan yayi saurin rufe bakinsa. “Daddy” “Good” Ta mike tsaye tana mita. “Wata kila ma yaran nan su Saifu sarakan kwadayi tun da sun ji an soyar abu kamshi ya kawo musu, shiyasa zama irin wannan area ta talakawa sai dole Wallahi” Ta kai hannu ta bude kofar sai arba tai da kawarta Ramlee, a take ta washe baki, Ramlee ta sakar mata murmushi tana wani irin kamshin turare irin na manyan masu kudi. “Yau gidanmu?” “Sai kace ban saba zuwa gidanmu ba” Ta fada a yayinda Baturiya ta kauce mata ta shigo. “Ki ce yau na shigo a sa'a kaji ma kuke ci, lallai Faruq yayi abun kai” Ta fada ta zigar zolaya da bugun ciki tana kallon Baturiya. A take Baturiya da bata shaye rada ta tsire baki tace. “Kina magana kamar baki san wa nake aure ba, Faruq din ne zai kawo min kaji?” “Ah gaskiya idan fa yana da shi yana yi” “Idan yana da shi kika ce, ke dai zauna na kawo miki ruwa” Baturiya ta mika mata kujerar da take zaune dazun, ita kuma ta karba ta zauna tana karewa gidan kallo kamar bakonta, ko gaisuwar da Sultan yake mata bata ji. “Baturiya kenan duk kyau nan naki kika kare a gidan nan” Baturiya ta aje mata ruwan a cup tana fadin. “To ya iya, kaddara rayuwa ta kawo ni nan” “Kika dai kawo kanki, ke kika so ai” “Hmmm Wallahi Ramlee babu irin cin mutunci da ban masa ba, amman yaki ya sake ni” “Ina ko zai sake ki, tun da be da kudin auro wata, kuma ya san yadda kike da kyau nan kina cika idda wani mai kudi zai aureki” “Da gudu ma, ni Wallahi ban taba zaton zan yi rayuwa a haka ba, bawan Allah nace masa idan mun yi aure zan cigaba da karatu yace ya yarda zai dauki nauyin komai, sai gashi abincin ma wannan wahala yake mana” “To miya hana shi?” “Ai lokacin da na aureshi karatu yake, ni na dauka, yana gama karatu zai samu aiki mu fancama yadda muke so, ashe ashe wahala ce ke kirana, gashi gurin auren ma sauki aka masa tun da auren gida ne, kawaye da muka gama secondary school a tare daga mai aure wani shege sai mai aiki a guri kaza ni ina nan zaune a wani shegen gidan duk yabi ya rugube, kuma na haya” Tana kai aya Ramlee ta saka mata dariya. “Ke kika so Baturiya, tsabar kyau fa Baturiya ake ce miki, gashi manyan mutane suna son farar mace, Wallahi ba ki ga yadda mutumen ya haukace daga ganin hotonki ba” Baturiya ta nufi namanta ta juya tana fadin. “Ke ni fa Ramlee duk iskancina ba zan iya zina ba” “Su kuma manyan mutane ai sun fi son matan aure saboda sun fi Sirri, wasu kuma ba sai kin fada musu cewar kina da aure ba, ki ga abun da be wuce 30-1hour ba an baki kusan 500k ko 300k” Baturiya ta juyo tana kallonta tana zaro ido. “Da gaske wai?” “Wallahi kuwa, ke auren ma ba rufi asiri ba ne a gareki, wanda ta haihu har wani tsoron fadawa maza take ma, kara ma budurwa ace ko dan gaba, amman ke fa? Kuma ko kudi aka ganki da shi za a ce na mijinki ne” “Tab humm ai sun san bakiri nake aure, shi kansa idan ya gan ni da wannan kudi sai ya tambaya ina a samo” “Ki ce tallafi ne kika samu, daga nan sai ki kirkiri sana'a ki fara yi, kin ga idan ma wasu sun shigo ba za a zarge ki ba, Wallahi cikin Shekara daya Fee'ah har makka sai kin je, kuma duk abun da kike so zaki siya a duniyar nan” Baturiya ta dawo kusa da ita ta zauna. “Amman su wani irin kudin banza ne da su haka?” “Masu kudi fa aka ce miki Baturiya, kina irin wannan area ko'ina kwata ai dole ki yi mamaki, da zaki yarda zan hada ki manya manyan yan kasuwa da yan siyasa, kuma ba haka nan ake zuwa musu ba ai, sai an gyara ki an shirya, ta yadda zai ji kamar be taba kusantar wata mace ba” “To shi zunubin zaki daukar min?” Baturiya tai mata tambayar rainin wayo. Sai Ramlee tai murmushi tana mikewa tsaye. “Baki ji matsi ba ne yarinya, kin san da Allah kika chat da maza a facebook? Har kina haduwa da su kina karbar kudinsu” “Wannan ai dabam, ban aikata ba sai dai na yi musu dadin baki” “To yayi kyau ki cigaba” Ta saka hannunta a jaka ta ciro 10k ta mikawa Sulta. “Sultan a siye minti ka ji, ni bari a dauki naman tun da ba za a min ta yi ba” Ta karasa gurin naman ta saka hannu ta dauka ta kai bakinta, Baturiya ta yi murmushi. “To ai ke dince kika dauke min hankali ” Bata sake ce mata komai ba ta nufi kofa, Baturiya sai kallo tsadadden lace dinta take, sai da ta fita sannan ta juyo. “Ni baki ma fada min ina kika samu nama ba, ko wani aka yaudara” “Wannan karon roka na yi” “Uhm wata rana dai zasu roki abun da baki so” “Ai da zarar na ga mutum da ruwan haka, sai na zubar da shi na kama wani” Ramlee ta yi dariya ta juya ta kama Hanya Baturiya kuma ta rufe gidan ta nufo gurin yaronta Sultan ta karbe kudin da Ramlee ta bashi. “Karka fadawa Daddy ka ji?” “Toh” Ya amsa ta yana kai hannu ya dauki cinyar kaza. Sai bayansa sallah isha'i Faruq ya shigo gidan, ba laifi ya samu masu haske har ya hada 500, tun da ya ji kofar gidan a bude ya tabbatar matarsa na cikin nishadi, domin idan tana jin rashin mutunci wani lokacin rufe gida take saboda yai ta wahalar kwankwasa a waje. Bayan ya shigo ya maida kofar gidan ya rufe, kamin ya karasa falon ya so ma jin waka ya tashi, ko kwankwato babu matarsa na cikin nishadi a yau. Sallama yai ya shiga ta amsa masa kamar ba ita ba. “Sannu da zuwa” Ya dan tsaya kallonta kamin ya amsa. “Yauwa, ya gidan” “Alhamdulillah” Ya zauna saman kujera yana kallonta. “Mun samu wani abu ne kike ta nishadi haka?” ‘Tun da a sanadinka aka samu ai za a sammaka’ Ta fada a ranta a fili kuma sai ta mike tsaye tana fadin. “Uhm wasu yan kudi ne na samu shi ne na siyo kaji na soya mana” Daki ta shiga ta debo masa a platecikin wanda ta soya ta kawo masa ta aje a gabansa. “Ina kika samu kudi?” Ya tambaya yana kallon naman da zai rabin kaza. “Allah ya ba ni” Ta amsa masa bayan ta zauna. “Haka kawai Allah zai baki kudi daga sama ba ta dalilin wani ba?” “Allah ne ya ba ni” “Ki dauke namanki, ki kawo min abinci, ba zan ci abun da ban san inda aka samo shi ba” “Matsalar talaka kenan ai, ga talauci ga girman kai, yaushe rabon da mu ci nama a gidan nan?” “Ba mu kadai ne a cikin wannan halin ba Rafi'ah, mutane da yawa suna ciki, mutane da yawa a da da kika san suna ci uku a wuni wssu yanzu biyu suke wasu daya, amman idan muka yi hakuri komai zai wuce, na san kina cikin hali Rafi'a, saboda kina ganin yan'uwanki da kawayenki a ciki wadata, hakan ba yana nufin Allah ya manta da ke ba, da ya ga dama da sai ya aura miki wanda yafi kowa kudi a duniya, amman ya jarrabaki miyasa ba zaki yi hakuri ba?” “Faruq kenan, yanzu duk hakurin da na yi na shekara biyar baka gani ba?” “Kin yi hakuri na sani, amman fadar sirrin gidana yafi komai yi min ciwo, idan na ci ko ban ci ba wani ya sani abun na min ciwo, bana son ki fada wani hali saboda halin da muke ciki dan Allah ki yi hakuri” “Ai dole kace na yi hakuri kam, ban da hakuri me kake da shi da zaka ba ni Faruq? Yanzu dan na samu kudi na siye nama na ci ya zama laifi? Ka san ina da ciki ina kwadayin abubuwa amman kai zargina ma kake, ni wannan cikin ma zubar da shi zan yi Wallahi, dan ba zan haihu ba ka yanka min bunzuru, wata kila ma ba zaka yanka min komai ba ka bar ni kyari da ido kamar kwaruru baki salab kamar Salamatu ina kallon yan barka ayi ta mana tsigumi” “Allah da yai masu kudi be manta da ni ba Rafi'a, ban san wace irin macece ke ba, idan na fita waje ina cikin damuwa da bakinciki a maimakon idan na dawo gida na samu nishadi sai na tarar bakinciki gida yafi na waje yawa, har fargabar shigowa nake” “To ka sake ni mana, ko zama da ni dole ne? Kai wai kana ganin Allah ba zai hukuntaka yadda kake azabbatar da mu da yunwa?” “Kika sake furta wata magana sai na mareki Wallahi” Ya fada cikin bacin rai, da muryar dake nuna da gaske yake. Ganin hakan yasa dole tai shiru domin ta san halinsa idan ya fusata be iya ba. TALBA POV. Zaune yake saman carpet yaran na zagaye da shi, sai kallonsu yake yana murmushin. Farincikin yara musamman marayu na daga cikin abunda yafi komai faranta masa rai, hakan ne yasa shi bude gidan marayu, kuma yana kai ziyara lokaci zuwa lokaci, wani lokacin kuma yana zuwa gurin ya wuni tare da su, ko ya dauke su ya fita da su zuwa gurin shakatawa. Ya kalli agogon hannunsa sannan ya daga yarinya dake cinyarsa da bata wuce 5 years ba ya mike tsaye. Sai yaran ma suka mike tsaye suka bi bayansa har zuwa gurin motarsa, ya saba musu idan zai tafi yana raba musu kudi ko alawa wani lokacin kuma chocolate. Sai da ya shiga cikin motar sannan ya mika hannunsa baya ya dauko ledar sweet ya bude ya fara raba musu, hannu biyu suke sakawa suna karba kamar yadda ya koyar da su, hayaniyar yaran yasa Ali dake driver side ya bude ya fita yana waya. Da dai daya Talba ya bisu yana basu, idan ledar ta kare sai ya bude wata, har sai da ya raba musu duka sweet din da ya zo da shi, sannan ya kwantar da kujerar motarsa ya kwanta yana jiran Ali dake waje yana waya. Bayan Ali ya kare ya dawo cikin motar ya rufe yana kallon abokinsa. “Ka gama da su?” Talba ya kalleshi kamar be ji abun da ya tambaya ba. “Har yanzu tunanin abun da kai ma Leila kake yi?” “Saboda Daddy da Momy na yi, kuma zan cigaba da yin hakan matukar hakan zai faranta musu rai” Yana rufe baki sakon Leila ya shigo wayarsa. “Ka zo ka kai ni shopping yanzu” Ya dauke idonsa bayan ya gama karantawa. “Leila tana ganin hakan ba zai saka na tsane ta ba? Ina son girmamawa Ali, ai ya kamata tace Yallabai, but look how she text me kamar wani direbanta” “Tana da gaskiya, ya kamata ka koyi girmama mace” “Ba macen da take kasa da ni ba, wannan ranar ba zata taba zuwa ba, ba zan taba zama wawa akan mace ba, sauke ni gida” Ali yayi murmushi yayi ma motar key, har suka isa gidan idon Talba a rufe, hannyensa kuma rumgume a kirji. Harabar gidan Ali yai farkin Talba be ce masa komai ba ya bude motar ya fita ya nufi kofar falon, kananan kaya ne a jikinsa, sai kamshin turare yake. Yana isa ya danna door bell din ya tsaya jikin kofar, cikin kankan lokaci aka bude masa kofar domin yanayin yadda yake danna door bell din dabam ne, da yasa ake gane shi ne. Dagowa yai a hankali ya kalli Baaba wanda ta bude masa kofar hawaye na sauko mata. Dan fuskar Mama yai domin ta saba idan ta bude masa zata masa sannu da zuwa angona, sai yai mata murmushi ranar da yan kwarai suke a kai kuma zai soma taba wasa da ita ko ya amsa mata. Shigowa yai cikin falon yana kallon Leila dake tsaye kusa da sofa ranta a bace, sai kuma ya juyo ya kalli Baaba. “Miya faru?” “Babu komai ranka ya dade” Baaba ta amsa masa sannan ta fara tafiya. Binta yai da kallo kamin ya maida dubansa gurin Amal dake tsaye upstairs tana zayyana masa abun da ya faru. “Ya Leila ce ta mareta” Talba ta kalli Leila. “Baaba ta ho dan Allah” Baaba ta juyo ta dawo kusa da shi ta tsaya cikin damuwa. “Bata hakuri” Talba ya fada yana kallon Leila, wani irin kallon mamaki tai masa, Momy na jin haka ta fito daga kitchen. “Ita fa tai min laifi” “Kin sani sarai bana maimaita kalma” “Baka san abun da ya faru ba” “Bana son na sani” Ya fada yana matsawa kusa da ita, kana kallon cikin idonsa ka san ransa ya bace. Sai da ta kalli Momy sannan ta kalli Baaba ta ce. “Ki yi hakuri” “Babu komai ya wuce” Baaba ta fada sannan ta nufi kofar fita falon zuwa BQ inda dakinta yake. Sai da ta fice sannan Momy ta karaso inda Talba yake tsaye tana fadin. “Wannan be kamata ba sam, taya zaka wulakanta yar'uwarka a gaban yar aikin?” “Be kamata ta dauki hannu ta mareta ba Momy, no matter what Baaba tai mata, ta yi jika da ita” “Gaskiya ka ci mutunci Leila, ka tauye mata hakki Talba, na yi shiru ne kawai saboda bana son na yi magana a gaban Baaba” “Kin san inda na fito Momy? Gidan marayuna, yaran da suke can basu da uwa ba su da uba, wasu ma a titi aka dauko su aka kawo su nan, wasu kuma danginsu basa iya kula da su, amman Leila Allah ya ba ta komai, kudi, uwa, uba, ilmi, dukiya, sai dan na saka ta ba da hakuri ne zai zama cin mutunci?” “Wannan kuma ai dabam ne, akwai tazara mai fadi mai tsawo tsakanin mai kudi da talaka, akwai abun da be kamata ayi agabansu ba, ko kuma a saka ayi musu, musamman inda muke da gaskiya” “Wannan zarar da kike magana, ban tana ganinta ba, kuma ba zan taba ganinta ba, ban taba jin na fi wani dan yana talaka ina da arziki ba, sai dai na ji nafi shi saboda yana kasa da ni a aiki ko a shekaru, ko kuma saboda ni ina miji ita tana mata, amman ba zan taba iya cin mutuncin wanda ya haife ni ba, wasu talakawan sun fi mu a gurin Allah” Yana gama fadar hakan ya nufi kofar fita a fusace. Momy ta bishi da kallo tana kada kai. “Finally, gatan Daddynka ya saka har ni kana iya tsayawa ka fadawa magana... ” Be juyo ba dan be ji akwai abun da zai sake ce mata. Balle kuma ta kuma ya kula Amal dake zayyana masa abun da ya faru daga can inda take tsaye. “Ya Leila ce ta kawo mata ruwa shi ne, gurin mika mata carpet ya tadeta ruwan ya zuba a jikin Ya Leila sai ta mareta...Shi ne abun da ya faru Ya Talba ko baka tsaya ba na fada maka, Ya Leila ce bata da gaskiya” Ta karasa ita da Leila suna watsawa juna harara, daman can haka suke kamar ba yan'uwa ba, basa shan inuwa daya. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe. Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo. Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -7️⃣ Bayan Baba ya sauke wayar ya kalli Inna cikin yanayin damuwa yace. “Bashiru ne yake mana maganar komawar mu can” Inna ta girgiza kai. “Babu inda zanje, ba a tserewa mutuwa a ko'ina take” “Na san da haka amman dai ya kamata mu bar garin nan saboda ance akwai yiyuwar su dawo, kuma kina gani kullum mutane barin garin nan suke” “Babu inda zanje Malam, na fi son mutuwata ta same ni a inda nake” “Ai kaji matsalarki kenan, shi kansa abun da yake ta magana kenan a lallaba masa ke” Inna bata sake cewa komai ba, har Baba ya ci ya shude. Duk abun da suke Aminatu na dama furar tana saurarensu, bayan ta gama ta kawo ma Inna ta zauna kusa da ita ta fara bata a hankali tana sha, Inna bata hana Aminatu shayar da ita ba, duk kuwa da kasancewar zata iya sha da kanta. Sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta rufe furar ta koma gurin girkin da take. Har ta girka ta gama bata cikin walwala da sakewar zuciya, ba na rashin yan'uwa ba, na tunanin kalaman da Inna tai mata? Ta ya zata rayu babu Inna? A hannu waye zata zauna ma? Ba ita kadai ba Baba ma ya zai ji idan suka wayi gari babu Inna? Ko da ace tana da aure rayuwa ba zata taba mata dadi babu uwa ba, balle kuma a yanzu da take tare da ita, Saurayinta Maniru ma yana cikin mutanen da yan bindigar suka kashe, bayan ta gama ta zubawa Baba nasa ta zubawa Isah a inda ake saka masa sannan ta kwashe sauran a Samira babba, ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta cire komai na jikinta sannan ta zauna saman dutsen da suke zama idan zasu yi wanka ta fashe da kuka. Kuka tai sosai sannan tai wanka ta fito idonta a kumbure, ta dora alwala ta shiga dakinsu tai sallah, bayan ta gama ta d hannayenta sama tana rokon Allah. “Ba ni da gata sai naka Allah, ka dauke yan'uwana a lokacin da ka so, ka sauya rayuwata zuwa yadda ka kaddara min, Allah ka yafe min ka jikan yan'uwana, ka ba mahaifiyata lafiya ka bar ni da ita Allah” Ta karasa hawaye na sauko mata, sannan ta shafa addu'ar ta mike tsaye, ta fito waje, sai da ta zuba ma Inna ruwa a buta sannan ta rika ta, ta kaita bandaki bayan ta fito ta taimaka mata tai alwala sannan ta shimfida mata abun sallah. “Allah ya miki albarka Auta” Inna ta fada tana kokarin gyara zamanta, domin a zaune take sallah a yanzu. Aminatu ta kalleta kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta amsa. “Ameen” Ta mike tsaye. “Bari naje na yi itace yamma ta yi” Kai kawai Inna ta daga mata, ita kuma ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka ta ta dauki zaren da take daure itacen idan ta yi, sannan ta saka talkaminta ta fice, ba ita kadai ba kusan duk yan matan garin da ma matan aure suna zuwa daji ne su yi kara da yamma saboda dafa abinci, abu ne mai wahala ka ga gidan da ake siyen itace a yanki, yawanci duk a daji suke yin kara. A da ta saba idan zata tafi yin kara akan biyo mata ko kuma ita ta biyawa wasu, sai dai tun bayan da aka tarwatsa rabin garin take tafiya ita kadai, saboda an tafi da wasu yan mata, wasu kuma sun yi gudun hijira, sauran da suka rage kadan ne. A gurin da ta saba tsayawa ta tsaya ta shimfida zanen sannan ta aje zaren a gefe, kana ta shiga tsintar karan, tana yi tana tuna yadda suke yi a da, ita da kawayenta, har tigengen suke cikin nishadi da walwala, sabanin yanzu da suka bar ta da kewa. Sai da tai rabin sannan ta samu kanta da mugun faduwar gaba, marar misaltuwa, a take ta nade wanda ta tara a daure ta dauka ta nufo gida da gudunta, kowa sai kallonta yake, kamin ta iso har hawaye ya fara sauko mata, bakin kofa ta jefar da karan ta rugo da gudun gurin Inna da ke kwance tana bachi ta taba ta. “Inna...Inna.... Inn” Bata karasa ba, Inna ta bude idonta da sauri tana kallonta. “Lafiya Auta?” Sai ta fashe da kuka, wanda hakan yasa Inna ta tashi zaune. “Tsoro nake ji Inna, gabana faduwa yake” “Tsoron me? Miya faru?” “Ban san ni ba, bana son na yi nisa da ke” “Auta kenan, kin isa ki tare min mutuwa ne? Da wani na tarewa wani mutuwa ai da na tarewa Yayana, kin san babu uwar da za a kashewa yaya a gabanta kuma ta kyale alhalin tana da ikon yin wani abu?” Maganar da Inna tai ya isa ya tabbatar da cewar ta fi jin bakincikin kashe mata yaya da akai fiye da keta mata haddi da aka yi. Aminatu ta yi kasa da kanta tana kuka sosai. “Kina kuka da wuri, ki adana kukanki saboda gaba” Ta kalleta. “Miyasa kike min fatan kuka Inna?” “Saboda zaki yi kuka mai yawa Aminatu, dole zaki yi kuka, ranar da zaki bude ido babu ni, ranar da zaki ga wata uwar idan kika tuna da taki dole ki yi kuka, ranar da kika ga wasu yan'uwa kika tuna da naki dole ki yi kuka, ranar da kika nemi wani abu kika rasa dole ki yi kuka, ni na riga na gama tawa rayuwar har na yi jikoki kuma na yi Auta, ke kuma yanzu rayuwarki take kan ginuwa, ta fara miki a haka, me kika tsammani a gaba? Dadi? Dadin yana tafe bayan wuya amman, yanzu na fi tausayin rayuwarki fiye da ta kowa Aminatu” Ta share hawayenta, ta kara matsawa kusa da Inna ta kwanta jikinta, ta lumshe ido, tana maida numfashi a hankali. “Allah ga yata, Allah ka zame mata gata” Inna ta fada a ranta hawaye na sauko mata, ba tana kalamai ba ne domin ta daga mata hankali, a a har ga Allah tana fadin abun da take jin ya kusa tabbatuwa a gareta ne, kuma tana jin nata mai kiran ya kusa kiranta, jikinta da mafarkanta suna bata haka, domin tana jin wani kalar yanayi na dabam a jikinta wanda bata taba jin irinsa ba, sai dai a kusa? Ko a nesa? Yau ko anjima? Shi ne abun da bata da tabbaci. Bayan sallah Magariba, Baba da Isah suna daki sun saka Inna a gaba suna ta kokarin convinced din Inna akan ta amince da magabar Bashiru su ma su yi hijira su bar garin amman ta ki, Aminatu kam tana zaune waje sai kallon hadarin dake haduwa take, ita kanta bata san na yi ba, tafiyar ko zaman? Inna tana da gaskiya idan sun tafi ba za su tserewa mutuwa ba, sai dai barin garin zai taimaka Inna ta manta wata damuwar, domin a cikin abubuwan da suke bata mata rai har da zaman gidan da take ganin an kashe yayanta kuma tana ganin a kowa ne dare kamar za su shigo ne su yi mata sallama kamar yadda suka saba, yadda rayuwa take a baya. Sai da akai kiran sallah isha'i sannan Baba da Isah suka fito waje, sukai alwala suka yi haramar zuwa masallacin. TALBA POV. Ya kusan minti ashirin a cikin motar sannan ta fito, kamin ta bude motar ta shiga ma wani aiki ne, ba karamin kufula shi tai ba, domin ya tsani jira ya tsani a bata matsa lokaci. Sai dai ko kadan be nuna mata ransa ya bace ba, ya ja motar suka fita fuskarsa ba yabo ba fallasa. Mai gadin be yarda ya tsaya jiran sai Talba ya danna horn sannan ya bude masa ba, tun a lokacin da ya ga ya shiga motar yai hanzari bude gate din ya tsaya, be bar gurin ba har sai da motar Talba ta fice daga gidan. Be kalli inda take ba, tukinsa kawai yake yana sauraren fm din dake gabatar da wani program, sai dai ita lokaci zuwa lokaci tana satar kallonsa, duk kuwa da kasancewar bata son su hada ido gudun kar ya ga tana kallonsa. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin titi, ya zata yi ta canja Talba? Shine tambayar da ta zo mata a rai, gata a mota daya da shi amman baya nuna mata wata alamar kauna, Baya ma son kallon inda take kamar ba masoyinta ba. “Na fasa zuwa shopping din take me home” Sai a lokacin ya kalleta tare da kiran sunanta. “Leila...” Ta kalleshi Irin duban nan na fusata, sai dai kwarjininsa ya hanata nuna masa fushinta. “I'm not your driver, and this should be the last time da zaki umarce akan wani abu” “Amman ni dazun ka cilasta ni na bawa Baaba hakuri bayan kuma bata cancanci haka ba” Ta fada idonta na cika da kwalla. “Me ka dauke ni ne Talba? Baiwa?” Be amsa ta ba, ya juya motar zuwa gida, kamin su isa hawaye da ya wanke mata fuska ya fi a kirga, yana yin farkin ta bude motar ta fita tana share hawayenta. Sai a lokacin ya juyo da fuskarsa yana kallonta har ta danna door bell din aka bude mata ta shige, sannan ya maida dubansa gurin Daddy dake tsaye jikin motarsa yana magana da Momy da gaba daya hankalinsu yake kan Talba. Bude motar yai ya fito ya rufe ya nufi gurin da Daddy yake tsaye yana wata irin tafiya kamar baya son taka kasa, kamin ya karasa ya zuba hannayensa aljihu kana ya sadda kansa kasa. “Ranka ya dade baka burge ni ba, da baka tura Leila gida gurin Gwaggo ba” Daddy ya fada yana kallon dansa, sai Talba ya kalli Daddy, kamin ya maida dubansa gurin Momy wanda hakan kr tabbatar masa da cewar Momy ta fadawa Daddy abun da yai ma Leila kenan. “Momy ba zamu iya yin abu a tsakaninmu ba har sai Daddy ya ji?” “Yes, ya kamata ya ji ne, saboda kana kokarin wuce guri” “Just because...” “It's just because? Tun ba yau ba Talba kana treating Leila kamar ba yar gidan nan ba, ya kamata ka sani ita ma tana da right fa!” “Miyasa karamin Abu zai bata miki rai Momy?” “Kai kaja komai, wacan yar aikin ma dana kora saboda kai na koreta Talba, saboda kana nuna kamar ta fi Leila gata a gidan nan, and now kana son na kori Baaba ko? Ka cigaba” Tana kaiwa nan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarenta, daga Daddy har Talba kallonta suke har ta shige, sannan Daddy Talba ya ce. “Ka saba da halin Momy ka ba tun yau ba, kar hakan ya dame ka” Talba yayi murmushi. “Daddy fita zaka yi?” “Yeah zan je gaisuwar Galadima ne” “Lemme drive you” “No tare da direba zamu je, go and rest” Murmushi ya sake yi ya dan ja baya, ya budewa Daddy motar sai Daddy ya shiga yana fadin. “Ance an kai hari Galadi, ya kamata A shirya wani abu a kai musu, mutanen nan suna cikin matsi” “Inshallah Daddy, ban ji ba two days ban duba news ba” “Sai na dawo” “Allah ya kiyaye” Ya fada yana rufe masa motar, sannan yaja ya tsaya har sai da driver ya ja motar Daddy suka fice daga gidan. Sannan ya nufi bangarensa, daga shi har Faruq da part dinsa yake kusa da nasa a kasa dakunansu suke, tsabanin bangaren Daddy da Momy da akai yi ma upstairs. Dakin da yake aje tardunsa ya nufa ya bude ya shiga cikin natsuwa ya zauna a kujera ya bude system dinsa ya cigaba da wani aikin da be karasa ba, be bar dakin ba sai kusan 6pm. Freezer ya nufa ya bude ya dauko ruwa ya zuba a cup ya surka da wasu sannan ya sha, bayan ya ajr cup din ya nufo kofar fita yana duba agogon hannunsa. Kai tsaye bangaren Momy ya nufa domin ya san izuwa yanzu ta huce fushin da take. Door bell din ya danna, yana dauke hannunsa Amal ta bude masa da sauri hawaye na sauko mata. “Lil Sis?” “Na'am?” “Me ya same ki?” Ya tambaya a yayinda ya saka kafarsa cikin falon yana dubanta. “Baaba ce...” Sai kuma tai shiru, shi dai kallonta kawai yake, as she knows ba zai sake tambayarta ba sai ta soma labarta. “Tana mopping sai ruwa ya zame ta ta fado...” Wani irin kallo tsoro yai mata. “Ta fado ina?” “Daga sama ta fado kasa!” “You're kidding me” “No Wallahi da gaske nake” “Ina take? Ta ji ciwo?” “Momy ta dauke ta sun tafi asibiti tare da Ya Leila tun dazu ba su dawo ba” “Yaushe abun ya faru?” “Lokacin da Daddy ya fita” Ya juya da sauri ya fita zuwa bangarensa domin a can ya baro wayarsa, yana shiga ya koma dakin karatunsa ya dauki wayar ya kira Momy, ringing tai sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. “Momy kuna ina?” “Gamu hanyar dawowa gida” “Ina Baaba?” Dan Jimm Momy tai kamin ta amsa masa. “Yaranta sun zo sun dauketa, sun tafi da ita, daman ciwon ba sosai ba ne” “Amman...” Be karasa ya lumshe idonsa sosai jin Momy ta katse wayar, hakan nan jikinsa ya ba shi kamar ba iya haka ba ne. Idan har ba babban abu ba ne, babu yadda za ayi Momy ta kaita asibiti da kanta, kuma har Leila ta bi ta su tafi tare. AMINATU POV. Tun safe take ta wanke tufafin Baba da nata har kusan daya da tabi, abun ka da marar aiki da kuzari, bata da kuiyar aiki kam amman bata da sauri, sai wuni ta kwana tana abu daya. Bayan ta wanke su fes ta matse ya daurewa ta soma sha shayawa, sannan ta bi tana kwashe wadanda ta shanya da farko suka bushe tana ninkewa, sai ta dora akai da haka har ta gama kwashe ta kai su daki, sannan ta fito ta shanya sauran. Ta dauke kayan da tai aikin da su cike da gajiya ta aje a inda suka saba ajewa. “Inna tashi ki yi sallah” Ta fada tana doso dakin, har zata shiga sai kuma ta juya ta dauki butar Inna ta cika da ruwa sannan ta nufo dakin, bata sake ce ma Inna komai ba har sai da jera tufafin Baba a inda ta saba saka masa sannan ta nufo inda Inna take zaune ta sadda kai kasa ta. “Inna...” Jin bata amsa ba yasa ta risina a hankali ta leketa, sai ta ga idonta a rufe, da sauri ta taba ta abunka da wanda yai nisan bachi sai ta zabura da karfi ta bude ido, da wanin irin karfi Aminatu ta hade yawu ta sauke ajiyar zuciya. “Inna anyi sallah, yi hakuri na tashe ki da karfi tsoro na ke ji” Sai Inna tai mata murmushi, sannan ta fara yunkurin tashi Aminatu ta kama ta ta mike tsaye, da taimakon Auta ta fito waje ta shiga bandakin, bayan ta fito ta rika mata butar tai alwala, sannan shimfida mata tabarma da abun sallah ta dauko mata hijabi. “Allah ya miki albarka” “Amin” Ta amsa tana kokarin rikata ta zaunar da ita, domin a zaune take sallah, saboda bata iya dadewa a tsaye. Sai da Inna ta fara sallah sannan ta dauki butar ta shiga bandaki bayan ta fito tai alwala ta zo kusa da Inna ta yi sallah, babu komai a cikin addu'ar sai nemawa Inna lafiya, domin shi ne abun da yafi komai tsaya mata a rai a yanzu. Kamar kullum bayan ta gama ta dora girki, sannan ta matsawa Inna furarta ta jiya ta bata. Baba be shigo ba sai bayan sallah isha'i. “Sannu da zuwa Baba” “Yauwa” Ya amsa yana sauke gajiya, kamar wanda ya wuni yana aiki, daman can haka yake tun da tsufa ya kama dan abu kadan sai gajiya ta tarar masa. Aminatu ta tashi da sauri ta dauko masa abinci da ruwa ta aje masa. “Allah ya miki albarka” “Amin Baba” Ta amsa tana jindadi albarka da suke yawan saka mata, ta san ko ba yau ba wata rana albarka nan zata bita. “Baba na wanke kayanka fes na ninke maka” “Eyeee Auta gayyar aiki, Allah kara miki albarka yar Baba” “Amin” Ta amsa tana murmushin data manta rabon da ya ziyarci kumatunta, Inna ma murmushin take tana kai hannu ta rage hasken fitilar dake kusa da ita. “Yau da wuri za'ayi bachi ko? Dan a san akwai gajiya” Cewar Inna tana kallon Aminatu, fuskarsa sai haske take duk da kasancewar dare ne, sai dai dan hasken farin wata daya haska ta da kuma fitilar dake kusa da ita yasa duk wanda ya kalleta zai yi arba da yadda fuskarta take ta haiba. “Jikina yau Alhamdulillah ji nake kamar ba ni ba” Baba yayi murmushi yana kallon Aminatu wanda ita ma murmushin take. “Ai na ga alama ga annuri nan a fuskarki” Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana amsa sallamar da Isah yai, kusa da Baba ya zauna sannan ya aje mata ledar yalo a gabanta. “Ga tsarabar kasuwa” “Allah ya maka albarka” “Amin” Ya fada kamin ya dora da amsa tambayar da Baba yake masa. “Wallahi kasuwa Baba taki ta koma kamar da, kowa a tsorace yake, saboda ana ganin mutanen nan kamar za su iya dawowa, kasan idan suka saka gari agaba sai sun ga bayansa, musamman garin da da suke da dade suna dafafe, tun da ba a taba shigo mana ba sai yanzu, gashi daman yan saka kai na yankin nan sun sha kashe mutane suna da haushin garin nan sosai” “Allah dai ya tsare, abun da Bashiru yake ta ce min kenan kullum, ga shi tsohuwar ta ku ta ki yarda mu bar nan” Cewar Baba. “Ku bar ni na mutu inda uwaye na da kakanina suka mutu, ai ba a tsirewa mutuwa” “Amman inna idan mu ka bar garin nan ke kanki hankalinki zai fi kwanciya fiye da nan” Amina ta fada, a karon farko kenan da ta saka bakinta a maganar. Sai Inna ta girgiza kai. “Babu inda zanje, kina ganina ko tafiya bana iyawa miya rage min Allah na tuba” “Mai ciwo da mai lafiya, duk daya ne a gurin Allah, sai kaga mutuwar ta dauke mai lafiya ta bar mai ciwo ai” Ta daga ma Baba hannu. “Dan Allah ku daina min maganar nan, ni ban hana ku tafiya ba, amman ni kam ba zan bar garin nan ba” “Allah ya kyauta” Duk suka amsa da Amin har ita. Ko da goma tai duk sun kwanta Inna da Aminatu suna daki, Isah da Baba kuma suna waje saboda garin akwai alamun hadari hakan yasa zafi ya tsananta, sai dai hakan be saka Inna fitowa ta kwanta waje, Aminatu kuma duk inda Inna take tana nan. Kowa yayi bachi ban da Aminatu dake ta tunanin abubuwa da dama ciki har da wasikar ta ta karshe da ta bawa Maniru shi ma ya bata, babu yadda be yi ba akan yana son tai masa iso gurin iyayenta ta hana shi saboda tana jin tsoro, ashe ba rabon gaisuwa da shiga tsakaninsa da iyayenta. Sai a yanzu take jin zafin mutuwarsa, kuma take ganin laifin kanta na hana shi ganin Babanta da tai. Ba shiri tai firgigit ta tashi zaune sakamakon kara bindigar da taji, a da can yan saka na yanki su kan harba bindiga idan dare yai, shi ma kuma ba kullum ba, sai dai tun bayan harin da aka kawo musu aka kashe wasu wasu suka tarwatse sai aka daina harbawar, ba ta hadda karar wacan bindigar da kuma ta yan ta'adda ba, balle ta iya banbanci ta su da kuma ta yan sa kai, sai dai yanayin yadda take ta jin tashin bindigar babu kakkautawa yasa hankalinta ya tashi sosai. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Daga waje ta ji muryar Baba yana neman agajin Allah. Kamin su soma jiyo hayaniyar mutane da alama gudu tsiratar da rai suke, Baba ya shiga dakin da sauri ya haske fitilarsa ya bude inda yake ajiyar kudi ya kwashe su ya saka aljihu. “Aminatu rikata tashi mu tafi yan ta'adda ne” Kamar an zare mata lakka haka Inna ta ji, sai jikinta ya kara nauyi, Aminatu ta shiga kokarin rikata da sauri amman ta kasa. “Tu tafi Malam, ku gudu ko dan saboda Aminatu” Aminatu ta girgiza mata kai da sauri tana kuka. “Ba zan tafi na barki ba Inna...” Ta shiga kama Inna da dukan karfinta tana jin kamar ace tana da karfin da sata iya daukarta ta dora akai, sai gashi tsaye ma ta kasa mikar da ita sai da Baba ta rika mata dayan bangaren, sun mikewa tsaye suka ji harbin kamar a bayan dakinsu, wani kuma a cikin gidansu. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Baba ya fada yana sako fitsari a wando sai kuma ya fara rawa yana tsalle kamar wanda ya tabu. “Allah ka batar da ni, Allah ka batar da ni kar su gan ni” A take cikinsa ya murda sai zawo, abun ka da mai tsoro sai yai cikin tufafinsa na sakawa ya tura kansa sauran jikin a waje, ga wandonsa sharkat da zawo da fitsari. Inna kam gaba daya hankalinta yana gurin Aminatu. Da hannu ta nunawa Aminatu karkashin gadon karfi alamar ta shiga domin bata ko ina magana. Da gudu Aminatu ta nufi karkashin gadon kamin ta karasa shigewa suka shigo dakin rike da magayen makamai, ga wata uwar fitila mai dan karen haske da suke haska ko'ina da ita kamar gulub. Dayan ya turo Isah cikin dakin da karfi, sannan ya karasa karkashin gado ya daga daga katifar ya jefar can gefe, sai ga Aminatu dunkule. “Fito ko na halbe ki” Dayan ya fada, da Aminatu ake sai dai tsabar tsoro yasa Baba ya ji kamar da shi ake, sai ya cire kansa cikin jakar kayan ya rarafo kusa da Isah yana ta kuka da karanta addur'ar da ta zo masa. “Yanarukuna bardan wassalamu ala ibrahim” Daga nan ya dora ta ayatul kursiyu, kamin su daka masa tsawa ya kama bakin ya rike jikinsa ta ko'ina rawa yake. Wani irin rawa jikin Aminatu yake tana ganin komai kamar ba gaske ba, yadda take fita da shigar da numfashinta kadai ya isa ya bayyana irin tsoron da take ji. “Dan Allah karku taba ta, ku kashe ni ita ku kyale ta” Inna ta fada, sai dayan ya saka bakin bindigarsa ya buga mata a kai, take gurin ya fara zubar da jini. “A kyale ta ita tafi sauran yaya ne? Kuna son ta kuka ja mata masifa ba kuri kuke ku kuna da jarumai a gari ba? Yayanka sai kashe mu suke duk inda suka ga bahillace sai ku kashe shi, Wallahi yau ko wa ba mu bari garin nan” Cewar wani tsukaken a cikinsu yana rike da ak47. Ko kamin ya karasa maganar har wani ya fara yaga tufafin Aminatu, a take ta fashe da kuka tana kiran sunan Inna tana jin kamar ace Inna ko Baba wani zai iya taimakonta. “Dan Allah ku kashe ni, ba zan iya ganin wannan abun ba...” Inna ta fada a rikece tana kallon Aminatu take ta kuka suna kokarin rabata da zanenta. “Kai bata giďa” Wani ya fada a take na kusa da kofa ya dauke ta da bindiga har harbi hudu. Wani irin ihu Aminatu ta saka jikinta na rawa idonta kamar zai zubo tana kallon gawar Inna dake kwance tana zubar da jini ido a bude, tassss wani ya dauke ta da mare wanda ya saka ta a take ta manta inda take, duniya ko lahira? Ba suma tai ma, sai dai jinta yayi karanci kamar yadda idonta suke ganin haske wutar marin da akai mata, sai dai ko kadan hankalinta be yi nisa da jikinta ba. “Bar shi ya fara yi” Dayan ya fada yana nuna Baba da ke jiran ace masa mutu ya mutu. Baba ya kalli Aminatu dake kwance tsirara sai kuma ya kalli mutane kamar be gane yarensu. “Tashi ka yi aka ce ko mu kashe ka” “Ya... Ya... Ya...ya.... Ya... Ta ce... Ce.. ” Daker ya furta, sai dayan ya saka bindigar ya halbe Isah dake gurfane kamar mai neman gafara yana kuka, halbi biyu yai masa a kai. “Ko ka yi ko mu kashe ka, ina ruwanmu da yarka ce, mu be dame mu ba...” Aminatu ta runtse idonta da sauri tana jin kamar ta bude ta ganta a wata duniyar...! ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe. Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo. Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -8️⃣ “Mutuwata zata fi min sauki fiye da aikata abun da kuka bukace ni da shi” Abun da ya fito daga bakin Baba kenan. Wanda hakan ya saka Aminatu bude idonta duk kuwa da kasancewar bata da tabbacin idan ta bude idon zata ga mutane, domin kamin ta rufe idon haske ne kawai take iya gani. Sai dai kallon be kare mata ma, domin ta yi arba da fuskar mahaifinta da suka haske da katuwar fitila mai haske. “Kai ba shi giďa” Idan suka ce aba wa mutum giďa yana nufin a halbe ka, take dayan ya daga bingida da zimmar harbin Baba sai bindigar ta ki tashi. Dayan ya sake daga ma ita ma taki tashi. “Kaga wani tsohon shige... Sa mai wuka” Dayan ya fada yana buga masa kan bindigar. Sai biyu suka kama shi suka kwantar da shi, dayan ya saka zabgegiyar wukarsa ya fara gagarawa a wuyan Baba, nan ma wukar bata kama ba. “Shege, samo dutse yau ba maganin karhe ba ko maganin mutuwa ka kasha sai mun kashe ka” Ban da kallon Baba babu abun da Aminatu take, ta kasa kuka hawayenta sun kafe, kamar yadda zuciyarta ta wanke tass, kwakwalwarta kuma ta zama fanko babu tunanin komai a ciki. Bata iya jin komai sai kalmar shahadar da Baba ke yi, duk yadda ta so ta kawar da kanta daga kallon yadda suke fasa kan Baba da katon dutse sai ta kasa ko da kwakkwaran motsi. Wani irin sanyi ne marar misaltuwa ya taso mata ya baibaye ilahirin jikinta, sai ta soma jin abu na mata yawo a cikin kai kamar hatsi. “Baba...” Ta furta daker tana kallon yadda suka rabe masa kai biyu a cikin dakin mahaifiyarta da suka harbe bayan sun kashe Ya Isah. “Tashi ki saka tufafinki” Dayan ya fada, sai ta kalleshi, duk da kasancewar hasken fitilar ba ya iya bari ya ta ga fuskokinsu, ba kuma dan ta fahimci abun da yake fada mata ba, sai dan hasketa da yai da fitila da yai, kana kallon kwayar idonta ka san bata cikin hayyacinta. Dayan ya kai mata mugun shuri a cinyarta. “Saka tufafinki dan ubanki” Maimakon ta saka tufafin sai ta juyarda fuskarta ta kalli inda ya shuri ta, ta kai hannu ta taba. “Baba....” Ta furta domin har yanzu tana jin sautin kalmar shahadar da yake a kunnenta, dayan ya fisgota sai ta mike tsaye sam ta manta a sirara take, yau ga ranar da bata kunyar siraicinta, ranar da dimauta da bakinciki suka saka ta manta babu sutura a jikinki. “Wuce mu tafi” Ta kalli inda mai maganar yake tana jin kamar ta taba jin kalmar. Tasss ya wanke mata fuska da wani irin mari mai zafi, sai ta rikice ta fara kuka. “Inna.... Baba.... Wayyo Baba.... ” “Saka tufafinki” Ras ta ji abun da ya fada, kuma ta fahimce shi, hakan yasa tai saurin nufar inda tufafin suke ta dauka, sai dai a maimakon ta saka sai ta rike tufafin tana ganin komai kamar a mafarki. Dayan cikinsu ne ya fisgota ya turo keyarta waje, sai ta samu kanta da bin bayan wadanda suke gabanta, abun da bata sani ba ashe a sauran gidajen nan ma sun fito da sauran matan da suka rage, tafiya kawai take tana jin kamar ba kasa take takawa ba, hade ta sukai da sauran matan dake ta rawar jikin tsoro, domin sun kasu kashi kashi ne, suna shiga gidaje. Kamar wandanda suka fito yakin duniya, haka kowa ganinsu, karyar mutun yace ga iyakarsu sai dai ya kiyasta a kiyasinsa ya fadi iya abun da idonsa ya gane masa, babura ne ko wane da goyon mutum uku dauke da makamai, wasu kuma mutum biyu ne a kai, wasu kuma a kafa sun saka manyan samarin maza a gaba dauke da hatsin da suka kwasa. Ba Aminatu ce kadai mace da suka tafi da ita ba, sai dai Aminatu ita kadai ce tsirara a cikin matan da suka kora zuwa daji, kamar sun kora dabbobi haka suka saka matan a gaba, wasu kuma suna daga gefe duk wanda yai kokarin guduwa daga cikin matan sai a halbeshi. Wasu mazan kuma suna bayan su Aminatu dauke da hatsin da suka dora musu, suna tafe suna dukan mazan a baya. Tafiya suke ta yi Aminatu na rumgume da tufafinta, bakinta kuma be daina furta Baba ba, da muryar da ita kadai zata iya ji, tana jin ta taka abu har ya huda fatarta ya shiga cikin kafarta, sai dai ko kadan tashin hankali be barta ta ji zafi ba, ko da ma ta ji bata isa ya tsaya cirewa ba, a cikin matan da suka tura gaba har da masu goyo, da kananan yan mata da matan auren, babu mai waiwaye balle ya taimaki wani, a cikin masu goyon wandanda yayansu suka fi takura musu da kuka sai su fige yaran su jefar, tsofafin da suka fara gazawa kuma sai su halbe su, masu sauran jini a jika kuma suna tafe suna dukansu. Zalincin da mutanen nan suke sai ka rantse da Allah ba zuciyar dan'adam ce a jikinsu ba. Ba su san wani abu tausayi ba, ba su ragowa ba, ba su san rai yana da muhimmancin ba, ba su wani abu imani ba, ba su san ragowa ba. Tun cikin dare suke tafiya a kafa suna ratsa wani irin jeji da Aminatu bata taba mafarkin gani ba, ba su isa inda za su je ba sai da hasken asuba ya fara ketowa. Ba ita kadai ba mata da yawa idan ka duba kafafuwansa zaka tarar sun kumbura, saboda babu mai talkami a kafarsa, kuma da yawa sun taka kaya wasu kuma ice ya shiga kafar amman ba damar cirewa, sai dai kai ta taka kafar a haka. Wani irin jeji ne da baka iya ganin iyakarsa, sai dai da alama mutanen kowa ne da dabarsa dabam, domin an raba matan ne wasu suka kora wasu zuwa yamma wasu kuma suka arewa, a cikin matan da aka kora arewa har da Aminatu dake rike da tufafinta.   Har ga Allah ba zata iya fadar inda take ba, har yanzu bata yarda ba rayuwarta ba mafarki bace, har yanzu kisan da akai Baba da Inna gani take kamar ba gaske ba ne. A wani kebantaccen guri aka tsayar da su, sannan wadanda suke manyansu suka taso da manyan fitilu suka haska matan, kamin su kalli mazan da su ma sun gama galabaita. “Wadanda ku kashe su kawai” Aminatu ta juya a hankali ta kalli mazan da bata iya tantance fuskar kowa a cikinsu saboda tana cikin nata tashin hankali. Kamar umarni suke jira a take suka budewa mazan wuta suka musu mugun halbi, wadanda bindiga bata kamawa kuma suka takasu da babur. Faduwa Aminatu tai durkushe ta fashe da kuka, domin a yanzu ta tabbatar ya baro duniyarta, ta shigo wata duniyar ta azzaluman mutanen da babu digon tausayi a zuciyarsu. Kukan da tai ne ya saka dayan sake haskata. “Wai iyakar matan kenan?” “Aa an raba dai, Daba... Ba ruwana ba zan fadi suna ba🤐, sun dauki rabi, kai duk mun watse garin nan fa yau babu wanda muka bari, Wallahi yau mun aiki” Dayan ya fada cikin mutanen da suka zo da su Aminatu, idan suka ce suna nufin gundu, domin akwai Babbar daba akwai karama, kuma daba kala kala ce, kowa da tashi, suna maganar yaron wata na kuka sai dayan ya ce. “Kai wacan ya dame mu da kuka” Wanda ke kusa da ita ya fisge yaron, sai ta rike masa kafafuwa tana kuka. “Dan Allah kai hakuri yaro ne be san komai ba” Ba su saurareta ba, sai suka aje yaron gefe suka halbeshi, da sauri uwar ta saka hannunta ta rufe bakinta saboda kar kukanta ya fito ita ma su halbeta. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Aminatu ta furta tana jin hawayen ya tsaya mata cak. Sai dayan ya haskata daga masa zuwa kasa. “Ku daure wadanda” Kamar dabbobi haka aka turasu zuwa wani gurin da babu wanda zai iya tantance shi, suka fara dauresu da sarka. Wasu kuma da igiya irin yadda ake yi ma dabbobi, idan an daure sai a saka igiyar a turke. Sauran da aka baro a garin suna da suke kan babura ba su iso ba sai kusan 6:30am daman can haka ake, idan za a saka mata to wadanda za su kura matan su zasu fara tafiya da su a gaba, su kuma sauran su biyo bayan idan sun gama na su aikin. Sai da haske safiya ya baibaye ko'ina sannan Aminatu ta tabbatar da ba ita kadai take ba, domin a gabansu wasu mazan ne aka daure masu yawan gaske, gafensu kuma akwai mata, gana ganin su kasan sun dade a gurin domin sun galabaita tufafin jikinsu sun yi datti sosai, mazan kuma wasu har gemu ya tarar musu, wasu gashin kai yayi musu yawa, a cikin wadanda suke daure akwai marasa lafiya. Sai dai wayewar gari zuwa karfe takwas an kashe mutun biyu a gaban idonta saboda sun cika tari, wai suna gudun kar su saka musu cuta, da zarar ka fara tari yayi yawa sai su ce a kashe ka kar ka saka musu cuta. A lokacin ne Aminatu ta samu kuzari da karfin zuciyar daura zanen dake hannunta ta suturta jikinta. A wani kebantaccen guri aka fito da abinci, aka fara bin wadanda suka dade a gurin ana zuba musu 3 Spoon na shimkafa fara babu mai babu gishiri babu komai a ciki, kowa aka zubawa jiki na rawa yake cinyewa yana hadeye yawu, ba a baka abinci wadataccen, kuma baka isa ka yi magana ba. Bayan an gama da su aka biyo gurin su Aminatu aka zuba musu a hannu, ita kam rike nata tai a hannu tana ta kallon abinci kamar wanda bata san abun da ake kira da shimkafa ba. Suna zaune a gurin har rana ta fara dukansu, daga ita sai ireirenta ne suke ta murkususun zafin ranar da ya tsanata, sauran wadanda suka tarar a gurin kam da alama sun sab da zafin rana domin ko motsi basa yi. Wadansu mutanen ne dabam suka nufo inda Aminatu take suka kwance ta tare da wasu matan suka zaga da su zuwa bayan wata zana da aka kafa aka kare ta kamar katanga. “Kwanta nan” Ya nuna mata wani karamin duhu dake shimfide a gurin. Sai ta kwanta kamar daman can an halittota ne kawai dan ta bi umarninsa, da kansa ya kama zanenta ya cire, ya bude kafafuwanta, sannan ya kwance wando ya kwanto samanta ya ratsa cinyoyinta yana kokarin ratsa jikinta, runtse ido tai, ta ja wani dogon numfashi kamar zata shude, sannan ta fashe da kuka.   Har cikin kwakwalwar kanta take jin yadda yake ratsa cinyoyinta yana kokarin shigarta da karfi, zabar da ta ji ne yasa ta fasa ihu, sai ya rika kanta ya buga da kasa, a take ta ji kan ya sara mata. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Take ta maimaitawa tana tuna nasihar da Inna tai mata. Bayan ya gama abun da zai yi ya tashi, sai wani ya shigo ya saka zanenta ya shafe gabanta, sannan shi ma ya kwanta jikinta ya aikata irin abun da mutumen farko ya aikata, bayan ya gama wani ya shigo, suka suka bi layi, tun tana iya ambaton Allah tana kuka har ta kai bata iya yin komai, Wallahi sun keta haddi Aminatu tun tana cikin hayyacinta har sai da hankalinta ya bace gaba daya, babu komai a tsakanin cinyoyinta sai jini da fatar gabanta data zazzago tana rawa, bayan sun gama suka janyota kamar shara suka fito da ita suka kawo ta a inda sauran matan suke suka barta nan kwance galala sai zanenta da suka rufa mata a jikin.   Ba Aminatu kawai sukai ma ba, kusan duk macen da suka dauko sai sun mata haka, suna yi ma mata fyade har sai sun fita hayyacinsu, ba matan kadai ba har da mazan suna keta musu haddi, sai dai ba kowa ce Daba ce suke haikewa mace kamar Dabar da aka kai su Aminatu ba, ta haka ne mazan da aka kama suke gane an ketawa mace haddi, ko kuma namiji, domin idan sun gama suna barin mutun a wulakance. LEILA POV. “So kike ki tonawa kanki asiri ne?” Momy ta tambaya tana kallon Leila, sai Leila ta girgiza kai tana share hawayenta. “To na ce ki yi shiru ya isa, babu abun da zai faru, amman wannan kukan da kike zai saka Talba ko Daddynku ya zargi wani abu, bana son tashin hankali kin sani” Kai ta daga mata, sannan ta kai hannunta ta dauki tissue ta goge hancinta, a daidai lokacin da Momy ta faka motar a harabar gidan. Kusan a tare Talba da Amal suka fito har ma da Kabir da ya shigo bangaren ba da dadewa ba.   Amal da Kabir suka karasa gurin Motar ban da Talba da ya tsaya jikin kofar yana kallon Momy da Leila da ta kasa hada ido da shi. Abun da Momy ta fadawa Talba shi ta fadawa Kabir, sannan ta nufo inda kofar falonta take wato inda Talba yake tsaye yana jiran karasowarsu. “Sannu da zuwa Momy” “Yauwa” Ta amsa masa sannan ta ratsa gefensa ta wuce cikin falon. Yana tsaye a gurin har Leila ta iso, idonta yayi ja sosai kana ganinta ka san ta ci kuka ba kadan ba, uffan Talba be ce mata ba, bayan kallonta da yake har ta shige cikin Falon. “Me Leila take yi ma kuka?” Ba Kabir daya tambaya ba, har Amal dake tare da Kabir din sai da ta Kalleshi, sai dai bata ce komai ba ta wuce cikin falon. Kabir ya saka hannayensa biyu aljihu yana kallon Talba da mamaki. “Really? Ina ce matar da zaka aura ce, miyasa ba zaka same ta da kanka ka tambaye ta damuwarta ba?” Talba ya dan daga kansa sama ya sauke. “Kabir Leila tana da matsala you know it” “Tana da matsala ko kana da matsala? Simple tambaya ba zaka iya ba” “No baka gane ba ne, ina son na san idan tana kuka ne saboda abun da ya faru da Baaba or not, saboda ban gansu da abun da Momy ta fada ba” “So Momy ta yi karya kenan?” Kabir ta tambaya yana masa wani kallo. Shiru Talba yai domin be san me zai sake ce masa ba. Ganin hakan yasa Kabir kai hannunsa ya tura kofar falon ya shiga ciki, Talba kuma ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi bangarensa. “Momy miyasa za ku dage sai Talba ya auri Leila ne? Ba ku tunanin kamar za ku takura masa ne?” Momy dake kokarin yaye mayafinta ta juyo ta kalli Kabir dake tsaye bayanta. “Ya maka wata maganar ne?” “No kawai ina ganin kamar Talba ba sonta yake ba” “Idan ba sonta yake ba wa yake so? Tun da kake a gidan nan ka taba jin ya yi maganar wata yarinya? Be taba yin maganar aure ba, sai da Engineer ya gabatar masa da Leila, kuma ya amsa yace yana son ta, idan kuma har baya son ta ai ba zai ce yana so ba” Kabir ya kwanto jikin kujerar yana fadin. “Ina ganin kamar ya amince ne saboda kar ya bawa Daddy kunya... ” Momy ta daga masa hannu. “Yana sonta baya sonta, saboda Engineer ya amince what so ever, ba damuwar mu bace, tun da ita Leila tana sonsa, daman shi ai be san so ba” “Amman tsakani da Allah fa zai cutu nan gaba, kuma ita ma....” “Kabir....!!!” Momy ta daka masa tsawa, tare da mikewa tsaye. “Ka daina yin abu kamar ciki daya kuka fito, kai yana tausayinka ne ko ya raga maka? Ba zaka gane hakan ba sai nan gaba, kullum maganar Talba kake baka duba yar'uwarka, baka tunanin idan aka fasa aure ita Leila zata iya shiga damuwa?” “Kara ta shiga damuwa a yanzu, da wanda zata shiga nan gaba... Domin abu ne mai wahala Talba ya canja rayuwarsa, imagine yanzu fa ni yake tambaya miyasa Leila take kuka ba zai iya tunkararta ya tambaye ta ba” “Zai canja, domin dole ya canja, dole ne mu gyara masa zama, idan ba haka ba zai wahala ne” “Ko kuma ita ta wahala ba..” Momy ta kalleshi da kyau. “Wai Kabir ko so kake mu bar Talba ya dauko mana wata bare can daban? Bayan ga yar'uwarsa a gida?” Ya dan tabe baki yana kallon Momy, domin ya san a yanzu ba zata fahimce ba. Daukar mayafinta tai da jakarta ta nufi upstairs rai a bace. Har zata shige dakinta sai kuma ta nufi dakin Leila ta murda kofar a hankali ta tura, sai ta same ta zauna tsakiyar gado hawaye shabe shabe a fuskarta wayarta makalle a kunne, da alama magana take da wani. “Da wa kike waya?” Momy ta tambaya with serious face. Sai da ta sauke wayar sannan ta kalli Momy. “Madina” Momy ta karasa shigowa cikin dakin gaba daya, tare da maida kofar ta rufe. “Leila wannan sirrinki ne, duk amintar da kike da Madina karki fada mata sirrinki” “Toh Momy” Ta amsa tana share hawayenta. “Ki dauka kuskure ne kowa ai yana kuskure, idan kina yawan kuka sai ki saka mutane su zargi wani abu” Saukowa tai da kafafuwanta a kasa, tana kara share hawayenta. Momy har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleta. “And for the very last time, zan sake tambayarki kina son Talba?” Leila ta daga kai. “Wallahi ina son sa sosai Momy, ina son shi, miyasa kika tambaye ni?” “Ba komai, ki kwantar da hankalinki” Leila ta daga kai alamar gamsuwa, sannan Momy ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. A hankali ta tura kofar dakinta ta shiga kai tsaye ta nufi gadonta ta sauke jakarta da mayafinta akai sannan ta zauna tana sauke dogon numfashi. “Allah ka yafe mana...” Ya furta tana lumshe ido, sai kuma ta busar da iskar bakinta. FARUQ POV. “Ina son anjima zan tafi kasuwa” Ya juyo ya kalleta yana kokarin saka agogon hannunsa. “Gurin me?” “Tufafi zan siyo, kuma zan siyawa Sultan ma” “Karki je ko'ina, kuma karki siyawa dana komai da kudin da ban san inda suka fito ba” Yana gama fadar hakan ya saka talkaminsa ya fice daga gidan gaba daya. Wani dogon tsaki ta ja ta murguda masa baki. “Wallahi sai na je, wato bayan talauci har da hassada tana damun talaka” Ta fadi zaune saman kujera rike da wayarta tana tabe baki, Data ta kunna ta shiga facebook, sai da ta fara duba notifications dinta, ta shiga comments tana duba yadda maza ke yaba surarta kowa da yadda yake yaba sabon hoton da ta dora, murmushi take tana ta bin comments dinsu da like har cikin zuciyarta take jindadin yadda suke yabonta. Bata da fargabar komai domin ta yi blocking din Faruq da duk wani dan'uwanta na kusa da ta san zai iya ce mata ta gyara ko ta daina, daga familyn Faruq har nata yan'uwan. Bayan ta gama karanta comments din ta leka inbox dinta, sakonni ta tarar da yawa cikin har da bakin fuskar da basu saba mata magana ba, kamin ta yi ma mutun reply sai ta duba profile dinsa ta duba abokansa aikinsa hotunansa da kuma inda yake zaune, da zarar ta ga alamar mai rufin asiri ne sai ta sake masa idan kuma ta ga sabanin haka sai ta yi blocking dinsa a take. “Ibrahim” Ta furta sunan dake profile dinsa sai kuma ta shiga duba hotunansa, da inda yake aiki kana ganinsa kasan mai abun hannun ne. Komawa tai inbox din ta amsa masa da thanks akan yaba kyauta da yai. Kasancewar yana online a take ya maido mata da amsa. “Babu godiya a tsakaninmu, wani ma yai rawa balle dan makadi” “Uhmm haka kace” “Haka ma yake, wani ya bawa mana matarmu balle kuma ni” Ba shiri ta zaro ido gabanta ya fadi. “Ya san ni kenan, ko kuma dai wasa ce” Ta fada tana tashi tsaye. “Matarku kuma?” Ta tambaya domin tantancewa. “Eh mana ba matar Faruq ba ce Rafi'ah?” “Ka san Faruq ne?” “Sosai ma tare muka yi makaranta da shi” Ta kara zaro ido. “Na shiga uku” “Gaskiya abokinmu yayi dacen mata, kina da kyau” Ya rubuto mata, sai ta koma ta zauna tana kokarin kwantar da hankalinta. “Da alama shi ma shegen ne” ‘Allah sarki, ashe kun yi karatu tare’ Ta amsa masa. ‘Eh sosai ma, na zo har aurensa ai, kuma ko lokacin da kika haihu na so na zo ban samu dama ba, ya Babyn?’ ‘Lafiya Kalau, ya naka iyalin?’ ‘Ni kam da saura har yanzu ban yi aure ba, sai na samu mai kyau irinki’ ‘Hmmm kana koda kyau na kamar gaske’ ‘Da gaske ne mana, Faruq be taba fada miki kina da kyau ba’ ‘Uhmmm’ Shine reply din da tai masa sannan ta kashe data ta aje wayar, ta nufi inda Sultan yake yana bachi ta tashe shi ta bashi ragowar kazar jiya ita ma ta ci ta koshi sannan ta shirya masa ita ma ta shirya ta dauki jakarta da mayafi ta riko hannun Sultan suka fito daga cikin gidan, sai da ta kulle gidan sannan ta nufi makontansu ta bada ajiyar Sultan ita kuma ta kama hanyar titi, ba yau ta saba satar hanya ta fita ba, wani lokacin idan ta tambaya ya yana ta ma fita take wani sa'in kuma bata ma tambayarsa, gashi idan ya fita baya dawowa sai dare, inda ba wani abun ya bijiro ba. Ko ma ya dawo ya tarar bata nan sai dai yayi hakuri ya danne abun a zuciyarsa. “Malam tsohuwar kasuwa” Ta fada bayan ta tsaya da mai adaidaita, kai kawai ya daga mata, sam bata lura da kofatun dake kafunsa ba ta shiga, sai da ta gyara mayafinta da face mask din dake fuskarsa sannan ta aje jakarta gefe. Kamar ance duba ki gani tana kallon bayan kansa sai ta ga kan kamar na tsuntsu har wani rawa yake kamar zai fado ga bayansa duk gashi kamar dabba. “Malam tsaya na fasa zuwa...” Ta fada da sauri tana runtse ido, sai mai Napep din ya faka gefen titi, tsabar tsoro yasa bata tsaya daukar jakarta ba ta fita da sauri tana haki, tana fita mai Napep din ya cigaba da tukinsa kamin ta rufe ido ta bude har ya bacewa ganinta, baya tai da sauri tana kara zari ido. “Innalillahi” Bata karasaba ta ji kamar ta taki abu, sai ta juya da sauri ta kalli Mahaukacin dake bayanta ya tara uban gashi ga tufafin jikinsa duk datti, wani irin tsalle ta daka ta ranta ana kare, wani irin gudun bala'i take mahaukacin na biye da ita shi ma da gudunsa. Wani shagon dake titi ta nufa kamin ta isa mutanen dake gurin suka watse da gudu domin sun san mahaukaci ba ya yi ma mutum da sauki, ita kanta bata taba sanin tana da gudu ba sai a yau, tana karya kwana ta samu wani gida ta shige ta turo kofar gidan da karfi ta rufe, tana ta haki kamar numfashinta zai fita. Mutanen gidan suka fito da sauri suna kallonta. “Lafiya?” Sun tambaya domin kama tai musu da mahaukaciya, kanta babu dankwali balle mayafi ga kafafuwanta babu talkami sai uban datti da suka yi, gashin kanta ma dake fake har ya yamutse, gumi sai sauko mata yake. “Mahaukaci ya biyo ni....” Ta fada daker tana haki, idonta har wani zurfin wahala sukai. “Subhanallahi tsokanarsa kika yi?” Dayar ta tambaya tana kokarin gyara goyonta, kamin ta amsa mata suka ji aka dukan kofar da karfi. “Zai iya balla mana kofa fa” Baturiya ya kauce jikin kofar da sauri ta dawo cikin mutanen tana kallon kofar. “Ban tsokane shi kasuwa zan je sai mai Napep...” Bata karasa ba tai shiru tsabar fita da numfashinta yake da karfi. “Wallahi haka yake, ranar fa tun daga rijiyar zaki ya dinga bin Marwa har unguwa uku” Baturiya ta kalli mai maganar, daman tun daga jin yanayin maganarsu ta ji ta banbanta data Zamfara, domin su kananci suke yi, gashi kuma an fadi rijiyar Zaki da unguwa Uku, wanda ta san ba a Zamfara unguwar take ba. “Baiwar Allah nan kuma wani gari ne?” “Kano... ” “Kano....?” Ta maimaita tana zaro ido, sai ta fadi a gurin zaune ta fashe da kuka. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe. Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo. Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -9️⃣ If you're not living around these people, you will never know what they are going through, fiye da haka ma yana faruwa, kawai dai Allah ya tsare mu su kuma yai musu mafita. Tun daga jin sunan Labarin kun san abun da ya kunsa. Ban san abun da readers suke so ba, idan an saka kudi da luxury life sai ace writers suna bude idon mutane, and when we're talking about reality kuma ba mu tsira ba, anyway if you don't like the story you can quit it.                   ***        ***        *** Har past 12am Talba yana zaune bangaren Momy doing nothing, haka nan kawai yake jin yanayinsa sai a hankali. Idan zaka tambaye shi damuwarsa ba zai ce maka ga matsalarsa ba. Mikewa yai tsaye ya isa gaban plasma ya kashe sannan ya wuce kitchen domin samu abun da zai sakawa cikinsa, rabonsa da abinci tun da rana, ko lunch din Momy ta hada be ci ba. Tea ya fara hadawa kansa sannan ya bude freezer dake kashe ya dauko cake ya kunna oven ya saka shi a ciki, sannan ya dauki tea ya rike a hannunsa yana ta kallon harabar gidan ta windows kitchen din, ko ina haske ne kamar rana. Juyowa yai a hankali jin kamar shesshekar kuka a falo, aje cup din dake hannunsa yai ya tako a hankali zuwa bakin kofar kitchen din ya tsaya. Sai ya hango Leila zaune a bakin stairs din sanye da kayan bachi riga da wando sai kuma safar dake kafarta, kanta ba dankwali sai hawaye take tana kallon wani bangare na falon, sam bata lura da shi ba har sai da ta juyo tana cigaba da rera kukan a hankali. Suna hada ido sai tai sauri share hawayenta ta dauke kai sannan ta mike tsaye ta juya a hankali zata hau stairs din. Har tai rabi ban da  kallon mamaki babu abun da Talba yake mata. “Leila...” Ya kira sunanta kamar wanda baya son magana, tsayawa tai cak gabanta na mugun faduwa, domin har ga Allah bata dauka yana zaune a falon har lokacin ba, da b zata fito daga dakinta ba, juyowa tai a hankali sai dai bata yarda ta kalleshi, sanin kanta ne ba zai tambaye ta me take yi ma kuka ba, kiran sunanta kawai da yai ya isa ya sanar da ita cewar tambayar damuwarta yake. “Na yi mafarkin tsoro ne...” Ta fada tana wasa da yatsun hannunta, bata tsaya jiran abun da zai ce mata ba ta juya da sauri ta haura sama. Da kallo ya bita har ta bace masa sannan ya juyo ya dawo cikin kitchen din, mamaki karara a fuskarsa. ‘Mafarki tsoro?’ Ya maimaita aransa, idan mafarkin tsoro tai me zai saka ta fito a nan ta zauna ita kadai? “Ko dai saboda ni ne?” Ya tambayi kansa yana kokarin kai hannunsa ya dauki tea, domin ya san abun da zai tashi hankalin Leila ba karami ba ne, and bayan shi ba ya ji akwai wani abu da zai saka Leila ta yi kuka ko ta shiga damuwa. Kamar wanda baya son bude baki haka ya kai cup din a bakinsa ya soma sha a hankali, dayan hannunsa ya saka a aljihu yana kallon oven din sai dai gaba daya tunaninsa ba a nan yake ba. Sai da ya sha rabin tea sannan ya kashe oven din ya ciro cake din daya dumama ya aje, ya dauki tissue ya saka a hannunsa sannan ya fara daukar cake din yana ci. Bayan ya gama ya kashe wutar kitchen din ya fito falo ya kashe wutar sannan ya wuce bangarensa. Shirt din jikinsa ya fara cirewa wanda hakan ya bawa kyakkyawar surarsa da murdaden kirjinsa bayyana, a kafadarsa ya dora rigar sannan ya nufi wani madaidaicin daki dake hannunsa na dama, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga, kai tsaye ya nufi teburinsa ya ja kujera ya zauna ya bude system dinsa yana duba sakon da Jahid ya turo masa na adadin kudin da za a kashe wannan watan na gidan marayu. “Okay” Ya furta sannan ya rufe system din ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kunna data ya shiga WhatsApp. ‘Zan rubuta maka cheque gobe, after that, ka bincika abun da yan gudun hijira suka fi bukata ka kirga ko nawa za akashe na mutun 300’ Bayan ya gama rubuta masaya kashe data ba tare da ya duba sako ko daya da yake shigo masa ba, balle har ya amsa. Fitowa yai daga dakin ya nufi Bedroom dinsa yana shiga ya aje rigar dake kafardarsa a muhallinta ya cire jean din jikinsa ya nufi bathroom ya jika jikinsa da ruwa ba tare da ya saka sabulu ba yai alwala ya fito, sai da ya tsane jikinsa sannan ya nufi closet din ya dauko kayansa na bachi. Wando kawai ya saka domin abu ne mai wahala ya kwana da riga komai tsananin sanyi, sai dai ya rufa da bargo, riga na cikin abun da ke takura shi ta hana shi sakewa idan zai yi bachin dare. BATURIYA POV. “Wallahi tun da nake a rayuwata ban taba zuwa Kano ba, ni fa ban taba barin Zamfara ba” Ta fada tana fyace hancinta daya cika da majina tsabar kukan data sha. “To ya akai kika zo nan?” “Agwagwa da buje na shiga nace ya kai ni tsohuwar kasuwa sai na ga kansa yan rawa kamar dan tsuntsu, bayansa kuma da gashi shine nace ya sauke ni yana sauke ni na fito da sauri, sai wannan mahaukacin ya biyo ni” “Minene kuma Agwagwa da buje?” Ta kalli wanda tai tambayar da idanuwanta da sukai ja abun ka da farar mace. “Keke Napep” “Oh Allah na wata kila aljanine ya dauke ki, kin san fa ance suma suna yin Napep din” “Ga zahiri na gani, wata kila da bance ya tsaya ba da yanzu na tsinci kaina a Russia ko Iraq” “Lallai kuwa abun na su ba wuya, to yanzu kina da waya a tare da ke?” Sai a lokacin ma ta tuna da jakarta, domin wayarta da kudinta har da makullin gidanta suna cikin jakar. “Na shiga uku Wallahi jakata na cikin napep din aljani nan kuma ya tafi da ita” A take ta fashe da sabon kuka, domin ta san samun wata wayar ma agareta yanzu abu ne mai wahala. “Subhanallahi, to kina da number wani akai ko mijinki ko Baba?” “Babana ya mutu sai dai mijina kuma shi ma ya siyar da wayarsa, yau ina cikin ukuba” Ta kara fashewa da kuka. “Baki da number kowa akanki” “Akwai ta yayata da Mamana” Sai da ta share hawayenta sannan ta karbi wayar ta saka number Mama tana shiga aka dauka. “Hello Sallamu Alaikum” “Mama ina cikin matsala Mama gani a Kano” “Kano kuma Rafi'a? Gurin me?” A nan ta labarta mata abun da ya faru, cikin labarin tafi nanatawa Mama cewar wayarta na cikin jakarta kuma ya tafi jakar, da alama ma batan wayarta yafi mata zafi fiye da ganin kanta da tai a Kanon cikin kankanen lokaci, yan kudinta ma duk suna ciki. Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Baturiya ta zama har wani yamutsar kai take. “Wallahi Takauci be yi ba, daman ance idan mutum ya kwana arba'in be ci nama ba idan yai maka baki zai ya kama ka, gashi nan ai laifin Faruq ne” “Wanene kuma haka?” Sai tai shiru bata fada ba, domin bata son tace mijinta ace bata jin magana tun da har ya hanata fita kuma ta fita duk kuwa da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya hanata kuma ta fita ba. Account din mai POS din unguwar aka karba aka turawa Mama ta turo mata kudin mota, aka ciro mata sai dai tafiyar ba zata yi a yau ba domin yamma ta yi gashi kuma hanyoyin nigeria babu kyau a dole ta hakura sai gobe da safe ta kama hanyar dawowa Zamfara. Kamar kullum sai bayan sallah isha'i Faruq ya dawo gida. A bakin kofar gidan ya tsaya ya kwankwasa yana sauraren ta bude masa amman shiru bata bude masa ba, ya sake kwankwasa nan ma ba a bude masa ba, yayi haka kusan sau hudu sai a na biyar ya saka makullin hannunsa ya murda ya bude kofar daman can a tunaninsa ko ta rufe kofar ne daga ciki kamar yadda ta saba, sai dai tun a yanayin yadda ya tararda gidan ya tabbatar masa da matarsa bata nan. Yayi sa'a akwai wutar nepa sai ya kunna gulob din waje dana falo ya shiga daki ma ya kunna, tsaye yai yana karewa dakin kallo komai a watse kamar yadda ya fita ya bar shi, daman yana fita ta shirya ta fita bata tsaya gyaran komai ba. Gashi kuma be tararda ita ba, ajiyar zuciya ya sauke. “Rafi'a Allah ya shirya ki” Ya furta cikin yanayin dake nuna alamar be jidadin daya sami gidan a haka ba, babu abun da ya fi bakanta masa rai ma kamar tararda ita da be yi ba a gidan, ko da yake halinta ne ko da ba zuwa unguwa ba takan fita makota tai taje can tana hira ko ta rika musu aiki alhalin ga nata aikin na gidanta ta bari, sai dai shi ya kasa sabawa da wannan halin, domin duk mai mata baya son ya shigo gida ya tarar matarsa bata cikin gidan idan ba da wani dalili ba, babu irin fadan da be mata ba amman bata canja ba, har ya gaji ya saka mata ido.   Gadon ya fara gyarawa sannan ya kwashe kayan data bari ya aje su a guri daya, ya gyara shimfidar Sultan ya dauko tsintsiya ya share dakin har zuwa falo, sannan ya zauna saman kujera ya daga kansa sama yana tunanin halin damuwar daya samu mahaifiyarsa a ciki, kusan kullum uwarsa bata rabuwa da damuwa domin idan babu na abinci akwai na rashin lafiyarta, sai dai a yanzu ta fi shiga damuwar fiye da koyaushe, a da tunanin na yadda zamu samu abun da za su sakawa bakinsu ne ko kuma na maganinta tsabanin yanzu da tunanin aurarda yarta wanda kanwace a gurin Faruq ya hanata sakat, ba Mahaifiyarsa kadai ba, idan aka fasa auren nan shi kansa zai shiga damuwa balle kuma ita kanwar tasa, domin mijin yace ya gaji da daga auren da ake ta yi, su kuma ba su da wani abun aurar da ita a yanzu, sadakin da suka karba da dadewa Mama ta saka shi a cikin kasuwancin da take ta zimmar zata dan juya ko zata samu riba, sai gashi ba wan ba kanen wato ba uwa balle kuma riba, daman sana'ar talaka sai Allah, balle kuma irin nata sana'ar da ake ci ciki. Bayan matsalar kanwarsa ga matsalar kudin hayan da ke jiransa next week, gashi ba shi da mafitar kudin a halin yanzu, dan aikin da yake ta applying shi ma shiru kamar wanda ya zagi gobnati. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya furta yana dafe kansa. “Allah ka kawo min sauki Allah ka yi min mafita” Ya fada yana mikewa tsaye ganin har goma ta kusa matarsa bata dawo ba, duk yawunta bata wuce tara na dare sai idan biki ake ko kuma wani abu ke saka ta kai dare, ko da makota ta shiga bata wuce 9pm. ‘Ina tunanin tafiya nijar zai fi min gurin ginar zinari, sai dai shi ma ai dole sai ka samu kudi, samun wanda zai baka rance ma a yanzu ai aiki ne’ Ya nufi kofa yana ta sake-sakensa da tunanin inda zai samu mafita. Babu waya a hannunsa balle ya kira ya tambayi inda take domin ya bada wayar jingina tun shekaran jiya ya karbo musu abinci, hakan yasa ya fara nufar gidansu Maman Amira makociyarsu domin Baturiya tafi zuwa can ta wuni saboda suna da rufin asiri daidai gwargwado, ba shi ma ko mutanen unguwar sun shaidi Baturiya da son shigewa masu kudi, idan ka ga tana shiri sosai da mutum to mai rufi asiri ne. Cikin almajiran dake zama bakin kofar gidan ya kira daya ya aike shi cikin gidan ya kira masa Rafi'a, almajirin na shiga ya fito dauke da Sultan dake bachi ya mikawa Faruq. “Ance wai bata nan, tun dazun da ta shigo bar Sultan tace zata je kasuwa bata dawo ba, kuma ta kira wayarta a kashe” Cikin fargaba Faruq ya karbi dansa ya juya yana yi ma almajirin godiya ya koma gida, kwantar da shi yai ya fito waje zuwa gurin mai shagon daya bada jinginar wayarsa. AMINATU POV. Sai da yamma lis ta farka, ta dade da farkowa daga suman da tai sakamakon ruwan da suka zuba mata ga kuma zafi rana dake dukanta. Kana kallon kwayar idonta zaka karanci gajiya, da wahala dake tattare da ita. Gaba daya jin take kamar babu mararta zuwa kasan cinyoyinta, ko motsasu ta kasa yi, hakoranta kuma sun dantse gam kamar a hade aka haliccesu, a kwance take amman jiri sai dibanta yake tana ganin hadarin dake haduwa yana juyawa. Ba ita kadai ce a cikin wannan halin ba, sai dai wasu sun fita juriya domin suna da aure wasu kuma sun yi har sun fa ra warkewa. Kamar jira suke ta farko sai wani yaja hannunta ayayinda sauran jikinta yake kasa zuwa gurin turken da suke daure matan, a kafa duka daureta kamar sauran matan, sai dai har lokacin a kwance take ta lumshe ido tana sauraren yadda numfashinta ke fita a hankali, babu tunanin komai a kanta tana son tai tunanin amman ta kasa, tana tai kuka ta kasa sai a yanzu ta gane ashe yin kuka ma wani babban gata ne, yin tunani ma wata baiwa ce, yau ta rasa ta ina zata fara tunani balle ya gayyato kukanta.   Sama sama take jin kafarta na mata zogi, saboda tafiyar data sha da kuma Ƙayoyin da suka taka, ba ita kadai ba kusan kowa yana fama da ciwon kafafuwan wasu sun taka kusa wasu kaya, sai dai basa jin zafi a lokacin sai a yanxu, wasu kuma daurin da akai musu ne yake musu ciwo, domin na da wasa suke daure mutum ba. Kamar dazu da safe haka aka biyo su ana ba su abinci a hannu cibi biyu wasu uku, kowa aka zubawa sai yai sauri ya cinye saboda yunwa ta ci su har ta galabaitar da su, daman idan suka ci cibi biyu ko uku da rana ba za su sake ci ba sai kuma dare, wani lokaci ma ci daya ake a rana.   Komai tsananin zafin rana ko sanyi ko ruwa ba a basu abun rufa ko gurin fakewa, sai dai sanyi ya kare akansu, haka ma idan ruwa ne sai dai ayi ruwa a gama ya jika musu kaya kuma tufafin ya bushe a jikinsu, idan rashin lafiya ta same su sai dai su mutum domin babu zancen basu magani balle kuma akai su asibiti. “Dan Allah ku kwance mu yi sallah magariba ta yi” Daya daga cikin mutanen dake daure ya fada, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake rokon su barshi yai sallah. Sai wasu kananan samari suka nufo inda yake suka kwance shi suka ware shi gefe suka saka bulala mai kyau suna dukanshi. “Wato kai shege ko, baka daddaraba” Duka suka masa ba na wasa ba, daman jikinsa da sauran bulala da suka masa dazun saboda yace su bar shi yai sallah, a kullum sai yayi magana kuma a kullum sai sun masa duka. (As I'm  writing this mutumen da yake cewa su bar shi yai sallah is no more, Wallahi sun kashe shi neighbor din mu ne, and they sent his friend wanda aka kamasu tare ya fadawa iyalinsa bayan an biya kudin fansar karbo shi) Bayan sun gama dukansa suka maida shi gurin da yake suka sake daure shi yana ta kuka, ga wahalar yunwa ga na dukan dazu dana jiya ga shi yanzu kuma sun kara masa da wani. Ana gama sallah magariba ruwa ya fara sauko, ta yanayin garin suke iya gane magariba ko azahar da la'asar domin babu masallaci balle su ji kiran sallah balle kuma agogo. Yan bindigar ne suke ta gudu suna neman gurin fakewa, mutanen da aka ma kuma suna daure aka fara ruwan kama da bakin kwarya yana sauka a kansu, iyakar abun da suke shi ne su dukar da fuskarsa saboda kar ruwan ya taba fuskarsu, wasu kuma su saka hannu su kare fuskar tasu, sai dai hakan be hana ruwa ya jika su. A cikin mutanen da ruwan saman ya jika har da Aminatu, dake kwance galabaice kamar sauran matan da basa da kuzarin yin komai, abincin da aka bata ma bata karba ba, komai ganinsa take kamar ba shi ba, har yanzu bata yarda mutanen da suka kashe mata uwaye da yan'uwa suka kawota daji suka keta haddinta yan'adam ne masu zuciya da jini a jikinsu ba. Ta kasa yarda a duniyar da ta sani take, gani take kamar daukarta akai aka jefata a wata duniyar ta dabam mai cike da azzalumai, kuma marasa tausayi da tsoro Allah.   Haka suka kwana a cikin sanyi cikin kwabon ruwa har safe, sam ita ko yunwar bata ji, sauran da suka dade nan kuma suna fama da yunwa domin sun sabu da gurin ya zame musu kamar gida, wasu sun yi wata uku wasu biyu wasu hudu har biyar ma.                   ***       ***        *** MONDAY MORNING 9:21am. “I wonder what wrong with our country? Kashe mutane ya zama kamar abinci?” Cewar Kabir yana kallon hotunan da aka turo na harin da aka kai a garinsu Aminatu, abun ya kazanta kuma yayi muni sosai, musamman harin nan na biyu yafi na farkon ma, domin a yanzu an bar garin ba kowa, tun a lokacin da abun ya faru suka kashe na kashewa suka tafi da wasu, sauran da sukai rai suka gudu zuwa wasu garuran gudun Hijira! Talba ya kalleshi yana kokarin gyara agogon hannunsa. Ba al'adarsa ba ce yin breakfast a bangaren a week days sai dai weekend, idan har zai karya to sai dai ya karya bangaresa ya sha tea ko kuma ya tafi office dinsa ya karya, sai dai ya zame masa al'ada shigowa ya gaisa da Momy kamin ya tafi aikin, sanadin hakan yasa suka sabu da Baaba idan ya shigo tana masa kirari ko da ba zai amsa mata ba zai mata murmushi ya gaishe ta sannan ya fita. Yau sai ya ji dabam domin ya saba idan ya shigo zai tarar ita take shirya abun karyawa sai idan weekend ne Momy take tayata su hada komai a tare. “Wai ya ake son talaka yayi ne? Su fa suke noma, yanzu an hana su noma wadanda sukai kuma a kone kuma a ashe su a dauke matansu kai jama'a wannan abun yayi yawa, nan gaba abinci ma sai yayi wahala” Momy ta kalle tana kokarin aje flakes din ruwan zafi a dinning. “Shiyasa ga su nan sun bi sun cika mana gari da bara kamar za su kwata da karfi” “Haba ai dole Momy, ki duba yadda mutumem kauye yake alfahari da noma amman su bar komai nasu su dawo inda babu kowa suna bara, abun tausayi ne Wallahi” “Su ma ai sun so, tun da su suka fara kashe Fulanin” “No wannan ba hujja bace Momy idan ma da gaske ne” Tabe baki tai ta cigaba da abun da take, har suka ci suka shude Talba be ce komai ba, daman shi ba komai ke saka shi magana ba, ko da kuwa abun ya dame shi. “Momy zan tafi aiki” “Yau da wuri?” Ya daga mata kai. “Allah ya tsare” “Ameen” Ya amsa sannan ya fito daga bangaren yana wani irin kamshi turare mai jan hankali yan mata da saukar da natsuwar mai shakarsa. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa sai da yai knocking sannan ya tura kofar sai ya jita a rufe, door bell din ya danna sannan yaja ya tsaya. After few minutes aka bude masa kofar. Sai da suka gaisa da Amal da ta bude masa kofar sannan ya karasa can ciki gurin Daddy. Sai ya same shi zaune rai a bace yana kallon wayarsa, domin labarin harin da aka kai ya karadi kafofin sada zumunta musamman Facebook. “Wa'alaikassalam” Daddy ya dago yana amsa masa sallamarsa, Talba ya zauna kusa da shi yana karantar bachin ran daya bayyana a fuskarsa.    >>>>>><<<<<< Sauran page daya mu gama free page, if you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank and sent the evidence via 08036126660. Yan nijar kuma za ku biya ta wannan number +227 90 16 59 91 sai na yi adding dinku a group. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.   Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. *💔 BAKAR WASIKA 💔* By Khadeeja Candy Page -1️⃣0️⃣ Talba ya mikawa Daddy wayar bayan ya gama dubawa. “Daddy ku da kuke kusa da gobnati ya kamata ace kuna fada musu halin da ake ciki mana, mutanen nan suna cikin bala'i, kamar ni ne, kana zaune kana rayuwarka sai a iskoka a koreka daga gidanka a akashe yayanka kuma a keta haddin matanka, Wallahi tausayi suke ba ni matuka” Cewar Talba cikin wani irin bacin rai da jin zafin abun da yake faruwa. Daddy yayi murmushi yana gyara zamansa. “Mu'az kenan, waya fada maka gobnati bata san halin da ake ciki ba? Sun san komai, wannan matsalar tsoro tana kawo kudi sosai, fiye da yadda kake tunani, duk jihar dake fama da matsalar tsaro kudin da ake ware mata dabam, idan har aka magance matsalar to abinci wasu zai tsaya, kuma duk jihar da kaga suna fama da matsalar tsaro to suna da cigaba da ake bukata” “Amman Daddy basa tsoron hakkin rai?” “Wannan kuma ai sai lahira, Allah dai ya kyauta kawai amman matsalar tsoro a yanzu abu ne mai wahalar magancewa, domin an fi samun kudi ta gurin tun daga manya har kanana, na mu dai addu'a ne, da kuma taimaka musu da abun da Allah ya ba mu” A hankali Talba ya busar da iskar bakinsa ya kalli Amal data doso inda suke sanye da uniform dinta na makaranta. “Na yi magana da PA zai yi list din abubuwan da zamu siya mu kai musu soon” “Maa Shaa Allah, hakan na da kyau” “Wa za a kaiwa? Baaba?” Amal ta tambaya tana aje fular abinci. Daga Daddy har Talba kallonta su kai, ta san ba maganar Baaba ake ba, kawai ta dauko maganar ne saboda tana son fadawa Daddy abun da ya faru ne, daman ita ce yar gulmar gidan komai akai a bakinta za aji. “Wace Baaba kuma? Yan gudun hijira ake magana” “Au na dauka Baaba za a kaiwa, Allah yasa dai ta ji sauki” “Miya same ta?” Daddy ya tambaya, a nan Amal ta zauna gefensa ta labarta masa irin abun da ta fadawa Talba. “Taya Doctor zata yanke wannan hukunci bs tare da sani na ba? Tafi ki kirata” Daddy ya fada rai a bace. Sai ta mike tsaye gabanta na faduwa. “Ya sai ka ce ni kai ka fada” Talba yayi murmushi, ita ma murmushin tai ta fice, bayan ta wuce Daddy ya kalli Talba. “Ka san da maganar ne?” Talba yayi shiru ba tare da ya amsawa Daddy da eh ko aa ba. Wanda hakan ya tabbatarwa da Daddy cewar ya sani kenan, domin idan be sani ba kai tsaye zai fadi cewar be sani ba. Daddy be sake cewa komai ba har sai da Momy ta shigo dauke da wasu manyan kulolin abinci ta aje a gabansa, sai da Momy ta kalli Talba sannan ta kalli Daddy tana karantar yanayinsu. “Lafiya dai engineer?” Daddy ya kalleta irin duban da ke fassara mata bacin ransa. “Baaba ta fado, har kun kaita asibiti amman baki sanar da ni ba” Dagowa Momy tai ta kalli Talba da kansa ke kasa. “Ina ganin kamar karamin abu.... ” “Karamin abu? Da gaske? Amina kin san abun da kike fada kuwa? Mutum ya fado daga sama zuwa kasa ki kira shi karamin abu? Idan har karamin abu ne yayanta zasu dauke ta su tafi da ita ne? Ko da ma karamin ciwo ne tun da har a nan ta samu matsalar ai ya kamata ki sanar da ni, kuma be kamata a bar yayanta su tafi da ita ba, a nan ya kamata a dauki nauyin komai na ta, shekara biyu tana aiki tare da mu” “Ranka ya dade, ba wani ciwo ne sosai ba, kuma na kaita asibiti sun bata magani sai ta kira yayanta tace zasu tafi da ita, babu yadda ban yi ba amman suka ki yarda, kuma ina da niyar fada maka anjima da dare idan ka natsu” “Yanzu idan wata ce a cikin yayanki ta fado zaki mata haka ne? Balle tsohuwa? Sometime kina abu kamar damuwar wani ba damuwarki ba ce” “Allah ya huci zuciyarka Engineer, amman be kamata damuwar wani ta dame mu ba, mu ma yanzu idan muka shiga cikin wata matsalar babu wanda zai damu da halin da muke ciki” “Okay, yayi kyau daga yau ba zan sake biyan mai aiki ba, indai zan dauki mai aiki ta taya yaranki aiki ne ba za a sake ba, idan har damuwar wani be kamata ya dame mu ba, karki sake gabatar min da wata matsalar yan'uwanki balle kawaye” Yana kaiwa nan ya mike tsaye a fusace ya nufi hanyar dakinsa. Momy ta rutse ido ta bude ta kalli Talba da shi ma kallonta yake domin ya san shi zata dorawa laifi. “Karamin abu ma, sai ka tasa mahaifinka a gaba kana tsegunta masa? Talba wacce irin rayuwa ce wannan? Mun yi fada hankalinka ya kwanta? Kuma zai fita be karya ba, ina tunanin haka kake so ai? Kai na ya fara kwnacewa da lamarinka” Uffan Talba be ce ba, har tai ta gama ta mike tsaye ta fice, mikewa yai tsaye ya ciro wayarsa dake ringing. “Ali” Ya fada bayan ya danna picking. “Talba ka fita office ne?” “No ya akai?” “No ina son magana da kai ne, na dauka kana office na biyo” “No yanzu zanje, yau da wuri zaka je aiki kenan?” “Eh muna da patients da aka kawo mana, kasan sojoji sun samu kwato wasu daga cikin wadanda yan bindiga suka tafi da su, akwai wadanda suka samu rauni sosai an kawo mana su” “Eh na ji an kai hari abun ba dadi Wallahi” “Sosai an kawo wasu shekaran jiya wadanda suka harba abun ya kazanta” “Allah ya kyauta, We can talk later” Ya sauke wayar, sannan ya nufi kofar fita yana kiran Jahid. AMINATU POV. Labarin harin da aka kai ya karade ko'ina a Nigeria, gidanjen jaridu da kuma kafofin sada zumunta. Hakan yasa aka turo jirgin sojijin tun daga jihar Lagos har zamfara. Kwashe gari aka bi su da danyen dankalin hausa a hannu duk wanda aka gutsawa sai yai sauri ya cinyewa, bayan sun gama ci kuma sai a bisu duka musamman wadanda aka akai maganar kudi da yan'uwansu ba su kawo ba. Sun fi dukansu fiye da kowa, duk abun da ake Aminatu na kwance bata iya komai ba, har yanzu bakinta a nauyaye yake, idanuwanta ne kadai abun da suke aiki a jikinta sai numfashi. Tana kwance galala ta daga kanta sama tana kallon jiragen sojoji guda biyu da suke shawagi a sama, kararsu kadai ta isa ta kurmantar da mutu, sun yi kasa kamar zasu saki wuta sai dai ba su saki wutar ba suka gangara can nesa da damarsu suka saki wutar a inda babu mutane. Bayan ya wuce barayin suka fito daga gidanjensu na bukka dake can nesa da inda aka daure su Aminatu, suna da yaya da mataye a cikin bukokin sai dai akwai tazara mai yawa a tsakaninsu. Suna isowa inda suke mutunen jiya ya sake rokon su bar shi yai sallah, sai suka hau shi da zagi. “Kawo shi nan” Dayan ya fada, sai sauran suka kwantoshi daga inda yake suka nufi wata bushiya inda mutunen yake, suka daureshi jikin icen suka sako kansa kasa kafafuwansa a sama yana ta lilo. Tun yana kuka yana rokon su kwance shi har ya gaji ya fara kalmar shahada, majina ta fara fitowa ta hancinsa tana zazzagowa kasa tare da hawayensa. Ba su kwance shi ba sai da su suka tabbatar rai ya bar jikinsa, sannan suka sauke shi kasa, lumshe ido Aminatu tai wasu hawayen suka cika mata ido. Bata sake bude idon ba sai da ta sake jin karar jirgin, wannan karon da fatan mutuwa take kallon jirgin burinta ya sako wuta kowa ya kone har ita, domin tana da tabbacin babu wata rayuwar jindadi a tare ita ko da rayu! Ta ina ma zata rayu? Taya zata fita a nan? Idan ma ta fita gurin wa zata je? Da wa zata zauna? Wa zai rike ta? A kashe mata kowa, yayyu da iyaye, idan zata nemi yan'uwan uwa ko na uba ta ina zata fara nemansu? Ina zata gansu? Zata fita a nan ma? ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ Ta maimaita a cikin ranta, domin bakinta ya mata nauyin da bata iya saka komai ta tauna balle har ta furta wani abu, wata kila kalamanta sun kare wata kila kuma har da rayuwarta, farinciki kam ta tabbatar da ya barta. Bayan sallah isha'i ta dan unkura ta tashi zaune tana jin kamar ba zata iya zaman ba kuma gashi ta gaji da kwanciyar. Hannunta ta kai ta damki kasar gurin ta junke a hannunta da wani irin karfin zuciya, sai dai na jiki kam babu shi ko kadan a kusa da ita, a galabaice ta dago kai tana kallon mutanen da suka doso inda suke da manyan fitulu suna haske su, matasan yan bindigar ne suka kwance matan kusan shiri maza takwas, a cikin mutanen da aka kwance har da Aminatu. “To ku fadawa sauran dabobi an yi diyya kar sai mun kama hanya su bude mana wuta” Wanda yai maganar fuskarsa a nade take da rawani babu ta inda zaka iya ganinsa balle ka shaida shi, sauran yan bidigar kuma wasu na sanye da rigar soja wasu kuka wandon suka saka wasu kuma duka biyu sai dai dukansu suna dauke da manyan bindigogi. “Ai dai hanyar da suka biyo zaku bi karku kuskura sauya hanya, idan ba haka ba zaku hadu da wata dabar, kuma za mu aika musu” Dayansu ya fada, sannan aka fara dukansu da bulala aka korasu kamar dabbobi. “Ku wuce yan iska, ni na tsani kado Wallahi” Cewar dayan yana dukansu, masu kuzarin cikinsu suka tashi suka fara tafiya ban da Aminatu da sauran da akai ma fyade kamar ta, ganin hakan yasa mutumen ya roki a dorasu akan babur, a fitar da su sauran da suke iya tafiya a kafa kuma a korasu a kasa. Wadanda aka kora a kasa suna tafe suna jin tsoro saboda daukin ba dadin da ake da babbar daba, daman can sun fi kowa dauka da zafi, karama daba kudin fansarsu ba su da tsada kuma ba da taurin kai kamar babbar daba, kasancewar karamar daba matasa ne masu tasowa wasu ma duk yara ne, babbar daba kuma manya ne wadanda suka dade a cikin harkar. Su Aminatu sun riga isa kusan da bakin dajin saboda an dauke su a babur, sai dai zubesu akai a kasa suka zauna a gurin har sai da na kasan suka karaso sannan aka hadasu aka nuna musu hanya. Sauran wadanda sukai musu rakiya kuma suka juya suka koma ana kusan kiran sallah asuba suka fiton daga dajin, Aminatu na tafiya daker tana hawaye, idan ta gaji da tafiyar sai ta zauna a kasa ta yi rarrafe idan ta gaji sai ta unkura ta mike tsaye ta fara tafiya.. Da haka har suka iso bakin gari a inda motocin sojojin suke. Da farko sun tsorata duk kuwa da kasancewar an fada musu akwai sojoji a gaba, sai dai ganin a cikin barayin ma akwai masu uniform din sai ya saka wasu suka tsorata, sai dai kana ganin wadandan sojojin kasan zaratan sojoji ne ba kamar yan bindigar ba. Karasowa sukai suka dauki mutanen a mota, Aminatu kuma da ire irenta suka daukesu suka saka a motarsu, suka kama hanyar gari da su. Ko da tara na safe ta yi, labarin nasarar da sojojin suka samu a kokarinsu na kwato mutanen da akai garkuwa da su ta kwarade ko'ina, labarin barin wutar da akai ya shiga lungu da sako na nigeria, ya leka gidan jaridu ya cika social media. Masu lafiya aka tafi da su inda za a buka fuskarsu ayi ado da su a jaridu, marasa lafiyar kuma aka wuce da su asibiti a sirrance. A tsakanin iskar dake dajin dana cikin gari zuwa na asibitin da aka wace da su Aminatu ko wane dabam, na dajin na tawaya ne da damuwa da bakinciki, shigowa garin kuma samun iskar yanci ne, sai dai shiga asibiti kuma na fata ne, wata kila ta rayu wata kila kuma rayuwar ta zaba mata mutuwa. Mutanen da suka zo da gudu suka karbeta a hannun sojan daya dauko ta, sai su ka yi mata kama da wata halittar da taban kasancewar suna cikin farin uniform ne na aikinsu. Lumshe ido tai tana sauraren yadda aka dagata sama aka dorata saman gadon asibiti ana turata. FARUQ POV. A gurin mai shagon ya karbi wayarsa, ya saka line sa ya kira number Baturiya ya jita kashe. Hakan ya saka ya kira ta kanwarta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta yi picking. “Hello Raliya ya kike?” “Lafiya Kalau Ya Faruq” “Yayarki ta zo?” “Aa, tana Kano fa” “Kano?” Ya maimaita cikin tsananin mamaki. “Eh Napep ta hau shi ne...” Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraren abun da Raliya ta fada masa, sannan ya sauke wayar yana jin babu dadi. Ya sani ba dan komai Baturiya take masa haka ba sai dan talauci, da yana da arziki da bata isa ya mata umarni ta saba ba, daman ai ta fada idan yana da kudi ba zata taba gujewa umarninsa ba, tabbas da yana da arziki da iyayenta sun nemi inda yake sun fada masa halin da matarsa take ciki, sai dai ba su yi hakan ba saboda ba kowa ba ne a idonsu, wannan dalilin ya saka a duk lokacin da ya kai kararta akan abun da take masa sai du bata gaskiya su goyi bayanta. Cire line yayi ya ya mika masa wayar ya juyo ya dawo cikin gida cikin yanayi na rashin dadi ya maida gidan ya rufe. BATURIYA POV. Washe gari mutanen gidan suka bata wani tsohon Hijab ta saka ta talkami, Bayan ta karya suka rakota har bakin titi suka tara mata Napep zuwa tashar mota. Su suka biya mata na napep din, tana ta musu godiya, idonta har yanzu be warware daga kukan da tasha ba, babu abun da take ji kamar wayarta, domin samun wata wayar a gareta yanzu abu ne mai matukar wahala a halin da suke ciki, har kara ma a gidansu wata kila mahaifiyarta zata iya taimaka mata da wani abu, yayanta ya cika mata sauran ta siye wata wayar, amman ba daga bangaren Faruq ba kam. Tun daga yanayin hausarta suka gane yar zamfara, abun ka da kanawa sai dariya suke mata ita kam bata ma bi ta kansu ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta data bata yadda zata samu wata wayar kawai take tunani, gashi hanyar samun kudinta ta facebook ne inda take yaudarar maza, yanzu kuma babu wayar yaudara ma. “Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ta furta wasu hawayen na cika mata ido. ‘Dan Allah aljanuna idan kuna jina ku taimaka min da wayata ku dauki kudin na bar muku’ Wannan karon a cikin zuciyarta tai maganar hawaye na sauko mata. “Malama Lafiya dai?” Wani matashin saurayi dake kusa da ita ya tambaya yana kallonta. Banza tai masa ta ta juya masa fuska, sai yai murmushi ya cigaba da danna wayarsa. Sai da motar ta cika sannan suka kama hanyar Zamfara suna tafe suna addu'a saboda yanayin hanyoyin nigeria kowa ya san yadda tafiya take a yanzu. Sai da tafiya tai nisa sannan aka kira saurayin a waya, Baturiya ta kashe kunne tana sauraren yadda yake amsa wayar a cikin har da amsar da yake fadawa cewar motar haya ya shigo saboda motarsa ta tsaya ya barta a nan Kano. Baturiya na jin haka sai ta juya ta kalleshi sai a lokacin ma ta lura da shaddar jikinsa babbar shadda ce, haka zalika wayarsa ma. Tun da suka kama hanyar direban be tsaya ba har suka iso Zamfara. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Baturiya ta fada da muryar kasa kasa tana fashewa da sabon kuka. A nan ma kallonta yai ya tambayeta. “Lafiya...?” Kai ta girgiza ta share hawayenta ta fada masa abun da ya faru da ita, sai dai ta canja cewar tana da aure, sai ta fada masa cewar mahaifitarta ta aiketa. “Subhanallahi, ki gode Allah ma be kai ki wata kasar ba” “Haka yan gidanmu suka ce, ni daman Allah ya sani gidanmu bama hawan Napep duk inda zamu je a mota ake kai mu yanzu ma tsautsayi ne” Ta fada kamar gaske, kallon lace din dake jikinta yai kamin ya kalli kyakkyawar fuskarta. “Allah ya tsare gaba” “Amin” “Amman miyasa kike kuka?” “Haba Malam dubi tufafin dake jikina fa? Ban taba kwana a irin gidan dana kwana ba sai jiya, yanzu kuma motar haya na biyo tun daga Kano har Zamfara abun da ban saba ba” “Ba dadi gaskiya, ni ma ban saba hawan motar haya ba sai dolen dole” “Ba dadi ai” “Gaskiya” Daga haka be sake cewa komai ba sai da suka isa cikin tasha. Bayan sun fito ta jero ita da shi suka fito titi, fitowarsa tai daidai da fakawar wata bakar mota mai kyau har wani sheki take tsabar sabuntaka. “If ba wani matsala zan iya sauke ki a gida ai” “Aiko da naji dadi Wallahi domin tsoron Napep nake yanzu.” Murmushi yai ya bude mata baya ta shiga, shi kuma ta bude front seat ya shiga ya zauna. “Ku gaisa da abokina” Ya fada yana juyowa ya kalleta. “Sannu ya aiki” “Alhamdulillah ya hanya” “Da godiya” Ta amsa sai ta maida dubanta gefen titi tana kallon motocin dake kai kawo. “Wace unguwa ma?” “Gada biyu” Ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, ko kadan tsoro be kamata ba balle ta ji faduwar gaba, ta saba shiga motar maza duk kuwa da kasancewar tana da aure, sai dai bata barin wanda ya santa ya ganta, wannan karon ma bata haufin ganinta ne saboda ta san yayanta ya san labarin bata tan idan ya ganta da wani ba zai mata fada ba. Har kofar gidan yayanta suka sauketa, kato gidan mai kyaun gaske, sai da tai musu godiya sannan ta bude motar zata fita. “Ga katina maybe zamu iya gaisawa” “Okay thank” Ta fada tana karbar katin sannan ta fice ta maida motar ta rufe sannan ta tura gidan ta shiga. “Ina ka hadu da wannan?” “Ta sha kuma ta min” Ya fada yana murmushi. “Tana da kyau gaskiya” Dukansu dariya sukai sannan abokin nasa yaja mota suka juya. LEILA POV. Tsaye take jikin windo tana kallon garden din dake cike da itatuwa, fuskarta dauke da hawaye, haka ma zuciyarta babu dadi ga rashin natsuwa da samun sukuni da take. Hannu ta saka ta share hawayenta tana jin wani irin nadama da bakincikin abun da ta aikata. “Why? Sometimes I'm very selfish” Ya fada tana kai hannunta ta shafa wuyanta, bakinta ta cika ma iska ta busar sannan ta juyo ta baro jikin window ya nufi kofar fita har yanzu jin take babu dadi, tsaye tai tana kallon bakin kofar dakin a daidai inda Baaba ta tsaya sannan ta dauke kai ta fara tafiya, sai da ta leka dakin Momy ganin bata ciki yasa ta sauko kasa gaba daya sai ta same ta zaune akan sofa tana amsa waya. Wucewa tai dinning taja kujerarta ta zauna tana ta kallon abincin dake gabanta kamar mai wani nazarin. “Leila...” Momy ta kira sunanta bayan ta gama wayar, sai Leila ta juyo ta kalleta da idanuwanta dake nuna alamar bata samu bachi da yawa ba. Tasowa Momy tai tana karantar damuwar yarta, a take ta nemi bacin ran dake tare da ita ta rasa, hannu ta kai ta rika fuskar Leila. “Dear ba ki bachi ba?” “Wallahi Momy na kasa bachi kamar yadda na saba, Wallahi dana rufe ido matar nan nake gani” Momy taja kujera ta matsa kusa da yarta sosai ta zauna. “Leila ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, babu wanda zai san wannan abun even if ma sun sani ba su isa su yi komai ba, they're poor ba su isa su ja da mu ba, kuma wannan abun ai kaddara ce, ki dauka haka Allah ya rubuta” Ta gyada kai cike da gamsuwa. Sai Momy tai mata murmushi ta share mata hawayenta. “Ko kadan bana son na ganku a damuwa, ku kenan uku Allah ya bani bana son kuna samun kanku a damuwa, wannan matsalar ma ta Talba zata wuce inshallah sai ya sauke duk girman kan nan” “Anya Momy Talba zai ce?” “Dole ya canja, sometime lamarinsa har daure min kai yake, yanzu maganar nan ta Baaba har ya kai ta gurin mahaifinki, simple abu Talba ya rika yinsa kamar wani mace ko karamin yaro, gashi na je Mahaifinku yace ba zai sake biyan mai aiki ba” “Ba zai rika dafa abinci kenan?” “Dole a aljihu zan rika biyansu, ai na yi magana da Hajiya Samira ta nemo min wasu yan aikin, a dole mu dauki wasu amman da ni zan biya su” “Ban san miyasa Talba ya fita dabam a gidan nan ba, ni na rasa gane wane irin mutum ne” “Shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki, domin bana son ya fara zarginki, ni kam ba dan kin matsa kina son Talba ba....” Kamin Momy ta karasa Leila tai saurin tare numfashinta tana rike hannunta. “Wallahi Momy ina son Talba, ina mugun sonsa, Wallahi idan ba shi ba ba zan iya auren kowa ba” “Shikenan ai ba zamu bari ya dauko mana bare ba, amman halin nan nasa ina ganin kamar zaki wahala idan akai auren nan” “Momy ba zan aure shi ba sai ya canja, zan canja shi inshallah na san yana son mu yi aure ai zan yi amfani da wannan damar na canjan shi” “Allah yasa yanzu dai sai ki karya” Ta daga mata kai ta kai hannu zata fara bude kular akai knocking, kusan a tare ita da Momy suka kalli kofar falon sai dai ta riga Momy mikewa tsaye ta karasa gurin kofar ta bude. “Madina...” Suka sakarwa juna murmushi, sai kuma Madina ta juya tana kallon Talba dake kokarin shiga mota, kamin ta juyo ta kalli Leila. “Fita zai yi?” “I think” “Kamar ya you think zai fita baki sani ba” “Kina abu ke ma kamar baki san Talba ba” “Ke ce ya kamata ki canja ba shi ba” Madina ta fada tana sake juyawa ta kalli motarsa, ajiyar zuciya ta sauke a sirance sannan ta shiga cikin falon gabanta na mugun faduwa, irin faduwar gaban da take yawan samun kanta a ciki a duk lokacin da tai arba da Talba. Alhamdulillah a nan na kawo karshen free page duk page din da zai biyo bayan wannan na kudi ne. If you want to subscribe Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660. Yan Nijar zaku biya ta wannan number +227 90 16 59 91. _____________ Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. 11 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle I'm on Instagram as ramla_incense. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa _____________________ “Madina ce” “Eh Momy ya gida?” “Lafiya Kalau ya Maman ki?” “Lafiya Kalau take” Ta amsa tana murmushi, sai Momy ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta dake kasa. Daga Leila har Madina binta su kai da kallo sai da ta shige sannan Madina ta kalli Leila. “Wai da gaske baki san inda Talba za shi ba?” “Ba zai wuce Office ba” “Amman ya karya kamin ya fita?” Ta daga fadunta alamar bata sani ba. “Sometime a office yake karyawa wani lokacin kuma a bangarensa” “Wani lokacin kina bani mamaki Leila, idan an yi magana ki ce kina son Talba, amman baki san abun da yake so ba, da wanda baya so, ba ki kokarin kiyaye bacin ransa” “Shi yana kokarin kiyaye nawa ne? Yana son a rika masa sakon soyayya ana tambayar Lafiyarsa an damuwa da shi, amman shi be damu yai min ba, ni fa macece be kamata na zubar da kai a kansa ba” “I know amman idan kin kula haka rayuwarsa, then why ba zaki bishi ku tafiyar da rayuwarku a haka ba, I'm sure idan kuka yi aure komai zai canja” “Zamu yi aure, amman sai na gasa masa gida a hannu tukuna, and kina bukatar sanin wannan, Talba wanda zan aura ne ba wanda na aura ba, me yace me zai ci rayuwarsa for now bata dame ni ba” “Haka dai kike gani, amman matakin kulawa daga yanzu ne, ni ina ganin ya kamata ma ki fara aiki ta haka zaku samu fahimtar juna sosai” Rausayar da kai Leila tai. “Madina, miyasa kike yawan damuna da maganar Talba ne? Ban shirya aiki yanzu ba sai na yi masters” “Ina tsoron kar ya kubuce miki ne!” “Really....” Leila ta fada tana dariya. “Ke a tunaninki akwai abun da zan nema na rasa a rayuwata? Haba Madina, ai Talba ko daga wani tsatson ya fita Daddy da Momy za su tsaya min na same shi, ballr kuma a jinina Talba ya fito, ba wai rasa shi ba, soyayyata ma ya hada da ta wata ma be isa ba, balle har ya hada ni da kishiya, haufi daya ne akan halayyarsa” Madina ta yi murmushi. “Leila kenan, na san kina da gata ta ko'ina, amman Talba yafi gaban yadda kike tunani, kar fa ki manta shi namiji ne” Leila ta juya ido. “Please My friend mu aje maganar Talba a gefe, kin san wai ko jiya na yi mafarki matar nan?” Madina ta zaro ido. “Da gaske?” “Wallahi, ina ganin kamar ko yawan tunaninta da nake ne yasa nake mafarkinta” Madina ta yi shiru tana kallonta kamin ta ce. “Amman kin san fa hakkin jini...” “Hakkin jini Madina sai kace wanda na kwantar na yanka? Kamar yadda Momy tace mistake ne, kuma kowa yana iya yin laifi ai dan adam ajizi ne ko?” “Yeah.. Amman wannan kamar da banbanci Leila... ” Ganin Leila zata yi mata wata maganar ta daban yasa Leila kawarta maganar ta hanyar dauko wata maganar. “Ya aikin ki?” “Alhamdulillah, ni aikin ma ya fara isata Wallahi” “Kamar ya?” “Ayukan ne basa karewa kuma gashi bama tashi da wuri, kuma zuwa kullum ne, ni da zan samu wani aiki ai da na aje wannan” “Kamar ya zaki samu? Kin fa yi karatu ne Madina” “Na sani amman idan ba irin kamfaninku ba ne da suke biyan ma'aikata da kyau kin san ba ko wane aiki zan iya ba” “Idan kina son aiki a kamfaninmu ai zaki iya samu” Madina ta wara ido tana murmushi. “Da gaske?” “Haba dai kina kawata ki nemi abu a gurina kuma ki rasa samu? Ki kawo takardunki kawai zan yi ma Daddy magana” Da sauri Madina ta bar inda take zaune ta rumgume Leila tana wani irin murna. Leila ta yi dariya. “Are you kidding me? Ai ko mahaifinku kika yi ma magana zai canja miki aiki domin su ne manya a gobnati, amman kina ta kewaye kamar wanda bata da kowa” “Ba haka bane, Leila na dade ina mafarkin aiki a kamfaninku Wallahi” “Amman shi ne baki fada min ba? Haba dai Madina ina ganin kamar mun zama daya ni da ke?” “Ai da nauyi, amman dai yanzu komai ya wuce na gode sosai zan kawo takardun anjima ko gobe Inshallah na gode sosai dear ina kaunarki” Leila ta yi murmushi. “Karki damu, i trust you” “Bari na tafi kar na yi latti” Ta fada tana daukar jakarta ta rataya, sai Leila ta rakota har gurin motarta sai da ta shiga ta bar gidan sannan Leila ta juya ta koma ciki. BATURIYA POV. Har ta huta ta ci abinci yayanta be dawo ba, daman idan ya fita gurin kasuwancinsa baya dawowa sai dare. Batan ta yi wanka ta fito ta tari Napep ta nufi family house dinsu. Tana shiga cikin gidan kannenta da mahaifiyarta suka hau murna kamar su hade ta. Ko minti talati ba ta yi da zama ba, Sultan ya shigo cikin gidan da gudunsa, kanwarta ta fara tare shi ta daga shi sama yana dariya. “Sultan kaga Mama ta dawo?” “Tace a daina cewa Mama sai Mommy” Ya fada da yar siriyar muryarsa yana kallon Baturiya dake zaune falon. “Kai da wa ka zo nan?” “Daddy yana waje” Wani tsaki taja ta dauke kai. “Zuwa zai yi ya fara min bakar masifar nan Ko?” “Aa ya isa? Ai Raliya ta fada masa halin da kike ciki, ko ma haka be faru da ke ba tun da ya ga baki dawo gida ba ai ya san ba lafiya ba, dole ya daga miki kafa” “Uhm Umma baki san halin Faruq ba, Wallahi ni da nake tare da shi kawai na san ukubar da nake sha a gidansa, zai iya zuwa a nan ya nuna babu komai sai mun koma gida ya fara min masifa” “Bayan duk hakurin da kike da shi? Cikin yan'uwanki ke kadai ce baki dace da daki ba Rafi'a, ba mu yi zaton haka ba” Wannan maganar da Umma tai sai ya saka Baturiya ta kara bata fuska. “Wallahi Umma ni kadai na san azabar da nake sha a gidan Faruq, bayan yunwa ga rashin sutura da kwadayi, ga masifarsa kamar ni na dora masa talauci” Umma ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yarta cike da tausayawa. “Shiyasa tun farko ni bana son auren nan na zumunci, mahaifinku ne ya dage sai an yi gashi nan ya tafi ya barki da wahala, haihuwa daya kenan nan gaba idan an tara yara me kike tunani” “Ni ma tsorona kenan Umma, haihuwa daya, rayuwa tana ta mana haka balle nan gaba, kullum dai dai tai ta min karyar aikin zai fito amman shiru” “Ni abun nasa har mamaki yake ba ni, wai ko dai be yi karatu mai kyau ba ne” “Ni ina na sani, tun da ba fada zai yi ba, ni Wallahi makaranta ma nake son komawa, kar na bata nawa future na zama irinsa” “Aiko da kin yi ma kanki abu mai kyau, sai ayi ma yayanku magana ya biya miki” A take murmushi ya cika fuskarta. “Da gaske Umma?” “To miye a ciki idan ma be biya miki ba, ai ni zan biya miki” Umma ta fi tausayin Baturiya fiye da kowa a cikin yayanta, domin ita kadai ce take auren matalauci talaucin da abun da zasu ci ma sai ya gagaresu wani lokacin. Ba wasu masu arziki ne can sosai ba sai dai suna da rufin asirin irin na yayan da suka dace da daki, domin kusan duk abun da ake ci a gidan yayyun Baturiya ne dake aure suke kawowa, sauran dawainiyar kuma babban yayansu ne yake yi, domin yana da rufin asiri irin na wanda kasuwanci yai ya aura. “Sultan je kace Daddy ya shigo kar ya ce an barshi a waje” Baturiya na fadi hakan Sultan din ya sauka daga kafafuwan kanwar mamansa ya nufi kofa da saurinsa, ko da ya fito Faruq na tsaye bakin karamin gate din gidan rumgume da hannayensa. “Daddy ance ka shigo” Faruq ya sakar masa murmushi sannan ya kama hannun dansa suka shiga cikin gidan, cike da nauyi ya shiga kasancewar baya samun riko musu komai idan zai zo, ba kamar sauran surukan ba da har mararin zuwansu ake saboda suna da rufin asiri, Baturiya ma ta sha fada masa shi kadai ne baya kawo komai idan ya zo, hakan yasa idan ba da wani babban dalilin ba baya son shiga cikin gidan duk kuwa da kasancewarsa dan'uwa, shi kansa ya san baya samun sakin fuska a gurin mahaifiyarta yadda ya kamata. A bakin kofar falon ma tsayawa yai sai da aka matsa iso, sannan ya shiga cike da kunya ya nemi guri kusa da matarsa ya zauna bayan ya gaishe da sarakuwarsa kuma matar Kawunsa. “Yanzu kika iso ne? Na dauka gida zaki wuce ai” “Ko naje gida me zan yi tun da ba abinci ke akwai ba, yunwa kawai zan sha” Juyowa yai da kyau ya fuskance ta. “Rafi'a wannan wane irin magana ce? Idan ma kasa kike ci naga ai gidan aurenki ne” “To karya na fada? Ni yanzu ga shi na rasa waya da sauran canjina” “Rashin jinki ne yaja miki ai” “Kaji ba bakar fata kawai yake min, shiyasa ai baka ma damu ka san inda nake ba sai yanzu” Uffan be sake cewa ba ya kama hannun dansa yana wasa da shi. “Ya kira ni ai ya tambaye ni” cewar Raliya kanwar Baturiya. Sai mahaifiyarsu ta tashi ta nufi dakinta tana fadin. “Allah ya kyauta” Bayan ta wuce, Faruq ya kalli Baturiya. “Tashi muje gida” “Yanzu yanzu fa na shigo, sai na huta zan tafi gida” Ta fada tana turo baki gaba tana hararsa kasa kasa. “Rafi'a me ke damunki, sai ki rika min abu kamar ba mijiki ba, danki ne ni?” “To idan naje gidan me zan maka? Yanzu fa na dawo ai sai ka bar ni sai na huta sannan anjima zan koma ai ban ce nan zan zauna ba” Sanin cewar idan ya biye mata za su siyar da hali ne a gidan da ba a ganin mutunsa da kimarsa ne yasa be sake ce mata komai ba ya saki hannun Sultan ya mike tsaye. “Raliya ki fadawa Umma na wuce” “Okay” Raliya ta amsa tana kallon Baturiya cike da jin haushin abun da yar'uwarta take yi a gabanta. Sai da ya fice sannan ta kalli Baturiya ta ce. “Wallahi Rafi'a baki kyautawa, talauci ba fa ba hauka ba ne, baki san budin da Allah zai masa nan gaba ba” Baturiya taja wani shegen tsaki. “Ki dauki arziki ki ba shi, idan mun zauna mu kadai kin san iya abun da yake min ne? Kin san yadda yunwa take halaka mutum kuwa? Dan Allah karki kara min da wata damuwar ki bar ni na ji da wanda nake ciki” Tana fadar hakan ta mike tsaye ta nufi dakin mahaifiyarta, Sultan ya bi bayanta. Family house dinsu ya nufa cikin rashin jindadi, daman ta saba masa a gaban yan uwanta, yan'uwansa kam daman sun san irin zaman da suke, hakan yasa kanensa basa sha'awar zuwa gidan sai da wani babban dalili, domin bata musu tarbar arziki. Mai achaba na sauke shi kofar gidan ya ciro kudinsa ya mika masa sannan yai sallama ya shiga cikin gidan, tun daga yanayin yadda ya ga gidan ya san ba su girka komai ba, domin murhunsu a bushe yake, a take ya ji ransa ya kara baci domin baya son ganin mahaifiyarsa a hali na yunwa, ga kuma damuwar halin da suke ciki na neman kudin aure. Da sallama ya shiga cikin dakin kanwarsa Aisha ta amsa ciki yanayi na damuwa. A bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon mahaifiyarsa dake lullube da wani tsohon zanen gado tana ta rawar sanyi. “Jikin ne?” Ya tambaya da muryar dake bayyana tsananin damuwarsa. “Haka ta kwana” Aisha ta amsa. “Miyasa ba a kira ni ba?” “Ita ce kar a kiraka kar a tayar maka da hankali” Runtse ido yai ya sauke ajiyar zuciya, ya dade a haka kamin ya bude idon ya nufi inda mahaifiyarsa take kwance ya zauna daf da ita, sai ta yaye mayafinta ta kalleshi da idanuwanta dake fassara irin tsananin zazzabin da take. “Faruq” “Mama damuwar nan ce kika dauka kika saka a ranki ko? Allah shi yake yin komai, kuma daman na yi tunani zamu hutar ta da kanmu da wani lefe ya bada kudin kawai a siya mata kayan daki da su” “Ko ya bada kudin ai ba zai wuce 100k ba kuma ba zai isa a siye kayan daki ba, ko kujeru kanana yanzu sai an siye su 60k ko fiye ma” “To ai sai a kara da wani abun idan Allah ya mana fatahi, dan Allah ki cire damuwa a ranki, Mama so kike ke ma mu rasa ki? Haba Mama” “Damuwa dole ce Faruk bayan ta auren yaran nan akwai ta yau da kullum, yanzu ga shi abun da zamu karya ma ya gagaremu sai da na ba Asiya ta siyar da tufafina sannan zamu samu su karya, tun safe har la'asar ace bawa bai saka komai a bakinsa ba” “Allah be manta da mu ba Mama, bayan wuya sai dadi, kuma idan ka ga tsanani yayi yawa sauki na tafe, Inshallah komai zai warware kamar ba a taba yi ba” “Allah yasa muna da rabon jindadi ko kadan ne Faruq, lokaci tafiya yake baya jiran kowa” Ta karasa tana runtse ido da karfi sakamakon bugawar da zuciyarta tai da karfi. Daga Aisha har Faruq hankalinsu tashi yai. “Sannu Mama” Kai ta daga musu cike da karfin hali har lokacin idonta na rufe saboda azabar ciwon da take ji. Ajiyar zuciya Faruq ya sauke ya mike tsaye ya bar dakin cikin damuwa, ji yake kamar ace yana da halin da zai magance damuwar mahaifiyarsa, kuma ya kaita asibiti a duba lafiyarta, amman ina? Talauci ya saka shi a gaba kamar wanda ya zagi arziki. LEILA POV. Rike da takardun Madina ta shiga dakin Momy ta zauna gefen gadonta. “Momy Could you do me a favour?” Momy ta aje plate din abincin dake hannunta ta kalli Leila dake sanye da doguwar rigar shadda ta sha aiki kamar sabuwar amarya. “Minene?” “Kin san kawata Madina ai...” “Har sai kin sake gabatar min da ita? Madina ai ta zama yar gida” “No Momy ina son ki gane cewar maganar da zan miki tana da muhimmanci ne, Wallahi ta min magana tana son aiki a kamfanin Daddy and i promise her zan saka a dauke ta” “And....?” Momy ta bukata tana tsattsage hakoranta na makka. “So daman dazun na mata magana ta kawo takardunta shi ne ta kawo, da na zo naje na samu Daddy kai tsaye da maganar amman na san zai ce na bawa Talba ne, Talba kuma zai iya cewa ba zai dauke ta ba, kuma kin san be kamata na kasa yi mata haka ba, ko da ba ita ba ma a kamfanin mahaifina ya kamata ace zan iya yin komai ina da ikon yin komai” Momy ta yi dariya. “Leila kenan, kina abu kamar ke ce Amal, idan za a dauki wani aiki ta dalilinki har sai kin tsaya wani kame kame? Ki same yayanki Talba da maganar mana” “No Momy ni fa bana son magana da shi sai idan wani babban abu ne, yadda yake jin kansa haka nakr jin kaina, kuma kin san zai iya amfani da wannan damar ya wulakanta ni ko ya fada min wata maganar marar dadi, idan kuma na rama ke da Daddy ni zamu dorawa laifi” “Wannan ai da ne Leila, amman yanzu na fahimci halin da kike ciki, halin Talba sai mai hakuri da kai zuciya nesa ni kaina yanzu ya fara min ai” “Shiyasa nake son ki saka shi ya dauke ta... ” Tana rufe baki Talba ya kwankwasa kofar dakin sannan ya murda kofar ya turo ya shigo, juyowa tai ta kalleshi, a take annurin dake fuskarsa ya auri idanuwanta, duk yadda ta so ta dauke kai daga barin kallonsa sai ta kasa har ya karaso inda Momy take ya zauna a saman kujera, lumshe ido tai tana ta yaki da numfashinta dake ta kokarin sauya mata kamshin dakin Momy zuwa na turaren Talba da ya cika daki. “Momy barka da dare” “Yauwa” Yanayin yadda Momy ta amsa masa ne yasa shi murmushi domin ya san har yanzu bata gama hucewa daga laifin da be aikata mata ba. “Allah yasa dai ba fushi kike da ni ba har yanzu Momy?” Uffan Momy bata ce masa ba, hakan ya saka shi kara yin Murmushi sai dai wannan karon be ce komai ba. “Abun da kake dai ba abu ne mai kyau ba, mata aka sani da tsegumi ba maza ba” “To ayi min afuwa ba zan sake ba, Leila...” Ya karasa yana kiran sunanta, sai ta bude idonta a hankali ta kalleshi ba tare da ta amsa ba, daman shi ma he called her name ne kar Momy tace ta ganta be mata magana ba, duk kuwa da kasancewar ita ya kamata ta fara masa magana a lokacin daya shigo a matsayinta na kanwarsa kuma wacce zai aura, ko ba komai ai ita ce karama. Mikewa yai tsaye sai Momy ta dauki takardun da Leila ta aje mata gefenta ta mikawa Talba. Sai da ya kalli takardun sannan ya mika hannu ya karba ya bude yana dubawa. “Ba mu fara daukar ma'aikata ba, muna da enough” Ya fada bayan ya dauke idonsa daga fararen takardun zuwa ga Momy. “Na sani, saka iya replacement dinta da wani ai” “Na dauka Madina tana aiki da ma'aikatar Alhazai ai” “Tana yi, yanzu nan take so kuma umarni ne so nake ka dauke ta” Ya hade yawun bakinsa, sannan ya kalli Leila da ita ma kallonsa take ya rufe takardun ya juya ba tare daya sake cewa komai ba ya fice, binsa Leila tai da kallo har ya fice sannan ta juyo ta kalli Momy. “Thank Youu Momy” “Karki damu, je ki samu abun da kika sakawa cikinki” “Okay” Ta mike tsaye ta fice daga dakin cikin jindadi. Ko da Talba ya fito Kabir na zaune kan center carpet tare da Amal suna shan kankana. Saman kofa Talba ya zauna rike da takardun yana kallon plasma. “Malam bismilla karka ce mun maka rowa” Kabir ya fada yana kallonshi, Talba kallonsa kawai yai ya dauke kai fuska ba yabo babu fallasa. Amal ta kalli Kabir sannan ya kalli Talba ta ce “Ya Talba Momy ta maka fada dazun?” Gira ya daga mata, wanda hakan yai daidai da saukowa Leila sai ya mike tsaye ya fice daga falon gaba daya. “Strangers, ban taba ganin masoya irinku ba, wai a haka zaku yi aure?” “Miye damuwarka ne Kabir? As long as yana so na miye ruwanka ne?” Yayi dariya ya mikawa Amal hannu suka taba. “Hi five Baby” Dinning ta nufa ta bude manyan kulolin tana duba abun da Momy ta dafa, wayar dake hannunta ta aje a gefe ta dauki karamin plate ta dauka ta fara zubawa, abun ka da wanda baya son cin abinci sai ta zuba kadan ta ja kujera ta zauna. Kamar zaman ake jira tai sai ga sako ya shigo wayarta. ‘Good Night Dear’ Wani irin kasaitaccen murmushi tai bayan ta gama karanta sakon dake dauke da hoton zuciya. “I love you” Ta furta a zahiri, sannan ta aje wayar ta juya ta kalli Kabir dake ta rigima da Amal akan waye zai karasa shanye watermelon din da suka raga mai tawa, sai kuma ta juyo ta kalli abinci. “Talba kana da wuyar sha'ani, wannan girman kan naka yana bani mamaki, ban taba ganin mai tsoro ko jin nakasu akan nuna soyayya ba kamar kai... But i love you..” Ta furta tana kara jin shaukin kaunarsa na ratsa zuciyarta. ________ Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.   Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah. Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci. 12 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa _________ *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Seven days later... FARUQ POV. A gabanta ya dire kofin dake dauke da koko ya dora mata suga a saman murfin. “Ga abun da muka samu” Wani banzan kallo tai ma kofin ta dauke ido tana turo baki gaba. “Koko kuma? Ni bana son shan koko gaskiya” Kallonta kawai yai ya dauke kai ya shiga dakin ya cire tufafin jikinsa ya daura wani tsohon tawul ya fito ya nufi inda ya jona ruwan zafi a electric a juye a karamin bokitin wanka ya fita waje ya sirka ruwan sannan ya dawo falon. “Ni fa bana son koko” “Wani yana can yana nema be samu ba” “Wallahi babu, ba dai sa'ata ba, sai dai tsofafi sa'o'ina kyawawa kam suna can suna neman arziki” Uffan be sake ce mata ba ya nufi hanyar dakin. “Ni fa ba zan sha koko ba, waina nake so da nama” Juyowa yai ya kalleta. “Idan ina da halin siya miki ita kin sani, kuma babu abun da zai hana na siya miki, idan kuma babu sai ki yi hakuri har Allah ya kawo” Sai ta mike tsaye. “Tsakani da Allah Faruq kana cutar da ni, yanzu haka zan yi ta zama cikin matsi? Kamar mu muka fi kowa? Duk wani abun da nake so baka iya siya min sai idan na siyawa kaina ko kuma an aiko min daga gidanmu, ni gaskiya na gaji kana cutar nan kuma na san Allah zai saka min domin baya son zalinci” “Gaskiya ne, Rafi'a baki da tunani ko kadan, kan mu farau talauci? Ko kuma mutum yana yi ma kansa arziki ne? Halin nan naki ya ishe ni..!” “Da ya isheka da ka sauwake min, da ya isheka da ka samawa kanka mafita, tsakani da Allah Faruq idan ba kaddarar aure ba babu abun da zai hada ni aurenka, daman can na dauka zaka samu aiki rayuwa ta tafi mana da kyau, ashe hauka nake, gashi na gagara samun abun da zan ci ma” “Saki kike so?” “Eh saki nake so, ka sake ni Faruq ka sake ni idan ka haihu” “Zan nuna miki na haihu” Yana fadar hakan ya wuce cikin dakin da bokitin ruwan ya shiga bandaki ya watsa ruwan ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya dauki makullin shagonsa ya saka aljihu, dayan aljihun kuma ya saka wayarsa, ko da ya fito tana zaune falon tana jiran ya mika mata takardar sakinta, tana ganinshi gabanta yai mugun faduwa. Be kulata ya nufi kofar fita daga falon yai ficewarsa rai a bace. Sai da ya fita sannan ta tashi ta fita ta rufe gidan ta dawo falo ta zauna, can kuma ta tashi ta fita ta dauko ludayi ta zo ta zauna ta bude kokon ta mutsa. “Ba zan saka sugan ba” Ta fada tana wurgar da kullin sugan ta fara shan kokon lami ba suga, ludayi biyu tai sai gata ta tashi ta nufi inda kullin sugan ya fashe ta kwaso a hannun ta nufo kokon ta zuba, ta zauna ta fara sha. Rabi ta sha ta bar ba Sultan dake bachi rabi, domin ta san bayan ya sha yanzu da rana ma zai iya nema. Tashi tai ta koma saman kujera ta zauna, ta mika hannu ta dauki keypad din da Umma ta siya mata kamin ta siya mata smartphone, tsaki tai bayan ta shiga contact dinta ta fito ta shiga inbox dinta, nan babu komai domin sabun line ne da tai welcome back, hakan yasa ta ji babu dadi domin wanda ya saba rika babbar waya yana chatting idan ya rasata zai ji kamar ya koma a wata karamar duniya. “Allah tsinewa Aljanin nan, ya dauke ni ya kai ni Kano kuma gashi nan ya rasa wayata da atm dina da yan kudina, Allah kasa min, Wallahi Faruq be da kashin arziki gashi nan na rasa komai” Ta fashe da kuka. Kamar jira ake ta fara kukan sai ga kiran Ramlee ya shigo wayarta, share hawayenta tai sannan tai picking call din ba dan ta gane mai kiran ba domin number babu suna. “Hello” “Baturiya ya kike?” “Lafiya kalau Ramlee ce?” “Ni ce fa baki gane ni ba?” “Number ba suna wayata ta bata ne na yi welcome back kuma numbers din ba su dawo ba” “Garin ya? No wonder na yi ta kirankin number ki ban samu ba, na yi mamaki domin na san baki kashe waya” A nan Baturiya ta labarta mata abun da ya faru, sai Ramlee ta saka mata dariya. “Farin jininki yayi yawa Baturiya abun har da su Malam aljani? Shiyasa na ji muryarki wani iri kuka kike ne?” “Ba dole ba Ramlee ina cikin matsala, ina son na ci da dadi na saka mai kyau amman abu ya garara, yanzu ko wayar nan tawa da ta bata ai daidai ne ya siya sabuwa amman sai da Umma ta siya min karama” “Fee'at kenan, wannan fa duk kika so, da kin yarda da yanzu kin dangwali arziki har ma ki raba mijinki ciki, Wallahi Baturiya da zaki sake jiki yadda kike da kyau nan da har kyautar gida sai kin yi ma wasu” “Ramlee ina fa da aure har da” “Mace nawa ce mai yaya uku hudu har biyar take biyawa kanta bukatar da jikinta? Ke ko a unguwarku idan aka ce za a bude wasu matan auren ki ga sirrinsu zaki sha mamaki Wallahi, ba ki san cewa aure yana rufa miki asiri ba? Ko da kin samu wani abu ba za a zargeki ba? Yadda kike da kyau nan Baturiya ba ke ba ko ni da maza suke ganin hotunanki a wayata suna hauka sai na samu arziki, wai kin san ma dalilin daya saka na kira ki?” “Sai kin fada” “Wallahi wani ne ya sake ganin hoton ki yace kina cikin irin matan da yake so, na fada masa ke ba irin mu bace amman ya saka ni gaba wai na lallaba masa ke dan Allah, kuma babbar mutum ne dan siyasa, yanzu haka haka 100k ya bani wai na baki na wankan hoton da kika yi” Baturiya ta mike tsaye tana dokan kirji idonta kamar za su fito. “Dubu dari fa kika ce Ramlee” “Wallahi ga su nan, tun shekaran jiya ya bani su jiya ma daker ya bar ni na yi bachi sai damuna yake da maganarki a waya kamar zai min kuka, shiyasa ma na kira ki da safen nan, Allah yasa ma mijinki baya nan” “Baya nan ya aje min wani shegen koko ya fita” “Kin gani yanzu da kina da kudi sai abun da ranki yake so zaki ci, idan kina free anjima zan zo na dauke ki a motata muje na siya miki sabuwar waya” “Da kudin?” “Aa da kudina dai, wacan kudin a cewa yai a baki kuma zan danka miki abun ki a hannu, amman ki yi tunani idan kika bada kai me kike ganin zaki samu? Bayan shi ma akwai maza da yawa musamman ace kina samun sakewa ana zuwa da ke hutu abuja ko kasar waje? Hmmmm Hajiyata ai kin take” “To zunubin fa?” “Allah gafurun raheem ne, kuma ban ce zaki dauwama a haka ba idan kin yi kin samu dan abun da kike so, sai ki daina amman ki yi tunanin future dinki dana yaronki koma nace yayanki na nan gaba Baturiya” “Shikenan zan yi tunani” “Yauwa Tawan haka nake son ji, ki yi tunanin kamin na zo kin ji? Yau ko wayar 500k kike so zan siya miki ita da yardar Allah” Baturiya ta yi murmushin jindadi. “Na gode kawata Allah ya bar min ke” “Ameen Allah ya bar mu tare” “Ameen” Ta sauke wayar tana ta murna. “Bari na yi sauri na gyara gidan kamin ta zo” Ta dauki zane ta fara kabe kujerun, sai ta ji an kwankwasa kofar gidan, saurin saving number Ramlee tai sannan ta goge kiran da tai mata domin a tunaninta Faruq ne ya dawo. Sannan ta nufi kofar gidan ta bude sai tai arba da Malam Musa dilalin, cikin mutunci suka gaisa duk da kasancewar babu mayafi a jikinta sai hullar dake kanta. “Mai gidan yana nan kuwa?” “Aa ya fita” “Oh dan Allah idan ya dawo ki ce masa na zo maganar kudin hayar nan, masu gida sun matsa, ko jiya da dare masifa yake ta min domin ganin yake kamar an bani kudin na kashe ne” “Idan ya dawo zan fada masa, dazun ma yake cewa da ya ganka da ka saka masa number mai gidan domin yana son yai magana da shi” “Indai maganar haya ne kar ma yayi domin Alhaji Sule be da mutunci ko kadan” “Aa karka ce haka Malam Musa, bari na dauko wayar” Kamin ya sake cewa wani abu ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta dauko wayarta ta mika masa. “Saka masa number a nan” Be karbi wayar ba, ya ciro tasa wayar ya karanta mata number ta saka a wayarta. “Idan ya zo zan fada masa sai na ba shi number” “To yayi na gode” Ta rufe gidan tana murmushi ta dawo falonta tana kokarin saving din number. “Ba Alhaji Sule kake ba ko Alhaji lule kake sai na ci ubanka, talauci ya matsa shi ne kai kuma zaka kunno mana wata wutar dan kana da shegen tsohon gida” Ta fada tana ƙwafa. FARUQ POV. Ya lalaba aljihunsa ya ciro naira 100 da ta rage masa ya mikawa Aisha. “Je ki siyo koko ku sha” Aisha ta saka hannu biyu ta karba. “Yaya Wallahi ko jiya Mama ba tai bachi ba, yanzu ma jikinta zafi yake” Ajiyar zuciya ya sauke. “Jarabawa ce, ga rashin kudi, ga rashin mata ta gari, ga rashin lafiya Alhamdulillah” Ya fada yana kallon mahaifiyarsa dake lullube bata ma san ya zo ba, karasa yai kusa da ita ya yaye mayafin data lulluba da shi ya taba jikinta sai ya ji shi da zafi sosai. Mikewa yai tsaye ya fito daga dakin cikin wani irin yanayi na rashin jindadi. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya rike a hannu yana kallo, ya san ko siyar da ita yai kudin ba zai isa ya kai Mama asibiti ba, jinginar daya bada ma daker ya samu ya biya mutumen ya karbo wayar. Bakin kofar dakin ya zauna ya dafe kansa, yana mamakin lamarinsa wani lokacin shi kansa abubuwa suna daure masa kai, ga karatu yayi kuma ya fito da kwali mai kyau amman aiki ya gagareshi, wadanda sukai karatu tare wasu duk sun samu aiki har sun bar kasa, wasu kuma suna Abuja wasu a manyan mukana gobnati wasu a manyan bankuna da kamfani amman shi ya kare a shagon Barber, shi ma daker ya samu wani kawunsa ya bude masa shagon. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allah ka kawo mana sauki” Ya furta yana dago kansa ya shiga contact dinsa ya nemo number abokinsa kuma amininsa Nura. Wayar bata dade tana ringing Nura ya dauka. “Hello Faruq” “Na'am Nura ya gida?” “Lafiya kalau kwana da yawa” “Sai godiya, ina su Sakina” “Lafiya kalau” “Wallahi Nura ina cikin matsala” “Subhanallahi miya faru?” “Abubuwa da yawa, yanzu dai wanda ya fi damuna rashin lafiyar mahaifiyata, kudi nake so rance idan zan samu na kaita asibiti” “Kash.... Wallahi Faruq yau da 500 na tashi na basu su karya, ka san abu ga ma'aikaci idan ba albashi akai ba, ba mu da kudi, kuma gashi albashin na jihar zamfara sai a hankali anki a gyara mana, ga kayan masarufi sai tashi suke, abun da zaka siya da 20k yanzu sai 40k shiyasa albashin baya mana auki” “Haka ne, Allah ya sauwake” “Ameen, amman da zaka iya da kaje gidan Alhaji Mu'azu Shimkafa ance suna da Foundation na taimakon marayu da mabukata, amman idan baka jin kunya kasan wasu basa son zuwa irin abu na neman taimako” “Haba Nura ina zancen kunya ga mai nema, suna nuna mutun a tv ne?” “No babu ma wanda zai san an maka, amman ance Dattijon yana taimako sosai gaskiya, ban san yadda ake bi ba, amman dai idan kaje can gidansa ba rasa taimakon da zai maka ba, har aurarwa suna yi ga marayu su masu komai” “Ai ban sani ba, ina dai jin ana fadarsa Tsohon Minister kudi ko? Ban san yana taimakom nan ba Wallahi, amman zan je yanzu Inshallah na gode sosai” “Allah yasa a dace, ya bata lafiya anjima zan shigo na dubata Inshallah” “Okay” Ya dauke wayar daga kunnesa ya mike tsaye da sauri sai a lokacin ya tuna da be tambayi unguwar da yake ba. Hakan yasa ya sake kiran number Nura. “Baka fada min sunan unguwar ba?” “Shimkafi Road, kana shiga unguwar kace gidan Alhaji Mu'azu Shimkafi kake nema, za a nuna maka” “Okay” Ya saka wayar aljihu be ma koma cikin gidan ba ya nufi titi, da kafa ya taka tun daga gadar gaba har unguwar Shimkafi road, akwai tazara amman a haka yai ta cin kasa saboda babu ko naira aljihunsa. Kamin ya karasa shiga cikin Quarters din wayarsa tai ringing, yana ciro wayar ya duba, a take gabansa ya fadi ganin number Malam Musa Dillali, hakan nan dai ya daure ya dauka. “Hello” “Hello Faruku haka ake daga karbar number sai ka ba matarka ta ciwa mutun mutunci?” Tsaya yai daga tafiyar da yake fuskarsa da mamaki. “Wane mutum kuma?” A nan Malam Musa ya fada masa yadda sukai da Baturiya dazun sannan ya dora da abun da mai gidan ya fada masa. “Wata kila kiransa tai ta ci masa mutunci, yanzu ya kira ni yana ta masifa wai wata ta kira shi Baturiya ta zage shi, ya baku daga yau zuwa gobe ku tashi ku bar masa gidansa” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Wallahi Malam ban san Matata zata yi haka ba, kuma Wallahi ban ce zan karbi number sa ba” “To yanzu dai sai ku san abun ba, Baturiya ko balaraba ta ja maka” Malam Musa na fadin haka ya kashe wayar, Faruq ya dafe kansa. “Na shiga uku wai me ke damun Rafi'a ne? Ta sake janyo mana wata fitinar kuma? Ina ruwanta da mai gida?” Wani irin kololon bakinciki ne ya taso masa, sai ya ji kamar na runtse ido ya bude a gansa a kabari ya huta, yana fama da wasu matsalolin yanzu kuma ta ballo masa wani. “Wallahi yau sai na miki mugun duka, Rafi'a sai kin dawo hayyacinki in ma baki da hankali sai kin yi shi” Ya fada rai a bace, duk abun da take masa na bacin rai bata taba mata masa rai irin wannan ba, domin be san inda zai je ba idan ya bar gidan haka nan ya cigaba da tafiya ransa a bace. Da tambaya ya aka nuna masa kofar gidan Alhaji Mu'azu Shimkafi, Gate din gidan kadai a abun kallo ne, balle kuma farar ginar da aka kawata da farin fenti ga shuke shuke itatuwa da fulayoyi, idan ka daga kanka kuma sai ka hango gidan sama daga can cikin gidan an kawata ko'ina da gilasai komai a tsare kamar ba za a mutu ba. Faruq ya girgiza kai. “Allah man yasha'u, ka baiwa bawa ba dan kana son shi ba, kuma ka hana Bawa ba dan baka son shi ba, Allah ka bamu na mu arzikin na halal, yanzu nan gidan mutum daya ne” Ya fa da yana mamakin tarin dukiyar dake gidan. Karasa yai bakin gate din yana kallon security cameras daka laka hagu da dama na gidan sannan ya kwankwansa kofar gate din. Ba dade wani police ya bude masa yana sanye da uniform dinsa. “Malam Lafiya?” Faruq ya mika masa hannu suka gaisa cikin mutumci. “Dan Allaj ina son ganin mai gidan ne matsala ce da ni” “To ganin mai gidan a yanzu ai, sai an jira domin be fito ba, idan zaka iya jira a nan wajen idan ya fito sai ka tare shi da matsalarka, duk dai baya son a ana mishi haka amman karka nuna masa na san da zuwan ka” “Ba Matsala na gode sosai” Faruq ya nemi wani gurin ya zauna a nan kusa da gate din, shi kuma police din ya koma cikin gidan ya maida gate din ya rufe. Be yi minti talatin da zama ba, aka sake bude gate din sai dai wannan karon gate din gaba daya aka bude ganin mota zata fito yasa yai saurin mikewa tsaye a zatonsa mai gidan ne sai ya nufi motar da sauri, ganin ya nufota yasa ta tsaya ta sauke gilashin motar tana kallonsa. “Ya akai?” “Daman na dauka mai gidan ne shi nake son gani” “Saboda me kake son ganinsa?” Ya tambaya tana kare masa kallon from head to toe. “Taimako nake nema” Hannu ta saka ta cire katon gilashin idonta. “Okay idan ana neman taimako sai azo har kofar gidan mutum a takura masa? Baka san yadda zaka bi ta Foundation ba? Ba ma taimako a gida sai ta karkashin kungiya, kaje can ka samu kungiya karka sake zuwa nan, Talauci ba hauka ba ne” “Haka ma Arziki ba hauka ba ne malama, karki nemi fada min maganar banza saboda na zo nema a gidanku, ni ba wulakantaccen ba ne” “Really” Ta bude motar ta fito tana masa wani banzan kallo. “Dubi ka! Ka zo nema a gidanmu kuma kana cewa kai na wulakantacce ba ne? To waye kai? Kai kama isa ka zo nema a gidanmu kuma fada min maganar banza?” “Maganar banza ana furtata ne a lokacin banza kuma ga mutanen banza irinki” “Ni...” Ta nuna kanta Faruq ya daga mata kai cikin bacin rai daman be gama wankewa daga na matarsa ba ita kuma tana neman kara masa wani, hannu ta daga zata mare shi sai ya rike hannun da mugun karfi ya jefar da shi. “Kika kuskura kai hannunki a fuskata sai na illataki, dan ina neman taimakonku ba shi zai baku damar wulakanta ni ba” Bata sake ce masa komai ba ta juya da sauri ta isa gurin gate din ta buga da karfi, daman Police din ya rufe gate din a lokacin daya bude mata ta fita, da sauri ya bude sai ta nuna masa Faruq. “Ku rike mutumen can” Da sauri ya fito shi da wasu Police din biyu suka nufi inda Faruq yake tsaye suka rike shi, ita kuma ta nufi cikin gidan da saurinta kamar zata tashi sama, Talba dake kokarin tashin motarsa yana kallonta ta danna door bell din kofar be kula ta ba ya ja motarsa zuwa gate ya hanna horn, dai dayan Police din ya dawo ya bude masa gate din ganin suna rike da Faruq ga kuma motar Leila dake bude a kunne yasa shi tsaya ya sauke gilashin motarsa. “Lafiya?” “Wallahi ba mu san abun da ya faru ba, Hajiya Leila ce tace a rike shi” Talba ya kalli Faruq daga sama har kasa, be masa kama da yan ta'addaba, kuma ya san halin yar'uwarsa mafi akasari fadan da take da mutane ita ce bata da gaskiya. Hakan yasa shi tambayar Faruq dake kokarin fisge kansa daga rikon da Police din suke masa. “Malam Lafiya?” “Lafiya ce zata saka Police rike ni? Daman idan za ku taimaki mutum sai kun wulakanta shi” Faruq ya fada cikin fusata, hakan yasa Talba ya bude motar ya fito ya nufo inda suke tsaye. “Ku sake shi” Ya fadawa Police din sai suka saki Faruq, Talba ya saka hannayensa aljihu yana kallon Faruq. “Bari na fada maka wani abu, ba a min tsawa kuma ba a fada min bakar magana, amman na maka uzuri saboda na fahimci kana cikin bukatar taimako ne, and bana son na yi ma mutun wani abun ta dalilin taimako, da ace a hanya na hadu da kai da zan iya maka cin mutunci fiye da kima, now tell me miya faru” Kalaman da Talba yai yasa Faruq sasautawa zuciyarsa domin ya fahimci ba fada Talba yake son yi da shi ba, idan ma sun yi fadan ba riba zai ci ba. Cikin bacin rai Faruq ya fadawa Talba abun da ya faru, sai Talba ya girgiza kai ya lumshe ido ya bude, ba dan baya iya bawa kowa hakuri ba, da sai ya bawa Faruq, domin ya fahimci halin da yake ciki. “Ka manta da abun da tai maka yanzu fada min wani iri taimako kake so?” “Mahaifiyata ce ba lafiya” Faruq ya fada domin yana jin cewar shi ne kawai abun da zai iya fada a halin yanzu, kasancewar shi ya fi damunsa. Talba ya juya ya koma cikin motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna, wani karamin diary ya dauko yai rubutu akai, sannan ya bude wani guri a cikin motar ya dauko 100k ya fito ya nufo Faruq. “Ga wannan Allah ya bata lafiya, and idan kana neman taimako a foundation din Mahaifina ka tuntubi wannan number, su za su tantance komai su sanar mana” Ya mika masa number bayan ya bashi kudin. Faruq ya saka hannu biyu ya karba cikin jindadi. “Na gode sosai Allah ya saka da alheri, ya kara sutura” Uffan Talba be ce masa ba balle har ya amsa da Ameen, sai juyawa yai ya nufi motarsa, yana kokarin shiga yaji dayan police din na fadin. “Hajiya tace a rike shi, ku rike shi” Juyowa Talba yai ya kalli Police din, sai suka fasa rikon Faruq. “Hajiya Babba ba Leila ba ita ta kira ni yanzu” Da kai Talba yai ma Faruq alama daya wuce sannan ya shiga motarsa ya danna horn suka sake bude masa gate din yai ribas ya shiga cikin gidan. A harabar Entrance din ya faka motarsa sannan ya fito ya nufi kofar falon kamin ya karasa sabuwar mai aikin Momy ta bude kofar da sauri da alama fitowa za ta yi. “Yauwa ranka ya dade Hajiya tace na kira ka” Shiga yai cikin falon hannayensa zube a aljihu sai kamshi turare yake zubawa, tsaye ya samu Momy Leila na gefenta dayan mai aikin Momy Zulai tana tsaye nesa da su, domin wannan karon har masu aiki biyu Momy ta dauka. Yana kallonta ya san ranta a bace yake, can kuma ya kalli Leila da ke hawaye, kamin ya kalli Kabir dake zaune rike da waya yana kallonsa. “Talba haka zamu zauna mutane suna ci mata mutunci kana daukar side dinsu” “Ta fada miki Abun da tai masa?” “I don't care, amman komai tai masa ai be kamata ya rike hannunta ba, har ya fada mata bakar magana alhalin shi yanzo nema a gidansu, har kuma ka bar shi ya tafi” Talba be ce komai ba, har Mairo ta shigo tare da police din da Momy tasa ta kira daman shi da Talba ta ce ta kira. Yana shigowa Momy ta nuna shi da yatsa. “Wannan ya zama na karshe da wani zai zo ya takura mana kofar gida, karka sake barin kowa ya shigo mana ba tare da saninmu ba, idan makamancin haka ya sake faruwa a bakin aikinka, ba wai a gidan nan kadai ba, no ka daina saka Police Uniform kenan har a bada mark my words” “Ayi hakuri ranki ya dade Inshallah zan kiyaye” Cewar police din sannan ya juya ya fita. Da ido Talba yai ma Mairo da Zulai alamar su fice daga falon sai suka fice da saurinsu. “Wannan abun yayi yawa Momy, ya kike Leila ta zama? Ba fa Amal bace, taya Leila zata raini yara masu tarbiya idan tana wannan halayyar? Saboda wani ya zo nema daga abun da Allah ya wadata mu da shi sai ya zama abun wulakantawa? And ji yadda kike fadawa Police din nan magana kamar wanda yai wani babban laifi” “To ya kake son na yi? Haka zamu yi ta zama Leila bata da yanci a gidan nan? Haka zaka rika mata idan kun yi aure ka bar ko wane kare da biri suna cin zarafinta? Shi ne jindadinka?” Talba ya kalli Leila cikin yanayi na rashin jindadi. “I wonder what kind of woman zan aura! Akwai karamci tarbiya a tare da ke, ba zan iya daukar wannan halin na ki ba kina bukatar ki canja rayuwa Leila...” “Kai kake bukatar canja rayuwa ba ni ba...” Ta fada mishi kai tsaye sannan ta nufi upstairs. Momy ta kara da nata. “Kana fada min Leila bata da tarbiya ko? An maka dole ka aureta ne? Ko kuma kana son ci min fuska ne Saboda ba ni na haife ka ba?” Talba ya kalleta da sauri, Kabir ma mikewa yai tsaye sai a lokacin ya saka bakinsa a maganar. “No haba Momy... ” Momy ta daga masa hannu. “Na san abun da yake nufi, duk abun da kake kana yi ne saboda ba ni na haife ka, kuma na sani, daman tsintacciyar mage bata taba zama mage ba, amman karka manta ni na raine ka, ko da ka bude ido baka san mahaifiyarka ba ni ka sani, na raine kamar uwa, so weather you like it or not I'm still your mother, karka manta da wannan...!” Tana kaiwa nan ta nufi upstairs ya bita da kallo kalamanta na ratsa kowane lungu da sako na zuciyarsa. Leila ma da bata karasa hayewa ba juyowa tai ta kalleshi cikin yanayin da ke nuna bata jidadin kalaman Momy ba, balle kuma Kabir da ya tsaya kamar hoto yana kallon dan'uwansa cikin yanayi na rashin jindadi. <<<<<>>>>> Na ce ba? Baturiya ko ba indiya ta taro mach da Faruq yau 🤔 Anya Leila zata ga Annabi kuwa? 😔 Momy ta kyauta a kalaman da tai ma Talba saboda Leila? Wai ina Aminatunan mu ne? 13 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Juyawa Talba yai ya fice daga falon, sai Leila ta sauko da sauri zata bi bayansa, kamar wanda ta tuna wani abu sai kuma taja ta tsaya cikin yanayi n rashin jindad “Yanzu ai kin jidadi ko?” Kabir ya tambaya yana gyara shirt din jikinsa. Sai ta kalleshi cikin yanayin damuwa domin har ga Allah bata son Talba ya shiga damuwa duk kuwa da irin son da take ya canja bata son ace saboda ita Momy ta yi masa Wani abun bacin rai domin ba su saba haka. “Wane irin dadi kuma? Kana jin kalaman da Momy ta fada masa fa” “Eh ai ke kika ja, ke dai burinki wulakanta mutane” Yana kaiwa nan shi ma ya nufi kofar fita falon cikin bacin rai, duk irin rashin jituwar da suke samu da Talba baya son wani abun bacin rai ko damuwa ta same shi, kamar yadda Talba ma baya son ganin bacin ran Kabir sai dai dukansu sun san cewa ba a komai na rayuwa suke shan inuwa daya ba, musamman ma Talba da yafi kowa girman kai a gidan. Juyawa tai ta hau stairs din ta nufi dakin Momy, ko knocking bata tsaya yi ba ta tura kofar ta shiga kamar zata fasa kuka. “Haba Momy wannan abun har ya kai ki fadawa Talba irin wannan maganar ne?” Momy dake zaune gaban madubi tana kokarin cire awarwaron hannunta ta juyo ta kalleta da mamaki. “Ba ki kalmar da yake jifata da ita ba?” “Da ni yake ba da ke ba” “No cewa yai baki da tarbiya, kai tsaye na fahimci inda kalamansa suka dosa, tun ba yau ba ai na lura da yadda ya canja kamar mai son yai kishi da ni” “Haba Momy Talba ne zai yi kishi da ke?” “Eh mana, bakisan wasu yayan suna tsanar iyayen da ba su haife su, Idan ba haka ba ai ba zai min kalaman banza ba, ko ba komai ni surukarsa ce right” “Momy yanzu zai ji babu dadi Wallahi ransa zai bace” “Ran nasa ya dade be bace ba, wannan wane irin so ne kike ma Talba wai? Shi fa baya son ki kamar yadda ke kike sonsa, kuma naga ke ma ai kina bata masa ran” “Eh amman Momy wannan ai matsalar mu ce ta dabam ba wai akan ba” “I don't care, idan ke baki san zafin abun da ya fada ba ni na sani” Mikewa tai tsaye cikin yanayin damuwa ta fice daga dakin tana ta sake sake, ko ta kira ta bashi hakuri akan abun da Momy tai ko kuma ta kyale shi, sai dai idan ta tuna cewar saboda ita komai ya faru sai ta ji wani iri. Dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira Madina ta labarta mata abun da ya faru, daman komai na duniyar ba zata iya boyewa Madina ba, no matter how Momy ta kwatseta akan abu sai ta fadawa Madina. “Amman Leila baki taba bata min rai irin yau ba, wai miyasa kike barin zuciyarki tana aikata abun da Talba baya so? Ke baki san yadda zaki faranta masa rai ba? Haba Leila ni kam da baki labarta min wannan abun ba da ban shiga damuwa ba Mtchssssss ” Ta yanayin yadda Madina take mata responding kadai ya isa ya karantar da ita cewar Madina ta fita shiga bacin rai ma. “Ni ma fa ban jidadi ba, that's why na kira ki ko zan samu mafita” “Mafitar me? Ni Wallahi kin bata min rai, i don't think i can eat today, kin bata ran bawan Allah, na sha fada miki haka rayuwarsa take ki bishi a haka mana sai ku samu zaman lafiya amman kin gagara daukar shawarata” “Look Madina na yarda a nan ina da laifi daya janyo aka fada masa magana marar dadi, amman maganar Allah ban ga laifi a abun da na yi ba, Talba yana shigar min hanci da yawa fa” “Yanzu dai na ji, idan kina son mu shirya da ke kije ki bashi hakuri” “Na bashi hakuri fa? Gaskiya ba zan iya ba” “To miye a ciki, ke fa kika ja komai, kuma ba akan abun da yai miki fada zaki bada hakuri ba, akan abun da Momy tai masa” “Zan ga idan zai yiyu” “Please do this for me, tsakani da Allah ko kadan bana son na ji ran Talba ya bace, Mutumen yana son ki Leila kin kasa ganewa ne, kina raina yadda rayuwarsa mata da yawa suna can suna sonsa a haka, ki bi a hankali” “Na ji” Ta fada tana juya ido, bata tsaya jiran abun da kawarta zata sake fada ba ta yanke wayar ta wurgar saman gadonta, sannan ta fadi kwance. TALBA POV. A lokacin daya fita daga falon cikin motarsa ya nufa ya zauna, ba karamin taba shi kalaman Momy sukai ba, duk yadda ya so ya ga laifin kansa kan abun da yai ma Leila sai ya kasa, zuciyarsa nata raya masa a daidai yake, hannu ya kai ya dauki wayarsa ya kira Ali. “Hello” “Kana ina?” “Office ya akai?” Iskar dake bakinsa ya busar ya kashe wayar ya aje gefensa sannan yai ma motar key yai reverse ya danna horn, tun kamin ya isa gate suka bude masa sai da ya fito ya ga motar Leila dake waje har lokacin sai dai wannan karon an kullenta amman motar tana kunne, horn ya danna har sau biyu wanda hakan ya saka Bello Police lekowa ya nufo motarsa da sauri, sai ya sauke gilashin motar ya nuna masa motar Leila, Bello na ganin ya nuna motar ya san abun da yake nufi na sai ya masa magana ba. Sai ya nufi motar Talba kuma ya hau titi, driving yake kamar wanda be san inda zai je ba, kadan kadan yake lafiya har ya isa asibitin FMC a inda ya saba fakin ya faka motarsa ya fito yana jin kamar ya juya ya tafi gurin aikinsa sai dai ya san he need someone to talk to, a duk lokacin daya shiga wata damuwa komai kankantarta Ali yake fara fuskanta ya fada masa damuwarsa duk kuwa da kasancewar wani lokacin za su rabu a fada ce ne. Kai tsaye office dinsa ya nufa and he got lucky Ali yana ciki sai dai office din ba shi kadai ba ne tebur biyu ne na dayan abokin aikinsa. Ko kallon gefen da abokin aikin na Ali yake be yi ba ya nufi teburin Ali ya zauna a kujerar baki. Ali na kallon abokinsa ya fahimci akwai damuwa. “Leila ce ko?” Talba ya dago ya kalleshi, sai kuma ya juya ya kalli teburin abokin aikinsa sai a lokacin ya lura da be shigo ba “No” Ya amsa masa cikin yanayin damuwa. “Na san dai abu ne mai wahala yadda Daddy yake ji da kai abu ne mai wahala ya bata maka rai, sai dai idan wata damuwa ce ta dame shi a san zata iya shafarka” Ajiyar zuciya Talba ya sauke, sannan ya labatawa Ali abun da ya faru. Ali ya kwanta jikin kujerarsa yana kallon Talba duk kuwa ya san kallo na daga cikin abun da abonkinsa ya tsana. “Momy dai ta fusata ne, kuma kai ke da laifi” “Amman Ali ban yi dan taji haushi ba, ba ina nufin bata bawa Leila tarbiya ba, kawai bata fahimci ni ba” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya nufi windows din office din. “Kuma na ji babu dadi, na san ba ita ta haife ni ba, amman ban taba mata wani kallo na dabam na bayan uwa, ita ta raine ni a hannunta na tashi na girma” “Kai ka ji zafin abun da ta fada maka balle ita? Yanzu dai ka manta da komai ka dauka cewar kuskure ne irin wanda kowa yake yi” “And seriously ba zan iya zama da Leila da wannan halin ba” “Kai da za a bibiya zata ce ba zata iya zama da kai saboda halinka ba, Talba dan adam duk tara ne be cika goma ba kowa ka ganin yana da inda be cika ba, abun da zai fi kawai ka dauke idonka daga gareta, musamman a yanzu da ka fahimci idan ka taba ta ran Momy yana baci, ka bita a yadda take sai a samu zaman lafiya” “And... ” “And ka koyi bada hakuri Talba, ba zaka ragu ba, mata rarrashi suke so, yanzu duk wannan abun daya faru idan ka koma gida ka yi kamar komai be faru ba, ka samu Leila ka lallabata ka bata hakuri” “Ba a hallici wannan macen da Talba zai bawa hakuri ba, ba ayi mace da zan yi ma yar murya ina lallabata akan tai hakuri ba, matukar tana kasa da ni” “Ya kamata ka sauke wannan nauyin daka dorawa kanka Talba life is very simple” Talba ya juyo ya kalleshi. “Ko?” Sai Ali yai dariya domin ya san halin abokin nasa yanzu zata iya bare musu su fara siyar da hali. “Yanzu dai forget about it, akwai maganar da nake son mu yi da kai” Talba ya juya ya cigaba da kallon harabar asibiti da yadda mutane suka zirga zirga sai dai hankalinsa da ears dinsa suna gurin Ali. “Akwai wata yarinya da aka kawo last week, tana cikin mutanen da yan bidiga suka raunata” Yana tsaka da maganar sai kuma yai shiru yana duba wata takarda dake gabansa. “To ta ina alakarta ta shafe ni?” Talba ya tambaya ba tare da juyo ba, jin Ali ya dauko masa wata maganar da be san ta inda zata masa amfani ba. Murmushi Ali yai yana jinjina halin abokin nasa. “Tana bukatar taimako ne sosai gaskiya” Juyowa Talba yai ya rumgume hannayensa yana kallon Ali. “Kai ina zuciyar taimakonka ta tafi ne? Ko baka taimako?” Ali yayi dariya. “Talba kasan irin taimakon da na yi mata? Tun da aka kawo su ba Gobnati bata sake waiwayarsu ba, babu wani tallafi da ake kawo musu, mostly yan uwa da iyaye ne suke daukar nauyinsu, sisin kwabo babu daga gobnati komai daga alijunsu dana yan'uwansu yake zuwa, wasu an sallame su sai dai wadanda albarushi ya shiga jikinsu ne kawai suke nan suna jinya har yanzu” Ya hade yawun bakinsa sannan ya cigaba. “But yarinyar har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, babu wani da yazo yace shi babanta ne ko yayanta, komai da ake biya daga aljihuna ya fita na taimaka mata saboda ta bani tausayi sosai” Ganin Ali yana maganar babu alamar wasa a tare da shi yasa shi tambayar abun da yake son ji daga gareta. “Miya same ta?” “Na farko dai she can't walk, she can't talk tun da aka kawo ta bata taba magana ba, idan dare yayi sai na yi mata allurar bachi sannan take iya bachi, kuma na yi na yi da ita ta ki tai magana, babu wata alama data nuna yarinyar tana magana, idan ma kaga ta motsa to na matso kusa da ita ne da allura, sai ta fara kallon allurar tana hawaye, and the most sadness part is an yi mata fyade sun lalatata ko mai haihuwa iyaka kenan” Kusan a lokaci daya komai dake aiki a zuciya da jinin Talba ya tsaya cak na dakiku. Kalmar fyade wata irin babbar kalma ce mai razanarwa da muni a kunnuwan tsabtattacin mutane irin Talba, shi din namiji ne ba mace ba, amman ya tsani jin duk wani abu daya shafi fyade balle kuma fyaden kansa, be taba ganin Aminatu ba, labarin wanzuwarta be taba ziyartar kunnensa ba, kamar yadda zuciyarsa da tunaninsa ba su hasaso masa mai irin rayuwarta ba, wani abu daga cikin cikin tausayinta ya kusa zuciyarsa ya samu guri a kusa da kirjinsa ya zauna, hankalinsa ya kara tashi sosai a lokacin da Ali yake kara fada masa halin da yarinyar take ciki. “I don't think kurma ce, domin idan na ce kee zata kalleni amman bayan haka bata yin komai, na sha jera sunaye ina kiranta da su amman bata taba min wata alama da zan gane sunanta ba, kuma kafanta ya kumbura wanda hakan ke nuna ta yi tafiyar da ta wuce kima kuma ta taka abubuwa da yawa gaskiya yarinyar tana bukatar taimako” “Ta ina ya kamata na taimaka? Irin mutanen kamata yai ace gobnati tana daukar nauyin maganinsu fa” “Wallahi kuwa ni ma abun da nake fada kenan amman sai kaga an barsu kara zube ba a kula su. Yanzu dai tana bukatar a duba lafiyar duka jikinta, a kula da kafafuwanta, private part dinta dai yana samun sauki sai dai da zata samu wanda zai kula da ita da zata fi samun sauki” Ali na kaiwa nan ya mike tsaye. “Zo muje ka ganta” “No ba sai na ganta ba, kasan akwai mutane sosai a gurin nan” “Haba dai irin abubuwan nan suna karawa mutum tsoron Allah, Allah kadai ya san halin rayuwar data shiga, ni ba abun da ya fi bani tsoro kamar rashin maganar ta, kuma gashi har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, and bata kallon mutane idan zan shiga inda take har na yi abun da zan yi na gama ba zata kalleni ba sai idan na dauko allura, and wani lokacin sai kaga hawaye na sauko a idonta, idan aka aje mata abinci bata ci yadda ka bar shi haka zaka zo ka tararda shi, idan ka danka mata abu a hannu bata rikewa” “Ya ake take rayuwa bata cin komai?” “Ta hanyar allurar da maganin da muke saka mata a drip” Talba ya lumshe ido ya bude. “Mutanen nan suna ganin rayuwa, farincikin da suke so, kadan ne amman ya gagaresu, a kashe su, a kwashe dukiya a kune kuma wandanda aka raunata a bar su da daukar nauyin kansu, Allah kadai ya san abun da akai mata ko ta gani” “Wallahi ai mu muna ganin abubuwa sosai” Ali ya nufi kofa Talba ya bi bayansa sai suka fito tare suka jera zuwa gurin da ake aje marasa lafiya, suna tafe Ali na masa hirar wasu da aka kawo da yadda sukai ta fama da su, Talba dai be ce Uffan ba har suka shiga female ward din suka doshi gado na 36 da inda Aminatu take kwance. Ko da suka isa sun tarar an ja mata lalube gurin da take, an rufe ta ta ko'ina ta yadda bata ganin kowa kuma kowa baya ganinta. Ali ne ya fara daga labulen ya shiga sannan Talba ya shiga. Kwance suka same ta idonta a rufe hawaye na saukowa ta gefen idonta. A zatonsa babbar mace ce sai da ganinta yarinya mai kananan shekaru yasa jin tausayinta ya karu da kashi talatin cikin dari, domin ya san fyade na daga cikin abun da yake lalata rayuwar ya mace, kuma yana daga cikin abun da mace tafi tsana balle kuma wannan da take karamar yarinya. Ali ya saka hannu ya dauki safar dake gurin ya saka a hannu sannan ya taba kafarta sai ta bude idonta da suka yi ja da alama ta dade tana hawayen ta sauke su akan Talba dake kallonta fuskarsa cike da haiba da annuri. Shi ma kallonta yake ba yabo ba fallasa, daga can cikin zuciyarsa cike take da tausayinta sai dai jinkai da rayuwarsa daya daukarwa kansa ya saka ya kasa barin hakan ya bayyana a kyakkyawar fuskarsa. “Da son samu ne, a ware mata daki daya ita kadai saboda halin da take ciki, so that ta samu kulawa ta musamman kuma tana bukatar ayi mata gwaje gwaje, tana ma bukatar jini” Ali ya fada yana kama hannunta ya tabawa. Har lokacin Aminatu Talba take kallo ji take kamar ta taba ganinsa a wani gurin sai dai bata san ko'ina ba ne, ji take kamar ta bude baki tai magana sai dai bara da kuzarin yin haka, kamar yadda take jin jikinta be da kuzarin riketa balle har hannunta ya jimke wani abu, tabbas yanzu kam ta tabbatar da kalamanta sun kare, kamar yadda take jin komai na rayuwarta a yanzu ya zama tarihi, bata yarda ita ce dai wacan Aminatun dake rayuwa a karkara tare da iyayen da yan'uwa ita ce a nan ba. Da ace zata iya bude zuciyarta ta sun yi arba da tarin bakinciki da duhu zuci, wanda idan suka karanta wata kila likitan zai tausaya mata ya daina bata taimakon da yake bata na drip da allurar so that ta samu ta huta ita ma tafi sahun yan'uwanta da iyeyenta. Har gobe tana jin karar bindigar da aka kashe mahaifinta da mahaifiyarta a cikin kanta, ta kasa manta yadda yan ta'addan suka rika yawo a jikinta a lokacin da suke kokarin keta rigar mutuncinta, idanuwanta sun ki su goge hoton fyaden da akai ma mahaifiyarta a gaban ido wai shin miya rage mata? Miyasa take a raye har yanzu? Ali ya kalli Talba dake tsaye ya kalli Aminatu data kafe Talba da ido, a zahiri shi take kallo, a badini kuma rayuwarta bayan take hange a cikin idanuwan mutumen da take jin kamar ba a yau ta taba arba da shi ba. Har lokacin hawaye ba su daina zubar a idonta ba. “Kallon mutane ba dabi'ar bace ko dai ta san ka ne?” Ali ya tambaya, kallonsa kawai Talba yai ya dauke kai. “Kin san shi ne?” Bata dauke ido daga kallon Talba da take ba balle har ta kali Ali ta amsa masa. Ali ya kalli Talba dake kallonta shi ma har lokacin. “Ka yi mata magana wata kila zata amsa” “A canja mata daki idan kana ganin hakan ya dace, idan ka yi list din ko nawa za a ashe sai ka fada min” Shine abun da Talba ya fada sannan ya sakar ma Aminatu murmushinsa mai tsada kadan wanda yafi kama da na yake ya juya ya fice. Yana fita sai ta lumshe idonta kamar mai bachi sak rayuwar da take a gidansu ita da iyayenta da yan'uwanta ya soma kawata idonta dake rufe. Juyawa Ali yai ya fice yana kokarin cire safar hannunsa. 14 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min. Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* BATURIYA POV. Bayan ta gama zazzagawa Alhaji Sule rashin mutunci ta shiga tai wanka. Ta shirya cikin farin lace sai aikin gogawa fuskarta powder take, can kuma ta mike tsaye tana kallon kanta a madubi, sai ta ji ana kwankwasa gidanta, jiki na rawa ta aje soson hodar dake hannunta ta fice daga dakin da sauri taje ta bude gidan domin ta san da zuwan Ramlee. Rumgume juna sukai ita da Ramlee kowa ne na murnar ganin wani kamar wadanda suka shekara basu saka junan a ido ba. “No no ba dai lace din nan kika saka ba? Ai yanzu kuma kin wuce saka kananan kaya” Ramlee ta fada tana yatsina fuska “Ke mai tsada ne fa, yayata ta ba ni shi, mai kudi take aure fa” “Baturiya kenan yanzu ai kin wuce wata ta kwance ta baki ki daura, sai dai ke ki kwance ki bawa wata ta saka, ga wata abaya nan na zo miki da ita kamin mu fara zuwa siyayen tufafi masu tsada” Ta karashe tana mika mata jakar dake dauke da abayar, wani irin tsalle Rafi'a tai ta dire tana murna. “Amman Wallahi kina da zuciya mai kyau, kamar kin san ina mararin abaya” Ta karba da sauri ta nufi cikin dakinta sai Ramlee ta bi bayanta tana murmushi, a falo ta zauna har sai da Rafi'a ta canja tufafin jikinta daga lace zuwa sabuwar abaya, ita kanta ta yaba yadda bakar abayar tai mata kyau kasancewarta fara, cikin zumudi ta nufo falo. “Allah ya miki sura Baturiya Wallahi kina da kyau” Ramlee ta fara tana kallonta. “Wallahi zaki sha kudi, manyan masu kudin nan suna son fararen mata amsu kananan shekaru” “Da gaske?” “Uhm har sai na rantse miki ma, a ciki ma zaki samu wanda zai ce miki aurenki yake so, ko ma be ce ba idan kin ga ya miki sai mu bada sunansa kawai a kama mana shi, dube ki gani fa Wallahi ke matar manya ce Baturiya” Baturiya ta yi murmushi tana jin wani irin dadi, sannan ta koma ciki ta dauko. Jakarta da karamar wayarta da makulli ta fito. “Ina Sultan” “Tun dazun na tura shi makota” “Aiko kin kyauta, domin yara akwai sa ido zai iya fadawa Babansa na zo” Suka yi dariya sannan suka fito daga falon kamin su fita daga gidan gaba daya Baturiya ta kulle gidan. Sannan suka nufi bakin titi inda motar Ramlee take, front seat Baturiya ta shiga Ramlee kuma ta ja motar suka kama hanya, suna tafe suna hira har suka shigo cikin gari, gaban wani katon shagon siyar da wayoyi Ramlee ta faka motar, kusan a tare suka fito ita da Baturiya, tana kokarin rufe motar ta hango Alhaji Garba jikin mota yana waya. “Ramlee bari na gaisa da mijin yayata ga shi can” “Ba zai ce wani abu ba?” “Zan ce ke na rako ai, ban sani ba ko zai ba ni wani abun yana da alheri ai” “Shikenan bari na jira ki daga ciki” Kai ta daga mata sannan ta nufi gurin da yake tsaye jikin motarsa yana waya, ganinta yasa yai hanzarin yanke wayar da yake ya kalleta yana murmushi. “Baturiya ina kika fito?” “Ai kai zan tambaya na sani ko wata budurwa ka rako” Yayi dariya. “Zaki bari ne? Ai kin tare kowa ya gida ya kowa ina mijinki?” “Kowa lafiya kalau, ina Anty” “Lafiya Kalau take, me kika zo yi nan?” “Wallahi wayata ta bata kwanan baya shi ne na zo siyen karama” “Oh haka fa, Yayarki ta fada min Allah maida alheri, ai da na san da zuwanki da na riko miki wani abu gashi bani da enough a mota” “Uhm Alhajina kenan ai kai babba ne, kuna da kudi sai dai idan ba ayi niyar ba mu ba, tun da alherin zuwa zuwa ne” Ya sake yin dariya yana kallonta. “Haka yayarki ta fada miki?” “Aa yayata bata fada min komai ba, haka dai na gani da idona” Ya bude motarsa yana dariya. “Baturiya sarkin rigima ashe dai mijin naki yana fama” “Kana dai fama zaka ce, ko ka bawa wani ne?” Yayi dariya mai sauti. “Zankadediyar mata irinki zan kyautar na dai ara masa shan miya, yanzu dai bari na siye bakin nan naki dan karki je ki fadawa yayarki kin gan ni a gurin siyen waya” Ya fada bayan ya zauna cikin motar, sannan ya ciro bandir din yan dari dari 10k ya mika mata. “Gashi na rufe bakin nan kar yayarki ta ji” Murmushi tai ta karba. “Karka damu Alhajin Allah, ai ko mutum ka yanke agabana ka bani wadannan ka rufe bakina babu wanda zai ji” “Da gaske? Ashe za a iya siye ki da kudi?” “Ba wai za a iya ba, ana ma yi ne” Ta fada tana wani irin kashe masa ido kamar wata tsohuwar karuwa. Binta da kallon da shi kadai ya san manufarsa yana murmushi har ta shiga cikin gurin. A bakin kofa ta samu Ramlee tana jiranta. “Yayarki tana da miji kamar wannan kike zaune a talauci?” “Uhmm yan uwa yanzu ai babu ruwansu da son zumunci idan sun samu daga su sai yayansu” “Shiyasa nake son ki gina kanki ki yi naki arzikin” “Wallahi kuwa, babu abun da yake burge ni kamar katon gida da katuwar mota da kayan sakawa da na ci masu kyau masu tsada, Wallahi ko hoto ake turowa a group zaki ga ko wace shegiya da katon falo, haka nake ta ganin friends dina a gida masu kyau da sutura mai tsada, ki duba ko yan'uwana kowa tana auren mai rufin asiri amman ni kullum abushe ko abunda zamu ci wani lokacin gagararmu yake” “Karki damu kin warke yarinya ke dai ki goge kawai ki iya dadin baki da kwarkwasa da jan hankali” Haka suka cigaba da nisawa cikin shagon suna ta hira, an tsara shago gwanin sha'awa camera a ko'ina ga gilashi da haske gulob kamar ba rana ba,.kana ganin gurin kasan na manyan mutane ne. A tare suka jera da Ramlee suka nufi gurin da aka jera wayoyin techno. Ramlee ce ta fara dubawa sannan ita ma ta kai hannu zata dauki wata sai ta ji an riko hannun nata, saurin kallon gefenta tai da tsoro sai tai arba da mutumen daya rage mata hanya a wacan lokacin da ta sauka tasha daga Kano, murmushi ta sakar masa kamar yadda yake mata murmushin shi ma, sai ta janye hannunta. “Sarki alkawari” Ta watsa masa wani irin kallon irin na masoya. “Daman na yi alkawari?” “Ba ki yi ba amman dai ai ya kamata ki ce min na isa gida lafiya ko?” Ta yi murmushi, shi ma murmushin yai ya gabatar mata da yarinyar dake gefensa. “Ku gaisa da kanwata, ya kamata ku san juna tun yanzu ai” “Sannu” Baturiya ta fada. Sai ita ma yarinyar dake kama da saurayin ta maido mata. “Yauwa sannu, sunana Salima” “Ni kuma Rafi'a amman anfi kirana Baturiya” “Yeah kin fi turawan kyau ai” Cewar saurayin sai duk suka yi dariya har shi. “Me kika zo yi nan?” “Waya na zo siya kasan wayata ta bata” “Oh haka ne, amman kin san na tashi koma gidan nan sai kuma wata zuciyar ta bani hakuri ashe rabon zan hadu dake ne a nan, gaba daya na kasa samun natsuwa tun da muka rabu Wallahi nake ta mamarin ganinki har Hajiya na bawa labarinki” Ta yi murmushi. “Gashi yanzu, ai mun hadu katin daka bani ya bata ne” “Ayyah” Ya fada sai kuma ya kalli Ramlee dake ta duba wayoyi. “Ko zaki bani aron kawar nan taki mu zagaya gurin masu IPhone” “Yeah ba matsala, zan jiraki a mota” Ramlee ta fada tana murmushi, sai Baturiya ta daga mata kai. “Okay” Bayan Ramlee ta wuce ya bawa kanwarsa key din motar. “Je ki jirani a moto” “Okay sai anjima in-law” Budurwar ta fada sai duk suka yi dariya, sannan ya nuna mata hanyar da zasu bi su bullo gurin da aka jera iPhone din. “Fahat sunana duk dai baki tambaya ba” Ta kalleshi ta yi murmushi, da kansa ya zaba mata iPhone mai kyau, sannan ya nufi wajen biyan kudi ya mika atm dinsa, kamar ance ta juyo, tana juyowa tai arba da Nura tsaye gurin biyan kudin, da alama wani ya rako, suna hada ido tai saurin dauke kai gabanta ya shiga faduwa da mugun karfi. Bayan ya biya ya rakata har gurin motar Ramlee ya sake ciro katinsa ya mika mata. “Ki tausayawa zuciyar nan tawa ki kira wayata ko zata samu sukuni” “Karka damu zan kiraka, na gode sosai” “Nine da godiya yau zan yi kwanan farinciki” Ya fada sannan ya rufe mata motar Ramlee yaja suka bar gurin. “Ina kika san shi? Baturiya Allah ya miki farin jini” Dariya tai kamin ta labarta mata yadda akai ta sanshi, sannan ta dora da na ganin da Nura tai mata abokin mijinta kuma amininsa. “Ke kar ya dame ki, idan ma ya fada masa ki bururuce ki ce ki kam sam ba ke bace, idan ya dage ke din ce kice tare da yayanki kika je siyen waya” “Kuma fa kin kawo shawara, idan ba haka ba kam zai iya fusata sosai domin dazun na ci mutun mai mana maganar kudin haya na san kuma za su fada masa” “Saboda me? Ai ba haka ake ba, nawa ne kudin hayar?” “80k” “Just 80k? Yanzu zan baki 100k da mutumen ya baki sai ki nemi inda mai hayar yake ki bashi gaba daya, wayar da ban siya miki ba zan baki kudin daman na yi niyar kashe miki 50k akan wayar dan haka zan baki su a hannu, gobe kuma zan kawo miki kayan mata masu kyau ki fara shirya kanki kamin lokacin da saku gana da Alhajin” “Har da wani shan kayan mata?” “Eh mana, kuma idan kika fara sha karki yarda ki bar Faruq yaje kusa da ke” “Ni daman bana shan kayan mata ai, mutum yana fama da talauci ko a sha kayan mata me zan samu? Shiyasa ba ruwana da shan su, kuma ba kullum nake barinsa yana damuna ba” “To ki dai kiyaye, yanzu kina isa gida ki fara neman mai kudin hayar ki bashi hakuri ki bashi kudinsa, kin ga idan ya dawo zai rage jin zafin tun da kin biya kudin hayar” “Haka zan yi Inshallah na gode sosai kawata” “Allah dai ya bar mu tare” “Ameen” A inda ta faka motarta dazun ta sake tsayawa, ta ciro kudin ta bata sannan sukai sallama, Baturiya ta fita ita kuma ta juya ta hau titi. FARUQ POV. Kamin ya isa gida sai da ya kira abokinsa Nura ya fada masa yadda sukai da abun da ya samu kana yai masa godiya. Ya isa gida cikin farinciki, ba zai ce be taba rika 100k ba amman ba kasafai ba, rabon daya rika 10k tashi ta kanshi ma ya manta. Yana isa ya zare dubu biyu ya bawa Asiya ya ta girka abinci, sannan ya shiga daki ya taba mahaifiyarsa dake zaune tana maida numfashi a hankali. “Mama ya jikin na ki?” “Alhamdulillah, Aisha tace ka zo dazun ina bachi” Ta amsa tana kallon yanayinsa dake bayyana irin farinciki da yake ciki. “Eh na zo na tararda jikin na ki ne sai a hankali...” Ya dora mata da labarin yadda komai ya faru ciki har da abun da Malam Musa ya kira shi yana fada masa Rafi'a ta yi, kamar wanda aka cirewa ciwo sai Mama ta nemi ciwon ta rasa zuciyarta tai fal, daman ciwon nata hawan jini ne na tunanin auren Aisha da kuma yunwar da suke wuni da ita su kwana da ita, abu ga talaka bawan Allah kadan ya ishe shi. “Amman Allah ya saka masa da alheri, Allah ya faranta rayuwarsa ya daummawar da farinciki a cikin zuciyarsa kamar yadda ya faranta ranmu” “Ameen, ni kaina ina tafe a hanya ina ta masa addu'a, Wallahi na jidadi sosai, domin rashin lafiyar nan naki ya dame ni, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi asibiti” “Aa wace asibiti kuma Faruq? Ai ni yanzu na ji sauki, daman ciwon ai na rashin kudin ne” Wata kalar dariya Faruq yai wanda ya manta rabon da yai irinta har ya manta. “Haba Mama saboda ciwon ki fa naje karbo kudin nan, kuma har ga Allah ni asibitin nai niyar kaiki” “Aa ai ciwo kuma ya warke, da aje a kashe kudin a banza ai kara a kara ayi hidima, Idan aka karbi kudin lefe aka rage wani abu cikin nan ai sai a dan kara, in yaso sai ka dauki rabi ka ba mai hayar ka bashi hakuri” “Ai ba za su isa ba, 80k ne muke biya shekara” “Eh ka bashi ko 50k ne dai ka bashi hakuri kamin Allah ya budo mana wata hanyar samu sai ka cika masa” “To Allah ya sa ya yarda, wannan matar ta kira min ruwa, Wallahi na gaji da halin Rafi'a Mama kullum da kalar fitinar da take bullo min da ita, bata da wata magana sai ta na sake ta” “Ka kara hakuri tana maka haka ne saboda tana ganin baka da kudin yin wani auren, da ace ta san kana da kudi da ba zata maka haka ba, koma na rayuwa dan hakuri ne wata rana zaka ga komai ya wuce kamar ba ayi ba” “Allah ya kara min hakurin domin har ga Allah ta kai kulu, ba wai zan sake ta ba ne bana son shiga hakkinta ne” “Yanzu dai tashi ka tafi gurin sana'arka in yaso gobe sai ka samu mai hayar na san zuwa lokacin ya huce sai ka ba shi hakuri ka bashi dubu hansin din, Allah ya warwareka yai maka albarka, zuwa da yamma zan tafi gidan Kanen mahaifinku na fada masa yayi ya aiko da kudin lefen sai a hada da dan abun da aka samu” “Toh Allah ya taimaka ni zan tafi” “Ka dai baro mata abinci ko?” “Eh akwai Taliya da wake, da cefane, idan na koma anjima zan siya mana abinci ina son na cire 5k a ciki” “To Allah ya taimaka yai maka albarka” “Amin Mama Allah kara miki lafiya” Ya fada yana mikewa tsaye sai ta bishi da kallo ina na uwa da da tana jin kaunarsa na karuwa a ranta, ta fi kowa sanin cewar idan Faruq yana da mafita da tuni ya share mata hawayenta. Kudin ya ciro ya cire 50 na mai haya sannan ya cire 5k ya mika mata 43k da suka yi saura, sannan ya fito ya nufi gurin aikinsa. A hanyarsa ta tafiya ya saye waina sannan ya karasa shagon daman yana da plate da spoon da dan copinsa a shagon bayan ya bude ya wanke plate din sannan ya zuba wainar ya ci, ya siyo ruwa ya sha, tukuna ya hau gyaran shagon kamar yadda ya saba. Be tashi ba sai 7:30 daman haka yake tashi kamin ya isa gida 8 tayi sai ya tsaya yai sallah a massallacin unguwarsu sannan ya shiga gida. A duk lokacin da zai shiga gida da tunani da fargabar abun da Baturiya zata masa, amman a yau haushin shiga gidan ma yake ji, har be san ta inda zai fara mata ba idan ya shiga. Kamar kullum sai da ya tsaya yai sallah, sannan ya biya gurin mai siyar da balangon unguwarsu ya siye na dubu daya, ya biya shago ya siye shimkafa da sauran kayan masarufi sannan ya nufi gidansa. Yayi mamakin ganin kofar gidan a bude domin bata saba barin kofar a bude ba, rufewa take wai a cewarta masu kudi ma basa barin gida bude sai takawa, hakan yasa duk wanda ya zo sai ya kwankwasa mata sannan ta bude. Sai dai yau kofar a bude ya same ta, sai ya shiga rike da ledodin a hannu nan ma sai ya samu kofar falon a bude, be yi sallama ba ya shiga saboda ransa a bace yake. Sultan kadai ya samu a falon zaune yana shan bobo, Sultan na ganin mahaifinsa ya sauko daga saman kujerar da sauri ya nufe shi. “Daddy sannu da zuwa” Sai da ya aje ledodin hannunsa sannan ya dauki Sultan yana murmushi. “Sultan ya keke?” “Lafiya” “Me kake sha?” “Bobo Momy ta siya min Bobo” Jimmm Faruq yai sannan ya sauke dansa ya bude masa ledar naman daya siyo ya aje masa a gabansa. “Zauna ka ci” “To” Ya zauna da sauri ya fara ci yana ta murna. “Momy ma ta siya min kifi dazun” Faruq be sake ce masa komai ba ya nufi kofar dakin tana tabawa ya ji a rufe, sai ya juyo ya kalli dansa. “Sultan ina mamanka?” “Tana ciki” Kwankwasa kofar ya fara yi. “Rafi'a ki bude kofar nan” Sai ta amsa masa daga can ciki. “Wallahi ba zan bude ba, ai na san dokana zaka yi” “Kin san abun da kika yi kenan?” “Eh mana, haka kawai muna fama da talauci zai zo ya kara mana da wata damuwar kudin haya shiyasa na karbi number sa na zage shi ai” “To kin jawa kanki ya bamu kwana daya mu tashi mu bar masa gidansa, Rafi'a mi yake damunki ne wai? Miyasa ke baki son zaman lafiya? Duk wani abu da zai tayar min da hankali shi kawai kike nema” “Ai na bashi 100k yau, na biya shi kudinshi kuma ya bada takardar ya yarda mu zauna” Natsuwa yake kokarin yi wai ko zai fahimci inda kalamanta suka dosa, ta bashi kudi haya? “Rafi'a” Ya kiranta a hankali, sai ta amsa daga jikin kofar da take, rike da sabuwar wayarta. “Na'am” “Maimaita abun da kika fada min” “Na ce na bashi kudin hayar har na kara masa da 20k sama” “Ina kika samu kudi?” “Yaya ne ya ba ni Umma ta cika min sauran” “Bude kofar nan mu yi magana” “Ba fa zan bude ba, tufafin ka nan a falo na fitar maka, kuma abinci ka yana nan kusa da kujera, kai da Sultan ku kwana a falo ba zan bude ba” Ba dukan abun da tai kawai take tsoro ba, har da na sabuwar wayar data siya da kuma kudin data biya hayar domin ta san abu ne mai wahala ya yarda da ita. “Ki bude kofar nan Rafi'a ba zan dake ki ba, na taba dukanki ne? Duka ai ba halina ba ne ina son nai magana ta fahimta da ke” Shiru tai masa kamar bata gurin. “Na samu 100k yau” “Da gaske? Ko dai dan na bude ne” “Wallahi da gaske ne, Rafi'a i need to talk to you seriously ki bude kofar nan ko kuma na tafi na barki ki kwana a gidan ke kadai...” “Wallahi Faruq dukana zaka yi idan na bude ni na san abun da na yi, duk abun da na yi ai dai ina sonka ka san dai ina sonka, bakin talaucin nan ne bana so, saboda farar kafa ce da kai Faruq, aurenka be karbe ni ba, da yanzu na yi arziki” Ta fada da muryar dake nuna tana daf fashewa da kuka. Murmushi jin yadda ta juya abun zuwa kansa, wato shi ne mai farar kafa ba ita ba. “Na ji bude mu yi magana” Ta dade tana tunani sannan ta nufi karkashin filonta ta saka wayar, ta nufo kofar ta bude cike da tsiro sannan tai baya ta haye saman gado, shi kuma ya shigo cikin dakin yana kallonta, yana bude baki yai magana sai wayarta tai ringing, yanayin yadda ta razana kadai ya isa ya nuna bata da gaskiya, saurin nufar inda wayar take ta yi ta dauka ta kashe ta gaba daya. “IPhone? Ina kika samu IPhone Rafi'a?” Ta yi shiru sai kallonsa take. Shi ma kallon tsoro yake mata domin lamarinta a yanzu ya fara bashi tsoro ta fara wuce tunaninsa. “Ko yaya ya siya miki?” Nan ma shiru tai, at first ya fusata sai dai a yanzu kwakwalwarsa cike take da tunani kala kala. Karasa yai kusa da gadon ya zauna gabansa n mugun faduwa, yana ta kokarin ganin ya kawarta yaye yayen da zuciyarsa take son masa akan Rafi'a. Zaunawa yai bakin gadon yana kallonta. “Rafi'a ki saka tsoron Allah a ranki, ina son ki san cewa duk abun da aka samu a duniyar nan a nan ake barinsa, ba a zuwa lahira da komai sai aiki da mutum ya aikata, Rafi'a dan Allah ki zama mai tunani ki duba future din Sulta da abun da yake cikinki, na san ni talaka ne ba zan iya miki komai yadda kike so ba, amman da ki je ki aikata wani mummunan abu da aurena kuma kina uwar yayana kara na sauwake miki ki auri mai kudi idan har hakan zai kawo miki mafita” Yana maganar idonsa ya cika da hawaye, domin har ga Allah be fatar matarsa ta aikata abun da zuciyarsa take raya masa. “Ina son ki Rafi'a amman Wallahi zan iya sauwake miki saboda yayana da aurena” “Ni fa ba iskanci na yi ba, Wallahi ban taba iskanci ba” Ta fada tana soshe soshe kamar mai kuraje. “To ina kika samu wannan kudin da wannan wayar?” “Yaya” “Kin yarda na tambaye shi?” “Eh na yarda” Ido ya kura mata domin ya san karya take, yayanta yana da rufi asiri amman ba zai iya siya mata iPhone ba, duk be san ko wace irin iPhone bace amman ya san tana da tsada tun daga yanayin wayar da kuma yadda yake ganinta ga yan mata. Kasa yai da kansa ya lumshe ido be isa yace ba zata rika wayar ba tun da har ta danganta cewar yayanta ne ya siya mata, ya san idan ya hana mahaifiyarta zata saka baki ko kuma tace zata yi fushi ta tafi gida, ko ma suce ya rabu da ita. “Ina da ciki idan ka dake ni ka daki cikinka” Dagowa yai ya kalleta. “Saboda ban da kudi shi ya baki damar yin duk abun da kike so?” “To Faruq kai ma kasan ni ba ajin ka bace amman...” “Haka ne...” Ya fada sannan ya mike tsaye. “Bari ki sauke abun da yake cikinki, labarin rayuwarki da tawa zai canja komai zai zo karshe” “Da gaske?” Ta tambaya cikin farinciki har ga Allah babu abun da take so kamar Faruq ya sake ta ta auri mai kudi, tana sonsa kan amman tafi son ta tafi inda zata huta. Kallonta kawai ya dauke kai ya fice daga dakin, falo ya dawo ya zauna yana kallon dansa cike da damuwa. “Dady ba zaka ci ba?” “Aa Sultan ci ka ragewa Momynka” Ya fada yana shafa kansa cike da so da kauna, haihuwar da Allah ya bashi kadai ya san wani babban arziki ne. 15 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* AMINATU POV. Daga jiya zuwa yau da aka canja mata daki sai ta ci kadaicin ya karu, domin a can tana jin hayaniyar mutune a wannan dakin komai babu kowa sai ita kadai, sai duk ta ji tana kewar gidansu da rayuwarta ta baya. Bata san dalilin daya saka aka canja mata daki ba, bata san ranar da wani zai zo nemanta ba, bata san ranar da rayuwarta zata koma daidai ba, har yanzu ji take kamar komai mafarki ne. Tana fara tunanin ta ji wani irin tsoro ya taso mata, sai ta ji wani abu yana mata yawo a cikin kai karar bindigogi ya dawo mata hayaniyar mutane da rokon da Baba yake musu ya dawo mata kamar lokacin yake faruwa. Wani irin abu ta rika ji kamar kanta ba zai iya dauka ba, gashi tana son ta yunkura ta sauka saman gadon amman dama domin kafafuwanta basa iya komai a yanzu, bakinta ma ya dantse gam duk yadda ta so tai ihu ko kuka sai ta kasa. Ji tai bata bukatar komai a lokacin sai tafiyar da babu dawowa. Da wani irin karfi ta tashi zaune ta fisgi robar ruwan dake hannunta wanda hakan ya bawa jini hanyar fita ya fara zuba, jiki na rawa ta fisgo robar da karfin da bata taba sanin tana da shi ba sai karfen ya fado gefen gadon, bata tsaya komai ba ta hada robar a wuyanta tana kokarin aika kanta da kanta inda take ganin kamar idan ta tafi ta huta da komai. Wannan karon ta samu sukunin bude baki, sai dai ko kadan hakan be bawa muryarta damar fita ba, hawaye kawai take babu kakautawa tana ta yaki da numfashinta, kamar an zare mata lakka haka ta ji wani abu ya sauko mata wanda ya zare duk wani sauran kuzari dake jikinta. Tun tana kallon kofa tana numfashi a hankali har numfashin nata ya fara nisa ta komai ya fara mata dishe dishe alamar ta fara ban kwana da duniya, ga jinin hannunta sai zuba yake. TALBA POV. As usual every weekend a falon Momy ko Daddy ake karyawa tare da kowa ciki har da Daddy da matarsa, sai dai mafi akasiri an fi cin abincin safe a bangaren Momy, Daddy zai zo bangarenta aci tare da shi, idan an gama ko kamin a fara duk wani mai wata bukata zai gabatar masa. Sai dai wannan karon a bangaren Daddy Momy ta saka masu aikinta su kai komai wanda hakan ke nuna cewar a bangarensa za a karya. Duk abun da ake Talba na zaune dinning yana lasa wayarsa, be dago ba har sai da ya ji saukowa Momy, sannan ya dago ya kalleta. “Momy ina kwana?” “Lafiya kalau an tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ya amsa yana tashi tsaye sai da ya bar dinning din ta kira shi. “Talba” Juyowa yai ba tare daya amsa ba. “Ka yi hakuri da abun da ya faru jiya, raina ne ya bace” “Babu komai Momy, ke ai uwata ce Wallahi ban rike ki da komai a rai ba” Wannan maganar da yai sai ya saka Momy ta dan ji nauyinsa, kasa hada ido tai da shi har ya juya ya fice daga falon. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa a bude ya samu kofar shiga falon, hakan yasa be yi sallama ba kamar yadda ya saba ya nufi gurin da suke karyawa. Leila kadai ya samu zaune a dinning din ta saka plantain a gaba tana ci, tana sanye da wani jan yadi kanta sanye da bakar hula, fuskarta ta ji hoda sosai sai dan janbakin data shafa, ta yi kyau sosai abu ne mai wahala mace ma tai mata kallo daya ta dauke ido balle kuma namiji. Talba yaja kujerar dake facing dinta ya zauna yana kallonta, shi kansa ya san ta yi kyau, sai dai ba al'adarsa bace fadawa mutum cewar yayi kyau ko yana da kyau, musamman mace, no matter yadda take da kyau ba zai taba iya bude baki ya furta cewar ta yi kyau ba, kuma ba zai zake da yawa gurin kallo ba gudun kar a ankara da shi. Dauke idonsa yai bayan ya zauna, sai a lokacin ya tuna cewar yau be tura mata sakon barka da safiya ba, kuma ba zai iya tura mata a yanzu ba gudun kar tace saboda ta yi kyau ne. Gaba daya ya tattara hankalinsa ya maida gurin wayarsa, sai yai kamar be san da zaman Leila a gurin ba, ita kam daman gaisuwa ba halinta ba ne bata saba gaishe da mutane ba bayan Momy da Daddy, balle kuma shi duk kuwa da irin sanin da tai na son a girmama da yake, sai dai ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa duk kuwa da irin bugawar da zuciyarsa take after every blink. Har ga Allah bata iya fadar irin son da take yi ma Talba, da ace ta dauki biro da zayyano irin kaunar da take masa da alkalumman rubutu da takardun duniya sun kare bata gama rubuta irin kaunar da take masa ba. Sai dai har yanzu ta rasa gane manufarta a kanta, miyasa ba zai dauki rayuwa da sauki ba? Ya sauko da kai su yi soyayya kamar sauran masoya? Har yaushe zata yi ta jiran ya canja rayuwarsa? Anya ma zai canja din? Bata raba dayan biyu ba ta ji yana amsa waya, bata iya fadar cewar kiransa akai ba ko kuma shi ya kira domin wayarsa a silent take. “Yeah ni ma na kwana da yarinyar nan a raina” Furucinsa ne yasa ta kara tattara hankalinta tana saurarensa. “Okay” Shine last abun da ya fada sannan ya sauke wayar, ya daga kansa yana kallo Amal data nufo inda suke sanye da riga da wando yan patistan. “Good morning Ya Talba” “Morning Little Sis” Ya amsa yana aikawa PA sa sakon kar ta kwana. ‘Ka yi magana da wannan number zai fada maka ko nawa yake bukata sai ka tura masa’ Aje wayar yai bayan ya aika sakon. Leila bata fahimci komai a wayar ba, sai dai ta fahimci da Ali yake magana domin yanayin yadda ya amsa wayar ya tabbatar mata da hakan. Sai da kalmar da ita na kauna a raina ya fi tsaya mata a rai. “Wace yarinya ce?” Ta tambayi kanta tana kallonsa, a take ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi, har sai da numfashinta yai sama, da sauri ta dauki cup din dake saman teburin ta zuba ruwan sanyi ta sha, sannan ta mike tsaye ta fice daga gurin zuwa karamin falon Daddy. Zaunawa tai tana haki, ji take kamar taje ta tambaye shi wace yarinya ce sai dai ba wannan damar domin ba ya hira da ita, da ma dai Amal ce ita kam har sirri yake da ita. “Wace yarinya ce Talba zai kwana da ita a ransa? Ban gane ya kwana da ita a ransa ba, as how?” Wannan karon a fili tai tambayar tana hade yawun bakinta, sai kuma ta mike tsaye. “Ko dai yayi ne dan na ji haushi? Amman kuma be taba min haka ba” Ta dafa kanta tana jin kirjinta kamar zai rabe biyu, ita kamta da akai musu baiko bata tana jin yace ya kwana da ita a rai ba sai wata? Wacece ma? Ba kasafai yake saka mutane a rai ba balle har ya kwana da su amman yace da yarinyar na kwana a raina. Haka ta sake sake a ranta, wani irin zafi ta ji zuciyarta na mata, irin zafin da bata tana jin irinsa ba, wata kila sabida bata tana jin Talba yana maganar wata mace a gabanta ba, hasali ma ba zata ce ga wata mace da yake so ko take burge shi ba, ko akwai be tana nunawa ba balle har ya fada. “What if wani abun bacin rai tai masa?” Ta sake tambayar kanta tana cire hular kanta, sam bata taba sanin wani abu wai shi kishi ba sai yanzu, domin Talba be taba yin maganar wata mace a kusa da ita ba, shiyasa kullum hankalinta a kwance yake bata da haufin komai, sai dai a yanzu tana jinta a cikin wani irin yanayi marar misaltuwa saboda ya furta ya kwana da wata a ransa. “Ko dai bata masa rai tai, ai be kamata ya kwana da ita a ransa ba, Indai har macece ko yaya ne be kamata Talba ya kwana da ita a ransa ba” Ta fada tana wasa da wayar hannunta, can kuma ta busar da iskar bakinta ta shiga contact dinta ta nemi number Ali ta kira shi. Kara wayar tai a kunne ta fara safa da marwa, kamin yai picking har ta matsu. “Hello Leila” “Ali ya weekend?” “Alhamdulillah” “Am akan maganar da kuke da Talba ne yanzu” “Okay...” Yayi shiru yana jiran yaji abun da zata ce, sai ta rasa ta inda zata fara ta san duk irin wayon da zata yi ba zai taba fada mata sirrinsa da Talba ba, sai dai idan ba sirri ba ne. “Ban fahimci abun da kuke magana akai ba, kuma na ga kamar ransa a bace” “Leila” “Na'am” “You should feel free to ask when ever kika ga Talba a damuwa ko matsala, shi ne fa mijin da zaki aura a tare zaku gina rayuwa idan kuna irin wannan zaman rayuwarku ba zata taba yin dadi ba” “Na sani, amman ka san halin abunka, zan iya tambayarsa ya ki fada min ni kuma na damu ne kawai” “Ki saka a rayuwarki ba ki da wanda yafi Talba, idan har kin damu da damuwarsa ya kamata ki tambaye shi” “Zan yi haka, amman for now ina jin akan wata yarinya ce da na nuna masa jiya tana bukatar taimako, yar gudun hijira ce” Shiru tai kamar mai tunani. “Subhanallahi, tana ina yanzu?” “Asibitin mu” “Okay Allah ya bata lafiya, amman idan ana bukatar taimako Ali kai na gida ne, ka san yadda komai a Foundation din mu yake, ba sai ka sake yi masa magana ba, domin ba zan taba lamunta Talba ya kwana da tausayin wata a ransa ba, an yi na farko kuma na karshe, bana son ya kwana da kowa a cikin ransa sai ni” “Ameen” Ya amsa addu'ar da tai a farko yana murmushi, sannan ya aje wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba domin ya san kishi ne. Sai ta sauke ajiyar zuciya tana dan jin sauki a ranta. “Ranki ya dade, Hajiya ta ce a kira ki” Ta juyo da sauri ta kalli Mairo, sai kuma ta rufe da masifa domin ba karamin razana ta tai ba. “Wai miyasa komai ba ku iya yinsa a cikin natsuwa ne? Mi yake damunku ne? Wannan ya zama na karshe da zaki sake kira sunana da karfi I'm not your mate” Ta karasa tana jan tsaki sannan ta nufi hanyar shiga babban falon, bata ko tsaya kula Mairo b dake aikin bata hakuri. Ko da ta isa dinning din kowa ya hallara har sun fara cin abinci. “Ina kika je?” Momy ta tambaya tana kallonta. “Waya na amsa” Ta fada sannan taja kujera ta zauna tana mikawa Daddy gaisuwa. Sai da suka nisa da cin abincin sannan Daddy yai gyaran murya ya ce. “Ina son na yi wata magana mai muhimmanci, Shiyasa na bukaci a shirya mana abun karyawa a nan, musamman mahaifiyarku” Jin hakan tasa kowa ya kalleshi har Momy. “Allah yasa ba laifi na yi ba” “Laifi kika yi kuma babba, laifin da ban saka ran zaki yi ba a matsayinki na uwa, sam ban tsammaci haka daga gareki ba, ban yi zaton rana zata zo da zaki dubi dana ki fada masa cewar ba ke kika haife shi ba...” Talba ya tsaya da cin abinci ya dago ya kalli Daddy dake maganar cikin tsananin bacin rai, Momy kuma tana kallon Talba a tunaninta shi ya fadawa Daddy abun da ya faru. “Again?” Momy ta tambaya tana cigana da kallon Talba rai a bace. “Ba shi ya fada min ba wacan karon ma ba shi ya fada min ba...” Kamin Daddy ya karasa Amal ya karba tana kallon Kabir. “Ni na fadawa Daddy, ni kuma Ya Kabir ne ya fada min” Momy ta kalli Amal kamin ta kalli Kabir. “Na ji na yi laifi amman Amal bata fada maka danka yana wuce gona da iri ba?” Da wani irin karfi da fusata Daddy ya daki teburin cin abinci. “Da na be yi komai ba Amina... Wannan dalilin ne yasa na tara ku duka anan, saboda Leila ba zan yarda ki rika batawa Mu'azz rai ba, ko da rana daya bana jin ya taba miki wani abu da zai banban taki da uwar data haife shi, akan me zaki zabi raba kan yarana? Ko bana da rai shi zai yanke hukunci a gidan nan kuma shi zai dauki dawainiyar komai, na tara ku a nan ne saboda na ja miki kunne kuma. Yaranki su daina kokarin wuce guri ko da mafarki ban tsammaci zaki iya furta kalaman da kika furtawa dana ba, saboda abun da Amal ta fada min jiya ban samu bachi da kyau ba, ko kadan bana son abun da zai raba kan yayana kuma bana fatan Allah ya nuna min ranar da Talba zai ji bakincikin rashin uwa” Yana kawai nan ya mike tsaye a fusace ya nufi dakinsa, kowa shan jinin jikinsa yai har Talba din da Daddy yake masifa saboda shi, domin ya san indai akansa ne tsab Daddy zai iya fushi da shi ko yai masa fada. Amal ma tashi tai da sauri ta bi bayan Daddy, domin ta san sakamakonta gurin Momy. Momy da hawaye ke sauko mata ta kalli Talba tace. “Mutum baya kuskure ne? Ni kaina na ji cewar ban kyauta ba, na ji cewar be kamata na furta kalaman nan ba” Talba yayi saurin girgiza mata kai. “Haba Momy kamar baki san halin Daddy ba? Yanzu zai hau kuma yanzu zai sauko, be kamata wannan ya dame ki ba, kin mu sanin Daddy fa, muma a tare muka bude ido muka ganku please ki yi hakuri dan Allah” “Ka yi hakuri kai ma, ban kyauta ba na sani, Allah ya muku albarka” Ameen. Duk suka amsa har Leila sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar bedroom din Daddy, hakan yasa Leila ma ta tashi ta nufi hanyar fita daga part din gaba daya. “Daddy's Boy?” Kabir ya fada yana kallon Talba, sai Talba yai murmushi kadan. “Har yanzu Daddy be yarda na girma ba, yana ganina kamar jariri” “Maybe sai ka yi aure ka haihu ya ga ka fara bawa yayanka kulawa” Ya dan tabe baki kadan. “Ni ma ina son ganin haka, you know i love children alot, but before then ya kamata ka iya bakinka, Amal parrot ce ba komai ake fada mata ba, yanzu kaga abun da taja mana” “Da gangan na fada mata ai, saboda na san zata tseguntawa Daddy, sincerely speaking Momy bata kyauta ba, she shouldn't say that, we're one family be kamata tai haka ba, rai na be taba baci irin jiya ba” Cewar Kabir with serious face. Talba ya dauki tea gabansa ya sha kadan. “You know mata suna da rauni Kabir, kuma tunaninsu gajere ne, shiyasa ba a zure musu kuma ba a kuresu, idan bama dauke kai ga wasu abubuwan zamu yi ta ji da ganin abun da bama so, ya kamata ace muna yafiya da manta kuskure, no body above mistake” “Yeah wani lokacin kuma muna yin abu saboda ya zame mana darasi so that kar mu sake aikata shi nan gaba” Murmushi kawai Talba yai be sake cewa komai ba, ya cigaba da cin abinci har sai da ya koshi sannan ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi kofar fita yana jin wani irin kaunar Daddy, ji yake yafi kowa sa'a a duniyar domin ba kowa ke samu uba kamar yadda shi ya samu nasa ba, kaunar da Daddy yake masa bata misaltuwa shi kansa ya sani. Fitowa yai daga bangaren gaba daya ya nufi bangarensa, yadda ya tsaya yana kallon harabar gidan sai rantse da Allah yau ya fara ganin gidan, sai hankalinsa na can wani gurin daban ya dade a tsaye sannan ya karasa entrance din ya murda kofarsa ya bude. Yana shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin shadda milk color ya saka hula sannan ya saka wallet dinsa da wayarsa aljihu da ya fito rike da makulli mota ya ja kofar. Leila na tsaye jikin window dakinta tana kallonsa da murmushi a fuskarta har ya shiga motarsa ya danna horn aka bude masa ya bar gidan. Sai ya fara biyawa ta shagon da yake siyen sweet da chocolate din da yake zuwa da su gidan marayu sannan ya wuce gidan abokinsa Ali domin a tare suka saba zuwa, wani lokacin Ali zai zo ya dauke shi wani sa'in kuma shi yake zuwa ya dauki Ali kamar dai yau. A bakin gate din gidan ya faka motarsa sannan ya ciro wayarsa ya kira Ali, Ali na yin picking sai ya kashe wayar ya aje. After like 5 minutes Ali ya fito ya bude motar ya shiga, Talba yai reverse sannan suka hau titi. “Ina yara?” “Lafiya Kalau Gwauro” Ali ya amsa masa yana kallonsa fuskarsa da dariya. Talba be sake cewa komai ba har suka kusa isa sannan Ali ya dauko masa zancen Aminatu. “PA ka ya turo kudi dazun Allah ya saka da alheri” Nan ma Talba be ce komai ba, har sai da Ali ya dauko masa zancen kiran da Leila tai masa dazun yana murmushi, sannan ya kalleshi. “Da kai tai waya da safe kenan?” “Yeah kishi take wai ba zata iya daukar ka kwana da wata a rai ba” “And...” Ali ya kalleshi. “And she's right” Tabe baki Talba yai be sake cewa komai ba har suka isa gidan marayun, tun kamin ya karasa harabar yaran suka nufoshi a guje suna murna da zuwansa, murmushi ne ya cika fuskarsa farinciki marayu na daga cikin abun da yake faranta ransa, musamman kananan domin Talba mutum ne mai matukar son yara. Da sauri ya bude motar ya shafa kansa yana tambayar lafiyarsu, sannan ya mika hannunsa ya dauko alawar daya siyo musu ya bude ya fara raba musu. “Uncle ni dai chocolate nake so” Wata yar karamar yarinya ta fada, sai ya amsa mata in a funny way yana dariya kamar ba shi ba. “Noooo chocolate dai anjima idan zan tafi” Ali ya bude dayan side din ya fita yana amsa waya. “Subhanallahi gani nan zuwa” Ya fada sannan ya saka wayar aljihu ya zagayo side din da Talba yake zaune a motar. “Zan barka nan na tafi asibiti” Wani kallo Talba yai masa wanda ke nuna alama ce ta tambayar lafiya. “Wai yarinyar nan aka samu ta suma hannunta nata zubar da jini kuma robar karin ruwa murde a wuyanta kamar an shaketa” Shiru Talba yai fuskarsa da mamaki sannan ya fito cikin motar gaba daya. “You can go with my car” “Thank you” Ali ya fada sannan ya shiga motar da sauri, Talba ya bude baya ya dauko ledar chocolate din sannan ya rufe har lokacin fuskarsa dauke take da mamaki, bin motar yai da kallo har sai da Ali ya fita gate din sannan ya maida dubansa gurin yaran sai dai gaba daya hankalinsa ya tafi akan dalilin da zai saka yarinyar ta aikata haka, he don't even think zata ma iya aikatawa kanta haka sai dai idan wani ne ya kashe ta ko kuma yake kokarin kasheta. Be wani dade sosai kamar yadda ya saba yi ba domin hankalinsa gaba daya ya tafi gurin yarinyar, and baya son azahar tai masa a nan saboda a tare suke cin abincin rana da duka Family kamar yadda suke yi da safe on every weekend sai dai idan akwai wani uzuri. After like 2 hours da wucewar Ali ya turawa direbansa sakon inda yake. Sannan ya bude chocolate din ya shiga raba musu yana Murmushi kamar ba shi ba. Bayan ya gama yai musu bankwana suka rakoshi har gurin da direban ya faka motar, domin ya dade a zaune cikin motar yana jiran Talba. Kamin ya karaso direban ya fito ya bude masa motar bayan ya shiga ya rufe, ya ya zagaya da gudunsa ya shiga driver side ya ja motar suka nufi gida. Tafiyar minti talatin suka iso unguwar shimkafi Quarters, Talba na hakimce cikin motar har direban ya faka motar a kusa da entrance din kofar Momy. Kamar ya bude baki ya ce ma direban ba bangaren Momy zai fara shiga ba, sai kuma ya ji ba zai iya ba, sai da direban ya bude masa motar sannan ya fito ya nufi bangarensa. Yana shiga ya bedroom dinsa ya bude bathroom yai alwala ya fito yana rike da agogon hannunsa, a inda ya saba aje shi ya aje sannan ya nufi inda Capet dinsa ta sallah take shimfide yai ikama ya fara gabatar da sallah nafila. Kamin ya sallame limamin gidansu ya fara kiran sallah hakan yasa yana sallamewa ya fito daga bangarensa ya nufi masallaci gidansu inda dukansu suke sallah da kuma ma'aikatan gidan. Bayan saukowa daga sallah azahar ya nufi bangaren Momy sai kamshi turare yake kamar wanda ya lullube jarkar turaren a jikinsa. Sai da ya danna door bell din sannan kuma yai knocking sai ga Zulai da gudunta ta bude masa. “Sannu da zuwa ranka ya dade” Kai kawai ya daga mata sannan ya nasa kafarsa cikin falon, saman sofa ya zauna yana kallon Plasma dake ta aikinta, babu kowa a falon sai Leila dake zaune a dinning rike da waya, yana shigowa sai duk hankalinta ya tattara ya koma kansa. Be yi minti biyar da zaman ba aka sake danna door bell din, Mairo dake kitchen ta fito da gudu ta nufi kofar ta bude, daman idan ba yan aikin gidan ba ko Kabir sai Amal sune kawai suke iya bude kofa idan ana kwankwasa, Leila tana ganin ta fi karfin haka, Talba kuma jin kai ba zai bar shi ba. “Baaba na nan?” “Ban santa ba gaskiya” Shiru yai yana kallon sabuwar yar aikin domin be taba ganinta ba, duk kuwa ba da yawan zuwa yake gidan ba amman dai akan aikoshi daga kauye gurin Kakarsa Baaba dake aikin gidan, hakan yasa police din dake gadin gidan suka san shi basa hana shi shiga a duk lokacin da ya zo. “To Hajiya fa?” Ya sake tambaya, sai Mairo ta amsa masa. “Eh tana nan wa za a ce mata?” “Ki ce mata Shamsu ne jikan Baaba” “Toh” Ta saki kofar falon dake bude ta nufi hanyar upstairs. Leila a hango shi ta mike tsaye da sauri. “Ki ce masa Baaba bata nan” Ta fada kamar wanda ya rikice. Mairo ta juya da sauri da zimmar fada masa, sai Talba ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. Mikewa yai tsaye ya nufi kofar Leila na ganin haka ta nufi upstairs da gudu. Shamsu na ganin Talba ya dan risina masa yana gaishe shi. “Shamsu” “Na'am ranka ya dade ya gida?” “Alhamdulillah, lafiya dai?” “Lafiya Kalau, daman daga can gida ne suka ce na zo na duba Baaba ko lafiya kwana biyu ba a samun wayarta” Kamar an dasa ice haka Talba ya tsaya jikin kofar yana kallon Shamsu da mugun mamaki, kwakwalwarsa ta cika da tarin tambayoyi, sai ma ya rasa abun da zai ce wa Shamsu. Yawun bakinsa ya hade a hankali yana kallon Shamsu har ya bude baki zai yi masa magana sai ya ji muryar Momy dake saukowa tana kiran sunan Shamsu da far'arta, abun da bata saba yi ma talaka ba musamman wanda yake karkashinta. 16 *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* “Shamsu ne?” “Eh Hajiya ina wuni?” “Lafiya kalau shigo mana” Talba ya juyo tana kallon Momy dake amsa masa da far'arta kamar ba ita ba. Sai kuma ya juya ya kalli Shamsu dake kokarin shigowa. “Baaba ka zo nema...?” Kamin Shamsu ya ce komai Momy ta daka masa tsawa. “Talba ka barshi ya huta ya sha ruwa mana, Mairo akai shi karamin falo a kawo masa ruwa” Momy ta karasa tana kallon mai aikinta Mairo, sai Mairo ta amsa a ladance. “Toh Hajiya” Ta wuce gab Shamsu ya bi bayanta, Momy ta gyara tsayuwarta tana kallon Talba. “Bangaren Mahaifinku zaku yi lunch” Ya gyada mata kai yana bin Shamsu da kallo. “Zulai ta kai komai a can Engineer kai kawai yake jira” Ta fada tana juya wayarta a hannunta, yanayin yadda tai maganar yana nuna masa son take ya bar mata falon. Ya san ba zai iya nufar falon ta ce akai Shamsu ba, idan ma yaje ba zata bari yai magana da shi ba, idan kuma ya ce zai musa mata zata yi korafi. Juyawa yai ya fice daga falon gaba daya zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala, a entrance ya tsaya yana kallon harabar gidan, sai kuma ya nufi gate din ya fice daga gidan gaba daya. Yana fita falon Momy ta rufe kofar da kanta tana sauke ajiyar zuciya. Lumshe ido tai ta bude tana kai hannu ta dafa kirjinta dake mugun bugawa da karfi, sannan ta bar jikin kofar ta nufi karamin falon inda Shamsu yake zaune, yana ganinta sai ya sauka daga kan kujerar ya zauna a kasa abun ka da mutunen kauye akaai girmama mutane. “Shamsu ya gida ya kowa?” Ta tambaya bayan ta zauna. “Lafiya kalau Hajiya” “Maa Shaa Allah, fatar su Baaba ma suna lafiya?” “Eh... Ai ita aka ce na zo na duba, kwana biyu an ta kiran wayarta baya shiga” “Ah ah Subhanallahi, Baaba ai yau kwananta tara ko takwas da tafiya gida” Shamsu ya kalleta da sauri. “Gida Hajiya? Wallahi bata je gida ba” “Subhanallahi Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lallai tabbas ni ma nayi ta kiran wayarta bayan tafiyarta ban samu ba, amman ban saka ran komai ba saboda na san kauye wani lokacin akwai matsalar network ko nepa, kaga ai shiyasa binciken yake da dadi Allah yasa ba mugun hannu ta fada ba, amman ka bincika aka ce bata je ba?” “Wallahi bata je ba, ai idan tana can dole zan sani saboda a gidan nake, kuma bata fada miki dalilinta na zuwa ba” “Eh to gaskiya bata fada min ba, na san dai kamin ta tafi tana dan jin jiki, domin da kaina ma na dauke ta muka je asibiti aka ce zazzabi ne da hawan jini, bayan mun dawo da kwana biyu tace min tana son taje kauye ta ga kowa hankalinta ya koma can a yanzu, ta inda nai kuskure ban tambaye ta me take tunani ba, domin hawan jini baya tasowa haka siddan sai da damuwa ko bakinciki har ma nake cewa ba zata kira ta fada a kauye ba tace bata son ta tashi hankalinsu” Wani kalar tashin hankali ne ya cika Shamsu, jin cewar Baaba bata gidan ga wayarta ma idan an kira ba a samu, Momy kuma ta fada masa cewar yau kwananta tara da tafiya. A gabansa Momy ta nemo number Baaba ta kira ta saka wayar a speaker, daga ita har Shamsu suka ji cewar wayar a kashe take. Shamsu ya mike tsaye “Wallahi haka nima suke ce min idan na kira, su ma can haka suka ce wayar a kashe take, amman yanzu zan kira na fada musu halin da ake ciki” “Gaskiya kam kara a dage da addu'a kuma a saka cigiya, ni ma Inshallah zan bada sanarwa gidan radio ko Allah zai saka a dace” “Zan tafi Hajiya” “To Shamsu bari na baka number na duk yadda kake ciki sai ka kirani” Ta fada tana karanto masa number ya saka sannan ita ma ta mike tsaye. “Bari na kawo maka wani abu ka hau mota” Tsaye a falon cikin tashin hankalin kamin Momy ta kawo masa 5k din har ya matsu domin hankalinsa gaba daya ya koma gurin inda yake tunanin Baaba zata iya zuwa. Ya karbi dubu biyar din data bashi yana godiya ya fice da saurinsa kana ganinsa kasan bayan cikin natsuwa. Har bakin kofar babban falon Momy ta raka shi tana ta masa addu'ar Allah yasa a gane ta ya amsa da Ameen sannan ya fice ta maida kofar ta rufe. Sannan ta hau sama da sauri ta nufi dakin Leila, Momy na turo kofar Leila ta zabura ta mike tsaye da sauri tana hawaye jikinta har rawa yake. “Miye haka? So kike idan ya gani ya fara zargin wani abu” Leila ta kama hannayen Momy ta rike tana kuka. “Momy tsoro nake ji” “Ki daina jin tsoro, babu abun da zai faru, idan kina nuna irin wannan hallayar sai ki tonawa kanki asiri, amman idan kika cire komai a ranki sai ki samu kwanciyar hankali” “Momy har yanzu ina mafarkinta Wallahi, kuma ina jin kamar asirina zai tonu” “Idan ma asirin ki ya tonu sai mu zuba miki ido akaiki gidan yare? Ko ayi miki wani hukunci? Noooo babu abun da zai same ki, je ki kwanke fuskarki ki shafa hoda ki same ni a bangaren Daddynku” Ta gyada kai wasu hawayen na sauko mata. “Momy akwai CCTV a gidan nan, Talba zai iya bincikawa, kuma idan ya gane zai iya cewa ba zai aure ni ba” “No kul bakinki ya daina furta wadannan kalaman, Talba ba shi da mata sai ke, ki kwantarta hankalinki zan saka a cire CCTV cameras din, je ki wanke fuskarki” Ta saki hannayen Momy ta nufi bathroom dinta Momy kuma ta fice daga dakin, tana saukowa ta nufi kofar da zata sadata da part din Daddy. Kamar zai tashi sama haka Shamsu ya nufi gate yana ciro karamar wayarsa ya ciro karamar wayarsa domin kiran yan'uwansa ya sanar musu halin da ake ciki, police din dake gadin gate din ya bude masa ya fita hankali a tashe. Talba dake tsaye wajen gate din ya kalleshi yana karantar irin tashin hankalin da yake ciki. “Ka fito” “Eh ranka ya dade, zan je can gida na fada musu halin da ake ciki” Talba ya masa kamar ya san abun da yake magana akai. “Oh ba su sani ba” “Eh Wallahi shiyasa suka ce na zo na bincika ai, ita ma Hajiya tace tana ta kiran wayar sai ta jita a kashe, Allah yasa dai ba mugun hannu ta fada ba” “Ameen” “Yanzu zanje can na fada musu, Hajiya ma tace yau kwananta tara da tace mata zata je ganin gida, ka ga ita bata san bata isa ba, mu kuma ba su san da zuwanta ba” “Haka ne, Allah ya bayyanata” Shine abun da Talba ya fada zuciyarsa na bugawa kamar zata fasa kirjinsa ta fito saboda bacin rai, zuciyarsa na ta dawo masa da abun da Ali ya fada masa akan halin da aka samu Aminatu. Bayan Shamsu ya amsa da Ameen Talba ya kwankwasa karamar kofar gate din suka bude masa, ya doshi cikin gidan, Momy na shiga bangaren Daddy Talba ya danna door bell din, Mairo ta zo da gudunta ta bude masa, kana ganin yanayinsa kasan ransa a bace yake, kai tsaye ya nufi stairs sai dai kamin ya karasa hawa Leila ta fito fuskarta cike da ruwa ko hodar da Momy ta ce ta shafa bata shafa ba, tana ganin Talba ta hade yawu da karfi ta dauke numfashi na tsawon dakika uku. “Yanzu zan iya sanin abun da kika yi ma Baaba?” A karo na biyu ta sake hade yawu da karfi a tana kallonsa kamar wanda bata fahimci abun da yake magana a kai ba. Ya kara matsowa kusa da ita cikin wani irin bacin rai sai ta koma baya da sauri tana kallon kofar da Momy ta fito. “Lafiya na shiga can ban ganku ba, Daddynku yana jira zamu ci abinci” “Answer me...!!!” Talba ya fada a tsawace yana Kallon Leila. Cikin karfin hali tace. “Ni ban gane abun da kake magana a kai ba” “Miya faru?” Momy ta tambaya daga downstairs din da take tsaye. Sai Leila ta amsa mata. “Tambaya yai wai zan iya sanin abun da ya faru da Baaba” “What? Me kake kokarin cewa Talba?” Talba be kula Momy ba ya kara yin sama ya matsa kusa da Leila. “I hope ba ke kika shakari yarinyar can ba, kike kokarin kasheta, saboda zafin zai zame miki biyu wahalar zata miki yawa...” Hawaye ne ya fara saukowa Leila. “Talba wace irin magana ce wannan? Me kake son fada?” Juyowa yai ya kalli Momy. “Momy kin san me nake magana a kai, I'm not a fool na fahimci komai, and i do hope Leila bata da hannu a kokarin kashe yarinyar nan...!” Yana kawai nan ya sauka a fusace ya fice daga falon gaba daya, Momy ta bishi da kallo, Leila kam ban da hawaye babu abun da take. “Wace yarinya yake magana akai?” Zubewa Leila tai a gurin ta fashe da kuka. “Momy....” Sai kuma ta kasa karasa, Momy ta hau saman da sauri ta rika Leila suka nufi dakinta. TALBA POV. bangarensa ya nufa wayarsa makalle a kunnensa yana ta kiran Ali, sai dai har wayar ta gaji da ringing ta katse Ali be daga ba, zaunawa yai saman kujera ya sake kiran wayar, wannan karon ma Ali be daga ba. Hakan yasa ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa ya fito ya ja motar da karfi, suna ganin ya kunna motar suka bude masa gate. Cikin saurin ya fice daga gidan, yana driving zuciyarsa na raya masa Leila zata iya yin yunkurin kashe yarinyar saboda ta tambayi Ali akan ta, wata kila zata iya zargin wani abu ne a tsakaninsu idan ma bata yi da kanta ba zata iya saka wani yai. Yana isa asibitin ya faka motarsa ya fito ya mufi hanyar da zata sada shi da office din Ali, kamin ya karasa Office din Ali ya fito daga ward din, yayi mamakin ganin Talba sai dai kamin yace komai Talba ya ce. “Ali ya yarinyar take?” “Ba dadi, but she's still alive” Wani deep breath Talba yai sannan ya bude office din suka shiga. “Ya akai abun ya faru?” Ali ya rufe kofar yana fadin. “Nurse Karima dai ta fada min cewar tana shiga dakin ta same ta a sume, robar a zagaye da wuyanta kuma an fisge robar hannunta jini ya zuba, yanzu haka sai da muka saka mata robar jini, daman jinin be isheta ba” Talba ya zauna saman kujera yana dan tunani kaminnya kalli Ali daya kai hannu ya dauki wayarsa yana dubawa. “Ali lokacin da Leila take tambayarka akan yarinyar nan ta tambaye inda take?” “Tace dai wace yarinya ce na fada mata tana asibitin mu” “Ka fada mata number dakin?” Alinya dago ya kalleshi. “No miya faru?” “Ali Leila can do this yarinyar nan bata da zuciya mai kyau....” “Noooooooooooooooo” Ali yayi saurin dakatar da shi yana daga masa hannu, domin maganar ta masa nauyi sosai har sai da ya runtse ido ya bude ya kalleshi. “Look Talba yanzu na fahimci baka son Leila, and it fine, ka ji baka son mutum normal ne amman kokarin dora mata sheri ba zai amfana maka komai ba” “Na san dalilin daya saka na fad....” Talba be kasara Ali ya daka masa tsawa. “Baka da wani dalili, and karka manta Leila yar'uwarka ce ko da babu alakar kauna a tsakaninku be kamata ka jefe ta da wannan ba” “Ali ba zaka gane ba ne, Leila can do this” Talba ya sake maimaitawa with full confidence, abun da ya kara fusata Ali. “Enough Talba, enough. Leila tana da damar da zata yi kishi, ta nuna bakincikinta ko bacin rai akan ka damu da wata, amman for now ka bar Leila ta ji da damuwarka karka kara mata wata” Ali ya fada cikin tsawa jijiyar wuyansa har tashi take. Talba ya mike tsaye yana kallon Ali cikin wani irin zafin nama. “So you're shouting at me...?” “Yes me ke damunka Talba? Why Leila? What if ita tai kokarin kashe kanta? What if kila ta akan wani abu dabam ake kokarin kasheta?” Talba ya matsa kusa da shi yana kallon idonsa. “Don't fool me, haka nan kawai zata yi kokarin kashe kanta saboda bata son kanta? Bayan ta samu ta fito daga daji? And you already told me babu wanda ya taba zuwa ganinta how could someone know tana a nan? Ali Let me tell you this, zan bincike yarinyar nan and if i find out Leila ta aikata abun nan, sai na bata mamaki” “And before you do this let me show you something, daga yau ba zan sake kula yarinyar nan ba, and i swear sai ta bar asibitin nan yau, ba zan zuba maka ido ka bata alakarka da matar da zaka aura ba kuma yar'uwarka saboda wata bare ba, kuma a dalilina ka san yarinyar nan and now na fahimci halin da Leila take ciki akanka” Talba yayi murmushi irin murmushin na bacin rai da mamaki a lokaci daya. “And remember you said yarinyar bata da kowa” “I don't care, idan ma mutuwa zata yi tai mutu, she's not my responsibility...” “And for now on she's my responsibility har sai ta dawo hayyacinta ta fada min komai... And believe me with or without you yarinyar nan zata rayu Doctor Aliyu Muhammad Bukar...” Talba na fadar hakan ya juya ya nufi kofa a mugun fusace, da mugun karfi yake taka kasar kamar zai fasata tsabar bacin rai, rabon da ya samu kansa cikin irin wannan bacin rai har ya manta. Har ya fito daga ward din sai kuma ya juya ya koma ciki, kai tsaye ya nufi gurin da sauran nurses din suke, mostly sun sanshi domin yana yawan zuwa asibitin gurin Ali kuma gashi sanannen mutum kuma dan babban mutum wato Alhaji Mu'azu Shimkafi, sai dai ba zai iya shadar sunansu duka ba musamman a yau da yake weekend ne ba faces din daya sani ba ne a gurin. “Who's Karima a nan?” “Ni ce” Ta amsa tana kallonsa. “Ali ya ce ki dauko yarinyar ki saka a motana zan canja mata asibiti” “Okay” Ta mike tsaye ta kira mutun biyu da za su rika mata ita, a gurin ya tsaya har aka fito da ita suka turota a kujera idonta a rufe. Yana gaba suna Karima na biye da shi wata mai aikin shara da dauko files tana rike da file din Aminatu, suna isa gurin Motar Talba ya bude gidan bayan Nurse din da matar suka rikata suka sakata ciki sannan suka rufe motar. Shi kuma ya karbi file din ya bude side dinsa ya shiga ya aje file din a front seat, hakan kawai ya samu kansa da juyawa ya kalli fuskarta, sai tausayinta ya kara kama shi, abun da Ali ya fada masa akanta ya dawo masa, ga kuma wanda yake tunanin Leila na kokarin kara mata. “Leila...” Ya furta bayan a dauke kansa daga barin kallon Aminatu, yana jin tsanar Leila na kokarin dasuwa a ransa. Key yai ma motar yai reverse, ya kama hanyar ficewa daga asibitin. Wata expensive private hospital ya nufa da ita, yana shiga ya nufi emergency, duk da kasancewar yau weekend ne ya samu ma'aikata da yawa a asibitin saboda private hospital ce da suka san aikinsu, sai dai ba kowa yake iya kai kansa ko wani nasa a can ba, sai ya tsaya da kafafuwansa. Sun karbi Aminatu da gaggauwa da kuma kulawa suka shiga da ita ciki domin bata taimakon da take bukata. Shi kuma ya tsaya daga waje ya ciro wayarsa dake aljihunsa tana ringing, ganin number Daddy yasa shi saurin picking. “Hello Daddy” “Mu'az kana ina? Mun ci abincin rana ba tare da kai ba?” Ya daga jikin motarsa yana kallon harabar asibitin. “Daddy ina asibiti” Sometimes idan yana gurin Ali a asibitin ya kan cewa Daddy yana asibiti, hakan yasa Daddy yai zaton ko yana tare da Ali ne? “An bata maka rai ne? Could we talk?” “No Daddy ina wata magana ne mai muhimmanci, bata shafe ka tsakanina ne da Ali” “Okay” Daddy ya fada sannan ya kashe wayar, Talba ya cikawa bakinsa iska ya busar a hankali yana kallon Nurse din data doso inda yake. “Dan Allah kai ne mijin yarinyar nan? Ko dan'uwanta?” Tsaye Talba yai kamar an dasa shi ya kasa amsa mata. “Tana bukatar jini da gaggauwa” “A ina zamu samu?” “Lab amman for now za mu bincika mu ga ko za'a samu jinin da zai dace da nata” Ya gyada mata kai a hankali cike da natsuwa, sannan ya bi bayanta suka nufi cikin ward din, ita ta nuna masa dakin da suka saka Aminatu. Ita ta fara shiga shi kuma ya bi bayanta ya tsaya jikin kofar yana kallon fuskar Aminatu dake ta bachi kana gani kasan bata san inda take ba. Nurse din ta yi abun da zata yi ta fita Talba yana tsaye jikin kofar idonta akan Aminatu, takawa yai a hankali ya karasa kusa da gadonta still ya kasa kauda idonsa akanta. “You need to survive” Ya furta yana jin kamar ya tashe ta ya tambaye ta waya mata haka, kuma ayi sa'a ta amsa masa cewar Leila ce. Yana tsaye akanta har na kusan mintuna talati, sai ga nurse din ta dawo tare da likitan daya karbi Aminatu a dazun. Sake dubawa yai sannan ya kalli Talba. “Ba mu da kalar jininta a yanzu, sai kaje babbar asibiti ko kuma ka samu wani daga familynta idan zai iya bada jinin” Uffan Talba be ce ba har sai da Likitan ya nufi kofar fita. “Ko zaka iya gwada nawa? O ne” Likitan ya juyo ya kalleshi. “Yes why not amman zamu fara maka test mu tabbatar baka dauke da kowace irin cuta gudun samun matsala” Ya daga masa kai kamar an masa dole, sannan ya bi bayan Nurse din dake nuna masa kofa. “Bismillah Malam” LEILA POV. Wani irin kuka take wanda ita kanta ba zata iya fadar dalinlinta na yin kukan a yanzu ba, na zargin da Talba yake mata ne ko kuma na laifin ne da yake kokarin dora mata? Taya zai zarge da da abun da bata san wanzuwarsa ba? Miyasa ma zai yi maganar wata yarinyar a gabanta? Ko kuma dai tana kukan ne saboda zuwan Shamsu? For now she can't tell, all what she know is dukansu is painful, daga zargin har zuwan Shamsu har zancen yarinyar da Talba yake. “Tun dazun kike ta kukan nan? Haka zaki yi ta yi a gaban mutane ki daure kanki?” Momy ta fada cike da tausayin yarta. “Wai wace yarinya ce ma yake magana akai?” A take ta amsawa Momy hawaye ma sauko matan “Wata ce, wata yar gudun hijira ce” “Yar gudun hijira kuma? Shine har zai zarge ki da kashe ta? Ke kin santa ne?” Ta daga kai tana goge hancinta. “Na santa amman Wallahi ban ma taba ganinta balle har na yai yunkurin kasheta? Miyasa zai zarge ni?” “Ke kika bashi fuska ai! Kina ta son bada kofar da za a zarge ki, koma dai miye ai be kamata yai wannan tunanin ba, and ko da kin aikata be kamata ya sameki kai tsaye da maganar ba!” Momy ta fada a fusace, sannan ta mike tsaye yana wani kashe ido. “Karki fito cin abinci, saboda Daddynku zai tambaye dalilin danuwarki, so ki zauna a nan zan fada masa kanki yana ciwo” Leila ta daga kai, sai Momy ta juya ta fice daga dakin tana mamakin yadda Talba yake son sauyawa. after like 40 minutes da fitar Momy wayar Leila tai ringing, hannu ta kai ta dauka tana duba number Ali dake kiranta, da kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga wayar ta kara a kunnenta tai shiru tana sauraren abun da zai fito daga bakinsa. “Kuka kike yi ko?” Ta daga masa kai kamar yana gabanta, wasu hawayen na sauko mata. Be damu da yaji abun da zata fada ya sauke ajiyar zuciya daga can cikin wayar. “I know na san abun da ya faru, can we talk? Gani a hanyar gidanku akwai maganar da nake son fada miki, please ki daure ki fito zan tsaya a gate” “Okay” Ta amsa masa tana jin wani sabon kuka na taso mata, sannan ta aje wayar ya lumshe ido, fuskar Baaba ce ta fara mata gizo, hakan yasa tai saurin bude idon ta mike tsaye ta nufi gurin windows din dakinta dafe kai wasu hawaye na sauko mata. 16 *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* “Shamsu ne?” “Eh Hajiya ina wuni?” “Lafiya kalau shigo mana” Talba ya juyo tana kallon Momy dake amsa masa da far'arta kamar ba ita ba. Sai kuma ya juya ya kalli Shamsu dake kokarin shigowa. “Baaba ka zo nema...?” Kamin Shamsu ya ce komai Momy ta daka masa tsawa. “Talba ka barshi ya huta ya sha ruwa mana, Mairo akai shi karamin falo a kawo masa ruwa” Momy ta karasa tana kallon mai aikinta Mairo, sai Mairo ta amsa a ladance. “Toh Hajiya” Ta wuce gab Shamsu ya bi bayanta, Momy ta gyara tsayuwarta tana kallon Talba. “Bangaren Mahaifinku zaku yi lunch” Ya gyada mata kai yana bin Shamsu da kallo. “Zulai ta kai komai a can Engineer kai kawai yake jira” Ta fada tana juya wayarta a hannunta, yanayin yadda tai maganar yana nuna masa son take ya bar mata falon. Ya san ba zai iya nufar falon ta ce akai Shamsu ba, idan ma yaje ba zata bari yai magana da shi ba, idan kuma ya ce zai musa mata zata yi korafi. Juyawa yai ya fice daga falon gaba daya zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala, a entrance ya tsaya yana kallon harabar gidan, sai kuma ya nufi gate din ya fice daga gidan gaba daya. Yana fita falon Momy ta rufe kofar da kanta tana sauke ajiyar zuciya. Lumshe ido tai ta bude tana kai hannu ta dafa kirjinta dake mugun bugawa da karfi, sannan ta bar jikin kofar ta nufi karamin falon inda Shamsu yake zaune, yana ganinta sai ya sauka daga kan kujerar ya zauna a kasa abun ka da mutunen kauye akaai girmama mutane. “Shamsu ya gida ya kowa?” Ta tambaya bayan ta zauna. “Lafiya kalau Hajiya” “Maa Shaa Allah, fatar su Baaba ma suna lafiya?” “Eh... Ai ita aka ce na zo na duba, kwana biyu an ta kiran wayarta baya shiga” “Ah ah Subhanallahi, Baaba ai yau kwananta tara ko takwas da tafiya gida” Shamsu ya kalleta da sauri. “Gida Hajiya? Wallahi bata je gida ba” “Subhanallahi Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lallai tabbas ni ma nayi ta kiran wayarta bayan tafiyarta ban samu ba, amman ban saka ran komai ba saboda na san kauye wani lokacin akwai matsalar network ko nepa, kaga ai shiyasa binciken yake da dadi Allah yasa ba mugun hannu ta fada ba, amman ka bincika aka ce bata je ba?” “Wallahi bata je ba, ai idan tana can dole zan sani saboda a gidan nake, kuma bata fada miki dalilinta na zuwa ba” “Eh to gaskiya bata fada min ba, na san dai kamin ta tafi tana dan jin jiki, domin da kaina ma na dauke ta muka je asibiti aka ce zazzabi ne da hawan jini, bayan mun dawo da kwana biyu tace min tana son taje kauye ta ga kowa hankalinta ya koma can a yanzu, ta inda nai kuskure ban tambaye ta me take tunani ba, domin hawan jini baya tasowa haka siddan sai da damuwa ko bakinciki har ma nake cewa ba zata kira ta fada a kauye ba tace bata son ta tashi hankalinsu” Wani kalar tashin hankali ne ya cika Shamsu, jin cewar Baaba bata gidan ga wayarta ma idan an kira ba a samu, Momy kuma ta fada masa cewar yau kwananta tara da tafiya. A gabansa Momy ta nemo number Baaba ta kira ta saka wayar a speaker, daga ita har Shamsu suka ji cewar wayar a kashe take. Shamsu ya mike tsaye “Wallahi haka nima suke ce min idan na kira, su ma can haka suka ce wayar a kashe take, amman yanzu zan kira na fada musu halin da ake ciki” “Gaskiya kam kara a dage da addu'a kuma a saka cigiya, ni ma Inshallah zan bada sanarwa gidan radio ko Allah zai saka a dace” “Zan tafi Hajiya” “To Shamsu bari na baka number na duk yadda kake ciki sai ka kirani” Ta fada tana karanto masa number ya saka sannan ita ma ta mike tsaye. “Bari na kawo maka wani abu ka hau mota” Tsaye a falon cikin tashin hankalin kamin Momy ta kawo masa 5k din har ya matsu domin hankalinsa gaba daya ya koma gurin inda yake tunanin Baaba zata iya zuwa. Ya karbi dubu biyar din data bashi yana godiya ya fice da saurinsa kana ganinsa kasan bayan cikin natsuwa. Har bakin kofar babban falon Momy ta raka shi tana ta masa addu'ar Allah yasa a gane ta ya amsa da Ameen sannan ya fice ta maida kofar ta rufe. Sannan ta hau sama da sauri ta nufi dakin Leila, Momy na turo kofar Leila ta zabura ta mike tsaye da sauri tana hawaye jikinta har rawa yake. “Miye haka? So kike idan ya gani ya fara zargin wani abu” Leila ta kama hannayen Momy ta rike tana kuka. “Momy tsoro nake ji” “Ki daina jin tsoro, babu abun da zai faru, idan kina nuna irin wannan hallayar sai ki tonawa kanki asiri, amman idan kika cire komai a ranki sai ki samu kwanciyar hankali” “Momy har yanzu ina mafarkinta Wallahi, kuma ina jin kamar asirina zai tonu” “Idan ma asirin ki ya tonu sai mu zuba miki ido akaiki gidan yare? Ko ayi miki wani hukunci? Noooo babu abun da zai same ki, je ki kwanke fuskarki ki shafa hoda ki same ni a bangaren Daddynku” Ta gyada kai wasu hawayen na sauko mata. “Momy akwai CCTV a gidan nan, Talba zai iya bincikawa, kuma idan ya gane zai iya cewa ba zai aure ni ba” “No kul bakinki ya daina furta wadannan kalaman, Talba ba shi da mata sai ke, ki kwantarta hankalinki zan saka a cire CCTV cameras din, je ki wanke fuskarki” Ta saki hannayen Momy ta nufi bathroom dinta Momy kuma ta fice daga dakin, tana saukowa ta nufi kofar da zata sadata da part din Daddy. Kamar zai tashi sama haka Shamsu ya nufi gate yana ciro karamar wayarsa ya ciro karamar wayarsa domin kiran yan'uwansa ya sanar musu halin da ake ciki, police din dake gadin gate din ya bude masa ya fita hankali a tashe. Talba dake tsaye wajen gate din ya kalleshi yana karantar irin tashin hankalin da yake ciki. “Ka fito” “Eh ranka ya dade, zan je can gida na fada musu halin da ake ciki” Talba ya masa kamar ya san abun da yake magana akai. “Oh ba su sani ba” “Eh Wallahi shiyasa suka ce na zo na bincika ai, ita ma Hajiya tace tana ta kiran wayar sai ta jita a kashe, Allah yasa dai ba mugun hannu ta fada ba” “Ameen” “Yanzu zanje can na fada musu, Hajiya ma tace yau kwananta tara da tace mata zata je ganin gida, ka ga ita bata san bata isa ba, mu kuma ba su san da zuwanta ba” “Haka ne, Allah ya bayyanata” Shine abun da Talba ya fada zuciyarsa na bugawa kamar zata fasa kirjinsa ta fito saboda bacin rai, zuciyarsa na ta dawo masa da abun da Ali ya fada masa akan halin da aka samu Aminatu. Bayan Shamsu ya amsa da Ameen Talba ya kwankwasa karamar kofar gate din suka bude masa, ya doshi cikin gidan, Momy na shiga bangaren Daddy Talba ya danna door bell din, Mairo ta zo da gudunta ta bude masa, kana ganin yanayinsa kasan ransa a bace yake, kai tsaye ya nufi stairs sai dai kamin ya karasa hawa Leila ta fito fuskarta cike da ruwa ko hodar da Momy ta ce ta shafa bata shafa ba, tana ganin Talba ta hade yawu da karfi ta dauke numfashi na tsawon dakika uku. “Yanzu zan iya sanin abun da kika yi ma Baaba?” A karo na biyu ta sake hade yawu da karfi a tana kallonsa kamar wanda bata fahimci abun da yake magana a kai ba. Ya kara matsowa kusa da ita cikin wani irin bacin rai sai ta koma baya da sauri tana kallon kofar da Momy ta fito. “Lafiya na shiga can ban ganku ba, Daddynku yana jira zamu ci abinci” “Answer me...!!!” Talba ya fada a tsawace yana Kallon Leila. Cikin karfin hali tace. “Ni ban gane abun da kake magana a kai ba” “Miya faru?” Momy ta tambaya daga downstairs din da take tsaye. Sai Leila ta amsa mata. “Tambaya yai wai zan iya sanin abun da ya faru da Baaba” “What? Me kake kokarin cewa Talba?” Talba be kula Momy ba ya kara yin sama ya matsa kusa da Leila. “I hope ba ke kika shakari yarinyar can ba, kike kokarin kasheta, saboda zafin zai zame miki biyu wahalar zata miki yawa...” Hawaye ne ya fara saukowa Leila. “Talba wace irin magana ce wannan? Me kake son fada?” Juyowa yai ya kalli Momy. “Momy kin san me nake magana a kai, I'm not a fool na fahimci komai, and i do hope Leila bata da hannu a kokarin kashe yarinyar nan...!” Yana kawai nan ya sauka a fusace ya fice daga falon gaba daya, Momy ta bishi da kallo, Leila kam ban da hawaye babu abun da take. “Wace yarinya yake magana akai?” Zubewa Leila tai a gurin ta fashe da kuka. “Momy....” Sai kuma ta kasa karasa, Momy ta hau saman da sauri ta rika Leila suka nufi dakinta. TALBA POV. bangarensa ya nufa wayarsa makalle a kunnensa yana ta kiran Ali, sai dai har wayar ta gaji da ringing ta katse Ali be daga ba, zaunawa yai saman kujera ya sake kiran wayar, wannan karon ma Ali be daga ba. Hakan yasa ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa ya fito ya ja motar da karfi, suna ganin ya kunna motar suka bude masa gate. Cikin saurin ya fice daga gidan, yana driving zuciyarsa na raya masa Leila zata iya yin yunkurin kashe yarinyar saboda ta tambayi Ali akan ta, wata kila zata iya zargin wani abu ne a tsakaninsu idan ma bata yi da kanta ba zata iya saka wani yai. Yana isa asibitin ya faka motarsa ya fito ya mufi hanyar da zata sada shi da office din Ali, kamin ya karasa Office din Ali ya fito daga ward din, yayi mamakin ganin Talba sai dai kamin yace komai Talba ya ce. “Ali ya yarinyar take?” “Ba dadi, but she's still alive” Wani deep breath Talba yai sannan ya bude office din suka shiga. “Ya akai abun ya faru?” Ali ya rufe kofar yana fadin. “Nurse Karima dai ta fada min cewar tana shiga dakin ta same ta a sume, robar a zagaye da wuyanta kuma an fisge robar hannunta jini ya zuba, yanzu haka sai da muka saka mata robar jini, daman jinin be isheta ba” Talba ya zauna saman kujera yana dan tunani kaminnya kalli Ali daya kai hannu ya dauki wayarsa yana dubawa. “Ali lokacin da Leila take tambayarka akan yarinyar nan ta tambaye inda take?” “Tace dai wace yarinya ce na fada mata tana asibitin mu” “Ka fada mata number dakin?” Alinya dago ya kalleshi. “No miya faru?” “Ali Leila can do this yarinyar nan bata da zuciya mai kyau....” “Noooooooooooooooo” Ali yayi saurin dakatar da shi yana daga masa hannu, domin maganar ta masa nauyi sosai har sai da ya runtse ido ya bude ya kalleshi. “Look Talba yanzu na fahimci baka son Leila, and it fine, ka ji baka son mutum normal ne amman kokarin dora mata sheri ba zai amfana maka komai ba” “Na san dalilin daya saka na fad....” Talba be kasara Ali ya daka masa tsawa. “Baka da wani dalili, and karka manta Leila yar'uwarka ce ko da babu alakar kauna a tsakaninku be kamata ka jefe ta da wannan ba” “Ali ba zaka gane ba ne, Leila can do this” Talba ya sake maimaitawa with full confidence, abun da ya kara fusata Ali. “Enough Talba, enough. Leila tana da damar da zata yi kishi, ta nuna bakincikinta ko bacin rai akan ka damu da wata, amman for now ka bar Leila ta ji da damuwarka karka kara mata wata” Ali ya fada cikin tsawa jijiyar wuyansa har tashi take. Talba ya mike tsaye yana kallon Ali cikin wani irin zafin nama. “So you're shouting at me...?” “Yes me ke damunka Talba? Why Leila? What if ita tai kokarin kashe kanta? What if kila ta akan wani abu dabam ake kokarin kasheta?” Talba ya matsa kusa da shi yana kallon idonsa. “Don't fool me, haka nan kawai zata yi kokarin kashe kanta saboda bata son kanta? Bayan ta samu ta fito daga daji? And you already told me babu wanda ya taba zuwa ganinta how could someone know tana a nan? Ali Let me tell you this, zan bincike yarinyar nan and if i find out Leila ta aikata abun nan, sai na bata mamaki” “And before you do this let me show you something, daga yau ba zan sake kula yarinyar nan ba, and i swear sai ta bar asibitin nan yau, ba zan zuba maka ido ka bata alakarka da matar da zaka aura ba kuma yar'uwarka saboda wata bare ba, kuma a dalilina ka san yarinyar nan and now na fahimci halin da Leila take ciki akanka” Talba yayi murmushi irin murmushin na bacin rai da mamaki a lokaci daya. “And remember you said yarinyar bata da kowa” “I don't care, idan ma mutuwa zata yi tai mutu, she's not my responsibility...” “And for now on she's my responsibility har sai ta dawo hayyacinta ta fada min komai... And believe me with or without you yarinyar nan zata rayu Doctor Aliyu Muhammad Bukar...” Talba na fadar hakan ya juya ya nufi kofa a mugun fusace, da mugun karfi yake taka kasar kamar zai fasata tsabar bacin rai, rabon da ya samu kansa cikin irin wannan bacin rai har ya manta. Har ya fito daga ward din sai kuma ya juya ya koma ciki, kai tsaye ya nufi gurin da sauran nurses din suke, mostly sun sanshi domin yana yawan zuwa asibitin gurin Ali kuma gashi sanannen mutum kuma dan babban mutum wato Alhaji Mu'azu Shimkafi, sai dai ba zai iya shadar sunansu duka ba musamman a yau da yake weekend ne ba faces din daya sani ba ne a gurin. “Who's Karima a nan?” “Ni ce” Ta amsa tana kallonsa. “Ali ya ce ki dauko yarinyar ki saka a motana zan canja mata asibiti” “Okay” Ta mike tsaye ta kira mutun biyu da za su rika mata ita, a gurin ya tsaya har aka fito da ita suka turota a kujera idonta a rufe. Yana gaba suna Karima na biye da shi wata mai aikin shara da dauko files tana rike da file din Aminatu, suna isa gurin Motar Talba ya bude gidan bayan Nurse din da matar suka rikata suka sakata ciki sannan suka rufe motar. Shi kuma ya karbi file din ya bude side dinsa ya shiga ya aje file din a front seat, hakan kawai ya samu kansa da juyawa ya kalli fuskarta, sai tausayinta ya kara kama shi, abun da Ali ya fada masa akanta ya dawo masa, ga kuma wanda yake tunanin Leila na kokarin kara mata. “Leila...” Ya furta bayan a dauke kansa daga barin kallon Aminatu, yana jin tsanar Leila na kokarin dasuwa a ransa. Key yai ma motar yai reverse, ya kama hanyar ficewa daga asibitin. Wata expensive private hospital ya nufa da ita, yana shiga ya nufi emergency, duk da kasancewar yau weekend ne ya samu ma'aikata da yawa a asibitin saboda private hospital ce da suka san aikinsu, sai dai ba kowa yake iya kai kansa ko wani nasa a can ba, sai ya tsaya da kafafuwansa. Sun karbi Aminatu da gaggauwa da kuma kulawa suka shiga da ita ciki domin bata taimakon da take bukata. Shi kuma ya tsaya daga waje ya ciro wayarsa dake aljihunsa tana ringing, ganin number Daddy yasa shi saurin picking. “Hello Daddy” “Mu'az kana ina? Mun ci abincin rana ba tare da kai ba?” Ya daga jikin motarsa yana kallon harabar asibitin. “Daddy ina asibiti” Sometimes idan yana gurin Ali a asibitin ya kan cewa Daddy yana asibiti, hakan yasa Daddy yai zaton ko yana tare da Ali ne? “An bata maka rai ne? Could we talk?” “No Daddy ina wata magana ne mai muhimmanci, bata shafe ka tsakanina ne da Ali” “Okay” Daddy ya fada sannan ya kashe wayar, Talba ya cikawa bakinsa iska ya busar a hankali yana kallon Nurse din data doso inda yake. “Dan Allah kai ne mijin yarinyar nan? Ko dan'uwanta?” Tsaye Talba yai kamar an dasa shi ya kasa amsa mata. “Tana bukatar jini da gaggauwa” “A ina zamu samu?” “Lab amman for now za mu bincika mu ga ko za'a samu jinin da zai dace da nata” Ya gyada mata kai a hankali cike da natsuwa, sannan ya bi bayanta suka nufi cikin ward din, ita ta nuna masa dakin da suka saka Aminatu. Ita ta fara shiga shi kuma ya bi bayanta ya tsaya jikin kofar yana kallon fuskar Aminatu dake ta bachi kana gani kasan bata san inda take ba. Nurse din ta yi abun da zata yi ta fita Talba yana tsaye jikin kofar idonta akan Aminatu, takawa yai a hankali ya karasa kusa da gadonta still ya kasa kauda idonsa akanta. “You need to survive” Ya furta yana jin kamar ya tashe ta ya tambaye ta waya mata haka, kuma ayi sa'a ta amsa masa cewar Leila ce. Yana tsaye akanta har na kusan mintuna talati, sai ga nurse din ta dawo tare da likitan daya karbi Aminatu a dazun. Sake dubawa yai sannan ya kalli Talba. “Ba mu da kalar jininta a yanzu, sai kaje babbar asibiti ko kuma ka samu wani daga familynta idan zai iya bada jinin” Uffan Talba be ce ba har sai da Likitan ya nufi kofar fita. “Ko zaka iya gwada nawa? O ne” Likitan ya juyo ya kalleshi. “Yes why not amman zamu fara maka test mu tabbatar baka dauke da kowace irin cuta gudun samun matsala” Ya daga masa kai kamar an masa dole, sannan ya bi bayan Nurse din dake nuna masa kofa. “Bismillah Malam” LEILA POV. Wani irin kuka take wanda ita kanta ba zata iya fadar dalinlinta na yin kukan a yanzu ba, na zargin da Talba yake mata ne ko kuma na laifin ne da yake kokarin dora mata? Taya zai zarge da da abun da bata san wanzuwarsa ba? Miyasa ma zai yi maganar wata yarinyar a gabanta? Ko kuma dai tana kukan ne saboda zuwan Shamsu? For now she can't tell, all what she know is dukansu is painful, daga zargin har zuwan Shamsu har zancen yarinyar da Talba yake. “Tun dazun kike ta kukan nan? Haka zaki yi ta yi a gaban mutane ki daure kanki?” Momy ta fada cike da tausayin yarta. “Wai wace yarinya ce ma yake magana akai?” A take ta amsawa Momy hawaye ma sauko matan “Wata ce, wata yar gudun hijira ce” “Yar gudun hijira kuma? Shine har zai zarge ki da kashe ta? Ke kin santa ne?” Ta daga kai tana goge hancinta. “Na santa amman Wallahi ban ma taba ganinta balle har na yai yunkurin kasheta? Miyasa zai zarge ni?” “Ke kika bashi fuska ai! Kina ta son bada kofar da za a zarge ki, koma dai miye ai be kamata yai wannan tunanin ba, and ko da kin aikata be kamata ya sameki kai tsaye da maganar ba!” Momy ta fada a fusace, sannan ta mike tsaye yana wani kashe ido. “Karki fito cin abinci, saboda Daddynku zai tambaye dalilin danuwarki, so ki zauna a nan zan fada masa kanki yana ciwo” Leila ta daga kai, sai Momy ta juya ta fice daga dakin tana mamakin yadda Talba yake son sauyawa. after like 40 minutes da fitar Momy wayar Leila tai ringing, hannu ta kai ta dauka tana duba number Ali dake kiranta, da kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga wayar ta kara a kunnenta tai shiru tana sauraren abun da zai fito daga bakinsa. “Kuka kike yi ko?” Ta daga masa kai kamar yana gabanta, wasu hawayen na sauko mata. Be damu da yaji abun da zata fada ya sauke ajiyar zuciya daga can cikin wayar. “I know na san abun da ya faru, can we talk? Gani a hanyar gidanku akwai maganar da nake son fada miki, please ki daure ki fito zan tsaya a gate” “Okay” Ta amsa masa tana jin wani sabon kuka na taso mata, sannan ta aje wayar ya lumshe ido, fuskar Baaba ce ta fara mata gizo, hakan yasa tai saurin bude idon ta mike tsaye ta nufi gurin windows din dakinta dafe kai wasu hawaye na sauko mata. 17 *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Madina ta jimmm bayan da Leila ta gama labarta mata abun da ya faru, gaba daya sai ta ji jikinta ya mutu. “Yanzu dai ki fita ki ji abun da Ali zai fada miki” “Zan je yanzu” “Ki kwantar da hankalinki komai zai wuce, amman da zaki dauki shawarata da kin fadawa Talba gaskiyar komai, barin kashi a ciki baya maganin yunwa Leila, kuma yanzu zaki yi ta samun rashim fahimta a tsakaninku ne” “Madina wannan sirina ne, Momy ma bata san na fada miki ba, amman na fada miki ne saboda na yarda da ke” “Babu wanda zai taba jin wannan maganar daga gareni Leila, amman ina baki shawara ne akan abun da nake ganin zai zame miki masalaha” “Yanzu dai bari na tafi Ali yana jirana” “Okay” Leila ta aje wayar sannan ta sauka saman gadon ta dauki wani karamin mayafi ta rufe kanta, sannan ta saka talkaminta ta nufi kofar fita idonta a kumbure saboda kukan da ta sha. Ko da ta sauko falon babu kowa, dukansu suna bangaren Daddy, yan aikin Momy kuma Momy bata basu damar zama a falonta hakan yasa idan ba wani aikin zasu ba abu ne mai wahala ka gansu a main house din kullum suna BQ. A hankali ya bude kofar falon ta fita gabanta na faduwa, domin ji take kamar zata yi arba da Talba ne, domin a yanzu bata son ganin fuskarsa, ba dan bacin rai ba sai dan bata da amsar tambayar da zai mata. Tun kamin ta karasa gurin gate din police din ta bude mata karamar kofar ta fice, tana fitowa ta ga motar Ali fake sai ta nufi inda motar take. Ali na zaune cikin motar yana kallonta har ta karaso gaba daya sai ya ji tausayinta ya kama shi, a da can yana bata laifi kamar yadda yake bawa abokinsa sai dai a yanzu ya fahimci abokinsa ne mai matsala ba ita ba. Bude motar tai ta shiga sannan ta rufe ta kalleshi da idonta da suka kumbura. “Ali” Sai da ya sauke wani dogon numfashi sannan ya amsa mata. “Na'am Leila, ya kike?” Tambayar ya take da yai sai ta ji kamar ya tsokano mata kukanta, a take hawaye ya cika idonta. “Ba Kalau ba Ali, ba Kalau ba” “Na sani, abokina yayi rashin tunani, amman ban dauka zai miki magana ba, a thought ya bar abun a ransa ne kawai, sai dai faga lokacin dana kira ki na ji yanayinki, sai tausayinki ya kama ni, and now na fahimci irin halin da kike ciki” Ya karasa yana kai hannu ya ciro tissue ya mika mata, sai ta karba ta share hawayenta. “Sometimes ina kasa fahimtar waye Talba, abokinka yana da wahalar sha'ani Ali, taya wanda zaka aura zai zarge ka da kisa? How? And Why? Saboda na nuna kishina? Talba be dadin zama wani lokacin” “Na sani, amman ban dauka abun zai kaishi haka ba” Cewar Ali yana kallonta gaba daya zuciyarsa ta cika da tausayinta, domin gani yake Talba baya sonta ita ce kawai sonsa ke dawainiya da ita. “And i respect your decision na cewar ba zaki auri Talba ba har sai ya canja” Juyowa tai ta kalleshi da kyau. “Dan Allah zaka fada min abun da ta faru da yarinyar?” A takaice ya labarta mata komai na yadda aka samu yarinyar, sai dai be fada mata cewar Talba ya dauke ta daga asibitin ba, haka ma be fada mata cewar sun samu tsabani ba, domin yana ganin kamar sirrinsa ne da be kamata kowa ya ji ba. “Amman me zai saka wani yai mata haka?” “Ni ma ban sani ba, kuma a iya binciken da na yi wani be shigo ba, so dole dai sai ta farka zata iya fada mana yadda komai ya faru” “Yanzu tana asibitinku?” “No na canja mata asibiti, and i am here to apologize saboda ni na janyo komai, Talba be san yarinyar nan ba, ni na hada shi da ita da neman ya taimaka mata saboda yarinyar tana bukatar taimako, amman ban yi tunanin abun zai zama na rigima haka ba” “Baka da laifi, na san ka yi ne da kyakkyawar niya, be kamata ka bada hakuri ba” Yayi shiru na wani lokacin kamin ya kalleta ya ce. “Amman Leila kin yi wani abun ne da zai saka Talba ya zargeki da taba yarinyar nan?” “Ban yi komai ba, amman kasan a gurin abokinka kullum nice mai laifi, kawai dai na fahimci wani abu... Talba baya so na ni ce kawai na mutu da kaunarsa, wanda yake sonka ba zai maka haka ba, ko da gaske na aikata zai nemi hanyar kare ni ne, ba ya tunkare da wannan laifi mai girma ba, abun akwai ciwo” Ta karasa wasu hawaye masu zafi na sauko mata, har cikin ranta tana fadawa Ali abunda ta fahimta ne akan zamantakewarta da Talba. Ali ya kawar dai yana jin irin tausayinta na kara kamashi. “Ada can na dauka miskilancinsa ne ya saka yake min abun da yake min, amman a yanzu na fahimci kauna ta ce babu abunsa, kawai ya amince ne saboda ba zai iya cewa Daddy a a ba” Ta runtse tana kokarin fashewa da kuka. “Kabir yana da fada min gaskiya amman na kasa ganewa, saboda kaunar Talba ta cika min zuciya amman yanzu na fahimta...” Ali yayi saurin daukar ruwan dake cikin motarsa ya mika mata. “Please sha ruwa” Sai kuma ya dauko tissue ya mika mata. “Ki daina damuwa dan Allah, kukan nan yayi yawa idonki har ya kumbura, me yasa zaki damar kanki akan Namiji?” Sai ta kalleshi hawaye na sauko mata “Talba be taba min haka ba, na gode” Ta fada sannan ta karba ya share hawayenta ta bude ruwan ta sha. “Ki je ki huta, karki saka damuwar komai a ranki komai zai wuce, kin san idan ya fusata yana aikata abubuwa amman zai sauko and ina tabbatar miki zai baki hakuri” Ta dan yi murmushi irin na bakinciki da kuma kin yarda da maganar Ali cewar zai bata hakuri domin ta san waye Talba, sai dai bata ce masa komai ta bude motar ta fita, Ali ya bita da kallo cike da tausayi har ta shige cikin gidan, sannan ya kai hannu ya dauki wayarsa dake carji a jikin motar ya kira Talba, wayar tai ta ringing har ta gaji ta katse be daga ba ya sake kiransa nan ma shiru, haka ya jera masa kusan 4 miss calls a na biyar ya ji wayar a kashe alamar ya gaji da kiran da yake masa kenan kuma ba zai yi picking ba. “Talba....” Ali ya fada yana jin kamar ace yana kusa da shi yai masa dan banzan duka a yau saboda kukan da Leila ta sha akasa. ‘Ina ka kai yarinyar nan?’ Shine sakon daya tura masa sannan yai reverse ya kama hanyar gidansa. TALBA POV. Be dawo gidan ba sai dare, domin bayan an gama diban jininsa sai ya fito asibitin ya koma gidan marayun, daman can yakan je idan yana cikin bacin rai ko damuwa ya wuni a can, sai ya ji damuwar tasa ta ragu saboda yara suna rage masa kewa, and ko ba komai zai ji cewar ba shi ne kadai a damuwa ba, su ma sun rasa iyaye da yan'uwa amman sun zaune a inda Allah ya tsara musu rayuwarsu kuma suna farinciki, balle kuma shi da Allah yai ma ni'imar aje su da ciyarda su, bayan tarin lafiya da ni'imar yan'uwa da kuma ta uba kamar Daddy da Allah yai masa. A can yai sallah magaba a can yai isha'i, be dawo gida ba sai ba tara saura, wunin yau bayan abincin safe be sake saka komai a cikinsa ba sai ruwa. Yana shigowa ya faka motarsa kusa da entrance din Momy sannan ya fito ya nufi kofar falon cikin yanayin da ba zai iya fada ba, kawai misaltawa yake idan har da gaske Momy da Leila suna da hannu a mutuwar Baaba ko batanta ya iyalanta za su ji? Yayanta da jikokinta? And ya ma akai komai ya faru? Idan ma kasheta sukai ina suka kai gawarta. Sau biyu yana danna door bell din sannan Amal ta bude masa kofar. “Ya Talba welcome” Ya amsa mata ta kai fuska ba yabo ba fallasa, sannan ya shigo cikin falon, hakan ta nuna alamar baya cikin walwala. karasa yai kusa da Kabir dake zaune a sofa yana cin tuwon samun miyar gayye ya zauna. Kallo daya yai ma tuwon ya dauke kai domin shi ba ma'aboci cin tuwo ba ne, wayarsa dake aljihu ya ciro ya kunna sai ga sakon Ali ya shigo wayarsa. ‘Ubanta ne kai?’ Shine reply din da yai ma Ali sannan ya aje wayar ya busar da iskar bakinsa.  Kabir ya kalleshi sannan ya kalli Amal dake zaune tana kallonsu dama haka take idan ta lura da ba a zaune kalau, so that ta samu abun tseguntawa Daddy. “Amal je ki yi bachi mana” Kabir ya fada, sai ta make kafada. “Bana jin bachi yanzu” A take ya zare mata ido, hakan ke nuna ba da wasa yake ba, ya saba wasa da ita sosai sai dai a duk lokacin da yake serious magana da ita ta san yanayinsa. Mikewa tai tsaye tana kallon Talba. “Ya sai da safe” Ta murgudawa Kabir baki sai ya kyalkyale da dariya yai mata gwalo. “Daddy's noy could we talk?” Talba ya kalleshi. “Leila ta fada maka ne?” “Nooo Amal dai ta shinshino ta shinshina min” Talba ya dan yi murmushi kadan yana kallon hannunsa. “Na bada jinina yau” Kabir ya duba shi duba na mamaki, ba zai ce ya san dukan abun da Talba yake yi ba, amman be taba jin yace zai bada jininsa ga kowa ba. “Something new...” Talba yayi murmushi. “Yeah.... I feel like..... ” Sai kuma yai shiru kamar mai tunanin abun da zai fada. “I feel honour.. I mean it was a great joy.... to do....something like this” A rarrabe yai maganar and he is very excited, he can't tell why amman yana jin yayi abu mai kyau. “Yeah at least wani zai rayu da jininka, and mutumen nan ba zai taba manta ka idan ya sanka, idan kuma be sanka ba, kai zaka ji cewar wani yana can yana rayuwasa saboda ka taimaka masa da jininsa ko da kuwa siyarwa kai balle kuma ace kyauta ka bada, more especially ace mutumen nan yana cikin yanayi na bukatar jini tsakanin rayuwa da mutuwa...” Talba yayi shiru yana sauraren kalaman Kabir, sai kuma ya soma tuna abun da ya faru a yau. Juyowa yai ya kalli Kabir. “Idan mutum ya suma zai dauke ki awa nawa kamin ya dawo hayyacinsa?” “Is depend on yanayin suman, ko kuma irin kulawar daya samu, but most wadanda tsoro yake saka su suma ko damuwa, ba su cika farkawa da wuri ba kamar wanda rashin lafiya ta saka shi suma, kuma ya danganta da kalar suman da mutum yai” Shiru Talba yai alamar nazari sannan ya sake tambayar Kabir. “Amman me ke saka mutum baya kuka da murya sai hawaye, kuma ba ya magana, baya cin abinci baya ma bude bakin” Kabir ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya dauki ruwa ya sha. “Depression... Damuwa tana saka wannan har fiye ma, tana saka hauka, rashin lafiya and so on, indai har ba wai mutum ya daman can haka aka haife shi ba, daga baya ne ya sauya gaskiya damuwa ce, tana tsoro tana saka mutum ya rika ganin abu yana imagination ko kuma zuciyarsa ta raya masa ya aikata ko ta saka shi hauka ko ya rika abu kamar mai aljannu, tana saka yawan mantuwa ko surutu ba akan abun da ake magana akai ba, you know komai n jikin dan'adam yana da limit din abun da yake iya dauka, so idan abun yai yawa ko yai kadan zaka tarar akwai irin illar da yake haifarwa” Silently Talba ya sauke ajiyar zuciya. “Idan mutum yana son yayi magana da mai irin wannan abu kamar ya tambaye shi wani abu ya zai yi?” “Ya zai yi kuwa? Most important thing is ka yi kokarin cire wannan mutumen a damuwa, idan wani abu yake so ka sama masa, idan tsoron wani abu yake ka nuna masa babu abun da zai same shi kuma zaka bashi kula, ka sake jikim da shi kana bashi kulawa kana nuna masa far'a da walwala kana dauke masa hankali daga damuwar, kai ta kokarin ganin ka faranta masa rai, da haka da haka zaka ga ta saki jiki da kai, ka yi ta cusa kanka kana bata abinci tun bata ci har ta fara ci” “Idan kuma ya ki fa?” “Taki dai... Zata ma ci idan ta ji yunwa, idan ana saka mata maganine a ruwa na abinci ko kuma ana bata ta hanci a daina, as long as zata iya tashi zaune ko ta kwanta bata bukatar irin wannan maganin, a kyaleta ta wuni da yunwa idan ta ji babu komai a cikinta zata karbi abincin idan an bata, da haka zata saba ta rika ci, amman a yanzu ai an hanata jin yunwa ne, kuma ace ana son ta ci abinci?” “But he cant walk fa” “That one is different, maybe damuwar ce ta haifar mata da hakan ko kuma wani matsalar dabam, amman rashin lafiyarta ba zai zama da matsala a cin abincin ta ba, indai ba wai tana kan wani magani da aka dorata ba ne, shi ma kuma sai dai ace ba zata ci wani ba wani zata ci” Talba ya yunkura da zimmar tashi sai Kabir ya kalleshi ya ce. “Ita ce yarinyar?” Da ido Talba yai masa alamar question mark, sai ya karansa tambayarsa. “Yarinyar da kake zargin Leila tana kokarin kashewa?” Talba be ce masa komai ba ya fara tafiya. “And do you really think Leila zata iya wannan abun?” Tsayawa Talba yai ya juyo ya kalli Kabir. “Amal ta baka labarin Baaba?” “No amman Momy ta fada mana yan'uwanta sun zo sun dauke ta right?” “Yes amman dazun nan jikanta ya zo nemanta, so kai tunani akai” A take Kabir ya cika da tsananin mamaki, Talba kuma ya juya ya fice daga falon. Bangarensa ya nufo kamin a karasa ya cire agogon hannunsa, sannan ya kai hannunsa na hagu ya bude kofar ya shiga, tafiya yake kamar baya son taka kasa ya karasa bathroom dinsa ya jefar da wayarsa saman gado, ya cire tufafin jikinsa ya daura tawul. Samun kansa yai da karasawa gaban katon madubin dake dakin wanda ke nuna iya tsayin mutun. Tsaye yai yana kallon kansa kamin ya kai hannu ya shafa kirjinsa zuwa cikinsa sai kuma ya dawo da hannun saitin inda zanen kirjinsa yake yana tabawa. Motsin shigowar mutum da yaji ne yasa shi juyowa da sauri domin ya san ba kasafai ake shigowa bangarensa ba, Momy ba tai musu wannan tarbiyar ba, ta shiga dakin juna barkaita sai dai idan da wani dalilin. Takawa ya fara yi kamin ya isa bakin kofar Bathroom din Leila ta shigo, tsaye tai cak tana kallonsa daga kasa zuwa sama, wani irin bugawa zuciyarta tai da karfi a lokacin da idanuwanta sukai arba da faffandan kirjinsa. Tun da take a rayuwarta bata taba ganin Talba babu riga ba sai yau, duk kuwa da kasancewar a gida daya suka tashi sai dai baya bayyana mata siraicinsa kamar yadda ita bata taba nuna masa nata ba sai dai dan abun da ba a rasa ba, kamar saka damammen kaya ko wando da riga, sai dai rika hannunsa ko taba shi ba wani abu ba ne a gurinta kamar yadda shi ma be dauke shi komai ba. “Ya akai?” Ya tambaya yana kallonta, ba karamin jihadi tai ba na ganin ta daidaita natsuwarta, sai dai hakan be hana numfashinsa yin nisan kiwo ba na tsawon dakiku, ta dauken kai tana kokarin dawo da numfashin a hankali. “Yarinyar ta fada maka wanda yai mata haka?” “Kina da wata maganar ne bayan wannan?” Juyowa tai ta kalleshi. “Ita wannan maganar ba mai muhimmanci ba ce?” “Mai muhimmanci ce a lokacin da ta fada min cewar ke ce ko ba ke ba ce, and kuma idan na gane gaskiyar komai a game da Baaba” “Duka biyun ban aikata ba, miyasa baka yarda da ni ba? And me zai saka ka zarge ni da kisan yarinyar da kai ma basan san ta ba” “She can't walk she can't talk, depression yana damunta, and now idan na gano da hannunki a ciki, i swear ba zan raga miki ba, you have no idea what she's going through” Ta kara matsowa kusa da shi tana kallon idonsa. “I don't care, she can't talk or walk is not my business, ta mutu ko ta rayu be dame ni ba, ina ta fito ina zata je me ya faru da ita duka ba matsala ta ba ce, all what i care is us....we... I mean us... Just us...” Yanayin yadda tai maganar ya bayyana bacin ran dake tare da ita, shi ma kallonta yake ido cikin ido yana kokarin hana zuciyarsa tsanarta. Sai da ta gama yawo da idanuwanta a fuskarsa sannan ta juya ta fice daga dakin a fusace. Tana dawowa dakinta ta dauki wayarta ta kira Madina ta san is late amman tana son ta yi magana da ita mai muhimmanci. “Hello Leila” Madina ta yi picking. “Madina fada yadda ake mantawa da mutum” “Ban gane ba” “So na ke na manta da Talba, na cire shi a raina gaba daya na manta da shi” Wani irin murmushi ne ya kawata fuskar Madina, ta yi saurin aje kofin ruwan dake hannunta. “Amman miyasa?” “Na gaji ba zan iya ba, sai na nuna masa ni din mai tsada ce kuma na nuna masa he is nothing to me” “Shikenan zan zo da safe, wannan maganar ba ta waya ba ce” “Okay ina jiranki” Leila ta katse wayar, sai Madina ta rike wayar tana kallo, rabuwar masoya ba abu ne mai kyau ko dadi ba, sai dai ita ya zo mata a dabam domin ta samu kanta cikin farincikin jin abun da Leila take kokarin aikatawa. BATURIYA POV. Kamar yadda Ramlee tai mata alkawarin kawo mata kayan mata da zata sha a jiya, ta kawo mata su cike kamar wanda zata sara ta kai su wani gurin, ita ma kanta ta yi mamakin tarin hakin mayen da Ramlee ta kawo mata, wanda za a hado da madara ko zuma a sha duka ta siyo mata madarar da zumar, yadda ta ware kudi ta siye mata kayan matan sai ka rantse da Allah yarta ce. Hakan yasa ta bude wardrobe dinta ta saka su ta rufe da makulli, idan zata sha sai ta bude ta debo ta sha ta rufe, ko Sultan bata yarda ya gani ba balle kuma Faruq uban gayya. Bayan ta gama gyara gidan yayi tsab ta dora girkinta da wuri, sannan ta shigo falonta ta dauki wayarta ta kunna data ta fara chat. Zata yi reply wani sako kiran Fahat ya shigo wayarta, da sauri tai picking ta kai wayar a kunnenta. “Hello” “Yan mata ya kike?” “Lafiya kalau, sai marmarinka” “Uhm mmn Marmari kamar gaske, ke da kin ki bari ma na zo mu gaisa, sai kwana kwana kike min” “Ai na fada maka gidamu ba za a bar ni ba, ba a barin mu zance gaskiya” “Amman ai kin yi girman da ya kamata ace ana barinki zance Fee'at” Ta lumshe ido tana jindadin yadda ya kira sunanta, daman haka take so ba kamar yadda Faruq yake kiranta da Rafi'a ta yi complain har ta gaji, sai yace mata shi ba ba ta soyayya yake ba, ta neman kudi yake da abun da zasu ci. “Ba zaka gane ba ne” “Na gane, kuma suna da gaskiya, wasu iyayen basa barin yayansu su na kula samari barkatai, amman idan kin amince min zan iya sakawa a zo a nema min izinin magana da ke har mu fahimci juna” “Da gaske?” Ta tambaya tana tashi zaune daga kwance da take. “Wallahi kuwa, Fee'at ni fa da gaske nake aurenki zan yi, ba da wasa na zo ba” “Uhmm” “Allah kuwa, Momyna ta dade tana min maganar aure, ansha kai ni gurin yan mata da yan'uwa amman wallahi ban taba jin wanda tai min ba, amman ke ina ganinki na ji wani abu akanki Fee'at you're different...” Ba karasa maganar da yake ba ta yanke wayar ta kasheta gaba daya sakamakon jin ana kwankwasar gidan. Fitowa tai ta isa gurin kofar ta bude sai tai arba da Faruq yana dauke da Sultan. “Har kun dawo” Sai da yai kamar kar ya amsa mata sai kuma ya amsa. “Eh, Sultan shiga ciki” Ya karasa yana sauke Sultan dake rike da ledar kifi kasa. Sannan ya juya ya “Zan tafi shago” “Allah ya tsare” Ta fada kamar ba ita ba har sai da ya juyo ya kalleta, rabon da tai masa addu'a har ta manta. “Ameen” Ya amsa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ita kuma ta maida kofar ta rufe taja hannun Sultan suka nufi cikin gidan tana tunanin maganar da Fahat yai mata. ‘Amman da gaske yake zai aure ni? Ko kuma dai wasa yake? Amman ai be san na taba aure ba, idan na fada masa gaskiya zai yarda ya auri bazawara?’ Ita kadai take ta haukanta ta saka wannan ta kwance wacan, gaba daya sai hankalinta ya tattara ya koma gurin Fahat tana ta ayyana irin rayuwar da zata yi, kasancewar sa mai kudi kuma dan masu kudin. “Momy Mama tace a gaishe ki” Sultan ya fada yana zaunawa ya bude ledar kifin. “A hanya Dady ya siya min, yace na ci rabi na baki rabi” Ba ta ma kula, gaba daya hankalinta yana gurin Fahat. “Amman fa na masa karyar arziki, wata kila yana min kallon yar masu kudin ne” Sultan ya kalleta. “Momy waye?” Sai a lokacin ta lura da a zahiri tai maganar ba a badini ba. “Ba kowa ba ci kifinka, ga abinci can akan wuta idan yayi zaka ci kaji” Ya fada mata kai ita kuma ta shiga uwar daka ta dauki wayar ta kunna, sai ga sakon Ramlee ya shigo mata. ‘Ki sha kayan nan da yawa, yace yana son ku hadu da gobe, na kira wayarki ban samu ba, idan kin gama karantawa ki goge sakon’ Dundundun ta ji gabanta yayi duka uku uku, ba dan bata saba haduwa da mazan da ba muharramanta ba, sai dai wata kila saboda wannan haduwar ta daban ce, saboda zata aikata sabo ne alhalin tana da aure da kuma da, ga kuma karamin ciki a jikinta. Saurin goge sakon tai kamar yadda Ramlee ta bukata, sannan ta mike tsaye ta isa bakin kofar dakinta ta tsaya tana kallon Sultan dake ta aikin cin kifinsa hankali kwance, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, duk wani dauki da take na son a bata kudi sai ta ji ya ragu, domin bata taba aikata alfasha ba, sai a wannan karon ne zata gwada. Juyawa tai ta koma cikin dakin tana busar da iskar bakinta. 18 *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* LEILA POV. Sam bachi ya gagari idonta saboda yunkurin da take a zuciyarta na naki da soyayyar Talba. Sai ta kasa samun hadin kan sassan jikinta ciki har da idanuwanta, da kuma zuciyar datai mata garkuwa da kaunar Talba. Sai yanzu ta gane ashe abun ba shi da sauki, daman taya zai zame mata mai sauki? Ta rayu da kaunarsa na tsawon lokaci a dare daya ta ce zata cireta? A maimakon ta ji kuzarin cirewar ta karfafawa kanta guiwa, sai ta samu kasala tana jin kamar ba zata iya rayuwa idan babu Talba ba.   Sai dai tana jin ajinta da martaba da kimarta ta wuce Talba yai mata haka kuma ta cigaba da sonsa ko waye shi kuwa? “Na girmi wannan... Amman why?” Ta furta tana jin kamar ba zata samu hadin kan zuciyarta ba. “Allah karka min jarawa da kaunar mutumen nan” Ta furta ta saka hanayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin window ta bude window ta tsaya a gurin tana kallon taurarin da suka kawata samaniya. “Do i deserve this? It's painful...” Ta fada wasu hawayen na sauko mata, a rayuwarta bata san zafin rashin ba, bata san ta nemi wani abu ta rasa, wata wani abu painful irin na wannan daren ba, a damuwarta akan halin Talba ne, amman a yanzu abun ya ninku tana jin kamar ba zata iya yakar kaunarsa a zuciyarta ba, kuma ba zata iya barin kaunar ta zauna ba then me zata yi? Ta yi kasa da kanta wasu hawaye na sauko mata, ta fashe da kuka marar sauti, sai kuma ta soma murmushi. “Ni Leila ina kukan namiji? Wannan ba ajina ba ne, at least na san Talba be isa yace ba zai aureni ba, amman ni din ai be kamata na aure shi bayan duk wannan abun da yai min ba, be kamata na damu ba” Ta share hawayenta, sai magana take da kanta tana kallon harabar gidan kamar wani bakonta. Can kuma ta rumgume hannayenta tana tuna kalaman Kabir cewar Talba yana son ta, sometimes akwai kamshin gaskiya maganarsa, amman idan har Talba baya son ta waye zai so? Dole dai ita din ce. “Akwai maza da yawa da suka fi Talba komai a duniyar nan, kudi, kyau, aji da komai ma, idan zan ba wa maza da yawa dama zan samu wanda zan so fiye da Talba ma” Wannan karon with full confidence tai maganarta tana jin cewar zata iya. Ba laifi ta dan samu karfin guiwa da dakiyar zuciya, hakan yasa ta rufe window ta dawo saman gadonta ta hau ta kwanta ya rumgume filo ta lumshe ido tana son bachi ya dauke ta. A nan ne bachi ya ce mata fir ba dai shi ba a yanzu, tunanin abun da Talba yai mata sai ya dawo mata a rai ya zauna, idonta zuciyarta kuma a bude, har kusan karfi uku na dare, Leila ba mace ce ma'abociyar karatu ba balle ma har tai tunanin raya daren da nafila. Bata yarda ta bude idon ba duk kuwa da kin bata hadin kai da bachin yai. Sai kusan asuba bachi yai gaba da ita.   Washe gari Sunday kamar jiya kowa ya hadu a gurin cin abinci ban da Leila, sai dai a yau bangaren Momy aka zauna ba kamar jiya ba da aka karya bangaren Daddy. Daddy ya gama duba kowa be ga Leila, hakan ya saka ya kalli Momy. “Doctor ina Leila?” “Tana dakinta i think” Daddy ya yi mata wani kallo da kyau. “So you think? Lafiya take na lafiya tana dakin ma ko bata ciki baki da tabbaci?” “Uhm wani lokacin kana bani mamaki Alhaji, yaran nan fada wayansu ya kamata idan muka gan su a wani yanayi da suke son kebancewa mu bar su a yanayin da suke ciki” “Amman idan suna da damuwa fa? Har kullum wanda ka haifa kana masa kallon yaro ne ko da kuwa ya girmi duniyar nan, irin wannan abun shi yake haifa da depression mutum yana da damuwa kuma a kasa maganance masa ita ko a ki kula da shi, wannan be dace ba, ko jiya bata ci abinci safe tare da mu ba” Momy ta tabe sannan ta kwalawa Mairo kira, Mairo dake kitchen tana wanke kayan da sukai amfani da su, ta amsa tana fitowa da sauri. “Shiga dakin Leila ki kirata” “Hajiya Wallahi ko dazun dana shiga gyara dakin fada tai tayi tace idan a sake shiga dakinta ba tare data fito ba ko kuma na tashe ta bachi sai ta mare ni” Mairo ta fada a ladabce. Sai Daddy ya kalleta. “Ta mare ki? Yarta ce ke?” “Wata kila fada dakin ne ba sallama ko knocked” Momy ta amsa. “No wannan ba dalili ba ne, at least ai ta girmamasu sun gurme ta nesa ba kusa ba” “Wallahi Daddy haka take musu, ko magana cikin tsawa take yi” Amal ta dora da nata, sai Daddy ya kalleta sai dai be ce komai ba ya cigaba da cin abincinsa, Daddy mutum ne mai matukar son yayansa, ko kadan baya son ya ga wani abun bacin rai ko n damuwa ya same su, sai dai hakan be taba saka shi ya kyalesu a inda ya kamata ya gyara musu ba kuma ya saka musu ido. Sai da Daddy yai rabin cin abinci sannan ya kalli Momy ya ce. “Yawan fushi ko tsana yana nuna akwai abun da yake damun mutun ne, musamman a kwana biyun nan da bata fitowa cin abinci, idan akwai wani abu da yake damunta ki sama mata mafita, akwai abun da ke ya kamata ki yi a matsayinki na uwa, zata fi sakewa da ke kuma ta bude miki cikinta ta fada miki damuwarta, and to you my friends idan akwai wanda yake mata wani abu da zai sakata a damuwa ko bacin rai dan Allah ku daina, ya zama tsintsiya madaurinki daya, idan dayanku yana cikin damuwa ku yi kokarin ganin kun kawar masa Allah ya hada kanku yai muku albarka” Duk suka amsa da Amin, sannan Daddy ya mike tsaye yana fadin. “idan kin yi magana da ita, ki fada mata ina son ganinta” “Okay” Momy ta amsa tana watsawa Talba harara kasa kasa domin har ga Allah yanzu haushinsa take ji, saboda yana kokarin wuce gona da iri. Sai da Daddy ya fice daga falon sannan Momy ta dakawa Amal tsawa “Amal... Wallahi idan na sake jin bakinki akan fadawa Daddy magana any how sai na baki mamaki, sai na miki hukuncin da baki taba mafarkin zan miki ba, cigaba karki fasa” Momy ta karasa tana dukan burin dinning din sannan ta mike tsaye ta bar gurin a fusace. Amal ta bata fuska kamar zata fashe da kuka, Kabir ya saka mata dariya. Talba ya kalleshi. “Kabir?” Ya sake bushewa da dariya yana yi ma Amal gwalo. “Sai a hana ni dariya? Yarinyar tafi kowa iya gulma, bata gidan amarya bata gidan ango ai maganinki kenan” Dariyar ya cigaba da yi mata yana cin abincinsa, ita kuma ta kara bata fuska kamar zata fashe da kuka. “Karki biye Kabir kin san halinsa ai, daman so yake ki yi kuka, karki yarda ki masa kuka” “Ai ba zan masa kuka ba, na fi karfin na yi masa kuka” Ta fada tana matse hawayen dake son fito mata. Kabir kam ban da aikin dariya babu abun da yake mata, daman shi haka yake gurin dariya da keta shine a gaba gaba. Talba be bar dinning din ba sai da cikinsa ya cika, sannan ya tashi yana handala da muryar da shi kadai zai iya jin kansa ya nufi bangarensa. Tufafin jikinsa ya cire ya saka gajeren wando sannan ya hau gadonsa ya kwanta, da zimmar bachi amman ya ji kamar ba zai iya bachin ba, hannunsa ya mika ya dauki wayarsa dake gefen gadon, sai ya tararda miss calls har hudu daga Ali. Ganin kiran na Ali ne ya tuna masa da Aminatu, sauka yai saman gadon ya nufi bandakinsa, ta bata minti talati yana jika jikinsa sannan ya dauki man wanka ya zuba ya soma gogawa a jikinsa. Bayan ya gama wankan ya fito daure da tawul dayan kuma a hannunsa yana goge jikinsa da shi, gaban madubin ya zo ya tsaya da alama dai kallon kansa a madubi abu ne daya zama masa al'ada, domin yana jindadin tsaya a madubin yana kallon kansa. Sai da ya tsane jikinsa sannan ya dauki wani mai ya shafa a jikinsa ya feshe jikinsa da turare, ya murza wani a shafa a jikin, sannan ya shirya cikin kananan kaya ya dauki turaren tufafi ya saka sannan ya murza wani a hannunsa, sai ya juya ya nufi gurin da yake aje agogonsa ya dauki wanda yake ganin ya fi dacewa da tufafin jikinsa ya saka, ya saka talkaminsa sannan ya dauki wayarsa ya da wallet dinsa ya saka aljihu ya dauki wata Jacket milk color ya dora sama. Sannn ya fice dakin rike da makullinsa na mota. Sai da ya isa gurin motarsa sannan ya daga kansa yana kallon windows din dakin Leila, bakinsa ya cika ma iska sannan ya bude motar ya shiga. Ko kamin ya juya motar har sun bude masa gate, kamar dominshi kadai aka shimfida titi, haka ya fige mota ya hau titi yana driving. Kiran Ali ne ya sake shigowa wayarsa, sai ya saka hannunsa ya dauko wayar daga aljihunsa yai piciking. “Hello” Ali ya fada daga dayan bangaren sai Talba ya amsa masa kamar baya son magana. “Ya akai?” Ali yayi dariya. “Kar kace min har yanzu fushi kake, Ni da n kira na fada maka ka ya kamata ka bawa Leila hakuri, sai kuma na ji ka a fushi har yanzu” “Ali taya na kusa da ni zai wulakanta dan adam ya muzanta shi kuma ka tsammaci abun nan zai wuce da sauri? Kawai fatan da nake ya zama na babu hannun Leila a taba yarinyar nan, and zan binka matsalar Baaba na tabbar idan akwai hannunta ko babu” “Wace Baaba kuma? Talba are you in sense? Miya samu Baaba and why za kai blaming Leila? Ban taba yarda baka son ta sai...” Ali be karasa Talba ya yanke kiran ya aje wayar ya cigaba da tukinsa, ya san idan zai bata lokaci yana ma Ali bayani a yanzu ba zai fahimta ba saboda yana ganin tausayin Leila kuma yana ganin kamar Talba yana mata haka saboda baya sonta.   Be sake bin ta kan wayar ba har ya isa asibitin ya faka motarsa a inda aka tana domin aje motoci, sannan ya dauki wayar ya bude motar ya fita.   Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da dakin da aka kai Aminatu, so kawai yake ta farka ya tambaye ta, idan ta amsa masa da eh zai dauki mataki akan Leila idan kuma ya zama tsabanin haka zai bata taimakon da take bukata be kuma zama lallai ta sake ganinsa ba. Ba dan wannan abun daya faru ba wata kila ma da ba za zai sake sakata a idonsa ba har abada. A hankali ya kai hannunsa ya tura kofar dakin, sai kuma ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta, kwance take idonta a rufe hawaye na sauko mata, an cire mata robar jinin an saka mata ta ruwa, sai kuma ledar pure water dake saman dan karamin tabur din dake kusa da gadonta. Silently ya shiga cikin dakin ya maida kofar ya rufe, sannan ya isa gurin gadonta yana kallon fuskarta, ko kadan bata ji motsin bude dakin ba balle kuma shigowarsa ba, sai dai kamshin turarensa ya dawo da ita duniyar tunanin da tafi, hakan yasa ta bude idon a hankali a karo na biyu ta sake saka idonta cikin nasa, bayan wacan karon da suka zo tare da Ali, sai dai yanayin fuskarta sa ya tsorata, da alama ba mutum ne alaka da sakin fuska da murmushi ba. Sai dai kallonta yake kamar yadda ita ma take kallonsa hawaye na cigaba da sauko mata. “Can you talk?” Ta tambaya domin burinsa ta amsa masa da eh ko aa. Sai ta maida idon ta rufe. “Keeee.!!!” Ya daka mata tsawa, sai ta bude idon a zarane ta tashi zaune jikinta na rawa ta fara dube dube, domin ta tsorata matuka, abu kadan sai zuciyarta ta fara bugawa tana ganin kamar abun da ya faru ne a baya zai sake faruwa. “Mi na yi, kashe ni za ayi?” Tsayawa yai kallonta a ransa yana jinjina irin tsoratata da Leila tai. Be ankaro ba ya ji ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, hakan ya saka shi matsowa kusa gadon. “Ba komai za a miki ba tambayarki kawai zan yi” Ta kalleshi jikinta na cigaba da rawa hawaye na sauko mata kamar ba gobe. “Me zaka tambaye ni? Inna? Ko Baba? Ko kuma yan'uwana?” Shiru yai yana kallon yadda idonta yai ja tsabar kukan da take, ya hade yawun bakinsa tare da maida numfashi a hankali. “Ki kwantar da hankalinki babu abun da za a miki, kawai ina son na tambaye ki ne ko akwai wanda yai kokarin kasheki kamar makura, saboda an samu hannunta yana zubar da jini kuma roba zagaye a wuyanki” Kokarin natsuwa take tana son tuna abun da ya faru, sai ta daga kanta tana kallon dakin, sai a yanzu ta tuna akwai banbanci tsakanin wannan dakin da wacan. “Zaki iya tunawa?” Ya sake tambaya. “Ban manta komai ba, komai yana cikin kaina, idanuwana suna ganin komai har yanzu” Ta amsa masa cikin rashin kuzari. “Good fada waya kika gani kamin su suma?” Ta kalleshi. “Ban ga kowa ba” “Wa yayi kokarin kasheki?” “Babu” “Amman an tarar da hannu da jini...” Be karasa ba ta bashi amsa, bakinta a bushe kana ganinta kasan yunwa da ciwon sun mata mugun kamu. “Ni ce ni na aikata” Kallonta yake irin kallon nan dake nuna so yake ya gano idan tana cikin hayyacinta ko akasin haka. Sai ya ware mata hannunsa. “Miye wannan” Ta kalli hannun nasa, sai kuma ta koma zata kwanta. “Keeee!” Sai ta zaburo masa kamar ba ita ba. “Miye? Me kake so? Me zan maka? Dan Allah ka bar ni da damuwata, ka bar na ji da abun da yake damuna” “Ni ma ba damuwa ba ne, i just want to ask miyasa kike son ashe kanki..” Shi ma a tsawace yai mata tambayar zuciyarsa na bugawa da karfi yana jin kamar ya dake ta saboda ta masa tsawa. “Saboda na mutu, na huta, na tafi inda yan'uwana suka tafi na tararda mahaifiyata da mahaifina, ta tafi inda ba a zalinci inda ba a danne hakkin kowa, na tafi inda....” Ta kasa karasawa sai numfashinta yai sama ta fadi kwance saman gadon wuyanta a lankwashe, da sauri ya kai hannunsa ya rikota ta gyara mata wuyanta. “Baba.... Baba.... Baba.... Baba...” Shine kawai abun da take ta fada tana kallon Talba da idanuwanta da suka fara rufewa. Fita yai dakin da sauri ya nufi inda likitoncin suke ya fada musu sai likita da nurse uku suka taso a guje suka nufo dakin, zai shiga wata nurse din ta dakatar da shi. “Malam ka tsaya a waje...” Sai yaja ya tsaya gabansa na faduwa, kalamanta sun ratsa shi ga tausayinta, a yanzu kan ya tabbatar tana da babba damuwa wanda zata iya haifar mata da matsala kamar yadda Kabir ya fada. Yana tsaye a wajen har suka fito. Likitan ne ya tsaya yana tambayar Talba yayin da nurses din suka wuce. “Ya kake da wannan mai rashin lafiyar?” Talba yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada. “Kanwata ce” “Dan Allah bismillah akwai bayanin da zan maka” Likitan na fadar haka ya wuce gaba, Talba ya bi bayansa har suka shiga cikin Office. Talba ya zauna ba tare da jiran likitan yai masa izini ba. “I'm sorry ban sani ba, ko an maka bayanin cewar yarinyar nan an mata fyade, fyaden da ya wuce na hankali, da alama ba mutun daya ba ne ko biyu, domin abun yayi effecting kwakwalwarta, tana jin tsoro gaskiya, so ya kamata ka kiyaye bacin ranta damuwa, kuma kai kokarin kwantar mata da hankali, and karka dame ta da tambaya ko son sai ta tuna abun da ya faru, domin a yanzu ta kai matakin da zuciyarta zata iya bugawa, kuma be zama lallai idan ta buga ta rayu ba, za a iya rasa ta” Ya karasa tare da mika hannu ya dauko wata takardar yai rubutu akai, ya mika masa. “Ka siyo wannan maganin ba mu da shi a nan” Talba ya kai hannu ya karba yana kallon takardar maganin. “And zata fara cin abinci daga yanzu, domin na ga a file dinta an rubuta cewar bata ci, sai dai jiya na gwada bata ruwa ta sha kuma ta sha, so from now on zata fara cin abinci” Talba ya gyada masa kai. Sannan ya juya ya fice daga office din jikinsa a mace, tafiya yake yana tuna kalaman da tai masa da kuma na likitan, and the most important part is fyade. Kamar marar kuzari haka ya bude motar ya shiga ya zauna. “She's too young for this, maybe sun ashe Mamanta Babanta and su kai raped dinta... Wow.... ” Ya furta yana runtse ido, yana ayyana yadda abun yake da mugun ciwo. Wayarsa ya ciro ya nemi number Kabir ya kira shi. “Ranka ya dade” “Kabir wane chemist ko pharmacy zan samu magani ko wane iri a yanzu?” “Wa zaka siya wa?” “Kai... ” Kabir yayi dariya. Sannan ya fada masa, Talba ya kashe wayar ba tare da sake ce masa komai ba, sannan yai ma motar key yai reverse ya fice daga asibitin. After ya siye maganin ya siyo ayaba da kankana da lemu a hanya sannan ya dawo asibitin, kamar wani barawo haka ya shiga dakin without making a sound, har gaban gadonta ya karasa ya aje ledodin. “Waye kai?” Ta tambaya a hankali idonta a rufe, kallon mamaki yai mata a zatonsa bachi take but maganar da tai ya tabbatar masa da tsabanin haka, sai dai idonta a rufe yake. “Talba, you can call me Talba...” Ya samu kansa da amsa mata yana kallon fuskarta. Sai ta bude ido a hankali ta kalleshi, ta sake maida idon ta rufe. “Idan kina bukatar wani abu ki fadawa likitan zai sanar da ni, kuma idan zaki iya fada zamu so sanin inda yan'uwanki suke sai a bincika so that su san kina raye kuma ki samu mai kula da ke” “Da rayuwata da mutuwa ta duka daya ne, saboda ba ni da kowa a yanzu” “Shiyasa kike kokarin kashe kanki? Ko kuma dai wani ne yake kokarin kasheki?” Ta bude idon ta tashi zaune cikin rashin kuzari tana kallonsa, idonta har ya yi baki yayi ja kamar tsabar damuwar da kuka. “Idan baka ci abinci ba akwai mai damuwa? Wani yana damuwa idan baka da lafiya? Idan ka shiga damuwa akwai mai kokarin faranta maka rai? Akwai wanda zai so abun da kake so, ya guji abun da zai bata maka ra?” Yayi shiru yana kallonta, kamin ya hade yawun bakinsa, ya daga mata kai alamar eh akwai. “Ni duk na rasa wannan, a cikin dare daya rayuwata ta sauya, a tsakanin awannin da dakiku aka min katanga tsakanina da iyayena, farincikina yana tare da yan'uwa kuma duka an kashesu, a ciki wuni guda aka juya duniyata, aka nesanta ni da farinciki, a kusanto da bakinciki, a cikin daren nan aka raba ni da martaba da, na kasa manta komai, hoton komai ya gagara goguwa a idanuwana, a tsakanin wacan daren da dararen da suka biyo bayansa bakinciki ne da tashin hankali, sum rusa duniyata, sun tarwarsa shirina...” Kallonta Talba yake a tsakanin hawayenta da duniyarta da take labarta masa sai ya rasa wane ne yafi tsaya masa a zuciya. Kujerar dake gefen gadon ya ja ya zauna yana kallonta. “Likita yace ki daina damun kanki, saboda yanayinki yawan tunani da damuwa zai iya haifar miki da wata matsalar...” “Akwai matsalar data wuce ta rashin uba da uwa? Rayuwata ta riga ta sauya, bana tsoron mutuwa....” “Amman baki yi tunanin miyasa mutuwa take gudunki ba? Na san kin shiga a gurin da za a iya kasheki amman ba a yi ba, kika samu kanki a nan kuma kika yi kokarin kashe kanki, still hakan be faru ba, rayuwata tana ta zabenki ke kuma kina neman mutuwa baki yi tunanin ya kamata ki rayu ba?” Ta lumshe ido tana jin bachi na son daukarta saboda allurar da akai mata. “Na rayu a inda ba a rufa idan akwai sanyi, ba a fakewa a idan ana ruwa, ba a gusawa idan rana ta kawo, a hannu ake raba mana abinci, idan an bada da safe ba za a sake ba badawa ba sai da dare, na ga wa ana dukan wasu, kuma a kashe da yawa a gabana, sun keta haddin mahaifiyata a gabana, sun yanka yan'uwana, sun kona abincin mu, suka akashe babana saboda ya ki yarda ya keta haddin ni, sanadin tafiyar da muka yi kafafuwana basa iya komai a yanzu, sun yanka yan'uwana sun fasa kan wasu da dutse, a haka kuma kake ganin rayuwata tana zabata? Wata kila saboda tana son na yi taraiyya da bakinciki ne” Hawaye ya sauko mata sai bachi yai baga da ita, ido ya sakar mata kalamanta na taba zuciyarsa, misali yake da kansa idan shi ne ya zai ji? Yana rayuwa cikin jindadi lokaci daya ace komai ya tarwatse! Shi kansa maraya ne, amman be san zafin rashin iyaye ba, be san zafin rashin yan'uwa ba, idan wani abun ya same shi da gudu za a kawo masa agaji, tsabanin it. Takurewa tai gurin daya ta jikinta na dan rawa alamar tana jin sanyi ga kuma hawayen har yanzu ba su daina zuba ba, murmushi mai sauti ne ya biyo bayan hawayen. “Inna....” Ta furta tana cigaba da murmushi, sai kuma tai fuskar kuka wasu sabbin hawayen suka zubo mata. Mikewa yai tsaye ya cire Jacket din jikinsa zai lulluba mata sai jikimta ya fara, tana numfashi da karfi ta kara rumgume kanta kana ganinta kasan a tsorace take, a hankali ya lullub mata jacket din sai kuma ya tsaya yana kallonta har lokacin hawayenta zuba suke, wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya juya ya fara tafiya a hankali zuwa gurin kofar. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Taya zan tafi na barki? Ko na gudu harbina zasu yi, ba zan tafi ba tare da ke ba...” Juyowa yai ya kalleta, kana ganinta ka san wani tashin hankalin ne take mafarki, da alama abun da ya faru ya shiga ranta sosai ya zauna, ya kusan minti biyar a tsaye yana kallonta sannan ya fice yaja mata kofar a hankali ya rufe. 19 *Dan Girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa FARUQ POV. Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin Rafi'a. “Faruq ka saka mata ido, duk abun da take tana yi saboda ta bata maka rai ne, kuma komai na rayuwar duniya jarabawa ne, ko da arziki ne Allah ya baka ya ga yadda zaka iya rike su, balle kuma talauci, da muguwar mata” “Wallahi Wani lokacin Rafi'a tana bani mamaki, ita kamar bata san Allah ke yi ba? Shi zai yi ma kansa arziki ne? Sai ta rika abu kamar ba yar'uwa ba?” Aisha ta dana da nata. Sai Faruq ya kalleta. “Wani lokacin ina jin kamar na sake ta na huta, sai dai idan na tuna irin wahalar da mahaifinta yai da ni a karatuna kuma ya dauki yarsa ya aura min duk da a lokacin bana da komai, sai na kamar idan na sake ta ban kyauta masa ba” “Haka ne, wani abu dole a daga mata kafa saboda mahaifinta, domin mutumen kwarai ne, kuma na tabbatar da yana raye Rafi'a ba zata maka wani abun ba, kasan Umma daman ba son auren take ba tun farko shiyasa komai tai bata ganin laifinta, amman kai hakuri Inshallah sauki yana tafe” Ya ja wani dogon numfashi ya sauke. “Ni da har na yanke shawarar na bi Yusufa mu tafi nijar gurin ginar zinarina nan” “Nijar kuma?” Cewar Mama ciki damuwa. “Eh kin ga masu zuwa suna samowa ba laifi, kuma ba kasan inda rabonka yake ba, amman zama haka ba zai yi Mama, hausawa sun ce idan hagu ta ki sai a koma dama” Mama ta girza kai. “Wallahi bana son tafiyar nan nesa Faruq, da dai ka hakura mu ga abun da Allah zai yi” “Mama duk inda rabonka yake sai ka tararda shi, ko kuma ya nemeka, kuma abun da Allah ya rubutawa bawa ko a ina yake zai same shi, na san dai ba zai wuce ki ce kina jin tsoron hanya ba ko abunda zai faru da ni, kawai ki min addu'a” “To Allah ya zaba mana abun da yafi zama alheri, idan tafiyar Alheri ce Allah ya shige maka gaba” “Ameen idan Allah yasa naje ko na siyen fili na samu ai na samu” “Haka ne, amman kudin motar zuwa can fa?” “Har cin abinci da komai zan iya kashe 20k haka Yusufa ya fada min, kuma yace ana kwana uku kamin a samu isa, wannan kudin da ban biya haya ba zan iya cire na mota ciki sai kuma sauran kuma na siya ma Rafi'a abinci na bar mata kamin mu tafi kuma mu ga abun da Allah zai yi” “Toh Allah ya shige maka gaba” “Ameen” Ya fada yana mikewa tsaye sai kanwarsa ta kalleshi. “Ya Faruq ance fa rame ake shiga, ko. Kwanan baya na ji ance rame ya rusga da wasu” Murmushi yai. “Allah shi ke tsarewa ai, ku dai kui ta mana addu'a” “Toh Allah ya tsare, yasa arzikinka na can” “Ameen ya Rabb” Ya amsa sannan yai musu sallama ya fice, ko da ya isa gida har ta gota, a bude ya samu kofar gidan, sai ya shiga da sallama ya maida kofar ya rufe sannan ya shiga falon, sai ya same ta tana waya sai dai ganinsa yasa ta sauke wayar ta kalleshi. “Sannu da zuwa” “Yauwa, ya gidan?” “Alhamdulillah” Sai ta tashi ta nufi inda abincinsa yake ta dauko masa ta aje masa tare da ruwa. “Ina Sultan?” “Yayi bachi” Ta amsa sannan ta zauna kusa da kujerar da yake zaune, kallonta yake har ta zauna din, gaba daya yau ta canja, daman can fara fes amman haskenta and yau ya karu sai wani sheki take tana ta kamshin hummura mai tsada. Dauke kansa yai ya maida dubansa gurin abincin data aje masa yana hade yawu, rabon da wata mu'amalar aure ta shiga tsakaninsu har ya manta, domin bata yarda idan ma ya neme ta, idan ya matsa sai tace ga ciki ba zata iya ba, shi kuma baya son yi mata da karfi hakan yasa ya dauke mata kai ta wannan bangaren ba dan baya bukata ba sai dan ba zai iya ja'inja da ita ba. “Rafi'a ina ta shawara da kuma neman zabin Allah” Ta kalleshi da sauri a tunaninta ko zai fada mata cewar daya faga cikin aikin da yake Applying ne wani ya fito. “Na me? Aikin ka samu ne?” “Aa, ina shawarar zuwa nijar ne?” Wani irin yatsine fuska tai kamar wanda tai arba da abun kyama. “Nijar fa kace? Ba dai gurin ginar zinari ba ko?” “Can mana” “No nonono, Wallahi ba zan yarda ba, so kake ka ja min abun magana a gari? Ace mijina ya tafi gurin ginar zinari? Talaucin har ya kai nan? Aa Wallahi ba zaka je ba” “Shi zuwa ginar zinari zunubi ne? Wace irin magana ce wannan nan?” “Kana tafiya za a ce talauci ya matsa mana har ka bar gari ka tafi nema nijar, ka ja min abun magana, kawaye na mazajensu daga masu aiki a kamfani sai banki sai ma'aikatun gobnati, ni kam ba zan iya ba Wallahi” “To sai na fasa saboda ke nan? Ni na riga na yanke shawara, kuma na zo na fada miki ne saboda na baki hakkinki” “To Wallahi ba zan yarda ka je ba, Wallahi sai dai ka sake ni ka tafi na san ba mu tare” Dubanta yai irin duba na mamaki. “Rafi'a me kike son ki zama? Ke kin isa ki yi ma kanki arziki ne, da abu kadan zaki fara cewa talauci?” Sai ta mike tsaye domin ya fahimci da gaske take. “Wallahi Faruq, na rantse da Allah ba zaka tafi nijar ginar zinari da aurena ba, sai dai idan tafiya ce zaka yi ta har abada, wanda babu dawowa, wai kai baka da zuciya ne? Baka san Annabi ya faku ba, na gaji da abun kunya Faruq, na gaji, aurena dole ne? Ni kadai ce mace a duniya nan ne? Ba zan iya ba, ga danka nan yayi wayo amman ka kasa saka shi makaranta, wannan da zan haifa ma na san dan taure zaka yanka min” “Sai ki saki kanki ai, ba saki ba? Ba zan saki ba kuma sai na tafi nijar din ki mutu, ina hakuri ne dake kawai saboda Mama da kuma mahaifinki” Ya fada yana mikewa tsaye, sai ta sa gabansa. “Wato ka fito gurin bakar tsohuwa ta kitsa maka abun da take so a kai...” Bata karasa ba ya wanke mata fuska da mari sai da ta fadi zaune. Ta fashe da kuka. “Faruq ni ka mara?” “Har abun da yafi mari zaki samu, matukar iskancinki da rainon wayo ya kai ki ga taba mahaifiyata, ai ko da ba ta hada komai dake ta cancanci girmamawa saboda tana sarakuwarki balle tana a matsayin kanwar mahaifinki” “Ita bata san da zumuncin bane ta barka kana ta cutar da ni? Ba zan iya ba, na ce bana so ka sauwake min mana” Har yayi kamar Ya bude baki yace na sakeki sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Be sake kulata ba ya shiga bedroom din, bakin gado ya zauna yana kallon Sultan dake ta bachi ya kai hannu ya shafa shi, makomar dansa yake zubawa idan har ya sake ta rayuwarsa zata zama abun tausayi, domin zaman zai zame masa a tsakanin gida biyu, gidan mahaifinsa da kuma inda Mahaifiyarsa. Tsabar bacin rai da tunani be ci abincin ba ya kwanta kusa da dansa, Baturiya kuma ta kwana a falo. Washe gari waina ya siyo musu abun kari kasancewar aljihunsa da dan nauyi irin na masu nema yau da gobe, bata gaishe ba tun da garin Allah ya waye, sai dai hakan be hana shi ce mata zai fita ba, da harara ta bishi babu Allah ya tsare balle addu'ar alheri. “Allah yasa kai hadari ka mutu..” Ta fada bayan ta ji karar rufe gidan, sannan ta tashi ta bude wainar ta zubawa Sultan, ita kuma ta nufi wayarta ta dauka ta kira Fahat, ringing biyu ya dauka. “Fee'at” Sai ga murmushi a fuskarta kamar ba ita ba, bata kula da Sultan ba ta cigaba da wayarta tana masa kalaman soyayya kamar yadda shi ma yake mata. Sun kusa awa daya suna abu daya sannan sukai sallama tana masa kiss a wayar, duk abun da take Sultan na kallonta sai dai ita bata lura da hakan ba. Fitowa tai waje ta fara gyara gidan domin Ramlee ta fada mata karfi goma za su hadu. Ko da tara tai Baturiya ta gama komai har ta shiga ta yi wanka. Sai da ta shirya sannan ta kai Sulta makota ta dawo gidan ta kara daukar wasu kayan matan ta sha daman Ramlee ta nuna mata wadanda zata sha idan tana kusan tafiya. Tara da rabi kiran Ramlee ya shigo wayarta, jiki na rawa ta dauka kamar ba ita ce ta gama jin tsoro ba a jiya. “Madam hop kin shirya” “Na shirya, ke kawai nake jira” “Haka na ke so, ba wasa ganin nan nima na kusa karasowa” “Sai kin iso” Ta aje wayar tana murmushi, ita ma kanta ta san ta yi kyau, sai kamshi take zubawa kamar sabuwar amarya, kamin Ramlee ta iso ta shafa hoda ya kai sau shida, turare kan ba adadi irin feshin da take masa. Tana jin sallamar Ramlee ta dauki wayarta da jakarta ta fito waje da sauri. “Wow yanzu kika fito da sunanki n Baturiya, amman mutumen idan ya ganki sai ya rude” Baturiya ta yi dariyar jindadi. “Da gaske” “Wallahi kuwa, sam sam baki dace da Faruq ba, ke din matar manya ce, amman fa karki fada masa cewar kina da aure domin na ce masa ke din bazawara ce” “Ke ma dai da wata magana, ya za'ayi na fada, Allah dai ya sa inda zamu je ba public place ba ne, domin akwai wadanda bana son su gan ni” “No guest house dinsa ne, muje dai kar mu bata lokaci” “Amman kin san me? Idan na fita da kwaliyar nan haka ina kamshi mutanen unguwa za su fara saka mana ido” “To ya zamu yi? Ke dai ina ruwanki da mutane ne wai?” “Aa bari dai a saka hijab da nikab idan na je can sai na cire a motarki” “Haka yayi yi sauri” Ta juya ta koma dakinta da sauri ta dauko katon Hijab ta saka tare da niqab sannan fito ta rufe gidan. Tun daga yanayin ginin unguwar da shuke shuken zaka san cewa unguwar manyan mutane ce, a gaban wani katon gate suka faka Ramlee tai horn Mai gadin ya leko tai magana da shi sannan ya bude mata ta shiga, a harabar gidan tai fakin ta ciro wayarta ta kira shi. “Alhaji mun iso” “To yayi Kyau Hajiya Ramlee a barta ta dan huta gani a hanya, garin sauri ma na kade wasu amman dai na gama komai zan iso yanzu” “To yayi Alhaji sai ka iso” Ta aje wayar sannan ta labartawa Rafi'a abun da ya faru da shi. “Kuma ki sake jikinki ki kwashi arziki, domin yana son ki Wallahi na fada miki hotonki kawai ya gani amman duk yabi ya rufe balle kuma ce ya yi arba da ke” “Inshallah ba zan baki kunya ba” “Yayi kyau, haka nake son ji, yanzu mu shiga ciki na nuna miki falonsa sai n fito na bar ku ku sha shagalinku” Ramlee ta fada tana murmushin jindadi. Sai Baturiya ta cire Hijab din da Niqab ta kai hannu ta bude motar wayarta tai kara. “Allah yasa ba mijin nan naki ba ne” Cewar Ramlee tana tabe baki, fasa fitar Baturiya ta yi ta ciro wayar daga jakarta ta duba. “Shi ne kuwa, ban san mi zai ce min ba, ko kuma ya dawo gida ne oho” “Karki dauka dan Allah zai wargaza mana shiri ne” “Ai ba zan dauka ba” Ya fada tana kallon wayar dake ta ringing har ta gaji ta tsinke, sai gashi ya sake kira sai dai wannan karon ta ji gabanta ya dan fadi. “Kai wannan miji na ki da ci yake, gaskiya ki kashe wayarki kar ya zo yana damunki da kira ya lalata mana shiri” “Wallahi kiran Fahat kawai nake jira, saboda yace zai kira ni anjima bana son na kashe wayar ya kira ya jita a kashe zai damu ne” Ramlee ta mata wani kallo. “Da alama dai shi ma dan hannu ne” “Aa Wallahi shi ai son aure yake min da gaske, na nuna Masa ni Budurwa ce” “Amman ke yar banza ce, ya zaki yi da Faruq?” “Haba Ramlee kina min fatar zama da shi? Ai rabuwa zamu yi, kin ga idan ya sake ni ina zubar da cikin nan na cika idda zai na yi aurena” “Kina ganin Faruq zai sake ki ne?” “Dole na idan na bude masa shikashikan rashin mutunci ai dole ya sake ni” “To dan fa ki yi yaya da shi? Ai kin san za a bincike ki musamman yayan manyan mutane basa aure zai sun zurfafa bincike” “Ai idan na fita zan bar Sultan a gurin Faruq ne, ba da shi zan je ba, kuma shi Fahat din ai yace min a Lagos yake aiki, kin ga zamanmu a can zai kasance ba a nan ba, zan iya boye komai” “Ki ce kema kin iya bala'i Sai duk suka saka dariya, kiran Faruq ne ya sake shigowa wayar, wannan karon wani tsaki taja ta kashe wayar gaba daya. TALBA POV. Sai da yai sallah azahar sannan ya karaso gida, tun kamin yayi fakin idonsa suka sauka akan Leila dake zaune a daya daga cikin kujerun da suke balcony rike da wayarta sai cup din lemu a gaban kujerarta tana taunar cingan har wani kis kis take. Yayi kusan five minutes a motar sannan ya bude ya fito ya nufo inda take zaune ya zauna ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya bata damar dauke kai daga gefen da yake ta maida wani gurin tana cigaba da taba wayarta. “Can we talk?” Ya fada ba tare da ya kalli inda take ba, sai ta juyo ta kalleshi. “Ta fada maka ba ni ba ce ba kenan?” Shi ma juyowa yai ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa. “Daddy ya damu dake ne i want us to talk” “Da gaske?” Sai ta mike tsaye ta dauki cup din lemun ta wuce ta bar masa gurin. Tana kokarin kai hannu ta danna door bell din kofar falon sai ga Kabir ya fito, ko kula shi bata yi ta shige, da kallo ya bita kamin ya juya ya kalli Talba dake kallon harabar gidan, har lokacin tunanin Aminatu yake. Karasa Kabir yai ya zauna a inda Leila ta tashi. “Ya jikinta?” “Da sauki...” Talba ya amsa ba tare daya kalleshi ba. “Ka yi magana da Leila ne?” Ya girgiza masa kai. “Wani lokacin baka sanin damuwar mutane idan baka kusantar su, you see yan gudun hijirar nan da kake gani a hanya wasu a fankon guri, suna da labaruka masu taba zuciya” “Ita ma tana daya daga cikinsu ne?” “Tana daya daga cikinsu ne?” “Yeah they raped her, killed her Father, mother suka gona musu gida, suka kashe yayyunta and raped her mother in front of her, labarinta akwai tsoro da taba zuciya, yanzu haka she can't walk saboda wahalar data sha gurin mutanen nan, and bata da kowa kuma tana bukatar kulawa sosai” Talba ya fada cikin yanayin dake nuna zuciyarsa ta tabu sosai da labarin Aminatu. “You know a lokacin da kake raina ni ni'imar da Allah yai maka, wasu da yawa suna can suna neman kadan, a yadda na fahimta now yanzu farinciki take bukata, saboda ya cire rai daga shi har tana neman kashe kanta, and Ali and wannan likitan sun fada min abun nan ya taba ta” Kabir ma saurarensa yake cike da tausayin Aminatu duk da kasancewar ba taba ganinta ba, sai dai ya san waye Talba duk abun da zai saka shi a damuwa ko tunani ba abu ne kadan ba. “Yanzu a wane matsaya take” “Tana samun kula a asibitin, amman babu mai kwana a inda yake kuma kasan da ace tana uwa ko wata yar'uwa a raye zata fi samun kulawa, tana jin tsoro sosai har magana take idan tana bachi, and likitan ya fada mim idan tana yawan damuwa zuciyarta zata iya bugawa, yarinya ce karama kamar Amal, bata san inda zata je ba” “Haka ne mutane suna cikin hali, sai dai idan baka shiga cikinsu baka sani” Talba ya mike tsaye yana saka hannunsa aljihu. Ya nufi bangarensa, Kabir ya bishi da kallo yana murmushi. LEILA POV. Tana shiga dakin ta dauki wayarta ta kira Madina ta fada mata abun da ya faru, a ciki har da kudinta na son ta fadawa Daddy cewar ta fasa auren Talba. “Anya idan kika yi haka baki yi kuskure ba? A Maimakon ki ta wannan haukan ba kara ki nuna masa kina son yarinyar ba ko da a munafunce ne” “Lallai Madina baki gama sanina ba, ke a tunaninki zan iya share miji ko saurayi da wata? Har sai na nuna ina son ta bayan duk abun da yai min, ni fa na san ba sonta yake ba kawai yana amfani da ita ne ya cusa min bakinciki?” “Idan har haka ne, ke me zai hana ki yi amfani da abokinsa ki rama abun da yai miki?” “Waye kenan?” “Ali mana, ta hanyarsa ma zaki iya tabbatarwa idan Talba yana sonki da gaske” “Kin kawo shawara, tabbas zan iya rama abun da yai min ta hanyar Ali” “Yes amman ina fatar hakan ba zai janyo matsalar da zata hana a dauke ni aiki ba, kin san fa ina nan ina ta jira” “Aiki ai dole a dauke ki, bari anjima ma zan yi ma Daddy magana, ki kwantar da hankali cikin kwana biyun nan za a dauke ki aiki” “Alhamdulillah, na gode sosai yau zan yi kwana farinciki ko ba komai ai hakan zai kara kusantar da alaka ta da ku” “Haba ai mun fi haka dake, zan kira ki anjima” “Okay thank you” Ta sauke wayar tana murmushi, har cikin ranta take jin cewar Madina ta sama mata mafita na bata shawarar ta yi soyayya da Ali, ta san idan tai haka zata Talba sosai kuma zai gane irin zafin da take ji ita ma. 20 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Khadeeja Candy* *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Zaunawa yai saman gadon yana goge ruwan jikinsa. Sannan ya kai hannu ya dauki wayarsa dake ringing. “Ali ka dame ni fa” “Ai dole na dame ka Talba, ka bawa Leila hakuri?” “Na yi maka kama da wanda zai yi wannan?” “Seriously Talba baka kyauta ba, kuma ya kamata ka bata hakuri, be kamata alakarku ta lalace saboda wata bare can da baka san inda ta fito ba” “Leila ta yi abun da yake bani mamaki ne, so dole na zargeta akan halin da yarinyar nan ta shiga, lastly karka sake min maganar bada hakuri” “Really kana ganin ka kyauta kenan? And me yarinyar ta fada maka?” Can sama sama Talba ya fada masa abun da Aminatu ta fada masa. “Yanzu ina yarinyar take?” Ali ya tambaya yana sauke ajiyar zuciya. “King's and queen's hospital” Cewar Talba sannan ya mike tsaye yana shafa fuskarsa. “Labarinta be taba ka ba?” “Kai ya taba ka kenan?” “Yeah, duk wani mai imani ne dole ne labarin yarinyar nan ya taba shi” “Kar tausayinta ya saka ka manta da yadda kake da Leila, tsakani da Allah yarinyar nan tana sonka kuma tana azabtuwa da irin abun da kake mata” “We can talk later” Yana fadar haka ya kashe wayar ya jefa saman gado, sannan ya shiga dan karamin dakin da aka tanada domin ajiyar tufafi ya saka riga da wando na suit blue sannan ya fito ya dawo gaban madubi yana duba kansa. Komawa yai ya dauki turare ya murza a hannunsa na fesawa kuma ya fesa a jikinsa. Sannan ya dauki abun da ya kamata ya dauka ya fice daga dakin yana kokari saka wayarsa aljihu. Ya fito bangarensa ya nufi bangaren Momy sai dai turarensa ya riga shi isa bangaren Momy saboda karfin kamshinsa, yau kam a bude ya samu kofar falon Zulai nata aikin mopping tana ganinsa tai saurin risinawa ta gaishe shi, sai dai be ma kalleta ba balle har ya amsa mata. Motsin da yaji a kitchen ne yasa ya nufi kitchen din, sai dai be karasa ciki ba saboda ya hango Leila a tsaye kusa da Momy da alama yau kamar a tare suke hada abun karyawan. “Momy ina kwana?” Momy ta juyo ta kalleshi, sai ta amsa fuska ba yabo ba fallasa. “Lafiya Kalau an tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ya amsa sannan ya juya da zimmar ficewa, sai Momy tai masa tayin abun kadyawan. “Ba zaka tsaya ka karya ba?” Kamar zai ce a a sai kuma ya juyo. “Idan an gama a saka min a kula zan tafi da shi” “Okay” Momy ta amsa sannan ta dauki abu ta shiga zuba masa dukan abubuwan da suka hada, yana ganin haka ya fice daga kitchen din, ko da ya fito Zulai ta gama mopping din sai ta bude masa kofa da sauri, ya fice yana addu'ar fita daga gida, sannan ya nufi inda Motarsa take fake, tun kamin ya karasa ya danna remote din hannunsa motar tai kara ta bude kanta daga lock. Hannunsa ya mika ya bude motar ya shiga ya zauna yana warming dinta, yana kokarin yin reverse da Motar, Mairo da fito da gudunta rike da kwadon abinci ta nufo inda yake, after yayi reverse din ta bude gidan baya ta saka masa sannan ta rufe motar tana masa addu'ar Allah ya tsare. Kamin ya isa gate ya daga wayarsa ya kira Daddy, domin ba al'adarsa ba ce ficewa ba tare da ya gaisa da Daddy ba, sai idan Daddy na bachi ko kuma baya garin, ko kuma wani ne, shi kadai ne ke saka shi fita ba tare da yayi ido biyu da Daddy ba. Har ya hau babban titi Daddy be dauki wayar ba, as usual idan ya kira sau daya ba a dauka ba zai sake kira ba. Sai kawai ya aje wayar ya cigaba da tukinsa, a gogon hannunsa ya duba a daidai lokacin daya faka motarsa harabar asibitin, sannan ya bude motar ya fito ya bude baya ya dauki abinci ya nufi ciki, akwai jama'a sosai a asibitin ba kamar jiya da shekaran jiya ba da suke ranakun hutu, yau kam Monday mutane sai hada hada suke, kamar bako haka ya tura kofar dakin ya shiga. Zaune ya same ta tana ta kallon kofar kamar mai jiran shigowar wani, hawaye suna mata zuba, sai da ya maida kofar ya rufe sannan ya karasa kusa da ita ya aje abinci. “Ya jikinki?” Sai ta juyo ta kalleshi, ta kasa amsawa. “Ya sunanki?” Ya tambaya yana cigaba da kallonta. Nan ma bata ce komai ba, sai ya matsa kusa da inda aka aje file dinta ya bude yana dubawa Ramlat Ibrahim ya ga an rubuta. “Ramlat...?” “Aminatu...” Ta amsa tana kallon wani wajen tare da kai hannu ta share hawayenta. “Mamana, ba ki gajiya da kuka?” Sai ta sake kallonsa a karo na biyu tana murmushin da ya fi kuka ciwo. “Baka san yadda nake ji ba, yanzu ba ni da mai damuwa da ni, babu wanda ya rasa kamar yadda na rasa komai a lokaci daya, yanzu bara zan koma a titi, ina zan kwana? Me zan ci ko na ci babu ruwan kowa, ni kadai na rage.... ” Kamar fada take maganar tana kuka mai karfi, sai kuma ta saka hannayenta ta rike kanta tana lumshe ido. Kallonta kawai Talba yake har ta fara yunkura sauka saman gadon. “Zauna karki sauka” Dagowa tai ta kalleshi, sai ta zauna din kamar yadda ya bukata ta rumgume kanta tana hadiyar yawun bakinta da ya bushe. Dukawa yai ya fara bude abincin yana dorawa a saman gadon da take sannan ya duba fruits din daya kawo mata jiya, domin tun jiya da ya kawo mata fruit din ya fita be sake dawowa ba. “Baki ci komai ba?” Ya tambaya yana kallonta. Sai ta daga masa kai. “Ina jin yunwa amman bana iya cin komai, kuma hannuna baya kaiwa” Be sake ce mata Uffan ba, ya bude mata abinci. “Zaki iya cin wannan?” Ta kalli abinci sai ta girgiza masa kai, alamar aa domin komai na duniyar baya burgerta. Zai sake yin magana likitan daya karbeta ya shigo dakin rike da takardu da wata Nurse a bayansa. “Yauwa, daman ina son magana da kai” Likitan ya fada sannan ya mika masa hannu suka gaisa. Sai kuma ya shiga duba Aminatu. “Kina jin wani ciwo ne?” “Kirjina yana ciwo sosai ksmar zai cire, kuma idanuwana ma suna ciwo suna kai kayi” “Ki daure ki rage tunani, da yawan kuka damuwace ke saka haka, ita kuma damuwa bata da magani kamar a gusar da abun da yake rai” Ya fada yana rika hannunta ya saka mata abun hauna bp ya aunata, bayan ya gama ya kalli Talba dake tsaye ya ce “Tsakani da Allah yarinyar nan na bukatar kulawa, akwai maganin daya kamata ace ana shafa mata a kafa kuma ana bata lokaci zuwa lokaci, and tana yawan kuka wanda hakan yana kara mata damuwa, kamata yayi ace akwai wani abu da zai dauke mata hankali, ka ga ko shiga bandaki ya kamata ace akwai mai rikata domin jiya ma a nan tai fisari sai da aka gyara gurin, sannan tana zaman kadaici ne kawai babu kowa a tare da ita a nan” Talba ya kalleta cike da tausayi, shi kansa ya san tana bukatar mai kula da ita, domin tufafin jikinta ma sun yi datti duk da kasancewar Ali ya saka an canja mata wasu tufafin tun a lokacin da take asibitinsa. “And jiya ma ance bata yi bachi ba sai magana take ta yi da kanta tana kuka, be kama ace kullum sai an mata allurar bachi sannan zata iya bachi ba, domin ita kanta allurar yawan yinta yana haifar da wata cutar ta dabam” “Ba ni da wanda zai kula da ita a yanzu gaskiya” “Ko da a gida?” Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada. Aminatu ta kalleshi da idanuwanta da suka sha kuka har suka canja kala. “A yanzu ba mu da gida, idan kun gaji da ni, to ku kai ni gurin da yan gudun hijira suke zama, ko kuma gidan marayu ko gidan nakasassu, ba ni da kowa...” Talba ya risina kusa da gadonta yana kallonta cike da tausayi. “Ba nasasa kika yi ba, ciwo kika ji, kuma zaki warke soon ko Likita?” Sai likitan ya daga mata kai yana murmushi. “Bata da kowa ne?” “I can take care of her zan kai ta gida...” Talba ya fada, sannan ya mike tsaye. “Okay, idan zaka kaita gida, za ta fi samun kulawa gaskiya, domin a yanzu damuwarci kawai ciwonta sai kuma kafafuwan. Amman a shawarce zai fi kyau ka samu likitan da zai rika zuwa yana dubata, ko kuma ka rika kawota time to time asibiti ana duba kafar” Talba ya daga masa kai alamar gamsuwa, Likitan ya kai hannunsa ya rika kan Aminatu ya bude idonta. [3/7, 11:34 AM] Zatuuu🦋: “Ki daina yawan kuka kina daga idonki sama saboda kar glass din idonki ya samu matsala” Ita dai bata sake ce masa komai ba har yai abun da zai yi ya fice. Sai da ya fice sannan Talba ya zauna a saman kujerar dake facing din gadon yana kallonta. “Ki zama mai jajircewa da hakuri, komai da kika gani na rayuwar duniya baya zuwa da sauki, kuma kowa da kalar jarabawarsa, and ina tunanin Allah ya hada ni da ke saboda na taimakeki, wata kila da dace da wani kika hadu shi ba ni ba, da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, so ki dauki haduwa ta dake a matsayin kaddara, akwai wani karon magana da ake cewar when life gave you hundreds reasons to cry, show life you have thousand reasons to smile, ina da tabbacin zaki zama jaruma, ki hade komai ki rayu ko dan iyayenki” “Kuka ya zame min dole baka san yadda nake ji ba, rashin iyaye yan'uwa abu ne mai matukar ciwo, lokaci daya na rasa komai” Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, hawaye nata wanke mata fuska kamar ba gobe. “Na san yadda kike ji, ni ma maraya ne kamar ke ba uwa ba uba, banbancina da ke shine, ni ban taba kukan maraici ba, ban taba neman wani abu na rasa ba, ke ma kuma za ki samu kulawa Daga yanzu har karshen rayuwarki, kamin ki gane danginki, zan sama miki wasu dangin da zaki zauna tare da su, su rika debe miki kewa, na san ba za a rasa wani daga familynki da yake raye ba, From now on babu abun da zaki nema ki rasa Inshallah, babu abun da ya dace da ke a yanzu sai farinciki!” Ta yi kasa da kanta tana hawaye. “Da gaske na rasa kowa kenan! Da gaske ni kadai zan rayu? Taya farinciki zai zama a tare da ruhin da bakinciki ya zagaye, kuka da damuwa suka masa masauki? Har yanzu na kasa yarda a duniya na ke, an raba ni da kowa” Ta fashe da sabon kuka tana jin wani irin bakinciki mai taba zuciya yana ratsata. “Faranta ran mutane na daga cikin abun da yake saka ni farinciki, musamman irinki, ta ya mutum mai imani zai same ki a irin wannan halin kuma ya kasa taimakonki? Ki saka a ranki daman can haka Allah ya rubuta kuma akwai irinki da yawa” Haka ya dage yana ta kokarin kwantar mata da hankali kamar na shi ba. So yake ta ji cewar ba ita kadai bace a cikin halin damuwa, so that ta kwantar da hankalinta, gudun kar abun yai mata yawa. “Ki ci abinci yanzu sai na yi ma likitan magana, ya ba ku takardar sallama” Wannan karon har dan guntun murmushi a fuskarsa. “Bakina akwai datti da yawa” Ya dan wara ido yana jin haka yasa mai tsabta ce. “Okay bari muje gida gaba daya sai ki wanke bakinki a can ki karya” Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai ya rufe abinci ya mike tsaye ya fice daga dakin. Be dade ba ya dawo rike da wata takardar sai wasu nurse biyu bayansa, su suka dauke ta suka saka ta a Wheelchair. Shi kuma ya dauki abincin kadai ba tare da ledar fruit din daya kawo ba sai kuma magani. Nurse din ce ta turo ta, shi kuma yana gaba har suka isa gurin motarsa, back seat ya bude musu suka saka ta sannan ya bude bayan motar suka saka masa wheelchair din, after ya rufe ya nufi driver seat ya bude ya shiga ya zauna. “Yanzu zaki ga sabon gidanku da kuma yan'uwanki” Ya fada ba tare da ya juyo ya kalleta. “Na gode Yallabai” Ta fada da muryar kuka, domin a yanzu ko kalma yan'uwa ta ji sai ta tuna da nata. “Talba sunana, daga yanzu ni yayanki ne, kin zama kanwata gashi kina da sunan Momy kin zama Shalele” Bata ce komai ba, har ya fara tukin motar ya fice daga asibitin, yana hawa babban titi ya fara gudu kamar yadda ya saba, sai jikinta ya fara rawa ta fara tsorata, abun da ya faru ya taba mata zuciya kuma ya shiga kwakwalwarta ya zauna, abu kadan sai hankalinta ya tashi. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ta furta da karfi tana runtse idonta. Hakan yasa shi juyowa ya kalleta sai ya rage gudun da yake, sai dai be ce mata komai ba, ita kuma bata yarda ta bude idon ba har suka isa gidan da bata san yadda yanayinsa da tsarinsa ba. Harabar gidan ya faka ya motarsa sannan ya fito ya dauko Wheelchair ya aje ya bude back seat din yai ma daya daga cikin mai aikinsu hannu, sai gashi ya zo da gudunsa. “Ka dora Wheelchair din nan a kofar falo, sai ka saka yarinyar nan ciki, ka dauko abinci yana ciki Motar” Ya fada yana kallon motar Daddy dake fake, hakan ke tabbatar da Daddy be fita ba kenan. Wayarsa ya ciro daga aljihu da zimmar kiransa sai ya hangoshi ya fito direbansa na rike da jakarsa, da sauri ya nufi inda yake Daddy na hango shi sai ya tsaya jikin motar yana jiran karasowarsa. “Daddy good morning” “Morning Mu'az har na fita?” “Yeah muna da meeting a office, amman ka rasawa na dawo na fada maka wani abu” Daddy ya masa irin kallon nan dake nuna ina saurarenka. Tun daga biri har wutsiya ya fedewa Daddy komai, ba karamin tausayin yarinyar Daddy ya ji ba. “Yarinyar tana ina?” “Gata acan na zo da ita, ina neman amincewarka, idan kuma hakan be maka ba, zamu iya duba wani gurin sa zamu iya ajeta, saboda gida marayunmu yawanci kanana ne ba su kai kamar ta ba, idan ma na aje ta a can zata sake shiga kadaicin ne” Daddy yayi murmushi jindadi ya kai hannunsa ya dafa kafadar Talba. “Ina alfaharin da kai Mu'az ka ci sunana kuma baka rago komai daga halina ba, mu gidan nan ai kullum muna marhabun da baki ne, kuma ni uban marayu ne karka manta da wannan, ko da ace tana da kowa nata a raye ta so zama da mu zan dauke ta kamar ya balle ma tana marainiya, ka yi tunani mai kyau ka ga yanzu kun zama ku biyar, Allah ya muku albarka” Talba yayi murmushi. “Thank you Daddy, amman Momy ba lallai ta yarda ba” Daddy yai masa wani kallo. “Momy ke da gida ko ni?” “For now ita ke da gidanta...” “Really to bari mu ga idan kai aure kai ne da gida ko matarka” Talba yayi murmushi. “Wannanai dabam, ni Talba ne kai kuma Daddy ne” Daddy ya girgiza kai yana murmushi tare da zolayarsa. “Za'a min izinin ganin yarinyar?” Ban da dariya babu abun da Talba yake, ya wuce gaba Daddy ya biyo bayansa, sai dai hakan be hana su isa kofar falon a tare ba. [3/7, 11:34 AM] Zatuuu🦋: Talba ya danna door bell ba dadewa aka bude masa sai ya matsa Daddy ya fara wuce sannan shi ma ya shiga. A tsakiyar falon ya hango Aminatu zaune a wheelchair ta sanda kanta kasa hawaye na sauko mata, Kabir na tsaye gabanta. Momy kuma na zaune a kujera daya ita da Leila suna kallon ikon Allah. “Ita wannan bata magana ne?” Kabir ya tambaya yana kallon Talba. “Ka dame ta da surutun ne ko?” Cewar Daddy. Sai Kabir ya ce. “Sunanta kawai na tambaya, sai ta rufe ido ta fara min kuka” Daddy ya karasa kusa da ita yana kallonta cike da tausayawa. “Sannu Allah ya baki lafiya” Bata bude idon ba har sai da ta ji kamshin turaren Talba, sannan ta bude ido ta kalli inda take jin kamshin na fitowa, ido biyu suka yi sai dai nata idon cike suke da hawaye. “Ya sunanta?” “Sunan Momy” Talba ya fada, sai Daddy yai murmushi ya kalleta. “Yar gata ce kenan, sunan matata kuma uwar yayana kin ga babu wanda zai taba ki a gidan nan! Ki kwantar da hankalinki ki dauki kowa kamar dan'uwanki ni kuma na miki alkawarin zama mahaifinki da yarda Allah, duk abun da zan iya yi ma yayana zan miki Inshallah” Talba yayi murmushi, sai Kabir ya wara ido. “Ji wannan daga zuwanki zaki karbe mana fada, bari fitinanniyar ta zo zata zalzaleki” Daddy ya girgiza kai yana dariya. “Aa yanzu ita ce auta, daga gani Amal zata girme ta ai” Ya fada sannan ya dago ya kalli Momy. “Hajiya karaso ki ga yar da muka samu kyauta daga Allah” Momy ta taso daga inda take zaune tare da Leila suka karaso inda Aminatu, sai da Momy ta kare mata kallo sannan ta ce. “Ya kamata a nemi izini na kamin a kawo ta, amman sai ganin musaka nai a falona, saboda ban isa da gidan ba” “Na fara magana da Daddy ne, kamin na yi magana da ke, ni ma ban yi zaton hakan zai faru ba sai da likitan ya fada min sai na ga kamar hakan ya dace” “To be dace ba, be kamata ka dauko min wata bare can ka kawo min a gida ba, yarinyar da ban san daga inda ta fito ba” A hankali Aminatu ta dago ta kalleta sai ta maida kanta kasa. “Momy karki tsorata mana, ba nan ya kamata ku yi wannan maganar ba” Kabir ya fada. Sai Momy ta watsa masa harara. “Idan na tsoratata sai ka saka zane ka goya ta ai” Daddy ya hade rai yana kallon Momy cikin rashin jindadi. “Bana son maganar nan, Danki zai fada miki komai” Sannan ya kalli Aminatu dake hawaye. “Aminatu ki kwantar da hankalinki kin ji, mu iyayenki ne” Ta kasa dagowa ta kalleshi ma balle ta ce masa komai, har sai da Talba ya kirata da sunan da Inna take kiranta da shi. “Auta...” Sai ta kalleshi da sauri tana jin wani tsam a jikinta. “Ki cewa Daddy kin gode” Ya fada yana mata murmushi kadan kamar na dole. Sai ta kalli Daddy da idanuwanta da ke zubar da hawaye. “Na gode...!” “Oh Really.. Zai ka mata umarni zata yi magana kenan” Kabir ya fada yana kallon Talba, murmushi kawai Daddy yai ya nufi kofar fita. “Zan tafi kar na yi latti, sai a gyara mana daya daga cikin dakunan da suke kasa nan” “Da a BQ na so ta zauna” Talba ya fada. “Why BQ ga dakuna a cikin gida? A bar ta nan BQ ai na amsu aiki ne, sai na dawo” A karon farko Momy ta kasa ce masa Allah ya tsare balle har tai masa rakiya. Bayan Daddy ya fice Talba ya risina gabanta ya nuna mata Leila. “Sunan wannan Leila kanwata ce, kuma matar da zan aura, akwai wata Amal tana makaranta, wacan kuma Momy mahaifiyarmu, muna da masu aiki biyu Mairo da Zulai idan kina bukatar wani abu ki fada musu za su miki. Wannan kuma Kabir, shine likitan da zai rika dubaki shi ma kuma kanena ne” Talba na ajewa Kabir ya tari numfashinsa. “No no no Malam shekara biyu ka bani ba, sai wani ji kake da kanka wai kanenka kar ta dauka da gaske” Talba be ce komai ba, daman ba komai yake saka shi dariya ko magana ba, sai ya kalli Momy. “Momy ina son zamu yi magana” Momy ta dauke kai daga kallon Aminatu ta kalli Talba tana jin wani irin zafi a zuciyarta. “Har a bada dan wani br taba zama nawa ba, nawa kuma be taba zama dan kowa ba” Kusan wannan ne karo na biyu da wata kalmar ta fito daga bakin Momy da bata masa dadi ba, bayan wacan karo da shigarwa Leila. “Momy yarinyar nan marainiya ce, ba uwa ba uba, kuma ban daukota na kawo ta nan ba sai dan nasan zamu iya kula da ita, kuma kin san muhimmanci rikon maraya, and ko dan ni ya kamata ki daga mata kafa...” “Saboda gaka Ubana? Ko kuma saboda mu muka fi kowa son lada? Waya sani ko karya ta tsara maka? Idan ma da gaske ne mu muka kashe iyayenta ne da responsible din ta zai dawo kanmu?” Da mugun mamaki Talba yake kallonta jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta, sai dai be ce mata komai ya kalli Aminatu ya dauke kai ya kalli Kabir da yanayinsa ke nuna be jidadin kalaman Momy ba. “Kabir kira Mairo” Momy ta ja tsaki ta nufi upstairs ta bar Leila tsaye tana kallon ikon Allah. “Mairo...” Kabir ya kwala mata kira, ya san daga muryar ne ba zai iya ba shiyasa ya saka shi kiranta ba wai dan yana nufin ya tafi yaje ya kirata ba. Da gudu Mairon ta fito daga kitchen hannunta da kumfa. “Gani ranka ya dade” “A wanke mata baki, a bata abun karyawa, sannan a gyara mata dakin kasa, ki taimaka mata tai wanka sai dai kafarta na ciwo sai kin yi a hankali” “To ranka ya dade” Ta amsa da sauri, shi kuma ya juya ya fice daga falon ya bar Aminatu sai Kabir da Leila. “Let me help you with brush and toothpaste” Kabir ya fada sannan ya juya ya nufi upstairs. Leila ta bishi da kallo sai da ya haye gaba daya sannan ta kalli Mairo tana yamutsa fuska. “Idan kika mata wanka, sai Momy ta ci ubanki” Mairo ta kalleta da duba na rashin jindadi. “Haba Leila kina ganina kin san na yi kanwa ta uku da ke, be kamata ki ce min haka ba, ko da kuwa kin san Hajiya zata yi fada ne, amman be dace ki zage ni ba” “Okay miya dace na fada miki? Ki zo aiki gidanmu sannan ki yi tunanin zan girmamaki? Koya min magana zaki yi ko mai” Yanayin yadda Leila ta rufe Mairo da masifa ne ya saka jikin Aminatu rawa, sai ta fashe da kuka. “Mtssss munafuskar banza” Leila ta fada tana hararar Aminatu, sannan ta nufi kofar baya ta falon tana danna waya. 21 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* BATURIYA POV. Sai da Ramlee ta shiga da ita har cikin falon sannan ta fita ta barta. Baturiya ta dade a falon sannan ta ji tsayarwar Mota harabar gidan, sai ta leka ta window ta hangoshi ya fito daga motar rike da wata karamar jaka, dayan hannunsa kuma rike da Makalle da waya a kunne. Babban mutum ne a haife ya haife ta kuma ya haifi yayunta, irin mazan nan ne da ake kira da sugar daddy. Wani irin faduwa ta ji gabanta yayi, sai hakan be hanata daidaita natsuwarta, Ta gyara zamanta sannan ta kunna wayarta ta saka ta silent, gabanta ya tsanata bugawa ne a lokacin daya turo kofar falon ya shigo, abun ka da wanda be saba ba sai ta mike tsaye tana kallonsa, shi kuma ya kare mata kallon tun daga sama har kasa sannan yai mata alama data zauna, sai ta koma ta zauna tana kirkiro murmushi, a kujera dake kusa da kofar ya aje jakar hannunsa sannan ya karasa kusa da ita yana murmushi ya zauna. Ita ma murmushin ta sakar masa, sai ya kai hannu ya shafa fuskarta ya nuna mata fuskarsa alamar tai masa kiss, ba musu ta mika bakinta ta sumbanci gafen fuskarsa sai ya rumgumeta yana shafa bayanta. “Yanzu dai Hajiya ki bari idan na dawo gida hankali kwance sai mu yi maganar, kisan Muhammad baya jin maganar kowa a yanzu so dole lallabashi za ku yi, idan yaji yana son ta ya amince daman abun da muke nema ne tun da yar'uwarsa ce, idan kuma yace sai wacan sai mu masa addu'a” Ya fada yana gangarowa da hannunsa ya cire mata zip din atamfar ya fara murza fatarta ta baya dake cike da taushi da fari. “Yanzu muna da meeting, idan mun gama kuma zan je na ga gwana saboda maganar kudin kwangilar nan, ba zan dawo da wuri ba sai dare” Baturiya ta yi shiru tana sauraren yadda hannunsa ke ta yawo a jikinta, Sai wani abu take ji na rashin jindadi, ta saba mu'amala da Faruq balle tace ko dan bata saba bane, wata kila kuma saboda wannan sabo ne tsabanin wacan da take samu lada. “Eh ya same ni da maganar ai, shiyasa muka taho tare sai kuma na buge wani mai acha, sun tafi da shi su kai shi asibiti, idan ya dawo nace ya same ni a gida mu yi maganar, so zamu zauna gani ga ki gashi sai mu yi maganar, sai anjima” Ya kashe wayar gaba daya yana kallon Baturiya. “Yan mata ya kike?” “Lafiya kalau ya aikin?” Ta amsa cikin rashin sakewa, shi kam sai murmushi yake abun nema ya samu. “Alhamdulillah” Ya fada yana kokarin cire mata dankwalin kanta gaba daya, ya fara shafa gashin kanta, sannan ya kamo hannunta ya saka a kirjinsa. “Ba za a taya ni cire tufafin ba agajiye nake fa” Sai da ta hade yawun bakinta sannan ta rika babbar rigarsa ta cire masa, da haka wasan ya canja salo, sai dai duk inda ya taba a jikinta sai ta ji wani iri musamman ma daya raba ta da rigar jikinta yana shafa kirjinta. “Taso mu watsa ruwa yadda zamu jidadin bachi” Ta dan yi murmushi ta mike tsaye, sai ya rika hannunta suka bathroom dinsa, a tare sukai wankan, yana ta labarta mata karamar haukar data same shi a lokacin da Ramlee take nuja masa honta a wayarta. Bayan sun gama suka fito sai kallon tsiraicin yake yana yabawa, tare da kai hannu ya taba inda yake jin ya masa. Kusan duk abun da Ramlee ta karantar da ita sai da ta aikata masa har abun da bata taba yi ma Faruq ba da sunan ya samu gamsuwa sai da tai ma Alhaji Haroon, sannan ta biyewa son zuciyarta ta budewa kanta babban file daga cikin manyan manyan files din zunubai. Ba shi ba ita kanta kanta ta samu gamsu irin wanda bata taba samu ba, sakamakon kayan matan da Ramlee ta bata ta sha, balle kuma shi da yai kamar zai haukace. Nan da nan bachi yai gaba da shi, ita kuma ta tashi zaune ta daura tawul ta fito falo inda ta bar wayarta ta dauka tana dubawa sai ta samu miss calls biyu daga Fahat, jiki na rawa ta mayar masa da kiran daman can yana cikin ranta tun da ta shigo gidan take jiran kiransa. Ringing daya yai picking “Na yi fushi yau duk ban ji muryarki ba kuma na kira wayarki na ji ta a kashe, na sake kira baki daga ba” “Bana kusa da wayar ne, kasan idan ina kusa da wayar babu abun da zai hana ni dagawa, ni ma ai tun dazun nake ta jiran kiranka” “Miyasa baki kira ni ba? Anyway yanzu dai bari na miki wani albishir na yi magana da Daddy, na fada masa cewar na samu mata” Hannu ta saka ta dafe kirjinta, farinciki da faduwar gaba suka zo mata a lokaci daya. “Da gaske? Amman me ya ce maka?” “Me zai ce min kuwa, daman ai sun dade suna jiran ranar da zan fada musu na samu wanda nake so, even though akwai yan'uwa da ake son hada ni da su, amman ni bana son auren zumunci gaskiya” “Allah yasa ya amince dai” “Zai amince ma, fatar ba zan samu matsala daga bangarenki ba” “Aa babu wata matsala Inshallahu” “Haka nake son ji, ya kike?” “Lafiya kalau, kai fa?” “Ni ma kalau nake” Sama sama take amsa masa duk wata magana da yake mata saboda bata son Alhaji Haroon ya ji tana waya da wani, ko da be nuna mata baya so ba ta san be dace tan a guest house dinta tai haka ba, domin maza suna da kishi no matter how old and young they are. Bayan sun yi sallama ta kashe wayar ta koma cikin dakin ta hau gadon ta kwanta, ba jimawa bachi yai gaba da ita. Sai da aka yi sallah azabar suka farka kowanensu ya gabatar da wanka sannan suka yi sallah. “Baby Fee'at me zaki ci na aika yarona ya siyo mana?” “Shimkafa jalof” “An gama gimbiyar mata” Ya fada har wani kashe ido yake, ita kuma tai murmushi, tana sauraren wayar daya dauka ya kira yaronsa fada masa abun da suke bukata. Yana aje wayar ya mika mata hannunsa. “Ta so zo nan” Babu kunya balle tsoron Allah haka ta sake zuwa ta biye masa suka sake tarawa kansu wani babban zunubin, suna gamawa yaronsa ya kira wayarsa ya fada masa ya siyo. “Ka aje a falo” Ya fada masa sannan ya aje wayar ya tashi ya fita, ko da ya fito yaron ya aje abinci yayi ficewarsa, daukowa kawai yai ya shigo da shi ciki. Jalof kawai ta bukata amman ya hado mata da farfesun kayan ciki da naman kai, ga kuma lemu mai sanyi da soyayyen naman kaza, zaunawa tai ta ci ta koshi nas, sannan ta tashi tana jindadi, rabon da ta ci abincin hotel har ta manta. Bandaki ta shiga ta sake yin wanka ta fito, sai ya kalleta da mamaki. “Wanka kika yi? Ai bamu gama ba, ni fa wuni ake min ba zaki koma gida ba sai dare, Ramlee bata fada miki ba” “Aa bata fada min ba, amman tun kai ka fada min ai ya wadatar” Murmushi yai ya bude nasa abinci ya fara ci yana yaba yadda ya sake me, da kuma irin gamsuwar daya samuna jikinta, ba karamin dadi ta ji ba domin Faruq ba mutum ne mai yaba mata ba idan ma ta gyara masa shimfidar, baya daga cikin mazan nan dake nuna jindadinsu a gurin matansu, ba dan komai ba sai dai be dauki yabon a bakin komai ba. Kamar yadda ya bukata haka ta biyewa sharholiyarsa suka wuni suna raya sabo, sai bayan sallah Magariba ya rabu da ita tai wanka ta shirya cikin tufafinta, tana kokarin daura dankwalinta ta dauko jakarsa ya bude ya kirga dubu dari hudu ya aje mata. “Ga wannan, sai kuma yaushe?” Juyowa tai ta kalli kudin, a take gabanta yai mugun faduwa, sai dai bata yarda ta nuna matsa yawan kudin sun tsoratata ba sai tai murmushi. “Sai kuma ranar daka tashi Alhajina” “Ni kullum ai ban ki mun hadu ba, idan son samu ne ma tafiyar nan da zan yi China naje dake, kin taba zuwa china?” “Aa Wallahi” “To ki shirya dake zamu je” Ta yi murmushi tana jin wani kalar dadi ya sakota gaba, duk kuwa da bata da tabbacin zata amince ta bishi din ko kuma aa, saboda aure da kuma Fahat. Wayarsa ya mika mata.. “Saka min number ki a nan, ya kamata ace muna da number juna, ba dole sai mun biyo ta bangaren Ramlee ba” Ta karbi wayar ta saka masa number, sannan ta dauki kudin ta saka a jakarta ta fito falo ta dauki wayarta ta saka mayafinta tai masa sallama ta fice tana mamakin yawan kudin daya bata, wannan karom bata yi shakkar saka gyaren ba saboda dare ne kuma a yanzu bata da kwaliya kamar dazun. FARUQ POV. Sai da ya fara biyawa gurin Mama ya gaisheta suka dan taba hira sannan ya kama hanyar zuwa shagonsa. Ba su karasa ba wani mai mota ya bugu babur din da yake kai, shi da mai achaban suka fadi gefen titi. A take mutane suka yo kansu da gudu mutumen daya buge su ma faka motarsa yai gefe ya fito yana dubasu. Kana ganinsa ka san babban mutum ne, domin shaddar jikinsa ma kadai abun kallo ce balle kuma bakar motar data buge su, a tare da shi a akwai direba sai kuma wata jar mota dake bayan tasa da alama take masa baya take ko kuma a tare suke. Daga mai achaban har Faruq daya ji ciwo a kafa zaune sukai mutane na musu sannu. “Akwai asibiti nan kusa?” Mutumen ya fada yana kallon direbansa, sai saurayin dake tsaye kusa da shi ya amsa masa. “No Abba ba kace kana uzuri ba, ka tafi kawai ni ni zan kai su” “Okay Muhammad idan an dubasu ka samu abun aka basu, idan mun hadu gida anjima zamu yi magana, yanzu jirana ake” “Okay” Dan nasa ya amsa sannan ya rika Faruq da yafi jin ciwo ya mikar da shi tsaye. “Muje ga motana can” Ya nuna masa jar motar da take bayan ta mahaifinsa, kamin su karasa gurin motar har mahaifinsa ya shiga tashi motar direban yaja motar sun kama hanya. A front seat ya zaunar da Faruq sannan ya bude back seat din ya ce da mai achaban ya shiga. “Aa kaje ka kai shi, ni ban ji ciwo ba” “Ka tabbata?” “Inshallah” Sai ya rufe motar ya rufe inda Faruq yake zaune, ya zagaya mazaunin direba ya kirga dubu biyar ya mikawa mai achaban, sai ya karba yana godiya daman haka tafi masa dadi. Ya hau achabansa ya kama hanya shi kuma ya shiga motar yaja Faruq suka isa asibiti. “Sannu ko kana da asibitin da kake zuwa?” “Aa” “Okay bari muje ta nan kusa, ai zaka iya jurewa ko?” “Haba sai kace ba namiji ba” Faruq ya fada yana murmushi, shi ma murmushin yai ya cigaba da tukin har suka isa asibitin, aka duba kafar aka bashi magani suka rufe ciwon. Sannan ya sake daukoshi a motarsa suka suka nufo unguwarsu, suna tafe suka hira kamar daman can sun saba, be yarda ya bar Faruq a bakin titin ba duk kuwa da kasancewar mota bata shiga har kofar gidansu, sai ya fito ya taka masa har kofar gidan yana masa wasa wai kar madan tace sun buge mata miji, Faruq murmushi kawai yai ya kai hannu ya taba gidan sai ya ji shi a rufe, key dinsa ya dauko ya bude ya shiga ciki. “Ina jin bata nan, daman tace min tana da biki zata je” Fada a kokarinsa na kare matarsa duk da kasancewar mutumen be san Rafi'a balle har ya munana mata zato. “To a gaishe ta, kuma a bata hakuri ga kuma wannan ayi cefane” Ya fada yana mikawa Faruq dubu goma. “Aa haba ai abu ne da Allah ya kawo...” Kamin Faruq ya karasa Mutumen ya saka rantsuwa. “Wallahi sai ka karba, kai shedan kadai ke maida kyauta” Murmushi Faruq yai a karo na barkatai ya karbi kudin yana masa godiya. “Na manta ban tambayi sunanka ba” “Faruq” “Ni kuma Muhammad Fahat na gode sosai Allah ya tsare gaba” “Ameen” Daga haka Faruq ya karaso cikin gidan shi kuma ya juya ya kama hanyarsa. A falo Faruq ya zauna yana kiran Baturiya a waya domin jin inda take, sai dai bata dauka ba daga baya ma sai yaji wayar a kashe, hakan kuma ba karamin bata masa rai yai ba, ba yau ta saba fita ba tare da izininsa ba sai dai ya fi jin zafin fitarta fiye da koyaushe. Cikin karfin hali ya shiga uwar daka ya tube tufafin jikinsa yai wanka ya canja wasu kayan sannan ya kwanta, nan da nan bachi yai gaba da shi. Kiran Allah azahar ne ya tashe shi, ya tashi yai alwala ya fita masallaci a can ya hadu da dansa da yabi yaran makotansu suka tafi masallacin a tare. Kusan kowa da ya gaisa da shi sai ya masa sannu da fatar Allah ya tsare gaba, shi kuma ya amsa da Ameen bayan ya labarta musu abun da ya faru. Sultan na ganin mahaifinsa ya rike shi suka dawo gida tare. Abun ka yaro yana shigowa ya fara tambayar Faruq ina mamansa. “Dady Momy bata dawo ba?” “Ina ta tafi?” “Bata fada min ba, amman na ji tana ta waya da yawa tana ta waya har ta ce ummouy” Ya nuna yadda tai kiss din da bakinsa. Faruq ya hade yawu yana jin wani bakinciki na taso masa. Haka ya wuni a gidan daga shi sai dansa girkin rana ma shi ya girka duk da kasancewar akwai ciwo a kafarsa, tun yana tunanin zata dawo da la'asar bata dawo gidan ba sai bayan magariba ana daf da kiran sallah isha'i wani gurin ma har an fara kiran. Sannan ta shigo da dan faduwar gaba, ganin cewar Faruq ya rigata dawowa, ta shigo falon da sallama, ya amsa mata ya mike ya fice ya bar mata falon, sai ta bishi da kallo kamin ta kalli danta. “Sultan yaushe Dadynka ya dawo?” “Tun da rana har ma ya ji ciwo a kafarsa” Bata sake cewa komai ba ta nufi dakinta ta aje jakarta a inda ta saba ajewa sannan ta fita tsakar gidan da saurinta saboda kashi ya matseta. Ko da ta fito ta dauki buta ta shiga bandakin yana tsakar gidan yana alwala, bayan ta shiga bandaki ya shigo falo daga inda yake tsaye ya hango Sultan na ciro kudi mai yawa a jakar Baturiya, da sauri ya karasa ya kara bude jakar da kansa yana duba kudin. Bandir din yan dubu daya ne har guda hudu sai kuma karamin canji dake kasan kudi. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya furta cikin wani irin yanayi na tsoro da bakinciki. Kamar an dasashi haka yai tsaye a gurin har ta fito daga bandakin ta shigo dakin, tana ganinsa tsaye kusa da jakarta sai ta yi tsaye a bakin kofar tana kallonsa. Tsayin da tai ya bashi damar kare mata kallo, lace din dake jikinta tsadadden lace ne da karfinsa be kai ya siya mata shi ba, sai dai ba zai munana mata zato ba saboda tana da yayyun dake auren masu rufin kudi, sai dai bata saka irin wannan tufafin sai zata je guri na musamman. “Ina kika samu wannan kudi?” “Ajiya aka ba ni” Ta amsa kai tsaye kamar da gaske, sai ya watsar da kudin ya daka mata tsawa. “Karki raina min hankali mana, wa ye zai baki ajiyar kudi mai yawa haka? Ina kika je?” “Gida gurin Umma” Ta amsa tana hade fuska. “Rafi'a kin wuce gona da iri, ban taba tunani zaki iya aikata abun da kika aikata ba, kuma abun bakinciki da jinani a jikinki” “Faruq.. Zarkina kake yi kuma? Zargi fa yana kashe aure” “Waya baki ajiyar wannan kudin?” “Ba zan fada ba, tun da zargina kake ai sai ka cigaba kuma Allah sai ya saka min, ka cutar da ni kuma yanzu ka fara bina da kazafin zina” Ta fashe da kuka. “Juya ki koma inda kika fito Ya fada yana nuna mata kofa. “Wallahi ba inda zan je sai idan sakina kai” “Tafi na sake ki saki daya, kuma duk kika cutar min da yaya Allah ya isa tsakanina da ke” Ta dora hannu biyu akai tana zaro ido kamar za su fado. “Faruq ka sake ni fa kace...?” Be bi ta kanta ba ya rika hannunsa dansa ya ratsa gefenta suka fice a fusace zuciyarsa na masa zafi. Zaune tai a bakin kofar dakin tana kallon kudin, ba kuka take ba, bata jin ma kuka ko bakinciki yana kusa da ita, farinciki kudi data samu sai ya koma mata ciki. AMINATU POV. A tsakar falon aka barta babu wanda ya sake bi ta kanta Mairo ta koma kitchen bayan ta karbi brush din da Kabir ya kawo mata ya fice, Leila kuma ta haye sama ta shige dakinta ya sauki wayarta ta kira Madina ta labarta mata abun da ya faru. “Leila wata mace da ba yar kowa ba, ba zata taba samun gurbi a zuciyar Talba ba, saboda yana ji da kansa sosai ba zai yarda ya auri wanda ba yar kowa ba, balle kuma yar gudun hijira” “Ni ma ai ban ce sonta yake ba na san ai ba zai taba sonta ba, amman ina jin zafin abun da yake mata, taya zaka tsinci yarinyar ka kawota gidanku shi yafi kowa tausayi ne” “Yanzu yarinyar tana nan gidanku?” “Eh, tana nan yace Mairo tai mata wanka ta bata abinci ni kuma na hana, kuma ko ban hana ba Momy ma b zata bari tai ba” “Gani nan zuwa yanzu, zan zo na ganta” “Okay” Ta kashe wayarsa sannan ta kira Ali tana fada masa abun da ya faru. Ba'ayi minti talatin ba, Madina ta iso gida, tana faka motarta ta nufo entrance din da saurita, kamin a bude mata kofar ta danna door bell din kusa sau uku, sannan Zulai ta bude mata. “Sannu da zuwa” “Yauwa sannu da gida, ina Momy?” “Tana sama” Ta shigo cikin falon tana rabon ido, sai ta hango Aminatu zaune a wheelchair kanta a kasa, karasa tai kusa da ita ta duka tana kallon fuskarta, wannan karon ba kuka take ba sai dai idonta a rufe yake ba kuma bachi take ba. “Hey...” Madina ta fada, sai Aminatu ta bude idonta a hankali ta kalli Madina. Sai Madina ta sakar mata murmushi. “Sannu Sunana Madina ke fa?” Aminatu ta maida idon ta rufe. Sai Madina ta mike tsaye ta kalli Zulai. “Ina Mairo?” “Tana kitchen Mairo” Ta karasa tana kwala mata kira. Sai ta fito tana amsawa. Sai da suka gaisa da Madina sannan tace. “Ba a mata wankan ba?” “Leila tace kar na yi, har buroshin da Kabir ya bani ban mata ba” Madina ta yi murmushi. “Amman Mairo baki san waye Talba ba, da zai baki umarni ki bini ki bi na Leila, ina brush din?” “Na aje shi a dakin da daya ce a ware mata?” “Wane daki?” Mairo ta nuna mata hanyar corridor dake kasa inda dakunan uku suke. “Na farkon” Zagayawa Madina tai ta fara tura wheelchair din, ta nufi corridor da ita, suna isa ta tura kofar dakin ta sannan ta sake turata suka shiga ciki. Bandaki ta nufa da ita ta kunna fanfo ta zuba makilin din ta a brush ta cire karamin gyarenta ta aje gefe tare da jakarta ta fara wanke mata baki, bayan ta gama ta taimaka mata ta cire tufafin jikinta ta daura mata tawul ta murza nata inda zata iya a jikinta ta bar mata ragowar ta karasa wankewa sannan ta dauraye mata jikinta. Ba tare data raba ta tawul din dake jikinta ba, bayan sun gama ta fito da ita, sannan ta fita dakin ta nufi kitchen abun da ya rage na safe ta dauko ta dawo da shi dakin ta dora saman karamin gadon ta fara bata. “Zan iya ci da kaina” Aminatu ta fada ganin tana kokarin kai mata abincin a baki, sai ta girgiza mata kai tana murmushi. “No bari na baki da kaina” Ta shiga bata abincin a hankali, kamar daga sama Talba ya shigo dakin Zulai na biye da shi rike da jakar Candy Collection, tsaye yai bakin kofar yana kallon Aminatu dake kan Wheelchair Madina kuma na zaune a bakin gado suna facing din juna tana bata abinci ga tawul din jikinta a tsike, wani irin dadi ne ya lullube Madina daman abun da take nema kenan Talba ya shigo ya sameta tana aikin da bana Allah ba. 22 *Khadeeja Candy* Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Ta yi saurin aje abincin ta mike tsaye tana kallon Talba. “Sannu da zuwa” Aminatu ta juya a hankali ta kalleshi, sannan ta kalli Madina, yadda ta ga yanayinta ya sauya tana kokarin shiga natsuwarta kadai ya isa ya saka ta fahimci cewar Madina tana tsoro Talba sosai. Shigowa yai cikin dakin fuska babu annuri, ba dan komai ba sai dan ya san irin amintar dake tsakaninta da Leila. Juyawa yai ya kalli Zulai. “Ba na ce Mairo tai mata wanka ba?” “Eh ranka ya dade, Leila ce ta hana ta” A take yaji ransa ta bace domin ya tsani ya saka mutum wani abu be yi ba, musamman ma ace wani ya hana shi, wanin ma wanda shi ma zai iya controlling dinsa kamar dai yadda Leila tai. “Ya kai tawul din jikinta ya ke da ruwa?” Ya tambaya yana kallon Madina. “Na taya ta wanka ne, to bata yarda ta cire tawul din ba shi yasa ya jike, kuma bata da wani tufafin da za a canja mata, kuma a san idan na tambayi Leila ba lallai ne ta bata ba” Talba ya kalli Aminatu sai kuma ya sake kallonta. “Waya ce ki mata wanka?” “Babu, ko da na shigo tana falo ne, sai na tambaya Mairo ta fada abun da ya faru, sai na yanke shawarar taimaka mata, amman ka yi hakuri idan hakan ya bata maka rai ba zan sake ba” Ta karasa tana risinawa a gabansa kanta a kasa, kamar wanda take a gaban sarki tana neman yafiya. Da hannu Talba yai mata alama data tashi tsaye, sai ta mike tsaye. “Zan iya cigaba da bata abinci?” Ta tambaya cike da ladabi kamar mai tsoronsa, Talba ya kalleta da duba na mamaki irin da gaske? Kamin ya kalli Aminatu da idonta ya cika da kwalla tana girgiza masa kai. “No” Ya amsa mata still yana kallon Aminatu. Kamin ya juya gurin Zulai. “Aje tufafin a can, ki taimaka mata ta saka” Da sauri Aminatu ta sake girgiza kai hawaye na sauko mata. Hakan ya saka Talba yai saurin dakatar da Zulai dake kokarin bude kayan. “Bar shi kawai tafiyarki” “To ranka ya dade” Ta amsa sannan ta fice da sauri, kana ya kalli Madina dake tsaye tana kallonsu. “Excuse me” Murmushi ta sakar masa alamar okay sannan ta fice da saurinta. Sai Talba ya karaso gurin Aminatu. “Idan kina son wani abu, ko kuma baki bukatar wani abun, ba sai kin yi kuka ba zaki iya yin magana ko ki yi alama da hannu ko da ido ko da kai, ba wai kullum ki yi ta kuka ba” Ta saka hannu ta share hawayenta. “Ki ce to zan yi haka” Ta maimaita abun da ya bukata da muryar kasa kasa kamar mai rada, hakan yasa shi risinawa ya kai kunnensa kusa da bakinta. “Fadi na ji” Ta sake maimaitawa saitin kunnensa. “Good, ki dai kuka ba komai ake yi ma kuka ba” “Ni ma ji nake kuka ya zo min” Ta fada a nan sai da ya sake kai kunnensa sannan ya ji abun da ta fada. “Okay na fahimta, yawan kuka zai iya zame miki matsala ne shiyasa, zaki iya canja tufafin da kanki?” Ta daga masa kai. “Okay ki duba tufafin da kike so sai ki canja” Nan a kan ta daga masa. Sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin yaja mata kofa, hannu ta kai ta dauki jakar ta bude ledar sama ta fara daukowa ta budewa sai tai arba da doguwar rigar abaya ash color, warware rigar tai ta soma sakawa daga zaunen da take, sannan ta cire tawul din ta aje a gefe ta daga kadan ta ja rigar zuwa kasa. ta daura mayafin ayabar a kanta sannan ta maida hankalinta gurin kofar tana sauraren shigowar wani, kusan kamar ta yi sara akan gaba ne, domin a tsakanin lurawa kofar ido da kuma kwankwasa kofar da akai ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. A hankali ya turo kofar dakin ya shigo idonsa a rufe alamar ba kallonta yake ba, domin bashi da tabbacin ta gama kintsawar ko akasin haka, duk da kasancewar ya bata mintuna daya kamata ace ta gama, ba kuma zai iya kiranta daga can wajen kofar ba ya tambaya idan ta gama. “Na gama” Ta fada kamar ta san manufarsa, sai ya bude idon ya sauke su akanta. “Ki karasa cin abincin, Zulai zata fitar da ke waje ki sha iska, ni zan tafi gurin aiki” Ta gyada masa kai, sai ya juya ya fice, ido kawai ta kurawa abinci ta kasa kai hannu ta dauka balle ta ci, ko dazun ma saboda yunwa ta matsa mata ne kuma Madina ta dage sai ta bata abincin. Ko da ya fito falon Madina na zaune a kan sofa, Leila kuma na saukowa downstairs. Kallo daya yai mata ya dauke kai ya maida gurin Zulai. “Idan ta gama cin abincin ki fito da ita ta sha iska” “To ranka ya dade” “Mairo da Zulai ni suke yi ma aiki, idan kana son a kula maka da wacan kazamar sai ka dauki mai aiki” Ya juyo ya kalli Momy dake tsaye dinning tana maganar, sai dai be ce uffan ya sa kai ya fice. Madina ta bishi da kallo cikin rashin jindadin furucin Momy, sannan ta kalli Leila. “Yar gari” “Kin ga abun mamaki a gidanmu ko?, gaba daya gidan nan neman hargitsewa yake” Madina ta kama hannu Leila ta zaunar da ita kusa da ita tare da rage murya. “Kina daina bari Momy tana ma Talba fada ko nuna be isa akan abu ba a gaban yan aiki, saboda kar su raina shi, ke ma kuma ki daina pls?” “Raini kuma na nawa? Ai ni na dade da raina wayonsa Wallahi, duk yadda yake ji da kansa yana wani mazurai ace zai dauko wata ya kawo a gidan nan har yana mata yar muryar mtsss” Ta karasa tana jan tsaki, sai Madina ta yi murmushi. “Leila kenan ba zaki gane ba, idan kan son mutum, lallaba shi kake kana nuna masa kauna, musamman Talba daya zama watsentsen mutum, yadda ya dauko yarinyar nan ya kawo sai ki nuna masa kin fi shi sonta, idan Momy tai masa abu ki nuna kin fi jin zafin abun...” “Uhmmm Madina kamar baki san wacece ni ba, kina tunanin zan iya wannan bautar? Ai ko aurensa nake sai ni na juya shi ba wai shi ya juya ji baki daina fada min magana kamar kin fini wayo” Madina ta sake yin murmushi a karo na biyu tana kallon Leila. “Ai na fiki wayo! Kuma very soon zan baki mamaki, ina fada miki gaskiya saboda baki da kawa kamar ni, nima kuma bani da kawa kamar ke, amman ba zan haramtawa kaina abun da Allah ya halattamin ba, kuma ba zan zabi cutar da zuciyata akan abun da nake ganinsa magani a gareta ba, ni da ke yake ne muke tsakanin zuciya da zuciya waye zai ci nasara? Allah shi ya bar wa kansa sani” Leila ta yi mata kallon rashin fahimta. “Ban gane ba?” “Ina yakar zuciyata ne ta fada miki gaskiya kuma ta nuna miki ita, ke kuma kina yakar zuciyarki ki hana ta daukar gaskiya” Ta karasa tana mikewa tsaye tare da daukar jakarta ta rataya. “Baki shiga kin ga yarinyar ba” Har ta yi kamar tace mata ai na ganta, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, domin ko da suka sauko sun same ta zaune, babu wanda yaga shigarta ko fitowarsa a dakin. “Okay muje na ganta” Leila ta nufi hanyar corridor Madina ta bi bayanta dakin kofar suka fara budewa sai suka hangota zaune a kan wheelchair din ta juyo tana kallonsu. “Kin ga musakar can, daya dauko ya kawo mana” Leila ta fada tana yamutsa fuska, sai Madina ta karasa kusa da Aminatu tana mata murmushi, sai da ta kawar da murmushi a fuskarta sannan ta juyo ta kalli Leila. “Ki daina haka, ke ma baki wuce Allah ya jarrabe ki ba, abun da Talba yayi abu ne mai kyau, kamata yayi ki taya shi sai ku ci ribar tare, taimakon maraya abu ne mai kyau ni kaina ba abun da nake so kamar wannan” Leila taja tsaki ta saki kofar dakin ta juya ta fice domin ta fahimci Madina ba zata gane abun da take nufi ba. Sai da ta fice sannan Madina ta rage murya ta kalli Aminatu. “Idan Talba ya dawo ki fada masa abun da Leila tace miki, da kuma wanda nace kin ji?” Uffan Aminatu bata ce mata ba, kuma bata nuna wata alama dake nuna ta ji ko bata ji ba. Madina ta mike tsaye tana sakar mata murmushi. “Zan dawo gobe na gyara miki kanki, wata kila ma anjima na sake dawowa, Allah baki lafiya” Ta fada sannan ta juya ta fice. Ko da ta fito Leila na zaune a inda suka zauna dazun tana tabin wayarta. “Ina Momy?” “Ta hau sama” Ta amsa mata ba tare data kalleta ba. “Tana sama” “Idan ta fito ki fada mata na tafi” Leila ta mike tsaye ta bi bayanta, rakata tai har gurin motarta, Bayan Madina ta bude motar ta shiga ta zauna ta kalli Leila ta ce. “Ina ganin kamar Talba ba zai iya son yarinyar nan ba, amman komai zai iya canjawa” Leila ta bushe da dariya. “Madina baki da hankali” “Really? Ai tausayi ne silar soyayya tun da har ya fara tausayinta, ba ki ga yadda yake son a kula da ita ba?” Wani irin zafi zuciyar Leila ta fara yi, ba dan ta yarda da maganar Madina ba, sai dan danganta alakar so da tai da Talba. “Madina kamar baki san waye talwba ba, yaran masu arziki basa aure sai masu arziki, amman duk wanda ya gaji arziki ya taso a cikinsa ya ginu a cikinsa ba zai taba son rabar talaka ba, a littafai ne ake wannan ko a fina finai, amman talaka sai talaka mai arziki sai dan arziki kaddara ma yana sonta kina tunanin Momy da Daddy za su saka masa ido yana aureta? Ni kuma yayi ya da ni?” Madina ta yi dariya. “Waya ga Leila da kishiya” “Har abada ba zan taba zama da kishiya ba” “Ko da ni ne?” Ta fada tana dariya, sai ita ma tai dariya. “Kin san wani abu? Taimako daya zan miki, ki yi yadda zaki iya yarinyar nan ta dawo karkashin kulawata” “Ya za'ayi haka ta faru? Kin san yanzu Talba ba yarda yake da ni ba, balle na bashi shawarar ya kai ta gurinki, tsaya ma me zai saka ya kaita gurinki?” “Saboda ya nisanta da ita, ki kuma ki samu kusanci da shi, amman idan tana gidan nan, kullum sai kun samu matsala da shi, hakan kuma zai ta lalata alakarku ne har ya kai inda ba a so” Leila ta yi shiru tana nazarin maganar, ta san gaskiya Madina ta fada sai dai tana ganin hakan kamar a dabara ba ne. “Kawai ki bari sai ina nan shi m yana nan, ki yi mata wani abun da zai zama na magana, daga nan sai ki yi rantsuwa ba zata zauna ba, sai ki bar min sauran aikin” Ta karasa tana kanne mata ido daya, Leila dai ta bita da kallon badan ta gamsu ba, har ta rufe motar tai reverse ta bar gidan. BATURIYA POV. Kamar an dasata a bakin kofar haka ta zauna tana jin kamar ba da gaske ne Faruq ya saketa ba, idan taje gida tace saboda yaga kudi a jakarta ya sake ta? Ai suma za su tambaya ina ta samu kudin, sai tace musu me? Kawarta ta bata ajiya ba lallai ne su yarda ba. Tana zaune a gurin har ya gama sallah masallaci ya shigo gida, tana jinsa sai ta saka kuka. A maimakon ya shigo dakin sai ya zauna falo yana bitar karatu da dansa. Ganin be kula ta yasa ta taso daga bakin kofar dakin ta dawo kusa da shi ta duka tana kuka. “Dan Allah Faruq kai hakuri, ka gafarta min, wannan kudin ajiya aka ba ni, Ramlee ce ta bani, kuma san zaka yi fada saboda baka son tarenmu da ita, shiyasa nace Umma ce ta bani ajiyar kudin, ba zan sake ba karba ba na maka alkawari” Ta hade hannayenta biyu tana rokonsa hawaye a fuskarta shabe shabe. Faruq ya sauke Sultan daga jikinsa ya ciro naira ashirin ya mika masa. “Je ka siyo minti” Sultan ya karba yana kallon mahaifiyarsa dake kuka cikin yanayi na rashin jindadi ya fice. Sai da Faruq ya tabbatar ya bar gidan sannan ya kalli Baturiya ya ce. “Hakan ne ya kara tabbatar da kudin nan ba ta hanyar kwarai suka fito ba, tun yaushe na raba ki da yarinyar nan? Yarinyar da a yanzu haka ba gidan iyayenta take ba? Yarinyar da ake zargin har lesbianism tana yi? Rafi'a ban isa na ce kar yi abu ba sai kin yi? Ban isa nace ki yi ba ki yi? Yanzu ai komai ya kare, na riga na sake ki sai ki tattara kayanki ki fice daga gidan nan” Mikewa tai tsaye ta share hawayenta tana watsa masa harara. “To na rantse da Allah babu inda zan je, zaman dana zan yi, kuma ai ga wani cikin nan a jikina, sai na haife shi dan haka sai na gama idda zan bar gidan nan, ai daman ni na biya kudin hayan ko? Sai ka tattara komai naka ka bar min gida, kuma dole ne ka rika ciyar da ni, idan ba haka ba sai na kaika kotu, kuma Wallahi yau ba zaka kwanar min da gida ba” Wani fusata Faruq yai be san lokacin daya kai hannu ya mareta, sai ta fadi a gurin ta fara masa ihu tana kuka, alaar mutane take son tara masa. Be bi ta kanta ba ya tsallake ya shiga dakin sai ta tashi ta bi bayansa, ta bude wardrobe dinta ta watso kayanta kasa ta fara tumurmuza gadon tana ta ihu, tsayawa yai kallonta da mamaki ganin zata fara masa abun da bata saba ba. “Wai kina da hankali kuwa?” Bata ko saurareshi ba ta cigaba da ihun iyakar karfinta duk wanda ya ji sai yayi zaton ko dukanta yake. “Dan Allah kai hakuri, Wayyo Allah cikina Faruq ina da ciki ka sani dan Allah kai hakuri” Sai ta sake fashewa da kuka ta dawo falo ta fadi kwance tana ta ihun. Makociyarsu ce ta fara shigowa tana fadin. “Subhanallahi lafiya Baturiya?” Kamin ta karaso cikin falon Baturiya ta tashi zaune da sauri ta nufi bakin kofar sai sukai karo da juna, takenta fada jikinta tana kuka. “Maman Siyama ki min rai, Faruq ya doke ni kuma ya sake ni saboda budurwarsa na shiga uku Maman Siyama, ga karamin ciki ga Sultan ina zan kai shi?” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Subhanallahi wannan abu be yi dadi ba” After shigowar Maman Siyama makotansu uku suka shigo suna tambayar abun da ya faru. Cikin kuka Baturiya take tsara musu karya wanda ta shiga kansu ta zauna das. “Tun kwana baya na ga Faruq ya canja, idan na tambaye shi miya faru sai yace na daina damunsa ko ya mare ni, yau kuma na fita ina dawowa ya samu yana waya da wata a kan gadona, saboda na yi magana ina cewa hakan da kake be dace ba Faruq, idan ma waya zaka yi ka fita can waje mana, amman ba a gaban idona ba, sai ya hau ni da masifa, wai ban isa na hana shi aure ba, na ce masa Faruq ba aure zan hana ka ba, amman ka duna halin da muke ciki muna fama da rashin abinci ga ni da ciki ga yaronka idan ka ce zaka yi aure dawainiyar ai sai ta maka yawa, Wallahi ko kudin hayar gidan nan sai daje gurin Yaya na samo sannan na biya, wani lokacin haka zamu wuni babu abinci sai wahala, dan Allah idan shi mai tunani har yayi zancen aure a wannan yanayin da muke ciki? Akan haka kawai ya hau ni da duka yana marena yana zagin iyayena ga tufafina can ya watsar a wai na tashi na bar masa gida ya sake ni” Ta kara fashewa da kuka. Kusan kowa dake dakin sai da ya cika da mamaki, domin kallon mutumen kirki suke yi ma Faruq sai yanzu suka gane kallon kitse suke yi na rogo. “Wannan maganar ta kai a duka ayi saki? Ya sake ki ne saboda ya kawo wata ne kawai amman in ba dan haka ba, ai gaskiya kika fada masa, kuma Wallahi kina da zuciyar imani, da wata ce ba zata yarda ta zauna a irin wannan talaucin ba, da kurciyarki? Har ki biya masa kudin haya? Haba kai Namiji dai be yi ba” Maman Siyama sai masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Sai dai duk fadan da take ita da sauran makotan ba su san Faruq na cikin dakin ba domin a falo suke. Badiya ta tabe baki tace. “Idan kana ganin mutum baka san halinsa ba, ni Wallahi a zatona Faruq ko hannu aka saka masa a baki a zai ciza ba” “Wallahi ni kadai na san irin ukubar da nake sha a gidansa, ga talauci ga rashin dadin hali, shi yai min mahaifiyarsa da kanensa su min kamar ba yar'uwarsa ba, sam basa kaunata ban san abun da na tare musu ba” “Ki yi hakuri jarabawa ce, yanzu ina Faruq din yake?” “Yana daki” Sai duk suka yi tsit kamar basa gurin, abun ka da mata yan gulma, Maman Siyama ce kawai tai karfin halin nufar dakin, kasancewar ta Babba domin tana da yaya har da jikoki ma. Ta daga lalulen tana kallon yadda aka watsa kayan Baturiya a kasa sai. “Baban Sultan taya zaka bari Sheidan ya shiga tsakaninku, shekara nawa kuna zaune a unguwar nan babu wanda ya taba jinku se yanzu?” Kasa daga kai yai ya kalleta, balle har ya iya furta wani abu, ba zai iya kare kansa ba, ba dan ba shi da abun karewar ba, sai dan baya son tona asirinta ne a matsayinta na matar dansa, taya zai fada musu sanoda ta shigo da kudin da ya ke zargin na alfasha ne? Ba shi ko ita abun zai taba ba, dansa Sultan da kuma wanda zata haifa ne abun zai yi effecting. Dole ne ya rufawa yayansa asiri. “Haba Faruq a rika sara ana duban baki gatari, ko dan yara” Sai a lokacin ya kalleta yana kara tsinkewa da lamarin Baturiya domin a yanzu ta wuce da saninsa. “Inshallahu hakan ba zai sake faruwa ba, an yi na farko kuma n karshe” “To Alhamdulillah, haka ake son ji, a maida komai ba komai ba, daman shi zaman aure sai da hakuri, a rika kai zuciya nesa ko dan saboda yara, shi auren zumuncin idan ya lalace har zumunci yake tabawa, kuma duk yadda kake ganin kyau matar waje da tarbiya ba tai ta gidanka ba uwar yayanka, dan Allah a gyara kuma ayi ta hakuri” “Inshallahu komai ya wuce, mun gode sosai” “To Alhamdulillah Allah ya muku albarka ya ba ku zama lafiya” “Ameen” Juyowa tai ta dawo kusa da Baturiya dake sharbar kuka ta zauna saman kujera. “Ki kwantar da hankalinki kar hawan jini ya kama ki, kuma cigaba da hakuri sakamakonki yana gurin Allah, Allah ya baku hakuri da zama lafiya, na masa magana kuma ya ji yace za a gyara, ke kuma ki kawarda idonki akan lamarinsa idan ma auren zai yi ya kawo ta a nan falonki ya aje sai ki saka masa ido ki kyale shi, kar na sake jin bakinki kin ji ko?” “To Maman Siyama, Inshallahu ba zan sake ba, na gode sosai” Dayar makociyarsu mai suna Rufa'atu ta tabe baki tana fadin. “Idai kika biye namiji sai ki kashe kanki ya auro wata” Maman Siyama ta bugi hannunta tana nuna mata kofar dakin alamar mijinta na ciki, sai ta daga kafada. “Ina ruwana shi be ji kunya abun da yai ba” Tana rufe baki Faruq ya fito ya nuna mata kofar waje “Malama fata ki bar min gida” “An dai ji kunya Wallahi, ana wulakanta matar gida saboda ta waje” Ta fada sannan ta fice Mamam Siyama na watsarta. Badiya ma ficewa tai tana Allah ya bada hakuri, Maman Siyama kan sai da ta tsaya ta sake musu nasiha sannan ta fita tare da dayar makociyarsu. Komawa Faruq yai dakin ya dauki jakarsa ta littafai ya bude ya dauko takardar da biyu ya rubutawa Baturiya wani sakin sannan ya nufo falon ya jefa mata takardar. “Dazu saki daya nai miki, yanzu kuma kin ja sakin ya zama biyu kuma a rubuce, ki je ki yi duk abun da zaka yi amman zama ni da ke ya kare, ba zan iya zama da mace da bata ganin mutuncina ba, macen da bata iya rufa asirin mijinta ko dan saboda yayanta, Wallahi Rafi'a na rufa miki asiri ne kawai saboda Sultan da kuma abun da ke cikinki, ba dan bani da abun fada ba, kuma wannan abun da kika yi ya kara fito min da halinki yanzu na gane wacece ke?” Mikewa tai tsaye tare da takardar tana karantawa. “To sai me? Ina ce dai ni na biya kudin hayar gidan nan, dan haka ka fice min a gida, kuma gobe goben nan idan na ga dama sai na zubar da cikin nan, daga kawai ka raba ni da wahalar talauci? Ina cika idda zan auri Saurayi, dan gidan masu hannu da miya har da manshanu, kuma ka zuba ido ka gani, sai na baka mamaki Faruq, sai n tabbatar maka cewar ni Baturiya ba ajinka ba ce” Ta fada kamar ba ita ce ta gama kukan munafurci ba a dazun, dauke kai yai ya fice yana taka kafarsa mai ciwo da karfi saboda bacin rai, yana kokarin saka talkaminsa ya hango Sultan zaune bakin kofar bandakin dake tsakar gidan yana kuka. Ajiyar zuciya ya sauke ya saka talkamin ya nufi inda yake ya kama hannunsa, kana ganinsa kasan a tsorace yake, domin be saba ganin Faruq yana fada da Baturiya ba. “Sultan kana son muje gidan Mama my kwana?” Sultan ya daga masa kai, sai Faruq ya sakar masa murmushi ya dauke shi suka fice. 23 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Aminatu na zaune a dakin har kusan la'asar sannan Amal ta leko tana kallonta domin bata nan komai ya faru sai dai Kabir ya labarta mata abun da ya faru, sai kuma ta fita ba tare da ce mata komai. Aminatu ta saka hannu ta share hawayenta sannan ta fara tura keken da nufi shiga bandaki sai taji abun ya mata karfi ba kamar yadda ta ji yana tafiya idan an turata ba, wata kila saboda bata enough kuzari ne, wata kila kuma idan an turo ta baya yake tafiya ne. Leken keken ta fara yi sai ta ji an bude kofar dakin an shigo, dagowa tai ta kalli Mairo dake dauke da plate din abinci da kofin ruwa ta nufota, kamin ta karasa Leila ta biyo bayanta. “Ke waya saka ki?” Mairo ta juyo ta kalleta. “Babu gani na yi an zubawa masu aiki na su, kuma an debar muku na ku, ita ma yanzu ai ta isa jin yunwa” “Okay ashibabba, yar neman suna, abincin na gidanku ne? Daga zuwa aiki har ki fara tunanin sarrafa gida yadda kike so?” “Saboda na zubo mata abinci shine abun sarrafa gida? Haba Leila miyasa kike fadawa mutum magana any how ne? A haife dai kin san na haife ki amman duk maganar da ta zo bakinki sai ki fada min kamar wata yarki? Saboda kawai ina aiki gidanku?” “Kawai ne? Kyauta kike aikin ne? Ba biyanki ake ba? Yanzu uban waye ya baki umarni kawo mata abinci?” “Keeeee karki sake zagina, idan ina aiki a gidan mu to na gama, arziki ai ba hauka ba ne” Mairo na kai aya Leila ta wanke mata fuska da mari. “Mi zaki dakawa tsawa kina ce min ke?” Mairo ta duka ta aje abincin sannan ta mike tsaye ta ware hannunta zata rama marin da Leila tai mata sai Leila ta rike hannunta ya wulgar. “Karki kuskura ki ce zaki taba ni da karamin hannunki, wawuya kawai” Mairo, ya girgiza kai. “Ina tausayin yadda rayuwa zata maida ke nan gaba, ki taka a hannu duniya ba gurin zama ba ce, ban taba ganin mutum mai wulakanta mutune ba irinki” “Wallahi idan baki wuce kin bar dakin nan ba sai na baki mugun mamaki” Mairo ta kalli Leila kawai sannan fice da Mairo ake fadan amman Aminatu ce ta fashe da kuka jikinta ya fara rawa tana yi ma Leila kallon tsoro. “Ke kuma me akai miki da zaki fara yi ma mutane kuka munafuka?” Ta dauki ruwan da Mairo ta aje ta watsa mata a jiki, wani irin zabura Aminatu tai ta kalli jikinta da ruwa ya jika, sannan ta hayayakomawa Leila a fusace. “Mahaukaciya wayuya, baki san darajar dan'adan, ki bar ni da abun da ya dame ni” Ta fada kamar ba ita ba har wani numfashi take da karfi hawaye a sauko mata. Leila kamar mai jira sai tai cikinta ta chakumota ta jefar kasa. “Ni zaki yi ma ihu dan ubanki” Ta kama tsorayen kanta ta rike gam tana fisger kan nata. Wani irin ihu Aminatu ta saka iya kar karfinta tana jin zafin har cikin kanta, sai ta soma jin abu kamar na wacan lokacin yana dawo mata, wani irin ihu take babu kakakautawa irin na fita hayyaci, Leila na ganin haka tai saurin sakinta ta fice daga dakin, sai kuma ta dawo ta cire key din ta rufe kofar ta waje ta cire key din, sannan ta nufi kofar fita daga corridor da saurinta, bata karasa ba Kabir da Amal suka shigo. “Lafiya?” “Ban sani ba, ihu take ta yi kuma ta rufe kanta daga can ciki” Ta amsa tana kallon Kabir, sai suka nufi kofar shi da Amal, hakan ya bata damar ficewa daga corridor. Sai da Kabir ya fara murda kofar ya ji ta a rufe sai ya shiga kwankwasawa. “Bude kofar” Ko saurarensa ba ta yi gaba daya ta fita daga hayyacinta sai ihu take. Duk yadda Kabir ya so ya bude kofar sai abun ya ci tura saboda an saka key. “Je ki tambayi Momy idan akwai extra key” Amal ta ja tsaki. “Shiyasa bana son baki, gashi nan Ya dauko mana mahaukaciya” Ta fito tana ta mita, domin Amina bata kwanta mata ba, musmman da taji cewar Momy bata sonta, ko bayan haka ma Amal bata son baki ko yan'uwa ne suka zo da sunan kwana biyu sai sun ga canji a gurinta balle kuma wannan da bata san inda ta fito ba, kuma bata san ranar barinta gidan ba. Upstairs ta nufa, sai da ta fara shiga dakinta ta canja tufafinta ta saka uniform din islamiya sannan ta fito ta nufi dakin Momy, daga bakin kofa ta tsaya. “Momy wai ya Kabir yace kina da key din dakin corridor” “Akwai key a jikin ko wane kofa” “Eh yarinyar ta rufe kanta ne, daga ciki kuma tana ta ihu” “Karki dame ni da maganar yarinya, ta kashe kanta” “Momy miyasa Ya ya kawo mana ita wai?” “Oho masa, neman suna mana” Ta saki kofar dakin ta nufo downstairs, kamin ta karasa saukowa ta hango Talba ya shigo yana jin ihun Aminatu ya nufi corridor da sauri, gulmarta ya sakata saukowa da gudu ta bi bayansa. “Miya faru?” Shine abun da ya fara tambaya. “I don't know, muna falo muka ji tana ihu, Leila tace rufe kanta tai daga ciki” Talba ya murda kofar sannan ya kwankwasa. “Auta... Bude kofar” Bata saurarinsa kuma bata fasa ihun da take ba. Baya yai da karfi ya daki kofar da kafarsa ya ji ta gam domin ba irin kofofin nan ba ne masara karfi, ganin kofar ba zata bude ba yasa ya fito daga gurin ya nufi inda suke ajiyar abubuwan a gidan ya dauko wani karfi mai karfi ya dawo ya fara bugawa, karar yadda yake buga kofar ne ya saka Momy da Leila saukowa su nufi corridor tare da Zulai da Mairo. “Talba me ye haka? fasa kofar zaka yi?” Be ko saurari Momy ba sai bugun kofar yake, Kabir ne ya amsa mata. “Idan ba a buge kofar ba babu yadda za'ayi a fito da ita” “Waya aiketa rufe kofar tun farko? Gaskiya yarinyar ba zata zauna Tana gidan nan tana mana hauka ba, wannan ai iskanci ne” Talba be saurara har sai da yai nasarar balla kofar sannan ya saki karfin ya shiga dakin da sauri, a kife suka same ta tana ta ihu, dago ta yai yana kokarin zaunar da ita sai ta fado masa a jikin jikinta nata rawa alamar tsoro still tana ta ihun. Girgiza ta yai kamin ya kai hannayensa ya rika fuskarta, ta yadda zata yi facing dinsa ta gane shi ne, amman ko kallonshi bata yi sai ihun take ta yi. “Akwai abun da za a mata ta daina ihun nan ne?” Ya tambaya yana kallon Kabir. “Allura” “Please” Talba ya fada sai Kabir ya fice dakin da sauri, Momy taja saki ta juya ta fice tare da Amal yayinda aka bar Leila a tsaye tana kallon Talba, zuciyarta na bugawa da karfi saboda rikon da yai ma Aminatu. “Shiiiiiiiiiii ya isa saurare ni, kina a cikin mutane ne ba daji kike ba” Kamin Kabir ya dauko allurar har Talba ya matsu saboda ihun da take bana wasa ba ne, sai da ya saka audiga ya goge mata hannun sannan ya soka mata allurar. Tana jin karfin allurar a hannunta sai ta fashe da kuka ta kamkame Talba, ko minti daya ba ayi ba bachi yai gaba da ita, sai dai hannayenta duka biyu rike suke da rigar Talba, kanta kuma kwance a kirjinsa. Kabir ya mike tsaye yana kallon Leila da hawaye ya cika idonta sai ta juya da sauri ta fice daga dakin, shi ma kallon Amina yai sannan ya fice aka bar Talba rike da Aminatu tana ta bachi wahala a kirjinsa. Ido ya kurawa fuskarta sai tausayinta ya kara kama shi, idonta rufe yake amman hakan be hana kumburinsu fitowa ba, ga hawaye a fuskarta shabe shabe, ta turo baki gaba lokaci lokaci sai ta sauke ajiyar zuciya. Yanayi ya so ji na dabam sakamakon rikon da tai masa gashi rabin jikinta yana kirjinsa, domin ta kwanto masa ne. Wata kila saboda be saba rumgumar mata ba ne, wata kila kuma saboda lafiya ta masa yawa ne. Kokarin daga yai daga jikinsa ya dauke ta ya kwnatar da ita saman gadon, ya gyara mata mata kwanciyarta sannan ya kai hannunsa ya taba kafarta a hankali sai ta motsa alamar ta ji ciwon taba kafar da yai. “Baba... ” Ta furta tana turo baki gaba kamar zai fado, samun kansa yai da murmushi, yana ganinta ya san shagwababiya ce. Sai da ya karewa dakin kallo sannan ya juya ya fice zuwa bangarensa. Kusan awa uku tai tana bachi bata farka ba sai tara na dare, kamin ta farka shogowar Talba biyu yana dubata, a na ukun ne ya same ta zaune tana hawaye. Shigowa yai ya zauna bakin gadon yana kallonta. “Mamana baki gajiya da kuka?” Sai ta dago ta kalleshi. “Taya zan rabu da abun da ya zame min azimun? Miyasa kake tunanin rabuwa da iyaye da yan'uwa abu ne mai sauki, taya zan manta komai a take? Saboda ta mutanen da basa maraba da kai abu ne mai wahala! Har yanzu na kasa yarda cewar na rasa komai, ina ta marmari kauyena, da mutanen kirki masu karamci dake cikinsa, na yi kewar mahaifiyata da Babana, har abada ba ni da mai maye min gurbinsu” Ta share hawayenta sannan ta soma wasa da yatsun hannunta wasu hawayen na sauko mata. “A da, ina rayuwa ne cikin wani karamin gari, mai cike da albarkar manoma, duk da kasancewar ban samu ilmin boko ba, na samu na addini daidai gwargwado, kuma ina zaune da yayyuna cikin jindadi da farincikin rayuwarmu ta yau da kullum, ni kadai ce mace bayan mazaje bakwai da mahaifiyata ta haifa, hakan ya saka na zama yar gata, ina jin kamar babu wanda ya fini more rayuwa, abun da ban sani ba, ashe kaddara tana nan tana min wani tsari, a lokacin da mahaifiyata take cikin rashin lafiya na bakinciki abun da akai ma yayanta kasan me ta fada min?” Ta kalleshi sai ya girgiza mata kai alamar be sani ba. “Tace kuka na yana nan gaba, sai na tambaye tana take ganin zan iya rayu idan bata raye? Tace min zaki rayu amman akwai kuka a gaba, a yanzu na gane abun da take nufi, tabbas zan rayu amman wace irin rayuwa zan yi? Ban sani ba, kuka da take fada min cewar zan yi na tabbatar shi ne na fara tun a yanzu, yanzu na fahimta wanda ya rasa uwa ya rasa ta har abada, wand ya rasa yan'uwa ya rasa su har abada, abu ne mai wahala farinciki ko murmushi ya sake kusantar fuskata...” Ta fashe da kuka sosai, Talba ya ja dogon numfashi a hankali ya sauke. “Baki taba tunani miyasa Allah ya hada ni da ke ba? Wata kila a yadda nake da rufin asiri idan na tare ki a hanya, ba zaki tsaya ba zaki ji tsoro, wata kila ni kuma ba zan taba jin a kamata na tsayar da ke na tambayi damuwarki ba, amman sai Allah ya kawo silar da zata saka na hadu dake cikin sauki kuma har na dawo dake da zama kusa da ni, idan Allah ya karbe wani abun sai ya maka hanyar wani, ki dauka duka wannan yana cikin jarabawarki, Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassalam yafi kowa gata a gurin Allah kuma Allah yafi kaunarsa da kowa, amman a haka Annabi ya girma babu mahaifiya babu mahaifi, ni da ke banbancin kaddararmu kadan ne, ni ma na tashi babu uwa ba uba, sai dai na zamu gata, irin gatan da nake kokarin baki a yanzu, ki dauke ni a matsayin yayanki, saboda ina ganinki kamar yar'uwata ne, duk abun da zan yi ma kanwata Amal ko Leila zan miki, ki sake jikinki, zan maida ke yar gata believe me zaki zama Shalele ta ko'ina” Kanta na kasa tana hawaye har ya gama magana, sannan ta dago ta kalleshi, be yi mata kama da mai karya ba, kamaninsa da cikar kamalarsa be nuna akwai gazawa a tare da shi ba. Sai dai me? Matar daya ambata da sunan cewar matar da zai aura ce zata yarda? Anya ma zata jure zama a gidan tare da ita? “Ina da tabbacin ba duka aka akashe yan'uwanki ba, Inshallah idan hankali ya kwanta kin samu lafiya zan muje mu nemi inda yan'uwanki suke, yanzu taso muje ki ci abinci” “Ina son na yi sallah, ban yi sallah ba ana biyana salaloli da yawa, dazun ma na fara tura keken naje na yi sallah sai.... ” Daga haka ta labarta masa abun da ya faru ciki har da wanda Madina tace idan ya dawo ta fada masa. Be jidadin abun da Leila tai mata ba, sai dai be nuna mata ba. “Okay amman yanzu bari ki fara cin abinci ki samu kuzari, sannan muje ki yi sallah okay?” Ta daga masa kai. “Zulai zata zo ta tura ki bathroom ki wanke bakinki sai ta fito da ke ki ci abincin ki yanzu” “Aa bana so yanzu wannan zata zo ta fara min masifa, kuma zata hana su yi min komai” Ta fada kamar zata fasa kuka. “Kina son na tura ki?” Ta daga masa kai, sai ya mike tsaye ya dauketa ya dora a wheelchair din. Ya turata da kansa har bathroom din ta wanke bakinta. “Zaki yi fitsari?” Ta girgiza masa kai alamar aa. Sai ya turo ta ya fito da ita sai da suka kawo gurin kofar sannan ta kula da kofar a balle take, sai dai bata ce komai ba tana ta kallon hanyar har ya fito da ita falon. Iyakar abun da ta sani Leila ta rika kanta tana ja da karfin tsiya, bayan baka bata san me ya faru ba, sai ganinta tai ta farka daga bachi. “Waya kwantar da ni kan gado dazun?” “Ni” Ya amsa mata a takaice sannan ya tura kujerar har gurin dinning, babu kowa a falon daga shi sai ita sai katon Plasma. Da kansa ya shiga zuba mata abincin, sannan ya mika mata. Sawun takun talkami da taji ne ya saka ta waiga ta kalli Upstairs din sai ta hango Madina da Leila suna saukowa a tare, suna hada ido da Leila tai saurin maida kanta kasa cike da tsoro. Kallo daya Talba yai musu ya dauke idonsa, kusan a tare suka kalli juna, ba Leila kadai ba har Madina ta ji zafin ganin Talba na zubawa Aminatu abincin da kansa, sai dai ta dannewa zuciyarta bata yarda ta nuna ba, duk da kasancewar Leila ta fada mata komai daya faru dazun. “Amman wannan wulakancin ne, haba Talba? Taya zaka zuba mata abinci a irin plate din da muke cin abinci? Kuma ka kaita har gurin dinning?” Madina ta yi saurin rike ta. “Haba Leila miye haka?” “Ai dole na yi magana, dazu fa har rumgumar ta yai...” Tana kokarin kai hannu ta taba Aminatu data make guri daya Madina ta yi saurin rike ta da karfi. “Leila miye haka wai?” “Wallahi sai ta bar gidan nan, na rantse da Allah ba zata zauna a nan ba” Ta fada da karfi kamin ta kwalawa Momy kira tana ihu. Uffan Talba be ce mata ba, ko kallonta be yi ba sai aikin zubawa Amina ruwa yake a cup. Kamar da gangan Madina ta saki Leila ta karasa gurin dinning. “Karki taba yarinyar nan” Furucin da yai mata ne yasa saka ta tsaya cak, domin bata ji wasa a muryarsa ba kamar yadda fuskarsa ma bata nuna wasan ba. Aminatu ta yi saurin sakin plate din abincin dake hannunta idonta cike da hawaye. Hango Momy na saukowa tare da Amal da Kabir yasa Leila ta dauki ruwan da Talba ya zuba a cup ta watsawa Amina. “Haba Leila miye haka?” Madina ta fada tana zaro ido tare da saka hannayenta ta rufe baki. “You should apologize ki bata hakuri yanzu nan” Talba ya fada yana nuna mata Aminatu. “No Leila ta yi kuskure, amman ba zata bata hakuri ba, you're just hurting her” Kabir ya fada, Momy na karasa kusa da ita ta maida Leila. “Ya isa haka Talba, ba zan yarda ka wulakanta Leila akan wata banza ba” “Momy kin san abun da ta yi” “Be dame ni, amman ta duka ta bawa wannan musakar hakuri ne ba zata tayi ba!” Nan da nan jikin Aminatu ya fara rawa, Talba ya kalli Momy. “Wannan ba daidai ba ne Momy” “Miye daidai tana yar riga kace ta bawa wata banza hakuri? Wai gata ka fi leila ne ko kuma miye?” “Kuma na rantse da Allah ba zata zauna a gidan nan ba, Wallahi Momy sai dai ku zaba ni ko ita...!” Leila ta fada tana buga kafa a kasa. Leila ta ji wani irin dadi, komai ya faru kamar yadda take so, duk da kasancewar bata yi zaton da wuri haka komai zai faru ba, daman ta zo gidan nan kawai saboda Leila ta kirata tana kukan rumgumar da yai ma Amina, sai dai a yanzu komai ya yafi kamar yadda take son ya tafi. Da sauri ta nufi Aminatu dake kuka taja kujerarta. “Madina ki kyale yarinyar nan a gurin nan?” Sai ta girgiza ma Momy kai. “Dan Allah Momy ki gafarce ni, be dace ku yi wannan fada a gaban yarinyar nan ba” Bata jira abun da Momy zata sake cewa ba, ta tura Aminatu zuwa corridor, a azaton Momy Madina ta yi hakan ne saboda bata son su yi fadan a gabanta kasancewar su yan'uwa. “Abun da kake ba kyautawa ba ne, Talba, be kamata ba, ko a dazun ka rumgume yarinyar nan a gaban Leila kuma kasan dole zata ji ba dadi ba, and now kana kokarim feeding dinta for what” Talba ya nuna Kabir da yatsa. “Don't you dare tell me what is right and wrong, don't you dare judge me, this is my life waye kai da zaka kalubalanci abun da na yi?” “So baka isa ka kawo wata a gidan nan just to hurt my sister in front of us? And now ba zamu zabi wata akan Leila ba, take her away” Wani irin kallon kallo suke tsakanin shi da Kabir ko wane zuciyarsa ta kawo kamar ya rufe dan'uwansa da duka yake ji. Daker Talba ya samu hade numfashinsa ya kalli Leila dake tsaye sannan ya nufi corridor da zai sada shi da dakin da Aminatu take ciki. Bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Madina dake rumgume Aminatu tana share mata hawayenta da dankwalinta, ita ma tana kuka. “Dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan, ban taba rasa kowa ba, amman na fahimci yadda kike ji, akwai ciwo sosai ki kwantar da hankalinki Inshallah Talba ba zai bari ayi miki komai ba, ni kuma zan kula da ke kamar kanwata Inshallah” Yadda take hawaye sai ka rantse da Allah kukan gaske take, zaka yi zaton da gasken gaske take tausayin Aminatu. A badini kuma tana yin hakan ne saboda ta ji kamshin turaren Talba ta san yana tsaye bakin kofar dakin ko ma cikin daki. Aminatu na hada ido da Talba ta saki Amadina tana kuka. “Dan Allah ka kai ni inda yan gudun hijira, ko wani gurin, bana son fada bana son fada dan Allah karka yi fada da su dan Allah...” Karasowa yai cikin dakin ya risina gabanta yana kallon fuskarta, magana yake son yi mata amman ya rasa ta ina zai fara. “Idan zamanta a nan zai kawo matsala, zan iya tafi da ita gidamu, Mamana bata da matsala kuma zan iya kula da ita, kamin Momy da Leila su sauko” Madina ta fada muryar na rawa, a ranta tana ala ala ya amince, a hankali Talba ya juyo ya kalleta. “You can trust me. Wallahi ba zan mata komai ba, tare na da Leila ba zai saka na cutar da wani ba, yarinyar nan ta cancanci rayuwa mai kyau...” A nan ma Talba be ce mata komai, ya juya yana kallon Aminatu. “Excuse us Madina” Murmushi ne ya cika fuskarta, saboda ya kiran sunanta, kusan tun da take da Leila ba zata iya tuna rana daya ta taji sunanta a bakinsa ba. 24 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* “Kar abun da Leila tai ya dame ki, tana da zafi ne, amman a sannu zata fahimta ta daina” Aminatu ta saka hannu ta share hawayenta, wasu a sauko mata. “Komai be da sauki a rayuwar duniya, komai ka sara yana da wahala ka samu abun da zai maye maka gurbinsa, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci, kuma tana da gaskiya, ni yar kauye ce marar gata wanda bata waye a komai ba, ba kamar ni ba talaka kuma yar kauye, be kamata na zauna a mazauninsu ba, ko kuma na ci abincin a inda suke so, muna da banbanci mai nisa a tsakaninmu” “Ban taba ganin wannan banbanci ba, ban taba jin cewar Leila ko ni mun fiki ba saboda dukiya, ita ma kuma kurciya ce ke janta” “Idan ita kurciya ce, Momy fa?” Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce mata. “Momy tana goya mata baya ne saboda bata son bata kunya a gaban mutane, ko da ni zan yi fada da Leila wani lokacin zata iya shigar min ta yi ma Leila fada” Ta yi shiru hawaye sai sauko mata suke. “Kalleni” Ta dago, sai idonta ta sauka cikin nasa, a karon farko ta ji kwarjininsa ya cika sa, akwai kalama a fuskarsa kamar yadda natsuwarsa take kara fito da siffar zatinsa. “Zaki iya zama a gurin Madina ko kuma na kai ki wani gurin dabam?” Ta kawarda fuskarta tana tunani. “Ban sani ba, wata kila ita ma iyalan gidanta kamar na ka ne, ba lallai ne su karbe ni, amman ka min wani alkawari dan Allah” Kallonta yake, ita ma kamar tasan ba zai tambayeta minene sai ta fada tana yawo da idonta a dakin. “Ka min alkawarin, zaka nema min gurin da zan zauna cikin yan gudun hijira yan'uwa, ko kuma ka nema min wasu daga dangina kamar yadda kai alkawari” Yayi murmushi kadan. “Kina tunanin yan gudun hijirar suna shan dadi ne? Suna wata irin rayuwa ne mai ban tausayi da tada hankali, abun da za su ci ma wahala yake musu, ba su da muhalli, wasu na fakewa a kangon makaranta ko tsohon gida, wasu kuma suna zaunawa inda yan'uwa ne, amman su suke ciyar da kansu, wasu bara suke su ciyar da kansu, wasu kuma surfe suke su yi wankakau ko wani aikin karfi sannan su samu ciyarda kansu, idan sun shiga wani gurin za a nuna musu kyara ana kiransu da mayu, sadakar ma sai wanda ya ga Allah ya ga Annabi yake ba su, ba rayuwa suke mai dadi ba, ya kamata ki daina wannan tunanin” “Ba jindadi nake so ba a yanzu, jindadi abu ne mai wahala a gareni, so nake na samu sakewa ina sonnna zauna da irin mutanen dake rayuwa kamar yadda nake, mutanen da basa kyamata, ina ma kasance tare da mutane masu irin rayuwata, wadanda suka san zafin rashi...” “Ina daya daga cikinsu ai” Ya fada yana mikewa tsaye. Sannan ya nufi kofar fita wa kusa da kofar ya samu Madina ta jingina tana jiran fitowarsa. “You should go and talk to your parents first, idan sun amince sai ki sanar da ni” Ta dago a hankali ta kalleshi. “Iyayena basa da matsala, amman zan je na sanar da su, sai dai ban san inda zan same ka ba” Tsayawa yai kallonta sannan ya mika mata hannunsa, tana ganin haka ta fahimci wayarta yake nufi sai tai saurin cire password din wayar ta mika masa. Yana saka number ya mika mata wayar sai ta karba da hannu biyu tana godiya. “Na gode” Be kula ta ya juya ya koma cikin dakin, sai ta yi tsalle ta dire a hankali ta kai wayar a hancinta tana shinshinar kamshin turaren Talba kamin ta kai wayar a kirjinta. Sannan ya fito corridor tana boye jindadinta, Kabir ta samu tsaye yana fada Leila. “Kishi ba hauka ba ne, kowa ya san akwai zafi amman ya kamata ki rika controlling kanki, idan ma wani abu ne ai shi yai miki ba ita ba” Madina dai bata ce komai ba har Talba ya turo Aminatu kam wheelchair ya fito da ita falon, kanta a kasa tana tsoron kallon mutane, shi ma kuma kofar fita daga falon kawai yake kallo. Momy da Leila har ma da Kabir na tsaye ban kallonsa babu abun da suke har ya fita da ita. “Aikin banza mtsssss” Leila ta fada tana jan tsaki. Sai da Madina ta leka windows ta hango ya tashi motar yana kokarin yin ribas sannan ta kalli Momy ta ce. “Momy zan tafi da yarinyar nan saboda anan zata haifar da fitana ne kawai, kuma idan tana tare da ni zata nisanta da shi ba kamar yanzu ba” Momy ta kalli Leila sannan ta kalli Madina. “Ke iyayenki za su yarda ta zauna ne?” “Eh zan musu bayani kuma ai kin ga ba dadewa za ta yi ba, na dan lokaci ne” “Shi zai yarda ki tafi da ita?” “Eh na masa magana, amman yace min na fara zuwa na yi magana da iyeyena” “Okay ba matsala” Momy ta amsa ta tana kallon yanayinta, sai ta yi ma Leila sallama tana fadin sai sun yi waya. Momy ta bita da kallo har sai da ta fice sannan ta kalli Leila ta ce. “Ki yi hankali da yarinyar nan, hankalina be kwanta da ita ba, idan b munafurci ba ta ya za ayi fada akan yarinya kuma ke ki ce zaki dauketa ki kaita gidanku?” “Momy da sani na tai, sai da tai shawara da ni, plan ne muke hadawa, Madina bata da matsala, ba yau na santa ba fa Momy” “Ki dai yi hankali, kuma ki san irin sirrin da kike fada mata” Kabir ya mike tsaye yana kallon Leila. “I hope plan din da kike hadawa ba cutar da yarinyar nan zaki yi ba, ba na goyi bayanki ba ne saboda ki samu damar wulakantata, no na yi hakan ne saboda na san kina jin kishin abun da Talba yake yi ma yarinyar nan” “Ba wanda za a cutar kawai zan nisanta ta da shi ne” “Dauketa za ki yi?” “Haba Kabir? Idan ma na dauke ta zan yi ai shi ya ja mata...” Uffan Kabir be sake ce mata ba ya fice falon. Ita ma tashi tau ta nufi upstairs aka bar Momy zaune tana kallon Leila har ta haye. TALBA POV. A entrance din ya bar ta, sai da ya fara isa ya bude motarsa sannan ya dawo ya saka hannunsa ya dauke ta ta saka a motar ya dawo ya dauki wheelchair din ya saka a bayan motar, kana ya zagayo ya rufe side dinta ya shiga driver seat yaja motar suka ce daga gidan. A hankali yake tuka motar yana kallonta, ita kuma tana ta kallon titi, da motocin dake kai da kawo har suka isa super market din da yake siyen chocolate da sweet da yake kaiwa a gidan marayu, fakawa yai a harabar sannan ya fita ya shiga ciki be dade ba ya fito ya dawo cikin motar, yaja suka dauki hanyar by pass. Har suka isa aka bude musu gate din ya shiga ciki ya faka motarsa Aminatu bata kalli inda yake ba, sai da ya bude motar ya fito, sannan ya zagayo gefenta ya bude mata. “Ina kujerar?” Ta fada tana kallonsa. “Ya kamata ki fara takawa” Ta bata fuska tana turo baki gaba kamar zata fashe da kuka. “Akwai zafi idan na taka” “Idan baki taka ba, then yaushe zaki taka kafar? Kullum haka zaki yi ta zama fa” “Ni dai ba zan iya takawa ba” A dole ya bude ya dauko mata kujera ya aje mata. “Ta so ki zauna” Ta kalli kujera ta kalleshi sai ta kara bata fuska. “Akwai nisa ai sai na yi taku har hudu” “Idan ba zaki taka ba, zan tafi na bar nan” “Sai na yi ta zama a nan ina ruwana” “Ni ma ina ruwana ki yi ta zaman to” Ya fara takawa kamar gaske, sai ta fashe masa da kuka. “Ashe kin iya kuka... Ya miki kyau” Ya fada ba tare daya juyo ba, hakan yasa dole ta fito da kafafuwanta ta taka kadan. “Wash wash wash...” Tana fada tana hannunta rike ta ganbun motar har ta karasa gurin kujerar ta zauna. “To na zauna” Ta fada cikin kuka. Sai ya juyo ya kalleta yai murmushi. “Daga yau ba za a sake turaki a keke ba” “Ni kuma ba zan yi tafiyar ba, ai saboda kasan akwai ciwon a kafata ne, idan kai ne Allah kadai ya san yadda zaka yi kuka” This time around murmushi yake mai sauti. Ya dawo kusa da ita ya tsaya. “Wato kukan zan yi, an fada miki ni rago ne kamar ke?” Ya fada yana kai hannu ya lasa kumatunta, sai ta kara turo bakin gaba. Murmushi yai ya bude back seat din ya dauko abubuwan da suka siyo ya dora mata saman jiki sannan ya koma bayanta ya fara tura keken. “Yaran da zan nuna miki yanzu, basa da uwa ba uba, ba yan'uwa ba kowa, amman sun zama kamar iyalai a nan, kuma suna farinciki, ba dan yau yana ranar karatu ba, suna makaranta da yanzu sun zo sun zagaye mota suna murna da ganina” “Waya kawo a nan to?” “Na yi miki karya?” “Aa ka fada min gaskiya dai, Babba ba ya karya karya ba kyau” Yayi murmushi. “Ni na kawo su a nan” “Amman da zaka yi karya me zaka ce min?” “Sai na ce Babana” “Babanka ba ya rasu ba?” “Yeah tun ina ciki mahaifina ya rasu, amman Daddy ai shi ne Babana gatan da yai min ko da ace Babana yana da rai ba zai min shi ba” Ya fada sannan ya turata har gaban ajijiwansu, yaran na ganinsa suka  taso ta gudu suna masa oyoyo. “Uncle Uncle” Yayi murmushi ya duka yana tambayar lafiyarsu. Aminatu na kan kujerar tana kallonsu cike da burgewa, irin yadda yake sake musu ya saka suka saba da shi sosai har taba jikinsa suke wasu na tsokanarsa. Mikewa yai tsaye ya dawo kusa da Aminatu ya dauki ledar sweet din ya bude ya mika mata. “Ki ba su” Ta kalleshi kamin ta kai hannu ta dauka ta fara mika musu duk wanda ya karba sai ya koma gefe, wasu kuma sai su dawo a kara musu, shi ma ya dauki daya ya fasa ya saka a baki, bayan sweet din ya kare ya bude chocolate ya bata tana dauka tana ba su, sai ga murmushi a fuskarta. Sai da ya kare sannan yai musu sallama suka koma ciki, shi kuma ya turo Aminatu har gurin Motarsa. “Yanzu ma ke zaki shiga da kanki” Ta bata fuska. “Wallahi akwai zafi tafiyar dazun ma daurewa kawai na yi” “Yanzu ma daurewa kawai zaki yi” “Yanzu ba zan iya daurewa ba” Ta fara matsar hawaye sai yai murmushi kadan ya ciro wayarsa dake ring, sai da yai kamar kar ya dauka sai kuma yai picking. “Ya akai?” “Talba... Kana ina?” Ya kalli harabar gurin. “Ina wani guri” “I need to see you akwai magana mai muhimmanci daya kamata ka sani” “Idan na dawo zan kira ka” Yana fadar hakan ya kashe wayar ya kalli Aminatu dake masa kallon tsoro. “Momy ce?” “Momy kike tsoro? Abokina ne” “Wannan likitan?” Ya daga mata kai, sannan ya duka ya saka hannunsa ya dauke ta ya saka a front seat ya rufe, ya nade kujerar ya saka ta a bayan motarsa, ya zagayo zai shiga motar wayarsa ta sake yin ringing, sai da ya zauna sannan ya duba wayar sai ya ga bakuwar number. Picking yai ya kara a kunne sai Madina ta yi masa sallama. “Assalamu Alaikum, Madina ce” “Ina ji” “Ka kawota gidanmu Hajiya ta amince” “Mahaifinku fa?” “Shi ma ya amince, baya gidan amman na yi magana da shi ta waya” Be sake cewa komai ba ya kashe wayar. Ya yi ma motar key yai reverse suka fice daga gidan. Be yi wata doguwar tafiya ba, suka iso gidansu Madina, horn daya yai aka bude masa gate din ko kamin ya faka harabar gidan Madina da kanenta biyu mata sun fito da saurinsu suna tarbonsu, ko wanensu fuskarsa a sake alamar suna maraba da zuwanta. “Ina fatar dai kina ra'ayin zama, bana son na cilasta ki, kuma zan rika zuwa kullum ina dubaki, idan kin ga wani abu na daman ki fada min” Ta daga masa kai, sannan ya bude motar ya fita kamin ya zagaya ya bude gefen da Aminatu take, har Madina ta ta rumgume Aminatu a gabansa, hakan da tai kuma ba karamin dadi yai masa ba, domin a ganinsa ko ba komai ta nuna mata rashin kyama. Da kansa ya fito da wheelchair din ya aje ta nesa da inda motar take, ita kuma ta riko Aminatu suka ta fito. “A matso da kujerar” “Aa ki taka a hankali, ki isa gurin kujerar, ya kamata ki rika takawa” “Akwai zafi sosai” Ta fada kamar zata fashe da kuka, Madina ta yi dariya. “Aiko kara ki saba, domin ni ba zan yarda ki yi ra zama kan kujera ba kullum dole ne ki fara tafiya” Da wash wash ta karasa gurin kamin ta zauna har ta kagu, Madina ta fara tura kujerar Talba kuma yana dagawa kanenta dake gaishe shi kai, sai kuma yai tsaye sai har sai da suka karasa gurin kofar falon sai ta juyo ta kalleshi ya sakar mata murmushinsa mai kyau, Madina ta ji gabanta yayi mugun faduwa, sai yanzu ta tabbatar Leila ta fita juriya, domin bata jin zata iya jurewa Talba ya rika kula Aminatu a gabanta, saboda shi, yanzu ma ba dan tana neman kusanci da shi ba da ba zata yarda ta karbi Aminatu ba. “Maraba maraba” Hajiya ta fada da fuskar dake nuna dole Madina tai mata ba dan tana so ba. “Ina wuni” “Lafiya Kalau” Tana amsawa ta kalli Madina sai kuma ta dan yi murmushi. “Yanzu bari mu fara cin abinci sannan ki yi wanka, ki huta” “Ina son zan yi sallah” “Okay” Ta turata har zuwa dakinta. “Nan zamu zauna, nan ne dakina so yanzu mun zama mu biyu” Aminatu dai bata ce mata komai ba, har gaban gadonta ta kaita ta fita ta debo mata abincin da aka girka shinkafa da miya. Da kanta tai feeding dinta sannan ya kaita bandaki ta hada mata ruwan wanka ta fito ta baro ta a ciki, bayan ta gama ta koma ta turo ta suka fito, wata doguwar rigar ta dauko mata ta taimaka mata ta saka sannan ta nuna mata gabas ta bata hijabi. Haka tai ta wuni tare da ita a dakin tana kunna mata tv can kuma ta jata da hira. Da dare ma a tare suka ci abincin dare, sannan ta dauko mata daya daga cikin tufafin na kwana ta bata ta saka. Sannan ta dauko wayarta ta rike. “Ko na kira miki Talba ki masa sai da safe?” Aminatu ta yi shiru kamar mai tunani. “Aa” Sai Madina ta kai hannu ta dafa ta. “Ai kara ki saba da gaisawa da shi, ai zai jidadi kuma zai ce kin damu da shi, kamar yadda shi ma ya nuna miki kulawa” “Toh...” Sai Madina tai murmushi ta nemi number sa ta kira shi. “Idan ya dauka ki ce kina son ki ji muryarsa ne kamin ki kwanta” “Toh” Wayar ta yi ringing ta katse be daga ba, tasan Talba baya son hayaniya, hakan yasa bata sake kira ba. “Be daga ba wata kila baya kusa da wayar” Aminatu ta daga mata kai sannan ta kwanta saman gadon. Tara da yan mintuna Madina ta sake kiran Talba, rejecting call din yai ya kira jiki na rawa ta dauka. “Hello” “Madina bana son yawan kira” “Ka yi hakuri dan Allah, ni ma ban so kiran ba, Amina ce tace tana son na kira mata kai” Yayi shiru be ce mata komai ba, sai ta saka wayar a hands-free ta mikawa Amina. “Fada yayi?” Amina ta tambaya kamin ta karba. “Ban yi fada ba, Shalele ba ki kwanta ba?” “Eh” “Akwai wata matsala ne?” “Aa kawai ina son na ji muryar ka ne kamin na kwanta” Yayi murmushi ya. “Shalele sleep tight” “Miye haka nan?” “Ba ki san abun da hakan ke nufi ba?” “Eh ni bana jin turanci” “To za a koya miki, ki kwanta yanzu ki yi bachi da kyau” “Toh sai da safe” “Sai da safe” Yanke kiransa yayi daidai ta sauke ajiyar da Madina tai yi, domin har ga Allah bata dauka tana kishin Talba har haka ba sai yanzu. A take yanayinta ya canja, ta kwanta ba tare da tace cewa Amina komai ba. Washe gari a dakinta ta kawo mata komai a karyawa, sannan ta nufi wayarta dake ringing ta dauka. “Hello” “Madina ya kika?” “Lafiya kalau, kamar Kabir” “Ni ne baki da number ta, ni ai ina da taki” “Uhm Ya aikin?” “Alhamdulillah, Yarinyar nan tana gurinki?” “Wai Shalele? Eh tana nan” “Shalele kuma?” “Eh haka na ji Talba na kiranta, na dauka haka kuke kiranta ne ai saboda tana da sunan Momy” “Aa zan zo na dubata yanzu” “Momy ta sauko kenan?” “No tana da ciwo a kafarta, zan duba ciwon ne, kuma ga maganinta nan kin manta” “Okay sai ka zo” Ta sauke wayar tana kallon Aminatu. “Shalele wai haka Talba ke kiranki ko a gida?” “Aa” Aminatu ta amsa mata a takaice cikin rashin sakewa. Tsayawa tai tana kallonta sannan ta fice tana kiran Leila a waya. Harabar gidan ta fito tana labartawa Leila abun da ya faru. “Yau fa be ma shigo nan ba, ko Momy ta waya ya gaishe ta, be leko bangaren nan gaba daya, kuma na san duk saboda na ce ba zata zauna a bangaren ba ne” “Ni abun har mamaki, taya zaka hadu da yarinya a titi kace zaka fifitata sama da yar'uwarka kuma matar da zaka aura” “Daman kin san bama sha inuwa daya, idan ba ganin yai raina ya bace ba hankalinsa ba zai taba kwanciya ba” “Jiya fa bata kwanta ba sai da ta ji muryarsa” “Da gaske?” “Wallahi kuwa, kin ji yadda yake kiranta Shalele” “Madina sai na ci uban yarinyar nan, me take nufi?” “Me yake nufi dai shi, idan bata ga fuska ba ai ba zata soma ba, amman fa karki ce ni na fada miki” “Ai ba zan fada ba, amman dole na dauki mataki?” “Matakin me zaki dauka? Har a bada, Talba ba zai taba auren yarinyar nan ba, ko da yana sonta, Wallahi ba zan bari ba, sai dai ina ganin yana yi ne saboda ya musguna miki, shiyasa na baki shawarar ki kulla soyayya da Ali, so that ya ji yadda kike ji, amman ko dan rashin sanin asalinta da kuma fyaden da akai mata ai ba zai aureta ba, besides ita fa ba yar kowa ba ce” “Na san da wannan, amman ko zai yi dan ya bata min rai be kamata yai da wannan yarinyar ba” “Zan kira ki anjima” Ta yi saurin katse kiran hango motar Kabir da tai, tana tsaye har ya iso kusa da ita ya faka motar ya bude. “Hajiya Madina...?” “Yau dai sai gaka gidanmu kamar wasa” Yayi dariya. “Na zo na goge laifina ne, kin san jiya ba mu kyautawa Talba ba, shiyasa na zo na goge laifina” “Hakan ya kamata gaskiya, bari na fito da ita” Ya mika mata maganin ta karba ta shiga ciki ba dadewa ta fito tare da Aminatu ta kawo masa har gurin motar. “Tashi tsaye” Ta girgiza kai. “Ni bana ita tashi yana min ciwo” Fitowa yai motar ya duka gabanta yana duba kafafuwan, sannan ya koma ciki ya dauko safa ya saka a hannunsa ya fara latsa kafafuwan. “Akwai zafi fa” Ta fada a shagwabe. Rikata ya mikar da ita tsaye, sannan ya saka dayan hannunsa ya janye kujerar yana kokarin sakinta. “Aa aa aa akwai zafi” “Haka zaki hakura ki tsaya idan baki tafiya ya za'ayi ya warke? Kin yi gudun daya wuce kima ne shiyasa amman kina fara takawa zai warke tun da an saka miki magani” Ya saketa sai ta fara rawa can kuma ta kasa tsayuwar ta fadi, tsakanin Madina da Kabir aka rasa wanda zai rika ta har ta kai kasa. “Kar a sake bari tai zauna, ku rika barinta tana tafiya” “Ton” Ya koma cikin motar ya dauko takardar yayi rubutu akai ya mikawa Madina. “A nemo mata wannan maganin duka na shafawa ne” “Okay” Ta fada tana karba sannan ya rufe motar ya juya ya fice daga gidan. Sannan Madina ta nufi inda take da keken ta rikata ta zauna. “Karki takura kanki da tafiya, idan ba zaki iya ba ki yi zamanki a nan kin ji?” “Toh” Ta fada idonta tab da kwalla. Suna shiga ciki Madina ta kalleta tace. “Anjima zan kaiki gurin gyaran kai, kuma zan muje da ke ki zabo tufafin da kike so, amman kamin mu tafi zan kira Talba ki fada masa inda zamu je, sai ki ce masa kina son ya raka mu okay?” “Toh” “Good, kuma idan yace zai je aiki ki ce masa kina son zaman a gurin aikinsa kamin na dawo daga nawa aikin, saboda ni ma aiki zanje yanzu” “Tohm” Kamar hadin baki Madina na daukar wayar da zimmar kiran Talba sai gashi ya kirata, murmushi ne ya kawata fuskarsa tai picking call din ranta fes. “Hello” “Shalele na kusa” “Eh” Ta amsa tana hade abu mai daci na kiran Aminatu da yai da Shalele sannan ta mika mata wayar. “Hello” “Shalele kin tashi lafiya?” “Lafiya kalau, yanzu zamu je gurim siyen kayan sakawa da kuma gyaran kai, idan kana nan ina son mu tafi tare” Ya dan yi jimmm kamar mai sauraren wani gurin, har sai da ta dauke wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake maida wayar. “Hello” “Already ina Office, ba zan samu zuwa ba kuje tare da Madina ki zabo duk abun da kike so” “Ita ma aiki zata je yanzu, ko ta kawo ni a nan idan ta tashi sai ta zo mu tafi tare” “Miyasa kike son zuwa inda nake ne?” Tayi shiru sai kuma ta ce. “Ka yi hakuri” “No ba zan cen na yi hakuri ba ne, bata wayar” “Gashi yace a baki wayar” Ta mikawa Madina. “Ki kawo ta nan idan zaki je aikin, idan kin dawo sai ki zo ki dauketa kuje siyayyar” “Wata kila zata fi sakewa idan muka je tare da kai, tun jiya bata da magana sai taka, tun safe take son na kiraka, ni kuma bana son ka ga kamar ina takura maka ne, and you know her situation duk abun da zai sakata farinciki shi ya kamata mu yi” Tana kawai nan ya yanke wayar, sai tai murmushi. 25 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Kamin su sai da ta kira ta fadawa Leila cewar zata je yi mata siyaya ita kuma tace sai anje da Talba kuma yana gurin aiki yace a kawo masa ita kamin ya tashi aikin. Sannan ta shiryawa Aminatu cikin atamfa mai kyau duk da kasancewar ta yi mata yawa domin tsawo da jikin Madina ba daya dana Leila ba, sai dai hakan he hana atamfar karbarta ta mata kyau sosai sannan ta saka mata hijab. “Ba zamu je da kujera ba, daurewa zaki yi ki rika takawa” “Ba zan iya ba akwai zafi” “Zaki iya ma” Madina ta rikota sai ta fara takawa a hankali da dan tsoro, tana jin zafi sai dai ba irin zafin da zai hanata takawan ba, wata kila dai da tsayin ne ba zata iya ba. Da taimakon Madina suka fito falon har da gaisa da Hajiya sannan suka nufi kofa ba laifi ta yi kokari domin da kafafuwanta ta isa isa gurin motar Madina, ta bude mata ta shiga ta zagaya bangarenta, dadi gurin Aminatu ba a magana, saboda ta taka da fafuwanta a zatonta ba zata iya ba. Sai da suka yi tafiyar rabin awa sannan suka iso Kamfani, wani irin shuki ne ya kama Madina ace wai mijinta ne ke da iko da katon kamfani kamar wannan, bayan kyau da cikar kalama da Allah yai masa. “Hmmm Leila kina wasa da damarki” Ta furta tana karewa kamfanin kallon, kalaman da ta yi ne suka saka Aminatu ta kalleta. Sai tai hade yawu ta ciro wayarta ta kira Talba ta mikawa Aminatu. “Hello” Jin muryar Aminatu ya saka ya amsa. “Shalele” “Na'am mun zo muna waje” “Okay, zan aiko a shiga dake yanzu nan” “Toh” Ta mikawa Madina wayar, Madina ta kai wayar a kirjinta ta rumgume tare da lumshe idonta bude. Ba jimawa wata mace sanye da suit kanta babu mayafi tana sanye da sarkar cross ta nufi inda suke ta gaisa da Madina sannan ta nunawa Aminatu hanya. “Malama Bismillah” “Ba zata iya tafiya ita kadai ba, sai kin taimaka mata” Matar ta rika Aminatu suka fara tafiyar a hankali har suka shiga ciki, sannan Madina ta koma motar ta tana ayyana irin kulawar da zata bawa Talba idan mafarki da take ya tabbata, sam bata hangowa kanta yadda taraiyar da Leila zata lalace idan har soyayya ta kullu a tsakaninta da Talba.   Aminatu na rike da hannun matar suna takawa a hankali har suka hau sama, daman kamfanin mai hawa biyu ne. Yadda take ganin mutane sai ya saka ta dan tsorata abun ka da bakauye, kamin su isa gurin office din Talba ya fito hannayensa duka biyu a aljihu, yana sanye da suit kala daya dana matar dake rike da ita, wato black color. Murmushi ya sakar mata sannan ya kalli matar ya ce. “Chidima sake ta, tafiyarki” “Okay Sir” Ta sake ta kamar yadda ya bukata ta juya ta bi wata hanyar, har lokacin murmushi yake yi ma Aminatu. “Tako ki zo nan” “Akwai zafi idan wani be rika ni ba ba zan iya tafiya ba” “To ni zan koma ciki idan ba zaki zo ba” “Wash.. Wash... Wash... Akwai zafi” Nan da nan har ta fara hawaye tana takawa a dolenta tana ta raki, hannunsa daya ya ciro ya miko mata alamar ta kama. “To ka matso” “Aa ki zo dai, Madina ta kyauta, ta gyara min ke kin yi kyau, kuma gashi har kina takawa” Daker ta karasa inda yake ta rika hannunsa suka karasa shiga karamin office din mai dauke da wata macen bahaushiya, da alama sakatariyarsa ce, sannan ya wuce office dinsa dake hannun dama. Yana shiga da ita ta fara rabon ido sanyin ac na ratsata, har gaban kujerar dake taburinsa ya kaita ya zaunar da ita. “Duk wannan katon office din naka ne?” Ya daga kai yana kallon office din kamar yadda take, sai ya dan tabe. “Ba Office dina ba ne” Ta nuna masa hoton Daddy sai ya juya ya kalli katon haton dake manne. “Abokin Daddyn ne mai kamfani shiyasa ya saka hotonsa, kuma yanzu yayi tafiya shi ne yace yana son na zauna a nan kamin ya dawo” Ta yi murmushi sai shi ma yai murmushi. “Murmushi na miki kyau, jiya ma kin yi shi da muna gidan marayun nan” Sai tai kasa da kanta. “Fada min me kika ci yau?” Ta daga hannunta tana taba teburin shi kuma ya zauna a kujerar dake facin din ta yana kallonta. “Da safe mun sha tea da birede kuma mun ci waina kwai, wannan kanenka ya zo ya duba ni, yana ta latsa min kafa yace wai Madina ta daina bari ina zaunawa, wai sai dai na yi tafiya” Tana fadar hakan Talba ya gane Kabir take nufi. “Ya kyauta, me kike son ki ci? Tea ko lemu” “Bana jin yunwa” Ya mike tsaye ya nufi firgin din ya bude ya dauko lemu ya zuba mata a lemu ya mika mata, sai ta karba da hannu biyu ta sha kadan ta rike raguwar. “Mai office din nan fada yake idan wani ya sha masa lemu ya rage” “Da gaske?” Ta yi saurin kai ragowar bakinta ta shanye da sauri ta mika masa cup din. “Na shanye duka” Ya karbi cup din ya juya yana dariya ba tare da ta gani ba. Sai da ya aje cup din sannan ya juyo ya dauki wasu takardun yana kallonta. “Mai office din nan baya son ayi masa bachi a office” “To ai ba bachi zan yi ba” “Ni ma ai ban ce bachi zaki yi ba, zan yi wani meeting ne kar na tafi ya shigo ya tarar kin yi bachi” “Ba zan yi bachi ba” Ya daga mata kai sannan ya dauki takardun ya fice a office din ya barta yaje meeting ko da ya dawo tana zaune tana kallon tv. “Ba ki yi bachi ba?” “Ai kai ce mai kamfanin bayan son ayi masa bachi, ban yi ba” Yayi murmushi. “Me kike son ki ci yanzu?” “Bana son komai” “To ni yunwa nake ji, bari mu kira Madina ta zo mu tafi siyayyar mu dawo na kaiku gida sai na je gida ni ma na ci abinci” Ta daga masa kai sai ya dauki wayarsa dake nan ya kira Madina, ringing daya ta daga. “Hello” “Baki tashi aikin ba?” “Ban gama ba, amman zan iya fitowa yanzu, tana bukatar wani abu ne?” “No ina son na tafi gida ne” “Okay gani nan zuwa” Ya aje wayar, sannan ya zauna a kujerar dazun yana kallon Aminatu. “Shalele, fada min me kika fi so lokacin da kina gida?” Ta fara bashi labarinta da yadda take rayuwar a kauye da yadda yayanta Sanusi yake yawan tsokanarta har zuwa abubuwan da suka faru sai gata tana ta kuka hawaye na sauko mata. “Ya Sanusi ai yana da gaskiya, ke raguwa ce abu kadan sai kuka, ungo wannan ki share hawayenki” Ya mika mata tissue, sannan ya tashi ya dauko mata ruwa ya zuba mata a wani kofin ya mika mata, ta karba ta sha wasu hawayen na sauko mata. “Shikenan komai ya wuce” Ya fada yana jin wani irin tausayinta ma kara kamashi. After like 30 minutes  Madina ta kira wayarsa ta sanar masa tana waje. “Ta so muje ta iso” Yana fadar hakan yai gaba sai ta ce. “Yallabai ba zan ita tafiya da kaina ba” “Raguwa” Ya fada sannan ya dawo ya rika suka fita tare, yana rike da ita har suka sauka kasa yana fitowa direbansa ya janyo mota ya iso inda suke tsaye, sai Talba ya budewa mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya kalli Madina dake tsaye. “Bismillah” Ta bude motar ta shiga duk kuwa da kasancewar ba haka ta so ba, a zatonta zai barta ta shiga front seat din ya saka Aminatu a baya, shiyasa ta bar motarta a gurin aikin ta hau Napep zuwa nan. Key din ya karba ya shiga motar yaja suka kama hanya. A hankali yake driving har suka isa Wani babban super market dake cikin garin gusau, yana yin fakin Madina ta bude ta fito ta zagaya ta sauri saboda ta samu rika Aminatu kamin Talba ya rika ta, har ga Allah bata son rikon da yake mata zuciyarta tana sosuwa ba kadan. Ta bude side din Aminatu ta rikota ta fito, yana gaba suna baya suka shiga super maket din. LEILA POV. Har wani huci take tana fadawa Momy abun da Madina ta fada mata. “Leila baki da wayo baki da tunani, yarinyar so take ta dora ki a keken bera, idan ba haka ba mi zai saka ta rika kiranki tana fada miki abun da yai ko yace? Ni fa gani nake kamar so take ta hada ku” “Haba Momy kamar baki san Madina ba, Wallahi ba zata yi haka ba” “Aman yadda take fada, ni na san Talba ba zai aikata hakan ba har da wani kiranta Shalele tana karawa abun gishiri kawai, zan dai iya yarda tace a kira mata shi, dan haka ki yi hankali da ita” Har Leila ta bude baki zata yi magana sai ga Amal ta shigo sanye da uniform din makarantar boko har dan gudunta. “Momy Daddy yana falo yana jiranki” “Yana jirana? Kamar ya? Wani abun kika fada masa ne?” Amal ta yi shiru tana kallon Momy, kamin Momy tai wani yunkuri har Daddy ya shigo dakin kana ganinsa kasan ransa a bace yake. “Amina kina ji kina gani Mu'az ya fita da yarinyar nan gidan nan?” Momy ta hade yawun bakinta ta kalli Amal. “Wallahi ban dauka abun zai kai haka ba, ban dauka Daddy zai dauka da zafi ba, Momy ki yi hakuri ba zan kara ba” Daddy ya kalli Amal sannan ya kalli Momy rai a bace ya ce. “Okay hakan yana nufi hanata kike ta fada min idan wani abun ya faru ko? Taya Mu'az zai dauko yarinya ya kawo ta a gidan nan sannan ke da yayanki ku wulakantata ki saka ya fitar da ita gidan nan? Ni kuka wulakanta ba shi ba ko ita, a tunani ko kare Ma'az ya dauko ya kawo a gidan nan ya kamata ki mutuntashi” “Ban ce ya fita da ita ba, Leila ta yi rantsuwa yarinyar ba zata zauna a gidan nan ba, tace sai dai ya zaba ita ko yarinyar, kuma ka san babu yadda za ayi na bar Leila na zabi yarinyar da ban san asalinta ba” “Miyasa baki tura Leila waje ba kin bar yarinyar? Ke har kullum ba zaki nuna cewa danki ba na ki bane dan wasu shi ne naki? Idan kin tozarta Mu'az kin ci mutuncin ribar mika ce? Akan Mu'az zan iya batawa da kowa, kuma ba zan dauki raini akan jinina ba, ba zan taba yarda a nuna masa isa ko rashin galihu ba” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Engineer wannan soyayya da kake nunawa Talba ta yi yawa, idonka ya rufe ruf baka ganin komai sai shi, ko yayanka baka so yadda kake son yaron nan, tsintacciyar mage bata taba zama mage ba, ni fa matarka ce amman idonka ya rufe akanTalba kana fada min magana son ranka dan Allah ka...” Momy bata karasa ba Daddy ya nuna kansa a razane. “Amina? Ni kike fadawa Tsintacciyar mage bata mage? Mu'az ne tsintacciyar mage? Yaron da ubansa ne sanadiyar arziki da nake ci a yanzu? Yaron da dan'uwana ya yafe karatunsa saboda ni na samu ingantaciyar rayuwa? Yaron da soyayyar mahaifinsa ta saka ya saka shi barin wasiyar idan an haifi masa da a saka masa sunana? Saboda uban yaron nan na samu ilmi har na zama abun da na zama a yanzu, karki manta babu abun da Mu'az yake nema a duniyar nan, dan'uwana be mutu ba sai da ya bar masa abun da zai isheshi kula da rayuwarsa, yaron da ba uwa ba uba? Ai ko da dan'uwana yana raye ba zan dauka a musgun ma dansa ba balle kuma ba shi da rai, dan'uwana yayi min komai Amina, dan'uwa na zame min uwa ya zame min uba, a lokacin da kowa ya kyare mu, dan'uwana shi ne ci na shi ne sha na, idan ina ciwo shi ne, saboda ni dan'uwana ya rasa rayuwarsa, yanzu kuma kike kiran dansa da tsintacciyar mage? Saboda ni dan'uwa na rabu da matansa biyu amman yau kin aibanta dan dan'uwana a gabana” Hawaye ya cika idon Daddy. “Na gode, indai maganar dana da nake ne ya zame miki fitina da tashin hankali, to na sauwake miki ki tafi inda zaki zauna ki samu kwanciyar hankali da natsuwa, ni kuma zan kawo wanda ke son dana wanda zata so abun da ya ke so, domin na tabbatar da Kabir ba zaki yarda ki masa wannan wulakancin ba, ba zan jure ko maganar banza a fadawa Mu'az ba, Wallahi ka bata masa rai kara a bata min rai, kuma har a bada ba zan wulakanta jinina ba...” Momy ta daki kirji da karfi tana fadin. “Engineer sakina kai?” Amal ta dora hannu akai ta fashe da kuka, Leila kuma ta yi sauri girgiza kai tana kallon Daddy daya juya zai fice daga dakin. “Daddy no please be kamata kai haka ba, abun da ba ayi da kurciya ba be kamata ka yi shi a yanzu da girma ya kama ma...” Juyowa Daddy yai ya kalleta. “Ba ke kika ja komai ba? Akan dana, zan iya batawa da kowa you too should be very careful...” Tsayawa tai cak tana kallon yadda ransa ya bace har wani huci yake irin ma su na manya. Sai da ya fice sannan ta juyo ta dawo gurin Momy dake tsaye tana ganin komai kamar a mafarki. “Momy dan Alla... ” Tassss Leila ta wanke fuskar Amal dake maganar da mari. “Dan ubanki ba ke kika ja komai ba? Duk abun da akai a gidan nan yana bakinki, komai aka yi sai ki je kin fadawa Daddy, yanzu ai kin ga ribar abun ko?” “Ya Kabir ne ya fada min, ni ban dauka abun zai saka a saki Momy ba..” Momy ta zauna tana nuna kanta. “Yau ni Alhaji zai saki saboda Talba? Abun da be taba min ba? Saki? Ni Aminatu?” Leila ta yi saurin dafata tana hawaye. “Momy dan Allah ki yi hakuri, zafin zuciya ne da bacin rai nasan anjima zai sauko ya gane cewar yayi kuskure” “Kar ma ya sauko, awa daya ba zan kara a gidan nan ba, je ki kira min Mairo ta zo ta hada min kayana ke da Shi sai kun dandana zafin rashina” Momy ta fada tana kallon Amal dake kuka. “Momy idan kika tafi mu zaki bari a damuwa dan Allah ki yi hakuri” Leila ta fada tana kuka. “Duk bakar yarinyar nan ce taja komai, duk ita ta haddasa mana fitina a gida” Amal ma ban da kuka babu abun da take, bata aikata wani abu taji ta yi nadamar aikata shi ba irin fadawa Daddy abun da ya faru. Momy ta mike tsaye a fusace ta sauka kasa ta nufi hanyar kitchen inda Mairo da zulai suke suna aikin hada abun karyawa. “Mairo Zulai ku shiga dakina ku janyo akwatunana ku zuba tufafi da yake wardrobe” “To Hajiya” Suka bar kicin din da sauri suka nufi upstairs, sai ta sake nuna kanta. “Ya sake ni? Lallai Engineer...” Ta girgiza kai tana jingina lamarin. FARUQ POV. Ko kadan sakin da Faruq yai ma Baturiya be yi ma Mama dadi ba. “Saki ba shi da dadi, amman halin yarinyar nan ya wuce inda muke tunani, sai dai bana son wannan abun ya taba zumuncin mu” “Inshallahu babu abun da zai samu zumuncin mu Mama, gobe zan je na kwaso tufafina na dawo da su anan, zan bar Sultan a nan ni kuma nan da kwana biyu zan bar garin nan na tafi nijar, idan Allah ya buda mana sai na samo a can idan na dawo sai na ayi wani auren, ita kuma zan cigaba da kula da ita saboda cikin dake jikinta” “Yaya ba za'a gyara ba?” Cewar Aisha cikin damuwa sai Faruq ya girgiza mata kai. “Bana son na yi uku, na riga na yi biyu kuma na riga na cire Rafi'a a raina, ba zan iya zama da ita a wannan sabon halin da ta fara ba, kuma duk wani cin mutuncin daya kamata ta yi min, ba ta inda ta raga min, nan gaba ban zan yadda abun zai zama ba” “Allah yasa haka shi yafi alheri ya baka ta gari, ita kuma ya shirya ta” “Amin, ranar alhamis din nan nake son tafiya inshallah, tare da Malam Sirajo” “To Allah yai maka fatahi a tafiyar, mutane na samowa, ko dan gidan Amadu ya samu yana dawowa ya siye gida da babur, amman tafiyar ce abun tsoro gashi ance ramen yana rusgawa da mutane” “Kawai ki min addu'a Mama dacewa kawai ake so” “To Allah ya datar da mu” “Ameen” Ya amsa sannan ya kwantar da Sultan dake jikinsa yana bachi kan shimfidar Mama. “Baka nan kenan za'ayi bikin Aisha” Mama ta fada tana kallon danta cike da tausayawa. “Bana son na kara sati a garin nan kam” Ba dan neman halal kawai yake son tafiyar ba, har da gujewa Baturiya saboda abun da tai masa da kuma sakin da yai mata ya tsaya masa arai yana jin babu dadi musamman idan ya tuna cewar saboda talauci tai masa haka. A dakin ya bar Sultan saboda Mama ta kula masa da shi, shi kuma ya nufi dayan dakin da ba a karasa ginewa ba ya shimfida tabarma da zane ya shimfida, sannan ya kunna maganin sauro ya kwanta, sai dai ko kadan bachin be ziyarce shi ba, sai tunani yake kala kala har safe. BATURIYA POV. Bata bar gidan ba sai da safe, sannan ta saka wasu tufafin ta saka Hijab ta rufe gidan ta tafi gidansu. Tun a Napep ta fara kirkirar kuka, sai dai kukan be zo mata har sai da ta sallami mai Napep din ta shiga cikin gidan, sannan ta fashe da kuka tana faduwa tana tashi hankali kowa sai da ya tashi a gidan. Cikin kuka ta fadawa Umma irin abun da ta fadawa makontata, a take ran Umma ya ace ta dauki waya ta kira Yayansu ta fada masa abun da ya fara sannan ta dada masa cewar tana son abi mata hakkin yarta. “Aa Umma ba a haka ko dan saboda zumunci” Cewar Alhaji Alfa daga can cikin wayar, sai Umma ta rufe shi da masifa. “Shi be duba zumuncin ba yai mata abun da yai? Ga ta da ciki yai mata wannan duka haka ga kuma cin mutunci saboda wasu karuwan banza a waje, ba zan lamunta ba idan kai ba zaka iya ba ni zan dauki mataki da kaina, domin ba zan lamunta aci zalin yata ba bayan bakin talauci sannan kuma ya hadota da saki bayan ya mata duka” “Zan yi wani abu akai Inshallahu, aman ita ma ki bincike ba zai yiyu haka siddan Faruq yai mata haka ba ba tare da wani dalilin ba, Faruq ba irin mazan nan ne ba Umma, amman yanzu zan yi wani abun inshallah” Da haka suka yi sallama, sannan Baturiya ta tashi ta shiga dakin Umma tana kuka kamar gaske, tana shiga ta bude jakarta ta dauko wayarta ta akashe ta saka wayar karkashin gadon Umma. “Kuma cikin nan Wallahi zubar da shi zan yi, ina zubar ba na cika idda na auri saurayi kai kuma kai ta fama da talauci auren ma sai ya maka wahala” Ta fada tana wani cika, sai a yanzu take jin zafin sakin da yai mata kukan na gaske da gaske ya zo mata. 26 Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Madina ce take ta mata zaben tufafin da zata saka, daga atamfa zuwa abaya da shadda da kuma lace ta daukar mata kusan kala 25, ban da talkami da hijab da veil. Suna zuwa gurin biya kamin su yi wani yunkuri ta mika atm dinta. Talba ya kalleta. “i can pay” “Dan Allah ka bari na yi wannan aikin ladar” Be saki cewa komai ba, ya kalli Aminatu. “Muje mu jirata a mota” Ba musu Aminatu ta mika masa hannu ya rikata tana takawa a hankali suka fice, kamar dazun a yanzun ma front seat ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya zauna a side dinsa. “You got lucky ba yayanki kadai yake son hidima dake ba, har da Kawar Matata” Kallonsa kawai tai ta sauke kai kasa, shiru ne ya biyo baya har Madina ta fito tare da masu rika mata ledodin kayan Talba ya bude musu bayan motar suka saka, sannan ta rufe ta bude back seat din ta zauna, yana kokarin yin reverse ta mika masa box din agogon hannu that worth 150k. “Zan yi farinciki idan ka karbi wannan kyautar daga gareni” Kallonta yai sai kuma ya kalli Amintu. “Shalele karba min” Aminatu ta karba ta rike ba tare data buda ba, har suka isa gidansu Madina be karbi agogon ya duba ba, balle yai mata godiya, hakan da yai sai yasa ta ji wani iri, yanzu kam ta tabbatar akwai babban aiki a gabanta, domin samun abun da zai burge Talba a take ko kuma ya dauki hankalinsa ba abu ne mai sauki ba. A harabar gidan ya faka motarsa, ya mika hannu ya budewa Aminatu. “Ki taka da kafarki ki fita, kuma ki rika tafiya ke kadai ba sai an rika ki ba” Ta lake kafada tana dan turo baki, sai dai bata ce masa komai ba kuma bata yarda ta kalli inda yake ba. Shi kam sai kallonta yake yana ayyana irin shagwabar da take a gaban iyayenta domin kana ganinta ka san shagwababbiya ce, dan farin ma wani yai shagwaba balle auta autar ma ta maza. “Yaya Madina zaki rika ni ko?” Ta fada tana jiya fuska ta kalli inda Madina take tsaye tana mikawa hadiman gidan ledidin hannunta. “Eh” Ta fada sannan ta nufo inda Aminatu take zaune ta rikata, sai da Aminatu ta aje masa agogon sannan ta fita Madina ta rufo masa motar. A tunaninta zai mata godiyar siyayyar da tai ma Aminatu amman bata ji hakan daga bakinsa ba, ta san kuma hakan ya masa dadi ko da ba a fada ba, sai a yanzu ta tabbatar da miskilacinsa ya wuce inda take zato. Sai da suka shige cikin main house din sannan ya ja motarsa ya bar gidan, at first restaurant ya so ya tafi ya ci abinci even though baya son cin abinci a waje sai dole, but yana son ya kaurace ma cin abincin Momy saboda ta fahimci be jidadin abun da tai masa ba, sai dai hakan ba zai saka shi gaba da ita ba, kamar yadda dazun ma be kasa kiranta a waya yai mata barka da safiya ba, bayan kuma ya saba da shiga part din ko wace safiya ya gaishe ta. Kamin ya karasa restaurant din kiran Amal ya shigo wayarsa, sai yai picking call din ya saka wayar a hands-free ya aje ta kusa da shi. “Lil Sis” “Yaya” Ta amsa masa cikin kuka, ya san halinta da shagwaba sometime kan sily abu sai tai ta kuka, hakan yasa be tashi hankalinsa ba. “Waya taba ki me kike yi ma kuka?” “Momy ce ta yi fada da Daddy, kuma har ya sake a ta debi wani tufafinta ta bar gidan, ta bar mu ni da Leila tun dazun sai kuka muke” Wani irin faduwar gaba ne ya same shi, sai yai sauri sauka daga titi ya faka motar gefe, ya dauki wayar ya kai kunnensa. “Ba a wasa da irin wannan maganar Amal” “Wallahi da gaske nake” “Miya faru?” “Ni na yi komai, Ya Kabir ya fada min abun da ya faru ni kuma na fadawa Daddy, shi ya zo bangaren Momy yana ta masifa and Momy ta kiraka da tsintacciyar mage, shi kuma yace ba zai dauka ba, shi ne ya saketa...” Be ce mata komai ba ya yanke wayar, ya shiga kiran Daddy, amman har wayar tai ringing ta gaji ta tsinke Daddy be daga ba, Talba ya sake kiransa nan ma the same thing, tun yana kira yana sa ran zai dauka har ya cire rai, hakan ya tabbatar masa da cewar ran Daddy ya bace sosai, domin abu ne mai wahala yai masa two miss calls be daga ba, amman a yau ya jera masa 11 miss calls be yi picking ba. Sai ya sake kiran Amal. “Yana gida?” “Aa ya fita” Ya yanke kiran sannan ya duba agogon hannunsa biyu saura kwata ya gani, take hau titi ya fisgi motar kamar zai bar gari, cikin yan mintuna sai gashi Harabar ma'aikatar su Daddy, ko fakin din kirki be yi ba ya fito da sauri ya shiga cikin ma'aikatan, kusan ya san mutane da yawa a ciki kamar yadda mutanen gurin ma suka san shi saboda yawan fadarsa da Daddy yake da kuma zuwa gurin, sai dai be tsaya gaisawa da kowa ba daman ba gaisuwar yake so ba, saboda ta zame masa kamar ta dole ce kasancewar su abokan mahaifinsa. Kai tsaye ya nufi bangaren da office din Daddy yake yana ta zuba sauri. Sai dai yana shiga sakariyar ta hana Talba ganin Daddy. “Yace baya son a dame shi kowaye ya zo kar a bari ya shiga ciki” “Kin san waye ni kuwa?” Talba ya nuna kansa. “Na sani dan Allah kai hakuri, aikina nake yi” Ta fada cikin damuwa, sai ya wuce ta ya karasa gurin office din ya bude ya shiga ita kuma ta biyo bayansa da sauri tana kokarin dakatar da shi. “Duk kika yi kuskuren taba ni sai na mareki Wallahi” Ya furta yana nuna ta da yatsansa, babu alamar wasa a fuskarsa. Daddy dake tsaye yana kallonsu ya ce. “Amman na tabbatar da kai ne, korarta zaka yi, yanzu kuma kana kokarin hanata aikinta, you can go Hannatu” Sai ta juya da sauri ta fice. Daddy ya kalleshi. “Ya akai?” “Haba Daddy miya saka zaka yi haka?” “Hey my friend, control your tongue, I'm your father and you're my son, so ni zan tambayi dalilin da zai saka kai wani abu ba wai kai tambaye ni ba” Talba ya karaso kusa da teburin Daddy cikin yanayin damuwa. “Daddy please, be kamata ba Wallahi, da girmanku ace kun rabu? Mu ya kake son ku yi? Baka duba Amal da Leila ba? Baka duba ni yadda zan ji ba? Da wane ido zaka kallemu? And baka yi tunanin yadda Momy zata ji ba?” “So a idonku nine mai laifi? Ni baku ayyana yadda zan ji ba?” “Ni kullum a gurina kai ne mai laifi daddy, kai namiji ne ya kamata ka rika kawarda ido, amman sai ka rika biyewa Momy da take mace? Hankalinta da tunaninta ba daya ba ne da naka” Daddy yayi murmushi ya nuna masa kujera. “Have a seat my friend” “No ni ban zo nan domin zama ba, kawai na zo na dauke ka ne mu tafi da kai ka bawa Momy hakuri ka dawo da ita” “Have a seat” Daddy ya maimaita wannan karon ya fada tare da zaunawa. Sai da Talba ya sauke ajiyar zuciya sannan ya zauna. “Fada min gaskiya, ban san ka da karya ba Son, abun da Amina tai be bata maka rai ba?” “I feel bad, amman be kamata ya saka ka yanke wannan hukuncin ba” “Ban yanke hukunci saboda ta kori yarinyar daka kawo ba, na yanke wannan hukuncin ne saboda ta kira ka da tsintacciyar mage” “Fushin zuciya... ” Daddy yayi saurin dakatar da shi with serious face ta hanyar daga masa hannu. “No, bari na baka wani labari da ban taba fada maka ba. A cikin wani babban gida mai rufin asiri mata har hudu, kowa a wannan gidan yana da manyan y’ay’a da kanana, ko wace mace a cikin matansa ta haihu shida wata tara wata goma sha daya, sai karamar matarsa ce kawai ta haifi yaya biyu maza wanda ta kasance karama ce kuma ita ce ta hudu, tana tsaka da rainon yayanta sai mutuwa ta sallamo mata, yaya da kanensa suna daji gurin noma, ka zo kiransu aka fada musu cewar mahaifiyarsu bata da lafiya, sai dai kamin su kawo rai yai halinsa, ita ce karama kuma ita ta riga tafiya ta bar kananan yayanta guda biyu, haka yaran biyu suka tashi cikin yan'ubanci da kuma kyara ta matan uba, idan uban ya dawo sai a nuna ana son su kamar za a hade su, idan kuma ya saka kafa ya fita abinci ma sai sun yi bara su ci, wata rana kwatsan wannan mutuwar ta sake kwankwaso kofar mahaifinsu, kuma ta dage sai da ta tafi da shi, daga lokacin sai rayuwa ta kara zame musu abun tausayi, domin a gidan da suka taso gida ne da babu hadin kai a ciki, kowa kansa ya sani kuma ga kishi da nunawa uba aka hada ba uwa ba, idan aka dafa abinci masu ake bawa, ba marasa uwa ba, idan sallah ta tashi sai dai yan'uwa mahaifiyarsu su yi musu dinki, wani lokacin abinci ma a can suke zuwa su ci, suna cikin wannan rayuwarsa sai yayan ya fara bin shanu yana rakiyarsu zuwa inda ake saidawa sai masu shanun su biyashi, sai kuma ya shiga daji yai itace sai ya shiga gidaje ya bada itacen a bashi abinci sai kawo wa kanensa, kudin da yake tarawa kuma idan kanensa yana jin yunwa ko rashin lafiya ta kama shi, zai siya masa magani ne, da haka ya fara faskare, da duk wani aikin karfi da yan'uwan mahaifiyarsa suka samu labari sai suka zo suka dauke su suka tafi da su gurinsu, sai dai hakan be kashe guiwar yayan ba, da yan kudin da ya samu ya saka kenansa a makaranta, kullum kokarinsa na yadda dan'uwansa zai gina kansa ne, da wannan tunanin ya tsallaka zuwa birni yana achaba, daga nan ya fara zuwa kudu, idan ya samu kudi sai yace a bawa Mu'azu, a siyawa Mu'azu abu kasa, a biya masa kudin makaranta, sannu sannu dan'uwansa yana ta karatu shi kuma yayansa yana ta neman kudi saboda rayuwar kanensa ta inganta, achaba da yake a can sai ya karbe shi har ya zamana yana zuwa siyen wasu abubuwa daga nan arewa ya kai can, wani abun kuma sai ya siyo ya zo da shi nan, kamin a ankaro kudi suka taso masa kofafin arziki suka bude masa, sai ya dawo a nan yai aure, ana zaune kalau kanensa yana zuwa makarantar kwana a birni idan hutu ya samu sai ya dawo gida, sai matar yayan ta fara nuna bata son kanensa tana hana shi yi masa wasu abubuwan daya kamata, ganin haka yace ba zai iya sake dan'uwa ba, amman zai iya canja mata, sai ya sake ta ya auro wata, ita ma da ta zo sai ta fara nuna wannan halin, a take ya sallame ta ya auro wata, bayan ya jaddada nata cewar shi kam a duniyar nan be da kamar dan'uwansa, sai matar nan ta rike kenan da mutuncin da amana, shi kuma ya maida hankali gurin kasuwancinsa, har ya zamana yayyunsa da suka wofintar da shi a wacan lokacin suka dawo suna neman ci a karkashin inuwarsa, wasa wasa ya fara siye gonaki da gidaje irin na kauye yana saidawa yana samun riba, kamin kace kwabo ya zama daya daga cikin masu kudin kauye na wacan lokacin duk da kasancewar yana da samarta ba tsoho ba ne, da haka ya fada siyasa sai kuma abun ya karbe shi kofofi suka bude masa, yai taraka kuma ya cinye, sai dai har kanensa ya gama karatu ya tafi jami'a Allah be bawa yayansa haihuwa ba, yana cikin karatun ya hadu da wata a jami'ar suka yi aure, yayan ya siya masa gida a birni suka zauna, ana wata na uku da saurensa ya samu aiki a babban gurin saboda yayansa babban dan siyasa ne na taraiya, a kuma wannan lokacin matar yayan ta samu ciki, a kullum wakensa idan ta haifa masa namiji za a saka sunan kanensa, idan kuma mace ta haifa za a saka sunan mahaifiyarsa, ashe Allah be yi ba zai ga abun da zai haifa, wata rana aka samu wani gurbi na babban matsayi a Lagos, sai ya dage akan sai kanensa za a bawa saboda yana da takardu da duk wani abu da ake bukata, sai dai abu na yan siyasa su ma wadancan suna so, bayan ya bada sunan kanensa da takardunsa, sai abokin hamayyarsa yace ya saurari abun da zai same shi matukar be janye kudirinsa ba, be fada masa baki da baki ba, amman ya fada ta inda zai iya ji kuma ya ji, amman be janye kudirin ba, abun ka da mutanen kauye ana zaune kalau kafarsa ta fara kumbura har ya zamana baya iya zuwa majalisa, har ta kai ko gidansa baya iya fita, cikin sati jikinsa ya kumbura kamin wani makon ya dawo ya ce ga garinku, haka muka ta jimamin rashinsa musamman ne kuma mutuwarsa bata hana Allah hukuncinsa ba na dora ni a wannan matsayin, ashe kuma wani kukan yana tafe a gaba, a lokacin da muke ta murna matarsa ta shiga watan haihuwarta zata haifa mana da ko ya, ashe ban kwana take ta mana ba mu sani ba, ranar da ta haihu aa fiti ana da lafiya kalau mahaifiyarsa kuma ta koma ga Ubangijinta... ” Tun da Daddy ya fara bawa Talba labarin be mumfasa ba sai da ya kai aya. “Ka san waye wannan yaya da kanen Mu'az...?” Talba ya kalli Daddy hawaye na sauko masa, kamar yadda suke saukowa Daddy. “Kai ne kanen Daddy shi ne Yayanka... ” Daddy ya girgiza kai yana cige bakinsa da karfin sosai yake yakar zuciyarsa yana hanata kukan dake son gabato masa da shi, daya wuce na zuciya har yake neman muhalli a bakinsa. “A haka kaka tunanin wata macen zata kalli kwayar idona ta kira dan 'uwana na jini da jini da tsintacciyar mage kuma na kasa fusata na kasa yin komai? Macen da take karkashin ikona da kulawata? Ina raye wata mace tana nuna min tafi son yayanta da dan'uwana na jini? Ina jin sonka a cikin jinina Mu'az, ina jin wani irin son a jini da zuciyata, bana jin akwai wani uba da yake son dansa kamar yadda nake sonka, ko kadan bana son na ji wani abu da zai bata maka rai, zan iya daukar komai ban da a taba ka” Talba ya mike tsaye hawaye na sauko masa ya nufi windows din office din Daddy ya tsaya. Sai Daddy ya dauko tissue ya goge hawayensa yana kallon Talba. “Ban taba baka labarin nan ba, saboda bana son ka ji a ranki cewar kai maraya ne, alhalin ina raye” Talba kamar jiran kalaman Daddy yake, sai ya fashe da kuka marar sauti irin na maza ya jimke hannunsa zuciyarsa na sosuwa da labarin da Daddy ya bashi. Da hannunsa na dama ya share hawayensa sannan ya juyo ya kalli Daddy yana jin wani irin shaukin kaunarsa. “Ka yi duk abun da ya kamata Daddy, shiyasa ban taba jin maraici ba, kuma ban taba tambayar labarin iyayena ba, ka bani gata ka nuna min kauna wanda ba ko wane mai uba ke samu ba” “Abun nan akwai ciwo Mu'az, saboda ni ma na taso a maraici, kana ji kana gani abu ya gagareka, kana gani a nun maka abu nan ba naka ba ne, idan aka bata maka rai, babu uwa ko uba da zai rarrasheka ya baka hakuri, musaman ma uwa, shiyasa ba zan taba bari kai maraici ba, idan har kaga ka rasa sai idan bana raye, ko da ma ace na mutu na ginaka kuma na bar maka abun da zai taimaki rayuwarka ba zaka taba rasa komai ba, ba zaka taba kukan rashin uwa ko uba ba, musamman uwa” Talba ya gyada kai wasu hawayen na sauko masa. “Kamar yadda na ji a yanzu nan Daddy, amman duk da haka Ina rokon Alfarma a yafewa Momy, ita ma ta rike ni kamar danta, na taso ban ta wata uba ba bayan ita, dan Allah Daddy ka dawo da ita” “Of course zan dawo da ita, do you think I can live without Amina? Zan dawo da ita amman sai ta karbi hukuncinta, ni ma ina fatar za a daga min kafa” Talba yayi murmushi idonsa na cika da wasu hawayen. “Ina kaunarka Daddy, Allah kara maka lafiya” “Amin Allah ya maka albarka” “Amin” Ya amsa sannan ya dauki tissue ya gyara idonsa, sannan ya nufi kofar fita. “Mu'az ina ka kai yarinyar nan?” “Gidansu Madina” “Ka dawo da ita gida” “A can din ma ta fi sakewa, Madina tana sonta” “Baka da inda yafi gida, kuma be kamata akaita ko'ina ba, bayan ga inda kake da iko” “Na ji, amman sai ka fara dawowa da Momy” Daddy yayi murmushi yana daga masa hannu alamar ya tafi, shi ma murmushin yai kadan ya fice yana jin zuciyarsa wani iri, samun kansa yai a motarsa yana ta sauke ajiyar zuciya, be taba jin irin yadda yake ji a yau ba. Sai dai babu wanda ta fado masa a rai sai Aminatu, shi da be taba ganin iyayensa ba, be san su ba amman a yau yaji yana marmarin ganinsu yana kewarsu balle ita data rayu da iyayenta ta girma tare da su ta san dadinsu ace an raba ta da su lokaci daya, kuma a gaban idonta, ya tabbatar abu ne da ba zata taba iya mantawa da shi ba, ba kuma zai gogu a zuciyarta da idanuwanta ba. A masallacin gurin yai sallah azahar sannan ya fito yana ta tukin ba dan ya san inda zai je ba, baya tunanin zuwa gida a yanzu, dan baya jin zaman gidan zai masa dadi, but ina zai je? Office? No baya bukatar komawa can, gurin Ali? Nope zai fara damunsa da maganar Leila, haka yai ta yawo idan ya gaji da tukin sai ya saka motarsa ya zauna a motar, uku da rabi ya nufi gidan marayunsa be fito ba sai hudu da rabi. Kai tsaye ya nufo gidansu Madina domin zuciyarsa ta bukaci ganin Aminatu, be kira Madina ya fada mata gashi zuwa ba, balle ta san da zuwansa, he just want go ba tare daya sanar mata ba, sai da ya isa gate din gidan sai kuma ya ji wani iri, kar mutanen gidan su ce ya cika zuwa, tun da dazun ma ya zo, gashi yanzu baya cikin yanayin na walwala. Amman ya kamata ya koma b tare da ya ga Aminatu ba? Bayan ya kudurtawa kansa son magana da ita? Hannu ya kai ya dannn horn sau biyu mai gadin ya leko ya ganshi sai ya koma ciki ya bude masa gate din. Tun kamin ya karasa harabar gidan ya hango Aminatu zaune a parking lot sanye da daya daga cikin rigar da suka siyo dazun picking color, bakinta ya sha man lebe har wani sheki yake gashin kanta kuma ya sha gyara, an basa mata shi ya sauko har bayanta, sai wata yar karamar farar hula wanda ke bayyana gashin tsakiyar kanta da kasan gashinta, sai a lokacin ya tuna dazun be kaita gurin gyaran gashin ba, and now he think Madina ta kaita ko kuma ta gyara mata. Tana zaune kan kujera kusa da wata mota, sai dan karamin teburi a gabanta mai cike da littafai textbooks hannunta rike da biro. Ana bude gate din ta dago tana kallon motarsa har ya karaso kusa da ita ya faka motar ya sauke gilashin motar yana kallonta. Ita ma kallonsa take har ya bude motar ya fito ya rufe a hankali ya karaso kusa da ita cikin yanayi na damuwa. “Ina wuni” “Lafiya kalau, me kike a nan ke kadai?” “Na gaji da zama ciki ne shi ne Ya Madina ta fito da ni tace wai na sha iska, ta bani abun rubutu” “Kin iya rubutu ashe?” “Ajami ba” Ya kai hannu ya dauki littafin da take rubutu akai. _Ina samun natsuwa a kalamanka, kamar yadda ganinka ke kwantar min da hankali, rashinka yana nufin mutuwata, samunka kuma farincikina_ Yayi murmushi bayan ya gama karantawa, sannan ya kalleta. “Ashe kin iya kalaman soyayya” Sai tai kasa da kanta tana murmushin daya kara bayyana kyauta da hasken bakar fatarta. “Ina rubutawa wani saurayina shi kuma yana rubuto min, idan zan tafi talla sai ya ba ni ta shi, ni kuma na a shi tawa, duk da ajami muke rubutawa, kamin rayuwarmu ta canja, ni na dawo nan shi kuma ya tafi inda ba a dawowa” Ta karasa idanuwanta na cika da kwalla. Sai ya risina gabanta yana kallon kyakkyawar fuskarta. “Kin rasa abubuwa da yawa, kina da juriya na injina miki, yanzu fada min ya kike ji?” Ta dago ta kalleshi. “Ba dadi, sabawa da mutanen da baka sani ba, abu ne mai wahala, na kasa manta iyalina” “Na fahimta” Ya fada yana kallon wani gurin dabam, hakan ya bata damar kare masa kallo, fari ne fes irin farin nan mai kyau da daukar ido, ga wani dogon hanci da sauko masa gashin kansa ma sai sheki yake, abu ne mai wahala a iya yi masa kallo daya a kawar da ido. Ba kyaunsa ne kadai abun da idanuwanta suke nuna mata ba, har da damuwar dake fuskarsa domin bata taba ganinsa a haka ba. “Kai ma kana da damuwa...?” Ta tambaya cikin tsoro da fargabar irin amsar da zai bata, juyowa yai ya kalleta sai tai arba da kyakkyawan Murmushin daya fadada fuskarsa. “Ya akai kika gane?” Ta yi shiru tare da sauke idonta kasa. “Ina ce miki Shalele kin cancanci sunan, saboda kin rayu da iyeyenki kin jin duminsu, kin san muryarsu, kin san farincikin da damuwarsu, a karon farko yau na ji ina kewar mahaifiyata duk da kasancewar ban taba ganinta ba, amman ina jin kamar na kirata ta amsa min, kamar tace Talba be dace kai wannan ba, wannan ya dace kai, ban san maraici ba amman ina jin son ganin mahaifiyata ko da sau daya ne a rayuwata” Yanayin yadda kalaman suke fitowa daga bakinsa kadai sun isar da kewar dake zuciyarsa. “To ai Daddy yana raye, ka rika kallon dabi'unsa da kamaninsa kamar na mahaifinka, mahaifiyarka kuma sai ka nemi hotonta ka rika kalla” Murmushi yake yana kallonta kamar ba shi ba. “Kina da wayo Shalele, kin fahimci damuwata a take kuma kin sama min mafita duk da karancin shekarunki” Ya fada yana kai hannu ya taba halshen gashinta. Sai ta kai hannu ta sanye gashin. “Waya gyara miki?” “Ya Madina, gata can” Mikawa tai tsaye daga ita har shi suka koma kallon entrance din da Madina ta fito sanye da dogon Hijab ta nufosu da saurinta. “Sannu da zuwa” Ta fada a yayinda ta karaso kusa da su, sai ya daga mata kai alamar ya amsa. “Ban san ka shigo ba sai yanzu bari na kawo maka ruwa” “Ka ci abinci dazun ka ce min kana jin yunwa?” Aminatu ta tambaya, sai ya kalleta ya girgiza mata kai alamar a'a. Sai Madina ta kalleshi. “Ko na dafa maka wani abu? Zama da yunwa be da kyau” “Ruwa kawai” “Okay” Ta juya da sauri sai ya kira sunanta. “Madina...” Ta juyo da saurin gabanta na faduwa a zatonta ko zai ce ya fasa shan ruwan ne. “Thank Youuuuuuuu” Suma ne kawai ba tai a gurin ba, amman ta yi mutuwar tsaye har ta kasa yarda da ita yake. Ita fa? Madina yace wa Thank you after celled her name kuma yace mata ya gode, godiya fa yake mata...? Murmushi ta sakar masa duk da kasancewar babu murmushi a tasa fuskarsa ta juya ba tare da tace komai ba ta cigaba da tafiya, tana jin kamar ta zuba ruwa kasa ta sha dan murna da jindadi, yadda ya kira sunanta ma abun alfahari ne a gurinta, sai ta ji kamar ba a taba kiran sunanta da lafazi mai dadi irin na Talba ba, lastly zai sha ruwan hannunta. 27 Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Yana tsaye a gurin kusa da Aminatu har ta fito da glass cup dayan hannunta dauke da gorar ruwa. Tana isowa ta mika masa cup din ya karba sannan ta bude ruwan ta zuba masa, sai ya sha kadan ya mika mata cup din, ya juya ya nufi mota ba tare da yace da ita komai ba, haka ma be yi ma Aminatu sallama ba, daga ita har Madina binshi sukai da kallo har ya shiga motar ya fice daga gidan. Sannan Madina ta kalli Aminatu. “Idan kin gama ki min magana zan shiga dake ciki” “Toh” Ta juyo tana ta kallon gate din kamar ance mata Talba zai dawo, ta nufi kofar falon cikin wani irin farinciki, ta shigo falo, bata ko kula Hajiya dake falon ba ta nufi kitchen, cup din ta aje ta kara ruwan gorar hannunta sannan ta dauka ta saita bakinta a inda Talba ya sha, tana sha tana murmushi. “Madina...” Ta juyo da sauri ta kalli Hajiya hannunta rike da cup din. “Na'am Hajiya” “Waya zo yanzu?” “Talba ne” “Miyasa be tafi da yarinyar ba? Ba kin ce kwana biyu zata yi ba?” Ta yi kasa da kanta. “Hajiya gaskiya ba kwana biyu zata yi ba, kusan zata zauna a nan ne kamin abubuwa su daidaita a can gidan, yanzu haka Momy bata gidan sun samu matsala da Daddy har ya turata gida” “Saboda yarinyar?” Ta daga mata kai. “Eh saboda abun da Momy tai ma Talba a kan yarinyar” “Amman shi Talba ba yana da yan'uwa uba da uwa ba? Miyasa be kaita can ba sai a nan? Saboda mu ya raina mu ko kuma saboda me? Ke baki tunanin aje a nan zai lalata alakarku da Leila ko mahaifiyarta? Ni kaina sai ki ga abun ya shiga tsakaninmu da Hajiya dan mutuncin da muke ma mu daina” “Bana fatar hakan Hajiya, kuma ba wai ya dauke ta kai tsaye ya ba ni ba ne, ni na bukata” Hajiya ta yi mata wani kallo na mamaki. “Saboda...” “Saboda na faranta masa rai” Ta amsa kai tsaye, sai kuma ta aje kofin hannunta ta karasa kusa da mahaifiyarta ta kama hannunta cikin yanayi na damuwa. “Hajiya ke mahaifyata ce, na san ko ban fada ba kin fahimta, Wallahi ina matukar son Talba na rasa yadda zan yi” Hajiya ta yi saurin janye hannunta daga rikon da Madina tai mata. “Kul...!!! Karki yarda son zuciya ya debe ki ya kaiki ya baro karki, Aminiyarki? Kuma mijin da zata aura? Ki ce kina sonsa? To me kike tsammani zai juyo gurinki ya bar zabin iyayensa? Anya kin shirya yin takara da Leila? Hajiya bata has akan yayanta, karki kuskura dinke rigar kanki inda kai ba zai fito ba balle sauran jiki, domin wahala kawai zaki sha ki tashi a tutar babu kuma tutar kunya” Hawaye ya cika idonta. “Na yi iya yadda zan yi na yaki abun nan Hajiya, na yi iya yadda zan yi na kawarda idona daga Talba, amman na kasa, na yi ta hangowa kaina matsalolin dake tattare da hakan, amman zuciya na raya min zan iya dauka, na san kawance na da Leila mai zurfi ne, mun taso tare an girma tare mun zama kamar yan'uwa, be kamata na yi hakan ba, amman wata kila wannan ce kaddarata, Wallahi Hajiya ina matukar son Talba fiye da yadda Leila take sonsa” Maganar take cikin kuka hawaye na sauko mata. “Ki gaggauta cire shi a zuciyarki, kuma bana son yarinyar nan ta wuce yau, ki fada masa na ce ya zo ya dauke ta, daman ai na lura da take taken ki ba tun yau ba” Hajiya na kaiwa nan ta juya ta fice, sai Madina ta durkushe a gurin ta fashe da kuka. Kuka tai sosai marar sauti sannan ta mike tsaye ta nufi dakinta tana shiga ta kulle kanta ta fara rusar kuka kamar wanda akai wa mutuwa, can kuma ya dauki wayarta ta shiga gallery wayarta ta kamo hoton Talba ta tisa a gaba tana ta kallo hawaye na yi mata sallama. Wani irin abu take ji marar misaltuwa, da daske yanzu kam ta tabbatar sonsa take fiye da kima, tun da har sonsa zai saka ta kasa ganin Leila kuma kunnuwanta su toshe daga maganganun da mahaifiyarta tai mata. tashi tai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito falon idonta har ya canja kala, sai da ta zauna sai kuma ta ji zaman baya mata dadi, sai kawai ta mike tsaye ta fice daga falon zuwa parking lot inda Aminatu take zaune. Tun kamin ta karaso Aminatu take kallonta da karantar yadda yanayinta ya canja daga far'a da jindadin da ta shiga da shi dazun, zuwa fitowa da damuwa da kumburarin idanuwa. Zuwa tai ta tsaya akan Aminatu ba tare da tace mata komai ba. Aminatu ta tsayar da rubutun da take tana sauraren abun da Madina zata ce mata ammam shiru bata ce mata komai ba har na tsawo lokaci. Hakan yasa ta dago kai ta kalleta sai ta ga hawaye na sauko mata. “Yaya Madina baki da Lafiya ne?” Madina ta lumshe ido wasu hawayen na sauko mata. “Ba ni da lafiya Aminatu, kuma ciwo ne da ba zan tana warke shi ba, ciwo ne da Allah ya dora min, kuma kowa ya kasa fahimtata” “Me ke damunki?” “Ciwon son, ciwon son wanda be san da wanzuwar son ba” Aminatu kan kallonta kawai take ba dan ta fahimci inda kalamanta suka dosa ba, sai dai ta fahimci son wani take amman wanenen wanda be san da wanzuwar son ba? Dukawa tai gaban Aminatu kamar mai neman gafara. “Hajiya tace dole ne na dauke ki daga gidan nan tsakanin yau da gobe, ni kuma bana son ran Talba ya bace, ban san yadda zan yi ba, daman na fada mata cewar zaki zauna na kwana biyu ne, bana son bata ran Talba, kamar yadda bana son tsabawa umarnin mahaifiyarta” “Shine kike kuka?” Ta girgiza kai. “Aa abun da nake yi ma kuka dabam” “Ki kirashi a waya Sai ki fada masa na ce bana son zama a nan” “Zai iya zargin wani abu, bana son abun da zai nisanta ni da shi, ko ya saka ya ga kamar ni ce bana son zamanki a kusa da mu” “Zan fada masa gaskiya ba amin komai ba” Saaz  ta fada tana Kallon Madina, sai Madina ta hade yawun bakinta ta saka hannunta ta share hawayen da suka zubo mata. Sai da ta kira Talba sannan ta kara wayar a kunne. “Hello...” Ta fada bayan ya dauki kiransa jin muryarta sai yai shiru be ce komai ba, bata damu ba ta cigaba da maganar. “Aminatu ce, ta dame ni da kuka na tambaye ta me ke damunta bata fada ba” “Tana ina?” Ya tambaya daga dayan bangaren. “Gata nan kusa da ni” Ta mikawa Aminatu wayar, sai ta karba ta kara a kunne. “Hello” “Shalele lafiya kike kuka?” Ta yi shiru tana kallon Madina. “Ko saboda na tuna miki da baya ne?” “Aa bana son zama a nan ne?” “Ba ki son zama kuma? Miya faru?” “Ba komai ni dai bana son nan ka zo ka dauke ni” “Ana miki wani abu ne da baki so?” “Aa ni dai ka zo ka tafi da ni” “Okay zan zo” “Yaushe?” “Yanzu ko anjima” “Toh” Ta mikawa Madina wayar. Sai Madina ta karba ta kai kunnenta. “Hello” “Akwai abun da akai mata ne?” “Wallahi babu, amman ban sani ba ko ita tana da abun da take son fada maka” Ne sake cewa komai ba ya kashe wayar yana busar da iskar bakinsa. Ali ya kalleshi. “Ya akai?” “Shalele ce, wai ba zata zauna a gidansu Madina ba tana son na zo na dauke ta” Ali ya masa wani kallon na mamaki. “Ka kaita ina?” Sai ya daga kafadunsa ya jingina da motarsa. “Wannan abun yayi yawa Talba? Sunan ma da kake mata ka daina domin Leila ba zata jidadi ba idan ta ji, kuma karka dauko ta daga can” “Idan kuma ana mata abun da bata so fa? Wata kila suna musguna mata ne, ba zata iya fada ba ne a gaban Madina” “Okay let assume that ana mata wani abun, idan ka dauko ta gidanku zaka sake maida ta saboda Daddy yace ka kawo ta? Kana ganin tunani ne mai kyau ka dawo da ita bayan Momy bata nan kuma saboda yarinyar komai ya faru?” “Ba gida zan kaita ba?” “To ina zaka kaita? Talba ka yi tunani please... Gidan wata gwaggonka ko yar'uwarka? No suma ba su maka kallon mai hankali da tunani ba” Ya mike tsaye yana kallon Ali. “Okay then zan ajeta a gidana i think babu wanda zai takura mata a can kuma ina da iko da can ai” Ali yayi dariyar mamaki. “Like seriously? Talba kana magana kamar baka san illar abun da zaka aikata ba?” “Idan na kaita can fyade zan mata? Saboda gani dan'iska ko?” “No don't take it serious, amman dai kasan idan mace da namiji suka ke be a guri daya shedan ne na ukunsu, yarinyar kyakkyawa kamar wannan, kai kuma gaka lafiyayyen mai bukatar aure? Duk abun da musulunci ya hane mu da shi ya kamata mu nisance shi, And aje wannan ma a gefe baka tunanin wasu za su iya amfani da wannan damar su yi blackmailing dinka? Kuma ya kake tunanin Daddy zai ji idan ya san ka aje ta a gidan ka yarinyar da ba matarka ba” “Me kake son yanzu na yi? Kai ma fa kasan halin da yarinyar take ciki! Bata da kowa sai ni sai Allah” “Bata da kowa dai sai Allah, kai din miye hadinka da ita? Kana kokarin bata alakarka da kowa saboda wata yarinyar da baka san asalinta ba? Ka bata hakuri daman ba zai yiyu mutum ya samu abun da yake so dari cikin dari ba, idan tai hakuri da zaman a can sannu sannu sai mafita ta zo mata, idan ta samu lafiya sai ka kaita gurin yan'uwanta, idan kuma ta ki yanzu ka dauke ta ka kaita gurin da yan gudun hijira suke zama ka siya mata abinci da dan wani abu mai dama ka bata” Talba ya rumgume hannayensa yana kallon Ali. “Karka zama marar tausayi Mana, abun da ya faru da ita zai iya faruwa da kowa, kuma ina ce kai ka gabatar da min da yarinyar nan saboda kana ganin tana bukatar taimako” “Amman ni ban yi tunanin zata haifar da matsala tsakaninku da Leila da kuma Momy da Daddy” “Babu matsalar data haifar, domin bata ce dole a taimake ta ba, kuma ba zuwa tai ta hada su fadan ba, daman na san damuna zaka yi da maganar Leila shiyasa bana son zuwa gurinka yanzu” Ali yayi murmushin takaici. “Allah sarki Leila baiwar Allah, yanzu har baka son maganarta? Ni daman shawarar da zan baka kawai ya daure ka sake yi mata maganar auren ka lallabata, idan ta aureka hankalinku zai kwanta zata samu natsuwa kai ma kuma zaka samu?” “That's the only solution, gidan zan kaita kuma wannan ya zama a tsakaninmu, ni Wallahi kasa ma na kara jin tausayin yarinyar nan, bata da gata ko kadan” Yana kawai nan ya nufi driver seat. Ali ya bishi da kallo. “Ya ina maka maganar Leila kana maganar wata yarinyar? Talba lafiyarka kuwa” “No ban da lafiya zo ka kai ni asibiti” Ya fada bayan ya shiga motarsa sai da yai mata key sannan ya rufe, yai reverse ya ja motarsa ya bar Ali tsaye bakin kofar gidansa.   Daga gidansu Ali family house dinsu ya nufa, sai da ya faka motarsa harabar gidan sannan ya soma jin wani yanayi na kadaici tunawa da Momy bata ciki. Ya dade cikin motar sannan ya bude ya fito ya nufi bangarensa, kamar wani bako haka ya shiga bedroom din ya zauna kan kujera yana maida numfashi, sai kuma ya dago wayarsa yana kallo kamar mai tunani, yawo ya fara yi da yatsunsa saman wayar har zuwa gurin number Madina sai dai be kira ba, kiran Amal ya shigo wayarsa saurin tashi yai zaune ya amsa kiran. “Lil Sis” “Ya ka yi magana da Daddy?” Ya kai hannunsa ya shafa hancinsa zuwa kasan bakinsa. “Yeah na yi magana da shi, kuma zai dawo da ita komai zai wuce, amman yana bukatar mu ba shi lokaci domin shi ma yana cikin bacin rai a yanzu” “Amman dai ai zata dawo ko?” “Eh dole ma ne Daddy ya dawo mana a ita, Ki kwantar da hankalinki” “Toh” Ya yanke kiran, ya mike tsaye ya fice daga idakin, motarsa ya nufa ya shiga tun kamin yai reverse ya danna horn, ko kamin ya isa gate din an bude masa. Kai tsaye gidansu Madina ya nufa, sai dai wannan karon be shiga ciki ba ya faka bakin gate din, ya kirata a waya ya sanar mata yana waje. Bayan kamar minti talati aka bude gate din ta fito rike da Aminatu, mai aikinsu kuma na rike da jakar tufafin Aminatu, daga cikin motar yake kallonsu har suka karaso sannan ya bude motar ya fito ya zagaya ya bude mata gidan gaba ta zauna ya rufe. Sannan ya juyo ya kalli Madina. “Thank Youu, zan so wata rana nima n rama abun da kika yi min na karamci” Murmushi take tana masa wani irin kallo mai cike da saukin so. ‘Ina ma zan iya buda maka zuciyata ka kalli irin kaunar da nake maka? Taya zan iya fada maka cewar kaunarka ita ce tukuicin abun da na yi maka?’ A ranta take ta wannan tunanin tana binsa da kallon da bata san tana yi ba, har ya bude back seat ya saka jakar tufafin ya rufe ya zagaya bangaren direba ya shiga ya ja motar, sai da yai horn sannan hankalinta ya dawo jikinta har ta zabura sai kuma ta lumshe ido tana maida mumfashi a hankali. Sai da yai nisa sannan ya kalli Aminatu ya ce. “Ana miki wani abu ne a gidan?” “Aa” “Miyasa baki son zama a can?” “Ba komai” Be sake cewa komai ba, sai dai duk bayan lokaci yana kallonta da karantar yanayinta. “Yanzu zan kai ki gidana ki zauna, a can babu wanda zai takura miki” “Gurin su Momy?” Ta tambaya tana kallonsa nan da nan idonta har ya cika da hawaye. “No gidana ni kadai ne a ciki nima kuma bana zama, yanzu ke kadai zaki fara zama a ciki” Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai kuma bata gama fahimtarsa, ba mutane kamar ya? Gida ne da zata zauna ita kadai? Ko kuma da matarsa? Amman ai yace mata Leila ce matarsa kuma da alama be aureta ba. Haka tai ta jerowa kanta tambayoyi tana yi tana kallonsa har suka kusa isa gidan, each and every single kallo da take masa sai idanuwanta da na shi sun yi tarayya. Wata sabuwar unguwa ce mai dauke da manyan gidaje na Alfama, a gaban wani katon green gate ya faka, sai ya kalleta. “Bari na bude gate din” Bata ce masa komai ba, ya bude motar ya fita tare da keys din hannunsa ya saka ya bude gidan ya shiga ciki ya bude gate din gaba daya sannan ya dawo yaja motar ya shiga da ita ciki, kato gidane mai matukar kyau da tsari, ya fenti ko'ina da golde color, ga manyan itatauwa da ko'ina daga bakin entrance din kuma flowers har harabar gidan. A inda ya faka motarsa guri ne da aka tanada aka kawata domin aje motoci kawai, a kusa da inda ya aje motar akwai mota biyu dake lullube. Sai da ya kashe motar sannan ya bude ya fito, ya isa gurin gate din ya rufe, ya dawonya bude bangarenta ya miko mata hannunsa. “Fito” Ta rika hannunsa ta fito, ya rufe motar ya da taimakonsa suka isa entrance din, sai dai a nan be tsaya jiran ta taka da kafarta sai ya sake ta ta isa gurin kofar falon ya bude, sannan ya dawo ya dauke ta cak ya shiga da ita cikin falon, babu komai a ciki sai dai an ware gurin yin komai kama daga dinning har zuwa gurin saka plama. Sai dai ba a saka kujeru ba, ba a masa kwalliyar komai ba. Bedroom din ya nufa da ita shi ma ba yi masa wani gyara ba sai dai an saka gado da standing mirror. A saman gadon ya sauke ta sai ta fara rabon ido yana karewa dakin kallo, ko'ina yayi datti alamar an dade ba a zauna a gidan ba. “Bari na kunna miki inji” Har ya juya sai ta mike tsaye tana jin tsoro. “Ni kadai zan zauna nan?” Ya juyo ya kalleta, babu komai a cikin idanuwanta sai tsoro da tashin hankalin da be san inda ya samu asali ba. “Kina jin tsoro ne?” Ta daga masa kai idonsa na cika da hawaye. “Ba zan iya zama a nan ni kadai ba” “Amman idan ba a nan ba, babu inda zan kai ki, duk inda zan kaiki za a takura miki ne” “Ni dai ba zan iya zama a nan ba” Ta fashe da kuka, tunani ya soma dawo mara, tana ganin kamar a nan din ma wani abun zai same ta. “Dan Allah karka bar ni a nan tsoro nake ji sosai” Ta fada tana ta kokarin takawa ta isa inda yake. “Ba zai yiyu na kai ki wani guri ba, kuma ba ni da inda ya fi nan, kuma ba zai yiyu na zauna a nan ba, saboda ni ba muharramin ki ba ne, taba ki ma da nake Allah kadai ya san zunubin da zan samu” Yana kai Aya saibta fashe masa da kuka sosai jikinta ya fara rawa, ta fara daga masa murya zata masa irin kukan da tai a lokacin da Leila ta mari Mairo. Sauri karasa yai kusa da ita ya rikata, sai ta fada jikinsa, nata jikin yana karkarwa numfashinta har rawa yake. “Ya isa ya isa ba zan bari ki zauna a nan ke kadai ba” Ta runtse ido sosai jikinta nata rawa numfashinta ma kamar zai fita ya bar jikinta. Sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ta taka tana a jikinsa ya zauna bakin gadon tare da ita. “Tsoro nake ji, bana son zama ni kadai” “Ba zaki zauna ke kadai ba, amman we have to plan, ba zai yiyu mu zauna sheidan ya rijanye mu, be kamata na yi kusanci da ke haka ba...” Ya fada yana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya dago ta a hankali sai ta kalleshi idonta har ya fada. “Zan zauna tare da ke, amman sai idan zaki yarda da wani sharadi da zan gindaya miki” “Minene?” Ta tambaya bakinta na rawa, jikinta na amsawa wani sanyi ya taso mata. Buaar da iskar bakinsa yai ya mike tsaye yana ganin kamar be dace yai mata wannan maganar ba, ya zata kalleshi? Ya zata dauki abun? Besides shi dai ya san ba sonta yake ba, amman dole yai haka saboda masa wa kansa mafita da kuma ita. Wayarsa ya ciro ya kira line Momy ringing biyu kamin tai na uku ta daga, da sallama. “Talba” “Na'am Momy kina lafiya?” “Lafiya kalau ya kuke?” “Momy kina ina?” “Ina gidanmu, ina zan je?” “Haba Momy ko da ace saki uku Daddy yai miki ai be kamata ki bar gidan nan ba, saboda kin tara mu sai dai shi ya tafi ya barki” “Uhm... Indai kuna lafiya ai shikenan zan dan yi wani aiki” Be ce komai ba har ta kashe wayar, sai ya juyo ya kalli Aminatu, sai kuma ya juya ya fita, kamin ya kunna injin din ya dawo har ta kawo bakin kofar falo tana hawaye, da tana dafa gini, har ga Allah tsoro take ji bana wasa ba, yanayin gidan da yadda yake shiru ga shi da girma sai yai mata kamar wacan dajin. “Har kin kawo nan?” Ya fada bayan ya bude kofar falon ya shigo, da mamaki ya kalleshi. “Ba zan zauna a nan ba, dan Allah ka kai ni wani gu....gu... rin...” Kamin ta karasa tai baya ta fadi duk kokarin da yai na riko be yi nasara ba har ta kai kasa babu numfashi. 28 MG'S COLLECTION. "Saudatu ki shirya zamu je gaishe da su Baba, kasancewar azumi ya yi nisa ya kamata ace sun samu wani tagomashi daga arziƙin haihuwa" Ta faɗa tana nufoni da ƙunshin kayan da ta soma zazzagesu. Galala yaro da wayau, haka na saki baki ina kallonta. "Amma Raulatu baki kyautamin ba, haka zan je gaishe da su hannu na dukan cinya bayan ke kin gama shiryawa?" "Ban fahimta shiri ba? Kina nufin ki ce min baki da labarin ƙayatacen wajen da suka sahalce mana yin Ramadan package?" "Ina kenan?" "MG'S COLLECTION mana. Wajan da ya tanadar mana da sauƙaƙiyar hanyar kyautatawa makusantamu ta hanya me sauƙi. Ingantattun kayansu masu sauƙi da kuma inganci. Ɗangin Turare, Darduma, Jallabiya, Agogo, Jaka da Takalmi. Har ma da Alƙur'ani mai girma" "Eh lalai ki ce sa'a tafi manyan kaya, da hanau gara manau" "Tabbas kuwa ba su tsaya iya nan ba, sun saida ingantatun kayan ɗa'a masu maida tsohuwa yarinya shar washar da ita.sannan munada set n gyaranjiki me matukar kyau yasakiyi haske meban shaawa,munasaida daddaya,kuma Akwai frams na ƙawata ɗakin amarya da uwargida" "Tabbas zan garzaya ƴar uwa domin kashe ƙwarƙwatar idanuna" "Za kuwa ki godemin, zaki same su a adireshinsu dake Kunemesu ta WhatsApp number nasu 07046881166, 08062991549 kan waɗanan lambobi. Ga sauƙi ga inganci ga kuma mutuntawa. *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Momy ta aje wayar tana murmushin takaici. “Waya kira?” Hajiya Yana ta tambaya, sai Momy ta kalleta. “Talba ne” “Bawan Allah, bayan duk abun da kike masa har kiranki yake” “Uhm Hajiya kenan, ke da Alhaji sai dora min laifi kuke” “Dole a dora miki laifi mana Amina, yaron da zai girma a hannunka be san wata uwa ba bayan ke, amman ya kawo wata ki masa haka saboda kawai ba ke kika haife shi ba” Cewar Mahaifiyarta Hajiya Yana. “Hajiya ni fa ba kamar ke bace, ni kam kaza ce mai son yayanta, ba zan iya yi ma yayana abun da kike mana ba, na nuna mana kin fi son yayan yan'uwa fiye da mu, yanzu fa zamani ya canja, Wallahi kowa kansa ya sani” “Allah ya wadaran wannan canji na zamani Amina, mu kam a da ko dan makoci dan ka ne balle kuma dan dan'uwa na kusa da nesa” “Hajiya ai ni ban hada jini da Talba ba” “Ban ga ta inda Talba ya babanta ki da mahaifiyarsa ba, bibiyar da yake miki ko Kabiru da kika haifa be fishi yi miki bibiyaya ba” “Babu wannan damar ne ai, da ace zai samu hanyar nuna min zai yi, ai ruwa be taba zama jini ba” Hajiya Yana ta girgiza kai. “Na yi tunanin sakin nan da Alhaji yai miki zai saka ki natsu ki gane kuskurenki domin yayi abun da ya dace, ya nuna miki jini ba abun wasa ba ne, ke kam dai halinki ya fita dabam dana yan'uwanki, ba ki dauko ni ba kuma baki biyo halin mahaifinki ba, sam wannan ba rayuwa bace” Mikewa tai tsaye tana dariya. “Hajiya idan kina min wani abun kamar ba ke kika haife ni ba, ni saki be tashi hankalina ba, amman ya saka na kara nazari da tunani da kuma fahimtar abubuwa, ina mai tabbatar miki sai Engineer yayi nadama sai ya zo da kansa yana neman afuwa yana kuka da hawayensa, abun da be min a kurciya ba yanzu zai min shi da tsufana? Da yaya? Ai duk wanda ya zama silar mutuwar aurenka a gidan mijinka da kake kauna kuma da yayanka manya ba kakana ba, ba masoyinka ba ne Hajiya...Hmmm” Ta karasa tana kashe ido daya, sannan ta kai hannu ta dauki wayarta tare da plate din data gama cin abincin ta nufi bedroom, Hajiya Yana binta tai da kallo tana mamaki yadda zamani ya lalace har zaka fifita danka akan son zuciya, domin a iya abun da ta fada mata bata hango Talba ko Daddy da wata matsala ba, duk abun da ya faru ita ta janyo komai, ba tun yau ba halin Amina ya fita dabam a cikin yayanta. “Allah ya kyauta ya shirya ki” Addu'ar da Hajiya Yana tai kenan ta cigaba da jan carbinta, tana gama tasbihin jikanta Kabir ya turo kofar falon ya shigo, juyows tai ta bishi da kallo har ya zauna, bata ce masa uffan ba domin ta lura yana cikin yanayi na bacin rai, domin ba haka ya saba shigo mata ba. Idan zai shigo ya kan yi sallama kuma ya shigo yana wasa da ita tsabanin yau da ya shigo kamar wanda akai wa dole. “Hajiya Yana Ina Momy?” “Bacin ran da ubanku ya saka muku shi ne zaka zo ka sauke a kaina?” Ya kalleta sai kuma ya hade yawu yana ta kokarin danne bacin ransa. “Hajiya ki yi hakuri, ina Momy?” Da hannu tai masa nuna da kofar dakin, har ya mike tsaye sai ta kira shi. “Kabiru... Zauna” Bayan ya juyo tai masa umarnin zama, sai ya koma ya zauna. “Karka dorawa mahaifinka laifi, karka kuskura ka biyewa mahaifiyarka abun da tai da kai da ita Leila duk ba ku kyauta ba, hakan da kuka yi kun nunawa Talba rashin gata ne da galihu, domin na tabbatar idan kai ne Amina ba zata maka haka ba” “Son da Daddy yake yi ma Talba yayi yawa Hajiya, ni ma sai yanzu na lura da haka, kuma da Talba ya dauki Momy a matsayin uwa ba zai tana yarda ta kawo yanzu a gidan nan ba, duk yadda zai yi ya saka Daddy ya maidata gidanta zai yi, saboda Daddy yana jin maganarsa kuma yana gudun bacin ransa, amman be yi komai ba, saboda ba mahaifiyarsa ba ce” “Aa Kabiru kar fushi ya rufd maka ido, ka rika ganin daya a matsayin biyu, baka san abun da yake kasa ba, kuma ka san halin Mahaifinka sani murdanden mutum ne, ba lallai ne wani ya iya saka shi abun da be tashi ba, yanzu kuma Amina ta gama waya da Talba” Kabir ya mike tsaye. “Ke ma kina goyon bayansa kenan? Akan mahaifiyata bana ganin kowa da gashi Hajiya, ya sha saka ta kuka saboda Silly abu Daddy zai rufeta da fada har sai ta yi kuka ranta ya bace, amman yanzu mai gaba daya Daddy yai, be dubi ni ko Leila ko Amal ba, abun da be yi da kurciya zai aikata da tsufa saboda Talba? Ya duniya zata kallemu da girmanmu ace iyayenmu sun rabu” Hajiya ta nuna shi da yatsa. “Kabiru me mahaifiyarka ta fada maka? Ka zurfafa abun nan” “Babu zancen zurfafawa Hajiya, ina fada miki gaskiya ne, har yanzu Talba ne kira ya min magana ba, kuma be saka kafarsa ya shigo gidan nan ba, that's mean ya jidadin abun da Daddy yai kenan? Yanzu na fahimci dalilinsa na kin nunuwa Leila kulawa wato baya son ta kuma ba zai iya cewa baya son ta ba, ai ya san kulawa tun da gashi nan yana nunawa yarinyar, and now da Leila ta kamu da kaunarsa ta saka a zuciyarta shi ne yake kokarin broken heart dinta and i won't let that happen, i will teach him a lesson” Yana fadar haka ya nufi dakin da Hajiya Yana ta nuna masa sai wani cika yake fushinsa yana kara hauhawa. TALBA POV. Kallonta yake yana ta tunanin ta inda zai fara mata bayanin, zata fahimta? No wait ya ma dace yai haka? Amman idan be yi ba yana da wata mafitar ne? Idan yace zai kaita wani gurin zata zauna? Zata jidadin rayuwa? Idan kuma ya zauna da ita anya zai iya rike ba tare da shiga hurumin da Allah ya haramta masa ba? Ta dan sakar masa murmushi ganin kallon yayi yawa har ta soma tsarguwa, sai shi ma yai murmushi yana cigaba da kallonta. “Kin san me?” Ta girgiza kai alamar aa. “Ina ganin kamar muna da mafita daya ni da ke? Ita kadai ta rage mana” Kamar ya san ba zata tambaye shi minene mafitar ba, sai ta ya cigaba da maganar yana kallon cikin idonta. “Idan muka zauna a haka zamu iya sabawa Allah, ba ina nufin mu aikata wani abu ba, no zan iya kula da kaina, amman rika hannunki taba jikinki ko taimaka miki da yin wani abu da zai saka na kai hannu a jikinki, idan kuwa har zamu zauna a gida daya a tare dole ne sai hakan ta faru, tsakani da Allah ban saba mu'amala da mata ba, taba mace kallonta ba halina ba ne, and duk abun da zan yi ina kokarin ganin ban shiga hurumin da ya haramta a gareni ba, ina kokari sosai wajen ganin n tsare mutuncina da na iyayena da yan'uwana, idan babu yan'uwa da iyaye kuma akwai Ubangijina, ban ce na fi karfin sheidan ba amman duk inda mace da namiji suka kebe na ukunsu sheida ne, haka ne?” Ta daga masa kai, sai ya zauna gefenta yana kallon gefen fuskarta a yayinda take kallon kofar bedroom din. “So ina son na yi wannan shawarar kuma na yanke wannan hukuncin akan yardarki da amincewarki, bana son na cilasta ki ko kadan bana son ranki ya bace akan komai, bana son ki cilasta zuciyarki ta karbi abun da baki bukatarsa a yanzu, ni kaina idan nace miki ina bukata na yi karya, domin zan jefa rayuwata a hadari ne da kuma na matar da zan aura Leila, kuma zamu yi wannan abun ne a bisa sharadi” Ta juyo ta kalleshi. “Minene?” “Shalele...” Sai kuma yai shiru yana tunanin dacewa da rashin dacewar aikata hakan, ita kanta ya zata kalli abun? “Ina son mu yi aure ni da ke....” Duk wani abu dake motsi a jikinta sai ya tsaya cak na tsawon dakika uku. “Aure...” Ta maimaita a raunane tana kallon wani gefen. “Yes... Aure ba saboda ina son ki ba, ba saboda kina so na ba, kuma ba saboda mun dace da juna ba, zamu yi wannan abun ne a karkashin sharadi guda daya” Ta sake kallonsa sai dai wannan karon hawaye har ya fara sauko mata. “Zan aure ki ne saboda gudun aikata abubuwan dana fada miki a dazu, amman Wallahi ba dan ina son ki ba, sai dan ina tausayinki, kuma saboda hakan zai zame mana mafita ni da ke, domin na san ke ma ba sona kike ba! Amman na miki alkwari ni Talba zan sakeke da zarar rayuwarki ta inganta, ma'ana kin gane yan'uwanki ko kuma kin samu wanda zai aure ki, kuma wannan auren zai kasance ne kawai a tsakaninmu, babu wanda zai san da wannan sirrin har mu rabu” Dauke kai tai tana jin abun wani iri, an taba aure ba yan'uwa ba kowa? Daga ita sai shi? “Zamu yi ne saboda tsare mutunci da gudun fushin Allah, kuma na rantse miki da Allah zan sake ki a duk lokacin da dayan biyun nan ya faru! Ko dai kin gane wasu daga danginki ko kuma kin samu wanda ke sonki tsakani da Allah zai aureki, karki damu da tunanin babu yan'uwa ko naki, zamu yi wannan auren ne saboda ke, domin ni ina da wanda zan aura, kuma mu yi wannan abun ne a rubuce kuma akan yarjejeniyar saboda ki samu natsuwa” Ya fada kamar ya san abun da ke ranta. Da gaske aurenta zai yi saboda abun ya fada ko kuma dai saboda wani dalilin ne na dabam? “Momy...” “Karki damu da ita, ba zata taba sani ba na miki alkawari” “Leila...” “Taya zan barta ta sani bayan kuma ita zan aura? Ya kike ganin zata kalli abun? Wannan abun zai zama sirrine a tsakaninmu” Ta girgiza masa kai. “Ba zan iya ba” Ya cikama bakinsa iska ya busar kana ya kai hannu ya shafa kansa. “Daman bana son cilas ta ki, yanzu dole mu nemo wata mafitar ta dabam, zan memo miki wani gurin da zaki zauna tare da wasu mutanen, amman kamin na samu wannan dole ki zauna a nan kamin mu samu wata mafitar” Sai ta rumtse ido wasu zafafan hawaye na sauko mata. “Inna ta yi gaskiya, ta fada min zan yi kuka a gaba, sabowa da wata rayuwar ba abu ne mai sauki ba, fuskantar kalubale bayan wani kalubalen abu mai wahalar gaske, ina a tsakankanin rayuwa da mutuwa, farinciki da sabo sun min nesa, samun sukunin na zuciya da ruhi ya min tsada” Har ya kai hannu ya kama hannunta, sai kuma ya maida hannun a cikin dayan hannunsa ya rike. “Miyasa ba zaki yarda da kaddara ki karbi duk abun da ya zo miki da hannu biyu? Wata kila idan kika bi rayuwar a yadda ta zo miki sai ki samu sukuni da walwala a gaba?” Ta bude idanuwanta da suka soma yin ja ta kalleshi. “Kana ta karfafa guiwa a inda babu karfi, taya kake ganin komai zai zo min da sauki? Na rasa uwa a gaban idona suka kashe mahaifina, aka kashe yan'uwana a dare daya na rasa komai, a tsakanin wadancan ranaku da na yau na rasa wacece ni, ina jin zafin abun a raina ina jin kamar zuciyata zata fasa kirjina ta fito babu abun da yake da sauki a gareni...” Ta karasa tana ta shesshekar kuka jikinta na rawa, hawaye na sauko mata kamar an yi su ne kawai saboda wannan ranar. Gaba daya jikinsa yayi sanyi sai tausayinta ya kara kama shi, ba tare da ya so ba ya kai hannunsa ya kama hannunta ya jimke sosai, sai kawai ta kara fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya. “Za ki iya yarda da ni?” Ta daga masa kai tana kuka. “Na miki alkawarin zan dawo miki da farinciki a rayuwarki, ban ce zan dawo da iyayenki da yan'uwanki ba, amman da yardar Allah sai na samo miki wadanda za su maye miki gurbinsu? Zan dawo miki da farincikin da kika rasa Amina i promise you this! Kin yarda da ni?” Ta sake daga masa kai, sai ya sauke numfashi a hankali yana jin kamar ya rikata ya saka ta a kirjinsa ya rarrasheta. A hankali ya zare hannunsa ya mike tsaye yana nuna mata gadon. “Kwanta” Ta kalleshi daker tana kokarin tsayar da kukan da take. “Ta.... Tafiya... Zaka yi....” Kamar ya ce mata eh sai kuma wata zuciyarta ta hana shi, wata kila idan ya amsa mata da eh zata iya cewa ba zata zauna ba, idan kuma ya ce mata aa ta kwanta ta tashi bata tararda shi ba zata dauke shi makaryaci. Be ce mata komai ba ya nufi inda bargon yake aje gefen gado ya dauka ya rike. “Kwanta, ki samu bachi” Ta hau saman gadon gaba daya ta kwanta sai ya dauki filo ya mika mata ta karba ya rumgume, sannan ya lullube ta. Baka jin komai a dakin sai saukar numfashinta da karfi, gefen gadon ya samu ya zauna yana kallonta, zaman da yai sai ta ji natsuwa har ma ta samu damar lumshe idonta, ta kai hannunta a baki tana cizawa a hankali. Kallonta yake for so many reasons, na farko rayuwarta yake hangowa, da kuma tasa ta ina zai sama mata duka abubuwan da take bukata? A dayan bangaren kuma yana tunanin Momy. Lokacin lokaci take sauke ajiyar zuciya da karfi tana shakar numfashin a hankali. Sai da ya tabbatar bachin nata ya nina sosai sannan ya mike tsaye ya karasa inda take ya kai hannunsa ya janye hannunta daga bakinta ya kara jan bargon ya lulluba mata har gurin wuyanta, sai kuma ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta, samun kansa yai da murmushi kamin ya juya ya fara takawa cikin izza ya nufi kofar dakin, hannunsa ya kai ya kunna ac dakin sannan ya juyo ya sake kallonta, kamin ya sa kai ya fice ya ja kofar a hankali ya rufe, this is the first time da yake taba kofa a hankalin saboda gudun katsewa wani bachi, after Daddy. Fita kofar falon ma a hankali ya jata ya rufe saboda kar karar rufe kofar ya tashe ta, sannan ya saka key ya rufe kofar daga waje, sai da ya fara isa ya gurin gate din ya bude sannan ya dawo ya fita da motarsa sai kuma ya dawo ya rufe gate din ya koma cikin motar. Kamin ta fita unguwar aka soma kiran sallah magariba, a kusa da wani masallaci ya faka motarsa ya fita yai alwala ya shiga masallacin yai sallah sannan ya dawo cikin motarsa yai mata key ya dauki hanyar gida. Kamin ya isa ya kira Daddy a waya, sai dai har wayar tai ringing ta gama be daga ba, hakan ya saka shi rike wayar a hannu ya cigaba da tukin da hannu daya har ya isa gida, yana danna horn sai ya ji babu dadi tunawa da Momy bata cikin gidan, har yake jin kamar ya juya ya koma domin shiga cikin gidan yana masa nauyi a yanzu, ya kasa daina ganin laifin Daddy na yanke irin wannan hukuncin kuma yana ganin shi ne silar komai, tun da yake da Momy ko fushi be tana ganin ta yi ba, balle kuma har saki ya shiga tsakaninta da Daddy, idan ma an taba ta an yi ta sigar da su ba za su gane ba. Har ya isa harabar aje motocin ya faka motarsa be lura da Kabir dake jingine jikin mota yana waya ba, duk da kasancewar ko'ina na gidan haske ne irin hasken nan da ko allurarka ta fadi zaka iya gani, ko da yake hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba. Sai da ya bude motar ya fito sannan ya kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Kabir, rufe motar yai ya karasa inda Kabir yake jingine ya tsaya tare da zuba hannayensa aljihu yana kallon harabar gidan kamar bako. “Ya akai?” Kabir ya bukata ganin ya tsaya a inda yake da alama jiran yake ya kare wayar, kallonsa Talba yai jin wata bakuwar kalma da be saba furta masa ba ga fuskarsa a gade kamar bakin hadari. “Come on.. Karka ce min ka zo nan ne saboda ka yi magana akan abun da ya faru? Kai da baka san zafin uwa ba? Taya za ayi ka ji wani abu?” Talba ya kalleshi da mamaki. “Kabir magana fa kake fada min kai tsaye” “Yes ko ni ma zaka saka Daddy ya kore ni ne? But I'm grown up now ba yaro ba ne ni” “Kabir me ke damunka?” Talba ya tambaya da mugun mamaki. “Babu abun da yake damuna, kawai ina fadar gaskiya ne da ace ka san wacece uwa da baka bari komai ya faru ba? And you won't be here standing in front of me, Momy ta raine ka for so many years amman a yau ka nunawa duniya cewar kai ba danta ba ne, and Thank you....” Yana fadar hakan ya bar gurin ya nufi hanyar falo, Talba binsa yai da kallon yana mamakin kalaman da Kabir ya fada masa kai tsaye! Ta dayan bangaren kuma sai ya ji kamar an caka masa wuka a kirji, how could someone like Kabir zai ce masa be san zafin uwa ba? For the second time after wacan karon da Daddy ya ba shi labarin komai ya samu kansa da jin wani yanayi irin na Aminatu. BATURIYA POV. “Na kira ne kawai na yi miki barka da safiya” Ta yi murmushi tana kara gyara kwanciyarta kan gadon Umma. “Na yi fushi baka kira ni da wuri ba har rana ya fito sosai” Ta fada tana ta zuba masa shagwaba kamar yana gabanta. Sai ya marairaice murya daga can cikin wayar yana bata hakuri. “Haba Babyna kin san bana son bacin ranki fa, amin afuwa ba zan sake ba, kuma ina tafe da wani katon albishir” “Na me?” “Sai kin ba ni goro zan fada” “Me kake so?” “Komai ma kika ban ina so, ai ni komai ni so nake” “To na baka kaina” “Wow na gode ko da yake ke ma din ai tawa ce” “To yanzu fada min” “Abbana ya amince, zai fada min lokacin da yake free sai na fada miki ki duba idan na ki Abbah yana free sai su hadu su ga juna” Ta dafe kirjinta gabanta na faduwa, ga wani irin tsoro da fargaba da suka rabeta a lokaci daya. “Da gaske?” “Haba ana wasa da irin wannan maganar ne?” “Wow Alhamdulillah, amman ka san me? Ni fa a gidan mu ba a san da maganar ka ba” “Yeah ai na fadawa Abbana, shiyasa ma nake son aje nema min aurenki so that na samu izinin magana da ke” “Kana ta maganar Daddy ban ji ka tabo Momy ba?” “Kin san Momy tana son na auri wata a familynsu ne, amman ita ma ta yi na'am saboda tana son abun da nake so, kuma Abbah ya bi bayana yace matukar suka yi bincike suka tabbatar babu wata matsala za su nema min aurenki” “Alhamdulillah Allah ya amince mana” “Amin kin san fa ni na gaji da wannan boye boyen da kike min kin hanani zance da ke, da na yi magana sai ki ce ana fada a gida, kuma ya kamata ace muna haduwa saboda mu kara fahimtar juna da kyau” “Haka ne, ni kaina ina son haduwa da kai, idan na samu free time zan kiraka sai mu haduwa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani akaina ni ma kuma na sani akanka” “Haka ne, idan kin samu sa'ar fita sai ki fada min inda zamu hadu” “Inshallah, i love you so much” Ta fada da muryar dake nuna farinciki take, sai dai a zahiri ba farincikin take ba, tsoron abun da zai je ya dawo ne a ranta. “Na'am Umma gani zuwa” Ta yi amsawar karya kamin ta ce. “Ina zuwa Umma tana kirana” “Okay i love you” Tun kamin ya aje ya yanke wayar ta tashi zaune tana dudu da hannayenta. “Kam uban nan, zubar da cikin nan ya zame min dole, amma...” Bata karasa ba Umma ta daga labulen dakin ta shigo tana fadin. “Rafi'a, ta so ga yayanki can yana nemanki” “Toh” Ta amsa sannan ta sauko saman gadon a ta dayan bangaren tana ala ala idan ba Faruk ya fada masa tsabanin abun da ta fada musu ba. Kamin ta karasa falo har ta fara tunanin irin karyar da zata yi ta kare kanta. Gabanta na faduwa ta zo ta zauna a kasa kanta a kasa Umma dake bayanta ta zauna kan kujera. “Yaya ina wuni?” Ta gaishe shi tana dan kallon yanayinsa, sai ya amsa mata fuska ba yabo ba fallasa. “Umma ta fada min abubuwan da suka faru, na kira Faruq har gida domin ji daga bangarensa, sai dai be fada min komai ba, kawai dai ya ce min ya gaji ne, yayi iya hakurin da zai iya da ke, yanzu kuma Allah ya kare abun, sai dai yayi ta jaddada min cewar ke yar'uwarsa ce kuma uwar dansa, ba zai fadi mummunna abu akanki ba, amman mu zamu fahimci komai da sannu, ina fatar babu abun da kike boyewa” Ta dago kai ta kalli Yayanta idonta cike da hawaye. “Haba yaya! A hannunka fa na tashi idan akwai abun da ba halina ba ai kai zaka fara sani” Umma ta tabe baki “Ai ni ba haka na so ba Wallahi, da ka biye ta tawa da police station zaka kai shi a lakada masa shegen duka kamar yadda shi ma yayi mata” “Ai an daga kafa wani gangaren ko dan zumunci, shiyasa na kira shi a gida na yi magana da shi” “Shi ai be duba zumuncin ba a lokacin da zai wulakantata haba” “Yanzu dai ayi hakuri komai ya wuce, Allah shi zai saka mata ai” “Aiko ya saurari abun da zai same shi domin hakkinta sai ya kama shi, kuma gobe gobe zan aika a kwashe mata kayanta duka da yardar Allah, daga ma ta huta da talauci da rashin abincin, kuma ba zamu rika masa dansa ba” “Yace ma zai rika aiko mata abinci duk wata saboda cikin da take da shi, Allah ya sauwake” “Ameen” Ta amsa a tare da Umma sannan ta taso ta baro musu falon da dawo dakin Umma ta zauna tana ta tunanin maganar da Fahat yai mata! Da sauri ta kai hannu ta dauki wayarta ta kira Ramlee ringing daya ta dauka cike da far'arta. “Yar gari yanzu fa nake son kiranki” “Lafiya?” “Lafiya sai alheri, Wallahi Alhajin nan ne ya fara damuna da maganar ki jiya, har yana ce min yana son ya leka chine da ke, bayan shi ma na samo miki wani Alhajin” “Uhmm ai yanzu fita ma sai ta min wahala Ramlee, Faruq ya sake ni” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya sake ki fa kika ce Fee'ah” “Wallahi kuwa yau kwana biyu....” Daga can cikin wayar Ramlee ta sauke ajiyar zuciya bayan Baturiya ta gama labarta mata komai. “Wato sai yanzu na gane kin ci ubana da iya makirci Fee'at” “Uhmmm ni ma ai ba ta wasa ba ce, ni yanzu kin san ma miyasa na kira ki?” “Sai kin fada” “Cikin nan nake son zubawar kin ga ina zubar da shi na gama iddata” “Haka ne, amman kar ki yi gaggawa Fee'at, saboda zai taba lokacinki a yanzu, maganar ba zai yi a waya ba, ina son mu hadu if possible” “Karki zo gida, zan kira ki idan na samu sararin fita” “Okay ” Ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya. 29 *_MATAYEN ƘWARAI SARAKAN ADO DA ƘAWATA JIKI DA KWALLIYA KUNA INA NE?._* _Maza ku garzayo da gudunku ga mutunuyar taku maida tsohuwa yarinya ta sake dawo muku da sabon salo, sabon sunfarin kayan gyaran jiki na mayika da sabulai ƴan gaske💃🏻._ *Kayan kwalliya na mg's skin care zasu maidaki shalele ƴar ƙwalisa tamkar wata ɗan daren sha biyar koda kina da kishiya ƴar Morocco bata girgizaki ba, balle saurayi ɗan son ƙyale-ƙyale da ƙawa ga burwallensa😂💃🏻*. _Kayan mg's skin care nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. *MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻 Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne? Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘 Soap:3k Beauty kit:11k Chat:08062991549 07046881166 07067210195 Call :07046881166 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰 Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲 Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝 Nd guest what🤩 Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃 Pamper your skin🧖‍♀️ Shine like a bride👰🏻 Glow     *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Slowly ya shiga bangarensa ya zauna kan kujera, yana maida numfashi a hankali. Kokari yake ya gano laifinsa amman ya kasa, sai kokarin ganin ya hade maganar da Kabir ya fada masa nan ma ya kasa, abun is so painful. Sai da ya hade yawu sannan ya mike tsaye ya nufi windows dinsa. Ya jingina da windows din ya kai hannunsa ya bude curtains din kofar yana kallon harabar gidan, for the first time ya ji yana marmarin ganin kakarsa, rabonsa da ita tun shekara biyu da suka wuce ita bata zuwa shi ma kuma baya zuwa, sai dai ya san duk wata Daddy yana aika musu da kayan abinci, idan lokacin sallah tai kuma sai ya aika musu da abun layya da dinkuna, amman ko kiranta a waya sai ya kwashe watanin be yi ba, abun da ya damu ne da shi kawai rayuwarsa ta nan, sai kuma Daddy da Momy, ya manta cewar yana da wasu familyn na mahaifiya bayan na mahaifi, amman a yau ya tuna saboda Kabir ya fada masa maganar data hana numfashinsa tafiya daidai. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya shiga ma'adanar lambobi ya nemo number kakarsa, ya aika mata kira yana kallon wayar sai da ta dauka sannan ya kara wayar a kunnensa. “Ashe ko yau za ayi ruwa, Mu'azu ya kira ni da kansa” Yayi murmushi tare da kai hannu ya shafa kansa. “Kaka kina lafiya?” “Ina nan lafiya kalau, sai ciwon kafa ya matsa min har yanzu” “Subhanallahi zan zo na kai ki asibiti Inshallah” “Kuna can birni kuna ta kula da wasu kun bar mu a daji, kamar ba mu da kowa, sunayen ku ma sai a radio muke ji, idan ba mu dauki waya mun kira ba kiran ayi gaisuwa ma ba ku yi sai idan mu muka kira” Talba ya runtse ido ya bude yana jin rashin kyautawa. “Ayi hakuri Kaka inshallah gobe zan zo na duba ki, amman na san baki bukatar komai a yanzu shiyasa ban cika kira ba, kuma kin ga a nan aiki yana mana yawa” “Ba ci da sha ne kawai abun da rayuwa take bukata ba, ba kai kadai na haifa jika ba, amman ka fi sauran kwanta min a rai, balle kuma ka tako kafarka garin nan, yau shekara daya da wata takwas Mu'azu, ni ma ai fushi na yi shiyasa na daina sakawa a kira min kai, kuma na ki na fadawa kowa na birni cewar ina fama da ciwo, idan na mutu ba sai ku zo ku tafi da gawata ba” “Kaka ke din ce kin ki ki dawo a nan ki zauna tare da mu, kin da ciwon nan na ki zamu sani ai, gashi a nan muna ta bawa bare balle kuma ke” “Ai daman haka masu arziki suke, ba kowa ne yake a cikin iyalansu yake cin amfaninsu ba, wani lokacin kamin na kusa ya ci sau daya sai na nesa ya ci sau dari, kuma ni ba zan baro kauye na dawo birni na zauna na ba, na fi son na mutu inda aka rufe uwayena da yan'uwana” “Garuruwan ma babu kyau a yanzu bandits suna ta kai hari kauyuka” “Toh mu dai har yanzu ba su shigo inda muke ba, kuma ina addu'ar Allah ya tsare mu” “Ameen Kaka, Inshallahu gobe zan zo na duba ki, kuma zan dauke ki na kai ki asibiti” “Toh Allah ya kaimu lafiya, Allah ya maka albarka ka yi marmarin matarka kenan” “Allah ya kara miki lafiya” Ya fada yana murmushi idanuwansa kuma suna cika da hawaye a lokaci daya, sai ya sauke wayar ya saki windows din ya juyo yana tafiya kamar wanda baya son taka kasa, bedroom ya shiga ya tube tufafin jikinsa ya daura tawul ya shiga yai wanka, sannan ya fito ya nufi wardrobe dinsa ya ciro jallabiya da gajeren boxer da vest ya saka sannan ya dauki wayarsa ya kira Line Leila ringing wayar tai har ta katse bata daga ba, saka wayar yai a aljihunsa ya nufi inda ya aje key din motarsa ya dauka ya saka aljihu tare da wallet dinsa ya nufi kofar fita yana ta sauri, kamar wanda ya manto wani abu a wani gurin. Bangaren Momy ya nufa kamin Mairo ta bude masa kofar ya danna door bell din ya fi a kirga. “Sannu da zuwa yan ranka ya dade” “Leila na ciki?” “Aa tun kamin Magariba ta fita tare da kawarta Madina” “Amal fa?” “Ita ma ta fita tun dazun, Kabir ne kawai a gidan” Kai ya daga mata ya juya ya nufi motarsa, sai da ya shiga ya zauna sannan ya kira sake kiran Leila, a yanzu kam sosai yake son jin muryarta domin ya san tana cikin damuwa, kuma be kamata ya kyale ta ita kadai tai ta fama ba, a nan ma ba ta yi picking call din ba, hakan kuma be han shi sake kiranta ba, abun da ba al'adarsa ba, idan yai ma mutun kira daya ba zai sake kiransa ba, not because saboda yana jin kansa no saboda ya san duk wanda aka kira be daga ba wata kila yana da uzuri ne. Sai da ya jera mata kira biyar sannan ya kira Amal. “Hello” “Amal kina ina?” “Ina gurin Hajiya Yana” “Gurin Momy kenan?” “Eh” “Amman kin san Daddy baya son kuna kaiwa waje da dare ko?” “Ina tare da Momy ai” “Leila tana tare da ke” “Aa na bar ta a gida” “Okay ki kula da kanki, kuma ki kira Daddy ki fada masa kina gidan Hajiya Yana” “Toh” Ya yanke wayar ya sake kiran Leila bata daga ba, sai ya yanke shawarar kiran Madina domin ya san suna tare a yanzu kamar yadda Mairo ta fada. Ringing daya Madina ta dauka tana wani irin kashe murya. “Hello Ya Talba” Be amsa ba, sai kawai ya gabatar mata da bukatarsa. “Leila tana tare da ke?” “Eh amman ni ina mota su kuma sun shiga vip” Yayi shiru kamar ya tambaya ita da waye sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai dai hakan be hana Madina fada masa ba. “Tare da Ali” “Okay” Ya fada a takaice ba tare da ya kawo komai a ransa ba, yana kokarin aje wayar ta dora masa da wata maganar. “Ina ta son na kira na tambaya halin da yarinyar nan take ciki kuma ina tsoron kar na kira ranka ya bace, ka. Taimaka min dan Allah ka fada min ya lafiyarta take? Ko na samu hankalina ya kwanta” “Lafiya kalau” “Alhamdulillah, idan tana bukatar zama da ni ko kuma wani gurin dabam, zan iya sama mata inda zata samu aminci da kwanciyar hankali inshallah” “No need” Ya aje wayar feeling some how, ya aje wayar yana ta kallon screen din wayarsa dake dauke da hoton Daddy, sai ya sauke numfashi a hankali sannan ya kai hannunsa yai ma motar key ko kamin ya reverse mai gadi ya bude masa gate. Driving yake amman ya kasa natsuwa, sai ya rasa abun da ke damunsa, be yi nisa sosai ba ya faka kusa da wani masallaci yai fita yai alwala ya shiga masallacin yai sallah, after ya fito ya shiga motarsa ya sake daukar wayarsa sai dai wannan karon ba kiran Leila yai ba sakon kar ta kwama ya aika mata wato sms, “If you need someone to talk I'm here” Sai da ya tura mata sakon sannan ya kira Daddy. “Hello” “Daddy yanzu dai na san ka huce” “Mace ne ni da zan yi yaji?” Talba yayi murmushi. “Daddy sarkin tsokana, ni dai yanzu na kira na sake rokon alfarmarka, kuma na tabbatar maka cewa dawowar Momy shi ne farincikina” Daddy yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. “And Rashin Momy ya saka Leila da Amal za su kwana gidan Hajiya Yana, ni ma zan tafi kauye gobe Inshallah” Daddy ya tabe baki. “Okay har da kai a masu yi min tawaye kenan” “This time around Daddy bana tare da kai gaskiya, kuma abun da kai ya saka ni a wani hali” “Karka damu komai zai wuce, amman ba sai kaje kauye ba saboda hanyoyin kasar nan basa da kyau” “Allah shi ke tsarewa Daddy, zan dawo lafiya inshallahu” “Sai mun hadu gida” “Okay” Yana aje wayar reply Leila ya shigo wayarsa. “No need ina tare da wanda ya san darajata, wanda kukana yake zame masa damuwa, farinciki ya zama burinsa” Ya karanta sakon sau daya sai ya ji kamar be gane ba har sai da ya sake karantawa. Yawu ya hade sannan ya aje wayar yai ma motar key, tafiya kadan ya tsaya ya shiga wani restaurant yai ma Aminatu take away na jalof da ruwa sannan ya dawo motar ya saka yi mata key, be faka ko'ina ba sai kofar gidansa, bude motar yai ya fita tare da takeaway ya rufe motar sannan ya doshi gate din ya saka key din hannunsa ya bude gate din ya shiga, kamar yadda ya saka key ya bude gate haka ya bude kofar ya shiga cikin falon silently.   Har yayi kamar ya aje ledar hannunsa a falo sai kuma ya zarce dakin kai tsaye, a hankali ya tura kofar ya shiga, duk kuwa da ya san ba lallai ne ya same ta har yanzu tana bachi ba, sai dai be yi zaton zai sameta a halin da ya same ta ba. Ta koma can karshen gado ta rakube kallo daya zaka mata ka karamci tsoron daya cika mata zuciya, har ya rabawa wani bangare a jikinta domin idanuwanta hawaye suke jikinta kuma yana ta karkarwa. Ya dade a tsaye yana kallonta sannan ya karasa kusa da ita ya risina a gabanta. “Shalele miya faru?” Kallonsa kawai take hawaye na sauko mata, me zata fada masa? Yana bukatar ta maimaita masa cewar tana jin tsoro? Bayan ya rufe kofar fita kuma ya barta ita kadai a katon gida? Har yanzu kukan rayuwar baya take ta rashin uwa da uba da family da kowa ko kuma dai tana kukan kalubalen dake gaba ne? Ta yadda zata saba da rayuwa ita kadai ba tare da kowa ba? “I'm sorry uzurin fitar ne ya kama ni shiyasa na fita, kin yi sallah?” Ta girgiza masa kai alamar aa jikinta har lokacin rawa yake. Kallon jikinta yai kamin ya kai hannunsa ya kama hannunta wai ko zata samu hankalinta ya kwanta. “You're safe now, babu abun da zai same ki, and na sama mana mafita, zan tafi da ke gobe a kauye can gurin Kakata na san za ki iya zama a kauye ko?” Ta yi shiru bata ce masa komai ba, kuma bata bar masa wata alama da zai gane tana so din ko akasin haka ba. “Tana da son mutane sosai, na san zata rike ki hannu biyu zaki jidadin zama a can Inshallah, abun nan is not easy arika passing passing da kai amman idan kika danne sai ki rayuwar ta zo miki da sauki” Ban da hawaye babu abun da Aminatu take. “Zaki iya yin kukanki, ba komai na fahimci halin da kike ciki, ni ma da ban taba jin kamshin mahaifiyata ba na ji wani iri balle da kika saba da su” Kamar jira take sai ta fashe da wani irin kuka, zaunawa yai a gurin yana ta kallonta tun tana kukan da karfi har ta gaji ta daina dan kanta, mikewa yai tsaye tare da ita ya nufi bandakin da ita, ya kai dayan hannunsa ya kunna fanfo ya tara hannun nasa ya debo ruwa ya wanke mata fuskarta sannan ya fito ya barota tai alwala. A nan ta samu damar karewa kanta kallo a madubin dake gabanta, a zahiri madubin take kallo a badini kuma rayuwarta take hangowa? Har mutum dubu nawa zata gani kamin ta samu wanda zai zame mata uwa da uba? Har guri nawa zata zauna kamin ta samu muhallin zama na dindindin, kalaman da Umma tai mata sai ya suka dawo mata sabin, jin take duk duniyar nan babu wanda zai fahimce ta, babu wanda zai gane damuwarta, tana jin wani irin yanayi mai wuyar sabo, ta kasa sabawa da rashin kowa! A rayuwarta bata taba ganin zalinci irin wannan ba, a kashe maka kowa kuma a keta maka haddi sannan a raboka da garin da ka bude ido kai wayo a cikinsa, yanzu kuma a barta a wahale tana neman sabawa da rayuwar da bata taba mafarki ba, yau ga ta a duniyar da bata san da wanzuwarta ba, hannu ta kai ta dafa gefen kanta tana shafa kan a hankali dishes dishe ta fara gani jiri ya fara dibanta sai ta fisgi numfashi da karfi tai Sulale kasa tana ambaton Allah, da gudu Talba ya turo kofar falon ya shigo ganinta a kwance kasa ya saka shi furta. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya saka hannunsa ya dago ta ya taba kanta, ya bude ido be ga wata alama dake nuna tana motsi ba, ga fanfon daya kunna mata yana ta zuba, dankwalin kanta ya cire sai gashin kanta daya sha gyara a hannun Madina ya zubo, daukarta yai ya dawo ta ita saman gado ya koma ciki ya dauki dankwalinta ya jika da ruwa ya matse ya zo ya saka mata a gaban goshi amman be ji ta yi wani motsi ba, sai ya kai hannunsa jikin hancinta, ya ji bata numfashi a take hankalinsa yai mugun tashi sai ya girgiza ta. “Amina.... Amina... ” Nan babu alamar rai a gangan jikinta, sake komawa yai ya jika dankwalin ya sake zuwa ya saka mata a goshi, ya sake girgirza. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya furta gabansa na mugun faduwa, zuciyarsa na raya masa Aminatu ta mutu, saboda an fada masa zuciyarta zata iya bugawa ta rasa rayuwarta. Wayarsa ya ciro da sauri ya kira Ali, ya kara wayar a kunne yana ta safa da marwa sai yawo yake da hannunsa yana ala ala Ali ya daga, amman har wayar ta gaji da ringing ta katse be daga ba, aje wayar yai ya nufi Aminatu ya sake girgiza ta a karo na uku, sai dai babu alamun zata farka ya dauke ta gaba daya ya nufi kofar fita da ita kamin ya isa kofar falon numfashinta ya dawo da mugun karfi kamar an jefo mata shi, har sai da taja numfashin da karfi tana fito da ido waje, ita kanta ta san ta lula wata duniyar dake mantar da mai ita komai na rayuwa. Durkushewa yai bakin kofar ya sanda kansa kasa ya rumtse ido yana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa da mugun karfi. Dago ta yai ya rungume a kirjinsa. “Kin zama daya daga cikin yan'uwana idan kika mutu a yanzu zan shiga wani hali, ki kasance mai karfin hali mana” Ta hade yawu daker hawaye na fito mata har lokacin numfashinta da karfi yake fita bakinta har ya soma bushewa. ‘Ya kake tsammanin tsayuwar dakin da rufinsa ya yaye katangarsa ta zube? Taya zata iya yin karfi hali? Zata iya hana kanta tunani? Ko kuma zata mantar da kanta abubuwa da suka faru ne? Ko kuma dai zata daina hangen future dinta...?’ Ita da shi saka daya suke da kalar zare daya, domin tunanin da take a zuciyarsa irinsa Talba yake mata a zuciyarsa, bude idon yai sai ya yi saurin rabata da jikinsa ya ajeta kasa yana kallonta kamar yadda take kallonsa da idanuwanta dake wani lumshewa kamar mai jin bachi kana ganinta zaka san babu karfi a jikinta. “Sannu...” Ya furta, kallonsa kawai take ba tare da ta ce komai ba. Can kuma ta lumshe idon ta bude sannan ta fara yunkurin tashi kyaleta yai ta gwada tashin da kanta ko zata iya, cikin iyawar Allah kuwa sai ta tashi zaune sai dai ta yi ginshikai da hannayenta. “Suma na yi?” Ya dauki lokaci yana kallonta kamin ya daga mata kai alamar eh. “Kin zufafa a tunani, kuma kin yi kankanta da haka, zuciyarki zata iya bugawa a ko wane lokaci kamar yadda likita ya fada” Sai kuma yai shiru damuwa ta bayyana a fuskarsa. “Kin tsorata ni sosai” Ya fada yana mikewa tsaye. “Zaki iya tashi ki yi sallah? Ga abinci can sai ki ci” Ta yunkura ta gwada tashi sai ta kasa, dukawa yai ya dauke ta ya shiga da ita bandakin, wannan karon tsayawa yai bakin kofar har sai da ta gama tsoro yake kar ya barta ta ta sake yin na dazun. “Ki gwada takawa mu ga” Ba musu ta daga kafar ta fara dakawa a hankali, ciwon ya ragu sai dai jirin ne be gama sakinta ba. Yana ta kallonta har ta iso bakin kofar fitowa bathroom din sannan ya fito yana kallonta tana takawa a hankali har ta fito gaba daya, kamin ta isa bakin gado ya zauna har ta tsawwala saboda gajiya da tai da tafiyar, tana zaunawa sai ya nufi akwaitin kayanta ya bude ya dauko wani dankwali a ciki ya shimfida mata. “Kin ga gabas nan” Ya nuna mata sai ta kalleshi. “Ban taba tsammanin mutane irinka suna da saukim rayuwa da arha har haka ba, ban tsammaci samunka a yadda ka zo min ba, na yarda Allah yana so na, kuma idan ya hana ka wani abun sai ya baka wani, shiyasa ya hada ni da babban mutum kamar kai kake ta hidima da ni, na gode Allah ya saka maka da alheri, ba ka dubi tazarar dake tsakanina da kai ba, kana ta hidima da ni kamar wata yar'uwarka” Yayi murmushi sannan ya nuna mata hijabinta. “Ki yi sallah a zaune idan ba zaki iya tsayuwa ba” Bayan ya fadi haka ya nufi kofa. “Ni kadai zan kwana a nan?” Tsayawa yai sai kuma ya juyo. “Aa zan zauna falo ne, a nan zan kwana, gobe da safe zamu kama hanyar Maradun zan kai ki gurin Kakata za ki zauna tare da ita, ina da tabbacin zata karbe ki hannu biyu” Ya sakar mata murmushinsa mai matukar kyau da tsada sannan ya juya ya fice. LEILA POV. A tare suka fito da Ali, ba laifi ta samu sakewar zuciya ba kamar dazun da take a cikin damuwa ba. Da kansa ya bude mata mota ta shiga front seat ta zauna sai Madina ta dubeshi tana murmushi. “Yayi kyau Aminin ango, lallai kasan ta kan amaryar nan ta ku, nan da nan har ka mantar da ita damuwarta” Leila ta kalli Ali tana murmushi, shi ma murmushin yake yai yana ganin kamar da biyu Madina ta fada masa maganar nan. “Dole ne na yi abun da zan iya na tare abokina kar ya fadi” “Yayi kyau, ai ka fi abokinka sanin darajar mata shiyasa kake damuwa da kukansu, matarka da huta Ali, Wallahi da ni na aureka da more miji” A zahiri da kanta take, sai dai a kasan zuciyarta tana ingiza mai kan tururuwa ne, saboda Leila ta soma dasa wani abu a zuciyarsa akan Ali. “Kina da son zolaya Madina, yanzu dai kuje gida ku huta” “Thank Youu Ali” Leile ta fada sai ya gyada mata kai ya rufe mata motar, Madina ta tashi motar tana fadin. “Angonki fa ya kira ni yana tambayar ina kike?” “Ai ina ganin kiransa na share shi” “Aa Leila be kamata ki yi haka ba ai sai ransa ya bace, kuma tun da har ya kira ai ya nuna miki kulawa” Madina na rufe baki sakon Talba ya shigo wayar Leila, tsaki tai bayan ta karanta sannan ta nunawa Madina, Madina kam dariya tai ta rike wayar da hannu daya tana rubutawa Talba amsar da take ganin ta dace da shi, sai da ta tura sannan ta mikawa Leila wayar. “Duba ki ga amsar da na bashi, ta nan zamu fara wana shi kuma mu gane irin son da yake miki” Leila ta tabe baki. “Ni yanzu ma ban sani ba, ina sonsa ko tsanarsa nake, bayan duk abubuwan da yake min, yanzu wannan abun da yai ya saka na fara jin tsanarsa a raina” Madina ta yi saurin kallonta tana tukin motar. “Da gaske? Wai kin bincika inda ya aje yarinyar nan kuwa?” “Yace be san inda ya kaita ba, ki kai ni gurin Momy can zan kwana” “Okay” Daga haka bata sake cewa komai ba, sai dai a zuciyarta murmushin jindadi take, domin Leila ce kawai zata zame mata matsala a tarayyarta da Talba, idan kuma har Leila ta juyawa Talba baya burinta zai samu ciki, a tunaninta Talba zai iya neman maye gurbin Leila da ita ko dan ya batawa Leila rai, a iya tunaninta Aminatu ba matsala bace a gurinta, domin ta san waye Talba kuma ya dade tana karantar rayuwarsa fiye da Leila da suka taso a gida daya. FARUQ POV. Yana tsaye a tsakar gidan rike da yar karamar traveling bag, yana sanye da kananan kaya kansa a kasa yana furta “Ameen” Idonsa yar rine yayi ja sosai kamar wanda ya wuni ya kwana yana kuka. “Allah ya baka abun da ka je nema Faruk, Allah ya shige maka gaba” Mama ta fada tana fashewa da kuka, ji take kamar idan Faruq ya tafi gurin ginar zinari nan ba zai dawo ba, shi kansa yana jin wani yanayi na rashin jindadi wata kila saboda be saba tafiya mai hadari da nisa kamar wannan ba ne. Dukawa yai ya kama hannun dansa yana kallon fuskarsa sai ya ji kamar kar ya tafi ya bar Sultan. “Dady yaushe zaka dawo?” “Ba zan dade ba, kuma zan kira a waya na gaisa da kai ka ji” “Momy fa yaushe zata dawo?” Faruk yai shiru kamar mai tunanin abun da zai fada masa, ya san shi kansa dauriya kawai yake balle kuma Sultan da yake karami, an raba shi da uwarsa yanzu kuma zai tafi ya bar shi hannun Mama. “Ita ma zata kira ka a waya ku gaisa, kuma idan zan dawo zan dawo tare da ita” Sai kawai ya fashe da kuka, daman tun da ya bude ido ya ga Dadynsa na shirin tafiya yake ta son yin kukan, Faruk ya kama shi ya rumgume zuciyarsa tana sosuwa da kukan dansa. “Dady zan bika, ka tafi da ni” “Ba a zuwa da yara, amman kai ta ma Dady Addu'a, idan ya samu kudi zan siya maka komai kake so kuma zai dawo lafiya” A take Sultan ya kara fashewa da kuka, sai Aisha ta zo ta kama hannunsa ta dauke shi ita ma hawayen ne kwance a idonta. “Kyale Dady zamu je mu siyo minti mu sha ba zamu je da shi ba ka ji?” “Dady zan bika zan bika Dady zan bika” Shi ne abun da Sultan yake ta maimaitawa har Aisha ta fice da shi. Sannan Faruk ya mike tsaye yana duba agogon hannunsa, hudu da yan mintuna gashi kuma abokin tafiyarsa ya fada masa da biyar za su kama hanya. Karasawa yai gaban mahaifiyarsa ya risina gabanta yana rokon gafararta. “Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na yi miki na bacin rai wanda na sani da wanda ban sani ba, kuma yi min addu'a, Inshallahu da zarar na isa zan kira ku, ga Sultan nn na bari a hannunki kuma a karkashin kulawarki, ko da Allah be kaddara min dawowa ba, Mama dan Allah karki bari Rafi'a ta dauke shi, kara yai ta zama a nan tare da ku da talauchi da ya koma karkashin kulawarta, ban zan iya abun da zata aikata nan gaba ba, kuma zan rika yi miki aike ke da ita saboda cikin dake jikinta Inshallahu” Ya karasa hawaye ya sauko masa, sannan ya mike tsaye Mama ta bishi da kallo tana hawaye kamar wanda aka cewa idan ya tafi mutuwa zai yi ba zai dawo ba, har ya fara tafiya bata ce masa komai ba sai da saka kafarsa daya a waje zai fita. “Allah ya maka albarka Faruk, Alhamdulillah ko Allah be ba ni arziki ba ya ba ni ɗa mai tarbiya, ni da kai ba a san gawar fari ba” Juyowa yai ya kalleta ita ma ta kalleshi sannan ya juya ya fice ba tare da yace mata komai ba. 30 Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* BATURIYA POV. “Amman kina ganin idan n zubar da cikin ba wata matsala?” “Wane irin matsala? Yau aka saba zubar da ciki ne ki rika yi ma kanki fata na gari mana” “Tsorona nake ji Wallahi kin san abun da baka saba ba” “Ba wata matsala kawai shawarar da zan baki karki yarda ki zubar da cikin yanzu, sai kin yi tafiyar nan da Alhaji kin dawo” “Ni fa bana son zuwa ko'ina Ramlee, iya abun da zamu a nan ya ishemu, ba sai mun tsallaka mun bar kasar ba, ka shiga jirgi kai sama da sunan zaka je aikata sabo?” Ramlee ta kalleta tana tabe baki. “Kar dai ki ce min tsoro kike ji? Ashe a gaishe da masu zuwa saudiya su aikata fiye da abun da kike tsoron aikatawa, ke matan da suka kware suka waye har lesbians suke fa da matan manya wasu kuma ta baya ake yi da su” Baturiya ta kwalo ido tana kallon Ramlee da mugun mamaki. “Yanzu Ramlee mutun zai taka jirgi ya tafi maka ka aikata sabo? Wannan kuma ai ya zama ganganci da isgilanci” “Babu ko daya Allah shi gafurun raheemun ne, ki rika kyautata zato mana, idan ka tara dan abun da ka tara kamin lokaci ya kure maka sai ka tuba ai, duk abun da zaki aikata wani yana can zai aikata fiye da abun da kika aikata na zubinu kuma Allah a cikin rahamarsa sai ya yafe masa ya saka shi aljanna, wani kuma zai aikata aikin lada mai yawa kuma daga karshe ya zama dan wuta” Baturiya ta sauke ajiyar zuciya. “Toh ai baka da tabbacin wuta zaka je ko aljanna, ni fa ina tsoron kar zunubin yai min yawa, ga kuma wani ina kokarin aikatawa yanzu cikin nan yanzu cikin wata na hudu yake” “Masu haihuwa su kashe yayan fa? Balle ke da be ma zo duniya ba? Gaskiya Baturiya kina da matsala ana nuna miki hanyar arziki kina sanyi jiki, ni dai yanzu fada min yaushe za ki samu fita sai na fadawa dan gidanki ya shirya?” “Fitar ce tawa yanzu zata zama aiki, idan ma cika fita za a fara saka min ido” “Shiyasa ni ban jidadin da kika kashe aurenki a yanzu ba Wallahi saboda Faruq be da matsala kina fita duk inda kike so weather ya barki ko akasin haka, su kuwa wadannan iyayene abu kadan sai ka fara jin tsinuwa da baki kala kala” “Wallahi kuwa, kuma kin ga za ayi saurin gane ni ce ba ni da gaskiya, domin ya ki fadawa Yaya abun da ya hada mu, sai cewa yai wai ko minene za su gani, shiyasa kudin ma na kasa kashewa, ina gudun na taba kudi Umma ta fara zargina” “Baki da wayo ne, ai wata hanyar zaki bijiro da ita ta samu kudi, kamar sana'a ko kuma ki nemi wani aikin ma wanda zai rika baki damar fita ki ga daga nan sai ki samu kafa kina yin yadda kike so hankali kwance” “Kuma fa da maganar ki, amman wace irin sana'a ce mai kawo kudi haka? Ni fa bana son zargi ko kadan” “Wannan kuma sai kin yi tunani, ko kuma mu samu hanyar yin aiki zai fi mana sauki ma” “Ssce ce da ni fa aiki zai samu da ssce? Na ga Faruq ma mai degree yana fama balle ni” “Ai ke da Faruq akwai banbanci, ke fa mace ce kuma a cikin matan ma mai kyau da daukar hankali, shi kansa da zai bada kasansa ga irin mazan nan da suke neman maza Wallahi na aiki ba har abun da yafi aiki idan yana so sai ya samu, yanzu fa duniyar ta zama yi min na yi maka ne, ba ni girishi na baka manda” “Ramlee kina da wayo Wallahi, ni kam sam irin wannan tunanin baya zuwa min” “Ba ki waye ba ne a abun, idan kika gwane ni kaina sai kin fara min wani gani-gani” “Uhm... Yanzu ki fadawa dan gidanki sai karshen satin nan za mu hadu” “Ni fa ce min yai ki saka masa ranar da zai rika ganinki, Wallahi Fee'at kina da farinjini da sa'a, kin ga manyan mutanen nan su suke sakawa mutum lokacin da za a gansu amman ke ya yarda ki saka masa ranar da zai rika ganinki” “Uhmmm yanzu ne zan tabbatar idan ina da sa'a ko akasin haka, sai idan na auri Fahat zan tabbatar da haka, duk kuwa da na san akwai kalubale mai yawa a gaba” “Kina ji zai aure ki da da? Kuma anya ya san kin taba yin aure kuwa?” “Be sani ba, kallon budurwa yake min, amman very soon zan fada masa na taba yin auren, sai dai ba zan nuna masa ina da da ba, kuma zan nuna masa cewar auren dole akai min, shi ma kuma saboda na ji yana cewa za ayi bincike gudun kar a binciko a gano wani abu” “Kina son Fahat din nan sosai Fee'at” “Uhmm ya hada komai ne da mace take so, kyau kudi, dan mayan mutane ga shi yana so na, jiya har tambayata yake wani kalar gida nake so yanayinsa da yadda zai kasance saboda yana son a fara gina masa gida irin tsarin da nake so” Baturiya na rufe baki kiran Fahat na shigowa wayarta, a take murmushi ya wanke fuskarta farincika kuma ya cika ruhinta. “Dan halak ka ƙi ambaton, kin ga shi ya kira” Ramlee ta yi murmushi kamar yadda Baturiya ma take murmushin tana kara wayarta a kunne. “I just call to say hi kin san idan ban kira ba hankalina baya kwanciya, bana gajiya da jin muryarki” “Yanzu kuwa nake zancenka a raina ina ta waken ganinka” “Da gaskiya ne ai da kin nemo mana hanyar da zamu rika ganin juna, amman sai rowar fuskarki kike min, muryar ma yanzu ba kullum nake ji ba” “Wallahi Umman mu ce take yawan fada idan ta ga ina waya, shiyasa sai na fakaici idonta nake kiranka ko na amss kiranka, yanzu haka ma ina tare da wata kawata” “Kin samu fitowa kenan? Amman shi ne baki kirani na zo mun gaisa ba? Ko shi ma Umma ta hana? Domin na lura Umma har yanzu bata san yarta ta girma ba” Ta yi dariya cike da nishadi. “Ai ba zata yarda na girma ba sai ranar da ka sace mata ni” “Ai na dade da sace ki, dauka ce kawai ban yi ba ita ma very soon zan mai da kulawarki karkashina” Kusan a tare suka saki murmushi ita da shi, kamin ya dora mata da. “Yanzu kina ina? Ina son na biyo mu gaisa i miss your face and your smile” “Ina nan bayan government house gidan wata kanwar Babana” “Okay yanzu zan karbo wani sako a tasha idan na fito zan same ki a can sai mu gaisa, ki min kwaliya mai kyau kamin na zo” “An gama Dear” “I love you” “I love you too” Ya sauke wayar yana murmushi, a can kasan zuciyarsa yai ma Baturiya muhallin, son ta yake so bana wasa ba, shi kansa yana mamakin yadda ya zurfafa a sonta. Tuki yake da hannu daya, dayan hannunsa kuma wayarsa ce a rike ya saka ajewa, daya daga cikin hotunan data turo masa ne ya saka a wallpaper dinsa idan ya kalli hoton har wani sanyi yake ji a ransa, fuskarsa dauke da murmushi zuciyarsa wasai yau zai gana da masoyiyarsa bayan tsawon lokacin daya dauka be hadu da ita face to face ba. Sabuwar ta sha ya nufa kamin ya isa ya kira direban ya sanar masa gashi ya kusa karasowa a ina zai karbi sakon. “Kace gurin Iliyasu Mai gadi ka karba sai ka bashi kudin” “Okay” Sai a lokacin ya samu aje wayar ya faka motar gefen titi domin baya son shiga da motar cikin tashar, ya fito ya nufi gate din. Kamin ya shiga ya tambayi wani mai talkami dake kusa da gate din ya nuna masa teburin da Iliyan yake zama, sai yai masa godiya ya nufi gurin da Iliyan yake zaune kamin ya karasa shi da Faruq suka rika kallon juna, yana ta kokarin tuna inda ya taba ganin fuskar Faruq, Faruq kam yana ganinsa ya gane shi, hakan ya saka ya mika masa hannu suka gaisa. “Kamar na sanka” Cewar Fahat sai Faruq ya mike tsaye yana murmushi. “Ni ai ina ganinka na gane ka, ka san ku manya ne ba ku saurin gane mutane, ni ne wanda ka kai asibiti lokacin da Mahaifinka ya kade ni” “Anyi haka to ya lafiyar jiki” “Alhamdulillah, gashi har muna shirin barin kasar” “To kaga kai ne babban kenan kasa” Kusan a tare suka yi dariya Faruq ya shafa kansa yana fadin. “Dole ne ai tun da kasar ta zama sai a hankali idan hagu da kiya ba sai mu koma dama ba” “Haka ne, Allah ya bada abun da aka je nema, koto zaku je ko togo?” “Nijar zamu leka mu samu rabonmu” “Nijar dai? Ba ku tsoron tafiya a mota kasar nan ba lafiya” “To ya za'ayi, dole ne mu fita daman ba asan maza da zama ba, kamin mu samu abun da muka samu mu dawo tun da aikin ya zama sai wane da wane” “Ka yi karatu?” “Na yi karatu Wallahi degree na yi, amman aikin ya zama sai a hankali” Da mamaki Fahat yake kallonsa domin this is the first time da ya taba ganin mai degree zai tafi nema a inda wasu suka ganin ko ba su yi karatu ba ba za su iya ba. “Da gaske?” Faruq yayi murmushi mai sauti. Sai Fahat ya ce. “Na yi mamaki Wallahi ba kasafai masu irin kwalinka suke yarda su yi aikin da zaka je yi ba, indai da har kwalinka yayi kyau ka turo min cv na maka alkawarin aiki inshallahu” “Da gaske? Allah yasa domin na raba cv gurare da yawa amman shiru ne har yanzu Wallahi” “Karka damu wani rabon nesa yake, me kake yi yanzu?” “Ina jiran abokan tafiyata ne” “Okay bari na karbi sako, sai mu je motana na baka number na da mail ka turo min cv ka, kuma ka kira ni Inshallahu zan sama maka aiki, ko dan sharar gidanmu ne na san sai ba zaka raina ba” Faruq yayi dariya sosai. “Ai ba zaka fara ba, nan gaba kadan ma kai zaka fara goge min talkami” Fahat ya kyalkyale da dariya. “Aiko zaka ga keta, Allah ya nuna mana lokacin” “Ameen ya Allah” “Bari na karbi sako sai mu na baka ko? Iliyasu nake nema mai gadi” “Gashi nan” Faruq ya nuna masa shi, ba dan ya masa wani farin sani ba sai dan yawan kiransa da yaji mutane na yi a daman zaman jiran abokan tafiyarsa da yake a gurin. Fahat ya karasa kusa da shi ya gaisa ya ciro kudinsa ya mika masa sannan ya karbi sakon takardun, suka jero tare da Faruq zuwa gurin motarsa, shi ya fara budewa ya shiga ya zauna ya dauki diary ya rubuta masa addireshinsa na email a kasa kuma ya rubuta masa number wayarsa sannan ya kai hannunsa ya bude front seat. “Bismillahi ban rike sunanka ba” “Umar Faruq” Faruq ya fada yana zama, sai ya mika masa takardar sannan ya bude ma'adanar kudi a motar ya ciro kudin da zai kai 20k ya mikawa Faruq. “Wannan a kara a sha ruwa, mail dina yana jiki sai ka turo min Inshallahu zan yi ma iya kokari” Faruq ya rasa da wane baki zai gode masa, ga wani uban mamaki daya cika shi na kyautar 20k a take. “To ai ni ka daure ni gaba daya, Wallahi ban san me zance maka ba” “Bana bukatar godiya, kawai kai min addu'a Allah ya cika min burina na auren wata yarinya da nake so” “Idan aurenta alheri ne a gareka, kuma ita din matar ka ce Allah ya shige maka gaba ka aureta” Fahat yayi dariya. “Mutun ya taba auren matar da ba tasa ba” “Sosai, zaka auri mace kai ta wahala da ita amman bata gani, kuma ku yi ta samu matsala ku kasa samun kwanciyar hankali saboda ba matar data dace da kai ba ce, kasan ance mata ta gari rabin jindadin duniya ce, I'm talking from experience, ko da yake kai kana da rufin asiri wata kila ba zaka samu irin matsalar da na samu ba” “Ta gujeka saboda talauci kenan ko kuma tana azabtar da kai” “Ba ma tare da juna yanzu, amman mace idan ba ta gari ba ce kuma ba alheri bace a gurinka kin aurenta shi yafi, duk da yake wani lokacin ba zamu san alheri ko sherin ba wani abu ba har sai mun kusancesu ko sun kusance mu” “Haka ne, ni ma zan yi ta addu'a kamar yadda Hajiyata take ce min, kuma kai ma wata rana zata dawo gareka tana neman yafiyarka idan ta gane kuskurenta Inshallah hope dai ba ku haihu da ita ba?” “Da daya, sai cikin dake jikinta yanzu” Faruq na maganar idonsa har ya sauya kala yayi ja alamar bacin rai. “Komai zai wuce, karki watsar da hakkin da yake kanka, ka yi kokarin ganin ka sauke duka nauyin dake kanka ba tare da ka zalince ba ko yaran, inshallahu Allah zai taimake ka, da kai yi zalinci kara azalince ka” “Haka ne na gode sosai, Inshallahu zan yi kokarin yin haka, Allah ya saka da alheri ya biya bukata” “Ameen nima na gode, Allah ya kaiku lafiya” Fahat ya mika masa hannu sukai sallama. “Ameen” Faruq ya amsa sannan ya fita motar ya rufe, key Fahat yai mata ya hau titi jikinsa a sanyaye, maganar da Faruq ya fada masa ta saka ya tuna da yawan nanata masa da Hajiyar take cewa ya rika addu'a idan alheri, sai dai shi yana kallon kamar tana fada masa haka ne saboda bata son ya auri wata sai wanda ta zaba masa. Wayarsa ya dauka ya kalli hoton Baturiya dake shimfide gaban wayar. “Ina fatar yadda kike da kyau nan, haka zuciyarki take, ko ma zuciyarki ta fi wannan kyau” Ya fada da murmushi a fuskarsa sannan ya kai wayar a bakinsa ya sumbace ta, kana ya cire key din ya kira Baturiya ta fada masa daidai inda gidan yake, yana driving din yana waya da ita har ya isa kofar gidan. “Gani kofar gidan” “Gani fitowa Dear” “I love you, sai kin fito” “I Love you too” Ya yi murmushi ya sauke wayar zuciyarsa cike da kaunarta. TALBA POV. A falon ya zauna kan karamin stairs din da kai ka sakiyar falon, domin ayi falon ne a kasa bedrooms da kitchen kuma a sama sai dai ba sama irin na gidan sama ba, wani tsari ne akai mai kyau. Yana zaune a gurin yana ta kallon falon da ba a saka komai a ciki ba sai farin fenti da kuma na'urar sanyaya daki, ya dauki enough time din da yake ganin ya kamata ace ta gama sallah sannan ya mike tsaye ya juyo da zimmar shiga bedroom din sai ya ganta zaune a bakin bedroom din tana kallonsa. “Kin gama?” Ta daga masa kai. “Kin ci abinci?” Ya sake tambaya yana karasawa kusa da ita. “Aa” “Ta so ki ci abinci sai ki kwanta” “Ni kadai?” “No nan zan kwana” “Toh” Ta mike tsaye tana dafa ginin ta koma ciki sai ya bi bayanta, a kasa ta zauna inda ledar abincin take shi kuma ya zauna kan gadon, da kanta ta bude ledar ta dauko takeaway din ta bude sai ta kalleshi. “Bismillah” “Ni na koshi, ci abincinki ki koshi” Ta maida kanta kasa ta fara cin abincin a hankali, shi kuma sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa, sai ga kiran Ali ya shigo wayarsa, yana kallon kiran har ya katse be daga ba, sai da wani ya sake shigowa sannan yai picking. “Ya akai?” “Ka kirani wayar na silent ban sani ba, I'm sorry” “Daman wata matsalar ce kuma yanzu ta wuce” “Gani kofar gidanka” Kai tsaye ya san a cikin gidansa yake nufi domin idan family house dinsu ne zai ce gashi a cikin gidansu, ba kamar yanzu da ya banbanta ta shi da gidansa ba. “Bana ciki” “Haba Malam ba halinka ba ne, ga motarka ka waje” “Toh bana son ka shigo” “Akwai maganar da nake son mu yi da kai” Talba ya mike tsaye ya kashe wayar ta kalli Aminatu. “Bari na budewa wani gate okay?” Kallonsa kawai tai ba tace masa komai ba har ya nufi kofar fita. “Karka ka dade tsoro nake ji” Ya juyo ya kalleta sannan ya daga mata kai alamar okay. Ya fice cikin izza da isa yake tafiya har ya isa bakin gate din ya bude karamar kofar ya kalli motar Ali. Ali na ganinsa sai ya bude ya fito ya rufe ya nufo inda yake yana murmushi, a can abu ne mai wahala su yi kwana daya ba su ga juna ba, idan dayan yana da wata matsala zai kira dayan ya sanar masa amman ya lura da Talba ya canja gaba daya ko irin sakewar nan ya daina masa. “Ya akai?” Talba ya tambaya sound so serious domin idan babu abun da ya kawo shi zai koma ciki ne ba zai tsaya saurarensa ba. “Ba zaka min tayin shiga ciki ba” Talba ya sakar masa kofar, ya juyo ya dawo cikin gidan, sai da Ali yai murmushi sannan ya shigo yana ta kallon gidan, Talba ya rigashi isa gurin kofar falon dan haka ya rigashi ganin Aminatu dake tsaye bakin kofar rana tana jiran karasowarsa. Be bukatar ya tambayi dalilinta na fitowa bayan ya san ya baro ta tana cin abinci, idan ma ya tambaye ta ya san amsar ta ba zai wuce tana jin tsoro ba. Da hannu yai mata alama da ta shiga ciki sai ta juya ta koma sai dai bata yarda ta koma bedroom din ba sai ta tsaya a falon har ya shigo, Ali ma ya shigo. Kallonta yai sannan ya kalli Talba. “What this?” Uffan Talba be ce masa ba, kallonsa kawai yake. “To be frank wannan abun be dace da kai ba sam, not because ina side din Leila but because I'm your friend, be kamata na ga abun da zai kai ka ga halaka ba ko ya taba mutuncin ka kuma ina gani na bari ka aikata, this is wrong very very wrong, kana tunanin idan Daddy ya gani ko Momy ko Leila da kanta za su jidadi? Haba Talba” “Kana da wata magana mai muhimmanci ne? Bachi nake son yi” “A nan zaka kwana kenan?” “Ina kake tsammanin zan kwana?” “Bana zarginka ko kadan Talba, amman sheidan mugun ne” Talba ya nufi kofa ya bude masa alamar ya fita, wani mugun mamaki ne ya kama Ali, ya san Talba yana da zuciya sosai amman be saba masa abun da yake masa a yau ba. “Okay” Ali ya fada yana jinjina kansa, kamin ya juya ya kalli Aminatu data rakube guri daya tana masa kallon tsoro. Sai kuma ya juya ya fice. “Kin ci abinci?” Talba ya tambaya sai ta daga masa kai, “Kin koshi?” Nan ma kan ta daga masa. “Shiga ki kwanta zan shigo da motata ciki” A nan bata samu damar daga masa kan ba, balle har ta amsa masa da to ko ta shiga dakin kamar yadda ya bukata. Be kula ta ba ya shiga dakin ya dauko keys dinsa ya fito tana tsaye ya fice daga falon, sai ta sake dawowa bakin kofar falon kamar dazun ta tsaya tana kallonsa har ya bude gate din ya shigo da motar ya rufe motar ya nufo kofar falon. Sannan ta kauce masa ya shigo sai ya wuce dakin kai tsaye, ganin ya dade be fito ba yasa ta bi bayansa. Sai ta same shi zaune kan dankwalin da tai sallah tana ta taba wayarsa, bata bukatar yace mata ta hau ta kwanta daman tun dazun bachi ke kawo mata hari bayan wanda tai. Sai kawai ta nufi gadon ta hau ta kwanta ta juyo da fuskarta ta inda zata rika ganinsa. Ko da wasa be kalli inda take ba har bachi ya dauke ta, sai da ya tabbatar bachin nata ya nina ta hanyar numfashi dake ta fita da karfi yana bada sauti, sannan ya tashi ya nufo inda yake aje bedsheet ya dauki daya kana ya doshi inda switch din wutar yake ya kashe, gudun kar ta farka yasa be rufe kofar ba ya fito falon ya shimfida bedsheet din ya cire jallabiyarsa yar vest din dake jikinsa ma sai da ya cireta, domin abu ne mai matukar wahala ya kwana da riga, no matter how hot or sanyin sa ake a gari ko a waje, baya sakewa idan ya kwana da riga, sai da ya rage hasken falon sannan ya kwanta a kasa, can kuma ya tashi yai addu'a ya sake kwantawa ya rufe ido ba dan yana jin bachi ba, kuma ba dan yana tsammanin bachin zai bashi hadin kai ba, sai dai be bude idon ba har kusan daya na dare. Yana jin motsin lokacin da Aminatu ta fito daga dakin ta tsaya bakin kofa, can kuma ta kwanta nesa da shi ba sosai ba tana facing dinsa, kamar dazun yanzu ma be bude idon ba sai da ya tabbatar da bachinta ya nina sannan ya bude idon ya tashi zaune. Fitilar wayarsa ya kunna ya haske fuskarta, sai ya hangeta tana bachi hankali kwance ta saka hannunta daya a cikin baki kamar mai tsutsar hannu. He spend more than thirty minutes yana kallo kyakkyawar hallitar Allah, an tsara mata komai cikin kwarewa da hikima irin ta Ubangiji, hancinta ya tsayu, kana gani kasan gwanin baiwa da rahama ne yai halinci komai na fuskarta, a kasan hancin an yanka mata wani karamin baki gwanin sha'awa da burgewa, idanuwanta dake rufe suka kara bayyanar da gashin idonta daya cika kamar ta aro. Fuskarta na ta sheki kana ganin fentin fatarta kasan ba dai mutum ba sai dai Allah, babu digon fari ko kadan a jikinta, sai dai hakan be rage ta da komai ba a kyau, sai ma kara bayyanar da godiyarta ga Allah na tsaya a yadda Allah ya yi ta. “Unique” Ya fada yana jin kamar a yau ya fara ganin bakar fatar da ta dara fararen mata kyau da aiba irin ta hallintar Allah Subhanahu Wata'ala. A yau ya tabbatar da akwai hikimar Allah na yin fararen mata da bakake, sai dai bakin mutum ya banbanta da kowa, domin ba a siyen baki. Daukar rigarsa yai ya saka sannan ya dauki bedsheet din da ya shimfida ya karasa inda take ya lulluba mata, ya tsakala ta ya shiga dakin ya dauko matashin kai ya daga kanta ya saka mata, kana ya hanye mata hannun data saka a baki, sai ta turo bakin kamar mai shirin fashewa da kuka, sai dai ba kukan zata yi ba domin bachi take. 31 Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Komawa yai cikin dakin yai alwala ya shimfida dankwalinta yai sallah nafila akai sannan ya cire rigarsa ya hau saman gadon ya kwanta. Misalin uku da wani abu ta farka, tana bude ido ta hango inda yake kwance babu kowa sai tai saurin tashi tana waige waige. Har ta yi kamar ta fara kuka sai ta hangoshi saman gadon hasken gulob din waje na hasko shi, tashi tai da sauri ta koma can kusa da gadon ta kwanta kasa ta takure kanta sosai kamar zata shige karkashin gadon. Bachi da bata farka ba kenan har sai da yai sallah asuba ya tashe ta. Sai ta farka a firgice duk da kasancewar a hankali yake tashinta. “Tashi ki yi sallah” Ta fara murza ido, sannan yunkura ta tashi ta nufi bandaki tana takawa a hankali kamar yadda take har ta shiga, bata sha wahala gurin kunna fanfo ba domin ta kula da yadda ya kunna mata fanfon jiya. Bayan ta gama alwala ta fito sai ta same shi zaune gefen gado yana karantu a alqur'ane da wayarsa, inda tai sallah jiya a gurin ta sake yin sallah asuba. Bayan ta gama ta daga hannunta ya yabi Allah ta miyar godiyarta a gareshi sannan ta yi salati fa Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wassalam, kana ta bijiro da bukatarta na naman gafara ga iyayenta, sannan tai ma maka na neman mafita da madafa, sai kuma ta rufe tana yi ma al'ummar Musulmi, ta dora da salati. Jinginawa tai jikin gado tana ta sauraren karatun da yake da muryarsa mai dadi saurare, sai ta lumshe ido kamar mai bachi alhalin ba bachin take ba. Sai da ya kai karshen suratul Ibrahim sannan yai addu'a ya aje wayar ya kalli inda take jingine jikin gadon idonta a rufe. Hakan nan kawai ya ji yana bukatar gyara mata kwanciyar kanta jikin gadon domin bata aje shi yadda ya kamata ba, wuyanta zai iya ciwo. Tashi yai ya karasa gefen gadon a haka ya kai kyakkyawan hannunsa ya kama fuskarta da zimmar kwantar da ita sai ta bude. Idanuwanta da na shi suka sarkafewa juna, ko wanensu ya kasa yin kawaicin dauke nasa, a zahirin kyaun idanuwanta yake kallo, a yayinda fuskarsa da idanuwansa suke mata kwarjini. “Ina kwana... ”   “Ina kwana... ” Suka furta a tare muryarsa ta muryarta sukai tarayya a lokaci daya, kamar yadda numfashinsu sukai auratayya da junansu, ta hanyar shiga da ita a tare. Ta kowace kusurwa a hancinta na shigar mata da kanshin turarensa, ya samu guri can kasan ruhinta ya kwanata. A yayin da shi shiga da fitar numfashin yake shiga tare da bugun zuciya mai tsanani. Ita ta fara dauke idanuwanta tana murmushi kadan, sai kuma murmushi ya cika bakinsa har ya kawata fuskarsa, mikewa yai tsaye yana kallon kofa. “Kar mu yi latti, ki shirya sai mu tafi waje mu karya, sai mu kama hanyar” “Toh Yallabai” Ta amsa tana kokarin mikewa tsaye, sai ya nufi kofar dake kallon yana jin sunan wani iri wai Yallabai, sound so funny. A falon ya dawo ya zauna har sai da ta fito sannan ya juyo ya kalleta he thought ko zata yi wanka ne ta canja tufafin jikinta. “Baki yi wanka ba?” “Baka ce na yi ba” Ya wara ido. “Komai sai na ce ki yi? Come on ba ki bukatar komai sai na fada miki fa” Juyawa tai ta koma ciki bathroom din ta shiga bata ga soso sai sabulu da shower gel kusan kala uku. Bata san abun da ake da shower gel din ba hakan yasa ba tai karanbanin tabawa ba, sai kawai tai amfanin da sabulun tai wanka, bata yarda ta fito ba sai da ta leko ta ga baya cikin dakin sannan ta nufi inda akwatinta yake da saurinta kamar ba mai ciwon kafa ba, ta bude akwatin ta dauko doguwar riga ta saka tana kokarin daura dankwalin ya shigo sai tai saurin juyawa ta bashi baya, shi kuma sai ya fice yana jin wani iri. Be sake dawawo dakin ba har sai da ta saka hijabinta ta fito falon. “Na gama” Juyowa tai ya kalleta ita ma kallonsa take kamin ta kalli jikinta ganin yadda ya kura mata ido. Sai ya mike tsaye ya shiga bedroom din ya hada tufafinta har Wadanda ta cire a cikin akwatin sannan ya janyo akwatin ya fito da shi, yana gaba tana binsa a hankali har suka fita falon, cikin karfin hali ta karasa gurin daya faka motarsa shi ya fara bude mata kasancewar ya rigata isa gurin motar sai ta shiga gidan gaba ta zauna, bayan ya saka akwatin a mota ya koma ya rufe kofar falon sannan ya nufi gate ya bude ya dawo cikin motar yai mata key. “Zan fara biya gida na yi wanka n canja tufafi sannan na tafi” “Toh Yallabai” “Talba, idan ba zaki iya ba ki kira ainahin sunana Mu'az” Ya fada yana reverse sannan ya fita da motar gaba daya, ya dawo ya rufe gate din sannan ya sake komawa cikin motar ya ja suka dauki hanyar Shimkafi road.   A lokacin daya isa kofar gidan sai ya faka motarsa daga waje, sannan ya fita ya nufi gate din yai knocking aka bude masa, ya shiga ciki suna ta mamakin ganin motarsa a waje kuma a jiya be kwana gida ba. Be shiga bangarensa ba sai da ya fara shiga part din Daddy ya gaishe shi sannan ya fito ya nufi part dinsa, a gaggauce yai wanka ya fito be tsaya shafa komai ba sai turaren daya zame masa jiki sannan ya dauki abubuwna bukatarsa ya saka aljihun shaddarsa ya saka agogon hannunsa sannan ya fito yana ta sauri kar Daddy ya riga shi fitowa ya ga Aminatu a motarsa, gashi yayi sa'a Daddy ya manta be masa maganar tafiyarsa kauye ba kamar yadda ya sanar masa a jiya, wata kila Daddy ya dauka ko sai da rana zai tafi ko kuma ya fasa ne, yana ta sake sake ya mai gadin ya bude masa gate ya fita. Sai ya hango motar Leila kusa da tasa motar rage tafiyar da yake yai yana nazarin a gidan ta kwana ko kuma yau ta dawo? Ta dade a gurin. “Miyasa kike zargina da abun da ba ni na aikatawa kaina ba? Ke kin fi karfin Allah ya jarabeki ne?” Aminatu ta tambaya cikin wani irin kuka marar misaltuwa. “Me ke faruwa” Talba ya tambaya a lokacin daya karasa kusa da su, Leila da ta baro motarta ta zo gurin Aminatu ta tsaya ta kalleshi. “Babu, kawai na tambaye ta ne ya ta ji a lokacin da mutum fiye da goma suka keta mata haddi? Kasan me? Kai nake kokarin tunawa cewa wannan gwanjo ce, wadanda wasu suka gama amfani da ita suka jefar wasu man kuma wulakantaccin mutane da basa wanka sai sun ga dama, basa sallah kuma kashe mutum ba ya musu wahala, amman ka dauko ta kake kokarin motsa kishi na da ita...” Tana kai aya Talba ya wanke mata fuska da mari cikin wani irin zafin nama da bacin rai. “Taya kina mace zaki aikatawa mace yar'uwarki haka? Allah ya wadaran halinki Leila” Ta dafe kunci hawaye na sauko mata, Aminatu kuma ta duka a gurin dafe da zuciyarta tana jin wani irin zafi da tukiki na kalaman da Leila tai mata, sai ta fi jin zafin kalamanta fiye da abun da mutanen suka aikata mata, ashe haka ake ji? Tabbas jawabi ba shi da dadi, yanzu bayan duk abun da ya faru har akwai wanda zata yi kokarin koranta mata a halin rayuwar da ba ta zaba ma kanta ba? “Ka mare ni Talba saboda wata bare? Ka dauko ka kawo har kofar gida, ban kwana a gida ba, yanzu na dawo amman ina da tabbacin ita ma din a tare da kai ta kwana! Ko kadai ne namiji daya rage a duniya na hakura da kai Talba...!” Ta fada kai tsaye hawaye na sauko mata, tana kallonsa ido cikin ido. “Idan ka haihu ga ta uba da uba, ka auri yarinyar Talba...! Ka aureta sai na san son da kake mata na hakika ne, sai na san ka cika ka tumbatsa da tausayinta, sai na san ka amsa sunanka Talba” Ta fada tana nuna shi da yatsa hawaye na sauko mata. Hannu ya kai zai kama hannunta sai ta kauce ta nufi motarta ta shiga ta fasa shiga cikin gidan ta juya ta koma inda ta fito tana fisgar motar. Sai ya ji babu dadi kamar be kyauta mata ba, not because of tace ta fasa aurensa but because of ya san kishi babu abun da baya sakawa ya kamata yai mata uzuri, and be kamata ya zo da Aminatu kofar gidan ba first place har ta gani, ba ita ba ko Daddy ya gani ya san ba zai jidadi ba. “Shiga mota mu je” Ya fada yana kallonta, sai ta mike tsaye tana kallonsa tare da girgiza masa kai. “Aa dan Allah kai yi hakuri, ba zan iya ba, ka taimake ni iya taimakon da zaka iya kuma na gode Allah ya biyaka, be kamata na shiga tsakaninku ba, karka yarda ka rasa yan'uwanka ba zaka taba samun mai maye maka gurbinsu ba, dan Allah ka bar ni na yi tafiyata” Be bi ta kanta ba ya kai hannunsa ya rika cinyar hannunta ya saka a motar da karfi ya rufe sannan ya zagaya ya shiga bangaren direba yaja motar suka kama hanya.   Kuka take sosai cikin motar mai sauti, and what he hate the most is kuka, ko na yara ne baya so, yana tukin yana kallonta sai be ce mata yi shiru ba balle kuma ya tattara kalaman bada hakuri ya bata. Sai da suka kusa fita gari sannan ya tsaya gurin wani restaurant ya siya mata abinci domin shi dai baya jin zai iya cin komai a yanzu bayan ruwan sanyi da riko ma kansa. A gidan baya ya aje ledar abinci ya dawo driver side ya zauna tare da ruwan gora a hannunsa, sai da ya fara sha sannan ya mika mata ba tare da ya ce komai ba. Sai ta karba ta kai bakinta ta sha kadan ta mika masa sai ya karba ya rufe gorar ya ajera a muhallin da aka tanada domin ajeta a cikin motar, sannan ya cigaba da tukin. Suna hawa babban titi zuwa sokoto sai ya kara ac ya kwantar mata da kujera, nan da bachi ya dauke ta.   Har aka isa cikin garin maradun bata sani ba, har sai da ya faka gaban wani wadataccen gida dake unguwar gabas, ya kashe motar yana kallonta, sai kuma ya sake daukar ruwan ya sha ya rike gorar a hannunsa ya bude motar ya fita, kamin ya zagaya side dinta har ta bude idon ta tashi zaune tana kallon garin da yai yanayi da na su. “Fito” Ta fito tana kara kallon garin da take kyautata zaton ta taba zuwansa sau biyu zuwa sau uku a rayuwarta, sai dai ba zata iya kawo kanta ba. Rufe motar yai ya matsa key din hannunsa, shi kansa yana missing din garin da gidan da kuma mutanen da suke cikin gidan. Yalwataccen gida ne da itacen dogon yaro suka kawata shi ta ko'ina daga ciki kuma irin dogon itacen nan ne da ake cewa bedin turawa, ko'ina na gidan ya sha simimti kamar ba kauye ba. Tsaye tai sai da ya fara wucewa ya shiga ciki sannan ta bi bayansa tana ta karewa gidan kallo. “Tsohuwa... ” Ta furta tana ta kara kallon gidan, Talba ya kalleta sai dai be ce komai ba ya cigaba da tafiyar har suka shiga cikin gidan, abun ka da family house a take gidan ya dauki ihu suna ta murna da ganinsa, wasu kuma na dan kallon Aminatu suna ganin kamar sun santa ita ma haka take ganin kamar ta taba ganin fuskokinsu. Sai da Talba ya gaisa da su, tabasansa suka hau tsokanarsa suna masa wasa da ce masa baya son zumunci. “Wannan fa ko ita ce matar ta mu ka zo ka nuna mana?” Ya kalli Aminatu yayi murmushi. “Aa” Shi ne kawai abun da ya fada sannan ya nufi bangaren Kaka. Kamin ya shigo murmushi da farinciki ya cika fuskarta, sai dai ganin Aminatu a bayansa ya saka ta manta da komai tana kallon Aminatu. Aminatu ma Kallonta take sai ta fashe da kuka ta karasa inda take da sauri domin ta manta da wani ciwon kafa, sai ta fada jikinta tana kuka. “Tsohuwa...” Kaka ma fashewa tai da kuka ta rumgume Aminatu tana kuka sosai, sai kara nerkewa take jikinta kamar zata shige cikinta. “Auta... Laaa sai yanzu na gane ta” Wata babbar mace dake tsaye kusa da Talba ta fada, sai Talba ya kalleta ya sake kallon Aminatu dake rumgume da Kakarsa tana kuka, mamaki ya hana shi cewa komai. “Aka ce an kashe kowa, ashe ba gaskiya ba ne” Matar da tai magana dazun ta sake fada, tana hawaye cike da tausayi. “Kun santa ne?” Talba ya tambaya. “Eh jikar kawo Bala ce dake Galadi” Talba yayi shiru yana mamaki, ya san kawo Bala dai dai ba kowa ya sani ba a cikin yayansa balle ya har ya sheidi jikansa, daman a familyn Mahaifiyarsa ba kowa ya sani ba, da dai na Daddy ne ko Momy sukan kusan zai iya shaidar kowa. LEILA POV. Da kuka ta shigo gidansu Madina, ko gaisuwar da ta saba yi ma mahaifiyarsu Madina bata iya yi ba a yau saboda kukan da take. Cewar da tai ta fasa auren Talba ya fi komai daga mata hankali miyasa ta fada masa haka? Bayan ta san har ga Allah ba zata iya rayuwa babu shi ba? Madina na ganinta ta kama hannunta suka shiga dakinta ta zaunar da ita gefen gadonta hankali tashe. “Subhanallahi, Leila mi ke faruwa?” Leila ta kama hannun Madina ta dora saitin zuciyarta da take jin kamar zata fashe. “Talba Madina Talba...” Madina ta fisge hannunta tana jan tsaki. “Ba ki taba ba ni haushi ba akan Talba sai yau, akan Namiji kike wannan kukan Leila? Me kuma ya faru?” Haka nan cikin kuka ta labarta mata abun da ya faru. Sai hankali Madina ya tashi fiye da na Leila, jin cewar Talba ya kwana gida daya da Aminatu, kuma har ya mari Leila akanta. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ta fada tana mikewa tsaye. “Bana son na je gurin Momy ne na tayar mata da hankali” Leila ta fada cikin kuka tana jin zuciyarta kamar zata nerke. “Leila kar fa abun da muke gudu ne zai faru, miyasa kika masa wannan furucin, kin san halin Talba da zuciya” “Ba zaki ga laifin abun da yai min ba? Sai nawa kike gani?” “Ba wai ban ga laifinsa ba ne, mafita nake nema mana” Ta dawo ta zauna. “Kin san me? Zan iya rantsuwa Talba ba zai auri yarinyar nan ba, amman kar shedan ya rinjaye shi ya fada a halaka mu kuma mu fada a komar da na sani” Madina ta rika Leila tana kokarin tashinta tsaye. “Kin san me? Je ki wanke fuskarki wannan lokacin ba na kuka ba ne, idan kalaman da kika yi zaki iya kiransa ki bashi hakuri” Leila bata musa ba, ta shiga bandakin tai wanke fuskarta domin ta san Madina bata dorata a shawarar banza. Bayan ta fito ta tararda Madina ta kawo mata ruwan sanyi da cup dai ta dauka ta zuba ta sha, ta sake zubawa ta sha sannan ta aje kofin tana kallon Madina. “Me minene mafita? Ni ba zan iya bawa Talba hakuri ba, yadda yake ji da kansa haka nake jin kaina, kuma shi ya kamata ya ba ni hakuri ai” “Ba ta wannan ake ba yanzu, kin san abun da nake ganin shi ne mafita? Ki lallaba Momy ta dawo gidan nan idan ta dawo sai ki sake lallabata ta saka Talba ya dawo da yarinyar nan gidan nan” Leila ta yi mata kallon rashin fahimta. “Ta dawo gidan kuma? Idan ta dawo ai sai abun ya fi haka ma, kin manta yadda ya fara yi ne akan wannan banzar” “Ai inda yake tare da ita a can yana kara kusanci da ita ne, amman idan aka dawo da ita a nan komai zai faru kina gani” “Wannan ba mafita ba ce, domin zai iya disgani a gabanta idan na yi mata wani abun” “Ai ba haka zamu samu wanda sai aureta, sai mu biya shi kin ga mun huta, ke kuma sai ki biro masa da maganar aurenki” Leila ta yi shiru tana nazari kamin ta kalli Madina da murmushi a fuskarta. “Haka yayi, amman Talba zai iya zargin wani abu” “Zamu yi abun ne cikin hikima ba tare da kowa ya gane ba, ke dai ki bar komai a hannuna, kuma ki bincike Ali domin mu san inda yake aje yarinyar” “Zan yi hakan, amman kina ganin Talba zai yarda” “Dole ma ya yarda, idan yarinya ta kamu da son mutumen me zai iya yi? Kin ga mun dauketa cikin rayuwarmu cikin sauki” Leila ta yi murmushi tana kallon Madina wanda ita ma murmushin take. “Yanzu ki kira Ali ki fada masa abun da ya faru cikin, kuka daga nan sai ki bincike inda yarinyar take” “Okay” Ta amsa tana ciro wayarta a jaka ta kira Ali fuskarta da murmushi kamar ba ita ce ta shigo dazun fuska sharkab da hawaye ba. Yana yin picking ta fashe masa da kuka. “Subhanallahi Leila lafiya dai?” “Ali ina cikin matsala kana ina dan Allah?” “Ina gurin aiki” “Gani zuwa, zan so na same ka yanzu” “Okay sai kin zo” Ta sauke wayar tana kallon Madina, sai su kai murmushi a tare. 32 Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud Sandal flakes Sandal wood Signature Kajiji Damboun kajiji Halud ball Wardrobe ball Coconut sandal exclusive gowe Black humra Body milk Kulaccam Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* Tana daga waje zaune cikin mutanen gida, sai dai hankalinta ya tafi wani gurin dabam, domin kana kallonta ka san tana zaune a cikinsu ne kawai amman bata sauraren hiran da suke. “Ai akwai makaranta mai kyau ko kaka?” Kaka ta kalleshi tana jar carbin hannunta, idonta har ya sauya kala saboda kukan data sha na labarin da Aminatu ta bada. “Akwai, akwai inda babu boko a yanzu? Ai sai dai idan mutum baya son saka dansa” “Sai a sama mata makaranta mai kyau a saka ta, tun da gaki a kusa da ita” “Karatu yana da kyau, amman ba karatu ne abun da Auta take bukata ba a yanzu, miji mai tsoron Allah wanda zai riketa da mana, domin a duk lokacin daka rasa uwaye, miji ne yake maye maka gurbinsu idan ka samu n gari, idan ni, ni ma ai ina kusa da mutuwa, wanda be tsufa ba ma ya jira mutuwa balle ni” Kaka ta saka hannu ta share hawayen daya zubo mata. “Mahaifin yarinyar mutumen kirki ne ga zon zumunci, ko dan'uwa be san shi ba shi sai ya san dan'uwa, zuwansa biyu da Auta zuwa na biyo ya dauke ni ya tafi da ni na ga iyalansa sannan ya sake dawowa da ni, ashe ganin karshe kenan na yi masa” “Allah ya masa rahama, amman ya kike da shi?” “Da ubansa da ni uban mu daya, ubanmu, ni an auro uwata daga nan aka tafi da ita can, a lokacin da Allah ya iyakance auren sai aka rabu, ta dawo a nan maradun tare da ni, shi kuma suka zauna can, wadannan Bandits sun hana yi kowa zaman lafiya, Allah ya isarwa yarinyar nan” “Ameen, tana ba ni tausayi sosai, shiyasa ma na yanke shawarar kawo ta nan ta zauna tare da ke ashe ma yar'uwa ce” “Ta fada min abubuwan da suka faru, ban jidadi ba mutum ko ba san inda ya fito ba ka ga yana bukatar taimako ai sai ka taimaka masa, balle har kai ka kawota, irin yarinyar nan ai bana jin ko bakar magana ta cancanci a fada mata” Kaka ta sake share hawayenta. “Ubanta be yi komai ba sai alheri, da shi ne da yanzu ya kame dan wani ya rumgume, amman ga tasa na watangaririya har ana wulakantata, mutane kwarai su ake ta kwashewa ana barin na banza” Ta saka tsumman dake gabanta ta share majinar hncinta, sannan ta kalli Talba dake zaune kan gadonta. “Da ace na isa da kai da na saka ka auri yarinyar nan...!” Talba yayi saurin kallonta. “Kaka ai... Ina da wanda zan aura kawai dai lokaci ne be yi ba” “Ban sani ba, saboda ba a fada min ba, ni ai talaka ce shiyasa ba a sakawa da ni balle a kwance, ganina ma sai ka ga dama kake zuwa yi, yanzu ma ba dan kana neman inda zaka aje ta b ada ba zan ganka ba wata kila sai na mutu, saboda uwarka na haifa ba uba ba, shiyasa ban isa na saka ayi ba ko hana, ban isa na san komai ba” “Ba haka ba ne kaka, idan kin kula Aminata ba aure take bukata ba a yanzu, kuma kin ga Daddy ya zaba min Leila taya zan zo masa da maganar wata kuma?” “Ba aure take bukata ba? Saboda bata kai mizalin auren ba? Ko kuma saboda ita jinin talauchi ce kamar ni? Ko kuma saboda kana dan Boko ita tana yar kauye? Ko kuma saboda tsatsona ce? Ita wacan da yake bangaren ubanka ta fito ai ka aminta ko?” “Ba haka ba ne Kaka kin yi min kuskuren fahimta, tun kamin yarinyar nan ta zo an tsayar da maganar auren mu da Leila, rana ce kawai ba a saka ba” “Amman ai ba a taba fada min ba, saboda an maida ni talaka, wato da sau lokacin auren yayi sai a fada mana ka yi aure ko kuma zaka yi? Daman tun da aka haife ka suka saka hannu suka dauke ka, ba suke waiwayar inda muke ba, dangin ubanka ai babu wanda baka sani ba, amman na nan sai dai su suce sun sanka, ina matsayin mace data haifi uwarka amman sai ka share shekara biyu baka zo inda nake ba, na tabbatar da in da arziki da kullum sai ka ziyarce ni, Shi wacan uban daya dauke ka be nuna maka ka so dangin uwarka ba, balle ya nuna maka ka bisu” “Ba haka ba ne, Kaka dan Allah karki fadi wata mummunar magana akan Daddy, ba shi da laifi a nan” “Daman ai ba zaka ga laifinsa ba, ba zaka yarda ka bata masa rai ba, amman ni da nake uwar data haifi uwarka a baka gudun bacin rai na, kuma baka damu da ni ba, to ni ma babu ruwana daga yau duk wani abu naka babu hannuna a ciki, ba aure ba ko mutuwa kai kar a fada min, kuma ni bance idan na mutu ka zo gaisuwa ba” Kaka ta karasa a fusace, tana dauke kafafuwanta daga dayan bangaren ta maida dayan. Talba ya mike tsaye da sauri yana furta “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ganin yadda karamar magana ta juye ta zame masa babba. Har ga Allah shi dai ba zai ce yana son Aminatu ba, ko a da can da yai yunkurin aurenta zai yi ne saboda gudun fadawa halaka da kuma tausayinta da yake amman ba dan yana sonta ba, a yanzu kuma yana ganin ta samu mafita na gaduwa da wasu daga cikin danginta yana ganin kamar komai zai zo masa da sauri ita ma ya zo mata, sai kuma Kaka ta zo masa da wani sabon zancen kamar saukar aradu. Zuwa yai ya durkusa a gabanta ya dafa hannayensa yana kallon kakar tasa data dauke kai. “Haba Kaka, ni ma ai abun tausayi ne, ina zan iya da mata biyu a yanzu? Kin san ni ba mai son rigima ba ne” “Ban sani ba, ai baka tashi a gabana ba balle na sani, su isassu su suka san abun da kake so da wanda baka so, ni ba zan cilasta ka aurenta dole ba, daman ai ban isa na yi hakan ba, amman Wallahi Mu'azu wannan ne abu na karshe da zan roki ka yi min, har kasa ta rufe idona” Ta karasa idonta na cika da hawaye. For the first time da Talba ya aikata wani abu ya ji ina ma be aikata shi ba, a yau kam ya ji kamar ace be zo garin nan da Aminatu ba. “Amman kaka yarinyar nan bata dade ba fa, yau yau muka zo sai kuma ki dauki min wata maganar aure? Ina laifin ma ki barta ta kwana biyu?” “Yanzu nake da wannan damar, idan ka saka kafarka ka tafi ba zan sake ganinka ba sai nan da wasu shekaru, wata kila sai na mutu. Ka yi hakuri Allah zai bata wani ai ba kai ne kadai dan'uwanta ba, zata samu miji na gari inshallahu” Gaba daya sai ya ji kalaman bakinsa sun kare, ya zai yi ya fahimtar da kaka sai ya rasa. Mikewa yai tsaye ya nufi kofar fita cikin yanayin damuwa. Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya bakin kofa ya fara tsayawa sai kuma ya fara takawa ya nufi gurin daya aje motarsa, be karasa ba ya juyo yana kalle kallen neman mafita sai ya hango Aminatu zaune gindin wani icen dogon yaro, ta bashi baya. Sai da ya sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya juya ya doshi inda take, ta bayanta ya fara tsayawa jin motsin mutum yasa ta kai hannu ta share hawayenta. Sai ya zagaya gabanta ya zauna kusa da ita a saman dutsen dake gurin, akwai hasken gulub a gurin amman haka be hana shi ciro wayarsa ya kunna fitilar ya haska fuskarta, arba yai da hawayen da take. “Kuka dai? Bayan na kawo ki gurin Kakarki har kina neman ki fini gata” Kallonsa tai wasu hawayen na sauko mata. “Baka san yadda nake ji ba” “Na sani, ni ma ai na rasa uwa da uba kin tuna?” “Ka san yadda ake ji idan an rasa uwa, da uba, amman baka san yadda ake ji ba idan an rabaka da su a gabanka, baka san yadda mace take ji ba idan aka ci zafinta.. Shi ma na kasa mantawa... ” Ta fashe da kuka. Sai jikinsa yai sanyi shi din ba mace ba ne, amman kalmar daya fi tsana ita ce fyade. Shiru yai yana sauraren kukan da take rerawa a hankali can kuma ya dauke kai. “Shi ma zaki manta nan gaba kadan” Daga haka yai shiru yana ta kallon wani gurin zuciyarsa kuma tana masa wani iri saboda kukan da Aminatu take, a kokarinsa na dauke mata hankali ya ce. “Kina son karatu?” Ta kai hannunta ta sake share hawayen da suka ki tsaya mata. “Da can, ina so ina da wannan mafarki” Sai ya kalleta “Yanzu fa?” Ta girgiza masa kai alamar babu. “A yanzu ina tafiya ne a yadda rayuwa ta zaba min na tafi, duka burina da mafarki ya ruguje” “Idan na miki alkawarin wani abu zaki yarda?” Ta daga masa kai tana kallonsa still hawaye na sauko mata. “Na miki alkawarin farinciki, kuma na miki alkawari zan cika miki wannan burin na karatu da duk wani buri naki da be fi karfina ba” Shiru tai bata ce masa komai ba, a yanzu kam tana ganin kamar cikin burinta ba shi da amfani, Domin an baro kyau ne tun a gurin wanka, ta rasa farincikinta dawowa da shi kuma ba zai yiyu ba. “Akwai sanyi ki shiga ciki” Ya fada bayan ya daga kansa yana kallon hadarin dake haduwa a samaniya. Ita ma kallon hadarin tai sannan ta mike tsaye. “Kaka ta ce idan ka tafi zaka yi shekara baka dawo ba, gobe zaka tafi ko?” Daga zaunen da yake ya sakar mata murmushi sannan shi ma ya mike tsaye. “Haka dai take gani, amman fada min kin saba da ni ne, za ki yi marmarina idan na tafi?” “Me zai saka ba zan yi marmarin mutum mai karamci da sanin darajar dan adam kamar kai ba? Yallabai wani ya taba fada maka kai mutumen kirki ne? Kana daya daga cikin mutanen da suke wahalar samuwaa wannan zamani, mutumen da baya duban dukiyarsa ko kyaunsa ko asalinsa yake nemawa wani musulmi dan'uwansa mafita!” Wani irin kallonta yake cike da shaukin kalamanta. “Wani ya taba fada maka zuciyarka mai kyau ce?” Ya girgiza mata kai alamar aa. “Ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da mutumci da sanin darajar dan'adam kamar kai ba” Yayi murmushi yana sanda kansa kasa. “Da ace ko wane namiji zai zama kamar kai, da rayuwar mutane da yawa ta inganta, baki yayi kadan ya gode maka, ina fatar Allah ya tsare gabanka da bayanka ya shiga gaba a lamarinka ya zama gatanka ya haska lamurranka” “Ameen” Ya amsa yana mata wani irin kallo da shi kansa be san na minene ba, tun da yake a rayuwarsa ba a taba tsaya a gabansa a yabe shi kamar yadda Aminatu tai masa ba. “Allah ya tsare hanya” Ta fada tana jin babu dadi, dan zaman da tai da shi sai ta ji kamar ta saba da shi, ji take kamar kar ya tafi ya barta. A nan shi ma kasa amsawa yai sai ya bita da kallo har ta isa bakin kofar gidan ta shige ciki. “Oopss” Ya furta tare da busar da iskar bakinsa, sannan ya zauna baki dutsen. Ma'adanar lambobi ya shiga neman number Ali sai ga kiran Daddy ya shigo wayarsa. Da sallama ya amsa yana mikewa tsaye ya nufi gurin motarsa. “Ranka ya dade idan zaka kwana a can ai sai ka fada mana, da zaka tafi ma baka fada mana ba, kuma ka san yadda hanyoyin nan suke” Talba yayi murmushi yana shafa kansa. “Ayi hakuri Daddy, ni ma ban dauka zan kwana ba, sai dai ganin na dade ban zo ba yasa na ce bari na kwana saboda Kaka” “Hakan na da kyau amman a rika addu'a, Allah ya tsare, tana kusa da kai ka bata wayar mu gaisa?” Sai da ya kalli kofar gidan sannan ya amsawa Daddy. “Aa ina tunanin ta yi bachi” “To a gaishe ta pls” “Inshallah thank you” Ya sauke wayar, sai kuma ya sake maida ita kunnensa bayan ya aikawa Ali kira. “Hello” Ali ya daga sai ya ji muryar yaransa a kusa da shi, da alama yana gida tare da iyalansa. “Kana gida ne?” “Yes gwaro kana da magana ne?” “Yeah” “Okay Ina jinka” Ya fada yana tashi ya fita daga falon, sai da Talba ya daina jin hayaniyar yaran sannan ya biro masa da abun da ya faru tsakaninsa har zuwa abun da Kaka tai masa. Ba karamin mamaki Ali yai ba jin cewar Aminatu da Talba yan'uwan juna ne. “I'm happy for her yanzu ta huta da rabe rabe” “Seriously? Bayan kana ta hanani?” “No bana son kana samun matsala da Leila ne, kuma ya zama ni ne sanadi, ba zan jidadi ba, kuma duk wani abu da zai taba mutuncinka ya zubar da kimar ka bana sonsa ka sani” “Yanzu miye abun yi ina cikin matsala Wallahi” “Kana da wata mafitar data wuce ka amince ka auri yarinyar ne?” “Wasa dai kake, na yi yaya da mata biyu” “Can da kai yi niyar aurenta ya zaka yi da ita?” “Wannan ai dabam ne, daman zai aureta ne saboda gudun abun da zai je ya dawo, kuma ni ada niyata idan ta samu wanda take so zan rabu da ita ta aure shi, daga baya kuma tunanin kawota gurin kaka ya zo min ashe wani sabon fitina ce zata bullo min, kuma ka san ban isa na ce zan yi auren sirri na munafucin Kaka ba, idan na yi haka zai zama akwai zalinci a ciki” “Ka lallabata idan ta fahimta shikenan idan kuma bata fahimta ba, kawai a auri yarinyar nan Talba, tsakani da Allah kai kanka kana bukatar aure, kuma ga Leila bata shirya ba a yanzu, kuma kai da Leila kun kasa fahimtar juna, dazun ma ta zo nan tana bincikar gurin da ka kai yarinyar, abun nan fa ya dame ta, tana son ka kai da ita girman kai ya hana ku fahimta, amman yanzu na fi yarda kana son yarinyar nan fiye da Leila” “Ali baka da hankali, miya kawo maganar nan?” “Haba Talba ka damu da damuwarta, ka dauke ta ka kaita gidanku har ka yi fada da Leila a kanta, sannan ka kaita gidanka yanzu kuma ka kaita gurin kakarta domin kawai ka sama mata mafita, zaka iya yi ma Leila haka?” “Me zai hana indai har zata shiga a halin da yarinyar nan ta shiga?” “Bari na fada maka gaskiya Talba, idan ka auri yarinyar ba zan jidadi ba, saboda zaku samu matsala da Momy da kuma Leila, kara ma Daddy na san yana son abun da kake so, kuma yana da saukin fahimta zai maka uzuri. Abu na biyu wanda nake ganin shi ne mafita a gareka shi ne auren yarinyar nan, saboda ka farantawa Kaka rai, kuma ina da tabbacin yarinyar nan zata samu kulawa yadda ya kamata, saboda ka san halin da take ciki ba zaka yarda ta shiga wani hali ba, tsakani da Allah yarinyar nan ta shiga damuwa da yawa a yanzu farinciki kawai take bukata idan kasan zaka aurenta ta zo ta samu matsala karka yi” Talba ya sauke ajiyar zuciya. “Tsofun nan rigima ce da su Wallahi” “Wata kila kuma lokacin auren ne yai, ka san komai yana da lokaci, ni yanzu ai ba za shiga tsakaninka da yar'uwarka ba, duk dai bana son a shiga hakkin Leila, ka fara fahimtar da ita idan ta ki sai ka yi magana da Daddy ka ji abun da zai ce, idan ya amince shikenan idan kuma ya nuna akwai matsala sai mu sake neman wata mafitar” Talba ya sauke ajiyar zuciya. “Ban dauka abun nan zai zame min haka ba, and ni dai ba sonta nake ba, ita ma bana jin tana so na” “Karka damu da sai ta soka, kai ma kuma na san kana sonta, ka kai level din da ya kamata ace ka aje yaya Talba” “Let me talk to Daddy first” “Okay, Allah ya zaba maka abun da yafi alheri, kai ta addu'a” “Abu kamar a film” Ali yayi dariya. “Haka Allah yake ikonsa, kaga zak taimaki yarinyar ta samu rayuwa mai kyau” “Ko ban aureta ba, na mata alkawarin rayuwa mai kyau, zan yi duk abun da zan iya na ganin na faranta mata rai” “Yanzu dai zabi ya rage naka” Be sake cewa komai ba ya kashe wayar ya rumgume hannayensa yana tunanin kalaman da Ali yai masa. Ba zai ce yana son Aminatu ba, haka ma ba zai sheidi tsanarta a zuciyarsa ba, tausayinta ya bi jini da jikinsa ya tsaya masa a rai. And of course idan ya aureta ba zai cutar da ita ba, amman ya zata ji? Aurensa ma wani sabon kalubale ne a gurinta. “Kaka...” Ya furta yana runtse ido, cike da rashin samun mafita. AMINATU POV. Tana baro gurin sai ta tsaya a zauren gidan ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba, wata kila saboda Talba zai tafi gobe ya barta ne, gashi kuma Kaka tace idan ya tafi sai ya shekara yake dawowa. Dukewa tai a gurin ta dafa kasa tana ta kuka sai bakincikin ya dawo mata sabo. Sai da tai kukanta mai isarta sannan ta share hawayenta ta shiga cikin gidan, kanta a kasa tana ta boye fuska har ta shiga dakin Kaka. Tun daga yanayin sallamarta da tai da muryar kuka Kaka ta gane kuka tai. “Wa'alaikissalam Auta” Yanayin yadda Kaka ta kirata sai ta ji kamar Inna ce ta kirata, kallonta tai sannan ta karasa kusa da ita ta zauna. “Kin ci abinci?” “Bana son komai, Tsohuwa na kwanta a jikin dan Allah” “Kwanta auta” Kaka ta fada cike da tausayi, sai ta kwanta a gurin ta dora kanta a cinyar kaka ta lumshe ido kamar mai bachi. BATURIYA POV. “Wai yanzu can ba a bar masa Sultan?” Babban Yayansu ya tambaya, sai Umma tai karaf ta ce. “To me zamu yi masa? Daman idan aka saki mace ai uba ne yake rika yayansa, ni Wallahi bana son ma rika yayan Faruq” “Aa Umma kar a zafafa, dan'uwa ne fa, kuma abun da ya faru baki san mai gaskiya a tsakaninsu ba, tun da shi dai be fadi laifinta ba yace ki minene zamu gani, ita ce kawai ta fadi na shi” “Ita ma dai ai ba zata masa karya ba, bayan duk hakurin da tai da shi, ga talauci” “Allah ya sauwake, wannan ai na Allah ne, ba ku san arzikin da Allah zai masa ba nan gaba” Duk maganar da ake Baturiya bata saka bakinta ba, har sai wayarta tai ringing sannan ya mike tsaye tana fadin. “Ranar Monday zan je asibiti Umma” “Allah ya kaimu, idan an rubuto magani sai mu kai masa ya siya” “A kawo dai na siya” Ya fada yana kallon wayar dake hannunta, sai dai be ce komai ba har sai da ta shiga ciki. “Waya siya mata wannan wayar?” “Tace adashe tai” “Wanda ke fama da talauchi ina zai samu kudin yin adashe? Idan har zata samu yin adashe a gidansa to karya take masa kenan na cewa yana barinta da yunwa!” “Dan Allah ka daina ma wannan maganar, mace ai tana da hikima kuma talauchi ba ita kadai ta fada ba, jikinta ma ai ya nuna haka, ko zuwa yai gidan nan haka zai fita sisin kwabo ba zai ba ni ba, rabon da yai min alheri har na manta” Mikewa yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya. “Allah ya sauwake, ni zan tafi idan an rubuta maganin sai a aika min da takardar” “Toh Allah ya maka albarka, ya kara rufa asiri” Sai da ya amsa da amin sannan ya gyara babbar rigarsa ya fice daga falon yana yi ma Umma sallama. Mai da kofar dakin tai ta kulle sannan tai picking. “Yan mata...” A take ta ji gabanta ya fadi, domin muryar babban mutum ta ji ba saurayi ba, gashi bata san ta bawa wani number ta ba. “Wake magana?” “Nine dai da ake ta yi ma rowa bayan a lasa min zuma” Murmushi tai domin ta gane mai maganar. “Aa waya isa? Sai idan baka bukaci ganina ba” “Aa wacan karon ma ni kadai na san wahalar dana sha kamin na samu ki amince min, yanzu kuma kin fara guduna, Ramlee tace wani saurayi ne yake dauke miki hankali, shiyasa na ce ta turo min number ki na yi rokon iri, ko za a laba ni na sha miya” Ta yi wata shu'umar dariya. “Alhajina kenan, ko dai a laba wasu su sha miya ba, kai ai ka wuce nan” “Anya dai, gani sai bibiya nake, ko maganar zuwa chine da na miki, ba ki ce min komai ba, ko da yake haduwar ma ta yi wuya balle zuwa wata kasar” Ta sake yin dariya sai dai wannan karon bata ce komai ba. “Yanzu dai a fada min yaushe za a sake labani?” “Fitar ce tana min wuya yanzu, amman dai ranar Monday za mu hadu” “Zan iya jira har Monday? Na zaku fa” “Haka nan dai zaka yi hakuri har Allah a kai mu, sauran kwana hudu ai” “To ya na iya tun da abun ya zama na manya, ina saurarenki Gimbiyata” “To yayi Alhajina zan maka shiri na musamman kuwa” Dukansu dariya suka yi sannan ya kashe wayar, ita kuma ta zauna bakin gado tana nazari, kamin ta kai hannunta ta saka cikin riga ta fara shafa cikin tana jin tausayin cirewar da zata yi, wata zuciyar na raya mata karta aikata, a yayinda dayar take ayyana mata rashin mafita a al'amurranta matukar bata yarda da zubar da cikin ba. ‘Idan na zubar shikenan na gama idda, zan samu damar auren Fahat, amman kuma zai yarda ya aure ni as bazawara? Idan kuma na boye dole a gaskiya zata fito za a ji’ Haka dai take ta sake sakenta, ta kulla wannan ta kwance wacan. Sam zuciyarta bata kawo mata Sultan kusa balle har tai tunanin a wane hali yake ciki a yanzu, gaba daya ta shagaltu da soyayyar Fahat. “Wallahi da na san zan hadu da shi, da ban auri Faruq ba” Mikewa tai tsaye tana jin wani kalar bakinciki ina ma ace ita din budurwa ce ba bazawara ba, da yanzu burinta ya cika. 33 *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* A dakin Kaka Aminatu ta kwana, kaka na kan katifa ita kuma tana kan gado, asubar fari ta farka ita da kaka sukai sallah. Kaka na jan carbi ita kuma tana azakar din data manta when last ta yi saboda rashin kwanciyar hankali da natsuwa. Bayan ta gama ta daga hannayenta ta mikawa Allah bukatar ta kuka kai kukanta. “Tsohuwa ina kwana?” Sai Kaka ta amsa masa da murmushi a fuskarta. “Lafiya kalau Auta, an tashi lafiya?” “Alhamdulillah” “Maa Shaa Allah, fatar dai idan kika yi sallah kina yi ma iyayenki addu'a domin mamaci babu abun da yake bukata kamar addu'a” “Ina yi tsohuwa ina yi sosai” “Toh Allah yai miki albarka, ya baki miki na gari” “Amin ya rabb” Ta amsa tana yin kasa da kanta, ba laifi tana jin sakewa a gurin tsohuwa fiye da ko'ina wata kila saboda tana jininta ne ko kuma saboda ta santa ne, ko kuma dai dan bata da kyara ne amman Madina ma ai bata da kyara sai da bata jin sakewa a can, duk kuwa da kasancewar kwananta daya a nan. Misalin Bakwai na safe aka shigo da kunu da kosai. Kaka da kanta ta dauki karamin kofi ta zubawa Aminatu nata sannan ta dauko mata sugar dake cikin wani bowl mai murfi. “Ki saka wanda ya isheki, anjima zaka kawo dumame sai ki ci, idan kuma indomie kike so ko kwai akwai a dakin ajiya sai a dafa miki” “Aa wannan ma ya isa” Ta fada tana jin marmarin kunun a ranta, rabon da tasha kunu tun lokacin da tashin hankali ya fara samunsu, daman mutumen kauye ba ka raba shi da kunu ko fura ba. Sosai ta zuba surgan ta motsa da karamin ludayin da Kaka ta saka mata sannan taja kunun gabanta ta fara ci tana cin kosan. Kaka ta janyo radio ta kamo bbc sannan ta aje radio kusa da ita ta cigaba da jan carbin. “Assalamu Alaikum” Talba ya shigo da sallamarsa, sai Aminatu ta dago ta sauri ta kalleshi tana shan kunu, Kaka ma juyowa tai ta kalleshi sai ta dauke kai ba tare da ta amsa ba. “Wa'alaikassalam” Aminatu ta amsa masa, sai ya zauna kusa da ita can Center carpet din da take zaune yana sakar mata murmushi. Kallonsa kawai take cike da shauki tana jin kamar tace masa kar ya tafi, daman jiya da tunanin tafiyar ta kwana a ranta, kasa dauke mata ido yai har sai da ita ta kawar da nata idon tana sannan shi ma ya dauke nasa yana kallon Kaka zai mika mata gaisuwa a yayinda ita kuma ta dago zata mika masa nata gaisuwar. “Ina kwana” “Ina kwana” Sun fada a tare, shi yana kokarin gaishe da Kaka ita kuma tana mika masa nata gaisuwar, sai suka kalli juna ita da shi murmushi ya biyo baya, wanda ya karawa kowanensu kyau da haiba. “Lafiya Kalau an tashi lafiya?” “Alhamdulillah” Ta amsa sannan tai kasa da kanta, shi kuma ya juya ya saka gaishe da kaka, kamar dazun yanzun ma bata amsa masa ba sai ta daga masa alamar amsawa. Murmushi yai ya kalli kunun da Aminatu take sha. “Kaka ni ba za a bani kunun ba? Saboda ni ba dan gida ba ne ko kuma me?” Kaka ta yi kamar bata ji shi sai jan charbinta take. Aminatu ta mikawa Talba nata. “Ka sha wannan” Ya mika hannu ya karba ba dan yana son sha ba, kusan zai iya cewa be taba shan kunu ba a rayuwarsa idan ma ta taba to ya manta, tashinsa Momy ta saba masa da tea ba kunu. Babu kyama ya kai kofin bakinsa ya kurba, sai yai saurin runtse ido, ba dan dadi ko rashin dadin kunun ba, sugar da Aminatu ta zuba ne ya ji shi har cikin kansa, saboda be saba shan suga da yawa ba, wani lokacin ma ya kan iya jika Lipton kawai ya sha ba tare da suga ba, idan ma zai saka sugar baya wuce one or two to three cube. “Shalele haka kike shan zaki ko Kaka ce take son bata ki?” “Ni na zuba” Daukar kunun yai ya kara a cup din ya motsa sai zakin sugar ya ragu, sai dai hakan be hana shi jinsa har cikin kansa ba, haka dai ya daure yana shan kunun idan yayi ludayi daya sai ya mika mata ta sha daya a haka har suka shanye kunun. “Idan baki koshi ba ki kara ki cika cikinki, sai ki kwanta kamin a kawo dumame” Kaka ta fada tana janyo kwanon da take ajiyar goro ta bude ta balla kadan ta saka a baki tana taunawa. “Na koshi” Aminatu ta fada tana lashe baki. “Kaka ni ban koshi ba” Talba ya fada yana kallonta, sai tai masa banza kamar ma bata san da zamansa a gurin ba. Murmushi yai ya tashi ya kuma kusa da ita ya zauna ya kai hannunsa ya dafa ta. “Haba Uwargida kin taba ganin matar dake son aljanna kuma tana fushi da mijinta” “Kai Mu'azu babu wani abun da zaka min ka wanke kanka, kar nake kallonka, kuma ka gwada min yan'uwan ubanka sun fi na uwarka, ba zan manta da wannan ba, ka nuna wasu dangin sun fi wasu” Saurin dauke hannunsa yai yana jin wani irin, har ga Allah ba manufarsa kenan ba, amman kaka ta kasa fahimtarsa. Kallon Aminatu yai. “Shalele zaki iya zuwa waje? Zamu yi magana da Kaka” “Toh” Ta amsa tana kokarin tashi sai Kaka tai karaf ta ce. “Babu inda zata je, ni ce uwarta ni ce ubanta a yanzu, bata da wasu dangin sai ni, idan zaka yi maganar kai a gabanta ko kuma ka je can gurin naka dangin kai magana ai kai kana da gata” “Haba Kaka wannan wace irin magana ce kuma?” Ta furta cikin rashin jindadi, sannan ya mike tsaye ya ciro kudin dake aljihunsa ya aje masa a gabanta. “Gashi nan a ci goro ni zan kama hanya, kuma zan aiko mota a daukeki saboda ciwon kafafuwan a kai ki asibiti” “Ai daman idan ka zo garin nan kamar ana tsikararka kake, shiyasa kowa baka sani ba na dangin uwarka, idan ka zo baka san kaje ko'ina ba, idan kuma ka tafi sai an sake ganinka. Ka dauki kudinka sisin kabo bana so naka Mu'azu, ai baka gan ni a wahala ba, komai bana so naka, kuma karka sake takowa garin nan da sunan zuwa ganina na yafe maka har na mutu” Sai a yanzu ya tabbatar da gaske kaka take, domin babu alamar wasa a fuskarta sai ma fushin dake kara bayyana a maganarta. Kallon Aminatu yai wanda ita ma kallonsa take tana mamakin yadda Kaka take masa magana da fushi, be ce komai ba ya dauke kai ya fice daga dakin cikin rashin jindadi. “Auta dauki kudin nan ki kai masa” Kaka ta fada tana nuna mata kudi, kamar marar kuzari haka Aminatu ta isa gurin kudin ta dauka ta fito daga dakin tana jin kamar ta tambayi kaka dalilinta na kin karbar kudin. Ko da ta fito waje yana zaune cikin motarsa ya bar kofar a bude yana kallon kofar gidan kamar ya san zata fito, tafiya take kamar wata hawainiya har ta isa gurin motar ta ja ta tsaya, ya dade yana kallonta ita kuma ta kasa daga ido ta kalleshi saboda kukan dake son zuwa mata. “Shalele ya akai?” Ta mika masa kudin da hannu biyu. Sai yai murmushi. “Kin ga na kawo ki nan amman kin fini fada, saboda ke Kaka take fushi da ni” “Ko dai tana jin an dora mata lalura ne?” Ta tambaya hawaye na cika idonta. “Aa wani abun ne dabam” Ta hade yawun bakinta. “Zan koma Gusau” Bata ce masa komai ba, kuma ta kasa daga idon ta kalleshi. “Ba zaki ce min Allah ya tsare ba?” Ya furta yana kallon yadda yanayinta ya sauya, shi kansa yana jin kamar kar ya tafi ya barta. Sai a lokacin ta kalleshi hawaye a sauko mata. “Da gaske idan ka tafi sai bayan shekara zaka dawo?” Ido ya kura mata sannan ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta still yana kallonta. “Ba ki son na tafi?” Samun kanta tai da daga masa kai. “Kina son na dawo?” Nan ma kan ta daga masa. “Zan dawo” “Yaushe?” Ta tambaya cike da shauki da kuma zakuwar ta ji yace mata gobe ko jibi. “Yaushe?” Ta sake tambaya. “Ba da dadewa ba” “Yaushe?” Ya shafa kansa zuwa hancinsa. “Cikin satin nan” “Ya za'ayi na yarda zaka dawo” “Saboda nace zan dawo, idan na ce zan yi abu, zan yi” Ta dauki idonta hawaye na sauko mata sosai, sai take jin kamar shi ma din idan ya tafi ba zai dawo ba. Ya kara matsowa kusa da ita cike da tausayinta. “Kina son na zauna ne?” Ta daga masa kai sai ya saka hannunsa ya dago kafadarta. “Idan kina son na zauna sai idan zaki yarda ki zauna da ni zama na har abada” Ta masa kallon rashin fahimta, sai dai kuma ta kasa tambayarsa abun da yake nufi da haka. Ganin haka ya saka shi yin murmushi ya dauke hannunsa daga fuskarta ya dan ja baya kadan yana kallon harabar gidan. “Kina son zama da ni?” Ta sauke kanta k'asa ta kasa cewa komai. He just ask dan ya gane idan tana son zaman da shi ko akasin haka, domin Kaka tana kokarin hada aurensu ne kawai ba tare da lura da suna son junansu ba ko a'a, hadi ne kawai take son tai musu irin na kauye na zamanin baya. “To ni ina son zama dake, shiyasa nake son Kaka ta bani ke...” Sai kuma ya kasa karasawa yana ta kallon reaction dinta. “Na aureki...” Dagowa tai da sauri ta kalleshi gabanta ya buga da mugun karfi, zuciyarta tai wani uban zillo kamar zata fito daga kirjinta ta fado kasa. Bata san miyasa take jin kamar kalamansa sun mata nauyi ba, alhalin ba a yau ya fara furta mata wannan kalmar cewar zai aureta ba, wacan karon ya ce saboda kar su sabawa Allah ne, har yace idan ta samu wanda take so ko yan'uwanta zai sake yanzu fa? Bayan gashi tana tare da kaka. Ganin ta yi shiru bata ce komai ba ya saka shi zaunawa cikin motar. “Zan tafi” Sai ta sake mika masa kudin a karo na biyu. “Ki koma ki kai mata, idan bata karba ba ki dauka na baki” Yaja motar ya rufe yai reverse tana tsaye tana kallonsa hawaye na sauko mata, sai da ya juya motar sannan ya sauke gilashin motar ya leko da kansa ya kalleta ya sakar mata murmushi sannan yaja motar ya kama hanya. Tsaye take tana kallonsa tun tana hangensa har ta daina hangosa, sai ta durkushe a gurin ta fashe da kuka ta saka kanta cikin guiwar hannunta tana kuka sosai. Sai da ta soma jin motsin mutane na wucewa sannan ta tashi ta share hawayenta ta shiga cikin gidan kanta a kasa tana tafiya kamar dazun.   Ko da ta shiga Kaka bata cikin dakin, sai kawai ta hau gadon data kwana a jiya ta rumgume kudin a kirjinta, can kuma ta juya baya ta fara kuka a hankali tana jin zuciyarta na mata mugun zafi. TALBA POV. Be taba rabuwa da wani abu ya ji yana marmarinsa ba so soon kamar Aminatu, baronta da yai a can har ya fara jin kewarta. Murmushi yai tunawa da tambayar da tai masa cewar yaushe zai dawo. Wayarsa ya dauka ya kira Daddy, ringing daya ya daga. “Ranka ya dade yanzu nake kokarin kiranka” “Daddy barka da safiya” “An tashi lafiya fatar ka kamo hanya” “Gani a hanya Daddy, fatar Momy ta dawo” “Kun fara damuna da zancen Momy fa, ni ma zan yi yaji na tafi Abuja na yi zamana” Talba yayi murmushi cike da kaunar Daddy daman san shi da barkwanci. “Haba Daddy idan ba Momy ai ba rayuwa, dan Allah kace min ta dawo” “I think dai yau ko gobe zata dawo” “Gani tafe, zan rakaka ka dauko ta akwai maganar da nake son yi da ku mai muhimmanci kuma ina fatar zaku fahimta” “Allah ya kawo ka lafiya” “Ameen” Ya katse kiran, sannan ya kira Leila kamar yadda ya tsammata bata daga kiran ba, sai ya kira Amal ya gaisa da ita sannan ya kira Momy. “Talba” “Momy barka da safiya” “An tashi lafiya” “Lafiya kalau Alhamdulillah” “Ance ka baka kwana a gida ba, ina kaje?” “Waya fada miki?” “Amal” Yayi murmushi mai sauti. “Allah ya shirya Amal ba zata daina gulma ba, naje kauye ne” “Amman kasan hanyoyin nan ba su da kyau Talba” “Nan ai da sauki abun be kawo ba, kuma gani hanyar dawowa, ina fatar kin dawo Momy” Ta yi shiru. “Rashinki ne ya saka muka bar gidan nan, gaba daya gidan baya mana dadi, kuma ina jin babu dadi idan na tuna cewar saboda ni komai ya faru” “Zan dawo ai, kuma ba laifinka ba ne komai ya wuce” “Zan zo anjima na daukeki” “Aa sai next week” “Momy do this favor for me dan Allah...!!!” “Shikenan” Yayi murmushi. “Thank Youu Momy ashe kina so na” “Wannan wace irin magana ce Talba? Bana son ka nake zaune tare da kai? Na taba cutar da kai a tsawon zaman da na yi da kai? Ta ya uwa zata zauna da tun yana jariri har ya girma a hannunta kuma ta ce bata taba son dan nan ba, bayan kuma yaron nan be mata komai ba? Engineer ya riga ya dasa maka wani mugun ice na kiyayata a zuciyarka shiyasa har kake min wani kallo na dabam” “Ko kadan Momy, ban taba kallo wata mace a matsayin uwata ba sai ke, ban san wata uwa ba sai ke, kuma Daddy be shimfida min komai ba a zuciyata sai kaunarki, ke da shi kun kasa fahimtar juna ne kawai, kina ganin kamar ya zurfafa a so na, shi kuma yana ganin kamar baki so ni a yadda ya kamata ki so ni ba, kuma duka na fahimcinku, fatar za a yafe min” “Baka yi komai ba, Allah ya maka albarka” “Ameen” Ya amsa da murmushi sannan ya kashe wayar, ya cigaba da tukinsa yana tunanin yadda zai gabatar da Daddy da Momy maganar Kaka. Ko da goma tai har yayi wanka ya canja tufafi, be tarar da Daddy a gidan ba haka ma Amal tana makaranta Leila ce kawai a bangare sai Kabir dake karyawa a dinning. Kallo daya Kabir yai masa ya dauke ido domin a yanzu be da makiyi kamar Talba, Leila kuma ta kura masa ido ta kasa daukewa har ya karaso kusa da ita ya zauna, sai gabanta ya buga da karfi, duk yadda take son hana zuciyarta soyayyar Talba sai ta kasa musamman ma idan yana kusa da ita wani lokacin har jin take kamar ta rumgume shi, sai dai gudun zubar da class dinta ya saka bata nuna masa haka, dauke idonta tai tana ganin wani uban kyau daya kara kamar an shafa masa hoda. “Ya kike?” Ta mike tsaye sai ya kalleta. “Can we talk” Tsayawa tai sai dai bata juyo ta kalleshi ba, kuma bata ce masa komai ba. “Zauna mana” Ta koma ta zauna. “Akwai abun da kike so ne?” Ya tambaya feeling some how kamar he's out of words, haka yake a duk lokacin da yake tare da Leila, duk kalmar da zai kama yai magana ta fahimta da ita sai ya ji kamar ba zai iya ba, except ta fada masa baka magana ne ko kuma ta masa wani laifi, on that point kam ya san abun da zai fada mata. Mikewa tai tsaye ta nufi upstairs sai ya bita da kallo yana ta kokarin hada kalmomin da zai yi mata magana ta fahimta amman ya kasa har ta haye sama. Tashi yai ya nufi kofar fita Kabir ya bishi da wani banzan kallo har ya fice, bangarensa ya koma ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa. Ko da ya isa gate har sun bude masa. Yana fita ya fisge motar da karfi ya dauki hanyar da zata kai shi gurin da Daddy yake aiki. A harabar ma'aikatar ya faka motarsa ya fito ya nufi ciki da saurinsa yana kiran Daddy a waya. “Daddy gani shigowa zan muje mu dauko Momy yanzu” “Bana gida” “Yeah na sani office dinka nake nufi” “Bana office, ina gidan Hajiya Yana, na yi marmarin abincin Doctor ne shi ne na zo na yi breakfast, amman idan na gama zamu dawo gida yanzu” Talba ya tsaya cak yana mamakin yadda Daddy ya fishi hikima da wayo, wato a can ma ya karya a maimaikon ya jirashi su tafi tare, and yes yayi abun da ya dace, daman shi yana son saka Daddy a gaba ne saboda yana ganin kamar baya son dawowa da Momy ne. “Fine sai kun iso” Ya fada sannan ya juyo ya dawo yana murmushi ya nufo motarsa. A ranar be yi maganar da Daddy ba, duk da kasancewar Daddy ya tambaye shi amman sai ya dauko wani zancen, ba dan komai ba sai dan ganin a ranar Momy ta dawo be kamata yai maganar ba, washe gari ma be yi maganar ba, har sai da aka kwana uku da dawowar Momy a gidan. In all these three days yana kiran Kaka a waya idan ta daga ta ji muryarsa sai ta kashe, last kiran da yai mata ma ya bukaci ta bawa Aminatu wayar amman bata ko tsaya saurarensa ba ta kashe wayar.   Sai da Amal ta tafi makaranta Kabir ma ya fita Leila kuma ta koma dakinta, sannan ya kalli Momy ya ce. “Momy ina son magana da ke da Daddy,  ko zamu iya zuwa can?” Momy ta kalleshi daman tun da suka zauna karin kumallon ta lura da babu abun da ya ci sai kofin tea yake ta juyawa. “Miya faru?” “Magana ce mai muhimmanci kuma ina son na yi ta ne tare da ke da Daddy” “Okay gani zuwa” Sai ya dauki tea din ya mike tsaye ya nufi kofar fita, Ta kofar gaba ya shiga bangaren Daddy a babban falonsa ya zauna yana shan tea a hankali. Sai ga Momy ta shigo ta kofar ciki, “Baka shiga ciki ba?” “I think yana karyawa” “Let me talk to him” Ta nufi hanyar karanin falon, sannan ta wuce bedroom dinsa. After like thirty minutes Daddy ya fito Momy tana bayansa, a karamin falo ya zauna sai Momy ta kira Talba. “Talba...” “Na'am” Ya amsa sannan ya tashi ya nufi falon, a kasa ya zauna Momy kuma na zaune kusa da Daddy, dukansu sun tattara hankalinsu guri daya suna kallonsa musamman ma Daddy da ya fahimci akwai damuwa a tattare da dansa. “Kana da wata matsala ne? Na ga ko breakfast ba ka yi ba” Momy ta fada, sai Daddy ya cire gilashin idonsa. “Mu'az akwai wata damuwa ne?” Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya ce. “Matsala ce kuma ba matsala ba” “Wani abun ne?” Momy ta sake tambaya. Sai Talba ya fere musu daga buri har wutsiya akan kudirin Kaka da kuma irin yadda ta dauki fushi da shi. Ba abun da kaka tai ne ya bawa Momy mamaki ba kamar jun cewar Aminatu yar'uwarsa ce, Daddy ya yunkuro yana kallonsa shi ma da mamaki. “Wato baka rabu da yarinyar nan ba Talba? Har da daukarta ka kaita gurin Hajiya, da ba yar'uwarta ba ce acan zaka aje ta kenan?” Cewar Momy cikin wani irin bakinciki na jin abun da Talba ya fada, sai Daddy ya daga mata hannu domin shi ba wannan ne damuwarsa ba. “Taimako ai abu ne mai kyau, babu laifi a abun da Mu'az yai, ki tattara wannan abun ki aje gefe daya, ki bari mu ji da damuwarsa. Kai kana son yarinyar” Daddy ya karasa yana kallonsa with serious face. Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce. “I don't know yet” “That's mean baka son ta, and no one can forced you shikenan” Daddy ya karasa masa domin yasan waye Talba idan yana son abu zai fito kai tsaye ne ya ce yana so, haka ma ida baya so zai fadi cewar baya so. “Ya ma za'ayi ya so ta? Yarinyar ai bata dace da shi ba, imagine an yi raped dinta kasan iya mutanen da sukai mata wannan aika aikan? And waya sani ko tana dauke da wata cutar, lastly Talba ba mutum ne mai son hayaniya ba bana tunanin zai iya zama da mata biyu” “Wannan ba matsala ba ce, da ace yana sonta za a iya bincikar lafiyarta kuma i will support him ya aureta, amman tun da baya son ta ba zai aureta ba” Daddy ya fada, gaba daya sai jikin Talba ya mutu kalaman bakinsa suka kare, domin ya san duk juyin duniyar nan da za'ayi Daddy ba zai yarda ya aureta tun da har be nuna cewar yana sonta ba, and yes shi kansa be san yana sonta ba, all what he know is yana tausayinta. “Amman... Kaka...” Talba be karasa ba Daddy ya tari numfashinsa. “Zan kirata zan yi magana da ita a waya, zan fahimtar da ita, yaushe rabon duniya da ayaraye, ai an daina wannan abu a wannan zamani, ko da ma ana yi ni ba zan bari ayi maka ba” Daddy na kawai nan ya mike tsaye ya nufi bedroom dinsa, daga Talba har Momy binsa sukai da kallo sai da ya shige sannan Talba ya mike tsaye da zimmar tafiya sai Momy ta dakatar da shi ta hanyar tsayar kiran sunansa. “Talba” Mikewa tai tsaye ta karasawa gurinsa tana kallonsa fuska a hade. “Karka kuskura ka bari Leila ta ji wannan maganar, domin akan 'ya'yana, bana da mutunci, bana da ragowa, bana son abun da zai daga musu hankali, idan ma ka fara son yarinyar nan ka bullo da maganar ta wannan hanyar to ka cireta a ranka tun wuri, kana gani ai, ni kadai nake a gidan mijina, haka ma yayana zasu zauna har karshen rayuwarsu, ko da wasa kar ka yi kuskuren hada soyayyar Leila da ta wata macen ko da ba wannan ba, balle kuma wannan kazamar da bandits suka gama wulakantawa, yarinyar da ingiyar aurena ta rabu saboda ita” Kallonta kawai yake da mamaki, kamar ba ita ce ta gama fada masa cewar tana kaunarsa ba, and yanzu ya gane halin Momy tana sonsa but when it's comes to her children bata saurarawa kowa. She got lucky ita ce ta fada masa haka b Leila ba, da Leila ce zai iya fada mata bakar maganar da har ta mutu ba zata taba iya mantawa da ita ba, but Momy ce ya zai yi bayan ya saka mata ido. Har ta yi gaba sai kuma ta dawo ta sake kallonsa. “And for the very last time karka sake shiga safgar yarinyar nan” “Yar'uwata a yanzu, ko a da na taimake ta balle a yanzu da bata da kowa sai ni sai Kaka” “I don't care, rayuwar kowa bata dame ni ba, ka haka rame ka binne maganar nan a inda aka yi ta, idan ba haka ba zan baka mugun mamaki Talba domin ba zan yarda a taba kimar yata ba...!!!” A falon ta bar shi tsaye ta nufi babban falo cikin fushi ta karasa kofar fita falon wanda zata sadata da bangarenta, shi kam binta yai da kallo har ta shige ta turo kofar sannan ya fito babban falon ya zauna yana tunanin yadda zai fuskanci Kaka, anya zata fahimta kuwa? Idan ta fahimta falillahil hamdu, daman haka yake so, sai ya cigaba da daukar dawainiyar Aminatu, sai dai idan kuma bata fahimta ba fa? Ya zai yi? Ya shafa kansa yana sauke ajiyar zuciya. Ya kusan awa daya a zaune, sannan ya tashi ya nufi bangarensa yana amsa wayar Ali, a tsanake ya labarta masa komai sannan ya nufi gadonsa ya kwanta ba dan yana jin bachi ba, sai dan ya rasa abun yi. Yana rufe ido wayarsa tai ringing sai ya kai hannu ya dauka ba tare daya bude idon ba, power button ya danna sai yai picking call din ya kara kunnensa. “Na cilasta maka aurenta ne da zaka turo ubanta ya rufe ni da fada, yana kokarin nuna min cewar ina son yi maka auren dole ne? Lallai Mu'azu ka nuna min ban isa da kai ba, kuma yanzu na gane dalilinka na watsar da mu da kake, saboda mu talakawa ne ko? Toh na shata layi daga yau kowa ya tsaya matsayinsa, yarinyar da kake kyama har ubanka yana fada min akwai banbanci tsakaninka da ita gata can ana mata karin ruwa, idan ta mutu aikowa ya huta” Sai a lokacin ya bude idonsa ya tashi zaune da sauri. “Bata da lafiya ne Kaka? Zata iya magana?” “Ban sani ba, na dai fada maka kar kaka sake turo min ubanka ya dame ni da wata maganar banza, idan abun da yake ganin yana bani ne yana daukar nauyina ban cilasta shi ba, kuma ba a yunwa ya gan ni ba” “Kaka dan Allah ki kwantar da hankalinki, daman na yi magana da Daddy ne saboda ya fahimtar da ke, ban yi tsammanin abun zai kai ga haka ba, na yi alkawari zan aureta” “Ba zan aura mata miji irinka ba, kaje can ka auri yar masu arziki, ai daman kishi yake taya yarsa, har yana nuna min cewar kuna da banbanci” “Zan shigo garin Maradu yau ko gobe kuma Wallahi sai kin aura min ita” Yana fadar haka ya ji ta mikawa wani wayar tana fadin. “Karbi kashe min, waya sani ma ko zagina zai yi yanzu kuma, bayan ubansa ya gama nasa” Dit... Ya ji ankashe wayar, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin da zimmar zuwa bangaren Daddy, sai ya same shi waje direbansa ya bude masa mota yana kokarin shiga. Sai dai hangoshi da Daddy yai ya saka ya dan jinkintar yana jiransa. Ya karaso gaban Daddy a natse. “Daddy aka yi magana da Kaka ne? Ta kira ni tana ta masifa” “Na yi magana da ita, ina kokarin fahimtar da ita ta kasa fahimta, sai maganar take saboda anga ita talaka ce shiyasa nake mata haka, kuma wai ina taya yata kishi for god sake ya za'ayi na taya Leila kishi ni ba mace ba? Ba wai bana goyon bayan auren nan ba ne saboda Leila, Wallahi bana goyon bayan auren nan ne saboda baka so” “Amman Daddy idan yin zai zama mafita why not...” “No baka so ba za'ayi ba, that's it” “Idan kuma ina so fa...” “No baka saba yi min karya ba, ni kuma ban saba canja kalamaina ba, ba zan yarda kai abun da baka so ba, kuma ba zan bari ka yi abun da zaka zo kana nadamarsa ba, ba za'ayi auren ba karka sake yi min maganar nan” Daddy na kaiwa nan ya shige motarsa, Direban ya zagayo ya rufe matsa sannan ya koma ya shiga driver side ya ja motar. Sai da Daddy ya fice daga gate din gaba daya sannan Talba ya koma bangarensa ya canja tufafin jikinsa ya dauki wallet dinsa da keys ya fito da sauri ya shiga motarsa sai da yai reverse sannan ya hango Momy dake tsaye a backyard tana kallonsa fuska a hade, dauke kai yai yaja motar yana danna horn da karfi kamar mai tsere. Sai da yai nisa da unguwar sannan ya kira Ali ya fada masa abun da ya faru. “Yanzu miye abun yi?” “Oho ni yanzu hankalina ma ya koma can gaba daya, saboda Kaka tace min gata nan ana mata karin ruwa waya sani ma ko wanda ke mata karin ruwan be wani kware ba, kuma wata kila ba a bincika ciwonta ba” “If ka damu da ita da lafiyarta Talba, be kamata ka nunawa Daddy baka son aurenta ba, kasan Daddy ya fika son abun da kake so, kuma yafi ka tsanar abun da kake ki, yanzu ya zaka yi kenan?” Talba yayi jimmm sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Aurenta zan yi, ba zan yarda zumuncin dake tsakanina da Kaka ya lalace ba akan abun da ina da iko da shi ba, kuma ba zan yarda Daddy ya samu matsala da Kaka ba” “Then ya zaka yi convinced din Daddy ya yarda ka aurenta? Kasan ba zai taba yarda ba, aje maganar Daddy a gefe ma, ya zaka yi da Momy da Leila?” “AUREN SIRRI no one would know, har sai komai ya daidaita, and i think Aminatu deserved a better life zan dawo da ita gidan nan” Ali yayi saurin mikewa tsaye daga zaunen da yake yana girgiza kai. “No karka yi haka Talba, zaka cutar da kanka kuma yarinyar zata cutu” “Sai dai ni na cutar da kaina, amman ba zan bari a cutar da Aminatu ba, kuma ba zan cutar da ita ba” “Maimakon haka, ai kara ka samo wani dabam ka aura masa Aminatu a matsayinta, saboda ba lallai ne ma idan a aureta ka iya zaman aure da ita yadda ya kamata ba” Talba yayi murmushi yana tuna kalaman Momy na dazun. “Saboda me? Saboda wasu mazan sun wulakantata? Ali bari na tambaye ka, idan kanwarka zaka so wani aureta? Ita ta kaddarowa kanta wannan abun ya faru da ita? Miyasa ake kyara mutanen da irin wannan kaddarar ta fada musu? Wallahi wannan abun ya fara min tausayinta kuma ya karfafa min guiwar aurenta, saboda ta cancanci zama da namiji irina, bayan ni a yanzu ban san wanda zai aureta ya zauna da ita da zuciya daya ba, and ba zan iya yaudarar Kaka tana kallon ni na aureta sai kuma na saka wani yayi? Ita kanta Aminatu ba zata ji dadi ba, and idan hawayen yarinyar ya zuba saboda ni ba zan taba yafewa kaina ba” Ali yayi murmushi. “Na taba fada maka lokaci zai da idonka zai rufe ka taka kaya ka jita kamar lad'a, kana son yarinyar nan believe me, zaka iya yaudarar Daddy da Momy da Leila amman ba zaka iya yaudararta ba, and you are telling me idan hawayenta ya zuba saboda kai ba zaka yafewa kanka ba... This is Love Talba, Welcome To the club” Talba ya natsu yana nazarin abun da ya fadawa Ali, did he say something wrong? No gaskiya ya fada masa ai abun da ke ransa. A hankali ya sauke wayar ya cigaba da tukin yana tunanin halin da Aminatu take ciki. LEILA POV. Tana fitowa daga dakin ta shiga dakin Momy, bata same ta a ciki ba, sai ta sauko kasa ta shiga kitchen nan ma bata ciki. “Ke Mairo ina Momy” Ta tambaya tana wani yatsinar fuska kamar wanda tai arba da kashi. “Tana sama” Mairo ta amsa mata ba tare da ta kalleta ba. “Wai Mairo har wani ji kike da kanki a gidan nan, Wallahi idan baki yi hankali ba sai na karya ki, ba ki san halina ba ne” Kallonta kawai Mairo ta yi ta dauke kai ta cigaba da abun da take, ita kuma ta juyo ta fito daga Kitchen, kai tsaye ta nufi upstairs kamin ta karasa Momy ta sauko rike da atamfa. “Momy ina kika shiga ban ganki ba” “Ina backyard” “Gurin me?” Leila ta tambaya da mamaki domin ba kasafai take shiga can ba. “Gurin kallon Talba, ashe har yanzu yarinyar nan tana ransa?” “Me yace ne?” “Ba komai kawai na lura da yanayinsa ne” “Yauwa Momy daman ina son na yi miki magana akanta, ki bincikar mana shi inda ya kaita dan Allah ko ma ki saka ya dawo da ita gidan nan if possible” “Saboda me?” “Madina ta ba ni shawarar mu samu wani mu biya shi ya aureta, kin ga ai mun huta, to na yi da bugun cikin Ali be fada min komai ba, sai ma ya nuna min kamar be san inda Talba ya kai yarinyar ba” Momy ta yi shiru tana nazari. “Indai haka ne, Madina ta kawo shawara mai kyau, amman akwai wani sirri da baki sani ba” “Minene?” “Wannan yarinyar da kakanta da kakar Talba yaya da kane ne” Leila ta gwalo ido waje tana bude baki cike da mugun mamaki. “What'? That's mean cousin dinsa ce kenan? How how Momy how? No ba gaskiya ba ne kina min wasa ne” A take idonta ya cika da hawaye jikinta ya fara rawa, sai Momy ta rika hannun ta koma sama da ita. “Shiiiiiiiiiii zo nan ki ji” Momy taja hannunta har cikin dakinta, hawaye kam sai sallama yake yi ma idanuwan Leila tana amsa masa da gaggawa. 34 *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660* AMINATU POV. Tana jin muryar Talba sai ta bude ido da sauri, domin tabbatarwa idan kunnuwanta daidai suka jiyo mata, tsaye ta ganshi a kanta yana ta kallon kyakkyawar fuskarta cikin damuwa. A take ta zabura ta tashi zaune. “Ina wuni” Sai ya zauna kusa da ita yana kallonta cike da kulawa. “Ya jikin?” “Alhamdulillah” Ta fada tana jin kamar an yaye mata ciwon an aje gefe daya. Hannunsa ya kai ya taba wuyanta sai ya ji shi da dan sauran zafi. A nan ya kalli Kaka. “Wane irin magani aka bata?” “Wanda ka kawo mata” Kaka ta fada masa tana wani tsuke baki, ta dauke kai kamar wata yar yarinya wai ita ala dole fushi take da shi. “Haba Kaka” Sai kuma ya kalli Aminatu. “Shalele wani irin magani aka baki?” “Mai dacin nan na malaria da na ciwon kai, sai kuma ya saka min ruwa, kuma ta min allura” Ta fada a shagwabe idonta na cika da kwalla ji take kamar ta fashe masa da kuka tunawa da zafin allurar da akai mata gashi kullum yake mata safe da yamma. “Kin gani ko? Ba ma wani kwararen ba ne, taya zaka baka maganin malaria da allura a lokaci daya, kuma ba a tsaya an auna mutum ba? Maybe ma hawan jini ne tun...” Kamin ya karasa Kaka ta daka matsa tsawa. “Can can ga kanka, sai dai idan kai ka shafa mata hawan jinin, dan dai ina da shi ne shine kake son murdowa ta nan kace ni na saka mata? Daman tun da ka tafi take ciwo tana kuka na kira dan Asabe ya dubata yace malaria ce” “Ba a auna mutun ba za a gano ciwonsa? Ni ban ce kin laka mata ba, daman ya za'ai wani ya saka ma wani hawan jini?” “Wai idan ma manufar ka kenan ai na san ba so na kake ba” Da gaske take maganar, a kokarin juya maganar zuwa wasa yai dariya ya amsa mata da. “Me zan yi da tsohuwa ga sabon jini na samu” Ya fada yana kallon Aminatu. Kaka ma kallonsa take. “Ko Shalele?” Aminatu ta yi kasa da kanta gabanta n bugawa da karfi. Sai yai murmushi “Kin ci abinci?” “Bata ci abincin ba ai gidan yan yunwa ka kawo ta ko?” Kaka ta amsa masa a fusace. Be kula ta ba ya cigaba da kallon Aminatu. “Bari na fita na bincika idan akwai inda ake siyar da abinci mai kyau sai na siyo miki, hankalina ya dauku shiyasa ban tsaya a hanya na siyo miki komai ba” Magana yake mata a hankali kamar mai kokarin fahimtar da ita. Sai ta daga masa kai a hankali tana kai hannu ta share kwalla da suka tarar mata. “Good Girl” Ya mike tsaye sai ta bishi da kallo har ya fice, Kaka kuma ta bita da kallo mamaki zuciyarta na raya mata wani abun. “Ke Auta...” Aminatu ta kalli Kaka da sauri, sai Kaka ta matsa kusa da gadon da take zaune. “Fada min lokacin da kuna can, yana miki wani abu?” Aminatu ta yi shiru domin bata fahimci inda Kaka ta dosa ba. “Yana tabaki ko ya rike hannunki ko ya dan shafa ki” Aminatu ta yi shiru tana tunanin irin amsar da zata bawa Kaka. “Karki ji tsoro ko kunya, kin ganshi nan jikana ne, duk yafi soyuwa a raina amman wacan kanen uban nasa da tsinanniyar matarsa da bata nuna masa son yan'uwan uwarsa ba, sun canja shi sun maida shi wani kala, ba san manufarsa a yanzu, na lura sai son shige miki yake kuma bayan ya nuna min shi ba zai aureki ba, har yana wani kiranki Shalele, wannan sunan yan iska ne, karki yarda ya sake ce miki haka kinji ko?” Aminatu ta daga mata kai, alamar eh sannan tai kasa da kanta tana tauna maganar Kaka ba cewar yace ba zai aureta ba, wa yai masa tayin auren tun farko? Amman miyasa zai aurenta bayan ita da shi akwai banbanci da tazara mai girma? ‘A'uzubillahi’ Ta fada a ranta tare da lumshe ido tana jin kamar ta yi banban sabo saboda zuciyarta na kusanto mata da aurenta da mutumen da ko a mafarki yafi karfinta. Taya mutum mai daraja da tarin dukiya da kyau da iyali kamar Talba zai yarda ya hada jini da irinta? Amman miye manufarsa ta yi mata furucin da yai mata a lokacin da zai tafi? Ta daga idonta ta kalli Kaka. “Tsohuwa ke kika ce masa ya aure?” “Eh, saboda ki samu rayuwa mai kyau, kuma kin ga dan'uwanki ne zai rike ki da amana, sannan ni bana son yarinyar can da zai aura, uwarta sau biyu kawai ta taba zuwa garin nan, ita yarinyar ma ban santa ba, amman suka zaba masa ita saboda sun ga yana da dukiya, sai juya shi suke kamar waina, ni bana son ya aureta ma, kara ya auri yar'uwarsa idan ma a nan zai aje ki ai kin ga dole ya rika zuwa yana duba ki mu ma muna ganinsa, kuma sai na nunawa wannan bakar matar ni ma na isa da shi, amman sai ya juya min baya harbda turo wannan uban nasa a waya yana fada min kabli da ba-adi da shika shikan kin aurenki” “Yana da wanda zai aura Kaka, kuma ba ki ga zubinsa ba? Akwai banbanci rayuwata da dasa, ni fa a kauye na tashi, sannan na rasa abubuwa da yawa da be zama lallai ma wani namijin ya so ni ba, balle kuma shi” “Ai ba wannan za a duba ba, hadin gida da zumunci ba ruwansa da wannan dan haka ki daina ma duba wannan” Kaka ta karasa tana mikewa tsaye ta gyara daurin zanenta. “Bari na yi fitsari” Aminatu ta yi kasa da kanta idonta na cika da hawaye. Kaka na shiga bandakin Talba yai sallama ya shigo, Aminatu ta kasa amsawa kuma ta kasa dago kai ta kalleshi, har ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa ya dago kansa sai yai arba da hawayenta. “Kaka ta miki wani abu?” Ta girgiza masa kai alamar no. “Toh miya faru ko kina jin ciwon ne?” Wannan karon ta samu damar amsawa. “Aa” Sai ya saka hannunss biyu ya share mata hawayenta. “Idan ina kusa da ke, hawaye basa da muhallin a fuskarki, ki daina kuka kin ji Shalele?” “Ka daina ce min haka dan Allah” Ya daga kansa sama yayi murmushi ya sauke. “Idan Kaka ta zo ki fada mata ba zan daina ba” Ya fada domin ya san ita ta kitsa mata wannan maganar, domin bata taba masa korafin kiran da yake da Shalele ba sai a yau. “Na bawa wani ya siyo miki abinci mai kyau, yanzu fada min Kaka ta miki gulma ta?” Ta yi shiru kanta a kasa. “Kaka tana fushi da ni, saboda na ce ta aura min ke taki” “Aa ba sai ka boye min ba, ni bana son aure a yanzu kuma na san akwai banbanci a tsakanina da kai...” Bata karasa ba ya kai hannunsa ya rufe mata baki. “Wallahi ban taba ganin wannan banbanci ba, kawai abun da nake tunani yadda zamu fuskanci juna ni da ke, kuma yanzu wannan zuwan da na yi ba zan tafi ba sai da igiyar aurenki” Ta sakar masa ido sai kuma ta matsa baya kamar mai tsoronsa. “Kana da wanda zaka aura, Yallabai ka rufa min asiri bana son na sake shiga wata matsalar idan ma Kaka tana fushi da kai ne saboda ka ce ba zaka aure ni ba, na fahimta” Yayi Murmushi ya kalli wani gefen sannan ya sake kallonta. “Yan mata, idan ma kin yi karya zuciya bata iya karya ba, na riga na karance ki kina kokarin hana zuciyarki abun da take so ne, a miyasa kika rika tambayar yaushe zan dawo a lokacin da zan tafi?” “Saboda na sabu da kai ne kawai na kwana biyu” “Miyasa a lokacin dana tafi kika kwanta ciwo sai a yanzu dana dawo kika samu lafiya?” Ta yi shiru. “Kin san saboda me?” Ta girgiza kai. “Saboda na tafi da zuciyarki, a yanzu kuma da na dawo na dawo miki da ita, karki yarda zuciyarki ta raya miki banbanci tsakaninki da wata ko wani, karki yarda ki sake nisa da mutanen da suke da muhimmanci a rayuwarki, domin zuciyarki ba zata iya daukar wani ciwon ba” Har lokacin kanta a kasa yake tana hawaye, shi kuma yana kallonta yana jin kamar ace yana da permission din rumgumarta ya rarrasheta. Kamar daga sama suka ji muryar kaka tana jan tsaki. “Maye ne kai da ka tafi da zuciyata, ka ji wata maganar banza idan son ta kake da gaske ai aurenta zaka yi” Runtse ido Talba yai ya bude ya kalli Kaka da be san tana cikin bandakin ba har sai da ta fito. “Kaka labe kike mana ne?” “Ina ce dai Dakina ne? Kuma ina jinka dazun kana min karya wai na hana ka Auta, ai ban mutu ba da rai na” “Dakinki ne, amman ni ma ina da hakki da shi ko? Kuma ai ban fadi karya ba na fada miki a waya zan zo kika ce ba zaki ba ni ba, kin dauka wasa nake? Wallahi Kaka ba zan bar garin nan ba sai na auri Aminatu” A take Kaka ta washe hakora, gaban Aminatu kuma yai dukan uku uku. “Aa dan Allah dan Annabi Aa” Aminatu ta fada cikin kuka, sai Kaka ta watsa mata harara. “Ke Wallahi baki isa ba ke ma, idan ba haka ba ni da ke ne, wannan abun farinciki da jindadi haka zaki ce wani aa, Mu'azu da gaske kake yi?” “Wallahi da gaske nake yi kaka, amman dan Allah karki cilasta mata ki barni zan yi magana da ita” “Mu can da aka mana aure, zabi aka bamu ne? Ko mazan ma ba mu sani ba sai da aka daura auren, karka biye shashancinta yarinya ce karama bata da wayo” Talba yayi murmushi yana kallon Aminatu dake hawaye. Kamin ya kalli kofar shigowa dakin Kaka na amsa sallamar Aminu baki har kunnen. “Aminu” “Na'am Tsohuwa ya jikin?” “Aa ni ai na warke, abun farinciki ya samu kuma ai” Har Aminu yayi kamar ya tambaya minene domin ya lura Kaka tana son labarta masa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai ya karasa gaban Talba ya aje masa kular abinci da ledar lemu ya mika masa canji. “No ka rike carjin” “To na gode Allah ya kara sutura” Aminu na fita Kaka ta bi bayansa domin labarta masa, abun da ya kasa boyuwa a ruhinta. Sai da suka fice sannan Talba ya kai hannu ya bude cooler kamshin ferfesun kayan ciki ya daki hancin Aminatu. “Sauko ki ci” “Aa” Ta fada da muryar kuka, domin kukan ne ya zo mata da gasken gaske. Kallonta yai. “Shalele? Kar dai ki ce min baki son auren nan?” Ta daga masa kai. “No please, kar mu yi haka da ke, ba wai zan aureki saboda Kaka ne kawai ba, zan aureki ne saboda na faranta miki rai, ina tunanin zaki so abun da zai faranta min rai kuma ya shirya tsakanina da yan'uwana, idan har ban aureki ba ina cikin matsala ba yar karama ba...” From a to z ya zayyana mata komai ciki har da kudirinsa na boye auren na su na wani lokaci. A nan ne hankalinta ya kara tashi. “Ina jin tsoron abun da rayuwa zata samar min a gaba, komai nawa ya banbanta dana kowa, rayuwata ta zama ba tawa ba, duhu ne ya fara bayyana a ciki, sai iska ya mamaye komai, kamin na ankara taurarin ciki sun tarwatse! Hakan ne silar rushewar duniyata... Talba ba ni da gata, ni fa yar gudun hijira ce kawai...! Ina jin tsoro abun da zai faru” Ta share hawayenta. Yayi saurin kama hannayenta, a cikin yanayin da ke nuna tsantsan tausayinta, fararen idanuwansa masu kamar madara suka rine da ja tsabar bacin rai da bakinciki. “Ashe ba ina kusa da ke ba? Ki daina tunani wannan tunanin Shalele da yarda Allah sai na mai da ke yar lele” “Taya? Kana da wanda zaka aura, kana da rayuwarka da mafarkinka, miyasa zaka rusa komai? Baka tsoron halin da zan shiga? Abun da iyaye basa so akwai hadari a yinsa” “Ki daina damuwa da iyayena ko Leila, ni mijin mace hudu ne, ba san ba zaki yarda alakar dake tsakanina da Kaka ta lalace ba akan abun da zaka iya yi min, zan sama miki wata rayuwar mai kyau mai inganci, zamu gina wata duniyar mai ciki da daula da jindadi mai cike da zuri'a” Ta fisge hannayenta hawaye na ta zirya a fuskarta, mikewa tai tsaye tana masa kallon tsoro. “Ta ya kake tunanin rayuwa zata zama mai sauki a gareni? Ya kake tunanin Leila zata ji idan ta san ka aure ni? Miyasa kake tunanin samun wasu Family a gareni mai sauki ne? Bayan na rasa kowa? Taya mace irina wanda ta rasa komai na kima da mutuncin mace farinciki zai rabeta, ta ya Yallabai...!” Mikewa yai tsaye yana kallon cikin idonta. “Kar bakinki ya sake furta irin kalamin nan, ina gargade ki a kan furucin... Ina son na roki ki wannan alfarmar Aminatu, dan Allah ki yarda ki aureni ba dan saboda kanki ba ko Kaka, saboda ni” Ta runtse ido hawaye na sauko mata, a take ta ji zazzabin ya dawo mata sabo. “Na san akwai wahala amman ki daure dan Allah” Ta bude idon ta kalleshi sai kuma ta sake rufewa sakamakon jirin data ji yana dibanta. “Ina son zan kwanta” Ta fara lalaben gadon tana kokarin kwantawa idonta a rufe. “Wannan maganar zata zama a tsakaninmu, bana son Kaka ta san cewa a boye zamu yi wannan aure” Nan ma bata ce masa komai ba har ta zauna. “Ki ci abinci sannan ki kwanta” “Bana jin yunwa” “Ba zan cilastaki ba, bana son na saka ki a cikin abun da zai haifar miki da damuwa, zan yi magana da Kaka” Bata ce masa komai ba har ya fice daga dakin. Ta inda yake jiyo muryar Kaka ya nufi sai ya tsaya daga bakin kofar dakin yana sallama. “Shigo Mana Mu'azu” Kaka ta fada da far'arta, sai ya cire talkamin kafarsa ya shiga dakin ya zauna kusa da Kaka yana kallon matar kawon nasa dake da far'ar da alama ita ma abun ya mata dadi. “Mu'azu yanzu nake jin abun alheri Allah ya tabbatar ya sanya alheri” “Amin na gode” Kaka ta kalleshi tana fadin. “Salamatu ce ta zo da wata magana wai idan Alhaji ya ji zai iya hanawa, ko kuma ya cilasta sai ka sake ta” “Kaka kar wannan na dame ki, da saninsa na zo nan, kawai dai yace babu ruwansa saboda na dage sai na yi auren, shiyasa nake son kamin ya canja shawara a daura mana aure da ita inya so idan tarewa ne sai a barshi har sai komai ya kamalla” “Amman Mu'azu hakan ba zai haifar muku da matsala ba? Baka ganin hakan zai iya sakawa su can su tsane ta?” Cewar Salamatu tana kallonsa. “Idan ma sun tsane ta, ni dai ina son ta kuma ba zan tana yarda a cutar da ita ba ko kuma ni da kaina na cutar da ita, a kokarin sama mata wasu iyalin na kawo ta nan, a can ma abubuwa da yawa marasa dadi sun faru saboda ni da ita, ina tunanin ko da a mafarki aka ce muku zan cutar da ita ko kuma na yarda a cutar da ita ba zaku yarda” “Wallahi ko kadan, ban kawowa raina Cewar zaka cutar da ita ba, ai babu wanda ya dace ta aura sama da kai, kai da kasan komai nata kuma kake tausayinta, kawai dai ina ji maka tsoron abun da zai faru ne a gaba, kasan za su iya fushi da kai” Salamatu ta sake fada tana kallon Kaka dake jinjina kai. “Wannan kuma ai mai sauki ne, komai zai wuce Inshallahu, ni dai yanzu ina son ku amince min ayi komai tsakanin yau zuwa gobe amman da idan har ta amince domin bana son na cilastata” Kaka ta dafa shi. “Karka damu ita fa bata san so ba, kuma ta sabawa kanta da kuka tun da ka tafi kullum kuka take sai ciwo, bata da wayo amman an mata auren zata yi hankali” Yayi shiru ya sauke kansa kasa can kuma yaja numfashi a hankali ya sauke. “Na yi magana da Kawo Hasan kuma ya nuna min cewar ba wata matsala, amman duk da haka ina son yi sake yin magana da shi, sai a yanka min sadaki kuma idan son samu ne a daura auren nan yau ko gobe kamin Daddy ya canja shawara”. “Ka yi gaskiya saboda bakar matar nan ma zata iya kitsa masa wani yace ya canja shawara ba zaka aureta ba, kuma dan be saka hannunsa ba, sai me ai mu masu yi maka komai ne, ba mu hana ka auri yarsa ba karawa kawai aka ce kai amman sai taya yarsa kishi yake, wannan abun da kai ni ka yi wa Allah ya maka albarka” “Ameen” Ya amsa sannan ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu. “Idan kun yi magana da su, sai ki sanar min domin ina son komawa yau, idan kuma hakan be samu ba, zan jira har sai zuwa gobe idan an daura auren” “To bari na nemo shi yanzu” Kaka ta fada sai ya sa kai ya fice ya bar Kaka da Salamatu kadai a dakin. Salamtu ta kalli sarakuwarta cikin yanayi na damuwa ta ce. “Inna baki ganin hakan zai iya haifa da matsala? Allah ya ma ba aurenta zai yi ya tafi ya barta ba sai an gansa” “Aiko da sun ci ubansu, daga shi har uban nasa, be ma isa ba, idan zai tafi kafarta kafarsa haka zai tafi da ita, idan ma wayonsa kenan ba zan yarda ya barta ba” “Toh sai dai haka nan, kam idan ba haka ba zai iya mana wani wayon kin san halin yaran nn na zamani, amman kam da ta yi miji yaro barakalla da shi gwanin kyau” Kaka ta tashi zuwa neman danta Hassan. A lokacin da Talba ya fita daga dakin Salamatu sai ya koma dakin Kaka, daga bakin kofa ya tsaya yana kallon Aminatu dake kwance rairai idonta a rufe, sai dai jin kamshin turarensa yasa ta shakar kamshi bada ta san yan tsaye bakin kofar ba, idan yaja numfashin da karfi sai ta sauke a hankali. “Kina son turarena amman baki son kusanci da ni” Ta bude idon ta sauri ta juyo ta kalli gurin kofar sai ta ganshi a tsaye, wani irin kwarjini da haifa ya kara a idonta. Idan har tace bata son Talba to ta yaudari kanta kuma ta yi karya, amman tana sonsa? Anya akwai son sa a zuciyar dake cike da damuwa da bakinciki? Anya ma ta gama karantar minene son? Ko kuwa dai sabo ne irin wanda ta ji a wacan lokacin da tafi ya barta, a yanzu ma idan bata amince ba zata sake ganinsa ko kuwa zai tafi ne har a bada ba zai dawo ba? “Tashi ki ci abinci idan ba haka ba zan kira wannan mutun ya zo yai miki allura” Daga inda yake tsaye ya fada, sai ta tashi zaune tana turo baki tana masa wani kallo dake nuna alamar kiris ya rage ta fashe masa da kuka. Sai yai murmushi ya saka kafarsa cikin dakin ba tare da ya cire talkaminsa ba. “Idan kika aminta kika zauna da ni, zamu rika ganin juna kullum, amman idan kika ki ni wata kila ba zaki sake ganina ba Aminatu, amman na san ba zaki bawa Kaka kunya ba ko?” Ta yi shiru sai kuma ta fashe masa da kukan da bata san na minene ba. Cooler ya dauka ya sake budewa ya saka hannunsa ya rika dauko farfesun ya kai mata a baki. “Bude baki” Ta bude bakin daker tana ta kukan shagwaba. Sai ya kai mata a bakin yana kallon kyakkyawan lips dinta. “Pretty girl” Ya furta yana hade yawu, even though be taba kissing lips din wata mace ba, he like her pink lips, dan karamin bakinta nan ya dauki hankalinsa sosai da yadda take tauna abinci a hankali kamar ya mata dole. Da hannunsa yake bata har sai da wayarsa tai ringing sannan ya saka hannunsa na hagu ya karba kiran kawo Hassan sannan ya mike tsaye yana fadin. “Okay gani zuwa” Be ce mata komai ba ya fice daga dakin, a harabar gidan ya kunna bohore ya wanke hannunsa sannan ya nufi dakin wajen, ba Kawo Hassan Kawai ya samu a gurin ba har da wane kanen Hassan din wanda shi na kawo ne a gareshi da kuma Kaka, kusan abun da suka tattauna a dakin Salamatu shine suka sake tattauna da Uncles din nasa, sai da ya tabbatar musu da babu wata matsala sannan suka amince akan gobe idan an sauke Sallah azahar za a daura masa aure da Aminatu a Masallacin kofar gidan. Kawu Hassan sai nuna bacin ransa yake akan abun da Daddy yai yana ganin kamar ya wulakanta kuma ya nuna shi kadai yake da iko da Talba, be jidadin da za a yi komai ba tare da shi ba, amman be tsammaci haka daga gareshi ba, sai dai dukansu sun raja'ah ne aka ce maganar Kaka cewar saboda ya maida su talakawa ne shi kuma yan ganin shi mai arziki ne. A garin Talba ya wuni har dare, sai guraren tara da rabi Daddy ya kirashi Saboda Momy ta fada masa Talba baya gidan, sai da ya fita waje can nesa da gidan sannan ya amsa kiran Daddy, ya fada masa cewar yana gurin Kaka. “Amman kasan yanayin kasar nan ki? Musamman kauye idan sun ga bakuwar fuska har hada kai ake azo a dauke mutum, sannan taya zaka yi tafiya baka fada min ba?” “Saboda zaka iya hanani da wannan hujojin naka daka zayyano a yanzu, ni kuma ina bukatar zuwa saboda na yi magana da Kaka ka san tana cikin fushin a yanzu” “Na ji ka dawo da wuri, Allah ya tsare, kuma ka yi addu'a sosai Wallahi ina tsoron garin nan” “Inshallahu Daddy babu abun da zai faru” “Toh Allah dai ya tsare, amman ka daina wasa da rayuwarka irin haka” “Inshallahu” Daga haka sukai sallama sannan ya kira Momy ita ma ya sanar mata inda yake ya kuma fada mata ba zai samu dawowa ba sai gobe. “Allah yasa dai ba gurin yarinyar nan ka tafi ba” Momy ta fada cike da gadara. “Momy kina manta cewar akwai zumunci a tsakanina da ita a yanzu, ko bayan ita kuma Kaka ta tana nan kuma tana raye dole ne na rika zuwa” “Hmmm Talba kenan, a hannuna ka tashi karka ce zaka min wayo, ni dai n gargadeka, kuma na ja maka kunne ka fita sabgar yarinyar nan tun wuri indai har ka dauke ni uwa, ina tunanin zaka ji magana ta” Ya sauke ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba, Momy ma bata sake cewa komai ba ta kashe wayar, sai ya koma cikin gidan ya ari wayar Kaka da sunan zai duba wata number yai blocking din number Daddy a wayar Kaka sannan ya goge number gaba daya, gudun kar Kaka tai karabanin cewa zata kira shi. Bayan ya gama abun da zai yi ya mika mata wayarta ya fita, Kawu Hassan ya shigo dakin Kaka ya saka Aminatu a gaba yana tambayar idan tana son Talba, sai dai Kaka bata bata damar amsawa da eh ko aa ba, duk inda Kawu Hassan yai sai a tare, tana cewa wai Aminatu bata da wayo bata san ciwon kanta ba, kuma ba san minene so ba. Ita kanta Aminatu da za a bata dama da bata san wace kalar amsa zata bawa Kawu Hassan ba, domin kanta a yanzu a duhu yake. Daga ita har Talba bachinsu kadan ne, misalin biyu da rabi ta tashi ta shiga bandakin Kaka tai alwala ta fara raya daren na Laraba tana kaiwa Allah kukanta da neman zaba mata abun da zai zame mata alheri da kuma rokin daukinsa a dukan al'amurranta, ta bangaren Talba ma sallah nafila ya kwana yi, a da can sai dai yai raka'a biyu yai karatu da addua ta kwanta sai dai wannan karon har asuba yana zaune a saman carpet din da yai sallah yana karatun qur'ane, bayan ya kamalla ya fadawa Allah bukatarsa da neman daukinsa a abun da yake kokarin aikatawa. Washe gari abun kari na musamman Kaka ta saka aka shirya masa, aka kawo masa har dakinsa, ruwan tea kawai ya sha ya kasa cin komai, sai abubuwan da suka faru a jiya suka rika dawo masa, ya sani akwai kalubale mai yawa a gabansa, sai dai yayi ma kansa alkawarin duk rintsi duk tsanana ba zai taba yarda ya cutar da Aminatu da saninsa ba. Misalin Tara da yan mintuna Kawu Hassan ya same shi da maganar Sadakin da kuma wanda zai masa walicci domin shi zai dauki bangaren Aminatu ne. “Na saka dubu ashiri Hajiya tace yayi kadan zai dai a saka arba'in” “Ba matsala Kawu zan bada 100k, Inshallahu” Kawu yayi murmushi yana mamaki. “100k fa kace Mu'azu, aa yayi yawa” “No be yi yawa ba, ita kanta Aminatun ina son ta ji cewar na dauke ta da kima” “Duk da haka dai dubu dari yayi yawa” “Be yi yawa ba Kawu, Allah dai ya tabbatar mana da alheri” “To amin” Talba ba mutum ne mai yawo da kudi mai yawa ba, haka ya saka dole sai da ya je POS ya cire wasu kudin sadakin ya bawa Kawu da kuma kudin da za a siye komai na al'ada na daurin auren. Bayan ya dawo ne ya kira Ali ya fada masa komai, at first Ali dariya ya fara masa kamin ya biyo da addu'a sannan ya tabbatar masa cewar da shi za a daura auren nan. Haka kuwa akai, kamin lokacin daurin auren ya iso garin tare da sabuwar shaddda mai masifar kyau da tsada sai kyalli take kana ganinta kasan ta ci kudi, fara ce sol zagenta ya fito kwar gwanin sha'awa, not just shadda hula da Talkamin da Ali ya siyo masa ma abun kallo ne. Misalin karfe biyu da yan mintuna aka daura aurensa da Aminatu, ba zai iya cewa happy marriage ba ne, and it's not the sad one, sai dai ya samu kasa da farinciki marar misaltuwa, wani irin annashuwa da natsuwa suka saukar masa, fuskarsa sai haiba take kana ganinsa ka ga ango. Ko kadan fuskarsa ko dabi'arsa da mu'amalarsa bata nuna cewar baya son auren ba, domin shi kansa yana jin matsayinsa da kwarjininsa su karu. BATURIYA POV. Kamar yadda tai masa alkawari, a ranar ta same shi a gidansa na hutawa, suka aikata masha'arsu kamar wacan lokacin. Sai dai wannan karon bata yarda ta kai dare ba saboda tana son zuwa asibiti ganin likita kamar yadda ta fada a gida da karyar zuwa asibiti ta samu fitowa. Wannan karon a account ya saka mata 450k a maimakon ya bata a hannu, saboda ta fada masa bata son kudin a hannu. Yadda yake santi yana yabonta har yafi na wacan karon, sai wani narke mata yake a jiki kamar zai shige ciki, daker ta kwanci kanta domin a ra'ayinsa ya so ta kwana a gidan ne, sai ta nuna masa tana a karkashin iyayenta ne za su iya zarginta idan ta kwana, sai dai bata yarda ta nuna masa cewar tana da aure ba, sai ma karyar da tai masa cewar mijinta ya rasu ya barta da yaro daya. Misalin hudu da kwata ta fito daga gidansa, sai da ta shiga Napep sannan ta kira Ramlee ta sanar mata cewar yanzu ta fito daga gida, domin bada sanin Ramlee ta hadu da shi ba, kuma ta san idan har taji sun hadu ta bayan fage zata iya zargin Baturiya. “To ki tsaya ta sokoto Road, zan zo a dauke ki” “Okay toh amman karki dade dan Allah” “Okay” Baturiya ta sauke wayar tare da shafa cikinta tana jin irin abun da take ji a duk lokacin da tai yunkurin zubar da cikin, sai dai bata da mafitar data wuce wannan, domin idan bata zubar da cikin ba zai iya bata matsala tsakaninta da Fahat, wanda bata fatan haka. A kusa da wani shagon mai Napep din ya sauke ta sannan ta fita ta ciro kudinsa ta ba shi taja gefe ta tsaya sai taunar cingan take tana wani kis kis kis, kamar wata tsohuwar karuwa, dan mayafin dake jikinta ma ba wani abun kwarai ba ne yadda kasan wata yar iskar budurwa haka ta fito, arzikinta daya abaya ce a jikinta ba Atamfa ko lace ba. Ta kusan minti talatin a gurin har ta fara gajiya ta fara takawa gafen titin tana tafiya sannan Ramlee ta kirata sai ta kwatanta mata inda take, tana sauke wayar wata Benz ta wuce gabanta sai kuma ya dawo baya ta faka daidai inda take tsaye. A hankali mai tukin motar ya sauke gilashin motar yana kallonta, suna hada ido sai ta sakar masa murmushi shi kam ya dade da yi ma fuskarsa ado da murmushin. “Hajiya ke ce haka dai?” Ta dauke kai tana fari da ido sannan ta sake kallonsa da kyau, shi din ne dai abokin Faruq da ta taba roka kudi ta WhatsApp a lokacin data saci numbersa a wayar Faruq. “Ni ce dai ranka ya dade, ya akai ka gane ni?” “Kyakkyawar mace irinki ai kowa ya gani zai tsaya, sai dai daga baya mutum zai tantance idan ya sanki ko akasin haka” Ta yi murmushi. “Ka dawo nan ne ko zuwa kai?” “To gani nan dai, Ina zuwa haka? Ina abokin nawa ya barki a rana tana gasa ki” “Abokin ka ai ya dade da yin tazara, duk kyau surar nan da kake gani ya zubar wata zai dauko” “Subhanallahi, lallai da labari a bakin naki mai kyau, da zaki taimaka min da kin shigo motar nan” “Wallahi kawata nake jira, zata zo nan ta dauke ni” “Okay” Ya dauko katinsa ya mika mata. “Gashi a taimaka a kirani, duk dai na san ba a rasa number” Ta yi murmushi bayan ta karba, sannan ta daga kai tana kallon Ramlee data faka a dayan gefen. “Okay zan kira ka Inshallahu” “Na gode kyakkyawa” Ya fada yana kare mata kallon irin kallon nan na yan iska. Sannan ya rufe gilashin motar ya hau titi, ita kuma ta nufi gurin da Ramlee ta faka motar ta bude ta shiga. “Waye wacan?” “Wani abokin Faruq ne” “Okay” Sai da suka hau titi sannan Ramlee ta kalleta ta ce. “Hope dai kin shirya?” “A shirye nake, kawai dai ina gudun a samu matsala ne” “Ba wata matsala, Dr KB kwararen likita ne, ba yau na saba aiki da shi ba, ki kwantar da hankalinki” Ajiyar zuciya ta sauke tana jin kamar kar ta aikata. ________________ Inshallahu a nan zamu dakata sai kuma bayan sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana ganin lokacin cikin koshin lafiya. Fatar Allah ya karba mana ibadar da zamu shiga ya yafe mana kurakuranmu. Ina neman afuwarku. Sai mun hade a Book 2 bayan Sallah inshallahu. Happy Ramadam