💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 1 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******* ****** ****** Zaune suke a falon su wanda yake a gyare sai tashin kamshi yake ga sanyin AC da ya karawa dakin ni'ima. TV na ta aiki, komai na dakin red kaa ne daga manya manyan kujerun har labulayen dakin da center carpet din dake tsakiyar dakin mai uban taushi, wata dattijuwar mata da ba zata wuce shekara arba'in da biyar zuwa da takwas ce zaune gaban ta system, sanye take da less mai kyau da tsada daga yadda take kallon system din zaka san aiki take a cikin ta. Sai gefenta wani dan yaro kyakyawa wanda a ido bai zai wuce shekara biyu ba, sanye yake da wasu riga da wando bakake wanda suka kara fito da hasken fatar sa, gashin kansa a kwance baki sidik sai sheki yake, wasa yake da mota, sai wata kyakyawar budurwa da bata wuce shekara sha tara ba sanye da maroon kalar hijab wanda yake har kasa, waya ce a hannun ta tana daddanawa gaba daya hankalin ta na kan wayar. Sallama akai dabwata muryar mai dadin da zaki, daga bakin kofa amsawa sukai a tare. Wanda yai sallama ne ya shigo cikin takun sa na kasaita sanye yake da suit ash kala wacce ta amshi shi sai bakin takalmi sau ciki baki, hannun sa rike da brief case din sa. Fari ne tas dogo ga saje, idanun sa manya wanda suke ko da yaushe a lunshe sai dogon hancin sa, da madaidaicin baki sa ai agaye da pink lips masha Allah kyakyawa ne sosai. Yaron dake wasa da mota ne ya d'ago yana ganin sa ya mike yayo wajen sa a guje yana fadin "Abbi Oyoyo!" Brief case din ya ajiye akan kujera ya daga yaron sama ya rumgume shi, yana murmushi wanda kumatun sa suka lotsa kan yaron ya shafa yace "My Son ya gidan?" "Abbi i miss you (nayi kewar ka)" Ya fada da harshen da zaka san magana bata gama zama a bakin sa ba. Matar dake aiki a system ce ta d'an d'ago tana kallon sa, ya karaso cikin falon ya zauna a kan carpet din dake tsakiyar dakin tare da d'aura kan sa a gefen kafar matar yace "Ummi nah sannu da gida ya aiki?" "Alhamdulillah Dr ya aikin?" Ta tambaya cike da kulawa. "Alhamdulillah!" Ya fada yana shafa sumar kansa da take kamar ta indiyawa sai sheki da kamshi take. Budurwar dake zaune ce ta dago fuska ba yabo ba fallasa tace "Sannu da zuwa Yaya." "Yauwah!" Kadai yace ya mike rike da yaron yai hanyar dining inda wata kofa take suka shige. Da kallo ta bisu ta d'an tabe baki mikewa tayi tace "Ummi bari naje wajen Inna." "To ki gaishe ta." Ta fita tana tafiya a hankali kamar ba zata taka kasa ba, saboda wayar da take dannawa kamar daga sama taji an zare wayar hannun ta da sauri ta d'ago fuska ta marairaice tana kallon wanda ya amshe wayar, wani kyakyawan saurayi ne wanda ba zai wuce shekara talatin ba, dogo ne fari tas dashi wanda yake da faffadan kirji, yana da idanu da hanci da bakin sa dan madaidaici, murmushi yake wanda ya kara masa kyau, fuska ta kara shagwabewa kamar zatai kuka tace "Yaa Faroukkk" Wanda aka kira da Yaa Farouk ne ya zuba mata ido wannan yasa tai saurin yin kasa da kan ta tana son wucewa ta gefen sa. Ya d'an kamo gefen hijab din ta, ta juyo yace "Kina tafiya kina danne danne sai kin fadi kinji ciwo ki barewa mutane baki kina kuka ko?" Ido ta zaro ta, tace "Kai Yaa Faroukkk ni din?" Ta fada tana nuna kan ta. "Eh ke din fa ke wa ya kai ki ragwanta, ko Haidar ya fiki jarumta." Baki ta dan turo tace "Uhmm ai kuwa na fishi wancan dan mitsitsin yaron." Yai murmushi yace "Shi fa. Yanzu ina zuwa?" Bangaren Inna ta nuno masa tana fadin "Wajen Inna." "Nima can zani. Wai me kike dadannawa a wayar ne ko chat kike da siriki nane?" "Kai a'ah ni ba ruwa na Yaa Farouk." "A'ah fah ki fadan gaskiya in dashi ne a bani mu gaisa." "A'ah Yaa Farouk ni bani da wani saurayi fa, da Jawahir muke chatting fa." "Wannan Jawahir din dai har na gaji da labarin ta ita bata kawo wa mutane ziyara ne?" Ido ta zaro tace "kai Yaa Farouk ranan fa nace maka tazo itama tana ta tambayar ka, kasan ma me? Kun fiya sabani shiyasa." "Duk tsiya dai watarana zan ganta in ma bakya so na ganta ne." "A'ah ni ba ruwa na." Suka karasa kofar sasheb Inna wanda yake babban compund ne da aka zagaye ahi da shuke shuke wanda ya karawa wajen kyau, kofar dakin Inna suka karasa sukai sallama ta amsa suka shiga. Daki ne madaidaici wanda yaci set din kujeru Ash kala da kayan kallo bakake, labulayen da center carpet din duk ash and black ne, dan a gyare yake sai kamshi da yake, tiles din kuka kamar kaga kanka a ciki haka kayan kallon sai kyalli suke kamar wanda aka shafe da mai. Maryam ce ta fara shiga tace "Inna tah." "Na'am Maryama yau ina kika shiga tin safe baki leko ba." Wata tsohuwar mata da zata kai shekara tamanin da wani abu, saye cikin atamfa super tai kwaliyyar tai maganar tana kallon Maryam din cike da so da kauna. Maryam ta zauna a kusa da ita tace "Ina can ina aiki na danyi sanitation ne a bangaren mu." Inna tace "Sannu ina Haidar din?" "Yana wajen Abbin sa." Baki Inna ta tabe ta kalli Farouk tace "Ai sai ka zauna ko ka tsaya sai kace wanda ya hadiyi tabarya." "To wa ya sani." Farouk ya fada yana danna wayar Maryam. Inna ta gimtse baki tace "Ai da ba lafiya." Maryam tai dariya tace "Ai kuwa dai Inna." Ya zauna yana kallon Maryam yace "Kina biyewa Inna Allah batawa zamuyi." "Yo ku bata din mana, sai me kuma me kake mata ci ko sha ko sutura." Inna ta tambaya tana hararar sa. "Dukka." Ya bawa Inna amsa yana zaro wayar a aljihu. "Ba mu gani ba." "Ai daman Inna ke ba komai kike gani ba." "Tinda ga makauniya ko?" "Nifa bance ba Hajiya Inna." "Kai ka sani dai." Inna ta kalli Maryam tace "Dazu nayi dambun nama ni dan ke nayi ma wallahi to sam baki shigo ba." "Zamu ci dadi." Farouk ya fada yana mikewa daga kishiginden da yake. Inna tace "Duk jikokin na babu kwadayeyye kamar ka Umaru kuma in naga dama dandanawa ba zakai ba." Dariya yayi yace "Mai gidan naki guda." "Kai tafi can ai na fiyi da wancan mai fuskar shanun." Baki ya bude yana dariya yace "Lalalah Yaa Haidar din Inna ai kuwa sai na fada masa." "Ba abinda yayi sai hada mutane fada to yanzu shi yaji ne amman kin ji shi wai zai fada masa salon dan abinda yake bani ya daina bani." Murnushi Maryam tayi tace "So yake ki sammishi kuma Yaa Aliyu ba yadda zai ba." "Ai dai mai hada husuma bashi ba Allah." Dariya Farouk yayi yace "Hajiya Inna ai kin fada dai." "Kai ka sani." Wayar sa ce tai kara da sauri ya dago yana kallon Maryam dake wa Inna magana sam bata san ma yana yi ba da sauri ya mike ya fita yana kara wayar a kunnen sa. "Hello Baby." "Kana ina Baby kace zaka zo kuma naji shiru." "Kinga magarib ta kusa ki jira ni bayan magrib zan karaso." "Ok ina jira." Ajiyar zuciya ya sauke ya koma dakin. Inna ta kalli Maryam tace "Yau na ganki duk wani iri me yake damun ki?" "Ba komai Inna yanayi ne kawai." "A'ah in akwai abinda ke damun ki ki fada min ko ita Aishan ce tai miki wani abu?" "A'ah Inna me Ummi zatai min?" "Ah na sani." "Ni ba abinda tai min." "Wannan mai fuska a dauren fa?" Baki Maryam ta tabe tace "Shi da dawowar sa kenan." "To shikenan." "Hajiya Inna kudi zaki bata kawai." Farouk ya fada. "To ina ruwan ka. In kudin take so ai zata fada min ko Maryama." Kai Maryam ta gyada tana jingina da kujera. Wayar tace tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dauka tayi ta kai kunne tace "Hello Jawa." "Na'am wai ya zancen addimision din kine?" "Nifa har yanzu su Ummi basu ce komai ba." "Kuma ke ba zaki iya musu magama ba?" Mikewa tai ta fita tana fadin "Ai suna sane na sani." "Shikenan ni dai gashi nan an amso min gobe Dady yace naje nayi registiration da so nayi muje tare." Kofar dakin Inna ta juya tana kalla tace "No Jawa kije kawai ba matsala in zan yi kya raka ni kar kije ki samu matsala." "Shikenan amman ki fadawa Yaa Aliyu mana." "Zan masa magana bai jima da dawowa ba ai." Juyowar da zatayi taga Aliyu tsaye a wajen Haidar kuwa har ya shige falon Inna. Kai tayi kasa dashi da sauri ya wuce dakin Inna ita kuma ta juya tayi sashen su. Ummi ta sama a inda ta bari sama kawai ta haye, Ummi ta d'ago tana kallon ta sai kuma ta d'auke kan ta. Tana shiga ta fada bandaki tai alwala ta fito ta tada sallah bayan ta idar tai addu'a Alkur'ani ta d'auko ta fara karantawa tana zaune har akai isha'i ta mike tai sallah tai addu'a tare da shafa'i da wuturi. Mikewa tai ta cire hijab tare da cire kayan ta, wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan bacci ta feshe jikin ta da turaren ta mai kamshi. Kan gado ta hau duk da ba bacci take ji ba amman so take ta dan huta. Tana kwanciyya aka turo kofar d'akin Ummi ce ta shigo da sallama mikewa zaune tayi. Ummi tace "Kin ci abinci ne naga kamar kin kwanta?" Cikinta ta d'an shafa tace "Ummi na koshi ne." "Me kika ci?" Kai tayi kasa dashi. Ummi tace "Tin abincin rana ko? To maza sauka kije kici abinci." Kafarta ta diro kasa ta mike ta d'auko hijab ta saka sannan ta fita a d'akin Ummi tabi bayan ta, ba kowa a d'akin dan haka ta karasa dining. Abinci ta fara ci kamar ba zata ci ba, sallamar sa ta jiyo sai ta ji Haidar ma na sallama a ciki ciki ta amsa ya shigo bai kalle ta ba yayi d'akin sa. Haidar ne ya karaso yace "Addah kalli abinda Abbi ya siyon." Ya fada yana mika mata ledar hannun sa, amsa tayi ta leka tace "Yaron Abbin sa kace angode?" Kai ya gyada tace "Good to jeka." Ya ruga a guje ya shiga dakin Abbin. Abincin ta karasa turawa da kyar ta mike tana kwashe kayan Haidar ya dawo yace "Addah Abbi yace kizo." "Ni!" Ta fada cike da mamaki. Kai ya gyada mata, tace "To jeka gani nan." Ta dibi kayan ta kai kitchen sannan ta dawo ta nufi dakin Aliyun. Sallama tayi ya amsa, ta shiga kanta a kasa, Masha Allah wani kamshi da sanyi ya doke ta, ta lumshe ido, ta bude yana daka kan kujera yana danna system. Komai na dakin fari ne tas sai kace ba a rayuwa a cikin sa, daga gefen kujerar ta durkusa tace "Gani Yaa Haidar." Da sauri ya dago kan sa ya kalle ta da lumsassun idanun sa, lumshe du yayi sai kuma ya dauke kan sa, envelope ya mika mata. Amsa tayi ta tsaya jin ko zai magana amman bai ba mikewa tayi tace "Nagode." Ta fita sama ta hau ta shiga dakin ta, ta ajiye envelope din akan side doruwa ta zare hijab ta hau kan gadon addu'a tayi ta kwanta ta gefen dama envelope din ta gani ta mike da sauri ta dauka budewa tayi ta zaro takardun dake ciki ta zube su akan gadon daya ta dauka ta fara karantawa da sauri ta zaro ido murmushi ya bayyana akan fuskar ta. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah nagode maka ashe nima zan yi karatun nan." Sai hawaye ya hau zubo mata a saman fuskar ta. Shin wa zata fara fadawa wannan abun farin cikin Ummi, da sauri ta mike ta fita a guje a dakin hannun ta rike da takardar addmision din, kofar dakin Ummi taje tai knocking Ummi ta bata izinin shiga da sauri ta bude ta shiga tana shiga ta karasa wajen Ummi ta rumgume ta tana fadin "Ummi kalli ki gani." Ummi ta amshi takardar tana dubawa itama murmushi ne ya sauka akan fuskar ta tace "Masha Allah. Allah yasa a fara a sa'a." "Amin Ummi nah ki tayani yiwa Yaa Haidar godiya." "To Maryama Allah bada sa'a da nasara." "Amin Ummi." Ta mike ta fita a dakin. Dakin ta ta koma ta duba dayar takaradar form ne na banki sai wasu kudi masu yawa kirgawa tayi taga dubu dari biyar ne. Ido ta zaro tace "Na menene kenan?" Tsaki ta dan saki tace "Yaa Haidar shi ba zai yai min bayani ba ni nasan menene da zai ban abu kawai ba bayani to da ban bude ba fa." Ta fada tana lallubar wayar ta. Jawahir ta kira tana dauka tace "Albishirin ki?" "Goro." "No ban son goro ni ba tsohuwa bace." "To chocolate." "Hmmm yanzu Yaa Haidar ya bani takaradar addmision fa." "Da gaske Angel?" "Wallahi yanzun nan fa." "Alhamdulullah kinga gobe sai muje registeration tare ko?" "Eh nawa ne registeration din?" "Sai mun shiga ckul amman dai naji Yaa Khalid yace kamar 150k ne." "Ok Allah kaimu goben." "Amin sai da safe." Sukai sallama. ** Washe gari da safe da wuri ta shirya tana kitchen tana aiki taji Haidar na kwala mata kira yana fadin "Addah Addah!" Da sauri ta leko, ta ganshi sanye cikin wandon jean da jar riga, sai agogo daure a hannun sa, ta kamo hannun sa tace "Ya akai Boy." Hannun ta ya hau ja zuwa dakin Aliyu tace "Haidar bari na sako Hijab d'ina." "Aah Abbi na so kizo yace." Yai maganar da gwaranci. Zatai magana Aliyu ya fito da sauri tai kasa da kai shima kallon ta ya danyi tana sanye da doguwar riga wacce ta kamata, daga sama, kan sa ya dauke yace "Kin cike form din da na baki jiya?" Kai ta girgiza, saboda ba ganin ta yake ba, ya dan d'ago ya kalle ta da shanyayyun idanun sa yace "Magana fa nake." 'Dagowa tayi sanye yake da wasu Blue kalar suit wacce tai masa kyau, gashin kansa ya kara baki sai sheki yake, leben sa ya kara yin pink sai kyalli yake kamar wanda ya shafa masa janbaki ko man lebe, suna hada ido sukai saurin kawar da idanun su, jiki a sanyaye tace "A'ah." "Ke zan tsaya jira to kije ki cike ki kawon kar ki batan lokaci." Tai saurin fita tai sama, da gefen ido ya rakata ya zauna akan kujera yana mai lumshe idanun sa. Tana zuwa ta cike form din. Hijab ta saka ta fito ta same shi a kasa. Tana mika masa ya mike har ya kai kofa yace "Nayiwa driver magana zai kai ki banki wajen aboki na shi zai bude miki account daga nan sai kiyi registeration dan a satin nan za a rufe." "To nagode Allah saka da alheri." Ya juya ya fita tace "A dawo lafiya." Hannu kawai ya daga ta koma ta karasa abinda zatai. Tana fitowa sai ga Ummi ta sauko cikin shirin ta na tafiya aiki. Ummi tace "Ya zancen registeration din naki?" "Yaa Aliyu ya bani kudin yace anjima driver zai kaini nayi." "To madallah ina Haidar din?" "Sun fita tare." "To shikenan sai kin dawo ki kula dai." "Insha Allahu!" Ta koma sama. Waya sukai da Jawahir suka dai dai ta fitar tasu wajen sha daya ta fita driver ya kai ta banki tana zuwa Jawahir na zuwa dan haka tare sukai komai nan da nan suka gama suka fito suka je ckul suka fara abubuwa wanda suka ga har an kafe time table next week za a fara exam haka suka koma gida. Tana shiga ta samu Farouk a compound yana ganin ta mike yace "Daga ina haka?" Tace "Makaranta?" "Wacce makaranta?" Murmushi tayi tace "Naje nai registeration yau." Ido ya zaro yace 'Masha Allah. Allah ya bada sa'a kace sai fara makaranta." Kai ta gyada yace "To ni mai zan miki na zuwa ckul?" "Addu'a." Kai ya girgiza yace "No anjima zan kai ki kiyi shopping na abinda zaki bukata a makaranta." "Ni me zan nema Yaa Farouk nagode ka barshi kawai." "Ba kyau mai da hannun kyauta baya." Tai murmushi tace "To nagode." Ta nufi sashen Inna ta sanar mata da komai sannan ta koma part din su dan yin aiki. Karfe biyar Ummi ta dawo anan ta same ta tace "Ya makarantar?" Nan ta hau bata labari Ummi tace "To a tsaya dai ayi abinda a kaje." "Insha Allahu." Bayan magariba, tana zaune sai ga Farouk da kan sa ya shigo ya fadawa Ummi inda zasu ta kalli Maryam tace "Sai kun dawo." Maryam ta mike tabi bayan sa dan daman da hijab din ta a jikin ta. Kaya masu yawa ya siya mata dan ita ta ki daukar komai shi ya dinga jidar mata dogayen riguna hand bags da sauran su haka suka biya akai total ya kashe mata kudi masu yawa suka fito suka yo gida. Yana parking taga Aliyu zaune a cikin mota shi da Haidar kai ta dauke ta fita. Farouk ya fito rike da ledar da yayo mata siyayya yabi bayan ta har sun kusa sashen su yaji wayar sa na kara zarowa yai yana dubawa yaga Mama ce kai ya daga yana kallo barender ta, wata farar mata mai jiki ce tsaye a barrender sanye da atamfa daguwar riga, kallon sa take wannan yasa ya dauke kai ya kai wayar kunnen sa yana fadin "Hello Mama!" "Kazo yanzun nan." Maryam ya kalla da ta kusa kofa ya kwalawa mata kira, ta juyo ya karasa tare da mika mata ledar yace "Sai anjima." Tai murmushi tace "Nagode." Ya juya yayi sashen su. Dakin ta ya shiga wanda ya gaji da haduwa da wasu purple kalar kujeru da labuyale, zaune ya same ta akan kujera kafa d'aya kan d'aya zama yayi yace "Gani Mama." "Me ya hada ka da wannan yarinyar?" Ta tambaya fuska a hade, kan sa yai kasa dashi yace "Yaa Aliyu ne ya aike mu." "Na fada maka bana son ina ganin ka kana kula yarinyar nan amman ka'ki kaji ko? Ka fita idona na rufe fa." "Kiyi hakuri Mama." "Tashi ka ban waje." Ya mike ya fita yana mamakin halin Maman sa shi sam bai ga aibun su Ummi da Mama take musu wata irin kiyayya. Sashen Inna ya wuce kawai. Maryam na shiga ta samu Ummi a Falo kayan ta dire tana nuna mata wayar Ummi tai kara ta duba tace "Hello Aliyu lafiya?" "Turon Maryam." "Ok." Ta kalli Maryam tace "Yayan ki ke kiran ki." "Ni kuma?" "Eh." Mikewa tai ta fita. A parking space din ta same su cikin mota yace "Shiga mana." Ta bude baya ta shiga ya tada motar. wani super market ya nufa dasu suna shiga ya kalle ta yace "Ki dauki abinda kike so." Yaja hannun Haidar sukai bangaren kayan maza. Fara zagaye wajen tayi tana kallon kayan wajen tafi rabin awa ba abinda ta dauka, har suka gama bata dauki komai ba sai kallon kayan da take dan burge ta sun burgeta amman kuma abun da sukai mata yana da yawa banda dawainiyyar ta anya kuwa. A haka suka karaso wajen basket din su cike da kaya kallon ta Aliyu ya tsaya yi can yace "Me kika dauka?" Kan ta tayi kasa dashi a hankali ta girgiza "Ba abinda kike so kenan ko?" Shiru tayi ya kama hannun Haidar yace "Muje!" Suka bar wajen bayan su tabi suka bayar aka gama masa total ya biya sannan suka fita mota ta shiga, ya ajiye Haidar ya koma ciki bai jima ba ya fito rike da leda ya bude motar ya shiga ya tayar suka koma gida. Tara saura suka koma gida dan haka ta dauki Haidar sukai sama. Wanka tayi masa itama tayi ta shirya shi ya kwanta sallah ta tayar kan ta idar har yayi bacci. Sauka kasa tayi dan ta zuba abinci ta samu leda a bakin dakin su, kasa ta sauka ta dauki nono ta zuba suga ta sha sannan ta fito tayi sama, kayan ta kwashe ta shiga daki. Akan gado ta zube su kaya ne masu kyau da tsada a cikin ledar dayar kuma under wears sai turarukan sa da su alawa biskit chocolate adana kayan tayi a wajen da ya kamata sannan ta kwanta. Bata jima da kwanciyya ba taji an bude kofar dakin dagowa tayi Ummi ce ta mike zaune tace "Kun dawo?" "Eh Ummi." "Abban ki ke son ganin ki." "Toh!" Ta fada tana mikewa hijab din ta ta saka ta bi bayan Ummi yana dakin sa ta shiga da sallama ta zauna a kasa tace "Barka da dare Abba." "Yauwah Maryam ya gida?" "Alhamdulillah Abba ya aiki?" "Alhamdulillah dazu Ummin ki ke fada min, Yayan ki ya samar miki addmision har da kudin registeration Allah ya bada sa'a ni gudunmawar me zan bayar tinda ya riga ya gama wadan nan?" Kan ta a kasa tace "Abba addu'a kawai nake bukata." "Kullum muna miki addu'a Maryam sai kuma me?" Kai ta girgiza. Yace "To ya kamata ki bude account ko dan kudin makaranta da abubuwa ko?" "Eh dazu Yaa Aliyu yasa an bude min." "To ai sai a bani account number ko?" "Nagode Abba." "Ba komai ina Haidar din?" "Yayi bacci." "To sai da safe." "Nagode Abba Allah tashe mu lafiya." Ta mike ta fita. Komawa dakin Ummi tayi ta same ta tace "Ummi na fito." "To sai da safe." Ta tafi dakin ta, ta kwanta tare da addu'a *** Washe gari da yamma tana bangaren Inna suna hira Haidar ya shigo a guje ya fada jikin Maryam ta dago shi tana fadin "Haidar ba zakana tafiya hankali ba ko?" Dariya ya hau yi mata tace "Yaushe ka dawo." "Yanzu Abbi na kiran ki." Ya fada yana zuwa ya zauna a cinyar Inna. Inna ta shafa kan sa. Mikewa tayi ta fita yana dakin sa ta shiga da sallama ya amsa, ta dan kalle shi, sanye yake da wando cotton dogo ruwan omo sai riga ruwan madara mai dogon hannu, idon sa a lumshe bai ko bude ba tace "sannu da zuwa." "Yauwah!" Ya nuna mata wata leda dake kan kujera da hannu yace "Dauki." Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa akan ta, wanda take jin su kamar me, baki ya dan cije yace...... *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 2 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa akan ta, ji take kamar me, baki ya dan cije kamar ba zai magana ba yace "Jeki." Ta dan durkusa tace "Nagode." Ta fita Ummi ta sama a falo ta mike mata ledar tace "Ummi Yaa Aliyu ne ya bani." Amsa Ummi tai ta leka tace "Madallah angode." Sannan ta mika mata tace "Jeki ajiye." Tayi sama akan gado ta zazzage kayan da wata riga tai arba wacce tin jiya ta burge ta sai dai ganin kudin ta ya hanata dauka sai wasu rigunan da atamfofi da wasu cover shoe masu kyau kamar yasan tana so kamar yasan su suka burge ta, ta d'auka ta ajiye tana murmushi ita kadai. Kasa ta sauka wajen Ummi suna hira har aka kira magariba. Suka wuce dan yin sallah. * Ranar lahadi da dare ya shigo falon, sanye da bakin wando jean sai riga longsleeve mai mabballi blue black ba karamin kyau kayan sukai masa ba sai hasken sa ya kara fitowa gashin kan nan nashi kwance sai shekki yake, fuskar sa tai wani fresh sai kyalli yake, kamshin sa kuwa ya gama cika dakin, Ummi da Maryam ne zaune Maryam na kallon Bollywood da suke wani indian film mai kyau. Akan kujera ya zauna Haidar ya karasa ya zauna kusa da Maryam yana mata surutu. Ta dago ta kallli Aliyu ta dauke kai tare da fadin "Sannu da zuwa." "Yauwah!" Ya fada yana lumshe idon sa, sai kuma ya dago ya kalli Ummi yace "Ummi dole fa yarki ta rage kallon nan in har karatun take son yi dan karatun su ba wasa a ciki." Dagowa Ummi tayi ta kalli Maryam tace "To ai gaka ga ta nan sai kai mata fadan ko?" Ya juyo ya kalle ta, wanda yai saurin dauke idon sa yace "To ban da kule kulen samari ki tsaya kiyi abinda ya kai ki." "Insha Allahu." Ya mike yana fadin "Bari na shiga daga ciki Ummi." "Kaci abinci ne son?" Ciki ya shafa ya girgiza kai yace "Ummi yau ciki na a cunkushe yake sam bana son cin komai." "A'ah fadi me kake so sai ai maka yanzu." "A'ah zan ci komai kukayi ma." "Yauwah to" Ta kalli Maryam tace "Hada masa abinci ki kai masa." Ta mike ta fara hadawa ta gama ta nufi dakin nasa. Ba kowa a ciki dan haka ta ajiye ta juyo tana kaiwa kofa ya fito juyowa tayi ta kalle shi sanye da jallabiyya yake blue black tace "Ga abincin ka nan inji Ummi." Tana fada ta juya ta fita. Shima daki ya koma ciki, gado ne kato wanda yake lullube da farin bedsheet dakin sai kamshi kan gado ya fada yana mai lumshe idon sa. Can ya mike ya dauki wayar sa ya fara neman layin sitti. Ba a jima ba ta dauka ya kai kunnen sa yace "Ni dai sam yanzu Sitti bata so na bare ta damu dani." "A duk duniya kana daya daga cikin wanda na fi kauna ba ranar Allah da zata bude ban yi maganar ka ba Abin so. Ina kaunar ka da tausayin ka, ina fatan kuma Allah ya baka mai kula da kai kamar marigayiyar matar ka. In ban kula da kai ba da wa zan kula Abin so?" Kai ya langwabe kamar tana kallon sa yace "Nayi kewar ki har ba adadi." "Yaushe zaka taho din?" "Tin da nai requesting har yau ba ai approving ba Sitti." "Nima nan duk ya ishen so nake Najwa ta karasa jarabawa sai mu taho gaba daya." "Yauwah Sitti dan Allah ki taho fa." "Insha Allahu Abin so." Tai murmushi yace "Kawai Sitti ina cikin maraici." "Maraici Abin so yau ko baka da uwa da Uba ai kana dani kafi karfin maraici bare kuma ga Ummin ka nan me yake damun ka." Ido ya lumshe yana cusa hannun sa cikin sumar kan sa yace "Sitti komai ma. Ji nake kamar nai ta kuka." "Subhanallah akan me to?" Ido ya bude a hankali yace "Sitti......" Ganin inuwa yasa ya dago Ummi ya gani tsaye akan sa yace "Sitti mayi magana anjima." Ya kashe wayar. Ummi ta karaso dakin ta zauna a kusa dashi tana fadin "Meyake damun ka Dr?" Kai yai kasa dashi yace "Ba komai fa Ummi ni kaina na rasa gane abinda yake damuna kwana biyunan." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Amman baka fada min ba." "Bana son hankalin ki ya tashi." "Kasan ko ka fadan ko baka fada ba ina sanin halin da kake ciki ko? Dan haka ka daina boyen abu sai dai na ganka kawai nayi shiru." "Na sani Ummi." Ya fada yana kwanciyya akan cinyar Ummi. Hannu ta daura akan sa tana shafawa tace "Ka dauki komai a sannu, kuma komai zai dai dai ta zurfin ciki ba inda zai kai ka fito ka fada min abinda kake so." "Ina kewar Matata Ummi...." "Shiyasa nake so kayi aure ai. Shekara nawa da rashin matar ta ka amman ka kasa cire abun a ranka. Aliyu ina shiga damuwa a duk lokacin da na ganka cikin damuwa. Duk yadda zan magance maka damuwar ka ba kamar matar ka ba zatafi sanin yadda zata rage maka ka daure ka cire Maryam a ranka ka rumgumi rayuwa ka samu wata ka aura kara girma kake Aliyu ko dan kaga su Abba sun maka shiru ne?" "Ummi ta ina zan samu mace kamar Maryam tinanin da nake kenan." "Ba a rasa na gari Aliyu zaka samu zaka iya samun sama da Maryam kada ka fidda rai da rahamar ubangiji." "Ki tayani da addu'a Ummi ki tayani da kai kuka na wajen ubangiji akan ya shiga lamari na." "Insha Allahu Dr a kullum ina maka addu'a kayi hakuri kaji." Ido ya lumshe ta kamo hannun sa tace "Taso kaci abinci." A baki ta fara bashi abincin har ya koshi tace "Dan Allah Son ban da tunani kaji." Murmushi yayi mata yace "Insha Allahu." Ta mike ta fita da kwanukan. A falo ta samu Maryam da Abba sai Haidar dake hawa kan Abba yana sauka sai wasa yake. Ummi ta kai kayan kitchen ta dawo tace "Sannu da zuwa." "Yauwah. Yau kuma rigimar dan taki ce ta motsa?" "To ya zanyi Aliyu yana bukatar me kula dashi." "Hmmm ba yaki yai aure ba da yai aure da matsalar sa zata ragu." "Kasan Aliyu ai kamar tsoron mata ma yake." Maryam tai murmushi tace "Hmmm Ummi baki ga yan matan dake son sa ba wallahi kyawawa fa yan gayu." "Hmmm Maryam ai shi Aliyu ba komai yake burge shi ba kin sani." Jingina tai da kujera tana fadin "Anty Maryam tayi fama." Haidar dake jikin Abba yai bacci. Wannan yasa ta mike ta dauke shi tai musu sai da safe tai sama. Abba ya bita da kallo sannan ya juyo ya fuskanci Ummi yace "Dole Aliyu ya fitar da matar aure fa. Ga kanin sa nan shima ko tunanin fitar da mata bayayi saboda ya gansa zaune shima ba auren." "To Abba zan masa magana." "Ya dai kamata." ** Ranar monday suka fara lecture sosai sukaji dadin makarantar bama da ya kasance suna tare department dinsu daya dan haka basu wani damu ba haka suka cigaba da zuwa makaranta. Aliyu ya bata ATM din ta wanda take yai mata transfer din kudin abubuwan makaranta da gudun ta tafi wajen Ummi ta nuna mata Abba ma da ya dawo yasa ta bashi account number shima ya tura mata kudi. Ummi tace "To ni dai duk abinda kike bukata ki fada min kinji?" Kai ta gyada tana murmushi tare da rumgume Ummi tana fadin "Nagode Ummi na Allah saka muku da gidan aljanna." A lokacin kuma Aliyu ya saka Haidar a makaranta duk da ba baki ne dashi sosai ba dan Ummi ta tafi aiki, shima aiki sai shi kadai sai ko wajen Inna da yake sata bari bari da aiki wannan yasa ya kai shi makaranta karfe biyu ake dauko shi lokacin kuma Ummi ta dawo dan bata fiya kaiwa yamma ba. Da dare Maryam suka fito daga bangaren Inna sukayo bangaren su, Abba ta sama zaune a falo ta zauna tana fadin "Abba sannu da zuwa." Ya dago yana mata murmushi yace "Yauwah daga ina?" "Wajen Inna." Farouk ne ya shigo da sallama suka amsa ya karaso ya gaida Abba, Abba yace "Engineer kai ba a ganin ka." Yayi murmushi yace "Ina nan Abba haduwa ne bama yi dai shiyasa nace yau dai bari nazo na gaishe da Abba na." "Toh Madallah ya aikin?" "Alhamdulillah!". Suka dan taba hira Farouk bai wani dade ba ya mike yace zai wuce, Abba yace "Baza ka tsaya mu ci abinci ba" Yai kasa da kai tare da fadin "Alhmdulillah Abba na ci abinci" Ummi dake dinning tana jera abincin tace "Anya Yaya Farouk" Dariya yayi yace "Ummi wllh na koshi" Tace "Toh shikenan" Sallama yayi ma Abba ya fita yana satar kallon Maryam da ke wasa da yatsun ta. Mikewa Maryam tayi ta nufi sama. Abba yace "Dawo nan Maryam nasan kina hawa ba saukowa zaki kici abinci ba." Kai tai kasa dashi tana murmushi tace "Abba na koshi ne." "Ban yadda ba shiyasa muke fada da Aliyu dan wani lokacin bai son cin abinci zo nan." Ta karasa ta zauna a kasa wajen kafar sa. Yace "Kinga kar ki zama kema yayan naki, kina cin abinci kinji." "Toh Abba." "Yauwah yar albarka ya makarantar ba dai matsala ko?" "Babu Abba." "Allah bada da sa'a ki tsaya kiyi karatu sosai kinji?" Kai ta gyada Ummi ta fito tace "To ku taso muci." Abba ya mike Maryam tabi bayan sa. Kujerar gefen daman sa ta zauna. Abba yace "Je ki kira su dan suma in ba a kira su ba baci zasuyi ba." Mikewa tayi ta nufi dakin Aliyu dake kusa da dining falon ta shiga kamar yadda ta tsamaci ba kowa dan haka ta karasa kofar bedroom tai knocking ji tayi yace "Yes come in!" Batai niyyar shiga ba so tai yazo ta fada masa abinda zata fada ta juya amman kuma bai zo ba, a hankali ta daura hannu akan mabudin kofar ta murda kofar ce ta bude ta tura ta a hankali, bata shiga ba a bakin kofar ta tsaya tana kallo shi zaune a bakin gado System a gaban sa akan stool sai Haidar dake sakale da wuyan sa yana kallon system din shima, ganin ba wanda ya dago yasa tace "Assalamu alaikum!" Haidar ne ya fara dagowa yana kallon ta ya sauko a gadon yazo ya rumgume ta, Aliyu kuwa a ciki ya amsa. Baki ta dan tabe tace "Abba yace ka fito kaci abinci yanzu." Tana fadar haka ta juya rike da Haidar dake tai mata surutu tana fita ta tadda har Ummi ta zuba mata abinci tare suka fara cin abincin ita da Haidar can sai ga Aliyu ya fito kujerar kusa da ita yaja zai zaune sai kuma ya mayar ya ja ta kusa da wacce zai zauna din ya zauna tare da jan plate din sa. Shiru wajen yai kowa ya dinga cin abinci kadan Maryam taci taji ta koshi sai Haidar da take bawa shima nan da nan ya koshi. Aliyu ma haka dagowa Maryam tayi ta kalli Abba sai ta kalli Ummi lokacin Ummi itama ta kalle ta marairaice mata fuska tayi kamar zatai kuka Ummi ta dauke kai. Abba ne ya kalle ta yace "Ah ya haka naga kin ajiye spoon." "Abba wallahi na koshi." Kai ya girgiza yace "Me kika ci? Ban yadda ba maza ki cinye shiyasa gaki na bakya gaba bakya baya, dauki ki karasa." Spoon ta dauka kamar zatai kuka ta fara turawa spoon biyu tayi ta kalli Abba idon ta har ya ciko da kwalla tace "Abba wallahi na koshi Inna ta ban fura nasha dazu." Dagowa tayi Abba yai murmushi yace "To shikenan." Ta mike tana murmushi ta dauke plate din ta kai ta juye sauran a wani abu da suke zuba ragowa sannan ta wanke plate din ta fito tace "Abba sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Tai sama. Daki ta shiga ta cire kayan ta ta watsa ruwa tana fitowa ta saka kayan bacci tare da shafa turarukan ta. Alwala ta dauro ta koma kan kujera jakar ta ta janyo ta fara duba aikin ta wanda kullum haka take kan ta kwanta takan dubawa. Har karfe goma ta mike ta dauki wayar ta suratul Bakara ta kunna dai dai nan Ummi ta shigo rike da Haidar, Maryam ta mike ta amshe shi, kaya ta canja masa sannan ta kwantar dashi sukai addu'a suka kwanta. Karfe biyar saura kwata ta mike ta dauro alwala sannan ta zo tai sallah Alkur'ani ta dauka ta fara karanta har aka kira sallah ta mike ta tada sallah. Tana idarwa tai azkar sannan ta mike ta fito falon sama ta gyara sannan ta sauka kasa ta fara gyara falon da dining. Tana cikin yi Ummi ta sauko ta durkusa ta gaishe ta, Ummi ta amsa cike da kulawa tare da tambayar ta ya ta tash ta amsa da Alhamdulillah. Turare dakin tayi ta nufi kitchen dan taya Ummi aiki, ta samu Ummi da mai aikin su na wanke wanke dan har ta gama fere abinda za a soya ta tafasa kayan ciki. Maryam ta karasa zata hada farfesun Ummi tace "Ba zaki makara ba?" "Eh Ummi ai shi kadai zan hada." "To." Nan da nan ta hada ta barshi saman wuta bayan ta rage wutar ta juye ruwan tea a flask sannan ta wuce sama. Ummi kuma ta karasa soye dankali ta kai dining. Tana shiga wanka ta shiga tayi, ta fito ta dauki Haidar tai masa wanka sannan ta gyara gadon ta shirya Haidar ya fice itama ta zauna ta shafa mai ta dauki wata doguwar riga pink kala ta saka, Mayafin ta three in one ta saka blue black sannan ta dauki jakar ta da takalmi ta shafa turare mai sanyin kamshi ta fito falo. Kasa ta sauka tai breakfast sannan ta koma sama dan yiwa Ummi Sallama. Haidar ta gani kwance yana wasa akan gado tace "Ummi na gama zan tafi." "Kin karya?" "Eh Ummi." "To a dawo lafiya Allah bada sa'a a tsaya ai karatu dan Allah banda abokan banza." "Insha Allahu." "To kiyi addu'a kan ki fita." "To Ummi sai na dawo." Ta karasa wajen gado ta sumbaci Haidar a goshi sannan ta wuce tana daga masa hannu har ta kai kofa ta juyo tace "Lah Ummi an bamu wani aiki zanje a typer min ban san nawa zai ci ba in na dawo zan fada miki." "Allah bada sa'a." Sannan ta fita Aliyu ta gani zai shigo sanye yake cikin wando baki da shiga long sleeve peach sai top din rike a hannun sa. Kan ta a kasa ta durkusa tace "Ina kwana?" "Lafiya lou." Ta mike ta fita da sauri. Tana fita ya shiga ya zauna a gefen gado Haidar ya mike yace "Good Morning Dad!" "Morning My Son ya kake?" "Alhamdulillah!" Ya durkusa yace "Ina Kwana Ummi?" "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Ya mike yace "Me naji tana cewa zatai a ckul?" "Assignment zata fitar." "System din ta tana daki tin ranar friday na shigo da ita, na manta amman in na dawo zan baki sai ki bata." "To Angode Allah kara budi Allah maka albarka." "Amin! Son ya karya?" "A'ah." "Taso muje kaci abinci na ajiye ka a makaranta." Suka sauka kasa tare sukai karya sannan suka fita. Inna sukaje suka gaisar ta amsa tana fadin "Yanzu kuwa Maryam ta tafi." Mikewa yayi yace "Sai na dawo." Ya fita shi ya kai Haidar makaranta sannan shima ya wuce wajen aiki. A bakin department driver yai parking ta fito, a hankali tace "To Baba Anas sai yamma zan fito zan kira ka in na gama." "Allah bada sa'a." "Amin nagide." Ta wuce, waya ta kai kunnen ta tana dan dube duben tace "Banganki ba." Ta baya taji an rufe mata fuska ta saki murmushi tace "Uhmm to sakar ni kar na fadi." Ta bude tana fadin "Ya akai kika so ki makara?" Murmushi tayi tace "Hajiya Inna da kyar na fito." "Wallahi kinji dadin ki Maryam ina ma nice nake tare da Kaka ta wallahi da na more shiyasa nake son nazo gidan ku muyi ta shan hira da Inna." "Hmmm muje kema uwar surutu." "Ni din?" "Eh mana." Suka shiga lecture hall. * Sai karfe uku suka fito Maryam ta kalli Jawahir tace "Yanzu me zamu fara?" "Abinci sai muyi sallah." "Amman yaushe mukaci cake." Ido Jawahir ta zaro tace "Tab wallahi ni yunwa nake ji." "Acici." "Naji jikin ai yana nunawa ke kuwa kowa ya ganki yasan bakya cin abinci." "Ai ba anan yake ba." "Ki ci kiga in baki kiba ba." Suka karasa cafteria wani waje suka shiga wajen mai kyau suka shiga VIP suka zauna, ba kowa a wajen suka zauna nan da masu aiki suka kawo musu ruwa da lemo, Jawahir ta amshi menu ta zabi abinda take so ta mikawa Maryam amsa tayi tai selecting shawarma kadai. Lokacin da aka kawo Jawahir tace "Shi kawai zakici sai fa 6 zamu tafi." "Ta ishe ni." Baki ta cije tace "Zaki sani wallahi Ummi zan fadawa." Dariya tayi tace "Ai dai ina ci." Haka suka ci sai wajen hudu suka fito sallah sukai sannan suka shiga dakin daukar karatu. Sai shida suka fito lokacin drivern su duk suna waje suna jiran su. Sallama sukai kowa ya shiga mota. Tana shiga gida ana kiran sallah ta fito a gajiye ta nufi sashen su, Mama ta gani ta fito zata fita, ganin sun kusa haduwa yasa Maryam tace "Ina yini?" Ko kallon ta batai ba, Maryam tai murmushi ta juya sai ta ga Aliyu rike da hannun Haidar. Haidar ya karaso yace "Adda welcome!" "Thanks!" Ya daga mata hannu suka fice ita kuma tai ciki Ummi na daki tana sallah dan haka Maryam tana lekawa ta koma dakin ta wanka tayi ta fito ta saka kaya marar nauyi tai sallah. Tana zaune tana tsabihi har akai isha'i sannan ta mike tayi sallah ta idar tai addu'a. Littafi ta dauko tana aiki a ciki har karfe tara sannan ta mike ta bude firij ta dauki nono ta sha ta koma ta zauna tana matsa kafafun ta. Kofar dakin aka bude Ummi ce, ta shigo Maryam ta dago ta shagwabe fuska. Ummi ta karaso tace "Ya akayi daughter?" "Ummi na gaji bayana ciwo yake da kafata." Jakar system ta ajiye tana fadin "Sannu." Ta isa gaban mirrow ta dauko man zabi ta karaso ta lakata ta shafa mata a kafa tana fadin "Sannu me kikai?" "Zama kawai." "Sannu." Ta fada tana matsa kafar ta. Zamewa tai ta kwanta tace "Me kika ci?" "Nasha Nono." "Shi kadai daughter nayi pepper chicken nasa a kawo miki?" Kai ta gyada ta mike tace "To ga kyauta nan daga Yayan ki sai kije ki masa kyauta." Jakar ta kalla Ummi tace "Eh!" Murmushi ta saki, taja jakar tace "Kai Alhamdulillah nagode sosai kuwa Yaya kamar yasan ina so. Allah saka da alheri." "Amin." Ummi ta fada. Har ta bude kofa Maryam tace "Ummi!" Juyowa tai tace "Dazu an min aikin 1500 ya amsa." "To Daughter ba da kudi a account ba, komai kikai sai kin fada min kudin kine fa in ya kare ki min magana zan dada miki ke dai kiyi duk abinda kikaga ya dace." "Nagode Ummi." Ta juya ta fita. Tana kwance akai knocking ta mike ta karasa mai aikin suce rike da plate da lemo amsa tayi tai mata godiya sannan ta koma shi taci ta sha lemon sannan ta mike ta wanke hannu. Haijab ta saka fuskar ta dauke da murmushin farin ciki ta fita rike da plate din ba kowa a falon kasa dan haka ta wuce kitchen ajiyewa tayi sannan ta fito ta nufi dakin Aliyu. Da sallama ta shiga falon yana zaune akan three sitter Haidar yana kwance a gefen sa yai bacci sai system dake gaban sa yana aiki akan stool. Amsawa yai ba tare da ya dago ba. Ta shiga ta zauna a kasa tace "Yaya!" A yadda ta kira sunan sa sai da gaban sa ya fadi ya dago yana kallon ta, da lumsasun idanun su, ba tare da ya amsa ba, tace "Yaya bani da bakin godiya a wajen ka, domin godiya tai kadan akan abubuwan da kake min, " Hawaye ne ya zubo daga idon ta amman murmushi take, tace "Abu da zan kasance ina maka shine addu'a baki na ba zai tabai daina maka addu'a ba, zan kasance kullum cikin maka addu'a Allah jikan Anty Maryam, Allah ya baka madadin ta, Allah ya saka maka da gidan aljanna, yasa ka gama da duniya lafiya, Allah ya maka tukwici da gidan Ajanna. Nagode sosai Yaya Allah ya biyaka." "Amin Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum menene na kukan to?" Ya fada cikin muryar mai sanyi dasa nutsuwa, tare da jingina kan sa da kujera. Kai ta girgiza yace "To tashi kije sai da safe." Ta mike ya kalli Haidar da ke bacci yace "Zaki iya daukar Haidar?" Kai ta gyada, yace "Zo ki dauke shi." Ta karasa ta dauke shi ta fita, ya bisu da kallo tare da lumshe idon sa wani murmushi ya saki wanda kumatun sa suka lostsa, lips din sa dan taune yana mai shafa sumar kansa. *** Sam Maryam bata da matsala a fanin komai, gida sai abinda take so Ummi ke mata, haka ma Inna sosai take ji da ita dan har snacks take mata in taje gaishe ta da safe ta bata, a fanin karatu ma basu da matsala dan suna ganewa sosai. Yawanci karfe biyu zuwa uku suke gama lecture sallah kawai suke su nemi abinci daga haka zasu shige library ita da Jawahir suyi ta duba abinda akai in da inda basu gane ba suje wajen na sama dasu su ganar dasu dan haka basu da matsala yawanci sai shida suke dawowa gida. Drivern ta kawai take kira nan da nan zaka ganshi sai dai in na Jawahir ya riga zuwa kan nata wani lokacin suke dire ta gida, shima da ta koma wanka kawai takeyi tai sallah zata Kara daukar littafai ko kasa bata fiya sauka ba dan bata cin abu mai nauyi da dare duk abinda take so light akwai a firij in ma babu kan ta shigo zata siya Wanda in wata yai Kuma ko weekend Yaa Aliyu sukan fita da Haidar suyo shopping to itama ba a barin ta a baya za a siyo mata abubuwan da take so, takanyi sati daya bata saka Yaa Aliyu a idon ta ba wani lokacin sai weekend Shima in ta leka wajen Inna to anan tafi ganin sa amman a sashen su kan ta ganshi sai ta sauko kasa wanda a yanzu bata fiya ba, bama da taga wani lokacin kamar in ya ganta yake barin wajen. Dan sau da dama da taje waje zataga ya mike tin bata damuwa har ta fara damuwa, gaisuwa ma a share take gani yana amsa ba, wanda hakan kesa ta shiga damuwa amman kuma ita ta rasa me tai masa da ya canja mata tasan da ba haka yake mata ba. Bangaren Farouk kuwa in yai kwana biyu bai ganta ba zai kira su sha waya ko in ya ganta a online su dan taba hira wani lokacin kuma suna haduwa a wajen Inna. Haidar kuwa daman in ya dawo karfe biyu isilamiyya yake zuwa wanda karfe biyar yake dawowa, a falo zaku ganshi yana damun Ummi da surutu wani lokacin shida ko shida saura Yaa Aliyu ke dawowa da gudu Haidar yake nufar sa ya rumgume shi, Shima haka zai dauke shi yana tambayar sa ya makaranta yaron yai ta masa dariya daki sukeyi ya dire shi akan gado ya cika masa gaba da kayan ciye ciye da na wasa shi kuma yakan shiga yai wanka kan ya fito an kira magarib tare suke tafiya masallaci har sai anyi isha'i suke dawowa suci abinci tare, wani lokutan tare suke kwana da Haidar bama week wanda sauran ranakun kuma yana tare da Ummi ko Maryam bama in Abba baya gari. *** *** *** *** Bayan wata biyu *** *** *** *** A haka rayuwa take tafiya har su Maryam suka zana jarabawar first semester, lokacin da suke jarabawar ko bacci batayi abinci ma ba sosai take samun damar ci ba, sati biyu sukai suka gama jarabawa sannan aka basu hutun sati uku. A gajiye ta shigo gidan dan ranar suka gama jarabawa kana ganin ta zakaga yadda ta fada, har bakin kofa driver ya ajiye ta, ta fito tana fadin "Baba nagode kai ma ka huta na kwanaki." "Allah dai ya bada sa'a Hajiya." Tsayawa tai tace "Haba Baba ni dai kace min yarka ko jikar ka yafi." "To 'yata. Allah bada sa'a aje a huta gajiya." "Nagode Baba kaima Allah huce gajiya." Ta fada tanayin hanyar kofar, budewa tayi ta shiga da sallama. Akan kujera ta fada tana sauke numfashi. Ummi ce ta sauko rike da waya, tana fadin "Daughter ta, ta dawo." Ido Maryam ta bude tana kallon Ummi da murmushi akan fuskar ta tace "Eh Ummi." Karasowa Ummi tayi ta zauna a gefen ta, tare da janta zuwa jikin ta, tana fadin "Allah bada sa'a yanzu kije kiyi wanka ki samu ki dan kwanta kan la'asar, zamu fitar da rana muje mu rakaki shakatawa na gama jarabawa." "Ina godiya Ummi na. Amman kan nan kunyi waya da sitti?" "Munyi menene?" "Naga missed call nata na kira bata shiga." "Ta miki albishir ne?" Kai ta girgiza tace "A'ah." "To in kunyi waya ta fada miki." Fuska ta shagwabe tace "Ni dai Ummi ki fada min?" Hancin ta Ummi taja tace "In Haidar yaga kina haka ya miki dariya." "Ina ruwa na ba Ummi na nakewa haka ba, shima yaiwa Abbin sa." "Ai yana abinda yafi naki." "To nima zan nayiwa Ummi na da Abba." "Tashi dai kije ki watsa ruwa yau na shirya miki special dishes." Rumgume Ummi tayi, ta sumbace ta a kumatun tace "Shiyasa nake son ki Ummi na." Ta mike tana daukar Jakarta da mayafin ta, tayi sama. Tana shiga ta kwanta saman gado tana salati Ido ta lumshe tana hamma tare da rufe bakin ta, tana salati, ido ta lumshe tana addu'a a cikin zuciyar ta, take bacci ya dauke ta. *** Kiran sallah la'asar shi ya tashe ta, ta mike tare da yin mika hadi da hamma, ta rufe bakin ta tana salati ta mike ta cire kayan ta, sannan ta daura towel bandaki ta shiga. Tana fitowa ta tsaya ta shafa mai, tai kwaliyya mai kyau ba mai yawa, sosai tayi kyau ta manta rabon da tayi kwalliya, dorowa ta bude ta dauki wata daguwar riga da Yaa Aliyu ya siya mata lokacin da sukaje shopping taki daukar komai. Rigar mai kyau da tsada pink-peach duk jikin ta stone ta saka under wears ta daura ta sosai tai kyau mayafin ta dauka ta yafa ta fesa turare wani half cover ta saka kalar rigar ta saka silver agogo tai kyau. Sallah tayi sannan tai addu'a da azkar ta fita. Tin kan ta sauka ta fara jiyo magana sama sama a kasa, murmushi tayi ta sauka tace "Yau baki mukayi?" *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:06] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 3 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Tana sauka taga wasu mata dayar babbace amman wacce zatai shekara hamsin saura sai ta gefen ta wacce ba zata wuce shekara talatin ba zaune suna hira, daga gani kasan jini daya ne dan kamar su daya dukka sai dai Ummi da Dayar da suke manyanta, da fara'a ta karasa tana fadin "Mami." Wacce aka kira Mami ta dauke kai tana fadin "Ba wani Mami." Jikin Mami ta kwanta tana fadin "Kiyi hakuri Mami wallahi makaranta shiyasa bana shigowa." Wacce take zaune ta kalla tace "Kinji ko? Wai makaranta Muna gida daya sai nai wata ko satituka ban ganta ba in ba fita zanyi ba ko na shigo nan." Jikin Mami ta shige tana fadin "Mami na kiyi hakuri Ummi ki sa baki " Ummi na murmushi tace "In zata yadda amman Wallahi Yaya tin kan exam Maryam bata dawo sai magariba, ko Inna kullum sai ta shigo ta min mita." Baki ta gefen Ummi ta tabe tace "Bare ni dake nesa ko ziyara ta batayi a shekara bai fi tazo sau daya ko biyu ba." "Haba Anty Asiya ai da cewa nai gidan ki zan zo hutu ko Ummi." Kai ta dauke. Ummi tace "Haka tace." Mami tace "To ya jarabawar Daughter?" "Mami Alhamdulillah." "Allah kawo sakamako mai kyau " "Amin!" Duk suka amsa. Mami ta taba jikin ta tace "Ya naga duk ta rame?" "Jarabawa Mami." "Gata nan ko abinci bata ci kwana take karatu." Ummi ta fada. Mami tace "Ah Daughter kina cin abinci da bacci kinji zakici jarabawa ai kina karatu." "Allah yasa." "Amin." Sallama suka jiyo ta Aliyu da Haidar duk suka amsa, Haidar ya shigo a guje yai wajen Ummi, Ummi ta dauke shi ta rungume Mami tace "Au mu ba asan damu ba ko mai gida?" Saukowa yayi ya tafi wajen Mami a guje yana fadin "Oyoyo." Ta dauke shi tace "Ya makaranta Mai gidan?" "Fine." Ta shafa kan sa. Kallon Anty Asiya yayi ya mike a guje yai wajen ta tace "Yaro na ya girma." Ta sumbaci goshin sa yace "Ina yini Anty?" "Lafiya lou Son ya school?" "Lafiya lou. Ina su Abid" "Suna can gidan Garnny din su." Ya tashi ya nufi Maryam yana fadin "Addah ya exam?" "Alhamdulillah!" "Allah bada sa'a." Ya fada da kalar bakin sa da magana bata fita sosai. Kallon sa tayi tana murmushi. Aliyu ya karaso sanye yake da milk kalaf wando sai riga longsleeve coffe kala, sai tashin kamshi yake, Ummi a kalla yace "Ummi barka da gida." "Yauwah ya aiki?" "Alhamdulillah!" Anty Asiya ta dago tace "Sannu da zuwa Yaya." "Yauwah ya gidan da yara?" "Lafiya lou." Ya kalli Mami yace "Mami Ina yini?" "Lafiya lou ya gida?" "Lafiya lou " "Sannu da zuwa Yaya." Maryam ta fada tana wasa da Haidar." "Yauwah ya exam din?" "Alhamdulillah." "Allah bada sa'a." "Amin nagode." Yayi dakin sa Haidar ya bishi a guje. Mami ta bisu da kallo tana fadin " 'Da da Uba kenan." Sukai murmushi Ummi ta kalli Maryam tace "Bafa kici komai ba." Ciki ta shafa tace "Zanci anjima" "Kin gani ko Yaya." "A'ah daughter kina cin abinci kinji ko?" Kai ta gyada. Farouk ne ya shigo da sallama, suka amsa Mami tace "Aisha duk kin dauke yara dai bangaren mu kullum shiru mu ke kuwa kalli fa." Ummi tai dariya tace "Shi wannan yanzu zai fita Haidar din ne dai." Ummi ya gaishe tare da Mami sannan ya zauna, Anty Asiya ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ya yaran. Sai kuma tace "Wai na gaishe shi Ummi ba na girme shi bama." Filon dake kusa dashi ya cilla mata yace "Kin rainani wallahi Asiya." Ummi tace "Ba dole ba ta ganta da yara kai kana zaune ba auren ma." "Kai Ummi." Ya fada yana bata fuska. Maryam tai dariya ya juyo ya dan harare ta sai kuma yace "Ya jarabawar?" Mami tace "Oh Daughter Yar gata kowa bai manta ba." Tai murmushi ya mike yace "Ummi Yaya fa?" "Yana ciki." Ciki yayi yana shiga ya tadda shi ya fito daga wanka shi da Haidar. Mai ya shafa masa ya saka masa wasu kayan, sannan ya kalli Farouk yace "Daga ina?" Haidar ya dauka yace "Na shigo gaishe da Ummi ne." "Ok!" Ya saka kaya ya fito yace "Lokacin sallah muje." Suka fice gaba daya, ba kowa a falon Mami ta tafi sai Maryam da Anty Asiya dake dakin ta Ummi na dakin ta Sai da suka idar suka fito tare sukaci abinci da Maryam sannan suka tafi bangaren Inna. Inna na zaune akan sallaya da carbi a hannu tana ganin Maryam tace "Ke 'yar nan ciwo kikayi ne?" Zama Maryam tai tana murmushi tace "A'ah." "Kinga yadda kika rame kuwa ko abinci ne Aishan bata baki." Anty Asiya tayi murmushi tace "Haba dai Inna sai a hanata abinci." "To gata nan duk ta kare, ya jarabawar?" "Inna mun gama" "Allah bada sa'a." "Amin." "Me zan samu yar tsohuwa." Cewar Anty Asiya. Inna tace "Ce nake tin da kika shigo kika gaishe ni kuka fice ke ko yar hirar nan ma bazaki zo mu yi ba." "Hajiya Inna zuwan ki daban ne zan zo na yinar miki." "Kan kizo, zamu zo ni da Maryam." "Allah ya kawo ku daman Inna kin jima baki zo ba ita kuwa wannan sai shekara shekara." Maryam tace "Kai Anty nafi zuwa gidan ki fa akan Anty Hanna." Wayar Anty Asiya ce tai kara tana dubawa taga mijin tane Maryam ta kalla tace "Tashi muje ki tayani hado kan kayana wajen Mami dan nasan yanzu zaki ganshi." Ta fada tana kai wayar kunnen ta fita sukai suka nufi Sashen farko na gidan wanda yake duk yafi sauran girma ko ciki suka shiga bangaren Mami suka shiga tana zaune tana kallo a TV ta dago tace "Juya ki koma." Karasowa Maryam tayi tace "Haba Mami ni ana ma zan yi hutun nawa." "Naga kafar ki ma." Sukai Dariya. Anty Asiya ta kalli Mami tace "Mami na dauki jug din?" "A'ah wai meyasa kike min haka Asiya ace ni kenan ban isa naiwa miji na kayan gari ba sai kina dauken." "Mami ai ku, kun tsufa" Maryam ta fada. "Oh kema haka zakice ko? Zanci gidan ku, kuma ba zan bayar ba to ni kada na tararayi nawa mijin ko?" "Ah Haba Hajiya Mamin mu dan Allah ki bata." Hararar Maryam tayi tace "Kuje daki na fito miki da naki saboda haka yanzu in naga abu nake siyar har bakwai sai kace mai siyar wa." "Mami bakwai kiyi me dashi?" "In na siya dole na siyawa yar uwata." Hada ido Maryam da Anty Asiya sukai suna murmushi, Mami tace "Gani da yan mata biyu ga ku uku da bakwa barina da abu shiyasa kullum cikin kashe kudi nake." Karasawa sukai wajen Mami suna fadin "Allah sarki Mamin mu Allah kara budi muna son ki Mamin mu." "Allah muku albarka." Wayar Anty Asiya ce tai kara ta dauka tana fadin "Ba dai ka karaso ba." Yace "Eh ina sashen Inna." "Ok sai ka shigo." Ta mike ta shige daki Maryam tabi bayan ta. Da katuwar leda ta fito suka shiga Kitchen Mami tace "Me kuma za a daukar min anan." Basu jima ba suka fito suna dariya. Mami tace "Allah in ma wani abu kuka dauka har gidan zan aiko a dauken abu na shikenan ni bazan abun arziki ba ke da son kyale kyale " "Hajiya Mami." Anty Asiya ta fada sannan a karasa tace "Bari naje nasan Abbin Abid sai ya tsaya a main falo." Ta fita tare suka shigo ya gaishe da Mami sannan ya mike ya fita. Maryam ta dauki ledar Anty Asiya sukai sallama da Mami sannan suka fita. "Zo muje nayiwa Mama Sallama." Waje Maryam ta nufa tace "A'ah je ki fito." Ta kalle ta, ta dauke kai. Mota ta saka kayan suka tsaya ita da mijin Anty Asiya suna ta hira bata jima ba ta fito suka nufi sashen Ummi dan ya gaishe ta Anty Asiya kuma tai mata sallama. A falo suka same ta suka gaisa yana tambaya ina su Aliyu tace "Tinda suka tafi sallah kila suna masallaci." "Tare suke da Abokina kenan." "Suna tare." Yace "To zamu tafi Ummi sai da safe." "Ku gaida gida ku gaida su Abid." "Zasuji." Suka mike suka tafi Anty Asiya ta shiga taiwa Inna sallama. Inna tace "Yanzu mai gidan naki yazo ya cika ni da alheri kai Allah masa albarka ya kara budi dai." "Amin Hajiya Inna ina zuba ido fa." "Zamuzo ai tinda abokiyar fitar tai hutu." Tai mata sai da safe suka tafi. Har mota ta rakata Abbin Abid ya debi kudi da yawa ya mika mata taki amsa sai da kyar tai godiya sannan suka fita ita kuma ta juya tai bangaren su. Ummi ta direwa kudin, Ummi tace "Na menene?" "Yaya Nazir ne ya bani." "To madallah angode sai kije ki ajiye." Zamewa tayi ta kwanta akan cinyar Ummi tace "Ki ajiyen Ummi." Ta dauki remote ta canja channel. Suna cikin kallo su Yaa Aliyu suka shigo zama su sukai shida Haidar. Maryam ta gyara kwanciyya tace "Ummi yaushe Abba zai dawo." "Kila sai weekend." Baki ta tura tace "Yau fa Talata da saura gaskiya." "Ai kamar yau ne." "Allah dawo dashi lafiya." "Amin." Ummi ta fada ta kalli Aliyu tace "Abinci fa?" Dining ya kalla yace "Yau na gaji ne wallahi." "Maryam ta zubo muku to." Shiru yayi wannan yasa Ummi tace "Zubo musu kinji Daugther." Ta mike ta zubo musu sannan ta nufi sama tace "Bari naje na kira Jawahir." Da kallo ya bita ya dawo da kallo kan abinci suka fara ci shi da Haidar tas suka cinye suka sha lemo da ruwa. Tana shiga daki ta fada saman gado tare da fadin "Wash Allah na" Wayarta, ta janyo ta fara dubawa missed call din Jawahir ta gani har guda biyar kira ta farayi amman sai da ta kusan tsinkewa aka dauka, cikin muryar bacci tace "Ina kika shiga ina ta kira tin dazu?" "Wallahi ina kasa badai har kinyi bacci ba?" "Wallahi ke baki kwanta ba." "Bana jin bacci ai kece kasa." "Naji ai bacci duniya ne. Ni sai da safe mayi waya" "To Allah tashe mu lafiya." "Amin." Ta kashe wayar ta mike itama ta shiga ta watsa ruwa tazo ta saka kayan bacci tare da yin sallah. * Tsaye take a bakin kofar dakin Inna, sanye da doguwar riga ta material black wanda akai zanen gida gida da fari da maroon, maroon kalar mayafi ta yafa sai cover shoe maroon da hancbag din ta rike a hannun ta, sai dayan hannun da take rike da waya, sai kamshi take, duk da batai kwalliya amman tayi kyau fuskar ta tai fresh alamun tana cikin jin dadi, Inna ce ta fito yafe da mayafi tana rufe kofar dakin nata, sai da ta gama ta karaso tace "Na tsayar dake ko? Kayan wutar na kashe Kar naje na jawo gobara tinda bama gidan, Ina kuma Haidar din?" "Yayi can gate." "To muje." Ta fada tana daukar ledar dake gefe amsa Maryam tayi Inna tai gaba Maryam na biye da ita a baya. Suna fita compound suka wuce parking space dake can gefen gate. Haidar suka gani cikin motar Aliyu, Inna tace "To Ina driver kira sa yazo mu tafi." Bakin gate ta nufa ta leka ta kira shi, ta karaso tace "Taho mu tafi Haidar." "Ina zaku?" "Gidan Anty Hanna." "Kuzo na sauke ku." To kawai tace ta nufi wajen Inna, Inna tace "Hanasa zuwa yai ko?" "A'ah wai muje ya Kai mu." Driver ta kalla tace "Malam Anas bari muje Aliyu ya dire mu kai zaman ka sai mun dawo." "To Hajiya Allah kiyaye ya tsare a gaishe su." Suka nufi wajen motar duk suka shiga baya, motar ya tayar suka dauki hanya gidan Anty Hanna Wata unguwa suka shiga mai kyau da tsari wanda gidajen manya ne duk layukan ma kwalta ne a kai. Horn yai a wani katon hadadden gida, Mai gadi ya leko yana ganin Aliyu ya hau bude gate sai da ya bude Aliyu ya tura hancin motar cikin gidan ya nufi can gefe yai parking. Yaran gidan jin mota suka fito a guje su hudu ne, suna ganin Inna suka tafi suka rungume ta suna fadin "Oyoyo Inna." Ta kama hannun Yar karamar tace "Takwara ta." Ta dauke ta. Sauran sukai wajen Maryam suna fadin "Oyoyo Anty." Da dai dai ta rumgume su, sannan suka karasa wajen Haidar Baban ne yace "Lah Uncle." Yai wajen sa a guje ya karasa yace "Ina yini Uncle?" "Lafiya lou Arfat ya school?" "Alhamdulillah." Ya shafa kan sa sauran sukazo suka gaishe shi. Ya kalli Maryam yace "Ni na tafi." "Bazaka shigo ba" Kai ya girgiza ya shiga mota. Anty Hanna ce ta fito cikin shigar ta mai kyau tace "Oyoyo Inna ta." Ta rumgume Inna, ganin motar Aliyu na reverse yasa ta saki Inna da sauri ta karasa tace "Yaa Aliyu ba dai tafiya ba." Ya tsaya, yana sauke glass din motar, ta karasa tace "Haba ai ka shigo ka sha ko ruwa ne ko?" "Sauri nake nagode." "Dan Allah Yaya ka shigo kai fa ba zuwa kake ba kuma yau kazo ai ka shigo mu dan gaisa dan Allah." "Ok!" Ya gyara parking lokacin su Inna har sun shige, ya fito sukai cikin gidan tana fadin "Amman naji dadi wallahi." Suka shiga main falon wanda yake katon gaske da set din kujeru sun fi set uku, ta Kara dosar wata Kofa yace "Ki barni nan Hanna." "Please Yaya." Yabi bayan ta. Wani hadaden falo suka Kara shiga wanda anan su Inna suka yada zango ta shiga ta nuna masa kujera tana fadin "Sannu da zuwa." Tayi kitchen da sauri sai ga masu aikin ta nan dauke da tray tray daya flask ne akai dayan Kuma wasu bowl ne masu murfin glass sai dayan kuma lemuka ne da ruwa da cups da plate and spoon. Anan kasa suka zube kayan suka gaida su Inna sannan suka koma ciki. Hannah ta fito tana murmushi tare da fadin "Sannun ku da zuwa." Ta karasa ta fara zuba masa lemo a cup ta mika masa tace "Ina yini Yaya?" "Lafiya lou ya gida da yaran." Ya fada yana kurbar lemon. "Alhamdulillah." Ya kalli Islam mai sunan Inna yace "Zo nan Yar tsohuwa." Ta karasa ya dauke ta yarinya ce yar shekara biyu Wanda Haidar ya girme ta da shekara daya. Yace "Ke bakya magana?" Hannah tace "Sai ta sake daku tukkuna." Ta karasa wajen Inna tace "Sannu Yar tsohuwa ya hanya?" Suka gaisa sannan Maryam ta gaishe ta tana tambayar yasu Ummi da Mami. Rabin cup yasha ya ajiye ya mike yace "Bari na tafi." Ta karaso tace "Ah haba Yaya bakacin komai bafa." "Ke wannan uban kayan da kika dire kadai ya sa mutum taji tsoron cin abinci sai kace wanda mutum hamsin zasuci. Ni na koshi." "Dan Allah Yaya ka zauna ko cake ne kaci." Kai ya girgiza ya zura hannu a aljihu ya zaro yan dubu dai dai sababbi fil ya kira Arfat yace "Ungo." Ya bashi guda biyar biyar sannan ya bawa Sharifat sai Annuwar da Islam har da Haidar duk suka hada baki su kace "Mungode Uncle Allah Kara budi." "Amin." Ya fita dauke da Islam Haidar na rike da hannun sa, Hannah tabi bayan sa har wajen mota suka karasa ya shiga ya debo kudi masu yawa ya mika mata tace "Har dani Babban Yaya nagode Allah kara budi. Allah jikan Anty Maryam." "Amin." Ya mika mata Islam ya kamo Haidar yace "Sai Kun dawo kaji my son." Hannu ya daga masa yace "A dawo lafiya Abbi." Ya rufe kofa yai reserve ya nufi gate ya fita hana fita motar mai gidan na karasowa dan haka ya tsaya a bakin gate da sauri Sagir ya fito ya karaso wajen Aliyu yace "Yau Babban Yaya ne a gidan kenan." Ya bashi hannu suka gaisa sannan sukai sallama ya koma mota ya wuce shi Kuma ya shiga gida. Yana parking ya nufi cikin gidan a falo ya samu su Inna nan ya zauna suka gaisa aka cigaba da hira da shi dan Sagir ba ruwan sa shi ko da su Mami yaje hira yake musu bare kuma Inna kaka da Maryam kanwa. Su Haidar kuwa suna can ana ta wasu abinsu. A gidan suka yini sai da sukai magariba suka ci abinci sannan suka fara haramar tafiya har gate duk suka fito dan rakasu. Hannah ta bawa Maryam babbar leda tace "Ke da Haidar." Ta bawa Inna wata leda tace "Nagode sosai Inna Allah kara lafiya da nisan kwana." "Amin." Sagir kuwa a envelope ya bawa kowa kudi da kyar suka amsa suka shiga mota drivern gidan ya tafi kai su gida. Suna zuwa gida suka tadda Aliyu ya dawo daga masallaci zai shiga gida. Tare suka karasa ya dauki Haidar sukai part din Mami, Maryam kuma ta raka Inna sannan ta fito ta koma bangaren su. Ummi ta Sama a falon sama ta Karasa tace "Yau kuma Ummi kina sama?" "Gidan duk da Dadi bakwa ban." "Ya gida?." "Alhamdulillah." Ya dire Mata ledar tace "Anty Hannah ta bani sai Yaa Sagir ya ban wannan." Ta mika mata, bude ledar tayi turaruka ne sai wasu fashion na dankunne da sarka da agogo da abin hannun sai kaya na Haidar Yaa Sagir kuma 20k ya bata. Ummi tace "Allah ya saka da alheri, dauki ki kai daki." "Ummi ki dauki turaren mana." "A'ah kiyi amfani da abun ki." Murmushi Maryam tayi ta nufi dakin ta ajiye a kan mudubi ta wuce bandaki ta watsa ruwa ta fito tayi sallah sannan ta fita falo, daga ita sai kayan bacci. Kusa da Ummi ta zauna tace "Anty Hanna na gaishe ku." "Muna amsawa. Saura gidan Bilkisu " Fuska Maryam ta taba. Ummi tace "Itama fa 'yar uwar kice kuma ba zataji dadi ba in taji kinje gidan su Asiya da Hannah bakije gidan ta ba." "To Ummi ai kinsan Mama bata so Ina zuwa gidan ta." "Amman me Abbi yace miki." Fuska ta tabata, ki daure kije kinji?" "To Ummi." "Gidan su Jawahir fa?" "Ummi nifa ban son zuwa gidan su, gidan su gidan 'yan gwamnati a hanani shiga ma." "A'ah Maryam ba mai hanaki ki daure kije mata dai ita bini bini tana nan ba ga ita ba, baga mahaifiyar ta ba ga alheri amman ke kinki kije haba Maryam." "Zan samu naje insha Allahu kan mu koma." "Allah ya yadda." "Amin " Sallamar Aliyu sukaji da sauri Maryam ta mike tai dakin Ummi, Ummi tai murmushi tana amsa sallamar ya karaso ya zauna yace "Ummi yau kuma ban kika shigo?" "Eh gidan ba dadi nayi kewar Haidar." Yai murmushi Haidar ya karasa yqce "Ummi ki kira min Abba." "Oh Abba zan kira maka?" Ya gyada kai ta dauki waya ta kirasa bayan sun gaisa tace "Wai Haidar ne yace a Kira masa kai." Abba yai murmushi yace a bashi nan Ummi ta bashi ya dinga ma Abba surutu yace "Abba yaushe zaka dawo?" Kwanciyya Maryam tayi a dakin daga haka bacci ya dauke ta. Sai wajen goma Aliyu ya tafi. Daki ta shiga taga Maryam na bacci dan haka ta canjawa Haidar kaya sannan suka wuce dayan dakin suka kwanta. ** Washe gari Yaa Farouk ya kaita gidan Anty Bilkisu duk yadda Bilkisu ke son Maryam ta sake da ita kamar yadda take sakewa da sauran 'yan uwan nasu, amman bata sakewa sai dai su dan taba hira suna hirar ne tace "Maryam ki cire yadda Mama ke miki dan Allah ki dauken kamar yadda kika dauki sauran 'yan uwan namu, Ina gani fa ko Najwa da bata kasar kin fi sakewa da ita akai na, Mama tana da matsala amman mahaifiyar mu ce muna hakuri muke da ita ban san me yake damun ta ba sam." Hannun ta Maryam ta kamo tace "Haba Anty Bilkisu ni daya na dauke ki da Anty Asiya da Anty Hanna, ki daina damuwa kuma Mama ai uwa tace nima." "Nagode. Amman meyasa bakya son zuwa da Haidar?" "Sun fita da Yaa Aliyu ne." "Shima Yaa Aliyu bai zuwa sai dai mukan yawan yin waya." "Hmm in dai Yaa Aliyu ne can ma ba zuwa yake ba, ke sai ya kira ma bai kira su ba haka Najwa ke mita kullum tace ita tana wata duniya bai kira sai dai taji suna waya da sitti. " "Allah sarki ya karatun kuwa?" "Alhamdulillah sauran kwana biyu ma mu koma." "Allah taimaka to." "Amin." Haka suka dinga Hira har akai la'asar ta kira Yaa Farouk yazo ya dauke ta amman bashi ya zo ba sai bayan magariba. Sukai sallama ta fito ta shiga mota suka dauki hanyar gida Suna tafe yace "Yaushe zaki gidan su Jawahir ne?" "Uhmm Yaya ni ban son irin wadan nan gidajen." "Saboda me?" "Gidan 'yan siyasa bana son Ina shige musu" "Jawahir din?" Kai ta gyada yace "Amman ba amana, ita kullum tana gidan ku." "Nima wata rana zani amman ba yanzu ba." "To Allah kaimu." "Amin." "Me kike so mu siya kan mu koma gida?" "Ni ba komai." "Ko furar." Shiru tai tana murmushi, yace "Da nama." Dan hararar sa tayi tace "Tinda ga kwadayayya ko?" "A'ah nifa bance ba." Ya isa wajen da ake ajiye mota yace "Zaki shiga?" Kallon wajen tayi ta girgiza kai tace "A'ah je ka dawo." "Ok Ina zuwa." Ya fita, harabar wajen take kalla bai Jima ba ya dawo ya bude mota ya shiga ya tayar suka bar wajen. Suna shiga gida yai parking ta fita, ya biyo bayan ta, da leda a hannun sa, suna tafiya tana gaba yana bin ta a baya wayar sa ce tai kara yana dubawa yaga Mama ce Ido ya lumshe ya daga kai yana kallon taga inuwar ta ya hango ya kai wayar kunne tace "Kazo nan." Wayar ya kashe yace "Maryam!" Juyowa tayi, ya mika mata ledar yace "Gashi sai da safe." Amsa tayi tana murmushi tace "Nagode Yaya " Shima murmushin ya sakar mata ya juya ya nufi sashen su, ba kowa a falo dan haka ya nufi bedroom din da sallama ya shiga amman Mama bata amsa ba, ya zauna yace "Gani Mama." Wani kallo ta jefa masa sannan tace "Menene ma a tsakanin ka da ita?" "Wa?" "Waccan yarinyar." Kai ya sosa yana murmushi yace "Mama....." Hannu ta daga masa tace "Yi min shiru. Nasan me zakace min, to kada ka soma dan wallahi na haramta aure tsakanin ka da wannan shegiyar yarinya ban aminta ba." "Saboda me Mama?" "Saboda bana so...." Ta mike tare da juya masa baya yace "Mama." "Fita ka ban waje Farouk." Ya mike ya zagayo gaban ta yace "Kiyi hakuri." Sannan ya fita a dakin. Abbi ya gani a bakin kofa ya juya yabu bayan Abbi har zai wuce Abbi yace "Zo nan Farouk." Suka zauna a nan falo yace "Meyake faruwa?" "Abbi akan Maryam ne wai dan ta ganmu tare shine take zaton soyayya muke." "Kai soyayya kuka?" Kai ya girgiza dan yasan in har Abbi yasan yana son ta to an gama shi kuma baya son tashin hankali. Abbi yace "Maryam 'yar uwar kace dan haka ka cigaba da kyautata mata, kada ka soma nuna musu bambamci tsakanin ta dasu Aisya." Kai Farouk ya gyada, Abbai yace "Tashi kaje." Ya mike yace "Sai da safe. Dakin sa ya shiga ya fada saman gado yana tunanin me Mama take yi ne. Maryam na shiga ta ajiye ledar hannun ta da wacce 'Farouk ya siya mata da wacce Anty Bilkisu ta bata, Ummi tace "Daughter 'yar gata 'yan uwan ta." Murmushi tayi tace "Alhamdulillah Ummi, ni kai na shaidace suna sona nima ina son su, ina kewar 'yar uwa Najwa." "Ai fa kila so take sai ta gama sannan ta dawo gaba daya." "To sitti fa?" "Wannan Yayan ku zaki tambaya." "Uhmmm." Ta mike ta dauko plate, zuba naman tayi ta dauki robar fura daya ta fara sha tana Santi, naman ma kadan taci sai furar da ta sha sosai Ummi taci itama sannan ta wuce sama tai wanka tare da alwala tai sallah ta kwanta. A haka suka fara shirye shiryen komawa makaranta. Ranar lahadi tana zaune bayan ta tsefe kan ta, saloon take so taje a wanke mata dan tasan in ta koma makaranta ba lokaci ne da ita ba. Saukowa tai daga bene sanye da doguwar riga abaya baka sai mayafin ta, da ta yafa tace "Ummi zan tafi." Ummi dake zaune ta dago tace "To amman za ai miki kitson ko?" Fuska ta bata tace "Ummi wallahi zafi kitson." "Sai kizo kina damuna da in miki calba ko?" "Ummi itama da zafi fa kike min." "Oh da zafi nake miki ko to ban sakewa." Jikin Ummi ta kwanra tace "A'ah Ummi kiyi hakuri wasa nake." "Shikenan sai kin dawo, na miki transfer kudin." Sumbatar Ummi tayi a kumatu tace "Nagode Ummi Allah Kara budi." Tai mata murmushi ta fita, tana fita ta nufi wajen motar su, Baba Anas ya karaso yana fadin "Kin fito?" Kai ta gyada tace "Kayi hakuri na barka kana ta jira ko?" "Ah ba komai Hajiya." " 'yar ka dai Baba." Yace "To 'ya ta." Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tace.... *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:06] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 4 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tana fadin "Baba Anas tsaya kaga Jawahir." Ya dakatar da driving din yace "Ban lura da ita ba." "Ba komai." Ta fada tana bude motar, Jawahir da har ta Isa bakin kofa tajiyo Maryam na kiran ta da sauri ta juyo, ganin Maryam ta dan hade rai tace "Nifa ba wajen ki na zo ba." "Ah haba Sister ta." Kai ta dauke sukai ciki tace "To me nayi ne wai." Ummi dake ciki tace "Baki tafi ba Daughter?" Ganin Jawahir yasa tace "Ah Jawahir ce sannu da zuwa." Kan Jawahir a kasa ta karasa ciki tace "Wallahi Ummi." Ta karasa ta zauna a kasa tana gaishe da Ummi, Ummi ta amsa tace "Koma sama ki zauna." Ta mike ta koma Maryam ta kawo mata lemo da ruwa ta dan harare tace "Nifa wajen Ummi nazo ba wajen ki ba." Ummi tace "Ai kuwa dai." "Haba Ummi ki sa baki ai nayi niyyar zuwa fa ni ranar me ma ya faru?" "Uhmm ke kika sani " Ummi tace "Ina Momyn taki!" "Tana gida tace a gaishe ki." Zama Maryam tayi tace "Allah yayi ba zamuyi sabani ba." "To Ina ruwa na ko munyi sabanin ma ai ba wajen ki na zo ba. Ina Haidar?" "Yana wajen Yaa Aliyu." Maryam ta bata amsa sannan ta kalli Jawahir tace "Gobe sai school ko?" Share ta tayi, Ummi ta basu waje, a haka dai sai da Maryam ta lallabata har ta sauko suna hirar su tace "Ina zakine wai?" "Gyaran Kai zani dan nasan aka koma ckul sai kuma Allah." "Ai kuwa tashi muje nima ina so a min kitso na jima rabo na da kitso." Ta mike sukaje suka fadawa Ummi sun fita. Jawahir ita tai driving nasu inda ake gyarawa Maryam kai sukaje akai musu wankin kai da kitso har da lalle Jawahir tasa akai musu ta biya kudin shida saura suka fito suka koma gida. Sallah kawai sukai Jawahir tace zata tafi Ummi tace ta tsaya taci abinci da kyar ta tsaya taci sannan sukai sallama. Suna jikin motar ta Yaa Aliyu ya dawo da Haidar da gudu Haidar ya karaso yazo ya rumgume Jawahir yace "Anty yaushe kika zo?" "Na dade gashi har zan tafi." Fuska ya bata tace "Zan zo wata rana kaji." Kai ya gyada ta dauke shi ta dago tana kallo Aliyu da yazo wucewa ya nuna bai ma san da su ba. Jawahir ta ce "Ina yini?" Bai jiyo ba ya amsa, ta sauke Haidar ta bude bayan mota ta dauko wata leda tace "Gashi nan." "Nagode Anty." Ya amsa ya bi bayan Aliyu da gudu Maryam tace "Ka daina gudun nan fa Haidar." Juyowa Aliyu da ya kai kofa yayi ya tsaya ya karasa ya kama hannun sa sukai ciki. Baki Jawahir ta tabe tace "Wannan Yayan naki ya fiya miskilanci da yawa." "Hmmm shi haka yake da Yaa Farouk ne sai kin toshe kunnen ki." Tai dariya tace "Ni da ake boyen shi, wallahi Maryam ko ki fada ko kar ki fada yadda Yaa Farouk ke miki kadai ya nuna soyayya kuke " Ido Maryam ta zaro tana dariya tace "Yaa Farouk din tab kinga budurwar sa kuwa kyakyawa ga aji da ilimi." Tsaki Jawahir ta saki tace "Ta kai ki." "Ta fini sosai da sosai." Baki ta tabe tace "Ba wacce zatafi Besty na." Ta bude mota ta shiga tace "Duk boye boyen ki fa wata rana zai fito fili Besty, ki gaishe shi in ya dawo ki fada masa kuma dole yabi ta waje na in yana son a so shi." "Allah ya shirya ki Besty nagode sosai ki gaida Momy please Ina nan zuwa." Baki ta tabe ta tada motar tace "Ban ji ba." Maryam tai dariya tace "Zama kiji ne." Ta matsa Jawahir ta ja motar ta bar wajen. Sai da taga fitar ta sannan ta koma ciki tana murmushi ita kadai. A haka rayuwa ta dinga gangarawa cikin hukuncin Allah komai yana tafiya dai dai duk da wani abun dole yazo da kalubale a cikin sa kamar bangaren Maryam wanda karatun nasu sai suka ga kamar wahala aka kara masa a haka suke kokari wajen ganin komai suna fahimta, kulawar ta ga Yaa Farouk kuwa sai gaba da ta kara dan ya zamana ko da bai ganta ba zai kira ta, banda kyaututuka da yake yawan mata, ko bata sani ba in yaje shopping sai ya siyo mata kaya duk abinda ya burge shi yaji yana so zai daukarwa Maryam, haka nan yakan yawan aiko mata da kayan ciye ciye ko da basu hadu ba, ita da Aliyu kuwa daga gaisuwa shikenan dan wani lokacin sai tayi sati ma bata ganshi ba duk da zata jiyo muryar sa a falon sama ko kasa ko in tana kitchen zai fita ko makamantan sa, wani lokacin ne ma yakan aika Haidar ya kira ta ya bata wasu sakonnin amman wai hira da sakin fuska a tsakanin su duk babu duk da tana daukar haka a halin sa na miskilanci da na rayuwar da ya tsinci kansa na rashin masoyiyar sa, a haka lokaci ya dinga tafiya har ya kai su Maryam sun shiga level 200 kuma cikin hukuncin Allah da result din su ya fito gaba daya basu da matsala dan 4point ta baro ranar da ta sanar a gida Ummi tai murna sosai haka Yaa Farouk amman Yaa Aliyu sai cewa yayi "Ki dai dage dan yanzu kika fara." Da kallo ta bishi ya mike yai dakin sa. Ummi tai murmushi tace "Haka ne ki dage dan yanzu kika fara karkiga point din ki, kuma ki tsaya wasa." "To Ummi nagode." Yaa Farouk kuwa sai wasa ta yake har da gift ya kawo mata na wata sarka mai kyau tai ta godiya kuwa. A daki Ummi ta samu Yaa Aliyu ta zauna tace "Son." Ya juyo yana kallon ta, tace "Son na rasa meyasa yanzu baka fadan damuwar ka." Tasowa yai ya zauna kusa da ita yace "Ummi akan wajen aiki ne." "Me ya faru?" "Ina karatun da nake ta naci su bar ni na tafi shekara uku baya?" Kai Ummi ta gyada tace "Eh." "Ummi shi suke maganar wai suna so su tura ni yanzu." "Ah Alhamdulillah menene na damuwa a ciki to?" "Ummi a baya na so amman yanzu sam bana so, nafi son na zauna a gida daku ga Haidar." Kallon sa Ummi tayi ta girgiza kai. Yace "Kwata kwata bana so nai nesa da gida." "To ya za ayi yanzu?" "Zance musu su saka wani." Kai ta girgiza tace "Kada ka soma wannan wata dama takace da ka jima kana nema in har mune muna nan zakaje ka dawo ka same mu da izinin Allah, haka Haidar zamu kula dashi kamar kana nan dan haka ka daina cewa ba zaka ba wannan nasarar taka ce shekara nawa abun?" "Baifi daya ba." "Ah to kaga shekara daya kamar yau ne inda rai dan haka ina mai baka kwarin gwiwa akan kaje ka cika burin ka insha Allahu zaka samu nasara akan komai mu kuma muna nan muna jiran ka, Haba My Son yau kafara tafiye tafiye ina acan ka kare karatun ka na shekara biyar ka koma kai shekara biyu yanzu ne fa ka saba da zaman gidan ni dai nasan yaro na jarumi ne zaije kuma zai dawo mana da nasara da sa'a da izinin Allah." "Insha Allahu Ummi but zanyi jewar ki Ummi." Ya kwanta a cinyar ta ta shafa kansa tace "Na sani my Son amman ai kace Japan zakaje kuma su Yaya suna can da Sitti." Kai ya girgiza yace "Sitti jira take kawai Najwa ta kare karatu su dawo tare." "To kada ka damu muna tare da kai kaji." Kai ya gyada ta shafa kansa tace "Amman meyasa kake wa Maryam haka?" "Me nayi ummi?" "Tazo tana murna ka sace mata gwiwa." Murmushi yayi yana mai lumshe ido kamar ba zai magana ba kuma sai yace "Ummi wannan shine kalar yadda zan sa ta zabura ne, Ummi in tayi abu ba sai ana nuna tayi ba in aka nuna mata zata san tayi next ta iya dakushewa amman a yanzu abinda na fada mata zai na sa tana zabura ko dan ta bani kunya ni kuma bata san nasan tana kokari ba kuma kunyar da take so ta bani shi zai bamu abinda muke so dagamu har ita." "Haidarrr....." "Uhmm Ummi nah." "Haidar." Juyowa yai yana kallon ta, zatai magana aka kira sallah, wata ajiyar zuciya ya sauke wacce sai da Ummin ta bishi da kallo ya mike yace "Bari nai alwala kada na makara." Ya shige bandaki da sauri. Murmushi tayi tace "Yaro man kaza, duk boye boyen ka dai watarana ka fito ka fada." Ta mike ta fita a dakin. *** Tafe suke a hanya za a kai ta makaranta wanda sauri takeyi dan exam din tara ce dasu gashi har takwas da rabi ta gota, suna cikin tafiya motar ta tsaya akan titi da sauri ta dago tace "Lafiya Baba Anas?" "Bari na duba." Ya fada ya fita dube dube ya fara ya dawo ya kunna amman taki tashi haka ya kara fita ya kara tattaba motar amman taki tashi, kara fita yayi Maryam ta fito kamar zatai kuka tana duba agogon hannun ta wanda ya nuna mata saura kwata, titi ta fara kalla amman kuma ba abin hawa dan titin ba a fiya samun motar haya ba. "Baba motar taki ko?" Ta fada tana matsawa wajen sa. Dagowa yai yace "Wallahi Hajiya bansan me ya same ta ba lallai na yadda da akace karfen nasara bai da tabbas in banda haka lafiya fa muka fito amman ta tsaya Allah yasa ba nan kusa zaku shiga jarabawar ba." Agogo ta kalla tace "Kaga saura minti goma ma." Ta fada kamar zatai kuka. "To ko mota zan samar miki?" "Baba ina kaga alamar mota anan?" "Bari na duba can kasa layin sai a samo." Ya rufe motar ya nufi titin da zai fitar dashi babban titi kai ya dafe tana duba agogo. Tin da ya taho ya hange ta, yana karasowa yaga damuwar dake kwance karara akan fuskar ta, parking yai a tsallake ya fito ya karaso wajen ta cikin cool voice taji ance "Are you okay" Da sauri ta dago tana kallon waye, wani dogon matashi ne da bazai wuce thirty two ba (Dan ba zai wuce Yaa Farouk ba), yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakin spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baza a sa shi a jerin farare ba, damuwar da ya kara gani a saman fuskar ta kamar zatai kuka ne yasa yace "Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss" Cikin rawar murya tace "Motar mu ce ta lalace kuma exam ce dani......" Ta duba agogo ta yarfe hannu tace "Kaga ko sauran minti biyar." Ta kare maganar cikin shagwaba kamar zatai kuka, jin shiru yasa ta dago ta kalle shi, shima kallon ta yake dan haka ya saki wani murmushi yace "Toh mu je in ajiye ki ga mota ta can" Ya nuno mata motar kallon motar tayi har zatace to sai kuma taji tsoro ya kamata kar taje dan kidnapping ne dan haka sai ta noke, gane abinda take nufi yasa yai murmushi yace "Am sorry daga gidan aboki na nake na amso wani abu shine na biyo ta nan tin daga nesa na gane kina cikin damuwa da bukatar taimako, shine nace bari naji ko zan iya taimaka miki to kuma naji zan iya shine, ni ba dan kidnapping ko yankan kai bane." Fuska ta rufe da hannayen ta da suke masu kyau tana murmushi kasa kasa, wanda kallon hannun nata ya shagaltar dashi, shima murmushin yake yace "Mu je to" Ta girgiza kai tace "A'a" Yace "Ohk in samar maki abin hawa tinda baki yadda dani ba?" "Ni ba haka bane ba kawai dai...." Yai murmushi yace "What?" Zatai magana taji Baba Anas yazo yana haki dan gudu ma yayi yace "Hajiya ban samu ba ya za ayi ko zaki zo mu karasa mu samu wani ya rage miki hanya." Sai ya kalli wannan saurayin yace "Sannu bawan Allah." "Ina kwana Baba?" "Lafiya lou." "Nace tazo na kai ta taki gani take ko dan kidnapping ne ina jin." Ya zaro wallet din sa ya ciro card din sa ya mikawa Baba sannan ya bashi number wayar sa yace "In bata dawo gida ba ga abubuwa na." "A'ah insha Allahu ma zata dawo gida kije Maryam kada ki rasa jarabawar." Ta kalli Baba ya gyada mata kai. Mutumin ya tsallaka Maryam tace "Baba ni tsoro nake ji." "Kiyi addu'a 'yata Allah yana tare dake kinji?" "To Baba nagode sai munyi waya." Ya tsallakar da ita titi ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna Baba ya rufe mata ta daga masa hannu ya tayar da motar a guje dan har tara tayi suka fice a kan titin da gudu, tuki yake cikn sauri har suka karasa makarantar "Wane hall zakuyi exam?" Ya tambaya. Fada masa tayi ya karasa yai parking ganin wajen ba kowa kuma alamar duk an shiga yasa ta bude motar da sauri bata tsaya fadin komai ba ta nufi hall din da gudu kallon ta ya tsaya yi, Jawahir dake corridor din hall din tana ta trying number Maryam ba a dauka ba ta kira Ummi tace ta fito amman suna hanya sam taki dauka tana ganin ta ta sauke wata ajiyar zuciya hannunta ta kama kawai sukai cikin hall din jaka suka ajiye suka karasa suka amshi booklet dan ba a raba exam question ba suka zauna. Sai da suka dauki awa uku suka fito. Suna fitowa Jawahir ta kalli Maryam tace "Me ya faru ne? Kikai latti." "Mota ce ta lalace ga ba abin hawa, wannan yasa da kyar na samu wani ya kawo ni fa." "Kai amman mungode masa Allah saka da alheri." Sai da tai maganar Maryam ta mike da sauri ta fito tana duba wajen. Jawahir ta karaso tace "Menene?" "Ban masa godiya ba fa?" Dariya Jawahir tayi tace "Shine kika zo neman sa tsayawa jiran ki zai yi?" "Ke kin fiya wasa wallahi." Tace "Bari na kira Baba naji ya motar an gyara." Ta kira Baba yace an gyara ya jarabawar sannan ta kashe wayar suka koma karatu. Sai Yamma Baba yazo ya dauke ta suka koma gida. **** Da wuri ta dawo daga makaranta, kasancewa yau juma'a kuma yau Abba zai dawo, jakarta ta ajiye a daki kawai ta fito ta shiga kitchen dan taya Ummi aikin tarbar Abba. Karfe daya saura suka gama komai, turare suka karayiwa falon suka kara hade gidan sannan duk suka wuce dakin su, Maryam ta shiga tai wanka ta fito ta shafa mai ta saka wata doguwar riga ash kala mai layi layin baki da fari, mayafin rigar ta yafa kan ta da yake a tsefe ta dago ta baya yayi kamar acuci maza tayi, turare ta shafa tai sallah, fita tayi ta isa dakin Ummi ta tadda Ummi na daurin dankwali, karasawa tai tana murmushi tace "Ummi Amaryar Abba." "Zanci kaniyar ki fa Daughter." "To Ummi ni me nace?" Ta amshi dankwalin tana fadin kawo na daura miki, ta amsa tai mata dauri mai kyau, Ummi ta karasa gaban mirrow ta kalli kanta tace "Wannan daurin ai sai ku daughter." "Ummi ki barshi wallahi har manya sunayi Kuma ke da ba fita zaki ba Abba fa zakiyiwa kwalliya." Ji sukai an bude gate da sauri Maryam ta karasa ta bude taga motar Abba ta gani an shigo da ita labulen ta saki da sauri tace "Abba ya dawo." Ta fita da sauri yana fitowa tana karasawa ta durkusa tace "Sannu da zuwa Abba." Kamo ta yayi yace "Yauwah My Daughter." Ta amshi yar jakar sa da wata leda suka nufi cikin gidan, Yaa Farouk da Yaa Aliyu da dawowar su daga masallaci kenan suka biyo bayan su, a falo ya zauna Haidar ya haye cinyar sa, nan suka gaishe shi sannan suka mike suka fice falon Inna, Maryam da Haidar aka bari suna taiwa Abba surutu, duk da Haidar yafi cika dakin. Tin kan Ummi ta karaso kamshin ta ya cika Abba, daga kai yayi yana kallon ta murmushi dauke a fuskar sa ta zauna tace "Barka da zuwa Ranka ya dade." "Barka da zuwa Madam ya gidan ya yara da kowa?" "Alhamdulillah." Ta mike ta isa firij din dakin ta dauko jug dake ciki ta zo ta tsiyaya masa lemon kwakwan da tayi a ciki, amsa yayi yace "Nagode." Ya kurba tare da lumshe ido, Maryam ta mike Abba yace "Shiga kitchen akwai sakon Inna ki mika mata." "To Abba." Ta fada tana kamo hannun Haidar, Ummi tace "Ki tafi mata da abinci." Duk da basa bawa Inna abinci dan tace ita da kan ta zatayi bata son jagwalgwalo amman in sunyi sakakke suna aika mata, abun ta dauka ta nufi sashen Inna, tana karasawa ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Aliyu ta gani zaune yana kallon Inna dake bada labari sai wani murmushi yake kasa kasa, da gudu Haidar ya dafe shi ya rumgume shi yace "My Son." Lafewa yai a jikin sa Aliyu ya shafa kan sa. Inna ta bawa sakon sannan ta juyo tai kofa, Inna tace "Oh ba zama zaki ba?" "Kaina ke ciwo Inna zanje na kwanta ne." "To kisha magani kinji je ki kwanta ki huta" Ta fita Inna ta daura mita "Haba ba dole kai yai ciwo ba kullum sai an fita ga karatu ko da yaushe kai mu kam munji dadi amman mutanen yanzu wahala kawai suke sha haba mu a da muyi zaman mu a gida miji na kula da kai amman yanzu kaine yawo karatu kaine yawo aiki kullum kana tsaye kana tafe duk kullum kana a kare." Aliyu dai bai tanka mata ba, Inna ta juyo ta kalle shi tace "Dadi na da kai miskilanci ina maka magana ka share ni bana son irin haka wallahi Ali." "To ni nasan dani kike Inna?" "To zan ta magana ne ni kadai haba dan Allah sai kace mahaukaciya." "Inna ai naga wani lokacin kina tabawa." "In abu ya ishen ba na rasa wanda zan fadawa kuma yana cina a rai ba." "To ni dai naji shikenan." Ya dauki Haidar ya fita. Ta bishi da kallon sa tace "Dan jakar uba." Yana ji yai murmushi kawai bangaren su suka koma ya shiga daki ya dauko magani ya bawa Haidar yace "Je ka kaiwa Antyn ka." Da gudu Haidar yaje ya same ta har ta kwanta ya hau kan gado yace "Adda." Ido ta bude yace "Gashi inji Abbi yace ki sha." Amsa tayi ta ajiye tace "Je kace na sha." "Adda bafa ki sha ba." "Zan sha jeka." Ta fada tana tura sa ya fita ya koma wajen Aliyu ya same shi zaune Aliyu yace "Tasha maganin?" "No Abbi tace inje zata sha wai." Mikewa yai ya nufi kitchen ya dauko ruwa sannan ya wuce dakin ta tana kwance taji knocking ta amsa masa, tana kwance akan gado gashin kanta duk ya barbazu, jin an shigo yasa ta dago ganin sa yasa da sauri ta ja mayafin ta tana rufe kan ta dan bata zata shi bane, ya karaso yana kallo ta yace "Kan ne?" Kai ta girgiza ya mika mata ruwan yace "Sha maganin." Fuska ta bata dan bata son magani yace "Bazaki sha ba." "Nifa kan ya daina ciwo." "Duk da haka ki sha nace." Ya fada tare da daure fuska dauka tayi ta balla ta amshi ruwan ta sha hannu ta daure a kirji tana yarfe hannu tace "Wayoo Yaya kaji shi ko bai tafi ba." Da sauri ya mike ya juya mata baya sai kuma yace "Kara ruwa." Yana fada ya fice ta kara shan ruwan ta koma ta kwanta ta kamar zatai kuka. ** Washe gari da yake weekend ne kuma shine na last a month din kamar yadda ya saba duk ending month yana daukar su ita da Haidar ya kai su, su dibi abinda suke so, tana kwance a daki rike da waya suna chat da Jawahir Haidar ya shigo da sallama yace "Adda kizo inji Abbi." Mikewa tayi ta yafa mayafi tabi bayan sa, yana tsaye a falo yana daura agogo ta karasa yace "Ki fito yanzu." Yai gaba Haidar yabi bayan sa, ita mema take bukata babu da ya barta ta zauna amman tasan ba kyale ta zai ba, to me kuma zata dauko a sama ta kalli kan ta kawai ta bi bayan su a haka a cikin mota ta same su ta zaune suka dauki hanya, suna zuwa suka shiga bata da abinda zasu dauka turare da mai ta dauka kawai sai chocolate da wasu ribom da ta gani, lokacin da a kaje biyan kudi Aliyu ya dinga mamaki dan abinda zata dauka baki ya tabe dan ya fara gajiya ace in ba shi ya dibar mata abu ba ita daga turare shikenan, gaba tayi dan ta riga su gaba tana tsaye jikin mota tana danne danne a wayar ta kamar ance ta ta dago taga wani tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, mamaki ta fara shin ita yake kallo ko kuwa, baki ta tabe ta cigaba da abinda take dagowar da zatai taga ita yake kalla sosai, tunani ta tafiyi can ta dago sai taga ya cire glass din idonsa yana cigaba da kallonta da kyau, murmushi ta saki tunawa da a inda ta sanshi, dai dai kuma karasowar Aliyu ya bude booth aka saka kaya sannan ya juyo ganin bata shiga ba, wanda a lokacin ta daga kai tana kallon mutumin Aliyu yabi wajen da take bi da kallo wani abu yaji ya tokare shi ya karasa wajen ta yace "Kinsan shine?" Kai ta girgza da sauri ta bude mota ta shiga, ta dago tana kara kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Aliyu ya lura dan har yai reservse mutumin take kalla dan haka a guje yaja motar suka fice daga wajen. Washe gari lahadi tin da tatashi taji yanayin jikin ta ya sauya, calendar ta duba ta zaro ido tana fadin "Watakila gobe." Gaban mudubi ta koma ta janyo tana dubawa ledar pad dinta, ta dauko taga saura daya komawa tai ta zauna sai kuma ta mike ta sauka kasa wajen Ummi zama tayi a kusa da ita tace "Ummi ina son zan je supermarket in siya pad" Ummi ta kalleta tace "Naga jiya kuka je." "Ummi na manta ban dauka ba." Wanda fada kawai tayi dan in har da Aliyu zasu shopping kunyar dauka take a gaban sa wani lokacin ne ma shi da kan sa in zai karayo mata siyayya yake hadowa da ita to gashi tana tsammanin gobe yazo dole taje ta nemo ta kan yazo mata. "Toh driver ya fita wa zai kaiki tinda ke kin ki, ki koyi mota ma." "Ummi zani da kai na, kuma Yaa Farouk yace da munyi hutu zai koyan." "Ya dai kamata Baba Anas ma ya huta da fitar safe ai." Maryam ta mike tace "Bana so magariba tayi min bari naje na shirya." Ta haye sama, siket ne da t-shirt a jikin ta dan haka ta dauki katon hijab ta zura wanda ya saukar mata har kasa, sannan ta dauki purse da wayar ta ta fita, Ummi ta sama a falo tace "Ummi na fito." Waya ta dauka tai danne danne wanda wayar Maryam yai kara tace "To sai kin dawo." Maryam ta duba taga 5k Ummi ta tura mata ta rumgume ta tace "Nagode Ummi." Tunda Maryam ta fito Yaa Farouk dake jikin motar sa fita zai yi ko dawowa yayi oho dai yake hangen ta murmushi yake ta saki, ta nufo gate bama ta lura dashi ba lokacin Mama ta fito zata sashen Inna, Maryam ta durkusa tace "Ina yini?" Ko kallon ta batai ba ta wuce mikewa tai tana murmushi ta karaso gate Yaa Farouk dake tsaye yace "Ina zaki?" Ba yadda zatayi tai murnushi tace "Super market." "Ke kadai kuma?" "Kai Yaya zan iya ai." "A'ah ni ban yadda ba ina Baba Anas?" "Baya nan Ummi ta aike shi." "A'ah ai kuwa ba zaki fita ke kadai ba bana son." "Kai Yaya sai kace wata yarinya." "Ita ce mana." "Ni din?" Yai murmushi zai magana kenan yaji Mama tana kiran sa "Farouk." Da sauri ya juya, ya karasa tace "Me kake anan?" "Daman zan anjiye ta ne." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:06] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 5 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* This page is for you *Momy* Hajiya Nafisa Allah ya kara lafiya da nisan kwana, Allah ya raya zuri'a yasa kiyi kyakyawan karshe Allah kara budi da wadata, Allah kara rufa miki asiri duniya da lahira amin Yai murmushi zai magana kenan yaji Mama tana kiran sa "Farouk." Da sauri ya juya, ya karasa tace "Me kake anan?" "Daman zan anjiye ta ne." "Ban yadda ba." Ta fada ta wuce su, ya karaso yana ya'ke yace "Sis Mama tace zan kai ta unguwa, kuma ba hanya daya bane da na ajiye ki mun wuce." "Ah haba ba komai Yaya nagode." Ta nufi bakin gate yace "To ai kya bari na samo Malam Bala driver ya kai ki ko?" "Dan Allah Yaya kada ka damu yau so nake na fita ni kadai, yanzu Ummi ma take magana akan koyar driving nace kace zaka koyan gwara ka koyan kaga da sai dai na dauki mota kawai na fice." "Haka ne bari na baki kudin mota." Kai ta girgiza tace "A'ah Ummi ta bani." Ya zaro kudi ya mika mata yace "Na Ummi da ban na Yaya daban." Amsa tayi tace "To Yaya nagoge." Ta juya sai ga Baba Anas nan Yaa Farouk yace "Yauwah." Ta juyo tace "Ni dai na tafi." Baba Anas ya fito yace "Ba dai fita zakiyi ba Hajiya?" "Baba 'yarka dai." "To 'ya ina zuwa?" "Unguwa." "Bari na kawai Hajiya sai nazo na kai ki." "A'ah da ka barshi." Farouk ne ya kalle ta yace "Wai kin taba fita ke daya ma tukkuna." "Kaji ka Yaa Farouk da wata magana." "To ai naga kullum driver ke fita dake." "Shiyasa nake so in fara yau, kan na fara driving ko?" "No tinda ya dawo ki hakura kawai." "Ya zanyi da Yaa Farouk ka zama kamar me?" Yai murmushi Baba Anas ya dawo ta shiga suka bar wajen. wani karamin super market ta gani tace "Baba mu tsaya anan ma." Ya karasa yai parking ta fito tana kallon wajen, kamar ance ya waigo ya hange ta ta fito a mota wannan yasa ya karaso shima yai parking motar sa, ciki ta shiga ya fito yabi bayan ta, tana shiga tayi wajen turarurruka, wani turare da ta dade tana nema ta gani ta dauka tana mai jin dadi dan taji dadin sa lokacin da Yaa Aliyu ya siyo mata duk lokacin da sukaje shopping sai ta duba sai dai bata sake ganin sa ba sai yau, tama dauka ta tafi bangaren su pad, ta durkusa ta dauki Virony da Moppid mai talatin da uku uku, tana cikin duba jikin su dagowar da zatayi suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa don rass ta ganesa, da sauri ta juya tare da ajiye pads din hannunta, kin juyowa tayi har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, duk da ta juya masa baya tana jin kallon da yake mata, tafiya ta farayi kawai sai taji wannan muryar tasa mai dadi yai mata sallama "Assalamu alaikum" Wani iri taji ta amsa a hankali ido ta runtse jin kamshin turaren sa, wanda ya kashe mata jiki, ya zagayo gabanta, yace "Ya kika?" Ba tare da ta kallesa ba ta "Ina yini?" A kunyace. Yai murmushi yace "Ya exam?" Shiru tayi sai ya kara murmushi yace "Oh baki gane ni ba?" Dagowa tai ta dan kalle shi yace "Ko da yake tin jiya nasan kin gane ni ma." Ji tayi ya gundure ta to me zatai masa daga ya taimaka mata sai yana bibiyar ta ko dai aljanni ne. "Ni ba aljani bane kawai dai Allah ya hada mu da farko, sai jiya na ganki yanzu ma zan shige na ganki nace bari nazo naji ya exam?" "Alhamdulillah." Ta fada ta juya ta fara tafiya, Pad din da ta ajiye ya dauka yabi bayan ta har ya kamo ta ya kama basket din ta da sauri ta sakar masa ya saka pad din ya mika mata, kai tayi kasa dashi yace "Ko kin gama?" Amsa tayi tai ciki da sauri tana kara dube dube tanayi tana waigowa ganin bata ganshi ba yasa ta saki jikin ta, ta cigaba da shopping dinta bayan ta gama tayo wajen counter dan biyan kudin ta ta ganshi tsaye a gefe, fuska ta hade ta karasa ta mika kayan aka lissafa ana fadar kudin zata mika atm din ta, taga ya mika nasa kan tai magana har ya saka pin, suka zuba mata a leda kan ta juyo har ya fice daga wajen "Innalillahi wainna illahir rajiun." Ta fada dan ita bata son wani abu ya hada ta da maza sam tana fitowa ta ganshi a tsaye kai ta dauke ya nufi motar su ya karasa yace "Kin fito?" Kai ta gyada kawai yai murmushi yace "Toh muje in ajiye ki a gida?" Kamar jira take tace "Nooo da da driver muke." Daga haka ta nufi motar su, Baba Anas na ganin ta ya karasa ya bude dai dai karasowar Mutumin ya karasa tare da bawa Baba hannu suka gaisa. Baba da ya gane shi yace "Kai ne?" "Nine Baba ya aiki?" "Alhamdulillah! Ga fa mutuniyar a ciki." Kallon motar yayi yana murmushin sa mai kara masa kyau yace "Ita na gano nace bari nazo mu gaisa" "Amman ka kyauta." Baba ya leka yace " 'ya ga mutumin nan." Ya bude mota ta dago ta kalle shi, fuska ba yabo ba fallasa tace "Ina yini?" "Lafiya ya makarantar?" "Lafiya." Ta kalli Baba tace "Muje ko?" "To Hajiya." Ya dago ya kalli Mutumin yace "Sai anjima." Mutumin yace "To ku gaida gida." Baba ya shiga ya tayar da motar suka fara tafiya juyowa tai taga yana tsaye yana kallon su, har sukai nisa yana tsaye kai ta dauke tana mai sauke ajiyar zuciya, godiya tai da Allah da yasa da driver suka fito da ace ita kadai ce da bata san ya zatai ba da gaskiya Yaa Farouk da yace sai tazo da driver ita kanta ba zatana fita babu wani ba tagane tsaro ne a tare da ita. A haka suka karasa gida ta fita a motar tai cikin gida. Aliyu ta sama a falo tin da ta shigo yake bin ledar hannun ta da kallo, ta gaishe shi bai amsa ba sai kallon ta da yake har ta wuce sama yace "Daga ina take?" Ya tambayi Ummi bayan ta haye sama, Ummi tace "Super market taje." "Super market tayi ne?" "Tace ta manta jiya bata siyo wani abu ba." "Wa ya kai ta?" "Ita kadai ta tafi." "Saboda me?" "Saboda Baba Anas baya nan." "Amman ai da sai ta fada min, Ummi ki daina barin ta tana fita ita kadai fa." "To shikenan." Ya mike yai dakin sa, kwanciyya yayi yana tunani tare da lumshe idon sa. ** Washe gari bayan Isha'i Maryam ta taho daga bangaren Inna da taje gaishe ta dan kwana biyu basa haduwa saboda makaranta a hanya ta hadu da Yaa Farouk zai je sashen Inna, gaisheshi tayi ya amsa yana kallon ta, tai kasa da kai, ya saki murmushin sa mai kyau yace "Jiya ban ganki ba da kika dawo daga shopping." "Ban ga motar ka ba da na dawo." Kai ya gyada yace "Yes na fita unguwar, to ina tsaraban shopping dina ne?" Ta dan fiddo da ido waje tace "To ai baka ce in siyo maka wani abu ba." "Oh sai nace ki siyon to ke me kika siyo." "Turare ne da...." Sai tayi shiru yana murmushi yace "Turare da me?" "Shikenan." Ta fada tana kau da kai daga inda yake yai murmushi yace "Nasan ba daya kika siyo ba sai ki ban wani a ciki." "Na matan?" Tai tambayar da mamaki, ya gyada kai yace "Eh na matan menene a ciki sai dai in ba zaki bani ba." "A'ah zan baka, muje na dauko maka." Ta fada tana yin gaba suna zuwa kofar part din su ya tsaya yace 'Ina jiran ki." "Ah Yaya ka shigo mana." Kai ya girgiza yace "Je ki kawon sauri nake." Ta juya ta shiga taje ta dauko masa guda daya a wanda ta siyo ta taho, ta same shi yana tsaye yana waya yana jin ta ya katse wayar yana juyowa tace "Kai da Anty nane ko?" "Wacce Antyn taki?" "Yaya ka dai ki ka hadani da Anty na." "Kece Antyn kanki ai." Baki ta turo tace "Ya dai kamata kuyi mana sabbin Aunties." Ta mika masa turaren ya amsa ya bude kamshin ya shaka ya lumshe ido yana budewa da sauri yace "Amman akwai dadi wa ya nuna miki shi?" "Yaya shi ya fara siyon shi na jima ina neman sa da kyar yau na samu." "Kuma kika bani." "Na siyi guda uku ai kaga na baka daya sauran biyu." "To nagode sosai." Tai murmushi yace "Bari naje." "Sai da safe." Ta fada ya juya, itama juyawa tai sai taga Aliyu tsaye bakin kofa, kai tayi kasa dashi ta wuce, ta gefen Ido Aliyu ya kalleta daga inda yake amman ba zakace yana kallon nata bama. Yau Asabar ba makaranta tin safe take fama da ciwon kai sam bata fito ba, wannan yasa Ummi ta nufi dakin nata a kwance ta same ta ta zauna tace "Yau bacci kike sha?" Dagowa tayi taga yadda idon ta yai jajir wannan yasa tace "Subhnallah me yake damun ki?" Kai ta nuna mata, Ummi tace "Bari ki ci abinci sai kisha ko paracetamol ne." Ummi ta fada ta fice bata jima ba ta dawo da dankali da tea da kyar Maryam ta sha ta koma ta kwanta sai bacci, Ummi ta fita bayan mintina ta dawo ta same ta tana kwance idon ta biyu, Ummi ta zauna tace "Kinsha maganin kuwa?" "A'ah Ummi." "Saboda me to?" Kamar zatai kuka tace "Ummi kinsan tsaya min yake a wuya." "A'ah tashi ki sha magani kinji." "Ummi..." Ta kira sunan ta. Spoon Ummi ta dauko ta dama mata maganin ta mike ta bata, ta shanye sannan ta kora da ruwa." Fuska ta dinga batawa ta koma ta kwanta a haka wani baccin ya kuma dauke ta, har yamma abinda take fama dashi kenan, ganin bata son ta kara kwanciyya yamma tayi yasa ta mike ta sauka kasa, a kitchen ta jiyo Ummi ta karasa tace "Ummi bari naje wajen Inna." "To ya kan?" Da sauki ta fada tana fita, sashen Inna ta shiga da sallama Inna dake kitchen tana yan soye soyen ta ta fito kwance ta ga Maryam ta karaso tace "Lafiya?" "Kaina ke ciwo ne." "Kinsha magani?" Kai ta gyada Inna tace "To bari naje a karasa soyar can na fito." Ta koma, Maryam ma ido ta rufe daga haka bacci ya dauke ta. Wajen shida saura ya shigo dakin da sallama Ummi ta amsa ya zauna ya gaishe da ita, shiru yai yana nazari yasan yau weekend suna tare da Maryam to tana ina da kamar ba zai magana ba sai kuma ya daure yace "Tana ina?" Ya fada yana nufar dakin sa, Ummi tace "Taje sashen Inna bata jin dadi ma." Juyowa yai da sauri sai kuma ya wayance yace "Me yake damun ta?" "Kasan ai ita ciwon kai dai ciwon kai." "To Allah sauwake." Ya shiga dakin sa, jakar sa ya ajiye sai kuma ya juyo ya fito da sauri ya fice da kallo Ummi ta bishi. Bangaren Inna ya shiga ya bude kofar falon yai sallama ya shigo dakin Innan tsaye yayi yana kallon Maryam dake bacci amman daga fuskar ta zaka sam bata jin dadi, dan tayi ja, karasawa yai wajen kujerar ya durkusa yana son daura hannu yaji zafin jikin ta amma kuma ya kasa, Inna ce ta fito tana goge hannu dan ta gama wanke wanke kenan tace "Ya kan." Ganin Aliyu a gaban tace "Lafiya?" Ido Maryam ta bude sukai ido hudu da Aliyu da sauri ya mike yace "Me yake damun ki?" Kai ta girgiza kamar zatai kuka dan tasan yanzu zai sata shan magani, Inna tace "Kan tane yake ciwo amman ai tasha magani." Juyawa yai ya fita Maryam ta mike tace "Inna yanzu zai lodan magani." Inna tace "Kyale shi kar ki sha shi ai haka yake sai ya lodawa mutane magani." Ta mike ta jingina da kujera Inna tace "Kinci abinci?" Kai ta girgiza tace "Na koshi." "Ai ita Aisha sam bata iya jinya ba ace haka zata barki ai sai tayi miki ko dan kunu ne kisha bari ina da ragowar na miki sannu kinji." Ta koma kitchen kiran Sallah akai Maryam ta mike tai alwala tazo ta tada sallah zama tayi tana addu'a bayan ta idar Inna ma ta fito daga daki ta koma wajen kunun ta dama ta zuba mata suga kadan sannan tazo ta ajiye mata tace "Daure ki sha kinji." Dauka tayi tana saisaita shi sannan ta fara sha, Yaa Farouk ne ya shigo dakin da sallama. Sanye yake da ash kalar rga da bakin wando, sai silver agogo, sai kamshin turare take, zama yayi ya gaishe da Inna sannan Maryam ta gaishe shi ido ya kure ta da shi can yace "Me yake damunki?" "Batajin dadi ne." "Ayya kinsha magani." "To mutum zai rasa shan magani bai da lafiya?" Inna ta fada. Murmushi yayi yace "Ai ke Inna bakya son magani kuma koyawa duk wanda yake tare da ke kike." "Gidan ku, nace gidan ku nice bana son magani?" Yai dariya yace "To so kike? Naga har kuka kike kan ki sha." Maryam tai dariya yace "Kema ai Ummi ta fadan bakya so har kukan kike." Baki ta turo tace "Kai Yaya." "Eh ya kan naki?" "Da sauki." "Allah sauwake." "Amin." Ya kalli Inna yace "Inna me zan samu?" Tace "Tinda Barira ce ta kawon ai sai na baka." "A'ah amman ai Abba ne ya kawo miki." "Baice na baka ba in yace na baka na baka kuma ba Suleiman din ne ya kawon abinda nayi yau ba da zakai min gori shehu ne ya kawon." * Aliyu yayi zarya a sama sau nawa yana tambayar Ummi ina Maryam sai tace bata dawo ba sai yayi kamar yaje sashen Inna sai ya fasa wajen karfe tara ya shiga wajen Inna ya samu, Farouk, Inna da Maryam suna ta hira zama yai fuska ba walwala, duk bayan mintuna sai ya duba agogo ganin har tara darabi tayi ya mike yana kallon Farouk yace "Dare yayi kaje ka kwanta." Agogo ya kalla yace "Yaya bacci yanzu." Inna ya kalla yace "Ke dai ki kwanta dan ana hira kina gyangyyadi." "A ina nayi gyangyandin kai Ali kaji tsoron Allah." Ya mike yace "Ni dai nace a kwanta." Farouk ya mike yace "Inna bari na tafi sai da safe." Maryam ta mike tace "Bari na bika." Ya kalle ta yace "Ai na zata anan zaki kwana." "A'ah." Taiwa Inna sallama ta fita, ba wanda yai magana har suka karasa gate din su Maryam suka shiga sai da ta kusa kofa ya tsaya yace "Sai da safe." Ta juyo ta daga masa hannu, yai murmushi yana kallonta yace "Good night" "Sweet dreams." Ta bashi amsa ya juya ita kuma ta shige, A bakin gate ya hadu da Aliyu yace "Sai da safe Yaya." "Allah tashe mu lafiya." Ya rufe ya nufi ciki a matattakala ya hange ta yace "Zo nan." Juyowa tayi ta nuna kan ta sannam tace "Ni?" "A'ah ni." Ya wuce dakin sa, fuska ta bata ta sauko tabi bayan sa akan kujera ta ganshi zaune ta zauna tace "Gani." Juyawa yai ya dauko leda ya fito da magungunan ciki sannan ya mika mata, kallo ta tsaya yi, yace "Amshi mana." "Yaya na warke fa." "Ina wasa dake ki amsa nace." Ta karba ya zuba mata ruwa a kofi ya mika mata ta amsa yace "Sha." Ido ta runtse ta zuba ruwa sannan ta watsa maganin ido ta kara runtse wa tana dafe kirji da sauri ta mike jin amai na taho mata kamo ta yai ya zaunar da ita tana son mikewa ya hana wannan yasa ta hau yo aman a jikin sa, sai da ta gama gaba daya sannan ta jingina da kujerar mikewa yayi ya zare rigar sa ya rage dashi sai singlet, a hankali ta bude ido tana ganin sa a haka ta mike da sauri zata bar wajen yace "Zo nan." Jikin ta har rawa yake leda ya dauko ya mika mata ta amsa ta juya da sauri ta bar wajen dakin ta ta shiga ta kwanta a saman gado tafi minti biyar ta mike ta watsa ruwa sannan ta dawo ledar ta dauko tana budewa taga fura murmushi ta saki tana fadin "Thank you Yaya." Ita ta sha sannan ta mike ya fita dakin, wajen Ummi taje ta samu har ta kwanta Ummi ta dago tace "Ai na zata a wajen Innan zaki kwana?" "A'ah Haidar yai bacci?" "Yana dakin sa." "To sai da safe." "Ya kan?" "Da sauki." Sai da safe." "Allah tashe mu lagiya." Ta juya ta tafi dakin ta. Daga sama ta sauko sanye da doguwar riga marar nauyi sai hijab madaidaici ta zauna kusa da Ummi tace "Ummi gidan su Jawahir nake son zuwa." Da kallo Ummi ta bita har sai da ta saka Maryam dariya, Maryam tace "Kai Ummi kallon fa?" "Ji nayi kince zaki gidan su Jawahir yau shekarar ku uku tare amman baki taba zuwa ba meya faru?" Fuska ta rufe da hannu tace "Ummi ai na fada miki wannan satin gaba daya batazo makaranta ba to ashe bata da lafiya kinga ya dace naje na duba ta." Kai Ummi ta gyada tace "Gaskiya kam jeki ki shiya kizo kije ki mata sannu kinji." Da sauri ta yi sama tana fadin "Thanks Ummi na." Kaya ta canja ta dauki wani less da akai mata dinkin doguwar riga dark blue ne mai adon peach da milk ta daura dankwali ta yafa peach mayafin ta, ta dauki milk din jaka da takalmi ta shafa turaren mai Oud Abiyad ta fito ta samu Ummi a falo, Ummi ta dauki purse din, ta mika mata dubu biyu tace "Ki siya mata lemo a hanya." "To Ummi nagode." "Ki dubata da jiki." "To." Ta fita ta kira Baba Anas ya karaso yace "Ina zamu?" "Baba gidan su wannan kawar tawa Jawahir zamu, amman in ka ajiye ni zaka dawo zan dawo da kai na." "To wacce unguwa ce?" Nan ta fada masa yace "Shikenan." Ta shiga suka tafi, suna zuwa unguwar yace "To wane gida ne?" Wayar ta, ta dauko ta fara kiran Jawahir amman bata dauka ba tace "Baba bata dauka ba ga ba mutane bare muyi tambaya." Kallon unguwar suka tsaya yi kasancewar unguwar masu kudi ce so silent ba kowa ko shago babu masu gadi duk suna gidan su, wata mota ce tazo zata wuce da sauri Baba ya fito yana tsaida shi tsayawa yai ya bude tint glass din, ido Baba ya zaro yace "Kai ne?" Mutumin yai murmushi ya mika masa hannu suka gaisa, Baba yace "Tambaya muke." "Allah yasa na sani." Ya juya yana kallon Maryam dake cikin mota sun hada ido tai sauri ta dauke kai, Baba Anas ya fada masa gidan da suke nema, yai wani murmushi yayi yace "Wancan gidan ne." Ya nuno musu Baba Anas yace "Mungode Allah ya saka." A bakin gate tasa ya ajiye ta sannan ta fada musu inda tazo sai da aka kira cikin gida aka fada sannan aka barta ta shiga, tsaki tayi dan abinda ta guda kenan daman, bangare biyu ne ta tambayi nasu Jawahir aka nuna mata sannan ta wuce, tana shiga masu aikin suka fara mata sannu da zuwa a hanya suka hadu da Jawahir tana ganin Maryam ta rumgume ta tana fadin "Da gaske ne ke nake gani ko Mafarki ne yau ga Maryam a gidan mu." Ta kara rumgume ta sai ta jawo hannun ta ta fara kwadawa Momyn ta kira tace "Momy Momy." Dakin Momy suka shiga Momy ta fito da sauri tana fadin "Lafiya?...." Bata rufe baki ba taga Maryam da sauri ta karasa ta kamo ta tace "Wa nake gani kamar Maryam." "Momy ita ce." Momy ta rumgume ta tace "Ah lallai yau muna da babbar bakuwa." Maryam ta zame tace "Ina yini Momy?" "Lafiya ya gida yasu Ummin taki?" "Suna lafiya ya jikin Jawahir?" "Ah Jawahir taji sauki sosai." "Allah kara sauki Momy tace ai mata sannu." "Mungode." Ta ajiye musu leda tace "Gashi inji Ummi." Momy tace "Kai har da wahala haka." Tace "Angode Allah saka da alheri." Kamo hannun ta tayi tace "Taso muje Momy zata kwacen kawa." Wani hadaden daki suka shige wanda nan ne dakin Jawahir suka zauna Maryam tace "Ai kinji sauki dama ban zo ba." "Ah haba ai naji dadi wallahi in ina so kizo haka zan nayi wallahi ina cikin bargo ana min waya akace nai bakuwa Maryam na mike dan nasan ba wata Maryam da zatazo waje na sai ke, har naji zazzabin ya sauka." "Ai kuwa har kin fada ya jikin?" "Alhamdulillah ai zan shigo ckul monday." "Allah kaimu amman naji dadi." Nan masu aiki suka hau shigowa da kayan sha da na ci, kan kace me an cika gaban Maryam da kaya ta kalli Jawahir tace "In kai wannan ina?" "Cikin ki." "Kema kinsan naci abinci ai." "Ban yadda ba malama ki zage kici abinci ni a gidan ku bana bakunta kema feel free gidan mune fa." Lemo kawai ta sha tace ba abinda zata ci nan suka hau hira, wanda sai kiran sallah sukaji na magariba Maryam ta mike tana fadin "Na shiga uku dare yayi gashi nasa Baba ya tafi." "To menene a gida fa kike." "Bana son yin dare wallahi." Sallah sukai, suna idar wa ta mike zata tafi Jawahir tace "Ai sai kinci abinci kuma sai kin gaisa da Dady nasan sai after isha'i zai shigo." Kamar zatai kuka tace "A'ah Jawahir Ummi zatai fada." "Kina gidan namune zatai fada kwana ne kawai banyi a gidan ku ba Maryam amman ni yaushe ma kika zo kyan ta ki kwana." Masu aiki ne suka fara shigo da wasu kalar girki Maryam tace "Ni da banci wannan bama kike bani wani." "Ki zabi wanda zakici ko naje na fadawa Momy." Kadan ta zuba taci tace ta koshi Jawahir ta mike tace "Zo mu shiga daki na kiga." Suka shiga bedroom din ta inda yake wata aljannar duniya zama tayi gefen gado, ta bude wani side na dorowar ta wanda sabbin kaya ne a ciki kawai ta kamo hannun Maryam tace "Zabi wanda kike so." Kai Maryam ta girgiza tace "A'ah Jawahir." "Wai meyasa kike min haka abu nawa naki ne ki zaba." "A'ah na gode ni hankali na yai gida." "Tinda a jeji kike ko?" "A'a...." Gani tayi Jawahir ta fara fito da riguna wajen biyar da sauri ta dakatar da ita tace "Sun isa dan Allah." "A'ah ba nace ki zaba ba kinki, sai ki barni na zabar miki." Ta karo biyu ta debo turaruka ta ajiye ta debo kayan zaki dukka ta hada ta zuba a wata jaka Maryam dai kallon ta ta tsaya tana gamawa sukaji kiran sallah isha'i sallah sukai Maryam ta mike. Jawahir ta harare ta, ta mike tace "Allah mun bata." Ta fita tace "Muje." Wajen Momy suka je, Momy tace "ba dai tafiya ba?" "Eh wai tafiya." "To yanzu Dadyn ki ya shigo kan ya zauna cin abinci ki kaita su gaisa ko?" "Toh." Ta kama hannun ta suka nufi sashen Dadyn wani sashe ne a ciki wanda yake mai kyau sosai yana falon sa zaune rike da carbi suka shiga ya dago yana amsa sallamar su fuska dauke da fara'a Jawahir ta karasa ta zauna a kusa dashi ta jaho Maryam suka zauna a kusa dashi ya kalli Jawahir yace "Daugther me aka samu ne yau?" Maryam ta nuna masa ya kalle ta sai yace "Maryam ko?" "Yess Dad itace gata dai yau tazo gidan mu." "Welcome Daughter." Sauka kasa tayi tace "Ina yini Dady?" Ya dago ta ya zaunar a gefen sa yace "Ya kike ya su Ummin ki da karatu? Ina Haidar?" "Yana gida." "To ku taso muci abinci." "Dady naci abinci." Jawahir ta kalle ta tace "Wai tafiya zatayi Dady." "Tin yanzu?" "Haka tace." Jawahir ta fada kamar zatai kuka. Yai murmushi yace "To menene ko zaki bita?" "No Dady ita sai so take ta tafi ni kuma na bita." Yai murmushi ya dauki babbar rigar da ya cire ya ajiye a gefe ya dauki bandir din 1k ya saka mata a hannu yace "A dage da karatu Allah yai muki albarka." Har kasa ta sauka tai masa godiya sannan suka fita dakin Momy suka koma. Momy tace 'Har kun dawo." Jawahir ta daga kai, bude kofar dakin aka yi duk suka kalli kofar, zaro ido Maryam tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya mata kallo daya ya dauke kai ya kalli Momy, Momy tace "Son ba dai sai yanzu ba." "Yes Momy." Jawahir tace "Yaa Khalifa kaga bestyna da nake baka labarin ta." Ya dan juyo ya nuna Maryam da hannu yace "Maryam ko?" "Yess ita ce." Maryam ta sunkuyar da kanta, yace "Maryama ya kike? Bayan labarin ki da aka jima ana bawa yan gidan nan for more than three years yau sai gaki kinzo lafiya?" Maryam ta kasa dago kanta sai wasa da take da yatsun ta a hankali tace "Ina yini?" yace "Lafiya lau" Momy tace "Ina zuwa." Ta shiga daki shima ya juya ya fita, Momy ce ta fito da leda a hannu ta mikawa Maryam tace "Ga wannan ba yawa ki gaishe min da Ummin taki." Har kasa ta durkusa tayi godiya, Momy tace "Kira min Khalifa tinda Khalid baya nan sai ya ajiye ta a gida ko?" "Momy da kin barshi ma zan hau napep." "A'ah a daren nan kuje zai kaiki gida. Ta kara godiya sannan suka fita Jawahir rike da ledar a corridor Maryam ta kalli Jawahir tace "Waye wannan da ya shigo?" *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:09] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 6 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Wannan shafin naki ne *SAMIRA MALAMI* ina godiya da addu'a da kulawar ki Allah ya bar kauna, nagode sosai😘😘 Jawahir tai murmushi tace "Yaya nane fa sunan sa Yaa Khalifa." "Tabbas kina min maganar sa amman ba sosai ba kin fi yin na Yaya Khalid." "Yaa Khalid dan yayar Momy ne wanda ta jima da rasuwa so yana wajen Momy as u can see am the only female daugther to my father sai kanne biyu da nake dasu maza, Yaa Khalifa is my stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu za ki fara gani, bai zama a kasar nan yanzu haka bai fi shekara da dawowa ba so shiyasa bamu wani shaku ba dan acan yai study nasa tin primary har yanzu da yake likita so kinga dalili but i love my brother " Maryam tace "Ayya!" A haka suka karasa conpound Jawahir na biye da ita, a compound suka same shi Jawahir ta karasa tace "Yaya Momy na kiran ka." Maryam ya kalla yai ciki kawai, bai jima ba ya fito yace "Muje to." Maryam ta tsaya a baya, Jawahir ta kamo hannun ta tace "Feel free sis Yaya nane fa." Ta fada tana mata wani murmushi itama mayar mata tayi ta bude mata gaban mota ta shiga aka bude baya aka zuba mata kayan da wanda Jawahir ta bata da na wajen Momy. Jawahir ta rufe kofar tace "Byee Besty sai mun hadu Monday, nagode sosai" murmushin karfin hali Maryam ta mata bata ce komai ba, Jawahir ta kalli Yaa Khalifa tace "Yaya ka kular min da Besty na." Hararar wasa yai mata bai ce komai ba yayi horn ya bar wajen, a haka suka fita a gidan, har suka hau saman titi babu wanda yace komai cikinsu, bayan wani lokaci yace "Wacce unguwar za ki?" Kan ta a kasa tana wasa da yatsun ta ta fada masa, bai ce komai ba, sai da suka shiga unguwar sannan yace "Wane layin?" Ta gaya masa, daga nan kuma ta dinga nuna masa Inda zai bi har suka shigo gate din layinsu, dai dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ya danna horn mai gadi ya leko yana ganin Maryam ya bude gate din suka shiga, sai da ya tsaya ta bude motar ta fita tace "Nagode" Ciki tayi ya bita da kallo zai reverse yaga kayan ta masu aikin ya bawa, sukai mata. Ciki ta nufa bakin gate din su, Aliyu ta gani bakin gate din alamar fita zai yi don makullin motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar da ta ajiye ta ya sake kallonta, kai tayi kasa dashi tai ciki da sauri gabanta na faduwa, sai da ta kai kofar falon su ta juyo ganin sa tayi tsaye har lokacin yana kallon ta kai ta dauke tare da turo baki ta shiga da sallama, Ummi na sama dan haka itama can ta wuce direct dakin Ummi ta shiga, Ummi tace "Ah Daugther sai yanzu ko?" "Ummi kiyi hakuri kinsan Halin Jawahir kememe taki ta barni na taho wai sai na gaida da Dady kiyi hakuri." "Daman Yayan ki ne yake ta fada yanzu ma gidan na fada masa ya tafi tahowa dake Allah yasa bai fita ba dan saukar sa kenan, sai fada yake dare yayi kuma baki fita da kowa ba driver ma haka, gashi ina kira baki dauka ba." "Na ganshi a kasa kinsan wayar tawa tana silent amman komi lafiya, Yayan tane ai ya kawo ni." Mai aikin su ce ta shigo da kayan ta ajiye Ummi tace "Na menene?" "Baba Anas yace a kawowa Maryam." "Oh nagode." Maryam ta fada tana fadin "Ummi ji uban kayan da suka bani." Nan ta hau babbudewa Ummi tace "Angode Allah ya saka da alheri ya jikin nata?" "Taji sauki." "Allah kara sauki." Motsi ta jiyo ta mike da sauri tai daki dan bata son ma ya shigo su hadu, zama yayi ya kalli Ummi yace "Waye ya kawo ta?" "Yayan Jawahir ne,." "Ummi dan Allah ki daina barin ta fita ita kadai." "Ba ita kadai fa ta fita ba kana gani Baba Anas ya kaita aka dawo da ita." Mikewa yayi yace "Ni fitar ma bana so gaba daya." "To ina Maryam take zuwa in ba makaranta ba, kana gani shekarar su sama da uku da yarinyar nan amman sai yau ta taba zuwa gidan su, kuma na yaba da hankalin yarinyar shiyasa na barta ita ba wasu kawaye ne da ita ba kai ma ka sani." Shiru yai kawai ya sauka. Maryam tana daki tana jin sa tai lakwas. Tin daga ranar suka fara yar boya dan da taji shi zata buya ko bangaren Inna kan ya dawo taje ta taho sai da sukai sati daya a haka, wata rana da dare ta baro sashen Inna tana tafe taji tayi karo da abu da sauri ta dago tana ganin shine ta juya zata koma da sauri ya kamo hannun ta, "Wayyo Yaya dan Allah kayi hakuri ba zan sake ba." Fuska ya hade yace "Waye ya ajiye ki ranan?" "Yayan Jawahir ne fa." "Ke Yayan ki ne?" Kai ta girgiza yace "To na kara ganin ki da wani namiji har ma naganki a motar sa sai na balla kafarki shige ki ban waje." Hawaye ne ya kawo a cikin idon ta da dan gudu ta bar wajen tana zuwa ta wuce sama ta fada saman gado ta fashe da kuka, da kallo ya bita sai kuma ya dan cije leben sa ya bi bayan ta zuwa sashen su har yayi hanyar bene sai kuma ya juya kawai ya nufi dakin sa. Sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta ta kwanta. Bayan wasu watanni. Ummi ce tsaye a kitchen tana rufe flask din da ta hada abinci, Maryam ta dauko jug ta saka a cikin katon gaske din da yake dauke da wasu manyan kuloli, dagowa tai tace "Ummi an gama komai ko?" "An gama je ki shirya tinda kince dake za a airport din." Kan Ummi ta rufe baki ma ta fice ruwa ta watsa ta dauko wata golding yellow din doguwar riga wacce akabi wuyan da hannu da red stone mayafin rigar ta yafa ta dauki wani flat sandal ta zura ta shafa turare ta fito tana addu'a Allah yasa Yaya Aliyu bai fito ba tana kan stair tajiyo bude kofar sa da sauri ta karasa sakowa ya bita da kallo tana zuwa matattakala ta biyun karshe ta gurde ta zamo da sauri ya karaso ya taro ta, ta kamkame shi tana fadin "Wayoo kafa ta." Daga ta yai ya zaunar akan kujera yace "Me ya faru da kafar?" Hannu ta hau yarfewa tana fadin "Zafi wayoo." Da sauri Ummi ta fito shima ya mike yayi daki bai jima ba ya dawo da wani kwalba, budewa yai ya lakaci maganin ya shafa mata a kafar ihu ta saki tana yarfa hannu tana kiran sunan Ummi, Ummi tace "Sannu!" Sai da ya matsa wajen ta kara sakin wani karar sannan ta shige jikin Ummi, mikewa yai yace "Sannu." Ummi tace "Garin yaya to?" "Rashin tafiya a hankali sai kace wata yarinya." Baki ta turo tace "Ummi sauri nake fa kar ya tafi ya bar ni." "To yanzu ba sai naga kafar zuwa ba." Hawaye ne ya cika idon ta tace "Dan Allah Ummi kice yaje dani dan Allah." "To ke zaki iya ne?" Kai ta gyada, Ummi ta kalli Aliyu tace "To Yaya ayi hakuri aje da ita." "Ummi da wannan kafar?" "To ba tace zata iya ba." Kofa ya nufa yace "Minti daya na bata ta fito." Da sauri ta mike sai kuma ta saki kara ya juyo da sauri yace "Malama ki fito a hankali." Ya juya ya fita. Ummi ta kamata tace "Da zaman ki kikai muka wuce can gidan Sittin." "A'ah ni zani Ummi." "Shikenan." A bakin karamin gate ta barta dan bata fito da mayafi ba, Maryam ta fara tafiya a hankali dan gurdewar da tayi yana mata zafi, cikin mota ta hango sa, ido ya zuba mata yana ganin yadda take tafiya a hankali tana dingishi a haka ta karasa ta bude gidan gaba kai ya dauke tana rufe motar ya tayar da motar suka fice. Suna zuwa sukaga har jirgin ya sauka matafiya sun fara saukowa, da dingishi ta fito Aliyu ya kalle ta, ta gefen ido yace "Ki zauna a mota." Kafada ta make yayi kwafa yai gaba abinsa, su Sitti ya hango ya karasa da sauri ya isa wajen ta ita da Najwa, rumgume ta yayi tace "My Habiby." "I miss u alot Sitti." "To ba gashi na dawo ba." Fuska ya bata yace "Ni kuma zan tafi ba." Yai maganar cikin shagwaba. Najwa ta dauke kai tace "Wai kai kadai kazo daukar mu Yaya ina Sister ta?" Hango Maryam tayi, wannan yasa ta saki jakar ta, ta rugo a guje tana fadin "Sister." Maryam ta dago itama ganin Nawa ta karaso a guje tana jan kafa suka rumgune juna suna dariya mutane da yawa sai da suka tsaya kallon su, Aliyu kuwa tsaki yayi yace "Ji yadda kuka tarawa nutane jama'a." Su basu sani ba sai sakin juna da sukai suna murnushi sai suka kara rumgune juna Sitti kuwa ba abinda take sai murmushi jakar Najwa ta dauka ta karasa wajen su tace "Ni bakya murnar ganina ko Maryam." Sakin Najwa, Maryam tayi ta rumgume Sitti tace "Sannu da zuwa Sitti." "Na sameku lafiya." "Alhamdulillah." "To mu karasa mota." Najwa ta kama hannun Maryam sukai gaba, suna tafe maryam na jan kafa Najwa tace "Ciwo kika ji sis?" Labari Maryam ta bata tace "Yaya yana nan da halin sa kenan." Baki Maryam ta tabe suka karasa jikin mota su Yaa Aliyu suka karaso ya bude musu mota, duk suka shige baya ya dago yana kallon su yace "Ni drivern ku ne?" Maryam ta shige jikin Sitti, tace "Sis ki koma gaba." "Ni a kusa dake zan zauna." "To mushiga tare." Wani kallo ya galla musu yace "Motar haya ce da zaku shiga ku biyu gaba, dallah sauko ki shiga." Najwa ta sauko jiki na rawa ta bude front seat ta shiga Maryam ta kara shigewa jikin Sitti tana mamakin fadan Aliyu duk da tasan bai da fuska amman bai yin fada, dagowa tai ta kalli Sitti tace "Sitti ki bashi hakuri." "Ni nayi laifin ku da kukai laifin sai ku bashi hakuri." Shiru Maryam tayi a haka suka karasa gidan sitti wanda aka gyara dan sabon fenti ma akayi masa saboda dawowar ta aka canja furnitures, suna shiga Ummi da Mami na compound wajen motar sukayo suka bude sashen da Sitti take Ummi ta kamo hannun ta, Mami ta amshi handbag din ta suka farai mata sannu da zuwa. Yaya Asiya, Yaya Hannah da ya'yan su ne suka fito duk suka rufe Sitti suna mata sannu da zuwa. Cikin katon falon ta aka shiga Sitti ta zauna akan kujera aka fara gaishe ta da mata ya hanya. Maryam da Najwa kuwa suna dakin Sitti sai hira suke cike da farin ciki ganin juna. A falo kuwa an cika Sitti da kayan abinci kala kala dan kowa sai da yayi mata girki na gani na fada, Sitti ta kasance cikin farin ciki ganin yadda suma suke farin cikin ganin ta da son faranta mata shekarar ta kusan hudu bata kasar in sun hadu dasu Mami sai dai ko a saudiya dan haka murnar da ya'ya da jikokin suke ciki ba a fada kowa kulawa yake bata da nuna kulawar sa a gareta, da kyar suka barta ta shiga dan ta watsa ruwa tai sallah la'asar, a daki tasamu su Maryam dan su ko abincin ma ba suci ba. Sitti tace "To anyi sallah dai." Suka mike sukai alwala sitti ta shiga tai wanka ta fita ta saka kaya tai sallah sannan duk suka fita, Maryam da Najwa dining sukaje sai da suka zabi abinda zasuci sannan suka zuba a plate suka fara ci. Aliyu ne ya shigo Sitti ta kalle shi tace "Habiby bakaci abinci bafa." Dining ya kalla yace "Eh yanzu zanci." "Ya kamata dai." Ya nufi dining ya zauna, Maryam ta kalle shi tace "Me zan zuba maka Yaya?" Abinci su ya kalla ya nuna mata kular Ummi dan yasan Ummi ce tayi, zuba masa tayi ta ajiye masa ruwa da lemo suna cin suna hira, dagowa yai ya wulla musu wani kallo shiru sukai suka karasa sukai daki. Kan gado suka kwanta Maryam tace "Bari na kira Jawahir." Nan ta kira ta saka musu a speaker sai hira suke dan tin ba yau ba Maryam ta hada Najwa da Jawahir suna chat sosai. Sai after isha'i mazajen su Yaya Hannah da Asiya suka zo gaishe da Sitti kowa da kayan dadi a hannu ya ajiye mata Sannan sukai sallama suka dauki matan su, basu jima da tafiya ba Abbi ya shigo a kasa ya zauna ya gaishe da Sitti yai mata ya hanya yar hira suka taba sannan Najwa ta fito ta gaishe shi yai mata murnar kamalla karatun ta, yai mata sallama shi ya dauki Mami suka tafi. Aka bar Ummi da Haidar dan Aliyu bai dawo daga masallaci ba, sai wajen tara ya shigo yace "Ummi mu tafi ko?" Sitti tace "Bazaka ka zauna mu kwana hira ba." Yai dariyar da bai fiya yin ta ba, wacce ta kara fito da ainahin kyan sa, ya shafa sumar kansa yace "Yau ki huta zan zo mu sha hira kan na tafi." "To shikenan." Ya kalli Ummi ganin ta dauki Haidar yace "Maryam fa?" "Ai tace anan zata kwana." "Ummi Amma...." "Au a wajen nawa ma ba zata kwana ba." Sitti ta fada kai ya shafa yace "Sitti to ki kula da ita." Tai murmushi tace "Da Ina cewa zan dauke ta, ta dawo wajena ita da Najwa duk da Najwa ta kusa ta tafi kaga ita ai sai mu karasa." "Tab Sitti sangartata ai zakiyi gwara tana gida Ummi na sa mata ido." "Kai sangarta ka nayi." "Allah Sitti ai na sani." Ummi tai waje yace "Sitti gobe zan zo na dauke ta. "Ba zaka barta tai ko sati ba." "Itama ba zama zatai ba Zaki gani." Ya karasa ya rumgume ta yace "Sai da safe." Ta mike ta rakasu har mota sannan ta koma ta rufe kofar Baban falo tayi cikin dakin da su Najwa suke, dariyar su ta fara jiyowa ta karasa tace "Oh ku bakwa jin bacci ko?" "Bacci tin yanzu Sitti kije ki kwanta ki huta sai da safe." "Shikenan ga wacan gashin naman kuje kuci kusa dayan a firij." "To Sitti Ina su Ummi?" "Sun tafi." Ido ta zaro tace "Anan zan kwana?" "Menene da nan din?" "Ni gida zan tafi." "To sun tafi sai ki bari gobe Kya tafi." Najwa tace "Kai Sis ni na zata zan samu 'yar uwa anan." Kafada ta make tace "Na bar Ummi ita kadai." Sitti ta juya tace "Uhmm ni sai da safe." Najwa tace "Bari na dauko mana Nlnaman." Wayar ta, Maryam ta dauka ta fara kiran Ummi, suna hanya Ummi taga kiran ta dauka tace "Daughter lafiya?" "Ummi shine kuka tafi?" "Au kin fasa kwanan?" "Ummi ni ba zan iya bacci anan ba." "Haba Daughter menene da nan din kiyi zaman ki gobe kya dawo kinji?" Kai ta gyada tace "Ina Haidar?" "Gashi yai bacci." "Yaa Aliyu fa?" "Gashi yana tuki." "Oh kuna tare?" "Eh!" "Sai da safe." Ta kashe wayar, Aliyu yace "Wacece?" "Kaima ka sani wai ita bata son kwanan kuma." "Hmmm." Yai murmushi yai horn a bakin gate din gidan nasu. Kwana sukai suna hira tsakanin Maryam da Najwa, anan Najwa take fada mata zancen saurayin ta Abdul cewar ya rigata dawowa Kuma yace tana dawowa zai turo ayi maganar auren su, Maryam tai murmushi tace "Kace nan kusa zamusha biki." Kai ta gyada tace "Ki fara shiri." Sukai dariya, Najwa tace "Nasan gobe zai zo to ya me zamu tsara masa?" "Ki bar min komai kawai " Suka tafa sai wajen uku suka kwanta kuma karfe biyar saura suka mike, sallah sukai sannan suka gyara gidan tsaf suka saka turaruka masu dadin kamshi sannan suka shiga kitchen hada breakfast sai da suka gama, suka shiga wajen Sitti dake zaune akan darduma tana jan carbi, har kasa Maryam ta durkusa ta gaishe ta sitti ta amsa tace "Ya gidan?" Murmushi Sitti tayi tace "Lafiya lou Sitti akwai abinda kike bukata ne?" "A'ah duk abinda kukai ya isa." "To bari na hada miki ruwa." Maryam ta shiga ta hada nata ruwan wanka, Sitti ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya tana fitowa falo suka fito suka jere mata kayan abinci Sitti ta kalli Maryam tace "Sannu Maryam da aiki." Ta faraci su kuma suka wuce sukai wanka suka shirya sannan suka fito tare suka karya sannan Maryam ta koma kitchen ta cigaba da hada kayan abincin rana da anda za ayiwa Abdul. Karfe biyu suka gama komai Najwa taje ta kwanta wai bacci za tayi, Sitti da Maryam kuma suna falo suna hira cike da so da shakuwa, jefi jefi makwabta da yan uwa na zuwa yiwa Sitti sannu da zuwa, har akai la'asar Maryam ta shiga ta tashi Najwa sukai sallah sannan ta shiga shiryawa biyar saura yana compound din gidan Najwa da Maryam ne suka fito shigo dashi. Yana tsaye jikin mota hannun sa daya cikin aljihun rigar sa dayan kuma yana danna waya yaci shadda har da hula idon sa sanye da glass yai kyau sai tashin kamshi yake, tinda ya hango su ya zubawa Najwa ido har suka karaso Maryam tace "Haba ai ko dan ni ka kauda ido." Nuna ta yai da wayar hannun sa yace "Maryam ko?" Kai Najwa ta gyada tana murmushi yace "Na sani ita zatai min haka." "To ai kai naga gaba daya baka da alkunya da ka bari in na bar wajen sai kai ta kallon ta." "A matsayin ki name?" "Sirikar ka mana." "Yess u re my in-law but sis Inlaw kuma karama ma ko?" Najwa ta kalla tace "Ban girme ki ba?" Dariya tayi tace "Hhhh lallai 'yar nan ni din." "Kai nice 'yar ki?" Sukai murmushi tace "Month daya muke fa." "Ah haba?" Abdul ya fada yana kallon su, Maryam tace "Kuma nice babba fa ni 1 ita 15." "Yes kece Babba amman ke ba yaya ta bace? Kin gane saboda nima jikan Sitti ne dan haka ni yayan ki ne ke kuma yayar Najwa yayi?" Najwa ta kalla tai wa gwalo, Najwa ta kalli Abdul tace "Kai Honey kagani ko tana min gwalo." "Rabu da ita ai ba zan bata tsaraba." "Kai a'ah rabamu zatai." Sukai dariya Maryam tace "To kazo mu shiga mun barka tsaye ko?" Suka nufi babban falo inda Sitti ke zaune suka zauna ya gaishe ta yai mata ya hanya suka taba hira sannan suka tafi dakin baki inda aka kai masa hadaddun girkuna da lemuka. Maryam da Najwa na zaune bayan ya gama cin abinci suna ta hira abinsu, bude gate sukaji Maryam dake kusa da window ta bude labule ido ta zaro ta maida labulen ta ajiye, Najwa tace "Waye?" "Yaa Aliyu." Baki Najwa ta tabe tace "Sarkin fada." Ciki ya shiga ya samu Sitti ita kadai rike da Alkur'ani ya shiga ya zauna yana fadin "Uhmm nagaji." Ta kalle sa tace "Ya aikin?" "Alhamdulillah." Ta mike ta zubo masa abinci ta ajiye ya amsa yace "Ya naji gidan shiru ina su Najwan?" "Abdul ne yazo suna wajen sa." "Waye Abdul?" "Wanda yake neman auren ta." "Kuma shine sukaje da ita Maryam din?" "To menene dan taje su gaisa yau dai su hadu." "Uhmmm" Ya dauki spoon din abinci ya kai baki taunawa yai ya hadiye ya dago ya kalli Sitti yace "Ummi ce ta kawo miki abinci?" "Me kaji?" "Dandanon girkin Ummi." Murnushi Sitti tayi tace "Maryam ce tayi." "Maryam ita tai girkin?" "Eh bata muku girkin ne?" "No Sitti kamar na Ummi fa." "To ita da Maman ta dan ta iya girki irin nata shine wani abu, yarinyar nan tana da tsafta da safe kan kace me ta gyara gidan nan ta saka masa kamshi ga breakfast lallai na yadda rainon Aisha ce dan Aisha ma akwai tsafta bata son kazanta sam ga iya girki to kaga itama kamar Aisha take." Abincin sa ya cigaba da ci yana gyada kai dan yai masa dadi gaskiya sosai, dan haka ya cinye tas sannan yasha ruwa ya jingina da kujera yace "Gida nake so na tafi na gano Haidar tin safe rabo na dashi." "To ka tafi mana." "Maryam nazo dauka." "Cewa tai zata tafi yau." "Gobe zata makaranta Sitti." "Kai da Aisha nasan ba zaku bar min Maryam ba, Hauwa kuwa haka ta bar min Najwa gashi yanzu ma muna tare kila aure ne zai rabamu kawai." "Itama fa ba iya zaman nan din zatai ba." Kiran sallah akai ya mike yace "Sitti bari naje nai sallah ki fada mata ina idarwa zan zo mu tafi." Ya fita yai alwala ya tafi masallaci. Abdul ma sallama yaiwa sitti ya tafi gaba daya. Sallah sukai suna falo suna hira Sifti tace "Yayan ki yazo wai zaku tafi." "Yauwah." "Au so kike ki tafi?" Najwa ta fada, murmushi Maryam tayi tace "A'ah gobe da makaranta fa." "Ba sai a kawo miki kayanki ba." "A'ah nayi missing Ummi na." "Kwana dayan." "To ina na taba zuwa na bar Ummi a cikin shekarun nan uku zuwa hudu." Sai bayan sallah isha'i ya shigo ya zauna Sitti ta shafa addu'a tace "Ka dawo?" "Eh tana ina ta fito mu tafi." "Tana ciki." Ya mike ya nufi corridor dakin ya kwalla mata kira da sauri ta mike tana amsawa ta fito tace "Gani Yaya." "Kizo mu tafi." "Toh." Ta koma tacewa Najwa dake waya "Sai gobe." Ta fice a dakin Najwa ta biyo ta, taiwa Sitti sallama Sitti tace "To sai yaushe?" "Zanzo da weekend." "To Allah kaimu sai da safe." Har bakin mota Najwa ta rakata suka tafi suna dagawa juna hannu. Tin da ta koma gida kuma sai ta mai da hankalin ta akan karatu suna waya da Najwa dan Najwa ma taje gidan ta gaida su Inna sannan ta koma wajen Sitti. A dawowar su Inna har an saka auren Najwa da Abdul wata bakwai, aka tsayar dan haka dagin har sun fara shirye satin su uku da dawowa tinda Yaa Aliyu ya dauko ta bata koma ba, shiyasa tin jiya Friday ta fadawa Ummi zataje. Saukowa tayi daga bene sanye da maroon kalar doguwar riga, sai brown kalar mayafi da ta yafa sai kamshi turare take wajen Ummi takarasa tace "Ummi na sauko." Dagowa Ummi tayi tace "Ah har kin shirya?" Zama tayi a gefen kujera tace "Eh Ummi." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:11] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 7 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dis page is for you Sis *AISHA BASHIR* thanks for ur support i reallu do appreciate 😘😘😘 Mikewa Ummi tayi ta shiga kitchen ta dauko wata babbar leda ta mi'ka mata ledar tace "Ki kai wa Sitti." Ta amsa sukai sallama ta fita ta shiga mota Baba Anas ya tada motar suka tafi, suna zuwa Sitti ta amshe ta da murnar dan tana son Maryam sosai Maryam ta rumgume Sitti cike da jin dadin ganinta ita ma, Maryam tace "Nayi kewar ki Sitti." "Ba wani nan, amman kika guje ni." "Kai Sittj nasan Najwa ce zata hada mu, Sitti makaranta shiyasa." "To anan hanaki zuwa za ayi?" "A'ah Amman na bar Ummi ita kadai." "Uhmm ke da Aliyu ban San wa yafi son Ummin nan ba." Murmushi Maryam kawai tai Sitti tace "Yasu Aisha da Hauwan da Barira?" "Duk suna lafiya." "Ina Innan taku?" "Tana lafiya lou sunce a gaishe shi." Mikewa tayi tai hanyar dakin Najwa tace "Tana Ina ne?" Ta shiga dakin kwance ta ganta akan gado tana waya juyowa tayi tana ganin Maryam ta kashe wayar ta rumgume ta, sai kuma ta sake ta, tace "Bama ruwa na dake." "To ba gashi na zo ba." "Sai yanzu wajen uku saura har na kira Abdul nace yazo fa." "Ah shikenan nayi hira ta da Stti na" Hararar ta tayi tace "Bari na kira nace ya fasa zuwa kawai." "Ah ah bari kawai." Ta dauki waya ta fara kiran layin Abdul bai dauka ba har ta kira sau biyu, Maryam ta mike tana ajiye mayafi tace "Me zan samu a gidan ne?" Ta fita tace "Sitti wane kayan dadin zan samu." Ta fito ta zauna a gefen Sitti, tare da dauka kan ta a kafadar Sitti. Sitti tace "Ina Haidar?" "Yana tahfiz." Ta fada ta mike ta Shiga kitchen bata Jima ba ta fito da bowl a hannun ta da lemo ta zauna a kusa da Sitti ta Fara ci, tana cikin ci sukaji sallama daga bakin kofa. Amsawa sukai Abdul ya shigo tare da abokinsa, Sitti tace "Sannun ku da zuwa, ashe mai gidanane." Murmushi Abdul yayi yana kallon Maryam da ta ki kallonsa Sitti tace "Bismillah ku zauna." Zama sukai Maryam ta dago tana ganin Abdul ta zaro Ido tace "Ashe ango ne." Yai murmushi ya durkusa yace "Ina yini Sitti?" Suka gaisa, Sitti ta kalli wanda suke tare tace "Muhammad ko? Kwana biyu tinda ka baro can ban kara ganin ka ba." Yai murmushi yana kallon inda Maryam take ita kuwa duk da tana jin Ido akan ta bata dago ba, murmushi yayi yace "Wallahi Sitti na dawo naji dadin gida Nigeria shiyasa nai zamana." Da sauri Maryam ta dago kai jin muryar kamar ta san me ita tana ganin sa ta sauke Ido duk ta kasa sakewa, Sitti tace "Ai yafi wallahi ya gidan da iyayen naka? Ya aiki? Ko kayi aure ne?" "Alhamdulillah suna lafiya A'ah Sitti tukkuna dai." "To Allah ya kawo mace ta gari mai sonka." "Amin Sitti nagode." Abdul yace "Maryama ya gida da school? Ai na miki magana a online shekaran jiya naga baki ban amsa ba." "Uhmm ni wayar fa wani lokacin mantawa nake da ita." "To saurayin ki fa?" Ido ta zaro tace "Saurayi kuma a'ah tukkuna dai." Yai murmushi yace "A'ah nifa ban yadda ba da kike cewa baki dashi." "Aliyu ne zai barta kula wani namiji." Sitti ta fada, tace "Kana ganin Najwa ma yaushe ta fara soyayyar ai sai da ta bar gida in dan ta shine ba zata fara ba cewa yake ma wai tai kankanta da aure." Dariya dukka sukai, Muhammad kuwa kallon Maryam kawai yake wanda idon sa da take ji akan ta ya hanata sakewa Sitti tace "Maryam kawo musu ruwa mana." Da sauri ta mike ta shiga kitchen jingina tayi da bango tana mai da numfashi kamar wacce tai gudu, Ido ta lumshe tace "Meyasa nake haduwa dashi ne?" Ta jima kan ta fito dauko tray mai dauke da lemo da ruwa da cups ta ajiye ta koma kusa da Sitti ta zauna kamar zata shige jikin ta, Abdul yace "Ya naga yau baki sakewa ne ko bakya jin dadi ne?" Kai ta girgiza sai kuma ta mike da sauri tace "Bari na kira Najwa." Tayi dakin da Najwa take, rike ta ganta da waya ta zauna tace "Me kike ne?" "Sai neman number Abdul nake taki shiga." Murmushi tayi tace "Wanne Abdul dake falo wajen Sitti." "Ah haba dai tin dazu fa nake kiran sa amman bai dauka ba." "To yanzu dai ki tashi kije." Najwa ta mike taje gaban mudubin ta shafa hoda da dan man lebe ta shafa turare mai kamshi ta dauki mayafi tace "Yaya?" "Kinyi kyau Amarya." "Tin yanzu da saura." "Kamar yau ne." "To Allah nuna mana." "Amin." Ta kamo hannun ta tace "Tashi muje." "No kije." Kallon ta ta tsaya tace "Kamar ya?" Ta bata fuska mikewa tayi tace "Muje." Suka fita sai hira suke da Abdul da Sitti, Muhammad dai sai murmushi yake yana danna wayarsa, su Maryam suka zauna suka gaisa da Najwa da Abdul da Muhammad nan aka cigaba da hira gaba daya a parlon Maryam dai na jikin Sitti a kai a kai Muhammad ke kallon ta, har kusan Asr, sannan suka fita sukai sallah da suka dawo a falon ba'ki suka zauna Najwa tayi tayi da Maryam suje amman taki zuwa dole ta tafi ita kadai. Har magariba sai da suka dawo daga sallah Muhammad yace "Wacece yarinyar nan Abdul?" Abdul yai murmushi yace "Ko dai kana ciki ne Muhammad?" Shafa kansa Muhammad yayi, tare da murmushi Abdul yace "Haka ne?" Murmushi Muhammad ya sake sannan yace "Na santa ne shi sa nake tambayarka" Da mamaki Abdul yace "Haba, amma ban ga ta nuna alamar ta san ka ba" Murmushi Muhammad yayi yana shafa sajensa yace "Ni na nuna alamar na santa banda yanzu da na fito?" Abdul yace "Kenan soyayya kuke?" "No!" "To menene tsakanin ku?" "Kafin nan wacece ita?" "Cousin din Najwa ce." "Na taba taimaka mata amman kar ka damu da wannan, 'kawar Jawahir ce." "Ah haba amman ta gane ka kuwa?" Murmushi Muhammad yayi yace "Ta gane ni bakaga yadda take ba ta kasa sakewa a wajen" Abdul yayi dariya yace "Ohh naga alama da akwai wani abu a kasa kenan" Muhammad yace "No at all " Tin kan magariba Maryam take son tafiya amman Najwa taki barin ta wannan yasa tana idar da sallah ta mike tace "Tafiya zanyi Sitti." Najwa tace "Da daren nan." "Eh." "Please ki kwana." "A'ah gobe akwai abinda zanyi." "To yanzu Yaya za ayi?" "Zanje na samu napep " Ido Najwa ta zaro tace "Kinsan halin Yaa Aliyu bai son ana hawa motar haya gashi drivern Sitti bai dawo ba." "Ke ni ko a kafa zan koma gida " Dariya Najwa tayi tace "Ah lallai sannu." Ta mike Najwa tace "Wai da gaske sai kin tafi?" "Yes " Sitti ta kalla tace "To bari naje wajen su Abdul in sun gama cin abinci sai su ajiye ta ko?" "Eh hakan yayi." Zama Maryam tayi Najwa ta fita bata jima ba suka shigo ita da Abdul da Muhammad suka zauna sannan Abdul yace "Sitti zamu tafi." "To Abdul a gaida mutan gidan." "Zasuji Sitti." Muhammad ya durkusa cikin muryar sa mai sanyi yace "Sitti zamu tafi sai wata rana." "To Muhammad a gaida mutanen gidan." "Zasuji." "Nagode sosai." Kudi Muhammad ya zaro ya ajiye mata sannan yace "Mungode." "Ah ah Muhammad meyasa haka?" "Sitti ki sa mana albarka kawai." "To Allah yayi albarka." "Amin nagode " Suka mike suka fita. Maryam ta kalli Sitti tace "Ni kamar na kwana." "Kuma dai" Mikewa tai tace "Sai da safe." "Allah kaimu ki gaida mutanen gidan." "Zasu ji." Fita tayi taga Najwa da Abdul a tsaye, Muhammad zaune a driver seat, tsayawa tayi a gefen tana danna waya Abdul ne ya dago yace "Ah kina tsaye ki shiga ki zauna mana." Motar ta bude ta shiga baya ta cigaba da danna wayar ta. Sai da sukai sallama da Najwa da Abdul sannan ta leko tacw "Sai kuma yaushe?" "Sai kin ganni kawai." "Uhmm daman ke! sai da safe ki gaida su Ammi kan nazo." "Sai kinzo." Sukai sallama Hira Muhammad da Abdul suke tayi a motar, ita dai danna wayarta kawai take, amma da ta daga kai za su hada ido da Muhammad ta madubi, sai tayi maza ta sauke kanta, bayan tafiyar kusan minti goma ta ji Abdul yace "Kaga Muhammad ajiye ni nan zan biya ta wajen Fu'ad mu hadu a gida in ka ajiye ta." Parking Muhammad yayi, Abdul ya fita yana kallon Maryam yace "Toh 'Kanwar ce ko Yayar?" Tai murmushi tace "In muna tare da Najwa ni Yaya ce in bama tare ni 'kanwar kace." Yai murmushi yace "To 'kanwata sai mun yi waya ki gaida Ummi, abokina zai ajiye ki gida" Fuska ta shagwabe zatai magana yace "Dare yayi ki barshi ya kai ki gidan nima akwai wanda zan gani in ban ganshi yanzu ba nasan da wuya na ganshi nan kusa please sorry kinji Muhammad babban aboki nane kuma dan uwa gareni zai kula dake kada ki damu." Kai ta langwabar kawai yace "Kar ki damu kinji?" Kai ta gyada, ya kalli Muhammad yace "Drive her carefully plss sai mun yi waya" Daga haka Muhammad ya ja motar suka hau saman titi, Maryam dai sai wasa take da fingers dinta, bayan wani lokaci ta dago a hankali tana kallon gaba suka hada ido ta madubi, da sauri ta sunkuyar da kanta, yayi murmushi yace "Kina tsoron kada in sace ki ko?" Kin cewa komai tayi, bayan kusan minti biyu taji cikin cool voice dinsa yace "I am Muhammad Auwal, mahaifi na haifaffen garin Kano ne kasuwanci, da siyasa su suka kawo mu Abuja da zama, a UK nai primary da secondary na, har sa University mun jima da Abdul dan tare mukai secondary har graduation, acan ma muna zuwa gaida Sitti sosai, am a doctor now." Kallon sa kawai Maryam take ta madubi, yayi murmushi yace "Kina kallo na, Jawahir kanwa tace dan mahaifin mu daya nine babba a wajen mahaifi na. So ki daina tsoro na ni bana yanke kan mutane." Daga haka yayi shiru ya kalleta yana murmushi yace "Zan iya sanin ki?" Shiru tayi da farko, can a hankali tace "Sunana Maryam" Ta kallesa don a hankali yake driving din kasancewar babu motoci sosai titin, ya gyada mata kai alamar yana ji, yana murmushi, murya can kasa tace "Kasan gidan mu da yan uwa na so me kake son ka sani, Jawahir 'kawatace mun hadu shekaru hudu baya tin da muka zana waec har yanzu da muke karatu tare." "Masha Allah Allah ya taimaka to." Murmushi tayi murya can kasa tace "Ameen" "Samarin ki nawa?" Ya jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba, ido ta zaro "Samari kuma?" Yace "Yeah" Ta girgiza kai tace "Tabb, ni bani da Samari" Yace "Sai dai friends kenan?" Ya fada yana kallon ta tare da wani murmushi. "Uhmmm." Ya fada ta bata fuska tace "A school bani da male friends, ka tambayi Jawahir." Dai dai lokacin da yai parking a kofar gidan su, da sauri tace "Ajiye ni anan ba sai ka shiga ba." Yai parking ta bude kofar motar tace "Nagode" "Kar ki damu ki gaida Ummi." "Zataji." Ta sauka ta rufe kofar ta nufi gate din su tsaye taga Aliyu rike da mukullin motar sa, kai tayi kasa dashi dan yaki bata hanya jikin ta sai rawa yake zuciyar ta na bugawa ciki yayi ta tsaya a wajen tana kallon yadda yake tafiya a hankali cikin nutsuwa, sanye yake da bakin wando da farar riga mai gayeren hannu, gashin dake kwance a hannun sa baki masu tsayi zara zara, ajiyar zuciya ta sauke sannan tabi bayan sa tana tafiya kamar ba zatai ba. Tana shiga compound din su tai karo da abu da sauri tai baya a mugun tsorata wanda hakan yasa rumfashin ta ya tsaya cak, da sauri ya taro ta, ta fado jikin sa fuskar ta ya fara jijjigawa jin tai masa nauyi lekawa yai ya tabbatar da abinda yake zargi, janta yai zuwa bakin famfam dake wajen ya kunna ya debo ruwan ya shafa mata wata ajiyar zuciya ta sauke ya dauke ta ya karasa da ita kan wata ginnanniyar kujera dake wajen, a hankali ta bude ido tana ganin sa ta mike zaune da sauri tana kallon wajen, ya hade rai yace "Waye ya ajiye ki a mota?" Ta zaro ido sai kuma ta turo baki bata san duk yana kallonta ba, yace "Ba tambayar ki nake ba" kamar zata yi kuka murya can ciki tace "Abdul ne fa" Fuska ya kara hadewa yace "Ni za ki ma karya?" Shiru tayi yace "Ba magana nake miki ba?" "Me?" "Nace wa ya ajiye ki?" Ta rufe idonta tace "Abdul ne" yace "Maryam." Dagowa tai tana kallon sa, yanayin sa kadai ya canja ya kada mata kai kawai tai saurin yin kasa da kanta tace "Yaya abokin Abdul ne fa, tare muke da Abdul shi sai ya sauka a wani anguwa zai ga wani shine abokin ya ajiye ni shi, ka kira Yaa Abdul din ma ka tambayesa wllh" Yana gyada kai yace "Akan me ya kawo ki to? Dan me kika hau motar Abdul din?" Kasa tai da kan ta yace "Ba magana nake ba?" "Yaya to ba mai kawo ni ne, ni kuma ba zan kwana a can ba." Wani kallo yake bin ta dashi yace "Meyasa baki kirani ba ko ki kira Ummi ta turo driver." Baki ta turo ya dauki hannu ya buge bakin yace "Ina miki magana kina turon baki?" Bakin ta dafe hawaye na taruwa a idon ta, yace "Na sake ganin kin fita ba driver sai ranki ya baci, na hana fitar ma gaba daya kina ji na ko?" Shiru tayi yace "Ba magana nake ba?" Kai tai saurin gyadawa yace "Tashi ki ban waje." Da sauri ta mike wani irin jiri taji tai saurin dukewa kasa tana dafe kan ta ya mike ya karaso yace "Me ya faru?" "Kaina jiri nake ji." "Tashi ki koma ki zauna." Mikewa tai tana runtse idon ta sai kuma ta bude tana kallon hanya a hankali tace "Zan iya tafiya." "Ok jeki." Ta fara tafiya a hankali har ta karasa bakin kofa, juyowa tai ta kalle sa dan yana tsaye bai motsa ba sai kallo ta da yake dauke kai yayi itama ta juya ta bude kofar ta shiga. Komawa yayi ya zauna yana dafe kan sa. Tana shiga Ummi tace "Ah ai na zata kwana zaki." Zama tayi tana dafe kan ta dake sara mata tace "A'ah." "To wa ya kawo ki?" "Abokin Abdul ne ya kawo ni." "Abokin Abdul kuma?" "Eh tare muke da shi." "Ok amman me yake damun ki?" Kai ta nuna tace "Kaina ke ciwo." "To kije ki sha magani." Fuska ta bata Ummi tace "An fadi makiyin ki ko?" Mikewa tayi tace "Haidar fa?" "Yana wajen Mamin ku." "Yau kuma can akayi?" "Mun shiga dazu shine ya zauna." Sama tayi ta shiga tai wanka ta fito tai sallah isha'i ta kwanta dan kan ta dake ciwo. Tin da ta shige ya koma inda suka tashi ya zauna, yafi minti goma yana zaune yaji ana kiran sallah mikewa yai ya tafi masallaci. Sai bayan yai sallah ya fito ya nufi sashen Ummi, a zaune ya same ta akan sallaya ya zauna yana fadin "Haidar bai dawo ba?" Ta gyada masa kai kallon sama yayi yace "Maryam fa?" "Ta shigo bayan fitar ka amman wai ciwon kai take." "Ta sha magani?" "A'ah kasan ta da magani ai." Mikewa yai ya shiga daki ya dauko magani har da allura ya fito ya nufi sama tana kwance har bacci ya dauke ta taji ana buga kofa cikin muryar bacci tace "A shigo" Ta koma ta kwanta murda kofar yai ya shigo tsayawa yai a gefen gado jin kamshi turaren sa yasa tai saurin bude ido dake cike da bacci da ciwo kuma. Kan sa yai saurin daukewa yace "Tashi kisha magani." "Yaya ya daina fa." "Oh ba zaki sha ba ko?" Shiru tayi ya ajiye ledar ya dauko siriji da ruwan allurar ya fara shirin zuka a firgice ta mike tace "Yaya amman bani zakai wa allura ba?" Bai dube ta ba ya fara zukar allurar, ta fashe da kuka tace "Dan Allah Yaya kada kai min wallahi bana so." "Zaki sha maganin?" Kai tai saurin gyadawa, yace "To dauki ki sha." Ta mike ta balli maganin ta sha tana dafe kirji sai ta fara kokarin kuma ta shi da sauri yace "Kika amayar sai nai miki allura." Ai a guje ta shige bandaki ta dinga kwara amai, bakin kofar ya isa yana tsaye ta gama ta dauraye wajen ta raba ta gefen sa ta fito, kan gadon ta kwanta tana mai da numfashi yace "Allurar fa." Mikewa tai ta fara yarfa hannu tace "Wayoo Ummi kizo Yaya zai min allura." Hararar ta yayi yace "Sai fa na miki tinda ke bakya son magani." "Zan kara wallahi zan kara." "A'ah ba zaki min asara ba." Hawaya ta hau yi ya matso yace "Tashi tsaye." kin tashi tayi yana matsowa ta mike da sauri tana yarfe hannu tace "Dan Allah Yaya kayi hakuri." Janyo ta yai ta fada jikin sa wani abu yaji ya tsarga masa da sauri ya matse hannayen ta ya zura mata allurar ta saman wandon baccin ta kuka ta saki ya dure ruwan allurar sannan ya zare allurar hannun sa ya saka yana mulmula wajen sannan ya sake ta da sauri ya nufi kofa, kan gado ta fada tana kuka tare da kiran sunan Ummi, a haka bacci ya dauke ta sai ajiyar zuciya da take saukewa. Cikin dare da ta tashi ba ciwon kai dan tai sallah ta koma ta kwanta. A haka ta cigaba da karatun ta, zaune take a dakin ta bayan ta dawo daga makaranta taci abinci tai wanka jakarta ta janyo ta zaro wayarta ta ajiye a gefe wani memo ta dauko ta bude tana karanta abinda ke ciki wayar ta ce tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dauka tayi tace "Ya akai?" "Question dinan zaki turon yanzu zan nunawa Yaa Khalifa." "To bari na turo miki." Ta kashe wayar missed call har biyu ta gani da sabuwar number bakinta ta tabe ta shiga whatsapp ta tura mata sannan ta ajiye wayar ta sauka kasa. Da dare ma tazo kwanciyya ta duba wayar ta kara ganin missed call din da thesame number dazu, agogo ta duba taga tara ta wuce to waye zai neme ta, kwanciyya tayi kawai. Washe gari bayan ta dawo daga makaranta tana kan sallaya ta idar da sallah jakar ta ta janyo sai taga missed call, dailing number tayi har ta katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga call din ya shigo wayarta, dagawa tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, ta amsa tace "Waye?" "Ya kike?" Aka tambaye ta, fuska ta dan hade tace "Uhmm nace waye?" "Ki amsa min mana yan mata." "Wa kake nema please wrong number." Zata katse taji yace "Wait mana. Ki tsaya na fada miki waye to." "Naga baka da niyya." "Muhammad ne, tin ranar da na sauke ki naso naji ya kika shiga gida to sai jiya Abdul ya ban number ki." Wani murmushi ta saki ta d'an bude ido da mamaki amma ta kasa cewa komai, yayi murmushi a hankali yace "To ya kike?" Murya can kasa cike da kunya tace "Alhmdulillah" Yace "Ya school?" "Alhamdulillah." "Masha Allah." Sukai shiru a hankali yace "Nasan yanzu kika dawo bari na barki ki huta sai anjima." "Nagode." Tin daga ranar kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, dan tana jin dadin yadda yake nuna mata kulawa yace taci abinci? Ya makaranta? Ko tana da wata matsala irin wadan nan abubuwan dai kullum yana kira su gaisa wani lokacin sai dai taga missed call dan ita ba ta wani damu da waya sosai ba sai dai ta kira in ta kira kuma bai dauka sai ta katse yake kira. Ranan wata Wenesday Maryam da Jawahir suka fito daga library a gajiye suna jiran driver wata mota ce ta karaso tai parking acan gefe wayar Jawahir ce tai kara ta duba tace "Yaa Khalifa." Sai ta kai kunnen ta dagowa kai tana bin motar gefe tace "Wallahi ban lura ba gani nan." Maryam ta kalla tace "Wai ashe Yaa Khalifa ne a motar can zo muje ku gaisa." Muhammad dake cikin mota tunda yayi parking idonsa ke kan Maryam, wacce take sanye da wani cream kalar less anyi zane da purple kalar zare sosai yai mata kyau ta saka mayafi three in one purple kala fuskar ta ta kara fresh, suna hada ido gabanta ya fadi, Jawahir tace "Yaya ga Maryam." Ta kalli Maryam tace "Kin gane shi ai?" Maryam ta d'an yi murmushi kawai, Jawahir tace "Yaya kai fa?" Shima murmushin yayi yace "Na gane ta ba bestyn ki ba?" Kai ta gyada. Maryam ta sauke idonta kasa tace "Ina yini?" yace "Lafiya lau, ya makarantar?" Tace "Alhamdulilalh" Ta dan dago suka hada ido wani lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana" Ta girgiza kai tace "Aa yanzu driver dina zai zo" Yace "Ohk" Ta dago ta kalli Jawahir tace "Sai gobe ki gaida Momy." "Zataji." Motar gidan su ce ta shigo, Jawahir tace "Yauwah kinga sai mu tafi tare ma." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:16] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 8 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dis page is for both of you, *Jamila Yusuf, Khadija Salisu, Amina Muhd, Zainab Muhammad, Ubaida Abubakar Fari, Aisha Maman Fahad* from MATAR HAIDAR FANS GROUP, ina godiya mutanen Amana Allah ya bar kauna. Bayan isha'i ta idar da sallah, ta mike ta nufi kofar fita wayar ta dake can kan mudubi ta fara ringing kan ta karasa ta katse, tana dauka taga Muhammad ne ya kirata, komawa tayi ta zauna tayi dialing, katsewa yayi ya kira cikin cool voice din sa yai mata sallama ta amsa tare da gaishe shi. Yace "Ba zan amsa ba bayan dazu nunawa kikai baki sanni ba." "Nima ai haka kai min." Tai maganar a shagwabe, yai murmushi yace "Nifa ba kuka nace ki min ba ko?" "Uhmm to ina yini?" "Lafiya lou ya gajiyar school?" "Alhamdulillah." "Masha Allah. Dazu kinyi kyau amman fa." "Hmmm kaji ka." "Allah da gaske ban gaji da kallon ki ba." "Uhmm ina Abdul kwana biyu." "Baku hadu ba?" "Eh kwana biyu banje gidan Sitti ba." "Yaushe zakije?" "Ban dai sani ba." "To ya shirye shiryen biki?" "Alhamdulillah." "Allah ya kaimu." "Amin." "To sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." "Amin." Ta kashe wayar ta mike ta fita. * Yau watan ta biyu kenan rabon ta da gidan Sitti ba wai zuwan ne batayi ba tayaya zata tambayi Yaa Aliyu zata take tunani tasan halin sa, da sauri ta mike tace "Shi Yaa Aliyun nan in yasan wata bai san wata ba Abba zan tambaya tinda yana gari." Ta mike ta nufi dakin Abba sallama tai yana zaune a falon sa ya amsa ta shiga ta zauna tare da marairaice fuska tace "Abba zan je gidan Sitti nayi ko sati daya ne tinda mun samu hutu." "To Maryam ki shirya ki tafi mana kin fadawa Maman taki?" "A'ah haka nace bari na fara fada maka." "Ok kije ki shirya to." "Nagode Abba." Ta mike ta shiga dakin Ummi a zaune ta same ta tana danna wayarta, ta zauna tace "Ummi gidan Sitti zani nayi mata sati daya." "To yaushe zaki tafi." "Yanzu in na gama hada kaya na." "To shikenan. Je ki hada kayan." Ta mike ta fita tana murna, dakin ta ta shiga sai ga kiran Muhammad nan dauka tayi tin daga muryar ta ya gane tana cike da farin ciki yace "Ya dai yar gida na?" Tai murmushi tace "Yau zani gidan Sitti." "Da gaske ko na zo na kai ki?" "A'ah." "Why?" "Ba komai." "No ba dai ki yadda dani ba ko?" "A'ah fa." "To in ba haka ba zan zo na kai ki." "To shikenan." "Da karfe nawa." "Yanzu." Yai murmushi yace "Gani nan." Ba ai minti ashirin ba sai ga Muhammad ya kira ta wai yazo, jakar ta ta rufe ta mike ta fita a dakin wajen Ummi ta shiga tai mata sallama sannan taje wajen Abba ta fita taje wajen Sitti tana fitowa daga wajen Sitti ta hangi Aliyu na tahowa sanye da wando nude colour sai milk riga mai dogon hannu, kafar sa da sandal baki, kamar ta koma ciki haka taji amman saboda ya ganta sai kawai ta maze ta fara takowa. Tinda ya hango ta yake kallonta, Maryam kuwa sai sunkuyar da kai take gabanta na faduwa, kallon sashin su yayi sannan ya kalleta yace "Ina za ki?" "Gidan Sitti" "Wa kika tambaya?" "Abba." Ta bashi amsa kamar zatai kuka. Akwatin dake hannun ta ya kalla tai saurin yin kasa da ido yace "Akwatin fa?" "Kaya nane a ciki." "Me zaki dasu?" Ya tambaya yana tsare ta da idanun sa masu birkitata. Da sauri ta dauke idon ta tace "Kwana zan." "Kwana?" Ta gyada kai, kallonta ya tsaya yi sai kuma ya juya ya bar wajen dagowa tayi taga ya bar wajen ta sauke ajiyar zuciya ta fara tafiya. A bakin babba parking space na bakin gate ta ganshi zaune cikin mota tana karasawa ya bude sit din gefen sa tare da mata nuni da gefen sa ta kalli wajen kamar zatai kuka tace "Yaya yanzu ka dawo kaje ka huta driver zai kaini." "No shige muje." Ya fada ba alamar wasa a tare dashi. Kamar zatai kuka ta shiga motar wayarta ta dauka ta fara rubuta masa text kamar haka "Am sorry kaga Yaya zai dropping dina nace ya barshi yaki kayi hakuri." Ta tura masa mota suka tayar suka fita a gate din. Muhammad yana mota yaji shigowar text din ta ya bude yana karantawa ya tada mota kan motar su ta fito ya bar layin, sai da yai nisa sannan yai mata reply "Ohk no problem, anjima da yamma zanje can gidan insha Allah" Sakon na shigowa ta bude tana ganin abun da ya rubuta ta sauke ajiyar zuciya ta kara typng wani da cewa "Kayi hakuri don Allah" Sakon na zuwa wani ya kara shigowa "Noo ba komai dear, ai Yaya ne, kar mu yi laifi ko" Ido ta lumshe sannan ta bude ta mai da masa da amsa da "Toh nagode" Duk abinda take Aliyu na kallon ta ta gefen idon sa tana gama typing Fuska daure Aliyu yace "Inga wayar?" Da sauri ta dago ya gyada mata kai yana mika mata hannu. Jiki a sanyaye ta mika masa wayar ya amsa ya zura a aljihu sannan ya cigaba da driving din sa. A haka suka iso gidan Sitti ba wanda yace da dan uwan sa kala, yai parking tai sauri ta bude motar ta fita shima kashe motar yai ya fito, ya bude boot ya dauko akwatin ta yai ciki da ita dan har ta shige. Sitti zaune parlor sai Maryam dake jikin ta kamar zatai kuka Aliyu ya shigo da sallama Sitti ta amsa ya zauna yana gaishe ta, Sitti ta amsa da fara'a tace "Ashe kai ka kawo ta?" Kai ya gyada kawai ya jingina da kujera yace "Daga aiki nake yunwa nake ji." "Ai ga abinci nan a dining je ka zuba ka ci.". A hankali ya mike ya karasa dining din, Maryam ya kalla yace. "Zo ki zuban." Da kyar ta mike ta karaso kamar ba zata karaso ba dan yadda take tafiyar ta zuba masa ta shige dakin Najwa kwance ta same ta tana waya ta daka mata duka ta dago da sauri tana ganin Maryam ta saki ihun murna tace "Oyoyo." Ta zauna Najwa tace "Ke da wa?" "Baki ta tabe tace "Yaya mana." "Sarkin yan fada." "Uhmmm." Kawai tace, Najwa tace "Meyake damun ki ne?" Kan gadon ta haye tace "Ba komai." Yana gama cin abinci ya mike yace "Sitti bari naje na dawo." "To sai ka dawo." Ya fita, Maryam da Najwa ne suka fito, Maryam ta kalli dining taga ba Aliyu da sauri ta karaso tace "Sitti Yaya fa?" "Yanzu ya fita." Da sauri ta fita dai dai lokacin da zai fita da mota tace "Yaya." Ya tsaya ta karasa tace "Yaya don Allah ka ban wayata" Wani kallo da ya tsoratata yai mata, ta koma baya a hankali, yaja motar ya bar gidan. Ciki ta dawo ta zauna a kusa da Sitti, Sitti tace "Kin same shi ne?" Kai kawai ta girgiza. Sitti tace "Ai zai dawo nan baya ya tafi." Gaban Maryam ne ya fadi, da sauri tace "Zai dawo kuma?" "Eh." Najwa ta kalla tace "Kina da number Muhammad ne?" "Wanne Muhammad?" "Abokin Abdul." "A'ah." "To kira Abdul din nai masa magana please." Wayar Najwa ta bata ta fara dailing number sa amman bata shiga sam, ajiye wayar tayi tana tsaki, Sitti tace "Lafiya?" Kai kawai ta girgiza ta mike tai cikin dakin Najwa kan gado ta kwanta tana tunanin mafita dan hankalin ta a tashe yake kar Muhammad yazo Yaa Aliyu kuma yana nan tasan kashin ta ya riga ya bushe, bama haka ba kada ya kira wayar ta tana wajen Yaya Aliyu duk sai ta kasa nutsuwa Har la'asar tana dakin Najwa na falo ita da Sitti dan ta shigo tana ta jan Maryam da hira amman da yake bata cikin nutsuwar ta sai ta kasa biye mata wannan yasa Najwa ta fita itama Maryam sai taji hakan ya fiye mata, can wajen biyar sai ga Najwa ta shigo tana makeup Maryam na kallon ta tace "Ina zaki?" "Abdul ne yazo." "Oh haba ki gaishe shi." "Ba zaki fito ku gaisa ba." "Ke kyale ni yau bana jin dadi." Dagowa tai ta kalle ta tace "Shikenan." Ta fita Maryam ta koma ta kwanta can bayan mintina ashirin sai ga Najwa ta dawo wayar ta ta mika mata tace "Ana kiran ki." Amsa tayi ta kara a kunne muryar sa taji cikin sanyi yace "Ina wayar ki ne?" "Tana motar Yaya." "Motar Yaya kuma?" "Eh na manta ne dazu." "Alright tare muka zo da Abdul duk da ni ina compound wajen ki nazo ina jiran ki." "To ina zuwa." Ta fada zuciyar ta na bugawa, kar ta fita Yaya ya dawo yanzu. Mayafin ta ta yafa ta fita falo gefen Sitti ta zauna murya cike da damuwa tace "Sitti wai Muhammad ne yazo yana waje." Kallon ta Sitti tayi tace "Wanne Muhammad?" "Abokin Abdul." "Me yazo yi?" "Uhm daman uhm yazo mu gaisa ne." Murmushi Sitti ta saki tace "Ah ko dai saurayin ki ne? Ai yaron yana da hankali." "Kai Sitti" Ta mike ta nufi kofa Sitti tace "To ke ba zaki shafa ko yar hoda ba." Fuska ta shagwabe tace "Sitti nifa ba saurayi na bane." "Naji amman zo nan." Ta koma tace "Shiga ki dan shafa hoda ko kadan ne." Maryam ta juya ta shiga ta shafa hoda har da man lebe tana fitowa falo Aliyu na shigowa, wata faduwar gaba taji tayi wanda sai da ta dafe kirjin ta, ciki ta koma da sauri tana jin sa ya shigo ya zauna. Komawa daki tayi a gefen gado ta zauna can ta mike tana son ta kira number sa amman wayar akwai security cillar da wayar tai dan ita tata wayar ba wani security kwanciyya tayi kawai. Muryar Sitti taji tana kwada mata kira ta mike da sauri amman bata amsa ba Sitti jin shiru ta mike ta shigo dakin dafata tayi ta dago da sauri alamar ta shiga wata duniyar tunanin, Sitti tace "Kin bar yaro waje fa." "Ai suna tare dasu Najwa." "Duk da haka dai kije ko gaisawa ne kuyi." Mikewa tayi tace "To Yaya fa?" "Ina ruwan sa dake tashi kiji maza kinji." Mikewa tai Sitti ta fita, Najwa ta leko tana leken Aliyu da kyar tai ta maza ta fito bata kalle sa ba ta fice Sitti ya kalla yace "ina zata?" "Zasu gaisa da Abdul ne." Shiru kawai yayi, a cikin mota ta ganshi ta juyo tana kallon kofar falon tace "Ni dai sauko mu shiga daki wajen su Najwa." "Saboda me?" "Yaya zai fada." Yai murmushi yace "To shikenan." Ya sauko ya rufe motar suka shiga dakin dasu Najwa suke gaisawa sukai da Abdul sannan suka zauna a dining space din dakin, kallon ta yake ita kuwa ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun ta yace "Long time ba haduwa." "Eh ya aiki?" "Alhandulilah." "Ina Jawahir?" "Tana gida." "Ka gaishe ta." Kai ya girgiza tace "Saboda me?" "Just." Yai murmushi tace "Uhmm." "Kinyi kyau sosai." Dagowa tai tana kallon sa sai kuma ta sauke idon ta da sauri yace "Da gaske ke me kyau ce." Boye fuskarta tayi tana murmushi, ya dinga kallonta, tace "Ina aiki da Sitti fa." Yace "Ni da nazo muyi hira to." "Ka bari ko gobe ko?" "Shikenan." "Kayi hakuri please." "No problem since we will meet tommorow." Ta danyi murmushi ta mike tace "To nagode sai anjima ko?" "Ok bye." Ta mike ta fita shima ya mikewa ya kalli Abdul yace "Am going fa." "Tin yanzu?" "To ni ai ba zance nazo ba ko?" Yai murmushi yace "Uhmm haka ne sai mun hadu to." "Aha bye." Ya fita ya shiga mota ya bar gidan. A kofa ta tsaya tana jin Sitti na magana "Gaisawa ne ta dade Aliyu meyasa kake haka ne?....." Sallamar Maryam ta katsewa Sitti abinda zata ce, ta shiga ta zauna tana sauke ajiyar zuciya jin komai yazo da sauki Muhammad zai tafi Aliyu bai gansu tare ba. Sitti tace "To gata nan ta dawo, a haka za ai min hutun kuwa." Murmushi Maryam tayi kawai ta kwanta a jikin Sitti. Bayan Magrib suna dakin Najwa zaune akan sallayar da sukai sallah basu tashi ba, Aliyu kuma yana masallacin bai dawo ba, wayar Najwa ce tai kara ta dauko taga sabuwar number dauka tayi taji ance "Uhmm Please Najwa, Maryam nake so ki bawa wayar zan mata magana." "Oh Muhammad ne?" "Yeah " Ta mikawa Maryam wayar, mikewa tayi ta fita ta nufi dakin Sitti ba kowa a ciki dan haka ta zauna gefen gado ta kai wayar kunne tace "Hello." Yace "Hello ya na baro ki?" "Lafiya kai fa?" "Gani nan dai da na rufe ido sai ina ganin fuskar ki." Dan murmushi tayi yace "Oh dariya kike min?" "A'ah kana da abin dariya ne." "Uhmm ina wayar ki?" "Tana fa motar Yaya." "Dazu naga ya shigo baki amsa ba." "Eh." Kawai tace, yace "Shikenan zan kira ki anjima." "To sai anjima." Mikewa tai ta fita ta koma dakin da Najwa take wayar ta mika mata Najwa dake kwance ta mike tace "Wai ina wayar ki?" Fuska Maryam ta bata tace "Yaya ya kwace min" Najwa ta zaro ido tace "Saboda me?" "Shi ya sani amman kila dan yaga ina wa Muhammad text dazu ne." Najwa tace "Kaji Yayan nan, toh shi ina ruwansa, ai yanzu an daina takurar nan duniya ta canja ace kina level 400 kuma ya hanaki kula samari" Baki ta tabe tace "Toh ko tanadi yake?" "Tanadin me?" "Auren ki." "Shi zai min tanadin Ummi ce zatai min bashi ba." Dariya Najwa kawai tai dan taga Maryam bata gane inda ta dosa ba. "Nima fa da yai min haka amman bai tsaurin naki ba." "Uhmm shiyasani." Tinda ta shiga daki bata fito ba sai wajen karfe goma, tana fita ta tadda Sitti zata shiga daki, Sitti tace "A ba bacci kike ba daman?" "Ni ina kwance Najwa waya take." "To ni kwanciya zanyi." "Yaya fa?" "Yanzu ya tafi. "Bai baki wayar ba?" "Bai bani komai ba." Juyawa tayi ta koma daki ta canja kaya kawai ta kwanta, Najwa na waya taji alamun ana kira katse wayar tai taga Muhammad Maryam ta bawa ta dauki karamar wayar ta ta fara kiran Abdul, Falo Maryam ta koma ta kwanta, wayar ce ta kara a kunnen ta yace "Baki bacci ba?" "Eh." "Nima yanzu zan kwanta nace bari nai miki sai da safe." "Nagode." "Aha kije ki kwanta ki huta gobe zamuyi magana." "To nagode sai da safe." "Allah ya tashe mu lafiya." Waahe gari karfe biyar sai ga Aliyu tin da yazo bai da shirin tafiya Maryam na daki taki fitowa da Muhammad ya kirata akan zai zo sai hanashi tayi tace zasu fita yaso yazo ya kaisu ma amman tace masa Yaya ne zai kaisu dole ya hakura, kusan kwana uku kullum da ya tashi a aiki gidan Sitti yake zuwa bai tafiya kuma sai wajen tara ko goma dan haka sam Maryam bata hadu da Muhammad ba. Ranar Alhamis da yake ko a gida bai fiya dawowa da wuri ba dan yana bawa mutanen sa appointment wannan yasa ko a gida wani lokaci yakan kai har bayan isha'i bai dawo ba. Sanin haka da sukai waya da Muhammad yace zai zo bata hanashi ba tace sai yazo. Da yamma tana zaune a daki Najwa ta shigo tace "Gashi Muhammad ya kira" Maryam ta mike zaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace "Na karaso." Tace "Toh bari in fada ma Sitti gani nan" Daga haka ta katse ta fita falo, samye da wani oramge material mai kamar boyel wanda akai masa ado da mint colour dinkin doguwar riga ce, ta yafa mint colour mayafi tai kyau duk da batai kwalliya ba amman tai kyau sai tashin kamshin intensive oud take, ta zauna tai kasa da kai tace "Sitti Muhammad ne yazo." Sitti tace "Toh ya shigo mana, kuje can sitting room din." Ta mike ta fita sam baya compound gate ta fita ta hange shi tsaye a jikin motarsa, sanye yake wata sky blue din shadda wacce tai masa kyau sosai, sai kamshin yake kansa ya saka hula baka da bakin takalmi, yai kyau sosai, ta karasa kanta a kasa ta tsaya daga nesa dashi, Muhammad kuwa ya kasa dauke idonsa akan ta, "Yan mata." Fuska ta bata yace "To Baby." Dagowa tayi ta dan harare shi yai murmushi yace "Kinga ai naga idanun ki." Juya masa baya tai tace "Mu shiga ciki ka tsaya anan." "Menene da nan din?" "Yayi hanya." Unguwar ya kalla ba kowa a layin yace "A hakan?" Kai ta gyada tai gaba yabi bayan ta, sitting room suka shiga ya zauna akan one sitter ita kuma ta zauna akan three sitter. Dagowa tai suka hada ido wannan yasa tai saurin dauke idon ta tare da dukar da kanta tana mai cigaba da wasa da yatsun hannun ta, "Meyasa bakya son ina ganin fuskar ki?" Kai ta girgiza yace "Gashi nan bakya iya kallo na kullum kan ki a kasa, rabo na daganaga fuskar ki sosai tin farkon haduwar mu." Fuska ta rufe da hannun ta tuna ranar da rashin yadar da tayi dashi, yai murmushi yace "Eh a lokacin an zata ni mai sace mutanene ko? Sai gashi ke a ranar kikai min sata." Da sauri ta dago kamar zatai kuka ta nuna kanta tace "Ni kuma?" Kai ya gyada yace "Kwarai kuwa." "Gaskiya ba abinda na daukar maka sai dai ko kayar da abun." "Ba a ganin abun ma bare na yar." Kallon sa take da rashin gane me yake nufi ya gyada mata kai yace "Anan abun yake." Ya nuna kirjin shi tace "Me kenan?" "My heart." Da sauri ta sunkuyar da kai yai murnushi yace "Yeas you stole my heart Maryam daga ranar kika sacen zuciya ta, ban kara ganin ki ba amman kika tafi da zuciya ta sai Allah yayi zan ganki a super market da gidan mu ashe kece wacce ake yanwan bani labari ban sani ba, sai ga Abdul ya kara hadamu ashe ba a banza kika dauken zuciya ta ba Allah yayi zan ganki har na bayyana miki kila ki zama matata uwar ya'ya na." Ya fada yana lumshe ido. "Ban taba son abu kamar yadda nake son ki ba, thur ba anan nai rayuwata wajen da nai rayuwa farar fata ne, dawowata ba dadewa muka hadu, kuma Allah ya jarabce ni da sonki please Maryam kar kice min A'ah wallahi na kamu da son ki ta yadda ba zan iya rayuwa bake ba ko a yau kika ce na fito zan fito." Saukowa yai ya durkusa agaban Maryam yace "Please ki amshi soyayya ta." Dagowa tai tana kallon sa durkushe a gaban ta duk kyan sa, ajin sa amman yake zube a gaban ta yana neman soyayyar ta, kai ta dauke da sauri tace "To ka koma ka zauna." "Sai ki amshi soyayya in ba haka ba, ba zan taba tashi daga durkushen nan ba." "To naji tashi ka zauna." "Kice kin amshi soyayya ta." Shiru tayi yace "Baki amsa ba kenan." Kai ta girgiza tana rufe fuskar ta da hannu yace "Ok to kin amsa?" Kai ta gyada ya mike yace "Alhamdulillah nagodewa Allah, Allah ka mallaka min Maryam ta zama matata kuma uwar ya'yana." Ita kunya yake bata daga ganin sarkin fawa sai miya tai zagi, haka ya dinga fada mata yadda yake jin ta da karai mata bayani akan rayuwar sa har kusan magariba suna tare sai daga baya sukai sallama ta fito har bakin gate ta tsaya tana daga masa hannu ta koma cikin gida. Tana zama taji an bude gate, ta taga ta leka taga motar Aliyu ta shigo mamaki ya kamata na zuwan nashi a yanzu sai kuma ta fara tunanin Allah yasa Muhammad ya tafi basu hadu ba, tana ganin sa ya fito sanye yake da coffe wando da brown kalar riga, yai kyau dashi baki ta tabe ta saki labulen ta koma ta zauna sitti tace "Waye?" "Yaya ne." Sai kuma ta mike kan tabar falon ya shigo amman bata juyi ba ta shige daki da kallo ya bita har ta shige sannan ya karaso ya zauna suka gaisa da sitti, sitti tace "kaje kaco abinci kan magariba" "Na gaji kira Maryam ta zuba min." Kiran Maryam Sitti tayi, Maryam ta fito, Sitti tace "Kawo masa abinci nan." Ta nufi dining ta kawo masa flask din tace "Ina yini?" "Lafiya." Har ta mike yace "Zuba min mana." Ta zuba masa sannan ta mike zata bar wajen yace "Zo nan." Komawa tai ta zauna yana cin abinci yana satar kallonta ta kasan ido ita kuwa sai turo baki take, shi dariya ma taso ta bashi to ita kadai sai abu take, sai da ya gama cin ya jingina da kujera yana lumshe ido kiran sallah aka fara ya bude ido a hankali ya sauke akan fuskar Maryam, mikewa yai ya nufi kofa yace "Bari nai sallah na dawo." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/23, 14:18] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 9 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Wannan shafin naki ne, Ubee from Sona Hausa Novel group i really appreciate😍😍 Ya fita, baki ta murguda ta shige daki, alwala tayi tai sallah tana zaune akan sallaya wayar Najwa tai kara Najwa na gani ta mika mata amsa tayi ta dauka ta kai kunnen ta yace "Kinyi sallah?" "Eh." "Ina fatan kin mana addu'a." "Eh." "Me kika rokar min?" "Allah biya maka bukatun ka na alheri." Wani murmushi mai sauti yayi yace "Nagode sosai, sai anjima." "Nagode." Sukai sallama ta ajiye wayar, bayan isha'i Aliyu ya dawo yana falo suna hira da Sitti har tara, sai da ya mike zai fita yace "Ina Maryam ne?" "Tana ciki." Sitti ta fada, Najwa ce ta fito daga daki, Aliyu na ganin ta yace "Turo min Maryam." Ya juya ya fita, cikin mota ya shiga, bai jima ba ta fito sanye da hijab har kasa ta karasa tace "Gani." "Waye Muhammad?" Kai tayi kasa dashi yace "Ba magana nake miki ba?" Nan ma tayi shiru yace "Ok sai da safe." Kan tai magana tini yaja motar ta dago tana kallon sa har ya kai gate mai gadi ya bude ya fice aguje kai ta dafe tace "Wai meyasa haka ne?" Baki ta murguda tace "Kayi ka gama." Ta juya tai ciki tai kwanciyyar ta. Gaba daya Aliyu bai bar Maryam ta sake ba dan kullum yana gidan da yamma kuma bai tafiya sai dare duk yadda Muhammad ke son yazo taki ta bashi dama dan tana tsoron haduwar su da Yaa Aliyu, a daddafe da kyar ta kwana bakwai tace zata tafi Najwa taso ta kara amman taki, Aliyu ne yazo da yamma ya maida ita gida. A compound din su ta samu Haidar na buga ball yana hango ta ya karaso a guje yace "I miss you Adda." Ta daga sa tana fadin "I miss you too." Ta sumbaci kumatun sa tana fadin "Ya makaranta?" "Alhmadulillah." Ta shafa sumar kansa tace "Masha Allah." Ya rumgume ta. Duk abinda suke Aliyu na tsaye yana kallon su sai murmushi yake mikewa tai ta dauke shi tana fadin "Ummi fa?" "Tana kitchen." Dire shi tayi tace "Bari naje naji dumin ta." Tayi ciki tana fadin "Ummi na kina ina na dawo." Ummi dake kitchen na aiki ta leko tace "Ah Daughter u re welcome." Maryam ta karasa ta rumgume ta tana fadin "I miss you." "Miss u more yasu Sitti?" Ta fada tana shafa bayan ta. Aliyu ne ya shigo Haidar a hannun sa sukai daki. Maryam ta shiga tace "Me kike?" "Girki." "Yau zanci girkin Ummi." "Sai kace wacce ta shekara." "Wallahi ni ji nake kamar na shekara." Tai murnushi tace "Yasu Inna da Mami." "Suna lafiya kullum Inna sai ta tambaye ki?" "Ayyah bari naje na gaishe ta." Ta juya ta shiga dakin Inna, tana bandaki dan haka ta dawo falo wayar Inna ta gani ta dauka ta fara rubuta number Muhammad kira ta tafi bai jima ba ya dauka tai sallama yace "Kece?" Kai ta gyada yace "Ina wayar ki?" "Ban ganta ba." "Ah haba ko dai kin yar?" "Kila since bata motar Yaya." "To wannan wayar wace?" "Ta Inna ce." "Bari na kira kar mu cinye mata kudi." Ya katse sai ga kiran sa dauka tayi yace "Kin dawo gida ne?" Kai ta gyada kamar yana ganin ta yace "Yasu Ummi da Haidar?" "Suna lafiya." "Yau kin baro Sitti da kewa kamar yadda kika barni ko?" "A'ah." "Hmmm shikenan yanzu ya labari?" "Yana wajen ka." "Nawa akan ki ne kawai." Tai murmushi yace "Please ki barni nazo mu gaisa." "To zan fada maka lokacin da zaka zo." "Nagode to sai anjima." "Eh." Ta kashe wayar Inna ta fito tace "Ke kuma dawa kike magana?" Waya nai da wayar ki." "Oh yaushe kika dawo?" "Yanzu." Ta sauka kasa ta ce "Ina yini?" "Lafiya lou yasu Hadizan?" "Suna lafiya." "Madallah ai bakya nan gidan shiru ba dadi." Maryam tai murmushi tace "Ina Yaa Farouk shi ko?" "Yanzu zaki gansa shi ke dauken kewarki. Ali kuwa safiya safiya nake ganin sa. Motsi suka jiyo Inna tace " kila gashi nan ma." Aliyu ne yai sallama Inna ta amsa tana fadin "Yau kai ne a sashe na?" "Kaji Inna sai kace bana shigowa." "Ka jima rabon ka dani." "To yau gashi na shigo ko korata zakiyi." "A'ah ya aikin?" Zama yai yace "Alhamdulillah." Sallamar Farouk suka jiyo ya shigo tin da yaga Maryam yake binta da kallo ta hade rai tace "Ni ba ruwa na dakai." "Haba kanwata afuwan." "Uhmm." Zama yai yace "To ba ina ta kira wayar a kashe ba, da farko ta shiga daga baya kuma a kashe, ina wayar ta shiga?" Hannu ta daga alamar itama bata sani ba. Farouk yace "Kamar yaya?" Ta saci kallon Aliyu shima ita yake kalla ta kasan ido tace "May be na yar ban sani ba." "Ayyah Allah mai da alheri wannan watan akwai siya waya kenan." Murmushi kawai tayi tace "Ya aikin to?" "Alhamdulillah yasu Sitti?" "Tana gaishe ku dukka." "Madallah." Mikewa Maryan tayi tace "Bari naje na gaishe da Mami." Farouk yace "Nima zanje sashen bari mu tafi tare" Ta kalli Inna tace "Inna sai anjima" Sannan suka fita, suna zuwa kowa yai bangaren wanda zai je. Da daren ranar fitar Maryam kenan nan daga dakin Inna. Ba kowa a dakin daga Inna sai Aliyu, wayar Inna dake gefe ce ta hau kara ta janyo tana fadin "To waye haka cikin daren nan?" Daukar wayar tayi ta danna inda ake picking ta kai kunne hade da sallama tace "Waye?" Muhammad jin murya Inna yace "Ina yini Inna?" Tace "Lafiya waye?" Yace "Muhammad ne Maryam nake nema." "Oh Maryam ai yanzun nan ta bar sashen nan sai dai ko ka kira wayar ta, au ashe fa tace an dauke to amman tinda ga Ali bari na basa sai ya kai mata zata kira in an kai mata kaji." "To Inna nagode sai da safe." Ta dago tana fadin "Dan Allah Ali maza mikawa Maryam wayar nan, kaga kiran ta ake." Amsa yai ya mike ya fita, number yasa a blacklist sannan ya shige dakin sa bai jima ba ya fito falo ya zauna anan dining space yana aiki. Can wajen goma yaji ana saukowa daga bene yana dagowa yaga Maryam ce sanye da kayan bacci sai hijab karami a jikin ta da yake garin da sanyi doguwar riga ce mai kauri sai dan hijab din. Tana ganin sa ta dauke kai ta shige kitchen mikewa yai yabi bayan ta ta dauko fresh yoo ta fito ta kusan cin karo dashi da sauri ta koma ciki ya biyo ta, taja baya ya dinga binta har sai da taje da jikin cabinet sannan ta rasa inda zata, tsayawa yai a gaban ta kamshin turaren sa ya cika har wani ido take lumshewa, a hankalu ta dago ta kalle sa take da mamaki zai magana kawai ya juya ya fice hannu ta daura akan kirjin ta tana sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Shi Yayan nan." Kujera ta sama ta zauna anan ta shanye fresh yoo din sai da ta gama sannan ta mike ta leko a hankali ba kowa a falon da sauri ta fito tayi sama ta shiga dakin ta ta kwanta. ** Washe gari da rana wayar Ummi ce kare a kunnen ta suna waya da Muhammad sai da suka gama Ummi tace "Da wa kike waya Daughter?" "Abokin ya Abdul ne" Ummi tace "Wane Abdul?" Kai tayi kasa dashi tace " Saurayin Najwa." "Me ya hada ki da abokin Abdul, a ina kika san sa?" Tace "Ummi a gidan Sitti." "Soyayya kuke?" Kai ta girgiza Ummi tai murmushi tace "A dai kiyaye." Ta mike ta haye sama jingina da kujera tayi ta lumshe idon ta ita ba zatace ga abinda take ji game da Muhammad ba amman dai tasan yana burge ta gashi dan gayu ga tsafta ga sanyin hali ga iya kwalliyya da kula. ido ta bude sai ta kara lumshe idon ta wani abu taji tana son tunowa amman kuma ta kasa takurawa kan ta da tayi da son tuno abin ya haifar mata da ciwon kai dole ta hakura da tunanin ta kunna TV ko ta dauke mata kewa amman ina sam babu abinda hakan yayi sai ji tayi wani abu ya tokare mata a kirjin ta, gaba daya ta kasa jin ya daukar mata zamewa kawai tai ta kwanta ba tare da tasan tunanin me take da abinda yake damun ta takamaimai. Har washe gari da ciwon kan ta tashi daga ka kalle ta zakaga alamun bata jin dadi ko tana cikin damuwa, da yamma tana kwance a falo, tai shiru kawai taji wayar Ummi na kara dan yawanci yanzu tana wajen ta, hannu tasa ta janyo, number Muhammad ce ta dauka bayan sun gaisa yace "Ina kofar gidan ku." Ido ta zaro tace "Gidan mu kuma?" Yace "Yes ko na tafi?" "A'ah bari na fadawa Ummi, ta mike ta nufi dakin Ummi ta jima tsaye a bakin kofar ta kasa shiga saboda batasan me zata ce mata ba, tuna yana waje yana jiran ta yasa ta runtsa ido tai sallama a dakin, Ummi ta amsa Maryam ta shiga ta zauna a kasa, Ummi ta kalle ta tace "Lafiya?" Kanta tai kasa dashi tace "Ummi Muhammad ne wai yazo yana kofar gida." Kallon ta Ummi ta tsaya yi can tace "To kije kada ki dade kinsan Yayan ki yana hanya yanzu." "To Ummi." Ta mike ta fita, Hijab ta saka ta fita a gidan a hankali take tafiya har ta isa gate, Yana ganinta ya bude motar ya fito ya rumgume hannayensa yana kallonta daga glass din idonsa, sanye yake da Dark Ash kalar wanda da bakar riga kayan sun masa kyau sai tashin kamshin turarren sa mai dadi yake, ta sunkuyar da kai har ta isa kusa da motar, cikin sanyayyan murya tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau dear, ya gida?" Tace "Alhmdllh" Ido ya zuba mata yana murmushi can ya kira sunan ta da wata irin murya "Maryam." Dagowa tai, murmushi ya sakar mata yace "Me yake damun ki?" Girgiza masa kai tayi. Yace "Amman yanayin ki ya nuna bakya jin dadi." Murmushi tayi tace "A'a lafiya ta lau" yace "To ina Haidar?" "Yana school bai dawo ba." "Ummi fa?" "Tana lafiya." Kai ya gyada, dagowar da zatai ta hango motar Aliyu na karasowa wani abu taji ya tsarga mata tai sauri ta dauke kai, tanaji ya karaso aka bude masa gate ya shiga, duk sai ta duburburce gane haka Mauhammad yace "To ni dai na ganki naji dadi kewar kice tai min yawa wajen kwana nawa banganki ba shine nace yau ko dame sai nazo daga wajen aiki na sauka anan." "Ayyah sannu." "Yauwah wani satin zaku koma makaranta ko?" Kai ta gyada yace "To Allah kaimu yaushe zaki zo gidan namu?" Ido ta zaro tana girgiza kai yace "Saboda zamu cinye ki ko? Yadda Jawahir ta damu dake ke baki damu da ita ba da tana garin nan akai hutu da tini tazo yafi a kirga gobe ko jibi zasu dawo please ki daure kizo ki mata sannu da zuwa." Murmushi kawai tayi yace "Oh dan ina gidan?" "A'ah nifa bana fita wancan ma da kyar aka barni na fita." "Shikenan." Zagayawa yai ya bude front seat ya dauko wata leda ya zagayo yace "Ga wannan ba yawa." Dagowa tai tana kallon sa, kai ta hau girgizawa tare da fadin "Aah nagode" yace "Karba please" tace "Aa Ummina zata min fada" Shiru yayi yana kallonta, ta girgiza kai tace "Dan Allah kayi hakuri." Yayi murmushi yace "Na yi." Tai kasa da kai yace "Zan wuce since na ga kyakyawar fuskar ki ki gaishe da Ummi." "Zataji nagode." Ya zayaga ya shiga mota ita kuma ta shiga gida. Tana shiga taga Aliyu ya hau mota zai fita da sauri ta shige ciki. Muhammad kuwa daga nan gidan Sitti yaje lokacin Abdul na gidan falo kai tsaye yaje yai knocking Sitti ta bada izinin shiga ya shiga da sallama tana ganin sa ta saki fara'a tace "Ah Muhammadu ne?" Ya zauna akan carpet yace "Nine Sitti." Tace "A'ah ka zauna akan kujera." "Nan ma ya isa Sitti." Ta mike ta kawo masa ruwa da lemo ta ajiye yace "Ina yini?" "Lafiya lou ya gida ya aiki?" "Alhamdulillah." "Masha Allah." Yai kasa da kai yace "Daman Wayar Maryam ce ta 'bata so shine nace bari na kawo mata wannan." "Ah haba Muhammad har da dawainiyya." "Sitti ba komai ai Maryam kanwata ce." "To angode Allah ya saka da alheri." "Amin. Ni zan tafi." "To baka sha ko ruwa ba ai." Ya dauki ruwan yace "Nagode sai ajima." "To ka gaida gidan." "Zasuji." Ya fita ya shiga mota ya fita, motar sa na fita a gidan ta Aliyu na karasowa ya shiga yai parking ya shiga falon Sitti da sallama, ansawa tayi yana shiga ya zauna a akan kujera tare da lumshe idon sa. Sitti tace "Lafiya?" Kai ya girgiza mata kawai. Sitti tace "Aliyu ya kamata kasan abun yi fa." Yana jin ta yai mata shiru tace "Zama haka ba zai yiyu ba ka samu kai aure ka zauna da iyalin ka." Kai Sitti yazo da damuwa tana son ta dada masa wata, mikewa yai yana fadin "Daga aiki daman nake za tafi." "Oh dan na maka maganar aure ko?" "Ba haka bane." Ya nufi kofa tace "To zo na baka sako." Ya juyo ta mika masa ledar da Muhammad ya ajiye tace "Ka kaiwa Maryam, waya ce Muhammad ya kawo mata saboda tata ta 'bata" Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa ya fice kawai. Sitti tace "Zama ka dawo ne." Ya shiga ya tada motar ya bar gidan. Yana zuwa ya wuce dakin sa wanka yai yai shirin masallaci sannan ya tafi sallah. Bayan isha'i yana zaune a daki ya aika haidar ya kira masa Maryam, gaban ta na faduwa ta karaso dakin, daga yanayin fuskar sa tagane ransa a bace yake, kai ta sunkuya tace "Gani Yaya." "Ai na ganki." Ya mike ya shiga daki bai jima ba ya dawo ya zauna yace "Waye kika fita wajensa dazu?" K'in cewa komai tayi ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba?" Still ta'ki cewa komai zuciyar ta sosai bugawa take, motsowa yai yace "Ke kurma ce?" Ganin zai mike yasa tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi? nace" cikin rawar jiki ta girgiza kai (to fa yau taurin kai ya motsa Maryam) Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo zuciyarsa na tafarfasa, so yake ya samu nutsuwar abinda yake ji amman ina, da kyar da ambaton Allah ya fara jin nutsuwa na zuwar masa yace "Toh daga yau Maryam, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan kinji na fada miki." Kuka ne ya kwace mata, ta kifa kai tana yi ya buga mata wata tsawa yace "Rufen baki dukan ki nayi?" Shesheka ta fara yace "Kuma shine kika roke shi waya ko? Kina son abu ni ba zaki tambaya ai miki ba na amshi wayar ki ba zakizo ki ban hakuri kiji dalili ba ke kinfi karfi ko?" "Ni ba roka nayi ba kuma ai ban amsa ba." "Baki amsa ba ai ya kaiwa Sitti tinda ita ta daure miki gindin kula samari to kinji abinda na fada miki wallahi na kara ganin ki da wani saurayi sai na lahira ya fiki jin dadi." Wayar ta ya cilla mata yace "Waccan din ba zan bayar ba tinda har ita Sittin ta amsa maimakon taki amsa to ba zan bayar ba tashi ki bani waje." Ya fada da sauri ta mike ta bar wayar ta a wajen yace "Bazaki zo ki dauka ba." Ta juyo ta dauka ta fice a guje, dafe kan sa yayi tare da sakin tsaki ya mike ya shige daki ya fada saman gado ji yake kansa na sara masa. Tana shiga daki ta fada saman gado tana kuka mai taba zuciya daman ga abinda yake damun ta gashi yazo ya dada saka mata damuwa wai tayi roko ita a rayuwar ta bata san wata roko ba ko tana son abu kan ta tambaya tana dadewa gwara ta hakura da ta roka amman wai tai roko ta jima tana kuka wanda daga baya ta rasa kukan me take dan sai gashi ya kara saka mata ciwon kai har da zazzabi, haka ta dinga juye juye da haka bacci ya dauke ta. Washe gari da kyar tai sallar asuba, da safe kuwa Ummi ta shigo ta ganta a wani mayuwacin hali da sauri ta sauka ta kira Aliyu da ya fita, a sashen Inna ta samo shi yazo Ummi ta kama Maryam ta saka ta a baya suka tafi asibiti, suna zuwa ya hau bata taimakon gaggawa sannan ya saka mata ruwa anan office din sa, tin safe take bacci sai wajen daya saura ta farka, Aliyu ya kira wata nurse ta taimaka ta kaita bayi tai alawa akan sallaya tai sallah tana dafe da kai tana idarwa ta kwanta a wajen. Karasowa yai ya zauna a gaban ta ya fara auna jini ta dagowa yai da sauri yace "Tunanin me kike?" Kai ta girgiza yace "Ba yanzu ba." "Babu." Ta fada da kyar, yace "Jini ki ya hau why? Fada min me yake damun ki?" Hawaye ne ya hau zubo mata Aliyu yace "Ni bance ki min kuka ba damuwar ki nake tanbayar ki?" "Babu." "To saboda me jini ki zai hau haka." "Ciwo ne kawai." Ta fada tana saka kanta a tsakanin cinyoyin ta kofa akai knocking ya bada izinin shiga abinci aka kawo masa ya amsa ya mika mata yace "Kici zaki sha magani da allura." Ya bude ya bata, a hankali ta fara ci cokali biyar tayi ace "Na koshi." Ya girgiza kai yace "No me kika ci kara kadan" Ta kara ci, yace kara mana. A haka ta danci da yawa sannan yace "Magani." Kamar zatai kuka tace "Wallahi amai zanyi." "To jeki kwanta." Ta mike ta hau gado ya fara hada allura tana cikin bacci sai jin shiga allura tayi a bayan ta kuka ta saki tana yarfa hannu ya mulmula mata yana fadin "Sannu yi hakuri." Ya koma ya zauna Ummi ce ta kira tace "Aliyu jikin ne har yanzu?" "A'ah bacci take yanzu taci abinci ta kwanta." "To ya jikin?" "Da sauki." "Allah kara sauki." "Amin." Sai bayan la'asar suka koma gida ba zazzabin sai ciwon kai Ummi ta kaita sama ta samar mata ruwa tai wanka sannan ta bata magani tasha da kyar ta koma ta kwanta. Wayar ta ta janyo ta kunna tana kunnawa kiran Jawahir na shigowa ta kai kunnen ta hade da sallama Jawahir tace "Subhanallah lafiya?" "Uhmm kun dawo lafiya?" "Me yake damun ki kinji muryar ki kuwa?" "Ciwon kai ne fa." "Sannu bari yanzu zan zo." Ta kashe wayar. Bacci ne ya dauke Maryam bata tashi ba sai kusan magariba Jawahir ta gani zaune kusa da ita ta mike tace "Yaushe kika zo?" "Tin dazu ya jikin?" "Da sauki." "Sannu." Ta fada tana kama hannun ta dayan hannun ta daura akan ta tace "Sannu me kike so?" Kai ta girgiza Jawahir ta dinga mata sannu, haka suka zauna a dakin har wajen tara da kyar Jawahir ta iya tafiya. Tana kwance aka bude dakin bata juyo ba ya shigo ya tsaya akan ta yace "Ya kan?" "Da sauki." "Allah kara sauki." Washe gari da ta kara shan allurai da magunguna sai ta dan samu ta wartsake tana kwance a d'aki wayar ta ta hau kara tana dubawa taga Muhammad ta dauka yace "Ashe baki da lafiya." Kwanciyya ta gyara, tacw "Eh." Yace "Yanzu zan zo me zan kawo miki?" "A'ah kai zaman ka." "Ba zan iya ba Maryam." Shiru tayi yace "Me kije so?" "Ba komai nagode." "To sai nazo." Har bacci ya dauke ta sai ga kiran Muhammad sanar mata yayi yana waje tace "Toh ka shigo" Muhammad ya d'an buda ido yace "Ni fa Ina jin kunyar Ammi" Murmushi tayi tace "Kai da kazo dubiya zan aiko a shigo da kai." Ta kashe wayar Ummi ta shigo ta fada mata mai aiki ta aika ta shigo dashi, sanna Maryam ta sauko ta dawo falo sanye da hijabi har kasa, tana zama taji sallamar a bakin kofa, ta kalli kofar ta amsa sallaman sa, ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi ya zauna saman kujera ya ajiye ledan hannunsa a kasa yana kallonta yace "Sannu Maryam, ya jikin?" 'Dan murmushi tayi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, me yake damun ki ne?" "Ciwon kai ne." "Sannu kina samu kina hutawa kinji?" Kai ta gyada masa, mikewa yayi ta kalle shi tace "Har me?" "Tafiya." "Ba zaka zauna ba daga zuwa." "In ta nine na kwana anan Baby, amman kuma naji na kasa sakewa ina son na zauna kuma ina son na tafi." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/28, 16:29] Maryam S Indabawa🥰:  💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 10 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dis page is ur Jameela from Matar Haidar fans group, thank you so much. Fuska ta bata ya sauko ya zauna a gaban ta akan carpet yace "No Baby kar kiyi fushi zan shiga damuwa in kina so na zauna zan zauna shkenan." Kai ta girgiza yace "To menene?" Kafada ta make yai murmushi yace "Rigima ko Baby, kar ki damu ina son shagwaba, in kina son abu a waje na da kin mun yar shagwaba zan miki ko menene sai dai in ban dashi i love you Baby." Fuska ta rufe tana murmushi yace "Yes i really do love u kefa?" Kai kawai ta gyada yai murmushi yace "Ke kam kin cika cikakkiyar bafulatana kina da kunya da yawa, any way zan iya tafiya?" Kai ta gyada yace "To ki gaida min da Ummi and please kina shan magani da hutawa, kiji?" Murmushi tayi ya mike itama ta mike suka fita daga dakin, ya kalle ta yace "Ki koma ciki." "Bari dai na karasa dakai waje, kafata duk tai tsami." Ya kalle ta yace "Ai da kinyi magana na matsa miki kafaffun." Ido ta zaro tana girgiza kai yace "Ko Jawahir zan aiko tai miki?" "A'ah nagode." A bakin kofa ta tsaya shima ya juyo yana kallon ta, tace "Naji dadi sosai da ziyara nagode." "Kar ki damu ai hakki nane." Tai murnushi yace "Ki koma kije ki huta Allah kara sauki." "Amin nagode." Yace "Ki koma mana." Tace "Kai dai kaje." Juyawa yai ya nufi motar sa, sai da ya isa jikin motar sannan ya juyo kai ta langwabe ya daga mata hannu yana mata bye bye, ta sakar masa murmushi dai dai danno kan motar Aliyu, dauke kai tayi da sauri, ta maida kallon ta kan Muhammad da ya kafeta da manyan idanuwansa, murya can kasa yace "I love you." Fuska ta rufe da hannu, dawowa yai wajen ta yace "I have always loved you from day 1, ranar da na fara ganin kin nan, ranar dai da ba a yadda dani ba," kasa kallonsa tayi dan in ta tuna itama abun kunya yake bata ga gaban ta dake faduwa ganin Aliyu ya karaso gate, ganin hankalin ta baya wajen yasa yace "Bari naje sai munyi waya." "To nagode." Ta fada tana juyawa dan shiga gate amman yadda gabanta ke faduwa yasa har jikinta ya fara rawa, a parking space ta hange sa kai ta dauke tana satan kallon sa ta gefen ido, shima ita ya bi ta da ido fuskarsa dauke da wani yanayi da ta kasa fahimta, ganin ya baro wajen da yake yasa ta fara sauri tana waiwaye bata ankara ba tai tuntube ta fadi, kafar ta rike tana yarfe hannu dan akan gwiwar ta, ta dira da sauri ya karaso yana fadin "Kina tafiya kin wai waye ba dole ki fadi ba." Hawaye ne ya hau zubo mata, ta fara yarfa hannu tana fadin "Wayoo kafata." "Sannu me take miki?" Ya kalli gwiwar ta da ta gurje ya janye hannun ta, jini ya gani a jikin siket din, cikin tashin hankali yace "Subhanallah sannu tashi mu karasa ciki sai nai miki dressing." Mikewa ta fara kokarin yi ya taimaka mata, tana taka kafar ta durkushe tana hawaye ya dago ta yace "Sannu taka a hankali." Tana kara takawa ta saki kara, ya kalle ta yace "Ba zaki iya tafiya ba?" Hannu ta hau yarfewa hawaye na zubo mata tace "Yaya zafi wayoo kafata......" Bata rufe baki ba sai ji tayi ya dauke ta gaba daya da sauri ta kamkame sa dan ji tayi kamar zata fadi a haka ya fara tafiya da ita, a falo suka samu Ummi tana ganin su ta mike tana fadin "Subhanallah me kuma ya faru?" "Faduwa tayi." Ya fada yana ajiye ta akan kujera, Ummi tace "Faduwa kuma a garin yaya?" "Rashin kallon gaba sai kace yarinya." Ya mike ya shiga daki, Ummi ta kalle ta tace "Garin Yaya?" "Ban lura ba nai tuntube shine na fadi." "To sannu." Aliyu ne ya fito daga dakin sa rike da first aid box Maryam na gani ta tsorata tini idon ta ya fara kaduwa, ya ajiye ya dage siket din farar kafar ta ta bayyana, ido ya runtse da sauri yana kau da kai, ya bude ya dauko spirit da cotton wool, ya bude ya dangwala ya goge wajen cikin sauri yai mata dressing din ya mike yana fadin "Kila bugewa ki kai. Ungo wannan ki shafa zata sake." Ya mika mata wani kwalba, yana bata ya bar wajen, da kallo suka bisa, sai kuma ta dauki kwalbar ta bude ta lakuta ta shafa a kafar, tana gamawa ta mike tana dingishi, Ummi tace "Zaki iya?" Kai ta gyada mata tayi sama, tana shiga ta fada saman gado ta kwanta tana murmushi, juyi tayi tace "Nima na iya wayyo ai." * Saukowa take daga bene tana danna waya, dagowar da zatai taga Aliyu na kallon ta, kai ta dauke ta cigaba da saukowa tana yamutsa fuska tana gama sauka ta fara dingisa kafa, da kallo ya dinga bin ta har ta karaso yace "Har yanzu kafar bai saki ba?" Kai ta gyada yace "Ko targade kikayi ne?" Kai ta girgiza tace "A'ah." Kallon ta yayi tai saurin yin kasa da ido yace "Tayaya kika san ba targade bane." "Ai naji ya rage zafin ba kamar dazu ba." "Ok ki cigaba da tafiya bakya kallon gabanki, gobe daga benen ma zaki fado." Yana fada ya fice ta murguda baki tace "In kai zaka turo ni ba." Ta cigaba da tafiyar ta normal ba dingishin. Monday suka koma makaranta amman bataje ba, saboda bata gama warwarewa ba har lokacin ba karfi a jikin ta sosai gashi bata samun bacci sosai da dare sai da safe ta fiya yi shima in Aliyu ya takura mata tasha magani sannan ne take yi. Jawahir duk ta damu bama da take zuwa makaranta ba kawar tata. Maryam tana kwace a falo kan three sitter, kallo take taji ana knocking mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, Jawahir ta gani tsaye bakin kofar ta saki murmushi tace "Sister." "Na'am jiki yai sauki kenan?" Kai ta gyada tana fadin "Bismillah." Suka shiga Maryam ta karasa firij ta dauko mata lemo da ruwa ta ajiye tace "Bari na zubo miki abinci nasan daga school kike..." "A'ah kinsan naci wani abu a school." "Wannan ba abinci bane." Ta shige kitchen ta fito ta ajiye mata abincin tace "Sauko kici." "Ni na zama acici daga zuwa sai ci ko dubaki ban ba." "Ni ba bakuwa bace, dan Allah sauko kici." "To ya jikin?" "Naji sauki fa. Yaya ne ma ya hanani zuwa wai sai na kara warwarewa." Tai murmushi tace "Yaya dai Yaya kullum Yaya ko dai." Duka ta kai mata tace "Bana so." "To sorry naga jiki yai kyau sai dai kin kara ramewa daman ke aba gaki ga kamar ki." Hararar ta Maryam tayi tace "Dame kwado yafi gaya?" "Da mai da yaji da magi kinga kuwa ai yafi sa." "Ni dai kici abinci." "Zanci ai ina Ummi?" "Ta tafi aiki bata dawo ba." "Ayyah yau sai ke kadai kenan." "Uhmm ai gobe ko ya hanani da ya fita zan taho." "A'ah ki zauna sai monday kawai kan nan kin kara murmurewa ba wani abu ake ba yanzu kinsan farkon komawa duk course outline suke bayarwa kuma baki da matsala." "Ah haba ai shikenan." Ta fara cin abincin suna hira har ta gama, tace "Alhamdulillah." "Ke da driver ne a kai masa ruwa ko?" "A'ah Yaa Muhammad ne ya kawo ni." Ido Maryam ta zaro tace "Kuma kika barshi a waje." "Tab Yaa Khalifa ai da tini ya tafi yaje bayan layin ku yace in ya gama zai kirani." "Ok yasu Momy?" "Momy bata dawo ba ni kadai na dawo saboda school nima da bari nai sai weekend din muka dawo tare kawai." "Gaskiya since ba wani abu ake ba." "Wallahi." Wayar Jawahir ce tai kara tana dubawa tace "Yaa Khalifa ya dawo kenan." Ta dauka ta kai kunnen ta tace "Gani nan." Maryam tace "Oh sai tafiya kenan." "Uhmm ai in na kara minti daya zai iya tafiya ya barni." Ta mike Maryam ma ta mike tana fadin "Nagode sosai da ziyara." "Kar ki damu mun zama daya." Suka fita tare, wata mota ce mai kyau da tsada ta gani bata zata shine a ciki ba sai da taga ya sauke glass din, yana kallon ta kamar zai hadiye ta, kai ta dauke suka karasa still kallon ta yake babu ko kiftawa babu, har suka iso sannan ya dauke idon sa, Maryam ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini?" Cikin cool voice dinsa yace "Lafiya lau" Ta kalli Maryam tace "Da kyar ya gane gidan fa ni kuma nace ba zan nuna masa ba tunda ya taba kawo ki, before cewa ma fa yayi ya manta ki, sai da nai masa kwatance." "Jawahir talkative wa ya tambaye ki to?" Ta bude ta shiga, tace "Yaya bakai mata ya jikin ba?" "Ohk." Ya fada yana kallon Maryam da tai kasa da kai yace "Ya jikin?" "Alhamdulillah." "Allah kara sauki, bansan nan zata kawo ni ba da na kawo miki kayan dubiya." Murmushi Maryam tayi tace "Nagode." Jawahir tace "Sis sai munyi waya ki gaida Ummi in ta dawo da Haidar." "Zasuji nagode." Ta dago ta saci kallon Muhammad tace "Ku gaida gida." Kai ya gyada mata yana kashe mata ido daya, da sauri ta juya, ya bi ta da kallo yana murmushi, Jawahir ta dan kalle shi taga Maryam yake kalla, tai murmushi tace "Yaya wannan kallon fa?" Kai ya dauke yana murnushi kawai, tace "Ko dai ko dai?" Hararar ta yayi yace "Bana son surutu." "To an ba da ita dai." "What?" Ya tambaya da sauri ta kyalkyake da dariya tana fadin "Na kama ka." "Da akai me? Ina nufin me ruwa da kike ce an bada ita." Dariya tayi tace "Ah ah fa." Kai ya dauke ya fara driving din sa bai kuma kula ta, ita kuwa sai dariya take kasa kasa. Bayan ta koma mamaki Maryam ta dinga yi meyasa Muhammad ke boye ma Jawahir bai san ta ba da yana son ta, tabe baki tayi ta cire hijab kwanta akan kujera tana lumshe idon ta da sauri ta bude ido tana duba agogo shida saura Yaa Aliyu bai dawo ba bayan yau laraba biyar ma wani lokacin yana gida, to ko wani aikin ya tsayar dashi, Haidar fa? Ko da yake tasan dole yana wajen sa tinda tare suke dawowa in yana da wani abu ma zai sa drivern sa ya kawo shi gida. Tsakanin Maryam da Muhammad kuwa soyayya suke duk da Maryam bata fiya sakewa ba, in tana wani abu sai taji ta incomplete ko ta kasa masa wani abun shi kuwa bai jin komai kulawa yake bata duk da tana hana shi zuwa amman shi a takure yake da gayya yake kai Jawahir makaranta dan su hadu, akwai lokacin da yace saboda me take kin barin shi yazo sai tace "Yaya ne baya so." Yace "Yaya baya so?" "Uhmm." "Jika ki zai ya shanye?" "Uhmm...." "Shikenan!" Kawai yace abin na basa mamaki ya rasa wa zai tambaya shin Yayan nan Yayan gaske ne ko kuwa a yadda take cewa Yaya shi ya dauka uwar su daya uban su daya amman ya fara tunanin wani abu in har haka ne da matsin bai kai haka ba, shi na miji ne dan haka yana gamin anya Yayan nan ba son ta yake ba. Zama yai yayi tunani ya samarwa kan sa mafita. Muhammad ya nunawa Maryam yana son ya aiko gida sai ta nuna tsoro take ji, cikin muryar sa mai sanyi yace "Maryam bakya so nane?" Kai ta girgiza yace "Maryam ni mutum ne wanda in ina son abu da zuciya daya nake son sa, ba zan iya cigaba da rayuwa a haka ba ina son nima na samu na yi aure bakiga Najwa ba sauran wata hudu auren su, so nake da an gama nasu a hau shirye shiryen namu ni da zaki yadda ma da an hada kawai." Murmushi tay tace "Kai a'ah karatun nawa fa?" Murmushi shima yayi yace "Wani lokacin in kikai abu kamar bakya so na." "Kada kace haka dan Allah." "To gashi nan." "Ni ba haka bane kasan irin karatun mu bama yanzu da zamu shiga asibiti in da aure abun zai min wahala." "To shikenan naji amman ni dai zan nemi su Abba su san dani please ki yadda." "Shikenan." "Kin yadda?" Tace "Eh." "Nagode my wife." "Tin yanzu?" "To kwana nawa ne?" Murmushi kawai tayi. Har ta manta da abin ma bayan kwana biyu Abba ya aika aka kira ta, ta same shi a dakin sa. Abba yace "Maryam kinsan wani Muhammad?" Dagowa tai da sauri ya sakar mata murmushi yace "Kinsan shi kenan?" Kasa tayi da kanta, yace "To je ki." Ta mike ta fita da sauri, Ummi ta shigo tace "Gani." Yace "Zauna mana." Zama tayi yace "Wani yaro Muhammad dan gidan Minister of petrol ne yazo waje na yanzu." "To Allah yasa lafiya." "Lafiya lou, Maryam ya gani yakeso yace yana son a bashi dama su dai dai ta kansu in hakan yayi sai a sanya rana da harkar bikin su." "Masha Allah amman Alhaji kan a basa dama a fara bincikar halin sa, kan su hadu dan kar muje kuma yana da wani halin a bar yarinya ta fara soyayya da shi kuma a zo daga baya agane hali." "Nima nai tunanin zanje muyi magana da Yaya zan saka Aliyu da Farouk su bincika mana." "Yauwah Allah yasa albarka." "Amin." Ya mike yace "Bari naje wajen Yaya dan naga motar sa kafin ya fita." Yaje ya samu Abbi, Abbi yai na'am suna zaune a falon ma ya kira Aliyu da Farouk da yake weekend ne duk suna gida, zama sukai Abba yai musu bayanin komai, Farouk ji yai zuciyar sa kamar ta fito Aliyu kuwa ba zaka gane a halin da yake ciki ba sam bayan Abba ya gama bayani yace "Muna so ku bincika mana ya yaron yake." "Insha Allahu Abba." Aliyu ya fada, Farouk ma yace "Allah bamun iko." "Amin." Suka tafi, duk sunje sunyi bincike Muhammad bai da wani mummunan hali ko kadan yaro ne mai tarbiyya da hankali, kuma ba wanda ya boyewa Abba dan shima Abba ya bawa wasu da yawa dan haka Abba ya kira shi ya ya bashi damar zuwa zance, murna wajen Muhammad kamar me? Aliyu na ta shirin tafiyar sa wanda ya rage kwanaki a cikin lokacin duk ya burkice Ummi ta rasa gane kansa, in tai magana sai yace yana kewar tane. Ranar da Muhammad yace zai zo da kyar ta sanarwa Ummi, Ummi na kasa a zaune ta sauko ta zauna a kusa da ita, Ummi ta kalle ta tace "Lafiya Daughter?" Kasa tayi da kai ta kasa magana, Ummi tace "Fada min mana me kike so?" "Ummi daman wannan ne yai min waya wai zai zo yau." Tana fada tai kasa da kai, Ummi ta kalle ta tana susunne kai tai murmushi tace "Ni kuma ake jin kunya Daughter?" Jikin Ummi ta shige tace "To Allah ya kawo shi." Da gudu Maryam tai sama, taso tai kwalliya amman ganin kada Ummi tace dan zai zo zata shiyasa ta hakura kawai, wata orange kalar doguwar riga ta saka wacce duk jikin ta stone ne ta mata kyau ta shafa turare tana gaban mudubi ya kira wayar ta, dauka tayi yace "Na karaso." "To ka shigo." "Ok." Ta mike ta fita falo, dakin Ummi ta shiga ta tsaya a bakin kofa Ummi tace "Ni dai na zama sirikar ki ko?" Kai ta girgiza tana rufe fuskar ta da hannayen ta, Ummi tace "Ya karaso kenan?" Kai ta gyada, Murmushi Ummi tayi tace "To jeki ku zauna a barrander ko?" "To Ummi." Ta fada tana juyawa, a babban compound ta same shi jikin motar sa, tinda ta fito ya zuba mata ido har ta karaso, tace "Sannu da zuwa." "My wife." Ta danyi murmushi, tace "Muje to." "Ok." Tai gaba yabi bayan ta, a barander suka zauna inda wajen yake da table da kujeru guda hudu ya zauna ta zauna a can gefe tace "Ina yini?" Kallon ta yake yace "Wannan kunyar fa haka Maryam?" Kai ta girgiza yace "To ki dago yau magana zamuyi dan mun fara kokarin sai ta rayuwar mu kinji." Kai ta gyada, mai aikin su ce tazo ta kawo masa lemo da ruwa yai godiya ta koma, Maryam ta zuba masa lemon ya dauka ya kurba ya ajiye yace "Nagode." Tai kasa da kai. Gyaran murya yai cikin muryar sa mai dadi da sanyi yace "Na miki bayani akai na tin kwanaki, kinga gidan mu, da yan uwa na da aboki na komai kike so ki bincika ki tambayi Abdul zai fada miki ba zai miki karya ba." Kai ta gyada yace "Akwai abinda kike so kuma kike son ki sani?" Kai ta girgiza yace "Shikenan kofa a bude take ko ba yau ba in kina bukatar jin abu daga gare ni sai dai ni ina da bukatar sanin wani abu akan ki, wannan Yayan naki Maman ku daya?" Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace "My wife." Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yace "Subhanallah meya faru?" Kai ta girgiza ta mike....... *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* [10/30, 13:46] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 11 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir rahmanir rahim* * Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace "My wife." Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yA yace "Subhanallah meya faru?" Kai ta girgiza ta mike tana fadin "Kayi hakuri." Sai tayi cikin gida da sauri, dakin ta ta shiga ta fada saman gado rayuwar ta take son ta tuno so take ko ta halin yaya ta tuno wani abu amman ina ta manta tasan dai ta kasance a wannan gidan wanda yake shine gatan ta a duniya kawai su suka rufa mata asiri suka zame mata iyaye da family, shin su waye iyayen ta? Ina suke? A baya ne take shiga wannan halin na son lallai sai ta tino su waye iyayen ta wanda in tai wannan tunanin yake saukar mata matsanancin ciwon kai saboda damuwa in ba sa'a ba sai ta kwanta ciwo ma. Bata san lokacin da bacci ya dauke taba, Ummi ta leko dakin ta ganta kwance ta rufe kofar kawai ta barta da dare Aliyu ya aika Haidar ya kira Maryam, lokacin har ta saka kayan bacci, kana ganin ta zaka gane tana cikin damuwa, hijab ta dauka har kasa ta daura sannan ta fita, ba kowa a falo dan lokacin tara ta gota, dakin ta nufa ta kwankwasa aka amsa ta bude a hankali, zaune ta same shi akan kujera da remote a hannu. "Gani." Ta fada tana duban shi sai taga ya daure fuska, itama fuska daure dan daman bata cikin walwala tun dazu da aka famo mata inda yake mata ciwo. A ranta tace "Miskilanci na shi ya tashi kenan." Bai kalle ta yace "zauna" Ta zauna, ya dago ya dube ta yace "Waye Muhammad?" "Nima ban san shi ba." Wani murmushi yayi yace "Bana son karya, ke kuma yanzu kina son ki koya ko?" Kai ta girgiza yace "Nasan kin sanshi tinda ke kika bashi dama zuwa wajen Abba, buri na akan ki, ki tsaya kiyi karatu, kamar yadda kike fita da point mai kyau ya zama har karshen karatun ki haka amman ke kin nuna kin girma aure kike so ko? Ki sani in nace a'ah ba wanda zai ce eh dan haka ba zan bar yaron yana zuwa wajen ki bane dan ya hanaki karatu, ko da tafiya zanyi bana son yawan zance a wata sau biyu ya isa dan ina da buri akan ki, wani can ba zai zo ya lalatan buri ba dan haka ki kiyaye ke kina son sa ne?" Banza tai masa dan ya fara bata mata rai ina ruwan sa da tana son sa ko bata son sa ya bari ya gani ko yaji mana, "Ba magana nake miki ba." Ya fada wanda hakan ya sa ta dagowa da sauri duk da yadda yaga idon ta a kumbure sai ya kau da kai yace "Uhmmm." Shiru tayi yace "Shawara daya zan baki kada ki soma yin kokarin rusa min buri na, in har kikai haka daga ke har ni ba wanda zai ji dadi, ki daure ki cika min buri na akan ki." Dagowa tayi tana son karin bayani gane haka yasa yace "Eh akan karatun ki." Kai ta dauke yace "Shine gatan mu, kuma ilimin shine madogarar mu, kina ji ko?" Kai kawai ta gyada, yace "Kar kice zaki bar karatun ki kiyi aure wannan duk bata lokaci ne da daurawa kai wahala." "Ni daman ba aure zan yi yanzu ba, karatu nake so na karasa kuma shima ya sani." "Na fada miki dai dan kar yazo ya hure miki kunne gashi ni zan tafi amman duk da haka zan saka ido akan ku, na sani ba wai son sa kike ba ko kina son sa?" Kai ta gyada yace "Karya kike Maryam, ki koma ga zuciyar ki ta fada miki wanda kike so amman ni nasan ba son Muhammad kike ba." "Yaya....." Hannu ya dauran akan bakin sa yace "Bana son naji wani abu, da kina son sa da dazu dana tambaye ki, kin sanar min amman kin kasa saboda har zuciyar ki ba son nasa kike ba, bana son kije inda za a wulakanta ki, ina son kije inda za a kula dake inda akasan darajar ki." Dagowa tai tana kallon sa, shima ita yake kalla yace "Tin ina yaro nake iya gane abinda wani yake ciki, wanda dana girma abin yake ban sha'awa, wannan dalilin yasa bayan na zama likita na koma na karanci halayar dan adam, ina karantar yanayin mutum nasan me yake ciki da manufar sa da yawa in anyi abu ina dauke ido ne kawai akan wasu abubuwan......" Ido ya lumshe ya bude yace "Dan haka kada ki min musu, kinso wani a baya kuma ba wanda zaki so a gaba sai wanda yake tamkar na bayan nan mai wasu daga cikin halaiyar sa, duk da kin manta wasu abu amman zuciyar ki ita zata kwadaita miki wasu abun, bama wannan ba in kin tashi mai irin sunan sa zaki aura zaki cike gurbin da a baya baki cike ba dan haka ki nutsu kada ki tsaya batawa kan ki da wani lokaci." Baki ta dan tabe kawai yai murmushi yace "Gobe zan tafi wanda zan jima acan shekara daya zanyi ko fi ban sani ba ko zan iya ko ba zan iya ba, amman dai zan tafi ga amanar Haidar nan, dan Allah ki kular min dashi, sannan in kina bukatar wani abu ko na menene kina iya nemana ta waya kar kiji nauyin komai kinji ko?" Kai kawai ta gyada dan jikinta babu karfi yace 'Shikenan daman sai batun karatu dan Allah kada ki bani kunya." Nan ma kai ta gyada dan ta kasa magana zuciyar ta na kusa in tace zatai magana zata iya kuka ne tasani, yace "Shikenan zaki iya tafiya." Ta mike a ranta ba dadi, har ta kai kofa tace "Bari na juyo na mishi kallon karshe kila sai shekara lokacin ko ina raye ko na mutu." Tana juyowa suka hada ido dan shima ita yake kallo, sun jima suna kallon juna sannan ta dauke idon ta hawaye ya hau zubo mata a wajen ta durkushe ta saki wani kuka mai taba zuciya da sauri ya karaso ya durkusa a gaban ta yana fadin "Menene?" Kuka kawai take wanda daga zuciyar ta yake tahowa, wanda yake taba tasa zuciyar, "Maryam!" Ya kira sunan ta, ta dago kai tana kallon sa hawaye na zuba a guje ta mike ta fice a dakin ya zauna a wajen yana dafe kan sa. Ranar abu biyu ne ya hadar mata ga tunanin dazu ga rabuwa da Yaa Aliyu, mutumin da ya zamo mata tamkar uba baya gajiyawa da kula da ita da kudin sa da aljihun sa da lokacin da komai nasa, yau zai tafi yai mata nisa a rayuwa. Ranar kwana tayi batai bacci ba wanda daga karshe ta mike tayo alwala tazo ta tada sallah. Hakika addu'a da tai ta rage mata damuwar ta sai dai ciwon kai da ya matsa mata dan daman ita ba dama ta shiga damuwa kanta zai farai mata ciwo, washe gari da matsananincin ciwon kai ta tashi wanda take jin kan kamar zai fadi ga damuwa da ta hadar mata, dama dama ma da tayi addu'a sai ta samu sassauci, amman da an kalle ta za'aga bata cikin walwala. Sanin halinta da rashin cin abinci yasa Ummi tazo ta kira ta har kasa suka sauka suka karya gaba dayan su, ita da Yaa Aliyu da ka kalle su zaka gane suna cike da damuwa abincin ma basuci wani na kirki ba suka barshi. Tana dakin ta a kwance, Haidar ya shigo da gudu yace "Adda Abbi zai tafi kizo ki masa bye bye." Bata so fita ba amman ko dan tai masa bankwana na karshe ta leka, ta dauki hijab din ta, ta saka har kasa ta fito yana tsaye a falo yana duba wayar sa Ummi na masa magana ta sauko dukka kallon ta sukai, ta sunkuyar da kai kawai ta fita, bangaren Inna ta nufa Aliyu ya kalli Ummi yace "Ummi me yake damun ta ne? Tin jiya naga sauyi a tare da ita tana da matsala taki fada min Ummi please ki tambayar min ita zan kira naji ko menene please Ummi ga Haidar nan ki kula min dashi." "Insha Allahu Aliyu Allah ya bada sa'a da nasara ka gaishe min da su Yaya." "Zasuji." Yace 'Bari naje naiwa su Mami da Inna sallama." "Ok Son." Ya fita bangaren Mami yaje yai musu sallama sannan ya nufi bangaren Inna anan ya samu Maryam da Haidar bayan sunyi sallama Farouk da zai kai shi gidan Sitti daga nan su wuce airport yace "Ko zaki zo muje tare?" Aliyu ta kalla taga ya mike ya fita, Yaa Farouk yace "Taso muje kiga gari ko Haidar?" Kai Haidar ya gyada ta mike kawai tabi bayan su, a baya suka zauna ita da Haidar Aliyu, da Farouk suna gaba, tin da ta shiga bata ce kala ba sai jingin da kujera da tayi ta lumshe idon ta, a haka suka zo gidan Sitti suka sauka suka shiga nan suka gaishe ta Maryam ta zauna a can gefe a haka sukai sallama suka fita zuwa airport har da Najwa da akaje airport kowa ya fita ya rage Maryam dake jingine da kujera bama tasan anzo ba sai Aliyu dake dannan waya ya dago zai fita ya hango ta juyowa baya yayi ya kalle ta yace "Maryam!" Bata san ma yanayi ba sai da ya kira ta wajen sau uku sannan ta bude idon ta, kallon ta yayi da damuwa yace "Tunanin me kike?" Kai ta girgiza yace "Ki fadan gaskiya." "Ba komai Yaya." Ta duba taga su Najwa a waje ta bude mota ta fice ya bita da kallo shima ya sauka suka shiga lokacin da zai tafi tana zaune Najwa da Farouk na tsaye kusa da Aliyu dake rike da Haidar, sai aka kira suna su kowa na masa sallama Haidar kuka ya saka, Farouk ya amshe shi yana lallashi Maryam na zaune tana kallon su, har zai juya sai ya hango Maryam tsayawa yayi yana kallon ta har Najwa ta juyo taga wa yake kallo? sai taga Maryam yake kallo kai ta kawar tana murmushi. Kai Maryam ta langwabar sannan ta daga mashi hannu alamar bye bye hannu ya daga mata ya juya ya tafi zuciyar sa ba dadi. Sai da sukaga tashin sa sannan suka koma gida, a cikin gate taga motar Muhammad tana fitowa ya kure ta da ido, Haidar yaje ya gaishe shi ya amsa ya karaso wajen Maryam da takasa takawa, "Good afternoon princess na kasa samun nutsuwa tin jiya, kwana nayi ban bacci ba saboda bansan damuwar ki ba gashi ina kira wayar ki a kashe." "Hmmm ina yini?" "Daga gani na zaki gane ba lafiya ba." "Me yake damun ka?" "Abinda yake damun ki, ke kike jin ciwon abun amman nafiki jin zafin sa, kalle ki fa Maryam me yake damun ki daga jiya zuwa yau kawai kin canja saboda kinsa damuwa dan Allah fada min damuwar ki." Kai ta girgiza kawai. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Wajen Ummi nazo." Dagowa tai tace "Ummi kuma?" Kai ya gyada yace "Ko bata nan?" "A'ah muje sai na fada mata." Suka shiga harabar gidan su, a nan ya zauna ya shiga ta samu Ummi a kitchen ta karasa tace "Ummi wai Muhammad ne yazo wajen ki." "Waje na kuma? Lafiya?" Hannu ta ta daga tai nuni da itama bata sani ba, Ummi tace "Jeki shigo dashi." Ta fito falo ta yafa mayafinta, Maryam ta fita ta same shi zaune tace "Ka shigo." Ya mike ya shiga dakin a falo ya samu Ummi, ya zauna akan carpet, Ummi tace "Taso ka zauna aka kujera." "Ummi nan ma ya isa." Tayi tayi amman yaki yadda, Ummi tace "To shikenan." Yai kasa da kai yace "Ina yini Ummi?" "Lafiya lou ya gida yasu Mamin taku?" "Alhamdulillah!" Sai yayi shiru, Ummi tace "Lafiya Muhammad?" "Lafiya Ummi, daman akan Maryam ne nazo." Sai yai shiru Ummi tace "Me ya faru tsakanin ka da Maryam din?" "Ummi ni bansan me ya faru ba tin jiya da naiwa Maryam magana naga tana kuka, ina ta kiran wayar ta ma sam bata dauka ba kuma yau da na ganta ma tana cike da damuwa, Ummi ni da gaske nazo da son auren ta, dan haka dole na shiga damuwa na halin da na same ta a ciki, dan Allah Ummi ki tambayar min ita me nayi mata in nine da laifi sai nasan menene sai na bata hakuri." Shiru Ummi tayi can tace "To nima tin jiya Aliyu ya damu da halin da ta shiga, yai min magana kuma nima naga canji a tare da itan zama ne bamuyi ba amman insha Allahu zan tambaye ta duk abinda ake ciki zan neme ka na sanar da kai. Nagode da kular da kai akan ta Allah saka da alheri." "Amin Ummi nagode." Ya russunar da kai yace "Zan tafi sai anjima." "To ka gaida gida dasu Mamin." "Zasuji nagode." Ya mike ya fita. Ummi ta mike ta koma kitchen ta cigaba da aikin ta. Maryam dake waje zaune jiran sa taga ya fito ta mike tana kallon sa, ya kalle ta yace "Zan tafi." "Tin yanzu?" "Kina so na zauna ne?" Shiru tayi yace "To bari na tafi sai munyi waya." Kai tai kasa dashi tace "Ka gaida gida." Ya juyo yana kallon ta, ta juya tai ciki da sauri. * Da dare Ummi ta samu Maryam kwance akan gado tai shiru ta kurawa waje daya ido, har ta zauna bata san ta shigo ba sai da ta dafa ta sannan ta juyo da sauri, ganin Ummi yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta matso da kanta ta daura akan cinyar Ummi tana fadin "Ummi yaushe kike shigo?" "Kina can tunani." "Ba tunani nake ba." "To me kike?" Shiru ta danyi sai kuma tace "Ummi Yaya fa?" "Ga tambayar da nake miki kina min wata ko?" Shiru tayi, Ummi tace "Tashi ki zauna muyi magana." Tashi tayi, ta zauna Ummi ta kalle ta tace "Dazu Muhammad yazo kuma akan ki ne. Me ya faru?" Hawaye ne ya hau zubo mata Ummi tace "Ni ba kuka nace ki min ba." Hawayen ta hau sharewa. Ummi tace "Tin jiya Yayanki ya lura da kina cikin damuwa, kuma nima naga haka, ki fada min me yake damunki?" Shiru tayi, Ummi tace "A duniya wa kike dashi, da zaki fadawa damuwar ki sama dani?" Kai ta girgiza tace "Babu." Ummi ta kama hannun ta tace "To fada min me yake damun ki?" Kuka ta fashe dashi ta rumgume Ummi, Ummi ta hau shafa bayan ta tana fadin "Fadamin damuwar ki shi zai kawo karshen damuwar ki, domin zanyi iya yi na ganin na cire miki damuwar ki, ko da zan rasa komai nawa ne, ki fada min me kike so? Me yake damun ki?" Shiru tayi Ummi tace "Ko Muhammad din ne bakya so?" Shiru Maryam tayi kawai, Ummi tace "Fada min kinji yar albarka." Hawayen idonta ta goge tace "Ummi ina mantawa dani ko wacece saboda yadda kuke bani kulawa wannan yasa bana damuwa da tina asali na, Ummi kin dauken tamkar yar cikin ki, kin bani so da kauna da kulawa gareni da abinda nazo muku dashi duk family din ku, kun dauken yar uwa bakwa nuna min bambanci da ya'yan ku wannan ya mantar dani rayuwata da koni wacece bana damuwa da komai da kowa." Ta shige jikin Ummi wani kuka yana kara taso mata, hawaye take wanda yake fitowa tin daga kasan zuciyar ta, ajiyar zuciya ta sauke tace "Ummi a jiya duk aka dawon da abinda na manta, a jiya aka dawo dani haiyaci na a jiya komai ya dawo min, naso a jiya na tino da kowa nawa amman sai dai tino dani din da akai bai sa na tina abinda ya mance a kwakwalwata, Ummi...." Sai tai shiru tana ajiyar zuciya kukan take so tayi amman yaki ya fito, ido ta runtse jin wani abu na damun ta a kasan zuciyar ta, Ummi ta hau shafa bayan ta tana jin damuwa akan halin da Maryam take ji, ita kanta ciwo take ji, zatafi kowa son sanin asalin Maryam amman tayaya ta ina zasu fara ko Bauchi zasu koma suyi cigiya tinda anan suka samo ta. Maryam ta kalla ganin ta dan samu nutsuwa sai ajiyar zuciya take saukewa Ummi tace "Ki daina damuwa mune komai naki, mune iyayen ki, yan uwanki, komai naki ki daina damuwa kinji daughter." Kai ta gyada Ummi tace "Yauwa waya tada miki wannan abun?" "Ummi a baya bana tunanin aure zai gagareni amman a yanzu ina tunanin ni da aure har abada saboda babu wanda zai auri mara asali, nasan duk wanda yazo neman aure na dole yaso sanin asali na, Ummi to tayaya zan yi aure a haka, ga yaro a tare dani, shin wasu wane kallo zasuyi min da yaro na, Ummi tayaya zan aure, a baya na zata zamu sasanta da Muhammad, sai dai haduwar mu dashi yasa ya dawo dani haiyaci na, Ummi jiya yaso sanin halakata da Yaa Aliyu wanda daga nan dole yasan wacece ni? Ummi yakamata Muhammad yasan wacece ni, dan zan bata masa lokaci ne, yadda yake so na zai shiga wani hali tin a jiya ya fara bani tausayi yadda yake kirana kiga fa yau haka ya taso yazo wajen ki akan sanin me yake damu na. Ummi ya zanyi to hakan ai shine yasa na fara janye jiki na." *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* Barka da hutun karshen mako. *Antty* [10/31, 09:18] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 12 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* *Happy Birthday Our Autah Hauwa'u Yasmeen wish your more benefit years ahead, Allahu ya kare ki daga duk sharrin abun ki, Allah ya buda miki kwakwalwa ya baki miji na gari mai son ki, Allah ya raya ki yasa ki zama mahadaciyyar Alkur'ani Allah yasa muyi alfahari dake, addini yai Alfahari da, really love you my lovelly sister. HBD once again* 🎂 🎂 🎂 * "Shikenan na gane matsalar da aka samu tin daga wajen su Abba ne ya kamata su farai masa bayani in yasan wacece ke shikenan, naji anan anyi ba dai dai ba, amman ki daina fadar ba zaki aure ba, menene aibun ki, ina da yakinin duk daga inda kike kina da asali da tsatso mai kyau, a halaiyar ki menene marar kyau, kina da hakuri tarbiyya ilimi ga hankali me za kuma a nema a wajen ki, ki bar damuwa da izinin Allah zaki tuna da kowa naki zaki ga iyayen ki kuma zaki aure ki kara haihafa dan Allah ki daina kuka da saka damuwa, ko Muhammad yaki ki wani zai zo ki duk aibun ki bare ke baki da wani aibu dan haka kiyi hakuri ki cire damuwa kinsan kina da ciwon zuciya ko so kike in rasa ki, kina zaton in na rasa ki wane hali zan shiga, ban taba haihuwa ba sai gashi Allah ya hada ni da yara biyu a lokaci daya ni me zanyi to nagodewa Allah na amshe ku to kema ki godewa Allah kuma mu kara tashi da addu'a zamu kara komawa asibiti a duba ki muga ko za a samu wani cigaba da yaddar Allah zakiga iyayen ki da yan uwan ki, ki daina kuka kinji?" Rumgume Ummi tayi kawai tana sauke ajiyar zuciya. Ummi ta shafa bayan ta tace "Sorry kinji Daughter." A haka bacci ya dauke ta, Ummi ta dade a dakin sannan ta mike ta rufe mata dakin. Daki ta shiga ta zauna tare da zuba tagumi, wayar ta ce tai kara tana dauka taji muryar Aliyu, ta sauke ajiyar zuciya tace "Son ka sauka lafiya?" "Lafiya lou Ummi ya gidan? Ina Maryam" "Tana nan kalau." "Masha Allah. Ummi kin tambaye ta?" "Aliyu ba yanzu ka sauka bane kaje ka kwanta ka huta ko?" "Ummi kar ki damu ki fada min me tace miki? Maryam na cikin damuwa Ummi bana son ya taba mata lafiyar ta please Ummi ki fada min." "Shikenan yanzu kaci abinci?" "A'ah Ummi bana jin yunwar Ummi." "To shikenan akan batun wanda yazo neman auren ta ne." "Cewa tayi bata son sa?" Ya fada da sauri, Ummi tace "Ba haka bane, bansan me ya mantar da Abba ba bai masa bayani akan wacece Maryam ba......" Da sauri ya katse ta da fada yace "Cewa yai baya son ta dan bata san iyayen ta ba?" "Haba Haidar cool down mana, ba haka bane, yaso yaji wani abu akan ta ne." "Bashi da hankali yaje yai bincike mana a wajen ta zai ji lallai...." "Aliyu ba haka bane ya tambaya ne kawai." "To me yace akan haka?" "Ba haka bane Aliyu, i think ma ita bata bashi amsa ba, shine abinda yake damun ta dai." "Shine take kuka dan kada yace baya son ta, ce mata akai ba zata samu wanda yake son ta ba haka? Menene da ita da za a 'ki tan?" "Aliyu dole ta damu ai." "Akan me? Akan me zata damu? Dan kada ya guje ta? Wai yaushe ta san shi ma da zata saka shi a zuciyar ta haka? In ba zai iya ba ya kyale ta mana me zatai da shi itama, ai tafi karfin sa, Ummi in ta tawa ce a hanata kula sa in har zai na saka mata damuwa bana so sam" "To menene na daukar zafi ne haka, ai laifin mune da bamuyi masa bayani ba zanwa Abban ku magana sai ai masa magana ya sanar dashi in yaga yana so to in baya so ni nasan wani zai zo mata insha Allahu." "Is better dai." "To kaje ka huta." "Sai da safe." Ya fada ya kashe wayar sa dan ransa ba karamin baci yai ba, kwanciyya yai akan gadon yana dafe kansa da yaji ya dau zafi, kila fa yanzu tana can tana kuka akan wani can yazo ya tada mata da hankali yasa mata damuwa. Mikewa yai ya dauki wayar sa, layin Maryam ya fara nema amman sai aka ce masa a kashe take kira ya kara yi same a kashe take wayar yai cilli da ita, ya mike ya shige ban daki. Yana shiga ya sakarwa kan sa ruwan ya jima a karkashin shower ruwa na zubo masa amman bai bar wajen ba, sai daga baya ya fito daure da towel, jallabiyya ya dauka ya saka, ya hau kan sallaya dan yayi sallah yana idarwa yaji ana knocking budewa yayi yaga Yasmeen yar yar Ummi ya saki murmushi yace "Baby Yasmeen." "Big bro Momy ce tace wai kazo kaci abinci." Hannun ta ya kamo yace "Am not hungry dear." "But Big bro u having eat any thing since u came." "Yess Baby i take something there." Kai ta gyada ta juya ta fita, komawa yai ya kwanta, bai jima da kwanciyya ba yaji ana knocking kofa kamar ba zai tashi ba amman jin muryar Antyn sa, yasa ya mike yana budewa ya koma ya zauna a gefen gado, Momy ta shiga tana kallon sa, ta jima a tsaye har sai da ya dago yana kallon ta sannan ya dan saki fuska yace "Momy nayi laifi ne?" Zama tayi akan resting chair dake dakin tace "Me yake damun ka? Tin zuwan ka na gane kana cikin damuwa." "Momy zuwan ne bana so kwata kwata." "Oh wajen namu ne baka son zuwa." "A'ah Momy in wajen ku ne nasan zanyi two to three week na juya amman yanzu shekara fa, ina da abubuwa da nake son yi a can da yawa." "But Aliyu naga kai ka nemi tahowa ko?" "A lokacin da na nema basu ban dama ba sai a yanzu da bana so." "To ka daina damuwa kaji kayi addu'a Allah yasa zuwan naka a wannan lokacin shine mafi alheri, ka sani ni ba zan yadda da rashin cin abinci ba, balle ka koma rame ayi zaton bana kula dakai ko da dura sai kaci kaji ko?" "Momy naci abu a jirgi fa yanzu hutawa kawai nake son yi." Mikewa tayi tace "Ni dai na fada maka za a kawo maka ko tea ne ka sha." Ta juya ta fita, kansa ya dafe yana mai lumshe ido, Basma Yayar Yasmeen ce ta shigo da tray a hannun ta, dagowa yai ta ajiye akan stool ta matso masa dashi gaban gado, dagowa yai ta zauna tace "Big bro ina ta zuba ido ka fito amman shiru?" Murmushi ya saki yana fadin "Na gaji ne." "Yasu Sitti?" "Suna lafiya suna gaishe ku." "Big bro dan kai ta tafi kaima kuma ka dawo." "Ni ba jimawa zan ba zan koma" Tai murmushi tace "Bikin Anty Najwa?" "Kila." Ganin bai son surutu yasa ta mike tace "To sai anjima." "Alright." Ta mike ta fita, kurawa kayan abincin ido yayi daga karshe saboda yasan halin Momy in bai ci ba da kanta zata zo ta tsaya har sai yaci wannan yasa ya dauki dan fulas din dake kan tray din ya tsiyaya tea din a cup, bai saka komai ba sai dan sugar ya dauka ya fara sha, yana gamawa ya mike ya shiga toilet ya jima a ciki ya fito yana kara tsane jikin sa da alama wanka ya karayi, kan gado yazo ya kwanta amman me sam bacci yaki ya dauke shi sai juyi ya dinga yi, abubuwa na damun sa ganin ba baccin zai ba yasa ya mike ya shiga ya dauro alwala akan sallaya ya kwana yana addu'a. * Washe gari Ummi ta samu Abba tai masa bayani kai ya dafe yana fadin "Wallahi Aisha na sha'afa sam saboda mantawa nake da Maryam ba 'yata bace amman insha Allahu zan kira yaro sai nai masa bayani in yaga yana son ta a haka shikenan Allah yasa mu dace." "Amin nima na damu bana son damuwar ta gaba daya." "Insha Allahu komai zai tafi normal." Kan Abba ya fita ya kira Muhammad yace yazo da dare in ya dawo daga aiki. Haidar ne ya tashi Maryam da safe yana fadin "Adda cornflask zan sha kinji Adda." Ido ta bude tana kallon sa tace "Ina Ummi?" "Ta fita aiki?" "Bakai breakfast bane?" "Nasha tea ni cornflask zan dada." "Ai Iyya na kitchen dan Allah jeka ta hada maka." Ta fada tana dafe kan ta dan har lokacin ciwo yake, baki ya turo kamar zai kuka yace "Adda nata ba dadi na Abbi na yafi, Adda ki kira min Abbi ya hada min." Kai ta dafe tana fadin "Ni muje na hada maka." Ta mike ta fita har ya kai kofa yaji wayar ta na kara komawa yai ya dauka ya fita a guje yana cewa "Adda ana kira." Bata falo har ta sauka dan haka ya bita kitchen tana hada masa madara ya karasa ya mika mata yace "Adda ana ta kira." Amsa tayi tana kallon screem din ganin sunan Yaa Aliyu yasa ta zubawa screen din ido tabbas itama tana son taji ya ya sauka tinda bata samu ta tambayi Ummi ba. Wayar ce ta kara yin kara ta duba da sauri ta dauka ta kai kunnen ta, sai dai ta kasa furta komai, sallama yai mata cikin muryar sa mai dadi da sanyi wacce take kwantar da hankalin mai sauraron ta ido ta lumshe tana amsawa a kasan makoshi tare da yin shiru. Aliyu dake kwance yace "Tinda baki iya gaisuwa ba bani yaro na." Duburburcewa tayi tace "A'ah Yaya ina kwana? Ya ka sauka? Da fatan ka sauka lafiya?" "Alhamdulillah ina Haidar!" Haidar dake zaune a dining ta kalla tace "Gashi nan." "Ok bashi wayar." Mika masa tayi tana fadin "Ga Abbin naka." Ya amsa ya kai kunne yace "Abbi ina kwana?" "Lafiya lou My son ya kake?" Ya fada yana jingina da kujera. "Alhamdulillah Abbi." "Masha Allah me kake yi?" "Abbi, Cornflask Ummi ta hada min nake sha." "Iyyee dan gatan Adda, na kira Ummi mu gaisa tace ta fita." "Yes Abbi." Maryam fita tayi daga kitchen din, Aliyu yace "Ina Addar taka?" "Ta fita Abbi." "Ok zan fita yanzu in na dawo zan kiraka kaji." "To Abbi yaushe zaka dawo." Dan murmushi yayi yace "Haidar kenan jiya fa na tafi zan dan jima ban dawo ba, ina son ka maida hankali a school sosai da sosai kaji?" Kai ya gyada yace "Insha Allah Abbi." "That is my good boy Allah maka albarka." "Amin Abbi." Yace "Ok bye ka gaida Inna da Mami." "To Abbi, bari naje na fada musu." Ya cire wayar a kunne ya karasa falo inda Maryam ke kwance ya mika mata waya, yana bata yace "Zanje wajen Inna da Mami Abbi ya aike." "To agaishe su." Ya fita da gudu, Maryam ta maida ido ta kwanta. Yini tayi tana bin waje tana kwanciyya, har Ummi ta dawo yace "Maryam jikin ne?" Kai ta girgiza tace "Bana jin dadin jiki nane." "Munyi waya da Aliyu likita zai zo ya dubaki yanzu." "Ummi ni naji sauki fa." "Daman tinda bakya son magani ba, kuma Allah yazo ya duba sai kinsha magani." Baki ta turo ta koma ta kwanta kawai, Ummi ta mike ta wuce sama tana fadin "Ki gama turo bakin ki, dan Aliyu baya nan ba zan zauna dake ina ganin ki, kina ciwo ba." Flash Back July 2017 Kano State *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 13 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* ~Flash Back~ ```July 2017 Kano State``` ```*MANS GIRLS COLLAGE* shine sunan dake rubuce a saman wani katon gini wanda aka kwata shi rubutun kan sa abun kalla ne, banda ginin da yake katon gaske wanda ginin mai kyau ne, da tsari dan ba dan an rubuta makaranta ba da ba zakace makaranta bane dan kyau da tsarin ginin, wanda yake da bene har wajen hawa uku. Wanda makarantar tai fice a cikin garin Kano da kewaye duk wani d'an wane wato masu kudi, yan siyasa, da masu mulki, da wanda ke ji da kansa nan ba wai dan tsadar makarantar ba a'ah sai dan yadda makaranta take da manyan kuma kwararrun malamai. Dan malaman duk kan su kwararrun ne kuma suma dan suna samun salary mai kyau shiyasa suke kara zama a wajen duk da wasu suna aikin gwamnati kuma suke kara zuwa suna aiki a wajen. Da ka shiga babban gate din babban harabar (compound) wanda yake dauke da wajen adana motoci (parking space) an saka masa rumfa an kwawata harabar wajen (compound) da shuke shuke, wanda har wani round about akai a tsakiyar makarantar an rubuta sunan makarantar da manyan baki kuma an kwatashi. Duk ka makarantar an malaleta da kwalta wajen yayi kyau, kato ne sosai dan in anzo ziyara (visiting) din dalibai duk anan ake ajiye motoci (parking) duk yawan mutane wato iyayen yaran da zasu zo wannan harabar (compound) din na dauke su kamar yadda yau yake ma cike da manyan motaci masu kyau, tsada duk ka dai saboda yau dalibai makaranta ake yaye su (graduation) wanda duk iyaye suka zo daukar yaran su. Ba motar da ta karewa kowa in zai fita duk da wajen ba kowa sai d'ai d'ai kun drivers sauran ma kuwa duk suna cikin mota iyayen kuma suna can cikin makarantar. Wanda bayan wannan harabar (compound) din akwai wani a ciki wanda anan bangaren malamai yake da ajujiwa (classes) din daliban makarantar shima wannan compound din an kwata shi sosai dan har filin (wasanni) sport, Assembly hall, meeting hall, da Special hall wanda anan ake duk manyan taro na yaye dalibai ko speech and price giving day da holidays da sauran abubuwan duk anan suke, wanda iya nan wajen da dalibai suke iya fitowa daga nan sai can cikin makaranta wanda a can ne hotel yake da sauran abubuwan entertainment na makaranta. To yau special hall ne ya dauka dan yau SS 3 student sukai graduation wanda tin 9:30am suka shiga exam suka fito 12:30pm suna fitowa dukkan dalibai cikin makaranta suka koma suka wanka sukai sallah sannan suka shirya cikin kayan su na graduation. Duk kan su yan mata ne wanda suke daga kan shekara 16, 17, 18 and 19 kuma duk wacce zaka kalla zaka gane yar hutu ce domin in kana *MGC (MANS GIRLS COLLEGE)* tamkar kana gida ne yadda ake kula da kai da komai na rayuwa dan kowa yana da system a hannun sa haka suna da wayoyi amman duk inda takwas na dare yayi an amshe wayoyin su haka nan karfe tara duk dalibai dole su tafi su samu entertainment sunyi kallo na awa daya zuwa awa daya da rabi da sun tashi kowa zai wanka da alwala sannan a kwanta kan sha daya dole kowa yai bacci kuma duk bayan awa daya zuwa daya da rabi Nanin dakin zatana mikewa tana duba lafiyar kowa wanda karfe biyar duk suke tashi suyi wanka suyi alwala sannan su shirya suyi sallah. Kan 6:00am sun gama komai har azkar wanda daga nan dining hall suke tafiya a can kowa zai zabi abinda yake bukata wanda kafin 7:00am an kawowa kowa nasa yai break daga nan su tafi assembly hall minti talatin suke yi ake tafiya aji wanda a ragowar minti talatin din zasuyi kintsa kan a fara class activities at 8:00am wanda karfe 10:30am ake fita tara, shima kowa abinda yake so zai zaba ya amsa, 11:00am ake dawowa 1:30pm ake tashi wanda ana tashi ake sallah daga nan abasu minti talatin dan suje suyi wanka suci abinci sannan su fito isilamiyya. 3:45pm kuma ake sallah sannan su koma sai 5:30pm ake tashi wanda anan kowa ake bashi wayar sa inda abinda zai yi yayi har ai magariba da isha'i a amsa. Haka rayuwar su take daga Litinin zuwa Laraba wanda Alhamis da Juma'a basa isilamiyya suna shiga catering class ne a koya musu girki kala kala wanda Asabar da Lahadi kuma tahfiz suke zuwa tin 7am har 5pm. Hatta uniform wanke musu ake kowa da sunan sa a jiki za a ajiyewa kowa nasa. Kuma basa taba saka kayan gida kullum kayan makaranta suke sakawa (personal wear they always put uniform) wanda suke da na normal school, na Isilamiyya, na catering, na tahfiz, sport, entertainment, da kayan bacci (sleeping dress) duk iri daya sai dai kowa da sunan sa ko kuma yan room kaza su zama on one colour like red, blue, yellow, pink etc Babu zancen wannan yafi wannan aji ace za a saka wani aiki ko makamantan su duk sun dauki junan su yan uwa bama in dakin ku daya ko hostel din ku daya. A ka'ida tin kana JSS 3 suke saukewa wanda suke walima mai kyau shima iyayen ka zasu zo a bada kyaututuka (gifts) da sauran su. Wanda a SS 3 kuma suke haddace Alkur'anin wanda ba a tashi walima da bada kyauta sai a ranar kammala karatun (graduation) gaba daya anan ake yi. Shiyasa duk iyaye da yan uwa da abokan iyaye dake wannan makaranta suke jiran wannan ranar domin kuwa rana ce ta farin ciki d'an ka ya haddace Alkur'ani mai girma kuma ya gama karatu wanda ilimin ke da inganci saboda samun kwararun malamai da kulawa da suke sosai. Karfe 1:30pm Special hall da aka kwata shi da decoration ya cika da iyayen yara maza da mata, wanda a hall din akwai sarakuna na mabambanta garuruwa da yawa ga gwamna da mataimakin sa da wasu kusoshin gwamnati ga manyan malamai da yan kasuwa dukka da iyalan su dan a cikin su kowa da akwai nasa da zai gama makarantar. Yara guda dari ne suka yi graduation da haddar Alkur'ani wanda suke aji guda hudu dan duk aji daya ana saka dalibai ashirin da biyar. Iyaye ne zaune atsakiyar hall din akan kujeru kowa gaban sa an anjiye masa lemo da ruwa da tissue wanda manyan baki kamar shugaban kasa da gwamna da sarkin garin da Babban malamin garin suke gefe suma gaban su lemo da ruwa ne. Dayan gefen kuma malaman makarantar ne a wajen. Wanda saman benen kuma gefe daya na sauran student dake JS 1 to 3, haka nan SS 1 to 2 wanda a gaban hall din kuma wajen zama ne na dalibai guda 100 din da suka gama makarantar. Suna zaune daliban suka fara shigowa cikin shigar su ta iri daya wanda kowa ya saka graduation gown a ciki kuma wasu kaya ne iri daya riga three quater da wando red colour sai farin hijab wanda ya sauko kan kirjin su. Sai takalmi cover shoe baki da white socks kowa wuyan sa sakale da tag kowa da matsayin sa kamar headgirl, assitant, prayer, da sauran su. Suna zama aka fara gudanar da taron kamar yadda aka fara. Wanda Babban malamin dake zaune a gefen Sarki uba ga daya daga cikin daliban shi zai bude taron da addu'a wanda aka kira sunan shi Sheihk Muhammad Jabeer Muhammad. Wanda ya mike cikin shigar sa ta babban malami yayi addu'a sannan ya zauna. Sannan akai national anthem da national plag, Daliban JS 1 aka kira dan suzo suyi barka da zuwa ga iyayen su. Nan suka sauko cikin shiga iri daya wanda kusan kan su daya haka kamar su ma iri daya ake gani suka zo sukai musu barka da zuwa da Hausa da Turanci sannan sukai da Larabci suka koma. Nan aka bada tarihin makarantar da irin nasarar da makarantar ta samu, haka aka dinga gudanar da program din har aka bawa kowa allon sa da certificate na cewar sun haddace Alkur'ani. Wanda a cikin manyan baki su suka dinga represnting suna bawa yaran wanda yan jarida gidan radio kamar Freedom, Express, Rahma, Dala, Gurantee, Vision, da gidan television na Arewa 24, NTA, ARTV, Farin wata, Tauraruwa da sauran su, suka dinga dauka haka nan photo graphers na makarantar sai aikin su suke yi. Wanda bakin iyaye ya kasa rufuwa kowa murna yake da farin ciki nasarar da yaran su suka samu. Maryam Muhammad Jabeer 'ya ga Sheikh Muhammad Jabeer Muhammad kenan wanda shine babban malami a jigar Kano babu wanda ya kai shi ilimi, shine sunan da aka kira wacce ita ce head of student wato headgirl, kuma tinda ta fara makarantar tin daga JS 1 har SS 3 ba ai daliba kamar ta ba mai kwazo dan ita ce overall duk section tana fin kowa mark kuma duk gasar da zata shiga sai tayi nasara dan haka ba karamin ji makarantar keyi da ita ba. Wani Balaraben saurayi ne ya mike da sauri, lokacin da ya hango Maryam tana saukowa dan zuwa inda akai kiran ta. Na kusa dashi ne ya kamo hannun sa, juyowa yai ya kalle sa. Kai ya dan langwabar masa sannan yace "Haba Aliyu ka zauna mana." Maryam ya kara kalla sannan ya kuma kallon na kusa dashi sai kuma ya kalli gefen mata yaga Ammi na kallo sa murmushi ya sakar mata sannan ya koma ya zauna. Na kusa dashi da yace ya zauna wanda daga kallo zaka san dan uwa ne ga Maryam saboda yadda suke kama da ita. Shima kyakyawa ne dan na rasa wane jinsi ne shi balaraben ne shi ma ko kuwa bafulatani ne. Muje zuwa dai a sannu zamu san su waye su. "Aliyu kana rage wannan abun fa!" Juyowa yayi ya kalle shi sai kuma ya mai da kan sa kan Maryam dake karasawa inda aka kira ta cikin tafiyar ta mai daukar hankali wacce a nutse take yin ta kamar baza ta taka kasa ba, ba yanga take ba sam haka yanayin ta yake a ko da yaushe. "Daliba mu mai kwazo wacce ta kawo mana cigaba da nasara marar adadi a wannan makarantar, jiha da kasa baki daya, wanda ita taci gasar musabaka da akayi last month wanda ta samu kujerar makkah da umrah, shugaban kasa kuma ya bata kudi har 1 million haka nan a yanzu makarantar nan ta dauki nauyin karatun ta na gaba wanda aka bata zabi ta zabi duk kasar da take so dan karasa karatun ta, domin hakika irin wandan nan yaran ba karamin cigaba suke kawowa ba." Dai dai lokacin da Maryam ta karasa ta tsaya inda aka dauko award da gift da akai raping nasa mai girma shugaban kasa da kansa ya mika mata wannan kyautar sannan aka miko mata kyauta daga bangaren isilamiyya wanda aka ce Malam, Sheikh Muhammad Jabeer shi zai bata a matsayin sa na malami kuma uba ga Maryam wanda wajen ya dau kabbara wasu suna fadin "Ah ai dole ashe yar Malam ce za tayi abinda yafi haka ma." Wata tace "Ai fa ko maganin karatu ya bata." Dayar dake gefen su wacce take mahaifya ga aminiyar Maryam tai murmushi tace "Hmmm daga Allah ne dan Malam bai taba basu abu dan suyi kokari ba dai dai tin suna yara na basu tsari da kuna duk abinda ya dace wanda tin a can suka samu gogewa a kwakwalwar kuma ma banda abin ku, ya'ya nawa ne a ya'yan nasa basu da kokari su kuma ace me?" "Ai fa kuma haka ne. Amman dai yarinyar ta burgeni kuma karama da ita." "Shekarar ta sha bakwai watan azumi zata shiga sha takwas" "Allah sarki Masha Allah." Ta fada ta mai da ido kan Maryam wacce hawaye ke zubo mata a idon ta. Lordspeaker aka bata dan tayi bayanin karshe a makarantar, wanda ta amsa tayi kasa da kan ta. Hawaye na zubo mata. Aliyu dake zaune ne ya fara kokarin mikewa da sauri na kusa dashi ya rike shi juyowa yayi yace "Menene haka Alkasim?" "Ina zaka je?" "Bakaga kuka take ba!" Ya fada kamar shima zai kukan. "Haba Aliyu wai meyasa kake haka yanzu can wajen ta zakaje ko......" Ai bai barshi ya karasa ba ya kwace hannun sa ya mike da sauri ya nufi stage din wanda security ke tsaye a wajen yana zuwa suka bashi hanya ya wuce. Handkerchief ya zaro a aljihun sa ya karasa ya amshi lordspeaker ya mika mata, dagowa tayi ta kalle shi ya sakar mata murmushi cikin muryar sa mai dadin sauraro yace "Goge mata hawayen ki *Matar Haydar* " Amsa tayi ta goge hawayen nata wamda kamshin turaren Aliyu ke jikinsa, abin da ya kara kwantar mata da hankali kenan, sai da ta share hawayen sannan ta dago, murmushi yake sakar mata, dan haka itama murmushin ta sakar masa. "Ma'ul ayn!" Ya kira sunan da yake kiran ta dashi dagowa tayi yace "Nasan kukan farin ciki ne but please kiyi komai kamar yadda aka tsara ina tare dake (am with you) kinji!" Kan ta tayi kasa dashi, tace "Stay by my side please (Ka tsaya a gefe na dan Allah) My Hayyat!" Kai ya gyada mata sannan ya mika mata lordspeaker ya koma bayan ta ya tsaya kamar bodyguard din ta. Rukayya da Aisha dake wajen zaman su wanda suke kawaye ga Maryam ne suka sakarwa juna murmushi. Rukayya tace "Oh Yaa Haiydar da Maryam ko?" Dariya Aisha tayi tace "Allah har so nake ayi bikin nan naje naga irin soyayyar da za a sha kina gani dai ko kwana biyu bayayi bai zo ya ganta ba." "Kinsan ni ba wannan ke dauren kai a soyayyar su ba sai ko ciwo daya yayi sai daya yayi." "Shakuwar tasu ce tayi yawa. Allah dai ya kaimu wani satin mu mika masa matar sa mu huta." "Sai su cinye kan su, mu huta ba. Ma huta da kullum yace *Matar Haiydar, ko Ma'ul Ayn" Sukai dariya. Aisha tace "Kin manta da *My din My* kenan" "Sunan nasu ne ba adadi but wanda suka fada din kenan *Matar Haiydar* sunan yana min dadi." "Ko *My din My* " Sukai murmushi. Maryam kuwa jin sa a bayan ta sai ya kara mata kwarin gwiwa tayi gyaran muryar sannan ta bude baki cikin muryar ta mai zaki da dadi tace "Assalamu alaikum!" Wanda sautin muryar ta mai dadi da zaki ya karade duk wajen ya janyo hankalin kowa ya dawo kanta, akai shirubkanarbruwa ya cinye su, sai ido da suka zuba mata, "Sunana Maryam Muhammad Jabeer wacce nake matsayin Head student ta wannan makarantar gaba daya. Ina Mai farin ciki da Allah Ya hadamu a wannann rana Mai Albarka wacce take cike da abubuwa da dama, ranar da ta kasance ranar farin ciki, Ina miqa godiya ta ga Allah (S.W.T) da ya hada mu a wannan rana, Ina miqa gaisuwata ga manyan ba'ki na musamman da malaman mu da sukayi tsayin daka dan ganin cewa burin mu ya cika, suka bada gudunmuwa dari bisa dari, Ina kuma mi'ka gaisuwata ga Iyaye na Yan uwa na, Yaye na, da suka tsaya min har na kawo wannan matakin da aljihun su da jikin su da addu'ar su, sannan ina mika gaisuwa da fatan alheri ga duk member ta makarantar nan class mate dina da duk suka ban goyan baya wajen ganin komai ya tafiyu dai dai dan ba wayo na bane ko da bara ta bace." Ta dan tsagaita taja numfashi sannan ta cigaba da magana wanda in tana maganar kamar baturiyya dan yadda take fitar da komai dai dai a tsare cikin nutsuwa da iyawa "Wannan makarantar tana daya daga cikin makarantun da wuya a same su amman cikin hukuncin Allah yasa na zamo daliba a ciki wanda wasu na neman gurbin da kudin su ma basu samu ba. Gaskiya fadin irin karuwar da muka samu a wannan makarantar ba karama bace, domin kuwa ko ba komai mun ilmantu kuma mun fa'idantu sosai, ko a yau na mutu na cika buri na, na zama hafiza na haddace Alku'ani wanda shine babban buri na a duniya, wanda ya tsaya maka wajen samuwar cikar burin ka kuwa babban masoyi ne a gareka wanda suka hada da malamai na, iyaye na, My Hayyat duk ina godiya dan ban da abinda zan biya ku sai addu'a Allah ya saka muku da gidan aljanna ya bani ikon amfani da abinda na sama" Hawaye ne ya zubo mata ta sa handkerchief ta dan share sannan tace "Nayi matukar farin ciki da har bansan da wane kalma zan mika godiya ta ba, da nuna farin ciki na ba zan bawa yan uwa na shawara akan mu dage mu samu mu cika burin mu da na iyayen mu dan duk wanda iyayen suka kawo shi wannan makarantar da kudin ya kusa 1M ya kamata ya tsaya ya basu farin ciki ya bawa kan sa da malaman sa farin ciki a karshe ina muku fatan alheri." Juyawa tayi ta fuskanci Malam Muhammad Jabeer ta dan duka tace "Fatan Alheri a gareka, " Sannan ta kalli Iyaye mata tayi musu haka ta juya ga Director da malamai tayi musu haka sannan tace "Nagode kwarai da karamcin da muka samu Ina fatan yadda muka hadu lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya. Maryam Muhammad Jabeer Bisalam!" Tafi aka dauka raf raf. Har ta bada lordspeaker zata juya Malamin yace "Maryam kan ki zauna ina son ki jan hankali akan ilimi da mahimmancin sa ga mata." Juyowa tayi ta amsa lordspeaker sannan ta kara sallama wanda yasa aka karayin tsit sannan tace "Alhamdulillah duk wanda yake nan nasan yasan mahimmancin ilimi amman nasan maganar da nake ba iya nan zata tsaya ba kila a wata kasa can ma wasu su gani ko anan kasar to ni fata na gareku ko da an gani ayi amfani da abinda zan fada. Ilimi shine haske da yake haskaka maka hanyar da kake zagaya duniya baki daya. Hakika daga lokacin da baka da ilimi ka zama makaho, kurma, bebe ku fadan tayaya mutum zai ji dadin rayuwa a haka to ilimi zai kore maka duk wannan abun. Masana na cewa in ka ilimantar da namiji ka ilimantar da mutun daya amman in mace ka ilimantar tamkar ka ilimantar da duniya ne. Ina masu cewa ilimin mace haram ne hakika ba haka bane sabida a duk lokacin da matar ka take da ilimi ko a mu'amala zamantakewar aure zaka ga canji da abubuwa dan Allah maza ku gwada in kana da mata guda mara ilimi auro mai ilimi wallahi hatta matar ka ta gida zata koyi abu a wajen ta shin ta samu ta kawar mata da wannan jahilcin ko kuwa haka nan ko ta tarbiyyar ya'ya in ka hada mai ilimi da marar shi zaka ga banbanci ta tarbiyya kai har kula da kai kan ka. Ba wai kin bawa mace ilimin zamani kawai ba har na addini ba wai in ka bata aka ce tai aiki ba babban aikin ta zaka ganshi a gida dan wallahi daga ranar da ka dauke ta ka kai ta, ta samu ilimi kai da kanka zaka gane banbanci. Babban misalin da zan baku shine akwai wata mata wacce tana zaune da mijin ta da yaran ta cikin rufin asiri mijin ta yafi karfin komai ya dauke mata komai na rayuwa wanda ya bata ilimi amman yace aiki sam ba za tayi ba haka ta zauna dashi lokaci daya Allah ya dauki rayuwar sa, bayan ya rasu ta koma gidan yar ta suka cigaba da rike ta da ya'yan ta bata da damuwar kowa, wanda kowa ke taimaka mata yaran in sallah tazo sai su samu kaya sama da kala goma, shekara daya a tsakani da mutuwar mijin ta mijin yar ta ya rasu, daga lokacin suna samun rufin asiri itama yayar bayan shekara ta rasu rayuwa ta fara basu kashi wanda a lokacin matar nan ta dauki takardun ta, ta koma ta nemi aiki ta samu dashi ta ke rike yaran ta da ya'yan yayar tata. Shin yanzu kunga amfanin ilimin nata ko? Da bata da ilimin wane hali kuke zata zata fada zata iya shiga ko wanne hali ko karuwanci, ko bara ko aikin wahala da karfi shin da wannan ba gwara aikin da zaka ci halak ba. Bance kowa zai fada wannan rayuwar ba amman kana hango kan ka a cikin ta. Bance dole sai aiki ba kina gida zaki na dan yiwa yara lesson da ilimin nan zaki operating business ta online da abubuwa da dama. Hakika amfanin ilimin mata yana da adadi bashi da iyaka dan haka iyaye maza mu daure muna samawa yaran mu ilimi domin in da ilimi barna zata ragu sosai wani yana fadawa barna ko halaka na rashin ilimi dan haka mu daure mu ilimantar da ya'ya mata. Nagode." Raf raf raf raf haka wajen ya dauki sowar tafi kowa da abinda yake fada akan Maryam domin yarinya karama mai hankali da nustuwa da kalamai kamar na manya. Lordspeaker ta bayar ta juyo ta kalli Aliyu da ya sakar mata murmushi yana bin ta da wani kallo mai ma'anoni wanda duk ya sakar mata da jiki. Dan hararar sa tayi ta gefen ido tace "My Hayyat please ka bari!" Ta fada tana yin gaba bin bayan ta yayi yace "Na bar me?" Juyowa tayi ta tsare shi da idanun ta da sauri ya runtse idon sa murmushi ta saki shi kuwa lips din sa ya dan datse da hakori yace "Zan kamaki ne ai nace ki dainai min irin wannan kallon kina zauta ni." "Ni kai min!" Kwafa yayi ya juya ya tafi. Murmushi tayi ta juya itama ta koma wajen zaman ta haka aka cigaba da bada kyauta ana basu damar yin bayanai da godiya. Takeaway aka fara rabawa iyayen yara da daliban wanda hudu saura aka tashi taro duk iyayen maza aka tafi sallah. Matan ma masallaci akaje akai sallah. 4:15pm hall din ya kacame an saka Kida yan matan sai rawa suke. Maryam na fitowa daga hostel junior din su suka biyo ta da gift din da aka bata wanda ba wanda ya samu kyauta kamar nata abubuwa masu yawa. Haka a cikin JS1 to 3 and SS 1 to 2 duk kowa akwai abunda zai bata kowa da sunan sa da class din ta dan haka kaya ne masu yawa ta hado su. Yaa Alkasim da Biba mai aikin su ne suka amsa suka kai mota sannan suka dauko mata bag din da zata raba wanda a jikin bag din an saka hoton ta tayi kyau tana murnushi kamar zatai magana a fili. A cikin jakar memo da pen da handkerchief da handpan da lemo da ruwa da snacks aka wasu an saka musu agogo wasu shoe wani hijab duk dai a cikin jakar. Special hall ta nufa inda tana shiga ta hango Ammin ta da sauri wanda in ka kalla zaka ce bama tafiyar take so ba ta karasa ta fada jikin Ammi tana fadin "Ammi nah!" Rumgumme ta Ammi tayi tana shafa bayan ta tace "Auta ta an girma fa. Allah yasa ki amfani karatun naki" Yaya Abdullahi wanda shi take bi ne ya karaso yana fadin "Wannan magen ce ashe." Ammi ta kalla tace "Wai Ammi nice mage." "Kyale shi kishi yake " "Ammi akan me zan kishi bayan daga next week zata bar gidan mu gaba daya ta barmin ke sai dai tazo da ziyara fa." Hawaye ne ya hau zubo mata ta matse Ammi a jikin ta tana fadin "Wai Ammi haka?" Yaa Fadima da Yaa Aliyu ne da Ummah mahaifiyar sa suka karaso leka fuskar Maryam yayi hankali a tashe yace "Kuka kuma wa ya taba min ke?" "Ba Yaa Abdullah bane wai daga next week zan bar Ammi "Waya fada masa a mu kullum muna tare da Ammi ko an mana auren ko?" Kai ta gyada masa dai dai karasowar Yaa Alkasim da Biba da mai daukar musu picture. Dagowa tayi a jikin Ammi ta juyo tana ganin Ummah ta fada jikin ta tana fadin "Ummah nah!" "Na'am Daughter na congratulations!" "Thanks Ummah na." Kan ta ta dafa tace "Muna alfahari dake " Murmushi Maryam tace "Nima ina alfahari daku Ummah na." Mai picture ya dauke su, nan ya fara daukar su. Can ta fara wage wage Yaa Aliyu dake gefen ta ya matso yace "Menene?" "Ina Abbi?" "Suna nan waje " "My Hayyat muje ai mana picture nasan Abbi yanzu sai yace tafiya zai yi." Tayi gaba yabi bayan ta, mai hoto yabi bayan su. A can parking space suka same su shida Gwamna da Shugaban kasa da Sarki. Suna tahowa Security suka tsare su saboda Shugaban kasa. Dagowa yayi ya hango su yace "Ku kyale su." Karasawa sukai. Ta durkusa har kasa ta gaisu Amsawa sukai Shugaban kasa ya kamo hannun ta yana fadin "Allah miki albarka." "Amin!" Suka amsa Abbi ta kalla ta dan karya wuya tare da shagwabe fuska tace "Abbi tafiya ko?" "Eh Maryam tafiya zamuyi." "Ayyah Abbi ba ai mana hoton tarihi ba fa." "To azo ai mana." Ya fada yana kiran Yaa Alkasim yasa ya dauko masa kati a jaka a can mota ya juya ya tafi. Nan akai musu sannan aikai musu har da shuganban kasa da gwamna da Sarki. Sannan Yaa Aliyu da ita suka saka Abbi a tsakiya akayi musu. Ana gamawa Yaa Alkasim ya dawo ya mika masa amsa yayi ya mikawa Mr president yace "Katin daurin auren yar ku sati mai zuwa!" "Wacce kenan!" Maryam ya nuna musu wacce tai sauri ta sunne kai sannan ya nuna Aliyu yace "Ga angon." "Masha Allah! Allah sanya alheri insha Allahu zan zo da izinin Allah." "Allah ya yadda!" Ya bawa Gwamna da Sarki nasu dukka sannan su Maryam suka koma ciki nan taje ta dinga raba bags din ga classmate dinta da junior din ta kowa ta bawa sai an musu pictures haka suka dinga yi suna tare ita da Aisha da Rukayya duk inda zasu je. Yaa Aliyu kuwa idon sa da hankalin sa duk na kan ta. Duk motsin ta ji yaje kamar ya dauke mata dan kar ta gaji. Haka akai ta taro wanda duk dalibai da malamai dai da ta bawa bags din kuma har ragowa sukai.``` *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 14 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin*  Karfe shida duk sun fito suna parking space sun rumgume juna ita da Aisha da Rukayya. Sai kuka suke. Yaa Aliyu ne ya karasa yace "Ma'ul Ayn menene na kukan?" Kukan take bayan ta sake su. Ya kalle ta cikin so da kulawa yace "Amman kinsan bana son kukan ki ko?" Kai ta gyada yace "To stop it in bakya so nima na fara!" Hannu tasa ta fara goge hawayen duk da tana gogewa yana kara zubowa ya sa handkerchief yana goge mata sai da ta daina kukan yace "To ku menene na kuka naga next week kuna tare fa." "Haka ne Yaa Haidar, Besty yaushe zamuje rabon?" "Rabon me?" Yaa Aliyu ya tambaya. "Kati man." "No My Queen ba rabon da zatai zan kawo muku kuje ku raba ku bar min Mata ta huta yadda take kwana bata bacci dis week ramuwar bacci zatayi ko Baby?" Kai ta gyada. Aisha tace "Mu kuma kada muyi?" "No ku da ita da bambanci ita aure zatayi gwara ta huta kan mu tare ko? Ku kuwa kullum zakuyi ta baccin ku, ku yini ku kwana kuna yi." Yaa Alkasim ne ya karaso yace "Please Aliyu ka barta suyi sallama kafiya jaraba kai kam." "What?" Ya fada yana kamo hannun sa sukai can gefe ya murda hannun sa yace "Ai Matata ce ina ruwan ka." "Za dai ta zama matar naka ka bari in ta zama sai ka takura mata, wallahi irin kune ke sa mace ta rame dan jarabar ku." A can kuwa Rukky ce tace "Allah Besty kinji dadi kin samu mai son ki." Murmushi tayi ta kalli gefen su Yaa Haidar sai ta saki murmushi tace "Alhamdulillah! Kuma zaku samu masu son ku da yaddar Allah." Aisha tace "Allah yasa. Amman fa naga Yayan namu zai yi naci Besty!" Rukayya ce tace "Itama ai da alama." "Kuji sharri mu ba ruwan mu." "Ku din kada ki manta ko ya yazo sai kin canja ki ta wani lumshe idanu kamar....." Duka ta kai mata tace "Iyee kace ido kika sa min." "Hmmm ni ai last dawowar da yayi da ita nan da taje ganin likita nasha mamaki naga love wallahi kamar ya dauke ta haka ya dinga yi. Gaskiya zan zo ina koyar course na soyayya." "Ji ku," Ta fada tana nuna su "Ku wa yasan ya kuke dan dai ni kullum yana zuwa shiyasa kuka saka mana ido." "Hmmm Allah Maryam ki godewa Allah Yaa Haidar na son ki kinyi dace sai dai muce Allah tabbatar da alheri. *Matar Haiydar* in the next seven days, Allah nuna mana." "Amin. Allah ya kaimu next week musha shagali mu mika ki dakin Yaa Haidar sai ku cinye kan ku." "Ai kam ko kadan bazamu rage kan mu ba." Maryam ta fada "Ku ba?" Rukayya ta fada. Kanwar Aisha ce ta karaso tace "Yaya Aisha wai kizo mu tafi" "Toh!" Ta fada tana fadin "Sister bye!" Har ta juya Maryam tace "Larabar zaki taho ko?" "Insha Allah sai munyi waya anjima." "Ok muje nayiwa su Mum sallama." Suka karasa sukai musu sallama sannan sukaje wajen Momy Rukayya sukai sallama ta juyo ta dawo kowa ya shiga mota. Motar Yaa Alkasim suka shiga, shi da Yaa Fadima a gaba, Ita da Yaa Aliyu a baya. Su Ammi da Ummah da sauran yayyane nata a mota daya masu aikin su a dayar motar. Kai ta jingina a jikin kujera tace "My Hayyat!" "Na'am Ma'ul Ayn!" "Na gaji!" "Na sani Bae taho in miki tausa!" Kallon sa tayi ta make kafada murmushi yayi ya matso da kan sa wajen kunnen ta yai mata rada, da sauri ta matsa tana rufe fuskar ta da hannunta dan ya bata kunya sosai. Shima murmushin yayi ya dan cije lips dinsa na kasa yace "Kika shigo hannu na ko?" Kanta, ta kwantar a jikin kujera tana fadin "Ni dai ka bari." Ta fada tana lumshe ido, kallon ta yake yana murmushi wanda kan suje gida har tayi bacci suna zuwa gida Yaa Alkasim da Yaya Fadima suka fita. Kallon ta ya tsaya yi Ido ya kura mata sai yai saurin dauke idon sa dan wani abu da yaji yana taso masa. "Ma'ul Ayn!" Ya kira sunan ta. Kara gyara kwanciyya tayi. Yace " *Matar Haiydar!* " "My Hayyat Bayana, kuguna kamar zai balle nagaji matsa mi...." Sai kuma tai sauri ta bude idon ta. Aliyu kuwa ido ya lumshe dan a yadda tai maganar cikin magagin bacci muryarta, ta saukar masa da wani irin kasala. Janyo ta yayi jikin sa yace " *Matar Haiydar* " "Uhmm!" Ta fada tana kara kwantowa jikin sa. Bakin sa ya kai dai dai kunnen ta ya farai mata rada wanda hakan yasa duk jikin ta kara yin sanyi dan yadda yake mata maganar ga numfashin sa dake sauka a cikin kunnen ta. Fuskarta, ta kife a kirjin sa tana jujjuya kan ta. Murmushin da baya taba barin fuskar sa ya saki sannan yace "Bae kar mu makara sallah fa 6:30pm gashi kinsa sai nayi wanka." "Wankan me?" Ido daya ya kanne mata yace "Kema kin sani in har ina tare dake sai naji...." Da sauri ta mike a jikin sa tana rufe fuskarta. Da hannu daya dayan hannun ta daura akan bakin sa. Hannun ta ya zame, Kansa ya matso dashi kusa da kunnen sa yace "Wai ni kike jin kunya?" Kai ta gyada yace "Oh really?" Hannu ta sa zata bude kofa yai sauri ya kamo hannun nata, yace "Dan lokacin sallah ya kusa ne amman da sai..." Ya matsar da bakin sa kan nata ya fara tsotsar lips din nata kamar ya samu alawa. Kokarin janyewa take yace "Ba kyau fa." Barin shi tayi sai da yai kissing nata na kusan minti biyar sannan ya sake ta, yana sakin ta tai sauri ta bude mota ta fice a guje. Katon compound ne wanda a kalla zai dauki motoci sama da ashirin gefe daya babban masallacin Malam Muhammad Jabeer ne wanda yake limanci sannan duk bayan sallah magariba yake karatu a wajen. Daya gefen kuma bangaren gidan sa ne wanda yake katon gaske bangaren maza daban sai dayan bangaren da yake na ya'yan sa ne masu aure. A guje ta shiga cikin gida, da kallo Yaa Alkasim ya bita wanda ya fito daga cikin gida. Yaa Aliyu ne ya fito a motar kallon sa Alkasim ya tsaya yi. Karasowa yayi kusa dashi yace "Menene ne?" "Kafini sani." "Ko?" "Kaga ana kira muje masallaci." "Sai nayi wanka." "Wanka kuma?" "Yes!" Ya fada yana yin cikin gidan. Murmushi Alkasim yayi yace "Abun ne ya motsa ni wallahi da Abbi zai yadda da ya daura auren before next week!" "Ai ni tarewa kawai nake bukata." Ya fada yana yin ciki. Dariya Alkasim yayi yace "Aliyu kenan." Yaa Muhammad ne ya fito yace "Me ka tsaya yi?" Kai ya shafa yace "Ba komai!" Suka wuce masallaci. Yana shiga ya tube ya shiga yai wanka ya fito ya zura jallabiya kawai ya nufi masallacin. Raka'a biyu ya samu sannan suka zauna daukar karatu sai da sukai isha'i suka koma cikin gida. Maryam na shiga bata tsaya ko ina ba sai dakin ta. Falo ne da bedroom da toilet da wani dan store. Tana shiga ta lumshe ido dan kamshin da yai mata sallama. Komai tsaf kamar tana nan dan duk sati ake gyarawa bama yanzu da aka san za ta dawo. Bedroom ta shige kawai ta wuce bandaki a can ta cire kaya tayi wanka ta fita daure da towel doguwar riga ta saka jin an tada sallah ta hau kan sallaya ta tada sallah tana idarwa ta dauko alkur'ani ta fara karantawa kan a yi isha'i. Ana tayar wa ta mike ta tada sallah. Bayan ta idar tayi shafa'i da wuturi sannan ta mike ba tare da ta cire hijab din ta ba ta nufo Babban falon su. Babban falo ta fito inda ta Fara jiyo hayaniyar yan gidan su. Fuska dauke da murmushi ta yi sallama duk a tare suka amsa. Yaa Muhammad, Yaa Ibrahim, da Yaa Abdullahi da matan su da yaran su duk da suka dawo anan suka zauna sai Yaya Fadima, Yaya Ummulkusum a cikin Yan gidan mutum biyu ne babu daga Yaya Zainab sai Yaa Alkasim da basu shigo ba. Yaran ne duk suka taho wajen ta a guje durkusawa tayi ta bude musu hannayen ta tana fadin "My sweet family I miss you!" Dai dai lokacin da Yaa Alkasim da Yaa Aliyu suka shigo dakin bakin su dauke da sallama, Amsawa sukai gaba daya Yaa Aliyu ya shigo Yaa Alkasim na biye dashi a baya, idon sa na kan Maryam dake rike da 'yar gidan Yaya Fadima, Iham karasawa yayi ya zauna a kasa ya dan tabo ta, ta juyo suka sakarwa junan su murmushi ya dago suka hada ido da Yaya Ummulkusum kai yai kasa dashi, Yaya Ummulkusum tace "Aliyu da Amaryar sa." "Amaren wani satin!" Yaya Fadima ta fada. Matar Yaa Muhammad Rabi'a tace "Iyayen soyayya ba ma huta ba." "Ku huta da me Anty Rabi?" Aliyu ya fada yana murmushi "In kun tafi gidan ku mana." "Ai Ma'ul Ayn tace zata fadawa Abbi a bamu part muma ko?" Ya fada Yana cilla wa Maryam tambayar. Kai ta gyada tana shafa kan Iham tace "Eh mana mu anan zamu zauna tinda kowa ma Yana nan." Yaya Fadima tace "Tab wallahi Aliyu zaka sha fama har yanzu Maryam fa bata girma ba." Da sauri ta dago ta kalli Yaa Aliyu tace "Wai haka My Hayyat?" Hannun ta ya kamo ya dan murza yace "Kyalle Fadima, ai kowa yasan Matata ta girma." Ya fada yana yin kasa da murya yace "Ko ba haka ba sai ma mun haifo Baby mai kama da ke ko?" Kasa tayi da Kai tana girgiza Kai yace "Me? Bakya so?" "Ina so amman ka bari kana ganin su Yaa Muhammad fa." "Me nayi naga matata ce kuma bayan ba abinda nayi ma." Ammi ce ta fito tana fadin "Kunga ki tashi kuje kuci abinci kan mazan ku su zo su tsaya jira." "Ammi Yaya Fadima kwana zatai." Maryam ta fada. Ammi ta kalle ta tace "Saboda me?" Fuska ta shagwabe tace "Sai bayan biki zata koma." "Ba anan ba tayi maza ma ta kira sa in lokacin bikin yazo tazo tai kwana daya ma ya isa ke in ta tawa ne ma tai zaman ta a gidan ta tana zuwa tana komawa." "Kai Ammi bikin autar guda." "Sai ta bar mijin ta. Tasan Abbin Kuma ba bari zai ba tai maza ta kira sa ko su Aliyu ku kai ta gida." "An gama Ammi daman ni ban ga amfanin tahowa ta kwana ba " "Kai Yaa Haidar kai da zaka bata baki." Fadima ta fada. Fuska ya dan hade yace "Ni yaron ki ne ko? Tashi kuje kuci mu kai ki gida." Yaya Ummulkusum ce ta mike tayi dining ta zubawa yaran sannan ta zubo musu mata a plate daya mazan kowa ya zuba. Bayan sun gama ci suka kintsa. Sukaje wajen Abbi sukai masa sallama, nan ya karai musu nasiha sannan ya saka musu albarka suka tafi Yaya Fadima ta shigo ta samu Yaa Aliyu da Maryam da Ammi. "To ka taso ka kai ni!" Ta fada tana kallon Aliyu. Ammi ya kalla yace "Ammi bari mu kai ta gida." Ya fada yana kallon Maryam. Da sauri ta mike tace "Muje to." Suka fita ya budewa Maryam gaba ta shiga, sannan ta zagaya ya shiga. Yaya Fadima da Iham suka shiga baya tana fadin "Yaa Aliyu nifa yayar ka ce." "Tayaya?" "Saboda Maryam mana." "Lallai yarinyar nan to ita ce zata zama Antyn ki." Murmushi Maryam tayi a haka suka karasa gida ta dake jan bulo. Har ciki suka rakata sannan suka mata sallama suka tafi. Shi ya kara bude mata mota ta shiga tana fadin "My Hayyat kana sangartani da yawa fa." "To Baby in ban sangartaki ba wa zan sangarta." Ya fada yana rufe motar. Kai ta jingina da jikin kujera tana mai lumshe idon ta. Shiga yayi ya kalle ta sannan ya tada motar. Hannun ta ya kamo wanda hakan yasa ta bude idon ta. Murmushi ya sakar Mata yace "Ina kaunar ki Ma"ul Ayn! *Matar Haiydar* " Hannunta take son janyewa amman yaki ta dan kalle shi tace "Ba kyau fa My Hayyat!" "Me din? A da kenan a yanzu fa kin zama tawa sauran kwana nawa ne mu kasance tare?" Murmushi tayi ta jinginar da kan ta a kujera tare da lumshe Ido, tace "Allah kaimu!" "Amin ni wallahi ji nake kamar lokacin bai gudu. Allah ya nunan lokacin nan yana daya daga cikin lokacin da nake da burin gani a rayuwa ta. Ban san irin son da nake miki ba, kece kadai rayuwa ta Habibty." Ido ta kara lumshe wa tana murmushi, parking yayi wanda hakan yasa ta bude ido ta juya taga ba gida suka zo ba da sauri ta kalle shi yace "Me zan siyo miki?" "My Hayyat ni bana jin yunwa fa muje gida kawai." "No har ice cream din?" Fuska ta rufe da hannun ta. Kissing hannun yayi sannan ya fita a motar ta bishi da kallo. Har ya bacewa ganin ta sannan ta dawo da kan ta, ta jingina a jikin kujera tare da lumshe idon ta. Wani bacci take ji wanda ya zamar mata jiki a ko da yaushe da ta kwanta sai bacci anya kuwa ba sleeping sickness take ba. Ta fada tana gyara kwanciyyar ta a jikin kujerar. Kan ya dawo har baccin ya dauke ta. Ledar ya ajiye a baya sannan ya gyara mata zaman kujerar yadda zataji dadin kwanciyya motar ya tayar suka nufi gida a lokacin tara ta gota. Yana parking ya juyo yaga tana bacci murmushi ya saki ya shafa kan sa dake cike da suma mai kyau da taushi. "Ina ma su ban Matata na huta." Ya sa hannu ya daura akan goshin ta, wanda ta bude idon ta a hankali, murmushi ya sakar mata yace "Mun iso gida fa." Gidan ta kallah ta fara kokarin mikewa zaune ta daura hannun ta a baki tare da salati ta fara hamma. Kofa ta bude tace "Dr Ina jin fa sai ka duba ni kwana biyu na zama kamar kasa nayi ta bacci duk inda na samu waje." Fita yayi yana murmushi yace "Kema kinsan gajiya ce da karatun dare da kuka dinga." Hamma ta kuma yi tace "Bari naje na kwanta sai da safe!" Ledar ya dauko ya bi bayan ta. Ba kowa a babban falo dan haka ta kalle shi tace "Kaga duk sun kwanta kenan." Ledar ya mika mata dai dai fitowar Ammi dan rufe kofar babban falo, ganin su tace "Sai yanzu kuka dawo?" "Eh Ammi!" Ta amshi ledar tace "Nagode!" Ya juya ya fita Ammi ta rufe kofa Maryam ta wuce dakin ta. Hijab din jikinta, ta cire sannan ta shiga tai alwala tazo ta canja kaya zuwa na bacci ta dawo ta dauki ice cream din ta saka a firij ta dauki roba daya ta fara sha. Dakin Alkasim ya tafi ya same shi kwance yana waya. Baki ya tabe yace "Tab wai nan soyayya kuke." Yai dariya ya ajiye wayar sa ya nufi bandaki ya watsa ruwa ya fito ya saka kayan bacci kan gadon ya hau yana jawo wayar sa. Number Ahmad ya fara nema ta can kasar da yake yana bugawa ya daga yace "Ango Ango! *Mijin Maryam* " Murmushi yayi yace "Wannan haka yake Angon Maryama." "To tana Ina?" "Yanzu muka rabu yaushe zaka dawo ne?" "Ina son na dawo kan bikin ku Amman ban sani ba ko zan samu dama." "Ahmad kada kace haka man." Dariya yayi yace "Kada ka manta dani fa akai wancan wannan shagali ne fa kawai." "Ni dai kazo." Alkasim da ya gama waya ne ya zare wayar yana fadin "Dan Allah kazo Ahmad, kaga yadda Aliyu ya koma marar kunya matar shi kawai yake so ayi a shafa ya dauke. Kazo muyi masa wa'azi dan naga kan sa na rawa da yawa." Wayar sa ya zare ya kashe yana fadin "Ba da kudin waya ta ba, matata zan kira. Kira da wayar ka." Ya mike ya fita, layin ta ya fara nema. Har ta fara bacci taji karar wayar ta hannu ta sa ta janyo dan tasan wa yake kira daga jin karar tasan Yaa Aliyu ne, ba tare da ta duba ba ta kai kunnen ta. Tace "Assalamu alaikum!" Tai maganar cikin muryar bacci. "Wa'alaikum salam. My har kin kwanta ne?" "Na fara bacci My, bana fada maka ba kwana biyu nai ta bacci ni bana so ka ban magani." Kan sa ya shafa yana murmushi yace "To shikenan, ki kwanta zan tashe ki, anjima ki sallah." Hamma tayi tana mika hade da salati tace "Sai da safe My!" "Allah bamu alheri I miss you." Ya kashe wayar ya koma daki ya samu Ahmad da Alkasim na waya duk akan bikin nasu ne. *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 15 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Washe gari, tin asuba da ta tashi bata koma ba saboda bata sababa dan ba kyau ma. Zaune take akan sallaya tana azkhar, Ash kalar hijab ne a jikin ta wanda yai mata kyau ya fito da aihin kyan ta dan ba karamin kyau hijab yake mata ba. wayar ta dake kan madubi ce tayi kara, karasa azkhar tayi wanda kan ta dauko ta katse, wani kiran ne ya kara shigowa. Hannu ta sa ta dauko ta duba sunan taga an saka *My* Ido ta lumshe ta danna received, ta kai kunnen ta tana fadin "Assalamu alaikum!" Aliyu dake zaune a kan three sitter sanye da wando three quarters sai riga marar nauyi a jikin sa. Gashin kan sa ya kara bakikirin sai sheki yake, jin sautin muryar ta yasa ya lumshe idon sa yana mai shafa sumar kan sa hadi da sakin murmushi, a hankali yace "Wa'alaikum salam My princess! Da fatan kin tashi cikin koshin lafiya?" "Alhandulillah Yaya na, kaifa ya ka tashi ya daren ka?" Numfashi ya sauke yace "Yadda yake kullum My love, kullum dake nake kwana dake nake tashi kullum in ta mafarkin ki, Baby ina kewar ki sosai da sosai fa." "Nima haka Yaya nah!" "A'ah fa Baby bai kai nawa ba, Baby ni dumin jikin ki ma kawai nake so na dan ji a nawa." "Yaya nahhh!" Taja sunan wanda yasa abinda yake ji ya kara daduwa duk jikin sa yai sanyi. Kasa magana yayi sai lasar leben sa na kasa tare da lumshe manyan idon sa. "My Hayyattt!" "Uhmm!" Kawai ya iya fada. Murmushi tayi ta mike ta koma kan gado tace "Ya dai?" Murya ya shagwabe Kamar zai kuka yace "Ba kece ba!" "Me nayi My?" "Uhmm uhmm Baby I need you." Murmushi tayi tace "Haba Miji nah kwana nawa ya rage yau friday kaga remain one week a daura na kasance da kai sai abinda kake so zan maka." "Why not now Baby!" "Please Yaya nah kayi hakuri seven days ne." "Wallahi gani nake Kamar seven years ne." Murmushi tayi, yace "Oh dariya ma kike min ko?" "No no kawai dai." "Shikenan ba ruwa na dake!" Ya fada a shagwabe sannan ya kashe wayar. Dariya tayi ta fara neman layin nasa, kin dauka yayi ta kuma kira sai da ta kira sau uku sannan ya dauka, tana jin ya dauka ta saki kukan wasa, ai nan da nan hankalin sa ya tashi, ya hau tambayar "Menene Baby? Meya faru? Dan Allah ki daina kukan nan, fada min menene?" Kukan ta kuma saki tana fadin "Ba kai bane!" "Ni kuna Baby me nayi?" "Fushi kake yi dani!" "Ni na isa, ba zan taba fushi da Matata ba, please stop crying kinji da wasa nake fa na kashe ne dan ki dan kwanta ki huta kinga safiyya tayi ko?" Dariya tayi tace "I love you My! Sai anjima!" Ta fada ta kashe wayar daga shi har ita murmushi suke wanda su kadai suka san ma'anar sa. Kwanciyya yayi yana karatun Alkur'ani ita kuma mikewa tayi ta nufi kitchen. Ammi ta gani da me taya ta aiki, har kasa ta durkusa tana gaishe da Ammi ta amsa tana fadin "Har kin tashi ko baki koma ba?" Kai ta gyada mata ta gaishe da Baba Ramma Mai aikin su ta amsa tana kara taya ta murnar kammala karatu ta amsa tana godiya. Baba Ramma tace "Kinga Maryam je ki kwanta nasan tinda kuka fara jarabawa ba wani baccin kirki kikai ba ai Ina jin kin ma daina shiga kitchen sai na gidan ki." Kasa tayi da kanta, Baba Ramma tace "Jeki abinki ki huta kinji!" Kai ta gyada ta juya ta fita, gidan sai kamshi yake dan an share anyi mopping an saka turaren wuta sai kamshi. Ido ta lumshe ta nufi bangaren Abbi. Shima ko Ina fes sai kamshi ke tashi a dakin da sallama ta shiga falon nasa yana ciki inda yake zama yayi ibada. Amsawa yayi ya bata izinin shigowa sannan ya dago yana kallon kofar dakin. Shiga tayi ta karasa ta zauna a gefen sa. Murmushi ya saki yana fadin "Mamanah!" "Na'am Abbi barka da asuba!" "Barka ka dai! Da fatan kin tashi lafiya?" "Alhandulillah!" "Masha Allah, Allah yayi albarka yayi jagora ya bada sakamako mai kyau. Hakika Ina alfahari dake uwata duk cikin ya'ya na kece kika fita daban ta fannin son karatu sosai bama na addini da kuma dagewa, daga ke sai Aliyu shi da bama 'dana ba amman ina zaton shi zai gajen a wannan fanin nan gaba Allah muku albarka!' "Amin Abbi!" "A cikin waccan satin Alkasim da Aliyu suka zo da zancen shagalin bikin ku!" Kai tayi kasa dashi, yace "Alkasim yaso a kwashe sati ana biki amman ni da Aliyu muka ce a'ah ayi kamu, yini da walima Friday a daura aure yafi. Kinsan Yayan naki wai shi ba party ko daya, Aliyu yace ba za ai ba shine yace shi ya dauki nauyi, ni ba zance a'ah ba amman nace ayi a tsarin addini banda kide kiden nan dan albarka muke nemar muku me kika ce ke?" Kan ta a 'kasa, kamar 'kasa ta bude ta shiga dan kunya tace "Abbi duk yadda ka yanke yayi mungode!" Sallamar Aliyu sukaji a kofar dakin. Suka amsa tare ita da Abbi dakin ya shigo ya karasa gefen Abbi dan Maryam na dayan gefen nasa. Gaishe da Abbi ya karayi dan sun gaisa tin da asuba. Kan ta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana murmushi. Abbi ya kalli Aliyu yace "Ina fada mata yadda mukai rannan ne!" Murmushi yayi ya kara 'kasa da kansa. Wani littafi ya dauko a gefen sa ya turawa Aliyu amsa yayi ya bude inda suke ya fara biyawa yana masa bayani har ya karanta shafi uku sannan ya dago ya dan kalli Abbi yace "A satin nan naga alama zan sauke." "Masha Allah! Allah ya amfana." Maryam dake zaune tana kallon su ce tace "Abbi tinda na gama karatu nima a saka min wani littafi da bamuyi ba a makaranta." Murmushi Abbi yayi yace "To Mama nah ai sai dai nace Aliyu ya samar miki kwana nawa ne zaki tafi shi sai yana koya miki ko Aliyu?" "Haka ne Abbi!" Ya fada yana yi mata wani kallo 'kasa 'kasa. Murmushi tayi kanta a 'kasa tace "To Abbi!" Mikewa Abbi yayi ya shiga daki. Aliyu ya matso yace "My love!" Kofar dakin Abbi ta kalla sannan ta dawo da kallon ta kan sa. Murmushi suka sakar wa juna. Aliyu yace "My love sai naga kin Kara kyau!" "Baka gajiya da fadar haka Yaya nah." Jin tahowar Abbi sukaji yai sauri ya koma gefen ita kuma tai 'kasa da kai tana wasa da yatsun ta. Wata jaka ya fito da ita ya ajiye sannan ya bude ya dauko wasu kati ya mikawa Maryam yace "Ko su Rukkaya kya bawa su bawa iyayen su ko?" Kai ta gyada tana godiya. Yace "Anjima Aliyu zai baki na yini da kati sai ki bawa kawayen naki ko?" "Nagode Abbi!" Aliyu yana zaune yana kallon su. Ta mike ta 'kara godiya ta fita. Ya bita da kallo ta kasan Ido. Abbi yace "To wane littafi zamu saka in kagama wadan nan." Kai a kasa yace "Zan kawo bayan biki sai a fara." "To shikenan!" Yana zaune Ammi a shigo hannun ta dauke da tray saman sa flask na abinci da na tea. Ajiyewa tayi, Aliyu ya gaishe da Ammi ta amsa ta dauko plate da cups ta ajiye. Abbi ta zubawa sannan ta kalli Aliyu tace "Ka zuba kaci." "To Ammi nagode." Ta juya ta fita, Abbi ya dauki kunun gyaɗa da yaji madara ya sha, kallon Aliyu yayi yace "Bismillah Aliyu." Cup ya dauka ya zuba kunun sannan ya zuba dankali da farfesun kayan cikin. Tare suka ci abinci sai da suka gama ya dauke ya fitar da kayan kitchen ya kai kayan hango ta yayi a gaban gas cooker a hankali ya karasa ya rumgumeta, ta baya ajiyar zuciya ya sauke ita kuma tace "Myyy!" " *Matar Haiydar* ina kewar ki da yawa fa!" Shiru tayi can tace "Yaya ba kyau fa." Juyo da ita yayi yana kallon lips din ta wanda yake pink sirara ga dauki sai kyalli yake ji yai kamar ya tsotse bakin yace "Sai aikin ba kyau *Matar Haiydar* kada ki manta fa, ni mijin ki ne!" Kofa ta kalla tace "My Hayyat kada wani ya shigo fa." "To menene! Me kike?" Gun gas ta juya tace "Indomie nake so." "Kawo na dafa miki." "A'ah kaje zan karasa." Kallonta, ya tsaya ita kuma ta zuba indomie dan ruwan ya tafasa sannan ta juyo dan dauko kwai ta fasa ta soya sai ta ganshi a gefe yana ta kallon ta. "Kallon fa *Mijin Nah* " Ido ya lumshe sannan ya bude yana murmushi ya matso kusa da ita yana fadin "Ina son ki *Matar Haiydar* " "Nima haka *Mijin Maryam* " Murmushi ya kara saki ya kamo hannun ta ya sumbata sannan ya saki yace "Bari naje kisan yau juma'a!" Murmushi ta saki tana kallon sa tace "Ayi kwalliyar juma'a nima zanwa mijina ya gani." Murmushi yayi yana shafa sajen sa yace "Godiya nake bari naje. I miss you!" "Miss you more!" Ya juya ya fita ta dauko kwai da kifin gwangwani sannan ta dawo ta yanka albasa ta juya kifin gwangwani da albasa sannan ta fasa kwan wanda yasa karnin ya dake ta, ta tafi sink da sauri ta fara amai sai da ta gama tazo zata soya. Biba ce tace "Ke Anty da bakya son karnin kwai." "Wallahi Biba har amai ya sani yau bari na dauko curry ya 'kara rage karnin ina son naci ne." Ta wuce ta dauko mata. Biba ta amsa ta soya tace "Amman naga abinda kike so Ammi tasa yau akai dan kin dawo." Fuska ta dan shagwabe tace "Ji nayi kuma bana so." Ta dauki plate ta juya indomie dinta saka kwan a gefe sannan ta dibi kunu ta nufi dining dake Babban falo. Tana zama Yaa Alkasim ya shigo ya kalle ta yace "Antyn kwadayi." Murmushi tayi tace "Ina Kwana?". "Lafiya ya gajiya?" "Alhamdulillah!" Yaa Abdullah ne ya shigo yana hango plate din ta ya karaso yana fadin "Daman yunwa nake ji." Fuska ta bata ta dago tana kallon Yaa Alkasim tace "Yaya kace masa breakfast din sa na kitchen ni bana son shi ne fa." "Nima wannan zanci." Yaa Abdullah ya fada. Yaa Alkasim yai murmushi yace "Ni ba za kusani rabon fada da safen nan ba amman dai Abdullah kaje ka dauko naka sai ta sammaka ko ka saka Biba ta girka maka " "Yaya nata yafi dadi" "To je ka dauko kaji" Ya mike ya nufi kitchen ta dauki plate da cup din ta tayi dakin Ammi. Ammi na zaune a kan kujera ta shigo ta zauna a kasa ta fara ci. Kallon ta tayi taga yadda take cin abincin tace "Yunwa kike ji ne?" Kai ta gyada tace "Kinsan bakwai mun karya a makaranta." Kai ta girgiza. Tana gama ci Abdullah ya shigo yana fadin "Ammi nan Maryam ta shigo?" "Gata nan!". "yauwa!" Maryam tayi murmushi tace "Ni na cinye abu na." "Wanda yaci shi kadai dai shi kadai zai mutu!" "Ko mu nawa mukaci ni kadai zan mutu ko Ammi?" Murmushi Ammi tayi tace "Haka ne kam." "Kai Ammi kice a'ah!" Alkasim ne ya shigo ya durkusa ya gaishe da Ammi sannan ya kalli Maryam yace "Kawon abinci ni." "Yaa Aliyu fa?." Maryam ta tambaya, Yaa Alkasim yace "Ai shi da Abbi suke karyawa, in ya tafi dani Abbi zai na karyawa dai." "Kana aikin bacci?" Ammi ta fada. Maryam ta dauke kanukan ta fita a dakin. Bayan ta kai masa ta shige daki tayi wanka ta shirya cikin wani less din ta peach kala da akai wa ado da maroon kala dinkin doguwar riga ne ya kama ta daga sama daga kasa ya bude da yake piece ce tai daurin ta mai kyau ta saka fashion dinta maroon ta dauki maroon mayafi ta yafa tana ganin yadda rigar ta, ta kamata tace "Ni karatun ma ko ramar dani bai ba!" Wayar ta taji tana kara ta dauko ta duba taga Aisha dauka tayi, Aisha tace " *Matar Yaa Haiydar* " "Na'am kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah ya gidan?" "Alhamdulillah yasu Mum?" Haka suka gaisa sannan sukai sallama ta kira Rukayya suna waya taji alamar ana kiran ta wannan yasa ta katse kiran ta dauki nasa. " *Matar Haiydar* kina ina ne?" "Ina daki!" "Ok!" Ya fada ya kashe wayar. Rukayya ta kira suka cigaba da magana bayan sun gama ta wuce gaban mudubi tana kara shafa turare kofar dakin ta ji an bude ta jikin mudubi tagan sa ya shigo cikin manyan kaya riga da wando farare tas sun masa kyau ya saka hula mai kyau da tsada sai tashin kamshi yake. Ba karamin kyau yayi mata ba, Yaa Haidar fari ne tas, wnda yake da faffadan kirji basi da rama kuma dogo ne masha Allah, yana da manyan idanu wanda suke a lunshe ko da yaushe sai pink lips din sa masu laushi, hancin sa dogo a tsaye, sai saje da ya zagaye fusjar sa, koyaya yai magana kuma motaa baki sai gefen kunatun sa ya dan loba, ido ta lumshe tana mai sakin murmushin da bata san ya fito ba a hankali ya karaso sai ji tayi ya sakalo da hannun sa ta gaban ta. Ya saka kan sa a kafadarta yana mai shinshinar wuyan ta wanda yake kamshin turaren da ta shafa Oud 24. ido ta bude da sauri tana kokarin ta zame jikin ta a nasa amman yaki sakin ta wannan yasa ta dago ta kalle shi ta mudubi sam bai ma san tanayi ba dan idon sa a lumshe yake sai shakar kamshin ta da yake yana sauke numfashi. "Myyy!" Ta kira sunan sa. Bai amsa ba ta kara cewa "My Hayyat!" A hankali yace "Uhmm!" "Kada wani ya shigo fa ka bari!" "To menene a ciki?" Fuska ta shagwabe kamar zatai kuka, "Please My!" Dagowa yayi yana kallonta ta jikin mudubi, "Menene to?" Kai ta girgiza. "Don't cry to!" Kai ta gyada ya dago yana fadin "Kinyi kyau *Matar Haiydar* !" "Kafini kyau *Mijin Maryam* " "Anya kuwa?" Ya fada yana kallonta ta mudubi itama kallon nasa takeyi kallo mai cike da so da kauna. Sakin ta yayi ya juya ya nufi kofa dan wani abu da yake ji game da ita. "Ina zaka?" Ta fada a shagwabe "Masallaci!" "Baka tambayen addu'ar da zakai min ba!" Juyowa yayi ya harde hannun sa a kirji yace "Kece duk kin rikita ni ai." Murmushi tayi tai 'kasa dakai. Yace "Wacce addu'a zan miki yanzu banda Allah ya bamu zuri'a mai albarka, da zaman lafiya, dan samun ki na riga na gama, kuma wannan kullum ne" A hankali ta dago tace "Ka roka min in riga ka mutuwa Yaya!" "Saboda me?" Ya fada cike da mamaki "My Hayyat bana son na rasa ka in na rasa ka ban san halin da zan shiga ba, kai kadai nake so kai kadai nake son rayuwa dashi dakai kadai na shaku na saba." Ta fada hawaye na zubo mata a ido da sauri ya karaso, wanda kana ganin sa zaa san hankalin sa a tashe yake dan a duniya ba abinda ya tsana kamar yaga Maryam na zubar da hawaye, kanta ya dago yana fadin "kada kiyi kuka insha Allahu tare zamu mutu mu hadu har a aljanna ki daina kawo wannan Allah zai iya jarabtar ki yaga halin da zaki shiga ki daina kinji ko dani ko bani zaki rayuwa." "Zan yi rayuwa tabbas amman cikin kunci Yaya please ka dage da tayani da wannan addu'ar!" Janyo ta yayi ya rumgume yace "Insha Allahu stop crying kinji my love, sai munga ya'yan mu da jikokin mu kinji." Kai ta gyada ya kalli agogo har daya saura ya sake ta yace "Bari naje sai na dawo zan kira ki." "Allah tsare ya dawo dakai lafiya." "Amin me zan taho miki dashi?" "Dabinon masallaci" "Wannan daman wajib ne, sai me?" "Duk abinda ka gani." "Bye!" Ya daga mata hannu ya juya ya fita, itama hannu ta daga masa ta koma ta zauna a gefen gadonta tana murmushi. Wayarta, ta dauka ta kunna data ta hau online tana hawa Aisha na mata vedio call. Dauka tayi suna kallon juna Aisha tace "Kai wannan kwalliyar fa Besty?" "Ina kwalliyar anan?" "A'ah gata nan ince Yaa Haydar akayiwa." Murmushi tayi tace "Wallahi shi nayi wa" "Ai na sani nidai har Allah, Allah nake wata friday tayi mu mika ki mu huta." "Au ku huta?" "Eh mana." Murmushi sukai Ammi ce ta shigo ta zauna Aisha tace "Bani Ammin mu gaisa!" Ta mika mata bayan sun gaisa ta bata waya sannan suka kashe wayar. Kallon Ammi tayi, Ammi cikin kunya tace "Yayar kice ta aiko miki mai gyara sun zo tin sauran wata daya a fara to makaranta tasa ba a samu an fara ba dan haka daga yanzu in an fara ba fita dan haka yau ki samu ki kaiwa su Aisha katin kinji ko?" "To Ammi!" "Yauwah! Anjima zata karaso." "Allah kawo ta lafiya!" "Amin. Ba abinda kike bukata ko?" "Babu Ammi. To Allah yayi albarka." Ta mike ta fita. Karfe biyu duk suna falo Yaa Muhammad, Ibrahim, Alkasim, Abdullah da Yaa Aliyu dawowar su kenan aka kawo musu lemo mai sanyi dan ba karamar rana ake ba. Sai da suka sha duk masu auren Yaa Muhammad, Ibrahim, sukai bangaren su, Yaa Aliyu da Abdullah da Alkasim kuwa dining suka zauna suka fara zuba abinci suna gamawa suka zauna a falo suna hira, sai da akai la'asar sannan suka tafi masallaci dan yin sallah. Bayan sun dawo garden Yaa Aliyu ya wuce ya samu waje ya zauna, number Maryam ya fara nema tana dauka yace "Gimbiyya ta *Matar Haiydar* kinga sakon ki ko?" "Nagani Yaya nagode!" "Kina ina yanzu?" "Ina ciki yanzu zan fito zanje gidan su Aisha da Rukayya!" "Me zakiyi?" "Zan kai musu kati ne!" "Oh fito na kai ki daga nan sai mu amso sauran ki basu." "Toh Yaya!" Ta kashe wayar sannan ta fito. A babban falo ta samu Ammi zaune ta karasa tace "Ammi na fito zan tafi!" "To waye zai kai ki?" "Yaa Haiydar ne!" "Ina Alkasim da ba zai kai ki ba shi?" "Ni ban ganshi ba kuma shi yace zamu biya mu amso sauran!" "To ki kula da kanki dai." Kan ta tayi kasa dashi tace "Insha Allah!" Sannan ta mike ta fita a parking space ta hango shi yana tsaye a gefen motar sa. Kallon ta ya tsaya yi har ta karaso bai daina ba gefe ta tsaya tace "Ba kyau dai!" "See ur mouth kamar ba kyau din!" Tai murmushi shima murmushin yayi yace "Naga Matata ce ko?" *Allah ya jikan iyayen mu yasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum MS Indabawa *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 16 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Murmushi tayi tai gaba zata shiga da sauri ya karaso ya bude mata mota ta shiga ya rufe sannan ya zagaya. Motar ya tayar mai gadi ya bude musu suka fita. Sai da suka hau titi yace "Ya zancen kudin kwalliya da gyaran amarya banji ance na bayar ba." "Oh amsa ake yi daman?" "Baki sani ba. Nasan da Fadima na nan da yanzu ta damen da zancen." "Ni ai nasan Abbi zai bayar ba sai ka wahala ba." "Wacce irin wahala kuma ai hakki nane nifa za a gyarawa ke." Ya fada yana kashe mata ido daya. Kai tai saurin daukewa tace "Kai Yaya ni ka bari." Dai dai karasowar su shagon da zai amshi sakon waya kawai yayi ya fito ya bashi sakon suka dauki hanya. Sai da suka hau hanya sosai yace "Me zan bari *Matar Haiydar* ni dake fa mun riga mun zama daya wannan kunyar please a ajiye ta gefe kar ta hanani sakewa da Matata." Murmushi tayi tace "Uhmm naga katin?" Mika mata bag din yayi ta bude kati ne kala biyu daya na kamu da yini ne dayan kuma na dinner ne duk sunyi kyau sosai ko wannen yana cikin envelope din sa na Dinner har da sit number. Bag din ta rufe tace "Amman sunyi kyau!" "Basu kai Matata kyau ba." Murmushi tayi tace "Yaushe Yaa Ahmad zai dawo." "Wannan dan iskan sai ja min rai yake yaki ya fada min yaushe zai taho amman ya kamata ace dai dis week end ya taso since wenesday za a fara biki." Murmushi tayi ya kalle ta yace "Monday in naje zan dauki hutu, wata nawa kike so na dauka?" "Wata kuma Yaya?" Ta tambaya tana zaro ido, murmushi ya saki yace "Eh wata nawa?" "Haba My Hayyat wata ai yayi yawa sati daya fa ake dauka zuwa biyu!" "Inji wa?" "Mutane!" "Baby nah ke daban ce wallahi sati daya ya min kadan zan ce su bamu three month dan daga nan zamu wuce honeymoon ko ya kika ce?" Hannu ta saka ta rufe fuskar ta tace "Kai Yaya aikin fa, kaga sati biyu ya isa honeymoon ai kullum muna cikin sa dan kaje ka dawo dai kawai." Motar ya tsayar ya juyo yana kallon ta wanda yasa tai saurin yin 'kasa da kan ta tana wasa da yatsun hannun ta. Hannun ta ya kamo yace "Ma'ul Ayn kinsan yadda nake jin ki kuwa a zuciya ta, ina yawan fada miki amman kamar kina mantawa daga lokacin da na sanki daga lokacin so, kauna, shakuwa, tausayin ki suka dadu a zuciya ta, wallahi ko awa daya bana so naji na nisanta dake, hakika Allah shi ya dauran son ki, tin baki da abinda za a kalla a soki, sonki shine rayuwa ta duk lokacin da na rasa ki mutuwa zanyi, ba da wasa nake ba duk fitar numfashi na ko bugawar zuciya ta da sunan ki suke bugawa, ki gane yadda nake kaunar ki, bana son na nesan ta dake ko na minti daya, kina gani dan haka nai 'kaura na dawo gidan ku, dan numfashi na da naki suna gauraya a cikin waje daya, hakika duk lokacin da muke tare zan nuna miki so da kaunar da bazaki taba mantawa da ita ba, Ina sonki da kaunar ki, fatana mu rayu dake har tsufan mu ki haifa min ya'ya shine kadai burina na gaba....." Hawaye ne ya fara zubo mata a idon ta ya dago kan ta yace "Kuka kuma Baby menene?" Ya fada yana lashe hawayen idon nata jikin sa ta fada ta rumgume shi sosai tana fadin "Na yadda da kai Yaa Haiydar shiyasa na baka duk rayuwa ta, Yaa Haiydar nasan bazan taba samun makamanciyyar soyayyar ka ba, da kai na rayu, na tashi nayi wayo son ka na budi ido na ganni a cikin sa dan Allah kada ka tafi ka barni, kada kayi nesa dani ko yaya ne Yaya na, zan kasance maka yadda kake so na kasance zan maka biyayya iya kar iyawa ta zan baka farin ciki Yaya nah ina son ka da kaunar ka, kaine hasken rayuwa ta." Kara rumgume ta yayi a jikin sa, yana sauke numfashi a hankali, jin kukan ta yake har cikin zuciyar sa, a hankali ya dago kan ta yana kallon cikin idon ta dake zubar da hawaye harshen sa ya saka yana lashe hawayen nata da sauri ta rumtse idon ta, sai da ya shaye su tas sannan yace " *Matar Haiydar* ki daure ki rage kuka wallahi bana son kukan ki ko kadan, nasan daga hallitar ki ce amman please ki rage su. Kuma ki sani ni *Aliyu Haiydar* ina nan tare dake har karshen rayuwar ki ko bana tare dake zan kawo miki mai saki farin ciki wanda zai karasa cika min burin ki, amman ki sani har abada *Aliyu Haiydar* nason ki kuma kece kadai *Matar Haiydar* kinji ko?" Rumgume shi tayi sosai abunda zai ce bata tabai masa ba sai dai lokacin yarinta sai ko in bata cikin haiyacin ta amman kalli yanzu yadda ta rumgune shi tsam a jikin ta. Shima hugging nata back yayi yana mai kara jin son ta da kaunar ta hadi da tausayin ta. Sun dauki minti kusan goma haka kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar sa, shine yai karfin halin cewa " *Matar Haiydar* ba kyau fa!" Kan ta, ta sunne a jikin sa sai kuma ta zame jikin ta daga nashi ta koma jikin kujerar motar tana fadin "Ai miji nane!" Ido ya zaro yana fadin "Da gaske?" Kai ta dauke tace "Mu tafi!" "Sai kin fada min da gaske?" "Kaima fa ka sani." "To naji dan Allah a taimakawa wannan mijin naki ya samu yar nutsuwa." "Kaje kai azumi kawai" "Wallahi da kansa yake karyewa." Fuska ta rufe da hannu tace "Ba kyau fa." Yai dariyar sa mai kyau yana shafa sajen sa hadi da bin ta da wani kallo yace "Naga Matata ce menene ba kyaun?" "Nidai mu tafi dan Allah!" Gyara zama yayi ya kunna motar suka karasa gidan su Aisha. Katon gida ne wanda tsarin gidan kamar zane ne gidan ya tsaru daga gani mai gidan ya tada kai da naira. A bakin gate yai horn mai gadi ya leko Aliyu ya bude window yana ganin sa ya rissina yana gaishe shi sannan ya koma da sauri ya bude masa gate din. Ciki suka shiga a parking space yai parking, inda wajen aka kawata shi da shuke shuke a compound din gidan ya kara kyau da sanyi. Bag din ta bude, ta dibi kati nan sannan ta kalle shi yace "Kada ki shanya Mijin ki dai!" Murmushi tayi tace "Insha Allahu!" Ta bude motar ta fita, ya bita da kallo yadda take tafiya a nutse yarinya karama ta gama tafiya da shi gaba daya. Idon sa ya sauke kan mazaunen ta da suke a bude a cikin doguwar rigar tata, ido ya lumshe yana cije lips din sa na kasa tare da shafa sumar kan sa. AC motar ya dado ya lumshe ido kamar mai bacci. Sallama tayi a bakin kofar sitting room din, aka amsa mata ta shiga Mum din su Aisha ce a zaune a kan daya daga cikin kujerun da suka kara kawata dakin masu kyau. Dakin sai kamshin yake da sanyin AC, tana ganin Maryam tace "Ah Maryam kece a tafe?" "Wallahi Mum! Ina yini?" Ta fada tana durkusawa har kasa suka gaisa sannan tace ya mutan gidan. Bayan sun gaisa tace "Aishan na ciki yanzu ta shiga bata ce min kuma zaki zo ba." Kan ta a kasa tace "Eh bance mata zan zo ba." "Ayyah to shiga tana ciki." Ta mike ta nufi dakin ta. Knocking tayi Aisha dake kwance akan gado tace "Yes come in!" Maryam ta bude ta shiga, Aisha ta juyo tana ganin Maryam ta mike da sauri ta sauko tazo ta rumgume ta tace "Daman kina hanya baki gaya min ba dazu!" "Nima bansan zuwan ba sai da muka gama waya." "Zauna bari na kawo miki lemo!" Ta nuna mata gefen gadon ta wanda ya sha zanin gado mai kyau ga laushi kayan dakin duk lemon green ne sunyi kyau sosai. Zama tayi tace "Daga gida fa muke kuma tafiya zanyi" "Haba daga zuwa." "Ni da Yaa Haiydar ne fa!" "Ah ai nasan ba zama zaki ba tinda kuka zo tare." Ta mike ta nufi fridge ta dauko mata lemo biyu da ruwa biyu tace "Kisha ki kai masa wannan!" Jakarta ta bude ta dauki kati nan tace "Gasu ki bawa Mum ni wallahi kunyar ta nake ji na bata da kai na. Dan Allah ki kaiwa su Abra, Widad, da Muwadad!" Yan uwan su Aisha ne wanda tare sukai graduation ya'yan yayen Mum din ta ne da kuma Kanenen Dad din ta. "Sannan duk wanda yake na kusa dake anan zan kaiwa Rukky ma please Sister kinga Ammi tace wai daga yau bazan kara fita ba." "Kada ki damu insha Allah zan bawa duk wanda ya dace zanyiwa Rukky magana sai muji yadda abin zai kasance." "Nagode!" Ta fada tana mikewa. "Menene na godiya ai mun zama daya." Ta dauki lemo kan tace "Tinda kinki dauka bari na kai masa da kai na." Suka fita a falo suka samu Mum ta kalle su tace "Ba dai tafiya ba Maryam?" "Eh wallahi!" "Mum kati ta kawo ga naki dana Dad!" Aisha ta fada. "Masha Allah! Allah sanya alheri ya kaimu lokacin." "Amin!" Aisha ta amsa. Maryam tace "To Mum sai anjima!" "To ki gaida Ammin taki!" "Zataji!" Suka fice ita da Aisha. Motar takarasa ta bude yana inda yake tace "Yaa Haiydar!" A hankali ya bude ido ya sauke akan ta murmushi ta saka masa ta shiga ta zauna wanda hakan yasa yaga Aisha dake bayan ta. Murmushi ya sakar mata yace "Kawar Amarya." "Na'am Yaa Haidar ina yini?" "Lafiya lou ya gida yasu Mum?" "Suna lafiya." "Amman tare dai zamuje gidan su Rukaiyyan ko?" "Ban fadawa Mum bafa." "To jeki fada mata kizo muje ma dawo dake." "To bari naje!" Ta mikawa Maryam lemon ta juya tayi cikin gida. Kofar ta rufe tace "Ga ruwa!" Ta fada tana bude masa ta bashi, amsa yayi ya dan kurba sannan ya bata tasha kadan ya kara sha ya rufe. Lokacin Aisha ta dawo ta shiga baya suka tafi gidan su Rukky. A compound suka same ta tana zaune a gefen gidan su inda garden din su yake tana ganin su ta mike tazo suka rumgume juna. Yaa Haidar ta gaisar sannan sukai ciki a falo suka sami Mom din ta suka gaishe ta, ta amsa sannan suka tafi dakin ta suna shiga mai aiki ta fara kawo musu lemo da kayan motsa baki. Maryam tace "Mu da zamu tafi!" "Uhmm ke haka kike daga zuwa sai tafiya." Murmushi tayi tace "Sauri muke!" Ta kwaso katin ta ajiye mata tace "Kema ki basa su Sakina, Hibba, Izzatullah, sannan sauran ku sasanta yadda zaku rabawa sauran yan ajin mu, gana Mom da Dada!" Ta bata amsa tayi tace "To Aisha ya zamuyi?" "Kinga kawai in zaki fita ki biyo ta gida mukai ko?" "Eh hakan yayi gobe sai mu fara kinga lokaci ya kure ko?" "Allah kaimu." "Yauwah wai yaushe zaku taho?" "In munzo ranar kamu shikenan ko?" "Har sai ranar kamu please kuzo Talata mana!" "Ba dai ranar Laraba kamu ba, Alhamis dinner, Juma'a daurin aure da yini da kai amarya so kinga muzo Laraba mu taho Friday ko?" "Lallai ma ni Talata zaku zo ku dawo Asabar!" "Kai Besty kin fiya rigima." "So kuke na zauna ba kowa a tare dani kunsan bani da kowa dai sai ku ko?" "To shikenan ya isa zamuzo Talatar amman sai yamma ko dare saboda zamu lalle da gyaran kai ko?" "Kuzo da wuri mu tafi tare ko?" "Shikenan zaki ji mu." Ta mike tace "To nidai na bar Yaa Haidar a waje fa." " *Matar Yaa Haidar* Allah tabbatar da alheri!" "Amin!" Ta nufi kofa. Rukayya tace "Ke bakici komai ba shima ba zaki kai masa komai ba." Aisha ta dibar masa suka fita sukai sallama da Mom. Mota suka shiga suka maida Aisha gida sannan suka tafi gida. Yana parking ya kalle ta yace "Nawa zan bayar kudin abubuwan ne?" "Ka barsu zanyi magana da Ammi in akwai bukatar abu zanyiwa Abbi magana." "Yakamata mu na hutar dasu Abbi by now zan turo miki kudi ko da bukatar su zata tashi, in kina bukatar dadi ki min magana." Har ga Allah ta manta da tana da wani account dan ko kudin da aka bata 1m ma yana ciki tacewa Abbi ya amsa yace ta ajiye a wajen ta, bayan Yaa Aliyu da yake yawan saka mata kudi banda duk lokacin da yaji alert har in ya samu kudi tura mata yake. "Tunanin me kike?" "Na tuna ina da kudi ne Yaya ba sai ka turon ba zanyi amfani dasu nagode!" "A'ah wannan hakki nane ki amsa kawai." "To nagode Allah saka da alheri ya biya maka bukatun ka. Ya rabaka da iyayen ka lafiya." "Amin *Matar Haidar* ki shiga gida ana kiran magariba bari naje masallaci." "Ai mana addu'a!" "Insha Allahu!" Tayi ciki shi kuma yai alwala anan compound sannan ya tafi masallaci. Washe gari tin safe aka farai mata gyara na musamman wanda daga daki sai daki ko babban falo bata fitowa duk abinda take bukata Biba ke mata ta kai mata. Wanda cikin kwana biyun nan ta kara haske sosai kirjin ta ya kara cikowa, kamshi kuwa har ya zauna a jikin ta duk inda ta zauna sai ya kama. Kwance take akan gado lokacin karfe goma saura sanye take da wando three quarter da vest a jikin ta kan ta sanye da hula waya kare a kunnen ta tana fadin "My kayi hakuri jibi zani lalle da gyaran kai sai mu hadu kaji!" "Ba zan iya ba wallahi ba zan iya ba kawai ki fito in ba haka ba zanyi knocking Allah ko Ammi tace menene zance ke kika kirani gwara ma ki tashi tinda Ammi ta kwanta kizo ki bude ki fito naganki kawai." "In ganina kake so kayi in hada mana vedio call!" "No bana son ido cikin ido nake so na ganki!" "Please....." "Ma'ul Ayn kada kice komai kinsan dai ba kyau ko?" Jikin ta ne yai sanyi dan daga yadda yai maganar ma kasan yana cikin damuwa. Mikewa tayi tace "Shikenan ka taho bari na bude maka!" "Ina kofar part din naku!" "Toh!" *Allah ya yafe mana ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe amin* MS INDABAWA ANTTY 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 17 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Ta saka hijab ta fito tana sanda a hankali ta fito ta bude ta juya ta kalli kofa sannan ta rufo ta fito da sauri. Tana juyowa taji ya rumgume ta. "Yaa Haidar ka bari a waje fa muke kada wani ya ganmu!" "Ina ruwa na, ni dai tinda naga matata." Tai murmushi ta tsaya kallon sa tace "Ai ka ganni ko sai da safe!" Ta juya zata shiga yai saurin kamo hannun ta wanda ya dada taushi kamar auduga, ido ya lumshe yace "Kin dai mai dani kakanki ko?" "Ah haba ina fa." Hannun ta ya kai hancin sa yana shinshinawa tare da sakin ajiyar zuciya hadi da lumshe idanun sa. Yace "Wannan kamshin fa? Wane irin turare ne haka?" Hannun take son janyewa ya janyo ta jikin sa gaba daya yana son cusa kansa cikin jikinta dan yadda kamshin ta ke tada masa hankali. Idon sa ya gama rufewa ga kewar ta ga kamshin ta mai tada hankalin ya rikita masa lissafi. Jikin ta sai rawa yake na tsoro a hankali tace "Yaa Haidar, Ammi fa!" Da kyar ya sake ta yana mai da numfashi yace "Wannan turaren ki daina saka shi sai mun tare kina ji ko?" Kai ta gyada sai yai sauri ya juya yace "Koma kije ki kwanta sai da safe!" Yai magana muryar sa a sanyaye. Gaban sa ta dawo tace "Menene Yaya nah." Murmushin karfin hali ya sakar mata yace "Ba komai!" Ya kamo hannun ta ya bude kofa ya saka ta sannan ya rufo maimako ya koma dakin Alkasim sai kawai yayi gidan su dake gefen nasu Maryam. Wanda a tsarin ginin da girman sa har yafi nasu Maryam girma da tsaruwa. Mai gadi yana kwance yaji knocking ya taso ya bude masa yana shiga ya wuce bangaren sa. Sanin ba anan yake kwana ba yasa bai rufe kofar ba kawai ya koma ya zauna. Aliyu yana zuwa bangaren sa ya shige wanda yake kamar na wani magidancin dan komai akwai. Yana shiga ya fada bathroom din sa ya fada ya sakarwa kan sa ruwa ko zai samu saukin abinda yake ji amman ina kamar ana kara masa wutar sha'awar ta. Kan gado ya fada yana jin yadda jijiyar sa ta mikewa tana bukatar agaji. Ido ya runtse dan jin yadda marar sa tayi tauri kamar dutse. Wayar sa dake cikin aljihun jallabiyar sa ce tayi kara da kyar ya saka hannu ya zaro wayar ba tare da ya duba wanda ya kira ba ya kai wayar kunnensa ya saki nishin wahala sannan yai sallama da kyar. Da sauri ta mike daga kwanciyyar da take ta amsa sallamar hadi da fadin "Lafiya Yaya meyake faruwa ne?" "Me kika ji *Matata* " "Jifa muryar ka, ka fada min me yake damun ka." "Ba komai fa." Kuka ta saka masa tana rokar sa ya fada mata wanda kukan nata ke kara ingiza yanayin da yaje ciki sai faman nishi yake da danna marar sa yana mai hade kafafun sa. "Dan Allah ka fada min!" "Zan fada miki amman ki min alkawari zaki sama min mafita." "Nayi Yaya zan sama maka nasan addu'a ce zan maka ka fada menene?" "I need you *Matar Haidar* wallahi ina cikin wani hali Matata, ki taimaken ki gusar min da wannan yanayin da nake ciki dan Allah " Hawaye ne yake zuba a idon ta, ta rasa me zata ce masa yace "Kina ji na?" Sheshekar kukan ta ya jiyo ya cije baki yace "Ni nasan ba zaki iya ba, ciwo na ba naki bane ko? Damuwa ta ba taki bace ba ko? Shikenan sai da safe ki kwanta kiyi bacci." Yana gama fadar haka ya kashe wayar gaba daya ya cilla ta gefe ya dinga fama shi kadai. Yana kashe wayar ta fada kan gado ta fashe da kuka a ranta take magana can ta dauki wayar tana girgiza kanta, ta fara neman layin sa amman a kashe. Da sauri ta mike ta saka hijab ta fita falon. Kofa ta bude tayi bangaren Yaa Alkasim tana isa ta tsaya ta kasa taba kofar tafi mintina sannan ta tura kofar a hankali taji ta a bude ciki ta shiga ba kowa a falo dan haka ta nufi kofar bedroom din sa ta fara knocking. Alkasim dake bacci ne yaji knocking ya mike yana salati ya duba yaga ba Aliyu mikewa yayi ya fita ya bude kofar. Maryam ya gani tsaye kallon ta yayi yace "Menene?" "Ina Yaa Haidar?" "Ina jin yana bandaki menene?" "Ina son ganin sa ne!" Ciki ya koma ya tsaya bakin kofa yace "To kai kayi sauri matar ka na waje tana jiran ka." Ya koma ya kwanta kawai. Maryam dake falo ganin kusan rabin awa yasa ta kara komawa tai knocking Alkasim yana bacci ya kuma mikewa. Agogo ya kalla yaga sha daya da rabi mikewa yayi ya kara fita da mamaki yake kallon ta wannan lokacin yace "Menene kuma?" "Ina yake?" "Wa?" "Yaa Haidar?" "Bai fito ba?" Kai ta gyada tana share hawaye komawa yai da sauri ya bude bandakin ba kowa dan haka ya fito yace "Kila ya tafi gida fa." "Yaa Alkasim dan Allah ka kira min shi mana." Waya ya dauka ya fara kira amman a kashe ya dago yace "Wayar tasa a kashe lafiya?" "Muje ka kira min shi dan Allah." "Dare yayi fa har sha biyu saura menene?" Durkusawa tayi tana kuka tace "Ni dai ka kira min shi." "Zan kira shi amman kinsan menene tashi kije ki kwanta kar Ammi ta leko taga kofa a bude kinji in na kirasa zan zo sai mu taho." Ta mike ya rakata har kofar part din su sannan ya fita amman sai ya kasa buga kofar gidan su Aliyu dan dare yayi kada ya tada musu da hankali ya jima a haka dai ya jingina da kofar ji yayi kofar taja baya ya shiga kawai ya samu mai gadi na ta baccin sa. Kai ya girgiza kawai yayi sashen Aliyu. Kwance ya same shi ko numfashi bayayi da sauri ya dago shi yana kiran sa amman ina bai ji. Ruwa ya debo ya shafa masa nan ma bai farka ba da sauri ya mike ya je ya taso mai gadi yazo ya taimaka masa suka sashi a mota ya tafi asibiti dashi yana zuwa aka amshi shi emergency, sai wajen daya sannan suka samu ya farfado allurai sukai masa sannan suka barshi dan ya huta take baccin wahala ya dauke shi. Alkasim ya shiga ya zauna a kusa dashi karfe uku ya farka yaga Alkasim akan sa dakin ya kalla ya mike da sauri yana fadin "Me muke anan? Tashi mu tafi." "Aliyu baka da lafiya fa!" "Ni lafiya ta kalou." "To bari na kira Dr!" Ya fita yaje ya taho da Doctor wanda abokin Aliyu ne yana zuwa yace "Alhamdulillah jiki yai sauki ko?" Kai ya gyada yace "Dadin tama dai ka kusa aure amman da baka kusa ba wannan matsalar zata iya halakaka, kana kiyayewa!" Kai ya gyada yace "Insha Allahu." Alkasim yace "Me yake damun sa ne?" Mikewa Aliyu yai ya fita. Dr yace "Yana da matsananciyar sha'awa wacce take sa shi shiga wannan halin in ta motsa masa." "Shege jarababbe ai na jima da gane hakan zan fadawa Abbi ai maza a daura auren kar ya mutu." Ya mika Dr hannu suna murmushi yabi bayan Aliyu. A mota ya same shi yana zaune kan sa jingine da kujera ya lumshe ido. Murmushi yayi yace "Ashe jarabarce ta motsa ince zuwa kayi ka tadawa yarinya hankali dazu tazo tana tai min kuka sai na kira ka." Bai motsa ba bare ya kulasa, Alkasim sai iya shege yake masa amman ya ki kula sa. Suna shiga ya wuce yai wanka ya shirya suka tafi masallaci. Shida suka dawo gida a falo ya kwanta Alkasim ya shige yana fadin "Bacci nake ji wallahi." "Wa ya hana ka bacci?" Aliyu ya fada yana gyara kwanciyya kan three sitter. "Au haka kace?" Alkasim ya fada yana yin ciki ya cigaba da cewa "Zaka sani ne." Ido ya lumshe ya fara karatun Alkur'ani a hankali cikin muryarsa mai dadi da sanyi. * Maryam kuwa gaba daya ta kasa sukuni dan ba alamun Yaa Alkasim ta kira sa amman baya dauka wajen daya ta koma dakin nasa babu shi ba Aliyu daki ta koma ta zauna akan sallaya sai kuka. Haka wajen biyu ma ta kara komawa amman babu su kwata kwata. Karfe uku ma ta kara zuwa babu su. Daki ta koma ta dinga kuka dan ta rasa nutsuwa me yake faruwa ina Yaa Haidar ya tafi. Har aka kira sallah asuba ta tashi tai alwala tai sallah. Ta na idar da azkar ta mike ta fito ba kowa a falo kitchen ta shiga ta gaisar da Ammi da Baba Ramma sannan ta fita ta nufi bangaren Yaa Alkasim tana bude kofa ta fara jiyo kira'ar sa, ido ta lumshe sannan ta shiga kwance ta ganshi akan three sitter da sauri ta karasa ta zauna a kasa gaban kujerar cikin muryar kuka tace "Yaa Haidar!" Idon sa ya bude a hankali ya sakar mata murmushi yace " *Matar Haidar* " Sai ya fara kokarin mikewa. Kallon sa tayi har ya zauna duk ya fada na lokaci daya. "Ka yafe min Yaa Haidar!" Hannun sa ya daura akan ta yace "Na yafe miki *Matar Haidar* na yafe miki. Kin tashi lafiya?" Hawaye ne ya zubo mata yace "To menene na kukan?" "Yadda kake so na, ni na bata maka na kasa kawar maka da bukatar ka duk da....." Hannun sa ya daura akan bakin ta yace "Kada kice haka ni nasan kina so na kuma kin damu da bukatata nasan dalilin ki na bijire min ba komai mun kusa mu zauna cikin inuwa daya wacce zamu kasance cikin nutsuwa nasan a lokacin zaki ban duk kulawar da nake so kada ki damu kinji sauran kwana nawa ne?" Kai tayi kasa dashi, yayi murmushi yace "Sauran kwana hudu ko?" Kai ta gyada masa a kunyace yace "Ina fatan kinyi bacci dai!" Kai ta girgiza tace "A'ah Yaya nakasa na kasa saboda bansan a halin da kake ciki ba nace Yaa Alkasim yaje ya kira ka amman bai dawo ba da tini nazo da kai na to kada Ammi tazo taga bana nan ne kayi hakuri!" "Ba komai, *Matar Haidar* bata laifi kuma bana fushi da ita." "Nagode Yaya nah!" Ta mike tace "Ban gaishe da Abbi ba bari naje!" Ta nufi kofa mikewa yayi yabi bayan ta yana fadin "Muje nima na gaishe sa." Tare sukaje suka gaishe sa ya sa musu albarka dukkan su ya karai musu nasiha sannan ya sallame ta shi kuma ya zauna shi da Aliyu suna tattaunawa. Bayan sun gama ya dago ya kalli Aliyu yace "Aliyu me yake damun ka ne?" Kai ya dan shafa yace "Ciki na ne ke ciwo da shi na kwana jiya." "Allah ya sauwake ya kamata ka samu magani akan ciwon cikin nan." "Insha Allahu Abbi." Tare suka karya sannan yaje ya shirya ya tafi asibiti. Sai yamma ya dawo yana dawowa gidan su ya wuce yai wanka sannan ya nufi part din iyayen nasa. A falon Mamah ya samu Mamah da Abbah. Zama yayi ya gaishe su. Mamah tace "Har ka dawo?" "Eh Mamah." "Yau ana can ana kafi a gidan naka." "Haka Ammi ta fada min dazu." "Masha Allahu Baba na ka rike amanar yarinyar nan duk da nasan yadda kake son ta amman zaman tare dole a saba wata rana kayi hakuri da ita kaji ka dauke ta matsayin kanwa in tai maka laifi kaji?" Kai ya gyada yace "Insha Allahu!" "Allah maka albarka." "Amin!" "Kaje ka gaishe da Umman taka?" Kai ya girgiza. Abbah yace "To kaje kaji dan albarka." Kai ya gyada ya mike ya fita. Bangaren Umma ya nufa yana zuwa yai addu'a sannan ya shiga bangaren Umman tana falo zaune akan kujera kafa daya kan daya tana kallo. Yai sallama ta amsa ko kallon inda yake batai ba. Zama yayi yace "Ina yini?" "In ban yini ba zaka ganni? In ma fata kake na mutu to ka sani kai ne zaka mutu da wannan shegun kuma ka sani sai tarihin ka ya bace a duniya." Bai tanka mata ba ya mike yace "Na barki lafiya." Ya juya ya fita yana girgiza kai da halin Umman nan tasu. Hakika yasan Mamahn sa na hakuri wannan yasa sam bai son zaman gidan dan in har yana gidan sai ya gaishe da ita abinda shi kuma baya so kenan dan da yaje sai ta bata masa ran sa da irin wadan nan maganganun. Waya ya dauka yaiwa Maryam transfer dubu dari biyar sannan ya koma dakin Mamah acan yaci abinci har akai isha'i ya kara komawa. Mamah ta kalle shi tace "Me yake faruwa ne yau?" "Me kika gani?" "Naganka a gida ne." Yai murmushi yace "Na fara missing Mamah na ne." "Kai din da kake dokin a daura maka aure ka dauke Matar ka, katafi ka bar ni." "Ah haba dai!" Sallamar Alkasim ce ta katse masa magana ya shigo ya gaida Mamah sannan yace "Ai na zata jikin ne?" "Bashi da lafiya ko?" "Jiya sai da mukaje asibiti amman da sauki ai." "Yanzu nake masa ai nace yau lafiya yazo ya makalen?" Mamah ta fada. "Tsoron mutuwa yake kar ta dauke shi shine ya taho wajen ki." "Ai mutuwa ba yanzu ba sai naga ya'ya na." Aliyu ya fada. Mamah tace "Me.....?" Da sauri ya mike ya fita yana dariya. Alkasim ta kalla tace "Me yake damun sa ne wai?" "Ciwon ciki ne amman an bashi magani ai." "Kasan kuma bai fada min ba." "Ai ba zai fada ba ko ita ma nasan bai fada mata ba." "Aliyu kenan." Haka suka dan taba hira sannan ya mike yai mata sai da safe dan har tara tayi. Dakin Aliyu ya nufa ya same shi har yayi shirin bacci zama yayi yace "Anan zaka kwana kenan?" Kai ya gyada yace "To ni bari naje sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Yana fita ya fara neman layin Maryam, dauka tayi tace "Yau ba ruwa na dakai Yaya!" "Ya salam menayi kuma?" "Yau baka neman ba sai zuwa naje dakin Yaa Alkasim baka nan." "Naje aiki ne! Sai yamma na dawo ina gida me kike so?" "In ganka kawai!" "Kina ina to?" "Ina falon Ammi." "Bari nazo to." *Gaskiya ina jin zan daina posting a whatsapp ace ba wani appreciation da kuke nunawa, always thanks ba wani comment kuma a haka kuke so ina muku two pages a rana, in har kuna son two pages a rana to naga ruwan comment nima nai alkawari daga gobe har na gama book din nan two page zan nayi amman fa sai naga comment, yawan comment yawan posting karancin sa ma zai na sai na gadama nayi posting, dan haka in kuna so naga sauyi. Ngd* *Allah ka yafe mana kasa mu cika da kyau da imani Amin.* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 18 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Ya mike ya nufi kofa ya fita. Gidan ya nufa ya shiga Babban falo ba kowa dakin Ammi ya shiga ya same ta zaune gaban ta gashin nama da madarar Ammi zaune tana duba wasu kaya. Zama yayi ya gaishe da Ammi sannan ya zauna a gefen ta yana fadin "Kayan dadi aka samu ashe!" "Muci!" Cikin sa ya shafa yace "Na koshi!" Tace "Shikenan!" "Goben zaku gyaran kai ko?" "Eh!" "Karfe nawa zan zo na kai ku.?" "A'ah kaje aikin ka ko driver ya kai su." Ammi ta fada. "Ammi na dauki hutu ai!" "Au to shikenan. Allah ya taimaka." Ta mike tayi cikin dakin ta. Ya kalli Maryam yace " *Matar Haidar* kinga Haidar din naki?" Kai ta gyada yace "Zan iya tafiya?" Fuska ta bata tace "Bamuyi hira ba fa." "In na zauna kar naje....." "Kar kaje me?" "Shikenan!" "Naga sako dazu Amman Yaya yai yawa!" Hannu ya daura akan lips din sa masu taushi pink kala yace "Kada kice haka sunyi kadan ma nake gani." Tai murmushi jin Ammi zata fito ya mike yace "Zanje na kwanta gobe wajen 10am zanzo sai mu tafi." "Allah kaimu nagode!" Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kara kallon ta, mikewa tayi yace "Muje na rakaka!" Suka fita. Bakin gate taga yayi tace "Ba anan zaka kwana ba?" Kai ya gyada, idon ta ne ya kawo ruwa tace "Saboda me to? Saboda jiya ko? Baka yafe min ba ko Yaya?" "Na yafe miki *Matar Haidar* ni namanta da wani abu ya faru ma jiya, kawai ina hada kayana da wasu abubuwan ne me kike so na baki?" "Ni da zaka kawo abin gidan mu in akwai abinda nake so in ka kawo na dauke." "Shikenan sai da safen ko?" Kai ta gyada ta daga masa hannu tana masa bye bye har ya juya ya fita. Juyawa tayi ta koma ciki. Dakin Ammi ta koma ta dauke kwanon dan kai wa kitchen Ammi tace "Amman naga baki ci ba fa!" "Ammi na koshi ne!" Kallon ta Ammi ta tsaya yi tace "Zo nan Maryam!" Karasawa tayi ta zauna, Ammi ta bita da kallo sannan tace "Meyake damun ki ne? Tinda kika dawo daga makaranta bakya cin abinci sosai ga tsurfar zabar abinci." Cikinta ta shafa tace "Nima Ammi ban sani ba." Ta karasa magana tana hamma alamar bacci takeji. "Je ki kwanta sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." "Amin!" Ta fita ta ajiye plate din sannan ta shiga tai wanka tare da brush tazo ta kwanta. Tana kwanciyya bacci ya dauke ta. Aliyu na shiga ya isa kan gadon sa, kwanciyya yayi yana mai lumshe ido, juyi ya fara akan gadon wanda sam ya kasa baccin har wajen karfe dayan dare mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa yayo alwala sannan ya fito ya hau kan sallaya nifala ya fara wanda har karfe uku idon sa biyu yana karatun Alkur'ani. Sai da yaji an fara kiran sallah sannan ya mike ya kuma watsa ruwa ya nufi masallaci. Ba mutane sosai ya shiga ya zauna yana karayin karatu, sai kusan rabin awa sannan Abbi da Alkasim suka shiga daga can aka kara kiran sallah sannan mutane suka fara shiga dan yin sallah, ana idarwa suka gaisa da Abbi sannan ya tafi. Alkasin ya zauna a gefen sa yana kallon sa yace "Ahmad yana ta kiran ka baka dauka ba." "Bansan inda wayar ma take ba, me ya faru!" "Zancen zuwan sa ne." Mikewa sukai suka fita, a kofar gida suka tsaya yace "Me yace maka?" "Ba zai samu damar zuwa bane saboda wani aiki da ya tasar masa aka tura shi wani waje kuma a cikin week din nan ake son ya kai report yace kayi hakuri da ya gama zai zo yaci girkin amarya." Tsaki ya saki yace "Yai zaman sa ma kawai dan rainin hankali." Ya juya ya nufi gidan su. Dakin sa ya shiga ya kwata anan falo bacci ne ya dauke shi, takwas da rabi ya tashi ya shiga yai wanka da sabulun sa mai dadin kamshi. Ya fito ya shafa mai ya saka bakin wando da farar riga mai gajeren hannu ya saka turaren sa na Oud Kareem mai kamshi da dadi ya gyara sumar kansa wacce take a kwance ko da yaushe luf luf, agogo ya daura a hannun sa ya kalli fuskar sa karfe tara har da kwata. Wayar sa ya dauka guda biyu ya fita dasu a hannu. Bangaren Mamah ya nufa yana tafe suna gaisawa da masu aikin gidan a haka har ya karasa bangaren Mamah, ba kowa a falon ta sai tashin kamshi da sanyin AC dake tashi. Bedroom din ta ya nufa yai knocking kofar tana daga ciki ta amsa masa ya shiga tana zaune gaban mirrow tana daura dankwalin ta ya shiga. Har kasa ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa tana dafa kan sa tare da saka masa albarka. Mikewa yayi yana fadin "Me kike dafa mana?" "Ni Abbahn ka na dafawa ba kai ba." Yai murmushi yace "Mamah sauran kwana nawa ne nima da zan tafi, kuma ko rabon Abbah ne ci zanyi ayi masa wani." Ya fada yana fita, Murmushi Mamah tayi tabi bayan sa tana fadin "Baka da magana sai ta tafiya kullum kace sauran kwana nawa ko? To ina fatan in ka tafi ba ka tafi ba kenan ai dole wata rana kana zuwar mana ko? Kuma kaci abincin dai wata rana ko?" "A'ah Ma'ul Ayn ba zata barni ina cin abinci a waje ba, dan haka abincin ki sai da kallo Mamah!" Ya fada yana daura kan sa a kafadar ta. Kan sa ta shafa tana fadin "Aliyu da Maryam kenan, Allah ya nuna mana ya tabbatar da alheri," "Amin!" Abbah ya fada yana shigowa, murmushi duk sukai, Aliyu ya durkusa ya gaishe da Abbah nasa ya kamo hannun sa yana fadin "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah!" Ya kamo hannun sa sukai duning table Mamah tai serving nasu suka gama suka mike Abbah ya ajiyewa Mamah kudi suka fita. Har bakin kofa ta raka shi tana masa addu'ar Allah kiyaye ya tsare. Aliyu yana murmushi dan yadda Mamah ke kula da Abbah sa ko fada sukai sai ta raka shi tai masa addu'a yana sha'awar zaman su yana fatan suyi irin shi ko fiye da haka da Maryaman sa. Bangaren Umma suka nufa, suna shiga tana fitowa daga bedroom sanye da kayan bacci kan ta ba dan kwalli sai kitson da akai mata da attachement. Kasa Aliyu yayi da kan sa daga bakin kofa yace "Ina kwana?" Kai ta dauke tace "Lafiya!" Sannan ta nufi dining, da sauri ya juya ya fita yaji Abbah yana fadin "Yau baki zasu fara zuwa fa!" "To me zan musu?" "A'ah na fada miki ne dai daman dan kar kiji zuwan nasu an gyara musu can boy quarter da bangaren Abubakar." Bata tanka masa ba ta zauna sai kuma tace "Kuna wahal da kanku ne fa." Kudi Abbah ya dauka ya ajiye mata yana fadin "Ni sai na dawo." Ko kallon sa batai ba har ya fita a dakin. Ya shiga mota ya bar gidan. Aliyu na fita ya fito da motar sa a kofar gidan su Maryam yai parking sannan ya dauki wayar sa har zai kira ta sai kuma ya fasa ya mike ya shiga cikin gidan. A falo ya samu Ammi da Baba Ramma da wasu mata a dakin dan har sun fara ba'ki masu zuwa kwana. Har kasa ya gaishe su, sannan ya mike ya shiga corridor dakin Ammi da Maryam, kofar dakin ta ya nufa ya tura kofar, fitowar ta kenan daga toilet daure da towel daga kirjin ta zuwa gwiwar ta sai hula akan ta, tana zaune gaban mirrow tana shafa mai taji an budo kofar da sauri ta dago, ganin Aliyu yasa tai saurin durkushewa tana kakkare jikin ta. Ido ya lumshe yana mai tasbihi a zuciyar sa. Hakika Maryam yarinya ce amman Allah yai mata baiwa da yawa wacce sai kana tare da ita zaka san wasu daga ciki. Duk da yarinya ce Allah ya hore mata diri mai kyau da daukar hankalin duk wani namiji, banda suffa ta kyau da take da ita Maryan ta gama yi ta ko wacce fuska. Ido ya bude a hankali ya karaso inda take a durkushe yace "Me zaki boye min *Matar Haidar* ? kada ki manta komai naki na *Haidar* ne." Kai ta hau girgizawa tana fadin "Yaya dan Allah ka fita na karasa shiryawa." Mikewa yayi ya harde hannu a kirjin sa tare da make kafada yace "Naki yau ni zan shirya ki!" Ya fada yana durkusawa ya dagota da sauri ta makale jikin sa dan kar ya ganta a haka, wanda jin ta a jikin sa yasa ya fara rasa nutsuwar sa. Hannun sa ya zura cikin towel din nata yana yawo dashi a ciki har ya isa kan kirjin ta wanda daga ita har shi suka sauke wata ajiyar zuciya. Kan nipple din ta ya kama yana wasa dashi, dayan hannu yasa ya zagayo dashi ta bayan ta ya tallafe bayan ta dashi. A hankali ya matsar da kan sa kusa da fuskar ta hancin sa dai dai nata goshin su a hade idon ta a lumshe yake in banda rawa ba abinda jikin ta keyi. Dago kanta tayi wannan ya bashi damar cafkar lips din ta ya fara tsotsa kamar wanda ya samu lolli pop. Maryam kuwa jikin ta ba karamin mutuwa yayi ba amman hakan bai hanata kokarin son raba jikin ta da nashi ba. Jin yana yin kasa da hannun sa yasa ta saki kuka marar sauti tinda bakin ta na cikin nasa, bai san tana yi ba sai kokarin faduwa da suke daga shi har ita dan kafar sa ta gaza daukar ta, kan gado ya nufa da ita ya kwantar ya rufa akan ta, hawayen da ya gani yana ta zuba yasa shi ya rude ya hau tambayar lafiya? Murya na rawa tace "Dan Allah ka bari Yaya bana so!" "Ni ina so!" Ya fada yana kashe mata ido daya. Ido ta lumshe ya saki kara da sauri ta mike tana kallon sa rike da ciki. Yana ganin ta mike ya fara tambayar "Menene Yaya? Cikin ne? Ayya sannu!" Ya saki murmushi ya matso yasa harshen sa ya fara goge mata hawayen dake zuba ta idon ta. Hannun sa ta kama cikin damuwa kamar zatai kuka tace "Ya daina?" Kai ya gyada tare da dafe kanta yace " *Matar Haidar* mijin ki is missing you, he need you!" Hannun sa dake cikin nata ta kara rikewa tace "Am sorry Yaya na, please be patient sauran kwana uku fa?" Tai maganar cikin lallashi. Hannun ta yai wa kissing sannan ya mike ya kai hannun nata kan marar sa yace "Kinji yadda yake min kwana biyu!" Da sauri ta janye hannun ta dan jin tudun abar sa wanda ya tabbatar mata a matukar bukace yake. Murmushi yayi yace "Sai na kara wanka kema kije kiyi, i will call you to come out!" Kunya ya bata tai kasa da kanta matsowa yayi yace "Kema fa sai kinyi! Da sauri ta juya masa baya ta make kafada, dariya yayi yace "Oh ko? To bari na saka ki da dalili!" Kamar tasan kamo ta zai ta diba a guje ta fada bandakin tana murmushi. Jingina tayi da jikin kofa tana sauke numfashi hadi da lumshe idanun ta. Hakika Yaa Aliyu ya iya soyayya. Shin ya rayuwar su zata kasance a gidan su. Murmushin ta saki shiga cikin bath ta fara wanka tana yi tana murmushi. Hakika tana kunyar Yaa Haidar amman da bata kunyar sa itama zata nuna masa ita ma fa eh ce dan itama tana bukatar sa, amman ba koma bari ta tare zatayi kokarin wajen ganin ta kare masa hakkin sa. Ita kadai ta dinga hirar ta, ta jima tana wankan tana yi tana murmushi ko ta lumshe ido wani abun har kunyar kan ta take ji. Aliyu yana ganin shigar ta ya saki murmushin ya juya ya fita a kofar dakin ya tsaya tayaya zai fita falo su Ammi na falo. A hankali ya karasa ya shige kitchen sannan ya fita ta kofar baya. Gida ya koma yai wanka ya fito ya shirya cikin wasu kananun kayan ya saka turare mai dadin kamshi. Fita yayi ya shiga mota ya fara kiran layin ta. Fitowar ta kenan taji karar wayar ta karasa ta daukan tana ganin shine ta saki murmushi ta dannan received ta kai kunnen ta hadi da yin sallama. Bayan ya amsa yace " *Matar Haidar* ke nake jira ki fito mu tafi!" "To gani nan." Ta fada ya kashe wayar, cikin sauri ta shafa mai bata saka komai a fuskar ta ba ta saka under wears din ta, ta shafa turare ta daura doguwar riga tai rolling mayafin ta, ta dauki wayar ta, ta fara neman layin Aisha tana dauka tace "Kin shirya dan gamu nan fa." "Sai kun karaso." Ta kashe ta kira Rukayya itama sannan ta fita falo. Ammi da Baba Ramma ne kadai a ciki tai musu sallama ta fita. Tinda ta fito yana daga mota yake kallon ta ido ya lumshe yana godiya da Allah da ya bashi Maryam. Har ta karaso ta bude gefen sa ta shiga bai san ma ta shiga ba sai da tace "Yaya!" Sannan ya bude idon sa a hankali ya sauke akan ta yana mata murmushi da sauri tai kasa da kan ta tana murmushi. Ya kamo hannun ta ya daura akan kirjin sa yace "Ko wanne bugawar numfashi dake yake ambato, hakika rabani dake tamkar rabani da rayuwa ta ce." "Bame rabamu, Ni taka ce kamar yadda kake nawa. *Matar Yaa Haidar* kadai kamar yadda kake *Mijin Maryam* mutuwa ce kadai zata rabamu itana ina fatan ta dauke mu tare in taki to ta fara dauka ta." Hancin ta yaja yace "Ni dai ai a zamanin nan in zaki lura maza kan fara mutuwa su bar ya'yan su da matan su fata na shine in har na riga ki mutuwa ki kular min da yara na, ki fada musu Dadyn su yana son su, kuma yana kaunar su." Take mood din ta ya canja murya a sanyaye tace "Mu tafi Yaya!" " *Matar Haidar* bata san zancen mutuwa why?" "Yaya baso ne banayi ba, a duk lokacin da akai zancen mutuwa ai muna kara imani da nutsuwa da komawa ga Allah, Yaya kai jigo nane, ka soni tin ban kai abin so ba tin ina ciki, har na fito na zamo baby kake sona da dawainiyya dani har na fara girma so da kulawar kake bani daga Ammi sai kai na fara sani daku kadai na shaku, Yaya ku ne jigo in akace mutuwa akan ku nasan zan shiga wani hali dan Allah ka daina kawo mutuwa akan ka kaji?" Hannun ta ya kamo yasa dayan na share mata hawayen dake zubowa yace "Naji *Matar Haidar* ba zan kara ba mutuwa ba yanzu ba sai na zama tsoho matata ta zama tsohuwa sannan mu mutu tare a burne mu ga kabari na ga nata haka yayi?" Kai ta gyada yace "To smile now!" Murmushi ta dan saki yace "No ban yadda da wannan ba." "Kai Yaya muje rana nayi kaga har 11:16 kai da kace 10 zamu fita." "To ba kece ba!" "Ni kuma? A'ah ni ba ruwa na." "Oh ko?" Ya tada motar suka bar wajen. Aisha suka dauka da Rukayya ya kaisu wajen da za ai musu gyaran kai da lalle ya biya komai sannan ya tafi ya barsu. *Allah ka yafe mana kasa mu cika da kyau da imani Amin* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 19 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* *HML Layuza Kabir Adam. Allah ya sanya alheri da albarka, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri'a mai albarka. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* Tin lokacin ake gyara amarya har karfe shida da ya dawo sannan aka gama mata, amman fa ba karamin kyau tayi ba, gashin nan nata mai tsayi ya kara tsawo sai sheki yake, haka nan lallen ja da baki kamar ajikin ta aka hallice shi dan yadda ya dace da kafar yai kyau sosai da sosai. Lokacin da ya shiga ya *same ta ana kankare bakin kasa motsi yayi sai ido da ya zuba musu ana gamawa ya karasa yana kallon kafar tata mai taushi fara tas sai zanen lallen da yake akai mai kyau da daukar hankali. " *Matar Haidar* kinyi kyau!" Mikewa tayi tana fadin "Wash nagaji wallahi!" Hannun ta ya kamo yana fadin "Sannu ai kwalliyya ta biya kudin sabulu." Kallon sa tayi ya sakar mata murmushi ya matso kusa da ita ya kai bakin sa kunnen ta yana fadin "Ai da zaki yadda da mun tafi gidan mu nai miki tausa na gasa miki jikin ki yadda zakiji dadin sa sosai ko?" Dan hararar sa tayi yace "Ni kike harara ko?" Waya ta dauka ta kira su Aisha akan su fito, suma duk sunyi kyau abinsu. Nan suka fita ya bude mata mota ta shiga ya zagaya ya shiga a hanya ya siya musu kayan motsa baki sannan suka karasa gida suna zuwa ana kiran sallah magariba dan haka sukai ciki shi kuma yai alwala ya tafi masallaci. 9:45pm yana kwance akan gadon sa wayar sa tayi kara hannu yasa ya dauka. Ahmad ne ya kai kunnen sa yace "Kada kace min komai!" Dariya Ahmad yayi yace "To nayi shiru ya shirye shirye?" "Alhamdulillah!" "Gobe sai kamu ko?" "Yes!" "Wallahi naso nai attending bikin nan amman Allah bai yi ba please am sorry my friend!" "In ban hakura ba ka fada min ya zanyi zan zo na dauko ka ne. Ka sani da nasan da haka da, da wuri zan zo na taho dakai ace biki na ba babban aboki kai abun ba dadi sam." "Ga Alkasim nan." "Duk da haka amman kai ma i need you by my side, ina da damuwa Ahmad!" "Meya faru? Wacce damuwar kuma ce zata dame ka bayan nasan *Matar* kace kadai damuwar ka, kuma a iya sanina ita ba zata samar maka da damuwa ba sai dai tai maka maganin ta!" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ahmad nasani amman akan tane dai." "What happened?" "Ahmad you know my problem....." "Me kenan?" "My health problem mana, about my feeling...." "I think this problem has already gone..." "Ina fa kasan *Matar* tawa akwai tsoro, sam taki bari na rabe ta ko dan rage zafi, dan Allah yadda muke da ita nan ai yaci ace komai ya wakana ta saba da komai amman ina? Tin na farkon nan fa, ko hannun ta na rike zata fara ba kyau fa." Ido ya lumshe yace "Am suffering, dan ranan Alkasim ne ya kaini asibiti abin yana son yafi karfi na, ina da kyankyami i can't go for any girl, ita kuma taki ta ban hadin kai, kullum sai tace sauran kwana kaza, i know sauran kwana kaza, but am afraid....... The thing is getting worse wallahi kwana biyu ban bacci bakaga ba duk na rame bani da nutsuwa kullum aba ta a tsaye ga marata a daure kamar dutse...." Ya karashe maganar cikin rauni. Sosai abokin nasa ya shiga tausayin sa. Can yace "Kasan me?" "A'ah!" "Ya kamata ka daure ta da jijiyoyin jikin ta, i know Maryam Love's you and she will not allow you to suffer, so you have to used this change and have her." "Tayaya kai na ya kulle Ahmad!" Nan ya masa wasu maganganu wanda na kasa gane ko me ya fada masa amman dai naga Aliyu yai murmushi yana fadin "Thank you so much friend i really appreciate with your help, please kai ma ka daure kai aure ka daina bin matan waje." Murmushi yayi yace "Zanyi aure matan waje kuma ana rage zafi ne kai bagashi nan ba sai wahalar da kai take amman ni kam da na fita na samu yar Baby zata dan kawar min da sauran sha'awa ta." "Ahmad please ka daina wannan rayuwa. Ba kyau fa. Na sha fada maka ba auren yarinya zakai ba kana yaudarar su, ni Maryam Matata ce kuma kaga yanzu dai remain few days to go...." "Insha Allahu friend tsokanar ka kawai nake insha Allahu kan ka gama amarci ka samo mana Baby nima zan zama ango inji abinda kaji, naso ma tare za ai dan kar kazo kana isa ta da...." "Ya isa dan Allah. Kai dan iska ne wallahi." "Naji amman ka fini jaraba ko?" "Nima Allah ya dauran amman na kusa ka daina ce min jarababbe tinda da na damu *Matata* a gefe kuma ba zakaji wani problem dina ba zatai min maganin shi nasani." "To *Angon Maryam* ana dai bi da yarinyar mutane a hankali kaga yarinya ce sosai." "Kaci gidan ku naga *Matata* ce nafika son ta da tausayin ta dan haka shut up your mouth, ka kyale ni na kwanta nayi tunanin matata ma." "Uhmm ko dai ka kirata ta dan rage maka zafi ko ta waya ne." Ido ya zaro yace "Wa wallahi sai dai ta hargitsani kuma kar kasa yanzu ido na ya rufe na shiga har cikin gida na nemi matata ba zan iya ba." "Ah haba dai ina kunyar ka take ne yanzu?" "Kaga please bari naje nai waya da *Matar Haidar* " "To Haidar *Angon Maryam* sai anjima." Ya kashe wayar. Tana kwance a tsakiyar Aisha da Rukayya ya kira ta mikewa tayi ta koma kan resting chair dake dakin, dariya sukai suka ce "Yanzu Yaa Haidar ba zai bar mu muyi hirar karshe ba,." Tai murmushi takai wayar kunnenta tace "Bakai bacci ba?" "Tayaya zan iya bacci *Matata* na nesa dani." "Haba Yayana ina tare dakai fa. Gani nan kusa dakai." "Bakya kusa dani da kina kusa dani Allah ba zaki bacci ba yau." "Me zamuyi to?" Ta fada tana murmushi. "Kwana zamuyi ibada!" "Yanzu ma ai sai muyi mu ta godiya da Allah ko?" "Wannan godiyar sai muna tare ake yin ta *Matar Haidar* ina kewar ki tare dani." "Yaa Haidar ina tare dakai fa a cikin zuciyar ka, dan haka ka daina feeling loneliness am always with you." "Hmmm to *Matar Haidar* me kike baki kwanta ba?" "Baka kira ni munyi sallama ba, sannan kasan muna tare dasu Aisha." "Sun hanaki bacci ko? To kice in basu barki kin huta ba yanzu zan zo na dauke matata." "To shikenan. Yanzu kaje ka kwanta sai da safe kai mafarki na." "Kullum ne ai." "Oh bye Allah ya tsare min kai ya tashe mu lafiya!" "Amin kema haka *Matata* " Suka kashe wayar akan kirjinta ta ajiye ta tana murmushi, ita kan ta she miss her husband tana son taji ta ajikin sa tana samun nutsuwa. A haka bacci ya dauke ta. Washe gari tin safe gidan ya kara haramar mutane daga gidan Ummah har gidan su Ammi babu masaka tsinke. Itama Maryam tana dakinta ita da su Aisha da Rukayya da yan uwan ta ya'yan yayen Abbi da Yayan Yaye da kannen Ammi, wasu duk sun girmi Maryam amman kuma duk suna son ta dan Maryam ta iya mu'amala da kowa ga ladabi da girmama na gaba da ita wannan yasa take zaune lafiya da kowa. kafin a kira la'asar tayi wankan ta dan Ammi tace basa son african time karfe biyar aka saka dan haka tace biyar tai mata a bakin wajen ko da ba a time din zata shiga ba ta kasance tana kusa da wajen. Tana sallah mai kwalliya da aka dauko har gida tazo ta fara aikinta. Fuska ta dauka don kwararraiyar mai kwalliya Yaya Fadima ta dauko ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan ba da fuskar mutum take canzawa gaba dayanta. Kwalliyar tai mata kyau dan mai kwalliyar ma kanta, ta yaba to daman a bace mai kyau gashi an kara mata kwalliya duk wanda ya kalle ta sai ya kara kallan ta. A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din sai Aisha da Rukayya da wata ta karasa musu kwalliyar a lokacin suma duk sun shirya. Wata mota ango ya turo mai kyau da tsada dan daukar amarya zuwa wurin biki. Wanda Yaa Alkasim ne ke jan motar. Aisha na gaba, Maryam da Rukayya a baya suna zuwa suka fita, Yaya Fadima ta leko tace "Yaa Haidar yana hanya sai kace wata mace ace har yanzu bai gama kintsawa ba." Tana cikin motar da Yaa Alkasim ya sakar mata AC taga shigowar jerin gwanon motocin angwaye wannan yasa zuciyar Maryam ta karu da bugawa. Saitin motar da take anan aka parking motar da Aliyu yake. Yana baya zaune a hakimce yana waya. Yana yi yana murmushi yace "Dan Allah ka barni naga Matata!" "Aliyu wallahi kai jarabbabe ne." "Naji!" Ya fada yana kashe wayar sannan ya fito, yana fitowa ko ina ya dauki kamshi. Motar da yake ya nufa, Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar sa. Daga Maryam har Aliyu sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden material peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi. Hannu ya zura mata dan ya san ya sake ya shiga motar nan to komai zai iya faruwa, hannunta da ya sha ja da bakin lalle da abin hannu ta daura akan nasa ya dago ta, ta fito a hankali, tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me. Nan aka fadawa MC isowar ango da amarya ya saka kida na musamman kawayen amarya masu anko suka fito sukai musu iso bayan su kuma abokan ango ne. A hankali take tafiya wanda shima yake taya ta yin irin takun da take so ba karamin dace da burge kowa sukai a wajen ba. Yaa Rabi'a da Yaya Hauwa matan Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim sai Yaa Ummulkusum da Yaya Zainab da Yaya Fadima da sukai ango iri daya suka karaso suna musu liki da 1-1k tin kan su karasa wajen zaman su. Bayan sun zauna ne aka bude taro da addu'a sannan aka kira Innah kakar Amarya da zuwan ta kenan itama ta karaso ita da kawar ta dan kama ango da amarya. Nan suka kama su aka cigaba da taro kamar yadda aka tsara. Haka aka cigaba da gudanar da taro anci ansha an raba gift na kasko turaren wuta da humra da turaren wuta da muhuci da sauran su. Amarya dai kan ta a kasa ango ta kuwa sam ya kasa dauke idon sa akan ta. Da suka fito fili ma an musu liki daga dangin ango har dangin amarya kowa yayi rawar gani. Ana magariba taro ya watse Yaa Alkasim ya mai da Maryam da Aisha da Rukayya, Ango kuwa anan sukai magariba sannan suka wuce daya daga cikin gidan da Abbah ya basu dan saukar bakin sa na nesa. Gida ne babba akwai komai a ciki, abinci kuwa Mamah ke akai musu kala kalar abinci. Washe gari dinner tin yamma aka farai mata kwalliya sai da akai magariba aka gama sallah tayi sannan ta saka kayan ta aka kara gyara mata kwalliyar ta. Kayan ta na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne baki sai adon golding yellow a jikin sa. Riga da siket aka yi mata. Fadar irin kyan da tayi bata baki ne domin amarya ta fito a amaryar ta tai kyau sosai da sosai. sai dai ace masha Allah kowa ya ganta sai ya furta masha Allah. Tini aka dauke kowa aka tafi dasu sai ita da Aisha da Rukayya da suke jiran zuwan ango. Mota biyu ce suka zo daukar amarya daya Ango ne a ciki wacce za a dauki amarya daya kuma Ba kowa su Aisha za a dauka da Rukayya wanda Yaa Alkasim ke tuka motar. Wani abokin sa ne a gaba yana jan motar shi kuma yana baya tinda suka fito daga gida ya kasa dena kallon Maryam, kunya ya bata ma kan ta a kasa, ta dan dago ta kalle shi, Itama yayi mata kyau sosai yana sanye da golding yellow din shadda tai masa kyau sosai da sosai. Wani kyau na musamman taga yai mata. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu ya kamo hannun ta mai taushi wanda a tare duk suka lumshe ido. Janyo ta jikin sa kawai yayi ya daura kan ta akan kirjin sa, ido ta lumshe shima haka a haka suka karasa wajen dinner basu san an zo ba sai da sukaji rufe motar da abokin sa yayi. Ido ya bude yaga sun iso wajen. Dago ta yayi ya gyara zaman babbar rigar sa sannan ya kamo hannun ta yace " *Matar Haidar* gobe ne fa!" Kasa tayi da kan ta, yai murmushi yace "Ina son ki, ina kaunar ki, kada ki taba mantawa da Ni Haidar naso ki, kada ki taba mantawa da duk duniya bani da tamkar ki, kece sirri na." Knocking glass akai ya saukar da glass din kasa yace "Ya akai?" Waya Alkasim ya miko masa yace "Ahmad ne yace yana kira baka dauka ba." Amsa yayi yace "Dan jaraba me kuma zan masa." Ya kai kunne yace "Menene?" Dariya Ahmad yayi yace "Ni nasan in kana tare da *Matar Haidar* ne kadai kake min wannan abun saboda bani da mahimmanci a gun ka in kuna tare ko? Ba komai kun karasa wajen ne?" "Yess yanzu zamu shiga!" "Ok a shiga lafiya ayi taro lafiya a gama lafiya nima na gama da wannan garin anjima zan tafi dayan in na siyi sim zan kira ka da na sauka insha Allah!" "Allah ya tsare ya kai ka lafiya." "Amin Ango tafiyar awa goma sha ce nasan zamu sauka a wata kasar kan mu karasa ban sani ba ko zan samu nai maka wishing Happy marriage life but i wish you all the best and may Allah bless your union, Happy Marriage life once again!" "Thank you so much!" Yai dariya yace "sai washe gari tariya zan kira naji ya kuka kasance." "Dan iska kasan wa zaka tambaya ba dai ni ba." Ya kashe wayar yana bude kofar juyowa yai ya kalle ta yace "Wannan dan isakan ne." "Kai Yaya, Yayan nawa!" "Oh ni kuma menene naki?" " *Miji na* , *Jigonah* " Ido ya lumshe yace "Muje kar kisa nayi abinda zakice -Ba kyau fa- " Ya fada yana kwaikwayar muryar ta in zatace ba kyau fa. *Allah ka jikan mu kasa mu cika da kyau da imani* *Amin* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 20 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* *HML KHADIJA SANI DAUDA AND MY SIS HASSANA, ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA YA KAWO ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN* Ya fita ya kamo hannun ta haka suka karasa wajen aka shiga da ango da amarya yau sosai wajen ya hada manyan mutane dan abokan Aliyu duk sun zo yau dan gobe daga juma'at za a daura aure dan haka an kara samun ba'ki masu kwana. An gudanar da biki yadda ya dace cikin nustuwa, girma da ilimi kowa abin ya burge shi, an yanka cake an sha rawa da hutu kamar ba gobe. Suna daga zaune ta hango Yaa Alkasim sit din su daya da Aisha suna ta hira murmushi tayi tace "Allah tabbatar da alheri zan so ki zama cikin zuri'a ta." Rukkayya ta gano da abokin Aliyu suma zaune tace "To ni kam da Yaa Ahmad nai miki kamu Allah ya hada kowa da rabon sa." "Tunanin me kike *Matar Haidar* " Kallon sa tayi tana murmushi nan masu huta suka samu abin yi, tai kasa da kai tace "Tunanin *Miji na* nake" "Gani wane tunani na zaki, ki ta kallo na kawai!" Ta kara dagowa sai tayi saurin yin kasa da kan ta a kunyace. Sai wuraren sha daya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Aliyu ya dubi Maryam wacce duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Key ya amsa wajen Abokin sa. Yace "Ka tafi zan mai da Matata daga nan a gida zan kwana sai da safe kawai." "Allah tashe mu lafiya." Sai da yaga tafiyar kowa sannan ya dawo cikin hall din wanda Maryam ce kadai a ciki. Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji dan yadda yake dan murza hannun nata cikin yanayin tsokanar mutum. Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin direba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan cinyar sa. A haka ya tayar da motar ya soma tuki cikin nutsuwa. Shiru tayi jin yadda yake mata tsoro da fargaba dan tini wani lokaci da ya wuce da haka ta faru, dan haka kanta ta jingina a jikin kujera kawai ta zubawa titi ido. A hankali yace "Tunanin me kike yi ne" Ta dan rufe idonta ta bude tace "Babu komai" muryar nan tata a sanyaye. "Are you sure, har tunanin abinda nake miki da wanda zai biyo baya?" Fuska ta marairaice ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda abun baya ya dawo bata sabo dal tin jiya ma ta fara tuna abubuwan bare yau da taga sauran kwana daya ta zama mallakin sa kowa ya shaida tasan Aliyu zai iyai mata komai duk kunyar sa akan ta zai iya yin komai. "Bana so ina ganin ki cikin tsoro Baby na." Ajiyar zuciya ta sauke yace "Zamuje gida zan baki sakon da na ajiye miki a daki na." "Da ka bari gobe ko Yaa Abdullah ka bawa ya kawon." Kai ya girgiza yace "Ke da kanki zaki amsa." A haka ya karasa cikin gidan su da mai gadi ya bude masa gate har bakin part din sa ya kai motar sannan ya fita ya zaga ya bude mata ta marairace masa fuska tace "Dare fa Yayi Yaya ka bari gobe." "Wai meyasa kike min musu ne *Matar Haidat* ba kyau dai kin sani ko?" Yana fada yai ciki ransa a dan bace. Compound din ta tsaya kallo ba kowa dan haka da sauri ta nufi wajen gate sai kuma ta tsaya tana tunani can ta juyo tana girgirza kan ta, ta nufi kofar dakin nasa. Baya falo dan haka ta nufi bedroom zaune ta ganshi ya cire rigar sa da babbar riga daga shi sai singlet da dogon wandon kayan da ya cire. A gaban sa ta durkusa tace "Kayi hakuri gani?" Bai kula ta ba ta marairaice kamar zatai kuka tace "Dan Allah kada kai fushi dani." Dagowa yai ya kalle ta sai ya mika mata hannu ta kama ya janyo ta ya zaunar akan cinyar sa. Yace "Yaushe ne daurin auren mu?" "Gobe ne!" "Har yanzu akwai wata rashin yarda tsakanin mu?" "Babu Yaya ban taba jin zaka cucen ba ban taba jin ban yadda da kai ba, kullum ina daukar ka wani sashe na. Kai ne sirri na." Kafar ta ya kamo ya cire mata takalmi yana mamatsa kafar tata yana jin kalaman ta masu sanyaya masa zuciyar sa. "Kece sirri na kinsan komai akai na ban boye miki ba abinda iyaye na basu sani ba akai na kinsan shi kinsan halin da nake ciki ko?" Kai ta gyada masa zuciyar ta na bugawa kada abinda ya faru baya ya kuma faruwa dan da haka aka fara. "Good girl, na sani na tabbatar ba mai so na sama dake ba mai tausayi na sama dake," "Me kake so Yaya me kake so nai maka ka daina kashen jiki da wadan nan kalaman naka." Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafo da kansa, suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba. Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Ya jima yana kissing nata sannan ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo cikin so kauna da shauki hadi da sha'awar ta. Hannun ta ya saka a kan kirjin sa yana fadin "Zuciya ta ke take muradi, ke take so, da son kasancewa dake." Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna, hawaye ne ya fara zubowa daga idon sa murya na rawa yace "Wallahi yau in ban same ki ba bazan iya kawai gobe ba, please ki taimaken *Matar Haidar* gobe kowa zai shaida!" Kai ta hau girgizawa yace "Ba zaki iya ba ko?" Kanta ta kifa a kirjin sa tace "Tsoro nake ji, tsoro naje, kada Allah ya tsinen kuma!" "In dai nine zan yafe miki sai dai zan kwana cikin wani mawuyacin hali." Kan ta, ta kifa a jikin sa tana fadin "Tayaya zan barka ka kwana cikin mawuyacin hali, tayaya? ba zan iya ba." "Allah miki albarka *Matar Haidar* " Ya fada yana zare mata head din kan ta, ya ajiye a kasa ya fara zuge mata zip din rigar ta sannan ya zare siket din ta daga ita sai vest da underwear. Kan gado ya ajiye ta ya shiga bandaki yayi wanka ya fito sanye da gajeren wando. Gaban mudubi ya karasa ya shafa turarukan sa masu dadin kamshi sannan ya nufo kan gadon ya kwanta ya janyo ta jikin sa shiru tayi tana jin wani irin fitinennen kamshin jikinsa da sanyin dakin suna ratsata. Hannunsa yasa ya kamo hannunta na dama ya juyota rigingine. Ya dan sunkuyowa kanta, hakan yasa suka dan fidda numfashi a tare, cikin nutsuwa taji ya manna mata kiss a goshinta, tare dasa tafin hannunsa bisa nata tafin hannun. Cikin wani irin sassanyan numfashi ya cusa kanshi tsakankanin wuyanta da kafadarta hancinshi ya manna kan fatar wuyanta, idonshi ya lumshe tare da kara shakan kamshin jikinta. Ita kuwa Maryam wani irin harbawa zuciyar ta take, a hankali ya dawo da kanshi kan fuskarta. Kasa yayi da bakinshi. Harshensa ya dan zaro ya manna da tattausan lips dinta, lasarsu yayi tare da fidda wani sauti mai tada hankali wanda yasa tsigar jikin ta tashi gaba daya, a hankali taji ya zira mata harshen sa cikin bakinta, A hankali ya lalibo harshen ta ya fara tsosa wanda haka yasa jikinta ya fara tsuma rumtse idanunta tayi da ƙarfi jin yadda yake tsotsar harshen nata. Kasa yayi da hannunsa cikin wuyan vest din ta, ido ta runtse ta kamo hannun sa tana girgiza kan ta. Wani kiss ya karayi mata mai cike da sabgogi masu birkitarwa. A hankali ya ture hannunta kana ya dage vest din da karfi yayi kasa dashi. shiru tayi tana jinsa saboda karkarwan da jikinta keyi ya fara yawa. hannunta sa zare cikin hannun vest din, ya zare shi kana ya jefar dashi gefe. Ya rage daga ita sai Bra da dogon siket din ta a jikin ta, zare bakinshi yayi daga nata. Haka yasa ta juya da sauri ta bashi baya tare da hade hannunta a kirjinta ta ƙanƙame kanta gam tana jin yadda zuciyarta ke buga lugude. shi kuwa matsowa ya kumayi a hankali ya manna ƙirjinsa da bayanta, Ɗan ronƙofowa yayi kanta ya cusa fuskarshi tsakanin wuyanta da kafaɗunta. Yana shaƙan ƙamshin turaren dake jikinta hannunshi ɗaya kuma bisa cikinta ya ɗaurashi a hankali murya can ƙasa yace. " *Matar Haidar* " Shiru tayi bata amsa mishi ba, sai wani tsuma da jikinta keyi. "Ma'ul Ayn!" Ya kuma kiranta a hankali cikin kunnenta. Murya can ƙasa tace. "Na'am". "In bari?" Kai ta gyada ya sake ta ya juya mata baya, ido ta lumshe hawayen dake ciki ya fara zubowa to ita yaya zatayi ne? Cikin sa ya rike yana juyi akan gadon ga gumi dake tsatsafo masa duk AC dake dakin. Kan sa tayi tana fadin "Menene cikin ne? Ayyah sannu ina maganin ka?" Hannun ta ya kamo ya daura akan marar sa tai tauri ga wani zafi da tayi wanda ya masifar bata tsoro yace "Danna min ko zai daina ki danna min!" Wayar sa ta lallubo ta dauka ta shiga call log number Ahmad ce a farko tana kira aka dauka yace "Kaci sa'a yanzu zan shiga jirgi har an tashi kenan." "Ba shi bane nice Maryam ce!" Ta fada cikin tashin hankali. "Lafiya Maryam me ya faru ina Aliyun?" Kallon Aliyu tayi wanda yake cikin mawuyacin hali tace "Gashi nan ciwon cikin sa ne ya tashi ya zanyi dan Allah marar sa tai zafi da tauri." "Nutsu kiji!" "Ina jinka!" "Ke *Matar Aliyu* ce dan haka kiyi hakuri ki taimake shi ki bashi ya zubar da abinda ke marar sa in ba haka ba komai zai iya faruwa ko da kin biya masa bukatar sa ba ma dole ne ya fita daga risk din da yake ciki ba dan haka kiyi hakuri ki taimaki mijin ki aboki na." Kuka ta saka ta ajiye wayar ta nufe shi tana fadin "Kayi hakuri Yaa Haidar kayi min duk abinda zakayi dan Allah ka tashi kaji." Ta juyo dashi tafin hannunsa yasa yana shafa cikin ta hankali. wani irin numfarfashi ta fitar a hankali a hankali, yayinda zuciyarta ke buga dib-dib ya zatayi? Yatsarshi manuniya ya zira cikin hudan cibiyarta, yana ɗan zagayeshi ta ciki, kana yayi sama da yatsar kana yayi cikin hudar cibiyar a hankali. cikin raunin murya mai nuni da fargabarta a hankali cikin rauni tace. "Yahhh Haidarrrr ashhh" A hankali yayi sama da hannayeshi duka biyu. Ya balle bra din ta ya ɗaurasu bisa mayan maman ta wanda suke farare tas a tsaye dasu. A tare sukayi wani irin numfashi wanda yake gab da barin gangar jikinsu. A hankali ta ɗago hannunta ta ɗaura kan hannunshi dake murza maman ta riƙe ba tare da ta janye nashi hannun ba. iska ya hura mata cikin hudar cibiyar ta har saida ta maƙe kafaɗarta a hankali yace "Kece sirri nah!" Cikin wani irin yanayi ya ɗan sunkuyo da kanshi, dai-dai kan hudar cibijiyarta, yayin da hannun shi kuma suna can sama maman ta. Wata irin fitinenniyar miƙa mai kashe dukkan sasan jikinta tayi lokacin da taji ya zira harshensa cikin hudan cibiyarta. Shiru sukayi gaba ɗayansu sai wasu tagwayen numfarfashi masu nauyi suke sauƙewa, kana zuciyoyinsu na bugawa. Wani irin zira harshen yakeyi yana in and out tare da nitsa hancinsa cikin fatan cikinta. Cikin wata iriyar murya mai cike da rauni tace "Ahhhhhhh Yaahhh Haidarrrr " Haka ta kirashi cikin wata daburtacciyar murya. "Uhummmmm!" Ya fidda sautin ba tare da ya daina abinda yake ba, A hankali ya ƙara yin sama da hannunsa dake ƙan ƙirjinta, Zare harshensa yayi kana a hankali yayi ƙasa da kanshi har ya iso kugun ta, siket din ya kama yai kasa dashi. haɗe bayanta yayi da ƙirjinsa sosai fatarsu ta manne da juna, hannunshi yasa kan ƙirjinta ya fara shafawa tare da murza bakin jajayen nimple ɗin ta. Cikin rauni da fita a haiyacin ta tace "Yaahhh Haidarrr achhh uhmmm Ba kyau fa." A hankali murya na rawa ya raɗa mata. " Ay... Ayyah *Matar Haidar* kar kice haka, kin dauki alkawarin kula dani da bani duk kulawar ki da sauke hakkin ki." Gaba daya baya cikin nutsuwar dan ji yake zuciyarshi na gab da faso ƙirjinsa ta fito waje, hannunsa ya kara daurawa kan nasu wani irin gigitaccen shafa da matsa mai cike da fitina da ɗimautarwa. Wanda ta sauke masa wani numfashi mai sauti cikin kunnen sa. Wanda ya kara hargitsa da kwance masa lissafi. Yatsunshi yasa ya kama nimples ɗin ta duka biyu yayi musu wani irin sahihin murza mai cike da taka tsantsan yadda bazataji zafiba. Ƙara cutsa yatsunta tayi cikin sumar kansa data meda hannunta ciki. A hankali yaji alamun hawayenta na ɗiga kan hannunshi kana jikinta duk yana tsuma da kerma dib-dib-dib haka yake jin alamun bugun zuciyarta. Cikin sanyi yayi ƙasa da hannusa ɗaya, ya zura cikin wandon ta, wanda zuwa lokacin gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi. "Uhmm Uhmm Yaa Yaa Ha.. Haidarr..." Maganar ta kwace ta kasa karasawa saboda jin hannun sa na shiga cikin wandon ta. A kunnen ta ya fara magana da kyar yace " *Matar Haidar* da dadi?" "Ni ka bari kayi haƙuri!" Zame wandon yayi gaba daya yace "Wallahi ba zan iya ba *Matar Haidar* ki taimakam!" "Yaa Haidar da zafi fa!" "A'ah Baby." A hankali ya ronƙofo kanta, cikin sanyi murya can ƙasa yace " *Matar Haidar* meyasa jikinki keyin rawa?" Cikin rawan murya tasa hannu ta riƙo damatsan hannunsa a hankali tace. "Tsoro nakeji Yaa Haidarr ina jin tsoron zafi..... zafi...." Kanshi ya maida bisa lafeffen cikinta, cikin hudan cibiyarta ya zira harshensa, da sauri ta rumtse idanunta saboda wani irin masifeffen daɗin da taji yana ratsawa cikin hudan cibiyarta. Hannunsa ya miƙa ya ɗaurasu kan tamtsan-tamtsan breast ɗin ta. yatsunta ta cusa cikin sumar kanshi, tare da fidda sassanyan sauti. "Ahhhhhhh Wayooo!!! Ammiii!!! Ammi!!!!" Zaro harshensa yayi kana ya fara lasan fatar cikinta tare da kissing cikin har zuwa sama. A hankali ta buɗe bakinta sai kuma ta kasa yin magana sabida, yadda ya zura harshensa cikin bakinta. Wani irin fitinenne kiss tongue to tongue yake yi mata mai, rikitarwa. Hannunshi kuma yana bisa breast ɗin ta yanayi musu wani murza, kanta ta fara jujjuyawa. A hankali ya zare harshensa ya dawo dashi bisa ƙirjinta, harshensa ya manna kan nimple ɗin ta ya fara yi mata wani irin tsotsa mai rikitarwa. Wani irin fitinenne zabura yaji abar sa tayi tare da miƙewa zamɓal ta fara harbawa, tamkar zataci babu. Hannunsa ɗaya kuma yana kan ɗaya breast ɗinta. Yana matsawa, gaba ɗaya ya gigitata, ya hautsina mata lissafi, jikinta yayi weak sai tsuma da yakeyi. A hankali yayi ƙasa da hannunshi yana shafa cikinta har zuwa kan mararta. Cikin wani irin yanayi ya tura yatsunshi cikin pp din fa, wani irin zillo tayi tare da buɗe baki tace. "Washhhhh, Achhh Yaa Yaaa Hai.. haida...darr". Sama yayi da sauri ya hade bakin su ya farai mata wani irin salo a pp din ta, Kerma jikinta ya fara, a gigice take jan numfashin tare da cafkar harshen sa tana tsotsa kamar ba gobe, hannunta kuwa na cikin sumar kan sa. Hannun ta daya ya kamo ya danka mata abar sa dake a mike, wani irin zabura da razani ne da tsoro suka risketa lokacin ɗaya............. A hankali ya sunkuyo da kanshi ƙasanta. Ji tayi wani abu ya tokare mata a gefen cikin ta ga wani fitsari da take ji, Aliyu kuwa kan sa na kasan ta yana jin Wani irin masifeffen ƙamshi turaren miski ne mai ɗan karen daɗin shaƙa ya bugi hancinsa, cikin rawan jiki ya manna bakinshi bisa pp ɗin ta. wani irin yunƙura tayi tare dasa tafin ta damƙi damatsan hannunsa da ƙarfi. cikin wata iriyar fitinenneyar murya tace. "Ahshhhhhhhhyyy Ciki na, wani abu a ciki na ya tokare wayoo zanyi fitsari Yaa Hai... " Yadda ya kara zura harshen sa yasa ta kasa karasawa, Hannunshi yayi sama dashi dai-dai kan marar tata da cikin ta da sauri ya bude idon sa sai hawaye kuma, shin me yake ji me kenan? Wani farin ciki ya taru ya cika masa zuciyar sa. A hankali ya fara ɗan shafawa. Yayin da ɗaya hannun kuma yana can sama yana murza breast ɗinta da mulmula nimple ɗin. Ita kuwa Maryam tuni hawaye keta shatata a fuskarta, murya na rawa jiki na rawa take cewa. "Yayahhh ina tsoro ni dai ka barni, bazan iyaba. Ka sakeni zan tafi gida, wayoo mutuwa zanyi Ammi ki yafen ki yafen Ammi...." *Allah ka yafe mana, kasa muyi kyakyawan karshe, Allah kasa mu cika da kyau da imani.* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 21 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Cikin sanyi ya buɗa sawunta kana yakawo bakinshi dai-dai kunnenta a hankali murya na rawa yace. "Matar Haidar, zan miki a hankali. Please ki bani hanyata" Cikin kuka tace. "Ciki nah Yayahhh, ka duba min wani abu anan ka duba min!" Ta fada tana daura hannun sa akan mararta. Kanshi ya cusa a wuyanta tare da cewa "Naji Ma'ul Ayn, Ba wata matsala bace kema bukatata kike?" Hannunshi yasa ya buɗa sawunta kana yasa hannunshi ya kamo abarsa ya saita ta yayi da muhallinta. Tare da cewa. " *BISMILLAH ALLAHUMMA JANNIBNAL SHAIƊAN WA JANNIBAL SHAIƊANA MARAZAƘTUNA.* " Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi jin wannan abar sa na ratsa jikin ta. "Wayoo Yayahhh wayooo Yahhh Haidar!!! Ammi!! Ammi!!! La'ilaha illahu Muhammad Rasulillahi (SAW) dan Allah ka bari zan mutu........." Lokacin ya shige cikin jikin ta, Ƙanƙameshi tayi da masifar ƙarfi tare da yunƙurowa ta cusa kanta cikin ƙirjinsa wata zufa ce ta karyo mata. Aliyu kuwa ba abinda yake sai ambaton sunan Allah da tasbhihi ga Allah yana fadin "Alhamdulillah, Yah subahanallah! Subahanallah!! Allahu Akbar! Subhnallahu wabihamdihi subhnallahu azim, Astagafurillah, Lahaila wallakuwata illa billah........" Sune kalaman da yake iya maimaitawa da alamun a gigice yake. Maryam kuwa cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa tare da riƙo damatsan hannunsa ta saki kuka mai cike da rauni sabida ta fara galabaita shi kuwa baiji bai gani bare ya sararamata, "Kiyi hakuri ki yafen Maryam *Matata* , Maul ayn, *Matar Haidar* ki yafen Allah yai miki albarka ya albarkaci rayuwar ki da zuri'ar mu, sam banyi dan son rai na ba, babu yadda zanyi ne, kiyi hakuri, ke jaruma ce *MATAR HAIDAR* ki daure kinji. I love u, i really love you Matata. Kece kadai sirri na kece kadai hasken idaniyya ta kece kadai jigo na, kece kadai garkuwa ta, uwar ya'ya na. Ina son ki da kaunar ki har ban san adadi ba. Allah ya yafe mana ya hadamu a aljanna. Amin......" Haka ya dinga mata addu'a da sumbatu tin tana jurewa har taga abin ba na karau bane, dan haka Kuka ta kuma sawa tare da ruggumeshi gam-gam a jikinta, tana fadin "Wash, wash, Wayyo ashh na gaji Yaa Haidar, baya nah uhmm uhmm." Aliyu kuwa a kiɗime yayi mata wata irin fitinenneyar kuma gigitacciyar rumgume, a hankali ya raba jikin ta da nasa ya koma gefe sai kuma ya lumshe idonsa saboda, wani irin fitinenne zazzaɓi mai masifar zafi da suka ƙasusuwan jikin daya rufeshi a take a lokacin ɗaya gaba ɗaya jikinsa karkarwa ya fara. So yake ya tashi ya tsarkake musu jikin su amma ya kasa saboda yadda zazzabin ya rufe shi. Jikin sa ya janyo ta ya rumgume tsam kamar wanda za a kwace masa ita. Sannan ya mika hannu ya jawo blanket ɗin ya rufesu da kyau. Tana ji a hankali yana kiran sunan ta daga yace " *Matar Haidar* " Sai yace "Ma'ul Ayn!" Ko kuma yace "Matata," "Nurul Hayyaty! Habibty Allah miki albarka!" Haka ya dinga fadi cikin zafin zazzabin hannun sa kuma akan cikin ta yana shafawa a hankali a hankali. Ita kuwa Maryam hawaye take ta kwaranyarwa. Tare da Shessheƙan kuka mai cike da rauni da wahala. A haka tana kukan baccin wuya ya saceta. Ko a baccin shessheƙan kuka takeyi tare da wasu surutai. A hankali ya juya kwayar idanunsa dake lumshe wanda ko buɗe su ya gaza, muryarta yakeji a hankali tana cewa. "Yaaa Haidarrr ciki na!" Duk da yanayi da yake ciki bai hanashi daura hannun sa akan cikin ba. Duk da yasan Maryam da raki da shagwaba. Suna a haka aka kira sallah asuba da kyar ya janye jikin sa anata, wanda har lokacin bacci take a hankali ya mike yaji marar sa sakayau hannu ya saka ya shafa tare da furta "Alhamdulillah!" Ya shiga bandaki yayo alwala yazo ya saka kaya ya wuce masallaci. Tare da Abbi sukai sallah yau wani nauyin Abbi ya karaji dan da kyar ya iya gaishe shi kan sa akasa kamar zai shige cikin kasa. Bai jima a masallaci ba, ya mike ya nufi cikin gidan su direct sashen sa ya wuce, yana shiga ya same ta kwance a yadda ya barta da sauri ya karasa ya dago ta yana fadin " *Mayar Haidar* " A hankali ta bude kumburarrun idanun ta da suka sha kuka "Am so sorry Matata! Kiyi hakuri kinji. Nine ko?" Kai ta gyada tace "Yaa Haidar wannan har yafi wancan zafi Yaa Haidar ciki na ciwo yake min!" Hannun sa ya daura akan cikin yana fadin "Kiyi hakuri ba zan sake ba, tashi muje kiyi wanka ki sallah ki tafi gida kar Ammi ta neme ki!" Kai ta gyada. Ya dauke ta suka shiga bandaki yai mata wanka bayan ya gama ya barta tayi na tsarki sannan ya nado ta cikin towel ya ajiye ta akan gado. Wardrobe ya bude ya dauko mata rigar sa ta saka under wear din ta da katon hijab ya bata ta saka ta mike a hankali ta tada sallah. Tana idarwa ta jingina kan ta a jikin gado. Karasowa yayi yace "Zo na duba ki kinji!" Ya kamo hannun ta ya mikar ya dauke ta ya daura akan gado hijab din ya cire mata ya dage rigar ta yace "Ina ne yake ciwo?" "Jiya da kana min abun wani abu ya tare min a ciki na." Murmushi ya saki yace "Yaushe rabon da kiyi ciwon mara?" "Tin wancan karon fa!" "Wane karon?" Ya tambaya yana shafa fatar cikin. Fuska ta shagwabe tace "Da ka dauken a makaranta mukai....." Sai kuma tai shiru yana murmushi yace "Mukai me?" Hannun sa ta buge ta mike tace "Ka ban magani Yaya!" Janyo ta yayi yace "Matata sirri nah, Matar Haidar, Farin cikin Haidar, Jigon Haidar, Hasken idaniyyar Haidar, Ruwan idaniyyar Haidar!......" Hannuta ta daura akan bakin sa tace "Yaa Haidarr!" Kallon ta yayi yace "Na gama gamsu cewa duk duniya, kece sirrina Maryam! Dole ki zamo suturata, kamar yadda nima zan zama suturarki, kamar yadda Allah (S.W.A) ya fadi." Ya ƙarashe maganar yana manna bakinshi da nata, lips ɗin ta duka biyu ya ɗan kamo ya tsotsa a hankali. sannan ya sake, kiss ya manna mata a goshi kana ya manna mata a tsakanin wuyanta da kafaɗarta, harshensa ya zaro ya manna bisa wuyanta yana ɗan lasawa. Hannun sa ta kamo tace "Yaa Haidarrr!" "Uhmm *Matar Haidar* !" Ya fada yana shinshinar wuyan ta, sannan yace " *Matar Haidar* yau duniya zata 'kara tabbatar wa da nine sirrin ki nine mijin ki." "Yauwah ina son muyi magana Miji nah!" "Uhmm ina jinki!" "Yaa Haidar menene hukuncin auren da zamuyi bayan...." Sai tayi shiru, hannunta ya kamo yace "Hmmm menene hukuncin auren mu, to yanzu ya za ayi me kike ganin za ayi?" "Yaa Haidar mu sanarwa iyayen mu halin da muke ciki!" "Kina ganin ba matsala?" "Insha Allahu babu Yaya." "Ok shikenan anjima zan fadawa Mamah ki fadawa Ammi ko Abbi zaki fadawa?" "No Ammin dai!" "Ok ki fada mata." Ya fada yana kai kunnen sa cikin ta, shiru yayi can ya dago ya kalle ta yana murmushi yace " *Matar Haidar* Uwar ya'yan Haidar Ina son ki, ina kaunar ki, ki yadda da son da nake miki, ki tayani raino da bawa ya'yan mu tarbiyya, ki fada musu Dadyn su yana son su, ki fada musu ina kaunar Momyn su dasu dukkan su. Ina kaunar ki Maryam, ina kaunar ki Maryam, ina kaunar ki Maryam!" "Nima ina kaunar ka Yaa Haidarr!" Rumgume ta yayi yace "Zanyi kewar ki *Matar Haidar* " Ido ta lumshe sai kuma ta bude a hankali. Da sauri ta mike Aliyu ma ya mike yana fadin "Kina yi a hankali fa." Fuska ta shagwabe tace "In Ammi ta gane ba a gida na kwana bafa?" "Dadin yadda zaki fada mata meke a tsakanin mu ma kenan." Hararar sa tayi tace "Kai Yaa Haidar ni dai na tafi." Ta juya zata tafi yace "Tsaya na rakaki mana." "A'ah!" Bayan ta yabi da sauri ta fice ta nufi gate yana tafe a bayan ta, har suka karasa bakin gate inda mai gadi yake, gaishe shi tayi ta fita Aliyu yabi bayan ta, tana shiga gida ta juyo ta daga masa hannu tayi cikin gida murmushi ya sakar mata ya juya ya fita. Tana shiga ta nufi dakin ta, su Aisha duk suna kwance suna bacci da wasu yan matan. Kan resting chair ta zauna tana mai lumshe ido tino abinda ya faru jiya tayi take tsigar jikinta, ta tashi. Wayar ta taji tana kara ta dauko ta zauna tare dakaiwa kunnen ta Yaa Haidar ne kwanciyya tayi tace "Yaya lafiya?" "Gani kwance a kan gado ina shakar kamshin turaren ki, wallahi kewar ki ce ta fara damu na, ban gaji da jin dumin ki da Jin muryar ki mai zaki ba." "Yaya Haidar kenan bana son kanasa damuwa da tunani aranka ka ba kada ka manta ni taka ce ba tin yau ba kawai dai yau zan dauwama taka, a karkashin kulawar ka mu kasance tare a ko da yaushe amman menene sabo, in doki ne nasan ba abinda zakai doki a waje na." "Waya fada miki? Wallahi Allah kinji nace Allah ko nafi jin dokin akan before a yanzu nafi bukatarki ba abun haramci mukai ba da Allah zai saka mana tsanar juna. Ki sani ina sonki kuma ba zan taba daina sonki ba har abada. Ki yadda dani *Matar Haidar* ki yadda ko bana nan zan bar miki jigo wanda zai taimaka miki wajen cika burin ki i love you my wife!" "Love you more Husband. Allah ya bamu zaman lafiya ya kade fitina ya hade kan mu ya kara mana fahimtar juna Amin!" "Amin Amin *Matar Haidar* fada min me zaki tanadar min anjima!" "Ni kuwa me zan tabadar maka bayan dan gyaran da akai duk ka shanye abinka" "Ai nasan anjima za a kara baki wasu kuma ba dukka na shanye ba fa na rage na anjima." "Kai Yaa Haidar!" Murmushi yayi yace "Da gaske man." "Ni dai ba ruwa na." "In fada miki wani abu da zaki sha ki kara...." Wayar ta kashe tana dariya. Kira ya kara, kamar ba zata dauka ba ta dauka, "Saboda me zaki kashen waya, ni kai na nakewa fa dan bake zakiji bane da, da gudu zaki ce eh to ni ba zan sha abinda zai sa kijini so sweet ba." "Yaa Allah yaushe Yaa Haidar ya koma haka ne?" Dariya yayi yace "Tin da nasan wacece Matata." "Iyeee wacece ita to?" "Itama jarababbiya ce kamar yadda Ahmad yake ce min jarababbe." "Lah lalah wallahi ni ba ruwa" "Oh ko zan mai daki da ruwan ki, indai kina tare dani. zan miki text din abinda zaki sha in babu kuma yanzu zan bayar akawo miki. Ko da yake Matata akwai sweet kin tina waccan karan bani da haufi akan ta nayi dace sosai ga ta kyakyawa ga ilimi ga tarbiyya ga ni'ima....." "Ni dai ba ruwana." Aisha ce ta tashi tace "Oh ku wai tin safe har kun fara soyewa dan Allah Yaa Haidar yai hakuri anjima dai za a kaiki dakin sa mu huta." "Kana jin ta ko Yaa Haidar?" "Barni da ita zan kamata ne. Kuma ai matata tace." Ta mike tace "Bari naje na gaida Ammi!" Ta fita ta nufi dakin Ammi, Ammi zaune ita kadai zama tayi a kasa tace "Ina kwana?" "Lafiya lou kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah!" Shiru tayi Ammi ta kalle ta tace "Lafiya?" "Ammi daman ina son muyi wata magana ne!" "Ina jin ki." "Ammi daman ni da Yaa Haidar ne.....' "Assalamu alaikum!" Yaya Ummulkursum tai sallama. Amsawa Ammi tayi ta kalle ta. "Ammi, Abbi ne ke kiran ki." "To!" Ta fada tana kallon Maryam tace "Ina zuwa." Yaya Ummulkursum tace "Taso muje na karasa baki wancan hadin!" Ta mike tabi bayan ta. Bangaren Yaa Muhammad suka nufa sai ga Yaa Abdullah nan da sauri ya shigo da leda a hannun sa. Mikawa Maryam yayi yace "Inji Yaa Aliyu!" "Nagode!" Ta fada tabi bayan Yaya Ummulkursum. Suna shiga sukai wani daki mai mata gyara ce a ciki, tace "Jiya ba ai ba yau ma ba za ai bane?" Kai ta girgiza tace "Gani ai!" Yaya Ummulkursum ta amshi ledar hannun ta tace "Menene wannan?" Ledar ta mika mata ta amsa ta leka tace "Wa ya baki wannan kayan arzikin bari na gyaro miki!" Ta shiga kitchen tai blendung ta zuba madara ta kawo mata tana sha ana mata gyara har sha biyu sannan aka gama ta shiga tai wanka ta fito aka sa ta fara turare jikin ta. Sai daya saura sannan aka dauko mata kayan wani farin less mai adon golding ajiki ta saka wasu dan kunne da sarkar gold wanda yake har kan kirjin ta haka abin hannun ta da agogon ta duk na gold ne. Farin mayafi ta yafa mai golding kala ta saka golding half cover. Ba ai mata kwalliya ba amman tayi kyau har ta gaji da kyau. Aliyu kuwa yana dakin sa ya fito da kayan da wani farar shadda wacce akai yar ciki da babbar riga ya ajiye akan gado yana zaune wayar sa a kunnen sa yana fadin "Kun shirya dai ko dan yanzu zan fito saura rabin awa dan Allah ku shirya gani nan." "Ok sai ka karaso." Mamah ce ta shigo da sallama ya amsa yana dagowa ya kalle ta. "Neman me kake min?" "Mamah wata magana ce daman zamuyi!" "Kuma sai dole yanzu Aliyu." "Tana da mahimmanci ne yanzu!" Wayar ta ce tayi kara tana dubawa taga Abbahn sa ne dauka tayi sai ta mike da sauri tana fadin "Gani nan ranka ya dade." Aliyu ta kalla tace "Bari naje ina zuwa." Ta juya ta fita komawa yai ya zauna cikin sa yaji yana masa ciwo mikewa yayi ya bude firij ya dauko maltina ya sha sannan ya dauko magamin sa ya sha. Kwanciyya yayi a hankali sai yaji cikin yana saki, mikewa yayi ya saka kayan wanda ya kara fitowa a ango yai kyau sosai. Ya shafa turare yana tsaye ya saka agogo Alkasim ya shigo yana binsa da kallo yace "Ango kaga yadda kayi fresh da kai." Tafawa sukai yace "Ko?" "Eh! Tare muke da su Ibrahim fa kazo mu tafi sauran minti goma a kira sallah fa." "Muje!" Ya fada yana neman layin Maryam tana zaune a dakin Anty Rabi ita da kawayen ta kiran ya shigo dauka tayi takai kunne yace " *Matar Haidar* na shirya na fito zamu tafi fa ai mana addu'a." "Adawo lafiya Allah bada sa'a." "Amin nagode." Ya kalli Alkasim da ya zuba masa ido yace "Ya dai?" "Zan zo ka koyan soyayya." Dariya yayi yace "Kai da Ahmad yan iska ne wallahi." Suna fita suka hadu da Mama a compound dake cike da mutaneya karasa ya durkusa yace "Mamah mun tafi." "Allah tsare ya bada sa'a!" "Amin nagode!" Suka juya suka tafi a masallacin Abbi dake sallah juma'a akai sallah juma'a bayan an idar dubun nan jama'a dake wajen suka shaida daurin auren Aliyu Haidar Suleiman da Amaryar sa Maryam Muhammad Jabeer. Waya ya zaro ya shiga text ya rubuta "Alhamdulillah Finally duban jama'a sun shaida Maryam ta zama *Matar Haidar* ina miki fatan alheri Matata. Allah miki albarka." *Allah ya jikan mu, yasa mu cika da kyau da imani, Allah yasa.muyi kyakyawan karshe, Allah ya jikan iyayen mu da kakkanin mu. Amin* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 22 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* * Maryam na zaune sakon ya shigo hawaye ta fara na farin ciki da sauri ta mike ta tada sallah godiya ga Allah ta idar ta jima tana addu'a su Aisha sai huto da vedio suke mata. In kaga Aliyu bakin sa ya kasa rufuwa sai Allah sanya alheri ake masa yana ta washe baki a ka'ida sai 3pm za a tafi reception dan haka daga nan gidan su Maryam suka isa. Bangaren Ammi suka fara shiga suka gaisheta da godiya Yaya Fadima tai musu jagora bangaren Yaa Muhammad. Suna shiga ya dinga baza ido dan ya gano Maryam a tsakiyar Aisha da Rukayya ya hango ta an rufe mata fuska da sauri ya karasa ya rumgume ta tsam a jikin sa yana fadin "Alhamdulillah finally jama'a sun shaida abin boye, Maryam ta zama *Matar Haidar* farin cikina, hakika ko yau na mutu buri na ya cika mutane sun shaida ke din Matata ce." Yan dakin suka hau Kabbara suna fadin "Allahu Akbar Allah ya bada zaman lafiya ya bada zuri'a mai albarka." Fuskar Maryam ya dago yaga hawaye hannu yasa ya goge mata yace "Kice Alhamdulillah Maryam komai ya faru dake mai kyau ko akasin haka kice Alhamdulillah Allah zai kara miki sama da abinda kika sama." "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!" Ta furta tana jin wani sanyi a zuciyar ta. Haka aka dinga daukar su picture masuyi nayi masu vedio nayi anan suka jima dan sai uku sannan suka tafi kamar kar su rabu ya tafi yana daga mata hannu itama haka. Wanda yana tafiya taji zuciyarta, ta tsinke gaban ta na faduwa. Nan aka fara yinin gida inda Amarya ta shiga dan canja kaya ta saka wani less mai kyau sea green ta yafa babban mayafi batai makeup ba yan matan amarya suka sha ankon atamfa green and blue sunyi kyau sallah la'asar sukai sannan suka fito suka zauna a inda akai decoration aka fara raba abinci ana ci ana sha ana kida da rawa mata ne kadai ke yini kamar yadda gidan Mamah ma suke can suke yi. Su Aliyu kuma suna can Meena event centre ana reception abokai sai abinci suke ci shi kuwa yana zaune a takure waje daya. Alkasim ne ya karasa yace "Ya dai Angon Maryam?" Hannun sa ya kamo suka fita a wajen yace "Buden mota na kwanta ciki na ke ciwo." Bude masa yai ya shiga baya yace "Ko mu tafi asibiti ne?" "A'ah kaje ka kula da sauran abokan mu kace musu bana jin dadi ne." Kwanciyya yayi Alkasin yace 'Ba matsala?" Kai ya gyada Alkasim ya juya ya tafi Aliyu ya rufe kofar motar ya kunna AC amman gumi yake dan haka ya mike ya zare Babbar rigar sa. Wayar sa ya dauko ya fara rubuta sako " *Matar Haidar* ki yafewa Haidar, Haidar yana son ki burin sa ya rayu dake har karshen rayuwar sa." Ya ajiye wayar yana dafe cikin sa dake juya masa wanda ya jike da gumi ya jingina kai yana fitar da numfashin sa da kyar. Maryam dake wajen biki hankalinta gaba daya baya wajen dan yadda zuciyar ta ke bugawa sakon Aliyu ne ya shigo ta karanta ta kuma karantawa amman ta kasa daina karantawa kuma gaban ta bai daina bugawa ba. Alkasim kuwa yana can yana fama da mutane wanda suke da yawa dan ka rantse lokacin aka daura aure kowa yana sha'anin gaban sa wasu na cin abinci wasu hira dan haka duk ba su lura da rashin Aliyu ba. Wani juyi da cikin sa yayi wanda yasa ya saki salati tare da lumshe idon wanda nan take numfashin sa ya fara masa wuya dawowa, haka ya dinga jan sa da kyar wanda in yaja baya iya dawo da wanda ya shiga sai dai ya nemi wata iska, dan haka abun sai ya hadar masa goma da ishirin ga ciwon ciki ga numfashin sa dake neman daukewa. Hannun sa akan cikin sa yana juyi ba abinda yake sai ambaton Allah Wanda a dai dai wannan lokacin Maryam ta fara fita daga hayacin ta dan wani irin haki take sai kace ita ce ke fama da ciwon nasa. Aisha ce ta lura da Maryam din na cikin wani hali ta karaso wajen ta hannunta ta kama ai kuwa Maryam ta damke hannun tana daura dayan hannun ta akan kirjin ta. Idon ta ya ciko da kwalla ganin haka ne yasa Aisha dago ta suka bar waje daki suka tafi ta zauna sai kuma ta fara neman layin Aliyu wanda yana kwance yana fama da ciwon ciki sam bai ma ji ringing din nata ba. Ta kira shi sama da sau biyar amman bai dauka ba Aisha ta kalla tace "Na kira Yaa Haidar but he did not pick!" "Haba Besty kema kinsan yana tare da mutane kila bai ji bane." "No Yaa Haidar ba zai dauki wannan tsawon lokacin bai kira ni ba and also har nai masa more than five missed call bai dauka ba. Aisha wallahi jiki na ba dadi, zuciya tin dazu take tsinkewa." Ta kamo hannunta, ta daura akan kirjinta tace 'Kinji ko kinji yadda take buga min da karfi ko, i feel like something bad will happened, ina son nasan halin da Yaa Haidar yake....." Ta kasa karasawa saboda yadda jikin ta yake rawa da kukan da ya kwace mata. "Haba Maryam ki nutsu insha Allah nothing bad will happened insha Allah be reciting Innalillahi wainna illahir rajiun." Amsa tayi ta dinga maimaitawa tana cigaba da kiran Aliyu. Aisha na kusa da ita tana ta bata baki, Yaya Zainab ce ta shigo ta gansu a haka tace "Me yake faruwa ne? Ke nake nema kije ki wanka magariba ta kusa." Idonta ta dago ta kalle ta tace "To ina Yaa Haidar?" "Me zai miki bayan yanzu za a kai ki kwa hadu a gidan ku. Aisha rakata bangaren Anty Hauwa tai wanka na hada mata ruwa kayan da zata sa suna dakin kuyi sauri gani nan ma dai." "To!" Ta fada. Mikewa Aisha tayi ta kama hannunta da har yanzu jikin ta rawa yake. Dakin suka shiga ta cire kaya ta shiga dan yin wankan. Karfe biyar da Rabi Alkasim ya fito jin shiru ba Aliyu ba alamun sa har lokacin ko cikin bai daina ba. Mota ya bude ya same shi cikin mawuyacin hali duk ya jigata da sauri ya dago sa yana kiran sunan sa amman bai san inda hankalin sa yake ba. Motar ya tayar ya fice ya nufi asibiti dashi ana zuwa aka amshe shi a emergency a bakin dakin ya tsaya yana zarya ya kasa zama kwata kwata. Tin shida saura amman har shida da arbain ba wanda ya fito a dakin domin jikin Aliyu ba karamin tashi yayi ba. Maryam na fitowa Yaya Zainab ta shigo da kwaskon turaren wuta ta ajiye ta zuba aciki ta sa ta turare jikin ta da kasanta. Kayanta ta saka wata atamfa fara ce mai adon purple, purple din anyi shi nai sheki. Riga da zani ne ta saka farin mayafi da farin flat takalmi duk abinda take jikin ta rawa yake. Kallon ta Yaya Ummulkusum tayi da ta shigo tace "Kinci abinci kuwa?" Aisha tace "Ba abinda taci." "Ai ga jikin ta nan yana ta rawa. Me za a samo miki?" Kai ta girgiza. Yaya Zainab tace "Barta angon ta ya ciyar da abarsa." Hawaye ne ya zubo a idon Maryam dan ita ta rasa a wane hali take ciki. "Kuka kuma?" Zama tayi gefen gado. Yaya Ummulkursum ta karaso ta kama hannun ta tace "Ki kwantar da hankalin ki wajen Yaa Haidar fa za a kai ki menene na kuka ko yaushe kike son ganin Ammi zai kawo ki, ki daina kukan kinji." Kai ta gyada tace "Tashi kiyi sallah kan azo a tafi dake." Kai ta gyada ta mike ta nufi kan sallaya dan tayo alwala ta tada sallah. Fita su Yaya Zainab da Yaya Ummulkursum sukai ya rage Aisha da ta shiga dan tayi alwala. Number Alkasim ta fara nema, yana dauka tace "Kuna lafiya? Ina Yaa Haidar?" Dakin da Aliyu yake ya kalla yace "Lafiya lou. Yana nan kalou menene?" "Maryam ta damu tana kira sa bai dauka ba ina fatan dai lafiya ko? Dan sai kuka take!" Shiru yayi Aisha tace "Hello!" "Aisha muna asibiti ne kada ki fadawa kowa Aliyu bai da lafiya amman insha Allahu komai zai zama normal ki kular min da kanwata please." "Ayyah Allah bashi lafiya. Insha Allahu!" Ta kashe wayar ta tsaya tunanin shakuwar Aliyu da Maryam wanda bashi da lafiya ma sai taji a jikin ta ko da yake ba yanzu suka fara ba haka suke ko a gida. Alwala tayi ta fito, ta fito ta samu Maryam ta daga hannu tana addu'a. Sallah ta tayar tana idar wa Yaya Zainab ta shigo tace "Aisha ku taso har wasu sun tafi ma! Ku taso." Maryam ta yunkura zata tashi tana mikewa tayi baya zata fadi da sauri Aisha da Anty Zainab suka kamo ta. Zainab ta rike ta suka fita. Bangaren Abbi suka shiga dakin shiru sai kamshi yake. Abbi ne zaune sai Inno da Hajja kakakanin Maryam sai Ammi da wasu daga cikin Yaye da kannen Abbi da Ammi duk suna zaune. A kasa aka zaunar da Maryam. Aisha ta tsaya a kofar falon Abbi. Wayarta ta dauka ta kara neman layin Alkasim bayan ya dauka tace "Ya jikin nasa?" Cikin muryar damuwa yace "Har yanzu shiru fa, ba wanda ya fito a cikin su." "To fa wai ciwon har haka ne." "Sai dai sun fito zamuji." "To Allah kara sauki." "Amin!" Ya fada a sanyaye ya kashe wayar. Abokan sa ne suka fara kira suna masa tsiya wai sun tafi sun bar su ina angon suna ta kira bai dauka ba. Hakuri ya basu yace gasu nan yanzu insha Allah. Zama yayi ya dafe kai kawai dan ya rasa yaya zai yi ma. Yanzu wa zai fadawa a gida wanda hankalin sa ba zai tashi ba. Abbah ya fada a ransa wayar sa ya dauka ya fara neman layin Abbah. Yana dauka yace 'Abbah kana ina ne?" "Ina hanya zan koma gida lafiya?" "Ka tsaya gani nan zuwa kana dai dai ina?" "Ina zoo road." "Ok!" Ya mike ya fita. Napep ya hau ya isa yana zuwa ya samu Abbah a tsaye a bakin motar sa. "Lafiya Alkasim ina Aliyun?" Kai ya dan sosa yace "Abbah muna asibiti baya jin dadi ne." "Me yake damunsa?" Abbah ya fada cikin damuwa. "Cikin sa ke ciwo tin dazu muke asibiti har yanzu likitocin basu fito ba." "Ya salam muje to muje!" Suka nufi asibitin Alkasim na tuka motar suna zuwa likita ya fito daga dakin da sauri Alkasim ya karasa yana fadin "Doctor ya jikin nasa?" Dagowa yai ya kalle su sai ya girgiza kai yace....... * Maryam ce zaune kan ta a kasa hawaye na zubo mata. Abbi yace "Ba abinda zance miki Mamana sai dai ina alfahari dake, Allah yai miki albarka. Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah yasa ki shiga a sa'a yadda kikai min biyayya Allah ya baki masu miki. Kiyi hakuri da rayuwar aure nasan Aliyu na son ki kuma zai rike ki da amana ki masa biyayya domin daga yau zai zama sirrin ki cikon rayuwar ki, zai zama jigo kuma garkuwa gareki. Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka." Duk yan dakin suka amsa da amin. Haka kowa ya tofa albarkacin bakin sa, sannan suka saka mata albarka da addu'ar gamawa da duniya lafiya. Alkur'ani da littafan addu'a da carbi Abbi ya bata. Ta amsa tana hawaye da yaki tsayawa. A gaban su Abbi da Ammi ta durkusa tace "Abbi da Ammi ku yafe min dan Allah ku yafe min." Abbi ne ya kamo hannun ta yace "Mun yafe miki Mama nah, Allah yasa ki shiga a sa'a baki taba bata min ba Mama nah." Ammi ta rumgume autar ta tace "Allah miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya. Allah ya baki ikon yin biyayya da daukar ko wacce irin jarabawa. Allah ya baki hakuri Amin. Allah miki albarka." Kanwar Ammi Anty Hauwa ta kamata ita da Yayar ta Anty Asibi suka mike Bayan su Kannen Abbi Anty Aisha da Anty Mariya suka fita. Gidan Mamah suka shiga har falon ta akai musu iso. Tana zaune itama da ka ganta zaka san akwai abinda ke damun ta amanar Maryam aka bata ta dauke ta amshe amanar Maryam ta saka mata albarka sannan ta bata kaya cikin wata jaka wanda tarkace ne turaruka da kaya da kudi a ciki. Aisha ta amso suka fito. Mota biyu ce ta rage Aisha ta shiga gaba. Maryam da Anty Asibi da Anty Mariya a baya dayar kuma Anty Aisha da Anty Hauwa suka shiga suka nufi gidan Maryam da har an fara dawo da yan ganin gida sai kadan daga yan uwa dan ana magariba aka fara kai su. Har dakin ta aka kai ta. Yan kawo amarya na ta yaba kyau da girma hadi da tsaruwar gidan wanda iyayen ta kuma suka zuba kaya masu kyau tsada da tsari wanda gidan ya kara fito kowa sai yaba shi yake dan wasu cewa suke ai wannan ita ce aljannar duniya. Haka suka zaunar da ita suka tafi aka bar Aisha da Rukayya sai Zarah yar Anty Hauwa da Yaya Fadima kan abokan ango su taho suka zauna suna kara gyara gidan. Maryam kuwa alwala tayo ta tada sallah tana sallah tana kuka ta idar ta jima tana addu'a ta rasa faduwar gaban me take yi. Aisha ta kira tace "Aisha ki kira min Yaa Haidar!" "Wayar sa a kashe fa." "Ikon Allah dan Allah ki kira Yaa Alkasim ni dai ki kira shi ya nemon shi ya hadani dashi dan Allah." "Toh!" Ta dauki wayarta, ta fara neman layin Yaa Alkasim. * Doctor yace "Yana cikin wani hali ba abinda yake ambata sai sunan Allah da *Matar Haidar* yana fadin a kira masa ita, in da hali kuzo da ita ko in ya ganta zai samu nutsuwa." Abbah ne ya kalli Alkasim yace "To bari naje na taho masa da ita." Ya juya ya fita. Doctor ya juya zai koma dakin Yaa Alkasim yace "Ya jikin nasa?" Cikin karaya yace "Da sauki amman yana bukatar addu'ar ku." "Insha Allahu!" Wayar sa ce ta hau kara ya zaro yaga Aisha ce. Dauka yayi yace "Aisha!" "Na'am Yaya daman Maryam ce tace na kira ka....." Wayar Maryam ta amshe tana fadin "Yaya ina My Hayyat ya shiga ka fada min ina ya tafi ya barni, dan Allah ka nemo min shi" "Haba Maryam ki nutsu mana menene na kuka ina aka ce miki ya shiga? ai yana nan." "To ka hadani dashi yana bandaki in ya fito zan fada miki." "Ok!" *Allah ya yafe mana kasa mu cika da kyau da imani. Allah yasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum* MS Indabawa *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 23 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Aisha ta amsa ta mike ta fita tace "Ya jikin nasa?" "Da sauki yanzu Abbah zai zo ya dauko Maryam din yana son ganin ta." "Yah Alkasim mufa muna gidan ta ma har an kawo ta gidan ta." "Au yau ne fa za a kawo ta ko wallahi na manta ma kwata kwata." "Allah ya kara sauki sai anjima." Ya kashe wayar. Kira ne ya shigo daga abokan sa ya dauka "Wai kuna ina ne?" "Muna asibiti fa. Aliyu ne ba lafiya." "What? Wanne asibitin?" Nan ya fada musu sannan ya kashe wayar. Abbah gidan su Maryam ya nufa kai tsaye yasa ai masa magana da Abbi. Har sitting room aka kai shi Abbi ya fito yana ganin sa suka kara musabaha yace "Daman kai ne?" "Wallahi nine." Suka gaisa sannan Abbah yace "Dan naka ne fa ba lafiya, " "Aliyu! me yake damun sa?" "To yana asibiti ma dai yanzu nima Alkasim yake fada min likita ne yace nazo na dauko masa Maryam da sai kiran sunan ta yake yi." "Ikon Allah! Ai yanzun nan aka kai ta sai muje mukai ta naga jikin nasa ko?" "To ba matsala." Suka mike suka fita tare. A kofar gida suka tsaya Abbi yace "Bari naga ko su waye a ciki!" Ya dauki waya ya fara neman layin Ammi, dauka tayi yace "Su waye a gidan Mama nah?" "Fadima suna can." "Shikenan!" Ya kashe wayar ya fita a motar Abbah ma ya fita suka nufi gidan knocking sukai Mai gadi ya bude su Abbah ya gani ya bude da sauri yana fadin "Barkan ku da zuwa!" "Yauwah!" Suka gaisa sannan suka nufi cikin gidan a bakin kofa Abbi yai knocking, Fadima ce ta fito tana ganin Abbi ta matsa yace "A'ah ba shiga zamuyi ba ina Mama nah?" "Tana ciki!" "Je ki taho min da ita kuma kuzo ku tafi gida kawai." "Lafiya Abbi?" "Lafiya lou." Ta juya tai shiga. Maryam na zaune akan sallaya ta shiga ta nufi wajenta ta kamo ta tana fadin "Taso!" Mikewa tayi tace "Su Yaa Haidar ne?" "A'ah Abbi da Abbah ne!" "Ina Yaa Haidar me ya faru me ya faru?" "Ke ki nutsu ba komai Abbi yace dai kizo." Ta kamata ta fita da ita. Bakin kofa suka hadu dasu Abbi ta nufi Abbi da sauri tana fadin "Abbi ina Yaa Haidar dan Allah yana ina?" Hannunta ya kama yace "Ki nutsu yana nan kinji ko?" Hawaye take kawai dan hankalinta ya dada tashi, ya kalli Fadima yace "Zan turo Abdullahi ya dauke ku, ku rufe gidan kunji!" "To Abbi!" suka fita Maryam rike da hannun Abbi jikin ta sai rawa yake a baya ya saka ta ya kalle ta yace "Kina ambaton Allah kinji?" Kai ta gyada ya juya ya koma gidan driver ya tada motar ya kalli Abbah dake kallon Maryam cike da tausayi yace "Wane asibitin zamu?" Fada masa yayi ya tada motar suka nufi asibitin sam Maryam bata cikin hankalin ta da zata san ina ma suke tafiya sunan Allah kawai take kira tana hawaye har suka isa Abbi yai parking ya fito ya rufe ya budewa Maryam kofa amman sai ta tsaya kallon sa hannunta ya kamo yace "Taho Mama nah!" Ta kama hannun sa suka fito harabar asibitin ta kalla ta kalli Abbi tace "Abbi me ya faru? Me yasamu Yaa Haidar?" Tayi maganar murya na rawa saboda kukan da yazo mata mai karfi. Kama hannun ta yayi yace "Ki daina kukan nan dan Allah!" "Na daina Abbi!" Tai maganar da kana kallon ta kasan bata cikin haiyacin ta. Abbah yai gaba Abbi na bin sa rike da hannun Maryam har suka shiga reception din suka nufi corridor da dakin da aka kwantar da Aliyu. Alkasim ta gani da sauri ta sakin hannun Abbi ta karasa wajen sa tace "Ina Yaa Haidar din?" Dakin da yake ya nuna mata da sauri ta nufi dakin ta bude doctor ne da nurses tsaye akan Aliyu suna jin an budo kofa suka juyo suna kallonta da sauri tayi ciki ganin Aliyu kwance akan gado daga shi sai farar singlet da dogo wando a jikinsa. Da gudu ta karasa ta dago kan sa tana fadin "Yaa Haidarrr! Yaaa Haidarrr!! Dan Allah ka tashi ka tashi ga *Matar ka* tazo ga *Matar Yaa Haidar* kaji *Mijinah* dan Allah ka tashi *Mijin Maryam* !" A hankali ya bude idanun sa da sukai rine dan azabar ciwo murya a hankali ya rike hannun ta daya ya daura kan cikin sa dayan ya rike yace " *Matar Haidar* ki yafe min mutuwa zanyi *Matata* mutuwa zanyi na barki...." Ya kasa karasa maganar jin wata rumguma da tai masa hawaye na zuba a idon ta tana kuka tace "Bazaka mutu ba, Bazaka mutu ka barni ba, bazan iya rayuwa ba kai ba dan Allah ka daina fadin haka dan Allah Yaa Haidar ka tashi mu tafi gidan mu Yaa Haidar kaji ka tashi." Sai kuma ta mike da sauri tana daura hannun ta akan marar sa tace "Irin wancan ciwon ne Yaa Haidar fada min Yayahh irin wancan ne?" Kai ya hau girgiza mata yana cije baki tare da fadin "Ciki na ke ciwo ba marata b....." Ya saki wani dan kara yana fadin "Ya ilahi! ya mujibadda'awati!" Ya fada cikin daga sauti sai kuma ya fara salati yana tasbihi ga Allah. Can kuma sai ya lafa gumi ya hau zubo masa ta ko ina duk da AC dake dakin. Mayafinta ta saka tana goge masa gumin tana fadin "Sannu! Sannu Yaa Haidar!" Ta kalli Doctor din tace "Dan Allah kuyi masa wani abu cikin sa ciwo yake." Ta fada tana shafa cikin tana tofi tana shafawa a cikin. Ruwa ta gani a roba ta dauko ta bude tayi tofi sannan ta kai bakin Yaa Aliyu ta bashi sosai yasha sannan ta daura kan sa akan cinyar ta tana shafa gashin kansa dayan hannun na cikin nasa sai da ya samu ya fada masa sannan yace "Allah miki albarka *Matar Haidar* " "Sannu Yaa Haidar! Ya kake jin cikin?" "Da sauki!" "To ka daina cewa zaka tafi ka barni ka manta abinda kace tare zamu rayu, mu tsofa, sannan mu mutu tare ga kabarin ka ga nawa." Ta fada hawaye na zubo mata. Hannu yasa ya share mata yana fadin "Haka naso *Matar Haidar* amman kinsa kowa akwai abinda Allah ya tsara masa, muna tamu Allah yana tashi kuma kinsan na Allah shine gaskiya, duk yadda mukaso abu sai kiga watakil ba namu ne alheri ba na Allah ne alheri kuma kullum alheri muke nema a gurin Allah. Kuma rabon wani shi ke kashe kashe wani, kuma kaddara ta riga fata. Fata na ki kasance cikin farin ciki ko bana raye." "Wane farin ciki zan shiga babu kai....." "Ki daina cire rai da jin dadi, ki daina kina zaune zaki samu me kular min dake wanda zai baki farin ciki fiye da nawa." Kai ta hau girgizawa tana fadin "Ka daina fadar haka Yaya babu wanda zai soni fiye da kai dan Allah ka bari zan haifa mana yaran da kake so ba Baby boy kake so ba, zan haifa maka shi mai kama da kai in saka masa sunan ka kaji ko baka so?" Duk da ya fara jin dawowar ciwon sai da ya sakar mata murmushi sannan yace "Ina so mana *Matar Haidar* ko bana raye zaki haifa min yaro *Ummu Haidar* " "Zama ka rayu damu, har da mai kama dani ko baka so?" "Ina so mana *Ummu Haidar!* " Duk nurses din dake dakin kallon su suka tsaya cikin tausayi da burgewa. A hankali Doctors din suka fita wanda Abba da Abbi suka yi kan sa da sauri. "Ya jikin nasa?" "Da sauki!" "Amman me yake damun sa?" Abbi ya fada. Yaa Alkasim yace "Zan iya ganin sa." Kai ya gyada ya kalli Abbi yace "Za ai masa sceening anjima na rasa gane ciwon cikin nasa mun masa allurai da sa masa ruwa dai yanzu Allah ya bashi lafiya." "Amin mungode!" Ya tafi suka shiga dakin. Suna shiga Maryam ta fara kokarin tashi Aliyu ya riko hannun ta kan ta tayi kasa dashi. Abbi da Abbah suka karaso suna kallon sa duk ya rame sai yanzu suka ga ramar sa sosai. "Sannu Aliyu ya jikin?" "Alhamdulillah Abbi!" "Allah kara sauki!" "Amin!" Abbah ya dafa kan sa yace "Sannu Aliyu!" "Yauwah Abbah!" Wayar Abbah ce ta hau kara ya dauka yace "Hajiya lafiya dai ko" "Lafiya Alhaji amman rabo na da Aliyu tin safe fa? Yana ina ne ko ya tafi ba sallama." "Muna asibiti ne bashi da lafiya fa." Da sauri ta mike tana fadin "Me yake damun sa? Yana ina? Ya jikin nasa? Innalillahi wainna illahir rajiun! Ku na wane asibitin?" "Ki nutsu jikin da sauki." "To amman kana wanne asibitin?" Nan ya fada mata ta mike da sauri ta fito compound kanwar ta Hajara ta biyo ta tana fadin "Lafiya Yaya?" "Aliyu ne ba lafiya!" "Me ya same shi?" Ta fada tana bin bayan sa. Dirver ta kira yazo ya tafi dasu. Alkasim yana gaban gadon abokan su suka kira sun zo suna wane dakin? Fada musu yayi dan haka da suka karaso sun kai su goma sha suka shigo dakin gaba dayan, su Abbah suka gaisar sannan su Abba suka fita. Sukai wa Aliyu sannu suna masa tsiyar, Alkasim yana ta kare shi dan shi sai murmushi yake musu suna musabaha da dai dai da dai dan su. Abdullah ya dauki su Yaya Fadima ya mai da gida. suna shiga Fadima ta nufi dakin Ammi. Ammi ta kalle ta tace "Har kun dawo?" "Eh Ammi amman fa Yaa Haidar ne ba lafiya yana can asibiti Abbi da Abba sunje sun dauki Maryam ma." "Me yake damun sa?" "Wallahi nima ban sani ba." "To ina Abdullah kira min shi!" Ta fita ta kira shi. Yazo ya zauna a gaban Ammi tace "Kira min Abbin ku kaji suna wane asibiti?" Wayar sa yazaro ya fara neman layin Abbi. Suna fita Abbi ya kalli Abbah yace "Wannan ciwon cikin yana bani tsoro anya ba za a fitar da Aliyu ba?" "Nima tunanin da nake kenan." "Gaskiya dai bari zanyi magana zuwa anjima muji ya abin zai kasance kalli yadda yaron ya rame lokaci daya kasan ciwon ciki ba dadi" "Haka ne nagode Sosai Malam." "Ba konai ai an zama daya." Wayar Abbi ce ta hau kara ya zaro yaga Abdullahi ne dauka yayi yace "Ka mai dasu gida?" "Eh Ammi ce tace na tambaya kuna wane asibitin?" Ya fada musu Abdullah ya amsa da "Toh!" Ya kashe wayar ya kalli Ammi ya fada mata. Nan sukai mota har biyu suka tafi asibitin. Kusan a tare suka shigo asibitin dasu Mamah a parking space suka hadu dan haka suka nufi dakin bayan sun kira Abbi ya fada musu inda suke. Suna zuwa suka shiga dakin da yake wanda hakan yasa abokan sa sukai masa sai da safe suka tafi. Maryam na ganin Ammin ta mike ta fada jikinta tana kuka. Ammi tace "To menene na kukan?" Mamah ta kamo ta tace "Ki daina kuka zai tashi kinji!" Ta kwantar da ita a jikin ta, ta kalli Aliyu tace "Sannu!" Kai ya gyada kawai yana kallon Maryam dake kuka. A haka sukai masa sannu dukka amman shi ido sa hankalin sa na kan Maryam. A hankali ta dago tana kallon sa. Ya mike mata hannu kin tashi tayi sai da Mamah tace "Tashi kije mana!" Ta karasa ya matsa mata gefen gadon ta zauna ya daura kan sa akan cinyarta ya kamo hannun ta daya ya daura akan cikin sa. Wani numfashi ya sauki sai kuma ya fara salati dan yadda cikin ya murda masa. Nan Maryam ta fara tofi Alkasim kuwa da sauri ya mike ya fita a dakin dan kiran likita tare suka dawo da likita yazo yace su fita, har Maryam ta mike amman Aliyu ya kamo hannun ta Doctor yace "Yi zaman ki." "Yi min tofi *Matar Haidar* " Ta dauki ruwa ta karai masa tofi ta bashi ya amsa ya sha sannan ya lumshe ido ya mike zaune ya rumgume ta a jikin sa. Fita doctor yayi ya barsu su kadai a dakin. Shiru sukai sai numfashi da suke saukewa can yace "Allah miki albarka *Matar Haidar* " "Amin Yaa Haidar nagode." " *Matar Haidar* ki yafe min zan tafi na barki zan tafi wajen Manzo na, fatan na ki amshi duk kalar jarabawar da zata zo miki da kalubalen rayuwa wata rana sai labari." Hannu ya saka ya shafa cikin ta yace "Naso naga abinda zaki haifa min *Matar Haidar* amman nasan ba zan gani ba ki kular min da yarona ki fada masa Abbi nasa yana son sa, yana kular min dake kada ya bari kiyi kukan komai. Ki kasance jaruma a duk inda kika tsinci kanki. Ki rike Allah shi kadai zai dafa miki ki dinga min addu'a ki sa yaran ki suna min addu'a. Ki sa yaran ki suna min addu'a ki fada musu suna da wani Abbi mai son su tin kan suzo kullum burin sa ya gansu. Ki yafe min *Matar Haidar* kada ki manta dani duk runtsi duk wuya. Allah ya shiga lamarin ki ya rabaki da duniya lafiya. Allah ya rabaki da Baby na lafiya. Allah miki albarka yai miki tukwici da gidan Aljanna. Ina son ki, ina kaunar ki, zanyi kewar ki. Allah miki albarka!" Ya fara maganar yana lumshe ido maganar sa kuma ta fara sanyi. Hawaye kawai Maryam take dan kalaman sa ba karamin dukkan ta suke ba ta kasa gane inda ya dosa ma gaba daya. "Bazaka tafi ka barni ba, bazaka tafi ka barni a wannan rayuwar ba. Ni matar kace kai kadai, kada ka manta kai ka fada *Matar Haidar* taka ce kai kadai dan Allah kada ka tafi ka barni ai ciwo ba mutuwa bane zaka rayu Yaya zaka rayu zan kasance mata ta gari mai son farin cikin ka da kula da kai. Kai ka dai ne farin ciki na. Yaran mu zasu tashi tare damu zasu san mu gaba daya su so mu ka daina cewa ba zaka san su ba, ka bari dan Allah." Ta kare maganar tana kuka ta dago sa ta rumgume a kirjin sa. Ji tayi ya sauke wata ajiyar zuciya ya sakar mata nauyin sa wanda a hakan yasa ta leka fuskar tasa gaban ta ne ya fadi ganin yadda yake mata murmushi amman idon sa a rufe. "Yaa Haidar!" Ta kira sunan sa. Shiru taji tace "Sannu ka samu bacci kenan sannu!" Ta kara tallafe shi. Sai dai me gaban ta ne yake ta yin luguden faduwa. Ammi da Mamah ne suka shigo dakin, kokarin janye shi ta fara amman ta kasa dan yai mata nauyi, Mamah tace "Bacci ya samu?" Kanta a kasa dan kunya tace "Eh!" Ammi ta karaso ta kalle shi sosai sai ta juya ta fita da sauri. Abbi ta kira ya karaso tace "Abbi kaje ka duba Aliyu kamar fa ya mutu!" "Me?" Ya fada yana cewa "Innalillahi wainna illahir rajiun!" Ya juya ta kara kiran sa ya juyo tace "Kaga dare yayi kayiwa su Mamah da Maryam magana su zo mu tafi kan su gane me yake faruwa!" Kai ya gyada kawai. Ya nufi dakin. Mamah ya kalla yace "Sha biyu saura tinda ya samu bacci ya kamata ku tafi ko?" "To Alhaji!" Ya isa ya janyewa Maryam Aliyu daga jikin ta, sannan yace "Ki kwantar da hankalin ki, kinga ya samu bacci da ya tashi zai ji sauki." Kai ta gyada tana zubar da hawaye. Mamah ta fita itama tabi bayan ta har ta kai bakin kofa ta dawo ta tsaya a gaban gadon tana kallon sa, ji take kamar ta kwana a gun sa dama Abbi yace ta kwana, dan ko ta tafi ba nutsuwa zata samu ba ita ta sani. Abbi yace "Kije Mama nah kinji." "To Abbi kai masa sannu in ya tashi,.." "Toh." Ta juya ta fita. Yaa Alkasim ta gani a bakin kofa tace "Yaya zan tafi in ya tashi dan Allah ka kira ni. " "Toh!" Ammi ta kama hannun ta suka fice da sauran matan aka bar Abbah da Abbi da Yaa Alkasim sai Yaa Muhmmamd. Abbi kuwa yana ganin Maryam ta fita ya matsa jikin gadon yasa hannun sa a hancin Aliyu yaji ba numfashi hannun sa ya dago ya taba jijiyar nan ma bata motsawa bayan kunnen sa yasa yatsan sa nan ma babu motsi kai ya girgiza yace "Allah ya jikan ka, Annabi ya amshi bakuncin ka." _*Comment din ku na jiya ya bani dariya da yawa gaskiya, abu daya zance muku shine wannan fa labarin baya ne, kada ku damu ku cigaba da bibiya ta a sannu kowa zai farin ciki kamar yadda nake yawan fada to yanzun ma haka ne, fata na dai ni sakon da nake son isar wa ya isa inda nake son yaje.*_ _Masu kuka da fadin Maryam ta basu tausayi, masu jin haushin Haidar sai dai nace ku cigaba da bibiyar alkalami na a sannu zaku gane komai, har yanzu dai bamu sani ba Haidar da gaske ya mutun ne ko me?_ ~Muje zuwa wasa farin girki~ *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* Maryam Suleiman *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 24 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Ya ja masa abu ya rufe fuskar sa. Yaa Alkasim ne ya shigo yana ganin haka yace "Abbi me ya faru?" Kai Abbi ya girgiza, Yace "Sai dai muyi hakuri!" Dai dai shigowar Abbah da Yaa Muhammad kenan. Abbah yace "Ya rasu ko?" Kai Abbi ya gyada masa kawai yai shiru. Abbah yace "Allah ya jikan ka Aliyu Allah yasa can tafi nan Allah ya yafe maka. Ni bakai min komai ba inma kayi a rashin sani ne kuma na yafe maka. Allah ya jikan ka Aliyu...." Ya kasa karasawa saboda muryar sa dake rawa. Abbi ya karaso ya dafa shi yace "Kayi Hakuri Allah masa rahma." "Amin!" Yaa Alkasin kuwa gaban gadon ya karasa cikin shock yake kallon Aliyu dake rufe bude shi yayi ya zuba masa ido yana fadin "Anya kuwa Abbi, kalli fa!" Ya nuna sa yace "Yana numfashi Abbi bai mutu ba, ba yanzu zai mutum ba Abbi kazo ka duba kaga." Abbi ya girgiza kai ya dawo ya kara duba Aliyu ya dago yace "Sai hakuri fa Alkasim!" Dagowa Alkasim yayi yace "Abbi kalli fa yana numfashi." Tausayi ya bawa Abbah, Abbi da Yaa Muhammad dan ba numfashin da yake yi. Abbi yace "Muhammad kira likitocin suzo su kara duba shin." Ya juya tare suka dawo da wasu nurse da Doctors su Abbi suka basu waje duk suka fita, aka barsu suna kokarin su dawo da nunfashin sa. Amman ina Allah ya amshi abinsa, babu yadda suka iya babu yadda zasuyi saboda wanda ya hallice sa ya dauke wanda ya fisu son shi ya dauke, wanda kowa na can ne, kowa ita yake jira can ne gidan gaskiya ba nan ba Allah ya bamu ikon cikawa da kyau da imani. Allah jikan musulmai yasa sun huta ya kyautata namu zuwan, Amin. Bayan minti kusan ashirin suka fito gaba dayan su. Da sauri Alkasim ya karaso yace "Bai mutu ba ko?" Kai ya girgiza sannan ya dafa shi yace "Am sorry to say...." Baya Alkasim yayi da sauri Doctor ya taro shi ya shiga dakin da Aliyu yake. Ruwa ya shafa masa ya farfado yana ganin gadon Aliyu ya mike ya nufi wajen yana fadin "Dan Allah kuce min karya ne bai mutu ba. Ku kalli fa yana numfashi wallahi yana numfashi kalli cikin sa yana dagawa da komawa." Kalla sukai sukaga sam ba abinda ke motsi a jikin sa dan haka suka kama Alkasim suka fita dashi suka samu Abbi da Abbah sukai masa bayani. Alkasim kuwa yaki yadda Aliyu ya mutu sai cewa yake su kara dubashi. A haka suka cike komai sannan suka dauki gawar Aliyu aka tafi gida da ita. * * * Tin da suka fita daga asibitin take kuka ta rasa na menene tasan dai tana tsoron kar abinda Aliyu ya fada ya tabbata kuma tana tsoron kada ya tashi cikin sa yai ta ciwo. Gaba daya ta gama rudewa da fita a hankalin ta domin kuwa bata gane komai da kowa sai zuciyarta dake ta dukan tara-tara kamar zata ballo kirjinta ta fito. A haka suka karasa gida Ammi ta kamata ta sukai ciki. A falo suka samu Inna, Yaya Zainab, Yaya Rabi, Yaya Ummulkurusm, Yaya Hauwa da wasu kannen su Ammi da Abbi. Suna shiga suka hau tambayar ya jikin nasa. Ammi ce tai karfin halin cewa da sauki sannan ta wuce da ita ta kai ta dakinta anan ta samu su Aisha da Rukayya da Zarah da Yaya Fadima duk idon su biyu suna jiran dawowar su. Jikin Yaya Fadima ta fada tana sakin wani kuka mai ban tausayi da sauri Ammi ta juya ta fita Aisha da Rukkayya da Zarah duk suka karaso suka rufe Maryam suna lallashin ta. Kuka take kamar ranta zai fita dan har numfashin ta yana daukewa yana dawowa. Mamah ma na komawa aka hau tambayar ya jikin sa. Kanwar ta Hajara ita ta basu amsa Mamah ta shiga daki ta zauna. Yaya Hauwa ce ta shigo ta zauna tace "Yaya dan Allah kada kisa damuwa ki masa addu'a!" "To Hauwa." Ta fada ta zuba tagumi kawai. Karfe sha biyu da rabi su Abbi suka karaso gida bangaren Aliyu aka wuce da gawar Aliyu. Abbi da Abbah ne sukai masa wanka. Abbi ya aika Yaa Muhammad ya debo kayan da za a bukata a dakin sa. Ta kofar baya ya shiga ya dauko duk abinda za'a bukata suka dawo akai masa wanka aka shirya shi cikin shigar sa. Suka ajiye shi anan falon sa. Aliyu ya kara tsayi da haske da ka kalli face din sa ta kara kyau sai murmushi dake dauke akan fuskar sai ka zata zai yi motsi. Alkasim kuwa kuka yake yana fadin "Abbi wallahi bai mutu ba dan Allah kada ku ce ya mutu ku bari ku gani zai tashi dan Allah zai tashi." Abbi ya kama shi yace "Alkasim mutuwa gaskiya ce fa kuma duk mai rai mamaci ne, shi da Allah ya kira haka Allah yayi muma muna tafe a ko da yaushe muna jiran zuwan ta. Kai shiru kai masa addu'a zuwa safiyya za a kai shi gidan sa na gaskiya in ya tashi kan lokacin shikenan. Kai da Muhammad ku zauna ni zanje na sanar da gida yanzu zan dawo." Abbah ya kalla yace "Kaje ka sanar da Hajiya Binta, halin da ake ciki ko?" "Toh!" Tare suka fita shi da Abba lokacin daya har da rabi. Abbah ya nufi sashen sa, Abbi ya tafi gida. Yana shiga ya zauna wayar sa ya dauka ya fara neman layin Mamah. Tana zaune akan sallaya taji karar wayar ta dauka yayi tana ganin Abbah ta kai kunne tana fadin "Ya jikin nasa?" "Kizo bangare na, na dawo yanzu." Ya kashe wayar. Jiki na rawa ta mike ta nufi dakin Abbah. Zaune ta same shi ta karasa ta zauna tace "Ya jikin nasa?" Shiru yayi yana kallon kasa. "Alhaji!" Ya dago ya kalle ta cikin tausayi. Tace "Nace ya jikin sa?" "Zauna kiji!" Ya kama hannun ta ya zaunar. Zama tayi ya kalle ta yace "A ko da yaushe yadda da kaddara mai kyau da mara kyau yana daga cikin shika shikan muslunci kuma Allah kan jarabci bawan sa dan ya gwada imanin sa." Hawaye ne ya fara zubo mata. Yace "Bance kiyi kuka ba, amman ina so ki amshi hukuncin Allah da yai mana shi ya bamu Aliyu kuma in yaso shi zai dauke abinsa. Daman amana ce Allah ya bamu to duk lokacin da ya amshi abin sa kar muce dan me. Kina gani dai yanzu ba mu san ina dan uwan sa ya shiga ba wanda kullum muna cikin tashin hankali da damuwa na rashin yana wane hali yana raye ko baya raye amman wannan munga makomar sa, Allah da ya bamu ya fimu so ya amshi abinda dan haka sai muyi masa godiya. Mu bishi da addu'a Allah ya jikan sa, Allah ya kyautata namu zuwan Allah ya jikan sa yasa Aljanna makomar sa, Allah ya yafe masa." Mamah ya kalla ya dauki hannun sa ya fara goge mata hawayen dake zubo mata, yace "Kada kiyi masa kuka kinji addu'a zaki masa." "Allah ya jikan ka Aliyu, Allah yasa can tafi nan. Halin ka na gari ya bika. Baka taba batan ba Aliyu Allah ya yafe maka. Allah ya gafarta maka Allah....." Muryarta ta fara rawa Abbah ya rumgume ta yana lallashin ta da bata baki akan kada tai masa kuka. Daga nan suka mike sukaje tai masa addu'a ta koma daki ta shiga ta sanar da kannen ta tace kada a tashi masu bacci da asuba sa ji. Haka ta zauna tana tai wa Aliyu addu'a zuciyar ta kuwa sai zafi take mata kamar zata fashe amman ta daure bata bari kuka ya zubo a idon ta ba. * Abbi na shiga bangaren sa ya shiga, Ammi ya aika aka kira takaraso da sauri tace "Alhaji ya ake ciki?" Kai ya girgiza mata kawai yace "Sai dai hakuri." "Innalillahi wainna illahir rajiun!" Ammi ta fada tana zama akan kujera. "Allah ya jikan ka Aliyu, Allah yai maka rahma, Allah yasa can tafi nan, halin ka na gari ya bika!" "Amin!" Abbi ya amsa. Sannan yace "Kada ku sanar da Mama nah halin da ake ciki yanzu." "Toh" Ta mike ta karasa bangaren ta ta sanar da yan uwan ta sannan ta kira Fadima ta fada mata tace kada su fadawa Maryam. Ta amsa ta koma. Akan sallaya ta samu Maryam zaune rike da carbi tana ja. Kallon ta tayi cike da tausayi sannan ta kalli su Aisha tace "Ku kwanta ku dan huta." Maryam ta juyo ta kalli Aisha tace "Kira min Yaa Alkasim kiji ya jikin Yaa Haidar din!" "Toh!" Ta dauki waya ta fara neman layin nasa amman har ta gama ringing bai dauka ba. Sau uku tana kira baya dauka ta kalli Maryam tace "Kila suna bacci ne." Hawaye ne ya zubo mata ta mike ta fita compound ta tsaya taga motocin gidan duk suna nan bangaren Abbi ta shiga taga ba kowa fita tayi ta nufi bangaren Yaa Alkasim nan ma ba kowa a ciki. Bangaren Yaa Muhammad ta shiga ta samu Anty Rabi zaune tana ganinta ta mike tace "Lafiya Maryam?" "Anty ina Yaa Muhammad?" "Basu dawo daga asibiti ba!" "Da motar wa suka je naga duk motocin suna gida." "Ina jin da motar Yaa Haidar ne." Mikewa kawai tayi ta fita. Dakin Ammi ta shiga ba Ammi dan haka ta juyo ta koma daki ta hade kai da gwiwa kawai tana kuka. Aisha ce ta taso ta dafata ta fashe da kuka itama dan fitar ta Yaya Fadima take fada mata Yaa Aliyu ya rasu. Dagowa Maryam tayi tace "Kukan me kike Aisha?" "Dole nai kuka mana Maryam tayaya kina kuka zan kasa kuka ba zan iya ba, kina karya min zuciya in kina kuka dan Allah ki daina kukan nan." "Ya zanyi to? Ya zanyi na rasa yaya zanyi kukan kawai nake ji Yaa Haidar nake son gani ko jin muryar sa amman tayaya danasani ban baro asibitin nan ba, danasani acan nai zamana, na kula da miji na." Ta kare maganar tana sakin kuka. Rumgume ta Aisha tayi tana fadin "Zaman ki ba abinda zai kara ko zai hana. Kiyi tawakalli ke kike samu a mahanga in mun kauce please ki daina kuka kiyiwa Yaa Haidar addu'a kawai." "Ina masa amman kinsan me jiki na yai sanyi." Ta kamo hannun Aisha, ta daura a kirjin ta tace "Kinji ko? Kinji yadda take buga min ko? Ina son Yaa Haidar ba zan so abu ya same shi ba na kasa nutsuwa da halin da na baro shi yana shan wahala ina ma ciwon zai dawo jiki na. Ke shaidace ko ya abu ya samu dayan mu dayan mu yana ji a jikin sa. Yaa Haidar wani sirri ne a rayuwa ta, Yaa Haidar rayuwa ta ne. Yaa Allah ka bawa bawan nan naka lafiya, Yaa Allah kada ka dauken wannan bawan naka nasan kafini son sa amman shine jigo na garkuwa ta. Allah ka cika mana burin mu, mu tsufa tare, mu haifi yara da jikoki tare sannan mu mutu tare ga kabari na ga nashi sannan Allah ka hadamu a aljanna. Amin Ya hayyu ya qayyum!" Ta fada tana shafawa. Wani sabon kuka Aisha ta saki dan sanin addu'ar ta ba mai amsuwa bace wacce take dan shi ya riga ya mutu shin ya zata dauki wannan abun in taji cewar Yaa Haidar ya mutu. Gefe kawai taja tana sakin kuka dan abin ita kanta ya bata tsoro. Mutanen da jiya ke tare ya rumgume ta yana godiya da Allah ta zama matar da kowa ya shaida ashe ba rabon zama ashe farin cikin kenan. Duk soyayyar da sukewa juna shikenan ta kare ta mutu lallai duniya abar tsoro ce. Sai tsoron Allah ya dada kamata ta rufe ido kawai tana mai jin tausayin aminiyar tata. Haka suka kwana a zaune Maryam na kuka Aisha na kuka an rasa me rarrashin wani ma. Suna zaune aka fara kiran sallah asuba, nafila Aisha ta tashi tayi dan Maryam ta kasa mikewa dan yadda kafafun ta sukai wani sanyi suna zaune sukaji an kira sallah asuba amman sam ta kasa tashi gashi tana son ta kara tada sallah. Sai da Yaya Fadima ta gama sannan ta kalli Maryam tace "Bakya sallah ne?" Hawaye ne ya zubo mata tace "Na kasa tashi kafafu na kamar ba ajikina suke ba ki taimakan." Mikewa Yaya Fadima tayi ta Kamata har bandaki ta raka ta, shigar ta kenan aka idar da sallah sannan aka sanar da jana'idar Aliyu da za ayi nan da karfe takwas na safe. Tana bandaki sam bata ji ba ta fito tana dafa bango dan har wani jiri take gani. Da sauri Aisha ta mike ta kamata ta tayar da sallah ta jima tana kan sallaya tana addu'a bayan ta gama tai azkar. Agogo ta dago ta kalla taga karfe shida da rabi. Aisha ta kalla dake rike da carbi tace "Ki kara kira min Yaa Alkasin naji ya jikin Yaa Haidar!" Wayarta ta zaro ta fara neman layin Yaa Alkasim amman me a kashe take wayar. ajiyar zuciya ta sauke tace "Kinji wayar tasa wai a kashe." "Dan Allah kira min Yaya Fadima!" Ta fada tana gyara zaman ta. Mikewa Aisha tayi ta nufi dakin Ammi. Anan ta samu Rukayya da Zarah suna ta kuka dan jin mutuwar tasu kenan da sauri suka fita dan tabbatar da cewa wane Yaa Haidar din, fada masu cewa shine yasa suka zauna suna ta kuka sun kasa tafiya wajen Maryam ma. A haka Aisha ta shiga ta same su Yaya Fadima na basu baki. "Yaya Fadima kizo inji Maryam!" Mikewa tayi tace "Ince dai bata ji sanarwa nan ba?" "Bataji ba so take a kira mata ma Yaa Alkasim taji ya jikin Yaa Haidar?" Ta karasa maganar tana share hawayen idon ta. "Muje!" Suka fita tare. Suna shiga suka jiyo sautin kukan ta, hannun ta rike da kan ta tana kukan. *Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan kasa muyi kyakyawan karshe.* *Amin.* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 25 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Dafata Yaya Fadima tayi tace "Dan Allah kibar kukan nan haka menene kuma ya faru?" "Dan Allah kicewa Ammi akai ni wajen Yaa Haidar, in ba mai kaini ni zan tafi dan Allah ki rokar min ita." "To naji! Ki bar kukan ko a haka zakije masa kina kuka ki dada tada masa hankali." "Wai tayaya kuke son na daina kukan nan nifa ban san yana fitowa ba nakasa rike shi dan Allah kije ki mata magana." Mikewa tayi tace "Toh!" Ta tafi dakin Ammi. Dawowar Ammi daga gidan Mamah kenan gidan da har ya fara cika da mutane ga na biki ga yan uwa, da makwabta. Mamah na zaune a gefen Aliyu sai addu'a take masa Abbah da Abbi da Alkasim da baya uhm bare Uhm uhm duk suna zaune. A cikin gida kuwa sai kuka ake. Zuwan Ammi ma dan Abbi yace tazo ta kira Maryam ne suyi sallama wannan yasa ta mike ta nufi gida shine suka hadu da Fadima. Tana ganin ta tace "Daman wajen ki zani!" "Meyafaru ba dai taji ba?" "Bata ji ba dan so take kisa a kai ta wajen Yaa Haidar." "Ikon Allah! Tayaya zan sanar mata ne. Bari naje dai." Ta nufi dakin Yaya Fadima na bin ta a baya. Tana shiga Maryam ta rarrafo wajen Ammi ta kama kafar ta tace "Ammi dan Allah kada kice min A'ah!" Kamo ta Ammi tayi tana boye hawayen idon ta tace "Ba zance ba, taso muje!" Ta kamota ta mike ta lafe a jikin Ammi dan yadda take ganin bibbiyu. Ammi ta kama ta tace "Menene?" "Jiri Ammi, biyu biyu nake gani Ammi!" "To rufe idon ki kinji!" Rufe idon tai Ammi ta lattafe ta suka fita a dakin. Suna fita Fadima da Aisha suka fashe da kuka. Fadima ce ta mike tace "Taso muje." Suka bi bayan su. Har suka fita compound idon ta a rufe yake sai da suka kusa kofar gidan su Aliyu ta bude ido. Mutanen da ta gani ne ya bata tsoro tace "Ammi me ya faru?" "Ba komai." "Waye zai kaini gun Yaa Haidar?" "An sallamo shi fa yana gida " "Ammi da gaske? Yaji sauki ko?" Kai Ammi ta gyada tana kama ta suka shiga gidan yadda taga compound din a cike wasu na kuka wasu na jimami yasa gaban ta ya kara yankewa ya fadi. Tunanin ta ya gushe dan ta kasa gane mutanen menene suka zo musu haka. Sai kace jiya ranar bikin su da daurin auren su. Kama ta tayi suka nufi bangaren Aliyu, yan tsakar gidan kuwa sai nuna ta suke da hannu suna fadin "Ga matar tasa. Allah sarki!" "Ai fa jiya jiya aka daura aure yau ba miji wannan wane irin tashin hankali ne." Haka suke ta magana kala kala dai. Suna shiga falon Aliyu gaban Maryam ya kara faduwa har sai da ta durkusa ta dafe kirjin ta. Ammi ta durkusa tace "Menene?" "Ammi kirjina, sai faduwa yake." "Kina fadin Innalillahi wainna illahir rajiun kinji?" Kai ta gyada ta fara ambaton haka a zuciyar ta. Ammi ta dago ta suka shiga. Abbah da Abbi ta fara gani sai Yaa Alkasim da Mamah daga kan da zatai ta gano Mutum kwance rufe da farin abu da sauri ta juya ta kamo hannun Ammi tana nuna mata abun hannunta na rawa bakin ta ma rawa yake ta kasa furta komai, sai nuna abun da take jikin ta na karkarwa. Tin kafin Ammi tai magana ta sulale zata fadi kasa da sauri Ammi takamo ta tana fadin "Innalillahi wainna illahir rajiun!" Abbi ya mike da sauri yayo wajen su yana fadin "Me ya faru?" "Suma tayi ko?" Ya dago ta ya karasa dakin da ita. Ammi ta dauko ruwa a firij ta shafa mata a fuska shiru bata farka ba, kara zuba mata tayi nan ma haka ruwan ta tuttula mata a kanta wannan yasa taja wata doguwar ajiyar zuciya wanda yasa kowa fadin "Alhamdulillah!" Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ta bude za ta sake ganin abinda ta gani, wannan shi ake kira mummunan gani. "Shin waye ma a kwance a cikin likafani? Tai tambayar a zuciya da sauri ta bude ido dan gwara ta gama sanin wanene ta tabbata dai ba Yaa Haidar bane. Ina Yaa Haidar ba zai mutu ya barta ba. Kasa-kasa take jin muryar su Mamah, Ammi suna fadin "Tana numfashi." Tofi taji ana mata a hankali ta bude idon ta. Abbi ta gani yana mata tofi. Idonta ta mayar kan gawar dake kwance sambal nuni tai musu da ita dan su fada mata waye a ciki amman duk suka gaza bata amsa. A hankali ta mike zaune ta dafe kai dake barazanar rabewa gida biyu, kallon gawar ta karayi sannan ta mike tsaye Ammi ta kamo ta cire hannun Ammi tayi ta tafi gaban gawar a dai dai kan sa ta durkusa jikinta na rawa ido na zubar da hawaye ta mika hannu ta dage Likafanin..... Fuskar Yaa Haidar ce wacce yake tai mata murmushi ta bayyana, bata san lokacin da zauna akasa ba ta tsurawa gawar ido ba abinda yake motsi a jikin ta har numfashin ta daukewa yayi cak idon ta na kafe akan sa kawai. Ammi ce ta gane ta shiga shock wannan yasa ta karasa kusa da ita da sauri tana zuwa ta taba ta ai take ta bingire a jikin Ammi. Yaa Muhammad ne ya miko ruwan dazu dan a shafa mata amman ko gezau, har juye mata akai amman sam bata farka ba kuma ko alamun rai babu a jikin ta. Ammi ce tace "Itama fa ta mutu!" Da sauri Mamah ta karaso tana fadin "Mun shiga uku, Yaa Allah kada ka jarabce mu da rasa yara biyu a lokaci daya Allah mun tuba in wani laifi mukai maka." Abbi ne ya karaso ya duba kai ya girgiza yace "Ai kuwa kamar itama ta rasu!" Kuka Ammi da Mamah suka saka. Ammi ta rumgume gawar Maryam tana jijjigawa.......... ~Please ku karata kasan nan~ *_Ban taba zato ba, ban zata haka ba*_ _Jiya naji dadi sosai dan ba a taba yin comment kamar jiya ba, daga facebook har whatsapp naga abinda akai ta tattaunawa shine MATAR HAIDAR abun ya bani nishadi duk da akwai taba zuciya, ba yau na fara rubutu ba, ba yau kuma in nayi wasu suke cewa sun daina karantawa ba dan ban musu yadda suke so ba, duk abinda kuka gani a littafin nan na rubuta shi sama da watanni bawai ko sama da haka kafin na rubutawa kuwa labarin yana kaina sama da shekara biyu sai a yanzu dai Allah yayi lokacin sa, ba dan nishadi kawai nake rubutu ba ina rubutu dan fadakarwa da zaburarwa so, ni akwai abinda nake son na isar am not after all this love in zakuyi duba irin wannan deep love din bai fiya kaiwa inda ake so ba, kuma ko a gaske muna son mutane Allah ke daukewa, masu cewa Maryam tayi wauta jarabawa ce Allah ya riga ya rubuta, mu bamu san irin wacce Allah zai jarabce mu da ita ba, fatan mu dai Allah ya bamu ikon cinye tamu kalar jarabawar, itama bamu san tukuwicin da Allah zai mata ba, kila Yaa Haidar ba alheri bane a gareta ba shiyasa ya dauke shi, kuma rabon wani a ko da yaushe yakan iya kisa dan haka kuyi shiru kawai ku dai...._ *Hakika naga kauna sosai Allahu ya bar zumunci, masu kuka kuyi hakuri mutuwa nasan ko ta wasa ce babu dadi nima nai kukan kuma duk lokacin da na karanta abun mutuwa yana kara kashen jiki da kara min imani wanda yake kara min kusanci ga Allah, abinda nake so daku kuma kenan. Allah jikan musulmai yasa muyi kyakyawa karshe yasa mu cika da kyau da imani* *Maryam Suleiman* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 26 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Yaa Muhammad ne yace "Abbi aje asibiti dai a kara gwada ta." Yaa Abdullah yace "Akwai likitoci, a waje bari na kira wani." Ya juya ya fita da sauri da daya daga cikin abokan Aliyu ne basu koma ba suka zo amsa jana'idar sa suka shigo Maryam ya dudduba sannan yace "A kai ta asibiti dan tana cikin mayuwacin hali in ba a kula da ita ba zata iya karasawa." Da sauri Yaa Muhammad ya dauke ta Ammi tabi bayan sa. A bakin bangaren Yaa Haidar su Aisha sukaga Yaa Muhammad ya fito da Maryam da sauri suka bi bayan sa Ammi ma ta fito mota daya suka shiga. Yaa Fadima na gaba Ammi da Aisha na baya rike da Maryam wacce take tamkar gawa. Suna zuwa aka amshe ta aka wuce da ita emergency likitoci ne suka hadu dan ceto ranta wanda suka kwashe sama da awa takwas akan ta amman sam bata dawo haiyacin ta ba da taimakon oxygen dai sun samu tana numfashi amma daga nan ba abinda yake motsi a jikin ta. Wanda asibiti zuwa wannan lokacin a cike yake dan wajen hudu na yamma lokacin har an sallaci Aliyu Haidar wanda ya samu hallartar mutane masu yawa aka kai shi gidan sa na gaskiya kowa sai addu'a yake masa dan Aliyu mutumin kirki ne bai taba fada da kowa ba kowa nasa ne dan haka kowa sai yabon sa yake. Ammi, Yaya Fadima da Aisha sune suke asibitin tin safe basu koma gida ba. Yaya Zainab, Yaya Ummulkursum, Yaya Rabi da Hauwa duk sun zo. Haka nan Innah da su Anty Asibi, Anty Hauwa da sauran suma kowa yazo yaga halin da Maryam take, kowa yazo da kuka yake tafiya. Innah ce ta kasa tafiya itama dan halin da taga Maryam ya tsorata ta gani take itama kamar mutuwa zatai. Suna zaune sukaji sallamar Mamah, da sauri Ammi ta mike tana fadin "Da kanki Hajiya ai wandan da suka zo ma sun wadatar!" Zama Mamah tayi tana goge hawaye tace " *Matar Haidar* ce fa, dole na rike masa amanar ta ko da bashi da rai domin ba tin yau ba yake ban amanar ta dan da yana da rai da shine mutum na farko da zai kasance akan ta to bashi da rai dan haka ni zan kasance mata tamkar Haidar insha Allahu. Allah ya bata lafiya domin Ita kadai zan kalla na tina haidar ita mutane da yawa zasu kalla suyiwa Haidar addu'a dan za ace ga *Matar Haidar* wanda ranar daurin auren su ya rasu....." Kasa karasawa tayi, saboda kuka. Innah ma kukan take tace "Tabbas ko ba aure shakuwar Ali da Takwara abin duba ne dole ta shiga wani hali, Allah ya tashi kafadun ta shi kuma munyi rashi yaro mai hankali da nustuwa ga zumunci takanas kafa ya kafa yake zuwa ya gaishe ni, Allah ya jikan sa yasa can tafi nan Allah gafarta masa." "Amin Amin! Amin Ya hayyu ya qayyum!" Haka duk yan dakin suka amsa. Bayan mintina Ammi ta kalli Mamah tace "Hajiya amman da kin koma gida saboda yan zuwa gaisuwa ko?" "Hajiya Aliyu ya riga ya tafi addu'a ce kawai abinda zamuyi masa, Maryam ita ke bukatar mu yanzu dan Allah ku barni anjima na tafi ganin Maryam nasa naji tamkar Aliyu nake gani". "Allahu Akbar! Lallai ku mutanen kwarai ne, Allah ya jikan Aliyu." Innah ta fada. Suka amsa da Amin. Sai dare da Abbi da Abbah suka zo sannan Mamah ta tafi aka tafi da Innah da Yaya Fadima dan Aisha sam taki tafiya itama sai kuka take iyayen ta dazu sun zo sunje gaisuwa suka biyo asibiti. sai bayan fitar su Abbi ya kalli Ammi yace "Alkasim ma fa yana gida ana masa karin ruwa tinda muka kai Aliyu yake kuka ya suma yafi sau biyar ga zazzabi dake damun sa ga rashin bacci da abinci." "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah mungode maka Allah mungode maka Allah ka yafe mana ka jikan Aliyu ka tashi kafadun yaran nan!" "Amin!" Abbi da Aisha suka amsa. Daga haka ba abinda suke ce. Can sai ga Yaya Ummulkursum da Yaa Muhammad ya kawo ta dan ta kwana da Maryam amman Ammi tace suje kawai zata kwana. Aisha taki tafiya Ammi tace a barta. Haka aka cigaba da zaman makokin Aliyu har kwana uku, har wannan lokacin Maryam bata farka ba, tana kwance yadda take likitoci sai kula da kai komo suke akan ta sai aikin karin ruwa da allurai. Alkasim ma har lokacin mutuwar bata sake shi ba, dan ya kasa cire abun ya rame ga ciwo na cin shi. Ya cire rayuwa da komai da kowa ko wayar sa tinda yasa a durowa bai kara bi ta kanta ba. Abokan su ana uku duk suka koma yan nesa. Aisha ma bata kwana a asibiti amman tin safe in tazo sai dare suke tafiya ita da Rukayya suma sun rame sun shiga damuwa sam basu da sukuni su kadai suka zauna a daki suyi ta kuka na tausayin kawar su da halin da take da wanda zata shiga in ta farka dan sun san bata gama jimamin rasuwar Yaa Haidar ba. Hakika suna tausayin ta suna tausayin kan su. Mamah ma kullum sai taje dubo Maryam Umma ce kadai bata taba zuwa ko addu'a bare sannu amman, kowa na gidan gaisuwa yaje ya dubo Maryam. Haka su Yaya Ummulkursum duk basu koma ba suna gida suma suna amsar gaisuwar Aliyu. A haka har akai sadakar bakwai akai addu'a aka bada sadaka aka tashi daga taron zaman makoki sai wandan da basa garin in sunzo sunji suke zuwa yiwa ahalin biyu gaisuwa dan duk wanda yasan Abbi yasan Aliyu dan in Ramadan yazo tare suke tafsir haka ko masallacin juma'a tare suke zuwa shiyasa Abbi yake ganin Aliyu shi zai gaje shi ashe ba nisan kwanan. Shi kan sa Abbi ba karamin jin mutuwar Aliyu yai ba yaro mai hankali nutsuwa, ladabi, ilimi ga kunya kullun sai yai masa addu'a. Yau kwana Aliyu goma sha biyu da rasuwa. Ammi ce zaune da Mamah da Yaya Fadima da Yaa Alkasim da ko magana ya daina sai da kyar zakaji muryar sa sai Yaya Rabi'a da Yaya Hauwa matan Yaa Muhammad da Ibrahim sai Yaa Abdullah wanda shima duk yai sanyi ganin kanwar tasa a wannan halin kullum tana kwance tamkar gawa. Suna zaune sukaga yatsan kafar ta ya fara motsi da sauri suka mike sai kuma suka ga ta motsa hannu sai kuma tari da ya sarke ta duk da oxygen dake makale da hancin ta. Da sauri Yaa Abdullah ya fita ya kira doctor da gudu suka karaso suka sa su Ammi fita sai da suka kwashi tsawon awa biyar sannan suka fito, Yaa Alkasim ne ya karasa yace "Ya jikin nata?" "Alhamdulillah ta dawo amman bata farka ba numfashin ta ya dawo dai dai kuma a ko wanne lokaci zata iya farkawa. Allah ya bata lafiya." "Amin mungode!" Suka koma dakin suna kallon ta. Lokacin yamma tayi amman gaba dayan su sun kasa tafiya so suke kawai Maryam ta farka akan idon su. Har Abbi da Abbah da sauran yan uwa aka fadawa cigaban da aka samu akan Maryam baku ga murna ba sai kace wanda akace ta tashi. Bayan isha'i suna haramar tafiya dan Ammi tace su tafi suna hada kaya ana dan hira sama sama duk akan Aliyu ne da rasuwar sa. Wanda tin da suka fara maganar sa Maryam ta farka amman batai motsi ba tana jin duk abinda ake. Sai da Yaa Abdullah yace "Munyi rashin Yaya mai son mu da kaunar mu. Allah ya jikan Yaa Haidar!" Wannan ya tuno kuma ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Yaa Haidar har abada. Ji tayi ina ma daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba? Hawaye ne ya zubo ta gefen idonta. Yaa Abdullah da ya karasa gefen gado dan dauko flask ya kalle ta sai yaga hawaye na bin gefen fuskar ta da sauri yace "Ammi ta farfado." Da sauri Mamah ta karasa gefen gadon tana fadin "Alhamdulillah!" Sai ta kamo hannun ta da ba a sawa karin ruwa ba, tace "Ki bude idon ki Maryam kinji." Yaa Abdullah yace "Alhamdulillah kwana goma sha yau Allah ya dawo mana dake dan Allah ki bude idon ki Maryam!" "Subhanallah! Innalillahi wainna illahir rajiun har kwana goma sha, Ta tabbatar ta rasa Yaa Haidar kenan. Garin yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta sake ganinsa ba? Saboda me akai mata haka?" Ta fada cikin zuciyar ta tana sake runtse idon ta, ji tayi gwara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi, amman tayaya zatai rayuwa ba Yaa Haidar. Ammi da sai yanzu ta mike ta karaso ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido, dan itama Maryam ba karamin tausayi ta bata tace "kiyi hakuri Maryam Shima ba gaggawa yayi ba. Mu kuma da kike ganin mu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda hakuri da tawakkali ya bari. Kiyi hakuri haka Allah ya tsara babu yadda zamuyi sai mu amshi jarabarwa mu muce Alhamdulillah!" Maganganun Ammi suka sake saka mutanen dakin kuka. Dan daman kukan suke tinda suka ga Maryam taki bude idon ta sai mutuwar ta dawo musu sabuwa fil. Maryam kuwa duhun da take gani ido rufe ya fiye mata akan hasken da babu Yaa Haidar a cikinsa. Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude idonta balle ta tashi zaune. Suna haka suka ji sallamar Abbi. Amsawa sukai ya shigo yace "Ya naga kuna kuka me kuma ya faru ta farka ne?" Ammi tace "Ta farka amman taki ta bude ido." Abbi ya karasa gefen gadon ya kamo hannun ta dayan hannun ya daura akan ta yana shafawa, zuciyar kowa ta kara karyewa har Maryam dake kwance tana jin komai. Abbi cikin sanyin murya yace "Mama nah kuka ba soyayya bane tsakaninki da Aliyu soyayyar shine kiyi masa addu'a da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Soyayyar da zaki nuna masa kenan addu'a. Da iliminki amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba." Jin haka Maryam ta bude idonun ta da suka kumbura da kyar. Dishi dishi ta fara gani a hankali kuwa taga Abbi tsaye gefen ta dayan gefen Mamah da Ammi, can kuma Yayen ta kowa hawaye yake yi. Wani kuka ne ya kwace mata nan ta shiga yi suna taya ta. Abbi ne yai karfin halin rarrashin su wanda Maryam kuwa tini numfashin ta ya fara neman daukewa da sauri aka kira likita ya zo ya saka mata oxygen sannan yace "A kula da abinda za a fada mata da zai sa ta shiga damuwa ko wani halin!" Jiki ba dadi su Mamah suka tafi. Washe gari da safe asibiti ya cika da yan uwa da abokan arziki saboda anji cewar Maryam ta farka. Wanda kowa yake murna sai dai me har goma da wani abu bata tashi ba. Abbi da kan sa yaje wajen likita dan jin ko lafiya Maryam bata kara tashi ba. Tare suka zo ya kara auna ta sannan ya basu tabbacin zata tashi a ko wanne lokaci. Wannan ya dan kwantar musu da hankali. Karfe daya mazan duk sun tafi masallaci sai matan da wasu ke sallah wasu na zaune jigum jigum. Aisha ce zaune a kan kujera gaban gadon, tana rike da waya tana dannawa akai akai tana kallon Maryam. A hankali ta bude idon ta, ta dinga bin dakin da kallo da sauri Aisha ta mike tana fadin "Besty kin tashi?" Juyowa tayi ta kurawa Aisha ido, ko me ta tuna sai kuma hawaye ta bude mata hannu da sauri Aisha ta karasa ta rumgume ta. Yaya Fadima da fitowar ta daga bandaki kenan ta karaso. Mamah ma da idar da sallah ta kenan ta tashi tana fadin "Alhamdulillah sannu Maryam!" Ido Maryam ta dago ta kalli Mamah wani kuka ne mai karfi ya kwace mata. Mamah ta karasa ta rumgume ta tana shafa kan ta hadi dabata baki. Lafewa tayi a jikin Mamah. Ammi ma bayan ta idar ta karaso tazo tai mata sannu matan Yayen ta da Yayyen ta da kannen Ammi dake waje duk suka shigo sukai nata sannu. Su Abbi bayan an idar da sallah suka dawo suka samu dakin cike dan Maryam ta tashi. Likita aka kira ya kara duba ta bayan ya gama yace "Me yake miki ciwo?" Kallon sa kawai tayi ta nuna kirjin ta, dubata ya kara yace "Ya yake miki ciwon?" Yan dakin ta kalla amman ta kasa magana, Abbi ya karaso yace "Mama nah fada masa ya yake miki ciwo!" Da hannu tai masa alama. Doctor ya kalla yace "Ka gane?" Kai ya gyada. Abbi yace "Amman meyasa ba magana?" *Wasu na fadin basu gane ba, to daga FLASH BACK na tafi rayuwar Maryam ne kan tazo gidan su Ummi da Yaa Haidar (rayuwarta ta baya) wanda a gaba na tabbata zaku gane, ba wannan Aliyun miskili bane ya mutu, wata rayuwar Maryam ce kan tazo wannan rayuwar da fatan kun gane, sannan ku cigaba da bina sannu a hankali, zaku gane komai insha Allahu.* *Allah ya jikan musulmai Allah yasa muyi kyakyawan karshe, Allah kyautata namu zuwan. Amin* Maryam Suleiman *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 27 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* "Muje office!" Doctor ya fada ya fita. Abbi da Yaa Muhammad suka bi bayan sa. Yan dakin kuwa sai murna suke suna mata sannu Maryam kuwa ba magana sai hawaye dake zuba a idon ta kawai. Abbi ne zaune shida Yaa Muhammad sai Doctor dake duba file din Maryam. Mikewa yayi yace "Ina zuwa!" Sannan ya koma dakin ta. Sallamar su yayi dan su basu waje aka barta ita dashi sai wasu nurses sawa sukai ta mike tayi tafiya sannan suka sa tayi motsi da wasu part din jikin ta, bayan ta gama yace "Yi min magana Maryam!" Idon ta ne ya kara cikowa da hawaye sai ta girgiza kai alamar ba zata iya ba. Duk yadda yaso tayi bata iya ba. Har suka gama suka kira Ammi akan abinda zasu iya bata taci wanda Nurse zasu kawo mata yanzun nan. Sannan ya koma office wajen su Abbi. Zama yayi yai danyi rubuce rubuce sannan ya dago yace "Kuyi hakuri dan Allah!" "Ba komai!" "A gaskiya Maryam ta shiga hatsari sai dai cikin hukuncin Allah, Allah ya kawar da hatsarin wanda halin da ta shiga wani daga shi yake mutuwa wani ya makance wani ya kurmance wani ya bebance wani kuma ya rasa wani bangare na jikin sa kamar rashin tafiya da sauran su. To yanzu daga can nake naje na duba ta Alhandulillah matsalar tata ba wata babba bace domin kuwa ciwon kadan ne dan naga magana ce ta dauke mata kuma insha Allahu zamu daura ta akan magani da yaddar ubangiji in da rabo sai ta warke amman gaskiya ba a fiya warkewa ba." "Innalillahi wainna illaihir rajun! Alhamdulillah! Allah mungode maka da wannan jarabawar Allah ka bamu ikon cin wannan jarabawar wannan yarinya Allah bata ikon dauka da cinye ta. Amin!" Abbi ya fada. Yaa Muhammad yace "Toh Allah yasa a dace!" Magunguna ya rubuta sannan ya mike yace "Zan kawo mata maganin yanzu!" Mikewa su Abbi sukai sukayi masa godiya suka koma daki inda Nurses suka shiga da ita bandaki Yaya Fadima ta taimaka ta gyara ta suka fito ta zauna akan kujera daya daga cikin nurse din tana hada mata abinci dayar kuma tana matsa mata kafafun ta. Maryam kuwa sai bin yan dakin take da kallo kamar bata san su ba. Gama hadawa tayi ta karaso ta zauna zata bata abincin kai ta dauke, tace "Haba My sister ki daure kici ko yaya ne?" Kai ta girgiza. Yaya Fadima ta amsa tace "Haba dai Kici kinji kanwata." Dagowa tayi ta kalli Yaya Fadima sannan ta girgiza ka. Aisha ce tace "To me kike so?" Hawayen dake makale a idon ta ne ya zubo ta daga hannu tai mata nuni da cewar Yaa Haidar shi take son ta gani. Abbi da ya gane me take nufi ya karaso ya kama hannun ta yace "Kiyi hakuri kinji Mama nah, Aliyu ya tafi inda ba zai dawo ba." Kuka ta fashe dashi tana girgiza kanta, Aisha ta rumgume ta tana jijjiga ta. Ammi ce tace "Wai Abbi rashin maganar nan fa?" "Zatayi da yaddar Allah!" "Toh! Allah ya yadda!" Haka kememe taki taci abinci, magani ma kin amsa tayi sai allura da akai mata har da ta bacci dan taki ta daina kuka tin da ta tashi kuka kawai take yi wannan yasa sukai mata allura. Kwana ta uku da farfadowa amman sam bata cin abinci sai karin ruwa kuka kuwa shi ya zaman mata abun yi ko da yaushe. Maryam ta rame sosai sai idanu da hanci da suka fito. In suka zauna ita da Yaa Alkasim tai ta kuka shima sai kukan baya iya lallashin. Kullum cikin nasiha da lallashi su ake a haka ta kwana ashirin a asibiti wanda a lokacin aka sallame su. Lokacin da ta koma gida komai sai ya dawo mata sabo saboda tina yadda suke rayuwa da Yaa Haidar a lokacin baya wanda kullum suna tare. Tana zaune a falo hannun ta rike da Kur'ani tana karantawa Ammi na kitchen tana hada mata kunu ko zataji dadin bakin ta. Yaa Alkasim da Yaa Abdullah suna zaune a gefen ta. Da sauri ta dago sai kuma ta mike tana kallon kofa. Yaa Abdullah ne yace "Menene?" Kofa ta nufa tana nuna musu da, musu alamun Yaa Haidar ne. Kasa ganewa sukai Yaa Abdullah ya mika mata paper da sauri ta amsa ta rubuta masa "Muryar Yaa Haidar ne yai sallama wallahi shine!" Tana bashi ta nufi kofa da sauri Yaa Abdullah da Yaa Alkasin suka mike suka nufi ta suna fadin "Ba shi bane Maryam gizo take miki!" Kai ta hau girgizawa tana nuna musu tare da tafiya kamo ta Yaa Alkasim yayi ya rumgume ta yana kuka yace "Wanda ya mutu baya dawowa Maryam ba Yaa Haidar bane? Haidar ya mutu kuma ba zai dawo ba." Kuka ta kuma saki tana girgiza kai a haka Aisha ta shigo ta same su, karasowa tayi ta ajiye basket din hannun ta tace "Menene?" Yaa Abdullah ne yai mata bayani sai ga Aisha ma na hawaye. Ammi ce ta fito da cup dan ta gamai mata ta gansu a haka. Ita har ta gaji da wannan kukan nasu kullum haka suke yini kuka a asibiti yau ma sun dawo gida wato zasu cigaba da musu ko? "Me kuma ya faru?" Duk suka juyo suka dawo dakin. Yaa Abdullah ya karai wa Ammi bayani. Kai Ammi ta girgiza ta kamo hannu Maryam ta zaunar tace "Kina da sani fiye da tunani mai tunani kin taba ji inda wanda ya mutu ya dawo?" Kai ta hau girgizawa. Ammi tace "To dan me kike cewa shine?" Paper ta dauka ta fara rubutu tace "Wallahi Ammi muryar sa naji Ammi dan Allah kuje ku duba min ko shine ya tsaya a waje dan Allah Ammi!" Ta mika mata Ammi na karantawa idon ta ya kawo ruwa ta dago zatai magana suka jiyo sallamar Mamah. Amsawa sukai Mamah ta shigo da sauri Maryam ta mike tana nuna mata kofa tana mata da hannu alamar wai taga Yaa Haidar, Mamah tace "Me take nufi?" Kan su bata amsa ta dauki memo ta fara rubuta mata tace "Mamah kinga Yaa Haidar a waje wallahi yanzu yazo yana sallama ni ban da bakin amsawa jin ba a amsa ba ya juya ina jin!" Amsa Mamah tayi tana karantawa itama idon ta ya kawo kwalla sannan ta rumgume Maryam tana fadin "Haidar ya mutu Maryam kuma ba zai dawo ba." Kwacewa tayi a jikin ta, ta sake rubuta mata "Mamah ke mahaifiyar Yaa Haidar ce kika sani ko Allah ya dawo mana dashi ko kuma zaki ji tsoro in ya dawo ne ni bazan ji tsoron sa ba Ammi dan Allah ku dubo ko shine ya dawo." Ta bata takardar. amsa Mamah tayi ta karanta. Kai ta girgiza Maryam ta kama hannun ta tana roko. Yaa Abdullah ta kalla tace "Kaga jeka ka dubo mana ko dai shi din ne?" Ta fada tana kifta masa ido ya juya ya fita. Mamah tace "Ya jikin nata Hajiya?" "Da sauki!" "Taci abincin kuwa?" "Ina fa kunu nayo mata na fito na same ta tana wannan maganar!" Ta mika mata kunun kai ta make. Mamah tace "In har baki sha ba ko Haidar din ne bazai shigo ba Da sauri ta amsa ta fara sha sai dai me bata sha rabi ba ta ajiye ta dafe ciki sai kuma ta fara juyi tana kuka, da sauri sukai kan ta wanda ta cigaba da juyi kan su farga har ta suma da sauri Yaa Alkasim ya dauke ta suka tafi asibiti suna zuwa suka aka amshe ta bayani sukai wa doctor ya duba ta ya bata gado kan ta tashi suga halin da take ciki. Bata jima ba ta farka tana ganin Mamah ta fara nuna mata da hannu wai Yaa Haidar din yazo. Tana gama nuna mata kuma sai ta rike ciki tana kuka dan yadda yake mata ciwo. Doctor yazo ya duba ta ya kara bata magani sannan ya samu ya lafa bayan awa daya yace zasu iya tafiya amman kada ta sha abu mai tsami kila ulcer saboda rashin cin abincin da batayi. Dakin ta Ammi ta kai ta, ta kwantar da ita amman duk bayan mintina sai ta tambayi "Ina Yaa Haidar a kira mata shi." Abbi yai mata rubutu amman abun sai dada gaba yake ba zaka taba ganin idon Maryam ba hawaye ba. Kullum cikin kuka. Kowa tausayin ta yake da kwantar mata da hankali dan yadda suka san tsakanin ta da Yaa Haidar dole ta shiga damuwa. Ta dada ramewa dan ba bacci ba cin abinci. Tin daga ranar duk abinda zata ci sai ta amayar dashi, duk ta rame kullum suna cikin yawon asibiti. Mamah ce zaune Maryam kwance a kan cinyar ta. Mamah tace "Gobe zamu tafi Umrah Amman sati biyu zamuyi mu dawo zan roka miki Allah ya baki lafiya Maryam!" Hawaye ne ya zubo Mata. Mamah tasa hannu ta goge mata. Ammi ce ta shigo ta zauna tana fadin "Kukan ake ne?" "Hmmm Hajiya gobe fa ne tafiyar!" "To Allah ya kaiku lafiya Amin!" "Amin ga amanar Maryam nan dan Allah a kular mana da ita." "Insha Allahu." Daga nan suka cigaba da hirar wanda kullum hirar dai ta Aliyu ce. Maryam na kwance tana jin su amman ba bakin magana. Sai yamma Mamah ta tafi. Tana shiga ta hadu da Ummah zata fito kallon ta, ta tsaya yi tace "Iska na wahal da me kayan kara, duk abinki ba zaki sake haihuwa ba Kuma yarinya ba zasu baki ita ba sai bibiyar su kike to zanyi maganin abun. Kuma ke da ake cewa mai haihuwa tinda kika haifi yara biyu kin kuma? Bama wannan ba yanzu ina yaran daya ya shiga duniya daya ya mutu kinga biyu babu daya kike da wacce bata taba haihuwar ba." Kai Mamah ta dauke tayi cikin kawai. Ummah tai dariya tace "Sai naga bayan ki da shegiyar yarinyar nan Maryam!" Ta fita a gidan fuska ba walwala. Washe gari dasu Mamah zasu tafi ta shiga yin sallama ta samu Maryam a bandaki tana ta amai tausayin ta bata bayan ta gama ta kama ta ta dawo ta zaunar da ita. Ammi ta gyara wajen Mamah tace "Amman ni da an koma asibiti wannan aman yai yawa ayi test da aune aune gaskiya." "Wallahi ni har na gaji da zaryar asibiti kusan wata kenan ana fama da abu fa." "To ya zamuyi, ai sauki sai a sannu yake zuwa da sannu zamu samu nasara." "Shikenan gobe na fadawa Alhaji muje." "Allah kaimu." Anan Mamah ta zauna har sai da Abbah ya shigo ya duba Maryam sannan Yaa Alkasim ya tafi kai su Airport Ranar kwana sukai Maryam amai dan da ta sha ko ruwa ne sai ta dawo dashi. Akan ta yan gidan suka kwana gaba daya sun tausaya mata. Ai kuwa ana dawo daga sallah asuba suka tafi asibiti amsar ta akai aka saka mata ruwa dan jiki ta yayi mugu weak bayan an saka mata ruwa wata nurse ta shigo ta dibi jinin ta dan yin test. Dakin cike da yan uwan ta ita kuwa tana ramuwar bacci da bata samu tana yi. Wajen karfe sha biyu Nurse din ta shigo da file a hannun ta, bude na farko tayi tace "Jinin ta ya hau dole a kula da ita dan yarinya ce bai kamata ace jinin ta ya kai har haka ba." Ta dauki dayan file din tace "Mun mata na malaria da typhoid all are negative!" Ta dauki dayan file din ta bude sai ta saki murmushi tace "Oh congratulation tana dauke da ciki ashe shiyasa take ta wahala har haka!" *Ai ban san ana bibiyar labarin nan nawa har haka ba, amman shine fisabilillahi ba dan comment bare vote, facebook ne kadai masu yin kokarin yin comment da liking, haba to zan daina nima na koma na kwanta. Gaskiya ku gyara in ba haka ba to nima posting sai naga dama.* *Allah ya jikan musulmai Allah ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* Maryam Suleiman 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 28 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Dai dai farkawar Maryam wanda taji abinda Nurse din ta fada. Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci. Kallon kallo suka fara yiwa juna. Maryam kuwa zuciyar ta kamar ta fito daga kirjin ta dan yadda take bugawa da tsalle. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin ta ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki. Takardar hannun nurse din Yaya Zainab ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Yaya Ummulkursum ta karbi takardar suka hada kai ita da Yaya Fadima da Yaa Abdullah suka karanta. Gaba dayansu takadar suka saki ta fadi kasa fuskar su cike da tsoro da fargaba. Ammi dake gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar. Kasa magana sukai. Yaa Alkasim kuwa ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan ya nufa ya samu Yaa Muhammad suna tattaunawa akan ciwon Maryam da rashin maganar har yanzu. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Yaa Muhammad ya mike da sauri yana fadin "Menene ko jikin Maryam din ne?" "Ina fa ba gwara jikin ta ba da abinda suka ce tana dashi. Wata mahaukaciyar nurse ce take fadin wai ciki ne da ita!" Ya maida kan sa kan Doctor yace "Ka taso muje ka duba ta da kan ka, dan ni ban yadda da aikin ta ba ko canjen result akai." "Is ok ka kwantar da hankalin ka kaji zan kara duba ta, na gani kaji!" "Is better!" Ya biyo bayan sa, suka nufi dakin gaba dayan su. A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ya dauki result din ya karanta. Kallon Yaa Alkasim yayi yace "Ba an daura mata aure ba, mijin ya rasu?" "Yes!" "So shine me?" "Kaga ka kara gwada min ita kawai." Sirinji ya dauko a cikin aljihun lab coat din sa sannan ya karasa wajen gado inda Maryam ke kwance komai ya tsaya mata cak. Jinin ta ya dauka sannan ya fita da kansa ya shiga lab ya kara yin gwajin. Sai da yayi sau uku yana bashi result iri daya dan haka ya dawo dakin. Kowa yasa ya fita sannan ya karasa wajen gadon inda Maryam dake jin duk abinda ke faruwa take. Ido ta bude wanda ya rine yai jajir, Paper ya bata yace "Zan miki tambayoyi kinji kanwata?" Kai ta gyada! "Wata nawa da auren ku?" Shiru tayi tana nazari kan ta ya kulle wanne zata fada to wannen ne dai dai in ta fadi wancan me iyayen su zasu ce. "Kanwata!" Ta dago ta kalli shi. "Fada min kinji?" A paper ta rubuta sannan ta mika masa. Amsa yayi ya gani yace "Are you sure?" Kai ta gyada yace "When last did you saw your period?" Abinda tin dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi dan zata ce tin kan su fara exam da tayi wani period marar ta tai ciwo har ta dawo gida bata karayin wani ba. Shin me hakan ke nufi kenan? Taiwa kan ta tambayar "Fada min kinji!" Rubuta masa tayi ya amsa sannan yace "Kin tabbata?" Kai ta gyada masa ya jin jina kai yace "Good" Fita yayi ya kira Ammi da Abbi sannan ya kalle su yace "A bisa binciken da nayi da kuma amsar da tambayoyi da nai mata, ya nuna tana da *CIKI* na kusan wata uku." "Lahaula walaquwwata illabillah........ La'ilaha illalahu Muhammad Rasulillahi Sallalahu alaihi wasalam!" Ammi ta fada. Mika musu result yayi sannan ya fita. Amsa Abbi yayi da zuwan sa kenan bai san me yake faruwa ba. Takardar ya karanta sannan ya juya ya fita kawai. Ammi ta bishi da kallo sannan ta kalli Maryam dake fidda numfashi kadan kadan. Hawaye na zubowa a idon ta. Zuciya ta kuwa bugawa take kawai tsoro, fargaba, farin ciki ta rasa wanne zatayi a duniya. Yaa Alkasim ne ya shigo da sauri yace "Ammi me ya faru?" Kai Ammi ta girgiza kawai ta juya ta fita. Karasowa yayi gefen gadon yace "Maryam menene fada min?" Hawaye take sai girgiza kai take. Ammi na fita ta kalle su tace "Ku tashi mu tafi gida!" Mikewa sukai Yaya Fadima tace "An sallame ta ne?" Ammi bata, bata amsa ba kawai ta fice sauran suka bi bayan ta ita kuwa dakin da Maryam take ta koma. Nan ta samu Alkasim yana tambayar Maryam amman sai kuka take. Fita yayi ya koma dakin doctor yace "Me result din ya nuna?" "Is positive!" Ido ya zaro yace "Impossible!" Sannan ya fita a dakin da sauri. Ya nufi dakin da Maryam take "Tashi muje wani asibitin a kara test ban yadda da wannan ba." "Oh haka suka ce da cikin dai?" Yaya Fadima ta fada. Kai ya gyada. Kallon Maryam sukai da jikin ta ke ta rawa dan wani zazzabi da ke son kamata. Kan ta sukai suna mata sannu ganin kamar tana firgita yasa ya kira likita allura yai mata bacci ya dauke ta. Yaya Fadima ce ta kalli Yaa Alkasim tace "Kai me kake tunani akan wannan lamarin?" "Bazan taba yadda ba, nasan Maryam ba yar iska bace wama za ace yai mata cikin?" Ya tambaya sai kuma yace "Haidar za a ce ni shaidane Maryam da Haidar ba mazina ta bane wallahi ba zasu taba aikata zina ba dan nasan halin su duk su biyu suna da imani da tsoron Allah, Allah ba zai jarabce su da wannan mummunan aikin ba domin suna kiyaye hukuncin Allah nasan ba dai dai bane ba wani ciki da Maryam take dashi shiyasa nace zamu je wani asibitin mu kara dubawa." Ajiyar zuciya Yaya Fadima ta sauke tace "Wannan haka ne Yaa Alkasim amman dole mu bari ba yanzu ba kaga halin da take ciki mu bari muga ya jikin nata in yaso sai muje wani asibitin! Amman ya kake ganin su Ammi suka dauki alamarin?" Kai ya girgiza yace "Ban sani ba!". "Cewa tayi duk mu tafi gida fa." "To abar wa a wajen ita Maryam din?" "Abinda yake bani tsoro kenan kar su Ammi su kasa fahimtar 'yar su, kar su zarge ta da wani abu." "Anya kuwa?" "To ban dai sani ba." Sukai shiru suna kallon Maryam dake baccin wahala dan da ka kalle ta zaka san ba baccin dadi take ba. A kofar gida duk sukai parking suka fito kowa cikin tashi hankali da baci rai suka shiga gida wanda fitowar Ummah kenan ta gansu a wannan halin ba karamin dadi taji ba. Falon Ammi duk suka tafi, Yaa Muhammad da Ibrahim sai Yaya Zainab da Ummulkursum zama tayi suma duk suka zauna. Ummah parking motar ta tayi ta fito ta nufi cikin gidan bangaren Ammi ta nufa wanda lokacin Yaa Muhammad yace "Ammi me ke faruwa ne?" Shiru Ammi tayi can ta dago ta kalle su tace "Mummunan abu na shirin ya faru damu koma nace ya faru damu... Ace acikin gidan nan za a samu wanda zai yi ciki ba aure." Tayi shiru dan abun ba karamin tsoro ya bata ba. Yaa Ibrahim yace "Da gaske cikin ne da Maryam?" Dummmm haka Ummah taji ta zaro ido da sauri tana fadin "Ciki ciki! Kuma Maryam?" "Shine likita ya tabbatar!" Maganar Ammi ta dawo da ita da tunani da zancen zucin da take da sauri ta juya ta nufi mota hankali a tashe take fadin "Ciki ciki! Maryam ke da ciki? Garin Yaya wannan jarababben yaron kan ya mutu sai da ya sadu da ita kenan, daga daura aure yaje wajen ta ko me?" Shiru tayi tana tuna abinda taji Ammi ta fada wai "Mummunan abu na shirin ya faru damu koma nace ya faru damu... Ace acikin gidan nan za a samu wanda zai yi ciki ba aure" "To suna so suce cikin ba na Haidar bane ko me ko suna so suce kan ai aure suka tara." Kai ta girgiza tana fadin "Nasan wane Aliyu ba zai taba kusantar zina ba kamar yadda nasan Maryam to ya akai abin ya faru. Dole na dauki mataki tin kan Hajiya Binta taji batun nan dan nasan a duniya ba abinda zata so kamar taga jinin Aliyu ko da kuwa shege ne wanda na tabbata da kyar in cikin nan shege ne dole na batar dake Maryam dole na batar dake da dan cikin ki, Binta ba zata taba ganin jinin ta ba ko na dan ta dole na batar da ke kamar yadda na batar da Abubakar daman da tamu dake da tamu da ta Hajiya Amina zan samu na jefi tsuntsu biyu da dutse daya za na batar muku da yarinya na saka muku tsanar ta sannan na batar da jini Hajiya Binta." Wata dariya tayi tana fadin "Komai zai zo yadda nake so kuma yadda zan tsara." Unguwa zata amman sai ta canja hanya ta tafi gidan bokan ta. * "Ammi amman kina ganin da gaske cikin ne?" Yaya Ummulkursum ta fada. "Nima dai abun ya bani mamaki anya kuwa?" Yaya Zainab ta fada. "Likita zai karya ne. zai yi mata sharri ne?" Ammi ta fada. Kai suka hau girgizawa. Yaa Ibrahim yace "Ba zai ba amman yakamata mu canja asibiti a kara zuwa wani a tabbatar ko?" "Haka ne Yaya!" Yaya Zainab da Ummulkursum suka fada. "Kai na ya daure na rasa wane tunani zanyi! "Ammi please ki nutsu ni a gaskiya bana zargin Maryam da aikata zina sai dai in wani tsautsayin ne ko wani abun!" Yaa Ummulkursum ta fada. "In wani tsautsayi ne ya hana ta fada mana!" "Ammi kinsan ta da kunya. Kuma abinda Yaya Ummulkursun ta fada haka ne amman yanzu in cikin ne na wa za a ce?" Yaya Zainab ta fada. "Kada ku daurawa bawan Allah dake kabarin sa kwance cikin rahmar Allah. Nasan Aliyu yaro ne mai imani da ilimi da kunya ba zai taba aikata haka ba, ba zai aikata zina ba." "Ammi ita kuma Maryam din fa?" Yaa Abdullah ya fada wanda ya jima yana tsaye yana jin tattaunawar tasu. Shiru tayi kawai can ta mike tace "Bari na gani ko Abbin ku yana ciki!" Ta mike ta fita suka zauna suna tattaunawa. Matan duk tausayin Maryam ya dada kamasu shi me yake shirin faruwa dasu ne wannan wane irin jarabawace Allah ya basu ikon cinye ta amman suna tsaka mai wuya. Ammi da ta shiga taga Abbi baya nan zama tayi tana tunanin mafita dan kan ta ya kulle gaba daya Maryam na da ciki kai karya ne itama ba zata yadda ba ace tana da ciki. Haka tai ta tunani har aka fara kiran sallah magariba da sauri ta mike ta dauro alwala tazo tayi sallah. Bayan ta idar ne kuma tai addu'a wanda ta dan samu nutsuwa har ta hau tunanin a wane hali Maryam take a lokacin. Mikewa tayi ta shiga bangaren ta, ta samu su Zainab da Ummulkrsum tace "Ku kira min Abdullah ya kaini asibiti ku kuma kuzo ku tafi gida kunji." "To Ammi!" Suna cikin kiran sa ya shigo tace "Yauwah muje ka kaini asibiti!" Suka tafi. *Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin* Maryam Suleiman "Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 29 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* A asibiti Fadima da Yaa Alkasim ne zaune sunyi shiru suna tunanin kowa da abinda yake tunani. shigowar Ammi ne ya sa suka mike da sauri ta kalle su, ta kalli Maryam tace "Ya jikin nata?" "Da sauki!" "Ki tashi Abdullah ya kai ki gida!" Ta fada tana kallon Zainab. "Ammi baya gari kuma na nemi alfarmar ya barni na kwana tare da Maryam." "Shikenan kije gida ni zan kwana da ita." "A'ah Ammi ni zan kwana kije ki huta dan Allah!" Zama tayi ta zuba ma Maryam ido tace "Tin yaushe take baccin?" "Bayan fitar ku jikin ya tashi shine akai mata allura." "Shiru Ammi tayi. Yaa Abdullah ya karasa yana kallon kanwar tasa da ta rame sosai tausayi ta bashi dan haka sai ya juya ya fita kawai dan zuciyar sa ba karamin karyewa tayi ba. Sai goma suka tafi suka bar Fadima a wajen ta. Ammi na komawa gida ta nufi bangaren Abbi wanda dawowar sa kenan. Zama tayi tace " Kaci abinci ne?" Dagowa yai ya aika mata da wani kallo wanda ya bata mamaki. Kasa shiru tayi tace "Na jima ina jiran ka dan ina so muyi maganar akan Ummi " Ummi take kiran Maryam wani lokacin saboda sunan mahaifiyar sa ne. "Ai yar kice duk abinda kika yanke ya dace!" "Bangane ba Abbi!" "Kome tayi da sanin ki!" "Wai kaima ka yadda da tana da cikin?" "Saboda me bazan yadda, naje asibiti yafi biyar ana min test ana fada min positive. Ke zan fara tambaya cikin waye a jikin ta, kada kice min na Haidar ne!" "Innalillahi wainna illahir rajiun Yanzu ni kake zargi akan cikin jikin Ummi, zan sani na boye maka shin me ka dauken da Ummi ne? Naga kafi kowa sani na da Ummi kasan halin mu dan me kuma zaka daura mana laifi baka taba kawowa ko fyade akai mata ko wani abu ba....." "Kinga ko kina son ki kare ta, in fyade ne wata uku dayi bata fada ba a haka tasan tana da ciki aka daura mata aure da yaron nan, Allah yaso baya raye da wane hali zai shiga kinsan dai yadda yake son ta." "Dan Allah ka daina fadar haka wa ka sani wanda ya taba zuwa zance gun Ummi. Haidar ne kadai mane min ta inma tuhuma za ai shi za a tuhuma." "Na fada miki kada ku daurawa yaro nan, yana can kwance cikin kabarinsa cikin salama, kada kisa a tashe shi ana tambayar sa dan Allah!" "Amman Alhaji......." "Dan Allah Amina ki kyale ni, tashi kije yanzu bana son magana ki kyale ni da abinda nake ji. Wai yau ni a cikin gida na 'ya ta take dauke da cikin da bamu san uban sa ba. Allah nagode maka Allah ka yafen in wani laifi nayi ka jarabcen da wannan masifar!" Ammi kallon sa ta tsaya yi yana gama fadin addu'a yai ciki. Hawaye ne ya zubo mata lallai suna cikin tashi hankali da gaske dai da cikin nan. Mikewa tayi ta koma bangaren ta, ta zauna kawai ta rasa abin yi har wajen sha biyu idon ta biyu daga baya ta tashi ta dauro alwala tazo ta tada sallah. Kwana tayi akan sallaya tana addu'a akan lamarin yau ko da cikin shege ne a jiki Maryam dole ta tausaya mata dan yarinyar tana jin jiki amman dan me Abbi ya yadda da Aliyu ya kasa yadda da 'yar cikin sa. Ita bata zargin Maryam da son zuciya amman to ta ina ta samu ciki dan me bata fada musu ba shin a ruwa ta sha ko me dole dai sai an tara ake samun ciki to ita a ina ta tara da kuma wa har ta samu ciki......... * Da safe da ciwon kai Ammi ta tashi na tsananin damuwa ko abinci su Baba Ramma ne sukayi. Yaa Alkasim ya amsa ya tafi asibiti. Akan sallaya ya samu Maryam dan sai wajen takwas ta tashi tin jiya da akai mata allura sallolin ta, ta rama ta zauna tana addu'a ga Allah da kuma Yaa Haidar wanda a ko da yaushe bata taba mantawa dashi a cikin addu'ar ta. Yaya Fadima ce ta gaishe da Yaa Alkasim sannan Maryam ta dago ta daga hannu ta gaishe shi. Ya amsa yana fadin "Ya jikin?" Da hannu ta amsa masa. Sannan yace "Allah ya kara sauki!" "Amin!" Yaya Fadima ta fada. Ya ajiye abincin yace "Ki hada mata ko tea ne ta sha!" Kai Maryam ta girgiza mikewa yayi ya dawo kusa da ita yace "Ki daure ki sha kinji kanwata!" Da hannu tai masa alamu da cewa in tasha amai zatai. Kai ya girgiza yace "Ba zakiyi ba insha Allah, ki daure kisha." Ya kalli Fadima yace "Hada mata!" Ta hada mata ta zuba mata dankali da aka soya da kwai, amsa yayi ya zauna a kusa da ita ya dibi tea din a teaspoon ya bata, amsa tayi ta hadiye da kyar tana runtse idon. Yaa Alkasim yace "Ko kefa *Matar Haidar* " Da sauri ta dago ta kalle shi sai hawaye. Kai ya hau girgiza mata yace "Kiyi hakuri kada kiyi kuka kinji!" Kai ta kife a jikin sa tana mai zubar da hawaye dago ta yayi yace "A duniya abun da Haidar yafi tsana shine zubar da hawayen ki, haba yanzu abinda baya so kike yi, shin kina ganin in bakya duniya zai abinda yasan bakya so. In har kiina son Yaa Haidar da son ya kasance cikin farin ciki akan ki kina kiyaye abinda yake so da wanda baya so. Kinji!" Dagowa tayi yasa handkerchief ya fara goge mata hawayen sannan ya kara bata tea din da kyar ta amsa ta hadiye tana dafe kirjin ta, ya dan shafa bayan ta a hankali yace "Sorry kinji!" Yaya Fadima tace "Dazu mukai waya da Abban Iham yace anjima zai dawo in kun gama sai ka kaini gida dan na kintsa ko?" Kai ya gyada ya kuma debowa ya bata ta amsa idon ta na cikowa da kwalla dan har ga Allah bata so damun ta yake a kirji ga cikin ta da taci abu yake mata ciwo. Dankalin ya dauko yai gefen bakin ta da sauri ta mike ta shiga bandaki a guje dan karnin kwan da ya doke ta duk da ya sha hadi an saka wadataciyar albasa da tafarnuwa da black papper ga curry sam ba karni amman ita da yake da dalili sai gashi ya tada mata da zuciya. Bayan ta gama ta fito tana haki yaya Fadima ta gyara bandakin. Nurse ta shigo tai mata allura sannan ta bata magani shima da kyar ta sha sannan Yaa Alkasim ya bukaci su basu sallama taje ta fadawa doctor yazo ya kara duba Maryam sannan ya sallame su. So sukai su fara kai Fadima gida daga baya sai su dawo gida amman Maryam tace ya fara kai ta taje ta kwanta dan jiri take gani. Dan haka a bakin gate ya ajiye ta, ta fito tana dafa bango fitowa yayi zai kamata ya shiga da ita ta girgiza masa kai tai masa alamar zata iya tafiya da kanta. "To shiga na gani!" A hankali ta nufi kofar ta shiga, yana ganin shigar ta ya juya ya koma mota suka tafi. Abbi na shirin fitowa yaga Maryam ta shigo ta nufi sashen Ammi. Karasa fitowa yayi tana shiga ta kwanta akan three sitter tana mai da numfashi, Ammi ta taso da sauri tana fadin "Sannu ya jikin?" Hannun Ammi ta kamo ta rumgume a jikin ta tana wani irin kuka mai taba zuciya. Ammi tace "To menene na kukan?" "Kukan munafurci ne kuma ba a gida na ba!" Abbi ya fada yana shigowa ya jefa musu wani kallo da sauri Ammi ta mike tace "Haba Abbi bakaga a halin da take ba...." "Ki min shiru Amina ke kike son daurewa yarinyar nan gindi, wallahi ba za a rainar min cikin shege a gida na ba....." Dum dum dum haka kirjin Maryam ya buga yanzu Abbi har yana yadda cikin shegene me yasa ba zai tsaya yai bincike ba, tasan Abbi akwai saurin zuciya amman ya kamata ya tsaya yai bincike kan ya yanke hukunci ko? "Me kake nufi?" Maganar Ammi ta dawo da ita daga tunanin da take. "Sai ta bar min gida ta tafi can wajen wanda yai mata cikin ta haife ya kula da ita tinda tana da wanda ya fimu zata bashi kan ta ba tare da sanin mu ba." "Abbi abi komai a sannu ni gani nake ko cikin nan na wani ne zai kasance in ba na Aliy....." "Na fada miki kada ki soma bari ki bata damar daura masa sharri tinda baya duniya bare yace ba haka bane." "Abbi...." "Amina wallahi ba wanda zai canja min hukuncin da na riga na yanke, in har bata son na tsine mata to ta bar min gida, kuma ban yadda taje wajen iyaye na ko yan uwan ta ba. Taje wajen wanda yai mata in ta haihu su dawo tare hukunci ya hau kan ta in ba haka ba kar ta sake ta dawon gida taje ta karasa abinda ta fara." Suman zaune Maryam tayi jin kalaman Abbin ta. Ammi kuwa cikin gigita tace "Me kake nufi?" "Abinda kika ji na fada. Dan haka ta tashi ta fice min a gida." "Ba inda zata in kuwa har Ummi zata bar gidan sai dai mu tafi tare!" "Kofa a bude take amman ban yadda ta zauna min a gida ba." Ya juya zai fita sai ya juyo ya kalli Maryam da sauri ya dauke kai daga kallon ta yace "Kada na dawo na sameki a gidan nan. Kije ki kawon uban cikin jikin ki in ba haka ba kada ki kara kallon gidan nan a matsayin gidan ku." Ya juya ya fita fuuuu. Ammi zama tayi tana kuka. Maryam ta dauko paper ta rubuta "Ammi ki daina kuka, ke kike hanani kuka mu dauki tamu kalar jarabawar nasan Abbi yana cikin bacin rai ne amman Ammi ki sani ba zan aikata abinda addini ya haramta ba. Ammi ni zan tafi kafin Abbi ya dawo!" Ta bata takardar ta shiga daki ta dauki check book dan bata san inda ATM din ta yake ba ta dauki jaka ta fito a bakin kofa ta samu Ammi ta durkusa alamar neman yafiya Ammi ta kamo ta suka shiga daki tace "Ba zan barki tafi wani wajen ba Ummi dole duk inda zaki na kasance tare dake, zan hakura da auren mahaifin ki na kula dake da abinda ke cikin ki, hannun ka baya taba rubewa ka yanke, bansan me Allah ya ke nufin mu dashi ba, zan kasance dake a ko da yaushe." Paper ta dauko ta fara rubutu, tace "Kada kice haka Ammi, akai na zaki rabu da zuri'ar ki nasan kowa yasan me nake tare dashi tsana ta zai yi zanje zan rayu da ciki na da abinda zan haifa tinda nasan ko na fadi na wane ba yadda zakuyi ba. Ammi ki sani zan kula da kai na, ki yafe min Ammi ki nemar min yafiya a gun Abbi!" "Bafa inda zakije!" "Amma kinji abinda ya fada ko? Ban taba sabawa wani a cikin ku ba yanzu ma bai kamata na saba muku ba bayan ni ce mai laifi gwara nabi komai a hankali wata rana sai labari wata rana komai zai wuce, fatana nima yanzu na mutu kawai nabi *Miji nah* bazan iya rayuwa ba Yaa Haidar ba, Ammi ki yafe min!" Ta rubuta ta mike Ammi ta kamata tana gama karantawa ta mike ta rumgume ta tace "Naji zaki tafi amman kije gidan Yaya Fadima zan miki visa ki tafi wajen Ummu ki!" "Ammi, Abbi yace kada naje gidan kowa nasa." "Na sani amman nasan Fadima mai iya rike kice ba tare da sanin Abbi na ku ba kuma nasan zata iya kare zata kula dake bazaki dade ba zaki bar gidan nata kije kinji. Ko bari nazo na kaiki da kai na." Kai ta girgiza tai mata nuni da A'ah Abbi bai sani ba ta zauna kawai. Mikewa Ammi tayi ta dauko kudi ta mika mata tace "Kudin mota kinji!" Kai ta gyada sannan ta mike Ammi na biye da ita suka je bakin gate fadawa jikin Ammi tayi ta rumgume ta tana kuka. Ammi ma kukan take tana fadin "Allah miki albarka ya tsare ki Allah ya shiga lamuran ki! Sai nazo naji komai game da cikin!" Kai ta gyada tana mai jin kunya da nauyin Ammi, har ta fita a gidan Ammi na kallon ta. Itama tana fita tabi gidan da kallo...... *Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe Amin* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 30 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Tana fita taji kirjin ta ya hau dukan uku uku ga kan ta da ya wani sara wanda hakan yasa ta durkusa tana dafe kan ta. Ta jima a haka sannan ta mike ta fara kalle kallen wajen sai kuma ta mike ta nufi babban titi tana tafiya tana haki a haka ta karasa kallon ababen hawa ta tsaye yi napep sai zuwa suke suna tsayawa a gaban ta amman ta kasa tsayar da daya a cikin, sam bata san me ko wanne hali take ciki ba a hankali ta fara taku wanda bata san kan titin ta hau ba wata mota ce taho a guje wanda tana ganin Maryam yasa ya danna wani uban horn tare da taka burki. Da sauri ta dago dan jin horn din shi ya dawo da Maryam daga tunanin da tatafi ta dago da sauri ganin yadda ya taho da gudu yasa ta rude sai kawai ta fadi a sume. Motar yai parking ya fito yayo wajen ta tare da mutanen dake bakin titin ganin bata numfashi yasa ta dauko ruwa aka yayyafa mata amman bata farfado ba da sauri yasa ta a mota ya bar wajen da sauri wani private asibiti ya gani nan ya shiga da ita nurses suka amshe ta. Cikin hukuncin Allah nan da nan ta farfado. Suka duba sukaga ba wata matsala bayani sukai masa sannan sukace zasu iya tafiya. Dakin da take ya shiga ya same ta zaune ta hade kai da gwiwa tana kuka. Karasawa yayi yace "Akwai inda yake miki ciwo ne?" Kai ta girgiza ba tare da ta dago ba. Yace "Kukan me kike to?" Kai ta kuma girgizawa. Kallon ta ya tsaya sai kuma yace "Tashi mu tafi" Da sauri ta dago sai ta zuro kafafun ta, ta mike tabi bayan sa. A haka suka fita compound din asibitin wajen motar sa. Mota ya bude mata sai ta tsaya kallon sa yace "Shiga mana!" Kallon sa ta tsaya sai ta girgiza kai. Murmushi yayi yace "Na miki kama da barawon mutane ne? Shiga na kai ki inda zakije." Addu'a tayi ta shiga sannan ya tada motar kallon ta yayi yace "Ina zakije?" Shiru tayi dan ita sam bata san ina zata je ba. Shiru tayi can sai ta dauko papper da pen a jakar ta ta rubuta masa. Amsa yayi ya karanta yace "Tafiya zakiyi?" Kai ta gyada yace "Wanne garin?" Kai ta dauke dan kuma me zai dame ta da tambayoyi tinda dai ta fada masa inda zata ba shikenan ba. "Fada min mana." A paper ta sake rubuta masa. amsa yayi yace "Yan uwan ki ne acan ko kece can!" Kai kawai ta gyada. Tasha ya nufa da ita sannan yai parking suka fito tana ta kallon tashar daman haka tasha take tamkar kasuwa, a tsorace ta dinga bin bayan sa har sukaje wajen motocin ya saka ta a mota ya biya sannan ya juya ya kalle ta yace "Allah tsare hanya kina kula in zaki tsallaka titi in ba zaki iya ba ki nemi taimakon wani kinji!" Kai ta gyada sannan tai masa godiya da hannu. Tana zaune a motar har ta cika aka tashi mota suka fara tafiya. Tafiya sukai mai nisa dan bata san hanyar ba kwata kwata bata taba yo nan wajejen ba a rayuwar ta to dan me zataje inda bata sani ba amman ta rasa amsar da zata bayar a hankali tana nesa da gida a hankali take manta komai dake tare da ita. Abu daya kawai take ji da jin zata kara nesa dashi shine Yaa Haidar shikenan garin da kabarin sa yake ma ta barshi, hawaye ne ya zubo mata ta daura hannu akan cikin ta da taji yana dan motsi a zuciya take fadin "Yaa Haidar yasan da cikin jiki na kenan kome? In bai sani ba tayaya yake min zancen dan sa na kula dashi nace yana son sa, saboda me yake ce min insa yana masa addu'a kuma na fada masa Dadyn sa na son sa, kenan Yaa Haidar yasan da cikin!" Zancen da take da zuciyar ta kenan. " *Ummu Haidar* " Zuciyar ta, ta ambata. Ido ta runtse tana fadin "Na tashi daga *Matar Haidar* na koma *Ummu Haidar* " Da sauri ta runtse idon ta tana fadin "Ba zan taba tashi daga *Matar Haidar* ba zan kasance matar ka har a aljanna da izinin ubangiji na yadda na amince ni *Matar Haidar* ce kuma *Ummu Haidar* " Sai ta saki murmushi wanda take yi hawaye na zubo mata a idon ta. Hannun ta, ta daura akan cikin ta, tana fadin zance a zuciyar ta "Tamu kalar kaddarar kenan mun rasa Abban ka. Allah ya jikan Abban ka." A haka suka cigaba da tafiya zazzabi na damun ta, ga ciwon ciki ga ciwon jiki ga gajiya. sai karfe biyu suka tsaya sukai sallah masu siyan abinci na siya sannan suka shiga mota suka cigaba da tafiya. Da akai la'asar ma haka. *Bauchi* Karfe shida suka sauka a tashar garin Bauchi. Kallon tashar ta dinga yi dan zatace tin da take bata taba zuwa tasha ba sai yau dazu da kuma yanzu gani tayi tamkar kasuwa duk da magariba ta doso kai amman sai hada hada ake yi. Kalle kalle ta tsaya yi wanda ta rasa ina zata dosa. Ga zazzabin da yake damun ta duk magariba zuwa asuba ya fara tasowa gefen wani shago ta zauna take kuma taji cikin ta ya hau kogin yunwa duk da a gida ba abinci take ci ba amman ko zata dawo dashi ana bata data zauna da yunwa ga karin ruwa da ake mata ko da yaushe. Rabon ta da abinci tin shekaran jiya dan jiya ba ma abinda taci gashi yau tea ne kadai shima cokali uku tasha taje ta harar dashi. "To me zanci?" Ta fada tana shafa cikin nata mikewa tayi tana zagaye kasuwar tana rurufe fuskar ta dan ganin mutane da yawa ga maza masu hankali da marasa shi nutsatsu da wanda ba nutsatsu ba ko a gida bata zuwa kasuwa iyakacin store shima bata fiya zuwa ba gwara ta rubuta abinda take so Biba ta siyo mata da taje in ta fita da Yaa Haidar ne shima tana tafiya tana buya a bayan sa. Mai gasa nama ta gano shi ya bata sha'awa dan haka ta karasa ta bude jakar ta dauki dubu daya a cikin kudin da Ammi ta bata, mika masa tayi tai masa nuni da ya saka mata gurasa guda daya sai nama na dari biyar." Zuba mata yayi ya bata taga mai saida lemon kwalba ta siyi guda daya da ruwa biyu komawa inda ta baro tayi ta zauna ta wanke hannun ta sannan ta juya wa mutane baya ta dauki gurasa daya ta kai bakin ta, da kyar ta cinye ta cire hannun ta, ta bude lemon nama daya ta dauka tana kaiwa bakin ta sai amai haka ta dinga kakarin aman da ba abinda yake fitowa sai gurasar da taci kawai. Rufe naman tayi ta dauraye bakin ta. Lemon fanta ta dan kurba ta hadiye ta rufe dan tasan yanzu zata dawo da ita itama. Amman cikin hukuncin Allah sai bata dawo da ita ba. So take ta dada amman tasan da ta dada zata dawo da shi, ido ta rufe tana kuka tana kiran Yaa Haidar a cikin zuciyar ta. A haka tana zaune aka fara kiran sallah magariba alwala tayi da ruwan da ya rage mata sannan ta ciro dakwalin ta, ta shimfida ta tada sallah. Tana zaune tana rawan sanyi a wajen har aka kira sallah isha'i sallah tayi, ta zaune ta hade kan ta da gwiwa tana mai cigaba da rawar sanyi ga ciwon kai ga yunwa. A hankali ta dinga jin hayaniyar tashar yana raguwa wanda tasan dare ne yayi ko ba a fada ba goma zata iya yi. Tunanin ta daya to ina zataje ina zata kwana. A haka ta rakube jikin wannan shagon wanda bacci barawo ya dauke ta ga zazzabi ga ciwon kai sai firgita take a haka har asuba da baccin ya dan dauke ta ciwo ke tada ta. Ganin an kira sallah yasa ta mike dan neman ruwa tai alwala. Cikin tashar ta dinga bi har ta hango masalaci ta isa ta debi ruwa tai alwala sannan tai sallah a kofar masallacin har karfe shida tana zaune can gefe taga wata mata mai kosai ta fito ta fara soyawa. Zata ce ita bata cin kosai ko a gida amman sai taji yau duk duniya shi kadai take son taci. Mikewa tayi ta karasa ta bata dari biyu tai mata nuni da ta bata kosan. Amsa tayi ta bata tashi da uban yawa komawa tayi gefe ta shiga hijab dan taci amman daya taci kawai taji ya tsaya mata a kirji. Wannan yasa ta bawa almajiran dake wajen sadakar sa. Haka ta koma inda ta zauna jiya lemon ta na jiya ta kara kurba shine kadai ya zauna a cikin ta. Har karfe goma tana wajen wanda a lokaci rana ta zo dan haka ta mike ta canja waje haka ta dinga garari a kasuwar gashi ta gaji tana son ta samu ta kwanta ta huta ga yunwa ga ciwo, a haka har magariba ta kara gabatowa. Wajen jiya anan ta kara zama anan ta kwana washe gari a masallacin cikin tasha taje tai alwala tai sallah gaba daya jikin ta damun ta yake ga ciwo ga rashin wanka. Lemo kawai ta sha bata ce zata siyi wani abu ba dan tasan in ta siya ma asara zatayi, tana zaune ta hade kai da gwiwa kuka kawai take yadda rayuwa ta juya mata. Duk da ba wani abu take tinawa a baya ba amman tasan bata saba da wannan rayuwar ba, abu daya take iya tinawa shine Ammin ta da Yaa Haidar. To Ina Ammi? Shine tambayar ta? Tana wane gari? Sai kuma Yaa Haidar da tasan baya tare da ita ya mata nisan da bazata taba ganin sa ba. Hawaye take dan ga ciwo ga rashin mataimaki. A haka ta yini sallah kadai ke tayar da ita sai lemo take dan kurba wanda in ta sha da yawa shima amai take wanda aman ba komai a cikin ta sai wahala da take sha kawai. Kwana ta biyu a tasha wajen da ta sauka anan yau ma ta kara zuwa ta zauna da akai sallah isha'i tana kwance wajen karfe goma sha dayan dare taji wasu samari suna fadin "Ata ina ma yarinyar take?" Daya a ciki wanda muryar sa take a buge yace "Wajen shagon Bala!" "To muje muga Allah yasa tana nan dan tin shekaran jiya yarinyar ta dauki hankali na." Maryam dake kwance ta jiyo su suna magana dan suna bayan layin shagon da take ta mike duk yadda jikinta ke ciwo ga zazzabi da ciwon kai a hankali ta bi ta layin gaban ta, ta bar wajen tana ganin ta musu nesa ta diba a guje ta fita daga cikin tashar. Titi ta gani babba wanda yake da hasken fitilu tafiya ta fara wanda bata san iya yadda tayi tafiyar ba. Sai da ta ji kafar ta na neman kasa daukar ta, ta zauna ana gefen titin ga yunwa ga zazzabi tana zama ta kwanta anan kasa take bacci ya dauke ta. Karfe biyar na asuba ta farka dan ta fara jin kiran sallah mikewa tayi tana tafiya dan ta samu inda zataga masallaci sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu wani gida Mai wanda gefen sa yar kasuwa ce ga masallaci a ciki. Ciki ta shiga bangaren mata wanda ta samu bandakin nasu a wanke wanka tayi duk da ba sabulu sannan ta fito tai alwala ta shiga masallacin tai sallah tana idarwa ta kwanta dan akwai wuta ga fanka. Bacci ne ya dauke ta wanda bata tashi farkawa ba sai wajen daya da wani abu shima kuma ciwon ciki ne ya tashe ta da motsin da taji cikin ta na mata. Dafe cikin tayi sannan ta mike ta fita yar kasuwar nan ta shiga ta siyi fura da nono da ta gani sannan ta siyi fanta. Masallacin ta dawo ta sha furar wanda tana gama sha ta fita ta amayar da ita. Alwala tayi ta dawo tai sallah sannan ta kurbi fantan ta kwanta. Da ta gaji da kwnaciyar ta isa inda taga Alkur'anai ta dauko Alkur'ani ta fara karantawa shi ranar ta yini tana karantawa. Har yamma da dare anan ta kwana washe gari ma anan tai wanka dan har sabulu ta siya sannan ta kara siyan abincin nata wato fanta wandan sai ta kwana biyu taba shanye daya ba, gashi shi kadai take iya sha a cikin ta. Kwanan ta biyar a cikin masallacin nan masu kula da wajen suka gane da zaman ta wannan yasa suka ce tabar wajen ba wajen kwana bane. Haka ta fito tana bulayin inda zataje ga jiri dake dibar ta dan rabon ta da taci abinci har ta manta duk abinda ta siya zataci loma daya take zata amayar dashi lemo da take dan kurba ya zauna shima ba da yawa take shan sa ba, kuma ko da yawa ne bashi da nutritive value da yake dashi a cikin ta da zai samar ta da duk abinda jikin ta ke bukata. A haka ta dinga tafiya, bata san iyakar lokacin da ta dauka tana tafiya ba, jin baza iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk gefe bawon rake da giginya ta zauna tana sauke numfashi a hankali, iskar wajen yasa ta saka jakar ta tayi pillow dashi, bacci ne ya dauketa lokaci daya a hakan saboda iskan da bishiyar ke ta bayar wa, bata san lokacin da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, da sauri ta mike tana kalle kallen wajen jakarta ta dauka a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta zauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai Maryam take, ganin ta a wani kasuwa ta dinga zaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga zazzabi kan kace me kasuwar yayi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga zaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska zai hura ta, ta fadi ga wani ciwon kirji da ta tashi da, banda zugi da azaba babu abinda yake mata. masallaci ta samu a kasuwar tai alwala tai sallah sannan ta mike ta cigaba da tafiya. *Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan amin.* *Antty*[11/13, 13:59] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 31 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* HML MY SISTER HASSANA ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN Har karfe hudu ba Alkasim ba wayar Yaya Fadima, wannan yasa hankalin Ammi ya dan tashi, amman kuma sai tai zaton ko Alkasim ya riga ya bar gidan Yaya Fadiman ya tafi wani wajen, ita kuma tana can tana aiki kila shiyasa bata kira akan zuwan Maryam din ba. Tunanin mafita take akan Maryam, tin da tayi sallah isha'i ta kasa tashi a wajen, ji tayi zuciyar ta ta karye so take ta tashi ta kira Fadima amman sai taji ta kasa tashi ta rasa me take ji, sallamar Alkasim shi ya katse mata tunanin da take, ta amsa ya shigo ya zauna a gefen gadon nata yana fadin "Daga dakin Maryam nake naga bata nan ina ta shiga?" Kallon sa tayi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tace "Dazu bayan kun kawo ta Abbin ku yace bai yadda ta zauna masa a gida da cikin da bai san uban sa, lallai sai taje ta nemo masa mahaifin yaron sannan ta zo a yanke musu hukunci." "What? Abbi me yake so yace? Yana so yace Maryam mazinaciya ce?" Kai ya hau girgizawa yana fadin "Ko duniya zata taro akan cewa haka ni ba zan yadda ba, me Maryam ta sani?" "Na shiga rudani da damuwa amman nace zan tura ta can Saudiyya wajen Ummun ku." Kallon Ammi yayi yace "To yanzu Abbi da yace ta bar gidan ina take so taje, meyasa idon Abbi ya rufe akan alamarin nan, ai dole abi komai a sannu bai ga halin da take ciki bane?" Tagumi Ammi ta sauke, ya mike yace "Ina yanzu ta tafi?" "Gidan Fadima tin dazu nace ta tafi." Da sauri ya juyo yace "Tin yaushe?" "Baku dade da kowa ta, yazo yai maganar lokacin ko azahar ba ai ba ta tafi." "Ammi har bayan la'asar ina gidan Fadima fa, kuma Maryam sam bata je ba." Ido Ammi ta zaro tace "Bangane bata je ba, daukon waya ta na kira dai naji ko taje daga baya." Wayar sa ya zaro ya fara neman layin Fadima tana dauka tace "Tin dazu nake so na kira naji ya jikin Maryam ka same shi?" Shiru yayi can yace "Bata zo gidan ki ba?" "Wa din?" "Maryam." Ya bata amsa. Kai ta girgiza tace "Bata zo ba nan tace zata zo." Wayar ya kashe ya kalli Ammi cike da damuwa yace "Ammi bataje gidan Fadima." "Anya Alkasim ko dai bata son ta fada ne dan Abbi yace kada taje masa gidan iyaye ko ya'ya tashi maza kaje ka gano min dan Allah." Mikewa yayi ya dauki mukullin motar sa ya fita a gidan da sauri mota ya shiga ya nufi gidan Fadima. Ba kowa a falo sai Ilham dake kallon TV ya shiga ya zauna ta karaso tana fadin "Uncle ina yini?" "Lafiya lou daughter ina Momyn ki?" "Yanzu Dady ya dawo ta shiga ciki." "To Aunty Maryam tazo yau?" "Uncle an sallamota a asibiti, zan bika na dubo ta." Fadima ce ta fito turus tayi ganin Alkasim tace "Yaya lafiya?" "Ammi ce ta aiko ni." "To me ya faru?" "Akan Maryam ne tace nazo na gani ko kin boye ta ne?" Zama tayi cike da mamaki tace "Bangane ba fa." Fada mata komai yayi salati ta saki tace "Na shiga uku to ina ta tafi wallahi Yaya Alkasim batazo ba ai sai bayan la'asar ka tafi kuma wallahi tin fitar ka ba wanda ya zo gidanan." Da sauri ya mike yace "Bari naje gidan Yaya Ummulkhairi Allah yasa can ta tafi." Ya fita can ma da yaje ba Maryam ba alamun ta, gidan Yaya Zainab ma, wannan yasa ya kira Aisha bayan sun gaisa yace "Maryam tazo nan ne?" "An sallamo ta ne dazu naso na shigo to yau na tashi da zazzabi shiyasa ban shigo ba." "An sallamo ta dazu bata zo nan ba kenan?" "Eh!" Rukayya ya kira nan ma ba wani good information take hankalin sa ya tashi,  a cikin daren nan ya dinga bin gidan yan uwa amman duk inda yaje ba Maryam hankalin sa ba karamin tashi yayi ba har sha biyu yana waje, Ammi taje neman sa ko ya dawo yafi a kirga amman shiru duk ta kasa bacci tana zaune a falo ya shigo gidan a matukar gajiye ga damuwa na rashin ganin Maryam mota ya ajiye Ammi ta leko taga zai yi sashin su ta kira sa juyowa yayi ya nufi falon ta koma ta zauna ya shiga ya zauna kansa a kasa tace "Tana ina kuwa?" Dagowa yayi cike da damuwa yace "Ammi bansan inda ta shiga ba nayi zagayen gidaje da yawa amman ba wanda yaga Maryam a cikin su...." "Innalillahi wainna ilaihir rajiun." Kuka mai sauti Ammi ta saka wanda yasa Alkasim shiga cikin wani tashin hankalin,  "Na shiga uku, ina kika shiga Maryam ina kika je, innalillahi wainna illajir rajiun." Haka ta dinga maganganu ita kadai kamar wacce ta fara zarewa, Yaa Alkasim ya koma gaban ta ya kama hannun ta yace "Ammi ki nutsu zuwa gobe da safe insha Allahu tana wani wajen da yaddar Allah." "Kayya Alkasim ina tsoron kar Maryam ta shiga duniya ban san wane hannu zata fada ba, ga ba lafiya ga rashin baki, ga karacin shekaru ga ciki, ga mutuwar Aliyu ga korar da akai mata ka fada min da wanne zata ji hakika ina tsoro ina ma nabi yarinya ta ina ma na hakura da wannan auren akan na barta ta tafi innalillahi wainna illahir rajiun, Allah ka kular min da yarinya ta Allah ga amanar Maryam nan ka samin ido akan ta a duk inda take Allah ka bayyana min ita" Abdullah da ya shigo yaji maganganun Ammi sai ga hawaye, Alkasim kuwa tausayin Ammi da Maryam yake ji, da tunanin inda Maryam take, A nan falo ranar suka kwana tin asuba suka fara buge bugen waya gari na fara haske kuwa Abdullah da Yaa Alkasim suka shiga gari sune gidajen kawayenta da yan uwa har da tashoshin mota tare da hoton Maryam suna tambayar ko an ganta. Da su Yaya Muhammad suka shigo ma ta fada musu sai suka bazama neman Maryam. Ammi tayi kuka har ta gaji. Su Yaya Fadima, Yaya Ummulkahiri da Yaya Zainab duk sun zo suna zaune jigum jigum, Abbi kuwa yana can bangaren sa sam bai san abinda yake faruwa dan shi fushi yake da Ammi sosai akan wannan abun." Da Umma taji batan Maryam wani dadi taji tai ta murna abinda take so ya tabbata. Yaya Zainab, Fadima, Ummulkhairi ne duk zaune a falon Ammi, sunyi jungum jugum tin safe suke zaune har magariba ba wani bayani, suna zaune Yaya Muhammad, da sauran yan uwan duk suka shigo zama sukai, Yaya Fadima tace "Yaya dai an dace?" Kai Abdullahi ya girgiza yace "Ba inda bamu karade ba a cikin garin Kano amman ba Maryam ba alamun ta." Dai dai shigowar Abbi da fitowar Ammi daga daki, kana ganin ta zaka sa bata cikin hayyacin ta, cikin yini daga duk ta rame, idon ta duk ya kumbyra saboda kukan da tasha,  tana fitowa taji abinda ya fada, kai  ta dafe hade da kirjin ta, juwa ta fara gani wanda kan ta farga ta yanke jiki ta fadi, cikin tashin hankali gaba dayansu suka nufi kanta, amma banda Abbi da ya daskare a gurin ya kasa motsi, Ammi suka dauka suka kwantar suka shafa mata ruwa farfadowa tayi likitan da da aka kira jin tana suruta tai mata allura take bacci ya dauke ta. Kallon su tayi tace "Jinin ta ya hau dole ku, kula da ita a kula kada a bari ranta yana baci, sannan kar ana fada mata abun da zai na tada hankalin ta." "Insha Allahu." Suka fada. Abbi da yake tsaye a kanta yai mata tofi, Juyawa Abbi yai zai fita Yaa Muhammad yace "Abbi Maryam ce fa ba a gani na." Juyowa yayi yace "Ko da kunga Maryam bana bukatar ta a gidan nan.." "Abbi dan kayi hakuri." Wani irin kallo Abbi ya juya ya watsa masa wanda yasa shi matsawa baya saboda tsoro, juyawa Abbi yayi ya maida hankalinsa kan su cikin wani irin bacin ran da basu taba ganinsa ba, sai da ya gama kare musu kallo sannan yace "Why Maryam? Why? meyesa ta lalata rayuwar ta haka? Meyesa ta bari shedan yaci galaba akan ta har ta aikata irin wannan danyen aikin? Wani irin son duniya ne yakai ta ga aikata zina? Me muka rage ta dashi a gidan nan? Irin sakayyar da zatai wa soyayyan da muka nuna mata kenan...?" Ya karashe maganan idanunsa na tsiyayar da hawaye hannu yasa ya share hawayen dan abun ba karamin damun sa yai ba, daga baya yace "Hakika Maryam tazo mana da babban Alamari a cikin zuri'armu Allah ya na gani na bata tarbiya iyakan iyawata tunda nake a rayuwata ban taba rike koda hannun mace ba, ban taba kallon mace da wata manufa ba amma sai gashi yau 'yar da na haifa a cikin cikina, 'yar da nake sonta tamkar raina, 'yar da na fifitata fiyeda yayana, 'yar da nakeji zan iya yin komai don ganin rayuwarta ta inganta ta kwaso mun abun kunyar da har na koma ga ubangijina bazan taba wanke kaina a idon duniya ba..!" Girgiza kansa yayi cikin kunan rai ya dafe kirjinsa da ya soma yi masa zafi cikin shakekkiyar murya ya cigaba "Hukuncin da na dauka akan ta shine dai dai ba zan iya cigaba da kallon mafi soyuwa a cikin 'ya'ya na dauke da wannan abin kunyar ba, a cikin gida na, ba." Yaa Alkasim ne yace "Dan Allah Abbi me yasa ka yanke hukunci akan abunda baka sani ba, Abbi kunsan halin Maryam kunsan abunda zata aikata da wanda bazata aikata ba ku yarda da ita wallahi ba haka halinta yake ba akwai wani abu a kasa..!" Bai kai ga karasawa ba yaji saukan wani gigitaccen marin akan fuskarta dafe kunci yayi,  Abbi yace "Ina fada kana fada, me kake so na bincika, ko kalawa yaro sharri yana kabarin sa ba zan taba yadda ba." "Abbi kayi hakuri amman tabbas Maryam kome ya faru da ita Kaddara ne." "Kaddara! Wannan ba kaddara bace son zuciya ce kawai irin nata da rashin godiyan Allah akan ni'imarsa me na rageta dashi da har zataje ta bada kanta ga wani ya lalata mata rayuwa..?" Yayan Abbi Alhaji Usman da ya shigo yace "Muhammad me kake fada ne haka? Kada zafin zuciya yakai ka ga sabawa mahaliccinka, kada ka manta fa babu bawan da ya isa ya tsallakewa kaddararsa kaima baka wuce hakan a gurin ubangiji ba bai kamata akan dan wannan  abu ka nemi sa kanka a halaka ba kayi tunani akan hakan..!" Ya karashe maganan yana mai kamo hannunsa cikin tsigar rarrashi, wani irin murmushin takaici Abbi ya sake yana kokarin kwatan hannunsa yafara cewa "Yaya Usman bazaka fahimci abinda nake ji ba...." Yana fada ya juya zai bar wajen, har ya kai kofa ya juyo yace "Ku barta ban yadda wani ya kuma neman ta ba tinda ta zabi can din taje Allah ya bada sa'a." Yana gama fada ya juya ya fita, Yaa Alkasim ya mike ya fice a dakin da sauri yana fadin "Sai dai Abbi ya koren amman neman kanwata yanzu na fara." Ya fice a gidan, wajen karfe goma ya dawo dakin Ammi ya shiga har lokacin bacci take saboda allurar da akai mata, ganin dare yayi duk suka tafi aka bar mata matan a wajen ta. *Allah ya jikan mu, yasa muyi kyakyawan karshen Amin.* *Antty* [11/13, 13:59] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 32 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* * Wani babban waje ta gani gefe wani katon masallaci wanda yake da bangaren maza da mata ga motoci da alama wasu matafiya ne suka tsaya yin sallah da cin abinci dan lokaci daya saura na rana. Ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta zaga bayi sannan ta shiga cikin masallacin ta tada sallah, tana ta zaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo ya buga karfe daya da rabi ta mike a hankali ta fita ta don duba abinda zata siya ta ci, tuwo da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta zauna ta bude ledan abincin tana gutsura guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar zata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari ta koma cikin masallacin ta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan tuwon ba, tana mayar da numfashi, ta kwanta ta dukunkunewa waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da zazzabin da ya rufeta lokaci daya, sai la'asar ta farka jin ana kiran sallah. Daren ranan a masallacin Maryam ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da zata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanzu, cike da fada take maganan, jikin Maryam yayi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lokacin saboda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga zazzabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda zata je ba, ganin ba zata kara ko da taku daya ba don kafafuwarta sun ma gaza daukar ta kuma ta fara tunanin ta nemi wani masallacin ta samu ta dan kwanta ko na kwana daya ne daga nan in sun kore ta ta kuma samun wani a bakin titi ta tsaya tana son samun napep dan bata jin zata iya yin tafiya kuma. Dayan hannun ne na tafiya dan haka ta nufi kan titin dan ta tsallaka wata mota ta taho da uban gudu tana dannan horn juyowa tayi duk sai ta rikice wanda me motar yana dannan burki amman yaki ya tsaya sai da yazo daf da ita sannan motar ta tsaya. Wanda Maryam ta durkushe a kasa dan ta rasa ina zatayi. Driver ne ya fito da sauri sannan masu motar da ake tukawa wasu dattawan Mata da Miji suka fito da sauri. Matar babba ce dan a kalla zatai shekara arbain da takwas haka, fara ce sosai wacce ke sanye da doguwar riga ta less army green ta saka milk mayafi akan ta. Indon ta sanye da farin glass, Wanda kana ganin su zaka san manyan mutane ne. Mijin ma manyan kaya ne a jikin sa milk shadda sai kyalli take ya saka yar ciki da babbar riga haka ya saka hula mai kyau da tsada sai tashin kamshi suke. Motar bayan su da take basu tsaro suma suka fito da sauri sukayo kan Maryam. Matar ce ta karasa ta dago Maryam wanda Maryam tayi baya zata fadi, da sauri matar ta kamo ta tana fadin "Suma tayi!" Mijin ta, ta kalla tace "Samo mana ruwa suma tayi!" Daya daga cikin security ta ne yai maza ya karasa ya dauko ruwa a mota ya kawo, amsa tayi ta zuba a tafin hannun ta, ta shafa mata tayi a fuska amman bata farfado ba. Dago ta tayi ta nufi mota da ita tana fadin "Ado a samar mana asibiti nan kusa please." "Ok Maah!" Ya fada ya shiga mota sauran ma suka shiga cikin mota. Mutumin da suke tare can gidan baya ya shiga matar da Maryam kuma suna gidan tsakiya. Sai da sukai tafiya mai nisa sannan suka samu wani private asibiti mai kyau ciki suka shiga Matar ta fito da ita da sauri suka shiga ciki. Nurses ne suka amshe ta suka wuce da ita emergency, nan da nan suka shiga wani daki da ita suka kwantar da ita suka fara ceto rayuwar ta. Ko da numfashin ta ya dawo allurar bacci sukai mata saboda sun gane bata cikin nutsuwar ta kuma tana bukatar hutu sannan suka saka mata ruwa. * Maryam bata sake sanin abinda ya faru ba sai bayan kusan awa takwas da faruwar abun. A hankali ta bude idonta da yayi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yayi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe kirjin ta dake mata zugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lokaci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wannan matar da ta fito a mota wacce ke zaune d'an nesa da ita idanuwan ta da hankalin ta gaba daya na kan wayar dake hannunta, kokarin mikewa zaune take da kyar har lokacin tana dafe da kirjin ta dake mata azaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, motsin ta da taji yasa ta kallo direction dinta, mikewa tayi da sauri ganin ta tashi ta karaso kusa da ita tace "Sannu ya kike ji?" Shiru tayi. Matar ta karaso ta dafa ta tace "Are you there?" Da sauri ta dago kan ta, ta gyada mata kan ta. Juyawa tayi ta fita bata jima ba suka dawo da nurse da doctor. Likitan ya karaso yace "Hello... how you feeling now?" Shiru tayi yace "Hey... Are you there?" Kai ta gyada yace "Ok... How you feeling madam?" Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tai musu nuni da hannu alamar "Alhamdulillah" Kallon ta likitan ya danyi sannan yayi murmushi yace "Daman bakya magana ne?" Kai ta gyada masa. Yace "Ok, hope babu Inda ke maki ciwo yanzu koh?" Ta gyada masa kai duk da azaban da kirjin ta yake mata. Yace "Good" Sannan ya juya ya fita, kallon matar dake tsaye tayi cikin sanyi matar tace "Sannu ya jikin?" Abun rubutu tai mata nuni da tana bukata jakar ta dake gefen ta dauko ta dauki memo da pen ta mika mata rubutu tayi ta rubuta mata "Me nake yi a nan?" Amsa tayi ta karanta sannan tai murmushi tace "Kar ki damu za a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, munzo zamu wuce ke kuma kinzo tsallaka titi shine kika tsorata daga nan kika suma muka kawo ki asibiti. Ina fatan babu wata matsala dai ko?" Kai ta gyada mata. Matar tace "Mun jima anan wajen eight hours ki bani number 'yan gidanku a kira i know duk inda suke hankalin su a tashe yake dan awa takwas da yawa. you passed out since in the afternoon... And this is...." Ta kalli agogo dake daure a hannun ta tace "Ten minute pass Eight pm" Waya matar ta dauka tai magana ba dau minti biyar ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, dayar kuma ledar abinci ne. ta ajiye tai mata sannu sannan ta fita. Matar ce ta matso ta bude mata abincin tace "Kici kinji!" Waya ta miko mata tace "Before then, ki kira gida ki sanar musu." shiru tayi bayan ta karbi wayar, ta fada mata sunan asibitin sannan ta fita, hawaye ya cika idon Maryam ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan minti goma ta dawo dakin... kallonta tayi sannan ta kalli abincin ta d'an daure fuska sai kuma ta karaso ta dauki cokali ta mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, matar tace "Kin sanar dasu?" Kai ta Gyada mata. Kallon ta tayi tace "Tayaya kikai musu magana." Ido tai tsuru tsuru dashi. Wani kallo matar tai mata sannan ta amshi wayar ta duba ko text tayi amman ba wani text kallon ta tayi tace "Ki ci abinci ki sha maganin yanzu, na maidaki gida." Dibar abincin tayi ta kai bakin ta. amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar zata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar zuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta. Kallon ta matar ta tsaya yi cikin tausayawa take tambayar kan ta ko dai bata da lafiya ne daman dan duk a rame take kuma ta dashe duk da ba sanin ta tayi ba before. Haka suka kwana a dakin Sam matar batai bacci ba tana kallon Maryam dake ta rawar sanyi da motsa baki wanda magana bata fitowa wanda ke nuna tana jin jiki. In zaka gane sunaye biyu kawai take motsa baki ta kira ko tace Ammi ko Yaa Haidar sune sunayen da take kira kawai. Suma sai da ta kurawa bakin ta ido sannan ta lura sosai. A haka aka kira sallah asuba matar shiga tai wanka ta fito ta canja kaya. Wani less ta saka blue black ta yafa farin mayafi sannan tai sallah anan kan sallaya. Bayan ta idar tazo ta tashi Maryam da har lokacin zazzabi bai bar jikin ta ba. Ita ta kamata ta kai ta bandaki ta hada mata ruwan tai alwala a zaune tai sallah dan jiri take gani. Tin jiya da dare aka sallame su amman saboda ba wanda yazo daga gida kuma itama tana gama cin abinci bacci ya dauke ta yasa suka kara kwana. Dakin likita taje ta sanar masa patient din nan fa bata da lafiya. Tare suka dawo ya same ta cikin tsananin zazzabi. Kallon Matar yai yace "Tasha maganin ta na jiya?" "Bata sha ba dan abinci ma tana yin one spoon ta amayar shine take ta bacci sai yanzu ta tashi." "Bari na aiko nurse ta dibi jinin ta naga ko akwai abinda ke damun ta." "Ok!" Ya fita bai jima da fita ba nurse ta shigo ta dibi jinin ta sannan ta fita. Tana zaune wayar ta, ta hau kara dauka tayi tare da murmushi tace "Son ka tashi lafiya?" Ta can gefen yace "Alhamdulillah sai dai missing Ummi na zai kashe ni." "Subhanallah! Am sorry my Son insha Allahu yau zamu karaso. Jiya mun samu dan accident ne!" Da sauri yace "Garin yaya shiyasa bana son tafiya mai tsayi a mota ya kuke ba wani problem ko?" "Haba Son Calm down ba wata matsala wata yarinya ce ta shiga gaban titi bama mu buge ta ba ta suma so shine muka kai ta asibiti yarinyar dai bata da lafiya ne ma tin jiya aka sallame ta amman ba wanda nata yazo shiyasa." "Ummi to ya take ya jikin nata?" "Da sauki yanzu za ai mata test duk abinda ake ciki insha Allahu zuwa anjima zamu taho nasan yanzu Abba ma zai karaso." "Ok Ummi ki kula min da kanki sosai da sosai." "I will insha Allahu! Ina Yar uwa ta?" "Tana nan ban fita ba yanzu na tashi da missing Ummi na." "Ok bari na kira ta mu gaisa. Nima nayi missing naka fa My Son two week din nan kamar two month haka nake jin su." "Love you Ummi!" "Love you too My Son bye!" Ta kashe wayar tana kiran number Yayar tata. Sun gaisa take fada mata matsalar da suka samu. "Kina da matsala wallahi Aisha ki taho kawai ba dai kin ce ta kira yan uwan ta ba sa zo su cigaba da kulawa da ita ke menene naki na tsayawa kina fama da ita uhmm!" "Yaya ai taimako ne ni nasan taimakon da zan nema nan gaba." "Ai kinyi na Allah. Allah kuma ya gani zai baki lada." "To shikenan sai anjima" "Aha!" Sukai sallama. Abba ne ya kira ta akan ya karaso tace ya shigo dakin ya shiga ta gaishe shi ya kalli Maryam dake bacci yace "Yarinyar nan amman tana wahala da yawa bata da lafiya dai ko?" "Haka nake tunani shiyasa nasaka Doctor yai mata test a gano me dame ke damun ta." "Allah bata lafiya." "Amin!" Ya kara kallon Maryam yace "Yan uwan ta basu zo ba." "Ina tunanin wani abu akan ta, bari dai ta farka muji." "To!" Knocking akai suka bada izinin shigowa, daya daga cikin securityn su ne ya shigo ya gaishe da Ummi sannan ya ajiye mata basket din ya shigo dashi. Suna zaune doctor yasa aka zo aka dauki Maryam a wani gado. *Allah ya jikan musulmai, ya kyautata namu zuwan. Amin* *Antty* [11/14, 12:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 33 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* ****** Kano A lokacin da Abbi ya dawo daga masallaci ya shiga bangaren Ammi a dai-dai lokacin Ammi ta farka daga baccin da take tun jiya cikin hanzari Abbi ya karaso yana mata sannu tare da taimaka mata ta zauna, bin dakin Ammi tafarayi da kallo a hankali abunda yafaru yafara dawo mata sabo fil a kwakwalwanta nan take hawaye suka fara zubowa akan kuncinta kallon mijin nata tayi cikin rawar murya tace "Shin da gaske ne abunda kunnuwana suka jiyemun ko kuma mummunan mafarki nayi..!" Abbi baice da ita komai ba, dan halin da yake ciki, mahaifin sa Malam ya aiko yaje a yau yau din nan wanda ya tabbata akwai matsala bai sam a yaya Malam zai dauki abun ba.  Kallon ta Abbi yayi ya mike ya nufi cikin toilet itako ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba bai dade ba ya fito yace "Ki tashi ki kimtsa kiyi sallah lokaci na tafiya..!" A hankali tafara saukowa daga kan gadon ta nufo inda yake ta dafa bayansa cikin sanyin murya tace "Alhaji Ina tambayarka kamun shiru ina Maryam take, da gaske ba a ganta ba?" Runtse idanu Abbi yayi cikin tsantsar bakin ciki da bacin rai ji yake kaman ya hadiye zuciya ya huta da kyar ya iya saita kansa ya juyo ya kwakulo murmushin dole ya daura akan fuskarsa saboda Dr yace a guji abunda zai bata mata rai ko ya tsorata ta nan kusa, dafata yayi cikin tsigar rarrashi yace "Kije kiyi sallah lokaci na wucewa zan miki bayanin komai zuwa anjima..!" Ya karisa yana mai kama hannunta ya nufi bakin toilet da ita, haka ta rika binshi duk da tana cikin fargaba da tsoro amma kuma haka nan taja bakinta tayi shiru tabi umarninsa, yana ganin ta shige ya juya ya fita falo bai jima ba ya koma daki akan sallaya ya tarar da ita tana lazimi don haka sai ya  koma sashen sa ya shiga  bathroom shima ya watsa ruwa har ya fito ya fara shafa mai bayan ya gama ya kimtsa a cikin fararen kaya a dai-dai lokacin ne ya koma sashen Ammi  ya same ta akan sallaya har lokacin tana ganin sa ta mike tana ninke sallaya hade da gaishesa fuskarsa dauke da murmushi ya juyo yana amsawa hade da tambayarta ya karfin jikin nata yanzun tace dashi Alhamdulillah da sauki sosai kafun ya sake cewa wani abu wayanshi dake kan gado tayi ringing. Sai da gabanshi yafadi ganin numbern dake yawo akan screen na wayar cikin sanyin jiki Abbi ya daga wayar "Malam yace a yau yake bukatar ganinka.." Iyakacin abunda aka fada kenan wayar ta yanke wani yawu mai daci ya hadiye, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoro dakyar ya saita kansa ya kama hanyar fita yana mai cewa "Idan kin gama shiri ina jiranki a falo kuma kiyi sauri munkusa makara.....!" Baki a sake ta bishi da kallo kirjinta na cigaba da bugawa tunani take ina Maryam take? Sannan me Abbi yake nufi da kin gaya mata komai? To wai ma ina zasuje can kuma ganin babu inda tunani zai kaita yasa ta bude wardrobe a kasalance ta dauko kayanta ta saka babu wani kwalliya ta dauki mayafinta kawai ta rufa ta fito a falo kuwa ta tarar dashi. Baice da ita komai ba ya nufi hanyar barin dakin ta bishi a baya suka nufi parking space inda Alkasim da Abdulah suke tsaye suke jiran fitowansu, da daddaya suka rika gaishe ta da tambayar ta ya jiki itama jiki a sanyaye ta rika amsawa tana mai karewa gidan kallo kamar ranar ta fara ganin sa, haka nan suka shiga suka tada motar maigadi na musu Addu'an dawowa lafiya. Alkasim ne ke Jan motar a yayin da Abdullah ke zaune a gefensa su Abbi kuma suna zaune a baya, duk yadda Ammi taso tambayan Abbi abunda ke faruwa hakan ya faskara saboda bai bata fuskan hakan ba haka suka cigaba da tafiya shiru babu mai magana. Dan su Yaa Muhammad da su Yaa Ummulkhairi sun rigasu barin garin tin safe saboda Ammi bata tashi ba shiyasa su Alkasim basu tafi ba, duk da Alkasim bai so ya tuka Abbi ba dan ba yadda zai yi amman yana jin ciwon abinda Abbi yayiwa Maryam yanzu ko tana wane hali duk damuwar sa ya take ya jikin ta. ****** ADAMAWA 4:20pm Tassss.... Kakeji Malam ya dauke Abbi da wani gigitaccen marin da ya tsorata dukkan wadanda ke cikin dakin saboda hakan bai taba faruwa ba a tarihin gidan, Malam mutum ne shi da bai yadda da dukan ya'yansa ba duk wani laifi da zakai masa sai dai ya kiraka yayi maka wa'azi ko matansa ne baya barin su dakar masa ya'ya sai dai idan a bayan idonsa amma sai gashi yau Malam harda mari, cikin tsananin bacin rai Malam yake bin Abbi da kallo idanun nan nasa sunyi jazur kaman garwashin wuta babu wanda bai tsorata da ganin yadda Malam ya koma ba saboda basu taba ganin hakan ba daga gareshi duk tsawon zamansu dashi cikin wani irin yanayi Malam yafara magana "Hakika Muhammad ban taba tunanin cewa baka da hankali ba sai yau, bantaba tunanin zaka aikata irin wannan danyen hukuncin batare da ka sanar dani ba" Cikin zubar hawaye Abbi ya kalli mahaifin nasa yana kokarin yin magana amma Malam ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, wani yawu mai daci ya hadiya kirjinsa na cigaba da bugawa, Malam maida idanunsa yayi ya kalli Ammi yace "Sannan ke kuma kika kasa kira ki sanar dani abinda ya faru tinda shi yafi karfin ya fada min ko? ya koreta daga gidan batare da kunyi yunkurin fada min ba ko? To ina zata in ba nan ba?" "Yace kada tazo wajen iyayen sa da yan uwan sa...." Wani kallo da ya watsa mata ne yasata hadiye maganartata ba shiri tana mai sauke idanunta kasa saboda bazata iya juran ganin nasa idanun ba, safa da marwa Malam yake yi a tsakiyan falon tsit kakeji kaman babu wata halitta dake motsi a cikin perlourn duk da cewa a cike yake saboda family house ne Abbi ne da Yayan sa Usman kadai suka bar garin da gidan, gaba dayansu a tsorace suke da yanayin mahaifin nasu don basu taba ganin bacin ransa haka ba juyowa yayi ya kara maida idanunsa kan Abbi sannan cikin kunan rai ya cigaba da cewa, "Dan kai ka hada mu da ita shine kake so ka nuna iko akan ta kace kar tazo wajen yan uwan ka, to ka sani zan iya rabuwa da kai amman ban rabu da ita ba, akwai wata karin hausa da aka ce abin kwan yafi kwan dadi...." Ya dago ya kara kallon Abbi yace "Hakika yau ina cikin wani irin bakin ciki da bacin rai wanda bantaba tsintar kaina a cikinsa ba tunda nazo duniya, wai shin anya ma kanada tunani kuwa, kana tunanin wannan hukuncin daka dauka akan Maryam kayi daidai kenan? Daka koreta gidan ubanwa kake so taje? Shin kayi tunanin hannun wa zata fada? Kayi tunanin wani irin hali zata shiga? Kana tunanin Maryam zata aikata wannan gagarumin laifin? Kafun ka tuhumeta yanada kyau kai kafara tuhumar kanka saboda Allah subhanahu wata'ala yace " idan kabi Matar wani kaima za'abi naka, idan kabi kanwar wani kaima za'abi naka, haka nan idan kabi yar' wani kaima za'abi naka" shin kayi tunanin hakan kafin ka koreta daga gidan ka..?" Malam ya karasa maganan yana mai bin dukkan mutanen dake falon da kallo zuciyarsa na suya kaman zata ballo kirjinsa ta fito, wuri ya nema ya zauna yana mai sauke ajiyar zuciya ya dauki tsawon lokaci kansa a kasa baice komai ba, a cikinsu babu wanda yayi koda tari ne saboda a tsorace suke, Abbi ne cikin sanyin murya ya fara magana "Ya Allah kaine shaida akan komai tunda nake a rayuwata ban taba aikata zina ba." "Shiyasa nake tabbacin cewa Maryam bazata taba aikata abun ashsha ba na tabbata kaddarace kawai ta fado mata saboda ban gina zuri'ata da gurbataccen jini ba kaman yadda nima nawa mahaifin bai ginani akan hakan ba, Allah ka wadatani da arziki dai-dai gwargwado ka kuma wadatani da ya'ya' ka horemun ilimin addini ka darajani a idon duniya tun ina matashina, a cikin ya'yana babu wanda ya taba dauko wata hanya da ta kwaucewa fadin ka ya Allah, tunda nake a rayuwata baka taba kaddaramun wani abu na batanci ba a cikin zuri'ata sai wannan abu da yafaru yanzun wanda ni inada tabbacin cewa wannan wata kaddarace wanda ka saukar mana a cikin zuri'armu baki daya amma maimakon mu rungumi wannan kaddara hannu bibbiyu mu kuma yi kokarin cinye wannan jarabawa daka daura mana sai gashi muna kokarin butulce maka muna kokarin mantawa da irin ni'imar da muke ciki na tsawon shekaru muka...........!" Malam kasa karasawa yayi saboda muryarsa da yafara sarkewa da alama kuka ne yake son kubce masa don haka sai yayi shiru kawai yana maida kansa kasa idanunsa kuma suna fidda ruwa, dukkansu kura masa idanu sukayi kowa jikinsa yayi sanyi jin furucin Malam hakika maganganun sa ya shige su sosai sai a yanzun ya tabbatar da ganganci da kuma kuskuren da ya tabka a rayuwarshi wani hawaye mai dumi ne ya zubo masa akan kuncinsa a hankali ya rarrafa ya nufi inda mahaifin nasa yake ya kamo kafarsa cikin muryan kuka yace "Dan Allah Malam kayi hakuri hakika ni Muhammad na zama mai butulci ga ubangijina bacin rai ne ya kaini ga aikata hakan amma dan Allah kayi hakuri karkayi fushi dani...!" Sai da ya dauki tsawon lokaci batare da yace komai ba kafun daga bisani ya mike ya basu baya cikin kakkausar murya yace "Na baku kwana biyu rak daga kai har yan'uwan naka kuje ku nemo inda Maryam take ku dawo da ita cikin gidan nan...!" Yana kaiwa nan ya fice daga falon ya nufi waje, suma da daddaya suka rika barin perlourn har suka watse ya rage daga Abbi sai su Yaa Muhammad da su Inna, a hankali Abbi ya matso kusa da Inna amma kafun yayi yunkurin yin magana ta mike tabar masa perlourn, zuba mata idanu yayi har ta bacewa ganinsa, Hajja ce ta dafa kafadarsa jiki a sanyaye ya juyo yana kallonta, cikin muryan rarrashi tace "Muhammad ka kwantar da hankalinka insha Allahu za'aga Maryam ka cigaba da yi mata addu'a kai mahaifinta ne fushin ka akanta mummunan hadarine a gare ta don haka addu'a shine maganin komai!" Kamo hannunta yayi cikin sanyin murya yace "Haka ne Hajja amma dan Allah ki tayani bawa Malam da Inna hakuri saboda bazan iya jure fushinsu akaina ba..! Maryam kuma na daina fushi da ita Hajja na yafe mata, Allah ya bayyana mana ita." Shafa kanshi tayi tana Murmushi cikin son kwantar mishi da hankali tace "Karkadamu insha Allahu zanyi iyakan kokarina akan hakan yanzun dai ka tashi kufara shirin tafiya saboda kufara bada cigiyar ta kasan da karfi karfi akan bugi karfe..!" Jinjina kai yayi yana mai mikewa a yayin da take mishi Addu'an Allah yabada sa'a, fita yayi ya nufi dakin mahaifiyarsa don bayajin zai iya tafiya batare da neman addu'a ta ba sai dai kuma ya shiga dakin ya kare maganarsa ko uffan batace dashi ba haka ya karashi zamansa ya fito, sai dai kuma wani abun mamaki a lokacin da suka shiryawa tafiya sai suka nemi Ammi suka rasa abun yayi bala'in dagawa kowa hankali cikin rawar jiki Abbi ya kira layin ta amma kuma yaki shiga kowa fa hankalinsa ya fara tashi magana har yakai kunnen Malam dake zaune a masallaci don haka cikin hanzari ya shigo cikin gidan don jin gaskiyar zancen. Inna ce take sanar sa Malam cewar Ammi da Alkasim sun tagi neman Maryam in sun dace to in basu dace ba tace can wajen Ummun ta zata tafi ba zata iya zama ba tare da tasan a halin da Maryam take ciki ba. Malam na jin haka ua juya kawai yayi ya wuce batare da yace komai ba, Abbi ji yayi gaba daya duniyar tai masa zafi shin da wanne zaiji da fushin iyayensa akansa ko kuma da rashin matarsa uwar yayansa? A haka yayiwa yan'uwansa sallama cikin sanyin jiki suka wuce shida su Fadima da Yaa Muhammad. Sai Yayan sa Kawu Usman, Kawu Abubakar, Kawu Aliyu da Kawu Umar saboda su shiga cikin gari su bada cigiyarta a gidajen redio ko Allah zaisa a dace  dan Malam gaba daya yake fushi dasu Su Abbi kuma sunje duk inda ya kamata su samu information akan Maryam amma shiru basu samu ba don haka suka wuce gidan TV da radio da kuma police station suka bada cigiyarta amma kuma duk da haka basu hakura ba sai da suka rika yawo a cikin garin Kano amma ko alamanta basu gani ba har washe gari, sai bayan kwana uku su Kawu Abubakar suka wuce Adamawa a yayinda shi kuma Abbi ya cigaba da aikin neman Maryam yana mai addu'a a cikin zuciyarsa akan Allah yasa a dace ga Ammi da dole sai yaje biko. Bayan su Kawu Usman sun dawo suka fadawa Malam ba wani abu da aka samu akan Maryam har lokacin, zama yayi a daki yai duba, a halin da yaga Maryam tabbas tana cikin wahala amman kuma yana ganin wani hasken alheri na tunkaro ta wanda yasa ya samu nutsuwa sannan a duban da yayi ya gane har da asiri a barin ta gida wanda ya rasa wanda ya aikata mata wannan abin, yarinya karama a jefa ta duniya, wannan yasa ya kara tashi sosai da addu'a ba gashi ba har ga almajiran sa wanda ake kwana mata sauka da addu'oi. *Allah ya jikan iyayen, yasa muti kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [11/14, 12:40] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 34 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Satin su Yaa Alkasim daya a Kano suna aikin cigiyar Maryam amman ba wani labari, wanda Ammi ta sa ya samar musu visa suka tafi, lokacin da Ammi taje gida yan uwan ta sunyi murna da zuwan ta duk da daga kallo daya suka gane tana cikin damuwa bayan an bata waje tai wanka taci abinci ta shirya ne, da yamma ta nufi dakin Mahaifiyar ta, Ummu na zaune ta shiga Ammi ta zauna, Ummu tace "Ina Maryama na zata tare zakuzo ai, tinda ba lafiya ce da ita ba." Damuwar dake kan fuskar Ammi ce ta kara daduwa tace "Mahaifin ta ya korata duniya Ummu, bamu san inda Maryam ta shiga ba, na taho akan ba zan koma ba har sai ya nemo min diya ta." "Me yake faruwa ne?" Zama Ammi ta gyara tace "Bayan doguwar jinya da Maryam tayi, mun dawo gida jikin yaki dadi gaba daya wannan yasa muka koma asibiti ana zuwa aka gane tana da ciki har na wata uku da kwanaki." Shiru duk sukai can Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ummu, wai ace Abbi ni yake zargi da daurewa Maryam gindin yin ciki ki fada min tayaya zan bar Maryam ta zubar da mutuncin ta, shin ya manta daga gidan da na fito ne ko? Bayan kwana biyu da aka sallamo mu yace sam bai yadda Maryam ta zauna masa a gida ba, ki fada min tayaya haka zata faru, bama wai gidan sa ba har gidan yan uwan sa, a ranar na tura ta gidan Fadima kam na shrya mata tahowa nan, to shine fa tinda ta tafi ba a ganta ba ba duban da ba ai ba, amman ba a ganta ba." "Innalillahi waina illahir rajiun me ya samu Muhammad ya yanke wannan danyan aikin da ilimin sa da sanin sa?" "Shaidan." Mahaifin Ammi ya fada yana shigowa dakin, zama yayi yana kallon Ammi yace "Shine a lokacin kika kasa kiran kowa ki fada masa sai a yanzu da abin ya lalace, kun batar da yarinyar ku me kika zo yi anan to?" "Abbu ba zan koma ba har sai ya nemon 'yata." Wani murmushi Abbu ya saki yace "Kinsan dai ba a yaji bare saki a gida na ko?" Kai ta gyada yace "Yauwa." Ya mike ya fita, Ummu tace "To yanzu cikin waye da Maryam din?" "Ummu nima ban sani ba bamuyi maganar ba ina son muyi ba lokaci." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Na yadda da Maryam, alamarin cikin nan tabbas akwai wani boyayyen abu a ciki, Muhammad bai kamata yai haka ba ya kamata ya bata dama ta fadi na wane in ma nemo sa ne ayi amman ba ace ita taje ta nemo sa ba sam wannan bai yi ba. Ina Malam shi me yace?" "Daga can muka taho nan yace lallai su nemo Maryam cikin kwana biyu ransa ya baci sosai." "Dole ai hukuncin da Muhammad ya yanke sam bai dace ba Allah ya kyauta Allah ya bayyana min Maryam dole a tashi da rokan Allah, Allah ya kare ta ya bayyana ta Amin." Shiru sukai, Ummu tace "Amman kema baki kyauta ba da kika taho me kike nufi kenan?" "Ummu tayaya zan iya zama ba Maryam yarinya karama shekarar ta duka duka nawa ko sha takwas fa batai ba Ummu na kasa samun nutsuwa kullum tunani na tana ina, wane waje take, wane hannu ta fada, kar abinda ake zato taje ta aikata dan na tabbata Maryam ba a son ranta ta aikata abinda ta yadda ta aikata ba." "Haka ne duk da ance ba'a shedar yaro amman nima ina ji a jikina Maryam ba zata taba aikata abinda ake zargi ba wannan boyayyen abun dai Allah ya kawo mai bayyana shi." "Amin." Ammi ta fada tana hade kai da gwiwa, dafata Ummu tayi tace "Ba kuka zaki ba addu'a zaki mata kinji?" Kai ta gyada tana mikewa ta shiga daki, kwana ta biyu Abbi yazo, zuri'a Alhaji Ahmad suka amshe shi hannu bibbiyu ba tare da nuna komai ba, sai da aka bashi masauki, da dare suna tare da Abbu, Abbi ya dukar dakai yace "Abbu nayi kuskure wanda tin ba aje ko ina ba nayi nadama wanda bansan har yaushe zan daina wannan nadamar ba." "Me ya faru?" Nan Abbi ya bawa Abbu labarin komai, Abbu ya girgiza kai yace "Muhammad ai hannun ka baya taba rubewa ka yanke, kayi kuskure kamar yadda ka fada wanda akace bakin alkalami ya riga ya bushe sai dai addu'a Allah ya bayyana Maryam da bayyana wannan gaskiyar." "Amin Amin." Sukai shiru, Abbi ya kara dukar da kai yace "Daman tahowar Ammin tasu yasa nace bari na biyo bayanta na bata hakuri." Murmushi Abbu yayi yace "Ba komai ai ta sani ba'a yaji a gida na bare saki dan haka dole ta koma ko tana so ko bata so, me kayi mata ai kaima yar kace in za taji ciwo kaima zakaji, ni ba zan yadda akan ta a farai min yaji ba, ko zalunta ake ci gwara ta zauna tayi ibada bare bata taba kawon karar ka ba, sama da shekara kusan arba'in dan haka dole ta koma a cigaba da hakuri, Maryam kuma mun bayar da addu'a insha Allah za a ganta kuma tana cikin waje mai kyau da izinin Allah." "Allah ya yadda." Daga nan suka fara hira a tsakanin su, har suka kusan raba dare, washe gari da safe da Abbi ya shiga gaishe da Ummu, Ammi na zaune a falon sam bata san yazo ba dan ba wanda ya fada mata sai ganin shigowar sa tayi, kai ta dauke suka amsa sallamar ya gaishe da Ummu, Ammi ta gaishe shi ba tare da ta kalli inda yake ba ya mike tayi ciki, da kallo ya bita sai da ta shige ya sauke kai yana fadin "Ummu ayi hakuri nima nasan nayi kuskure sharrin shaidan ne." "Ba komai Muhammad wannan tamu kalar kaddarar kenan yanzu fatan mu kawai Allah ya bayyana Maryam, kuma yasa tana hannu na gari." "Amin Ummu." Bai jima ba ya bar wajen, Ammi da Alkasim kuwa kwana suke yi a harami suna addu'a Allah ya tsare Maryam. Kwanan Abbi biyu yacewa Abbu zai koma dan ya cigaba da cigiyar Maryam, Abbu yace tare da Ammi zasu tafi, sam Ammi bata so ba har da hawaye haka tabi Abbi suka bar kasar har da Alkasim. * Bauchi Tinda aka fita da ita sai daya aka dawo da ita lokacin ta farka. Tea matar ta hada mata ta bata amsa tayi idon ta na cikowa da kwalla dan tasan ba iya sha zatai ba kuma yunwa take ji. "Menene?" Kai ta girgiza. Tace "To kisha kinji!" Baki ta kai tea din bata sauke cup din ba sai da ta sha kusan rabi dan yadda take jin yunwa tana gama sha ta mike a guje ta shiga toilet ta fara kwara amai tin tana iya yi har ya zama sai kakarin kawai. Ummi na dafe da ita har ta gama sannan ta dauraye mata baki ta fito da ita ta kwantar ta gyara wajen. Dankalin ta dibar mata tayo wajen gado dashi. Maryam na ganin haka ta juya mata baya tana girgiza kai. "Ki tashi ki daure kici rashin ci shi yake sawa kike wahala a aman da ba komai a cikin ki." Ta fada, tana dagota kuka ta sakar mata, Matar tace "Dan Allah ki daure kici kinji!" Ta dauki fork ta dauki dankali daya takai bakin ta, bata gama hadiyewa ba ta fara kakarin amai kan ta kai bandaki ta dawo dashi a tsakar dakin. Anan kasa ta kwanta tana dafe kanta da kirjinta. Ummi ta kamata ta shiga bandaki da ita ta dauraye mata baki ta dawo da ita kan gado wajen ta gyara sannan ta fita ta kira doctor dan ya saka mata ruwa tinda ba abinda take iya ci. Ruwan ya saka mata sannan tace "Ya gwaje gwajen?" File din da ya shigo dasu ya dauka yace "Yadda nayi bincike na gane rashin maganar ta ya samu asali ne na shiga shock da tayi, sai ciki da take dashi na wata uku, bayan nan jinin ta ya hau sosai, ga ciwon zuciya dake son kama ta. Ko cikin zai sa jinin ta ya hau ya saukar mata da zazzabi da ciwon kai to bare ga hawan jini kuma gashi ba ruwa sosai a jikin ta dan bata iya cin abinci and she is too young tana bukatar kulawa sosai dan tana bukatar abubuwan gina jiki, dan ba jini da yawa a jikin ta." "To yanzu ya za ayi, bata iya cin koma fa da taci abu sai amai ya za ayi da haka?" "Babu wani magani da zai magance hakan sai dai tana samun abunda take so zan dai bata maganin rage aman." "Toh nagode ya sallamar tamu fa!" "A gaskiya halin da take ciki gwara ku kara zama a dan kula da ita sosai zaman ta a gida hatsari ne" "To shikenan!" Ya ajiye magani yace "In ta tashi ta daure ta sha wadan nan." "To insha Allahu!" Abba ta kira tai masa bayanin komai yace to bari ta farka suji inda yan uwan ta suke dan ba zasu tafi su barta a haka ba. Bayan sallah la'asar tana zaune akan sallaya Maryam ta farka. Ummi ce ta taimaka mata tai wanka ta dauro alwala wata doguwar rigar ta, ta bata ta saka tayi sallah sannan ta zuba mata abinci da juice a cup. Juice din ta dauka ta kurba da yake na orange ne da dan tsami tsami sai taji dadin bakin ta ita ce har da shanye cup daya ta lumshe idon ta. Gyaran murya Ummi tayi wanda yasa Maryam bude idon ta. Ta gyara zama Ummi tace "Mu ma tafiya ne munzo Bauchi satin mu biyu a jiya zamu juya muka samu accident dake wanda yasa har muka kwana anan. jiya da na baki waya da nace ki kira gida baki kira kowa ba saboda me?" Idon ta ne ya kawo ruwa. Matar ta bata paper ta amsa ta rubuta "I don't have anybody to call, ni bansan ko ni wacece ba i only know two people in my life My Ammi and Yaa Haidar, bansan inda Ammi na take ba da Yaa Haidar ba....." Ta kasa karasa rubutun dan yadda kuka ya kwace mata. Amsa matar tayi ta karanta sannan tace "What is your Name?" "Maryam Muhammad Jabeer!" Ta rubuta. amsa tayi tace "Where is you Father?" Da hannu tai mata alamar bata sani ba. "Your relative?" Nan mata tai mata haka. "Ina ne garin ku?" Shima tai mata alamar bata sani ba. Kallo ta sosai Matar tayi tace "Ki fada min gaskiya Maryam bana son karya kinga taimakon ki nayi." Paper ta dauka ta fara rubutu "Wallahi bansan komai ba na ganni ne kawai anan ina rayuwa i can't recall my past My Ammi kawai nake tunawa ita ce Mama na. Sai Yaa Haidar my husband, wamda i know i loss him." *Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* *Antty*  💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 35 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Wata ajiyar zuciya Matar ta sauke duk da bata gama yadda da yarinyar ba amman jin cikin ta yana da uba yasa ta dan ji dadi. Kallon ta tayi tace "Na fada miki bana son karya ki fada min gaskiya." "Wallahi Allah gaskiya na fada miki ban san kowa da komai ba wadan nan mutane biyun su kadai na sani. Wallahi da gaske nake ba karya nai miki ba. Dan Allah ki taimaken ki kai ni gidan marayu na karasa rayuwa acan ba wanda na sani anan. Am just suffering here ba inda na sani please help me" Ledar magani ta janyo ta miko mata ta bata idon ta ne ya kawo ruwa. Ummi ta dan bata fuska tace "Bazaki sa nayi asarar kudi a banza ba daga jiya zuwa yau an rubuta magani na sama da dubu goma sannan ace ba zaki sha ba in baki sha ba tayaya zaki samu lafiya. In baki amsa kin sha ba bazan taimakeki ba zan tafi na barki kinji ko?" Amsa tayi ta bata ruwa ta watsa maganin ta sha kirji ta dafe tana son ta mike dan amai take ji. Da sauri Ummi ta kamo ta, ta fara shafa bayan ta a hankali a hankali. Ahankali taji ya fada mata amman da yake ita makiyar maganice har da kukan ta. tace "Tashi kije ki kwanta." Mikewa tayi ta hau gado tana kwanciyya ta lumshe ido take bacci ya dauke ta. Wayar Ammi ce ta fara ringing ta dauka tace "Ya akai My Son!" "Ummi banji daga gareki ba." "Name fa?" "Na tasowar taku!" "Oh Aliyu... In mun taso zan sanar maka wallahi yarinyar nan ce she is suffering tana bukatar kulawa daga likitoci sosai da sosai." "Ummi where is her relative!" "Aliyu yarinyar ce sosai bama wannan ba abubuwan dake damun ta suna da yawa na daya bata magana a yadda na lura kamar tayi losing memory tana rayuwa ne ita kadai gata yarinya tana cikin hatsari ban san ya zanyi ba." "Ummi ki bata duk kulawar da ya dace but please Ummi your Son is missing you wallahi ko abinci bana iya ci you know abincin ki nake iyaci kawai" "Ina na Innar ka!" "Kai ki bar innan nan ai kinsan halin ta dan bakya nan rowa take min in tai abu ta boye bata sammin" "Kai kuma bakin kwadayi ko?" "Ummi kinsan Inna ai tasan all what i likes eating to da gayya in ina dakin ta take girkawa kamshi yana busoni taki sammin." "Ai gwara tai maka haka kaga kayi aure a huta ko?" "Kai Ummi wane aure ana zaune kalau. Ai ni na gama aure Ummi." "My son shekaru na tafiya fa shekarar Maryam nawa da rasuwa amman ace bazaka kara aure ba. Shekara sama da takwas fa, auren shine cikar ka na babban mutum gaka har babban mutum amman baka cika ba dan auren shi zai sa ka zama babban mutum." "Ummi ya jikin yarinyar da kuke tare?" Kallon Maryam dake bacci tayi tace "Da sauki." "Allah sauwake." "Amin" "Please Ummi duk yadda za ai gobe ki dawo." "Insha Allahu my Son." Sukai sallama. Abbah ne ya shigo tai masa bayanin komai. Shiru yayi yace "Ya kike ganin za ayi!" "Alfarma zan nema a wajen ka!" "Ina jin ki!" "Zan tafi da Maryam na cigaba da kula da ita har ta sauka lafiya tayi recovery in ta tino komai sai mu maida ta ga ahalin ta." "Aisha kenan. Kina son taimako. Allah baki ikon kulawa da ita kinsan ba zan hanaki ba kuma yarinyar na bukatar taimako. Allah baki ladan taimakon." "Amin!" Washe gari da safe. Da kan ta, ta taimakawa Maryam tai wanka ta fito ta shafa mata mai sannan ta bawa wata rigar tata ta saka. Tea ta hada mata ta miko mata. Fuska ta bata. Ammi tace "Ki daure ki sha kinji ko zaki dawo dashi wani zai samu ya zauna. Ko akwai abinda kike so?" Kai ta gyada. Matar ta mika mata wani paper Maryam ta amsa ta rubuta mata. Amsa tayi tace "To ki fara shan tea din kan na bayar a kawo miki." Amsa tayi ta sha kadan ta ajiye. Ammi tace "Koke fa kinga bai dawo dan dada kadan." Kai ta girgiza mata sai ta mike tayi bandaki a guje sai da ta amayar da duk tea din sannan tazo ta bata magani shima da kyar ya zauna. Likita ne yazo ya kara duba ta sannan matar ta bata, lemon da tace tana so irin na jiya. Amsa tayi ta sha sosai sannan ta kwanta tana mai da numfashi. Wayar Ammi ce tai kara ta dauka. Tace "My son will never leave me to rest!" "Hmmm na kasa nutsuwa da hutawa Ummi na. Ina kwana?" "Lafiya lou ya gida dasu Inna?" "Tana lpy ni ba ruwana da ita." "Ah haba kai da Innan taka zama kai ruwa da ita ne." Yai dan murmushi yace "Ya me jikin?" "Da sauki!" "Allah kara sauki." "Amin!" "Nayi muku booking flight a Kano nan da karfe uku zai tashi dan Allah duk yadda za ai ku karasa kan three!" "But Kasan muna da patient ko?" "Ummi yaushe kika ga warkewar ta ku dawo gida zan kula da komai nata na miki alkawari." "Da gaske?" "Yes Ummi i promise." "Shikenan bari na fadawa Abban ku sai mu nemi transfer ko?" "Yes Ummi yau zanga My Ummi!" "Ji ka sai kace wani karamin yaro." "Ummi duk girman yaro a gun iyayen sa yaro ne kamar yadda nake daukar kai na 5 years old child a gun ki!" "In da kayi aure ka haifa kai ma ai ka samu wanda zai na maka haka ko?" "Ummi su Yasmeen, Hanan, Afanan, Afrah, Annur, Ayman duk sun ishe ni wallahi." "Shikenan nidai bari naiwa Abba maganar." "Ok Ummi nah." Suna kashe waya ta kira Abba dauka yayi yace "Kun tashi lafiya?" "Alhamdulillah! Ya jikin?" "Da sauki!" "Allah kara sauki!" "Amin! Yanzu d'an ka ya kira ni." "Aliyu kenan!" "Yayi mana booking flight a kano by 3pm zai tashi shine yake son mu tafi yanzu!" "Ya condition din jikin yarinyar zata iya wannan tafiyar mai yawa?" "Zan tambayi doctor duk yadda mukai sai na fada maka." "Alright ina jiran dan in da hali kada muyi rana ko?" "Haka ne ranka ya dade." Ta kashe wayar ta nufi office din doctor bayan ta shiga suka gaisa sannan tace "Muna son mu tafi ne shine muke son transfer dan mu koma gida can a cigaba da kula da ita. Sai abu na biyu zata iya tafiya mota nan da Kano." "No problem akan transfer zan baku tafiya ma zata iya insha Allah!" "Yauwah to please a gama komai a bamu copy din file din dan kar a samu matsala wajen cigaba da kula da ita." "Insha Allahu Hajiya yanzu duk zan gama komai." Nan ta koma ta kira Abba kan ya taho. Bai jima ba ya zo, Maryam na bacci sai da ta tashi doctor ya basu duk abinda zasu bukata suka biya kudin su sannan suka fita dan tafiya * Gaba daya Ammi sai tarasa walwala dan kullum tunanin ta inda Maryam take, satin su daya da dawowa su Mami mahaifiyar Haidar suka dawo, wanka kawai tayi ta nufi gidan su Ammi domin acan duk bata samun wayar Ammi. Ammi na zauna a falo rike da carbi tayi nisa cikin tunani Mami ta shiga tana ta kwada sallama amman bata ji ba har ta shiga ta ganta a wannan halin cike da damuwa ta karasa ta zauna tare da dafa Ammi da sauri ta juyo sai ta sauke ajiyar zuciya, tace "Hajiya ashe kun dawo." "Meyake faruwa ne? Ko har yanzu jikin Maryam din ne? Ina can hankali na duk yana nan na kasa samun wayar ki gaba daya bare naji ya jikin nata?" Hawaye ne ya zubo daga idon Ammi, take Mami ta shiga cikin tsoro tace "Menene Hajiya ki fada min jikin Maryam din ne? Tana ina?" Hawayen Ammi ta goge tace "Hajiya Maryam ta 'bata, yau kwana Maryam sha uku rabon ta da gidan nan." Wata zabura Mami tayi tana fadin "Innalillahi wainna illahir rajiun! Bangane ba Hajiya bangane Maryam ta 'bata ba." Sai kuka, Mami kuka Ammi kuka aka rasa me lallashin wani sai da sukai mai isar su sannan sukai shiru Ammi ta bawa Mami labari komai, shiru Mami tayi tana nazari, tabbatas in har za a ce Maryam tana da ciki to ko wanene zai ce cikin Haidar ne, Mami zata so haka amman ba ta wannan hanyar da suka same shi ba, amman duk da haka zata rike jinin Haidar ko dakuwa shege ne, zata nema masa gafarar ubangiji dan tasan daga Maryam har Aliyu ba mazina ta bane sai dai in kaddarar su ce, shekarar Aliyu nawa tare da Maryam ba a taba ganin wani abu na Allah wadai a tsakani su ba. "Ina ma ina nan ina da no zan riki Maryam da cikin ta ko da ace ba na Haidar bane ballanta na ina da yakinin cikin nan na Haidar ne, bani da kowa a duniya a yanzu iyaye na kadai suka rage min yaran da Allah ya bani shi Abubakar ya bace shi kuma Aliyu Allah ya amshi abunsa hakika bani da kowa kamar yadda Hajiya Mama ke min gori cewa daya nake da wanda bai haifa ba bani da baya bani da wanda zan kalla naji dadi amman Alhamdulillah Allah ya tsairar da Maryam da d'an cikin ta Allah ya kiyaye min su." Haka ta dinga maganganu tare suka gama kukan su da Ammi suka jajanta sannan Mami ta mike ta tafi gida. Tana shiga ta hadu da Umma, gaban Mami ta sha tana fadin "Ah mutanen Saudiyya an dawo ashe sai kika dawo kika ji mummunan labari batan sirikar ki ko? To ki daina murna da cikin jikin ta a sannu zai bare kuma ita da gida har abada." Mami bata taba tankawa Umma in tana wannan abun amman a ranar sai ta dago tace "Rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya, ki sani in kina taba wasu kina zama lafiya wata rana zaki tabo wanda ba zaki kwan ba, kuma ta Allah ba taki ba, in Allah yayi yaro zai zo duniya ko ana muzu ana shawo sai yazo dan haka ki daina tutiya kuma Alhamdulillah ko ayau za a bada shaida da tarihi cewa na haifa daya ya mutu, daya kuma ya 'bata kuma kila nan da wata rana Allah ya bayyana wanda ya bata ban taba ji a raina Abubukar ya tafi kenan ba ina ji yana can cikin rayuwa mai inganci kuma zai dawo min gidan nan da jikoki masu yawa da albarka." Tana fada ta juya, duk da jikin Umma yai sanyi amma batajin zata ki tankawa Mami dan haka ta hau tafa hannu tana fadin "Ayi mu gani." *Allah ka jikan mu, kasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty*  💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 36 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Mami ta shige dakin ta, ta fada saman kujera tana fashewa da kuka, wanda tana cikin kukan ta fara tuna komai na rayuwar su, Alhaji Suleiman saurayin ta ne tin tana makarantar sakandare, wanda anan suka hadu lokacin yaje musu bautar kasa, wanda tin lokacin yake son ta yaso suyi aure da sun gama makaranta sai dai mahaifin Mami dan boko ne baya aurar da yaran sa har sai yaga ya sama musu gurbi a makarantar gaba da sakandare wannan yasa da Abba yaje akan yana son a bashi damar ya turo amman Baba yace sam a'ah, wanda shi kuma Abba a gida an matsa masa dan a lokacin ya gama bautar kasa ya fara aiki kuma suna da rufin asiri, rashin bashi damar aure shi yasa ya fara neman Masauda Hajiya Umma kenan wanda sukai aure ba tare da sunyi wata soyayya mai tsayi ba sai da sukai aure Abba ya gane wasu halaiyar Umman da basu da kyau sam, bata da kunya sannan bata da ladabi, a haka Abba yake hakuri da ita shekara daya, biyu, uku, hudu Umma bata taba ko da batan wata ba, gashi Allah ya daurawa Abba son ya'ya wannan sam bai dame shi ba yana addu'a Allah ya kawo mai albarka. A shekara ta biyar ne suka hadu da Mami wanda a lokacin har ta gama degree din ta wannan shi ya dawo musu da soyayyar sa wanda a lokacin ya tura iyayen sa cikin hukuncin ubangiji akai komai na auren su, wanda lokacin da za a kawo Amarya nan jikin gidan su Ammi aka kawo Mami, wanda tare suka tare da Umma dan sabon gida ne sai sa Mami zata tare itama Umma ta tare bayan Abbah yai mata komai na gidan. Mami macece mai hakuri, da ladabi da biyayya, tin da tayi sati yan uwan ta suka zo suka rakata makwabta wannan yasa tin lokacin suke zumunci da Ammi, Umma kuwa ba inda ta shiga a unguwar haka suka cigaba da zama sam Mami bata shiga harkar Umma dan sashen kowa daban amman in dai Umma zataga Mami to sai ta shiga harkar ta Mami kuwa bata kula ta dan in ta ganta zata gaishe da ita amma Umma bata amsawa, ana cikin haka Mami ta samu ciki, zo kuga murna wajen Abbah da yan uwan sa nan soyayyar kowa ya dawo kan Mami dan daman tafi kyautata musu akan Umma, kowa murna yake tin da cikin Umma take mata asiri akan cikin ya bare amman da yake Allah yayi da rabon cikin a haka har cikin ya girma ya isa haihuwa Ammi ita ta kai Mami asibiti ta haifi dan ta kato kyakyawa namiji, wanda ba wata matsala a ranar aka sallamo su, nan yan uwa aka cika gidan kowa yana zuwa ganin Baby, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Abba aka saka masa Abubakar suke kiran sa da Sadik, tin daga Sadik Mami bata kara samun ciki ba har lokacin wanda Ammi a lokacin ta haifi Ummulkhairi, ta haifi Zainab, duk da itama ba kwaninka take ba wasu ta zarar shekara uku wasu ma hudu, banda Yaya Ibrahim da yake babban dan da kadan Yaa Muhammad ya dan girmi Abubakar da shekara biyu, bayan shekara wajen takwas Mami ta kara samun wani cikin wanda tana laulayi Ammi itama ta samu ciki, Mami ta haifi da namiji aka saka masa sunan mahaifin ta Aliyu suka kiran sa da Haidar, wanda bayan wata uku Ammi ta haifi namiji itama aka saka masa Alkasim tin daga nan Mami bata kara haihuwa ba, Ammi kuwa bayan Alkasim ta haifi Fadima shekara uku tsakani ta haifi Abdullah wanda bata kara samun ciki ba sai da Abdullah ya shekara shida wanda har ta fitar da rai, a lokacin kuma Alkasim da Aliyu suna da shekara goma goma, a wannan cikin sosai Ammi tasha laulayi da bata tabayin irin sa ba, Haidar kuwa dan gidan Ammi ne ko da yake ba shi kadai ba har Abubakar saboda yaran gidan da amintakar Mami da Ammi yasa yaran ma kan su a hade yake. Tin Haidar na yaro yake da tausayi ko yaya yaga mutum bai da lafiya ko yana jinya zai ta damuwa yana kula dashi to haka ce ta faru tsakanin sa da Ammi domin tana laulayi shi ke kula da ita da mata sannu komai ya samo kuma yace Ammi, wanda wannan ya kara sa musu shakuwa da Ammi, lokacin da ta bar laulayi kuma ya dinga addu'a Allah yasa Ammi ta haifi mace, a haka cikin Ammi ya isa haihuwa, Mami ita ta kai ta asibiti, ta haifi yar ta mace kyakyawa dan duk ya'yan Ammi duk kyaun su saboda sun hada mahaifn su bafulatani mahaifiyar su kuma jisin larabawa yasa suke kyawawa dasu dan haka Maryam tafi dukka kyau, lokacin da suka dawo Haidar ya dauke ta ya kalli Ammi yace "Ammi ina son ta zaki bar min ita?" Ammi tai murmushi tace "Na bar maka ita Haidar." To fa wannan statement din Ammi shi yasa Haidar kara son Baby, ranar suna aka sakawa yarinya Maryam sunan mahaifiyar Abbi, dan sauran ya'yan nasa duk suna ya'yan Manzon Allah ya saka musu sai a yanzu da ya sakawa Maryam sunan mahaifyar sa. Kowa son Maryam yake dan ita ce auta gashi Ammi ta jima bata haihu ba sai kan ta, dan haka Maryam ta tashi cikin gata da soyayyar ahalin ta bama Haidar bai yadda sam Maryam tayi kuka, dan ko rigima take duk abinda take so zai samar mata, itama kuma da taga Haidar ta bar rigima in kuwa tana kuka yana lallashin ta kamar shima yai kukan haka yake ji, sosai suka shaku komai shi yake mata, da aka yaye ta kuwa ko kukan nono batai ba dan tare suke yini suna gida wajen Mami yai ta bata kayan ciye ciye wata rana ma shi ke mata wanka ya shirya ta sai dai suje wajen Ammi su gaishe ta. Kowa yasan yadda Haidar ke so da kulawa da Maryam, da aka saka ta a makarantar su, ita sha biyu ake tashin su, ana tashin su yake daukar ta tare suke komawa aji tin malaman su na hanawa har suka daina dan a lokacin yana SS 1. In homework ne ba me koyawa Maryam sai Aliyu dan in zakai mata ma zata ce baka iya ba ita dai Aliyu, a isilamiyya ma rabi tana ajin su tana ajin su Aliyu ko an korata zata dawo. Komai Haidar ya samo Maryam duk kudin sa Maryam, in yaga kayan wasa ko kayan ado duk ita. Shekarar sa sha biyar yai graduation hade da sauka inda yai jamb duk ya samu lokacin Yaya Abubakar yana can kasar waje yana karatu shi da Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim, so akai a tura Haidar amman sam yaki saboda Maryam, haka kullum yake rakata makaranta lokacin tana nursery 2. Haka rayuwar su take tafiya kullum duk abinda zai yi sai ya saka Maryam da bukatar ta a gaba, wanda kullum shi yake kai ta makaranta da yamma ya dauko ta weekend kuma ta tafi tahfiz. Tin tana yarinya take da hazaka. Kwance yake a dakin Alkasim cikin bargo yana baccin sa, Maryam ce ta fito daga bangaren Ammi sanye da uniform din ta sabbabi dasu, wando ne blue black sai riga mai dogon hannu wacce take har cinyar ta sai hijab dan karami bayan ta rataye da jaka kafar ta sanye da cover shoe baki da farar safa, sai kamshi ta, Ammi ce ta leko tana fadin "Kar kije ki tashe shi fa Ummi." Juyowa Maryam tayi tana mata murmushin ta mai kyau wanda dimple din ta ya lotsa tana fadin "Ammi ganin sa fa kawai zanyi." Tsayawa Ammi tai tana kallon ta, ta juya ta nufi sashen su Yaa Abdullah, dakin Yaa Alkasim ta shige kan gadon ta fada tana fadin "Yaa Haidar ka tashi zan tafi school ka tashi kaga kwalliya na yau zan tafi primary 1." Bai ko motsa ba ta bude bargon ta ja hancin sa da sauri ya bude ido, yana daurawa akan ta ya saki wani murmushi ya mike yana kallon ta, yace "Baby na kinyi kyau iyyee Baby na ta zama babba." Mikewa tayi tana juyawa tace "Yes Yaa Haidar zan tafi school nace bari nazo na gaishe ka." "To ai baki gaishe nin ba." Durkusawa tayi tace "Ina kwana Yaya?" Ya dago ta yana fadin "Kin tashi lafiya?" Kai ta gyada ya mike suka fita yana fadin "Muje na rakaki makarantar naga sabon ajin da princess din na zata shiga." Keyn mota ya amsa ya tayar suka nufi makarantar ajin ta na da suka je dan amsar promotion letter bayan ya amsa ya bude yaga an mata double promition, da ya tambaya malamar tace zata iya a abar ta a ajin. Wannan yasa Maryam ta fara daga primary 2 kuma cikin hukuncin Allah ita take daukar ta d'aya dan Maryam da ka koya mata abu sau daya ya zauna akan ta, ga kula daga Yaa Haidar dan zai tsaya tai homework har lesson yake mata dan haka bata da matsala sam. Abbi na son Maryam dan tin tana karama take da hangen nesa ga ladabi da biyayya. Shakuwa sosai sukai da Aliyu dan ko d'aya bai da lafiya to tabbas daya ma zai kwanta ciwo dan tare suke jinyar su, ita Maryam akwai raki da kuka da rashin son shan magani haka Aliyu zai ta lallashin ta. In kuwa shine ba lafiya shima tai ta kula in yana shan magani tana kuka tana masa sannu tana fadin da zafi ko? Lokacin dasu Abubakar suka dawo dasu Yaa Muhammad Abba mahaifin Abubakar ya danka masa daya daga cikin company sa wanda wannan yasa Umma kamar ta mutu, nan ta kara tashi da bin malamai, wani uwan asiri da tayi wanda Sadik yana kwance cikin dare kawai ya mike ji yai gidan gaba daya ya masa zafi da sauri ya debi kayan sa ya fara hadawa a cikin akwati da takardun sa, haka ya gama ya fito daga cikin gidan yana kallon harabar gidan yana son gidan amman wani abu yaji gidan yai masa zafi da sauri ya fice wanda zuciyar sa ta fara tura sa ce masa kawai take ya bar wajen. A haka ya dinga tafiya yana nausawa bai san inda yake tafiya ba. Washe gari an sha neman Sadik amman ba a same shi ba sosai hankalin iyayen ya tashi da aka je neman taimako aka duba musu cewar yaron yana raye sai dai yayi nesa da gida, a haka aka cigaba da masa addu'oi da neman kariya a gareshi. Umma kuwa ko a jikin ta inda ta fara aika mugun nufin ta ga rayuwar Aliyu. Domin tayi alkawarin tinda bata haihu ba, ba wamda zai gaji dukiyar Alhaji kuma Mami ma ba zata taba ganin jinin ta ba. Anan BUK Haidar ya fara medicine din sa, wanda ko yana makaranta aka tashi su Maryam shi zai dauko ta, shekarar da zata shiga JSS 1 shekarar ya gama karatun sa, wanda lokacin Abbi ya kai ta MANS College, lokacin da aka gamai mata komai zo kuga kuka zata tafi ta bar Yaa Haidar, shi ya dinga bata kwarin gwiwa da lallashin ta kuma yai mata alkawarin duk sati zai na zuwa yana ganin ta. Ranar da za a kai ta makaranta da safe ta fito cikin uniform din ta daga kallo daya zaka gane tana cikn damuwa bata samu tai bacci sosai ba, tsaye yake jiki motar sa sanye da bakar shirt da shudin wando jeans hannayensa duka zube cikin aljihun. Ya kara zama cikakken namiji, wanda yake fari kyakyawa dan iyayen sa gaba da baya fulani ne, gashin kan nan nasa yai baki sidik sainkyalli yake, idanun sa manya wanda suke a lunshe dai dogon hancin sa da madaidaicin pink dun lips dinsa. A hankali ta ambaci sunansa "Yaya Aliyu?" Ya lumshe idanunsa da suka kumbura suntum saboda rashin isasshen bacci da shima bai samu ba, ta karasa ta fada jikin sa tana fashewa da kuka dago ta yayi yana goge mata hawayen dake zubowa yace "Baby na kina so nima nai kukan ne?" Kai ta girgiza tana mai kallon kyakyawar fuskar sa yace "To in bakya nai miki kuka kiyi shiru." Hannu tasa ta goge hawayen da yake akan fuskar ta yace "Yauwa koke fa Matar Haidar." Ta saki murmushi, a motar sa ya kai ta makaranta suka je akai mata komai da komai da wanda har an bata aji da komai. Bayan su Abbi sun mata sallama sun tafi har Yaa Aliyu ya juya zai tafi sai kuma ya juyo, idanuwanshi sun sauya launi daga farare sol zuwa na damuwa, "MARYAM!" Ya kira sunan ta da wata murya tamkar ba tashi ba. A hankali ta juyo ta ce, "Na’am Yaya Aliyu!" Ya ce, "Zo" Tare da ya fito ta da hannun daman shi. Ta karasa ta je gare shi suka tsaya suna kallon juna kamin ta sadda kanta kasa a dalilin nauyin da kwayar idanunshi yai mata. "Don Allah Maryama ki tsaya ki yi karatu sosai kin ji? Nasan bazaki bani kunya ba....." Ta dago ta dube shi idanunta fal da hawaye, ta ce, "Insha Allah Yaya Aliyu zan dage fiye da a gida." A haka yai ta lallashin ta har tai shiru, daga nan sukai sallama ya juya ya fara tafiya yana juyowa yana daga mata hannu itama tana daga masa har sai da ya daina hango ta dan sun tafi. Ai kuwa haka ya maida makarantar kamar gida, dan duk sati yana hanyar makarantar duk security sun san shi, haka principal din da yake abokin Abbi ne ma yasan Aliyu da sauran malaman makarantar. Bata da matsala dan in yazo tai tai masa shagwaba shine kawo mata kaza da kaza dan haka sai bata damuwa tinda duk sati yana tafe. Sai da ya tafi service din shine ta sha wahala wanda kullum kuka in ya kira ta a waya tai tai masa kuka da shagwaba shima baya wata bai zo ya ganta ba in kuwa sukai hutu shima daukar hutu yake ya dawo gida yai ta biyewa shirmen ta. *Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Allah ya yafe mana. Amin* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 37 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* A haka Maryam ta tashi da soyayyar Aliyu, wanda yana gama service ya samu aikin dan haka bai wata wata ba ya siyi filaye ya dankara gini, lokacin da ta shiga SS1 ne Haidar ya fara nunawa Maryam zallar soyayyar da yake mata, wanda a gaban kowa yake kiran ta da *MATAR HAIDAR* babu wanda a lokacin bai san soyayya Maryam da Aliyu ba, makaranta kuwa a sati sai yaje sau biyu sau uku, dan haka ita ji take tamkar ma a gida take, Haidar ya gama koya mata yadda zata so shi da yadda zatai rayuwa dashi, soyayya suke mai tsafta wanda kowa yake sha'awar su. Tana SS2 tazo hutun second term yana cikin mota yana jiran ta ta fito zasuje shopping, wanda ta fito sanye da doguwar riga, da hijab din ta zuwa gwiwa tai kyau ta karaso tana yamutsa fuska fitowa yai yana fadin "Menene yake damun *Matar Haidar* ?" Kofa motar ta kama ya bude mata ta shiga ta zauna ya juyo yana kallon ta yace " *Matar Haidar* " Dagowa tai tana cije baki yace "Fada min me yake damun ki?" Hannun sa ta kamo tace "Yaya tin jiya gefen ciki na yake min ciwo sai naji yana soka min." "Dai dai ina?" Hannun sa ta kamo ta daura a kan marar ta, tana lumshe ido, murmushi ya dan saki yace "Baki ga komai ba kuma?" Baki ta dan turo tace "Me kenan?" Wajen kunne ta yai da baki sa yace "Blood." "Which kind of blood?" "Haila." Ya fada a hankali. Ido ta zaro tace "Yaya nifa ban fara ba har yanzu kuma ma ni wallahi bana so na fara yanzu." "Why?" "Ni kawai bana so nafi jin dadi yanzu ba ruwana da wani kazanta." Murmushi yayi yace "Dole kuma kiyi ba, yarinya ki fara shirya masa daga yanzu zuwa ko da yaushe dan kin girma." Dagowa tayi ta aika masa da wani kallo, ido ya lumshe yace "Zaki zautani da wannan idanun naki." Kai ta dauke sai kuma ta dan cije bakin ta tace "Wallahi Yaya yana damuna ka bani magani." "Muje daga nan ma biya clinic ko?" Ya tayar da motar suka bar wajen yana fadin "In kuma abin yazo yanzu ya zaki ji?" "Yaya Allah bana so ni nafi so after i graduate naga fa yadda wasu ke wahala a school yana bani tsoro ni da ace ba zan nayi ba." Tai maganar cike da damuwa, yace "Ki rufa mana asiri mana, in bakya yi akwai probability ba zaki haihu ba fa." "Kai kuma kana son kids ko?" "Yes now." "Shiyasa nake tsoron kar na haifa maka yara ka maida son da kake min kan su." "See dis girl ke har kina da bakin magana, ni dake wa yafi son yara, ni ne ma na fi jin wannan tsoro kar daga kin haihu a daina ji da ni kuma." Kallon sa tayi tace "Ba mai kwace maka fada ta a wajen na." "Bare ni, zance musu wannan ita ce duniya ta." Tai murmushi sai kuma ta jingina da kujera tana fadin "Yaya ciki na" "Ko mu fara zuwa clinic din dai?" "No muje in mun dawo ma biya." Haka suka karasa wajen, a ciki ma shi ya dinga dibar mata kayan da zata bukata amman ita ta rasa me yake damun ta, da aka je biya ma fita tayi dan ji tayi wajen gaba daya yai mata zafi, dakyar ta samu take daga kafar ta wajen motoci ta nufa, tana dafe da cikinta cikin tsananin azaba a take jikinta ya hau rawa kaman mejin sanyi sakamakon iskan gurin dake busowa kasancewar ta hada zufa a jikinta, cigaba tayi da tafiya a daddafe, ta kusa da karasawa wajen motar maranta tai wani irin murdawa wanda ya haddasa mata tsala wani kara mai karfi nan tayi baya ji kake tim ta fadi a kasa, a daidai lokacin ya fito ya hangota cikin wani irin masifar firgita Haidar ya kwalla mata kira daga inda yake at once ya nufi gurin da wani mugun gudu, amma koda ya isa gurin sam bata numfashi. Jijjigata yake cikin rikicewa yana ambaton sunanta amma ina ko motsi batayi, cikin hanzari ya mike ya ciccibeta ya nufi motarsa da ita, a baya ya shimfideta sannan shima ya shiga kanta ya daura akan cinyarsa yana cigaba da ambaton sunanta. Gaba daya ya rasa ma me zai mata can idanunsa suka sauka akan goran faro water dake gaban motar, cikin rawar jiki ya mika hannunsa ya dauko goran ya bude bayyi wata-wata ba ya kwara mata gaba daya ruwan akan fuskarta. Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara bude idanunta a hankali, sam bata fahimci inda take ba kokarin tunano abunda ya sameta take Sai ko taji muryan Haidar. "Yaa Haidatrrr!" Ta fada cikin wata irin murya sai kuma ta kama hannun sa ta matse jin mararta yayi wani irin murdawa wanda ya haddasa mata rumgume shi sosai, kai ta hau jujjuya tana salati cikin wata murya mai ban tausayi, ta kara damke hannun sa tana jujjuya kai. Haidar kuwa ya kara rikicewa ya rasa me zai yi mata sai kalman sannu kawai yake jera mata ko tambayar abunda ke damunta ya kasayi, yama rasa wanne taimako zai bata. Maryam cikin kuka da tsananin azaba take cewa "Dan Allah ka taimakeni ciki na wayyoo Yaa Haidar..." Abunda kawai take iya nanatawa kenan da alama ma bata cikin hayyacinta, shiko sai a lokacin hankalinsa yafara dawowa jikinsa har ya fahimci kome ke damunta nan ko hankalinsa yadada tashi don yasan Period zata fara kila, Allah yasa kar yana zuwar mata a wannan wahalar. Don haka cikin muryar lallashi yace "kiyi hakuri bari in kaiki Asibiti.!" Cikin sauri ya gyara mata kwanciya sannan ya fito ya koma mazaunin driver, da mugun gudu yaja motar ya fice daga cikin super market din. Tuki yake yana kallonta At once kuma yana kalon hanya ko zayi katari koda da chemist ne tunda tsakaninsu da Asibiti akwai nisa gwara kawai yakaita chemist a mata su bata ko da pain relief ne, Maryam na kwance a baya babu abunda take sai kuka da ambaton sunansu Abbi sosai takejin azaba wadda bata taba jin irin ta ba shikam tuki yake yana jera mata sannu, kasancewar dare yafarayi don lokacin karfe 10 saura hakan yasa kafa yafara daukewa, sai da sukayi tafiya mai nisa sannan suka samu clinic, cikin sauri ya fakin motarsa ya nufi cikin clinic din. Daukar ta yayi ya shiga nurse na ganin sa suka gangaro gado suka shiga da ita, gefen ya tsaya sai sannu yake ta faman jero mata, ita kam ta rike hannunsa gam kaman jinjirin da ya rike nonon uwarsa. Cikin kankanin lokaci yafara bata taimakon gaggawa, dan karamin ruwa ya saka mata yayi rushing dinsa a jikinta sannan ya mata allurai har guda biyu duka a jijiya cikin kankanin lokaci abun yafara sauka kafun kace me bacci yayi awon gaba da ita. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Kallon Haidar yayi sannan ya umarcesa da suje waje, Koda suka fito ya bashi kujera ya zauna sannan yafara mishi bayani kamar haka "Karka samu damuwa yanzun munyi mata duk abunda ya dace wannan bacci da take zai iya daukanta daga yanzun zuwa nan da awanni koma fiye da hakan sannan kada a tasheta sai idan har itace ta tashi da kanta, hakan zai taimaka mata wajen samun saukin ciwon sosai, sannan inaga kafun lokacin jinin zai iya fitowa..!" Jinjina kai Haidar, wani Dr ne ya hango Aliyu ya karaso yana fadin "Dr AS kai ne anan." Hannu ya mika masa sukai musabaha, dayan likitan da ya duba Maryam yace "Shima likita ne?" Kai dayan ya gyada yai murmushi yace "Amman na tsaya maka bayani ai zaka iya kula da ita kuma kasan abubuwan dake kawo ciwon kila ko sanyi, ko kuma tana daga cikin jerin masu tsananin sha'awa da take bukatar namiji nan kusa kasan dai matsalolin?" Kai ya gyada yace "Kuma kaga wannan ne na farkon ta." "Ikon Allah, to ya kamata a dauki mataki dan kar tana shan wahala." "Insha Allahu." Dayan yace "Mara lafiya ka kawo?" "Eh wallah." "To Allah sauwake kai me ya hanaka duba ta?" "Na rikice na kasa gane mema zan mata." "Ko dai madan din ce." Sukai tafa suna dariya. Bayan tafiyar sa ya koma dakin da maryam take Ammi ya kira ya sanar da ita suna asibiti nan ta hau tambayar me ya faru, bai boye mata komai ba ya fada mata, Ammi tace suna ina zata zo yace ba sai ta zo ba. Yana zaune har wajen sha biyu sannan ta farka ya karasa da sauri yana fadin "Sannu *Matar Haidar* " Dagowa tayi tana kallon sa fuska cike da damuwa ta kalle shi yace "Sannu tana miki ciwo har yanzu?" Kai ta gyada yace "Bari ina zuwa, " Ya fita nurse ya tura mata, shi kuma ya fita mota ya dauko mata pant da pad har da wata riga dan daman kamar yasani ya siyo mata su, ciki ya koma ya bawa nurse din ita ta taimaka mata ta gyara jikin ta Maryam na gane me ya faru da ita sai ta hau kuka a haka ta fito tana kuka, da sauri ya karaso ya durkusa a gaban ta yace "Me kuma ya faru Baby?" "Yaya abin ne yazo fa." "Wane abun?" Ya tambaya dan bai sa me take nufi, tace "Abun da ka gama ja min yi dazu." Ya saki murmushi yana fadin "Please yanzu fa kin kara girma." "Ni bana son girman." Ya mike yace "Bakya so ki haifa min Baby ko?" Baki ta turo tana yamutsa fuska kamar zatai kuka tace "Yaya ni ka kaini Ammi ciki na ciwo yake har yanzu." Ta fada tana yarfe hannu, mikewa yayi yace "Muje to." Yaje ya biya kudi sannan suka tafi gida, a mota ma shiru tai masa kawai dan ciwo take ji sosai wannan yasa ko motsi bata so tayi. Suna zuwa ya bude mota yace "Baby mun karaso." Ta dago ta kalle shi tace "Yaya kafata ta rike ba zan iya ba." Kallon wajen ya fara sai kuma ya zura hannu a aljihu ya fara neman layin Alkasim yana dauka yace "Kana ina ne?" "Ina compound kazo." Ba bata lokaci ya fito yana fadin "Lafiya?" "Please daukar min ita mu shiga ta kasa tafiya." Tin da Maryam ta shiga shekara goma Aliyu ya daina daukar ta da taba ta, in har ya taba ta bai fi ta kamo hannun sa ba shima yana janye wa haka tinda ta kai lokacin ko tazo zata rumgume shi yake dakatar da ita wannan yasa su Ammi basa kara damuwa da shakuwar tasu saboda sosai suke kiyaye hakkokin dan da ta girma ma bata zama ba hijab a gaban duk yayyen ta wannan kuma tarbiyyar Ammi ce. Kamo ta yayi, Haidar ya kwashi kayan sukai ciki anan falo ya ajiye ta Ammi ta mike tana fadin "Mata ana ciwo." Ta sagwabe fuska tace "Ammi kamar zan mutu fa kinji ciki." Sai ta fara hawaye Yaa Haidar ya durkusa yace "Haba my jaruma, bar yin kuka zata daina kinji." Ya mike ya shiga kitchen sai gashi ya fito da ruwan tea a cup sai ruwan dumi a bowl, tea ya bata ta amsa ta sha daya kuma ya bata karamin towel yace ta gasa marar tata, Ammi ta dauke ta sukai dakin ta gasa marar tayi wannan yasa ta dan ji dadi har bacci ya dauke ta. Tin asuba ta tashi, Ammi ta koya mata yadda zata saka pad ta saka ta fito ta saka wasu Pakistan riga da wando sannan ta saka hula ta haye gado, dan har lokacin marar ta yana tai mata ciwo, tana kwanciyya bacci ya dauke ta. Karfe takwas ya shigo sashen Ammi, ba kowa a falo, kitchen ya leka ya samu Ammi ya gaishe ta yace "Maryam ta tashi?" "Kila ta tashi har yanzu tana can tana raki." Dakin ya shiga ya same ta kwance akan gado, kan gadon ya karasa ya zauna daga gefen ta yace "Dear." A hankali ta motsa tana bude idon ta, ganin Yaa Haidar yasa tai maza taja abin lulluba, murmushi Yaa Haidar yayi yace "Morning My Love." "Morning too dear." Ta mike tace "Yaya...." "Sannu my love ya jikin?" Fuska ta shagwabe tace "Uhmm ba sauki Yaya har yanzu ciwo take min, kafa na ma ciwo take min." Ta kara yamutsa fuska tace "Amai nake ji Yaya." "Sannu kinji yanzu zan samo miki pain relief dan ba a son ana shan maganin ciwon marar nan." "Yaya ko mutuwa zanyi ne?" Kai ya hau girgiza mata yace "Wa yace miki daga ciwo sai mutuwa." Ido ta runtse tana cije baki tace "Yaya..." "Sannu Baby kin ci wani abu?" Kai ta girgiza ya mike ya fita bai jima ba ya dawo da ruwan tea ba sugar ta mike zaune ya fara bata tea din tana sha a hankali bayan ta gama Abdullah ya kawo maganin da Haidar ya ake shi ya siyo bata yayi tana kuka tana komai ta sha maganin, ranar ko aiki Haidar bai je ba sai zama jinyar Maryam ai kuwa sai shagwaba take masa daga tace zataci wannan sai wancan kuma in an kawo ba abinda take ci a ciki, har dare haka sukai ta fama. Kwanan ta biyu ya dauke sai kuma shagwaba da ta dadu, haka Aliyu yake biye mata yai ta lallabata Ammi dai sai zuba ido tayi, dan har da Mami a daure musu gindi. Ummah kuwa a duniya ba wanda ta tsana kamar Ammi da Mami, ji take kamar ta kashe su. Haka rayuwar Maryam da Haidar take duk wanda yasan Haidar to yasan Maryam haka duk wanda yasan Maryam yasan Haidar, soyayyar su mai tsafta ce dan ko hannun ta bai tabawa, zabin su iri daya burin su daya koman su daya wannan soyayya ba wanda bai san ta ba daga family din Haidar har Family din Maryam both side. Lokacin da ta shiga SS 3 ne aka tsayar da ranar auren su, a lokacin shakuwar Haidar da Maryam ta kara tsanani, dan ko ciwo Maryam tayi Haidar yana gida yana ji a jikin sa ma in period din ta yazo sosai take shan wahala tai ta suma a haka yake kullum yana hanyar zuwa makarantar su dan bai da shamaki da zuwa wajen ta a ko da yaushe, suna second term kan su fara aka kawo lefen ta da sadaki wanda aka saka sati daya da graduation bikin, Shin don mene ne Maryam ba zata so Aliyu ba. Hakika Maryam na son Aliyu so ba na wasa ba kuma tabbas ya cancanci a so shi domin mutumin da ya kwashe shekaru goma sha yana kula da ita, kulawar da iyayen da suka tsuguna suka haife ta basu yi mata ita ba domin duk abinda su Ammi zasuyi mata kan suyi ya riga yayi tin tana karama yake dawainiyya da ita yake bauta mata, yana dadada mata, yana faranta mata, In har bata so Aliyu ba, tabbas ta zama butulu ce cikin butullun ababen halitta wanda zuciya ba ta aiki a jikinsu. A wannan tsukukun kuma Aliyu yafara wani matsifaffen ciwon ciki wanda in ya tasar masa shima har suma yake yi, lokacin duk sai ya fara ramewa da ka kalle shi zaka san bai jin dadi. Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana me cigaba da tunanin wani abu da ya fado mata. Tabbas abun da ya fara daurewa Mami kai shine tin da suka shiga third term zasu fara exam ba a kara yo waya akan Maryam tayi ciwom mara ba wanda a da duk wata sai an dawo da ita gida ko asibiti ta kwanta wannan yana nuni da tin kusan lokacin kenan Maryam ta samu sauki, wanda ba zata manta ba akwai wani dr da ya taba fada musu samuwar lafiyar Maryam sai tayi aure ta tara da mijin ta. Da sauri Mami ta mike tuna wasu abubuwa a wadan nan lokutan, sune Haidar ya kara sa son Maryam a ransa wanda yasha fadawa Mami shi a daura musu aure kan tayi graduation amman Mami tace zataiwa Abba magana Abba yace ya bari saurin me yake ne ai an kusa a wannan lokacin ya janye batun sa sai dai wani kalamai da ya taba fadawa Mami shine "Nifa Mami Maryam ta gama zama matata buri na kawai ku bani abata mu tafi duk wannan shagalin da za ayi bidi'a ne." A lokacin bata damu da kalaman sa ba dan sai take ganin kamar ba wani abu bane kawai zumudi ne, sai kuma ranar daurin auren su da ya kira ta akan yana son suyi wata magana tabbas basu samu dama ba dan Abba ya aika tazo daga nan da ta koma kuma bata ganshi ba inda bata kara ganin sa ba sai gawar sa da aka kawo mata, shin me yake son ya fada mata, hakika zuciyar Mami ta karaya dan ta tabbara daga Maryam har Haidar ba mazina ta bane daya a cikin su ba zai taba yin zina ba amman to me hakan yake nufi tayaya Maryam ta samu ciki, tayaya? Shin cikin wa Maryam take dashi? Bata so ta sa aranta cewar Haidar da Maryam sun aikata zina dan haka tai sauri ta mike ta shiga daki ta fara wani abu da zai dauke mata wannan mummuna tunanin. *Allah ya yafe mana, ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 38 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* * Abba na gidan tsakiya Ummi da Maryam na gidan baya, Maryam kwance akan cinyar Ummi tana ta bacci dan yanzu ba abinda take yawan yi sai bacci. Har suka Iso Kano bacci take. Suna shiga Kano, ta mike ta matsa jikin Ummi tana karkare wa kamar me tsoron wani abu. Ummi tace "Menene Maryam?" Jikin Ummi ta fada ta rufe fuskar ta tana girigiza kai, "Alhaji akwai abinda zakuyi kan mu karasa airport?" Ado Driver ya tambaya. "Aah! Mu zarce airport kawai. Madam ko kina so wani abu!" "A'ah Maryam ko kina son wani abu ne?" Kai tai sauri ta girgiza kan ta a boye a jikin Ummi. "Mu tafi airport din lokaci ma ya kusa." Direct Aminu Kano Airport suka tafi suna zuwa suka shiga suka dan huta, Aliyu ta kira ta shaida masa yanzu zasu taho yai musu addu'a sannan yace "Ummi ina asibiti da kyar na samu na dauko ku." "Kada ka damu kaji." "To Ummi zan aiko Baba Halliru sai ya dauko ku tinda naga Baba Ado ne ya kai ku nan ko?" "Eh sun taho suma nasan nan da magariba zasu karaso." "Allah kawo su lafiya." "Amin!" "Ya me jikin?" Kallon Maryam tayi wacce ke jikin ta a dukunkune tinda suka shigo Kano take a haka wanda ta ki ta saki Ummi sam kamar wanda ke ganin wani abu. "Gata nan!" Ta fada tana shafa kan ta." "Ai mata sannu!" "Zataji!" Sukai sallama sannan ta shafa kan Maryam tace "My Son na miki sannu!" Kai ta gyada kawai. Karfe uku jirgin su ya fara haramar tashi. Karfe biyar saura suka fito daga cikin airport din cikin wasu jerin gwanon motoci wajen guda biyar biyu a gaban tasu biyu a bayan tasu an saki jiniya a haka suka ratsa babban titi suka nufi gida kai tsaye. Bakin wani katon hadadden gida sukai horn security ya bude katon gate din ciki suka shiga a jere. Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta zauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku manya masu fenti iri daya, ko wanne sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko da na biyu, wanda na farko shi zaka ci karo da bayan shigowar ka gate din zamanin dake babban gidan ba dai girma ba wanda girman sa daya da tsaruwa a komai da na kusa dashi. Manyan gida ne masu girman gaske sai parking space gari guda dake gefe., a cikin ko wanne. Banda na main compound da yake dauke da securities room da boy quaters. Gidan ya tsaru iya tsaruwa da kyau ko ina neat sai kamshi yake ga ni'ima saboda shuke shuken da suke dashi. Suna parking suka fito Ummi rike da hannun Maryam da ta gama galabaita saboda gajiya da tayi ga ciwo ga yunwa duk ita kadai. Second part dake cikin gidan suka nufa, hannu ta saka ta karkashin wata tukunyar shuka sannan ta dauki key. Abba ta bawa ya amsa yai bismillah ya zura key din ya bude. Kamshi ne ya dake su tare da sanyin AC. Shiga yayi da sallama Ummi tabi bayan sa rike da hannun Maryam. Katon falo wanda yake dauke manya manyan kujeru wajen set uku maroon kala and milk, labulayen ma maroon kala ne da adon milk sai milk center carpet da center table a tsakiyar dakin. Gefen kujerun kuma side stool ne yan kananu a tsakan kanin kujerun. Can gefe kuma dan step ne wanda ke dauke da dining table da dining carbinate an saka musu wani labule mai igiyoyi milk an maroon ka. Ta gefen dining akwai kitchen, sai gefen dining da wata kofa, da matattakalar bene sannan akwai corridor dake dauke da three room two bedroom da resting room. Suna shiga Maryam ta lumshe ido ta saki Hannun Ummi kasan tile ta kwanta tana mai lumshe ido. Ummi ta kalle ta sannan ta karasa ta kamata tace "Ba a son kwanciyar kasa fa." Akan three sitter dake gefe ta kwantar da ita Abba kuwa har yayi kan stair. Ummi tabi bayan sa daki ta same shi har ya shiga bandaki babbar rigar da ya cire ta ninke sannan ta wuce dakin ta. Alwala tayi ta fito ta tada sallah. Tana idarwa ta mike ta fita. Abba ta sama zaune akan sallaya. Bandaki ta shiga ta hada masa ruwan wanka sannan ta fito tace "Yallabai na hada maka ruwan wanka fa." "Nagode Allah yayi albarka!" "Amin!" Ta juya ta fita. Kasa ta sauka ta karasa kusa da Maryam da har bacci ya dauke ta. Dafata tayi ta bude idon ta a hankali. Hannun ta ta kama tace "Taso muje kiyi wanka kiyi alwala ki sallah sai ki kwanta ko?" Mikewa tayi jiki a sanyaye tabi Ummi sama. Dakin dake kusa da nata ta kai ta ta shiga ta hada mata ruwan wankan. Wardrobe ta bude ta dauko mata sabon pant da doguwar riga. Ajiye mata tayi akan gado da hijab. Maryam na fitowa ta zura kayan ta hau kan sallaya ta tada sallah. Tana idarwa tai addu'a tare da azkar kwanciyya take son yi amman kuma bata son in ta kwanta tayi bacci dan yamma tayi sosai. Kai ta jingina a jikin gado tana jan carbin da ta gani a gefen gado. Ummi ce tai sallama itama tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi an mata dinkin bubu ta daura dankwalin kayan sai kamshi take yi. Hannun ta rike da juice da cup ta shigo. Ajiye wa tayi tace "Sannu ya jikin!" Murmushi Maryam tayi tai mata magana da hannu alamar Alhamdulillah. "Allah kara sauki!" Kai ta gyada. Ummi ta bude juice din ta tsiyaya mata a cup amsa tayi ta shanye shi tas sannan ta rike cup din ta fara kokarin kwanciyya a kasa. Ummi tai saurin kamata tana fadin "Ki daina kwanciyya a kasa tashi ki hau gado amman kada ki bacci kinga yamma tayi ko?" Kai ta gyada ta koma kan gadon ta kwanta kawai. Ummi tace "Zan fita me kike son na dafa miki?" Kai ta jujjuya alamar ba komai. Ummi ta shafa kan ta tace "Sannu!" Ido ta lumshe mata ta juya ta fita. Tare suka sauka ita da Abba. Bangaren dake gefen ta wanda bai kai nasu ba flat ne shi bai da bene nan suka nufa. Tin daga compund din da zai dauki akala mota sama da uku wanda yake dauke da shuke shuke yake a share tas. Har kofar falon suka karasa sukayi sallama. Inna dake goge goge ta dago tana amsa sallamar tasu. Shiga sukai suka zauna akan kujera, ta karaso ta zauna hannun ta rike da handkerchief da take goge goge wanda na rasa me take gogewa domin komai na dakin yana nan tsaf sai daukar ido yake. Daki ne mai kyau falo madaidaici an zuba masa kujeru masu kyau da tsada milk colour an saka milk kalar labule wanda kasan dakin ma duk milk tile ne sai kyalli yake da sheki kamar ba a rayuwa a dakin kuma kamar ba dakin tsohuwa ba. Dakin sai kamshi turaren wuta yake da sanyin AC da ta kunna. "Ina yini Inna?" Suka hada baki wajen gaishe ta, baki ta tabe ta ce "Lafiya lou ashe kun ga dama kun dawo mutanen da suka ce kwana goma sha hudu zasuyi yau kwanan ku nawa?" Ta fada tana tsare su da ido. Ummi tai kasa da kai Abba yace "Inna matsala aka samu, kuma kinsan halin tafiya ita ke da kai ba kai kake da ita ba." Baki ta tabe Ummi tace "Kiyi hakuri Inna mun sameku lafiya ya gidan?" "Gida yana nan kalou sai dai fa tin da kuka tafi waccen ta daina kawon abincin ta sam ke dai yayar kice nasan ba yadda zaki ba. Daman ganin ido ne yasa take kawon dan taga kina kawon ita kar ace bata kawon ko? Ita kuwa dayar yo ko ta kawon ai baci zan ba girkin ta sam ba dadi, ke ni wallahi kyamkyamin ta ma nake." Ummi tai murmushi tace "To Inna ai na dawo sai na cigaba da kawo miki." "To ai shikenan a haka kuma wancan gantalallen yaron nata yake zuwa min nan kwadayi da gayya nake abu mai dadi na cinye ko sammasa bana yi." "Waye a ciki Aliyu ko Umar?" Abba ya tambaya yana murmushi. "Waye banda Aliyu uban yan kwadayi!" "Inna amman shima ai yana kawo miki kayan kwadayin!" "A shekara sau dayan. Kasan Allah Shehu a shekara sau daya yake kawon!" "To ai muna kawo miki ba shikenan ba." "Amman dai Shehu yadda nake dawainiyya da yaran nan tin haihuwa ya dace ace haka suka dauken kamata yayi komai suka samo su kawon ko dan Allah." "Haka ne Inna!" "Uhmm to kana ji sai mu shekara biyu kwandala bata hadamu ba kayan ci kuwa bai fi a shekara sau daya ba fa!" "To Inna sai hakuri yaran zamanin haka suke ai!" Ummi ta fada. "Daman ku kuke kara daure musu gindi, Allah yaso na haifi Shehu da Suleiman da Nusaiba ga kuma Abubakar shi ya dauken uwa duk da bani ce uwar sa ba to me abun Aliyu da Umaru zai karen a duniya bayan yara nab basu dauken komai ba." "Ayi hakuri Inna." "In ban hakura ba ya kike so nayi Aisha?" Abba yai gyaran murya yace "Inna bakiji dalilin dadewar mu ba fa!" "Zai wuce ka ce min aikin ka ne baka gama ba Shehu!" "Ba haka bane Inna mun gama aiki a iya ranar da na dauka sai dai mun taho shine muka samu dan hatsari a hanya." "Na shiga aljanna ban fito ba ni Hauwa'u ina fatan dai ba abinda ya same ka ko?" "Babu Inna wata yarinya muka so mu buge amman Allah ya takaita wahalar wanda tsoratar da tayi yasa ta suma!" "Kaji raguwa daga an kusa a bege ka sai suma amman wannan kwai raguwa da zan ganta da na ga mai mata kuwa." Murmushi Ummi da Abba sukai sannan Abba yace "Shine muka kai ta asibiti to kinga mune silar sumar bai kamata mu tafi mu barta ba, dan haka muka zauna har wajen awa takwas bata farfado ba." "Kai duniya abun mamaki baya karewa yanzu daga an kusa bige ka sai suma har kayi awa takwas sai kace ba mutum ba anya mutum ce kuwa Shehu. Aisha dan Allah mutun ace ba a bige ka ba ka hau suma haka ake yi?" "Wallahi Inna muma mun tsorata sai da likitoci suka kwantar mana da hankali shiyasa muka dada kwana dan sai dare ta tashi wanda muka so mu dankata a hannun iyayen ta sai kuma yarinyar ashe bata da lafiya." "Ahaf kaji zance ai daman da walakin ace daga an kusa bige ka sai suma." "Wallahi Inna yarinyar dai ashe bata ma magana daga cin abinci sai amai baki ganta ba yarinya karama duk ta rame ta dashe haka muka kwana zazzabi mai zafi a jikin ta wanda washe gari Aisha ta sanar dani nace ayi wa likitoci magana shine sukai bincike sosai akan ta." "Inna in kinga yarinyar abin tausayi wai ashe tayi rashin lafiya shine ta rasa maganar ta, sai jini ta da yai mugun hawa." Ido Inna ta zaro tace "Duk ita kadai yarinya karama." "Inna ba ma wannan ba ciwon zuciya ya kamata ga karamin ciki dake wahalar da ita." Tagumi Inna ta zuba tace "Duk ina iyayen ta?" *Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe Amin.* *Antty* [11/17, 14:03] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 39 By *MARYAM S INDABAWA* HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Abuja Kallon Abba Ummi tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace 'Inna ina zaton yarinyar tayi losing memory dan bata iya tuna komai na rayuwar ta sai mutum biyu Ammin ta da Yaa Haidar da ta fada min. Wanda Yaa Haidar din shine mijin ta!" "Allahu Akbar. Allah yasa ba irin halin Aliyu nan gidan ne dashi ba. Yanzu ya jikin yarinyar?" "Inna likitoci sunyi mana bayani yarinyar tana bukatar kulawa sosai. Dan tana cikin hatsari wannan abun shi yafi damu na, na rasa ya zanyi ya zan ajiye ta. Dan garari kawai take a cikin garin Bauchi bata san garin da kowa dake cikin garin ba bata tina kowa da komai a rayuwar ta ta baya." "Ikon Allah wannan wacce irin jarabawa ce ace ka rasa komai naka da mijin ka ga ciki ga bakasan inda kake ba." Abba yace "Shine Aisha ta nemi alfarma akan tana son ta karasa kula da yarinyar har lokacin da Allah zai sa ta tuno yan uwan ta." "Hakan yana da kyau!" "To shine yau Aliyu yayi mana booking flight muka taso har yarinyar." Ido Inna ta zaro tace "Kuka taho da ita ina?" Kallon kallo akai da Abba da Ummi. Abba yace "Nan gidan!" "Yanzu Shehu baka ganin ba matsala ka dauko yarinyar da baka sani ba ka kawo cikin iyalin ka. Haka fa kukayi mana shekarun baya. Shin kuka sani ko aljanna ce ma. Ni da farko na ji tausayin ta kuma na yadda da labarin amman kuna cewa kun kawo ta kuma sai naji tsoro nake ganin anya da gaske ne kada fa ta cutar da mu." "Inna ta kenan da mukai haka a shekarun baya yanzu wa yafi ki jin dadin sa. Naga ya dauke ki kamar yadda kike a wajen mu. Kuma Inna ina ce ke kan ki baki taba kawo laifin sa ba tinda muke sai a yanzu kuma haba Inna. Nasan Inna ta ba abunda take tsoro a duniyar nan daga mutun har aljanna. Allah kadai take tsoro. Kuma nasan Inna ta akwai tausayi imani da taimako nasan zata taimakawa ko wanene dan Allah shi zai biya ta in ma ya cutar da ita dan kansa. Nasan Inna zata taya mu rikon yarinyar nan tsakani da Allah ko Inna ta?" Abba ya karasa yana lankwasar da kan sa da neman taimakon Inna. "Daman ai ni bana tsoron kowa, kuma ina son taimako yanzu me zance sai dai nace Allah ya bamu ikon rike ta da amana, Allah yasa ta tina da gida ya sauke ta lafiya." Baki Abba da Ummi suka hada suna murmushi suka ce "Amin Inna." "Ya jikin nata?" "Da sauki sai dai ba abinda take iya ci." "Allah sarki haka za ai jinya ba cin abinci bari maza na tashi na samar mata abu da zata dan ji dadin bakin ta." "To Inna me za a kawo?" "Ba abunda za a kawo dan jiya Aliyu yayi min cefane kayan da nake bukata." "To Inna godiya muke." Ta mike ta nufi kitchen tana fadin "Bari na shiga kan a kira magariba." "To Inna muma mun tafi sai anjima!" Suka mike suka fita. Ummi tace "Ni nasan daman Inna sai tace wani abu!" "Amman kuma ai kinsan tana da saurin sauka ko?" "Haka ne kasan ta ai wata rana ta nuna tana son abu wata ranan akasin kowa mai laifi ne in tai niyya." "Haka ne amman ku da yaran ku zaku taimaka mana mu rabu lafiya." "Kai ma kasan muna iya kokarin mu." "Haka ne." Abba ya nufi gate din da zai sada shi da masallacin gidan Ummi kuma bangaren dake kusa da nasu iri daya ta shiga. Da sallama ta shiga sashen amman ba a amsa ba ciki kawai ta shiga. Hajiya Barira na zaune tana kallo. Ummi tai murmushi ta kalle ta tace "Sannu da gida Hajiya!" "Yauwah!" Ta amsa ba tare da ta kalli inda take ba. Kai ta dauke tayi sama itama bata bi ta kanta ba. Tana zaune a daki hannun ta rike da waya ta jiyo muryar Ummi na sallama. Da sauri ta dago tana fadin "Ummin Aliyu ashe yau din dai kuna tafe!" "Wallahi Yaya, Aliyu ya saka mu a gaba sai fa cewa yayi kawai yai mana booking flight." "Au da kenan ba yau zaku dawo ba." "Gaskiya dai da wuya dawowar mu yau din nan, saboda jikin yarinyar amman Aliyu yace mu dawo zai kula da ita komai da komai." Fuska ta sauya tace "Har yanzu jikin dai to ina yan uwan ta?" "Yaya bata san inda suke ba sam bata magana fa ba wanda ta sani nata fa." "Me kike nufi?" Bayani Ummi tai mata. Tagumi ta saki tace "Tarihi na son maimaita kan sa dai kenan ko?" "Wancan da banbanci da wannan, wannan fa har da ciki." "Hmm duk da haka ke kuma kece uwar yan tsuntuwa ko?" "Yaya to menene Allah dai ya bayyana alhalin su gaba daya." "Amin to ya jikin nata?" "Da sauki!" "Dan Allah dai ki kula tinda bamu san wacece ba kar muje me cutar wa ce." Murmushi Ummi tayi tace "Insha Allahu haka ba zai faru ba Allah zai dubi zuciyoyin mu, yanzu." Kai ta gyada kawai. Ummi tace "Yakamata muje kigan ta ko?" "To muje!" Suka mike suka fita ba kowa a bangaren nasu dan haka suka fita kawai. Bangaren Ummi suka nufa nan ma ba kowa sama suka nufa suka shiga dakin da Maryam take duk yadda taso kar tai bacci bata san lokacin da baccin ya dauke ta ba. Kallon ta suka tsaya yi. Ummi tace "To kingan ta Yaya!" "Na ganta gaskiya yarinya ce sosai, Allah sarki!" Ta karasa tana leka fuskar ta sosai. Sannan ta dago tace "Allah bata lafiya daga gani duk inda ta fito cikin jin dadi ne. Kalli fatar ta smooth duk da bata da lafiya." "Haka ne!" Ta mike ta nufi kofa tana fadin "Bari naje yau Inna tace na mata farfesun tarwada." "Hajiya Inna kenan!" Ummi ta fada tana bin bayan ta. Fita sukai tace "Ai da bakya nan kullum sai tayi fada wai kinje kunki ku dawo in ke ba zaki dawo ba ki bar dan ta ya dawo." Murmushi Ummi tayi lokacin da suka karaso bakin kofa tace "Ai nasan za ai haka. Allah dai ya rabamu da Inna lafiya." "Amin sai anjima!" Ta fita ita kuma ta shiga kitchen abincin dare ta daura musu wanda bata jima da daurawa ba aka kira sallah sama ta hau ta shiga dakin da Maryam take ta dauro alwala sannan ta fito ta tada Maryam dake bacci. Bandaki ta shiga tai alwala ta fito ta tada sallah anan dakin. Ummi na idarwa ta koma kitchen ta karasa abincin daren ta. Ana isha'i ta gama ta jere komai a dining sannan ta gyara wajen da ta bata sama ta hau tai wanka ta canja kaya sannan ta fito ta shiga dakin Maryam kwance ta same ta akan sallaya. Karasawa tayi ta leka fuskar ta. Ido ta bude a hankali ta fara kokarin mikewa. "Yi kwanciyar ki!" Komawa tayi ta kwanta. Ummi tace "Me kike so na samar miki kinga ba kyau zama haka da yunwa ba ko?" Kai ta girgiza. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke tace "Ko dan kisha magani kya samu wani abu ki danci fadamin me kike sha'awa." Bata fuska tayi kamar zatai kuka ta girgiza kai. Ummi tace "To shikenan bari naje naga ko Abbah ya dawo na bashi abinci ko? Ko zaki sauko kasan?" Kai ta girgiza ta lumshe idon ta kawai dan ita kadai tasan me take ji. Mikewa Ummi tayi ta fita. Abbah ta sama a falo yana kallon TV. Zama tayi tana fadin "Ashe ka dawo sannu da zuwa!" "Yauwah ai nasan kina can wajen 'yar ki!" "Haka ne. Nagama abinci muje kaci ko?" Mikewa yayi ya nufi dining Ummi na binsa a baya. Bayan ya zauna ya kalli Ummi da ta fara serving nasa tuwon farar shinkafa da miyar agushi da taji jan nama sai kamshi take. "Ina Maryam din ita?" "Kasan ba zata iya ci ba!" "To me take so?" "Tace bata son komai tin dazu nake tambaya in akwai abinda take so nai mata amman tace babu!" "To amman haka zamu zauna ba ci ba sha?" "Nima dai abin dake damuna kenan amman bari Aliyu ya dawo naji ya za'a ko?" "Allah kawo shi lafiya." Ya fara cin abincin ya kalli Ummi dake zaune yace "Ke bazaki ci ba?" "Sai anjima!" "Alright!" Ya gama ta kwashe wanda yaci ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito. Tana fitowa Inna na shigowa bakin ta dauke da sallama. Amsawa Ummi tayi ta amshi basket din hannun ta tana fadin "Sannu Inna!" "Yauwah ina mai jikin?" "Tana sama!" Suka karasa falon. Abbah ya mike yana fadin "Sannu da zuwa Inna!" "Yauwah Shehu tin dazu da kuka fita ina kitchen sallah kadai ke fito dani sai yanzu na gama na tsaftace wajen na taho kawo mata Allah yasa dai bata ci wani abun ba." "Sannu Inna ba abinda taci tana kwance!" Ya kalli Ummi yace "Aisha kira ta!" Ummi tai sama Inna tace "Barta bari nazo da kai na." Tabi bayan Ummi Abbah shima ya mara mata baya. Tana kwance akan sallaya suka shiga. Ummi ta karasa ta dafa ta. Ido ta bude a hankali ta fara kokarin mikewa Ummi ta taimaka mata ta zauna ta jingina da gado tana dafe kan ta dake mata ciwo ga jiri kamar zai fadi. "Sannu!" Duk sukai mata ta jinjina kai kawai. Inna tace "Sannu Uwa tah ya jikin?" Ido Maryam ta bude ta gyada mata kai. Inna tace "Sannu Allah sauwake!" "Amin!" Suka amsa da Amin. Inna ta amshi basket din ta dauko flask ta ajiye ta dauki serving spoon ta bude flask din kamshi ya cika dakin. Ido Maryam ta lumshe. Fita Abbah yayi Inna ta dauki plate ta saka serving spoon ta zuba mata ta dauki spoon ta saka sannan ta dauki cup ta zuba mata kunun da tai mata ta ajiye. Maryam ta kalla sannan ta kalli Ummi tace "Taimaka mata taci!" Dauka Ummi tayi. Maryam ta hau girgiza kai tana nuna mata amai zatai in taci. Inna Ummi ta kalla. Sanna tace "Inna wai in taci amai zatai" "Waya fada mata. Ta gwada ci dai!" Maryam ta kalle ta fuska kamar zatai kuka. Inna tace "Duk wahalar da nai a banza kenan. Ai kuwa sai kinci kinji ko!" Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace "Daure kici kinji ko kadan ne!" Ta diba tayi wajen bakin ta dashi a hankali ta bude bakin ta Ummi ta zuba mata ido ta lumshe ta hadiye da kyar. Tsami tsamin faten yasa taji dadin bakin ta dan haka sai ta dinga amsa Ummi na bata sai da sha rabi sannan ta kau da kai. Kunun Ummi ta bata amsa tayi shima tsamin yasa ta dan kurba sannan ta kau da kai. Kai ta jingina a jikin gado tana sauke ajiyar zuciya. Inna ta washe baki tana fadin "Yauwah kuke fa Uwa ta. Sannu Allah yasa ya zaun...." Bata karasa maganar ba Maryam ta mike a guje tayi bandaki. Amai ta dinga yi kamar zata amayar da kayan cikin ta. Ummi tabi bayan ta, ta dafe bayan ta tana mata sannu. *Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [11/17, 14:04] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 40 By *MARYAM S INDABAWA* Hakuri da Juriyya Online ✍ HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Wata Motoci kirar Rolls Royce, Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai she'ki da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine 'kal sai glass d'inta daya kasance tint mai duhu. Wani kyakyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine 'kal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa. Shigar kanannun kaya ne a jikin sa masu kyau da tsada. Bakin wando ne da orange kalar riga, sai bakin takalmi cover mai masifar tsada. Sai sheki yake haka nan hannun sa makale da bakin agogo mai kyau da tsada. Yana da doguwar fuska wacce take zagaye da saje mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya kwanta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido. Bayan sa jingine da kujera hannun sa daya akan sitiyarin motar dayan kuma counter ne a hannun sa yake ambaton Allah. Fararen idanun sa ya lumshe bayan ya iso bakin gate din gidan su tare da dannan horn din motar wanda daya daga cikin security yai sauri ya bude gate din. A hankali ya bude idon sa ya sauke akan sa yace "Welcome Doctor!" Hannu ya daga masa yace "Thanks!" Sannan a hankali ya karasa tura hancin motar cikin katon compound din nasu wanda duk da dare ne wajen tamkar rana saboda hasken wajen ko allura ce ta fadi zaka gani a wajen. Idon sa ya juya ya kalli bangaren Ummi. Murmushi ya saki ganin bangaren Ummin da haske ba kamar kwanakin baya ba da bata nan. A hankali yai parking a wajen da ya saba parking sai da ya dauki minti wajen goma sannan ya bude kofar motar ya zuro kafafun sa kasa. A hankali ya fito ya zura wayoyin sa cikin aljihun wandon sa. A hankali yake taku cikin nutsuwa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar bakin sa dake zage da siraran lips yana motsi a hankali a hankali hannun sa na pressing counter din sa. A haka ya karasa bakin kofar Ummi,  knocking yayi, Abbah ya bashi izinin shiga. Ya shigo a hankali,  A hankali ya shigo cikin tafiyar sa a nutse, karasowa falon yayi a kasa ya zauna kan sa a kasa yace "Barka da dare Abbah!" "Yauwah Doctor Ya kake?" "Alhamdulillah. Abbah kun dawo lafiya ya hanya da mai jiki?" "Alhamdulillah!" Ya dan kalli dakin yace "Ina Ummi na?" "Tana sama ita da Inna!" Mikewa yayi ya nufi stair yana fadin "Me Inna tazo yi da daren nan!" "Tazo ganin marar lafiya." "Tab tazo dai damun ta!" Ya fada a hankali ya karasa hawa. Yana hawa ya fara jiyo muryar Inna na fadin "Na shiga uku har yanzu aman yaki tsayawa!" Dakin da yajiyo muryar ta ya karasa yai sallama a hankali ya bude dakin ya shiga. Inna ya gani tsaye a kofar bandakin tana ta magana. Karasawa yayi a hankali ya ra'ba ta gefen ta ya shiga ciki. Ummi ya gani rike da Maryam. Amsar Maryam yayi a hannun Ummi ya cire mata hijab ya dafa bayan ta hade da tallabo  ta. Ido ta lumshe ta daura kan ta a kirjin sa tana sauke ajiyar zuciya. Famfo ya kunna ya janyo ta ya dauraye mata baki sannan ta koma jikin sa ta kwanta tana ta numfarfashi. "Sannu!" Ummi ta fada. Hannun ta ya kamo suka fito kan gado ya ajiye ta yana kallon dakin. "Menene wannan kuma?" Ya fada idon sa aka plate din da Maryam ta gama shan faten "Fate ne!" Inna ta fada "Menene fate? Zaki bata wannan abincin haba ai dole ya sata amai tsaki ne ma fa! Menene value nasa a jiki?" Kallon sa Inna ta tsaya yi sama da kasa sai da ya gama tace "Kai kasan menene value din? Kuma naga uwar ka shi taci da tana da cikin ka ma. Kullum shi take sawa nake mata dan shi take jin dadin sa abakin ta har kazo duniya shin me ya faru da ita zaka zo ka ishe ni da wani kaza da kaza!" Ummi ya kalla da ta fito ta gama gyara bandakin kamar zai kuka ya kalli Maryam da ta kife akan gado yace "Ummi dan Allah ki daina bata abinda zai na saka ta amai." "Aliyu ko taci ko bata ci ba amai takeyi ai gwara ace ma taci ta dawo dashi da ace bata ci ba tana amai!" "Kyale shi dai ba abinda ya sani sai haka ai. Kai ka samar mata abinda zataci kada tai amai wai shi likita..." Inna ta fada ta karasa wajen Maryam ta dafa ta tace "Sannu 'yar nan!" Shiru taji ta leka fuskar ta taga ta fara bacci tace "Aha kunga ba har ta samu bacci ai ko yaya ne ya zauna dai da ace bata cin ba." Ta mike ta kalli Ummi tace "Ni zan tafi sai da safe in kika biye ta wannan yaron kuwa zai kashe 'yar mutane dan kyale ta zai yi bataci komai ba haka ake fisabilillah ai ko dura a mata da ta zauna bata ci komai ba." Ummi tabi bayan ta tace "To Inna an gode!" Suka sauka ta zauna wajen Abbah tana fadin "Ka rabani da yaron nan na wajen Sule haka ake rayuwa ina ruwan sa dani ni shiga harkar sa ne shiyasa fa na daina shiga ma harkar sa yanzu duk abinda nayi bai gani ba yana can yana fada dan taci faten da nai mata sai kace wacce na saka guba." "Kiyi hakuri Inna kinsan likitocin nan ba komai suke so ana ci ba." Ummi ta fada. "Likitan banza likitan wofi mu a da ba haka muke rayuwa ba, ba wasu likitoci muke kula da kanmu da cimar mu kuma bamufiku lafiya ba? Haba dan Allah sai kuma ace bamu iya ba dan zamani dai." Ummi tace "Kiyi hakuri bari na koma sai da safe!" Ta juya ta koma sama. Inna ta bita da kallo ta kalli Abba tace "Sam Aisha bata son nayiwa yaron nan fada na rasa saboda me kamar ta zane ni take ji in nai masa fada." "Ah haba dai Inna itama ai tana masa, yanzu dai kiyi hakuri bata ci ba!" "Wallahi shehu taci da yawa baka gani ba,  sai da ta gama sai ga amai nan haka tai tayin sa kamar zata amayar da kayan cikin ta da kyar ya tsaya shine fa dan tayi aman ya hau ni da fada dan me na kawo mata abinci wai bai da mene da menene kaji yaro." "To Inna kiyi hakur!" "Bazan hakura ba kai masa magana ya daina shiga harkata to." Ta mike Abbah ma ya mike yace "Zan masa tafiya zakiyi?" "In ban tafi ba ai sai yaron nan ya koreni ina jin baka ga fa yadda ya dinga min ba kamar zai doke ni dan ba uwar sa bace in uwar sa ce ai ba zai mata haka ba." Tare suka fita tana ta mita har ya rakata bangaren ta sannan yai mata sai da safe ta rufe kofa ya juyo yana murmushin. Falo ya koma ya zauna yana aiki a system. Aliyu kuwa bayan su Inna su fita gadon ya dinga kallo a haka Ummi ta dawo yai sauri ya dauke kansa yai kasa dashi. Yace "Ummi gaskiya ki daina bata komai tana ci yana da kyau ta samu abu mai kyau taci dan ya gina jikin ta da na Babyn amman kalle ta fa yanzu duk jikin ta ba kwari saboda bata cin abun gina jiki." "To shikenan amman wannan ma fa is nutritive ta saka protein as gyada, ta saka alayahu as vitamin and some vitamin, she put fat and oil, ga carbohydrate it's balance." "Ummi she should eat first class protein not second class." "Shikenan ni bamu gaisa ba." Kai ya shafa yana murmushi ya karasa wajen ta ya rumgume ta yana fadin "Ummi na Barka da dare da fatan kin dawo lafiya ya hanya?" "Alhamdulillah! Ya kake ya aikin?" "Ji yadda duk na rame Ummi wallahi I miss you!" Kansa ta shafa tace 'Na dawo ai kaci abinci?" Cikin sa ya shafa sai ya kalli gado yace "Rabo na da abincin kirki tin tafiyar Ummi na." "Ai na dawo muje kaci abinci!" "Ummi yanzu ya zamuyi da yarinyar nan ita me zata ci?" "Taki cin komai faten Inna ta dan sha da kunu to suma tai amai amman tinda muka hadu abinda taci da yawa kenan!" "Allah sarki!" Ummi ta kwashe kwanukan ta bar basket da flask din tea sannan ta wuce Aliyu yabi bayan ta yana tafe yana waiwayon dakin har suka sauka. Ba kowa a falo, zama sukai a dining Ummi ta bude flask ta zuba masa abinci ya janyo ya wanke hannun sa a bowl sannan ya faraci yana ci yana lumshe ido hadi da gyada kai ko magana ya kasa malmala daya yaci yai hamdala yasha lemo da ruwa sannan ya kalli Ummi yace "Ummi ta dawo ciki na ma yasan Ummi ta dawo dan yau ya koshi." "Allah shirya ka duk yunwar ai na zata zakaci more than two ball!" "Ummi more two inkai ina ai in samu ince dai kar ya zama ban cin ba. Kinsan jiya Inna wani gashin tukunya tayiwa kaza kinji kamshi dukka gidan nan amman cinya daya ta sammin ta tadan kwadayi fa." Ummi tace "Sai kaje ka siya ai!" "Kinsan ko na siya bazai dadin nata ba fa. Kuma Ummi da gayya tayi min haka!" "Ai sai ka lallabata!" "Ummi sai da ta gama tsokanata na gamai mata sannan ta fara aikin da gayya tayi haka ai Ummi!" "Ni dai ba ruwa na tsakanin ku da Inna kun fi kusa." "Da Innan Allah kiyaye ni kam ai sai su Abbi da Abba su kadai zasu iya da ita." "Kuma zaku iya da itan duk hakuri zamuyi tayi Allah rabamu dasu lafiya." "Allah dai ya rabaku da ita,  mu kuma ya rabamu daku lafiya." Agogo ta kalla tace "Dare yayi gashi na gaji dan bana iya bacci a asibiti let me go and rest!" "Ok muje na duba jikin nata naga magungunan ta zuwa gobe sai muje clinic na duba jikin nata sosai ko?" "Allah yayi albarka my son!" "Amin Ummi nah!" Ta shafa kansa. Ta mike yabi bayan ta. Tana yadda suka barta. Magungunan ta bashi da file din ta sannan ya fita yana mata sai da safe. Dakin sa na bangaren Ummi ya nufa dake kasa. Ya bude ya shiga a kan bedside ya ajiye file din da magungunan da wayoyin sa sannan ya rage kayan jikin sa. Bathroom ya wuce wanka yayi tare da alwala a cikin bathroom nashi mai kyau da tsafta sai ka rantse daki ne dan yadda yake da kyau. Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower glass wanda yake cike da  ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets  boxes and pants kana towels da rigunan wanka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma threequater da kuma turaruka dasu brush da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske private part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai. Sai kamshi yake komai fes dashi gwanin sha'awa. Sai da ya gama wanka sannan ya karasa yai rolling sure ya koma ya dauki boxes ya saka sannan ya cire towel din jikin. Sannan ya wuce ya dauki wasu cotton kayan bacci milk kala a wanke a goge ya saka ya shafa turare mai dadin kamshi. Bayan ya fitone, ya nufi bakin gadon shi ya zauna, idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower. Wacce take haske ya sa hannun sa ya dauka. A hankali ya saka a kunnen sa. Sallama yayi sannan yai shiru. Bayan sakkanni yace "Haba matar ni dai na nayi kewar ki. In Uncle Salis ba zai dawo dake ba tabbas na kusa komowa kasar. Sai muyi zaman mu tare ko?" "Gaskiya ne amman kan lokacin zan so kazo ka duba cikin yan uwan ka na nan ko akwai wacce zatai maka ta maye maka gurbin Maryam!" "Grandma please kiyi hakuri banki ta taki ba amman a duniya ba wacce zata iya maye min gurbin Matata. Nasan kinsan wacece Maryam Sitti!" "Ba a cire rai da rahmar Allah Abin so, duk da yadda kake ganin Maryam daban sai kaga Allah ya kawo maka wacce tafi Maryam cikin rayuwar ka. Da kasan zaka samu Maryam din ne a matsayin mata ai baka sani ba amman Allah ya baka dan haka yanzu ma kada ka cire rai da rahmar Allah. Allah yana sane da kai da izinin Allah zai baka wata Maryam din insha Allahu. Yanzu dai bana son kace zaka saka damuwa akan maganar nan amman Abin so ka girma ya kamata by now ace ka kara samu kayi aure ka samu mai taimakon ka da baka shawara a rayuwa." "In nazo zamuyi maganar Sitti na. Amman masu taimako da ban shawara kun ishe ni Grandma! Ina son ki da kaunar ki!" "Nima ina son ka da kaunar ka ya gidan dasu Ummi dinka?" "Grandma Ummi yau ta dawo bamu jima da rabuwa ba. Tazo mana da bakuwa......" Nan ya bata labarin zuwan Maryam da komai. Murmushi matar tayi tace "To Allah bata lafiya ya raba lafiya!" "Amin! Yaushe zaki dawo Nigeria?" "Sai lokacin da Salisu ya barni ya nace wai ban gama ganin likita ba ni kuma ina da kai wane likita zan ta tsayawa gani!" "Gaskiya ne dan bana nan ya dauke ki ne amman da ba zai dauken mata ba." Haka suka gama wayar su sannan sukai sallama bayan tai masa addu'a. Dayar wayar ce tayi haske ya dauka yace "Mami yanzu nake shirin zuwa fa." Yai murmushi yace "Ummi na ai ta dawo sai a hankali kafin ki ganni!" Yai murmushi sannan yace "Sai da safe!" *Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* "Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 41 By *MARYAM S INDABAWA* Hakuri da Juriyya Online Writer's ✍ HAJOW File din da ya ajiye ya dauka ya fara dubawa a nutse sai da ya dauki kusan 1 hour yana duba file din da nazarin abinda ke ciki sannan ya dauki bag din medicine duba su yayi ya ajiye. Kan gado ya hau ya bude hannun yai addu'a ya tofa ya shafe dukka jikin sa. Ya kwanta yana mai ambaton Allah a zuciyar sa da saman leben sa. Karfe 3:30am ya mike bandaki ya shiga ya watsa ruwa ya fito daure da towel, ya fito yai rolling din sure ya dauki wata brown kalar jallabiya wacce take a goge ya saka ta sannan ya dauki hula, tashi ka fiya naci ya saka ya shafa turare mai dadin kamshi. Kan sallaya ya hau yin sallah sannan ya zauna yana tasbihi ga Allah. A haka aka kira sallah ya tafi massalaci yana zuwa yai rala'atanil firij sannan aka tada sallah asuba. A masallaci ya zauna yai karatun Alkur'ani da azkar. Karfe bakwai ya fito daga masallacin dake jikin gidan su wanda masallacin ma a cikin gidan su aka cire shi. * Ummi kuwa daki ta koma tai wanka ta shirya cikin kayan bacci dakin Abbah ta nufa ta same shi yana aiki a system zama tayi tace "Ranka ya dade bakai bacci ba?" "Banyi ba wallahi aikin nan nake son na karasa!" Kai ta karya tace "Daman nazo nai maka sai da safe ne!" Dagowa yayi yace "Ina zaki?" "Alfarma nake nema zani wajen yarinyar can kaga halin da take ciki in da mutum a kusa da ita zata fi jin dadi!" "Ni kuma sai ki barni." 'In ka barni in kace a'ah kuma ba zani ba. Amman nasan ka da taimako." Hannun ta ya kama yace "Bazan hanaki ba amman tayaya zakina kula dani?" "Baka da matsalar wannan insha Allah!" "Shikenan tashi kije ki kula da ita." "Nagode sai da safe!" Ta mike ta fita. Maryam tana ta bacci kan gadon ta hau ta kashe wuta ta kwanta. Can dare Maryam ta tashi da yunwa da ishi mikewa tayi ta kunna fitila sannan ta diro kafar ta kasa. Basket din dazu ta gani ta nufa ta bude ta dauki spoon ta fara shan faten, tana cikin sha Ummi ta mike ta tsaya kallon ta tasha da yawa ta shiga bandaki ta dinga kakarin amai amman batai ba. Can ta fito ta zauna a bakin gado tana rawar sanyi. Ummi tace "Zazzabi kuma kike ji?" Kai ta gyada ta miko mata bargo ta lulluba baccin da basu koma ba kenan dan yadda jikin Maryam yai zafi. Sai asuba bacci ya dauke ta Ummi tai sallah ta tashe ta tayi sallah ta koma bacci mai nauyi ya dauke ta A hankali yake taku cikin kamala da nutsuwa a haka ya karaso cikin gate din nasu da yake gaisawa da securies din gidan nasu sannan ya nufi sashen Ummi kai tsaye. Ummi daga nan dakin Abbah taje suka gaisa sannan ta sauka ta fara aikin gidan duk da ba datti yai ba ta saka turare mai dadin kamshi sannan ta shiga kitchen Ba kowa a babban falon dan haka dakin sa ya wuce kai tsaye yana shiga ya cire tattausan jallabiyar dake jikin sa ya shiga bathroom daga shi sai gajeren wando da singlet. Wanka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi. Yana fitowa, ya wuce gaban dresing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikin shi ya karato. Gaban wardrobe ya karasa ya shirya cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wando kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue black color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi, hular itama farace sai ratsin blue black, hakama takalman sawunshi da suka kasance half cover,  Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai. Yai wanka da turare wanda nan da nan kamshi ya kara cika dakin. Wayoyin sa ya dauka ya zura a aljihu sannan ya dauki jakar system ɗinshi ya ɗauka da hannunsa na hagu kana hannunshi na dama rike da counter yana dannawa a hankali tare da motsa lips din sa dake ta sheki kamar wanda ya shafa man lebe. A haka ya fito daga cikin ɗakin nashi. Ya karaso cikin tamfatsen falon Ummi. Ido ya lumshe lokacin da ya shaki kamshin turaren da Ummi ta turara mai dadin kamshi. Ji yayi an dafa shi. A hankali yake juyo yana ganin Ummi ce ya rumgume ta yana fadin "Good morning My Ummi!" "Morning too my son how are you,  how was your night?" "Alhamdulillah! Ya gajiyar ku ya mai jiki?" "Alhamdulillah!" Ta kamo hannun sa suka karasa dinning area, kujera ya ja ma Ummi ta girgiza kai tace "Zauna" Zama yayi bisa kujerar, kana, ya kalli Ummi yace "Abbah fa?" "He has alot to do har ya fita!" Ta janyo flask ta tsiyaya masa ruwan tea,  zata zuba madara ya rike hannun ta yana fadin "Ummi kina kara sangartani fa shiyasa in bakya nan nake wahala kawai!" "In ban maka ba wa zanyi wa?" "No one Ummi but by now you have to rest ni na cigaba dayi miki ko?" "Ah haba ni kuma in ka tafi ka barni fa." "Ina zan tafi na barki Ummi?" "In kai aure mana." "Ko nai aure i will always be with you Ummi!" "Tayaya My Son!" "Dauke ki zanyi ko muyi zaman mu anan." "Oh yadda kuka min da ko? To in kana son haka sai dai ka auri ta gida ita ce zata iya rayuwar da kake so kullum kuna nan, gidan ku a rufe amman in ka auro ta waje kuwa bazata iya jura ba zataga an takura ta." "Ummi na kenan kina so dai kice nayi auren gida ko? Ummi u know who is Maryam please from all my slibing wacece take da hali da dabi'u irin na Maryam? Ta riga ta sangartani da komai nata i can't  live with any girl expect her, she is my only love Ummi!" Ya mike a hankali. Ummi ta kamo hannun sa ta nuna masa inda ya tashi komawa yai ya zauna ta hada masa baƙin tea da zuma dan bai shan suga zuma mai kyau yake samo musu sukai using. Bread din da ta gasa da kan ta yaji inibi ya gasu ta bude masa da dankali da kwai a wani bowl sai pepper soup din kayan ciki. Tea din kadai ya sha ya dan kalli Ummi yana shafa ciki yace "Ummi na koshi fa!" Fuska ta bata yai saurin saka hannu ya dauki slice na bread guda daya ya gusura wanda dadin sa da laushi yasa ya lumshe idon sa. Shi ya cinye sannan ya karya wuya yace "Dan Allah Ummi ki tausayawa yaron ki wallahi na koshi!" "Allah in nai tafiya ka kara damu na akan na dawo bakan cin abinci sai na kara sati akai." Kunne ya kama da hannu yace "Affuwan Ummi! Muje naga Yarinyar can anjima zan turo a daukon ita." Ya nufi stair tabi bayan sa a bakin dakin ya tsaya Ummi ta karasa cikin dakin da sallama sai da ta shiga sannan ta bashi izinin shiga ya shiga da sallama. Tana kwance kudundune cikin bargo dan yau da zazzabi ta tashi kuma. "Ya jikin nata?" "Bacci take amman da zazzabi ta tashi?" "Me taci?" "Ba komai tin jiya da taci abincin Inna!" "Bayan ta dawo dashi." "No ta tashi cikin dare ta kara ci!" "Ya zauna kuma?" "Eh ya zauna." Agogon hannun sa ya kalla yace "Zan aiko anjima a tafi da ita!" Ya juya ya nufi kofa Ummi na binsa a baya sai da ya fita ta fito ya tsaya tai gaba yabi bayan ta. A falo suka tsaya ya durkusa yace "Ummi zan tafi pray for me!" "Allah kai ka lafiya ya dawo dakai lafiya, Allah ya tsare min kai a duk inda kake ya baka halak din ka ya kare ka daga cin haram ya sa maka albarka a neman ka. Allah maka albarka!" Hannun ta ya kamo yaiwa Kiss sannan ya amsa da "Amin Ummi na jazakallahu bil khair!" "Same to you son!" Ya dauki jakar system din da dake kan dining ya nufi kofa yana daga mata hannu. Yana fita ya hadu da wani matashin saurayi wanda yake fari dogo dashi. sanye yake da dogon wando pencil,  crazy sai riga t-shirt kyakyawa ne shima dan gayu sai tashin kamshi yake. Daga gani sashen Inna ya nufa, karasowa yayi yana murmushi yace "Barka da safiyya Akee!" "Ka tashi lafiya?" Ya fada ya juya! Amsar jakar system din sa yayi suka nufi sashin Inna sannan yace "Alhamdulillah!" "Banganka da asuba ba?" Aliyu ya jefa masa tambayar. Kansa yai kasa dashi yace "Na dan makara ne Hamma amman ai na samu last raka'at!" Ya fada yana shafa sumar kan sa mai cike da gashi irin gyaran yan samari yan suwaga din nan. Kai kawai Aliyu ya gyada. Compound din Inna a share tsaf dashi tin daga daki har wajen kamshi yake yi. Ido ya lumshe ko ba komai yana son tsaftar Inna duk da ta tsufa bata wasa da tsafta ta tsani kazanta. A hankali suka karasa kofar falon cikin muryar sa mai sanyi yayi sallama. Inna dake zaune gaban ta tea da bread da wainar kwai da fura da nono dukka ta dago ta amsa tana fadin "To fa!" A hankali ya shiga dakin ya nemi kujera daya a ciki ya zauna. Kanin sa Farouk dake bayan sa ya shigo ya samu kusa dashi ya zauna. Kallon sa Inna tayi tana Murmushi tace "Miskili kafi mahaukaci ban haushi." "Ina kwana?" "Lafiya lou wallahi ni na gaji da ganin ka kana zuwa gaishe ni da safe ina laifin da rana ko yamma wato lokacin kayi aure kazo daga gidan ka. Haba wa Malam ai sai yafi armashi." Shiru Aliyu yayi ya zuba mata ido. Inna ta  rausayar da kai tace "Eh mana ka kuwa san ni'imomi da falalar da ni'imomin dake cikin aure, ko auren da bakaji dadin sa bane da kaki ka kara wani ai aure shine cikar mutunci da kimar kowa a duniya amman kalle ka babban mutum mai kima amman ba aure wallahi wani ana fada masa baka da aure zai ji kimar ka ta ragu a wajen sa. Farouk ne ya miƙe tare da fadin "Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya. In baki nemi fada ba kya nemi rigima ni na tafi dan inada aikin yi." Hararar shi tayi tare da cewa "Tafi daga nan!" Sai kuma ta juyo ta kalli Aliyu tace "Dan Allah wa ya saka dashi ne wai? Ni me ma ya kawo ka waje na? Kar kace gaishe ni kazo yi dan baka gaishe ni ba sai rashin kunya da kazo kai min. Ina ruwa na ma da kai ne dan Allah." Harara ta yayi kana ya juya ya fita. Inna ta rike haba tace "Kayiwa Uwar ka!" Aliyu kuwa kai ya jingina da kujera sai kuma ya dago ya kalle ta yace "Maganinki ya kare koda saura?." Da sauri tace "Kai ni kyale ni da shan magungunan nan lafiya ta lou fa. Bana bukata." Mikewa yayi yace "Kin huta kudi na ya huta ni na tafi sai na dawo!" Ya zura hannu a aljihu ya zaro 2k ya ajiye mata. Tace "Allah yayi albarka Allah kiyaye yaron kirki!""Amin!" Ya amsa ya juya ya fita. Farouk ya sama makale da waya a kunne yana ganin sa yace "Am sorry my love ga Yaya bari na raka sa i will call you later!" Ya karashe maganar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Aliyu kauda idon shi yayi yaci gaba da tafiyar sa. Sannan suka jero suka nufi sashin Mami. Suna shiga yayi gefen dama, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali suka karasa cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi. Abbah suka sama zaune akan kujera hannun sa rike da carbi ga Alkur'ani a gaban sa banda sautin da yake tashi na karatu a hankali. Zama sukai sannan sukai kasa da kansu gaba daya. Aya ya kai sannan ya dago yana tasbihi a bakin sa ya kalli yaran nasa ya saki murmushin jin dadi hadi da fadin "Allah muku albarka!" "Amin!" Sannan Aliyu ya kara yin kasa da kansa yace "Barka da asuba Abbi!" "Barka kade da fatan an tashi lafiya?" "Alhamdulilah!" Sannan Farouk ya gaishe shi ya amsa yana musu nasihar sa ta kullum akan suji tsoron Allah a duk inda suke su rike gaskiya da amana sannan ya sallame su suka fita. A babban falo suka samu Mamah tana zaune tana ganin Aliyu da Farouk ta harari Farouk tace "Me kake har yanzu baka tafi ba?" Kai yai kasa dashi. Aliyu ya kalle shi ya mika masa car key yace "Keep the bag inside thank you! Take care bye!" Ya fada yana durkusawa yace "Ina kwana Mamah!" Ba tare da ta kalle shi ba tace "Lafiya lou!" Ta mike ya fice Farouk ma fita yayi amman bai tafi ba ya tsaya a wajen motar sa. *Alla jikan musulmai ya kyautata namu zuwa Amin.* *Antty* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 42 By *MARYAM S INDABAWA* Hakuri da Juriyya Online ✍ HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* Stair ya nufa yana tasbihi har ya karasa kofar dakin Mami. Knocking yayi ta bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune a gefen gadon ta ya karasa ya zauna akan center carpet din dakin sannan ya zame hular kansa. Hannun ta ta daura akan sa tai masa addu'a sannan ta dago tana kallon sa. "Ina kwana Mami?" "Lafiya lou! Ya kake ya aiki?" "Alhamdulillah!" "Ya Ummin naka da me jiki?" "Da sauki!" "Masha Allah!" Kai yai kasa dashi sannan yace "Mami ni zan tafi!" "To Allah tsare yai albarka ya kare a kula a kiyaye aiki da neman halak duk inda haram take ka guje ta dan abinda zata kara maka,  sharri ne tare da ita halak kuwa duk kan kantar ta zaka same ta da albarka a cikin ta. Allah tsare!" "Amin Mami nagode! Sai na dawo!" Sannan ya mike Mami ma ta mike tare suka fito suka samu Mamah a falo ya nufi kofa ita kuma Mami tayi sashen Abbi. Daga nan parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau. Ya nufa,  Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi. Wajen wacce zai shiga ya nufa blue black ce sai sheki take ya nufi ta ya sa hannu zai bude Farouk dake cike ya bude kallon sa ya tsaya. Ya fito yana murmushi yace "Na jira ka fito mu tafi ne!" Ya bashi hanya ya shiga ya rufe masa kofa. Glass yai kasa dashi wanda yake tint yace "Me kake so?" Kai ya shafa yace "Ba komai Hamma!" "Kai dai!" "Please Hamma motar ka dayar nan nake so tinda naga ka daina hawan ta!" "Wacce a ciki?" "Red colour din!" "Ok key din yana clinic in naje zan dauko maka yayi maka?" "Yes Hamma na godiya nake Allah saka da alheri ya kara budi!" "Amin! Ka kiyaye kaji abinda Abbi dai ya fada Allah tsare!" "Amin Hamma Allah tsare hanya!" Ya daga kai yana fadin "Amin!" Sannan ya tada motar Farouk sai da yaga ya fita sannan ya nufi motar sa ya shiga yabi bayan sa. Cikin nutsuwa yake driving yana yi yana tsabihi da addu'ar tsari a haka har ya karasa babban asibitin da yake aiki. A cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Aliyu Suleiman a samanta anan yai parking sai da ya dauki minti sama da goma sanna ya bude murfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito. Wani massenger sa ne ya karaso da sauri car key din ya bashi ya bude ya dauko system din sa da wayoyin sa. Cikin nutsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin. A nutse yake tafiya massenger sa na take masa baya har suka shiga cikin asibitin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa. "Barka da hantsi Dr A.S" Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, tafiya mai tsayi yayi ya shiga  cikin wani ɗan corridor dake gefen daman sa  wanda shi zai sadashi da office din sa. Yana zuwa bakin office din ya tsaya da sauri messenger dake biye dashi rike da jakar system din sa ya karaso ya bude masa. Da Sallama hadi da bismillah ya saka kafar sa ta dama cikin office din. Ajiyan zuciya yaja a hankali saboda ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, Office din ya hadu iya haduwa kai ba ka ce a cikin asibiti kake ba dan tsaruwa da kyau da tsabtar sa. Yana shiga Office dinshi, ya nufi kan katon table din dake gaban sa wanda ya ke katon gaske zama yayi messenger ya ajiye masa bag da wayoyin sa. Budewa yayi ya dauko ta ya kunna ya fara aikin daya kawoshi. Bayan minti na ya dago ya kalli agogon hannun sa har goma da rabi, messenger dake tsaye yace "Hassan Abubakar shine first call him!" Ya juya ya fita ba a jima ba patient din ya shigo cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ya duba shi ya sallame shi. Haka ya duba mutane biyar da sukai booking ganin sa wanda lokacin ya kai masa karfe daya wanda daya yake tashi dan yaje yai sallah kan ya dawo ya cigaba da aiki. Alwala ya shiga yayi ya fito ya nufi masallaci daya da kwata sukai sallah sai daya da rabi ya fito. Wayar sa ya zaro a aljihu ya kai kunnen sa yace "Ok kaje gida yanzu ka dauko min wata patient ban son bata lokaci fa." Ya dauke wayar ya koma office. Zama yayi yana aiki a system. Karfe biyu da kwata akai knocking dagowa yayi ya kalli kofar sannan ya bada izinin shiga wasu nurses ne guda biyu suka shigo rike da Maryam. Kan gadon dake dakin suka kwantar da ita sannan suka juya suka fita. Wayar sa ce tai kara ya dauka yace "Thank you!" Sannan ya kashe. Gadon ya zubawa ido na wasu dakiku sannan ya karasa a hankali yana zuwa gaban sa yaji wata muguwar faduwa gaba har sai da ya dafe kirjin sa. Ido ya lumshe a hankali ya dago ya kalle ta duk da ba abinda yake gani a tare da ita dan hijab ne har kasa a jikin ta fuskar ta kuma ta rufe da hannun ta. "Ya sunan ta?" Ya fada a zuciyar sa, tare da lumshe ido, a hankali ya juya wajen jakar laptop din sa ya bude zip ya dauko folder ta dake ciki. Idon sa ya kai kan sunan ta wanda ya karasa bugun zuciyar sa daduwa. "Maryam Muhammad Jabeer!" Ajiyewa yayi a hankali ya karasa yace "Maryam!" Ya fada kamar me tsoron yin magana, a hankali ta bude fuskar ta tana kallon sa. Kan sa na kasa ta fara kokarin mikewa. Juyawa yayi yace "Zaki iya tashi ki taso!" Kai ta gyada ya nufi kujerar sa, ita kuma ta mike ta fara tafiya taku daya, biyu, uku, hudu taji jiri na dibar ta neman wajen da zata dafa tayi ta rasa baya tayi zata fadi wanda shi kuma lokacin ya juyo kenan ganin ta a wannan halin yasa cikin zafin nama ya karaso ya taro ta ta fada jikin sa, ninkawa bugun zuciyar sa tayi, wannan yasa yai saurin runtse idon sa da karfi. Maryam kuwa ta riga da ta saddakar kawai waduwa zatai taji ta a jikin mutum kara rike shi tayi kam tana mai da ajiyar zuciya. Ido ya bude a hankali akan fuskar ta. Wacce take fara tas ga ciwo ga rama wanda ba abinda kake gani sai dogon siririn hancin ta da idanun ta da suka zurma a ido rufen ma. Sai lips dinta sirara pink kala. Ido yai saurin daukewa daga kallon ta sannan a hankali ya karasa gaban table din nasa ya zaunar da ita ya juya ya koma wajen zaman sa. A hankali ta daura kan ta akan table din ta lumshe idon ta. Shiru yayi yana kallon system din sa bayan kusan minti goma a hankali yai gyaran murya dagowa tayi tana kallon sa da idanun ta da suka rame take jin ciwo har cikin idanun ta dan ita ciwo take ji a ko ina na jikin ta hatta farce yana mata ciwo. A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta. Kanta a sunkuye fuskar ta gwanin tausayi dan daga fuska zaka gane tana cikin wani irin yanayi na ciwo, wahala,  da neman taimako A hankali ya kalli Folder ta dan tsoron ambaton sunan ma yake, idanunshi ya lumshe saboda wani irin bugu da yakeji zuciyarshi yana son Maryam amman meyasa ko me sunan yaji hankalin sa yake kasa kwanciya ji yake ina ma ace ita ce. Sunan na masa kwarjini da wuyar fada. Kamar me koyon magana yace "Maryam ko?" Kai ta gyada kan ta a kasa. Shiru ya karayi can ya mika mata wani memo yace "Magana zamuyi zaki iya?" Sai a sannan ta dago ta kalle shi taga yana turo mata memo da pen, kai ta gyada ta amsa. Yace "Ki fada min gaskiya wacece ke?" Kallon sa ta tsaya yi. Ya gyada mata kai. Pen ta dauka shi kuma ya maida ido kan system ya fara danne danne, bayan sakkani ta mika masa. Amsa yayi ya duba "Bansan ni wacece ba wallahi ban san komai nawa ba bansan kowa nawa ba!" Ya karanta ya dago ya kalle ta sannan ya mika mata yace "Kika ce sunan ki Maryam!" "Eh Sunana Maryam Muhammad Jabeer!" Ta rubuta masa, kai ya gyada yace "Tayaya kika san sunan ki?" "I didn't know!" Ta bashi amsa a rubuce ya kalle ta yace "Wa zaki iya tunawa a rayuwar ki!" Hawaye ne ciki idon ta ta fara rubutu tace " *Mijin Maryam* miji na kawai zan iya tunawa Yaa Haidar!" "Where is he?" "I just didn't know i only know Yaa Haidar as my husband and i loss him from their i can't recall any thing except My Ammi." Kura mata ido yayi can ya dauke kansa yace "Ummi na macece mai tausayi da son taimako i hope zaki zauna da ita tsakani da Allah kuma ba zaki cutar da ita ba!" Kai ta gyada tai masa bayani da hannu kan cewa bazata cutar da ita ba. Ta gode kuma. Kai ya jingina da kujera yace "Yanzu me yake damun ki?" "Komai ciwo yake min bana jin dadin komai na rayuwa!" Ta fada idon ta na cikowa da kwalla. Tausayin ta ne ya kama Aliyu yace "How old are you?" "Seventeen year old!" Tai masa nuni da hannu. Tausayin ta ya kara ji dan yarinya ce sosai ace tana cikin irin wannan rayuwar ga ciki ba miji and babu iyaye ko wani nata yanzu in da ba Ummi ce ta dauko ta bafa wane hali zata shiga. Waya ya dauka yai magana da daya daga cikin nurses din sannan ya ajiye wayar ya cigaba da aiki a system din sa. Ba a jina ba akai knocking ya bada izinin shiga nurse ce ta shigo tace "Gani Dr A.S" Paper ya zara yai rubutu yace "Gasu nan wadan nan test din nake so ai mata ina son result din yanzu, wanda ba zai samu yau ba ayi kokari a samar min su gobe." Amsa tayi ta kalli Maryam dake kwance jikin table din nasa. Kallon ta yayi yace "Ko ba zaki iya bane a kawo kujera?" Kai ta girgiza ta mike a hankali tana cije baki,  nurse din ta kama hannun ta suka fara tafiya a hankali. Da ido ya bisu har suka rufe kofar dakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kan sa da jikin kujera. Awar su biyu da fita suka dawo da Maryam direct kan gadon dakin ta wuce da ita dan ba karamin galabai ta tayi ba ga zazzabi ga yunwa ga ciwo. Kwanciya tayi, Aliyu yana kallon su sanna Nurse din ta karaso ta mika masa result din amsa yayi ya duba agogon hannun sa 3:52pm lokacin sallah la'asar yayi dan gashi can ana tada harama mikewa yayi ya fita a office din masallaci yaje bayan an idar da sallah ya dawo. Wayar sa dake aljihun sa ta hau kara zarowa yayi ya tsaya kallon kiran har ya katse sannan ya bi kiran yana saka wayar a kunnen sa. Amsa sallamar yayi yace "Ummi ta biyo 'yar ta!" "Na kira dai naji ya jikin nata?" "Da sauki Ummi tana office tana bacci yanzu zan koma!" "Alright me ta ci kuwa dan yau bata ci komai ba!" "Ba abinda taci bari naje na tambaye ta me zataci!" "Ok please ka kular min da ita." "Insha Allahu!" "Allah maka albarka ya kiyaye ku!" "Amin ya Hayyu ya Qayyum Ummi!" Ta kashe wayar ya tura kofar office din tana kwance ya karasa bakin gadon yana kallon ta. Kai ya dauke yace "Anyi sallah fa!" Hannun ta da daura akan ta tai masa nuni da jiri take ji!. Nurse din dazu ya kira yace "Take her in and perform abulution!" Ta kama ta suka shiga bandakin tayi alwala suna fitowa ta shimfida mata sallaya ta zauna a zaune tai sallah. Bayan ta idar ya mike ya dawo gaban ta ya ajiye mata memo da pen yace "Kina jin yunwa ne?" Kai ta gyada masa yace "Me kike so kici?" Da hannu tai masa alamar da ba komai. Ya dan kalle ta ya dauke ido yace "Ba abinda kike sha'awa?" Kai ta gyada masa. Mikewa yayi ya koma kan kujera ya dauki folder da aka kawo da result na test da screening da akai duk ya duba sannan ya dauki waya yai typing sannan ya ajiye bayan minti na Messenger sa ya shigo da katuwar leda. Ajiye masa yayi. Aliyu yai godiya sannan ya hau rubutu bayan mintina ya dago ya mika masa yace "Ka amso min a permarcy!" Ya amsa ya juya ya fita. Bai jima ba ya dawo da leda guda ta magunguna da allurai ya bashi ya amsa ya kara godiya. Mikewa yayi a hankali ya dauki ledar magani da wacce ya shigo da ita dazu ya koma gaban Maryam da kan ta ke kasa. Durkusawa yayi ya bude ledar farko ya ciro park uku daya shinkafa da miya ne, daya fried rice, daya tuwo ne miyar taushe sai ya fito da dayar ledar da suke dangin snack ne meat pie, cake, semosa, spring roll, da sauran su. Sai lemuka kala kala daban daban yace "Ki zabi abinda zakici kinji!" Dagowa tayi ta kalli gaban ta taga kayayyakin ba abinda ya bata sha'awa a ciki amman yadda cikin ta ke jin yunwa yasa ta dauki spoon ta dibi fried rice din tana kaiwa bakin ta, ta bata fuska kamar zatai kuka ya dan kalle ta ta gefen ido yace "Mene ne?" Kai ta girgiza sai ta dauki spoon din ta dibi rice and stew din, shima bata fuska tayi sai ta ajiye spoon din dan duk basuyi mata ba. Maltina ta dauka ta bude ta sha kadan ta ajiye tana mai da numfashi a hankali da sauri ta mike wanda batai aune ba ta zame kara kokarin mikewa take ta kasa yazo ya kamata yana fadin "Mene ne?" Kokarin mikewa take dan amai take ji amman ta kasa gane mai take nufi yasa ya dago ta suka shiga bandakin tana rike a hannun sa. Suna shiga ta shiga yin aman wanda dan abinda taci ta harar sai kuma kakarin da take tana yi yana shafa bayan ta har ta gama ya bata ruwa ta dauraye bakin ta sannan suka fito tana rike da hannun sa. Kan gado ta koma ta kwanta ya bita da kallo. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu xuwan yasa mu cika da kyau da imani.* *Antty* [11/19, 12:34] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 43 By *MARYAM S INDABAWA* Hakuri da Juriyya Online ✍ HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* *Wannan shafin naki ne, Zarah Muhmmad Sani Kibia (My Habibty) ina godiya, Allah ya bar kauna da zumunci Allah ya baki zuri'a masu albarka ya kara muku fahintar juna tsakanin ki da mijin ki Amin.* Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli kayan abincin da ba abinda ta taba, rufewa yayi ya koma ya dauki ledar maganin ya hada ruwan da zai saka mata ya hada allura da wacce ya zuba a ruwan ya saka mata. Tana bacci taji shigar allurar a hannun ta ya saka mata ruwa, bude ido hawaye na zubo mata dan zafin da taji yace "Sannu!" Ido ta lumshe tana ji yace "Gyara na miki allura!" Idon ta ne yai raurau dan tasan faman da suke da Yaa Haidar a gida ma kenan in bata da lafiya. "Bafa da zafi zan miki ba!" Ya fada yana kallon ta. Kalaman Yaa Haidar kenan in zai mata allurar yace ba da zafi zai mata ba. Juyawa tayi ya dage hijab din ta doguwar ta bayyana ta ciki ya zura allura ya zira mata wata yar kara ta saki sai kuma ta fashe da kuka a zuciyar ta take kiran Ammi, Ammi nah! Yatsa ya saka yana mulmula wajen sannan ya mike a hankali ya koma wajen da yake zaune. A hankali yasaka zuwan ruwan saboda yabi jikin ta sosai. Wannan yasa tin hudu har shida leda na biyu ko rabi bai yi ba. Wayar sa ya dauka ya kira Ummi. Ummi da ke hanyar komawa gida ta daga kira ta na fadin "Ba dai kun dawo ba na nan ba?" Maryam ya kalla sannan yace "Aah muna asibiti ruwa nake kara mata daga wannan ya kare zamu taho sai bayan magariba." Ya fada yana kallon agogon hannun sa dan lokacin shida har ta gota. "Ya dai jikin nata?" "Ummi da sauki!" "To Allah kara sauki. Allah dawo daku lafiya." "Amin!" Ya kashe wayar ya shiga yai alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da akai isha'i. Nurse din da yasa ta kula da ita tana zaune ya shigo ta mike da sauri. Ya kalle ta yace "Ta tashi ne?" "A'ah!" Ruwan ya kalla yaga saura kadan bai fi minti biyar ba zai kare. Zama yayi a kujera yana danna system din sa. Bayan minti hudu ya mike ya karaso wajen ya zare mata ruwan sannan ya koma ya cigaba da aikin sa. Karfe takwas ya rufe system din sannan ya saka a jaka ya mike ya nufi bakin gadon nata. "Maryam!" Ya fada zuciyar na bugawa. A hankali ta motsa tana bude idon ta. Kai yai saurin kaudawa yace "Tashi mu tafi ko?" Kayan abincin gaba ta ta kalla ta zuro kafar ta kasa ta sauko ta zauna a gaban abincin tuwon da bata ci ba ta bude ta fara ci sai dai batai loma uku ba amai ya taso ta yunkura zata tashi ya rike ta yana fadin "Ki daina tashi a gujen nan fa." Kan ta kwace jikin ta ta dinga kwara aman anan wajen. Sai da ta gama ya daga ta suka shiga ta dauraye bakin ta sannan ya kira nurse yace a gyara office din a bawa messenger sa key. Maryam yasa daya daga cikin nurse din ta kamo messenger sa ya dauki jakar system din sa da magunguna ya bi bayan Aliyu. Mota ya shiga ya zauna messenger ya bude gidan baya ya saka masa kayan nurse din suka karaso da Maryam ta bude dayan side din ta saka ta rufe mata kofa tace "Allah kara sauki!" Kai ta gyada Aliyu ya amsa da "Amin ya Hayyu ya Qayyum!" Sannan ya tada motar yana motsa bakin sa dake tasbihi a haka suka fuce daga asibitin yana driving cikin nutsuwa da sannu da sannu suka karasa gida. Yai horn mai gadi ya leko ya bude masa yana daga masa hannu da masa sannu da zuwa. Wajen da yake parking ya karasa yai parking sannan ya fito ya bude mata kofar mota ya kamo hannun ta, suka nufi sashen Ummi. Yana karasawa bakin main falon Ummi ya jiyo muryar Inna na fadin "To sai yaushe zasu dawo tin safe fa ta fita!" "Inna nasan suna hanya!" Bata rufe baki yai sallama. Ummi ta amsa tana mikewa da sauri ta karaso ta kama Maryam ta karasa da ita kan kujera ta kwanta. Ummi ta kalle ta tace "Sannu!" Ta juyo ta kalli Aliyu da har ya kusa kofar dakin sa. Yana shiga ya cire kayan sa ya shiga yai wanka ya saka three quarter wando da riga marar nauyi. Wayar sa ya dauka ya kai kunne yace "Kaje mota ta ka daukon bag system dina da wata ledar magunguna ina part din Ummi!" Ya kashe wayar yana duba sakon da ya shigo masa. Da kallo Inna tabi shi tana tabe baki tace "Kai ka sani!" Sannan ta dauko flask din da tazo dashi na faten dankali da tai mata da wake da alaiyahu da hanta ta zuba mata ta mikawa Ummi tace "Bata taci kila haka ya barta ba abinda taci tin safe!" Ummi ta amsa tace "Tashi kici kinji maryam!" Mikewa tayi ta amshi kwanon ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan so take ko zai dawo wani itama ya zauna a cikin ta sai da taci da yawa sannan taji yana son ya taso mata ajiye plate din tayi tana dafe kirji. Inna tace "Sannu aman ne?" Kaita gyada tace "Sannu!" Ido ta runtse. Dai dai fitowar Aliyu kenan ya dinga kallon ta da plate din gaban ta. Karasowa yayi a hankali ya zo ya dauki plate din yana duba abinda ke ciki hannu ya saka ya dangwala ya kai bakin sa sannan ya tabe baki yace "Mene ne kuma wannan?" "Wallahi Allah ka fita hanya ta Aliyu ni dai ban saka da kai ba kuma ba kai naiwa ba ah toh!" Ummi ta kalle shi ya dauke kai yace "Taci ne?" "Taci ina jin shi yake damun ta tinda taci amai take so tayi ma ta kasa." Inna ya kalla yace "Kinga kin kara mata wahala ko? Dame zata ji da ciwon ko da aman dake damun ta." Mikewa Inna ta yi tace "Ni dai ba ruwa na da kai balle ka sa min ciwon kai. Kai da ba a iya maka me taci tin safe ta ci wannan da yawa kai da zakai godiya zakai min fada. Ni dai ba dan kai nake ba dan uwarka nake kuma da tausayin yarinyar amman dan takai wallahi ba zan ba." Ta fice tana mita. Ummi ya kalla. Ummi tace "Menene aibun wannan din?" "Ummi but ai damun ta yake!" "To ta dawo dashi ne da ta zauna da yunwa fa? Me taci acan clinic din?" "Na siyo mata komai amman ba abinda taci da tayi spoon daya sai amai." "To kaga ai gwara wannan ya dan zauna ko?" Da sauri ta mike zatai sama Aliyu ya kamo ta sukai toilet din falon nan tai ta amai sai da ta harar da duk abinda taci. Tana aman Farouk ya shigo jin kakarin amai duk ya daga masa zuciya ya bata fuska shi a lallai kyamkyami yake. Ummi na bakin kofa tana tai mata sannu. Sai da ta gama Aliyu ya fito da ita. Kallon su Farouk ya tsaya yi da mamaki wace wannan kuma. Akan kujera ya kwantar da ita ya cire mata hijab. Juyowa yai ya kalli farouk da ya tsaya kamar statue. Hannu ya mika masa bag din maganin ya amsa ya balli wanda zata sha sannan ya mika mata ruwa. Fuska ta bata kamar zatai kuka yace "No don't cry take it kinji zai sa ki rage jin ciwo." Ta amsa Ummi ta fito ta nufi dining ta dauko lemon da Maryam ke so ta taho dashi ta kalli Farouk tace "Ya kake tsaye kai kuma?" Fuska ya yamutsa sannan ya ajiyewa Aliyu system yace "Tafiya zanyi!" "To!" Ya juya ya fita yana tofar da yawu. Da kyar ta sha maganin sannan Ummi ta bata lemon da ta kusan shanye shi sannan ta koma ta kwanta take bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya Ummi da Aliyu suka sauke sannan Ummi ta kalli Aliyu tace "Kai me kaci?" "Ba komai!" "Gwara kaje kaci ko dare nayi!" Mikewa yayi ya nufi dining yana fadin "Abbah fa!" Mikewa tayi tace "Yana sama bari naje!" Ta tafi shi kuma ya zuba abinci kadan yaci ya ture ya 'kurawa Maryam dake bacci ido. Yafi awa daya a zaune Ummi ta sauko cikin shirin bacci ta tada Maryam sukai sama. Ta kalli Aliyu tace "Zaman me kake ne?" Mikewa yai yana shafa kai ya dauki jakar system yace "Sai da safe!" "Allah bamu alheri!" Ya nufi dakin sa ya ajiye system ya zauna bakin gado yai shiru kawai. Sai wajen daya ya kwanta karfe uku kuma ya tashi ya yafi masallaci. Acan suka hadu da Abba da Abbi har farouk duk acan suka baro shi sai bakwai ya koma gida. Ummi ya sama a falo tana gyara dining ya karasa ya durkusa a kasa yana fadin "Barka da safiya Ummi!" Ta shafa kan sa tace "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah! Ya me jiki?" "Da sauki! me yake damun ka?" Kai ya girgiza yai kasa da kai. Tai murmushi tace "Shikenan!" Ya mike yace "Yau ta tashi da zazzabin?" "Eh tana can kwance!" Sama ya nufa ya haye Abbah ya sama zaune a falo ya karasa ya durkusa suka kara gaisawa sannan ya mike ya nufi dakin da take. A bakin kofa ya tsaya ya kalle ta tana kwance cikin bargo. Juyowa yayi ya sauka ya koma dakin sa. Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani dogon cofee wando mai layi layin milk ya saka milk riga mai dogon hannu ya shafa turare sannan ya nufi falo. Abbah da Ummi ya sama a dining ya karasa ya zauna. Ummi ta mike zatai serving nata yai saurin rike hannun ta yace "Ummi zan zuba fa." "Nasan hali kila kaki ci ne?" "Zan ci Ummi, amman Maryam fa?" Ya karashe fada da sunan ta a hankali. "Kasan ba ci zatai ba." "Ummi ban son rashin cin abincin nan matsala ne ga ita da kuma Babyn." "Amman kasan ba yadda zamuyi ko?" "Haka ne Ummi amman fa haka Maryam tayi suffering wanda sai da tai wata biyar ta fara cin abinci Ummi am affraid kar abinda ya same ta ya samu wannan ma." "Insha Allah ba abinda zai same ta. Itama haka Allah yayi zata mutu da Babyn tayi shahada dan haka ka daina saka damuwa da tsoro nasan abinda ke damun ka kenan daman." Kai yai kasa dashi ta hada masa tea din ta tura masa da abincin amsa yayi ya sha tea din ya dan cakuli abincin wanda tini Abbah ya fita. Bayan ya gama ya bi Ummi kitchen yace "Ummi am thinking of me zanwa yarinyar nan ta samu lafiya!" "Ciwo ne fa Allah ya daura mata kuma a sannu zata warke, insha Allahu naka dai ka bata kulawa da addu'a." "Allah bata lafiya to!" "Amin amin!" "Na daura ta akan maganin rashin maganar nan in ta kiyaye insha Allahu zata dawo mata since ba dashi aka haife ta ba ina ganin in ta fara maganar wani abun zai zo da sauki amman ace ba magana ga ciwo abun zai mata yawa" "Allah saka da alheri kuma Allah bata lafiya ta tuna komai da iyayen ta shine farin ciki na." "Nasa an bincika min ko lossing memory tayi but ba wani matsala a game da wannan Ummi what are you thinking?" "Allahu a'alam!" Mikewa yayi yace "Let me go an greet Inna and Mami i will come back and check on her!" "Ok!" Ya fita. Sashen Inna ya nufa a falo ya same ta tana ta goge goge wanda ba abinda take gogowa dan yadda wajen yake a gyare tsaf. Kai ya girgiza ya zauna akan kujera. Ta juyo tana fadin "Wallahi daman nasan sai kai. Kai ne baka magana a fili sai a ciki in ba haka ba yanzu in nace bakai sallama ba sai ka rantse da Allah kayi muryar ma rowar ta kake kai kam ka shige su ban san tayaya kukai rayuwa da Maryam ba wallahi yarinyar nan tayi hakuri da rayuwa da kai Allah dai yai mata rahma amman nasan ka cutar da ita da yawa." "Hajiya Inna i just come to greet you not listen to dis you gist!" "Kai ka sani! Me ma ya kawo ka waje na? Naga nace ba ruwa na da kai ko? Kaga ni bana son ma ina ganin ka wallahi tinda baka son gaskiya." "Dan Allah Inna ki bari mu gaisa in tafi ni." "Na hanaka gaishen ne?" "Ina kwana?" "Da ban kwana ba zaka ganni ne?" Mikewa yayi ya nufi kofa tace "Au yau ko na sa albarka ba zaka bani ba." Hannu ya zura a aljihu ya zaro 3k ya ajiye mata sannan ya juya ya fita yana jin ta tana fadin "Ko kai fa Allah yayi albarka ya tsare ka ya jikan Maryam!" "Amin ya Hayyu ya Qayyum!" Ya fada a zucya. Sashen su yaje ya samu Mami a falo zata shiga sashen Abbi tare suka karasa. A kasa ya zauna ya gaishe da ita sannan ya gaishe da Abbi sukai masa nasiha sannan ya tafi sashen Ummi. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin" *Antty* [11/19, 12:34] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 44 By *MARYAM S INDABAWA* Hakuri da Juriyya Online ✍ HAJOW *Bismillahir Rahmanir Rahmin* A sama ya same ta a dakin Maryam, ta taimakawa Maryam ta shirya tana zaune tana lallabata ta sha ko tea ne amman taki sai lemon da ta sha kawai. Shigowa yayi ya durkusa a gaban su. Ummi ta mike tana fadin "Ina zuwa bari na kira office naji dan yau da kyar zan fita ban san wa zan barwa Maryam ba." "Ba aikin da zakiyi ne?" "Wallahi akwai wani case da aka kawon nake son na fara aiki akan sa amman ban san tayaya zan ba ina ganin ko na samo me kula da ita." Zama yayi sannan yace "For today u can go and do your work since i will not go any where!" "Kai amman nagode kuwa Son kaga na samu nayi abu da yawa yau." Ta juya ta fita. Ya juyo ya kalli Maryam da ta hade kan ta da gwiwoyin ta. Gyaran murya yayi yace "Kinsan ba za dai ki zauna haka ba komai a cikin ki ba ko? Ko kina son ki rasa Babyn dake cikin ki?". Da sauri ta dago tana kallon sa hannun ta akan cikin ta. Sai ta hau girgiza kan hawaye na zubo mata. Yace "Fada min me kike so?" Kai ta girgiza ya dauki cake din gaban ta ya mika mata. Amsa tayi ta kai bakin ta kadan ta gutsura ta tauna ya kalle ta yace "Kara mana!" Ta dago ta kalle shi, murmushi ya dan mata yace "Kici kinji!" Kara gutsura tayi dai dai lokacin da Ummi ta shigo cikin shirin ta na tafiya aiki. Ta kalle ta ta saki murmushi tace "Tana ci kenan!" "Eh tana dan ci." Ya bata amsa, ta karasa wajen Maryam ta dafa ta tace, "Daugther zan fita aiki but i will soon come back, ga Yayan ki nan he will take care of u if u need any thing else tell him. Allah baki lafiya!" Hannun ta ta kama tai mata godiya sannan ta mike ta kalli Aliyu tace "Son am going take care!" "Insha Allah!" Ya mike zai rakata tace "No ka zauna wajen ta takarasa kaji!" "Ok!" Ta juya ta fita yana mata addu'a sannan ya kalli Maryam yace "To ki dan sha Tea din!" Idon ta ne ya ciko da kwalla. Yace "Try it!" Cup din ta dauka ta kai bakin ta dumim tea din yasa ta kafa kai sai da tasha rabi sannan ta ajiye, kirji ta dafe yace "No kar kiyi kinji!" Kai ta gyada amman yadda take jin tashin zuciyar bata san lokacin da ta mike da sauri tayi bandaki ba. Da sauri yabi bayan ta. Ummi na sauka ta samu Farouk zaune a falo. Kallon sa tayi tace "Ah Farouk kai kadai zaune anan!" Kai ya shafa yace "Nazo wajen Hamma ne!" Sama ta kalla tace "Yana sama ai! Kaje ka same shi!" "Toh fita zakiyi?" "Eh zani aiki ne!" "Adawo lafiya Allah tsare." "Amin!" Ta juya ta fita shi kuma ya haye sama ya nufi dakin Ummi ya murda. Kakarin aman ta ya jiyo da sauri ya juya ya fita yana yamutsa fuska. Anan falon sama ya zauna yana pressing phone nasa. Ganin ya kwashe wajen minti goma bai fito ba yasa ya nufi dakin. Ganin su yayi sun fito a toilet din Maryam na gaba Aliyu na bayan ta. Kan gado ta kwanta taja bargo ta rufa ya karaso cikin kulawa da tausayi yace "Sannu!" Kai ta gyada ya dago yana kallon Farouk dake tsaye fuska a yamutse dan Farouk ba dai kyamkyami ba. "Kaje daki na ka daukon wata leda akan kujera!" Da sauri ya juya bai jima ba ya dawo ya mika masa leda ya juya ya fita. Ruwa ya dauka a ciki ya hada ya saka mata nan take bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kwashe kwanukan wajen ya fita dakin Farouk ya gani zaune ya kalle shi ya nufi stair da sauri Farouk ya karaso yana fadin "Kawo big bro!" Ya amsa ya sauka Aliyu yabi bayansa. Kitchen ya kai ya dawo ya sami Aliyu a kasa yace "Hamma wai wacece wacan ne?" Dagowa yai ya kalle shi sai yai sauri yai kasa da kansa yace "Uhmm ina kwana Yaa Haidar!" "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah!" "Mukullin motar yana kan dressing mirrow!" Yana fadar haka ya fara danne danne a waya. "Nagode Allah kara bude!" "Amin!" Ya juya ya nufi dakin sa. Wayar sa ce tai kara ya dauka yace "Ummi menene?" "Anjima mai aiki zata zo shine nace bari na fada maka." "Allah kawo ta lafiya." "Ya me jikin?" "Na saka mata ruwa bacci take yi!" Ya fada ya mike ya nufi sama dai dai fitowar Farouk ya kalle shi ya fita kawai yana tunanin to wacece wannan yarinyar. Bacci ya same ta take yi sauka yayi ya koma dakin sa ya fara aiki a system din sa. Har karfe sha biyu yajiyo ana knocking ya sauka ya ga mai aikin ce. Suka gaisa sannan ya bata hanya. Kitchen ta shiga tai wanke wanke ta gyarawa Ummi kayan miyan da ta saka ta dan basa mata girki iyakar su wanke wanke da sauran su. Aliyu na bude mata ya juya ya koma dakin lokacin ruwan ya kare ya zare mata ya sauka ya zauna a falo. Yana zaune yajiyo sallamar Inna kai ya dafe ya amsa. Ta shigo ta zauna tana fadin "Ina mahaifiyar taka?" "Ta fita aiki!" Mikewa tayi tai sama tace "Ba wajen ka nazo ba ai da kake sha min kamshi!" Ya bita da kallo sannan ya dauke kai. Maryam ta sama kwance amman idon ta biyu ta kalle ta tace "Sannu Uwa ta ya jikin?" Mikewa tayi tai mata alama da hannu ina kwana? Inna tace "Lafiya ya jikin?" Tai mata alama da da sauki. Tace "To Allah kara sauki!" Ta amsa da amin a zuciya. Sannan tace "Kina jin dadin nan din ne?" Kai ta gyada mata tace "Ko dai zaki zo daki na?" Kai ta gyada! Tace "To taso muje kinji!" Ta mike Inna ta fita Maryam tabi bayan ta. A kasa suka samu Aliyu bata kula shi ba ta yi gaba Maryam ta kalle shi sannan tabi bayan inna. Kai ya jingina da kujera yana mai lumshe idon sa. Suna shiga tace "Kinga dan dakin nawa ko? Zauna akan kujerar kinji!" Ta zauna tana bin dakin da kallo kamar dakin amarya ga kyau ga tsafta. Inna tace "Me zan kawo miki?" Kai ta girgiza. Inna tace "Ki saki jikin nice mahaifiyar wanda ya kawo ki gidan nan su hudu na haifa Baban shine babban wannan na dakin da muka baro wai shi Dr sunan sa Aliyu baban nasa shine babba sunan sa Suleiman sai wanda kike wajen matar sa, Usman sai Takwarar ki mai sunan mahaifiya ta wacce ta mutu tin suna yara, sai autar su Nusaiba dake aure acan kasashen waje. Su uku suka rage min amman alhamdulillah ina jin dadi kamar me ya'ya goma dan suna kulawa dani. Babar Aliyu uwa da uba daya suke da wacce kike wajen ta Aisha ita kuma sunan ta Hauwa ya'yan ta hudu Aliyu ne babba sai mata guda uku ta aurar da biyu Asiya da Hannah daya tana can makarantar kwana me suna Najwa, sai abokiyar zaman ta Barira wacce ta haifi ya'ya biyu Umaru da Bilkisu. Sai Aisha wacce da ta haihu yaran suke mutuwa ta haifi ya'ya biyar amman duk babu mai rai. Wannan yasa take rike da Aliyu duk da dai tin kan ta fara haihuwa yake wajen ta dan tana son yara gashi Allah bai bata ba. Sam Barira bata da dadin zama ta saka Aisha a gaba yadda ta tsani Aisha ko Hauwa kishiyar ta bata tsana ba na rasa dalili ni kuma Allah ya dauran son Aisha dan yarinya ce mai tarbiyya da ladabi ga kyauta ita ta koyawa Aliyu shiyasa hannun sa yake a bude dan duk safiyyar Allah, in zai fita sai ya ban kudi yadda yake min tamkar ni na haife shi bar shi dai da miskilancin sa. Sai dan banzan kwadayi a cikin sa. shi kuwa Farouk sai kyale kyale kamar me haka kullum yake kamar mace ba shi da aiki sai surutu inya zauna ya cikan kunne to kinji kadan daga yan gidan a sannu zan na fada miki irin rayuwar da muke ciki wata ma da idon ki zaki gani." Murmushi Maryam tayi Inna tace "Oh na manta ban fada miki siriki na Abubakar ba mijin Nusaiba wacce nace suna waje yaron kirki kenan wallahi uwa ya dauken yana sona ya'yan su uku da Ammar, Widad sai Muhsin." Kiran sallah aka tada Inna tace "To kinji sallah tashi muje kiyi alwala kizo muyi sallah nayi dambu zaki ci ai ko?" Tin da ta samu ciki yau ne aka fadi abu taji tana son ci sai dai tasan in taci me zai biyo baya. Bandakin Inna ta kai ta wanda yake a wanke a goge tas dashi. Alwala sukai anan falo sukai sallah bayan sun idar Inna ta zauna tace "Ina wannan Aliyun da kika gani to ba fa aure ne dashi ba yayi aure shekara biyar kenan da mutuwar matar amman yaki ya sake auren ni tsoro na daya ma kar muje aljanna ce ta kuma aure shi." Aliyu ne ya shigo wanda tin daga bakin kofa yake jin muryar Inna ya shigo da sallama ya samu kujera ya zauna. Ta kali Maryam tayo kasa da kai cikin muryar rada tace "Kinganshi ko?" Kai ta gyada Aliyu ya dauke kai. Inna ta mike tace "Bari na kawo mana abinci!" Ta shiga kitchen ta hado musu abinci kowa a plate din sa. Ajiyewa Maryam tayi tace "Allah yasa yai miki dadi!" Ta zauna ta fara cin nata tace "Ai dai ba nama bane bare kace na maka rowa." Maryam ta dauki spoon ta dibi dambun Aliyu ta kalla da yake kallon ta. Maida spoon din tayi ta tura masa abincin kai ya girgiza sai kuma ya mike ya dauki plate din ya kalle ta yace "Tashi muje kici a can kisha magani." Bai jira jin ta bakin Inna ba ya fice. Inna tace "Oh kada ta zauna a waje na kenan lallai Aliyu!" Maryam ta mike ta kalle ta, tanaiwa mata alamar zata dawo ta fita. A hankali ta fara tafiya zuwa sashen su. Farouk da ya dawo zai je sashen Inna ne ya kusan yin karo da ita dan waya yake dannawa bai kallan gaban sa, da sauri taja baya, ya dago da sauri yana ganin Maryam yai baya da sauri yana hade fuska yace "Menene haka bakya kallon gaban ki ne?" Hannu ta hade tana bashi hakuri, wani kallo ya watsa mata ya bar wajen da sauri, itama da sauri ta nufi sashen Ummi tana waiwaye. Aliyu ta sama a falo ya nuna mata kan kujera ta karasa ta zauna ya mika mata maganin da ya ballo sannan ya bata ruwa. Amsa tayi ta fara sha tana sha tana hawaye dan bata son shan magani. Bayan ta gama ya kalle ta yace "Me kike so ki ci?" Plate din da ya shigo dashi na dambun da Inna tayi ta kalla, yace "Zaki ci wannan ne?" Kai ta gyada ya kalli dambun yace "Kar ya saki amai fa!" kai ta girgiza alamar ba zai sa ta ba Daukowa yayi ya dauki spoon yai cokali daya, yayi dadi yaji gyada da zogale dan haka ya mike mata, amsa tayi sai kuma ta mika masa tai masa alama da yaci. Kai ya girgiza yace "Ci abinki!" Diba tayi taci cokali uku taci ta ajiye dan ji tayi ya tsaya a wuyan ta. Ruwa ta sha ta koma ta kwanta a gefe. Ya kalle ta yace "Har kin koshi?" Kai ta gyada kawai ta lumshe idanun ta. System din sa ya janyo ya cigaba da aikin da yake yana yi yana satar kallon Maryam dake kwance har bacci ya dauke ta. A ransa yace "Tana can ta cika mata kunne da hira ko wa yace mata hira take so yanzu hutu take bukata." Ya dan saki tsaki yana cigaba da aikin sa. Yana zaune mai aikin su Baba Habi ta fito dan a bangaren su Mami take ita da sauran masu aiki ta karaso falon tace "Dakta na gama ni zan tafi sai Hajiyar ta dawo." "To Baba sannu sai anjima!" Ta fita ya cigaba da abinda yake yana zaune akai sallah la'asar, Maryam ya tasa ya shiga yai alwala ya fita masallaci. Alwala tayi tai sallah ta dauki Alkur'ani tana karantawa. Hudu da kwata ya dawo kitchen ya shiga ya bude firij ya dauko Fresh Yoo ya dawo falo ya same ta tana karatu a cup din tangaran ya zuba ya fara sha yana aiki yana kallon ta. Bayan ya gama ya mike ya kunna TV ya koma ya cigaba da aiki, karfe shida saura Ummi tayi sallama a kofar dakin nata. Aliyu ne ya amsa Maryam kuwa sai bin kofar tayi da kallo. Ummi ta shigo ta karasa wajen Maryam dake ta kallon ta tace "Sannu ya jikin?" Da sauki tai mata nuni sannan ta kalli Aliyu tace "Doctor ya gidan da me jiki?" "Alhamdulillah!" "Allah kara sauki!" Ta mike tace "Bari na hau na sauko!" Ta mike tayi sama. Bata jima ba ta sauko ta canja kaya hannun ta rike da leda ta karaso ta dafa Maryam tace "Sannu!" Kai ta gyada ta kalle Aliyu tace "Dr sannu da jinya Allah ya saka da aheri!" "Haba Ummi sai kace wani abu nayi ai is my job!" "Allah maka albarka!" "Amin." "Me zamu dafa ne?" "Ummi just do sometime simple dan naga kin gaji!" Maryam ta kalla tace "Daughter ke me kike son ci?" Kai ta girgiza ta kalli Aliyu tace "Me taci ne yau?" "I can say nothing since she just eat three spoon of dis thing!" Ya nunawa Ummi plate din da ya rufe na dambu. Ummi ta bude tace "Wa ya bata?" "Kema kin sani. Inna ce." "Maryam to bakya so?" Kai ta gyada ta kalli Aliyu tace "Kai fa?" Baki ya tabe ya girgiza kai. Ummi tace "To ni bari naci da a zubar sai na girka ko supagette ce!" Ta zauna ta ci sannan ta shiga kitchen ta wanke yalon da ta siyo sannan ta fito ta ajiyewa Aliyu da Maryam ta koma kitchen dan yin aiki. Daya Aiyu ya dauka ya mike yabi bayan ta. Tana aiki suna hira akan aikin ta yawanci yace "Ummi yanzu ya za ayi da yarinyar nan?" "Name fa?" "In zaki aiki da safe wajen wa za a barta!" "Ba matsala ko da Baba Habi na barta kan dai mu dawo." "Ummi tana bukatar kulawa fa." "To Aliyu ya za ai?" "Shekara ta kusa karewa gashi ban dauki hutu ba i think, i am going to take it now dan na kula da ita sosai dan akwai magani da allurar da na daura ta akai na matsalar rashin maganar ta ne me kika ce?" "Hutun ai ba zai fi 1 month ba Son!" "Yes is just one month Ummi! But by then nasan cikin ya kara girma since yanzu yana four month ina sa ran in ya kara kwari zai rage bata wahalar nan me kika ce?" "Bansan me zance ba Aliyu, my son u are such a kind person Allahu ya biya ka ya baka lada yai maka albarka Amin!" "Amin ya Hayyu ya Qayyum thank you so much Ummi!" "U are always welcome my son!" "Ramadan remain three week fa!" "Allah nuna mana zaki Umrah ne?" "Tayaya zan tafi na bar Maryam.". "Sai ku tafi tare!" "Ba wahala?" "Mu bari muga yanayin jikin ko tinda goman karshe zamu tafi." "Shikenan! Abbah naji yace in anyi 15 zai tafi shima yai min magana nace Maryam." "Insha Allahu by then jikin ya kara sauki." "Allah ya yadda!" "Amin!" A haka take girkin yana taya ta aiki har suka gama fried supagette da papper chicken suka jere a dining. Maryam kuwa taji dadin yalon taci da yawa. Tana zaune su Ummi suka gama. Aliyu ya shiga yai alwala ya tafi masallaci Ummi da Maryam sukai sallah anan falo. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.* 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 45 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Karfe takwas da kwata Aliyu ya shigo tare da Abbah a falo suka zauna Abbah ya kalli Maryam yace "Ya jikin?" Tai masa alama da sauki. Sannan ya kalli Aliyu yace " ya jikin nata kuwa?" "Abbah da sauki sosai!" "Allah kara sauki ta ci abinci kuwa?" "Ai kasan sai a hankali zatana ci a sannu zata daina duk aman nan da rashin cin abincin insha Allahu." "Allah ya yadda!" Ya mike yai sama. Ummi tabi bayan sa, sun jima sannan suka sauko Abbah sanye da jallabiya daga gani wanka yayi dining suka shige. Ummi tace "Ku taso muci abinci!" Aliyu ya mike yana kallon Maryam dake girgiza kai. Yace "Bazaki ci ba!" Kai ta gyada ya nufi Ummi ta fara zuba masa ya dakatar da ita wai ya ishe shi. Ta kalli dan abincin tace "Haidar what wrong with you!" "Nothing Ummi!" Abbah ya dago ya kalle su yace "Me yake faruwa?" "Abbah baya son cin abinci fa sam!" Kai yai kasa dashi yace "Ciki na ne ya cunkushe two days kuma ban jima da shan youghurt ba." "Alright kadai na kiyayewa bana son rashin cin abinci da girman ka." "Insha Allahu Abbah zan kiyaye!" Suna Dining suka jiyowa Inna, Ummi ta mike tana fadin "Barka da zuwa Inna!" Aliyu da ya gama ya mike ya shige dakin sa. Inna ta bishi da kallo tace "Yaron nan ya nuna min iko akan yarinyar nan yanzu dan Allah abinda yai min dazu ya kyauta." Abbah ya mike yace "Me Aliyun naki yayi?" "A'ah naku dai. Wallahi yaron nan muna tare da uwata yazo ya dauke ta dan na bata abinci ni fa tsurfar sa na damuna ace mutu ba zai ci abincin gargajiya ba sai na zamani rayuwa ta tafi a haka kuwa. Yana yaro dai kato dashi amman yanzu rashin cin abinci da tsurfa duk tasa ya kare." "Kiyi hakuri Inna." "Wai me yasa baku da aiki sai nayi hakuri karfin ku Aliyun yafi da zai abu baza ana masa fada ba." "Kiyi hakuri Inna za ai masa." Ummi ta fada. Inna tace "To Allah yasa." Ta nufi Maryam da ta jingina da kujera tana fadin "Sannu Uwata ya jikin?" Dagowa tayi ta sakar mata murmushi tai alamar da sauki. Inna ta mika mata cup din kunun da tayo mata tace "Maza sha abin ki kan wancan bokan turan ya fito ya hanaki sha bana son ki kwan da yunwa sam!" Amsa tayi ta kafa kai kadan ta sha ta ajiye cup din dan bata so tasha yadda zai saka ta amai. Inna tace "Yai dadi ko?" Kai ta gyada. Inna tace "Ai nasan zai miki dadi." Ta mike tace "Bari naje na kwanta sai da safe ko?" "Allah bamu alheri Ummi da Abba suka fada." Abbah ya bita suka fita. Suna fita Aliyu ya fito yana bata fuska. Ummi tace "Zo nan!" Aliyu ya karasa tace "Bana so daga yau ka kara hanata cin abun Inna naga ba wani cin abincin take ba bare ace zai mata illa da ace bata ci ba ai gwara taci ko yaya ne ko? Kana gani anan baci take ba na Innan take dan tabawa kadan fa." "To shikenan Ummi ba zan sake ba." "Allah maka albarka." "Amin ya hayyu ya qayyum tasha maganin ta taje ta kwanta ko?" Da kan sa ya bata sannan ya nufi dakin sa. * Washe gari tare suka je asibiti dan Ummi ta tafi aiki dan haka tana kwance yana mata karin ruwa ya gama abinda zai yi karfe biyu bayan ya dawo daga masallaci suka koma gida lokacin Ummi ta dawo dan ranar da wuri ta dawo. A falo suka zauna gaba dayan su. Karfe 5:15pm suna zaune Mami ta shigo dakin da sallama. Suka amsa ta karaso tana kallon Maryam. Mikewa Ummi tayi tana fadin "Sannu da zuwa!" Samun waje tayi ta zauna sannan ta kalli Aliyu dake daddana waya. gaisawa sukai da Ummi sannan Aliyu ya dago yai mata barka da gida. Ta amsa Maryam ta gaisheta da hannu ta amsa tana fadin "Ya jikin?" "Jiki da sauki!" Tai nuni da hannun ta. Ummi ta kalli Maryam tace "Wannan sunan ta Mami ita Yaya tace kuma mahaifiyar Aliyu mata ga Yayan miji na kin gane?" Kai ta gyada tana murmushi. Mami tace "Ya jikin nata dai?" "To da sauki zamuce amman fa ba abinda take ci, ko taci zata amayar ne." "Ikon Allah irin cikin Maryam kenan. Irin wannan cikin wahala ne dashi wallahi Allah ya raba lafiya dai amman kinyiwa Inna magana a samar mata na hausa kuwa?" " 'Dan naki zai yadda ne?" Mikewa yayi ya kara waya a kunne ya fice. Da kallo suka bishi sannan Ummi tace "Kisan sa sam bai yadda da traditional things din nan. Kina gani common dan abu Inna ke kawo mata amman sai yayi ta kwakwafi ya ga abun is nutritive in na fada ma sai ya fara cewa is not first class kaza da kaza, kinsan likitocin nan sam basu yadda da gargajiya ba su dai komai nasu ne mai kyau." "Ai fa nasan za ai haka kin manta Maryam dauke ta yayi suka bar kasar amman kuma da Allah yayi ba rabon yaron da ita suyi rayuwa gaba ba gashi mun rasa su ba kinga kuwa dole ya saka ido sosai akan ta dan kar abun da ya faru baya ya sake faruwa." "Haka ne Allah ya raba lafiya!" "Amin. Abbi na son ya shigo yaganta but late yake dawowa ya fita da wuri amman yace na duba ta Allah bata lafiya." "Amin Yaya!" Ta mike tace "Ni zan koma sai da safe!" Mikewa Ummi tayi tabi bayan ta. Lokacin dan har bacci ya dauke Maryam. A bakin kofa suka samu Aliyu yana jin motsin su ya kara waya a kunne. Ummi ta karasa tace "You better stop this pretending!" Kai yayi kasa dashi ya nufi kofa ya shige da sauri, Dariya Ummi da Mami sukai. Sannan suka cigaba da tafiya suna tattaunawa akan aiki daga baya suka dawo maganar Maryam. A bakin gate din Mami suka tsaya suna cigaba da hirar. Suna tsaye motar Hajiya Mama ta shigo aka shige akai parking sai da ta jima a cikin mota tana kallon su sannan ta fito fuska a hade. Zata shige ciki. Ummi tace "Sannu da zuwa Hajiya Barira!" Ko kallon ta batai ba ta shige. Mami tace "Ai maganin ki!" "Yaya ni ba zan iya gaba da ita bayan babu kyau." "To ai sai kiyi tayi." Ummi tai murmushi tace "Bari na wuce sai anjima!" "To sai anjima!" Mami ta fada tai ciki Ummi ta nufi sashen ta. ** Washe gari Ummi a gida ta zauna da Maryam dan yau da amai ta tashi zuciyar ta tai ta tashi da Aliyu yai mata allura ya dan lafa bayan ya tafi aiki kuma sai abun ya kara gaba ga ciwon ciki ga kirjin ta da take ta kuka dashi. Wannan yasa ba shiri Ummi ta dauke ta suka nufi asibiti. Yana zaune a office yana tunanin ko a wane hali Maryam take ko ya jikin nata. Wayar sa ta hau kara dauka yai ya duba yaga Ummi ce take kiran sa. Dauka yayi yace "Ummi ba dai jikin nata bane." "Gamu nan karasowa asibiti!" "Sai kun karaso!" Ya fada ya mike yafita ya fara zagaye parking space yafi minti ashirin a wajen duk motar da zata shigo sai ya kalla dan yadda ya kafe bakin gate din da kallo. Yana tsaye motar Ummi ta karaso da tai parking ya karasa ya bude baya inda Maryam ke kwance dafe da kirji tana juyi. Ummi ta fito ta zagayo ta kamata wasu nurse biyu suka karaso da kujerar tura mara lafiya aka daura ta akai office din Aliyu suka nufa gaba dayan su. Kan suje har wasu likitoci sun shiga suna jiran su suna zuwa aka rufa akan ta. Allura sukai mata ta samun relief sannan suka farai dubata. Aliyu na tsaye ya kasa komai dan sam ya rasa me zai sun dauki kusan rabin awa kowa ya tafi yin gwaje gwajen da zasuyi da Maryam. Ummi da Aliyu na zaune duk sun kasa magana. Sai bayan wajen awa daya suka dawo da ita aka kwantar. Doctor Hauwa ce ta pkaraso tana fadin "Doctor gaskiya jikin ta ba kwari Sam rashin cin abincin ta yana neman illata ta da babyn cikin ta ga ulcer da take da ita. Daga ita har babyn are suffering!" Ta mika masa result din ya amsa yana kalla, Doctor Lukman ne ya shigo da file a hannu ya samu waje ya zauna Yana fadin "Doctor Ina yan uwan ta yarinya nan she is in danger fa, abun yai yawa ga ciki, ga hawan jini, ga ciwon zuciya sannan babban illa ne ga mai ciki fa..." Ya fada cikin damuwa da halin da Maryam take ciki. Kai Aliyu ya dafe ya amshi file din yace "Thank you all doctor Allah saka. Zan dau hutu na yau insha Allah zan kula da komai, komai zai zo da sauki." "Allah Kara sauki!" Suka juya suka fita. Ummi ta mike ta koma gaban gadon da Maryam take bacci, Ummi tace "Son ina tsaro kar mu rasa yarinyar nan ba tare da taga iyayen ta ba." Wani kwarin gwiwa yaji duk da zuciyar sa na karyewa shima wani lokacin a hankali ya mike ya karasa gaban Ummi ya kamo hannun ta yace "Kada ki karaya Ummi na. Ki cigaba da addu'a zan tayaki da kula da ita sai yadda karfi na ya kare insha Allahu zata tashi da kafafun ta da bakin ta zata koma gida cikin aminci da izinin Allah." Hannun sa ta matse a nata tace "Allah ya yadda ya bamu sa'a!" Ta fada hawaye na zubo mata. Ya saka hannu ya goge mata ido sannan ya ja mata kujera ya zaunar da ita yace "Bari naje na amso magungunan da suka dace sai nazo mu tafi gida ko?" "Ok!" Ya fita. Ta kamo hannun Maryam tana kallon ta hawaye na zubo mata na tausayin ta. Yarinyar ta kuma ramewa gaskiya tana wahala. Hannu ta daura akan ta tana shafawa a haka Aliyu ya dawo ya same su. Ya karasa yace "Bata tashi ba?" "Eh!" "Mu bari ta tashi sai mu tafi ko?" "Eh!" Ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su. A haka aka kira sallah ya tafi masallaci Ummi tayi anan. Yana dawo ya samu Maryam zaune akan sallaya. Zama yayi yace "Ummi ta tashi kenan?" "Eh har tayi sallah!" "Zamu iya tafiya?" Kai ta gyada ta mike ta kama Maryam ta zaunar akan kujera sannan ta ninke sallaya. Ta kama hannun ta suka fita Aliyu na binsu a baya. A haka suka karasa parking space ya amshi key din motar Ummi ya bawa messenger sa akan ya kawo masa gida ya shiga tasa su Ummi a baya suka tafi gida. A main parking space yai parking ya fito ya zagayo wajen su Ummi ya bude musu kofa. Ummi ta fito rike da maryam. Dai dai fitowar Hajiya Mama daga gate din su kenan. Kallon su ta tsaya har Ummi tai gaba Aliyu ya mara musu baya da ledar magani. "Wacece wannan kuma?" Ta fada tana kankance ido ta ina zata san su waye wannan. Ciki ta koma da sauri ta dauki waya ta fara kiran Farouk. Yana dauka tace "Kana ina?" "Mama ina hanya akwai abinda kike bukata ne?" "Da ka dawo kazo kaji ko?" "To Mama." Ya kashe wayar yana fadin "Allah yasa lafiya dai!" Da sauri ya shigo gidan ya nufi sashen su. Dakin Mama ya nufa ya same ta tsaye a bakin kofa tana safa da marwa da sauri ya karasa yana fadin "Lafiya dai ko Mama?" Juyowa tayi ta zauna akan kujera sannan ta kalle shi tace "Zauna mana!" Zama yayi ya zuba mata ido, tace "Wata yarinya ce a gidan nan?" "Gidan nan kuma Mama? yarinya kuma?" "Eh a sashen Aisha take!" Shiru yayi yana nazari. Mama tace "Naga kamar bata da lafiya!" "Ohhh wata yarinya ce!" Ya fada yana ya mutsa fuska. "Yar wajen wacece?" "Mama gaskiya ban san ta ba duk yayan su Anty Umma na san su amman wannan ban san daga ina take ba." "Ina son na san wacece ka tambayar min Aliyu!" "Wanne Aliyu Mama? Kinsan Hamma ba magana yake so ba bare nai masa magana ya ban amsa wallahi ba zai fadan wacece ba." "To ya za ai ina son nasan wacece?" "Amman Mama saboda me? Ina ruwan ki dasu?" "Ban sani ba." Kai yai kasa dashi. Tace "Tashi kaje ina son ka samon wacece yarinyar nan ko a wajen Innar kuce!" Mikewa yayi ya mike ya fita. Ya nufi sashen inna yana fadin "To ita Mama dan Allah ina ruwan ta da su bayan ba shiga harkar su take ba." Inna na zaune tana cin gashin naman da tayi Farouk ya shigo da sallama. Dagowa tayi ta amsa tana fadin "Umaru har ka dawo kenan!" Zama yayi yace "Eh ya gidan?" "Lafiya ni kuwa su Aisha sun dawo daga asibitin ka kira min su dan Allah muji ya me jikin?" "To Inna amman wai wacece yarinyar nan?" Gyara zama tayi tace "Aisha ce ta samo ta kasan Aisha da tausayi fa." "Bangane ba Inna!" "Kai fa haka kake da tambaya kamar dan jarida in kai shiru ma ai zan fada maka kasani. Ba ranan Aisha da Shehu sunje Bauchi ba?" Kai ya gyada yace "Eh yafi sati nawa da dawowar tasu ma." "Yauwah to acan suka same ta." "Kamar yaya kenan wai Inna?" "Suna cikin tafiya suka kade ta daga nan shine fa ta suma to da tafarka kuma ba lafiya haka sukai jinyar ta na kwanaki wanda a jinyar suka gane ta samu matsala ta manta iyayen ta da komai. Abun dai kamar aljanu kamar asiri ga ciki mutum biyu take iya kira daga mijin sai mahaifiyar ta. To fa shine suka taho da ita Aisha ke dawainiyya da ita yarinyar kirki mai hankali da nutsuwa. To kaji Aliyu ke ta dawiniyya da ita. Yau dai jikin yaki yi tin safe take amai wannan yasa Aishan suka tafi asibiti har yanzu ban sani ba ko sun dawo." Baki Farouk ya tabe, ya zaro waya ya fara dadananawa. Wayar ta Inna ta miko masa tace "Ni dai nasan wayata da kudi bare ka wulakantani nace ka kira min Aisha kaki, danno min a wayata." "Nifa bance ba zan kira ba!" Fara neman layin Ummi yayi lokacin tana zaune Aliyu na sakawa Maryam ruwa. Wayar ta ce tayi kara Aiyu ya miko mata ta amsa ta kai kunnen ta. Inna ya mikawa, Inna ta rafka sallama Ummi ta amsa tana fadin "Inna barka da rana!" "Yauwah Aisha ya jikin Maryam din?" "Inna da sauki mun dawo ma yanzu." "To madallah bari nazo naga jikin!" Tashi tayi ta mikawa Farouk wayar dan ya kashe mata tare da fadin "Tashi muje mu duba ta?" "Inna muje kuma? Kije dai!" Wani kallo tai masa sannan ta mike tace "Sai kaje wallahi ka duba ta kila baka tabai mata sannu ba." Ta yafa mayafi ta kalle shi tace "Tashi muje!" *Allah ya jikan mu, ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.* *Antty* *Antty*[11/20, 12:32] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 46 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ya mike ya fita tabi bayan sa tare da rufe dakin ta da key. Bangaren Ummi suka nufa ba kowa a falo wannan yasa Inna ta nufi sama tana fadin "Suna sama kenan. Ni benen nan sam bana son sa ciwon kafa kawai zai saka mutane mu da bamuyi rayuwa dashi ba yaya bare ku da baku da abin yi sai gini da bene kamar tsuntsaye." "Ke inna kin fiya mita wallahi ina ruwan ki to ai ba bangaren ki akayiwa benen ba." Lokacin suka karaso bakin kofar ta tura kofar tare da sallama. Aliyu dake zaune ya mike ya nufi kofa, Inna na shigowa ya fice Farouk ya sama bakin kofa ya shige sa ya sauka, da kallo ya bisa. Inna tace "Kana ina Umaru?" Ya shigo dakin yana ya mutsa fuska, Inna ta zauna gefen Maryam, tan fadin "Sannu ya jikin?" Da hannu tai alama da sauki. Inna ta juyo ta kalli Farouk ya hade fuska yace "Ya jikin?" Bai jira ta basa amsa ba ya juya ya fita. Inna tace "Ja'iri yazo ya cikani da tambaya akan ta dan me ba zan ce yazo ya duba ta ba shi ko tausayin ta ma bai ji?" Ummi tace "Kinsan Farouk ai kyankyami gare sa." "Mene abun kyankyami a gun Maryam?" "Amai yaji tanayi kinsan sa ai!" "Oh ni yasu aman ma sai kyankyami menene a cikin sa. Allah ya kyauta to." Inna ta kalli Maryam tace "Kinga har tai bacci Allah sarki me taci?" "Ba abinda taci!" Mikewa Inna tayi tace "Bari naje na samar mata abu kan ta tashi." "To Inna muna godiya!" Ta fita, a falo ta samu Aliyu zai fita tace "Wai me kake gani game da jikin yarinyar nan ni dai da zaka bi tatawa da an gwada na hausa." "Dan Allah Inna kiyi hakuri kar kice zaki ta bata abubuwa ki barta haka nima ina kula da ita kuma naga abun nan ciki ne in lokacin karshen wahalar yai ai zai wuce amman gamje gamjen nan duk bai da amfani sai yazo ya haifar mata da wata matsala kuma." "Hmm ai shikenan amman da haka uwar ka har ta haife ka shin me ita ya same ta, a lokacin wallahi ba asibitin da muke zuwa duk yadda Suleimanu yaso na hana kuma ya hanu sai ni ke bata na gida kuma da ta tashi haifar ka duk gidan nan ba yaro kato mai lafiya kamar ka amman wai kai ke kushe maganin gargajiya anya kuwa Ali, wai kai bokan turai wannan sun sauya kane kawai." Bai tanka mata ba har ta gama ta fita ya koma ciki ya zauna a falo yana danna waya. Sitti ya gani akan allon wayar tana kira dan murmushi ya saki ya kai wayar kunnen sa yana fadin "Matata!" "Hmm Ali kenan ya gidan ya aiki?" "Ina yini Sitti?" Ya dai dai ta magana cikin girmamawa. "Alhamdulillah ya gida da aiki?" "Alhamdulillah!* "ya mai jikin?" "Da sauki Sitti but wallahi Sitti tana wahala sosai ba abinda take ci fa." "Ya kuke barin ta haka ina Hajiya Hauwa ita ba zata dan mata wani abu da zataji dadin ci ba." "Haba Sitti, me Inna zata iya zata bata abinda zai cutar da ita ne tana girka komai ta bata bayan yarinyar tana bukatar abun gina jiki ne amman ita tana bata traditional thing wanda ba abinda zai kara mata." "Ai nasan za a rina Ali. Nasan zaka aikata haka amman banda abin ka mu a da din aka ce maka cimar mu bata kara lpy a jiki ne? Ku kuke ganin bama hada abun da zai gina mana jiki amman wa ya kai mu cin abun da zai gina mana jiki. Kaga mu bama rabuwa da kayan lambu wanda kai kan ka ko a likitan can kasan yana daya daga abinda aka fi so muci sosai. Duk abinda zamuyi sai mun saka wake ko yar gyada a ciki banda nama da kifi to me kuma za a fada mana in har kana so yarinyar nan tana samun abinda zataci ka lallaba Inna tasan me zata bawa masu irin matsalar ta kaji ko?" "Sitti....." "Kai shiru kawai kaje. Shin da ta zauna babu mai gina jikin babu mara gina jikin ba gwara ko yaya ne ta samu taci ko ba zai amfaneta da komai ba rashin cin abinci matsala ne shi kadai zai iya jefa mutum a halaka bare ga ciki ga ciwo dan Allah Aliyu ka bari ana bata wani abu nasan halin ka." "Shikenan Sitti." "Yauwah Allah maka albarka ai da ina nan waje na za a kawon ita, kai yanzu ma ko zaka kawon ita!" "Zan duba in gani Sitti!" "To shikenan!" "Ya jikin?" "Nifa yanzu ba abinda ke damu na." "Masha Allah Allah kara sauki." "Amin Allah yayi albarka." "Amin Sitti sai anjima." "To kada ka manta fa." "Insha Allahu!" Suka kashe wayar jingina kai yayi da jikin kujera tare da lumshe ido. 2012 ```Ba abinda ya fado masa sai Maryam matar sa lokacin da tana da ciki. Farkon cikin ta da wani matsanan cin ciwon kai ta fara wanda sam bata fada masa ba dan Maryam akwai dauriya duk dawainiyyar sa bata daina ba ta yadda ya gane tana da ciki in ta gama girki kauri gas sai yasa tai ta amai amman a haka take masa komai. Wannan yasa ya dauki jinin ta awon farko ya nuna tana da ciki murna gun Aliyu ba a cewa komai haka su Ummi sai dai tin daga lokacin lafiya tai kaura daga Maryam dan sai ta daina cin komai ko ruwa ta sha sai amai wannan yasa ya mai da ita gida wajen Ummi suka kula da ita ba karamin damuwa Aliyu yai akan cikin Maryam dan shi kan sa daina cin abinci yayi dan sam ba zai iya ci Maryam bata ci ba. A haka Inna ta fara mata dure duren abincin ta wanda wani da tayi cokali biyu zata dawo dashi amman sam Inna bata daina duk da bata so amman in Inna ta kawo amsa take ta ci ko da zata dawo dashi. Kwana suke basu bacci ba saboda zazzabi wani lokacin ciwon ciki duk magungunan da zai bata ba sauki. Ummi tace "Aliyu ka kwantar da hankali kila in cikin yai kwari zata samu rangwami!" Aliyu kan ce "Ummi har yaushe wata uku zuwa hudu muna fama da abu daya." Inna ta shigo da kwano a hannu tana fadin "Haka fa kowa yai fama ba akan ku aka fara ba da zaka na tada wa mutane hankali." Maryam dake zaune ta mikewa kwanon ta amshi maza kici zakiji dadin bakin ki. Amsa tayi amman kasan ranta bata so dan bakin ta sam ba dadi kuma tasan da taci zata dawo dashi amman a haka ta amsa ta fara ci tana ya mutsa fuska Aliyu kuwa kamar yai me dan Ummi ta hana sa ne amman da ba abinda zai bari taci mikewa yayi ya fice a fusace. Inna tace "Ana musu gata basa gani dan kan uba gaba yazo yana godiya ai." Ummi tai murmushi Maryam ta mike da sauri ta nufi bandaki Ummi tabi bayan ta yana falo yaji kakarin ta da sauri ya shigo kamar zai kuka yace "Kinga ko Ummi tana zaman zaman ta an janyo mata amai." Ya kamo Maryam suka fito suka sauka zuwa dakin sa. Inna ta girgiza kai tace "Ni ba muguwa ba ce ai in abinda kake tunani kenan." Irin wannan yasa ya dauke matar sa suka bar kasar gaba daya. A can shi ya dinga kula da ita kullum sai karin ruwa a haka cikin yai wata biyar wanda daga nan ta samu sauki sai kuma kwadayi da ciye ciye cikin lokaci kan ta sauya tamkar batai laulayi ba tayi kyau tai kiba ga cikin da ya dan fito yai mata kyau. Wacce kulawa ce Aliyu bai bata ba komai take so shi yake mata ya daura rai akan cikin nan in ya zauna yana hira da cikin kamar me hira da mutum. Cikin watan ta tara su Ummi suka matsa ya dawo ba yadda ya iya haka suka koma lokacin cikin ta ya kara girma kamar zai fado kasa. Da suka koma kowa yai murna ganin su da jin dadi yadda Maryam ta warke a haka suka cigaba da rayuwa wanda satin su biyu da dawowa da safe nakuda ta taso mata Aliyu na bacci ya jiyo numfashin ta a bandaki da sauri ya shiga ganin halin da take ya kira farouk bai sanar da kowa ba suka tafi asibiti sai da sukaje ya kira ya fadawa gida ai kan kace me aibiti ya cika da yan gida, Maryam ta sha wahala dan tin safe har rana tana fama kai abu kamar wasa har dare wajen bakwai sauran likitocin suka samu Aliyu akan ya kamata ai mata CS dan karfin ta ya fara daukewa yaron ma ya daina motsin dan ya galabaita shi ya daina turo kan nasa da yake hankalin Aliyu ya tashi nan da nan yasa hannu kan a shiga da ita ya nufi dakin da take. Kwance ya same ta idon ta a lunshe ya karasa ya kamo hannun ta da sauri ta bude ido tana ganin sa ta bude baki a hankali tace "Yaa Haidar...." "Na'am Habibty sannu Habibty!" Ya daura hannun sa akan ta. Ido ta lumshe tace "Yaa Haidar ba zan haihu ba, Yaa Haidar ba zan cika maka burin ba, Yaa Haidar naso na zama sirrin ka ta har abada, na so na cika maka buri na haifa maka ya'ya masu yawa amman Yaa Haidar ba zan iya ba." "Zaki iya Habibty zaki iya kice zaki iya kinji!" Kai ta girgiza tana fadin "Yaa Haidar Ciki na!" Da sauki ya mike yana tofa mata addu'a a cikin, ido ta lumshe ta kamo hannun sa tana fadin "Nasan tafiya zanyi Yaa Haidar ba zan iya ba. Kan na tafi zan gode maka abisa yadda ka kyautata min da yan uwan mu, ina son ka Yaa Haidar amman ba yadda zan haka zan tafi na barka. Dan Allah Yaa Haidar kar ka taba mantawa dani kana sani a addu'a kaga ban bar baya ba kai kadai gareni sai iyaye na. Kaji Yaa Haidar!" "Dan Allah ki bar yi min wannan kalaman naki masu kama da wasiya na fada miki zaki haihu mu cigaba da rayuwar mu i know my Baby jaruma ce ko?" Wani murmushi tayi, tace "Ka yafe min Yaa Haidar! Ka yafen!" "Baki min komai ba Habibty i forgive you!" "Thank you my soul mate, thank you my love, i love you, i will miss you, Allah sadamu a aljanna." Kiss ya kaiwa goshin ta yace "Za a shiga dake aiki Baby a ciro mana nasan Matata jaruma ce. *Matar Haidar* jaruma ce ko?" Murmushi kawai tayi yace "Say yes!" "Yaa Haidar jarumi nah!" Ta fada tana lumshe ido sai kuma ta bude a hankali tana kallon sa ba ko kitawa, nurses ne suka shigo da likitoci za a tafi da ita ya mike ta kamo hannun sa sai kuma ta dafe cikin ta da dayan hannun yadda yaji rikon da tai masa yasa ya gane azabar ciwo ne, likito ne suka yo kan ta nan sukaga yadda dan ke son fitowa, amman ba karfi a jikin uwar da babyn fara taimaka mata sukai sai ta fara salati hannun ta rike da na Aliyu jin tana salati yasa ya durkuso kan ta yana mai yi tana amsa a hankali yaji tai shiru sannan ta saki hannun sa da sauri ya dago yana fadin "Habibtyyy...." Wannan yasa hankalin sauran likitocin dawowa kan su, zata sukai numfashin ta ne ya dauke dan haka suka fara dubawa wasu na son mata connecting oxygen. Dayan doctor dake duba tane yace "Ta mutu fa!" Da sauri Aliyu ya karaso yana fadin "A'ah Doctor Abbas bata mutu ba duba dai!" Ya karaso yana kama hannun ta dan dubawa, Doctor Khaleel ya karaso yana fadin "Bari na duba doctor!" Doctor Fateema dake gefe ta karaso tana saka hannu a bayan kunnen Maryam Doctor Khaleel kuma rike da hannun ta. Ajiye hannun yai Dr Fateema ta girgiza kai. Dr Abbas yace "Am sorry Dr Aliyu but she...." Bai karasa ji ba ya zube a wajen da sauri suka dauke shi suka fice a dakin da shi wanda yan uwa hankali ya tashi sunga an fita da Aliyu kamar gawa. Da kyar ya farfado yana farfadowa ya mike yana fadin "Ina Matata?" Ya dire kafa. Dr Abbas yace "Ka tsaya Aliyu!" Bai saurare shi ba ya fita yabi bayan sa a lokacin har an fito da Maryam za a tafi da ita gida. Abbah ne ya kamo hannun sa suka fita. Aliyu yace "Abba bata fa mutu ba." "Na sani Aliyu muje gida kawai." Kamar mara laka haka ya bisu a baya suka fita a wajen. Da sukaje Abbi ne ya rarashe shi da nuni akan ta mutu fa a lokacin aka suturtata aka kira Aliyu da mahaifin ta. Dakin suka shiga mahaifin na rike da hannun Aliyu. A gaban gawar ya zauna ya kura mata ido ga cikin ta nan kato a jikin ta. Karasawa yai a hankali ya yaye mata fuska. Fuskar nan shar da ita kamar zakai magana ta amsa da sauri ya rufe fuskar yana fadin "Inna lillahi wainna illahir raiun. Allah ya jikin ki ya amshi shahadar ki na yafe miki Maryam Allah yasaki a aljanna firdausi nayi rashin mata mai so na." Da kyar aka lallashe shi lokacin da yaga an daga ta za a fita da ita kuwa a lokacin Hankalin Aliyu ya tashi sosai dan gani yake a lokacin kamar mafarki yake so yake ya farka kawai. Abbi ya kamo sa suka fita a mota suka je makabarta inda har an haka kabari, aka ajiye Maryam a bakin kabarin Abbi yace "Aliyu kamo kan!" Kallon Abbi yai. Abbi ya gyada masa kai karasawa yai a hankali ya dago kan da bismillah mahaifin ta ya kamo kafafu suka saka ta wanda aka fara rufe ta ganin da gaske ya rabu da matar sa yasa ya fada jikin Abbi daga nan kuma bai sake sanin me ya faru ba.``` * * * * * Kiran sallah magariba shi ya katse masa tunanin da yake a hankali Aliyu ya bude idon sa da yai jajir dashi. Ummi ce ta sauko suka hada ido da sauri ta karaso tana fadin "Lafiya Son?" Mikewa yayi murya a shake bata fita sosai yace "Ba komai Ummi!" Ya nufi daki yai alwala ya fito ya tafi masallaci. Acan akai sallah bai tashi ba sai addu'a da yakewa Maryam bai fito ba har kai ishai yana masjid din sai wajen tara ya fito yana tafiya a hankali ya shigo gida. Ba kowa a falo dan haka yai dakin sa. Kwanciyya yai akan kujera yana pressing counter dinsa. Ummi jin shiru har goma ba Aliyu yasa ta fito lekawa tai ta window taga ga motar sa dakin sa ta nufa a kan kujera ta same shi kwance karasawa tai ta dafa shi sai a lokacin ya san da mutum a dakin. Mikewa zaune yayi ta kalle shi tace "Me yake damun ka?" "Ummi am missing my wife, i can't stop recalling Maryam. Maryam is such a good and kind lady she loves me, she give me all i want, she always want to see my smile my happiness how should i forget her Ummi.... Nasani zakice naki daukar takwalli Ummi in dai zan tina Maryam to zuciya ta na raunana ina ma ni na mutu ita ke raye." *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe, Allah ya jikanmu. Amin* *Antty* [ [11/21, 10:19] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 48 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Kano A haka suka cigaba da neman Maryam ba dare ba rana, Alkasim kuwa saboda Maryam ya dinga tafiye tafiyen gari gari duk inda yaje yake bada cigiya ko zai samu wanda zai ga Maryam. Wani aiki da ya kai shi Bauchi ranar da ya gama zai dawo kamar da wasa duk inda ya tsaya sai ga nuna picture din Maryam ko akwai wanda Allah zai sa ya ganta, a lokacin ya tsaya a wajen wani mai siyar da lemo a hanya bayan sun gaisa ya nuna masa picture din Maryam, kallon hoton mutumin yai, sai ya shiga shago da sauri ya dauko wata jaka ya mika masa, a zabure Alkasim ya amsa dan ba zai manta ba tare suka siyo jakar, sunje shopping zata makaranta taga jakar tace lallai sai ya siya mata, dan haka yana amsa ya hau budewa yana fadin "Ina Maryam din a ina take?" Kai mutumin ya girgiza yace "Yau kusan wata biyu kenan, da na tsinci jakar nan, anan saboda akwai wata rana wata yarinya tazo tsallaka titi wanda anan wasu suka zo suka kusan kade ta, to bamu sani ba dai tana da rai ko bata da rai suka tafi suka bar ta, sai bayan sun bar wajen naga jakar shine na dauka na ajiye, to kaji a inda na samu jakar." Wata rumguma Alkasim yayiwa jakar hawaye na zubo fuskar sa yace "Ina suka yi?" Hanya ya nuna masa yace "Amman kila asibiti suka kai ta." Daga nan ya shiga bin asibitoci wanda a ranar bai koma gida ba sai da ya dada sati akan neman Maryam amman ba Maryam sama ko kasa. Hankalin sa ya tashi domin kuwa yaga samu yaga rashi, a haka ya koma gida cike da damuwa. **** Zaune yake cike da damuwa a dakin sa, wayar sa ce tayi kara kamar ba zai duba ba, dan rabon sa da waya tin mutuwar Haidar, tin lokacin komai ya fita a ransa sannan ga rashin kanwar sa, mostly ma wayar a kashe take, in bai kashe ba kuwa tana flight mood, janyo wayar yayi yana kallon da sauri ya mike yana kai wayar kunnen sa, wani kuka yaji yana son ya taso masa yace "Ahmad." "Ba wani Ahmad ku me yake damun ku ne, daga aure duk kun kashe waya, kai sai kace kai ne kayi aure, na shiga damuwa na rashin samun ku a waya amman nasan wancan dadin aure yasa ya manta dani ya kashe waya....." Sheshekar kukan da yaji ne yasa yai sauri dauke wayar a kunnen sa ganin wayar nayi yai sauri ya mayar kunnen sa yana fadin "Alkasim meyake faruwa?" "Ahmad mun rasa Haidar, Haidar ya tafi ya barmu." Cike da razani Ahmad ya dago yana fadin "What? Me kake nufi? Ina ya tafi ya barmu?" Kai ya hau girgiza yana fadin "Haidar has died for more than three month." Wani duhu-duhu Ahmad ya fara gani da kyar ya iya cewa "kai karya ne Wallahi. Haidar din? Haidar aminina fa, a'ah dan Allah kada kai min wannan wasan Alkasim." Alkasim yasan za'a rina. Ahmad da Haidar abokai ne tin yarinta sannan suka kara karatu tare matsala daya ba a gari daya suke ba sai kuma da ya samu aiki ya bar kasar amman Ahmad shine aminin sa a ta dalilin haka ya zama abokin Alkasim, dan a da ma haka kawai zai zo yai kwanaki a Kano, a garin su Ahmad Aliyu yai service dan a gidan su ma ya zauna. Cikin nutsuwa ya labartawa Ahmad abinda ya faru. Tamkar karamin yaro haka Ahmad ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace "Innalillahi wainn illahir rajiun!" Abinda ya fada kenan wayar hannun sa ta subuce ta fadi, komawa yayi ya zauna hawaye na bin fuskar sa, Alkasim ma na gefe yana kuka, dan kiran Ahmad ya dawo masa da komai baya. Shi kadai yai jinyar rashin abokin nasa, yana gamawa ya tashi ya fara shirye shiryen barin kasar dan ji yayi ba zai iya kara zama a garin ba. Ranar da zai sauka ya sanar da Alkasim shi yaje ya dauko shi, a airport da suka hadu suka rumgume juna suna kukan rashin Haidar wanda sai ka zata a lokacin akai rasuwar, daga nan gida suka wuce, wajen Mami suka fara nan suka zauna a gaban ta suna ta kuka, da kyar Mami ta lallashe su, daga nan dakin Haidar suka je nan ma kuka suka ci sannan suka tafi gidan su Alkasim. Wajen Ammi suka je ya gaishe ta yai musu ta'aziyya, bayan sun koma daki ya kalli Alkasim yace "Ni kuwa ina Maryam? Wane hali take ciki? Na tabbata rashin Haidar ba karamin barazana yai ga rayuwar ta bane." Hawayen dake idon Alkasim ne ya zubo yace "Tabbas domin a rashin Haidar muka kusa rasa ta itama, a halin da ake yanzu Maryam bata magana saboda shock din da ta shiga na rashin Haidar." "Ni na sani, tana ina?" Kuka Alkasim ya fashe dashi yace "Maryam bata gidan nan." "Tana ina?" "Bayan rasuwar Haidar, Maryam tayi jinya na kusan wata wanda duk muke zaton alhini ne sai dai ashe abu biyu ne bayan alhini sai muka gane Maryam na da ciki har na wata uku." Da sauri Ahmad ya dago yana fadin "Da gaske?" Cike da murna yai tambayar kallon sa Alkasim ya tsaya yace "Kasan me nace kuwa?" "Naji kace Maryam tana da ciki, kai Alhamdulillah burin Haidar kenan, amman naji masa dadi ya bar baya mai kyau, Allah ya jikan sa ya raya abinda zata haifa Allah ya bamu ikon kula dashi, dan Allah ka tashi ka kaini naga Maryam na kwantar mata da hankali." "Ka gane me nake nufi kuwa?" "Na gane mana Maryam na da cikin Haidar." "To meyasa kake murna bayan kasan ba a daura aure ba ta samu cikin." "Wa ya fada maka?" "Ahmad a ranar daurin auren fa Haidar ya rasu, tayaya kuma zaka ce haka." Ido Ahmad ya lumshe sannan ya bude yana fadin "Yanzu wata shida da auren Maryam da Haidar." "Wanne Haidar din?" "Kaga kaini naga Maryam tukkuna." Fuskar Alkasim ce ta sauya yace "Ahmad a lokacin da Abbi yasan da cikin Maryam yaki amsar cikin ne." "What Ammi da Mami fa?" "Ammi ya zatayi she sent her to our sisters house, Mami bata gari but kasan me?" "No." "Tin ranar bamu sake ganin Maryam ba yau sama da wata biyu kenan." Da sauri Ahmad ya mike yana fadin "Ba a ga Maryam ba to ina ta shiga Innalillahi wainna illahir rajiun." "Abinda bamu sani ba. Amma Malam ya fada mana tana nan kamar an samu wani mugun ya kawar mata da hankali daga gida, tunani hannun wadan da zata fada domin Maryam bata da lafiya, ga ciki, ga rashin magana." "Ba zama zamuyi ba ai Alkasim." "Kasan watan mu nawa muna neman ta? Kasan gari garin da akeje neman ta? Allah ya boye ta a wani wajen muna fatan nan gaba Allah ya bayyana mana ita." "Innalillahi wainna illahir rajiun shi Abbi bai tambaye ta game da cikin ba?" "A lokacin ran Abbi ya baci bai tsaya jin komai ba, yace Haidar ba zai taba aikata zina ba." "Maryam ma haka. Nasan waye Haidar tabbas ba zai taba aikata zina ba dan lokacin da ya samen da matsalar sa cewa nai ya nemi yan mata ya rage zafi amman sam yaki aminta yace gwara ya mutu da haka in ya mutu mai zai cewa Allah, hakika koni Haidar ke min fada akan kula yan mata Haidar yana da tarbiyya da halaiya masu kyau tabbas ba zai aikata zina ba kamar yadda ita Maryam din take ko da abin ya faru da kyar ta yadda ta aminta." "Ka warwaren wannan zargen ko na gane me kake nufi?" Zama yayi yace "Lokacin baya Haidar yazo ya samen akan yana fama da sha'awa wanda ya shasha magani abun bai raguwa dan kai shaida ne har suma yake yi to da ya fadan nace ya samu wata ya rage zafi yaki, ba sau daya ba ba sau biyu ba ya kawon wannan matsalar ta shi wanda a karshe nace ga Maryam nan zai samu nutsuwa yace ba zai taba tunkarar ta da wannan abun ba Maryam matar sa ce, wannan dalilin ma yasa ya fara janyewa Maryam amman ita kuma sai ta fara shiga damuwa idan har yaje ya ganta a makaranta ranar dawowa yake da ciwon ciki mai tsanani. Tinda ya dauke mata kafa, abin ya dame ta................ Haka ya zayyanawa Alkasim komai daga shi har Alkasim kuka suke na abinda ya faru. * Ba karamin tashin hankali Ahmad ya shiga ba domin kuwa ya tausayawa Maryam, take rasuwa Haidar ta saka masa soyayyar Maryam, domin yanzu burin sa ya nemo Maryam ya aure ta ya bata kulawar da Haidar bai samu ya bata a lokacin baya ba, fatan sa yasa tana hannu na gari sannan ta sauka lafiya hakika babyn ta zai samu so da kulawa tamkar baban sa, baban sa mutumin kirki ne ya dauke shi a matsayin amini masoyi, tabbas yayi kewar aminin sa saboda ba shi da tamkar sa shi bashi da mai basa shawara da daura sa akan hanya Haidar ne kawai, sai a yanzu da suka kulle da Alkasim wanda suka kara bazama neman Maryam sosai suka bincike a Bauchi amman duk da ba wani cigaba da aka samu, duk da haka Ahmad da Alkasim basu hakura ba duk wasu garuruwa in suka samu sukaje sai sun bincika. Abuja Washe gari Mama na tsaye a window tana ganin fitar Ummi ta fito ta yo sashen Ummi yau ma a falo ta samu Aliyu sai ta kara tsarguwa ya dauke kai ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar me jiki sannan tayi sama. A kwance akan sallaya ta samu Maryam na jan carbi, dan walha ta idar ta dan kwanta. Mama ta karasa ta zauna a gefen gado tace "Ya jikin?" "Da sauki!" Tai mata nuni. Mama tace "Nazo muki da wani karuwa ne in har kika yadda zan biki 5million nasan zata ishe ki kije kiyi rayuwar ki ba takura da sa ido." Ita fa Maryam tin zuwan matar nan jiya taji bata kwanta mata ba dan haka sai ta tsaya kallon ta kawai. Mama tace "Nasan irin ku da yawa wasu karuwanci ya fito dasu suka samu ciki su rasa mai amsar ciki su zo su makalewa wasu. To abu daya nake so ki min da wannan cikin duk da nasan bai da uba yanzu zan masa uba zan je na fadawa mahaifin yaron nan cewa kin fada min cikin nan na Aliyu ne shi ya hada komai har kuka hadu da Ummi ta kawo ki gidan nan ki nuna musu anan ma neman ki yake in har kikai min haka ko?" Mama ta fada tana murmushi tace "Ni na miki alkawarin baki wajen zama da 5 million kamar yadda na fada miki ya kike gani zaki iya?" Mikewa Marym tayi ta dauko memo da take rubutu ta fara rubutu sannan ta mika mata. Amsa Mama tayi ta fara karantawa. "Ciki na yana da uba ba zan taba sheganta shi ba dan haka ki rabu dani, ni ba abinda ya kawo ni ba fatana na samu na tuno rayuwa ta ta baya na koma wajen iyaye na. Yau ko da ace cikin shege ne ba zan taba lakabawa Aliyu shi ba mutanen da suke kai na dare da rana ke kuwa me Aliyu yai miki kike son saka sa a wannan halin?" "Ban sani ba aiki na kawo miki in zaki min shikenan in ba zaki min ba shikenan arziki ke neman ki kike son guje masa." Rubutu Maryam tayi a paper ta mike mata amsa tayi ta fara karantawa "Dan Allah ki kyale ni naji da abinda yake damu na. Arziki na Allah ne in ina da rabo zanyi shi." Mikewa Mama tayi ta fita a falon sama suka hadu Inna ta hau durkusawa tai ta gaishe ta. Inna tace "A'ah A'ah bana cin mike ai kinsan sashe na wa ya hanaki kizo ki gaishe ni in kina son ki gaishe nin?" Tayi ciki. Mama ta harari bayan ta ta fice. Aliyu ta sama a inda ta barshi ta fice da sauri ya girgiza kai kawai. Kuka Inna ta samu Maryam nayi da sauri ta karasa ta dafa ta tace "Me ya faru dake Uwa ta?" Hawaye ya zubowa Maryam ta girgiza kai. Inna tace "Ko dai waccan matar ce tai miki wani abu?" Nan ma girgiza kai tayi. Inna tace "To me akai miki?" Kai ta girgiza. Inna ta mike ta sauka ta samu Aliyu a kasa tace "To gata can sai kuka take taki ta fada abinda akai mata kaje kai ko zata fada maka." Da sauri ya mike yai sama ya same ta tana ta kuka ya durkusa a gaban ta yace "Menene kike kuka?" Kai ta girgiza yace "Ko wani abu ke miki ciwo?" Nan ma ta girgiza kai yace "Me kike so to?" Nan ma same. Nan yai ta lallashin ta da kyar ta samu tai shiru tana sauke ajiyar zuciya a haka bacci ya dauke ta ya tsaya kallon ta yana tunanin to me Mama tai mata. Mikewa yai ya fita ya nufi sashen su. Ba kowa a falo sashen Mama ya nufa a falo ya same ta zaune ya tsaya a bakin kofa yace "Kada in kara ganin kafar ki a sashen Ummi, sannan ba ruwan ki da yarinyar can in ma wani abu kike bukata da ita tafi karfin ki." Yana fadar haka ya juya ya fita. Mama ta yi kwafa tace "In ban ga bayan ka ba, ba sunana Barira ba." *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya Amin.* *Antty* [11/21, 10:19] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 47 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta janyo shi jikin ta da sauri ya daura kan sa a kafadar ta. Kansa take shafawa tana fadin "Say Alhamdulillah and you should always say it if good or bad things happen Allah will give you the best of best for you." "Alhamdulillah!" Ya furta wanda furtawar da yayi ya sa ya samu saukin abinda yake ji. "Nasan wacece Maryam Aliyu amman in kai hakuri ka amshi kaddarar ka Allah zai sauya maka da mafi alheri. I know a zamanin nan samun mace like Maryam is not a small thing but anything if we say Allah, that Allah will do it for us. Kai ma baka zalunce ta ba so Allah willl not let someone to bullying ur life so be patient Allah is with u!" "I love you Ummi!" "I love you son. Amman kaga da ka amshi Maryam's sister ai da ka dinga kallon copyn ta." "Ummi ba zan iya ba gani zan yi kamar naci amanar Maryam ne, ya zanyi dasu a aljanna ina son na tashi da Maryam a gidan aljanna so gwara na auri wata daban." "Kamar gaske ka samo watan." Kai ya shafa yace "Ummi na kasa, my heart has close and the key is with Maryam how should i open it, i am not the one whose control my heart!" "Aliyu ya kamata ka samu kai settling life dinka girma kake fa Maryam tatafi ba abinda zamuyi mata sai addu'a itama samun nutsuwar ta ta ganka cikin nutsuwa da farin ciki." Kai ya lafe a jikin Ummi. "Tashi muje kaci abinci i left Maryam alone!" Da sauri ya mike yana fadin "Na manta maganin ta." Ya dauko suka fita. Maganin ya bata ta sha sannan suka sauko da Ummi da kyar ya samu yaci abinci ya tashi yaje ya wanka sannan yai alwala sallah ya hau yi yana wa Maryam addu'a. Haka ya kwana kan sallaya sai wajen hudu wani bacci ya dauke shi. * ```Zaune ya hange ta a cikin wani lambu sanye da fararen kaya ta kara haske tana tai masa murmushi karasawa yayi yace " *Matar Haidar* " " *Mijin Maryam* " "Ita kadai!" Fuska ta bata tace "Bana son haka Yaa Haidar wa yace maka ana halittar mutum dan abu daya kawai. Ka daina fadar ni kadai. Allah ya baka ni kuma ya amsa sai ace me? Sai ace ba zaka kara aure ba. A'ah fushi kake da wa da ba zaka kara aure ba please Yaa Haidar in har kana son farin ciki na ka samu kai aure kaji Maryam zatai farin ciki in kuwa ba kai ba zanyi akasin haka. Kalle ka duk ka rame kana saka damuwa a ranka baka cin abinci ni da na tafi menene na damuwa to ina tare da kai ka bar damuwa ko bama tare muna tare a jikin juna. Yaa Haidar ka cire damuwa ka sani kai kaidai nake so. In kai aure baka ci amanar soyayyar mu ba ka raya sunna Allah zai baka lada." Dagowa yai zai magana``` Kiran sallah ne ya tada shi ya fara waige waigen dakin salati yayi tare da addu'a ya nufi bandaki ya kara watsa ruwa ya tafi masallaci. Bai dawo ba sai bakwai ya nufi sashen sa ya kara wanka ya sauya kaya ya fito falon su. Ba kowa sai kamshi dake tashi. Kitchen ya nufa ya samu Ummi na gyara wajen ya karasa yace "Barka da safiyya Ummi nah!" Kansa ta dafa tace "Ba kai bacci ba jiya saboda me?" Idon sa ya shafa yace "Aiki na danyi!" "Uhm uhm fah Haidar!" Yai murmushi yacs "Ummi ya me jiki?" "Da sauki Alhamdulillah!" "Zazzabi fa." "Shima yau da sauki ba zafi sosai." "Allah sauwake!" "Bari naje wajen Inna!" "Agaishe ta kan na shiga!" Ya mike ya fita. Sashen Inna ya nufa tana Kitchen tana ta aikin abinda zata ci ya shiga da sallama. Sam bata ji ba sai da ya kusan minti nawa yana zaune ta fito rike da flask din tea tana ganin sa ta dafe kirji tana fadin "Ni dai gaskiya in za a shigo min ana daga sauti a wani shiga hakki ne tin ban san da mutum yanzu da na yanke jiki na fadi fa saboda tsoro." Bai ko tanka mata ba har ta gama fadan ta ajiye flask din tace "Dadi na da kai ai ta magana ka maida mutum mahaukaci yau miskilancin yafi na ko yaushe kenan, ni dai wallahi yau ka shiga hakki na." Mikewa yayi ya zura hannu a aljihu ya zaro kudi ya ajiye sannan ya wuce ya bar ta tsaye tana ta magana. Sashe su ya nufa a compound ya hadu da Farouk zai je gaida Inna. Ya gaishe dashi sannan ya juya ya tafi. A inda Aliyu ya barta anan Farouk ya same ta tana ta fadan ya zauna yana fadin "Ke kuma Inna haka kike ke kadai ma ki ta magana." "Kada nayi dan uwanka ne ai ko me ma ya sakani magana." "Kai Inna ke kullum baki da aiki sai tsokanar Yaya dan kinga baya tanka miki ne shiyasa." "Na tsokane shin ko zaka rama masa ne kaji mutum ni akwai wanda ya isa ya rabani da Aliyu ne ko uwar sa karya take bare kai yaron da a guna ya tashi kuma dan yayi ba dai dai ba, ba za'ai masa fada ba haka ake duk iyayen ku su suka bata ku bakwa laifi su muku fada." Mikewa yayi yace "Ke kika tarbiyyar dasu a haka ai!" "Au zakace min nima ya'yan nawa basu da tarbiya ko me?" "A'ah fa ni na isa nace mahaifana basu da tarbiyya bayan duk duniya ina ganin babu mai tarbiyya kamata kuma wa ya bamu in basu ba ni dai kada ki hadani da Abbi da Abba dan nasan halin ki sam bakya son zama lafiya." Ya juya ya fita. Inna tace "Wallahi Umaru zaka hadu dani kuma sai Suleimanu yazo ya fada min shi ya baku damar min rashin kunya ko kuwa? Yara kowa sai rashin mutunci shi wancan ana magana ya tanka ma yaki sai kace wani kurma ai wannan shine dukum din, shi kuma wannan sai dan banzan baki kai su Suleiman dai sun iya haihuwa Allah ya shirya musu zuri'a." Yana fita ya nufi parking space ya bude motar sa zai fita kenan wayar sa ta hau kara yana dubawa yaga Mama ce dauka yayi tace "Kana ina tin jiya nake neman ka!" "Gani zan fita!" "To kazo ina son ganin ka!" "Lafiya dai ko?" "Lafiya Ahamdulillah!" Ya kashe motar ya fita ya koma cikin gida. A dakin ta ya same ta ya shiga da sallama ya zauna. "Fita zakai baka zo mun gaisa ba." "Mama gaisawa ta nawa kuma?" "To ba zaka biyoni daki ba ka sani ko akwai ahinda nake bukata sai ka gaishe ni a gaban kowa haka kaga dan uwan ka yanayi ko ya gaishe da uwar sa sai ya bita daki sun kara kuskus." "Kai Mama shima fa ba kullum ba kina gani sai su kwana nawa ma Mami bata ganshi ba" "To naji ya ake ciki maganar yarinyar nan?" "Wacce yarinya?" "Au kama manta wacce nace ka binciko min." "Oh Mama na tuna Ummi ce ta tsince ta a hanyar su ta dawowa yadda na gane shine Yaa Haidar ke kula da lafiyar ta. Dan ciki ne da ita." Nan ya dan mata bayani kadan. Shiru tayi tana nazari can tace "Shikenan tashi kaje!" Ya mike yace "Sai na dawo!" Ya fita. Da sauri ta mike ta nufin sashen Abbi. Yana zaune shi kadai ta zauna tace "Amman dan Alah abinda ake min a gidan nan ana kyauta min kenan?" "Me kuma ya faru Barira?" "Har a kawo yarinya gidan nan tai kwana da kwanaki amman ba za a fadan ba ai ko ba zanje na duba ta na mata sannu bare ina son samun ladan duba ta." "To kiyi hakuri ni kai na har yanzu banga yarinyar ba itama Hauwa sai shekaran jiya ta samu ta ganta kiyi hakuri kije ki duba ta Allah bada lada." "Ah toh shikenan!" Mami ce ta shigo ta zauna Abbi yace "Mita take wai ba a fada mata zuwan Maryam ba." "Ayya tayi hakuri!" Mama ta mike tace "Ai dai ko dan na samu ladan duba mara lafiya a fada min!" "Ba dai nace ki hakuri ba to." Mami ta juya ta kalli Abbi tace "Yau zanje unguwar da na fada maka." "To Allah kiyaye!" Mama ta fita tana murmushin mugun ta sannan tace "Zaku dauko wacce zata tarwatsa muku farin ciki indai aikin ku dauke dauke." Tayi dakin ta. Ummi ce ta fito cikin shirin ta, ta samu Aliyu zaune a falo tace "My Son!" Dagowwa yayi daga kallon system din da yake yace "Ummi na kin fito!" "Na fita son zan tafi Maryam na bacci please ka kular min da ita ba zan dade ba." "Insha Allahu!" Ya mike ya rakata har ta fita sannan ya dawo. Bai jima da dawowa ba yaji sallamar Mama mamaki ya fara me ya kawo Mama bangaren Ummi bayan yasan basa shiri sam Mama bata zuwa sashen Ummi. Tana sako kai ta tsaya tai turus dan bata taba zaton ganin sa ba tayi zaton ya tafi aiki. Cikin borin kunya ta fara in ina tana fadin "Uhmm dama.. dama... daman zuwa nayi na duba yarinyar da aka ce ba lafiya dan kar ace ban zo ba." "Tana sama!" Ya fada ya cigaba da dannan system din sa da sauri tai sama tana hawa ta sauke ajiyar zuciya dakin dake farko ta nufa ta bude a kwance ta samu Maryam amman idon ta biyu mikewa tayi ganin mutum Mama ta karasa ta zauna tana mata murmushi tace "Sannu!" Hannu ta daga tai mata nuni da yauwah. Mama tace "Ya jikin?" Nan ma nuni tai mata. Mama tace "Bakya magana ne?" Kai ta gyada mata. Mama tace "To sannu zuwa nai na duba ki sannan na taimake ki." Shiru Maryam tai tana kallon ta tace "Kin ganni nice kishiyar Babar Aliyu ina fatan zaki ban hadin kai a taimake ki?" Kai Maryam ta gyada. Mama ta mike tace "To sai gobe zan fada miki abinda zaki kinji?" Kai ta gyada Mama ta mike ta fita. Aliyu na a inda ta barshi ta fito tanayi tana waiwaye. Ya bita da kallon gefen ido kawai ya cigaba da aikn sa bayan minti ashirin ya mike ya hau sama dakin da Maryam take ya shiga tana zaune lokacin ya tsaya a bakin kofa yace "Ki sauko kasa!" Yana fada ya juya ya fita. Dining ya nufa ya dauko flask din Inna ya ajiye ya dauki ledar magunguna suma ya ajiye yana zama yaji saukowar ta daga benen ta zauna akan carfet tana mikar da kafar ta. Ya kalle ta, da gefen ido yace 'Gashi nan ki dauka ki sha!" Kallon flask din tayi ta janyo ta bude kamshin kayan kamshi ya doki hancin ta wannan yasa taji kwadayin son shan sa. Ta dauki cup din ta tsiyaya kunun sannan ta dauka tai bismillah tare da runtsa ido ta fara sha. Tsami tsamin kunun yasa ta saki idon ta sai da ta shanye wanda ta zuba sannan ta ajiye cup din ta daura kan ta akan kujera. Duk abun da take yana kallon ta ta gefen ido. Lemo ya mika mata wanda take sha da sauri ta amsa ta bude ta kafa kai sai da ta shanye sannan ta ajiye tana mai da nunfashi tin da ta baro gida yau ne taji cikin ta ya cika dan da ta fara shan abu sai amai. Sai da ta jima ya balli magani ya bata amsa tayi kamar zatai kuka ta sha sai ta hau dafe kirji dan amai taji yana taso mata tin tana daurewa har sai da ta mike ta shige bandaki a guje taje tai aman. Yana daga falo yana jin tashin aman nata abin tausayi a hankali ya mike yabi bayan ta sai kwara aman take, dafe mata baya yai har ta gama sannan ta jingina da bango tana son zamewa ta kwanta kamo ta yayi tai sauri ta lafe a jikin sa dan yadda jiri ke dibar ta ya kamata suka fita ya kwantar akan kujera ya koma ya gyara bandakin. Kan ya fito har tai bacci ya kwashe kayan ya dawo ya zauna yana aiki yaji knocking yana budewa yaga mai aiki ya bata hanya ya koma ciki bayan sun gaisa. Karfe uku Ummi ta dawo lokacin Maryam ta kara shan lemo da magani tana zaune rike da Alkur'ani Aliyu na dining area yana shan fresh yoo Ummi ta shigo da sallama Aliyu ne ya amsa Maryam kuwa dagowa tai tana binta da kallo direct wajen Maryam ta nufa ta kama hannun ta tace "Ya jikin?" "Da sauki!" Tai mata nuni da hannu sannan tace "Sannu!" Ta mike ta nufi dining ta ajiye ledar hannun ta tace "Sannu my son ya me jikin?" "Alhamdulillah!" "Allah kara sauki ya baka lada yai maka albarka." "Amin Ummi nah!" Ledar da ta shigo dashi ta tura masa tace "Ga fruit nan ka wanko ka kawo mata ko zata ci bari na watsa ruwa." Tayi sama ya mike ya shiga kitchen. Ya bude ledar Water melon, pineapple, Pawpaw, Banana, orange and Apple. Dauka yayi ya wanke ko wanne sannan ya yanka mata Apple ya ajiye a gefe yai blending banana da madara ya hada a cup ya dauka ya fita falo. Cup din ya ajiye mata da bowl din Apple da fork. Yace "Ki sha wannan!" Dauka tayi ta kai baki ta kurba ido ta lumshe dan tana son Banana tas ta shanye shi ta dauki fork taci slice din Apple guda biyu ta ajiye fork din tana mai lumshe ido. Ummi ce ta sauko sanye da daguwar riga marar nauyi ta nufi kitchen tana hada abincin dare. Karfe shida saura ta gama ta fito ta dawo falon ta zauna tana fadin "Wa kinje wajen Inna?" Kai ta girgiza. Aliyu ta kalla tace "Kai ka hanata ko?" "Haba Ummi batace zataje bane kuma ma bacci tai tayi sai da na dawo daga masallaci ma fa ta tashi shine tai sallah kika dawo." "Tayi aman ko?" "Da ta sha kunu ne tin safe!" "Me taci da rana?" "Juice kadai ta sha." Ummi ta kalle ta tace "Bakya sha'awr komai?" Kai ta gyada ta shafa cikin ta tai mata alamar ta koshi. Aliyu ta kalla tace "Sannu Allah maka albarka!" "Amin!" Ya amsa ya mike ya fita. *Allah ya jikan mu ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe.* *Antty*[11/22, 13:46] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 49 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dakin da Maryam take ya koma ya same ta tana bacci fitowa yayi falo ya zauna yana tunanin me to Mama ta fadawa Maryam lallai yasan halin Mama sosai. Zaune yake har Ummi ta dawo ta kalle shi, shi kadai a dakin tace "Ina Maryam kuma?" Sama ya kalla yace "Tana daki!" "Lafiya dai ko?" "Eh na tashe ta dai tayi sallah ban sani ba ko ta koma." Sama tayi tana fadin "Amman kuma ai yamma tayi ta sauko." A haka ya cigaba da kula da Maryam na tsawon sati biyu shi ke bata magani na safe, rana da dare haka nan Ummi in ta fita taga dan abu ta kawo mata shi kuma yan kayan kwadayi in suna gida yake hada mata duk da wasu da ta ci take yin aman su. Haka nan Inna ba ta daina kawo mata abun ba wani taci wani ko kalla bata yi. Jikin dai da sauri dan maganin da ya daura ta akai kuma sun koma asibiti jinin ta yai kasa, zuciyar ma da sauki, kuma ta fara samun sauki dan sai ta kusan yini tana bacci. A haka aka Fara azumi wanda Maryam taso tayi amman Aliyu ya hanata sam. Da azumi Ummi ko ta fita kafi karfe 2 ta dawo da ta dawo take shiga kitchen duk yadda Maryam ke son taimakawa Ummi a kitchen da ta shiga taji kauri ko wani abu za tai ta amai wannan yasa Ummi ta hanata. Aliyu kuwa a daki yake yini karatu Alkur'ani wanda da anyi la'asar baya dawowa gida sai an sha ruwa dan a can masallacin alfurqan yake jin tafsir. Ana tashi zasuyi sallah da ya sha ruwa yake tahowa gida ko ya dawo ba wani abun kirki yake ci ba. Tea ne sai dabino kawai. Daga nan in ya tafi masallacin sai goma zai dawo. Da ya dawo zai wanka ya dan kwanta karfe daya yake tashi kwana yake akan sallaya haka rayuwar su take gudana a koda yaushe. A haka azumi ya Kai goma sha biyar lokacin tafiya Umrah Ummi hakura tai da zuwa saboda yanayin jikin Maryam. Abbi da Abba da Aliyu ne suka tafi. Mami sai saura sati daya sallah ta tafi. Gidan sai ya rage daga Inna sai Mama da Ummi da Maryam. Aliyu ma acan ba zama yai ba kullum yana harami yana sallah da addu'a ga matar sa da Maryam akan Allah ya bata lafiya. Kullum zai kira Ummi sau uku ya tambaye ta ya jikin Maryam kuma a tafiyar sa taje an kara dubata tare da cigaba da shan maganin ta. Sosai ta dan samu sauki dan cikin ya kara kwari. * Bayan Sallah da sati daya su Aliyu suka dawo, Ummi ce ta hada musu abinci na tarba, kala kala, lokacin da Aliyu yaga Maryam yai mamaki domin kuwa ta dan murmure ba kamar da ba. Inna ta mike ta fita tana fadin "Bari naje na bar wajen nawa ba kowa!" "To Inna sai anjima angode! Maryam tai ma mata godiya ta tafi. Ummi tace "Kina shiga kuna gaisawa da safe kinji?" Kai ta gyada. Suna zaune a haka Aliyu ya shigo ya hangi Maryam zaune da dan cikin ta a gaba. Kai ya dauke dan ganin ta a wannan yanayin ya tino masa da Maryam matar sa. Ido ya dauke da sauri ya shiga dakin sa. Da kallo Ummi da Maryam suka bishi, yana shiga ya fada saman gado yana lumshe idon sa. Maryam kawai yake gani tana masa gizo a indon sa. Ido ya runtse yana fadin "May your gentle soul continue to rest in peace Hayyaty" Da kyar ya mike ya shiga ya watsa ruwa ya dauro alwala kiran sallah yaji ana yi ya fita da sauri, rike da ledar da ya shigo da ita. Ba kowa a falo Dan haka ya ajiye akan dining ya fita. Bai dawo ba sai wajen Tara. Ummi, Abba da Maryam zaune akan dining. Ummi da Abba na cin abinci, Maryam Kuma gaban ta gashin kaza ne sai lemo da take Sha. Aliyu ya karaso yana kallon ta, ta gefen ido sannan yaja kujera ya zauna a gefen Ummi. Yace "Barka da dare Abba!" "Ya kake Aliyu?" "Alhamdulillah!" Ya kalli Ummi yace "Sannu da gida Ummi!" "Yauwah Aliyu ka dawo lafiya?" "Alhamdulillah!" Ya kalli Maryam ya dauke Kai da sauri tare da fadin "Ya jiki?" Da hannu tai masa Alama da sannu. Abba ya kalle ta yace "An samu abin Dadi ko motsin ta ba a ji." Sukai murmushi gaba dayan su. Aliyu ya mike Ummi tace "Abincin fa!" "Ummi zanci amman sai anjima." Ya fada yai cikin daki. Ummi plate ta dauka ta zuba abinci sannan ta kalli Maryam tace "Kisha maganin ki fa!" Fuska Maryam ta bata. Ummi tace "Kin fison allura ko?" Kai ta girgiza. Ummi tayi dakin Aliyu kwance ta same shi a kan gado ta ajiye abincin ta karasa ta dafa shi ya juyo yana kallon ta. Ta kamo hannun sa suka dawo kan kujera ta mika masa plate. amsa yayi ya fara ci sai da ya cinye ya sha ruwa sannan ta mike ta fice a dakin da kallo ya bita yana mai kara jin son Ummi yau da ba Ummi ya rayuwar sa zata kasance. Ummi itace hope din sa yana godiya ga Allah da ya bashi Ummi kamar yadda Ummi ke godiya da Allah da bai bata haihuwa ba amman ya bata yaro mai son ta da jikan ta. * Washe gari kafin Ummi ta tafi aiki tace mata tashi ta gaida Inna. Ta amsa bayan mai aikin su tazo ta gama aikin ta ta rufe sashen ta tafi wajen Inna. Sosai Inna taji dadi komai ta zakulo a dakin in ta dauko ta ajiye mata sosai Inna tai tayi mata hirar. Tin fa daga ranar kullum Ummi ta tafi aiki Maryam wajen Inna take zuwa su sha hirar su sosai Inna ke son Maryam dan akwai biyayya ga aiki duk da bata magana amman Inna zata cikata da hira wanda Maryam sai dai nuni da hannu ko murmushi a haka suke rayuwa. Tin safe in taje sai Ummi ta dawo da yamma take komawa sashen su. Dan haka tsakanin Inna da Maryam sun saba da shakuwa da juna ba tsawon watannin da suke kasancewa tare. Cikin Maryam na dada girma jikinta na wani murjewa da kara kyau a lokacin cikin ta wata bakwai in dai zata awo Aliyu ke daukar ta suje a duba ta daga nan a asibiti suke zama sai zai dawo suke tahowa tare. Sosai ta saba da Aliyu ta kuma ji ta aminta dashi domin yadda yake dawainiyya da ita ba dare ba rana da kudin sa da jikin sa. Dan ba zata manta ba lokacin da tana kan laulayi sun sha kwana akan ta shi da Ummi. Abu da zata iya cewa shine Aiyu bai da fara'a sosai amman akwai biyayya da kyautatawa. Zaune take a falon Inna bayan ta idar da sallah magarib din ta, mikewa tayi ta kalli Inna tai mata nuni da zataje taga ko Ummi ta dawo. Inna ta ce to. Ta fita a hankali ta nufi sashen nasu ba kowa dan haka ta juyo tayo sashen Inna. Fitarta kenan ya shigo ya nufi sashen Inna. Wanda bai jima da zama ba ta bude labuye ta shiga da sauri ya dago dan ganin wanda zai shigo ba sallama. Kai yai saurin daukewa yana son ya tuna a ina yasan fuskar nan tata. Ta shiga ta wuce kusa da Inna tai mata nuni da basu dawo ba Inna tace "To Allah sa lafiya har yanzu!" Farouk ya mike kenan Ummi tai sallama ya amsa yana komawa ya zauna ta shigo dakin Maryam ta mike ta karaso ta amshi jakarta tana mata murmushi. Itama murmushin tai mata tace "Ya jikin?" Ta amsa mata da kai. Ta kalli Inna suka gaisa Farouk ya gaishe tana yana satar kallon Maryam. Inna tace "Ai sai zarya take baki dawo ba." "Allah sarki mantawa nai ban fada mata ba yau munyi meeting ne amman lafiya kalou!" "To Allah kyauta." Suka yiwa Inna sai da safe sanna suma fita. Suna fita Fatouk yace "Inna wannan ba dai yarinyar na bace?" "Ita ce me ya faru?" Baki ya tabe kawai ya mike ya fita. Maryam ce ta taya Ummi girki suka gama suka wuce sama ta watsa ruwa ta kwanta. Karfe tara da minti biyar Aliyu ya shigo gidan a gajiye. A falo ya zauna yana lumshe ido dan bacci ya fara ji. Ummi ta sauko tace "Ah ka dawo?" Kai ya gyada yace "Eh wallahi Ummi na gaji ne" "To fa ga Maryam can na jiran ka wai ice cream din ta ya kare!" Maryam ce ta sauko daga bene tai masa sannu da zuwa da hannu tai masa alama ido ya lumshe ya mike ya nufi kofa tabi bayan sa. A parking space ya tsaya yana kara wayar sa a kunnen sa, bayan ya dauka yace "Kana ina?" "Ok tsaya nazo na baka sako!" Ya nufi kofar tsayawa tai ya juyo ya kalle ta. Yace "Menene?" Tai masa alamar fita take son tayi. "Muje sai kuje tare ni wallahi na gaji wanka nake son naje nayi na kwanta " Bayan sa tabi a bakin gate suka samu Farouk a cikin mota. Aliyu ya karasa gefen taga yace "Gata nan kuje zata siyo ice cream!" Dagowa yai yana hango Maryam a bayan Aliyu, fuska ya tsuke. Ya mika masa Atm din sa yace "Kuje sai kun dawo!" "Hamma Aliyu ta fadi abinda take so zan siyo mata. Ka bar kudin ka." "A'ah so take ta dan ga wajen! Kuje kawai." Aliyu ya bude mata mota tashiga gaba ta zauna ya rufe yace "A tafi a hankali!" Ya juya ya koma ciki. Kallon ta, ta gefen ido yayi ya dauke kai ya tada motar. A bakin super market din yai parking ya fita itama ta fita. A bakin wajen ya tsaya yace "Kije ki dauki abinda kike so na baki minti goma!" Ita dai ciki tayi ta je ta zabi ice ceam din da take so da wasu chocolate sannan ta taho, wani saurayi ya amsar mata basket din duk da ba wasu kaya bane amman yadda take tafiya ga ciki ga kayan ya bashi tausayi ya amsa. Shi ya biya mata kudin ma dai dai lokacin da Farouk ya karaso yana tambayar nawa? Saurayin ya mika kudin yana "Na biya mata ai!" "Akan me?" "Saboda Allah!" Saurayin ya fada ya mika masa ledar kallon sa yayi yace "Ka bata abar ta!" Hannu Maryam ta mika zata amsa yace "Zaki iya?" Kai ta gyada tai masa alama da hannu cewar ai ba nauyi. Mika mata yayi ta amsa tana godiya sannan ya fice. Bayan sa tabi ta tsaya a jikin mota, Farouk ya karaso ya bude motar ya shiga ta sa hannu ta bude itama ta shiga ta zauna. Da gudu ya fusgi motar ya bar wajen suna shiga parking space Mama na dawowa parking tayi shima Farouk yayi ta fito ta tsaya kallon sa taga an bude dayan sashen. Maryam ta zuro kafa, Mama ta kalla sai ta tuna karshen haduwar su tinda taki aminta da bukatar ta bata kara ganin ta ba. Wani kallo ta dinga binta da shi. Maryam ta durkusa ta mata alama da hannu da ina yini ko kallon ta batai ba ta kalli Farouk tace "Daga ina kake?" "Uhmm Hamma ne daman....." "Ka samen a daki yanzun nan!" Tai gaba Farouk ya bi bayan ta, Maryam tayi sashen su. A dining ta hangi Aliyu na shan coffee ta karasa fuskar ta dauke da murmushi ta ajiye ledar nata agaban sa ta karya wuya. "To aje aci lafiya!" Hannayen ta, ta hade tana godiya ya mike rike da cup din hannun sa yace "Gud nyt!" Ya shiga kitchen tayi sama tana murmushi. Ummi ta sama a falo ta zube mata kayan da ta siyo a gaban ta. Ummi tai murmushi tace "To kije kici abinki ko?" Tura mata gaban ta tayi alamar ta dauka hannu ta sa ta dauki chocolate daya tace "Nagode!" Daukar kayan tayi ta saka a firij sannan ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci. Ice cream din ta sha tai alwala ta haye gado tai addu'a ta tofe jikin ta. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani Amin.* *Antty* [11/22, 13:46] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 50 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Tana shiga ta cire mayafin jikin ta ta juyo tana kallon sa. Kai yai kasa da shi tace "Kai me ya hada ka da wannan yarinyar?" "Nifa ba komai. Kawai Hamma Dr ne yace na kai ta super market!" Wani kallo ta jefa masa tace "Kada na kuma ganin ka tare da yarinyar nan." "Mama..." "Mama me? Kada na kuma nace!" "To Mama!" Ya mike yace "Bari naje nai wanka." Bata kalle sa ba ta shige daki ya mike ya fice shima. * Tinda cikin ta ya shiga wata takwas kuma sai hankalin ta ya fara tashi dan da ta kwanta bacci ba abinda take sai mafarkan Yaa Haidar da Ammi. Dan haka bata bacci sam, kwana take sallah duk ta shiga damuwa da ka ganta zaka ga tana cikin damuwa da kuma ta kadaita sai kuka. * Yau lahadi yawancin kowa yana gida yana hutun karshen mako, tin safe Maryam bata sauko ba Ummi ce ke ta aikace aikacen ta Aliyu na dining area tinda ya gama breakfast yake aiki a system din sa shi kan sa da yaji motsi a stair yake daga kai yaga ko Maryam ce amman shiru har wajen 12. Dan ba karamin sabo sukai da Maryam duk da bai fiya magana ba amman a irin wannan lokacin suna tare wani lokacin tana kwamce akam kujera shi kuma yana zaune a dining ko tsakiyar falo yana aiki duk wani motsi da za tai akan idon sa abu kadan zai juya ya kalle ta, sannan duk abun na bukatar mai ciki na kwadayi bata rabo dasu shiga dari fita dari sai ya shigo mata da abu. Ummi ce ta fito a kitchen ta kalle shi tace "Wai lafiya har yanzu bata sauko ba?" "Kila bacci take." Ya fada yana pressing system dinsa. Kallon sama tayi tace "Let me go and check dai!" Ta nufi sama ya bita da kallo. Dakin ta nufa ta bude kofar dakin, acan kuryar dakin ta hango ta akan sallaya ta hade kanta da gwiwa. Karasawa tayi a hankali ta dafa ta, da sauri ta dago idon ta duk hawaye. Zamewa Ummi tayi ta zauna tana fadin "Lafiya meyasa kike kuka ko wani abu kike ji?" Kai ta girgiza ta hau goge hawayen idon ta. Ummi tace "A yanzu baki da kowa sama dani ki dauke ni as your Ammi, u should call me Ammi, come to me with all ur problem i promise to help you out insha Allah. So now tell me what is wrong with you?" Hawayen idon ta, ta kara gogewa tana girgiza kai. Paper Ummi ta miko mata tace "Fada min kinji!" Amsa tayi tace "Ummi i miss my past, i want to recall back." "Dole kiji haka Maryam amman fada min wani abu akai miki?" "No Ummi bana son na mutu ban gansu ba, ina tsoro kada wajen haihuwa na mutu." Hannun ta Ummi ta kama tace "Wa yace miki zaki mutu. Mutane nawa ne suka haihu shin mutuwa suke. Bazaki mutu ba insha Allahu sai kin tuno kowa kin koma gida cikin yan uwan ki. But before than ki dauke mu as your family kinji mu kan mu mun dauke ki yar mu kinji ko? Ki kwantar da hankalin ki." Rumgume Ummi tayi tana kuka sosai. Ummi na lallashin ta da kyar tai shiru. "Me kike so?" Kai ta girgizawa Ummi. "Akwai abinda kike ji?" Nan ma ta girgiza kai. Tace "To ki sauko kasa zama waje dayan ba dadi ai ko?" Mikewa tayi ta dauko Alkur'ani da carbi ta biyo bayan Ummi. A dining ta hange sa bata kalle sa ba ta nufi falo ta zauna akasan carpet dan tafi jin dadin zaman kasa ta mike kafafun ta ta fara karantun Alkur'ani idon ta kan Alkur'anin take karantawa a zuciyar ta. Tin da ta sauko yake kallon ta. Sanye take da hijab har kasa dan three quarter wando da wata armless riga ce a jikin ta shiyasa ta saka Hijab dan yanzu duk bata iya saka kaya duk da an dinka mata masu fadi amman tafi gane saka kananu budaddu. Cikin nata ya kara kasa kuma yaga yadda fuskar ta tadan daga da kafafun ta. A hankali ya mike ya koma cikin falon a gaban ta ya durkusa ya kai hannun sa kan kafar ta ya latsa kallon wajen yayi ya dago ya kalle ta itama shi take kalla suna hada ido duk suka kawar da kallon junan su. "Me ya samu idon ki?" Kai ta girgiza hawaye na ciko idon nata. "Bakya exercise ko? Anjima zamu fita sai kin zagaye unguwar nan sau uku dan kiji sannan gobe ki min wanki kinji ko?" Dagowa tayi tana kallon sa a razane murmushi ya dan saki ya mike yace "Ki shirya ya kamata kina motsa jiki kada haihuwa tazo kina a haka ba wani motsa jiki da kike." Ya koma dining yana cigaba da aikin da yake. Ummi ce ta fito ta karaso tanan fadin "Dr ina son anjima ka kaimu super market mu kara shopping." "Me zaku siya kuma?" "Kayan Baby!" "Kai Babyn nan dan gata ne. Har yanzu ba a gama masa siyayya ba. Zai kwacen fada wajen Ummi na. Ko da yake Ummin sa ta kwacen ma." Kallon Maryam yayi bama ta san me suke yi ba dan ta lula duniyar tunani. Yace "Ummi ina jin jinin ta fa ya hau." "Na shiga uku bana son hawan jini da ciki fa." "Ai illa ne Ummi. Kuma naga alamar tana cikin damuwa me yake faruwa ne?" "Kawai fargaba ce." Shima ji yai jikin sa yai sanyi da tunawa da Marym da yayi. Shiru yayi Ummi ta koma kitchen tana fadin "Sai kace kaine da cikin har ka shiga damuwa ai Allah zai raba lafiya mutane nawa ne suka haihu lafiya." Komawa yayi ya jingina da kujera tare da lumshe idon sa hakika yana tausayin mata tin bai aure ba da yai aure sai abun ya dadu haka da matar sa ta samu ciki nan ya kara tausayin mata da masu ciki hakika yana tausayin Maryam. Mikewa yayi ya koma daki ya kwanta kawai. Bai fito ba sai da akai sallah azahar yai alwala ya tafi massalaci bai dawo ba sai bayan sallah la'asar a falo ya same ta zaune gaban ta flask din abinci ta kasa ci tayi shiru tana jan carbin hannun ta. Karasawa yayi ya zauna a gaban ta ya tankwashe kafa yana fadin "Kinci abincin kuwa?" Ya dauki plate ya fara zuba mata abincin a ciki. Kallon sa tayi har ya gama ya tura mata gaban ta yace "To kici." Kasa tayi da kai, ya dauki spoon ya debo ya nufi bakin ta dashi yana fadin "To bude nai feeding naki." Dagowa tayi ta kalle shi idon ta cike da kwalla, ya girgiza kai yace "Open ur mouth!" Budewa tayi a hankali ya bata ta amsa ta fara ci. Tana cinye na bakin ta ya kara debowa ya nufi bakin ta da spoon din dai dai shigowa Farouk dauke da jaka a hannun sa. Tsayawa yai yana alajabin abin Hamman sa ke bawa wata abinci a baki har sai da ya mutsuka ido amman ya tabbatar da gaske abinci yake bata a baki. Sallama ya karayi ya juyo yana kallon sa wanda hakan yasa yai saurin yin kasa da kai "Kai min daki." Ya juya ya tafi ya ajiye ya fito ya same sa yana bata lemo kai ya dauke ya fice a dakin da sauri shi ka dai ya rasa sukuni akan abinda ya gani shi dai yasan yayan sa bai shiga harkar mata sam to amman menene halakar su da yarinyar nan. Bayan ta gama ya dauke kayan ya kai kitchen sannan ya dawo falon ya zauna. Ummi ce ta sauko tace "Biyar saura ya kamata muje ko?" Maryam ya kalla yace "Zaki iya zuwa?" Kai ta girgiza dan yau ko fitar ma bata so. Yace "Kada ki manta anjima ma zaki zagaye unguwar nan three times sannan ki min wanki." Ummi tai murmushi tace "To ai ko kai akace ka zagaye unguwar nan sau biyu an hade ka da aiki bare ita." "Ummi bata son motsa jikin ta kullum fa tana zaune anan ko part din Inna ta dan daina zuwa." Kallon Maryam tayi cikin damuwa dan yanzu Maryam na cikin damuwa da son kulawa ta jima da sauyawa tin da cikin ta yai wata takwas ta fara sauyawa ta rage walwala da kuzari akan kan ta wanda tin lokacin kan taje wajen Inna hira sai ta kwana biyar ko sati ma kan taje ta gaishe ta Ummi na kula da ita sai a yau da kuma ta same ta tana kuka wannan ya kara sa ta jin tausayi da karaya akan Maryam. Ya kalle ta yace "Haba *Matar Haidar* ki tashi muje ki dan motsa jikin ki, ki zabarwa Namesake kaya masu kyau ko bakya so." Tin da ya kira ta da *matar haidar* ta dago tana kallon sa. Ya gyada mata kai ta fara kokarin mikewa tai sama. Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka wata armless rigarta budaddiya ta dauki hijab wanda iyakar sa gwiwa ta saka ta shafa turare mai saukin kamshi ta saka flat shoe ta sauko kasa. Ummi ta sama zaune da mayafi a jikin ta tana ganin ta ta mike tana fadin "Yauwa kin sauko?" Kai ta gyada. Umm ta kama hannun ta suka fita. Aliyu suka hanga cikin mota yana ganin su ya karaso da motar. Ummi ta bude gidan baya ta shiga Maryam ta bude gidan gaba ta shiga. Can wani hadadden super market suka shiga, wajen kayan babies suka karasa tana zuwa ta hango wasu kayan na baby skyblue da ratsin milk wajen ta karasa ta dauka kayan sanyi ne mai laushi sosai. Aliyu ne ya karaso yace "Sun miki kenan?" Kai ta gyada yace "Kuma fa zaiwa namesake kyau!" Hannu tasa ta rufe fuska ya amsa ya saka a kwandon da yake turawa. Wasu takalma ta hango na yara ta karasa ta dauka tana jujjuyawa Aliyu ya karaso ya tura mata kwandon yace "Saka mana!" Ta saka suka cigaba da zagayawa duk abinda taga yai mata sai ta dauka shi kuma yace ta saka da taga ta diba da yawa sai ta daina dauka tace sun isa amman Aliyu ya cigaba da jidar duk abinda yake so. Ummi na can tana dibarwa Maryam nata kayan. Daga nan suka wuce wajen kayan ciye ciye. Duk ya san abinda take so da haka da kan sa ya zazzabar mata sai da suka kusan awa a shagon sannan sukaje akai total kudi masu uban yawa haka suka biya suka fito suka saka a mota sannan suka wuce gida suna shiga ana magariba da haka a falo Aliyu ya ajiye ya shiga yai alwala ya tafi massalaci. Sai da akai isha'i ya dawo Ummi kadai ya sama a falo tana kallo ya zauna yace "Ina take?" "Tana daki wajen kayan baby!" Mikewa yayi ya hau sama dakin ya nufa ya same ta zaune a tsakiyar kaya tana kuka zama yayi daga gefe yace "Meyasa kike kuka?" Hannu ta saka ta goge hawayen dan bata ji shigowar sa ba. Yace "Tashi muje!" Kallon sa tayi sai tai saurin yin kasa da kai dan wani kwarjini take mata, ta mike a hankali ya fita tabi bayan sa. A kasa suka samu Ummi yace "Zamu zaga Ummi!" "To a dawo lafiya kar a gajiyar min da ita dai!" Suka fita. Farouk suka sama zai yi hanyar Inna yana ganin su yaso ya juya sai dai kan ya juya sun hada ido da Aliyu dan haka ya karaso yana fadin "Barka da dare Yaya Dr." "Barka ka dai ya aiki?" "Alhamdulillah" Ya fada yana yin gaba Maryam na bin bayan sa. A haka suka fita suka fara zagaye unguwar sannu a hankali sukai dan tafiya sannan suka juyo suka dawo gida. Tara saura suka shigo gida ba kowa a falo dan haka kowa yai dakin sa. Tana shiga ruwa ta watsa ta saka kayan bacci sannan ta saka hijab ta sauko dan cin abinci. A dining ta same shi zaune yana cin abinci shima ya canja shiga daga gani wanka yayi karasawa tayi ta zauna ya dago yana fadin "Me zaki ci?" Abinda yake ci ta nuna ya mike yai serving nata sannan ya tura mata gaba ya zuba mata lemo ya ajiye ya koma ya karasa cin nasa sannan ya mike ya koma dakin sa. Tana gamawa ta dauke kwanukan ta kai kitchen ta dawo ta wuce sama. A falo ta samu Ummi da Abba ta karasa ta zauna a kasa. Abba yace "Ya jikin?" Tai masa alamu da hannu da sauki. Yace "Allah kara sauki." Ummi ta amsa da amin. Mikewa tayi tai musu sai da safe ta shiga daki. Dakin ta ta shiga ta wanka ta dauro alwala tazo ta kwanta tare da tofa addu'ar bacci ta lumshe ido. Juyi ta fara dan sam baccin yaki yazo tana ji Ummi ta shigo ta duba ta. Har karfe daya da kusan rabi ta kasa baccin mikewa tayi da kyar tana dafe bayan ta dan yadda taji ya rike mata da kyar ta shiga bandaki tai dauro alwala tazo ta tada sallah tana zaune a wajen tana lazimi har aka fara kiraye kirayen sallah jin ana kiran sallah yasa ta fara kokarin mikewa amman sai ta kasa tana cikin wannan halin Ummi ta shigo, ganin ta a durkushe yasata karasa wajen ta da sauri tana fadin "Lafiya me yake miki ciwo." Kai ta girgiza. Takarda ta mika mata, ta amsa tai rubuta mata "Ummi ba fa komai jimawar da nayi a zaune ne." Dagata Ummi tayi tace "Sannu to meyasa?" Ta kamata suka shiga bandaki tai wanka tare da alwala tazo ta kara zama. To fa ciwon baya kuma ya kamata dan da kyar ta idar da sallah anan kasa ta kwanta wani bacci mai dadi ya dauke batai rabin awa ba wani ciwon mara ya tashe ta mikewa tai zaune da kyar ta jingina bayan ta da gado tana cije baki tana ambaton Allah cikin ranta can kuma sai ya saki komawa tayi ta kwanta tana mai maida nunfashin wahala. Sai wajen takwas bayan Ummi ta gama break ta leko dakin ta same ta kuma tana bacci fita tayi taje tai wanka sannan ta sauka ta debo mata abinda zata bukata. Tana kan matattakalar bene Aliyu ya fito daga dakin sa. Ta juyo tace "Ka zauna kaci ina zuwa." Tayi sama dakin ta koma ta same ta ta daina ta hade kai da gwiwa. Dafa ta tayi ta dago ta kalli Ummi cike da karaya da tsoro. Ummi tace "Lafiya?" Kai ta girgiza ganin har hankalin ta ya tashi. Ummi tace "Ki fadan in da wani abu." Kai nan ma ta girgiza. Ummi tace "To ga abinci nan ko akwai abinda kike so?" Kai ta girgaza ta ja faratin dan yunwa take ji. Sai da Ummi taga taci sosai tasha magani sannan ta dauko kwanukan ta sauko kasa. Aliyu ta sama zaune a dining yana jagwalgwala abinci ta zauna tace "To kai ma me ya faru?" Murnmushin da bai kai zuci ba ya zaki tace "Allah ya shirya min kai da zurfin ciki." Sama ya kalla yace "Ya jikin nata?" "Da sauki." "Tana shan maganin kuwa?" Ya tambaya cike da damuwa. "Tana sha." "To Allah raba lafiya. Na fara fitar da rai da maganar ta gaskiya Ummi." "Saboda me?" "Naga na daura ta akan magani tana sha kuma shiru more than five month." "Haba Dr kai fa likita ne kai zaka bawa wasu kwarin gwiwa ba karya gwiwa ba, ai sauki sai a hankali insha Allahu wata rana zatai magana da izinin Alah." "Allah ya yadda abinda ke damuna kenan yanzu dan in tana maganar zata samu ragin wata damuwar ba tai ta rubutu ba." "Haka ne Allah bata lafiya ya sauke ta lafiya." "Amin ya Hayyu ya qayyum." Ya mike yana fadin "Zanje asibiti inda wata matsala a sanar dani." "Shikenan Allah tsare ya bada sa'a." "Amin Ummi na." Ya juya ya fita. Wajen Inna ya wuce ya gaishe ta tare da ajiye mata ihsanin da ya saba bata, sannan ya shiga wajen su Mami suka gaisa. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani amin.* *Antty*[11/23, 12:32] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 51 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Sam bata sauko ba dan a hankali dai nakuda take ita kuma sam bata sani ba za dai taji marar ta ko bayan ta sun rike sai kuma taji ya saki wanda yana sakin ta take bingirewa da bacci da ya tashi kuma zai tsayar da ita daga baccin da take. Ummi na hawa wani ta ganta na bacci wani idon ta biyu haka dai kuma duk tambayar da zatai mata sai ta girgiza kai kawai. Aliyu ma ya kira yafi sau nawa yana tambaya ya jikin ta dan ya kasa samun sukuni har yamma da ya dawo ma a kitchen ya samu Ummi yace "Ya jikin nata?" "Da sauki fa ka kwantar da hankalin ka." "Ummi bata ce komai na damun ta ba." "Bata fada ba meyasa ka tada hankalin ka ne?" "Yau ne EDD ta shiyasa nake tunanin ko zata sauka a yau." "To ai kasan zata iya karawa ko ragewa ko daga yanzu dai zuwa ko da yaushe zamuna tsammani ne." Saman ya kalla sai ya juya ya nufi sama da dan saurin sa. Knocking yai wanda in taji knocking tasan shi ne dan haka ta dauki hijab ta zura tare da mikewa a hankali ta bude masa kofar taja baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna, tin da ya shigo yake kallon ta har ta karasa ta zauna. A jikin bango ya jingina yana binta da kallo. Dagowa tayi jin shirun ita yake kalla idon ta, tana gaishe shi da hannu amsawa yayi yana fadin "Me yake damun ki?" Kai ta girgiza ya karaso ya durkusa a gaban ta yana kallon fuskar ta, kan ta ta rasa kasa dashi dan idon Yaa Haidar ba karamin kwarjini yake mata ba, dan murmushi ya saki yace "Kin tabbata?" Kai ta gyada yace "Good ki sauko muje ki motsa jikin ki." Dagowa tayi da sauri idon ta cike da kwalla yace "Menene?" Kai ta girgiza yace "Ki fada min abinda yake damun ki." Ka ta girgiza yace "To tashi mu tafi." A hankal da kyar ta mike ya bude mata kofa ta fita yabi bayan ta. Kitchen suka karasa wajen Ummi tana ganin su tace "Ah ta sauko?" "Gata nan zamuje ta dan tattaka." "To a dawo lafiya." Suka fita yana fadin "Kinyi azhkar dai ko?" Kai ta gyada yace "Good girl." Dan murmushi ta saki suka fita a gida suna tafe in ta gaji ta tsaya ta huta su cigaba sun yi tafiya mai tsayi ta tsaya ta marairaice idon ta dan yadda taji kafar ta da bayan ta sun rike kallon ta yai yace "Ya dai?" Hannu ta yafe ta nuna masa bayan ta, yace "Ko haihuwar ce?" Ya tambaye ta dan ya manta Maryam bata san wata haihuwa. Kai ta girgiza ta masa alamar ba zata iya tafiya ba. Napep ya tsayar ta shiga ya shiga suka koma gida kan suje gida har kafar ta saki da kan ta ta shige gida ya biya mai napep yai alwala ya wuce masallaci. Tana shiga ta wuce sama da Ummi ma bata kasa alwala ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta tada sallah a zaune tayi tana idarwa wani bacci ya dauke ta. Cikin baccin taji wani a zababen ciwo ta farka tana ciccije baki tare da addu'a a cikin zuciyar ta. A hankali taji ciwon na sauka zuwa can koma taji komai ya lafa. Ummi ce ta shigo tace "Maryam sauko kici abinci." Kai ta girgiza, Ummi ta durkusa tace "Dan Allah meyake damun ki? Ki fada min ki dauken a matsayin uwa na fada miki." Kai ta kuma girgizawa. Ummi ta kalle ta tace "To sauko kici abinci." Nan ma kai ta girgiza. Ummi tace "Yau fa baki ci komai ba ki fada min ko akwai abinda kike so sai nai miki." Dagowa tai tana kallon Ummi idon ta cike da kwalla. Gyara zama Ummi tayi tace "Bana son kukan ki sam Maryam ki fadan me kike so?" Hannu Ummi ta kama ta matse a cikin nata tare da lumshe ido, Unmi ta bita da kallo daga baya ta saki hannun nata ta sakar mata murmushi abun da take rubutu ta dauko tace "Ummi bana bukatar komai ki daina damuwa." "To shikenan me zaki ci?" "Bana jin yunwa Ummi." "Yau fa tin karin safe baki ci komai ba ko dan cikin ki ai kya ci wani abu ko? Bari Dr ya dawo nai masa magana ya samo miki wani abu." Ta mike ta sauka. Bayan Isha'i Aliyu ya shigo ya zauna a falo yana kallon kafar bene Ummi ta sauko tace "Yauwa daman kai nake jira." "Haihuwar tazo ne Ummi?" Ya tambaya da sauri. Murnushi Ummi tayi tace "Oh oh oh likita ba ita bace." Ajiyar zuciya ya sauke yace "To menene Ummi?" "Taki cin komai tin safe rabon ta da abinci fa." "To me take so?" "Sai da a tambayo ta wai ita bata jin yunwa." Mikewa yayi ya hau benen kofar dakin ya isa ya buga kofa fitowar ta daga bandaki kenan ta saka hijab ta nufi kofar ta bude, sannan ta juya yace "A'ah dawo ai fita zamuyi." Dagowa tai ta kalle shi cikin fuskar tausayi yai murmushi yace "Ban daukar wani excuse zo muje kema kya samu nishadi a waje." Ba dan ta so ba ta biyo bayan sa suka sauko. Ya kalli Ummi yace "Zamu fita Ummi sai mun dawo." "A dawo lafiya." Ummi ta fada tana kallon Maryam da katon ciki sai kace na yan biyu. A hankali tabi bayan sa suka fita. Shi da kan sa ya bude mata kofa ta shiga sannan ya rufe ya zaga ya shiga dayan side din ya nufi gate yaba saka kai Motar Mama na shigowa kallon juna sukai yace "Barka da zuwa Hajiya Mama" Tsaki ta saki ta dauke kai ya saki murmushi yaja motar ya bar wajen ta bisu da kallo tana fadin "Na tabbata akwai wani abu tsakanin yaon nan da yarinyar nan sai rainawa mutane hankali ake bari dai yau naje na samu Alhaji." Ta shiga da mota tai parking ta fito ta nufi sashen su. Dakin ta ta shiga ta ajiye jakar ta da mayafi sannan ta fito ta nufi bangaren Abba. A falo ta same shi yana kallon BBC ta shiga tana fadin "Ashe ka dawo?" "Daga ina kike da daren nan." "Haba Alhaji naga na fada maka zani bikin yar Hajiya Karima ko?" "Amman karfe nawa yanzu bayan isha'i ake dawowa daga unguwa na fada miki bana son ana fita ana kaiwa dare amman ke sarar ki kenan." "Kayi hakuri." "Kada ki sake na fada miki." "Naji." Ta fada ya dauke kai daga kallon ta gyara zama tayi tace "Wai Alhaji kayi bincike kuwa game da yarinyar da Aisha ta kawo gidan nan?" Juyowa yai yana kallon ta yace "Me ya faru?" "Eh to nifa ban yadda da wai tsintar yarinyar nan sukai ba ina ganin ko dan ta ne ya dirkawa yarinya ciki iyayen ta suka koro ta shine suka kawo ta nan ta haife su mai da ta gidan su." "Wane d'an kenan?" "Zai wuce Aliyu tinda ita bata ganin laifin sa sam, komai yai dai dai ne ita ke daure masa gindi shiyasa ya raina mutane yake abinda yaga dama yanzu ma fa na ganshi tare da yarinyar sun fita me yake hadasu in ba wani abu tsakanin su." "Keee ya isa haka Barira na rantse da Allah ki kiyaye ni da kwason ko wanne irin shirgi kina fada min. Yanzu a gaban ido na kike tuhumar d'ana da fasikanci, kada ki manta Aliyu fa d'anane na ciki na amman ko kunya bakya ji, waye zai boye miki gaskiya. Wallahi Barira ki fita a ido na da irin wadan nan halin naki, shikenan ba zasuyi taimako saboda Allah ba da izinin Allah ban haifi fasiki ba bare wanda zai kawon dan shege ba dan haka ki kiyayen tashi ki bani waje." Mikewa tai tana magana kasa kasa "Uhmm kada ka yadda ai nasan ko banza na saka maka wasi-wasi kuma nasan zaka bincika Allah yasa cikin sane in an bincika a lokacin naga da wane ido da baki zakai min bayani." Ta fice a daki komawa Abba yai ya jingina da kujera yana tunanin maganar, Mami ce ta shigo da sallama yana daga inda yake ya amsa ba tare da ya bude idon sa ba. Juice din da ta shigo dashi ta ajiye akan center table sannan ta karaso ta zauna a kusa dashi tare da dafa shi tace "Lafiya Alhaji?" Ta saka dayan hannun ya kamo hannun ta tana wasa da hannun nasa sun jima a haka wajen minti uku sannan taji ya sauke ajiyar zuciya. Sakin sa tayi ta mike ta zubo masa juice din a kofi ta kawo masa a baki ta saka ya kurba tare da lumshe ido yana mai kara sauke wata ajiyar zuciyar. Sai da ya sha rabi ta janye ya kalle ta yace "Matar Aljanna Allah miki albarka." Wani dadi Mami taji a cikin ranta tace "Amin Mijina kana hakuri da halin da ka tsinci kan ka kada kace zaka dauki wani mataki a duk abinda za ai maka mai hakuri shike da riba kuma ko wanne tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana tare da mai hakuri kayi hakuri Mijina." "Madallah ga matar Aljanna ina alfahari da kasancewa tare dake a ko da yaushe kin ban soyayya kin bani yara masu albarka ba abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da mafificin Alheri." "Amin godiya nake miji na taso muje kaci abinci." Ta mike tana son kamo hannun sa. Kamo hannun ta yayi yace "Zauna muyi wata magana tukkuna." Komawa tayi ta bashi hankalin ta ya kalle ta yace "Me kika sani akan yarinyar da su Aisha suka kawo gidan nan?" "Oh Maryam ina ce Inna tai maka bayanin komai." "Ina so na kara ji daga bakin ki dan nasan ba zaki boye min komai ba baki tabai min karya ba kuma nasan ba zaki fara ta a yau ba." "Me ya faru ne Alhaji?" "Ba komai fada min." "To kasan tafiyar da sukai Bauchi a can suka dawo da ita a hanyar su ta dawowa suka kade ita yarinyar da aka kai ta asibiti bata farfado ba har washe gari to kaga ba zasu tafi su barta ba to data farfado suka so su gana da dagin ta amman bata san komai akan rayuwar ta ba kamar tayi losing memory kuma bata magana wani abun al'ajabin ma ciki da ita amman tace tana da miji da mahaifiyar ta abinda take iya tinawa kenan. Kasan Aisha da tausayi wannan yasa ta kasa barin ta acan, dan bata san wane hali zata fada ba kaji dalilin tahowar ta da ita gida." Tinda Mami ta fara magana yake kallon ta har ta gama yace "Kin tabbata?" "Eh Alhaji." "To tashi muje." Hannun ta sa ta kamo tace "Meyasa kai min wannan tambayar?" "Ba komai." Ya fada yana mikewa tabi bayan sa dining ta zuba masa abinci yaci sannan ya shiga dan yai wanka bayan ya fito ya shirya cikin kayan bacci ta window ya leko yana kallon harabar gidan ko ina tsit dan dare ya fara lokacin kusan goma da wani abu. Mami ce ta karaso tana fadin "Alhaji baka kwanta ba daman?" Ya juyo yace "Eh aiki ma nake son nayi ko zan samu ruwan dumi." "Bari na kawo maka." Ta fada tana ficewa. System ya dauka ya koma barandar gidan ya zauna yana aiki a haka Mami ta kawo masa ta juya ta koma daki ta kwanta har sha biyu saura yana wajen yana aiki. *Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* *Antty* [11/23, 12:32] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 52 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******* Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo bata taba ganin waje mai kyau da tsari haka ba. Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo duk da hanyar wucewa ce amman an kawata ta. Sai da sukai tafiya mai tsayi sannan ta fara ganin wajen saida abubuwa kala kala. Wani waje ya shiga da ita suka nufi can karshe duk da wajen ba mutane suka zauna. Basu jima da zama ba aka kawo musu lemo da menu. Amsa yayi yai ticking sannan ya mika mata, rasa me zata zaba tayi ya amsa ya zabar mata sannan mutumin ya juya. Kallon wajen take dan wajen ya matukar burge ta, ga sanyi ga ni'ima suna zaune aka kawo musu abinda suka zaba. Maryam ta dauka ta fara ci Ido ta lumshe tana jin wani dandanno da dadi a bakin ta. Sun dauki kusan awa a wajen sannan suka bar wajen dan ya riga yai musu transfer. Cinema suka nufa, nan ma suna zama aka kawo musu pop corn da lemo aka ajiye a gaban su. Aliyu ne ya fara ci amman ita ko kallon sa batai ba Idon ta na kan film din da ake nunawa. Dauka yai ya bata ta amsa batai niyyar ci ba yace "Kici da dadi." Diba tayi tai Bismillah ta kai bakin ta, tana taunawa ta lumshe Ido dan ji tayi kamar Madara kadai take taunawa ga wani dadi da bazata iya misalta shi ba. Kadan Aliyu yaci ya ajiye amman sai ga Maryam ta tashi da nata gaba daya. sai da aka gama film din suka mike zasu tafi ta kalli Aliyu ta kalli ragowar 🍿 din yai murmushi yace "Dauko mana muje ma mu siyarwa Ummi dan tana sonsa." Kan ya rufe baki har ta dauki abin ta suka fita ya siya da yawa zasu fita ta kalli shi ta nuna masa wajen da suka fara zuwa yace "Wani abu kike so?" Kai ta gyara suka shiga ya amshi menu ya bata ta kara zabar abinda ya siya mata dazu aka bata ya biya suka fita tana gaba yana bin bayan ta. Suna fita suka nufi wajen motar su zasu shiga wata mata da tin da suka shigo take kallon su dan ba karamin burge ta sukai ba bama da yazo ya bude mata ta shiga ya rufe ya zuba kayan a baya har ya zagaya ta karaso wajen inda Maryam ke zaune tace "Sannu 'ya ta." Dagowa tai ta sakar mata murmushi. Dai dai shigar Aliyu ya kalle ta yace "Sannu Hajiya." "Yauwah sannun ku. Allah raba lafiya Allah kara baku zaman lafiya." Tana fada ta juya Aliyu ya bita da kallo Maryam kuwa ragowar popcorn din sa take ci a haka suka bar wajen suka nufi gida. * Sha biyu saura suka karasa gida. Abba yana ta zaune a inda yake yaga shigowar su ya zuba musu Ido har Aliyu ya fito ya bude mata mota ta fito tai gaba yabi bayan ta da kallo ya bisu har suka shige bangaren Ummi. System din gaban sa ya rufe ya mike ya shiga dakin baccin su. Mami tai bacci shima kwanciyya yai yayi addu'a ya kwanta. Suna shiga tai sama shi kuma yai dakin sa. Kayan jikin ta cire ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta saka kayan baccin ta ta hau kan gado tana addu'a Ummi ta bude kofar ta dago tana kallon ta. "Sai yanzu kuka dawo cikin daren nan?" Kai tai kasa dashi dan itama sai yanzu taga dare yayi sosai har haka. Ummi ganin tayi kasa da kai tace "Kinci abincin?" Kai ta gyada mata. Shigowa tayi ta rufe kofar ta kwanta tace "To kiyi addu'a kinji." Kai ta gyada tai addua ta tofe jikin ta. Sannan ta kwanta. Tin da cikin ya shiga watan haihuwa Ummi ta bar barin ta ita kadai suke kwana tare dan kar nakuda ta zo musu cikin dare. Da asuba ta tashe ta ta shiga tayo alwala ta tada sallah tana idar wa ta fita a dakin. Maryam ta tasa ta fara sannan tayo awala tazo ta tada sallah tana idar wa ta yunkura da nufin ta mike sai taji wani irin ciwo ya kunno mata komawa tai ta zauna da sauri tana runtse idon ta hadi da ambatar sunan Allah. Jin azaba tai azaba ta bude idon ta tana fitar da wani nishi mai sauti kan kace me ta fita daga hayacin ta gaba daya ta rasa inda zata saka kan ta. Da kyar take iya fitar da numfashi. Karfe bakwai ya fito cikin shirin sa na tafiya asibiti dan yau yana da aikin da zai yi da karfe takwas. Kitchen ya leka ya tadda Ummi na soya dankali karasawa yai ya durkusa ya gaishe ta. Ta amsa tana fadin "Dr yau fitar sasafe ce kenan." Dankalin da ta tsame ya diba a wani dan karamin plate yana fadin "Akwai aikin da zamuyi tin last week aka saka za ai aikin sai kuma aka samu akasi ba ai ba shine aka saka shi yau da karfe takwas." "To Allah yasa ayi a sa'a." "Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!" Ya gama ci ya dauki fresh yoo a firij yana fadin "Sai na dawo." Har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Ummi Maryam fa?" "Tana sama ina jin bacci take." Fita yai ya nufi sama yana zuwa ya tsaya a bakin kofa yana knocking amman shiru ya buga yafi sau biyar ba a amsa ba har ya juyo zai bar wajen sai kuma ya koma da ya kasa kunnen sa a jikin kofar nishin ta ya fara jiyowa sama sama da sauri ya saka hannu ya murda kofar dakin ya shiga a can gefe gado ya hango ta zaune tana fitar da wani irin numfashin wahala ta kan gadon ya dira ya karasa wajen ta yana fadin "Maryam! Maryam!!" Ina bata san ma me yake ba dan azabar ciwon da take ciki dago ta yai ya fita dakin da ita a haka suka sauka daga benen yana kwadawa Ummi kira. Ummi dake wake kayan da tai amfani dasu ta fito tana fadin "Ah Dr daman baka tafi ba...." Maganar tace ta tsaya lokacin da ta ganshi dauke da Maryam a hannun sa har ya kai kofar dakin. Da gudu tabi bayan sa ya saka Maryam a bayan mota sannan ya shiga wajen mai tuki. Ummi ta shiga wajen Maryam da sauri tana janyo ta jikin ta tare da mata sannu. Yana yiwa motar key ya dannan wani uban horn wanda kan ya karasa har masu gadi sun bude masa kofa a guje ya fice a gidan cikin minti takwas suka karasa asibitn dan gudu yake kamar zai tashi sama. Suna shiga nurses din dake wajen suka karaso da gadon daura mara lafiya. Motar Ummi ta bude ta fito suka fito da Maryam suka daura ta akan gadon sannan sukai cikin asibitin da ita da gudu. Labour room suka nufa da ita Ummi da Dr suka bi bayan su da sauri a bakin kofa Ummi ta tsaya Aliyu ya shiga yana kallon yadda Nurses din ke bata taimakon gaggawa. Daya daga cikin nurse din ya kalla yace "Jeki ki kira min Dr Nusaiba ki fada mata yanzu yanzu dan akwai emergency aiki please." "Ok Sir." Ta fada ta fice daga dakin. Yana daga nesa yana kallon su. Ba ai minti uku ba sai ga Dr Nusaiba tare da nurse din da ya aika tana zuwa ta wuce kan Maryam tana dubata. Karasowa yai yace "Haihuwa ce ko?" "Eh Sir amman kuma lokacin ne bai yi kila amman daga yanzu zuwa ko da yaushe zata iya sauka." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ba dai wata matsala ko?" "Babu insha Allahu." "Alhamdulillah please Doctor ki kula da ita sosai." "Insha Allahu." Ya fita daga dakin Ummi ya sama tana safa da marwa daga wannan bangon zuwa dayan bangon. Da sauri ya karasa yana fadin "Muje Ummi ki zauna insha Allahu yanzu zata sauka." "A'ah Aliyu ba zan iya tafiya na bar ta a wannan halin ba." Hannun ta ya janyo yace "To taho ki zauna anan." Ta zauna shima ya zauna yana fadin "Bamu fadawa kowa a gida ba." "Kira Abba na sanar masa kada ya tashi yaga ba kowa ma a gidan." Nan Aliyu ya kira Abba da Mami ya fada musu sannan ya kashe wayar yana fadin "Allah sauke ta lafiya." "Amin ya Allah." Dukkan su cikin tashin hankali suke suna zaune a wajen har karfe takwas amman shiru kasa zama yai ya mike ya shiga dakin ganin ta yai tana ta fama duk ta galabaita. Karasawa yai bakin gadon yana mata tofi sai da ya gama ya dago yana kallon Dr Nusaiba da Dr Yasmeen yace "Har yanzu ko?" "Eh Wallahi amman ka kwantar da hankalin ka insha Allahu in less than 30 minute zata sauka." "Allah ya yadda. Bari naje." Ya fita ya samu Ummi tace "Har yanzu ko?" "Eh wallahi Ummi." "Bani wayar ka na kira Mami nace a samo mata rubutun nan." "Ummi rubutu kuma." "Bani nace kai komai ba dai dai bane a wajen ka." wayar ya mika mata nan ta fada mata abinda take so ba ai minti goma ba aka kawo musu rubutun da kan ta ta shiga ta bawa Maryam ta sha. Duk ta galabaita. Abu kamar wasa har karfe biyu na rana Maryam na fama da nakuda daga ita har likitocin duk sun galabaita. Ummi kuwa duk ta tsorata. Ba wanda yafi Aliyu shiga wani hali dan gani yake abinda ya faru da matar sa shi ne yake shirin kara faruwa ya kasa tsaye ya kasa zaune ko yaje kan ta ba abinda yake iya aikatawa ga tausayin ta da a lokaci guda ta rame idanun ta duk sun kara fiffitowa ga ba baki sai nishi da hawaye dake zubowa kawai. Hakika duk wanda yaga Maryam a halin da take ciki sai ya tausaya mata masu raguwar zuciya kuwa sai sun zubar mata da hawaye. Inna ma ta zo asibitin dan ta shiga wajen Ummi mai aikin take fada mata tana asibiti Maryam zata haihu cikin tashin hankali tace "Tin yaushe kuma?" "Nima da nazo wajen sha daya ba kowa duk suna asibiti." "Ba zama ai." Ta fice tana kwadawa Farouk kira lokacin dawowar sa kenan ya karaso yana fadin "Haba Inna me ya faru? Wannan kira sai kace ana yaki." "Kai ni rufe min baki, kazo ka kaini asibiti." "Me yake faruwa?" "Kaini dai kawai." Kallon ta ya tsaya tace "Mahaukaciya ka maidani ne ko? In ba zaka kai ni ba bari na kira Shehu da Suleimanu su kaini." "A'ah Inna muje." Yai gaba ya bude mata kofa, ta shiga ya rufe suka nufi asibiti. A can suka samu Mami da Ummi. Inna ta karasa tana fadin "Ya jikin nata?" "Tana ciki dai." "Innalillahi Allah ka sauki yarinyar nan lafiya. Haihuwa yakin mata tana ina naganta." "Inna kinsan basa bari a shiga dakin ai." "Ni da kun bar ta a gida na amshi haihuwar ta ko me asibitin suka iya?" Aliyu ne ya fito ya samu waje ya zauna tare da dafe kan sa. Ummi ta mike tana fadin "Ya dai Dr?" "Ummi har yanzu dai she is suffering." "Allah ka dubi baiwar ka, ka saukaka mata wannan ciwo." "Amin Ummi." "Kada ka saka damuwa Aliyu zata sauka lafiya da izinin Allah." "Allah ya yadda." Farouk sai yaji zuciyar sa ta karye tausayin ta ya kamashi shima sai gashi yana addu'a Allah ya sauke ta lafiya. Suna zaune har akai la'asar Aliyu da Farouk suka tafi masallaci Ummi kuma sukai sallah a ofishin Aliyu. Suna idarwa suka koma kofar dakin basu jima ba sai ga Su Aliyu sun dawo. Suna zaune wajen biyar sai ga Abbi da Abba sun shigo. Abba yace "Wai har yanzu ba matsala kuwa Dr kasan ba a son doguwar nakudar nan." "Abinda na ke tunani kenan Abba to daman da naji zaku zo nace in kunzo mayi maganar gwara a aikin sai ka sa hannu ko?" "To ya kuka ce?" Abba ya fada yana kallon su Abbi da Ummi. Hawayen Ummi ta goge tace "Gwara ayin ko ta huta itama." "To shikenan." Aliyu ya shiga yaiwa Dr magana suka fara shirin aiki. Ya kawo wa Abba takarda Abba ya saka hannu wanda cikin rabin awa an gama shirye shiryen shiga aiki. Aliyu ne ya shiga dakin da Maryam take, har lokacin tana kwance ya karasa ta dago ta kalle shi cikin sarewa ta nuna masa waje tana masa alamar ya kirawa mata wani a waje. Ko bata fada ba yasan ba wanda zata bukaci gani a irin wannan lokacin sai Ummi dan haka da sauri ya fita ya kamo hannun Ummi suka shigo dakin. Ummi na ganin Maryam ta karasa da sauri ta kama hannun ta tana fadin "Sannu 'Ya ta insha Allah za ai aikin nan lafiya da izinin Allah." Kai Maryam ta fara girgizawa hawaye na fita a idon ta. Ummi tace "Ki bar kuka kinji Maryama da yadda Allah zaki tashi kiyi rayuwa da yaron ki." Nan ma kai ta girgiza ta kamo hannun Ummi ta daura aka cikin ta sannan ta kamo hannun Aliyu ta daura akan na Ummi tai nuni da ta basu abinda yake cikin su rike mata shi amana. Hawaye ne ya zubowa Ummi ta hau girgiza kai tana fadin "Kema zaki rayuwa da dan ki insha Allahu." Aliyu ta kalla wanda tashin hankalin da yake ciki har ya saka jijiyoyi kan sa sun fito rada rada dan shi halin da Maryam take ciki yana tino masa da halin da tashi matar ta shiga a baya. Juyawa yai ya fice a dakin ya wuce office dinsa kawai. Yana shiga ya hade kan sa da table din sa addu'a kawai yake a cikin ransa Allah ya sauki Maryam lafiya. Ummi ma da kuka ta fito suna tsaye aka fito da Maryam daga dakin akan gado suka nufi dakin da za ai aikin Maryam na ganin Ummi ta daga mata hannu tana mata bye bye abinda ya kara karyawa su Mami da Ummi zuciya kenan. Farouk kan sa dake wajen sai da hawaye ya ciko idon sa tausayi Maryam yaji sosai. Abba da Abbi ma sun mata addu'a Alah yasa ayi aiki lafiya. Bakwai saura kwata suka farai mata aiki lokacin Abbi, Abba, Farouk da Aliyu suna masallaci duk da sun idar da sallah amman sun kasa fitowa daga Asibiti su Abba ko gida sun kasa tafiya. A cikin asibiti kuwa su Ummi, Mami da Inna bayan sunyi sallah Inna sai kuka take tana fadin "Yarinyar kirki Allah yasa ayi a sa'a." Ita kadai sai surutai take yi. Suna masallaci aka kira isha'i suka gabatar sannan suka addu'a. Farouk ne ya fara fita a masallacin can inda dakin ya karasa su Ummi ya sama zaune a wajen. Bai jima ba Abba ya karaso wayar farouk ce ta hau kara yana dubawa yaga Mama ce kamar ba zai dauka ba sai ya dauka. "Kana ina?" "Ina asibiti Mama wana..." "Kanwar uwar kace ko ta uban ka?" Ta fada cikin fada. "Mama....." "Rufen baki ka baro asibitin nan yanzun nan." Abbi ne yace "kai da waye ne a wayar?" "Mama ce." "Bani ita nan." Ya mika masa. Ya kai kunne yace "Kowa yana asibiti ke me kike a gida?" "Kanwar uwa tace a asibitin da zan zo na rashe." "Ohk!" Kawai yace ya kashe wayar. Farouk ya kalli Abbi yace "Ni zan tafi Abbu." "Akan me? Ita tace ka tafi ko?" Shiru yayi yace "To ba inda zaka tinda ita bata zo ba kai ka tsaya nasan an kusa fitowa kaima in ka tafi hankalin ka ba zai kwanta ba gwara ka tsaya kaga fitowar tasu." "To Abbi." Ya koma ya zauna. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* *Antty*[11/24, 12:23] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 53 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Aliyu kuwa yana can masallaci yana ta addu'a ya dukufa a wajen sai wajen tara saura sannan ya mike ya fito jiki a sanyeye zuciyar sa sai bugawa take kamar zata fito daga kirjin sa. Inda su Ummi suke ya dosa yana shan kwana ana bude dakin aikin daya daga cikin nurse din ce ta fito rike da baby a hannun ta da sauri ya fara takowa Ummi ta mikawa Ummi na amsa ya karaso ya zura hannu ya amshe yaron yana leka fuskar sa. Murmushi ya saki sai kuma yai sauri ya mikawa Ummi ya kalli Nurse din yace "Ya Maman sa?" "Tana ciki komai lafiya." A take a wajen ya juya ya kalli gabas ya durkusa yai sujudul shukur ya dago yana fadin "Alhamdulillah Alhamdulillah." Dakin ya shiga yaga sun fara turo gadon da Maryam take kai da sauri ya karasa wajen kan ta yana kallon ta idon ta a lumshe amman ta kwarmin idon ta zaka gane ta fad'a bin bayansu yayi. Su Ummi kuwa suna waje sai murna suke Mami ta amshi Baby, Tana fadin "Masha Allah tabarakallah!" Inna ta amsa tana fadin "Masha Allah, Allah ya raya mana kai." Farouk ya karaso yana fadin "Nima a bani dan Allah." "Iya daukar yara kai?" "Kai Inna." Ta mika masa ya amsa yana leka fuskar Babyn yace "Wow fine Baby me kyau Tarakallah." Ya mikawa Abbi da Abba suma suka amsa sukai masa addu'a yadda mutanen nan ke farin ciki zaka rantse d'an cikin su ne ko jikan su. A haka su Aliyu suka fito ana tura gadon da Maryam take kai. Bayan su suka bi har aka karasa da ita dakin da aka tanadar dan kula da ita suna shiga su Ummi suka karaso rike da Baby. Bakin Gadon Aliyu ya karasa ya amshi Babyn hannun Ummi yace "Ummu Haidar Bude idon ki, kiga Haidar din ki." A hankali ta bude idon ta, ta sauke akan fuskar Baby dan Aliyu ya dago mata da fuskar Baby yadda zata gani tana daga kwance "Yaa Haidar ya tafi Yaa Haidar ya dawo." Ta fada, da sauri duk suka kalle ta suna son suji daga ina maganar ta fito babyn ta amsa ta kifa a saman fuskar ta tana sakin wani kuka mai ciwo tare da fadin "Allah ya raya min kai Haidar, Allah ya maka albarka ya kare ka daga duk abin ki ya baka ilimi mai albarka, Allah yasa alummar musulmi suyi afahari da kai, Allah ya raya min kai Haidar kai kadai ne gata na, Abbin ka ya tafi ya barmu sai gashi Allah ya dawon da me kama dashi." Ta karashe magana tana mai cigaba da kuka, wanda kukan kanaji daga kasan zuciyar ta yake fitowa. Dago Babyn Aliyu yai yana fadin "Yau naga raguwar Ammi kuka zaki fara koyawa Babyn ke da zaki masa addu'a gaskiya ba zan yadda d'ana ya koyi ragwantaka ba jarumi ne kada ki manta mai asalin sunan jarumi ne." Hannu ta saka tana share hawayen idon ta, wani bacci ta fara ji yana fizgar ta bata fargaba ya dauke ta. Ummi tace "Aliyu kuma bacci take?" Ya duba yace "Eh allurar bata gama sakin ta ba." Ya mikawa Ummi Babyn. Abba yace "Ba wata matsala dai ko?" "Babu Abba." Abbi ya kalli agogo tara da rabi yace "To Alhamdulillah dare yayi sai mu tafi ko? Tinda komai ya tafi lafiya." Mami ta mike tana fadin "To Ummin Aliyu mu zamu tafi sai da safe amman Aliyu yazo ya amso miki abinci tin safe bakuci komai ba, itama mai jegon kada ta tashi cikin dare tana jin yunwa ko?" "Haka ne Mami mungode. Dr kaje ka kai su gida sai ka dawo din ko?" "To Ummi!" Lokacin har Abbi da Abba sun fita Mami da Inna suka bi bayan su. Farouk ya mike ya karaso wajen Ummi tare da zaro wayar sa dake cikin aljihu yace "Bari na dauki hoton Babyn mu." Ya dauke shi sannan yai masa kiss a goshi yace "Ummi sai da safe ki kular mana da Babyn." Ummi tai murmushi Aliyu ya fita yana daddana waya. Abba ne ya dauki Inna, Abbi kuma ya dauki Mami Aliyu da Farouk kowa ya dauki motar sa. A kusan tare suka karasa gidan. Abba ya raka Inna har bangaren ta sannan ya dawo sashen sa. Aliyu na shiga ya nufi dakin sa yai wanka ya canja kaya sannan ya fito. Dakin Maryam ya shiga hado musu kayan da zasu bukata sannan ya fito. Bangaren su ya nufa ya samu Mami a kitchen tana hada wa su Ummi abinci har ta gama dafa tea. A basket ta saka masa da kayan tea da su lemo da ruwa sannan ya dauka ya koma asibitin. Lokacin da ya koma Ummi na rike da Baby ya shimfida babbar carpet din da ya shigo dashi sannan ya ajiye kayan da yazo dasu a inda ya dace. Ya bude flask ya zuba ma Ummi abinci yace "Ummi taho kici abinci nasan yau baki ci komai." "Kai ma haka ai Dr." "Ummi na dan ci dankali da safe." "Wannan dashi da babu duk daya ai. Taho muci kaji." Ya taho ya zauna kusa da Ummi zai dauki plate ta miko masa spoon tace "Muci tare." Tare suka ci suka sha ruwa sukai hamdala sannan yace "Ummi bari naje office na danyi aiki." "Yaushe zaka tafi gida dare na yi?" "Ummi anan zan kwana." "Anan kuma Dr ka tafi gida gobe da safe kazo kaji." Yai shiru tace "Jeka kaji dan albarka." Dawowa yai ciki ya amshi Babyn yai masa addu'a sannan ya sumbaci goshin sa ya mikawa Ummi yana fadin "Sai da safe to me zan taho muku dashi gobe?" "Zan duba in akwai abinda muke bukata zan fada maka kan ka fito." "To Ummi." Ya kara matsawa kusa da gado ya leka Maryam dake ta baccin ta, sannan ya juyo ya kara leka baby da kyar ya iya cewa "Ummi sai da safe." Ya fita. * Washe gari tin asuba da ya dawo daga masallaci ya shiga kitchen shi yai musu breakfast ya hadawa Maryam abinda yasan zata iya ci marar nauyi ya hada komai a basket. Karfe bakwai ya fice ya bar gidan bayan ya gaida Abba tare da gabatar masa da abincin sa. Yana zuwa ya samu Ummi har taiwa Baby wanka ta shirya shi cikin kayan sanyi sky blue sai kamshin turare yake. Amsar Babyn yayi ya zauna yana fadin "Ina kwana Ummi na?" "Lafiya lou ya gidan?" "Alhamdulillah ya my son da Maman sa?" "Gata nan tana ta bacci har yanzu bata tashi ba." Gadon ya kalla ya dauke kai ya mai da kallon sa kan Babyn yana fadin "Baby nah yayi kyau Ummi tai maka kwalliya kai kyau my baby." Ya sumbaci goshin sa tare da zaro waya ya dauki babyn hoto yana fadin "Ummi yaron nan tubarkallah kato dashi gashi kyakyawa." "Ya maman sa take?" "Ya fita kyau fa." "Kai dai kace kafi son yaron ka." "No ba haka bane Ummi yanzu dai ki yi break din ki tukkuna." "A'ah bari na fara wanka dai." Ta debi kayan ta ta shiga bandaki yana zaune rike da baby har ta fito cikin shiri sannan ta karya. Karfe takwas sukaji ana knocking kofar dakin izinin shiga suka bayar sai ga Farouk ya shigo da sallama suka amsa ya karaso ya zauna gefen Aliyu yana fadin "Ina kwana Hamma?" "Ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah!" Ya fada yana leka Babyn sannan ya dago yace "Ummi ina kwana?" "Lafiya lou ya gidan?" "Alhamdulillah!" Ya kalli Aliyu yace "Hamma ka ban Babyn mana nifa shi nazo na gani kan na tafi aiki." Mika masa yayi sannan ya mike yana fadin "Bari naje Ummi ba abinda kuke bukata?" "Babu Dr." Ya juya ya fita. Bai jima da fita ba mai aikin su ta kawo abinci daga wajen Mami. Farouk sai da Ummi ta kore shi sannan ya tafi da kyar wajen tara. Karfe goma Maryam ta farka Ummi ta karasa tana fadin "Sannu Maryam!" "Yauwah Ummi nagode." Murnushin fuskar Ummi ne ya dado jin da gaske maganar Maryam ta dawo. Ummi tace "Bari a kira Dr dan ya duba ki ko?" Kai ta gyada Ummi ta kira Aliyu ta sanar dashi, Dr da tai mata aiki ya kira ai kuwa nan da nan tazo ta duba ta komai normal bayanin abinda zataci tai mata da yadda za ai mata wanka dan kar ruwa ya taba inda aka manne dan ba dinki akai mata ba cealing (like) wajen akai. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin* *Antty* [11/24, 12:24] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 54 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Zaune yake a office dinsa, system din sa ya janyo ya fara kiran Sitti ta ciki dan vedio call yake so suyi yana kira Najwa ta dauka tana fadin "Yaya ni baka kira na mu dan gaisa kaji ya karatu sai Sitti ko?" Kai ya shafa yace "Ke meyasa ba zaki kirani ba. Bawa Sitti wayar nan ko da yake ina system din ki? Ki hada mu tanan zan kira yanzu." "To mu gaisa mana." "Ki kira in kina son mu gaisa." Ya kashe ta tabe baki tana fadin "Kai Yayan nan haka kake. Uncle Abubakar kuwa kullum cikin kiran mu yake, haka Yaa Farouk amman kai sai Sitti komai Sitti." Ta dauko system din ta ta fita falo inda Sitti take, Kaykyawar tsohuwa ce zaune akan kujera amman ba tsufa sosai tai ba dan tana samun kula daga ya'yan ta tayi shekaru kusan tamanin amman in ka ganta sai kace batafi shekara sittin ba, karasawa tayi wajen ta, ta tabe baki tare da fadin "Yaya ne ya kira." "Yana ina bani wayar?" "So yake ya ganki." Nan ta kunna ta kira sa ta mike ta bar wajen. Fuskar Aliyu na bayyana tace "Likita bokan turai. Abin so! Jikana dan Albarka." Wani murmushin ne ya kara sauka a fuskar sa yace "Sitti na, farin ciki na, gwarin gwiwa ta ina kaunar ki." "Fadan albishir din Abin so." "Mu fara gaisawa Sitti." "To ya yan gidan ina fatan kowa lafiya?" "Alhamdulillah Maryam ta haihu jiya an samu Baby Boy." "Alhamdulillah Masha Allah. Allah kara mata lafiya ita da babyn Amin." "Amin Yaa Hayyu ya Qayyum!" "Wannan shi ya saka farin ciki abin so?" "Shine Sitti ban taba jin son wani abu a duniya kamar yaron nan ba Sitti baki ga babyn ba tubarkallah!" Ya fada yana daukar wayar sa ya nuna mata hoton babyn tace "Masha Allah Tubarkallah Allah ya raya yai masa albarka." "Amin Ya hayyu ya qayyum." "To ya aikin ina Babyn da Maman sa?" "Sitti aiki akayi mata dan jiya yanzu mun fitar da rai da ita tasha wahala amman yanzu komai ya wuce tana lafiya ita da Baby." "Alhamdulllah Masha Allah. Anjima ka hadani dasu mu gaisa." "Insha Allah!" "Madallah." "Sitti bari ma naje dan naga wannan tsohuwar na can dakin ma yanzu." "Kawar tawa kake cewa tsohuwa ai nafita tsufa." "Kai Sitti ita waccen kinsan dai halin ta." "Sai hakuri ai kasan in mun tsufa ai." "Ke bakya haka." "Kowa da irin sa ita daman haka take tin da kuruciyar mu tana da fada" Baki ya tabe yace "Bari naje zan kira ki a wayar ki, yauwa ki daina barin yaran nan na daukar wayar ki." "To Abin so a daki na batar ita kuma tana ciki shiyasa." "To bari naje." Ya kashe ya nufi dakin. Acan sukai waya da su Ummi da Mami har da Inna da maijego. * Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin kwana biyar din da Maryam tayi taga kulawa gata daga wannan ahalin sosai suke bata kulawar su da nuna mata kauna baga ita ba baga Babyn ba. Farouk kuwa safe, rana, dare sai yazo kuma kullum da siyayyar da zai yo wa Baby. Aliyu kuwa in ya dauke Babyn sai su Inna sunzo sun ishe shi da kira yake dawo dashi. Sam ya hana a bawa yaro ruwa dan yace a nonon ma akwai ruwa dole suka hakura duk fadan Inna sai cewa tayi "In ya kashe shi ai shikenan." A haka sukai kwana biyar aka sallamesu suka koma gida Maryam ta cigaba da jego. Ranar suna kuwa Abba ya siyo rago Aliyu kato sa ya kawo yace a yankawa Baby Aliyu Haidar. Mami da Abbi kuwa kaya masu tsada da kyau sukaiwa Maryam da Babyn ta Inna ma ba abarta a baya ba ta kawo mata atamfafofi da kayan Baby da turare da sabulu Farouk kuwa kullum akwai siyayar da yakewa Haidar Abba ma ya bada kudi masu yawa yace ayi duk abinda ya dace. Abinci mai rai da lafiya akai aka yi walima yan gidan su Yaa Asiya, Hannah da Yaya Bilkisu da masu gadi da masu aikin gidan sai yan kawayen Ummi na gun aiki da suka san da zaman Maryam din. Maryam ranar suna ta sha kuka bama da taga gatan da aka nuna mata ta tabbata ko a gidan su sai haka ta samu abinda bata taba tunani ba. Babyn ta ya zama dan gata wanda kowa ke so da son faranta masa da ita dan haka ba abinda zatace sai Alhamdulillah. Da dare bayan kowa ya tafi Ummi tanawa Baby wanka, Maryam ce ta fito daga wanka, daure da towel ta zauna a gefen gadon Ummi tace "Ina fatan dai ruwan bai taba wajen?" "Eh Ummi." Ta dauki mai ta fara shafawa, wayar Ummi ce tai kara ta dauka tana fadin "Mutanen Canada!" "Ummi ina yini yasu Maryam da Babyn?" "Suna lafiya, gasu nan." "Bani mu gaisa tinda baki ya bude ai ana gaisawa yanzu ko?" Mikawa Maryam wayar tayi ta amsa suka gaisa, sannan yace "Me take so?" "Ba komai Uncle." "Kin tabbata?" Kai ta gyada yace "Shikenan ga Auntyn taki tace zaku gaisa." Amsa tayi suka gaisa sannan ta mikawa Ummi, Ummi tace "To Sadik sai anjima?" "Eh Ummi amman gobe zan sako kaya a jirgi in yazo zasu kiraki kayan Maryam da Baby ne." "To madallah Allah yayi albarka." "Amin Ummin mu Allah kara miki lafiya ina alfahari dake." "Nima ina alfahari dakai Sadik." Sukai sallama, doguwar riga Maryam ta saka ta zauna a gefen gado tana shirin kwanciyya akai knocking, hijab ta zura sannan suka bada izinin shigowa, a hankali ya bude dakin ya shigo, sanye yake da milk din wando da blue din riga sai kamshi yake ya shigo daki da sallama suka amsa ya karasa wajen Ummi dake zaune a kan carpet rike da Baby Haidar, amsa sa yayi ya mike yana kallon sa, addu'a yai masa yace "Yau yasha hannu." Ummi tace "Ai baka ga ba shiyasa ina masa wanka ya fara bacci." Kwantar dashi yayi yana kara tofa masa addu'a ya kalli Maryam yana fadin "Akwai abinda kike bukata ne?" Kai ta girgiza ya kalli Ummi yace "To sai da safe Ummi." "Allah bamu alheri." "Amin." Ya juya ya fita. * Haka Ummi ta cigaba da kula dasu suna jego cikin sati uku Haidar yayi wata uwar kiba ya kara kyau kamar sa da mahaifin sa ta kara fitowa sosai yaron kamar d'an larabawa gashi da farin jini duk wanda ya ganshi sai yaso ya dauke shi dan in sunje asibiti ma ai ta son daukar sa wannan yasa Ummi take tofe shi tare da saka maman sa ta tofe shi a ko da yaushe. Ba abinda Maryam take sai jegon ta kullum tana daki daga wanka sai ci sai kwanciyya itama cikin sati ukun tai kyau ta murnure kai ba kace ita ce me shayarwa dan kuruciyyar ta sai ta kara fito wanda a da cikin yasa zakaga kamar babba ce amman yanzu kowa ya ganta yasan yarinya ce karama. Ba abinda takewa Haidar Ummi da mai aikin da ke tayata kula da ita su ke masa komai dan in ba shan mama zai ba, bata ganin sa a wajen ta daga bayan Ummi sai bayan Karima dake tayasu aiki. Da yamma kuwa Aliyu na dawowa zai dauke shi duk aikin da zai yana tare dashi yake aiki dan Haidar bai da rigima sam ba zakace da yaro a gidan bama dan kan yai kuka ana jima. In zaije sallah ne zai kaishi amman da ya dawo yana wajen sa kwana ne kawai bayayi a waje sa. Yana son Haidar dan komai ya gani sai kawo masa. Maryam kuwa sai suyi sati ma bai ganta ba dan tana sama da ya dawo yaga yaron sa shikenan ya manta da ita a office ne wani lokacin yakan yawan tina ta. Farouk ma kan ya fita sai yazo ya ganshi haka in ya dawo shima duk abinda ya gani na yaro da na babba da ya burge shi zai kawowa Haidar. Wani Ummi har dariya take dan kafin yai amfani dashi ma yasan za a dade. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har sukai arba'in. Maryam ta zama budurwa sosai ko dan shayarwa take ne ita da yaron ta kullum kara kyau suke Haidar kuwa ya zama dan lukuti sam Aliyu bai bari a bashi komai mama kadai yake sha yace sai yayi wata shida Inna tai fadan har ta gaji in Maryam taje tai ta zugata wai ta bashi ruwa su daina daukar hakkin yaro Maryam sai tace to tana dariya. **** **** **** Yamma ce mai cike da ni'ima wacce ya hade da sanyin damuna ta fito cikin atamfa riga da zani lemon green da akai kwalliya da red colour riga da zani ne, rigar ta zauna cif a jikin ta sai zanin dake zaune a 'kugun ta yai das dashi. Ta saka dan kunne da sarka na gold wanda Ummi ce ta siya mata, ba makeup a fuskar hoda ce kawai sai man lebe ta sauko daga bene kafar ta sanye da wani red flat half cover sai hijab din ta ja dake rike a hannun ta. Ummi ta gani zaune a kan kujera Haidar na hannun ta tana masa wasa. Zama tayi a hannun kujera tace "Haidar da matar shi." Dariya Ummi tayi tace "Ah kina so dai ki ganmu a rana ne kawai ko?" "Uhmm Ummi wajen Inna zani." "Zauna ki bashi ya sha dan nasan kika fita sai an ganki." Dariya tayi tace "Ummi wannan yaron ya fiya ci." "Dadin ta jiki na nunawa ko zakin fama." "Wallahi Ummi ni dai na fara gajiya da shan shi." "Kai Maryam in ba dan na ganki ba kila har ayi magariba bai nema ba, kawai dai dan kar ki fita ki jima ki dauki hakkin sa ne." Zama tayi ta juyawa Ummi baya tace "To zugen." Ummi ta sa hannu ta zuge mata sannan ta sauka kasa ta zauna akan filo ta tankwashe kafa dan Aliyu ya hanata zama akan kujera ta bashi mama yace in ta zauna a kasa sai ita da yaron sun fi jin dadin. Maman ta fito da shi ta saka masa a baki tare da furta bismillah cafkar da yayi yasa ta runtse idon ta tana fadin "Ummi zai cire mamana." "Wallahi Maryam ke raguwa ce, ace har yanzu kinki ki saba da shayarwa." Ido ta bude tana cije baki tace "Uhmm Allah da zafi Ummi." Tai maganar kamar zatai kuka. Murmushi Ummi tayi, Maryam ta kalli Haidar dake shan maman yana lumshe ido hannu ta daura akan sa tana shafa sumar kasa wacce take kwance luf luf a haka har ya koshi ya zare bakin yana bangale mata bakin sa yana mata dariya kumatun sa na lotsawa. Tissue ta dauka akan center table tana goge masa gumin da ya tattsafo masa a goshi, tana masa murmushi sai da ta goge ta dagashi ta daura a kafata tana shafa masa baya gyatsa yayi ganin Ummi a bayan sa ya dinga mata dariya yana mika mata hannu alamar ta dauke shi. Amsar sa tayi Maryam ta mai da maman ta sannan tace "Ummi zugen." Ta zuge mata ta mike tana fadin "Har ya zuke ni bari naje wajen Inna ko zan samu kayan dadi." "Kwadayi dai zaki daman." Dauke filon tayi ta saka hijab din ta tana dariya tace "Sai na dawo." * Ta fice daga dakin tana fita compound Farouk na karasowa wajen daga gani bangaren Ummi zai je, "Sannu da zuwa Yaa Farouk." Ta fada kan ta a kasa. Kallon ta yai yana murmushi yace "Yauwah ina my son." "Yana ciki." Yayi bangaren Ummi ita kuma ta juya tayi bangaren Inna. A compound ta same ta tana gyara shuke shuken dake harabar wajen. Ta shiga da sallama Inna ta dago tana fadin "Ai da zan zo biko." Murmushi Maryam tayi tace "Biko kuma Inna?" "Eh mana ina jin jiya da shekaran jiya fa baki zo ko gaishe ni ba, bare yar hirar da muke." "Lah Inna jiya ne fa shima kuma dan munkai Haidar asibiti ne. Ai yau gani nazo mu sha hira." "To shiga gani nan shigowa." "Ah haba dai Inna kawo na karasa." "A'ah a'ah je ki zauna na gama wanke tsintsiyar kawai zanyi." Tayi ciki Inna ta karasa bakin famfo ta wanke tsintsiya sannan ta shiga dakin. A kan kujera ta samu Maryam ta shige kitchen bata jima ba ta fito da dan bowl tana fadin "Dan ke nayi fa jiya kuma baki zo ba, shine nace zan zo biko sai na taho miki dashi." "Kai Hajiya Inna shiyasa nake sonki." Ta bude bowl din kaza ce akai mata pepper chicken ajiye bowl din tayi tace "Bari na wanko hannu na." *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.* *Antty*[11/25, 11:27] Maryam S Indabawa🥰:  💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 55 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ta shiga kitchen ta wanke ta fito dauke da lemo mai sanyi ta zauna tana ci Inna na bata labari tana ji tana dariya hade da lumshe ido dan dadi nama bata farga ba taji sallamar mutum dankwallin ta dake ajiye akan kujera tai saurin dauka ta yafa a jikin ta, tin kan ya shigo kamshin sa ya danno kai. Dakin ya shigo, sanye yake da dogon bakin wando da farar riga, mai dogon hannu, ba a inda idon sa y fada sai akan Maryam, kai ya dauke ya karaso gaban Inna ya ajiye mata ledar da ya shigo ya juya ya nufi kofa Maryam tace "Sannu da zuwa." "Yauwah." Kawai ya fada ya sa kai za fita, Inna tace "An gode Allah maka Albarka." "Amin!" Ya amsa tare da ficewa. Inna ta tabe baki tana fadin "Duk jikoki na nafi son yaran nan amman shi matsala wani lokacin miskilanci da nukufarci ji dai yadda ya ke magana kamar bai so. Dubi dai yanzu fura ya kawon da nono kusan kwarya guda dan yasan ina so." Ta fada tana leka ledar da ya ajiye mata. Murmushi Maryam tayi, Inna tace "Wallahi shima yana so na, da sam ba haka yake ba yaro mai fara'a da son mutane amman daga mutuwar matar sa duk ya koma haka, nayi nayi suyi masa aure sunki, da sun masa da kila ya koma yadda yake Allah dai ya bashi mai tausaya masa da son sa kamar matar sa. Ina fada miki yar yayar Babar sa ce acan turai suke inda Najwa take karatu in kinga yadda suke soyayya a da sai sun burge ki, wallahi ban taba ganin Aliyu da ita sunyi fada ba tana da sanyi hali da hakuri yarinyar kirki mai tarbiyya da son mutane ga kyauta to Allah ya fimu son ta shekarar su biyu bata haihu ba sai da ta samu ciki kuma ya hau bata wahala, haka aka sha fama ke dauke matar sa yai ya kai can uwa duniya sai da cikin ya isa haihuwa da kyar ya kawo ta gida ashe rabuwar ta kusa lokacin basu kwana ashirin ba ta tashi da nakuda ina fada miki, ta sha wuya baki ga yadda ya tashi hankalin sa ba ke kace shi ke nakudar haka sukace ba zata iya haihu da kanta ba shine fa za a shiga aiki, ba ai aikin ba Allah ya amshi a barsa kan ai wata wata yaron yabi uwar zo kiga Aliyu wallahi kamar ba zai rai ba ya daina ci ya daina sha ga tunani ai fa nan ciwo yai raf dashi, ciwon nan da yanzu ba tsoho ba babba ya kama shi wai hawan jini, mu dai Allah raba mu dashi ace yaro sai kaji shi da hawan jini ai duniya ta zama abinda ta zama, ina fada miki ga ulcer yaro sai ya hau tsamurewa da kyar da addu'a da rokan Allah, Aliyu yake rayuwa amman da tini shima mun rasa, to fa shikenan tin lokacin ya canja ko magana bai fiya so ba yafi son ya kadai ta abinci kuwa kina ganin sa zandamemen nan sai Aisha ta saka shi a gaba da lallashi, da komai kamar jariri, ai ita dai Aisha yar albarka ce, ta iya riko, kinga yadda ta riki Aliyu kuwa ko uwar sa bata rike shi kamar yadda ta raine shi ba, ita dai tana son yara amman Allah bai bata zaunanne ba, kinga fa haka ta samo mana wani yaro Abubakar wanda na fada miki yana auren yar autata suna can Canada da ya'ya su har hudu, ai Aisha Allah ne kadai zai biya ta, ta kula da Aliyu da matar sa, ke yau suna gidan ta gobe suna gidan su basu da wajen zama tsayayye ita ke dawainiyya da su, ai kuwa itama taji mutuwar haka da rokan Allah fa aka fara samk kan sa, to kinji fa tin rasuwar matar sa ni ban 'kara ganin sa cikin nishadi ba sai haihuwar ki da yadda yake wa yaron ki, dan Allah da iyayen zasu dau tawa ai da an masa aure ko shima zai ga gudan jinin nasa ko? Ace yaro ya girna amman ba aure ga farouk nan ma yana koyi da dan uwan nashi." Idon Maryam har yayi ja jin labarin Aliyu maikon kwallar dake kwarmin idon ta, ta saka hannu ta goge tana fadin "Allah mata rahma. Ina rashin masoyi babban damuwa ce ni gani nan na rasa nawa na rasa iyaye na, na kasa sanin kowa nawa sai ku." Maryam ta fada tana fashewa da kuka. Inna tace "Haba yar nan ke kuwa kada kiyi kuka wani yazo ya zata wani abu nai miki dan Allah kiyi hakuri, ke kuwa kike da masu son ki, wallahi zan iya rantse miki da Allah ina jin ki tamkar jika ta dan haka ki bar kuka komai kike so ki fada min ni nai miki alkawarin kula dake da miki duk abinda nake so kinji?" Kai ta gyada tace "Ban taba haduwa da mutane masu karamci kamar ku ba kun min komai duk da baku sanni ba Allah ya saka muku da gidan aljanna nagode sosai da sosai." "Ba komai yiwa kai ne kai kasan halin da naka zai fada a ciki? Ki daina kukan to." Hawaye ta goge Inna ta cigaba da mata hira tana sata dariya har ta dan sake amman abun na damun ta dan labarin Aliyu ya taba mata zuciya. Fura Inna ta dama musu har da madara da kwakwa Maryam ta saka afirij dan ta dan yi sanyi sannan ta fito tai alwala dan an tada sallah magariba sallah tayi tana zaune tana addu'a har akai isha'i sukai sallah sannan ta mike tace "Inna zan tafi sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Har ta kai kofa Inna tace "Oh zo ki anshi furar ki." Ta dauko jug Inna ta zuba mata da yawa sukai sallama. Ta fita, ta kusa zuwa sashen Ummi sai ga Farouk nan kallo daya yai mata ya gane tana da damuwa ba kamar dazu da ya ganta ba dan haka ya tsaya kallon ta can kuma yace "Lafiya dai ko?" Dagowa tayi dan ita bata san dashi ba. Kai ta dauke tace "Ba komai." "To sai da safe." Suka bar wajen yai bangaren Inna ita kuma tai bangaren su. Tana shiga ta samu Ummi da Aliyu, Haidar a hannun Aliyu yana jijjiga shi, sama tayi Ummi da Aliyu suka bita da kallo Ummi tace "Lafiya kuma?" Hannu ya daga alamar 'Waya sani.' Haidar ya kalla yaga yai bacci ya mikawa Ummi yace "Ummi a kwantar dashi, daga nan kiji me yake damun ta?" Amsar sa tayi tai sama. Dakin Maryam ta shiga taga bata ciki, motsi taji a toilet ta kwantar da Haidar tare da dauko masa kayan baccin sa ta saka masa ta lullube shi sannan tai masa addu'a zaman jiran fitowar ta tayi. Bata jima ba ta fito daure da towel da hijab a saman kan ta. Ummi ta kalla ta dan saki murmushi ta nufi doruwa ta dauki kayan baccin ta, ta koma ta saka sannan ta fito hula ta saka akan ta ta nufi gadon tana fadin "Ummi, Abba bai dawo bane?" "Ya dawo menene?" "Na ganki a zaune anan ne." "To me zanje nai masa?" Murmushi Maryam ta saki tace "A'ah ba komai wai nace yaci abinci ne?" "Yaci nasan yanzu ma ya kwata zauna muyi magana." Zama tayi a gefen ta Ummi ta kamo hannun ta tace "A duniya a halin yanzu baki da sama da Haidar to amman Haidar ba zai iya tambayar ki damuwar ki ba, ni din dai nice makusanciyar ki fiye da kowa a yanzu dan haka ki fada min me yake damun ki?" "Ummi ba komai. Ni ba abinda yake damuna. Me zai damen ina dake?" "Kin tabbata?" Kai ta gyada tace "To Allah ya dafa bari naje na kwanta kiyi addu'a sannan kiyiwa mai gidan nawa." "To Ummi." *Allah ya jikan mu ya sa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [11/25, 11:27] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 56 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Bayan wata hudu. Tsaye take a kitchen tana karasa miyar da ta daura, Ummi na gaban sink tana wanke kwanuka, gas din ta rage ta rufe miyar sannan ta tafi wajen Ummi tana fadin "Ummi nace ki bari na karasa dan Allah!" Ta dauki kwanon tana dauraye wa. Ummi tace "Ai na kusa bari kawai na karasa." Haka suka cigaba dayi Ummi na wankewa Maryam na daurayewa. A haka har suka gaba Maryam ta kwashe ta kai ma'ajiyar, Ummi kuma ta dauraye wajen. Sallamar Aliyu suka jiyo suka amsa Ummi na fadin "Mai gida ya dawo." Ta fita Maryam ta karasa wajen miya ta kashe gas din ta zuba a flask sannan ta dauraye hannun ta. Fita tayi zuwa falo. Haidar ta gano yana daddafa kujera yana tafiya tare da gwaranci. Aliyu na zaune ya jingina da kujera Ummi na kallon Haidar tana fadin "Wato Haidar dai ya dage kan ya shekara sai ya taka." Yana ganin Maryam ya fara daga mata hannu yana fadin "Ammmmiii Mommmi Annnttti." Karasowa tai ta dauke shi tana fadin "Oyoyo yaron Ummi." Ta dauke shi tare da kallo Aliyu da tin da ta haihu ya daina sakar mata duk wannan kulawar ya daina sai dai Haidar ita daga gaisuwa shikenan. A hankali tace "Sannu da zuwa Yaa Aliyu!" "Yauwah!" Kawai ya fada ba tare da ya kalli inda take ba ya cigaba da danna wayar sa. Ummi dai bata tanka ba itama sai ta cigaba da kallon Haidar dake tai mata gwale gwale shi alallai labari yake bata ita kuma tana ta biye masa can Aliyu ya mike yai daki dukkan su da kallo suka bishi. Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace "Zo nan Maryam!" Mikewa tayi rike da Haidar suka karasa, Ummi tace "Kada ki damu da halin yayan ki, haka yake wani irin miskili ne ba kasafai aka fi gane abinda yake so ba, amman zan fada miki Aliyu bai son rawar kai sam duk da nasan ke ba ruwan ki, yana son nutsatsen mutum kamar yadda kike bai son hayaniya dan haka please kar ki sa damuwa kinji?" Murmushi Maryam ta kwakwalo dan sam bata son wannan canjin daga gareshi da safe da rana da dare sai ya dubata da lallashin ta me take so da matsa mata akan abu ko zuwa motsa jiki in tana damuwa yafi kowa damuwa amman yanzu ya canja bai damu da ita ba ko zasuyi kwana nawa bai ganta ba bai damu ba, sam bata son haka amman ya zatayi tinda haka yake zata daure ta daina damuwa insha Allahu. Dagowa tayi ta kalli Ummi tace "Ba komai Ummi na jima da gane hakan." "Yauwah Maryama." Ta mike sukai sama ita da Haidar tana fadin "Bari nai masa wanka kan ai magariba." * 8:15pm Dakin sa ta Shiga da sallama, ya amsa ta Shiga, yana zaune akan carpet gaban sa system Haidar na kan gado gaban sa biskit, alawa da chocolate. "Ummi!" Haidar ya fada yana mika mata wata alawa. "A'ah Haidar kayan zakin nan ai sai ku." Ta zauna tana fadin "Shiyasa kake gudowa nan, dan sai abinda kake so kake yi ko?" Aliyu ya kalli Haidar dake shan alawa, murmushi yayi ya juyo yace "To Ummi ai gwara abarshi yai abinda yake so ko?" "Hmmm wajen ka nazo Doctor." Dagowa yayi yace "To Ummi lafiya dai ko?" "Yadda kakewa Maryam kasan bata da kowa sama damu a yanzu dan haka dole mu jata a jiki Dr dole mu sakar mata." "Ummi ni kuma ke dai amman ni me zan mata kuma? Duk abinda take so ta fadan zan mata insha Allahu." "Duk da haka nasan kai daman halin ka wani lokacin kana da wuyar sha'ani." Haidar ne ya sauko ya gangaro yana son ya dauke shi, daukar sa yayi ya amshi chocolate din hannun sa ya bude masa sannan ya mika masa amsa yayi ya saka a bakin sa sai kuma ya fito da ita ya saka a bakin Aliyu ya gutsura ya mikawa Haidar yace "Sha abinka." Ummi ya dago ya kalla yace "Ummi ni ina da shawara akan Maryam." "Ina jin ka." "Mai zai hana ta zana jarabawa daga nan mu sama mata addmision dan shine kadai gatan ta a duniya." "Na jima da yin wannan shawarar amman ganin tana shayawar shiyasa na dakata." "Haidar bai da matsala, kuma kinga an kusa zana weac ana ta registeration har anyi kan lokacin fara makaranta ta fara ko yaye shine tayi tinda kinga bai fiya damuwa da maman ba." "To shikenan Allah taimaka yanzu ya za ayi?" "Gobe zan turo a dauke ta aje ai mata komai." "Shikenan Allah yayi albarka." "Amin Ummi." Ummi ta mike tace "Haidar ko zamu tafi?" Aliyu ya kamkame yana shigewa jikin sa. Ummi tace "Zaka zo ka samen." Ta fita. Haka akai ciki hukuncin ubangiji akai mata registeration wanda Aliyu ya dauki mai mata lesson kan a fara exam wata daya da registeration suka fara exam sannan aka saka ta wata isilamiyya dake unguwar da taje akai mata interview komai ta wuce yan makarantar dan haka suka samu Aliyu sukai masa bayani kan cewa da za su same ta a matsayin malama zasuyi murna. Wannan yasa Aliyu ya sanar da Ummi, Ummi ta samu Maryam, Maryam tace ba matsala dan haka ta fara zuwa suka bata aji tana koyar wa. * Ranar da zata fara exam da safe Maryam ta fito daga dakin ta shirye cikin goggagun uniform din makarantar da zata zana jarabawa, sakowa tayi daga bene, kitchen ta shiga gun Ummi, Ummi dake juye ruwan shayi a flask ta juyo tace "Yan makaranta an fito?" Murmushi tayi tace "Eh Ummi, nazo na karasa." "A'ah bari ai na gama." Ummi ta karasa ta mika mata flask din ta fita dashi dining Ummi ta fito da flask din da ta zuba dankali da kwan da ta suya. Maryam ta hada tea ta zuba dankalin ta ci. Maryam na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauraye ta samu Ummi a sama ta shiga ta dauki hijab din ta ta fito tace "Ummi zan tafi." Ummi dake aiki a system ta dago tace "Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka." Dakin ta juya ta shiga ta dauko sannan ta fito tace "Ummi sai na dawo" Ummi tace "Ohk Allah ya tsare kiyi addu'a kafin ki fita, driver na waje." Fita tayi ta nufi can parking space din Farouk ta gani a jikin motar sa yana worming din ta, tinda ta fito yake bin ta da kallo har ta karaso, kai tai kasa dashi tace "Ina kwana Yaa Farouk?" "Kin tashi lafiya yau sai makaranta ko?" Tai murmushi ta gyada kai." Driver ne ya karaso ya gaishe da Farouk sannan ya kalli Maryam ya gaishe ta, amman sai taki amsawa ta gaishe shi. Farouk ne yace "Bari na kai ta, kazo daukar ta." "Ok ranka ya dade." Ta kalli farouk zatai magana ya daura mata hannu a kan leben sa yace "Shiiii!" Tare da mata nuni da ta zagaya ta shiga. drivern ta kalla tace "Yaa Aliyu ya baka time table din ai ko?" "Eh ya bani dazu da zai fita." "Yauwah sai kazo dauka ta." Ta karasa ta shiga shima ya shiga ya fitar da mota. Suna tafe a hanya yana dan jan ta da hira har suka karasa makarantar har cikin school din ya shiga da ita sannan yai parking ya zaro kudi a aljihun sa ya mika mata yana fadin "Allah bada sa'a." "Amin." Ta amsa ba tare da ta amshi kudin hannun sa ba yace "Ki amsa mana?" Kai ta girgiza tace "Ummi fa ta bani." "Na Ummi daban nawa daban amshi kinji kanwata ba kyau maida hannun kyauta baya." Amsa tayi da hannu biyu tace "Nagode!" Ta rufe kofar ta juya ta nufi wajen wasu dalibai da ta gani dan tambayar exam hall. Tana zuwa ta tambaya daya a cikin su tace "Muma can zamuje muje." Suka dunguma suka karasa karfe tara suka shiga kowa ya zauna a sit din sa tara da rabi aka fara raba booklet suka fara exam. Da yake da Biology ce awa biyu aka bayar karfe sha biyu har sun fito. Da motar gida tai tozali ta karasa wajen Driver na gani ya taso ya bude mata ta shiga suka kama hanyar gida. Ummi na wajen aiki amman har ta gama girki dan haka tana komawa ruwa ta watsa tai alwala tai sallah lemo kadai ta sha ta rufe sashen su ta tafi bangaren Inna. Inna na kitchen ta shiga jiyo muryar Maryam tace "Gani nan shigo daga ciki." Maryam ta karasa tana fadin "Hajiya Inna me ake soya mana?" Cincin take soyawa Maryam tai murmushi dan bata taba ganin tsohuwa kamar Inna wacce ta iya komai daga na zamani har na gargajiya ba abinda bata yi in tana sha'awa bata fiya son kayan shago ba da kanta take fi yin komai. Maryam tace "Inna ina yini?" "Lafiya lou yau ina kika shiga na jiki shiru naje bangaren na same shi a rufe." "Ai yau muka fara jarabawa shiyasa." "Ayyaho Allah ya bada sa'a." Ta fada tana tsame ragowar cincin din ta zuba a collender tace "Ina Haidar din shi kuma?" "Ai Inna ni yau banga Haidar ba ma kwata kwata. Kila Yaa Aliyu ne ya fita da shi." "Dan kar yazo waje na ya fice dashi to wane aikin kirki zai da yaro dan Allah." "Nima dai ina mamakin ta yadda yake aiki da Haidar." "Hmmm ai dan kar yazo min nan ne nima ban neme shi ba suje can su karata sai fa nai wata ban saka yaron nan a ido na ba ko zai zo gaishe ni bai zuwa dashi." "To kiyi hakuri Inna zan kawo miki shi anjima." "A'ah A'ah bar mishi tinda bai so yazo waje na." Suka zauna suna hira har akai la'asar Maryam ta koma dan tasan Ummi ta dawo a lokacin ai kuwa ta dawo tana sama tana watsa ruwa dakin Ummi ta shiga rike da kudin da farouk ya bata. Ummi ta fito tace "Yan makaranta an dawo?" Kai ta gyada tana murmushi tace "Sannu da zuwa." "Yauwah ya makarantar da jarabawa?" "Alhamdulillah." "Ince tai sauki." Murmushi ta saki tace "Sosai Ummi." "To Allah bada sa'a." "Amin nagode." Ta fada tana mko mata kudi "Na menene?" "Dazu Yaa Farouk ne ya kai ni shine ya ban wannan kudin." "To angode." "To Ummi ki amsa." "A'ah ki ajiye a wajen ki." "To ni ki ajiyen." "To nawa ne?" Kirgawa tayi ta fada mata tace "Dubu biyar ne." "Angode." Ta amsa ta saka a cikin dorowa Maryam ta mike tace "Me za a dafa?" "A'ah ke da zaki karatu." "Ummi gobe ba jarabawa ko da dare nayi." "To kije kiyi abu mai sauki." "To Ummi." Ta juya ta fita. Ummi ta shirya ta sauka tare suka gama abincin suna gyara kitchen su Aliyu suka dawo. Da gudu Haidar ya rumgume Ummi ya sake ta yayo wajen Maryam ta dauke shi tana fadin "Haidar." Ya hau mata dariya ta dire shi tana fadin "Na kusa daina daukar ka nauyi kake karawa wallahi." Ummi tace "Haidar din." "Allah Ummi baki ji yadda ya kara nauyi ba." Dariya Ummi tayi tace "Dan dai baki saba ba amman da ace nacewa ne dashi da kullum yana goye a bayan ki fa." "Ai nagodewa Allah." Ummi ta dauki Haidar suka fice Maryam ta karasa aiki. Aliyu ta sama a falo yace "Ummi ya gidan?" "Alhamdulillah ya aiki?" "Alhamdulilah." Yai shiru yana so ya tambayi ya exam kuma baya so can yace "Ina Maryam ya jarabawar tata?" "Bari ta fito ta fada maka." "A'ah Ummi kema ai nasan ta fada miki...." Sallamar Maryam ce ta sa yayi shiru ta shigo tace "Ina yini Yaa Aliyu." "Lafiya lou." Tai hanyar sama. Ummi tace "Zo ki fada masa ya jarabawar mana." "Ummi alhamdulillah." "To Allah bada sa'a." Ya fada ta amsa da Amin itama ta haye sama. Haka suka cigaba da jarabawar acan ta hadu da wata yarinya Jawahir yar minister ce tana son Maryam duk da Maryam bata sake da ita ba amman ita ta makale mata har number Ummi ta amsa a wajen Maryam dan suna gaisawa bini bini in ba exam kuwa ta kira ta su gaisa. * Sati uku sukai suna jarabawa suka gama tayi jamb sai zaman jiran result. Haidar kuwa lokacin ya yaye kan sa sam ya daina shan nono sai kayan da Aliyu ke siyo masa ga tafiya ko ina yana iyawa dan a lokacin ya shiga shekara daya, yaron gwanin sha'awa ga farin jiki gashi duk abinda aka saka masa kyau yake masa ga fara'a ga kyau kamar shi yayi kansa. Maryam ma in yana bacci ta zuba masa ido ko in yai wani abu dan sosai yake kama da Abban sa. Shiyasa take jin wani son sa a zuciyar ta na daban. Satin da suka gama jarabawa Ummi ta siya mata waya mai kyau da tsada ai kuwa Jawahir ta fara kira ta bata number sannan ta fita nunawa Inna. A falon Inna ta samu Farouk yana cin abinci ta shiga da murnar ta tana ganin sa tai kasa da kan ta ta karasa wajen Inna tana fadin "Inna kinga wayar da Ummi ta siyon." Amsa Inna tayi tana fadin "Kai masha Allah. Allah yasa rai akaiwa." "Amin." Farouk ya dago yace "Ni ba za a nuna min ha." Mika masa tayi ya amsa yai danne danne sannan ya mika mata yace "Allah sanya alheri bari na saka miki kati." Sai jin karar shigowar sako tayi tana dubawa taga dubu biyar ya saka mata tace "Nagode." Sannan ta mike ta koma bangaren Ummi. Tana falo tana danne danne su Haidar suka dawo yayo wajen ta a guje yana fadin "Oyoyo." Ta rumgune shi tana fadin "Zo ka taya ni murna Ummi ta sai mana waya." Aliyu dai daki ya shige nan suka hau hotona ita da Haidar har Ummi ta sauko yayi wajen ta. Satin su daya da yin Jamb result ya fito ta samu 250 daman medicine ta cike ana haka wanda wata daya da gama exam shima ya fito tana da A guda biyar sai B guda hudu murna wajen Maryam kamar me? Ummi ma ta tayata murna sosai haka ta dauki dan ta tana ta juyi dashi. Da dare Aliyu na zaune a falo Ummi ta shiga dakin Maryam lokacin Haidar yai Bacci Ummi tace "Kin nunawa Yayan naki kuwa jarabawar?" "A'ah Ummi." "To kije ki nuna masa kinji." "To Unmi." Ta mike ta saka hijab akan kayan baccin ta sannan ta fice ta sauka kasa hannun ta rike da waya da takardar. Da sallama ta karasa ya amsa ta zauna a kasa tare da fadin "Ina yini?" "Lafiya lou." Ya fada shiru tayi sai kuma ya mike zai bar wajen murya na rawa dan ganin ko kallon ta bai ba kuma yake kokarin mikewa tace "Daman jarabawar muce ta fito shine na kawo maka." Hannu ya mika, ta miko masa ya kalla yace "Allah sanya alheri." Yasa kai yai cikin dakin sa. Da kallo ta bishi wayar ta ce tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dan haka ta dauka tace "Ya dai yan mata." "kin dubo exam?" "Na dubo A5 B4" "Masha Allah nima yanzu aka dubo min amman ni da C." "Masha Allah Allah sa albarka.". "Amin dan Allah kice a kawo ki makarantar da na cike." Murmushi Maryam tayi tace "Sai yadda su Ummi suka ce." "Ke dai bakya so mu hadu ko?" "Bani da kawa ko daya sai ke kinga kuwa ai zan so mu hadu tare amman ban sani ba a jamb ai can aka cike in Allah yayi sai kiga nazo nan din?" "To shikenan Allah yasa su kawo ki nan mu hade." Tace "Amin" Aliyu ne ya fito ya shiga kitchen ya dauki abu tana falo suna waya da Jawahir har ya koma itama tai sama ta kwanta bayan ta tofe su da addu'a. Basu san komai akan harkar karatun nata ba dan lokacin har an fara addmision har Maryam ta fitar da rai, Ummi kuma a lokacin tana busy dan akwai wani case dake hannun ta wanda bata zama kullum tana aiki akan sa duk da abin na ranta amman sai ta sha'afa in tana son ta tambaye shi. A haka ne Aliyu yai tai mata ciko ciko ba tare da sanin ta ba sai kiran ta da yayi kawai ya bata admission letter da kudin registration *Page 1/2* ~Flash back finish~ *Allah jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani Amin.* *Antty*[11/26, 18:57] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 57 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ~Cigaban labari~ Da dare, Ummi, Abba da Maryam suna zaune a falo, Maryam na kwance akan three sitter an saka mata karin ruwa, bacci take sama-sama, sai Abba da Ummi dake magana akan zuwan Muhammad, wayar Abba ce tai kara Ummi ta mika masa ya amsa, wanda karar wayar yasa Maryam ta bude idon ta a hankali, sai kuma ta mai dasu ta rufe. Abba ya dauki wayar yace "Muhammad ka karaso to ka shigo mana." Da sauri Maryam ta bude ido tana kallon Abba to wanne Muhammad din? Ido ta mayar ta rufe dan wani bacci ke son dibar ta dan har da allurar bacci akai mata saboda ta samu hutu da nutsuwa dan jinin ta har ya hau. Ummi tace "Ai bangaren Abbi zaku ko?" "Eh bari na kira naji ya dawo?" Sallama Muhammad yayi ya shigo, su Ummi suka amsa masa ya karaso ya durkusa ya gaishe da Ummi da Abba suka amsa Ummi tace "Zauna mana." Kan sa a kasa yace "Ummi nan ma yayi." Ya zauna a gefen carpet, Maryam ya saci kallo yaga yadda idon ta ke motsi alamar ba baccin take ba bude idon ne bata so, Ummi ya kalla saboda Abba na waya yace "Ummi bata da lafiya ne?" "Eh bata jin dadi." "Allah sauwake." "Amin mungode." Abba ya gama waya yace "Tashi muje." Muhammad ya mike yabi bayan Abba, har cikin babban falon sa suka karasa, ya zauna akan carpet, Abbi yace "Ah Muhammad yi zaman ka akan kujera." "Nan ma ya isa." Ya fada yana gaishe shi. Abbi ya amsa sannan yai gyaran murya, zai magana kenan Farouk ya shigo, ya gaishe da su Abbi sannan ya mikawa Muhammad hannu ba yabo ba fallasa suka gaisa, gyara zama yai shima akan carpet, Abbi yace "Muhammad mun kira ka ne akan Maryam, hakika wani lokacin ina manta alakar mu da ita domin mun dauke ta tamkar yar cikin mu, zan iya ce maka tafi wasu ya'yan namu a wajen mu, yarinya ce mai ladabi da biyayya wacce take da addini da ilimi, mai son kyautatawa kowa bata da hayaniya bare fada tin zaman mu da ita a gidan nan na sama da shekara hudu ban taba jin wani yace tai masa abu na batanci ba sam, kullum cikin kyautatawa mutanen gidan nan take, duk wanda ya samu Maryam ya dace kuma ya samu babba rabo. Ba ina fada maka haka bane dan na yabeta ko in kara maka son ta ta yadda zaka kara kwadaituwa da ita ba, sai dan naga kai ma kana da hankali in har haka zata faru zamufi kowa jin dadi dan fatana kenan Maryam ta samu me rike ta tamkar tana hannun mu bana son tai maraicin komai da kowa." Abbi ya dakata Muhammad kan sa na 'kasa sai yanzu ya gane cewa Maryam ba yar gidan nan ba kila yar kanin su ko wansu ce, kila iyayen ta ne suka mutu. Maganar Abba ce ta dawo da shi daga tunanin da yake, "Mun tsinci Maryam shakara hudu da wani abu da suka wuce a garin Bauchi lokacin munje wani aiki da mai daki na akan hanyar mu ta dawowa muka bige ta wannan dalilin yasa muka kai ta asibiti, dole mu tsaya akan ta muga yanayin jikin ta wanda a dalilin haka muka kwana a asibitin duk da cikin dare ne amman da mai daki na ta bukaci ta kira gida sai muka gane bata da kowa, ko kuma nace tamkar ta rasa komai na tunanin ta, dan bata tuna kowa sai mutane biyu a rayuwar ta da muka tambaya ina suke kuma bata sani ba, gashi kuma bata magana, a wannan halin da muka same ta muka sa likita ya bincika mana lafiyar ta wanda anan muka gane matsalar ta na da yawa tana da ciwon zuciya, ga damuwa, kuma rashin magana ma razana ita ta dauke mata ita sai abu na karshe shine tana da cikin watanni wajen uku." Da sauri Muhammad ya dago, Abba ya gyada masa kai, sannan ya cigaba da magana "A gaskiya a halin da muka ganta ba zamu iya barin ta ba dan tana fama da laulayi kuma tana bukatar kulawa wannan yasa mai daki na ta bukaci mu taho da ita, haka muka zo da ita gida mukaci gaba da kulawa da ita ta sha jiki wanda daga baya Allah ya bata lafiya har ta haifi yaron ta Aliyu Haidar, a haka mukaci gaba da rayuwa da ita kuma har yau bata tuna komai game da bayan ta, muna jin dadin zama da ita dan mun dauke ta tamkar yar cikin mu, bana baka labarin nan ne dan ka taimaka mata ba, in har kasan wani abu ya taba zuciyar ka, ko son da kake mata ya ragu, ko ka fara zargin wani abu dan Allah ka janye tin bata fada tarkon son ka ba, da farko ya kamata mu sanar maka to matsayin ta a wajen mu ya mantar damu dan ji nayi tamkar Najwa aka zo nema aure, bana son Maryam tai kuka akan wani abu a rayuwa, kullum addu'a Maryam ta tuno gida dan dole wata rana za ta so sanin asalin ta, duk da mu bamuce mu ba nan asalin ta bane muma asalin tane kuma gatan ta, na fada maka wannan saboda aure kazo nema a aure ba a karya." Jikin Muhammad sosai yai sanyi ya rasa me ma zai yi ya rasa tunanin da zai yi zuciyar sa kuwa sai dukan uku uku take, Farouk kuwa ransa ne ya baci, dan me za a zo a fadawa wani na waje wannan bayanin dan yaje ya yayatata kila ya guje ta kila yaje yai mata wani sharri shi in ta shine sam ba za ai wannan abun ba shiyasa yaso ya aure ta ko dan rayuwar ta ko dan gudun wannan alamarin amman ina tayaya bayan Mama ta lalata komai tayi Allah ya isa a duk lokacin da ya aikata haka dole ya hakura ba dan baya son ta ba sai dan samun ya rabauta amman yana ji yana ganin sam ba zai taba yadda wani ya wulakantata ko yaci zarafin ta ba tabbas sai inda karfin sa ya kare. Dakin ne yai shiru kamar ba kowa a ciki, Abbi yace "Kaje kai tunani Muhammad ba ai maka dole ba kai kazo neman auren ta haka ba zamuce kada ka janye ba kaje kai tunani sosai akan lamarin." Kai ya russuna sannan ya mike yace "To Abba, amman ni ina ganin ba wani tunani da zanyi, duk da haka ina son ta." Kai Abbi ya girgiza yace "Kaje dai kayi sosai kaga in da yiyuwar abun." "To shikenan ina godiya Allah ya saka da alheri." "Amin Amin." Ya durkusa yace "zan tafi." Abba ya kalli Farouk yace "Raka shi Umar." Farouk ya mike Muhammad yabi bayan sa a haka suka karasa har wajen motar sa, Farouk ya kalli Muhammad yace "Muna son kanwar mu ba zamu lamunci bacin ran ta ba, a dalilin ka ciwon ta ke son tashi, in har kasan haka zaka cigaba da sa rayuwar ta a matsala to kada ka soma shiga cikin rayuwar ta dan ba zamu lamunci wannan ba." Wani Murmushi Muhmmad yayi yace "Da da cuta nazo ga Maryam bazan fito ba, hakika ina son ta kuma ita ce rayuwa ta kuma damuwar ta ta wace dan haka kar ka damu akan wannan fata na ka tayani addu'a Allah ya bani ita dan naga alamun ita din mai sa'a ce gwana ce kowa so yake." Yana fadar haka ya shiga cikin mota yace "Nagode Bro in-law." Ya daga masa hannu ya fice, Farouk yabi sa da wani banzan kallo sannan ya koma wajen su Abba. Suna zaune suna tattaunawa Farouk ya zauna yai kasa da kai yace "Amman Abba sai naga kamar bai dace a fada masa ba tinda bamu san irin son da yake mata ba kada yaje ya yayata mana yar uwa kasan mutane." Murmushi Abba yayi yace "Kada ka damu, ina ji a jikina Maryam daga babban gida take kuma koman daren dadewa zata koma gida kuma gaskiya zatai halin ta naji na yadda da ita dari bisa dari so komai zai faru da ita kadaddar ne Allah bata ikon cinyewa." "Amin." Ya fada, Abba ya mike yace 'Bari naje sai da safe, " Abbi shima ya mike yace "Muje naga jikin nata." Farouk ya mike yabi bayan su.. Tana zaune, dan ba a jima da cire mata karin ruwan ba, gaban ta bowl ne na farfesu, da Ummi ta kawo mata, amsa sallamar su Abba tayi suka shigo suka zauna, Abbi yace "Ya jikin 'ya ta?" Kanta a kasa tace "Da sauki Abbi." Farouk yazo ya zauna kusa da ita yana fadin "Yar gatan Ummi ni ina nawa?" Ya dauki spoon ya dauki tsoka ya kai bakin sa, ido ya lumshe yace 'Uhmm dadi." Abbi yace "Kai baka kawo mata ba kazo kana cinye mata ko?" "Yanzu zanje na kawo mata ta fada min me take so?" Kai tai kasa dashi, Abbi yace "Yakamata kasan me take so ai ba sai ka tambaye ta ba." Abba yace "Ai kasan in mutum bashi da lafiya yana canja abinda yake so ko?" Abbi yace "Haka ne 'ya ta me kike so?" Kai ta girgiza, Tace "Ba komai Abbi." Ummi ce ta fito daga kitchen suka gaisa da su Abba ta zauna tana fadin "Kici ko kyaji dadin bakin ki." Farouk ya dau spoon ya kara ci yana fadin "Bari na bata." Ya dauki guda daya ya mika mata ta amshi spoon din ta kai bakin ta ta fara ci, su Abbi sun jima sannan suka tafi. Maryam ma sama tayi tana shiga taga wayar ta tai haske dauka tayi taga missed call din Muhammas guda goma, sai message guda biyu zama tayi ta fara karantawa na farko ya rubuta "Kin ban mamaki Maryam da kika kasa gane da wa kike tare, na fada miki ina son ki kuma da gaske nake son ki ba da yaudara ba kina zaton wani abu zai raba mu ba abinda zai sa son ki ya fita a raina ko yaya kike ko me kika aikata bare wannan bansan kaddarar da ta baro ki da gida ba kuma ban sa a rai na cewar marar kyau bace ina kallon ki da son gaskiya ba zan taba saka zargi a tsakanin mu ba ki sani Muhammad na son ki da duk zuciyar sa da rayuwar sa." Hawaye taji yana zubo mata bata taba jin son sa irin na yanzu ba dayan sakon ta bude ta fara karantawa "Wallahi ba yaudara a zance na ki bani dama zan zame miki duk abinda kika rasa zan kasance dake a duk runtsi dan Allah ki bani dama." Sai na ukun da yake fadin "Ki dauki waya ta dan Allah Baby." Ido ta runtse hawayen dake idon ta ya hau zubowa, kwanciyya kawai tayi dan zuciyar ta ta fara raya mata wani abu kar taje tausayin ta kawai Muhammad yake ji shiyasa ba zai barta ba ita sam bata so. Da irin wannan tunanin bacci ya dauke ta. * Washe gari da safe tana kwance bayan tai wanka ta canja kaya, Ummi ce ta bude kofar ta shigo rike da tray ajiye tayi ta karasa tana taba jikin Maryam, ido ta bude, mikewa tayi tace "Ummi." Ummi ta kamata ta mikewa tace "Ya jikin?" "Da sauki.' Ta dauko tray ta mike mata cup, amsa tayi ta kurba ta bude bowl din da ta hada mata dankali a cikin kwai, fork ta dauka ta bata ta amsa taci sai da ta ci da yawa sannan ta ajiye plate din, magani ta dauko, Maryam ta bata fuska, Ummi tace "Please kike daurewa daughter bana son ina ganin ki a haka." Amsa tayi ta runtsa ido ta sha, Ummi ta hau shafa mata baya, lamo tayi a jikin Ummi sai da ya tsarga mata, sannan ta kwantar da ita ta mike ta fita, tana fita wayar Maryam ya hau kara da farko ta zata Muhamamd ne amman tana dubawa taga Aliyu ne, dauka tayi ta kwanta, muryar sa tajiyo yai mata sallama, wanda sai da ya haifar mata da faduwar gaba, dan yadda taji muryar tata har cikin kwakwalwar ta tsigar jikin ta ta tashi, ido ta lumshe tana amsawa, yace "Ya jikin naki?" "Da sauki." "Allah kara sauki." "Amin." Sukai shiru sai kuma yace "Kan na tafi na farai miki magana akan Muhammad, kinga abinda kika jawowa kanki ko? Kina zaune lafiya kin dauko wanda yake shirin ruguza miki rayuwarki, ki kula, ki sani ba kowa ke da gaskiya ba wani yana son ki ne dan wani abu naki ko makamantan su, dan haka ki kiyaye ki ajiye wasa ki nemi wanda kike so baki sani ba ko shima yana son naki." Ido ta lumshe yace "Zaki ce baki da lafiya na cikaki da surutu ko? To gwara na ja miki kunne tin yanzu." Yana fadin haka ya kashe wayar bata ji komai a ranta ba dan tasan kusan gaskiya ne amman ita to wa take so da zataje ta fada masa har shima kuma ya amshe tan? Juyi tayi kawai bacci ya dauke ta. Tana kwance a falo akan doguwar kujera Ummi na kusa da ita akai knocking mai aiki ta leka sai ta dawo ta durkua tace "Ummi wai Muhammad ne." "Je kice ya shigo" Ta koma ta fada sai gata ta shigo dauke da manyan ledoji guda biyu, Ummi ta gyara yafen mayafin ta Maryam kuma ta mike zaune, tana gyara hijab din ta. Muhammad ya shigo sanye da Shadda Ash kala har da hula ba karamin kyau yai ba kamshin shi ya cika dakin, zama yayi a kasa ya gaishe da Ummi, Ummi ta amsa yai mata ya me jiki sannan ta mike. Mai aiki ce ta kawo masa ruwa da lemo. Maryam na zaune kan ta a kasa tace "Ina yini?" "Lafiya lou My wife ya jikin?" "Da sauki." Ta fada taba rufe fuskar ta da hijab din jikinta, murmushi yayi yana kallon ta yace "Allah kara sauki." Ya matso yana fadin "Magana nazo muyi." Dagowa tai ta kalle shi, yadda yake zaune a gaban ta kamar dalibi da malama. Tace "To ka tashi ka zauna akan kujera." "A'ah nan ya isa." Ta langwabar da kanta. Yace "Me yasa kika kasa fada min?" "Ba zan iya ba bansan ta ina zan fara ba." "Amman ai kinsan ina son ki." "Na sani amman kasan rayuwar nan, wani akan abu kadan zai iya rabuwa da wacce yake so." Kai ya girgiza yace "Sai dai in baya son ta." "Ko yana son ta sau nawa akayi." "Ba son gaskiya yake mata ba, ni kuwa son ki nake yi da gaske, ban da buri da ya wuce naga na mallake ki da ana bude zuciya da kinga abinda yake ciki wallahi Maryam da gaske ina son ki." Dagowa tai tana kallon cikin idon sa, sam a da bataji tana son sa ba kamar a yanzu da ya amshe ta a yadda take amman me sai take tantama dan Aliyu ya sake saka mata tsoro dazu. "Tunanin me kike dear?" Kai ta girgiza tana fadin "Ba wai ban yadda da kai bane, amman tabbas nasan tausayi na ne ya rinjaye ka." "Kar kice haka Maryam duk inda so yake to da akwai tausayi a cikin sa, amman ni da gaske son naki nake kuma ina tausayin ki, in kin ban dama ko yau zan turo magabata na ai mana aure Maryam sai ki yadda cewa da gaske ina son naki." Kai ta dauke daga kallon sa yace "Baki yadda ba ko?" Kai ta girgiza tace "Na yadda da kai." Murmushi yayi yace "Yauwah my love ina yaro na." "Yana wajen Mami." Matsowa ya kuma yai yace "Banga kin sake dani ba, please ki ban dama in nuna miki yadda nake son ki da kaunar ki." "Na baka dama ba tin yau ba tinda har na baka damar zuwa ga magabata na." "Nagode My love kwana biyun nan nasha wahala na rashin ki dan Allah ko da zamu samu sabani kada ki kara hukuntani da kashe waya ko kin daukar wayata ta kinji?" Kai ta gyada yace "Yauwah to dago ki min murnushin ki mai kyan nan." "A falon Ummi dai muke." "Ai dakin Ummi nane ni fa ban san wani sirika ba." Tai murmushi tace "Wato sirikin zamani ne a dakin sirikar sa ma soyayya zai yi." "To menene a ciki?" "Ah babu." Yai murmushi yace "kema zakiyi a dakin Ammi" Gaban ta ne ya fadi jin ya ambaci Ammi, dakewa tayi tace "Dan kai baka da kunya nima bani da ita?" "Eh saboda zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin....' "Ban dani.' Yai dariya yace "Har dake." Ta sunkuyar da kanta. Farouk ne ya shigo, ganin Muhammad zaune a gaban Maryam ya bata masa rai, fuska ya hade yai kicin kicin, ya karaso, duk suka juyo ya zauna a kusa da Maryam yana fadin "Ya jikin my sister?" Ta dago tana fadin "Da sauki Yaya ya aikin?" "Alhamdulillah zan dawo na biya na siya miki fura since yesterday Abbi na min dan biki wai bansan me kike so ba." "Kai amman nagode daman tin dazu nake tunanin me zanci baki na ba dadi." "Ah ai suya zakici bari ai magarib zan kawo miki." "Thank you swt bro." Ya mike yana fadin "Ummi fa?" "Tana sama." Har ya juya tace "Yaya kaga fa." Ta nuna masa Muhammad dan kallon sa yayi yace 'Ai banganshi ba." Ya dan daga masa hannu yace "Ya kake?" Muhammad ya dago ya kalle shi yana fadin "Alhamdulillah ya aiki?" Gaba yai yana fadin "Alhamdulillah!" Ya juya yai sama. Maryam ta kalli Muhammad dake danna waya fuskar sa ba yabo ba fallasa, tace "Ya dai?" Ya dan dago ya kalle ta yace "Ni me yasa baki fadan kina son wani abu ba." "Ni ba wani abu fa nake so ba." "Gashi nan shi da yake dan uwanki, kin fada masa." "Kai dear rigima." "Ba wani rigimi, please ki dauken a matsayin Yayan ki, abokin ki, kuma mai sonki, komai kike so ki fada min kinji as bro, friend and ur love kar kiji kunyar komai am always there for you." "Thank you so much dear." Ya dago ya dan kalle ta tai saurin dauke idon ta yai murmushi yace "Bari na tafi magariba nayi." "Nagode sosai a gaishe da su Ammi." "Zataji insha Allah." Ya mike yace 'Kicewa Ummi na tafi." Kai ta gyada ya juya ya fita, furar ta dauka ta dauki spoon ta fara sha, Farouk ne ya sauko yace "Yan mata kin gama zancen?" Baki ta dan turo tace "Ni ba zance nayi ba." "To me kikai?" "Dubani fa yazo oh baka sanshi ba ko? Abokin Abdul ne kuma yayan Jawahir." Baki ya tabe yace "Ko?" Kai ta gyada yace "Yayi kyau." Ya fita a dakin. Roba daya ta sha ta ajiye sauran a firij ta hau sama dan tayi alwala. Yadda take samun kulawa daga yan gidan nasu da Muhammad yasa nan da nan ta warware dan kowa na kokarin ganin ya dauke mata kewa da damuwa, Aliyu yana kira da safe da dare, duk da in ya kira ba wani hira suke ba karkari su gaisa ya tambayi Haidar tana ganin su zasu sha hira na rabin awa har na awa daya. Duk da haka tana da damuwa wacce in ka titsiye ta ba zata fada maka ba abinda ke damun ta ba, dan tin tafiyar Aliyu take jin ta wani iri, a haka sukai exam wanda ita kanta tasan ba zata samu abinda ta saba samu ba dan ba karamin damuwa take ciki ba bata iya zama babu tunani da haka suka gama jarabawa suka samu hutu. Kana ganin Maryam zakaga ta kara ramewa saboda rashin nutsuwa, wannan yasa Ummi tace taje gidan Sitti ko ta samu sauki, ai kuwa zuwan ta gidan ya dan rage mata damuwa dan Sitti na mata nasiha da bata nishadi haka nan da Najwa ta ganta a damuwa zata sa su fita zaga gari sune wannan park din sune wancan wani lokacin Abdul da Muhammad ne suke kai su. Matsalar ta daya tin da tazo gidan Sitti basuyi waya da Aliyu ba wani lokacin tana zaune suke waya da Sitti sai sun gama zata hau tambayar ya yake? Sitti ta kanyi murnushi tace "Kira ki tambaye." Sai dai tai murmushi kawai, satin ta biyu ta koma gida suka fara shirin komawa makaranta, wanda a lokacin bikin Najwa saura wata daya, satin su biyu da komawa suka fara rabon katin bikin Nawa duk bata da lokaci dan wani lokacin daga makaranta suke wucewa ga shirye shirye da suka faman yi. Najwa taso Maryan ta dawo gidan Sitti har ayi biki amman tace sai an fara zata taho wannan yasa ta ma daina kiran ta da yake sun gama rabo, ko an kawo musu dinki bata kira ta fada mata balle ta nuna mata, ita kuma Maryam har da rashin kiran Aliyu da bata so tayi kewa dan ko banza in tana gida zai kira kuma zasu gaisa ko da kuwa Haidar zai wa magana, kuma in ya kira Ummi bai samu ba zai kira ya aike ta, to ita ta rasa meyasa take so taji ya kiratan, dan in suka kwana biyu basuyi wayar ba tai ta damuwa kenan, gashi in ta zauna tai ta tunanin sa, tana zaton ko dan yadda yake taimaka mata ne dan duk da baya gari duk wata da kudin, zuwa makaranta da na shopping dinta ita da Haidar har extra yake dada nata to ita kuwa me zatace da Aliyu in ba godiya ba, wannan yasa kullum bata da aiki sai tunani wani lokacin bata sanin ta fara tunanin sai an kirata bata amsa ba. Jawahir tai fadan har ta gaji dan wani lokacin ma ko lecture suke haka take zubawa allo ido tai ta tunanin da bata san tushen sa ba. Shiyasa yanzu take a kare ko da yaushe Ummi tayi fadan tayi nasihar amman duk a banza sai abinda ya dadu in kana son kaga farin cikin ta to taga kiran Aliyu har zumudin dauka take yi. Ranar da zasuje lalle tana zaune a daki tayi nisa cikin tunanin da take Najwa ta shigo, tsayawa tayi a bakin kofa tana kallon ta, tafi minti biyar amman bata sani karasowa tayi ta zauna a gefen ta sannan ta dago tana fadin "Yaushe kika shigo?" "Kina can tunani tayaya zaki sani." Tai murmushi sallamar Jawahir suka jiyo suka amsa ta shigo, Najwa tace "Akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar min." Jawahir tace "Abinda nake fada kenan kullum ban taba boye mata komai ba amman ita ta fiya zurfin ciki." Shiru tayi tana tunanin me za tace masu can dai tace "Najwa da Jawahir ba haka bane." Murmushi Najwa tayi tace "Kin fada soyayya to saboda me kike tunani ko ba wanda kike so bane ya kawo kansa." Kallon ta Maryam tayi, "Yanayin ki na nuna wani kike so kin kasa fada rashin shi ke saki a damuwa. Haka ne?" Jawahir ta fada, gaban Maryam ne ya fadi shin da gaske ne halin da take ciki to wa take so din. Dafata Najwa tayi tace "Menene ki fada mana." Hawaye suka soma zubawa a idon Maryam dan ta rasa madafa. *Allah ya jikan musulmai Allah kyautata namu zuwa yasa muyu kyakyawan karshe Amin.* *Antty* [11/26, 18:57] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 58 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Wayar ta ce tai kara da kamar bazata dauka ba sai kuma ta janyo ta ganin sunan dake kan wayar yasa tai saurin goge idon ta tare da danna received ta kai kunnen ta "Assalamu alaikum." Taji yai sallama ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya ta, dan a duk lokacin da zataji muryar Aliyu ita kadai tasan me take ji, a hankali ta amsa da "Wa'alaikum ssalam." Ido ta runtse tai shiru, shima shiru yayi sai can yace "Me ya samu muryar ki?" Shiru tayi yace "Kuka kikai ko?" Kai ta girgiza kamar yana ganin ta. Yace "Karya kike kinyi kuka." Mikewa tai ta fita yace "Ummi fa?" "Tana gidan Sitti." "Ke fa?" "Ina gida." "Ke da wa?" "Ni da Najwa zamuje lalle ne." "Haidar fa?" "Yana wajen Inna." "To sai anjima." Sukai sallama ya kashe wayar dakin, Ummi ta shiga ta wanke fuskar ta sannan ta fito ta koma daki. Jawahir da Najwa suna hira ta shiga tace "Muje ko?" Suka mike suka fita. Daga lalle saloon suka wuce sai dare suka koma gida. Da sukaje gidan Sitti ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arziki, yan garin su duk sun zo duk da washe gari za a fara biki, Maryam dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane. Suna zaune sukaji an shigo da sallama, dagowa sukai suna amsawa wata kyakyawar yarinya ce ta shigo sanye da wata doguwar riga maroon kala sai dan mayafi da ta yafa hannun ta rike da waya da jakar ta, Najwa ce ta mike a guje tana fadin "Tasleem oyoyo." Dagowa Maryam tayi tana kallon ta, Tasleem ta huging Najwa tana fadin "Amarya ta sha kamshi." Sai ta kalli yan dakin, hannu ta daga musu tace "Sannun ku." Maryam tace "Yauwah sis ya hanya?" A share ta amsa da "Ahamdulillah." Jawahir ta mike tace "Ni tafiya zanyi." "Waye zai kai ki gidan?" "Yaa Muhammad." "Nima gida zan tafi." Najwa ta juyo tace 'Saboda me?" "Gidan ya cika ni gwara na koma wajen Ummi kema kizo mu tafi." "Amman nan yafi in na tafi can ma sai na dawo nan." "Shikenan gobe nazo." Ta mike tace "Jawahir muje ku ajiye ni." Babu yanda Najwa bata yi da ita kan ta zauna amma taki, lokacin da taje wajen Sitti sallama ta zauna Sitti ta kalle ta taga yadda take yamutsa fuska, Sitti tace "Ko dai za ki wuce gida ne?" Kai ta gyada Sitti tace "To waye zai kai ki?" Kai tayi kasa dashi tace "Muhammad ne zai kai Jawahir gida sai ya ajiye ni." Sitti tace "To tashi ki je, sai da safe." Tunda Maryam ta fito Muhammad ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau." Jawahir ta shiga gaba ita kuma ta bude baya ta shiga ta zauna tare da jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lokaci lokaci Muhammad ke satar kallonta sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai gate din gidansu yayi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode" Ta kalli Jawahir tace "Thanks Sis sai goben." "Allah kaimu." "Amin." Ta juya ta shiga gida, tana shiga taji sako ya shigo wayar ta bata duba ba ta shiga gani tayi har Ummi ta rufe kofa knocking tayi, Ummi ta sauko tana tambayar waye. Tace "Ummi nice." Budewa tayi tabi Maryam da kallo tace "Daga ina?" "Ummi ba zan iya kwana ba." Hanya Ummi ta bata tace "Allah ya shirya ki duk fa yan uwan ki ne." "Ummi ni ba haka bane yasa na kasa ba, kawai gida nake so." "To ai shikenan." Ta wuce sama, wanka tayi ta fito ta kwanta wayar ta taji tai kara ta dauka ta kai kunne yace "Dear kinga yadda kikai kyau kamar kece amaryar." "Kai ina wani kyau." "Hmmm wallahi baki gani ba, gaskiya ina jin ba zan iya jimawa ba tare dake ba, ina son ki Baby, ina son kasancewa dake, please Baby ki so ni ko daya bisa darin da nake son ki ne." "Kana son kana dawo da abu baya, kullum ina fada maka ina son ka ina sonka." "Na sani amman bai kai kwatan nawa ba yadda nake jin ki ko?" "Meyasa kake boyewa Jawahir?" "Saboda ina son nai mata surprise nan gaba kadan lokacin da za a zo tambayar aure a lokacin zata san wacece matata nasan zataji dadi sosai." "Uhmmm." "Eh ko ya kika ce." "Yayi." "Bari na barki kiyi bacci, saboda gobe nasan kila da wuri zaki tashi, zakuyi kamu ko?" "Eh." "Allah kaimu." "Amin." Sukai sallama ta kwanta. Da wuri kuwa ta tashi. Washe gari kamu, da safe yan UK suka sauka, su Momy, da ya'yan ta Yasmeen da Basma, Yayar Ummi ce, dan haka a gidan Ummi suka sauka dan gidan Sitti a cike yake da mutane, duk da Maryam da Basma basu taba haduwa ba amman Basma na ganin ta ta rumgume Maryam tana fadin "Sister." Sama suka nufa, a daki suka zauna suna hira tamkar wanda suka taba ganin juna wanda iyakar su waya ne ko vedio call, a gida suka yini dan sai yamma mai make up tazo har gida Basma tayiwa, Maryam da farko cewa tayi ba zatayi ba sai da Momy ta sa baki sannan tace ai mata light make up. Ta saka wani jan material, dinka riga da siket duk yanda mutum ya kai ga hassada ba zai kushe Maryam ba a wannan rana takalmi da jaka bakake tayi amfani dasu, fitowa sukai dan su Ummi duk sun riga da sun tafi. Waya Maryam tayiwa Jawahir take fada mata an kwashe kowa suma yanzu suna hanya, compound suka fita dan ta kira driver ya kai su, suna fitowa gaban ta yai wata mummunar faduwa saboda hango Aliyu da tayi a compound din gida, Basma dake waya ta karaso tana fadin "Waye zai kai mu?" Kasa magana Maryam tayi, dan kallon Aliyu dake sanye da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi yai kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran tashi kuwa kamar wacce aka dasa, ji tayi kamar ta juya sai kuma ta dake tunda bai ganta ba. Wata mota ce ta shigo compound din Basma tayi gaba, Aliyu taiwa magana sannan ta karasa wajen motar da ta shigo ta tsaya, gaba Maryam tayi zata wuce. Wanda ya ke driving ne ya fito yana kallon Najwa, kofar da take ta mai zaman banza ma aka bude wani kyakyawan saurayi ne ya fito, gaisawa sukai da Basma, har Maryam zata shige Basma tace "Sister meet Fauwaz." Juyowa tayi ta dan kalle su, tace "Sannun ku da zuwa." Suka fara gaisawa dayan da yake abokin Fauwaz ya zuba mata ido, kai ta dauke ta kalli Aliyu wanda yayi wani kicin kicin da fuska kamar ba zata gaishe shi ba sai ta daure tace "Ina yini?" "Lafiya." Ya amsa a ciki tare da mikawa Fauwaz hannu yana fadin "Ashe kana gida." Ya mikawa dayan hannu fuska a hade suka gaisa, Gefe Maryam tayi, Aliyu ya nufi motar sa yana shiga ya fara dailing number wayar, wayar Maryam ce ta hau kara, kallon wayar tayi, ganin Aliyu yana kiran ta yasa ta dago tana kallon sa, kai ya dauke kamar bashi ke kiran ta ba, a hankali ta fara tafiya har ta karasa, batai magana ba yace "Zagayo ki shigo." Ba musu ta zagaya ta bude motar ta shiga, "Kira Basma mu tafi." Ya fada ba tare da ya kalle ta ba. Waya ta dauka ta kira wayar Basma, karasowa tai Aliyu yace "Shigo mu tafi." Fuska ta shagwabe tace "Please Yaya ka barni na tafi dasu kaga danni suka zo." "Ku biyo motata." Tace "Ok." Ya tada mota ya fita, sukabi bayansu har hall din da ake bikin yai parking zata fita ya saka lock, juyowa tayi ta kalle sa, kai dauke yace "Naga kamar kanki yana rawa ki kula, nasan Muhammad ya zo ko? Abokin Abdul ne bana so kinji ko?" Kai ta dauke ba tare da tai magana ba, hannun ta ya kamo ta juyo da sauri dan wannan ne karo na farko da Aliyu ya taba ta ba cikin wani lalura ko taimako ba, wanda daga ita har sai da sukaji wani shock, bata gama mamaki ba taji ya matsa hannun ta da sauri ta runtsa ido tana fadin "Da zafi fa Yaya." Wani kallo ya watsa mata yace "Ina miki magana kina dauken kai ni sa'an ki ne?" "Nifa ba kai na dauke ba." Hannun ta ya saki ta dago hannun tana kallon hannun har yai ja, ya kada mata yatsun hannun sa yace "Ki kula." Sannan yayi unlock din motar da sauri ta fice ya bita da kallo, wajen Basma ta karasa tace "Ke wai yaushe Yaya ya dawo?" Murmushi Basma tayi tace "Uhmm tare muka dawo ni ban so ya biyo mu ba dan nasan ba zai barmu mu sake a bikin nan ba, dama yai zaman sa." "Gaskiya." Maryam ta fada wanda iya kar sa baki ne dan kasan zuciyar ta taji dadin ganin sa, suna tsaye motar su Najwa ta tsaya, Tasleem ce ta bude gidan baya ta fito sanye da wani ash kalar material dinkin fitat gown ya kamata sosai, ta saka hill takalmi, sai jaka a hannun ta sai yamutsa fuska take, Basma ce ta saki tsaki tana fadin "Wai a haka take son Yaya ya so ta." "Wanne Yayan?" "Yaa Aliyu." Basma ta bata amsa. "Yaa Aliyu,....." Maryam ta fada cike da mamaki tana kara bin Tasleem da kallo, "Yes tinda Aunty Maryam ta rasu take son Yaa Aliyu ya aure ta, Kisan Yaya shi da fi'ili ba kowa ke burge shi ba, bare ita da bata da kamun kai duba fa ita a dole yar mai kudi acikin yan uwan ma sai ta nuna jiji da kai, zo mu tafi dan Allah." Ta kama hannun Maryam zata bar wajen, wayar Maryam tai kara tana dubawa taga Najwa dagawa tayi taji tana fadin "Ina kuma zaku, ku zo mana." Ta juyo sai taga Tasleem tayi wajen motar Aliyu bude front seat tayi ta zauna, kai Maryam ta dauke su kai wajen Najwa tayi kyau sosai, tare suka shiga hall din. A can aka kama amarya aka cigaba da shagalin biki, lokacin da aka kira yan uwan amarya gaba daya su Anty Asiya, da su Maryam, Basma suka shiga fili suka dingai mata ruwan kudi kamar basu san zafin su ba. Sai da aka kusan tashi sannan da abokan sa suka zo, tinda Muhammad yazo yake baza ido yaga ta ina zai ga Maryam, can gefe ya hango su ita da Basma, sai Fauwaz da abokin sa, karasawa yayi yai sallama suka amsa tare da gaisawa, Muhammad ya kalli Maryam yace "Ranki ya dade minti biyu mana." Basma ta kalla tace "Ina zuwa." Suka fita daga compound din Aliyu dake cikin mota ya hango su nan da nan ya hade fuaka yai kicin kicin, daman ransa ya baci, Tasleem dake waje tace "Lafiya swt Yaya?" Bai kula ta ba ya dauki waya ya kai kunne Maryam dake tsaye da Muhammad ta dauka ta kai kunnen ta, yace "Ki kira Basma zan mai daku gida." "Yaya ba fa a tashi ba kuma zamu tafi da su Ummi." "Bana son magana kije ki kirata." Ya kashe, Muhammad ta kalla, tace "Zamu tafi." "Bikin Najwan kuma tin yanzu?" "To Yaya ne." "Wanne Yayan? Farouk ko?" "Yaa Aliyu." "Ya dawo ne?" Kai ta gyada tace "Bari na kira Basman." Ta koma ciki wajen su Basma taje ta same su ta kamo hannun ta suka matsa gefe tace "Yaya yace kizo mu tafi." "Tab tin yanzu?" "Haka yace." "Gaskiya ba zan iya ba kije kice baki ganni ba." "To ni kadai a gida dan Allah." "Ai ni gidan Sitti zan tafi ma wajen su Najwa." Wayar Maryam ce tai kara tace "Wayoo kinga ko yana kira." Dauka tayi ta kai kunnen ta, tace "Yaya ban ganta ba." "To fito mu tafi." Ya kashe wayar, Basma ta kalla kamar zatai kuka tace "Kizo mu tafi." Kafada ta make tace "Kema kije kice masa a gidan Sitti zaki kwana." "Ba sai zai barni ba." "Ki gwada." Ta juya ta nufi kofa, Muhammad ta hadu dashi yace "Wai tafiyar zakiyi." Kai ta gyada tace "Ai zamu hadu gobe." "Shikenan Baby take care." Ta fita ta nufi motar Aliyu, tana bude front seat taga Tasleem zaune maida kofar tayi ta tsaya a waje, Aliyu ya kalli Tasleem yace "Zamu tafi." "Yaya nace zan biku." "No kije kwa taho dasu Ummi." "Swt bro..." "Please Tasleem sauri nake." Ba dan taso ba ta bude motar ta fito, Maryam ta kalla ta harara, Maryam ta tabe baki, bata shiga ba sai da ya kira ta, ta dauka takai kunne yace "Bazaki shigo ba." Baki ta turo ta bude motar ta shiga ya tada motar suka fice a wajen, maimakon suyi hanyar gida sai taga ya dauki hanyar asibiti, suna zuwa ya kashe motar yace "Muje." Ta bude ta fita, bayan sa tabi har suka isa office dinsa sannan ya bude suka shiga zama yayi yana duba wasu file, sannan ya mike ya fita, tana zaune a wajen har akai magariba tai sallah ita ce har bakwai babu shi har bakwai da rabi sannan ya dawo, kallon ta yayi yace "Muje." Kamar zatai kuka ta mike suka fita, daga nan gida sukai amman har lokacin su Ummi basu dawo ba, yana parking ta fice a motar tai cikin gida da kallo ya bita yana murnushin kasa kasa, masallaci ya tafi dan yaji an tada sallah, bayan ya dawo ya shiga gida ba kowa a gidan sai shi kai dai. A falo ya zauna ya fara neman layin ta, har tai wanka tayi sallah taji kiran wayar ta, ta dauka yace "Kizo ki samen a kasa." Ta mike ta fito ta karaso ta tsaya a gefe tace "Gani." "Zubo min abinci." Dining ta nufa ta zubo masa abincin ta kawo zata bar wajen yace "Zauna, " Ta koma ta zauna, yana ci yana kallo har tara saura sannan su Ummi suka dawo, Ummi tace "Ai ina ta neman ki Basma tace Yaya ya taho dake." "Eh ni gidan Sitti zani." "Ba inda zaki." Ya fada yana barin wajen. Ummi ta kalla tace "Dan Allah Ummi ki masa magana." "To yanzu kije ki kwanta ko gobe ne kya kwana a can." Kofa aka bude Tasmeen ta shigo tana tafiya da kyar ta zauna tace "Ummi ana zan kwana." "To shikenan." Maryam ta mike tai sama, Ummi ta shiga kitchen, tana zaune har wajen goma a kasa Ummi ta sauko tace "Tasleem ki shiga ki kwanta mana." "To Ummi zan hawo." "Ok ni dai na tafi, kya shiga dakin Maryam ko?" "To Ummi." Ta juya tai sama, kwanciyya tayi akan kujera tana kallo, around 11pm taji an bude kofa da sauri ta mike, tana kallon sa ta hau fari da ido, bai kalle ta ba ya dau hanyar dakin sa, tabbas da ya san zai same ta anan da ya wuce dakin sa na bangaren su, "Swt Yaya." Ta kira sa sanin halin ta sai tace zata bi sa yasa ya juyo ta mike ta karaso tana tafiya tana karairaya, kai ya dauke yace "Menene?" 'Swt Yaya please ya kamata mu zauna mu tattauna mu cikawa iyayen mu burin su." "Burin su kamar yaya?" "Tinda Anty Maryam ta rasu, Yaya me zai hana ka auren tinda nima yar uwar kace, tin ina alkunya kana gani har na daina please kai ma ka ba da kai." Fuska ya daure ya dago ya kalle ta yace "Tinda kinsan da haka ai da ina bukatar ki da tin da na nuna to bana bukatar ki, in baki sani ba ki sani bakya cikin tsarin matan da nake so, ki haska rayuwar ki da ta Maryam ki gani, kije wajen Ummi ta fada miki irin matar da nake so in kina da irin qualites din to zan aure ki." Yana fada ya shige daki, da kallo ta bishi tana jin wani irin zafi a zuciyar ta duk mazan da suke son ta taki ita kullum sai Aliyu amman shine yake mata haka, kan kujera ta koma ta zauna ta fara kuka, ranar a falo ta kwana ta kasa bacci sai kuka da take saboda da gaske take son Aliyu tunda Yayar ta ta mutu taji duk duniya ba wanda take so sai shi. *Allah y jikan musulmai Allah kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin* *Antty* [11/27, 14:18] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 59 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa Da asuba da ya fito zai tafi masallaci ya ganta kwance akan kujera kai ya dauke ya fice kawai, Ummi ce ta sauko ta ganta sosai tai mamaki ta zauna tana tashin ta, ido ta bude wanda suka dan daga saboda kukan da ta sha. Ummi tace "Me ya samu idon ki fuskar ki duk tai ja, idon ki ya kumbura." Mutsuka idon ta take tace 'Ummi Yaya ne, Ummi wacce irin mace Yaya yake so?" "Kije alwala kiyi sallah tukkunan." Ta mike ta wuce sama wanka ta farayi sannan ta fito ta canja kaya, Maryam na zaune akan sallaya tana karatun Alkur'ani ta fito, ta tada sallah sannan ta koma kam gado ta kwanta. Da safe Maryam na falo kwance akan kujera sanye da hijab har kasa, hannun ta daure da counter tana yin tasbihi, Ummi na kan two sitter, Tasleem ce ta fito sanye da dogon wando da riga karama kan ta ba dankwalli, ta zauna a kan hannun kujerar da Ummi take, Ummi ta kalle ta yace "Abinci fa." Cikin ta ta shafa tace "Tukkuna Ummi ki fada min Ummi meyasa Yaya baya so na, wai wacce irin mata yake so?" "Me ya kawo wannan to?" "Shi yace na tambaya." "Hmm Aliyu kenan, to shi Aliyu yana da wuyar sha'ani miskili ne bai son mutum mai surutu da rawar kai, yana son mace mai kamun kai da shiga ta mutunci duk kyale kyalen nan basa gaban sa fatan sa ya samu salihar mace, ai ke shaidace akan yar uwar ki ba ruwan ta ba sawa ba sakawa to dalilin da yasa ya so ta kenan kuma har yau yake kan son ta, kiyi kokari ki koyi wasu halaiyar nata in kina son Aliyu ya so ki." "Ummi ai Yaya Maryam bata waye ba gaba daya tayi rayuwar waje amman kullum bata waye ba, da ba dan Yaa Aliyu ya aure ta ba da ina zaton ba mai auren ta a zamanin nan." Ummi tace "A haka kuma yaso ta yaki ki fa, ku kun dauki wayewa a zubar da mutunci ai zubar da mutunci mana, kalli fa yadda kika sauko kanki ba dan kwallin kuma ina tunanin acan ma zaki iya fita kusan haka, bayan a addini bai kamata wanda ba muharramin ki ba ya ganki a haka, bansan me yasa Yaya yake barin ku a haka ba, ga Maryam nan dai a gidan nan ko da mayafi ba zaki ganta ba kullum hijab amman ke kalli yadda kika sauko ba ruwanki wani ya ganki a haka wanda ba dai dai bane." "Ummi Yaya ne fa." "Yayan muharramin ki ne? Naga da aure a tsakanin ku." Baki ta turo, Ummi tace "Zagi na zaki?" "Nifa Ummi a'ah ba abinda nace." "Uhmm wallahi ki kula ace duk Yaya ya barku haka sai abinda kukayi, ko da yake laifin mahaifiyar taku ce tinda shi ba zama yake ba." Fuska ta daure. Sallamar Aliyu ita tasa Ummi tayi shiru, suka amsa sallamar, a gefen Ummi ya zauna, Ummi ta kalle shi tace "Ni sai naga duk ka rame Yaya bata kular min da kai ko?" Yaya da take saukowa tace "Allah yaso nazo da sai dai ai min sharri, wannan yaron naki dai yana da damuwa nayi nayi dashi ya fada min yaki, ko dan ni ba uwar sa bace, nasan ke ya fada miki, kullum bai cin abinci sai ya raba dare idon sa biyu sam bai hutawa ke daga kallo daya zaki gane yana da damuwa amman yaki ya fada kullum sai munyi fada dashi akan abinci sai kace wani yaro." Ummi ta juyo tace "Haba yaron kirki " "Ummi nifa kewar ku nake kawai." "Jika sai kace karamin yaro, Aliyu ka rage wannan kwulaficin naka ka girma fa in da ba dan kaddara ba ai kaima da yanzu kana da iyalai wanda zasu na maka haka amman kai kake yi, mufa tamu ta kusa karewa in kuma muka mutu fa shikenan zaka ce ka daina rayuwa ne? Dan Allah My Son kana ragewa kaji yaro na." Kansa ya daura akan kafadar ta yace "Ummi ba yanzu zaku tafi ku barni ba bana so Ummi dan Allah ki daina maganar nan, Maryam ta tafi ta barni so kike kema ki tafi ki barni?" "Ba tafiya zanyi na barka ba, ina fada maka abinda ya dace ne kaji." "To Ummi." "Abinci fa meyasa bakaci." "Ummi kinsan in ba girkin ki ba, ba wanda yake mun dadi " Dakuwa Yaya tai masa tace "Kaniyar ka, da kai na nake shiga na girka masa abinci amman yaron nan ko kallon sa bayayi sai ya mai dani karya nai ta fada sannan zai dan taba." Dagowa Ummi tayi ta kalli Maryam da ke danna wayar ta suna chat da Muhammad tace "Daughter kawo masa abinci yanzu." Ajiye wayar tayi ta mike, Ummi tace "Yau sai ka dawo da kibar da ka rage." Yaya ya kalla yace "Momy ki fada mata ai ina ci aiki ne fa kawai yasa na fada." "Wane irin aiki ne wanna Son?" Kai ya shafa, ya mike ya dauki wayar Maryam ba security yana dauka yaga suna magana akan dinner anjima da za ayi, wani murmushi ya saki, ya maida wayar ya ajiye, Maryam ta karaso ta ajiye ta dauki wayar ta tai sama. Tasleem kuwa tana zaune sai bata fuska take, Yaya ce tace "Ita kuma wannan fa?" "Dan na mata fada ne." "Akan me?" "Kinsan su, su ya'yan turawa ne ina mamakin yadda su Basma basa wannan rayuwar dasu suke ko da yake a gidan nasu ma marigayiya batai ba amman wannan kingan ta ta dauki dabi'ar su gaba daya ita take yi kuma laifi uwar tasu ce ai." "Uhmm Allah ya shirya shine take bata fuska dan an mata fada." "Gashi nan dai sai cika take ba." Aliyu ne ya dago ya kalle ta kai ya dauke yana tabe baki, yace "Wannan shigar kuma fa? Ina dankwalin ki? Tashi kije ki saka hijab." Mikewa tai tayi sama da sauri idon ta na kawo ruwan hawaye, Maryam ta sama kwance akan gado tana rike da waya a kunne sai murmushi take, zama tayi a gefen gado tana goge hawayen idon ta, can ta mike ta dauki wata after dress wacce ba abinda ba a gani a jikin ta sai dan mayafi da ta daura akanta, ta dauki jakar ta, ta fice a dakin da kallo Maryam ta bita tana tabe baki. Tana sauka ta samu Aliyu na cin abincin sa hankali kwance, Ummi ce ta fara ganin ta tace "Ina kuma zaki?" "Gida zan koma." "Dan an miki fada ke kin fi karfin ai miki fada kenan ko?" Hawayen idon ta ta hau gogewa ta fashe da kuka tace "To Momy ya zanyi? Me nayi?" "Oh duk fadan da akai miki ma baki san me kikai ba?" Kuka ta kuma saki Aliyu ya mike ya fita a dakin gaba daya da kallo ta bishi, Ummi tace "Ina zaki yanzu?" "Gidan sitti zan koma." "To kije driver ya kai ki, sai anjima in mun hadu." Jakar ta taja ta fita a gidan. A waje ta same shi yana rike da waya a kunnen sa, tsayawa tai tana kallon sa, har ya gama ya juyo yana ganin ta ya hade fuska yace "Yanzu nai miki magana akan shigar ki a haka kike son ki fita ko?" Kallon kanta tayi tace "To Yaya menene da wannan kayan?" Kai ya dauke yace "Muje na sauke ki." Dadi taji ko ba komai zata kasance dashi, mota ya shiga ta shiga gefen su a hanya yace "Tasleem abinda Ummi ke fada gaskiya ne dan haka ki kula." "To Yaya zan gyara in munyi aure ma hijab zan na sakawa har kasa." "Kiyi tin yanzu shine zan gane zaki ko ba zaki iya ba gaba." "Yaya da zafi fa, ita wannan ta gidan naku da take saka hijab kullum bata jin zafi ne?" "Kije ki tambaye ta." "Kaga wani gani gani da take min." "A'ah Tasleem Maryam bata da matsala kwata kwata, dan haka karkice haka kila ke kikai abinda take miki wani gani ganin." "Yaya yanzu baka ganin laifin ta." Dai dai zuwan su gida, ya kalle ta yace "Sauka kije." "To Yaya zaka zo anjima." "May be." "Please Yaya kazo" "Ok." Ta bude ta fita ta daga masa hannu tace "Thank you dear." Ya dauke kai ya tada motar ya bar wajen. Karfe takwas ta fito daga sashen su ba kowa a gidan tsit, compound ta fita ta duba taga motar da ita kadai ce a harabar gidan bata san motar ba dan haka ta tsaya daga nesa da motar to yanzu wa zai kai, wayar ta duba, dan Kiran Muhammad, dan daman yace zai kai ta tace a'ah to gwara yazo su tafin kawai. Aliyu dake cikin mota sanye da wata brown kala shadda, ya saka hula kalar kayan har da glass agogon hannun sa na azurfa yana ganin zata kira wani ya danna horn da sauri ta dago tana kallon motar, horn aka kara dannawa wannan yasa ta karaso wajen motar, dan ita a tunanin ta Yaa Farouk ne gefen inda driver yake ta tsaya yana daga ciki ya sauke glass din motar sai da jikin ta yayi yarrr yanda ta ganshi yayi masifar kyau kyamshi ya kara fitowa tamkar shi yayi kanshi, da sauri ta sauke kan ta kasa, kofar motar ya bude yai mata nuni tare da fadin "Shigo." Jiki a sanyaye ta zagaya da kallo ya bita har ta shiga wani kamshi da sanyi taji a hankali ta lumshe idon ta, zama tayi ta rufe kofar ya tada motar ya bar wajen ba tare da yayi mata magana ba sai kira'ar sudais dake tashi a cikin motar, can wayarta ta soma ringing a jaka hannu ta saka ta ciro ta Ummi ce, dauka tayi takai kunnen ta Ummi tace "Kina Ina?" "Muna hanya." "Ke da waye?" Aliyu ta dan kalla ta dauke kai tace "Yaya ne." "Ok sai kun karaso." Ummi ta kashe wayar, ya juyo ya dubeta, sannan ya dauke ido ya mai da kan titi yace "Wanene?" "Ummi ce." Parking yayi a gefen titi ya dago yana kallon ta, dagowa tai idon su ya hadu waje daya kasa daina kallon juna sukai sai da suka dauki minti kusan uku sannan tai karfin halin janye idon ta, shi kuwa ido ya lumshe sannan ya kara kallon ta yace "kinyi kyau sosai, wa yai miki kwalliya?" Dan murmushi tayi tace "Nagode." Ya daga mata gira yace "Wa yai mki kwalliyar?" Ita a ganin ta ba wani kyau da tayi dan da kanta tayi kwalliyar yar kadan wanda ba karamin kyau tayin ba, kanta tai kasa dashi saboda jin idon sa akan ta tace "Ni nayi." "Oh daman kin iya?" Kai ta gyada yace "Amman bakya yi a gida why?" Shiru tayi shima jin zai saki layi yace "Tayi kyau." Ya zuba mata ido ita kuwa kan ta a kasa ta kasa duban shi, numfashi ya ja sannan yace "Maryam!" Wani iri taji dan sai da tsigar jikin ta ta tashi, ta dago ta kalle shi da sauri ta dauke kanta, dan bata iya jurar kallon idon sa, wani abu take gani yana fitowa yana shiga nata wanda hakan ke haifar mata da mutuwar jiki, shiru yai kamar ba zai magana ba sai kuma yace "Bayan tafiya ta kin shiga wani mawuyacin hali wanda ni kaina da bana nan na shiga makamancin sa, a dalilin rashin daukar shawara ta abin yaso ya taba miki rayuwar ki, in nine ke ba ruwa na da wani samari karatu na zan rika a gaba zaki samu masu son ki wanda kema a lokacin kin kama kasa amman a yanzu karatun shine ya dace da ki sa a gaba, kina zaune wani yazo zai tarwarsa miki rayuwa akan me? Me sonki na gaskiya ba zai taba barin ki ba ko tuhumar wani abu akan ki, yana da kyau ki nutsu ki gane mai sonki, da wanda kike so." Hannun ta ya kamo wani iri taji waninshock wand ashima sai da yaji tsargawar sa, dan murazawa yayi sannan ya saki yace "Dan Allah ba danni ba ki bar harkar wasu samari ki riki karatun ki, ki taimakawa Haidar, a gaba zaki samu mai son ki wanda baki taba tsammani ba amman ba yanzu ba kinji." Mamakin Aliyu take saboda me yake hadata da Allah bayan rayuwar tace, shi bai aure ba itama kada tayi kenan anya ba aljanu ne dashi ba wanda basa son aure to aljanu mana. Hannun ta ya dago yace "Yes nasan zaki ce ina ruwana da rayuwar ki amman ki sani rayuwar ki na da mahimmanci ga mutane da yawa ingantata zai bawa mutane da yawa farin ciki ki tsaya ki nutsu ki duba kinji little sister dita." Baki ta turo yai murmushi yace "Wato bakiji ba ko?" Hannu ta daura akan bakin ta, yace "Kin fiso ki ta tara maza suna zuwa su taso miki da son sanin wacece ke ko?" Ji tayi zuciyar ta ta karye dan tabbas duk wanda ya ganta zai so ya mallake ta kuma tana yawan samun masoya amman ta ina zata fara sam bata fatan abun da ya faru akan ta da Muhammad ya kara faruwa bata fatan tarihin ta yai ta yawo ana mata wani kallo wanda bata san dai dalilin komai ba amman kuma tabbas duk abinda Aliyu yake ada gaskiya ne, amman tayaya zata na gujewa samarin dake kawo mata hari, tana lura da wanda suke tare da Fauwaz yadda yake ta shishige mata bata san ya akai ba sai kawai jin hawaye tayi na bin kumatunta tabbas tasani rayuwar ta abin tausayi ce shin ko ta auri Muhammad wane hali zata shiga a gidan sa, kada wata rana ai mata gori da ya zataji anya kuwa batai gangancin amsar soyayyar Muhammad ba, Aliyu ganin hawaye a idon ta ya hau lallashi amman ina kana dada tunzurata yayi, wannan yasa ya janyo ta jikin sa ya rumgume ta hadi da runtsa idon sa, dan abinda yaji a tare da shi, tana jin ta a jikin sa taji wani nutsuwa wanda bata san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba, take kukan nata ya dauke, so take ta bar jikin nasa amman kuma ya matse ta a jikin sa. Ido ta lumshe muryar sa mai taushi taji yana fadin "Kiyi hakuri banyi niyyar na saki kuka ba amman gaskiya na fada miki, damuwa ki tawa ce zan fiki shiga damuwa da gaske nake, ina jin ki tamkar su Najwa a tare dani dan haka dole na damu da damuwar ki, ki daure ki cika min buri na akan ki Maryam." Ido ta runtse ya dago kanta daga jikinshi yasa hannunshi ya rike fuskata yana duban idota hawaye na zuba, idonshi cikin nata yake kallonta, da sauri ta runtse idonta dan ba zata iya jure kallonshi ba ya sakar mata fuska sannan ya dauko handkerchief ya fara goge mata hawayen fuskar ta sai da ya gama sannan ya amshi jakar ta yace "Kwalliyar duk ta baci duk da daman ba so nake a gani ba amman dan shafa hoda kadan ba da yawa ba kar maza su kara rikice miki." Kallon sa take dan a wani lokacin in yai abu mamaki yake bata ta kasa gane ina ya dosa, shima gane yasaki layi yace "Saboda tsaro fa kar azo a saka miki damuwa." Kai kawai ta dauke, ya bude jakar ya mika mata hoda ta amsa ta fara shafawa kura mata ido, har ta gama ta juya ta kalle shi, ya saki murmushin sa mai kyau ya juya ta kalli agogo har tara saura, tace "Yaya lokaci na kurewa fa." Bai Kalle ta ba duk da yaji dan in ta shine ba wata dinner ganin bai juyowa ba tace "Yaya." Ya dago yana kure ta da idon sa yace "Menene?" "Yaya dare nayi fa." "Agogo ya kalla yace "ko mu koma gida?" Yadda ya hade rai yasa ta dauke kai kawai, ya gyara zaman sa ya tada motar suka bar wajen. Ko da suka je har ango da amarya sun shiga ana ta biki. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin* *Antty* [11/27, 14:18] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 60 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Suna parking ta fara kokarin bude kofar da sauri ya dannan lock ta juyo zatai magana, ganin ba fuska yasa ta koma ta jingina a jikin kujera, sai da ya gama danne dannen sa sannan ya dago yana kallon ta hannu ya saka a aljihu ya zaro yan 500 bandir biyu ya mika mata, amsa tayi tace "Nagode." Unlock yayi ya fita itama ta bude ta fita, gaba yai yana tafe tana bin sa a baya, a bakin hall din suka hadu da Tasleem wacce akai mata wata heavy makeup ga shi ta saka wani material mai kyalli an mata gown ta kamata sosai ba mayafi sai yar jaka da waya a hannun ta da hill shoe, tana ganin sa ta taho tana fadin "Yaya ina ta jiran ka fa." Kamar ba dashi take ba haka yazo zai shige ta kamo hannun sa ya dago a zafafe da sauri ta saki hannun nasa ya bita da wani bazan kallo, Maryam dai shigewa tayi ta barsu a wajen, tana shiga taga Muhammad zai fito, hanya ta bashi amman sai yaki yabi ya tsaya kallon ta, dagowa tai tana kallon sa tare da kallon bayan ta ko Yaa Aliyu ya shigo, a hankali tace "Ina zaka?" "Nemo ki mana. Ina ta kira bakya dauka." Wayar ta kalla tace "Tana silent ne." "Wa ya kawo ki to?" "Yaya ne." "Oh ya dawo ne?" Kai kawai ta gyada ta fara tafiya yabi ta yana fadin "Amman kinyi kyau my love." "Ka fini yin kyau in Jawahir ne?" "Naganta tare da dayan Yayan nan naki." "Oh Yaa Farouk, kace sun hadu." Ta karasa wajen Najwa da ta dauke kai tace "Haba Amatya ya da bata rai." "Wai sai yanzu zaki zo " "To kema yaushe kika zo din." "Au haka ma zaki ce ko?" "To ya zanyi Yaya ne ya tsaya harkar gaban sa." "Meyasa kika zauna ya kawo ki ai kinsan halin sa." "Kinga mu bar maganar nan, amman fa kinyi kyau." Ta kalli Abdul tace "Ango kunsha kyau fa." "Yace ai fushi muke. Ta hade hannaye tace Tuba nake, sannan ta bar wajen tana murmushi, wajen su Jawahir taje suka gaisa sannan taje ta samu Momy da Ummi daga nan ta samu waje ta zauna tana mai daukar wayar ta, ta fara danne danne akai akai tana dagowa tana kallon yadda ake gudanar da abubuwa "Amarya ta." Ya fada cikin cool voice din sa ya zauna tai murmushi kawai yace "Wallahi Baby kinyi kyau kamar na hadiye ki." Murmushi ta saki, tana yin kasa da kan ta ya daga hannu ya kira MC ya karaso yace "Ina son fili amare dani da tawa amaryar." "An gama ranka ya dade." Ya fada yana barin wajen, yan 1k ya dire mata a gaban ta har guda uku Maryam ta dago tana fadin "Na menene?" "Liki." "Yaya ya bani fa." "Wannan na mijin ki ne ba yaya ba." Zatai magana ya daura hannunsa akan lips din sa yace "Ba kyau mai da hannun kyauta baya." "Amman ai sunyi...." "Dauki kawai." Dai dai lokacin da MC ya fara kiran suna Muhammad Auwal akan ya fito ango da amarya na jiran sa, kirari ya farai masa Muhammad ya mike ya juyo ya kalli Maryam da bata da alamar mikewa, yace "Dear!" Dagowa tai ya kafe ta da idanun sa yace "Taso mana." Ba yadda zatai ta mike yai gaba tabi bayan sa, ganin yai mata nisa yasa ya tsaya har ta karaso suka jera in kagansu sai sun baka sha'awa dan kuwa sun dace da juna, amarya a tsaye da ango suka hau stage din dai dai shigowar Aliyu ya hange ta a saman stage tana liki wani abu yaji ya tsaya masa a makoshi bai kara shiga damuwa ba sai da yaga Muhammad a gefen ta ji yai kamar ya bar hall din amman ya samu waje ya zauna tare da zaro wayar sa yana danne danne, hakika bai so zuwa dinner ba dan shi bai fiya zuwa biki ba in ba daurin aure ba amman dan ya kula da ita yasa yazo sai dai zuwan na neman ya sa masa hawan jini, in ya dago yaga yadda Muhammad yake mata magana kasa kasa yana mata liki ji yake kamar ya tashi yaje ya janye ta, sun jima Muhammad na barin kudi sai kirari MC yake masa sai da Maryam ta bar wajen sannan yabi bayan ta, zuciyar Aliyu kamar ta buga bayan sun zauna aka kai musu lemo ya bude mata ya mika mata ta dago ta kalle shi ta amsa tana murmushi ya kufala duk a kan idon Aliyu da ya kasa daina kallon su, kiran yaye da kannen amarya akai wannan yasa su Anty Asiya duk suka fita, Farouk ma ya fita ganin ba Aliyu da Maryam ya je ya kamo hannun Aliyu da kyar ya kai shi kan stage ai kuwa kannen sa duk suka hau zuba masa kudi, Maryam ya hango yaje ya kamo ta suka hau stage din, rafers din yan 1k Aliyu ya balle ya dinga zubawa kannen sa, suma suna masa liki, sauran suna rawa, Maryam dake gefe a tsaye ba abinda take ya juya yana zubawa kudi take camera man da mc suka hau kirari tare da fadin "Yayan ango da tashi amaryar Allah ya kara dankon soyayya." Aliyu kuwa sam idon sa ya rufe sai da ya juye mata su tas sannan ya bar wajen, juyawa tai zata bar wajen Najwa ta kamo hannun ta tana dan jujjuga ta Maryam bata iya rawa ba hasalima kunya take ji, a haka ta koma wajen zaman ta duk bata da nutsuwa akai akai tana dagowa tana kallon Aliyu da ya hade rai kamar bai dariya. Iyayen amarya da aka kira shi yasa Maryam fita ta hau yiwa su Ummi liki suma suna mata, a haka kai musu picture gaba dagan su. Har karfe sha dayan dare shagali ake sha, Maryam na zaune ita da Muhammad da sai hira yake bata tana dariya dan Muhammad ya iya daukewa mutum kewa da sasu nishadi, Aliyu dake hangen su yazo wuya, a fusace ya mike ya karaso inda suke tana ganin sa ta dauke kai yace "Tashi muje." "Yaya ba fa a tashi ba." Wata tsawa ya daka mata wannan yasa ta mike da sauri tayi waje ya bi bayan ta har bakin hall din ya kalle ta yace "Shige muje." "Yaya ni zan taho da su Ummi wallahi ba zan iya zama ni kadai a gida ba." Bai kula ta ba ya nufi wajen da yai parking tabi bayan sa kamar zatai kuka ya bude mota ya nuna mata, ta shiga ya rufe ya juya ya bar wajen da kallo ta bishi a tunanin ta lokacin zai fito amman me tin tana jiran fitowar sa har ta fara jin tsoro, wayar ta ta dauka ta fara kiran layin Basma tana dauka tace "Ina Yaya?" "Gashi can." "Me yake?" "Danne danne ke kina ina?" "Shikenan." Ta kashe wayar ta fara neman layin sa ko ya manta da ya barta a mota ne amman har ta gama ringing yana gani bai dauka ba sai da ta kira sau uku amman bai dauka ba kashe wayar tayi dan haushi shi yana can yazo ya kulle ta anan wai dan me yake mata haka ne yayiwa su Basma mana sai ita da ya raina. Kuka ta saki a haka wanda ta kudundune waje daya, bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba. Sha biyu saura su Ummi suka tafi wanda sha biyu nayi Aliyu ya hau kada kan kannen sa duk sai da ya ga tafiyar su har amarya sannan yayo wajen motar sa, lokacin sha biyu da rabi tuni Maryam tai nisa a baccin ta, mota ya bude wanda yasa Maryam ta bude ido da sauri tana ganin ta a inda take ta saki ihu, da sauri ya rufe mata baki yana fadin "Menene haka kiyi addu'a sai ihu ko?" Ajiyar ta sauke ya kunna wutar motar duk da ta ganshi amman jikin ta sai rawa yake. Ganin a tsorace take yasa ya kamo hannun ta yana murzawa a hankali yace "Is ok am sorry kinji." Idon ta lumshe ya saki hannun ta yace "Me dazu nace miki?" Yadda ya daure fuska sai da ya bata tsoro tai saurin yin kasa da kan ta yace "Wato ke bakya jin magana ko?" Shiru tayi ya girgiza kai zai magana wayar ta, ta soma ringing shi ya dauki wayar yana duban sunan ganin Ummi ce yasa ya kai kunnen sa yace "Ummi." Tace "Kuna tare?" "Eh Ummi yanzu zamu taho na tsaya naga kowa ya tafi ne shiyasa." "To shikenan sai kun karaso." Ta kashe wayar ya mika mata yace "Ummi taga dare yayi." Ya fara yana duba agogo daya saura kwata ya tada mota suka har wajen a hankali yake tafiya kamar wanda bai son tukin bai damu da ganin dare yayi ba ita dai Maryam tana jikin kujera tana ganin ikon Allah kamar ba zasu ba a haka suka karasa gida. A compound din Ummi yai parking zata bude taji a rufe take ta juyo ta kalle shi kamar bai san me take nufi ba ya dage mata gira, ta kalli kofar tace "Yaya bacci nake ji." "Shine bana so kiyi kamar yadda nima ba zan ba." Ya fada yaba danne-dannen waya, dagowa tai ta kalle shi tace "To saboda me?" Leben sa ya cije tace "Dan Allah ka buden wallahi bacci nake ji." Kamar ba zai bude ba sai ya bude da sauri ta fice a motar tai ciki, kan ya fito ya rufe har ta haye sama, wanka tayi tana fitowa ta fada saman gado bacci take ji amman sai sam ta kasa da ta rufe sai taga fuskar Aliyu wanda a haka ta dinga juyi har wajen biyu da wani abu, can wajen biyu da rabi kirshirwa ta ishe ta, ta mike ta bude firij din dakin ta sam ba ruwa, sauka tayi kasa ta shiga kitchen dan dauko ruwa, fitilar falon a kashe sai hasken fitilin waje da ya leko, tana shiga ta dauka ta samu ta zauna tana sha, sai da ta sha sannan ta mike rike da guda daya, a bakin kofa taci karo da mutum tayi baya kamar zata fadi, da sauri ya taro ta, baki ta bude da nufin yin ihu da sauri ya daura hannun sa akan bakin ta, ido ta zaro jin ta rumgume jikin mutum, a hankali ya raba jikin su yana kallon ta, ganin Yaa Aliyu ne yasa ta saki kuka dan sosai ta tsorata bata taba tsammanin ganin mutum a lokacin ba, kirjin ta in ban da bugawa ba abinda yake. Hannun ta ya kamo ya dan murza alamar rarrashi, yace "Ya isa to menene na kukan meyasa da kika sauko baki kunna fitilar ba, me ma ya fito dake da daren nan, me ya hanaki bacci?" Hannun ta, ta janye tayi hanyar bene da sauri ya kamo ta wanda hakan yasa ta fado jikin sa, matse ta yai a jikin sa yana kallon fuskar ta. Hawaye ne ke bin kuncin nata, hannu yasa yana goge hawayen dake bin kumatun ta, a hankali cikin muryar sa mai dadi yace "Ya isa to kinji am sorry daina kukan kinji." Haka yai ta lallashin ta har tai shiru sannan ya sake ta ta hau sama tana shiga ta fada saman gado tare da lulluba addu'a tayi sannan ta hau tunanin abun da ya faru bata jima ba bacci ya dauke ta. * Washe gari da wuri ta tafi gidan Sitti dan kar Aliyu ya hanata fita, ranar lunching akai a wani event centre, tare Maryam da Najwa suka tafi makeup akai musu, karfe biyar aka gamai musu, ana gamawa Abdul da Muhammad suka daukesu, Maryam na gaba, ita da Muhammad, Abdul da Najwa ba baya, a haka suka tafi wajen lunching din ranar sakayau taji ta saboda babu Aliyu amman ita kuma taji kewar sa. Yana zaune a falo yana danne danne a waya Ummi suka sauko da Yaya zasu tafi wajen Lunching din dagowa yai yana fadin "Lafiya zakuyi?" "Eh." Kallon saman yayi yace "Ina Maryam din?" "Ai su sun jima da tafiya." Da sauri ya mike yana fadin "Bari na shirya sai na ajiye ku." Da kallo suka bishi, ya shige daki bai jima ba ya fito sanye da dogon wando na jean da orange kalar riga, yace "Muje." Sukabi bayan sa, ya shiga suka bar wajen. Karfe shida saura sukaje wajen suka sauka ya shige, Maryam na ciki, cikin kawayen ta ana ta shagali wayar ta ta fara ringing tana dubawa taga sunan Aliyu, gabanta ne yai wata mummunan faduwa ta dauka tana sallama amsawa yayi yace "ina jiranki a waje." Yana fada ya kashe wayar sa, shiru tayi tana nazari Jawahir ta dafa ta tace "Menene?" "Yaya ne wai yana waje." "To kije kiji mana." Mikewa tayi ta nufi barin wajen fita tayi tana dube duben ta ina zata hango shi, tana tsaye taji ana mata horn, juyawa tayi ta karasa wajen motar, kofar motar ya bude ta shiga ta zauna yace "Rufe kofar." Tana rufewa yaja motar ya bar wajen, wayar ta ce ta fara kuka tana dubawa taga Muhammad ne dauka tayi takai kunnen ta yace "Ina kika je naga fitar ki na biyo ki bakya nan." Wayarta ya amsa, ya kashe, juyowa tayi tana kallon sa ya hade rai ya ajiye wayar, wata unguwa suka shiga wacce ta gama haduwa duk zagayen ta a garin bata taba zuwan ta ba ta hadu sosai, bakin wani katon gida mai kyau suka karasa yai horn mai gadi ya bude suka shiga, parking yai ya fito ya rufe kofar ya zagaya ya bude mata, ta sauko tabi bayan sa ya nufi kofar wacce take da tumbprint din sa, hannu ya saka a kofar ta bude suka shiga wani hadadden falo ne wanda yake dauke da kujeru orange da lemon kala, haka labulaye da center carpet sai kamshi dakin yake ga wani sanyi mai dadi, kujera ya samu ya zauna ya kalle ta yace "Wa yasa ai miki wannan kwalliyar?" Shiru tayi yace "Ba magana nake ba?" "Sitti ce tace sai nayi." Mikewa yayi ya dauko lemo a firij, ya zauna yana kallo TV yana shan coke kallo ta yayi yace "Zauna man." Kamar ba zata zauna ba ta dan zauna a gefen kujerar ta zauna ya dauki waya yana dan danne danne a haka ya gama shan lemon ya dan shafa cikin sa sannan ya dago yace "Yunwa nake ji, ki shiga ki samar min wani abunda zan ci." Mikewa tai tace "A ina zan dafa maka?" Ki shiga waccan kofar akwai wani corridor ki bi nan ne kitchen." Ta juya ta shiga, wani falo ta kara shiga wanda yafi wanda suka zauna kyau, tana mamakin gidan wanene nan, corridor tayi ta shiga kitchen din, yai kyau, babu ce kawai babu, dan yai kyau a gyare wajen yake ta bude firij taga akwai wasu kayan amfani, kaza ta dauka ta wanke ta daura akan wuta ta dauki dankali ta yanka ta daura masa farar taliya da miyar kaji da dankalin turawa tana gamawa ana kiran magariba ta fito ta tada baya nan a kitchen tai alwala ta fito a tada sallah a falo tana zaune ya shigo ta dauko masa abincin ya dauka ya fara ci, ya dago ya kalle ta yace "Ke bazaki ci ba?" Kai ta girgiza yace "To." Ya cigaba da cin abincin sa sai da ya gama sannan ya zauna yana kallon ta, ta dago tace "Yaya don Allah ka kai ni gida." Banza yai mata har sai wajen bakwa da rabi sannan ya tashi yace "Muje." Ta mike yabi bayansa suka shiga mota, yana zuwa gida ta bude mota ta fita, zata wuce yace "Ungo wayar ki." Ta juyo ta amsa ta bar wajen da sauri ranta a matukar bace, tana shiga ta fara neman layin Farouk yana dauka tace "Yaya kana ina?" "Ina gidan Sitti." "Please kazo ka dauke ni Yaya anan zan kwana." "Meyasa kika koma gida?" "To ba Yaya bane." Tai magana kamar zatai kuka yace "To gani nan zuwa." Ya kashe waya sallah kawai tayi Farouk ya kira ta, tai wa Ummi sallma ta tafi. Suna zuwa ta shiga dakin Najwa yan matan amarya ne a wajen Najwa na zaune kan sallaya ta karasa ta zauna, Najwa ta kalle ta tace "Ina kika je ne?" "Ba Yaya bane ya dauke ni kawai." "Wane Yayan?" "Wanne kuwa? Yaya dai." "Wai shi Yaya mai yake damun sa ne." "Uhmm." "Ace ba zai barki ki sake ba, haba kina da saurayi amman yabi ya kankane?" Wata kawar Najwa Hauwa tace "Amman ba thesame father suke ba ko?" "Yes cousin ne Yaya na fa." "Ah son ta yake amman ko?" Wani kallo Maryam ta bi Hauwa dashi da mamaki tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Hauwa tayi dariya sosai tace "Baya takura miki akan samari?" "Uhmm ko waya baya so tayi dasu ba, ya hanata kula su sam." Najwa ta fada, Hauwa ta kuma dariya tace "Wai amman kinji Yaya ne, to haka kawai bazai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki waya, idan babu wani abu a kasa" *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakhawan karshe. Amin* *Antty* [11/28, 13:42] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 61 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Maryam ta hade rai, Hauwa tai dariya, Maryam tace "Kai ke wallahi baki san Yaya bane ko ke bai miki haka ba?" Ta fada tana mai da tambayar kan Najwa. "Ya min amman ba kamar naki ba." "To ai ni dan muna tare ne." "Uhmm cewa fa yayi kar ta tsaya kula samari ta riki karatu dan Allah kalli wannan budurwa mai kyau wai ita za a cewa kar ta kula samari." Dariya suka sheke da ita Basma tace "Uhmm kalli fa yadda Affan ya rikice daga ganin ta." Dariya Hauwa tayi tace "Tabb, lallai Yaya Aliyu" Maryam dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Hauwa tace "Toh wallahi son ki yake...." Maryam ta zaro ido ta koma baya da sauri tace "Don Allah ki daina cewa haka plsease, wallahi Yaya na ne fa, ke ai Najwa kinsan Yaya fa" Najwa tayi wani murmushi tace "Tinda ba ciki daya kuka fito ba ai an gama Maryam, ki daina tinda manyan yan soyayya suka gane to da wata a kasa fa. Ni daman na fara zargin sa dan yadda da kika zo hutun nan ya adabe mu da zarya har sai da kika koma sai muyi sati nawa bamu gansa ba amman kina nan kullum yana nan kuma bai son ya barki ki je ko ina ke kulawar Yayan tai yawa. Yadda Yaya yake miki ma ai bai mana ba, ke dai ce ban san lokacin da zaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai Yaya ne. A'a ba Yaya ba..." lokaci daya hankalin Maryam ya tashi wai Yaya son ta yake, ji tayi ta kasa nutsuwa sai kara tabbatar wa suke Hauwa na kara zuga Najwa, Maryam tace "Wallahi ku daina cewa haka ba kyau, ni ai Yaya yafi karfi na wallahi ba ruwan sa." Dariya kawai Hauwa take don Maryam tayi mugun bata dariya, haushi suka bata ta mike ta bar dakin, dakin Sitti taje ta zauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, Sitti ce ta shigo ta zauna a gefen ta tace "A'ah Yaushe kika dawo." "Yanzu." Ta fada tana kwanciyya akan gado, Sitti tace "Meyake damun ki?" "Ba komai Sitti bacci nake ji." "To kinci abinci ne?" Kai ta girgiza tace "Na koshi." Bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci a jikin ta ta kwanta akan gadon Sitti. * Washe gari yini da safe duk yan mata na dakin Najwa, Maryam kuwa na dakin Sitti kwance Najwa tayi tayi ta fito taki dan tin jiya bata kara komawa wajen su ba Basma ce zaune suna hira jefi jefi, wayar Maryam ce tai kara ta dauka ta kai kunnen ta tace "Asslamau alaikum." "Wa'alaikum salam." "Ya kk ya gida?" "Alhamdulillah." "Jiya kuma sai kika gudu." "Kai nane yake ciwo." "Ayyah ya kike ji yanzu?" "Ya daina." "To sannu ya anjima fa? Nazo na kai ki?" Kai ta gyada tace "To in mun shirya zan maka magana." "Shikenan sai anjima." Sukai sallama, ta kashe wayar, Basma tace "Wai da Muhammad za ayi ne? Affan na damu na fa." "Ke kyale wani Affan dan Allah." "Uhmm shikenan." Ta koma ta kwanta. Biyar har an fara kwashe yan tafiya wajen yinin bikin sauran yan matan suna waje suna jiran motoci, yau Maryam bata bi Najwa ba dan tin jiya ma bataje wajen ta ba da zasu tafi makeup tazo su tafi amman taki tace ba inda zata. Biyar da rabi ta fito zuwa compound din gidan Sitti sanye take da less cream kala wanda akaiwa ado da coffee, ita tai kwalliyar ta kuma sosai tai kyau batai wani shafe shafe mai yawa ba amman ita kanta sai da ta kalli kanta ta kuma kalla dan tayi kyau, coffe kalar mayafi ta yafa, da wani half cover takalmi da jaka, sai dankunne da sarka da ta saka golding sosai tai kyau kamar ita ce amaryar. Suna tsaye ita da wasu yan mata motar Muhammad ta karaso, wayar ta ce ta hau kara ta zata shine tana dubawa taga Najwa ce dauka tayi tace "Kina gida ne?" "Eh ke kina ina?" "Mun fito yanzu zamu karaso akwai wata friend dina da zasu karaso yanzu please ki samu wani ya kawo mana su." "Ok." Ta kashe waya, Muhammad ne ya fito ya karaso, yana murmushi, ya karaso yace "Amaryar Muhammad." Tai kasa da kai yace "Gaskiya ina kishi kar wani ya kalle min kyakyawar matata kinga yadda kikai kyau kuwa?" "Kai Muhammad kai dai maganar ka kenan." "Ai gaskiya ce shiyasa nake nanatawa kullum." Murmushi tayi yace "Zamu iya tafiya?" Kai ta girgiza tace "Akwai wasu da zan baka ka kai mana su, in Yaa Farouk bai zo ba sai ka dawo ka dauken amman yanzu please dear ka kaisu." "An gama ranki ya dade suna ina?" Nan ta shiga ta kira su, suka zo suka tafi a bakin mota yace "Zan dawo fa." Tace "Toh." wata hadaddiyar mota ta kunno kai harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta, kai ta dauke zata juya, jakarta ce ta fadi ta durkusa ta dauko tana juyowa taga Yaya Aliyu ya fito cikin wata shadda yar gaske sai maiko take, yayi wani irin kyau wanda duk wanda ya ganshi sai ya kyasa. Idon 'yan mata kuwa kamar ya fado dan kallon da suke masa, ta ganban ta yazo ya wuce ya shiga dakin Sitti bai jima ba ya fito, tana tsaye suna magana da wasu yan mata ta kai su wajen wata mota aka zuba su kenan ta juyo suka hada ido kai ta dauke ta nufi cikin gida wayar ta ce ta hau kara tana duba taga Aliyu ne dagowa tayi tana ganin sa bai magana ba kuma bai daina kallon ta ba karasowa tayi tana tsayawa ya shiga tare da bude dayan gefen yai mata nuni a hankali ta karasa ta shiga ta zauna motar ya tayar wannan yasa ta rufe kofar dan kada ta fadi in ya ja, Sanyi da kamshi dake cikin motar su suka saka ta lumshe ido, cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dube ta ba cikin gwaninta ya fisgo motar da gudu sai da suka hau titin wayar ta, ta dauka ta saka a silent dan kar Muhammad ya kira, dagowar da zatai taga sun dauki hanyar gidan da ya kai ta jiya, tsoro ne ya kamata da fargaba kar fa ya hanata zuwa wajen yinin nan, amman bari taga gudun ruwan sa, har ciki suka shiga ya bude ya fita kamar jiya ya dawo ya bude mata kofa, kallon sa tayi tace "Yaya wajen yini fa zani." Kai ya girgiza yace "Ba inda zaki dan nima ba zani ba, bana son hayani gwara kema ki saba da rashin son ta, bama wannan ba kina so kije maza suyi ta kallon ki a haka ko? Kinga yadda kakai kyau." Kai ya girgiza, cike da damuwa take kallon sa tace "Yaya nayi gayyata kuma wasu daga kawayen Najwa ni suka sani ba dadi." Kallon ta kawai yake ta dago suka hada ido da sauri ta kawar da idon ta yace "yunwa nake ji banci komai ba Unmi batai mana girki ba yau, mu shiga ki min abinci." Kallon sa tayi ganin fuskar shi ba alamun wasa yasa tai kasa da kai tace "Ayyah Yaya muje wajen anyi abinci sai na kawo maka." Jingina yayi da motar sa tare da harde hannu a kirji yana kallon ta tace "Kin taba ganin naci abincin waje bare na wajen biki?" Shiru tayi yace "Gwara ki sani bana cin abincin waje duk uzurin ki, sai kin min abinci kan kiyi abinda kike so." Ya fada yana yin cikin gidan, tsayawa tayi a wajen kamar ta fasa kuka amman ba yadda zatayi tafi minti biyar tsaye ta rasa me zatayi taji wayar ta na vibrating dubawa tayi taga shine, kin dauka tayi amman sai ga wani kiran nasa nan, dauka tayi ta kai kunne yace "Yunwa fa nake ji." Yadda yai maganar sai da yasa tsigar jikin ta ta tashi. Wayar ta kashe tace "To ina ruwa na." Sai kuma ta juya ta nufi cikin gidan, tana shiga baya falon farko na biyu ta nufa ta same shi kwance akan kujera yana kallo a TV kitchen ta nufa tana shiga ta dauki indomie ta dafa masa ta saka kifin gwangwani ta dafa wani kwan wani ta soya ta dauko ta kawo masa falo, a gabanshi ta jera komai ta koma ta zauna ya dube ta yace "Me kika dafan?" "Indomie." "Ni bana cin indomie." Ya fada yana tsure ta da ido, kai ta dauke ya janyo stool din yace "Amman tinda kin dafa yaya zanyi?" A ranta tace "Kada kaci." Ya bude kamshi ya daki hancin sa ya lumshe ido yace "Zo mu ci." kai kawai ta girgiza dai dai lokacin da taji vibration din wayar ta a cikin jakata ta ciro wayar har ta katse ta duba taga uban miss call ta duba su Jawahir ne da Muhammad da Basma dagowa tayi ta dube shi, sai abincin sa yake ci hankalin sa kwance, baki ta tabe tace "Dan Allah yaya kai sauri suna jira na." "Nai sauri muje ina?" "Wajen bikin." Dagowa yayi yace "Amman ai nace baza a ba ko?" "Yaya bikin fa Najwa ne." "Bikin Najwa bikin ki ne?" Shiru tayi ya cigaba da cin abincin shi sai da yayi dam sannan ya mike yai ciki. Sai da yaji ana kiran sallah sannan ya fito ya fita anan tai sallah sai bayan ya idar ya kira ta a waya yace "Fito mu tafi." Ta fita suka shiga mota suka bar gidan ganin sun dauki hanyar wajen bikin yasa ta fara murna amman sai taga ya dauke hanya, ranar dai a haka suka yi ta yawo a gari har taran dare, kuka ne kawai Maryam bata yi ba dan haushi wai ace biki kamar na Najwa bata guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe sai tara ya maida ta gidan Sitti shima da kyar dan da cewa yai gida zai kai ta sai da tai ta rokan sa sannan ya kai ta gidan Sitti. Tana shiga ta wuce dakin Sitti ta fada gado tana sakin kukan da bata samu tayi shi ba, Najwa da Jawahir dake compound sukaga wucewar ta suka biyo ta da fada Najwa ta shigo amman ganin tana kuka sai ta sakko tana tambayata menene? cikin kuka takece mata Yaya ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin yinin, Najwa tace "Ba komai kila shima yana da dalili." "Wanne dalili? shidai burin shi ya ga raina a bace." Nan dai ta shiga lallashin ta sannan ta fita Jawahir ta kalle ta tace "Wai Yayan nan ba son ki yake ba kuwa?" "Kema zaki fara ko?" "Allah naga takurar tai yawa." Dan tsaki ta saki ta haye gado tana fadin "Dan Allah Jawahir kada ki fara." "To taso muci abinci yanzu Yaa Muhammad ya kawo." Shiru tai mata Jawahir ta hau gadon ta juyo da ita yace "To wai menene?" "Yaya ne mana duk ya batan yau dina." "To menene sis yanzu fushin zai dawo miki da lokacin ne?" Kai ta girgiza, Jawahir tace "To please forget about it, let continue celebrate the rest day." Ta kamo hannun ta suka sauka kasa tace "Bari na kira Basma." Ta mike ta fita tare suka ci Basma da Najwa da Jawahir da Maryam, nama ne da wani hadin salad, bayan sun gama suka zauna hira sune har karfe biyu idon su biyu, sannan suka kwanta. Washe gari aka daura auren su Najwa da Abdul, da safe, bayan anyi reception, suka karaso gidan Sitti, anan akai hutuna, Maryam na daki akwace wayar ta ta hau kara, tana dubawa taga Muhammad ne yace "Ina kika buye ban ganki ba sai zuba ido nake." "Ina daki kunzo ne?" "Yes gamu a sitting room naga kowa ban dake." "Uhmm." Yace "Common my dear zo inga kwalliyar ki ai mana picture kinji." Yana fada ya kashe wayar ta mike ta dauki rigar ta da ta cire ta saka wata army green kalar shadda wacce tai mata kyau ta dada haskaka ta, red mayafi ta yafa a kafadar ta, ta saka wani flat red takalmi ta daura dankwalin ta ta nufi stting room tana shiga ya taso ya karaso waje ta, a bakin kofa ta tsaya ya durkusa a gaban ta ya zaro wani box a aljihun sa ya bude wani zuben gold ne mai tsada a ciki ya dago yana kallon ta yace "Will you marry me?" Kallon sa ta tsaya yi, ya sakar mata wani murmushi mai sanyi ido ta lumshe tana sakin murnushi tare da gyada masa kai, yan dakin ne suka hau tafi ya kamo hannun ta ya zura mata zoben ta dago hannun ta tana kallon zoben, ya mike ya karasa wajen ta nan aka hau daukar su pictures tare akai musu da amare da ango Jawahir na wajen Yaa Farouk bata san me akai ba, Hauwa kawar Najwa tace "Wannan shine Yayan naku?" Najwa tace "A'ah abokin Abdul ne fa." "Tab gaskiya shima yana son ta, ko Yaya za ayi?" "Uhmm ita tace Yaa Aliyu ba son ta yake ba." "Uhmm kinga banganshi ba ko? Amman duk wanda zai ji yadda yake mata wallahi yasan son ta yake." "To ni dai dukka ina son su, zan fi son ta da Yaa Aliyu dan indai da gaske Yaa Aliyu na son ta to tabbas ba son wasa yake ba dan ko matar sa da ta rasu hadasu akai amman ita kuma ace yana son ta after so many year of lossing his wife kai da naji dadi wallahi." Tai murmushi tace "Allah ya zaba mafi alheri ai Maryam abar so ce." "Gaskiya ba ruwan ta gata da hakuri sosai." "Uhmm Allah sarki." Wajen su tayo suka gaisa da Hauwa dan bata san zuwan ta ba anan mazajen suka tafi suka bar yan mata suna yinin su. da daddare aka kai Najwa gidan Abdul Suna zaune a dakin Najwa Muhammad ya kira ta, ba dan taso ba ta mike ta nufi bakin gate yana cikin mota layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Baby." "Masha Allah an gama biki lafiya Allah basu zaman lafiya" tace "Ameen" yace "Sauran namu ko?" Fuska ta rufe da hannu, yace "Eh mana dan kin nace sai kin gama karatun nan naki ne amman da nima kwanan nan zamuyi mu huta ko?" Shiru tayi yace 'Ke za a bari yar zaman daki." Ido ta zaro tace "Da girma na." Yai murmushi yace 'Gaskiya ke zaki sa musu ido su kasa sakewa ko?" Tace "Yaushe ango zai zo ne gida nake son tafiya." "Ah haba tin yanzu ai sai anjima kar ki damu ni zan kai ki gida da kai na." Shiru tayi tace "To ni dai su Ummi na ciki bari na koma kar su zo tafiya su ganni waje da kai." "Ke kuma gaki bafulatana ko?" "Uhmm." Yace "Ban gaji da ganin ki ba." "Uhmm please ba anjima zaka dawo ba." "Kawai dai dan kince su Ummi zasu fito ne." Motace tazo ta tsaya a wajen, ta juyo tana kallon motar, Gabanta ne ya fadi ta juya da sauri, Muhammad yace "Kamar Yayan ku ko?" Kai ta gyada tace "Shine" *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Allah mana rahma ya yafe mana. Amin* *Antty* [11/28, 13:42] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 62 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Aliyu tinda yai parking yake kallonsu, Muhammad yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali yace "Ko bakya so?" Tayi murmushi tana girgiza kai yace "Bakya son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni zan shiga ciki dan nasan su Ummi yazo dauka" "Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Aliyu da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Muhammad kuma ya nufi inda yake, sauke glass Aliyu yayi ya bude motar ganin Muhammad, ya fito yana kallon direct cikin ido, Muhammad ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Aliyu ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Muhammad yace "I am Muhammad Auwal" Aliyu ya gyada masa kai kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "Aliyu Suleiman." Muhammad yace "Masha Allah it's nice meeting you" Aliyu yace "Same" Muhammad yace "Alright zan koma, zamu rako ango sai da safe" Aliyu yace "Ohk." Suka kara musabaha sannan ya juya ya tafi, cikin mota ya shiga ya zauna, su Ummi suka fito ya kalli Ummi yace "Ummi Maryam fa?" "Tana ciki sai abokan ango sunzo zasu kawo su." Kallon Ummi yayi yace "Why?" "Ai ba sa bar ta ita kadai ba ko?" "Ita da waye a ciki?" "Ita da Basma ne." "Ummi please suzo mu tafi kawai me zasuyi mata dare nayi kalli agogo fa tara saura, sai yaushe kuma zasu zo please Ummi." "Shikenan." Ta juya ta shiga. Tana zuwa ta same su a zaune tace "Yayan ku yace ku taso mu tafi." Mayafin Najwa ta bude tace "Ummi dan Allah su bari su karaso." Kai Ummi ta girgjza tace "Me zasuyi miki, tinda sun gyara ko ina kuma ba abinda zasuyi miki kawai su taso nasan suma suna hanya dare yayi kiyi hakuri kinji." Kuka Najwa ta saka Ummi ta kalli su Maryam tace "Ku tashi mu tafi" Suka mike suka ce "Sister sai gobe." Ko kula su batai ba tana kuka suka fita. Maryam na fita ta shige baya, Basma ta shiga gaba, sai da Ummi ta lallashi Najwa sannan suka fito suka tafi gida. Bayan gama bikin Yaa Aliyu bai kuma damunta ba sam gaisuwa ke hada su, bayan biki da sati daya su Momy da Basma da Yaa Aliyu suka fara shirin tafiya. Yau a gidan Sitti ta yini, dan tinda aka gama biki bataje ba da dare tana shirin tafiya sukaji sallamar Yaa Aliyu, ya shiga ya zauna suka gaisa da Sitti, Sitti tace "Ai nazata zaka tafi baka zo mun gaisa ba." "Haba dai Sitti, in banzo ba ai ba zan tafi ba kenan." Tai murmushi tace "Uhmm nayi mamakin zuwan ka bayan nasan kai baka fiya son taro ba amman kana wata kasa ka dawo." "Akwai wani abu da nake so nayi ne Sitti kuma nayi kinga sai na koma." "Sauran wata nawa ka dawo?" "Nan da wata takwas." "To ni dai fatana kana dawowa kai aure kaji." Yai murmushi yace "Sitti kenan. Bari na tafi." "To dan nayi maganar aure ko, Maryam tana ciki tafiya zatai sai ku tafi tare ko?" Ya mike ya fita, ta kira Maryam tace "Kije ku tafi tare." Tace "Sitti sai da safe." Tunda suka dau hanya ita da Yaa Aliyu ba wanda yayi magana can yace "Gobe zamu koma." "Allah ya tsare hanya." 'Me kike bukata?" "Ba komai." "Kin tabbata?" Kai ta gyada, dai dai lokacin da ya shiga cikin gidan, ya dan saci kallon ta ya dauke kai, yace "Sauran na tafi ki cigaba da kula samari." Yana fada ya fice ta tabe baki ta fita tabi bayan sa. Washe gari suka tafi, Maryam da Basma har da kuka haka suka rabu. Makaranta suka koma suka cigaba da daukar karatu satin Najwa uku suka shirya zuwa gidan ta da Jawahir. Ranar asabar suka shirya zuwa wajen Najwa gida Jawahir tazo suka tafi sunga tarba wajen Najwa kamar tai musu me aka cika musu gaba da kayan abinci da na sha kala kala sai dare suka tafi. Abu daya ta kasa ganewa game da Yaa Aliyu yadda ya canja mata gaba daya, yakan yawan kiran ta tare da mata tambayoyi akan rayuwar ta da karatun ta, tin tana dar dar dashi ganin ba fada yasa ta dan sake take iya fada masa duk abinda take ciki, sai dai in yana bugar cikin ta akan Muhammad ne take shiru, amman bini bini zai kira ta wani abun lokacin ma ya rasa me zai fada mata, amman wannan ya bashi damar kara sanin ta da sanin a halin da take ciki. Yasan lokacin da take karatu da zuwa makaranta da komai. Zaune suke ita da Muhammad a harabar gidan su suna hira, bai yi awa daya da zuwa ba amman ta amsa wayar Aliyu yafi sau biyu, kallon ta yayi yace "Wai da wa kike waya ne?" "Yaya ne fa." Fuskarsa cike da mamaki yace "Wanne Yayan?" Tace "Yaa Aliyu." Jingina yayi da kujera yace "Wani lokacin ina jin tsoro Maryam." "Tsoran me kuma?" "Tsoron rasa ki." Wani murmushi tayi tace "Tayaya zaka rasa ni?" "Yayunki suna son rabani dake." Dagowa tayi tace "Kamar ya kenan?" "Yadda na lura dukkan su son ki suke." Da sauri ta dago tana girgiza kai dan bata son ana fadin haka, ita ta sani Aliyu tausayin ta yake kawai, Yaa Farouk kuma me yayi za a ce son ta yake bayan bai taba nuna mata ba in banda kyautatawa ita da Haidar me yake yi da za ace son ta yake. "Ke ai ba zaki gani ba, bansan kuma saboda me ba?" "Saboda na yadda dasu kuma na dauke su a matsayin yayye na kuma suma haka." Wani murmushi yayi yace "Shikenan ko a yanzu wani bai fada miki ba a gaba zaki gane tabbas son ki suke." "Dan Allah kabar fadar haka a duk lokacin da aka fadan ana tada min da hankali." "Akwai wanda ya taba fada miki kenan?" Mikewa kawai tayi tace "Zan shiga ciki ka gaida su Momy." Tana fada tai ciki, cikin wani irin yanayi, dakin ta ta shiga ta zauna tare da dafe kanta tana so ta gano son da ake cewa Aliyu yana mata sam ta kasa gano shi dan in zata tuna sam Aliyu bai son zama a inda take a baya dai da tana da cikin Haidar ta dan samu kulawar sa amman tinda Haidar yazo duk kulawar ta koma kan sa wanda sai ta kwana nawa bata ganshi ba, kuma ina tana waje bai faya zama ba, takura mata da ya fara akan Muhammad ne yaso ya tada mata hankali akan son sanin asalin ta, wanda take ganin tausayin ta da fargabar kar ta fada wani hali ne yasa yake bata wannan kariyar to tayaya za a ce Yaya yana son ta, ai Aliyu yafi karfin ta tasan ruwa ba sa'an kwando bane ba takai matsayin da zai so ta ba sam ta girgiza kai, kiran sa ne ya shigo taki dauka amman sai da ya kira sau uku sannan ta dauka murya a sanyaye, ya amsa sallamar tare da tambayar ta me yake damun ta? Ido ta lumshe tace "Ba komai." "A'ah Maryam muryar ki ta riga da ta fada tunanin me kike?" "Tunanin rayuwa." Ya dan ja numfashi yace "yana da kyau amman kar a zurafafa." "To." "Ina Haidar?" "Yana waje." "Ke kina ina?" "Ina daki." "Ok sai anjima." Ya kashe wayar, ta dafe kai tana mai ambaton sunan Allah, kawai dai kishin Muhammad ne yasa yake son yace son ta suke. Haka next zuwan nasa da yazo Aliyu ya dinga kiran ta fuska ya hade yace "Wai ke da waye ne?" "Yaya ne fa." Fuska ya kara hadewa yace "Ranan na miki magana akan Yayan ki na sonki kin ki yadda to meyasa yake yawan kiran ki." Wani kallo tai masa tace "Shikenan kuma ba zamuyi waya da dan uwa na ba" "Bance ba amman abun yai yawa yau da muharamin ki ne wallahi ba zan damu ba amman ni ina tsoro kar na rasa ki." "Kana kishi dai, yanzu kai dan yar uwar ka ta kira zan hanaka yin waya da ita ne? Ni kake dauren fuska dan ina waya da su, yaye nane, kuma dole ka amshe su a haka duk da ba ciki daya muke ba amman sun min abinda ko yaye na da muke uwa daga uba daya zasu yi min dan haka bana son wani abu ya shiga tsakanin ku, ba zan yadda su bata maka ba kaima kuma haka." Ganin ranta ya baci sai ya lallabata a haka suka rabu. Yau tin karfe biyar yake kiran ta amman wayar tana daki ita kuma tana tare da Muhammad da suke hira a compound din gidan ta bar wayar a daki ne dan tasan zai ta kiran ta ita kuma bata son ko da yaushe suna samun matsala da Muhammad akan wannan lamarin. Zaune suke suna hira cikin so da kaunar juna Muhammad yace "Dear tinda yanzu kuna asibiti karatun ya ragu, nasan da kun dawo ba wani karatu zakuyi kamar na baya ba ki bani dama azo a fara shirye shiryen auren mu, wallahi na kosa naga kin tabbata tawa ina tsoron rasa ki." "Jarumi baya tsoro." Ta fada tana murmushi kasa kasa, yace "Haka ne amman akan ki dole ayi dan ke din abar aji tsoro ce dan nasan akwai masu son kawon farmaki." "Hmmm to Allah zaba mana mafi alheri." "Ki ban dama na turo gida a saka mana rana." Dagowa tai ta kalle sa, ya sakar mata wani cool smile tai saurin yin kasa da ido, yace "Eh saboda asan da gaske nake kar wani yazo yai min kwab daya." "Aikin kenan kar a kwace maka ni, please ka rage kawo abu a ranka sannan akai na ka amshi kaddarar ka duk wacce zata zo mana." "Zanyi kokari." Bayan ya tafi ta koma daki ta samu missed call din Aliyu har guda biyar, zama tayi ta dafe kai ta fara tunanin me zata fada masa in ya kira, bata tsaida ma tsaya ba wayar ta, ta hau kara ta dauka ta kai kunnen ta, Yace "Ina kika shiga?" Yai tambayar Murya ba wasa, tace "Muhammad ne yazo." "Oh har yanzu kuna tare ko?" Shiru tayi, sai kawai ya kashe wayar, wayar tabi da kallo tana jin ba dadi dan bata son bacin ransa kwata kwata bama yadda yake kyautata mata. Samun kan ta tayi da neman layin nasa, yana gani ta kira amman bai dauka ba, kara kira yayi sai da ta kusan tsinkewa sannan ta dauki wayar, yace "Hello." "Yaya dan Allah kayi hakuri." "Uhmm da akai me?" Shiru tayi can yace "In baki da abin fada sai anjima." Ya kashe wayar, ajiye wayar tayi tana mai lumshe idon ta, kwanciyya tayi akan gado, sai bayan isha'i ta sauka kasa, Ummi ta gani da Haidar suna zaune, zama tayi a gefen Ummi, Ummi ta kalle ta tace "Me yake damun ki ne?" Kai ta girgiza tace "Ba komai." Jingina tayi da jikin kujera tana mai lumshe ido. Haidar ya tashi ya dawo kusa da ita yace "Adda kira min Abbi." Ido ta bude ta mika masa wayar ta, amsa yayi ya fara dailing number Aliyu yana kwance yaga kira da sauri ya dauka dan shima so yake yaji muryar ta dan ya saba da jin muryar ta duk bayan wasu lokuta, wanda ya zame masa jiki, jin muryar Haidar yasa yace "Ina Addan taka?" "Gata nan." Ya mika mata waya, ta amsa tana kaiwa kunnen ta, "Shine baki kirani ba?" "To Yaya ba na kira ka kashen waya ba." "Shine kikai fushi." "A'ah." "To ni na fada miki bana son kina kula samari ko?" Shiru tayi yace "Uhmm." "To Yaya ni yaya zanyi? Su Abba sun riga sun bashi dama yaya zanyi?" "Ki daina bashi fuska." "Hmmm to." "Oh Hmmm ko? Ba zaki iya ba ko?" "Nifa bance ba." "Bani Haidar." "To kayi hakuri." Ta bashi wayar tana mikewa, fita tayi ta bar wajen Haidar yace "Abbi ya aiki?" "Alhamdulillah Son ya makaranta?" "Alhamdulillah." "Abbi naga wani abu da nake so ka kawon." "A in ka ganshi?" "A school dazu." "To gobe in kunje kasa Baba Driver ya samar min picturen sai Adda ta turo maka kaji?" "To Abbi nagode." "Ummi fa?" Mika mata wayar yayi ta amsa, Ummi tace "Aliyu ya aikin?" "Lafiya lou Ummi ina yini?" "Lafiya yasu Yaya?" "Suna lafiya." "Masha Allah." Ta mikawa Haidar, Haidar yace "Abbi sauran kwana nawa?" "Kusan three month fa Son da saura." "Abbi i miss u." "Miss u more Son. Kunje shopping dis month?" "A'ah." "To zan turo muku kudi Adda ta kai ka kayi shopping kayi wasa kaji?" "To Abbi nagode." "Ina Addan taka?" Tana kitchen." "Bata wayar." Ya tafi kitchen ya bata wayar, amsa tayi ta kai kunne yace "Uhmm me kike a kitchen?" "Abinci zanci." "Baki ci abincin rana ba ko?" "Uhmm a'ah." "Kina nan da rashin cin abincin ki ko? Shiyasa gaki nan kullum bakya gaba." "Kai Yaya kaima fa ba son ci kake ba." "Oh ni zaki kwaikwaya?" "In kanwa ta kwaikwayi Yayan ta menene a ciki?" "Hmmm zan kamaki ne, but seriously kina cin abinci kinji my dear." Murmushi ta dan saki tace "Ok Yaya." "Kici abincin i will call u later." "Alright." Ta kashe wayar tana zubo abinci, falo ta dawo ta zauna tana cin abinci tana kallo, Ummi tace "Me ya hadaki da Aliyun ne?" "Akan Muhammad ne." "Me Muhammad din yayi?" "Ummi Yaya baya son ina kula samari wai kar abinda ya faru kwanaki ya kara faruwa kuma ni naga Muhammad din kawai nake kulawa." "Hmmm Allah kyauta to, banda abinsa tinda Muhammad yasan komai ai shikenan wanin ne dai bama fata ya kara zuwa bare ai ta fada masa rayuwar ki, tin kana haduwa da mutanen kirki har kazo ka hadu da na banza." "Ummi shiyasa nake tsoron mazan nan, wallahi basu da tabbas a haka ma sun nuna suna son ka sun wulakanta ka ina ga ba wani son ka suke ba, rayuwa dai ta baci kowa ba amana Allah yasa mudace." "Amin. Shiyasa ban fiya son doguwar soyayya ba shima Muhammad zanyiwa Abbi magana ai masa magana in da gaske yake ya turo iyayen sa ayi komai a huta, kusan shekara kuna tare." Kasa tayi da kanta, Ummi tace "Ko bakya son sa." Shiru tayi Ummi tai murmushi tace "Shikenan." *Allah kai mana rahma kasa muyi kyakyawan karshe amin." *Antty* [11/29, 18:54] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 63 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ta mike ta kwashe kwanukan takai kitchen ta dawo ta wuce sama, har tayi shirin bacci Muhammad ya kira ta, dauka tayi tace "Baka kwanta ba?" "Yanzu zan kwanta nace bari na kira My happiness." Murmushi ta dan saki, kira taji yana shigowa ta dauke taga Aliyu ne ido ta dan zaro tace "Please bari na amsa wani call." Ta kashe ta dauki ta Aliyu, "Dawa kike waya?" Ya tambaya, "Uhmm uhmm da Jawahir ne." "Me kuke fadi?" "Yaya akan makarana wani aiki?" "Wane aikin?" Idon ta ne yai tsilli tsilli yace "Uhmm ina jin ki." Wani case ta lalubo ta fada masa yace "Ganewa ne baki ba ko me?" "Eh." Bayani ya hau yi mata, tana ji sosai take ganewa, Muhammad ya kira yafi sau uku sai yaji call waiting sun dauki kusan awa daya sannan yace "Ina fatan kin gane?" Kai ta gyada yace "To kije ki kwanta nasan dare yayi muku sai da safe." "To Yaya nagode." Ta kashe wayar, tana kashewa Muhammad na kiranta, dauka tayi yace "Dawa kike waya?" Shiru tayi tana mamakin wai meyasa suke mata haka ne kowa bai son tai waya da wani, gwara shi Muhammad ta sani kishi ne Aliyu kuma tausayi ne da kulawar da yake mata, dan tsaki ta saki tace "Suna sani ina yin karya." "Hello!" Ya fada tace "Uhmm ina jin ka." "Nace dawa kike waya?" "Yaya ne yana koya min wani karatu ne." "Uhmm Yaya a wannan lokacin yake koya miki karatu." "Eh!" Kawai ta fada a dan fusace wannan yasa yace "To shikenan sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Ta kashe wayar kawai. Kwanciyya tayi tana mai rufe idon ta kawai. A cikin satin Abba ya kira Muhammad akan ya turo magabatan sa akan zancen auren su da Maryam, Muhammad ma da yake a shirye yake yana fadawa Dadyn sa, Dadyn sa yasa ya tambaya yaushe zasu zo suka saka rana, lokaci nayi suka shirya da Dadyn sa da yan uwansa biyu da aminin sa sukaje, sosai akai musu tarba sukace dan su yaga yarinya yana so in an basu dama zasu kawo kudin saka rana da komai na biki dan su haka suke yi, su Abbi suka yadda akan haka. Bayan wata daya suka dawo da kudin saka rana da sadaki har da lefe suka saka wata uku masu zuwa wanda a lokacin su Maryam sun samu hutu suna komawa shekara daya zasuyi karatu sun gama gaba daya. Bayan tafiyar su Ummi da Mami suka shiga ganin uban kayan da aka kawo kamar wanda za a bude shago dasu, kaya ne masu kyau da tsada ko akwati nan har da ruwan gold aka hada aka yi su, Lokacin da Mama ta gani ba karamin tashin hankali ta shiga ba, dan Mama irin matan nan ne masu bakin ciki ba sa son abu ya samu wani sai su kadai, Inna kuwa sai saka albarka take har da kuka na murna Maryam zata samu gidan hutu mai sonta, gwala gwale kuwa an saka mata har guda uku, banda zobe da awarwaro duk a ciki, bangaren Ummi aka mai da kayan su Anty Asiya, Najwa duk sun zo sun ga kaya. Maryam ce zaune a dakin ta tana neman layin Jawahir tana fara ringing ta dauka ta kai kunnen ta Jawahir tace "Ke albishirin ki?" "Goro ya akai?" "An kai kayan auren Yaa Khalifa fa, nan da wata uku muna da biki." "Ah haba Masha Allah Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya." "Amin." "Nima yau aka kawo lefe na fa." "Me?" "Abinda kika ji." "Dan Allah da gaske kike ko wasa kike?" "Wallahi da gaske nake." "Lallai ma Maryam amman da waye wannan, ko da yake bama sai kin fada ma nasan yar gida za ai ni nasan shiyasa ma baki fadan ba dan kina ta boye boye ko? Allah Maryam baki kyauta min ba ace za a kawo kayan auren ki ban sani ba sai bayan an kawo." "Kiyi hakuri daga zuwa tambaya fa su Abba sukace ayi komai a gama shine fa suka hado komai da komai ai ba yanzu bane bikin sai mun gama da asibiti." Wayar kawai Jawahir ta kashe ta tafi wajen Momyn ta, tana daki ta shiga tace "Momy kinsan me?" "A'ah." "Yau aka kai kayan auren Maryam fa." "Wacce Maryam." "Maryam dina amman Momy wai yanzu take fada min" "To kiyi hakuri kila sha'afa tayi yanzu ba gashi ta fada miki ba." "Bari naje gidan nasu." "Ki gaishe da Ummin tata kice ina mata Allah sanya alheri." Ta fita driver ne ya kai ta, tana shiga ta wuce dakin Maryam kwance ta same ta suna waya da Muhammad tana shiga ta katse wayar tana fadin "Tuba nake." Zama tayi tace "Ai kya tuba tunda kin min laifi." "Ai na fada miki uzuri na." Baki ta tabe tace "Ina kayan?" "Suna dayan dakin kije ki gani." "Ke fa?" "Ni kunya nake ji wallahi." Mikewa tayi ta fita acan ta samu su Ummi suka gaisa Ummi tace "Sai kikaji an kawo kaya?" "Ai yanzu na gamai mata Ummi bafa ta taba fada min ba." "Ai abun ne yazo a haka ba mu zata haka da wuri za ai ba." "Allah sanya alheri." Jawahir ta matsa wajen kayan tana kalla tin daga akwatin nan taso ta shaida kayan amman ganin wannan lokacin su ake yayi yasa ta share kawai ta fara kallon kayan wasu ta sansu dan Momyn ta ita ta hada kayan wasu ita tayo order Muhammad ya gani yace yana son su amman sai ta share a haka ta gama gani ta koma wajen Maryam tace "Wai waye wannan mai sa'ar?" "Ki bari zan kirasa sai ku gaisa." "Bana so sai yanzu." "Nifa ba laifi na bane." "Laifin waye?" "Nashi ne." "Hmmm." Wayar Maryan tai kara ta dauka takai kunne ta mike ta fita, yace "Ke da waye ne?" "Jawahir ce tazo tana ta mita ban fada mata za a kawo kaya ba." Dariya yayi yace "Jawahir kenan jiya ta ishe ni da sai na kai ta wajen Antyn ta." "Yanzu dai na fada mata anjima zaka zo sai ku gaisa ko?" Dariya yayi yace "Shikenan sai anjima zan biyo sai mu wuce gida tare." "Shikenan." Sai bayan magariba yazo suka fita dan a bakin gate ya ajiye motar, yana ganin su ya fito, ido Jawahir ta zaro tana zancen zuci kenan abokin Yaa Khalifa ne saurayin Maryam kenan tare zasuyi aure haba no wonder naga wasu kayan iri daya da nasa. Karasowa yayi yace "Lil sister." Jawahir leke leke take tana son ta ga ta ina zataga saurayin Maryam, Muhammad yace "Me kike nema ne?" Kallon sa tayi tace "Kai da wa kazo?" "Ni kadai." Ya fada yana maida kallon sa kan Maryam ya dan matsa gefen ta yace "My wife!" Ido Jawahir ta zaro, Maryam tai kasa da kai tace "Ina yini?" "Lafiya lou yasu Ummi da Haidar?" "Kowa lafiya." Ya kalli Jawahir da ta kasa magana sai kallon su take ya sakar mata murmushi yace "Finally meet ur in-law Maryam." Ya kalli Maryam yace "You too meet your sister in-law Jawahir!" "Please Yaya are u serious?" "Yess!" Wata rumguma taiwa Maryam tace "Da gaske Sister?" Kai ta gyada sai ta fada jikin Muhammad tace "Amman Yaya naji dadi sosai kasan wacece kuwa Maryam wallahi ka dace Allah ya barku tare ya bada zaman lafiya amman kun dace da juna." "Ni kadai nai dace?" Dariya tayi tace "Itama tayi dace amman ai ba zan yabe ka ba kar taga kamar dan d'an uwa nane ta gani da kanta." Murmushi kawai Maryam take, Jawahir tace "Amman Yaya tin yaushe kuke tare?" Maryam ya kalla yace "Tin kan na ganta a gida na santa." Ido ta zaro tace "Amman kuka dinga boye min ko? Sam ban taba ganewa ba kai Yaya? Ko da yake ita ce ma" "A'ah ba ruwan princess, saboda ni na hanata fada miki nasan ki da surutu." "Oh ko? Ai kuwa zakaga ina da surutu sai naje gida duk na fadawa kowa na gidan nan har Dady." Maryam tace "A'ah ni dai kiyi hakuri." Dariya tayi tace "Nasan wa kike jin kunya wallahi ita zan fara fadawa kai koma kiranta zanyi ne tin kan na koma gida." Hararar ta Maryam tayi tace "Ni zan shiga gida sai da safe." Muhammad yace "Ok sai munyi waya." Ta kalli Maryam tace "Bye." Jawahir dake cike da mamaki na wai da gaske dai Yayan ta shi zai auri aminiyar ta, tace "Ok bye." Suka shige mota suka bar wajen. Canada A gajiye ya shigo gidan ya samu Mami da Basma na kallon waya, karasawa yai ya leka yace "Me kuke kalla?" Basma ta dago tace "Yaya lefen Maryam aka kawo." Cak ya tsaya, jin kamar bai ji mai tace ba yace "Laifen wa?" "Laifen Maryam." "Wacce Maryam?" "Ta Ummi mana." Mami ya kalla dan samun karin bayani yace "Mami da gaske ne wai?" "Kai ta gyada tace "Eh an kawo lefen Maryam yau an saka wata uku kaga lokacin ma kana can za ayi." Bai kuma magana ba sai hanyar dakin sa da yayi, yana shiga ya zauna a gefen gado kansa ya dafe jin abun a bazata wai an kawo lefen Maryam wato aure zatayi kai ya dafe ya dauko wayar sa neman layin ta ya fara amman ba a dauka ba sai da ya kira sau uku amman ba a dauka ba wayar sa yai cilli da ita ya runtse idon sa. Mikewa yayi ya cire kayan sa ya shiga yin wanka, yana fitowa ya haye gadon ya kwanta wani iri ya dinga ji a cikin zuciyar sa, daga baya ya tashi zauna yana jingina da gado, ido ya lumshe kawai yana tunanin wani abu, daga baya ya mirginawa ya kwanta wayar sa yaji tana kara da sauri ya tashi ya dauka yana dubawa ya zata zai ga Maryam ce amman sai yaga Ummi ce sai da ta kusan tsinkewa ya dauka ya kai kunnen sa yai sallama cikin sanyin murya. "Lafiya Dr?" "Ina yini Ummi?" "Lafiya me yake damun ka?" "Ba komai." "Anya kuwa Dr?" "Ba komai Ummi." Yai maganar cikin jarumta dan bai so ta san halin da yake ciki. "To shikenan na bugu na fada maka an kaso kayan Maryam ne." "Ok." "An saka wata uku." Numfashi ya fesar mai zafi yace "Allah kaimu lokacin." "Amin." "Ina Haidar?" "Yana wajen Inna." "Ok sai anjima kaina ciwo yake Ummi zan dan kwanta ne." "Ni ai nasan akwai abinda yake damun ka kasha magani kaji." 'To." Kawai ya fada ya kashe wayar, kan sa ya dafe yana kwanciyya ido ya rufe so yake ya runtsa amman ya kasa wani irin yake ji a zuciyar sa abinda bai taba ji ba kenan. * Maryam na shiga daki ta ga missed call din Yaa Aliyu, zama tayi tana dafe zuciyar ta dan tinda Muhammad ya turo iyayen sa take cike da wani fargaba ba kamar yau da aka kawo lefen ta gaba daya ji tayi ta rasa nutsuwar ta, fara neman layin nasa tayi amman har ta gama ringing bai dauka ba sai da ta kira sau uku amman bai dauka ba ajiye wayar tayi sai kuma ta dauka ta fara rubuta masa sako "Yaya ina ka shiga haka? Naga missed call din ka na kira baka dauka ba. Ya kake ya aiki?" Ta tura masa yana kwance yaga dukkan missed din nata amman bai dauka ba jin shigowar sakon ma yagani amman bai duba ba sai matsar da wayar da yayi, dan ya rasa hope me ma zai fada mata, me zaice mata, hakika ya fara sarewa, ranar kwana yayi bai bacci ba kan safe ya farka da wani ciwon kai, da zazzabi da kyar ya shirya ya fito, a falo ya samu Mami tana zaune ya durkusa ya gaishe ta, ta kalli shi tace "Dr me yake damun ka ne?" Ido ya lumshe ya mike yace "Zani asibiti Mami bana jin dadi ne." "To sannu Allah sauwake." Ya mike ya fita, a asibiti sai da aka saka masa ruwa da magunguna amman kamar dada masa ciwo ake. Sai yamma ya koma gida ba kowa a falo dakin sa ya koma ya kwanta kawai. Sai bayan goman dare Mami taga bai dawo ba ta leka taga motar sa a waje dakinsa ta shiga ta same shi kwance cikin bargo yana rawar sanyi da sauri ta karasa tana fadin "Subhanallah Aliyu jikin ne?" Ta karasa ta dafa sa zafi taji a jikinsa ta dauke hannu da sauri tace "Innalillahi wainna illahir rajiun." Ta mike ta fita da sauri mai gidan ta ta fadawa, ya shigo ya daga shi yana fadin "Sannu Dr!" *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan, Allah mana rahma. Amin.* *Antty* [11/29, 18:54] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 64 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Wayar sa ya dauka ya kira likita ba ajima ba likitan ya karaso, taimako ya bashi wanda nan da nan zazzabin ya sauka, bacci ya dauke shi, washe gari da ciwon kai ya tashi sai rashin karfin jikin sa. Wanka kawai yayi ya koma ya kwanta wajen karfe takwas Mami ta shigo dakin a gefen gado ta zauna ta taba jikin sa, ido ya lumshe yana me kokarin mikewa "Yi kwanciyyar ka Aliyu." Kwanciyya yayi yace "Ina kwana Mami?" "Lafiya lou Son ya jikin?" "Alhamdulillah." "Allah kara sauki." "Amin Mami." Fita tayi bata jima ba ta dawo da kayan abinci taimaka masa tayi ya zauna tana fadin "Kaci abinci sai kasha maganin ko?" "To Mami." Ta fara bashi kadan yaci yasha magani ya koma ya kwanta, maganin da ya sha shi yai ta saka shi bacci dan ranar yini yayi yana bacci Ummi ta kira ma sai Mami ce ta amsa wayar tace yana bacci, sosai Mami ta kula da Aliyu, haka yai ta ciwo a daddafe a daddafe wanda lokaci kadan ya rame da yaje asibitin su akai masa check up likita yace ya rage tunani da damuwa. Maryam ma ba karamin damuwa tayi da rashin kiran nasa ba, gashi Ummi tace mata bai da lafiya ko ta kira baya dauka wani lokaci ne ma Mami ke dauka ko tace yana bacci. * Zaune suke, Maryam sanye da Hijab har kasa, kanta a kasa sai murmushi take, Muhammad yace "Oh dariya na baki, Yes I have been counting down since but kamar ba a tafiya fa." Zaro ido tayi ta kallesa, yace "Sure, ni daman a rage wallahi da yawa lokacin" "Aa ba wani lokaci mai yawa." Ya lumshe ido ya bude yace "Wallahi da yawa Baby" Maryam ta kallesa tace "Kamar yau ne fa in muna raye" "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Promise me something please...." Maryam tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baza ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I will and will never leave u for any reason" Lokaci daya jikin Maryam yayi sanyi tace "Ae an riga an baka ni, so there is nothing to worry about" yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins" Da mamaki tace "Cousins dina kuma? Again?" Ya d'an yi murmushi yace "Yes kada su min fin karfi...." Maryam ta kasa daina masa kallon sa da mamaki tace "Sau nawa zan ce maka su Yaa Aliyu Yayyena ne ba so na suke ba" Muhammad ya girgiza kai yace "I saw their reactions ranan, more especially wanda baya garin nan" Maryam gabanta ya shiga faduwa, Muhammad yace "They might not tell you now amma kada watarana su zo su ce suna sonki, ki mance alkawarin mu, kada ki min haka please Maryam..." Cike da damuwa ya fadi haka, Maryam ta ji kamar ta fashe da kuka tace "Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na cikinsu duk yayyena ne su wallahi, ba komai tsakanin mu, sanin tarihi na bashi zai saka kana jin haka akan su ba, suna so na kamar yadda suke son yan uwan su, haka suke ga duk kannen su, shiyasa nima suke treating dina thesame, they are only disturb saboda kar naje inda za ai min gori ko na samu matsala." yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba gimbiyata, reminder ne" Maryam ta boye fuskarta da Hijab, yayi murmushi yana kallonta, murya can kasa yace "I love you." "I do love u too." Agogo ya kalla ya mike yace "Am going My Happiness." "Since now? "Yes Ammi ta aiken so that is why." Ta mike ta rakasa gate, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace "Thanks so much." * Bayan sati daya, wayarta dake hannu ta danna sannan ta kara a kunnen ta, Aliyu na kwance ya mike yana duba wayar, yana ganin sunan ta ya runtse idon sa yana tunani ya dauka ko kuwa yana son ya dauka baya son ya kara fama inda ke masa ciwo ba, har wayar ta katse yana tunanin, sai da wayar ta kara shigowa sannan ya dauka ya kai kunnen sa tare da yin sallama, amsawa tayi tana fadin "Yaya ya jikin ka?" Ido ya lumshe yace "Alhamdulillah." "Yaya me yake damun ka?" "Ciwo ne daga Allah." "To Yaya kana cin abinci?" "Eh." "Magani fa?" "Eh." "To Allah kara sauki." "Amin ya makarantar?" "Alhamdulillah." "In Son dina?" "Yana nan." Sukai shiru a hankali tace "Yaya ranan naga missed call din ka na kira baka dauka ba daman zan fada maka cewar an kawo....." Tari ya fara da wata irin kwarewa yayi sai kace shine yake maganar nan ta hau masa sannu amman ina sai da ya ajiye wayar da kyar tarin ya tsaya ya koma ya kwanta yana dafe kirjin sa, yana mamakin kansa Bai san yaya zai ba, amman zai daure ya cire damuwar nan ya karasa abinda yazo yi ya koma gida shi kuma tashi kalar kaddarar sa ya rasa matar sa ga wata jarabawar Allah ya bashi ikon cinye jarabawar sa amman halin da yake ciki a yanzu yana ji a da bai shiga kamarsa ba, kwanciyya yayi sai kuma ya mike yana jingina da gado. A haka ya dinga ciwon sa shi kadai yasan me yake damun sa Mami sai dai taga duk ya rame ya kara rage magana da walwala kuma in tai magana sai yace ba abinda yake damun sa har ta hakura ta saka masa ido. A haka ya cinye sauran lokacin sa ya fara shirin komawa, haka ya shiga kasuwa yayo wa su Maryam da Haidar tsaraba mai yawan gaske. A haka yai booking flight ya sanar da Ummi zuwan sa. Maryam na zaune sukai waya da Aliyu duk da danna waya take amman gaba daya hankalin ta na kam wayar da Ummi keyi suna gamawa ta juya tana fadin "Ummi Yaya ne zai dawo." "Eh shine zai dawo jibi." "Masha Allah. Allah kawo shi lafiya ya tsare. Amin." Murna Maryam kasa boyuwa tayi sai dai can ta koma ta zauna tana fadin "Ni kwana biyu yama daina kira na tinda yayi ciwon nan." "Haka Mamin ku ke min complain ya daina walwala gaba daya." "Uhmmm." A satin Maryam ta gyarawa masa dakin sa, ta wanke ban dakin sa komai yakoma fess dashi. Ranar da zai dawo kitchen ta shiga ita ce girka wannan dafa wancan ita da Haidar sai murna suke suna gamawa ta shiga suka shirya ita da Haidar dan zuwa tarbar sa. Saukowa take daga bene sanye da doguwar riga orange kala mai haske, tayi rolling kanta da mayafin rigar da aka sakawa stone coffe kala, sai tashin kamshi take waya ce kare a kunnen ta, falon ta sauko ta tadda Ummi ma a tsaye kallon Ummi tayi tace "Ina Haidar din?" "Ya fita." "Muje to." Suka fita, a harabar gidan suka same shi tsaye yana ganin su yace "Ummi kuyi sauri." Ummi tai murmushi, suka karasa wajen mota driver ya bude Haidar ya shiga gaba, Maryam da Ummi suka shiga baya motar suka tayar suka bar harabar gidan. Suna isa Airport din taji gaban ta yai wata muguwar faduwa, da sauri ta daura hannu ta ta dafe kirjin ta, ta bude mota ta fita, a lokacin har jirgin su Aliyu ya sauka an fara saukowa, Haidar sai lekawa yake kamar ance ya daga kansa ya hango Aliyu tafe yana jan trolly dinsa, Sanye yake da bakin dogon wando da ornage kalar riga mai dogon hannu sai top baka, idon sa sanye da bakin glass, kafar sa cikin takalmin sa sau ciki, ya kara haske sai dai ya rame, Haidar dake rike da Ummi ya saki hannu Ummi ya kwasa a guje yana fadin "Abbi! Abbi!" Yadda Haidar ke kiran Abbi yaja hankalin mutane da yawa a ciki har da wata mata da miji da suma saukar su daga jirgin kenan, matar na da ciki sai mijin ta dake rike da hannun ta dayan hannun yana jan trolly, tsayawa kallon yaron sukai, da sauri Maryam ta dago ta hango Aliyu yana murmushi kafin ya durkusa ya bude masa hannu Haidar ya fada jikin sa yana fadin "I miss you Abbi." Rungume shi Aliyu ya karayi a jikin sa yana jin wani so da kaunar yaron na dada shigar sa, "Miss you my Son!" Sun jima a haka sannan Aliyu ya mike dashi suka nufi wajen Ummi, Maryam na ganin sa gaban ta ya kara yankewa ya fadi da sauri ta juya tana dafe kirjin ta, da kallo kawai ya bita ya karasa ya durkusa a gaban Ummi, Mata da mijin da suka kasa daina kallon Aliyu da Haidar ne suka sauke wata ajiyar zuciya, sannan suka kalli juna, Matar ce tace "Honey kaga abinda na gani kuwa?" "Na gani Baby." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yaron yai kama da Yaa Haidar sosai." Ajiyar zuciya mutumin ya sauke yace "Ina ma Haidar ya bar baya, da tabbas ni zan maye masa gurbin mahaifin sa amman Allah baiyi ba." Idon matar ne ya ciko da kwalla, mijin ya saka handkerchief ya goge mata yana fadin "Ki musu addu'a kawai." Hawaye ne ya zubo mata, "Ko dai......" "Ko dai me? Kila kamace, kina ganin yaron da uban suna kama suma, kawai dai kama ce." Kai ta gyada tana goge hawayen dake zuba a idon ta, janye ta yayi suka bar wajen suka nufi inda su Aliyu suke, da suka karasa sai da suka kara kallon su Aliyu da Ummi ta dafa kansa tace "My Son barka da zuwa." "Yauwah Ummi da fatan na same ku lafiya." "Alhamdulillah!" Kai suka dauke, Maryam kuma jin gaban ta na tsanan ta faduwa ta dago da sauri, tana kallon mutanen wata irin juwa taji tana mata yawo aka, da sauri ta dafe kanta tana mai cigaba da kallon mutanen da suka nufi fita a wajen, Ummi ce ta juya taga Maryam a wani hali dafe da kai dayan hannun akan kirji da sauri ta karasa tana fadin "Lafiya." Hanyar da mutanen suka bi ta hau nunawa Ummi ta kalli wajen taga mutane na wucewa da sauri ta dawo da kallon ta gun Maryam wacce take kokarin zubewa a wajen da azama Aliyu ya taro ta yana fadin "Daman bata da lafiya ne?" Kai Ummi ta girgiza daukar ta yayi cak, suka bar wajen a cikin mota ya kwantar da ita yana bata taimakon gaggawa, da kyar numfashin ta ya dawo sai kuma bacci da ya dauke ta, gida suka nufa suna shiga ya bude mota ya dauke ta sukai ciki, dakin sa dake kasa ya shga da ita ya ajiye ta akan gado, first aid box ya dauko yana dubata sannan ya dauki wayar sa ya fara neman layin Farouk. Yana dauka yace "Ga text nan na maka kai sauri ka kawon magungunan." "To Hamma." Ya kashe wayar, Ummi ya juyo ya kalla yace "Ummi me yake damun Maryam?" Zama tayi a gefen gadon tace "Bata fada min ba, kamar yadda kai ma kaki ka fada min, Aliyu ka ganka kuwa? Kalli yadda ka rame Aliyu me yake damun ka dan....." "Kar ki hadani da Allah Ummi, zan fada miki insha Allahu." Kai ta girgiza tace "Zurfin ciki ba inda zai kai ku, gwara ku fito, ku fadi abinda ke damun ku ko a taimaka muku." Murmushi yayi ya mike yana fadin "Bari nai wanka." Ya dibi abinda zai bukata ya shiga bandaki, da shirinsa ya fito ya samu Ummi bata dakin sai Haidar, ya dauke shi suka fita yana tai masa surutu shekara daya kawai amman sai yaga yaron ya girma sosai, a falo suka zauna Ummi ta sauko tace "Dr Abinci fa?" "Ummi sai anjima bari naje wajen Hajiya Inna." Ya fita rike da Haidar, bai jima da fita ba Farouk ya shigo rike da ledar magani, amsa Ummi tayi tace yana wajen Inna can ya tafi yai masa sannu da zuwa tare suka tafi wajen su Mami da Mama da ta amsa masa sallamar ba yabo ba fallasa. Sai da akai isha'i suka dawo kuma har lokacin bacci Maryam take, da kyar Ummi ta matsa masa yaci abinci sannan ya koma daki, a yadda ya barta a haka yazo ya same ta, ya zauna a resting chair yana danne danne a waya, motsin ta yaji, ya kalle ta mikewa tai zaune tana kalle kallen dakin, "Sannu." Taji muryar sa da sauri ta juyo sai ta dauke kanta ya karaso ya zauna agefen ta yace "Me yake damun ki?" Kai ta girgiza ya kure ta da ido tai saurin yin kasa da kai yace "Fada min." "Yaya ba komai." "Haba My Baby Sis tell me kinji." Da sauri ta dago tana kallon sa shima ita yake kalla, ya rame sosai, kai ta dauke tace "Yaya baka da lafiya ne?" "Me kika gani?" "Duk ka rame." "Kema haka?" Kai ta kas dashi ta dire kafar ta a kasa tana fadin "Bari naje daki." Kan yai magana ta fice, ya koma ya zauna yana jingina da kujera, daki ta shiga ta cire kayan ta tai wanka, tare da daura alwala, tana fitowa ta saka kaya ta hau yin salla sai da ta idar ta fara addu'a sannan ta dafe kanta, tunani ta fara me ya same ta haka? Kasa tuno komai tayi wannan yasa ta mike ta haye gado, tana kwanciyya ana bude dakin, ta dago tana kallon Ummi, ta shigo, mikewa tayi tana kallon ta, Ummi ta zauna a gefen gado, ta kamo hannun Maryam tace "Me yake damunki Daughter?" Kai ta hau girgizawa sai hawaye kuma, Ummi ta daura hannun ta akan fuskar Maryam tana goge mata hawayen dake kan fuskar ta, kai ta girgiza mata tace "Ki daina kuka kinji daughter me yake damun ki fada min." Ta bude baki zatai magana kenan aka bude dakin Aliyu ne ya shigo hannun sa rike da leda, ya mikawa Ummi yace "Ummi taci abinci ta sha maganin nan kan gobe mu shiga asibiti." "To Aliyu." Ya juyo ya kalli Maryam, karasowa yayi gaban gadon yace "Ki daure ki sha maganin kinji?" Kai kawai ta gyada masa ya mike ya fita, Ummi ce ta kawo mata abinci da kyar taci sannan ta bata magani ta sha da kyar ta koma ta kwanta. Wasu irin mafarkai ta dinga yi wanda ta kasa gane abinda ya faru, da ta tashi kuma da safe ta manta, cikin kwana daya kawai tayi zuru zuru. Zaune take a falon sama tayi nisa cikin tunanin da take taji an tafa hannu, da sauri ta dago taga Yaa Aliyu, ajiyar zuciya ta sauke ya zauna a kan kujera yana bin ta da kallo, kanta tayi kasa dashi tace "Ina kwana?" Bai amsa ba sai kallon ta da yake, jin bai amsa ba yasa ta dan dago, ido suka had'a tai saurin kautar da idon ta, yace "Tunanin me kike?" Kai ta girgiza yace "Daman baki da lafiya ne?" Kai ta kara girgizawa, kallon ta yai yace "Ciwon baki kike ne?" Kai ta girgiza tare da fadin "A'ah." kamar zatai kuka. Wannan yasa ya dogo yana kallon ta, matsowa yayi yace "Maryam yanayin ki kawai ya fada min kina cikin damuwa fada min me yake damun ka?" "Yaya yanayin ka yafi nawa nuna kana cikin damuwa, kaga yadda ka rame kuwa?" "Kar ki damu da nawa, ciwon da nayi ne amman Alhamdulillah naji sauki." "Allah kara sauki." "Amin kefa?" Ya fada yana zuba mata narkakkun idanun sa wanda tana dagowa ta mai da kan ta kasa..... *Allah ya jikan musulmai Allah ya kyautata namu zuwan, Allah yai mana rahma ya yafe mana. Amin* *Antty* [11/30, 12:53] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 65 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Dagowa tayi tana kallon sa, ya dage mata gira yace "Yes common tell me." Idonta ta saukar kasa tace "Yaya bansan me yake damu na ba, kwanakin nan duk banajin dadi bana jin nishadi bana jin farin ciki, rayuwa kawai nake yi Yaya." Ta karasa maganar murya na rawa saboda yadda kuka ya taho mata kan ta ta hade da kujera tana sakin kukan ta, ya taso ya durkusa a gaban kujerar da take yace "A yadda na san ki, kina da addini da karatun Alkur'ani shin kina kan yi har yanzu?" Dagowa tayi tana kallon sa dan yadda yai maganar cikin damuwa, duk da tasan Aliyu na son ta, ido ta lumshe hawayen dake cikin idon ta ya gangaro, a hankali yace "Bana son damuwar ki, in har na ganki cikin damuwa ina daura alhakin damuwar akai nane, in da yadda zanyi naga na cire miki ko wacce irin damuwa yanzu taso muje kinji." "Ina zamu?" Mikewa yayi yace dauko mayafin ki ya juya ya sauka, a hankali ta mike tana tafiya da kyar ta shiga ta dauki mayafin ta tayi rolling, ta saka flat takalmi ta fito, a hankali take tafiya har ta fito falon nasu yana tsaye rike da mukullin mota, Ummi ya kalla yace "Ummi zamu fita?" "A dawo lafiya." Maryam ta karasa ta zauna kusa da ita, Ummi tace "Menene?" Kai ta langwabe tace "Jikin ne?" Kai ta girgiza, Ummi tace "To tashi kije yana jiran ki." Mikewa tayi ta daga mata hannu tace "Sai mun dawo." "Allah ya kiyaye hanya." "Amin." Ta fita, a wajen motar sa ta same sa tsaye ya bude mata gidan gaba ta shiga ya zagaya ya shiga cikin mota ya bar gidan, Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo, wani murmushi ta sakar masa shima ya mai da mata, dan tina wajen, wajen ya kawo ta kusanin lokacin haihuwar ta, lokacin taji dadin wajen ya debe mata kewar wajen, shima Maryam matar sa yake kawo wa wanda tin da ta mutu bai kuma zuwa ba sai da ya kawo Maryam wancan karan sai wannan karon. Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo murmushi shimfide a fuskar ta tin a haka ta samu nutsuwa da ragin damuwar ta sosai da sosai. Yana kallon ta yace "Mu shiga park ki hau lilo?" Kai ta gyada suka nufi wata hanya suka shiga, a bakin kofa ya tsaya ya biya suka shiga, liluka ne kala kala a wajen ta shige ta barshi tsaye yana kallon ta ita ce hau kan waccan ita ce ta sauka a ta hau kan wancan a haka suka kwashe sama da awa daya, wanda suna fitowa suka shiga wani waje lemo aka kawo musu da menu sukai selecting abinda suke so, aka kawo musu sai da suka gama sannan suka fita suka fara zagaye wajen sune shiga can fita can haka sukai sha yawo sai da suka gaji suka shiga wani wajen suka zauna lemo aka kara kawo musu da menu na abinda suke so basu zabi komai ba dan a koshe suke, lemon kawai suke sha, ya dago ya dan kalle ta yace "Fada min me yake damun ki?" Fuska dauke da murmushi, ta kalle shi tace "Ka kawar min da komai." "Nagani amman before fa?" "Yaya ban sani ba, na fada maka yanayin da nake tsintar kai na a ciki, Yaya wani lokacin ji nake kamar nai ta kuka, a jiya na shiga rudani na wani mafarki da nayi, ban gane komai ba naso na tina amman na kasa komai ya gudar min amman abun ya tsaya min a rai." "Mafarki ba gaskiya bane dan haka ki daina damuwa akansa, nidai abu daya zan fada miki shine ki kara mikewa da addu'a kinji Allah ya kawo mana dauki." Ajiyar zuciya ta sauke tace 'Insha Allahu." Agogo ya kalla yace "Magariba ta gabato muje muyi sallah ko?" Suka mike masallacin mata ta nufa shima ya nufi masallacin, sai da suka idar da sallah sannan suka fita yace "Mu tafi?" Kai ta gyada sai kuma tace "Yaya!" Juyowa yayi yace "Menene?" "Yaya wannan popcorn din nake so." "To muje." Haka ya siyo mata sannan suka fita suka nufi wajen motar su, kamar ance ta dago ta ga Muhammad yana kallon su, kai ta dauke da sauri, murmushi ya dan saki ya yo wajen da suke ya karasa wajen Aliyu ya mika masa hannu, fuska ba yabo ba fallasa, ya mika masa hannu sukai musabaha yace "Ashe ka dawo." "Yes na dawo jiya." "To Allah taimaka" "Amin nagode." Ya bude mota ya shiga, Maryam ya kalla wacce kan ta ke kasa, karasowa yayi yace "My dear ya kike?" "Alhamdulillah." "Nazo amsa sako ne, bari naje sai munyi waya." Kai kawai ta gyada ya juya ta shiga motar ta rufe, jiki a sanyaye, dan bata so Muhammad ya gansu da Yaa Aliyu ba daman kullum yaba cewa son ta suke kada ya saka wani abu a ransa, wannan yasa tafiyar tasu ta zama ta kurame ba kamar dazu ba dan suke hira ba, yanzu gaba dayan su tunani suke. * Haka suka dinga rayuwa tsakanin Maryam da Aliyu Ummi ta rasa gane kansu dan duk sun sukurkurce bata gane kansu sam. A haka bikin ya karato wanda ya rage sauran wata daya a lokacin yar gidan Inna autar su Abba ta sauka a kasar da mijin ta. A bangaren Inna ta fara sauka, lokacin Maryam na dakin suka shiga ita da yaran ta da mai gidan nata wanda yake tamkar yaro a wajen Inna. Lokacin da Maryam ta ganshi sai da gaban ta ya fadi domin wani abu da ta gano wanda yake mata kama da Haidar din ta, sai dai dan Haidar fari ne sosai kuma shi yaro ne amman duk wanda ya nutsu yaga Haidar yaga Yaa Abubalar mijin Yaya Nusaiba yasan tabbas sun haka da jini. Jiki a sanyaye tai masa sannu da zuwa Yaya Nusaiba ta rumgume ta tana fadin "Amaryar December." Tai murmushi suka karasa daki, nan suka hau dawainiyya da su cikin so da kulawa, yaran na wajen Maryam suna ta wasan su, nan suka hau gaisawa da Inna tana tambayar su ya hanya. Sai da suka ci suka koshi sannan Yaa Abubakar ya bar bangaren Inna ya tafi bangaren Ummi wanda take uwa sannan marikiyar sa. A falo ya same ta ya karasa fuskar sa dauke da fara'a, Haidar dake gefen ta ya mike yana fadin "Oyoyo Uncle." Ya daga sa yana fadin "Son ya girma." Haidar yace "Ina yini Uncle ina su Sultan?" Suna wajen Inna." Da gudu ya fice Ummi ta bishi da kallo tana fadin "A daina gudu Haidar." Yaa Abubakar yabi, yaron da kallo kallon sa ya dawo dashi kan Ummi yace "Ina yini Ummi?" "Lafiya lou Sadik ya hanya kuma?" "Alhamdulilah mun same ku lafiya?" "Lafiya lou ya bayan rabuwa?" "Sai godiya shekara biyar kenan rabon mu." "Ah gaskiya ai kun jima." Yai murmushi yace "Yanayin aikin namu ne ga yara suna makaranta lokacin da zasu samu hutu kila bana nan in na samu su kuma suna tsaka da karatu." "Haka ne amman dai ko yaran ai kwana turo mana su amman ace baku basu gaba daya ai hakan bai ba ko dan bamu muka haife ka ba amman ai ita Nusaiba zata so taga magaifiyar ta ko?" Matsawa yai wajen kafar Ummi yana fadin "Dan Allah kada kice haka Ummi, ke ma uwa tace ban taba kin zuwa gareku dan cewa baku kuka haifen ba kullum ku nake dauka a nawa saboda ban san ina nawa ahalin suke ba, kune gata na kun min abin da ba zan taba mantawa daku ba kun inganta rayuwa ta kun bani mace ta gari da gata da na rasa tayaya zakice dan baku kuka haifen ba dan Allah Ummi ki daina fadar haka." "Na daina Sadik Allah ya taimaka yai muku albarka." "Amin." "To ai ka samu kaje ka watsa ruwa ko?" "Eh Ummi gida ma zan je anjima zan dawo Ina Aliyu?" "Yana asibiti." Ya mike yace "Bari na shiga wajen su Mami sai na tafi." "To sai anjima" Ya fita. * Sauran sati uku biki. Tana zaune a daki taga kiran Muhammad dauka tayi takai kunnen ta yace "Amaryar Ina waje ina jiran ki." "Gani nan." Ta kashe wayar ta mike ta saka Hijab ta shiga dakin Ummi bata nan kasa ta sauko ta same ta a kasa ta karasa tace "Ummi Muhammad ne yazo." "To kada ki dade dan nasan yanzu zakiga mai gyaran nan tazo kinji ko?" "To Ummi." Ta mike ta fita. Baya compound wannan yasa ta fita, a waje ta same shi jingine da motar sa, sanye yake da bakin wando sai t-shirt ja yai kyau sosai sai tashin kamshi yake, tinda ya daura idon sa akan ta ya kasa daukewa ta karasa kan ta a kasa tai masa sallama sannan ta gaishe shi Muhammad dake rike da waya ya mayar aljihu yana kallonta yace "Invitation na kawo Gimbiyya ta Thursday za ayi dinner...." Yana magana ya bude mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, yace "Akwai na daurin aure da na yinin ku da kika ce wenesday ko?" Kai kawai ta gyada yace "Ina son account number ki saboda ko zaku bukaci kudi." Kai ta girgiza tace "Ba abinda zanyi dasu." Dagowa yai yana kallon ta yace "Mijin ki zan zama a yanzu meyasa har yanzu kika kasa bani matsayin nan, ko matsayin Yayan ki baki bani ba bare friend din ki, ba zan matsa miki ba amman ya kamata ki sauya wannan dabi'ar taki, tinda kince haka zanje wajen Najwa duk abinda ake ciki zan sanar mata tin da naga na zama sirikin ki ace bikin mu ba zaki bude baki kiyi min bayanin abinda kike so ba komai sai kice duk yadda nace." Idon ta ne ya ciko da kwalla tabbas gaskiya ya fada to amman ita tana rasa me zatace me zatayi ita fa rayuwar take amman gaba daya hankalin ta da nutsuwar ta suna wani wajen daban, dan haka murya na rawa tace "Kayi hakuri." Matsowa yai yace "Dago kan ki." A hankali ta dago kanta yace "Kinga ko, hawaye ne fa a idon ki, nace ki fada min me yake damun ki amman kullum kice min ba komai to yanzu menene na kukan?" "Ni dai kayi hakuri." "In kina so nai hakuri ki turon." A take ta dauki wayar ta ta tura masa yana tsaye taji shigowar sakon ya dago yana murmushi yace "Ko kefa." Sannan ya danyi danne danne wayar ta taji tai kara tana dubawa taga alert ne na 1m da sauri ta dago tana fadin "Amman ai sunyi yawa." Hannu ya daura akan lips dinsa yace "Sam ko daya, ki tambayi su Ummi me suke bukata venue dukka na samar karki damu kinji amarya ta." Ta dan saki murmushi yace "To ni zan tafi." "Nagode ka gaishe dasu Ammi da Momy." "Zasuji bye." Ta juya ta fara tafya sai yace "Baby." Juyowa tai tana kallon sa yace "Ki sani ina son ki ba zan taba daina son ki ba har karshen numfashi na, in kina fargabar wani abu ne ki sani Muhammad naki ne ke kadai." Wani murnushi ne ya sauka akan fuskar ta tace "Ina godiya da soyayyar ka a gareni." Ya daga mata hannu itama ta daga masa ta juya tai cikin gidan. Akan idon Haidar duk abinda ya faru, ido ya lumshe kawai ya bar unguwar. * Ita kadai ce kwance a daki, sai kuka take sai kace wacce aka doke ta, Ummi ce ta shigo dakin tana fadin "lafiya kike kuka?" Maryam bata tanka ta ba sai hawaye da take gogewa wani na bin wani, Ummi tace "Maryam ko auren ne bakya kike ta kuka?" Jikin Ummi ta fada tana kara fashewa da wani kukan. Murmushi Ummi tayi mai ciwo ta kara rumgume Maryam tace "Haba daughter, kuka kuma haka?? Ko kina da damuwa ne?" Maryam bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, "Kiyi hakuri kar ki sake kuka kinji, it's always like this for every lady, duk a haka muka saba uhmm?" Maryam ta fara wani sabon hawayen, Ummi ta rungume ta tana lallashinta, Aunty Nusaiba ta shigo dakin ita ma ta dinga kwantar mata da hankali, sai da suka tabbatar tayi shiru gaba daya sannan suka fita dakin. Mama kuwa gaba daya hankalin ta a tashe yake akan auren da taga ana ta shirye shiryen sa dan gani take in har Maryam ta samu jin dadi Ummi ma zata nutsu taji dadi ita kuma a duniya ba wanda ta tsana taga yana cikin jin dadi kamar Ummi, dan haka ko zatai yawo tsirara tayiwa kan ta alkawari cewa sai ta sakawa Ummi kunci a ranta. Da wannan tunanin ta bar gidan cike da zulumin abinda zatai masa. Ranar litinin akaje akai kafi, wanda ba karamin kudi aka kashe ba, Aliyu ba karamin kudi ya kashe ba duk wanda ya dawo daga gidan sai sambarka, su Basma duk sunzo gidan ya cika da yan uwa. Washegari talata da safe driver ya kai su Maryam saloon, inda ake mata gyaran kai, Sai ta kara ftowa a cikakkiyar amarya ta kara yin wani haske da fresh sai glowing ko ina na jikinta yake kamar balarabiya, da yake da Jawahir aka je Yaa Khaifa yasa ta amshi account number matar ya tura mata kudin gyaran da akai musu dukkan su. Sai kusan azahar suka koma gida suna komawa gida mai lalle da aka kira ta zo gida yi mata lalle, Inna ce ta shiga dakin da Maryam take rike da flask din pepper soup din da tayi mata da kan ta, tace "Ni duk kin rame Maryam ko abinci ne bakya ci maza sha ki samu ki kwanta ki huta." Basma tace "Mai lalle fa tazo." Inna ta kalli Basma tace "Abincin ne ba zata ci ba?" "A'ah amman...." "Dan Allah rufen baki, ki barta taci tukkuna, tun safe take garari a titi wai gyaran gashi yanzu kuma daga ta fito wanka na zuba mata abinci sai kizo kice ai mata lalle." Tsoka biyu taci ta ture ta mike zata fita, Inna tace "Oh ba zaki ci ba?" "Inna na koshi baki na dukka babu teste." "To me zan miki yanzu." "Barshi kawai Inna bari naje ai min lalle." Ta fita. Aka fara lallen sai kusan Magrib aka wanke lallenta da yayi kyau ba kadan ba. *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.* *Antty*[11/30, 12:53] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 66 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Washe gari Kamu da Yini, bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta zo tayi ma Maryam very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani lace mai tsadan gaske da Abba yayi mata an mata dauri da head din kayan, ko tsinke ba a taba ba a lefenta ba, gaba daya kayan da zata yi fitan biki Abba ne yayi mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Muhammad da Step mum dinsa Momyn Jawahir duk sun zo, da friends dinsu duk sun zo suma, da Ummi da Mami da Momy lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka, Mama ma ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya basu Mami mamaki sai dai basu ce komai ba. A haka aka cigaba da shagalin biki, Ummi na lura da Maryam throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa. Bayan anyi kamu angwaye suka zo sosai Muhammad yai kyau sai sheki yake da tashin kamshi, abokan sa sosai sukai masa kara, shi kansa ya gane Maryam bata cikin haiyacin ta a haka aka tashi taron yana kara lallashin ta. * Washe gari haka akai dinner mai kyau da tsari wacce ta hada manyan mutane yan boko. 10pm har an tashi dan Ummi tace bata son ai abun dare nan, suna dawowa Ummi ta ja Maryam dakin Aliyu wanda rabon Maryam dashi wajen sati daya, wanda ko wajen shagalin bikin ta bata ganshi ba. Ummi ce ta zauna ta kamo hannun Maryam ta zaunar tace "Maryam ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have any problem da baki son fada min ne?" Maryam ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Ba komai Ummi...." Sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara taruwa idonta, Ummi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace amarya ke yi da zulumin barin gida ne ke damun yar tata, ko kuma tana tsoron rayuwar da zata shiga a cikin wadan da bata sani bane, da haka sai ta jawota kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Maryam dai sai gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ummi ta rumgumeta tace "Bana son wannan kukan Maryam, today is ur happy day, ki saki ranki please" A hankali Maryam tace "Na daina" Ummi tace "Good ki koma daki ki kwanta ki huta kinji." Kai ta gyada sai kuma Ummi tace "Zauna ina zuwa dan nasan ba kici komai ba." Shiru tayi, Ummi ta fita. Aliyu ne ya shigo dakin cike da damuwa ya fada saman kujera yana mai lumshe idon sa sheshekar kukan da ya jiyo yasa ya mike da sauri yana kallon ta. Sanye take cikin kayan dinner ta wanda yake wani dakakken army green ne an daura mata head shima army green ba karamin kyau yayi mata ba da yake fara ce sai ya kara fito mata kyan ta, ga make up din da akai mata kamar a dauke ta a gudu, ko a wajen dinner haka Muhammad ya dinga yaba yadda tai kyau, yan uwan sa ma sosai suke fadin Muhammad yayi dacen mata. Kamar tasan kallon ta yake ta dago wanda tana dagowa suka hada ido, da sauri ta mike ta karaso inda yake zaune a kasa kan carpet ta zauna tace "Yaya me yake damun ka? Kaga yadda ka koma kuwa?" Murmushin karfin hali yayi ya jinginar da kansa da kujera tare da lumshe idanun sa, tace "Yaya." Ta kasan idon sa ya kalle ta yace "Na'am." "Yaya me yake damun ka?" Kai ya hau girgizawa, cikin tausayawa hawayen dake idon ta suka zubo tace "Kagan ka kuwa Yaya ka rame sosai kalli fa." Murmushi yayi kawai tace "Please Yaya ka fada min me yake damun ka i promise to help you throughout insha Allah." Ido ya lumshe yace "It's too late" kallonsa kawai Maryan take, kafin tace komai yace "Yanzu me kike bukata wanda ba a siya miki ba?" Rufe fuskarta tayi da sauri da hannayen ta da suka sha lalle sukai kyau dasu, kamo hannun ta yai yana kallon hannun ta can ya dago yana kallon ta yace "Kin zabi aure akan karatun ki ko?" Ido ta dan zaro tace "Burin Yaya na zama cikakkiyar likita yaga na gama karatu na dogara da kaina, to ina mai son sanar maka burin ka zai cika zan kasance maka yadda kake so Yaya." Kai ya hau girgizawa kawai tare da lumshe idon sa, tace "Yaya please kai ma ka daure ka fitar da mata wacce zata kula da kai, kaga da kana da aure da yanzu matar zata kula dakai, ji yadda ka rame." Ido ya bude yace "Bani da mai so na, mai sona Maryam ce kadai, kuma yanzu bata raye, a baya na zata bayan ta ba zan sake son wata 'ya mace ba amman sai gashi kwanan nan son wata ya shiga rai na, wacce son ta daga Allah yake shi ya halicce shi a zuciya ta, ban taba son wata mace kamar ta ba, ita ce macen da nake ma son da ni kaina ban san irinsa ba" Da mamaki Maryam ke kallon sa tace "Wacece wannan Yaya ka fada mata." Yanayin sa ne ya canja launin idon sa ya canja zuwa ja, a hankali yace "Da farko ban zaci son ta nake ba dan ba irin wannan kalar son nai mata ba, tausayin ta nake da burin naga na inganta rayuwar ta ta yadda zatafi karfin komai da gori a rayuwar ta, ina tsananin tausayin ta wanda ni kaina ban taba tunanin tausayin da nake mata zai rikide ya koma so na aure ba, amma...." Maryam dake ta kallonsa ta zaro ido tace "Yaya tasan kana sonta kuwa?" Ya girgiza kai a hankali yace "Taki ganewa har yanzu" Maryam tai murmushi hade da tagumi tace "Meyasa baka fada mata ba?" "Ina tsoro kar taki amsar soyayya ta ne bansan wane hali zan shiga ba." "Akan me zata ki amsa soyayyar ka Yaya, bayan you are very handsome... After that ma, Yaya menene aibun ka na dabi'u ko wacce mace zata so ta same ka, ka bar wani tsoro ka tunkare ta kawai ni na fada maka zata amshe ka fiye da tunanin ka. Kana da kyau, and you are a gentle man so babu macen da zata iya wofantar da bukatar, you should stop being afraid zata amshe ka, kila ma tana ganin ka taji tana sonka Bai san lokacin da wani murmushi ya subce masa ba yace "Me ya saki kuka?" "Yaya bari mu gama naka mana ka fada min a ina take zan sanar mata da burin zuciyar ka." "Na fada miki it's too late domin an bada ita auren ta ma za ayi." "Ayyah Yaya to ya zamuyi Yaya nauyin bakin ka ya jayo amman kasan me i will always put you in my prayers Allah ya kawo maka mace ta gari mai son ka." Murmushi kawai yayi yace "Uhmm fada min me yasa ki kuka?" "Ban sani ba tinda aka fara bikin nan am restless and Yaya meyasa u didn't attend my wedding?" "Shagalin mata ne but tomorrow i will be there insha Allah." Ya fada yana dage mata gira murnushi tayi yace "To sai me kema kin rame amarya da rama me kika sa a ranki?" "Am thinking of leaving you all Yaya, zanje inda ban sansu ba zanyi wata rayuwa Yaya ban sani ba ko zasu amshen da so da kulawa." Tana fada hawaye ya fara zubo mata, magana ta cigaba da yi cikin kuka tana fadin "Na kasa nutsuwa akan alamarin nan ina tsoro da fargaba Yaya." Hannun ta ya kamo yana murzawa a hankali, shiru tayi ya saki hannun ya dago kanta ya fara goge mata hawayen yana fadin "Ki daina kuka i am there with u always so kar ki saka damuwa kinji?" Ido ta lumshe hawayen dake ciki ya gangaro ya saka handkerchief ya goge mata yace "Yanzu me kika ci?" Kai ta girgiza yace "Bari na kira Ummi a samar miki abinci." Ummi dake bakin kofa tana jin duk hirar Aliyu da Maryam ta bar wajen ta koma kitchen kiran Aliyu ne ya shigo ta daga tace "Son lafiya?" "Ummi kinbar 'yar ki da yunwa." "Gani nan ina kitchen ai." Ta kashe wayar ta dauki tray din ta fito ta nufi dakin Aliyu, ajiyewa tayi ta zauna tana fadin "Ana sallama ne?" "Eh gata nan sai kuka take sai kace akan ta aka fara aure." Tai murnushi ta mike tace "Bari naje Abban ku ya dawo." Ta mike ta fita, da kan sa ya zuba mata abinci ya mika mata ta dauka zata ci ta kalle sa tace "Kaima baka ci komai ba Yaya." "Ke dai kici." Fuska ta shagawabe kamar zatai kuka tace "Please come and join me." Ta saka masa spoon tare suka ci abincin a plate daya suna cikin ci Ummi ta shigo har suka gama sannan Maryam ta dauke kwanukan ta dawo tai masa sai da safe ta tafi. Aliyu kuwa wanka yayi yazo ya kwanta dan yai bacci amman sam bacci yaki yazo sai tunanin da yake wanda ya haifar masa da zazzabi da ciwon kai, duk da halin da yake ciki haka ya mike yayo alwala akan sallaya ya kwana har asuba bai bacci ba sai da ya dawo daga masallaci yasha maganin bacci da kyar bacci ya dauke shi. A bangaren Maryam ma haka bayan tai wanka ta kwana a kusa da Basma kasa baccin tai sai juyi da take wanda ganin zata bata lokaci ne a tunani ta mike ta tada sallah kwana tayi tana sallah da addu'a akan auren ta da rayuwar ta ta baya Allah ya dawo mata da komai wanda ta sha kuka kan asuba idon nan ya kumbura, fuskar ta tai jawur ga wani ciwon kai tana sallah asuba bacci ya dauke ta a wajen da tai sallah. Karfe goma ta farka da wata matsananciyar faduwar gaba, mai gyara ce tazo dan haka nan aka hau mata wanda ya dauke su awa biyu sha biyu aka gama ta shiga tai wanka da ruwan turare ta fito ta turare mata jikin ta da kamshi mai dadi da sanyi, zama tayi mai make up tazo zatai mata kememe ta hana tace bata so, wani ubansun less fari tas aka dauko mata ta saka riga da zani ne sai farin mayafi wanda duk stones din su fari tai daurin ta normal amman sai tai kyau sai kyal-kyali take da ka kalle ta zaka san bata cikin nutsuwar ta, gefen gado ta koma ta zauna Jawahir ce ta shigo tana buda hadi da fadin "Amarya ta ango." Maryam ta dago ta kalle ta cikin wani yanayi mai wuyar fasallatawa, Jawahir ta karaso cike da damuwa tace "Lafiya Sister me yake faruwa ne tin jiya naga yanayin ki ya canja dan Allah ki kwantar da hankalin ki yaya yana son ki muma muna son ki to damuwar menene su Ummi kuna tare na tabbata Yaya zai miki abinda kike so dan Allah ki saki ranki Yaya ta uwar Ya'yan Yaa Khalifa, Yayar Jawahir." Najwa da Basma ne suka shigo suna fadin "An gama shiryawa ne?" Najwa tace "Ah ya ba ai make up din ba?" Basma tace "Tace bata so." "Amman saboda me Maryam?" Kai kawai ta dauke dan ko magana ma bata so, Najwa ta mike tace "Uhmm kinci abinci to?" "Bata ci komai ba." Basma ta fada. Najwa tace "Jeki ki debo mata ni bana son amarya da rashin cin abinci dan nima lokaci na ban zauna ba cin abinci ba." Jawahir tace "Miskilancin Amarya ya tashi yau ango zai sha fama." Najwa tace "Da ta shiga hannu zata sake." Sukai dariya. Wayar Najwa ce tai kara ta kai kunnen ta tana fadin "Hello Aisha." Tai shiru tana sauraran ta can tace "To shikenan zan turo miki ai nazata yau ma ba zaki iya fitowa ba." Tai shiru sai tace "To sai kinzo." Ta kashe wayar tana kallon Maryam da take danna wayar ta wanda bata san me take dannawa ba dan bata jin dadi duk jikin ta wani iri yake mata ga damuwa da take ciki, ga faduwar gaba, Najwa tace "Ina makwabciyya ta da nake baki labarin sun dawo daga Canada last month ita ce zata zo kinsa bata samu tazo kowanne event ba saboda tsohon ciki gareta bata jin dadi amman tace yau zata zo." Wacce akewa maganar ma bata san anayi ba sai da Jawahir ta tabo ta, ta dago da sauri, Najwa tai dariya tana fadin "Wai wannan har bakin ya mutu yau za a shiga hannun mazaje ai ke ki godewa Allah ma da saurayi ne, hmmm wallahi in da mai mata ne ko,? Ko irin su Yaa Aliyu da aka jima da rasa mata sai ya kusan kashe ki." Dagowa Maryam tai idon ta cike da kwalla, Najwa tai saurin matsowa tana fadin "Me ya faru Sister dan Allah ki kwantar da hankalin ki." Ido ta lumshe kawai. Basma ce ta shigo hannun ta rike da tray ta ajiye a gaban Maryam tace "Ummi tace ki shanye peper soup din nan tas." Ture kayan tayi tana kokarin kwanciyya akan gado Najwa ta taro ta tana fadin "Kisha ko tea ne da peper soup din, wallahi zaki wahala in kika ce ba zakici komai ba." Ummi ce ta shigo tana fadin "Ina Maryam din maza kici abincin nan kinji ko?" Maryam ta kalle ta cike da damuwa Ummi tace "Dauki kisha naza ina kallon ki." Tea'n da Ummi ta hada mata mai kauri ta dauka ta sha jin dumin sa yasa ta shanye tas Ummi ta sata agaba ta sha peper soup sai da ta gama sannan ta fita, komawa tai ta kwanta, karfe daya tayo alwala ta tada sallah. * Bangaren Aliyu ma sai wajen sha biyu ya farka dan rabon sa da bacci yau kusan kwana uku in ya kwanta ko awa bayayi yana bacci sai tunani da kwana akan sallaya, jiki a mace ya mike ya shiga ya jima a bandaki ya fito ya zauna a gefen gado yana goge jikin sa mai ya shafa sannan ya mike ya taje gashin kansa. Wata sabuwar farar shadda ya saka wacce take kyalli ta warwali, yar ciki da babbar riga ce agogon azurfa ya saka ya murza bakar hula ya saka bakin takalmi hadi da feshe jikin sa da turare agogo ya kalla yaga daya saura, da sauri ya mike dan yana son ya samu hudubar juma'a, Counter ya dauka tare da wayar sa da mukullin motar sa, fita yayi a dakin yana mai dannan counter din bakin sa na motsi alamar tasbihi yake yi, a haka ya fito falo wanda yai dai dai da fitowar Ummi daga bene har ya kai kofa tace "Dr!" Tsayawa yayi ya juyo yana amsawa, ta karaso tana fadin "Na shiga yau wajen uku kana bacci kaci abinci?" Agogo ya kalla yace "Ummi in an sauko zanci bari naje kar na rasa sallah." "Wanne masallacin zaka kasan dai yau za ai daurin auren Maryam." "Ummi ai acan muke sallah." "To adawo lafiya Allah kiyaye hanya." "Amin." Ya juya ya fita. A bakin gate din masalacin suka hadu dasu Abbi bayan yai parking motar sa, ya karaso yana kallon su duk kansu basa cikin walwalar su, ya durkusa ya gaishe su, Abba yace "Allah maka albarka." Kai ya amsa yana fadin "Amin Abba." "Kayi hakuri da duk abinda yazo maka a rayuwa wani abun alheri ne a rayuwa, sai daga baya za a gani, mu iyayen ka ne duk abinda zanuyi maka rashin so ba zai saka muyi maka ba sai dai son da muke maka Allah maka albarka." Kasa gane maganganun su Abbi yayi, Abbi yace "Mu shiga daga ciki." *Allah ya jikan musulmai ya kyautata nanu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya. Allah yai mana rahma. Amin.* *Antty* [12/1, 18:00] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 67 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Suka shiga a gefen Abbi Aliyu yai sallah. Ana idar da sallah liman ya nemi shaidun madaura auren da za ayi, Abba da Abbi da Yayan su Ummi suka karasa wajen Liman, nan aka bada health status din amarya da ango Abba ne ya zaro kudi a aljihun sa ya ajiye a take aka daura aure. Aliyu dake zaune a inda yake bai taba zaton sunan da yaji an kira na angon ba ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba da Abbi ko kiftawa babu, Farouk ma cike da mamaki yake kallon su Abbi. Aliyu kuwa ko motsi ya kasa, can ya lumshe ido ya bude zuciyarsa na bugawa. Abba ne ya karaso wajen ya sakar ma Aliyu murmushi yace "Ina fatan ba zaka bani kunya ba. Allah ya taya ka riko." Kasa gane inda zancen Abba, Aliyu yayi..... * Maryam ce kwance akan gado bayan ta idar da sallah counter ce a hannun ta tana dannawa tare da motsa bakin ta, idon ta a lumshe yake, Jawahir da Najwa na falo suna zazzaune, Basma ce kadai zaune a gefen gadon, kamar ance ta bude idon ta ya sauka akan agogon dakin su wanda ya nuna biyu da yan mintuna, bugawar zuciyar ta ce ta dadu tai saurin mai da idon ta, ta rufe tabbas tasan by this time an riga da an daura auren shikenan ta zama matar Muhammad Auwal, wani yanayi ta fada wanda ta kasa gane wane iri ne, mamakin ta daya zuwa biyu, shine na rashin ganin sakon Muhammad wanda tasan a duk halin da yake yai alkawarin shi zai fara shaida mata daurin auren su, to amman meyasa bai fada mata ba ko da yake dama fada ce tasa kawai tayaya yana cikin mutane zai samu damar sanar mata. Guda taji ana yi a kasa wanda ya kara sawa faduwar gaban ta, dan har sai da ta dafe kirjin ta, ta runtsa idonta, tana karanto addu'a a ranta ko zata samu natsuwa daga bugawan da zuciyarta ke yi, Daga masallaci gaba daya gida suka yo, Aliyu kasa tukin ma yayi gaba daya, Abba da Abbi na mota daya a haka suka shigo cikin compound din wanda yake cike da yan uwan su dan yadda suka dauki Maryam tamkar yar Ummin ce dan haka tai gayya abokan ta da yan uwa haka ma Mami, ga Hajiya Inna gasu Anty Asiya da Hanna kowa da tawagarsa, Mami ce ta fara hango su Abba daga ganin yanayin su ya nuna mata basa cikin nutsuwar su ba tin yanzu ba tin kafin su fita ma, tana ganin Aliyu ya fito a mota ya nufi bangaren Ummi, Abba yace "Aliyu!" Juyowa yayi yace "Zo muje bangaren Abbin ku akwai maganar da zamuyi." Suka juya suka nufi bangaren Abbi, da sauri Mami tabi bayan sa, a falon Abba da Abbi ne da Yayan su Mami zaune akan kujera sai Aliyu da Farouk dake kasa, Mami ce ta shigo da sallama a bakin ta, suka amsa ta karaso tana fadin "Lafiya kuwa?" Kai Abbi ya girgiza ya fada mata duk abinda ya faru, Zama Mami tayi cike da damuwa tana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Aliyu ta kalla wanda yake jingine da kujera ta kasa gane a wane hali yake amman tabbas yana cike da shock din abunda yaji. Abbi ya kalli Mami yace "Kije ki kira Aisha da Maryam har da Inna da Sitti dan suji ko me yake faruwa." Mami ta mike ta fita, Mama ce ta shigo kamar an jefo ta dan hankalin ta a matukar tashe yake bata son wannan auren ya tabbata taki jinin taga Maryam cikin jin dadin rayuwa dan haka ganin shigowar su Abbi ya sa tasan lallai da akwai damuwa, magana zatai Abbi ya daga mata hannu tare da nuna mata waje yace "Zauna." Zama tayi tana kallon yan dakin, ba a dauki mintina ba Ummi ta shigo dakin tare da Anty Nusaiba autar Inna, ba a jima ba sai ga Inna da Sitti nan sun shigo, cikin kaya iri daya wanda Aliyu ya dinka musu dan yin fitar biki. Ummi ce ta kasa nutsuwa cike da damuwa dan har jikin ta wani irin tsuma yake ta kalli Abbi tace "Meya faru ne Abbi?" A hankali Abbi yace "Lafiya lau" Ba tare da ya kalle ta ba, jikin ta ya kara sanyi, dakin yai shiru Inna da Sitti kuwa sai kallon su suke, can Inna tace "Shanyar bata bushe bane Suleimanu?" Mami ce ta shigo dakin rike da hannun Maryam da ta yafa mayafin ta akan ta, tafiya take kawai amman bata san inda take saka kafar ta ba a haka suka karaso parlon Abbi, ta zaunar da ita a gefenta. Kan Maryam a kasa cike da fargaba wanda yasa gabanta sai faduwa yake, Abba ya bude wajen da addu'a sannan a hankali yace "Babu amfanin tsaya jan zance ko wani boye boye, kuma ina son kowa a nan ya dau abinda ya faru yau a matsayin kaddara wanda aka ce ta riga fata, mu ma ba haka muka so ba, kowa ma ba haka ya so ba, sai dai kawai mu kara gode ma Allah don shi ya san dai dai, kuma duk abinda ya faru ga bawa mai kyau ko akasin sa kaddara ce daga Allah wanda in ka cinye wannan jarabawar Allah zai maka sakayyah da abu mai kyau a rayuwa, duk abinda ya faru da bawa mai kyau ko akasin sa ce ne Alhamdulillah Allah zai baka lada dauke ka amshi jarabawar kada kace kai kadai Allah ya daurawa abu kaza....." Inna tace "To Shehu jan ran yai yawa dan Allah ka daure ka fito ka fara fada mana me ya faru dan bakaji yadda ciki na ya murda min ba." Abbi yace "Akan zancen auren Maryam ne wanda a takaice dai babu zancen auren Maryam da Muhammad..." A razane mutanen dakin suka dago suna kallon Abbi da yai maganar cike da razana da gigita bama Ummi da tafi kowa rudewa, Mama kuwa murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta kasa boye abinda ke ranta abinda yasa yan dakin basu gane me take ciki ba saboda damuwar da suke ciki ne. Shiru dakin yayi kamar ruwa ya cinye su, baka jin komai sai numfashi da karar fanka da AC, Sitti ce tai karfin furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Suleiman" Yaya Shuaib babban dan Sitti yaya ga su Ummi yace "To sai dai ayi hakuri, bamu taba zaton haka ba, komai ya samu bawa a duniya dama rubutattce ne, kuma babu wanda ya isa ya kauce ma kaddararsa, wannan yaro Muhammad dai Allah ya rubuta daman can ba mijin Maryam bane dan haka duk abinda ya faru sanadi ne, kullum addu'a mu Allah ya zaba mana mafi alheri to kila rashin alherin yasa haka, wanda kuma aka aura mata a yanzu muna fatan ya zama alheri a rayuwar ta." Kalaman Daddy ya sanyaya musu rai sai dai duk da haka suna cike da fargabar abinda zai faru, Abba yai gyaran murya. Yesterday @11:00pm "Jiya Muhammad yazo, wanda ina can bangare na aka zo aka fada min wai Muhammad yana nema na, gane wane Muhammad yasa nasan akwai abinda yake bukata dan haka na nufo wajen Yaya inda na same shi na sanar dashi zuwan Muhammad din, Farouk ya aika akan ya shigo dashi, inda suka shigo dakin tare, cikin nutsuwa ya karaso amman daga saman fuskar sa zaka gane yana cike da damuwa da tashin hankali, anan ya zauna yai kasa da kan sa. Gaishe mu yayi cikin ladabi da biyayya muka amsa sai yai shiru Abbi ne yai karfin halin cewa "Muhammad ina fatan lafiya?" Kasa magana yayi kuma ya kasa dagowa ya kalle mu, wanda abin ya bamu mamaki daga ni har Yaya kallon sa muke cike da mamaki, kasa magana duk mukai sai daga baya nace "Muhammad kai mana bayani." "Bansan ta ina zan fara ba amman tabbas ina cikin tashin hankali kuma tabbas ku zaku ceto ni daga halin da nake ciki tinda iyaye na sun kasa, idon su ya rufe sun ki yadda dani da abinda naje musu." Yai maganar yana sheshekar kuka, wanda ya saka mana fargaba dan bamu san akan menene ba. Nine nayi karfin halin fadin "To Muhammad yi min bayani mai ya faru?" Nan yai min bayanin komai........ Kallon mamaki ni, Yaya da Farouk muka bisa dashi, duk muka kasa magana sai can Yaya yace "Amman Muhammad meyasa tin farko da mukai maka bayani baka yiwa iyayen ka ba tin alokacin in suna da ja sai asan me ake ciki ba yanzu ba." Kansa a kasa yace "Banyi haka da wata manufa ba nayi hakan ne dan kara samar mata mutunci tinda ba wanda yasan ita din ba yar ku bace wanda in naje na fada ko a gida basu ce komai ba nasan yan uwa wasu zasu samu abin fada wanda abinda bana so kenan a saka min mata a damuwa dan nima da naso sanin ta shiga damuwa bare kuma taji a duniya duk da eh na yadda amman kasan ba kowa ne zai yadda ba, Yanzu ma ina da tabbaci wanda yasan Maryam shi yaje ya kai maganar gida dan na tabbata da ba dan haka ba su Ammi ba zasu yadda ba." Yaya ne yace "To yanzu me kake so muyi Muhammad kazo mana a kurarren lokaci kana gani gobe za a daura aure wanda bai kai nan da awa sha biyu ba." "So nake kuje wajen Dady na ku bashi hakuri tare da masa bayani." Kai na fara girgizawa ina fadin "Wannan ba mafita bace Muhammad tayaya zamuje mu bashi hakuri kenan tallan ta muke masa ko? Yadda za a kara kin ganin yar mu da daraja in har mahaifin ka na son ka da son abinda kake so ya kamata yazo ya fara jin ba'asi wanda daga nan sai ya yanke hukunci amman gaskiya abinda kake nema ba zai taba faruwa ba kayi hakuri..." Rarrafowa Muhammad yayi gabana yana mai rokata Allah da annabi akan muje wanda naki tanka masa domin ba zan iya yin wannan danyen aikin ba. Ganin yana ta wannan kukan ya bamu tausayi, Abbi ya dago Muhammad yace "Ka daina kuka Muhammad zamu duba insha Allahu duk yadda ake ciki zakaji zuwa gobe." Nan ya zube yana tai mana godiya sannan ya mike Farouk yabi bayan sa abakin kofa ya barsa ya koma daki wajen mu ya dawo shiru ya same mu ya zauna bayan mintina na sauki ajiyar zuciya ina mai furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ita ka dai na dinga furtawa domin ita ce kawai ma fita kai na ya kulle abinda ake gudun dai gashi ya faru, amman tayaya gidan mace zasuje neman bikon mijin tin ba ai aure ba sam wannan ba abun yiyuwa bane, Yaya ne yai karfin hali yace "Kaga Usman kada ka damu, haka Allah ya tsara kuma Alhamdulilalh, da abin yazo tin kan a daura aure nima ban ga dalilin da zamuje neman auren ba tinda mahaifin nasa yace a'ah zamu hada musu kayan auren su a mayar musu, Allah yasa haka ne mafi alheri." Abba yai wani murmushin karfin hali yace "Amin kuma ba zan taba basu auren Maryam ba tinda sun nuna su kananun mutane ne, suzo su fara bincika mana suji halaiyar ta, shin ko karuwanci aka kama ta tana yi ai yanzu bata yi amman bakuyi bincike ba kuzo ku yanke hukunci zasuyi danasani tabbas, ai Muhammad dan sune suje suyi masa yadda suke so nasan yana son Maryam duk halin da ya shiga na rashin ta su suka jiyo, amman tabbas ba zan basu auren 'ya ta." Abba ya mike zai bar wajen Abbi yace "Shehu." Juyowa Abba yayi Abbi yace "Kada ka fadawa kowa komai bari har zuwa gobe?" "Yaya ai ya kamata a sanar da fasa daurin auren ko?" Kai Abbi ya girgxa yace "Mu bari goben dai." Kallon sa Abba ya tsaya Abbi yace "I mean it." "Allah kaimu sai da safe." Ya juya ya fita dan lokacin wajen sha biyun dare kenan. Farouk yana wajen but he is speechless, sai da Abbi ya kalli shi yace "Farouk dare yayi jeka ka kwanta." Mikewa yayi jiki a sabule yaiwa Abbi sallama ya tafi ya kwanta, kasa bacci shima yayi a daren dan yana tunanin tayaya zai nuna yana son Maryam a gobe a aura masa ita bayan abinda Mama ta fada dole ba zai bi Mama domin uwar sa tace matsawar yace yana son Maryam bata yafe ba sai ta tsine masa dan haka ko da son Maryam zai kashe shi ba zai furta ba yau in su Abbi sun bashi zai musu biyayya tinda shima uban sa ne. Kwana yayi addu'a akan Allah kawo mafita kada iyayen sa su zama kananun mutane bayan sunyi gayya. Today @12pm Cikin shiri Abba ya fito ya nufi sashen Abbi, sanye da farar shadda sabuwa kal yar ciki da babbar riga sai zuba kamshi yake zaune ya same shi shima cikin irin shigar sa yace "Barka da asuba Yaya?" "Barka ka dai ya muka ji da wannan alamarin?" "Sai godiyar ubangiji jiya gaba daya na kasa runtsawa saboda wannan matsalar." "Nima haka amman da fatan ka samo mana mafita?" Numfashi Abba yaja yace "Babu tunani wandan da suka zo daurin aure yaya za ayi dasu ga mata nan sai cigaba da shagulgula suke." Abbi yace "Kyale su suyi ni nayi wani tunani akan lamarin ban sani ba ko zaku yadda dashi?" "Wane tunani ne?" "Allah ya bamu yara maza dole a ciki zamu dauki wani mu aurawa Maryam ko dan ceto martabar ta nasan in ba haka ba zamuji kunya itama rayuwa ta zata kara gurbacewa nasani mai son ta tsakani da Allah zai iya auren ta a haka amman matsalar shine iyayen sa da yan uwa kamar yanzu dai Muhammad yana so iyayen basa so to bana son taje inda za a tsangwame ta sam." "Haka ne amman kai Yaya yanzu a cikin Aliyu da Farouk wa kake ganin za a aurawa." "Zan so na aurawa Farouk ita." Kallon sa Abba yayi yace "Saboda me?" "Yauwah Farouk yana da saukin kai da hakuri na tabbata zai rike ta da hakuri kuma naga yana kula da ita da tausayin ta." "Haka ne saboda me ba za a bawa Aliyu ba?" "Aliyu yana cike da damuwa har yanzu, bama wannan ba kasan Aliyu da zafin rai ga miskilaci ba kowa ne zai iya rayuwa dashi ba ina son inda Maryam ba za tai kuka ba." "Amma Yaya kasan abinda muka guda shi zai faru in har Farouk ya auri Maryam kai kan ka shaida ne akan halaiyar Barira kana tunanin zata samu nutsuwar da muke so? Aliyu mun isa dashi kuma burin mu yai aure in har muka bar wannan damar ban san kuma tayaya zamuyiwa Aliyu aure ba dan kullum bai da budurwa ko bai so Maryam akwai tausayi na sanin wacece ita kuma zasu taru su rufawa kansu asiri kuma Mami ba zata tsangwame ta ba zata cigaba da rike ta tamkar yar ta me kace Yaya?" Kai Abbi ya jinjina yace "Gaskiya ne amman Barira ai bata fi karfi na ba." "Na sani amman hanyar lafiya abita da shekara Yaya muyi abinda ba zamu zo muna danasi ba ko? Ana cizon yatsa." "Shikenan!" Ya kalli agogo yace "Daya tayi har da kwata tashi muje Allah yasa haka ne mafi alheri." "Amin." Suka mike suka fita akan idon Farouk wanda shima yabi bayan su, basu jima da fita ba Aliyu shima ya mara musu baya tare da sauran hadiman gidan dan duk a masallacin zasuyi sallah juma'a. * *Cigaban labarin* 3:15pm Abba ne yace "To wannan yasa muka daura auren Maryam da Aliyu." Yana fadin haka, Abbi ya fiddo kudi a aljihunsa ya mika ma Abba. Abba ya amsa yace "Ga sadakin Maryam 200k." Gaba daya dakin kabbara aka dauka. Aliyu da tinda yaji sanarwar auren ya kasa yadda da abinda aka ce yanzu Abba na maimaitawa ya sunkuyar da kansa yana mai tsabihi ga Allah. *Am sorry for the late update, today am so busy* *Allah yai mana rahma, Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/1, 18:00] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 68 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Yesterday 10:00pm* At Auwal House. Abinda ya faru jiya bayan dawowar su daga dinner, wanda lokacin goman dare, yana shigowa gidan aka fada masa Dady na neman sa wannan yasa ya nufi bangaren mahafin nasa, zaune yaga Dad dinsa Ammin sa na safa da marwa wanda hakan ya nuna akwai wani abu da ya faru, da kallo suka bishi har ya shiga ya zauna. Kansa a 'kansa yace "Dad lafiya?" Kan Dad yai magana Ammi ta hau fada "Kana da hankali kuwa?" Dagowa yayi ta koma ta zauna tace "Ashe baka da hankali ace kana neman yarinyar da ba a sam asalin ta ba karuwa...." Har tsakar kansa yaji wannan mummunar kalmar cikin damuwa ya dago ya kalli Ammi yace "Ammi ba karuwa bace sam...." "Rufe min baki, Khalifa in har ni na haife ka to ka sani ba kai ba waccan yarinyar ace har dan shege ne da ita amman kake son ta a haka? Shin asirce ka tayi, amman ka bani kunya to wallahi kaji na rantse ba zaka auro mana karuwa a cikin zuri'ar mu ba." Rarrafawa yayi wajen Ammi yana fadin "Ammi ba haka bane ku tsaya nai muku bayani." Ido Ammi ta zaro tace "Ashe kama sani har so kake ka kare ta." Ganin Ammi ba zata saurare shi ba ya karasa wajen Dad hawaye na zubo masa yace "Dad dan Allah ka saurare ni wallahi ba haka bane, Maryam yarinya ce mai ladabi da biyayya ga hankali da nutsuwa..." Hannu Dad ya daga masa yace "Khalifa ka makaro ba zan saurare ka ba sam, meyasa tin tini baka fada mana ba, duk matan garin nan ka rasa wacce kake so sa wacce ba asan asalin ta ba, a gaskiya ba zan iya wannan abun ba kayi hakuri amman tabbas bakai ba auren wannan yarinyar." A razane Muhammad ya dago yana girgiza kai, Dad ya mike yai daki kallon Ammi yayi ya rarrafa wejen ta ta mike tana fadin "In ka sake kai min wannan magana akan wannan yarinyar tabbas ranka zai baci." Tana fada ta mike ta bar wajen, kai ya hade da gwiwa yafi minti uku sannan ya mike ya nufi dakin Dad a zaune ya same shi ya shiga yace "Dad dan Allah kayi hakuri wallahi ina son Maryam ita ce rayuwa ta in kuka hanani auren Maryam wallahi mutuwa zanyi....." "Sai dai ka mutu Khalifa ba zan taba yadda d'ana ya auri wacce bata da asali ba dan azo ana mana yarfe kasan ni dan siyasa ba abinda bakai tsamani bama zakaji dan haka ba zan yadda ba kayi hakuri kawai." "Dad amman ka duba a yanzu naje musu da zancen nan abun ba zai musu dadi ba sam..." Kallon sa Dad yayi yace "Maganin su da basu sanar mana ba." "Wallahi Dad sun fada min kuma sunce na fada muku..." "Me ya hana ka fada manan?" Shiru yayi, Dad yace "Maganin marar neman shawara da fadar gaskiya da tin can ka fada haka ba zai faru ba zamu taka maka burki wallahi Khalifa ban yadda ka auri wannan yarinyar ba dan haka tashi ba bani waje" Ya fada yana nuna masa kofa, yadda yai maganar cikin bacin rai yasa Muhammad tashi ya fita da sauri, yana fita ya shiga mota ya bar gidan, gidan su Maryam ya isa wanda ya kira Abba ya sanar masa anan akai wannan abun. * Yadda yaga rana haka yaga dare, sam ko bacci bayaji haka da safe ko yunwa bai ji ba bare yaci abinci yana dawowa daga masallaci ya nufi sashen Dad, wanda shi har ya shige anan falo ya zauna yana jiran fitowar sa, har karfe goma sannan Ammi ta shigo tana ganin sa ta dauke kai ta nufi sashen Dad da sauri ya sha gaban ta dago tana kallon sa idon sa cike da hawaye yace "Ammi ke uwa tace dan Allah kada ku hukunta ni ta wannan hanyar wallahi ina son Maryam Ammi dan Allah...." "Khalifa, ka riga ka bata mana rai wanda yasa ran Dad dinku baci dan haka ba abinda zan iya." Ta shige komawa yai ya zauna wajen karfe goma sha daya Dad ya fito ya nufi dining karyawa yayi sannan ya mike zai fita Muhammad ya karasa cike da tashin hankali yace "Dad dan Allah kayi hakuri naji ku hukuntani amman ku aura min Maryam dan Allah." "Khalifa kayi hakuri domin na yanke hukunci zan aura maka yar wajen kanwar Ammin dan na riga na gayyato mutane ba zan yadda sunana ya baci akan ka ba." Yana fadar haka ya juya ya nufi kofa har ya karasa Dad ya juyo yace "Ina jiran a masallaci." Anan ya zauna ya dinga kuka, Ammi ta fita da kyar ya mike ya nufi sahsen Momy wacce tana falo cike da yan biki taga shigowar tasa da sauri ta mike ta jasa suka nufi wani daki ta zaunar dashi tace "Lafiya Khalifa?" Ido ya runtse yace "Momy akwai matsala fa." "Wacce irin matsala karfe nawa yanzu? Kana nan baka shirya ba." "Momy bansan wanda yazo ya fadawa su Dad cewar wai Maryam bata da asali wannan yasa su Dad suka ce to ba zan aure ta ba, Momy dan Allah ki taimaken wallahi ina son Maryam in ban samu Maryam ba zan iya mutuwa." "Innalillahi wainna illahir rajiun me hakan ke nufi? Yanzu ya ake ciki? Meyasa tin jiya baka sanar min ba, tabbas in Maryam taji wannan abun zata rasa sauran lafiyar ta, Allah ka tausayawa wannan yarinyar." "Na shiga uku." Muhammad ya fada. Momy tace "Je ka shirya insha Allahu komai zai zo dai dai." Cikin sauri yaje ya shirya yana fitowa ya samu Abdul a falo, Abdul yace "Me ka tsaya yi ne har lokaci yana son kurewa." Dagowa yai ya kalli Muhammad yai kyau cikin farar shaddar sa daga kallo kasan ango ne sai dai yadda idon sa yai jajir ya nuna cewa akwai matsala. Da sauri Abdul yace "Lafiya Muhammad?" "Muje zamuyi magana a mota." Suka fita Abdul ke tuki suka nufi masallacin da za a daura auren, Muhammad ya fada masa komai, Abdul cike da mamaki yace "Bansan da haka ba a tunani na Maryam yar uwar su Najwa ce." Dai dai lokacin da suka karasa masallacin wanda har an tada sallah, jam'i suka hau wanda aka tayar da sallah, bayan an idar yaji an kira waliyan amarya da ango yana zaune inda yake banda bugawa babu abinda zuciyar sa take, lokacin da yaji ana fadin an daura auren Maryam da Aliyu, yai dai dai da tsayawar numfashin sa wanda ya fadi anan da sauri Abdul da wasu abokan sa suka dauke shi suka fita dashi ruwa suka shafa masa amman sam bai farka wannan yasa suka tafi asibiti dashi. * Duk abinda ake Maryam bata fahimta sai da taji abinda Abba ya fada a karshe wato an daura auren ta da Aliyu, sai a sannan ta gama fahimtar abinda Abba ya fada few seconds ago, don tun bayan maganarsa taji komai na kanta ya kwance ta kasa apprehending, da kyar ta gano me yake nufi, ji tayi kirjin ta yai nauyi, kan ta kamar an daura dutse a hankali ta dago kai tana kallon mutanen dakin kowa fuskar sa babu wani tashin hankali, Aliyu ta kalla wanda kansa ke a kasa, ba zata gane a wane hali yake ba sai Farouk da ke gefen sa cikin sarewa yake kallon yan dakin, kan ta ta mayar saman cinyar ta bata kara magana ba a haka su Inna da Sitti suka gama tattaunawa wanda bata san me suke fada ba dan tayi nisa a tunani abinda Aliyu ya gudar mata kenan gashi nan yau ya faru, lallai wadan nan mutanen masu son ta ne ji yadda suka rike ta ba kyama duk da basu san asalin ta ba har yau suka bawa dansu auren ta wannan wane iin mutanen masu tausayi tabbas ko bata son Aliyu zata zauna dashi tai masa biyayya ko dan ta saka masu da hallicin da sukai mata. To amman ta ina Aliyu zai so ta bayan yana rike da soyayyar marigayiyar matar sa ita kuma haka Allah ya kaddarar ta mata rayuwa daga wannan sai wannan amman ba abinda zata ce sai alhamdulillah. Kuka take wanda bata san tanayi ba dan a yau take kukan rashin sanin wacece ita so take ta tuno wacece ita amman ta kasa sam. Anty Nusy ce ta kamata suka fita a dakin suka koma bangaren Ummi inda su Jawahir, Najwa, Basma da Aisha kawar Najwa da take cewa zata dawo, sai Hauwa'u wacce take kawa ga Najwa tace in bikin yazo a fada mata kuma ta gayyato tan. Bedroom Anty Nusaiba ta shiga da itace "Kinga dai muna da baki dan Allah kada ki tada hankalin ki kinji?" Kai ta gyada, kawai Anty ta juya ta fita. Najwa da Basma ne suka shigo dakin, suka samu Maryam na ta kuka wanda ya daga musu hankali suka rasa kukan me take? Duk yanda Najwa tayi da Maryam ta gaya mata abinda ya faru ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita amman taki ta ce mata komai. Basma da Najwa hankalin su ya tashi ba kadan, Anty Asiya da Hanna ne suka shigo. Anty Asiya tace "Wai meye haka Maryam? what's happening, talk to us plsss" Fadawa jikin Najwa tayi ta kara rushewa da wani kukan tana shessheka, Anty Hanna ta dinga kallonta tana fatan Allah yasa ba tunanin da take bane ya tabbata da sukaji ana cewa ba aure tsakanin Maryam da Muhammad. Anty Hanna jikinta yayi sanyi ta zauna gefen gadon ta ma rasa abinda zata ce tayi tagumi tausayin Maryam ya cikata, Hawaye Basma tafara yi tana dago Maryam tace "Don Allah me ya faru Maryam ki gaya mana, wani abu ya sami Muhammad din ne? Ki mana magana don Allah" Mikewa Basma tayi ta fita dakin a sanyaye hawaye na sakko mata. Mami, Anty Nusaiba da Ummi ne zaune a falon Mami. Mami tace "Wallahi ni yanzu nafi samun kwanciyyar hankali." Anty Nusaiba tace "Nima haka amman halin da yaran zasu shiga shine damuwar mu, kina ganin Maryam ba cikakkiyar lafiya ba ga Aliyu yadda yake." "Haka ne komai mai sauki ne nasan Maryam zata amshi Aliyu ko da baya son ta, shi kuwa wannan nasan ko tausayin da yake mata ba zai sa ya kuntata mata ba zai amshe ta a sannu su dai daita. Fatana dai Allah yasa alheri." "Haka ne yanzu ya Maryam din take?" "Na tura mata su Asiya nasan zasu lallashe ta." "Amman iyayen Muhammad basu kyauta ba." * "Fada min me ya faru Maryam" Dafata Anty Asiya tai ta dago murya na rawa tace "Anty wai.. Ba da Muhammad aka daura auren ba da Yaa Al.. Ali..yu aka daura." Maryam ta karasa fada tana fashewa da kuka, ido Anty Hanna da Asiya suka zaro cike da mamaki, Anty Asiya yace "To menene na kukan? Kiyi hakuri haka Allah ya kaddara cewa Muhammad ba mijin ki bane, kuma ya baki Yaya shin menene aibun Yaya, namiji ne na nunawa sa'a mai hankali nutsuwa ilimi ga kyau to me zaki nema wallahi na tabbata Yaa Aliyu yafi Muhammad so dubu dan haka kiyi hakuri kinji." "In yafi Muhammad amman Muhammad yafi shi so na." "Wannan ba matsala bace Maryam kema zaki saka Aliyu ya soki, amman dole kiyi hakuri dan rayuwa da miskili akwai wahala amman daga baya zakiji dadi." Haka suka dinga lalallashin Maryam har ta daina kuka sai dai yadda kanta da kirjin ta ke ciwo kamar zai fashe yasa ta kwanta kawai. Ganin tana bukatar hutu suka mike suka fita. A falo suka samu su Najwa suna hira da kawayen su, Najwa na ganin sun fito ta mike ta karaso tana fadin "What happened Aunty?" "Hmmm auren ne fa aka daura da Yaya ba da Muhammad ba." Ido ta zaro tace "Are sure?" Kai ta gyada tace "Sure." "To meya faru?" "Nima ban sani ba bari muje ta kwanta ne shiyasa." Komawa ciki tayi ta zauna wanda a lokacin taga Jawahir ta mike rike da waya ta nufi stair, Basma tace "Lafiya kuwa Najwa?" "Hmmm auren ne fa aka daura da Aliyu ba da Muhammad ba." Hauwa tace "Ke kice Allah." "Wallahi." Buda Hauwa tayi tace "Kai ba shi kuke fada yana son ta ba." "Uhmm Yaya ba'a iya masa fa, shine amman." "Ke zasu dai daita, bama da take ita macece tinda shi da alamun ehhh...." Aisha dai batai magana ba sai cewa tai "Allah sanya alheri." Suka amsa da amin. Daki Najwa ta shiga ta samu Maryam a kwance ta zauna tace "Antyn mu." Wani kallo ta aika mata, sannan ta juya mata baya, Najwa tace "Please dear ki daina wannan damuwar ni naji dadi banji dadi ba rashin jin dadi saboda..." "Dan Allah Najwa ki kyale ni bana so wannan maganar." Ta fada tana kifa kanta akan filo tana mai fashewa da wani kukan, lallashin ta Najwa tayi ta mike ta fita. A haka aka cigaba da yini wanda amarya tana daki, taki ta canja shiga bare ta fito da Ummi ma tazo dan tasa ta shirya ta same ta kwance zazzabi ya rufe ta dole yasa ta hakura ta bar ta a daki, amman Mami tace ta daure ko dan jama'ar da aka tara, mai make up Mami ta shigo da ita ta saka tai mata light make up ta shirya cikin wani coffee less wanda akaiwa ado da brown tai kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu duk da tana jin zazzabi haka ta fito ta saka flat brown half cover mayafin aka ta daura wanda ya dan rufe fuskar ta. Najwa da Basma suka kamata suka fito har harabar gidan dake cike da mutane inda aka tanada dan zaman amarya aka kai ta, suka zauna aka fara shagali amarya na zaune half face nata rufe da mayafi aka dinga shagalin bikin, wanda ko liki za ai mata har inda take ake mata liki. Har doshin magariba sannan aka bar kidan, Najwa ta kama Maryam da har jikin ta rawa yake saboda zazzabi da faduwar gaban da take, sama suka nufa wanda ta shiga daki ta hada mata ruwan dumi dan tayo alwala ta fito. Falo ta karaso inda Aisha ke zaune tace "Maman biyu sannu." Aisha tai murmushi tace "Kema kin kusa zuwa hakan." Tai dariya tace "Uhmm taso kiyi alwala ko?" Da kyar ta dafa kujera ta mike suka shigo dakin wanda yai dai dai da fitowar Maryam, Najwa tace "Yauwah Aisha ga Amarya dai ranar da suka zo kawo kati bakya nan yau ma baku hadu ba." Dagowa Aisha tayi tana kallon Maryam da kanta ke kasa, wata uwar bugawa zuciyar ta tayi ta kurawa Maryam da ta dago tana daura dan kwalli ido "Mar....yam....." Aisha ta fada tana nuna ta, Maryam ta dago a razane tana kallon wacce ta kira ta, kallon ta take ba ko kiftawa na seconni, wanda a hankali Maryam ta sulale ta fadi kasa sumammiyya. Da sauri Aisha da Najwa suka karasa wajen ta suna kwada mata kira, Najwa fadi take "Maryam Maryam dan Allah tashi." Aisha kuwa rumgume Maryam tayi tana fadin "Alhamdulillah, Masha Allah yau Allah ya nuna min ke Maryam bayan shekaru masu yawa da rabuwar mu Maryam dan Allah ki tashi kizo muje su Ammi su ganki ko sa samu nutsuwa, Maryam Maryam." Ta fada tana girgiza ta, Basma ce ta shigo taga halin da suke cike wannan yasa ta nufi firij ta dauko ruwa mai sanyi shafa mata tai amman ko gezau wannan yasa ta tuttule mata shi amma sam bata farfado ba. Fita tai a guje dan Najwa da Maryam sun rasa hankalin su a kasa ta hadu da Ummi ta nuno mata sama tana fadin "Ummi Mar..ryya...am" "Me ya faru da Maryam din?" Ummi ta fada tana yin sama a guje, itama ruwan ta shafa mata amman bata farfado ba wannan yasa ita da Najwa suka kamo ta dan tafiya asibiti suna matatakala Aliyu ya shigo dakin dawowar sa daga masallaci kenan, da sauri ya karasa yana fadin "Meya faru da ita?" *Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe amin.* *Antty* [12/2, 11:07] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 69 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ya amshe ta yai dakin sa da ita akan gado ya kwantar da ita yana fadin "Meya faru?" Kuka kawai Najwa da Aisha suke sun kasai masa bayani, duk kokarin sa na ya samu nunfashin ta ya dawo ya kasa wannan yasa ya kira Farouk ya fito da mota, shi kuma ya fita da ita a hannun sa, asibiti suka nufa Ummi da su Najwa uka mara musu baya, office din sa ya shiga da ita ya kwantar akan gadon marar lafiya, tin kan ya karaso yaga kira likita da nurses dan haka a bakin office din ya same su, yana ajiye ta suka rufa akan ta suna kokarin taimaka mata sai da numfashin ta ya dawo sannan sukai mata allurai, take ta fara bacci. Aliyu dake tsaye a gefe yana kallon yadda suka taimaka mata take numfashi har tai bacci tana maganganu kasa kasa wanda ba ajin me take fada ya kalli Dr Yasmeen yace "Me kika gano matsalar ta?" "BP ta ya hau Dr and zuciyar ta tana kara rauni in tana cigaba da saka damuwa zata iya rasa rayuwar ta dan jijiyoyin sunyi rauni sosai kuma saka damuwar ya haifar mata, bama wannan ba a gaskiya yarinyar nan tai kankanta da wadan nan matsalolin ga hawan jini, ga ciwon zuciya, Dr tana bukatar kulawa da lallashi please a bata kulawar da ta dace." Yana jingine da bango hannun sa harde a kirjin sa yake sauraron ta, har ta gama yai mata godiya ta juya ta fita ido ya lumshe a hankali ya sauke akan Maryam dake bacci, abinda ya fara guje mata kenan heart broke domin yasan ba ko wanne ahali ne zasu amshe ta ba yasan da haka amman a time din ta kasa fahimta su Ummi ma haka, in ta shine Maryam ba zata taba soyayya da wani a waje da zai cutar da ita ba su suka fi sanin matsalar ta dan haka su zasu iya zama da ita da kula da ita. Gashi nan yanzu tana neman halaka kan ta kenan tana son Muhammad har haka ta kasa hakura dashi yau in ya mutu wa gari ya waya, su dan shi gashi can an daura masa aure nan da wani lokaci zai manta da ita su kuwa da Haidar har abada ba zasu manta da ita ba. Ido ya kara lumshewa yana mai fadin "In har aure nane bakya so Maryam zan sauwake miki ba zan taba takura miki zama da wanda bakya so ba har hakan ya kara jefa rayuwar ki cikin hatsari." Fita yai dakin Ummi ta karaso tana fadin "Ya dai Aliyu?" Dakin ya nuna musu yace "Bacci take me ta gani yasata a wannan halin?" Najwa ta saki kuka tace "Ni na rasa menene dan mune dai a dakin daga Aisha ta kira sunan ta ta dago shikenan ta kura mata ido ta zube a wajen." "Ina Aishan?" Aliyu ya fada yana kallon ta waige waige ta fara sai ga Aisha nan ta taho daga wata hanya bayan ta wani namiji na biye da ita da kallo suka bisu har suka karaso, namijin shi yai karfin halin mikawa Aliyu hannu suka gaisa, Aisha tace "Nan aka shiga da ita." Da mamaki Ummi da Aliyu ke kallon ta dan so suke suji wa aka shiga da ita. Alkasim ya dago ya kalli Aliyu a karo na biyu yace "Sunana Alkasim Jabeer ni dan garin kano ne aiki ya kawo ni garin Abuja ga mai daki na sunan ta Aisha, mu makwabtan Najwa ne wanda bamu jima da dawowa daga Canada ba muka tadda anyi auren ta, matata tazo bikin yar uwar Najwa inda yanzu ta kirani take shaidamin taga Maryam dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan dan ina mamakin ta ina ta ganta ban sani ba ko gezo ta farai mata dan kwanaki tazo tana fada min tana mafarkin Maryam tana fada mata tana kusa da ita dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan?" Ummi da Haidar kallon sa suka tsaya sama da shekara biyar basu taba ganin wanda yace yasan Maryam ba sai a yau kenan da gaske wadan nan sun san ta ko kuwa? Aliyu ne yai karfin halin fadin "Tabbas sunan ta Maryam amman bamu sani ba ko wacce kuke nema ce, amman kafin nan a ina kuka san ta ko ince menene alakar ku?" Ajiyar zuciya Alkasim ya sauke yace "Kanwata ce uwa daya uba daya." Kallon sa Aliyu da Ummi sukai sosai, sai kuwa suga kamar da suke da Maryam, dan haka Aliyu yace "Muje ka ganta dan bata cikin hankalin ta an mara allurar bacci zata iya daukar awa goma ko sama da haka tana bacci dan ana son ta samu nustuwa." Suka shiga dakin har da Ummi, yana shiga dakin ya karasa wajen gadon da sauri yana ganin Maryam da gaske ya kalli alkibla ya tada sallar yayi godiya ga Allah sannan ya dago ya rasa me zai yi sai ya kama Aliyu ya rumgume tsam a jikin sa yana fadin "Alhamdulillah!" Ummi da Aliyu dai kallon sa kawai suke, Alkasim da ya kasa daina murna yace "Me yake damun ta? For how long take tare da ku?" "Likita yace taga wani abu da ya sa ta shiga shock ta zurfafa a tunani wanda ake tunanin ko ita matar taka ta gani take son ta tuna a ina ta san ta." "Alhandulillah Allah ya bata lafiya." "Amin." Ummi ta fada yace "But please for how long is she with you?" "Ummi tace "Six years." Kai ya jinjina yace "Tin batanta kenan da karamin ciki?" Kai Ummi ta gyada tace "Haka ne." "I am sorry for the questioning but please ina babyn?" Ummi ta girgiza kai tace "Ba komai, Haidar yana gida he is fine ya kusa six years dan he is five and half." Kai ya jinjina yace "Bari na waya da gida na sanar musu anga Maryam." Ya fita a dakin ya fara kiran layin Abbi, yana zaune a falo suna magana da Ammi wanda akan Maryam ne dan ba a kwana biyu a gidan ba ai maganar Maryam ba batan Maryam sam bai sa sun manta ta ba kullum basu sare ba kullum cigiya suke da addu'a. Wayar ya dauka yace "Assalamu Alaikum Alkasim." "Abbi Albishirin ku. Ina Ammi sa a speaker." Abbi yasa a speaker yace "Ina jin ka Alkasim Aisha ta sauka ne?" "A'ah Abbi yau dai Allah ya amsa addu'ar mu munga Maryam." Dif kake jin su Abbi, dan sun shiga mamaki da gaske anga Maryam. Ammi ce ta amshi wayar tana fadin "Hello Alkasim me kace?" Cikin murna da farin ciki yace "Tabbas Ammi yau naga Maryam" "Alhamdulillah Alla kulli halin, Akasim tana ina? Ya take? Ina cikin? Bani ita." "Ammi ki kwantar da hankalin ki yanzu muka rabu amman zuwa da safe zan kai mata sai kuyi magana" "Ba zan iyaba Alkasim hadani da 'ya dan Allah." Abbi ne ya amshi wayar ya fita ya maida ta normal yace "Alkasim fada min me yake faruwa?" "Abbi, Maryam tana asibiti bata cikin hankalin ta saboda ganin Aisha da tai ta suma to bata farka ba amman tabbas naga Maryam yanzu ma muna asibitin." "To shikenan zan sa ai mana booking flight insha Allahu gobe da safe zamu iso ka kula da yar uwar ka." "Insha Allahu." Ya kashe wayar ya koma wajen dakin Maryam inda ya samu su Abba da Abbi sun zo suka gaisa Ummi tai musu bayani, suka kalle shi sukaga tabbas suna kama da Maryam. Karfe goma Abba yace kowa yazo a tafi gida a bar Maryam, Aliyu yaso ya zauna amman Ummi ta kada shi, haka Aisha ma dan haka duk suka tafi cike da fargaba. * Washe gari kan goma asibiti ya cika da yan uwa dan su Anty Asiya, Hanna, Bilkisu, Aunty Nusaiba, Najwa da Basma ga Farouk duk sun zo, duk sammakon su Yaa Alkasim da Aisha sai suka tadda su sunyi mamakin wannan alamarin da karamcin wadan an mutanen sosai. Amman har lokacin bata tashi ba Aliyu hankalin sa ya tashi ya kira likitoci suka kara dubata da kansa ma ya duba komai lafiya dan baccin ma lafiya zai kara mata dan in ta samu wadatacan bacci zai sa damuwar ta ta ragu sosai da sosai. Karfe sha biyu jirgin su Ammi ya sauka da tawagar Yayen Maryam su Yaa Muhammad, Yaa Abdullah, Yaya Fadima Har da Mami mahaifiyar Haidar. Wanda daga nan asibiti suka taho kai tsaye, wanda wajen da suke ya cika ba masaka tsinke dan har daki guda aka basu dan sun cika kofar dakin da Maryam take. Bayan sun shiga sun zauna Ummi tace "Sannun ku da zuwa." Suka gaisa cikin mutunta juna. Ummi ta nuna Ammi tace "Kece mahaifiyar Maryam ko?" Kai ta gyada, Ummi tai murmushi tace "Ga kama nan." Ta nuna Fadima tace "Wannan yayar ta ce kenan?" Kai ta gyada. Ummi tace "Yanzu Aliyun zai zo sun shiga dakin da su Abba ne shiyasa..." Bata rufe baki ba Abba da Abbi suka shigo dakin bayan su Yaa Aliyu sai Yaa Abubajar dake biye dasu a baya, wanda yana shigowa Mami ta mike tana kallon Abubakar shima kallon ta yake cike da kaduwa tace "Sadik...." Ya matso yana nunata bakin sa yai nauyin furta komai, sai kuma a hankali ya sulale ya fadi kasa a sume ruwa aka yayyafa masa ya farfado yana waige waige tare fadin "Ina Mami na dan Allah ku kira min ita." Nami ta dafa sa tace "Sadik gani nan nice." Da sauri ya shige jikin ta ya rumgume ta tsam, Ummi, Mami da Abba da Abbi mamaki suke to wacece wannan kenan Maryam tana da alaka da Abubakar tinda ga gashi a yan uwan Maryam ne Abubakar yaga wannan matar yake kiran ta Mami wanda basa dai kama amman ta jini zaka gano akwai alaka. Abbin Aliyu ne yace "To Alhamdulillah, wadan nan ne iyayen Maryam din?" Suka gaisa sosai sannan Abba da Abbi da Abbin Yaa Aliyu suka mike suka nufi dakin da Maryam take aka bar matan suna dan tattaunawa amman gaba daya hankalin Ammi naga taje ta ga yar ta. Dasu Abbi suka shiga sukaga Maryam ba karamin samun nutsuwa yayi ba ya sauke wata ajiyar zuciya wacce bai taba sauke mai dadin ta ba iri ta yau dan sai da ta bayyana yace "Alhamdulillah." Ya karasa yai mata tofi suka fito, sannan su Ammi da Ummi duk suka shiga Ammi da taga Maryam kuka ta saka ta rumgume ta tana taba ta sai ta kara rumgume ta tana ganin tamkar mafarki ne Yaa Fadima ma sai kuka, Mami kuwa mutuwar Haidar ce ta dawo mata sabuwa dan ganin Maryam sai ya tuno mata da abubuwa masu yawan gaske. A haka suka bar dakin dan ba a son hayaniya haka su Ammi dasu Ummi suka zauna a daki suna tattauana batu akan batan Maryam da Abubakar. Wanda Mami mahaifiyar Haidar ita ce mahaifiyar Abubakar, a take aka kira Dadyn sa aka fada masa nan shima ya kamo hanya. Da yamma dasu Inna suka zo ganin jikin Maryam suka taho da Haidar, wanda su Ammi na ganin Haidar sukaga tsasan kamar sa da Aliyu. Rumgume shi sukai suna kuka yaron kuwa sai share musu hawaye yake yana cewa "Ummi me akai musu suke kuka?" Sai kuma yace "Ummi ina Adda ta banganta ba jiya Ummi ki kaini wajen Adda ta." Aliyu ya gani ya tafi wajen sa a guje yace "Abbi ina Adda ta." Daukar sa yayi yace "Addan ka bata da lafiya Haidar muje kai mata addu'a kada kai kuka nasan Haidar dina jarumi ne ko?" Kai ya gyada suka shiga, Haidar har da tofa mata ayyatul kursiyyu falaki da nas da amannarasulu ya tofa mata yace "Allah ka bawa Adda ta lafiya." Haidar ya rumgume Haidar a jikin sa yace "Almin my son." Haka asibiti ya zama kamar gidan biki dan safiyya nayi yake cika wanda har dare sai wajen goma zuwa sha daya kowa yake tafiya Ummi ita ke kula da Maryam, su Ammi an basu boys quarter acan suke zaune duk da su Abbi sun so su kama hotel ko gidan Alkasim, Fadima ce ta tafi can gidan Yaa Alkasim da safe kuma su dawo asibiti. Kwana ta uku a wannan halin a na hudun ta farka wanda kan kace me likutoci sun hau kanta, suna gwaje cikin hukuncin Allah ta samu nutsuwa domin kuwa jinin ta ya sauka, sai da tai wanka Ummi ta bata abu mai ruwa ruwa ta sha sannan yan uwa suka fara shigowa suna mata sannu, su Yaya Asiya, Yaya Hanna, Yaya Bilkisu, Najwa, Basma, da Yaa Farouk duk suka duba ta bayan su sai Mami da Yaya Nusaiba da Inna da Sitti bayan sun fita ne Ammi da Abbi da Alkasim da Yaa Muhammad da Yaa Abdullah, da Yaya Fadima suka shigo da sallama dagowa Maryam tayi da sauri tana ganin Ammin ta, ta dire kafar ta daga kan gadon da take ta sauko ta karasa a guje ta fada jikin ta tana sakin wani kuka mai taba zuciya. Ammi ta rumgume ta tana mai kukan itama Abbi ne ya lallashe su suka zauna ta kwanta a jikin Ammi tana mai jin tamkar a mafarki take ganin Ammi gata ga Ammi ga Abbi ga yan uwan ta. Sallama ta juyo wanda tana dagowa taga Mami ce da Dady da Yaa Abubakar wanda yake dauke da Haidar sai a yanzu ta kara ganin kamar da suke sosai, take mutuwar Haidar ta dawo mata ta mike a jikin Mami tana kokarin sauka a gadon Mami ta karaso tace "Yi zaman ki Maryam yi zaman ki." Sai ta rumgume ta suka hau kuka kamar ransu zai fita duk dakin kuma sai kuka banda mazan amman idon Alkasim har ya kada dan sosai ya ke jin kewar Haidar da jin mutuwar sa. Dagowa tai ta nuna Yaa Abubakar tace "Mami waye wannan? Tin gani na dashi a shiga shakku akan sa duk da ba sanin sa nayi ba." "Shine yayan Aliyu." Kallon sa take tana kara ganin kamar sa da Aliyu da kuma Haidar. Dan Haidar ba abinda ya baro Baban sa. Hawaye kasa tsayawa yai a idon Maryam Haidar ya sauko yazo yana goge mata har da rumgume ta kamar yadda take lallashin sa yana fadin "Adda Ammi ki daina kuka nima kina so nayi, in bakya so nayi ki daina inji Adda ina sonki Adda." Ba wanda Haidar da Maryam basu bawa tausayi ba. Haka dai rayuwar asibitin ta ranar ta zama ta farin ciki sai da idon Maryam yai ta zubar da hawaye da ta daga kai taga yan uwan ta sai hawaye anyi lallashin anyi amman taki ta daina. A jikin Ammi take tin zuwan su, har yanzu da yake yamma likis, kofar dakin aka turo aka shigo da sallama. Ammi ta amsa Maryam ta dan kalle shi ta kasan idon ta da yai jajir dan a hakan ma hawaye take. Har kasa ya durkusa ya gaishe da Ammi, Ummi dake bandaki ta fito tana fadin "Yau ina ka shiga ne Dr?" "Ummi munyiwa wasu aiki ne, ban samu kaina ba sai yanzu ya jikin nata?" Ya tambaya yana karasawa wajen gadon, a hankali Maryam ta dago suka hada ido, ya kali Ummi yace "Ummi me kuma akai mata take kuka?" "To Haidar ai gaka nan gata sai ka tambaye ta ko?" Ta juya ta fita, Ammi ma mikewa tai ta fita ya karasa wajen ta ya zauna a gefen gadon ya kamo hannun ta, wanda sukaji wani irin abu da ba zasu taba jin irin s ba, dan murza hannun yayi yace "Me yake damun ki yanzu?" Kai ta girgiza hawaye na taruwa a idon ta, yace "Kin tabbata?" Kai ta gyada yace "Kinga yadda abu ya koma ko?" Shiru tayi ya dago kanta suna kallon junan su yace "Kiyi hakuri ki daina tada hankalin ki, a yanzu kin fi kowa gata, ke da aka guda saboda rashin asali yau ga asalin ki, yau ga zuri'ar mu, mu daku duk mun zama daya kin samu dadin zuri'a dan har abada kin zama zuri'ar mu, dan haka ki bar damuwa ga su Ammi, da Ummi nan gasu Asiya da Fadima nan gasu Haidar so me zai saki kuka uhmmm?" Hawayen da ya gangaro kan fuskar ta yasa yatsan sa yana goge mata yace "Ki bar kukan nan, bana son naga hawayen ki na zuba sam, in har aure dani ne bakya so ba zan miki dole ba, nai miki alkawarin zan sauwake miki sai ki auri Muhammad tinda ga asalin hakan yayi miki?" *Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karahe. Amin.* *Antty* [12/2, 11:07] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 70 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Kuka ta fashe dashi ta fada jikin sa wanda suka kara jin wannan abun da ya tsarga musu har tafin kafar su, kuka take sosai wanda yake jin sa har cikin kasan zuciyar sa, hannun sa ya daura a bayan ta yana lallashin ta tare da fadin "To ya isa kinga bakya jin dadi kuma ba ason damuwa a tare dake ko akan wani can zaki mana asarar kanki, kin fi son sa akan ahalin ki?" Kai ta hau girgizawa yace "To ki daina kukan kinji." Kai ta gyada ya hau lallashin ta har ta daina ya dago ta yana taba jikin ta da ya dau zafi yace "Me yake miki ciwo yanzu?" Kanta ta nuna masa ya daura hannu akan zuwa wuyanta wanda tsigar jikin ta ta wani irin mike yace "Zazzabi ma nake ji a jikin? Kin sha maganin ko allura zan miki?" Fuska ta shagwabe ta koma ta kwanta ya rakwafa yace "Oh allurar kike son kenan ko?" Da sauri ta dago wanda hakan yasa fuskar su ta hadu da juna hannayen sa yasa ya tallafonta yana dage mata gira a hankali yace "Ayi allurar?" Kafada ta make sai kuma ta fashe da kuka yace "A'ah da wasa nake ba za ai miki allura shikenan." Kai ta gyada dai dai jin an kwankwaso, suka bada izinin shigowa Aisha ta shigo hannun ta rike da basket tace "Sannu Patient." Ta kalli Aliyu tace "Sannu Dr ya me jikin?" "Da sauki." Basket ta ajiye tana ganin Maryam na matsawa daga kusa da Aliyu, kai ta dauke tace "Abinci na kawo mata Dr gashi nan ka bata taci." Wani kallo Maryam ta zabga mata tace "Ni na koshi." "Kasan Allah tin tea bata kara shan komai ba, yanzu naje nai mata pepper soup din ko zataji dan dadin bakin ta." "To sannu mungode." Ta juya tana wa Maryam gwalo ya dauki bowl ya zuba mata ya dauki spoon ya ajiye akan stool ya karasa ya daga ta ya jingina ta da filo ya fara bata da kansa sosai taci sannan ya barta da dabara ya bata magani ta sha lokacin likita yazo ya kara dubata, bayan ya gama Aliyu yace "Ya jikin nata?" "Da sauki sosai sai dai naji zazzabi yanzu." "Abinda na gani kenan." "Zan bata maganin insha Allahu zai sauka." "Please in ba damuwa a bamu sallama mu karasa a gida kaga yadda muke cika asibitin nan." "Eh ba wata matsala sai ka cigaba da duba ta a gida din amman dan Allah a kula da bata mata rai, sannan ki rage tunani kinji?" Ya fada yana kallon Maryam. Kai ta gyada yace "Allah kara sauki." Ta amsa da amin ya juya ya fita. Daga nan suka hada kayan su suka tafi gida. * Washe gari gaba dayan su ne zaune a falon Abbi, banda Mama da ko asibiti bataje duba Maryam ba da taji anga ahalin sai ma karyawata tayi dan bata so ba, ta so rayuwar ta ta lalace gaba daya. Abbin Maryam ne yace "Ba abinda zamu ce muku sai godiya da yadda kuke rike mana Maryam da Abubakar Allah ya biya ku da gidan aljanna hakika ku mutanen kirki ne samun irin ku sai an tona ba abinda zamuyi muku sai addu'a Allah ya saka muku da mafificin alheri ya biya ku da gidan Aljanna." "Ah haba ai yiwa kai ne, dan yanzu daga Maryam har Abubakar ai duk namu ne duk mun zama zuri'a daya." Abbin Haidar ne yai wannan maganar. Mami dake zaune jikokin ta a jikin ta ta rasa ina zata sa kan ta dan murna yau ita da ake cewa ba zata taba ganin jinin ta ba sai gata ga danta ga jikoki har guda shida na Abubakar biyar na Haidar d'aya, kai alhamdulillah, hakika a baya Allah ya jarabce ta amman amsa kaddarar ta yau Allah ya bata wannan tukwincin ba abinda zata ce sai Alhamdulillah, Haidar kuma Allah masa rahma. Dady ne yace "To yau zamu juya kamar yadda muka sanar muku, sai dai muna neman alfarmar a ara mana Maryam da Abubakar da mai dakin da jikokin dan mu kai su gida, yan uwa su gansu in yaso sai su dawo gaba daya, kuma muna fatan zaku zo inda muke dan zumunci yanzu muka fara dan hakika kun mana abinda ba zamu taba mantawa ba." Abba ya saki murmushin farin ciki yace "Ah haba ba komai Allah ya kiyaye gaba ya tsare na baya ba komai kuje dasu Insha Allahu zamu muma mu zo muga gidan gaba daya." Haka aka cigaba da hira, da muyasar number waya da address, Maryam na daki a kwance idon ta lumshe amman ba bacci take ba, kan ta ke mata wani irin ciwo, Yaya Fafima da Aunty Asiya da Najwa da Hannah da Aisha sai hira suke, Aisha ce ta kalli Maryam ta mike ta karasa tace "Besty wai jikin ne?" Mikewa tayi ta jingina tare da sakin murmushin karfin hali kawai. Ummi ce ta shigo tace "To Daughter ya jikin?" "Da sauki Ummi." Wajen durowa ta karasa ta bude ta dauki akwati ta hau zuba mata kayan da zata bukata tana fadin "Yau sai Kanon dabo Daughter." Gaban ta ne ya fadi, dan tabbas ta tino komai na rayuwar ta ya tsayar mata da tunani kan Haidar da gaske ta rasa Haidar da gaskiya ba zata kara ganin Yaa Haidar ba, bata da damuwa a yanzu sai ta rashin Yaa Haidar wannan kadai ke sata kuka da damuwa sosai. Kallon Ummi take har ta gama hada mata kayan sannan ta fita dasu ba a jima ba ta shigo tana fadin "To ku taso." Maryam ta mike ta fada jikin Ummi tace "Ummi yaushe zaki zo?" "Insha Allhu kwanan nan kusa dan ni zan zo na dauko amaryar Aliyu." Sam ta manta da wani Aliyu ma sai yanzu ta tuna da auren su da Aliyu da haka sai ta share kawai haka suka fita ita da Ummi a falo taga su Ammi ta karasa ta gaishe su sannan suka mike zasu fita, har ta kai bakin kofa ta juyo tana kallon kofar dakin Yaa Aliyu ko yana ina, juyowa tayi ta nufi dakin nasa, tana bude kofa suka kusan cin karo da Aliyu da sauri tai baya wanda ta kusan hantsilawa da sauri ya taro ta ta fada saman kirjin sa, kamshin turaren sa mai dadi ya doki hancin ta, dagowa tayi tana kallon kasa. Aliyu yace "Ya akai?" Da sauri ta janye jikin ta tare da juyawa tana girgiza kai, wucewa tai ta nufi kofa ya kalle ta ya saki murmushi suka bar wajen. Bangaren Inna su Ammi suka nufa wannan yasa itama ta bisu can, duk suna zauna suna tattaunawa da Inna, Maryam ta shiga da sallama duk suka kalle ta, Inna ta mika mata hannu tace "Zo Uwata zanyi kewar ki duk da ba jimawa zaki ba." Maryam ta karasa Inna ta rumgume ta tana fadin "Kunganta nan ko, tana daya daga cikin jikoki na da na fiso, wallahi yadda nake jin ta ko su Asiya bana jin su, naji dadi da su Shehu suka aura ta ga Aliyu, dan na yaba tabbas da Maryam wanda in wani ya same ta munyi asara, matsala daya ita ce sai tayi hakuri da mijin nata dan miskili ne dan taimako tabbas ya mata dan zan iya cewa yafi su Aisha ma kula da ita to shi matsalar sa kenan da sun tambayen daman da zance su aurawa Umaru to amman ba yadda zanyi tinda sun aurawa Alin Allah yasa albarka ya basu zaman lafiya, kuma ina fatan su kawo min ya'yan su." "Insha Allahu Inna muna kara godiya da yadda kuka amshi Maryam a matsayin taku ba tare da kyama ba duk da tazo da ciki a tare da ita, har kuka aura mata d'anku a haka kuka rike ta da yaron ta, tabbas ba abinda zamu iya saka muku dashi." Ammi tai magana hawaye na kawo idon ta. Ummi tace "Haba Ammin Maryam ai yiwa kai ne." "Haka ne Allah kuma ya jikan ku ya bamu ikon kyautata muku." "Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!" Suka fada, Mami tace "To mu zamu wuce sai kunzo din." Duk suka mike suka fita, Maryam da Inna suka fito Inna rike da hannun ta har wajen mota suka rakasu, Farouk ya ja mota daya Aliyu dayar duk suka shiga suka nufi airport. A airport Maryam na jikin Mamah dan wasu abubuwan sai a yanzu take kara recalling nasu jikin ta yai sanyi, Haidar na wajen Ammi, har aka kira su, sukaiwa su Ummi da Yaa Haidar da Farouk Sallama, Maryam ta karasa wajen Ummi ta rumgume ta, Ummi tace "To menene na kukan Daughter?" Kai ta girgiza tace "Kije ki huta nan da sati biyu zamu zo insha Allahu." Kai ta gyada sannan ta Kalli Najwa ta karasa suka rungume juna sai wajen Basma, sannan ta karasa wajen Yaa Farouk tace "Yaa Farouk kaima zakazo gidan mu?" Kai ya gyada ta dan saki murnushi tace "Promise?" Ya gyada kai yace "I do." Juyawa tayi tana satar kallon wajen da Yaa Haidar yake Ummi tace "Ba za ai wa Yayan sallama ba?" "Ummi ai ban ganshi ba." Maryam ta fada tana juyowa, Ummi ta saki murmushi tace "To gashi." Ta nuna mata wajen da yake, karasawa tayi kanta a kasa tace "Yaya mun tafi sai kunzo." Kamar ba zai magana ba dan har ta juya taji yana fadin "Allah ya tsare ki kular min da Haidar." Kai kawai ta gyada ta bi bayan su Ammi, Mamah dake jiran ta ta karasa suka dunguma gaba dayan su. *KANO* Lokacin da jirgin su ya sauka a garin Kano bayan sun sauko ta kalli wajen wata ni'ima take ji na ratsa ta yau gata a mahaifar ta, cikin yan uwan ta, su Yaya Rabi, Yaya Hauwa, Yaya Ummulkairi da Yaya Zainab da Yaa Abdullah ne suka zo tarbar su gaba daya dan sun kasa tsayawa a gida lokacin da ta gansu hawaye ta hau yi, kowa so yake ta fara zuwa wajen sa, wajen yayyen nata ta nufa Yaa Abdullah sakon nata yazo ya rumgume ta yana fadin "Ni zaki fara yiwa oyoyo." Kamkame shi tayi tana sakin wani kuka mai taba zuciyar ta, dan ganin su gaba daya sai ya dawo mata da rashin Yaa Haidar, dan duk da Yaa Haidar ba dan gida bane amman in har zaka ga kowa to tabbas dashi a cikin su, lallashin ta Yaa Abdullah ya hau yi, Su Yaa Ummulkursun suka karaso duk suna bata baki, dagowa tayi tana bin daya bayan daya tana rumgume su ji take tamkar a mafarki yau gata a cikin ahalin ta bayan shekaru da ta kwashe ba tare dasu, ba, a baya ta manta da kowa nata a yanzu kuma ta tino da duk kansu wannan ma wata mu'ujizace ta Allah, a haka suka karasa gida kowa Maryam, Maryam kuwa sai kuka take dan da suka shiga unguwar tasu ma ta fara ganin sauye sauyen da aka samu, sai ta tuna fitowar ta ta karshe da ba zata manta ba, sai ranar da Haidar ya rasu da safe da Ammi tazo tafiya da ita wannan ne zata iya dorarwa da suka shiga gida kuwa taga yadda gidan ya kara kyau girma dan an gyara da abubuwan zamani, bayan sun fito a mota idon ta ya sauka a bangaren Yaa Alkasim bangaren da sukai dadabdala da Yaa Haidar take wani kukan ya kara taso mata, sai da ta kalli inda yake parking mota, ji tayi kamar zataga motar wajen ta kure da kallo hawaye na zubo mata Haidar ya karaso yace "Adda meyasa kike ta kuka ko gun Abbi da Ummi zaki koma, Adda su Ammi ma fa suna son mu ki daina kuka suma zasu na baki sweet ko Ammi!" Ammi ta karaso ta dauke shi tace "Sosai ma Haidar duk abinda kuke so shi za ai muku dan haka kada ka damu kaji." Ya kalli Maryam da hawaye ke bin kumatun ta yace "To Adda Smile and stop crying." Ya sa rigar sa yana goge mata hawayen murmushi ta dan saki wani hawayen na kara zubo mata Ammi ta kamo hannun ta tace "Na san tunanin da kike yi, kiyi hakuri, ki rumgumi kaddara, ki dauki hakan a matsayin zananniyar kaddararki. Haka Allah Ya tsara ma rayuwarki kinji?" Kai ta gyada hawaye na cigaba da zuba a idon ta ciki suka shiga bangaren Ammi an kara kawata shi an canja komai na ciki, har dakinta Ammi ta rakata a yayinda Yaa Fadima take binsu a baya dauke da Haidar. Maryam na shiga daskarewa tayi a tsaye tanabin dakin da kallo saboda haduwarsa, kallon dakin take cike da so da mamaki wanda da alama komai na cikin dakin sabo ne saboda walkiyan da yake, dakin yayi bala'in haduwa, komai na cikin dakin abun kallo ne, Maryam fadawa tayi a jikin Ammin hade da fashewa da kuka, da kyar Ammi ta rarrasheta tayi shiru, "Ki watsa ruwa sai ki fito kinji, bari naje na yiwa Haidar wankan shima." Ta juya ta fita dauke da Haidar, bayan ta tabi da kallo hawaye na taruwa a idon ta, kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet shi kansa toilet din ma abun kallo ne, acan ma sai da tayi kuka son ranta sannan tayi wanka ta fito, Gaban dressing mirrown ta dake cike da kayan kwalliya, jiki a sanyaye ta zauna akan karamin kujeran dake gaban dressing din, bata iya yin komai ba mai kawai ta shafa ta fesa turare sannan ta tashi a gurin, koda bataga akwatin da ta dawo dasu ba sai ta nufi wardrobe a tunaninta ko kila an saka mata kayan nata a cikin wardrobe din. Wardrobe ta nufa ta bude, wani hawaye ne ya kara gangaro mata akan kuncinta a yayinda idanunta sukai mata karo da kayakin dake cike a cikin wardrobe din kuma gaba daya sabbi, cikin sanyin jiki ta zabi wata bakar doguwar riga a cikin kayan ta saka sannan ta hau kan sallaya sallah tayi ta idar tana addu'a wacce rabin ta Yaa Haidar takeyiwa, tana cikin addu'ar Haidar ya shigo a guje yana dariya tare da kwadawa mata kira yana fadin "Adda! Adda!" Juyowa tayi kan tai magana ya fado kanta ya fara nuna mata picture din dake hannun sa yace "Adda wai wannan ma Abbi nane?" Picture din ta kalla, wanda Yaa Haidar a tsaye a jikin mota sanye da bakin wando da jar t-shirt yai kyau yana murmushin sa mai kyau kumatun sa ya lotsa kamar ka kira sa ya zo hawayen da ke cikin idon ta ne ya fara zubowa Haidar yace "Adda we look alike, ko?" Ya fada yana dagowa ya kalle ta ganin hawaye a idon ta ya tada hankalin sa ya hau goge mata fuskar sa kanar zai kuka yace "Adda, Abbi fa yace ba kyau ana kuka, ko nima inyi Adda?" Hannu tasa tana goge hawayen amman wani na kara zubowa, rungume Haidar tayi tana jin wani son sa da kaunar sa, da tausayin sa. Yaya Fadima ce ta shigo tana fadin "Wai Maryam har yanzu kukan nan kike?" Ta zauna a gefen gado tana fuskantar ta, tare da fadin "Haba Maryam ki bar wannan kukan dan Allah, yanzu godiya zakiyiwa Allah da ya hada ki da ahalin ki kika samemu lafiya. Kukan me kike? Na rashin Yaa Haidar ko na farin ciki? Yaa Haidar ya riga ya rasu ba abinda zaki masa a yanzu sai addu'a, adduar ki kawai yake bukata kuma kada ki manta ke matar aure ce a yanzu in har kikai tunanin sa ba ta hanyar dai dai ba haram ne, dan Allah Maryam kiyi hakuri ki dauki wannan kadaddar taki, ki sawa zuciyar ki salama kinsan kina da matsalar zuciya in har kika ce zaki na saka damuwa to tabbas ba zaki taba yin lafiya ba, muna murna munga yar uwar mu kuma sai ta dawo mana a cikin damuwa muna son ki bama son damuwa ki sam, dan Allah ki bar kukan nan. Wallahi tin daga ranar da kika bar gida bamu kara samun nutsuwa da jin dadi ba irin na yanzu kuma ace kizo da damuwa in kinsan yadda muka shiga na rashin ki bazaki taba dawo mana kina kuka ba, sam bana son damuwar ki har cikin raina abin yake damu na fada min me yake saki kuka? Yaa Haidar ne ko Auren da akai miki ne bakya so?" *Allah ya jikan musulmai Allah yai mana rahma. Amin* *Antty* [12/3, 11:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 71 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Kai ta girgiza kawai, Yaya Ummulkairi da Zainab dake bakin kofa suka shigo suka saka yar uwar tasu a tsakiya, Yaya Ummulkairi wacce take babba a cikin su tace "In kika duba rayuwar ki ta baya tin daga haihuwa har ranar graduatin din ki me zaki ce ga Allah? Na tabbata godiya ce saboda a lokacin baki fuskanci ko wanne kalubale ba, rayuwa kike cikin gata da soyayya, komai naki sucess. To a haka bawa zai ci gaba da tafiya babu jarabawar rayuwa? A'a! In har Allah bai jarabtar ka ba ma to ka tuntubi imanin ka, amman ke kin tashi cikin gata sai ga wannan jarabar ta rasa miji a gareki wanda shine hope din ki, shine farin cikin, bayan nan ya dauke miki magana sannan ya jarabce ki da abubuwa masu yawa har kika bar gida kikaje wani wajen kikai rayuwa mai tsayi wanda suka rike ki da amana a karshe sai ya baki d'a duk da Allah ya dauke miki uban shi sai ya baki magajin sa, wanda gashi nan kikai masa takwara shin wannan ba wata ni'ima bace, bayan kin bar gida kinyi rayuwa mai kyau a wani waje wannan ba ni'ima bace a karshe rashin ahalin ki na asali duk da kin samu asalin su yasa ba a aure ki ba amman wadanan mutane masu karamci suka bawa dansu mafi soyuwa a gare su wannan ba ni'ima bace, wanda zai rufa miki asiri kinsan me, a yau da kika dawo wallahi ba kowa zai yadda da ina kika je ba wasu cewa zasuyi wayon karuwancu da makamantansu kika je amman ganin ki da miji zai cire wanna aransu dan haka abinda zance miki rayuwa juyi juyi ce yau fari gobe baki ki godewa Allah kuma ki amshi jarabarwar ki kinji." "Kullum a cikin gode masa nake Yaya Ummu, amman yau zuwa na gida ya tadan hankali ji nake tamkar yau na rasa Yaa Haidar abubuwa da dama nake tunawa na rayuwar mu Yaya Ummu, kunsan wanenen Yaa Haidar kuwa?" Ta fada tana binsu da kallo, murmushi sukai dan sun sanshi farin sani tinda tin ba a haife ta ba sukai rayuwa. "Ku tayani da addu'a kawai amman zuciya ta ji nake tamkar zata tarwatse da gaske dai na rasa Yaa Haidar, da gaske ba zan sake ganin sa ba ya tafi inda ba a dawowa." Ta fada taba kife kanta a jikin Haidar dake ta kallon picture Abban sa yana jin son sa a cikin zuciyar sa, hawayen da yaji na Addan sa yasa ya juyo yace "Adda kalli Abbi na murnushi yace ba kyau kuka ki daina shima yace ki daina." Yaa Alkasim ne ya shigo yace "Tabbas Haidar kayi gaskiya abinda Abbin ka yafi tsana yaga Maryam tanayi kenan kuka, in har zai ga Maryam na kuka to tabbas hankalin sai yayi dubu ya tashi ba zai taba samun nutsuwa ba har sai yaga tana murmushi amman yau bayan idon sa ba zata masa wannan alfarmar ba wanda da yana nan yanzu tasan bashi da kwanciyyar hankali, ki godewa Allah Maryam da komai na rayuwar ki Haidar ya tafi ga wani ya dawo, kin tabbata *Matar Haidar* dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan bana so sam bana son kukan ki." Kallon yan uwan nata take ganin yadda duk suka shiga damuwa dan sunganta tana kuka, murnushi ta kirkiro tana goge hawayen idon ta hadi da fadin "Insha Allahu ba za ku sake ganin hawayena ba da damuwa ta ba na daina kuma ku daina damuwa kalle ku dukka akai na kun shiga damuwa in kai hakkin ku ina, ni ma na daina insha Allahu kuna tayani da addu'a ina fatan kuna saka Yaa Haidar a addu'ar ku?" Kai suka gyada tace "Nagode Allah saka muka da gidan Aljanna Allah ya bar min ku." Suka amsa da Amin. Yaa Alkasim ya kamo ta yace "Taso muje muci abinci." Ya dauki Haidar. A parlour ta tarar dasu Yaa Muhammad suna zaune suna jiran fitowar ta, Rumgume juna sukayi itada Anty Rabi'a cikin jindadi kafin daga bisani suka nufi Dining dukkansu, Ammi duk wani abu da tasan Maryam naso shi aka dafa. Cikin barkwanci da farin ciki suke cin abinci har suka kammala. A wannan rana dai wannan ahali haka suka yini cikin farin ciki har da matan su Yaa Muhammad Aisha ma tazo, a haka Abbi yazo ya tarar dasu shima aka dora hiran dashi, sai wajen karfe 11 na dare suka warwatse shima da kyar Hakika Maryam taga kauna, kulawa da tattali dan sam ba a barin ta ita kadai da anga tai jigum za a hau tambayar ta da sata nishadi, baga Abbi ba, baga Ammi da yayyen ta ba gaba daya sun zama yan gata sai abinda suka so ita da Haidar. Haidar abinda yake nema ya samu dan ga yara a gidan yayan su Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim, Yaa Abdullah ne kadai bai aure ba. * A gidan Mamah ma murna haka suka dinga kula da Yaa Abubakar da Matar sa da yayan su, Abba ne ya shiga bangaren Umma ya same ta a cikin daki, tana ganin sa ta mike ya karaso ya rumgume ta yace "Albishirin ki?" "Goro!" Ta bashi amsa yace "To bari kiga." Ya kulle mata fuska da kyalle suka fito falon wanda anan Abubakar da Nusaiba suka zaune da yayan su biyar har da Haidar na shida, suna fitowa ta ji hayaniyar yara ya bude mata ido, idon ta akan Haidar ya fara sauka da sauri ta fara nunasa tace "Alhaji wannan fa?" "Wannan shine dan wajen Haidar da Maryam." Da sauri ta dago tana kallon sa ya nuna mata inda Yaa Abubakar da Nusaiba suke zaune tana kallon wajen ta zabura tai baya ta fara fadin "Na shiga uku shikenan yau asiri na ya tonu boka na kan tudu yace indai Abubakar ya dawo gidan nan shikenan zan haukace, lahhh wai Haidar ma ya bar baya daman? Wadan nan ya'yan fa Alhaji?" Ta fada tana kallon su Arfat, wanda ga kamar Abubakar a tattare dasu wata dariya ta barke da ita tace "Wai da gaske wadan nan ya'yan Abubakar ne ni da nai alkawarin tin da ban haifa ba itama ba zata ga jinin ta ba amman yau ga Abubakar ya dawo sannan ga jikoki har...." Ta daga hannu ta fara kirgawa tana fadin " 'daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida." Sai ta barke da dariya ta kalli Abba tace "Nice nan na batar da Abubakar nice nan, sannan Aliyu ni na masa asiri ya kamu da wannan matsananciyar sha'awar wanda duk buri na shine yaiwa shegiyar yarinyar nan fyade da yake yana da tsoron Allah shine yaje ya dauke ta sukai aure....." Ta kara sakin dariyar tana fadin "Itama Maryam din, jin tana da ciki yasa na saka aka batar da ita aka kuma cire mata komai a kwakwalwar ta, uban wa ya gano ta dan an fada min in har taga wanda ta sani ne zata tino komai waye ya gano ta ya bata min aiki?" Ta fada tana fashewa da kuka, sai kuma ta saki wata uwar kara ta zabura a guje ta fice a dakin da gudu Abba yabi bayan ta sai dai kan ya karasa har ta fice a compound din Yaa Abubakar ya bi Abba suka bi bayan ta amman wani uban gudu take yi a haka ta fice a layin Abba ya koma ya dauko Mota Yaa Abubakar shida suka bita suna karasawa titi ta hau saman titi dai dai zuwan wata katuwar daf ta ture ta tabi ta kanta ta tatse ta take kanta ya fashe, wanda bata kara shurawa ba ta mutu. A kan idon Abba abun ya faru haka aka dauke gawar ta aka tafi gida dan ai mata sutura akai ta gidan gaskiya inda in ka aikata mai kyau zaka girba in ba akasin haka ne same. Haka su Abba suka dauko ta aka zo akai mata sutura, aka kaita gidan ta na gaskiya. Haka akai zaman makoki na kwana bakwai wanda ranar da Ummah tai kwana bakwai aka hada family meeting din gidan Abba wanda yan uwa suka zo sosai anan aka gabatar da Yaa Abubakar da matar sa da ya'yan sa, tare da Haidar. * Zaune take a dakin ta Haidar kwance a jikin ta yana ta game da wayar ta, ba bacci take ba amman idon ta lumshe ta lula duniyar tunani wasu lokaci da suke shede da mafarin komai ```Kwance take akan gadon makaranta waya kare a kunnen ta kuka take yi tinda ta dauki wayar, hankalin Haidar yayi dubu, cikin murya damuwa yace " *Matar Haidar* dan Allah ki bar wannan kukan ki fada min me yake faruwa." 'Kin magana tayi yace "Kina so nima nai miki kukan?" A yadda yai maganar sosai rauni ya bayyana, a cikin muryar sa, kai ta girgizawa tamkar yana ganin ta, yace "To *Matar Haidar* fadawa mijin Maryama abinda yake damun ta me take so fada min." Wani kukan ta kara fashewa dashi tana fadin "Yaya ba kai bane." "Naji nine fadamin abinda nai miki ni kuma nayi alkawarin hukunta miki kai na" "Au baka san mema kai min ba?" Ta fada tana sheshekar kuka, ya sauke ajiyar zuciya yace "Na sha'afa ne, *Matar Haidar* ." Wani kukan shagwaba ta kara saki, wanda yake haifarwa da Haidar wani abu a jikin sa da zuciyar sa, tace "Yaya yau kwanan ka nawa baka zo kaga Matar ka ba?" "Baby amman na fada miki aiki ne ko?" "Aiki yafi ni ko?" Tana fada ta kashe wayar, wayar yabi da kallo ya dago ya kalli Ahmad dake gefen sa. Ahmad yace "Kukan kaima zakayi ne yarinya karama na juya ka kamar waina." Wani kallo Haidar ya aika masa yace "Wayar fa ta kashe, shin kasan yadda nake ji na rashin ta kuwa nima da kyar na iya daurewa." Dariya Ahmad yayi yace "Shugaban soyayya." "Naji." Ya mike ya shige daki wayar sa ya dauka ya kara kiran ta, tana gani tana kuka taki dauka domin kuwa, ita kadai take jin kewar sa, ji take kamar tai tsuntsuwa taje wajen sa ta manta rabon da tai sati biyu bataga Yaa Haidar ba, amman yau ita ce tai sati hudu ba Yaa Haidar, hakika bata san haka ake ji ba in anyi kewa, a baya tana jin kewar sa amman na yanzu yafi na da ji take kamar ba ita ba, jin ta take incomplete, tana jin wayar na kara har ta gama bata dauka ba, da kyar ta katse bata dauka ba yana kara kira ta dauka ta kai kunne tace "Uhmmm." "Anya kuwa *Matar Haidar* ce?" "Uhmm uhmm me ka gani?" "Ban taba ganin *Matar Haidar* ta kashewa Haidar waya ba." "Yaya...." "Na'am nayi laifi Matata amman kiyi hakuri nima ba yadda zan yi gobe zan zo zan fada miki dalili amman ki min alkawari sama min mafita." "Nayi." "Yauwah my Love, fada min Ya My love take?" "Ba lafiya." Da sauri yace "Meyake damun ta?" "Kewar ruhin ta take." "Haba Baby na ko da ace ruhin mu na nesa da juna na tabbata ina tare da ke a zuciyar ki." "Ni dai Yaya wallahi i miss you." "I miss you more dear am sorry ba zan sake ba." "Promise?" "Yes i promise." "To gobe da yaushe zaka zo" "After mosque." "Allah kaimu." "Wacce kwalliyya zanyi miki?" "Kaima ka san ai kowacce shiga kai kyau kake Yaya." "I love you Baby." "I love you more Yaya." "To aje a maida waya a kwanta kinji?" "To Yaya sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." "Amin." Ta kashe wayar ta lumshe ido tana jin wani so da kaunar sa na kara shigar ta, hakika bata san halin da zata shiga ba in ta rasa Haidar mikewa tayi ta maida wayar ta sannan ta dawo ta kwanta ita kadai. Rukayya da Aisha ne suka shigo dakin suka same ta kwance suka karasa suna fadin "Ya dai?" "Kewar Yaya nake." "Kai Maryam kefa ko?" "Ni fa me? Ku kunsan soyayya kuwa, Yaya ya gama zama jini da hanta ta, wallahi baki ji yadda nake ji ba na rashin sa, ji na nake incomplete kamar bani da lafiya kamar bani ba." Filo ta rungume tana fadin "Myyyy." Aisha ta mike tace "Allah shirya ki." Juya musu baya tai tare da lumshe ido tana tuna wani daga cikin moment din da sukai spending da Haidar a haka bacci ya dauke ta cike da mafarkansa. Washe gari kamar yadda ya fada bayan an sako daga masallaci ya wuce makarantar su, bakin gate din ya karaso, tint glass din ya sauke, fuskar sa ta bayyana gate man din da sauri ya washe baki yana fadin "Barka da zuwa Dr." Hannu Haidar ya mika masa yana fadin "Ya aikin?" "Alhamdulilah kwana biyu?" "Wallahi aiki ya mana yawa." "Allah sarki jiya Baba Khamis yake maganar ka yake cewa kwana biyu Allah yasa lafiya." Dan murmushi yayi ya zura hannu ya damko kudi ya mika masa yana fadin "Alhamdulilah." Amsa yayi yana godiya nan da nan ya bude masa gate din ya shige parking yaje yayi sannan ya fito, sanye yake da sky blue din shadda sai kyalli take ya saka bakin takalmi sau ciki, da bakin agogo, hannun sa rike da hular sa, sakawa yai akan sumar sa mai yawa ga taushi sai sheki take, sosai yayi kyau, ciki ya shiga ya nufi office din Principal kai tsaye, yana tafiya suna gaisawa da ma'aikatan wajen, a haka har ya karasa office din principal din yana shiga ya ganshi zai fito amman ya koma yana fadin "Aliyu kwana biyu." Kai ya sunkuyar yace "Wallahi Abba aiki ne ya janye ni." "To ya aikin yasu Alhaji Suleiman din?" "Suna lafiya." Sakatare din sa ya kalla yace "A kira masa Maryam in ya gama ka rufe min office din." "Ok Sir." Ya juya ya tafi Haidar ya masa godiya yana zaune suka shigo su uku, Maryam ta tsaya jikin kofa tana kallon sa, cike da so da kauna, su Rukayya suka karasa gaisawa sukai da Rukayya da Aisha sannan ya mike yana kallon Maryam dake kallon sa, ya karasa gaban ta ya durkusa yace "Doke ni dan Allah." Su Aisha suna dariya suka fice, sai da suka fice ya dago yana kallon ta sai kallon sa take, mikewa yayi ya kamo hannun ta suka zauna akan three sitter, dan murmushi ya saki ganin sai dauke kai take, yace "Tinda ba zaki gaishe ni ba ni bari na gaishe ki ina yini?" Dan murmushi ta saki tace "A'ah." Yace "To me?" Kafada ta make sai kuma ta mika hannu ta shafa fuskar sa tace "Yaya baka da lafiya ne?" Hannun ta ya kamo yace "Kema baki da lafiya ne? Duk kin rame." "Ban kai ka ramewa ba Yaya." Ido ya lumshe, yace "I miss you Baby." Hannun ta ta janye tace "Nima haka." Ya dago yana kallon ta cike da so da kauna, ji yai wani son ta yana kara shigar sa, tai masa kyau duk da sanye take cikin farin hijab amman gashin gaban goshin ta duk ya kwanta, na girar ta ma ya kara yin baki kamar tayi jagira, ga na idon ta da ya kara yin gazar gazar, sai lips din ta da suka kara pink dasu kamar ta shafa man lebe da sauri ya dauke idon sa daga kallon ta a hankali ya fara magana "Kan na ce komai ina mai baki hakuri da rashin zuwa na na kwana biyu nima ba a son raina bane, domin na fiki shiga halin damuwa saboda na riga na saba da kasancewa dake hakika na sha wahala na rashin ki *Matar Haidar* " "Ba komai Yaya, amman wannan wane irin aiki ne ya rike min miji na ba ruwa na dashi." Tai magana cike da shagwaba.``` *Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/3, 11:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 72 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ``` "Maryam....." Ya kira sunan ta a hankali da sauri ta dago tana kallon sa, dan kan Haidar ya kira sunan ta ana dadewa in kuwa ya kira ta tabbata babban abu ne, dan haka ta mika masa hankalin ta gaba daya tace "Na'am Yaya." "Maryam ina da matsala ina da damuwa." "Amman Yaya baka fada min ba." "Bana son hankalin ki ya tashi bama in kika kasa magancen." "Allah ba zai kawo abinda zan kasa magance maka ba." "Ko menene?" Kai ta gyada, ya dago yana kallon ta sai ya dauke ido sa yace "Maryam ina bukatar ki." Murmushi ta saki tace "Nasan da haka Yaya." "Wannan bukatar daban da waccan, a kwanakin baya ina fama da wani ciwon ciki wanda da kai na na gano dalilin sa, aure nake so, mace nake so, da farko na dauki ciwon da wasa amman a yanzu ciwon na neman ya kwantar dani, in yaci jiki na zan iya rasa rayuwa ta a ko da yaushe, solution daya ne Maryam shine nayi aure na tara da iyali na, nayiwa Ummi maganar a matso da auren mu tace wata nawa ne ya rage, a yadda nake ji na Maryam ba zan iya kai wannan lokacin ba ina bukatar mace a tare dani, na sani ko wanne namiji yana da bukatar mace amman ni nawa na yanzu abun yai yawa bansan ya akai haka ba. A duk lokacin da nazo na ganki na koma hankali na na bala'in tashi nakan rasa nutsuwa ta na kan shiga wani mawuyacin hali wannan yasa na yanke shawarar rage zuwa sai dai shima bata haifar min da d'a mai ido ba dan koyaya naji sautin muryar ki ni kadai nasan halin da nake shiga ga kewa da son ganin ki, Maryam yaya zanyi na rasa madafa." Ya fada idon sa na canja launi, saukowa tayi daga kan kujera ta kama hannayen sa hawaye na zubowa a idon ta na tausayin Aliyu, ya kalle ta, yana share mata hawayen sannan yace "Matsalar mu kusan daya ce domin kema wannan ciwon marar naki ba zai taba barin ki ba in ba aure kikai ba." Kai ta hau girgizawa tace "Yaya kana kuma azumin?" Hannun ta ya kama yace "Ina yi, amman yanzu da kyar yake kaiwa." "Yaya to ya ya zamuyi?" "Yaya ko Ammi zanwa magana?" "A'ah!" "To yaya zamuyi? Ka samo mana mafita." Shiru yayi tace "Kaji Yaya." "Shikenan zan samo insha Allahu," Ya mike yana fadin "Bari na tashi." "Ina? daga zuwan ka." "Babyyy." Ya kira sunan ta da wani sauti da yasa sai da tsigar jikin ta ta tashi, ido ta lumshe tana fadin "Uhmm uhmm Yaya..." Tai maganar kamar zatai kuka. "Ki barni na tafi kar nai abinda ba kyau." Tai murmushi tace "Ina kaunar ka Yaya na." "Nima ina kaunar ki Baby na." Ya nuna mata hanya yace "Muje!" Ba musu tabi bayansa ya dauki ledar da ya kawo musu abu ya fita, a bakin office din ya tsaya tace "To Yaya sai gobe ko jibi?" Wani kallo ya aika mata yace "Sai kin ganni dai." "Please Yaya kada ka dade kamar yanzu." "To Baby na, wannan shagwabar kara zautani take." Ta dago tana masa wani kallo ya matso daf da ita yace "Kina son ki haukatani ko?" Juyawa tai tana girgiza kai hadi da murmushi yace 'Ungo sai munyi waya." Ya mika mata ta rissina ta amsa tace "Thank you Yaya." "Ba godiya hakkinane." Tai murmushi tace "Ka gaishe min da su Ammi da Mami." "Zasuji." Ya juya yana juyowa yana daga mata hannu, itama hannu take daga masa tare da sakar masa murmushi, juyowa yai yana kallon ta a hankali ta motsa bakin ta, ta furta "I Love you Yaya!" A hankali ta furta wanda dan yana ganin ta yasa ta gane me ta fada, ido ya lumshe yana furta mata "I love u more." Sannan ya juya ya fice a gate din itama tayi cikin hostel din su, daki direct ta shiga ta kwanta a saman gado tana mai lumshe idon ta, wani son Yaya Haidar taji na azalzalar zuciyar ta, hannu ta daura akan zuciyar ta, tabbas bata da wanda take so, Yaa Haidar shi ya sabar mata da komai, shi ya koya mata wannan son ta, ta yadda ta aminta Yaa Haidar ba zai taba cutar da ita ba domin kuwa ta sani kowa da yasan alakar su tin tana karama duk inda zashi tare suke zuwa har yanzu da yake aiki, wanda a wajen aikin sa duk wanda yasan waye Haidar to tabbas yasan Maryam domin daga dakin Haidar, motar sa, office din sa duk hutunan Maryam ne a makale, kuma duk abinda yake akwai lokacin Maryam, wanda kome yake zai katse shi dan baya shiga lokacin ta bama in yana gida, iyayen su kowa har mamakin wannan irin soyayyar suke, kowa fatan alheri yake musu a rayuwar su. Bayan kwana biyu da magariba ta samu kiran sa, dauka tayi cike da zumudi tace "Yaya nah." "Na'am Matata." "Yaya ya aikin?" "Alhamdulillah." "Yau da kasala da faduwar gaba na tashi duk bana jin dadi Yaya me yake damun ka?" Ido ya lumshe yana mai dan cije lips din sa yace "Baby ciwon cikin nan ne yau ya tasar min, nayi niyya nazo na ganki amman ban samu dama ba." "Ayyah sorry My, kaje asibiti? Ya cikin? Ya kake ji? Sannu Yaya kasha magani?" Jigina yayi da gado yana lumshe ido yace "Baby na fada miki matsala ta, maganin ma sam ya daina min aiki." "Innalillahi yanzu Yaya ya zamuyi?" Ta fada hawaye na zubo mata, tare da shesheka. Cikin dauriyya yace "Dan Allah ki bar kukan nan ina nan ina samo mana mafita insha Allahu cikin week din nan zan samo mana mafita kinji?" Sheshekar kuka ta fara yace "Wallahi zafin yadda kike zubar da hawayen ki yafi zafin ciwon da nake ji." "Na daina Yaya." "To my Baby yanzu ya karatun?" "Uhmm Alhamdulillah." "Exam sauran kwana nawa?" "Few week Yaya." "Baby ta kusa ta tabbata a *Matar Haidar* kenan, bai kai three month bafa." Kai ta gyada yace "Allah nuna mana wannan lokacin." "Amin Yaya yanzu ya kake ji?" "Da sauki my love yanzu ma zan fita na je na gaishe dasu Abbi yau tin asuba bamu hadu ba." "Agaishe min dasu ina Yaa Alkasim?" "Bai jima da fita ba." "Ok!" Daga nan suka dan taba hira sukai sallama. Ammi ta fara kira Ammi na ganin kiran ta katse wayar ta kirata, dauka tayi ta kai kunnen ta ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa tace "Meyake damun ki Ummi?" "Ammi, Yaya ne bashi da lafiya." Ta fada tana sheshekar kuka. Ammi tace "Kuma shine kike kuka?" Sheshekar kukan tta cigaba dayi, Ammi tace "Yi shiru to ki fada min kema baki da lafiyar ne?" "Tin safe nake jin faduwar gaba Ammi, ga zazzabi dake son rufeni, uhmm Ammi dan Allah kukai Yaya asibiti a dubashi a fada masa me yake damun sa, kuma Ammi yace....." Sai tayi shiru, Ammi tace "Me yace?" "Uhmm uhmm ba komai amman Ammi please ku kaishi asibiti." "To za a kaishi ki daina kuka, kar kisa damuwa kinji zan kirasa yanzu sai muji me yake damun nasa." "Yauwah Ammi ina Abbi?" "Yanzu ya shigo ya shiga watsa ruwa." "Ammi ki gaishe shi yaushe zaki zo?" "Zan shigo insha Allahu." "To sai da safe." Sukai sallama, Ammi tabi wayar da kallo tana jinjina soyayyar Maryam da Haidar, tana cikin tunani taji sallamar Aliyu cikin sanyin murya yai sallamar daga ji kasan baya jin dadi. Ta amsa ya shigo sanye yake da wandon jean sai farar riga mai gajeran hannu sai kamshi yake duk ya rame ya zauna a kasa kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" "Lafiya lou Haidar ya kake ya gidan ashe baka da lafiya me yake damun ka?" Kai ya dan sosa yace "Ciwon ciki ne Ammi amman ai yayi sauki." "To kaje asibiti yanzu Ummi ta kira tana kuka wai mukai ka asibiti." Murmushi yayi, Abbi ya shigo yana fadin "Waye ba lafiya?" Ya shigo ya zauna Ammi ta ce "Haidar ne." Ya kalli Haidar da kansa ke kasa duk ya fada yace "Me yake damun ka Haidar?" "Abbi ciwon cikin nan ne dai amman da sauki." "An maka sceening kuwa ya kamata kaje ai maka." "Insha Allahu Abbi, ina yini?" "Lafiya lou ya jikin?" "Naji sauki." "Allah kara sauki." Abbi ya janyo katon tray din da Ammi ta ajiye zai zuba Ammi ta sauka ta zuba masa, ya kalli Haidar yace "Taho muci Haidar." Kai ya girgiza Abbi yace "Bashi ragowar papper soup din yaje yaci." Ammi ta bashi flask din zai gardama Abbi yace "Tashi maza kaje kaci, zan maka tofi in nagama ko Alkasim ne na bawa ya kawo maka Allah kara sauki." "Amin Abbi nagode." Ya mike ya fita, da Alkasim sukaci karo tare suka tafi gidan su ya zauna a falo yasha pepper soup din har goma sannan sukai sallama. * Waya ce a kunnensa yace "Ahmad yanzu me kake ganin zamuyi?" "No best solution shine kuje kuyi auren sirri a daura muku aure in yaso ka samu ka biya bukatar ka kaga ai bakai sa'bo ba." "Baka ganin mun sa'bawa iyayen mu." "Aliyu wannan ita ce last chance ko zakaje ka fadawa su Abba kana fama da sha'awa suyi maka aure, tinda baku sa'bawa Allah ba ai mai sauki ne, su kuma iyayen naku kwa fada musu daga baya, bayan bikin ma ba daukar lokaci za ai ba tana makaranta kaje ka dauko ta friday a daura auren kuyi weekend tare waya sani babu uhmmm." "Zan je wajen ta gobe zamu tattauna duk yadda ake ciki shikenan." "To amman fa sai ka kashe ta da kalamai tinda tana son ka ma na tabbata zata aminta." Da wannan shawarar sukai sallama. * Washe gari ya nufi makarantar su, lokacin da tazo ta ganshi kuka ya saka masa, cikin tashin hankali ya mike ya dawo gaban ta ya durkusa yace "To kukan menene Baby?" "Yaya kaga yadda ka rame kuwa? Kana shan magani?" Ya dan saki murmushi yace "Ina sha mana. Yanzu dai daina kukan nan muyi wata magana." Dagowa tayi tana kallon sa idon ta duk hawaye yace "Solution na samo mana." Hawayen ta hau gogewa ya zauna yana kallon ta yace "Mun tattauna da Ahmad kuma matsaya daya muka samu in ba ita ba ni ban ga wata mafita ba." Batai magana ba kallon sa kawai take tana jiran taji mafitar yace "Aure zamuyi Maryam amman auren sirri." Da sauri ta kalle shi cike da alamar tambaya, kai ya gyada mata yace "Yes, shine kadai solution tanan ne kadai zan same ki a halak dina kuma mu samarwa kanmu mafita, ba haramci zamuyi ba da auren mu." "Yaya ba wata mafitar sai wannan." "Babu ko kina son mu mallaki kanmu ta haramtaciyar hanya ne?" Kai ta hau girgizawa yace "To ko zakije ki fadawa su Abba cewa ga abinda yake damuna?" Nan ma kai ta girgiza yace "Ko kin samo mana mafita?" "A'ah Yaya." "To fada min menene abun mafitata, ni a gani na tinda ba mu sa'bawa mahallici na ba ai ba wata matsala kuna kwana nawa ya rage mana." Ajiyar zuciya ta sauke ta karaso tana fadin "Yaya in akai auren zaka warke?" "Insha Allahu." Hawaye ne ya zubo mata tace "Na amince." Kallon ta ya tsaya yi, tai kasa da kanta hawaye na zubo mata "Tinda ba haram bane dan na taimake ka ne Yaya na yadda zan baka komai nawa in har bai zama haramci ba zan baka farin ciki na da rayuwa ta, na yadda dakai kai mai so nane da kauna ta ba zaka tabai min abinda zai cutar dani ba, na yadda Yaya na zama *Matar Haidar.* " "Allah miki albarka!" "Amin." Ya mike yace "Tafiya zanyi zanzo ranar Friday sai mu tafi ko?" "Allah ya kaimu." Sukai sallama. * Ranar juma'ar da ba zata manta ba ita ce ranar da Yaa Haidar yazo mata da kudurin sa wanda ya bada card cewar likita zata je ta gani kamar yadda take zuwa lokaci zuwa lokaci ana dubata, ba bata lokaci saboda sun san Haidar aka bashi ita, suna shiga mota ya kalle ta yace "Zamuje wajen wani malami Ahmad yana can zai zama waliyi ki, ni kuma Malamin zai zama waliyi na ina fatan ba matsala." Kai kawai ta gyada, a haka suka karasa gidan malamin Haidar ya kashe motar ya fito ya zagaya ya bude mata, ta fito jiki a sanyaye suka karasa rumfar, wanda Malamin ne da Ahmad a zaune, a gefen Haidar ta zauna suka gaishe dashi, ya amsa yana fadin "Itace yarinyar?" Kai Aliyu kawai ya gyada, Malamin ya kalli Maryam yace "Ya sunan ki?" "Maryam." Ta fada murya a sanyaye, yace "Aliyu ya min bayanin komai akan lalurar sa wanda yace ya sanar dake haka ne?" Kai ta gyada, yace "Da gaske kina son sa zaki aure shi?" Kai ta gyada yace "Kin yadda a daura muku aure yanzu?" Kai nan ma ta gyada, duk abin nan da ake akwai mai musu vedio, har ya gamai mata tambayoyi sannan ya kira aminan sa, a take aka daura auren Maryam Muhammad Jabeer da Aliyu Suleiman Abubakar akan sadaki dubu dari ga dan kunne da sarkar da abin hannu na gwal, bayan an gama aka basu certificate din su sannan sukai sallama da Malam Aliyu ya amshi wayar da akai musu vedion komai.``` *Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/4, 17:33] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 73 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* _Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono) Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani da maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko da nono suyi bul² nono ko yakai silifas yamushewa kikai amfani dashi zakiga canji Maganinmu bashi da side effect mun hadashi da tsirrai da saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state da yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606_ ```Mota ya saka Maryam ya dawo wajen Ahmad yace "Thank you so much friend." Ahmad ya murmushi yace "Never mind, yanzu dai matsala ta 'kau, amman please abi da yarinyar nan a hankali kaji?" Wani kallo ya watsa masa yace "Baka fini son abata ba ai." Yai gaba yace "Sai na kira ka." "Ok aci amarci lafiya." Daga nan ya shiga motar ya tada ta, suka fita daga unguwar, wani super market yai parking ya kalli Maryam da ta lafe jikin kujera yace " *Matar Haidar* " Dagowa tai tana kallon sa, hannun ta ya kamo ya dan murza yana sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar masa, yace "Ina zuwa kinji?" Kai kawai ta gyada ya mata kiss a kumatu ya saki hannun nata tare da fita, super market din ya shiga bai jima sosai ba ya fito aka biyoshi da manya manyan ledoji boot ya bude aka saka kayan ya shiga ya tada mota ya juyo ya kalli Maryam da ya kasa gane a halin da take, hannun ta ya kamo ya fara murzawa a hankali ta d'an d'ago ta kalle shi, ido suka hada tai saurin kawar da idon ta gabanta na faduwa yace " *Matar Haidar* !" Ido ta lumshe domin kuwa yau ta yadda ta tabbata *Matar Haidar* burin ta kenan a rayuwa Allah ya amsa amman kuma babu iyaye a ciki anya kuwa sunyiwa iyayen su adalci? Abinda ya tsaya mata kenan. " *Matar Haidar* ya naganki wani iri ne shin bakya murna da wannan ranar da kika zama mallakin Haidar?" Ya fada yana kamo hannun ta, kai ta girgiza ya kawo hannun ta wajen bakin sa yai kissing din sa yace "Yau kin zama mallaki na halali na komai zai faru tsakanin mu sai samun lada a cikin sa, so damuwar fa? Fada min uhmmm?" Murmushi ta dan saki tace "Bani da damuwa Yaya sai tunanin iyayen mu shin mun kyauta musu?" "A gaba in sukaji abinda mukai sai dai su sa mana albarka tinda ba mu biyewa shaidan ba muka samar wa kanmu mafita mai kyau, yau ko d'a muka samu kinga d'an sunna ne, kuma duk abinda zamu aikata lada zamu samu, na zama naki kin zama tawa kina da hakki akai na nima haka sai muyi fata da addu'a Allah ya cika mana burin mu ya bamu ikon sauke hakkin kowa." Ido ta lumshe ji tayi yana mata wani irin abu a hannu wanda ya kara kashe mata jiki, yace "Zan kai ki gidan mu na shirya mana shi, ko bayan auren mu zamu cigaba da zuwa muna sha'katawa." Murmushi kawai ta saki, wani mai kaji ya gani ana gasawa wajen har da resturant, parking yayi ya sauka yaje ya siyo ya dawo da ledoji ya saka a baya ya ajiye, ya tayar da mota, lokacin da suka karasa shida saura dan haka suna zuwa ya sauka ya bude gate ya shigar da motar ya dawo ya rufe. Kofar motar yazo ya bude mata ta fito tana kallon harabar gidan ba sabo bane a wajen ta amman wancan zuwa duk da ana aikin gidan ne sai da aka gama yau gata ta shigo gidan a matsayin matar mai gidan, hannun ta ya kamo ya janyo ta ya rungune ta yana fadin "Alhamdulillah!" Lafewa tayi a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, sunkuyawa yayi ya dauke ta, tai saurin kamkameshi, a haka suka nufi enterance din gidan wanda akai masa yar barander da kujeru da shuke shuke ya bude kofar suka shiga wani madaidaicin falo, wanda suna shiga sanyi da kamshin dakin yasa ta lumshe idon ta a hankali ta bude tana bin dakin da kallo, komai na ciki sabo ne, set din kujeru ne Brown kala da coffee sunyi kyau sosai sai kayan kallo bakake da labulaye brown kala, can gefe dining area ne sai kitchen sai wasu kofofi guda biyu daya bedroom ne da toilet dayan kuma wani falo ne again da bedroom da toilet bai dire ta ba sai da suka shiga bedroom din ya ajiye ta akan gado yace "Magariba ta gabato, ki shiga kiyi wanka kiyi sallah kinji?" Kai ta gyada masa kawai ya juya ya fita, kayan ya shigo mata dasu sannan ya fita, tashi tayi ta shiga tai wankan ta dauro alwala ta daura towel, tunanin take tayaya zata fita lekawa tayi taga ba kowa a dakin da sauri ta fito ta karasa wajen kofa ta rufe sannan ta nufi ledar da ya shigo da ita, budewa tayi kayane amman duk wanda ta dauka ta daga sai taga ba zasu wuce gwiwa ko cinya ba daga riga da wando sai doguwar riga sai siket da riga, komawa tayi ta zauna jin ana kiran sallah yasa ta mike, wata doguwar riga ta saka wacce ita ce ta kai mata gwiwa sannan ta saka wani katon hijab da ta gani a ciki, sallaya ta shimfida ta tada sallah, bayan ta idar ta zauna tana addu'a wanda yawanci akan rayuwar suce, har akai isha'i tana addu'a ta mike ta tada sallah bayan ta idar ta tada shafa'i da wuturi, tana cikin yin wuturin taji shigowar sa, ya shigo ya zauna. Idarwa tayi tana addu'a ya sauko ya zauna a gaban ta ta gama ta shafa. Ya kalle ta, ta shagwabe fuska dan murmushi ya saki yace "Baby!" Baki ta dan turo ya dan zaro ido yana fadin "Zakiyi bayani ne." Ya mike yace "Tashi muyi sallah ta godiya ga Allah ko?" Ya dauki wata sallayar ya shinfidda ya tada sallah tabi sa, raka'a biyu sukayi, bayan sun gama sukai addu'a juyowa yayi ya matso daf da ita ya daura hannunshi na dama ya dafa goshinta da shi, ya fara furta "Bismillahi! Allahumma inni as'aluka khairaha, wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a'udhubika min sharriha, wa sharri ma jabaltaha alaihi." Yana gamawa ya saki kan nata da murmushi a saman fuskarsa ya ce " *Matar Haidar* tawa, ina miki maraba da shigowa cikin rayuwa ta, wannan rayuwar ta yanzu ta wuce ta baya, sai dai fatan Allah ya sanya mana albarka a cikin ta." Kanta a kasa ta kasa dagowa sam jin ta take wani iri, ji take tamkar mafarki take wai yau itace ta zama matar Yaa Haidar, jin hannun sa tayi a habar ta ya dago kanta suka hada ido, wani murmushi ya sakar mata wanda bata san lokacin da ta maida masa martani ba, ya saki kan nata yace "Tunanin me kike?" Kai ta girgiza yace "Ina zuwa." Ya mike ya fita bai jima ba ya dawo hannun sa rike da plate da cup, ya dauki leda ya karaso ya zauna ya fara bude ledar wanda yana budewa wani kamshi ya bayyana ido ta lumshe take taji cikin ta na kukan yunwa, wani gashin kaza ya zuba a plate din ya dauki madarar da ya shigo da ita ya zuba a cup ya matso da plate din ya dauki tsoka yai wajen bakin ta da shi, kai tayi kasa dashi dan wani nauyin sa taji tana ji, duk da a gida yasha bata abinci a baki amman wannan sai taji wani iri, ya matso jikin ta yana fadin "Haa mana Baby." A hankali ta bude bakin ya saka mata ta hau taunawa sannu a hankali kamar ba zataci a haka ya dinga bata, sai da taji ta koshi ta girgiza masa kai ya bata madarar ta sha sosai sannan ya fara ci, mikewa tayi ta shiga bandaki ta wanke bakin ta, sannan ta fito ta zauna a gefen gado, yana zaune har ya gama ya kwashe kwanukan ya fitar dasu ya dawo ya shiga ya yi wanka ya fito daure da towel da sauri ta fada saman gado tana juya masa baya, yai murmushi ya saka boxer da singlet kadai yayo kan gadon yana fadin "Ke bakya jin zafi ne?" Ya fada yana dago hijab din ta kamkame jiki ta tayi yace "Dashi zaki kwanta?" Kai ta gyada, yace "To tashi muyi magana." Mikewa tayi zauna suna fuskantar juna, hannayen ta ya kamo yace "A duniya ba abinda nake so kamar ke Maryam, yau buri na ya cika kin zama mallaki na, babu abinda ya rage min na buri na kuma sai ganin gudan jini na dake, yau ni zan zama su Abbi dan haka zan miki nasiha kamar su Abbi da Yayan ki, shine kibi mijin ki sau da kafa nasan kinsan menene aure kuma kinsan hakkin miji akan matar sa da hakkin mata akan mijin ta ba sai na tsaya cewa ga hukuncin wanda ya kasa sauke hakki daya a ciki ba, amman zan fada miki mijin ki yana bukatar ki sosai dan haka kece kadai mafitar sa ke zaki cire shi daga halin da yake ciki, kin yadda dani?" Ya tambaya yana murza mata hannu da wani irin salo, kai ta gyada masa ya kara murza hannun nata yace "Har yanzu akwai wata rashin yarda tsakanin mu?" A hankali ta bude baki tace "Babu Yaya ban taba jin zaka cucen ba ban taba jin ban yadda da kai ba, kullum ina daukar ka wani sashe na. Kai ne sirri na." Hannun nata ya dan matse yace "Zuciya ta ta hanani kar in so wata sai ke, kwakwalata bata tuna kowa sai ke, in za a tambayen wa na fi so amsar dai sai ke, rayuwa ta in zan sadaukar ga wata sai ke, soyayyar ki ta zarce lissafi kwakwalwata bata kwatanta kaunar ki, ke kadai nake so da kauna, nafi sonki akan kowa da komai da kaina dan haka ki yadda dani ki cigaba da yadda da aminta dani kinji? Ina kaunar ki." "Inda abinda ya zarce kauna zan baka, inda abinda ya zarce raina zan baka, bani da buri kullum sai na ganni a damar ka ya zamto ina mai kula dakai, soyayya ta kulle idanuna ta sanya bana ganin laifin ka komai kace ina ganin dai dai ne. Bani da kowa bani da komai sai kai, banajin kowa ban ganin komai ko a duhu sai kai, kaine haske na, kaine farin ciki nah, na baka ragamar rayuwa ta na baka yadda ta Yaya." Tana fadar haka ta fada jikin sa tana fashewa da kuka dago ta yayi yana lalashin ta. Tana jin sa a hankali ya fara cire mata hijab har yai nasarar cire mata gaba daya, kwantar da ita yayi ya tashi ya kashe fitilar dakin, ya dawo ya kwanta tare da janyo ta jikin sa, shiru tayi tana jin wani irin fitinenne ƙamshin jikinsa da sanyin d'akin suna ratsata. A hankali ta fara fidda numfashi. Hannunsa yasa ya juyota rigingine, d'an sunkuyowa kanta yayi. Hakan yasa suka d'an fidda numfashi a tare, cikin nutsuwa taji ya manna mata kiss a goshinta, tare dasa tafin hannunsa bisa nata tafin hannun. Cikin wani irin sassanyan numfashi ya cusa kanshi tsakankanin wuyanta da kafaɗarta hancinshi ya manna kan fatar wuyanta, idonshi ya lumshi tare da ƙara shaƙan ƙamshin jikinta. Ita kuwa Maryam wani irin harbawa zuciyarta ya fara can. Aliyu kuwa a hankali ya dawo da kanshi kan fuskarta, 'kasa yayi da bakinshi. Harshensa ya d'an zaro ya manna da tattausan lips 'dinta, lasarsu yayi tare da fidda wani matacce sauti. A haka ya dinga aika mata da wasu salo masu birkita kwakwalwa wanda ya gama hargitsa Maryam gaba daya ta susuce masa shima haka sai da yasan ya gama kashe mata jiki sannan ya fara neman......... "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Wayyoooooooo Allah na Wayyo, Wayyo Abbi, Wayyo Ammi na Wayyo Yaya Alkasim dina, wayyoooooooo Mami Yaa Haidar zai kasheni, Ammi kizo ki ceceni, kice ya barni" Sune abinda kawai take iya fadi, sai kuma ta fara fadin "Wayoo Allah, innalillahi wainna...." Jin yadda take zurma ihu da kiraye kirayene yasa ya manne bakinshi da nata lips ɗinta duka biyu ya haɗe ya fara yi musu wani fitinenne tsotsa tamkar zai tsinkesu ya haɗiyesu, yana yi yana cimma inda ya sa gaba, bai san lokacin da ya saki bakin ta ya fara fadin "Ah ah Yaa Allahu, Yaa Rahman, Yaa Rahim, Alhamdulillah, Yah subahanallah! Subahanallah!! Allahu Akbar." Daga shi har Maryam kuka suke ita kukan azaba da rashin sabo shi kuma kukan ni'ima dan bai taba zaton haka rayuwa aure take ba bai san haka ake ji ba, duk da shima yaji jiki a matsayin sa na saurayin da bai tabayi ba gaba d'aya kafafun sa da cinyoyin sa sunyi tsami, yafi awa uku yana abu daya wanda da kyar ya samu ya sake ta ya fada gefen ta kana ya janyo ta jikin sa ya rumgume ta tare da lumshe idonsa saboda, wani irin fitinenne zazzaɓi mai masifar zafi da suka ƙasusuwan jikin daya rufeshi a take a lokacin ɗaya gaba ɗaya jikinsa karkarwa ya fara. Maryam banda sheshekar kuka babu abinda take, sam ya kasa lallashin ta duk da yana jin kukan har cikin zuciyar sa, a haka bacci ya dauke ta tana mai sauke ajiyar zuciya, shi kuwa zafin zazzabi ya hanasa baccin sam sai surutai yake, yanaji ana kiran sallah amman sam ya kasa tashi sai da kyar ya janye jikin sa ya shiga ya hada ruwa yai wanka tare da gasa jikin sa.``` *Allah ya jikan musulmai Allah yai mana rahma ya yafe mana. Amin* *Antty* [12/4, 17:33] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 74 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono) Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 ```Hannunshi yasa ya fara janye blanket ɗin. Ya bude yana kallon ta ido ya lumshe yana lasar leben sa dan take yaji wata sha'awar ta na kara fizgar shi, ya daura hannu akan ta yana mata tafiyar tsutsa cikin gashin ta, a hankali ta bude ido, tana ganin sa ta tabe baki zatai kuka ya daura hannun sa a kan bakin ta yana zagaye shi yace "Haba Baby yi hakuri tashi kiyi wanka kinji?" Kallon kanta tayi da sauri tasa hannu zata ja blanket din ya rike tace "Yaya ka ban kaya to." Ta fada tana sakar masa kukan shagwa'ba, kanshi ya ɗan kauda kana a hankali ya janye borgon tare da cewa. "Baby kiyi haƙuri ki dena kukan kinji ko bana son jin kukanki." Yana fada ya cicciɓota ya dauke ta, da sauri ta rumtse idanunta tare da cusa kanta cikin ƙirjinsa. Bathroom ya wuce. A hankali ya sauƙeta cikin ruwan ɗumin. Wani irin zillo tayi tare da yarfa hannun da kuma sakin ihu mai sautin rauni. "Wash Allah na Yaya zafi na kone." Cikin sanyi yace. "Sorry kiyi haƙuri zakiji daɗin hakan, yanzu zaki warke". Ina sai zillewa take son yi. Da sauri yasa hannunshin ya danne ta cikin ruwan ta zauna daɓas, hannunta ta fara yarfawa tare da zubda hawaye, bakin bath ɗin ya zauna, kanta ya jawo ya manna da jikinsa, kana yayi shiru yana jin yadda jikinta ke karkarwar tamkar mazari. Wata fitinenneyar zuface ta fara karyo mata tako ina na, jikinta, sai kuma ta fara sauƙe ajiyan zuciya. Sai da ruwan yai sanyi sannan ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye, ya zubar da ruwan ya kara hada wani yana fadin "Zamu ƙara wani ruwan ɗumin kinji." Ƙara tusa kanta tayi jikinsa, tare da manne ƙirjinta da nashi wai bata son yaga breast ɗinta. Wani ruwan ɗumi ya kuma sawa, kana ya zaunar da ita ciki. Sannan a hankali yace. "Aha Gud girl!" Sai da ya hada mata sau uku sannan yai mata wanda ya hada mata wani ruwan yace "Kiyi wankan tsarki bari na dawo." Ya juya ya fita, tai wankan ta tas, kasa fita tayi tana tsaye bakin kofa ya budo kofar, ya karaso yace "Kinyi?" Kai ta gyada kanta a kasa, ya kamo hannun ta dan su fita amman me tana daga ƙafarta, ta runtse ido tare da cije laɓɓanta, kana ta ɗan ware ƙafafuwanta tare dacewa. "Wash" Ido ya ƙurawa yadda take tafiyar. Kanshi ya jinjina sannan a hankali ya karaso ya dauke ta suka fita a gefen gado ya ajiye ta, kaya ya dauko wata riga a wanda ya siyo wanda take tamkar babu ya saka mata yana yi yana kallon ta, hijab ya bata ya mike yajasu sallah Ita kuwa Maryam tana idarwa ta zauna tana sharce hawayenta dake silalowa tana mamakin wasu zantukan Yaa Haidar da abubuwan da yai mata, amman kalle shi yanzu yana abu ko a jikinsa kamar bashi yayi wannan abun ba. Tana shafa addu'a ya juyo ya kalle ta, jikin sa ya janyo ta wanda yaji da zafi zau, rumgune ta yayi yana lallashin ta da kalamai masu dadi da tsada wanda take ya shige zuciyar ta, ta saki komai ta manta duk azabar da ta sha, ya cika ta da soyayyar sa, shi yasan bai da matsala da Maryam tinda daman yasan abarsa yasan lagon ta, yasan ta da raki da son jikin ta, to ta wannan hanyar da yabi ya mantar da ita komai dai, hannun ta daga ta kamo fuskar sa, zafin da taji a jikin sa yasa ta daina kukan shagwabar da take tana fadin "Yaya jikin ka zafi." "Baby na ai naki yafi nawa zafi, yanzu zamu sha magani kinji?" Fuska ta bata hawaye na cika idon ta alamun bata so kenan, ya rumgume ta yana lalashin ta daga haka kuma ya fara romancing nata. Wayar sa ce tai kara ya dago yana duba mai kiran, mikewa yayi yana rakwafowa yace "Ina zuwa Honey!" Ya mata kiss a lips din ta sannan ya juya ya fita bai jima ba ya dawo da ledoji plate yaje ya dauko ya juye musu abincin da yayi order, dankali ne da kwai, sai peppersoup din kayan ciki da gasashen nama, kitchen ya je ya dauko tea da kayan madara yazo ya hada mata, shi ya dinga bata tanaci a hankali a hankali har ta koshi ya bata magani da kyar tana kukan shagwaba ta amsa tasha ya hau shafa bayan ta. Kan gado ya kwantar da ita yaci abinci sannan ya fitar da kayan, kan gadon ya hau wajen ta ya dago ta ya daura a jikin ta yana fadin "Ina kaunar ki Baby, a jiya kin cikan buri na saura guda d'aya wanda shine ki haifa min yara kyawawa kamar ki, ina godiya da kyautar da kikai min na rasa dame zan saka miki, ji nake komai na baki yayi kadan na samu nustuwa da wani irin dadi da ban taba samun sa ba. Na gama gamsu cewa duk duniya, kece sirrina Maryam, Dole ki zamo suturata, kamar yadda nima zan zama suturarki" Ya ƙarashe maganar yana manna bakinshi da nata, lips ɗin ta duka biyu ya ɗan kamo ya tsotsa a hankali, sannan ya sake, kiss ya manna mata a goshi kana ya manna mata a tsakanin wuyanta da kafaɗarta, harshensa ya zaro ya fara lasar wuyanta yana ɗan yin kasa dashi tare dasa hannunsa cikin hijab yana shafa ta a hankali a hankali, cikin sigar shagwaba tace "Yaya bacci!" Hannun sa ya zaro ya zare hiab din ta ya rumgume ta a jikin sa yana jijjiga ta tare da massaging din jikin ta a haka bacci ya dauke ta, ya mike yana kallon ta, ido ya lumshe yana jin yadda son ta da kaunar ta ke kara daduwa a cikin zuciyar sa, a haka shima baccin ya dauke shi. 12:45pm A hankali ya fara bud'e narkakkun idanunsa, ya sauke akan fuskarta, wacce take a saman k'irjinshi a kwance. Hannunsa ya sanye ya zura cikin kasan rigar ta, jin ba zazzabin sai dumi kawai, ido ya lumshe yana mai kokarin kwantar da ita wanda hakan yasa ta bude idon ta wani tsadaddan murmushi ya sakar mata mai kashe dukkan gaban jiki, ya kama hannunta ya manna mata kiss ya saka yatsarta k'arama cikin bakinsa yana tsotsa ya kashe mata ido d'aya. Mik'a tayi had'i da turo kirjin ta wanda kallon kirjin ta kawai yasa sa ya fara jin wani yanayi a jikin sa, dagowa yayi ya kalle ta itama ta dago wanda haduwar idanun su yasa ta lumshe nata idon, murmushi ya saki yace "Menene Baby?" A shagwab'e tace “My Jikina ciwo uhm uhm.!" Ta karasa magana tana sakin kukan shagwaba wanda ta kusan zauta Haidar dan gaba daya tsigar jikin sa sai da ta tashi, wannan yasa ya cafki bakin ta yana bata wani zafaffafen kiss, da kyar ya saki bakin nata ya sauko daga gadon ban daki ya shiga ya hada mata ruwan dumi sannan ya dawo dakin ya same ta lafe akan gadon, batai aune ba taji yai sama da ita ya shiga bathroom, rigar ta ya zare mata tai sauri ta daura hannun ta tana kare kirjin ta, ya saki wani murmushi yana mai taune lips din sa, daukar ta yayi ya saka a cikin ruwan jin dumin ruwan yasa ta lumshe ido, ji tayi ya shiga cikin ruwan tare da hade bayan ta da kirjin ta wanda yasa tsigar jikin ta ta tashi, kansa ya zuro wajen wuyan sa yana daura hannayen sa akan kirjin ta wanda ya ta dan zabura tare sa sauke wata ajiyar zuciya, wata iriyar soyayya ya dinga nuna mata Maryam in ban da numfashi ba abinda take saukewa dan gaba daya Haidar ya saka ta a wani hali da ta kasa gane komai, dan ta gama basa kanta gaba daya bata ji bata gani wanda shi kuma hakan ya bashi damar yin abinda yake so, ita kuwa sai kukan shagwaba take masa wanda yake kara rikatashi da jefa shi a wani halin, daga baya dauko ta yai gaba daya suka dawo daki, sai da suka bata wajen awa kusan d'aya sannan ya sarara mata, Maryam kuwa taji maza ta lafe a jikin sa kawai tana maida nunfashin wuya. Sai da ya ji kwarin jikin sa ya mike ya shiga ya kara hada musu wani ruwan zafin tare suka shiga ya farai nata wanka wanda yana yi yana kara tattabe ta sai da tayi da gaske amman da sai an kara maimaitawa. Da kansa ya shirya ta cikin wasu kananun kaya wanda siket din yake iya cinya sai rigar da iya kar ta cibiya, kallon ta ya tsaya, ta dauki hijab ta saka tana fadin "Allah Yaya ba kyau, kalli agogo uku saura." Murnushi ya saki yai k'asa da kansa, dan hakika yana son Maryam da kaunar ta in ta tashi ne ba zai taba barin ta ba, shiryawa yayi ya jasu sallah bayan sun idar ya dauke ta sukai falo, kayan kallo ya kunna musu ya zauna tare da manna ta da jikinsa, a haka aka kira shi ya fita bai jima ba ya dawo da kayan abincin su, da kan sa ya bata taci suka cigaba da kallon su tana jikin sa ya kanainaye ta hannunsa na yawo sassan jikinta. Haka suka wuni cur yana bata wata irin kulawa tamkar zai maidata cikin cikinsa, itako sai shagwab'a take zuba masa, yana nan nan da ita, Weekend din ba abinda ya dinga sai kula da Maryam wacce zallar shagwaba take masa, komai shi yake mata abinci daga na safe har dare order yake da kayan motsa baki ba inda yake zuwa sai massalaci suna makale da juna cikin kwana biyun nan so, kauna da tausayin junan su ya ninku, shakuwar su ta kara daduwa duk yadda yake bukatar Maryam daurewa yayi dan yasan bai mata ta sauki ba, ta sha wahala sai dai ko ba komai yana rage zafi tinga zai yi romancing nata bata hanasa sam. Amman jikin ta yana fada mata, dan kirji ta in banda zafi na tsosa da matsa da suka sha ba abinda suke mata. Bai so mai da ita ranar Monday ba amman ganin ranar Laraba zasu fara Waec yasa ya fara shirye shiryen kai ta amman a safiyyar ranar ba karamin wahala ya bawa Maryam ba dan dakyar take iya tafiya sai da ya kara gasa ta har yana fadin "Baby ko dai sai gobe zaki tafi?" Kafada ta make tana girgiza kai tace "Yaya Exam kuma kar Ammi tazo tace min zatazo this week." Ba dan yaso ba ya shiryata wajen sha biyu suka koma *MI College* wanda tana tafiya yana mata sannu ji yake kamar ya dauke ta ji yake kamar yai mata tafiyar., ita kuwa cinyoyin ta ne suke mata wani irin ciwo da kyar take takawa. Da su Aisha suka zo dan debar mata kaya sunga soyayya dan yadda Aliyu ya dingai mata itama tana kara shagwabe masa kamar zatai kuka ido da hanci suka saki suna kallon su, da zasu rabu kuwa har da hawaye ji take kamar ta bishi haka ya rumgume ta yana lallashin ta a school compound sosai sukai mamaki dan Yaa Aliyu bai rumgume ta amman sai suka dauki hakan amatsayin lallashin a haka suka rabu da kewar junan su. Tin lokacin wata soyayya ta kara kullewa da shakuwa dan in suna waya jin muryar junan su kadai kan tayar musu da hankali in kuwa yazo principal ya bar musu office yai ta lugwiwitata, wanda irin haka zata ce "Ba kyau ba." Shi kuwa ya kanyi murmushi wani lokacin yace "Ai matata ce." Tin daga lokacin bai jin nauyin kowa zai ce shi matar sa kawai yake so a bashi duk abinda suke so bidi'a ne sam su Mami basa ganewa, a haka suka fara jarabawa ranar da suka fara ranar Ammi tazo daga kallo daya taga Maryam ta sauya ta kalle ta tace "Daughter baki da lafiya ne?" Gabanta ne ya fadi tana tsoron ba dai Ammi ta gane sunyi wani da Ya Haidar ba, kai ta girgiza Ammi tace "Kar kisa damuwa fa akan jarabawar nan zaku ci da izinin Allah." Haka ta dinga bata kwarin gwiwa tatafi. Aliyu bai kwana uku bai zo ba kuma in har yazo daga shi har Maryam sai yanayin su ya canja ganin in har yazo tana kasa karatu tai ta kasala da shiga damuwa yasa ko yazo iyakar su school compound dan baya so yai mata abinda zai takura ta ta kasa sakewa wanda itama a lokacin ba abinda take so sai ta kasance da shi taji dumin jikin sa, taji yana lalube ta. Suna tsaka da exam ta fara samun canji wanda da ta kwanta sai bacci ga yawan tashin zuciya ko tai ta tsurfa da zabar abinda zataci a har suka gama exam ta dawo gida aka fara shirin bikin su.``` Wanda ranar daurin auren su Aliyu ya rasu, ranar da take zaton burin su ya cika zasuje su sha soyayya su kula da juna amman sai gashi Allah ya dauke Aliyu, wanda daga nan kaddarar ta ta fara sai gashi ta bar gida da cikin Aliyu taje tai rayuwa a wani wajen da suka rike ta tamkar 'yar su suka bata duk wani gata da soyayya, suka rike ta da amana ita da danta shin me zataiwa wadan nan mutanen, wanda a karshe basu kyamace ta ba suce basu san d'an waye ba ko a ina tai ciki suka aura mata dansu da suka fiso shin ita dan me zatai butulci. Ta sani tana son Yaa Haidar amman kuma ya zatayi Allah ya dauke shi ya kawo mata wani Yaa Haidar din sai a yanzu ta tuna abinda yake fada mata ko ya tafi wani zai zo ya kula da ita, zata kasance matar Haidar kuma Uwar Haidar. Hawaye ta goge tuna yanzu fa ita matar aure ce, ta sani Yaa Haidar yafi karfin ta kuma bata isa ya sota ba amman tayi alkawarin zama dashi a haka tinda tata kalar kadaddar kenan Allah ya bata ikon cinyewa. Wayar tace tai kara ta dauka tana duba screen din Yaa Haidar ta gani bata dauka har ta tsinke ya sake kira tana gab da tsunkewa takai kunnen ta murya a hankali wacce ta sha kuka tai sallama Aliyu dake kwance ya mike da sauri yana fadin "Me ya samu muryar ki?" "Ba komai." "Fada min gaskiya kuka kikai ko?" Ji tayi zuciyar ta tayi rauni bata san lokacin da kukan ya fito fili ba, kai ya dafe dan a duniya ba abinda ya tsana kamar kukan mace macen ma kuma matar sa. A hankali yace "Is ok bar kukan ki fada min menene? Auren mune bakya so ko? Kinsan na miki alkawari in har bakya so zan sauwake miki sai ki nemi wanda yake sonki kike son sa wanda ya fi cancanta dake." A zuciyar ta ta ce "Ba wanda ya camcanta dani sai kai, dole zan zauna dakai ko dan taimakon taka rayuwar kamar yadda ka taimaki tawa amman matsalar tayaya zan fara bayan baka so na." "Ki bar kukan to." Ya katse mata tunanin da take, shiru tayi yace "Ki cire damuwar auren mu kinji?" Kai ta gyada yace "Alright ina Son dina." Kallon Haidar tayi dake bacci tace "Bacci yake." "Ok shi na kira daman muyi waya tinda bacci yake sai anjima ko?" "A'ah Yaya...." Sai tayi shiru yace "Uhm mrenene?" "Ya aikin?" Ya dan saki murmushi yace "Alhamdulillah." Tai shiru yace "Uhm shikenan?" Kai ta gyada kawai jin shiru yace "To shikenan sai anjima zan kira muyi waya da My Son." "Toh." Ta fada tana kashe wayar. Kwanciyya tayi tana lumshe ido, fuskar Yaa Aliyu ta bayyana kyakyawa mai nutsuwa da kwarjini wanda samun sa sai an tona mai ilimi both arabi and boko shin me zatayi yau in Yaa Haidar ya sake ta wa zai aure ta wanda take so a gida duk wanda zai aure ta sai ta hadu da kalubale wasu baza su ta'ba yadda cewa da aure ta haifi Haidar ba wasu ko sun yadda to tabbas zasu ce taje yawon duniya mafita daya ce shine ta hakura ta zauna da Yaa Haidar, ta sani tana kallon Yaa Haidar a matsayin Yayan ta duk da wasu lokutan takan manta wane irin feeling take ji game da shi, amman ta sani yana daga cikin irin mazan da take so da wadan nan tunanin bacci ya dauke ta. Kiran sallah la'asar ya tashe ta a bacci ta samu Haidar kwance rike da waya a kunne yana fadin "Abbi yaushe zaka zo?" Ta mike ta shiga bandaki taji yana fadin "Abbi, Adda ta tashi yanzu." Kofar bandaki ya kalla yace "Toilet ta shiga" Ya sauka akan gadon yace "Abbi an kiran Sallah zanje nayi Sallah a kusa a Abbin Adda, ka kira anjima bye." Ya ajiye wayar ya fita dai dai fitowar Maryam ta dauki wayar tana fadin "Ko tayaya aka kira ban ji ba." Aliyu da bai kashe wayar ba yana jin ta, ta ajiye ta dauki Hijab ta saka ta tada sallah. * Kwanan su goma Abbi yasa Aliyu da su Ummi suzo dan aje Adamawa dasu gaba daya, har da Abba aka zo da Sitti da Innah da Yaa Farouk, bangaren biyu na gidan da ba kowa wanda sai su Yaa Alkasim sunzo suke sauka anan sai na Yaa Abdullah da bai aure ba anan aka sauke su, sunga kulawa sosai dan ba abinda ba a ajiye musu, tinda suka zo Maryam na wajen Ummi sai shagwaba take zuba mata dan har lokacin bata jin dadi gaba daya ta kasa sakewa ta kasa sabawa da sabuwar rayuwar ta ta yanzu kewar su Ummi ta dingayi dan haka da suka zo tana jikin Ummi, Ammi da Mami kuwa sosai sukaji dadi dan ganin su Ummi kadai ya sanya Maryam sakewa, tinda suka zo bata ga Yaa Aliyu ba kuma ance tare dashi suka zo, ko da yake shi a gidan su Mami ya sauka bangaren Yaa Haidar na da, Yaa Abubakar kuma suna boy quarters. In Ammi taga yadda Maryam take sakewa a cikin su Sitti da su Ummi wani dadi take ji da nutsuwa ashe yar ta a cikin gata take sai taji hankalin ta ya kwanta sam bata da damuwa auren da akai mata ma da taga Yaa Aliyu sosai ta jinjina abin dan Aliyu namijin nunawa sa'a ne bama da Yaa Abubakar ya karai musu bayani waye Aliyu duk sai suka ji sanyi duk da basu san Muhammad ba amman hankalin su yafi kwanciyya da auren ta da Aliyu akan da Muhammad. Dan su Aliyu sun san Maryam sun kuma dauke ta tamkar 'yar cikin su basu nuna kyama ba yau ko Aliyu bai son Maryam ai ba zasu ce a kunce auren ba bare yadda yake son Aliyu ya dauke shi tamkar d'an sa da yadda yai dawainiyya da Maryam ma zai nuna akwai tausayi da shakuwa tsakanin su, wanda so yana farawa ne daga tausayawa juna dan haka sai Ammi ta samu nustuwa a yanzu bata da damuwa sai na ganin farin cikin yar tata kawai dan haka zata kara bata kwarin gwiwa akan ta zauna da mijin ta lafiya duk da tasan Maryam yarinya ce mai hakuri ladabi da biyayya. * Kwance take a jikin Sitti, Ummi na gefen kafar ta tana danna waya sukaji sallamar sa da sauri ta rufe idon ta, su Ummi suka amsa ya shigo ya zauna a gefen Ummi yana gaishe su, Inna tace "Kai dai Aliyu tinda muka zo ban kara ganin ka ba." Kallon ta yayi yace "Ai Inna ke uzuri za a na miki dan wallahi kin gama tsufa kin fara rikicin tsufa." Ummi tai murmushi yace "To Ummi dazu fa na shigo kawai dai ita ce ina jin ta fara daina gane mutane." "Kaniyar ka nace, ai ba wanda ba zan gane a cikin ku ba kiji fa Hadiza ina tsufan da zan kasa gane Ali ko na kasa gane kowa ai na gane kai, yaron da ni na raine shi a hannu na ya girma." Maryam juyi tayi tana fuskantar Aliyu kamar mai bacci amman idon ta biyu ta kasan idon ta take kallon sa sanye yake da milk kalar boyel wanda tana gano singlet din sa. Kansa sanye da brown kalar hula ya kara kyau da haske kamshin sa ya cika dakin, yana lura da ita yadda gashin idon ta ke motsawa alamar idon ta biyu, kafar sa ya mike yana fadin "To shikenan Hajiya Inna." Sitti tana dariya tace "Ai gwara tai maka dai." "Ni dai na tuba ban shirya fada dake ba." Ya kalli Ummi yace "Ina Haidar ne?" "Yanzu ya fita fa kila yayi can cikin gida yazo yaga yan uwa ai ba zama kasan Haidar da son mutane." Kai ya gyada ya mike yana kallon Maryam dake kwance jikin Sitti yace "Ita kuwa wannan baccin la'asar Ummi, kuma dan ta karya min mata gaskiya ta daina kwanciyya a jikin Sitti." Baki ta dan turo, ya dan yi murmushi ya juya ya nufi kofa ta bude ido tana binsa da kallo yana kaiwa kofa ya juyo ido hudu sukai ya kanne mata ido daya yai, tai saurin rufe idon ta ya saki murmushi kawai ya fice. *Allah ka yafe mana kai mana rahma, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/5, 13:30] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 75 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Washe gari da daddare wajen karfe tara ta fito daga bangaren Ammi zata wajen Ummi, tinda ya fito daga compound ya hango ta wannan yasa ya koma ciki da sauri ya buya a jikin flowers din dake wajen, ta karaso wajen ta shiga, hannu yasa ya janyo ta jikin sa baki ta bude zatai ihu yai saurin daura tafin hannun sa akan bakin ta yana fadin "Ke kar ki taran mutane." Ido ta zaro tana kallon sa kirjin ta na dukan uku uku, ta marairaice ta zame bakin ta tace "To Yaya ba tsoratar dani kayi ba." Ya dan harare ta yace "Shine zaki min ihu to." Baki ta dan turo, yana kallon ta yace "Wato ke yanzu baki iya gaisuwa ba ko? In kinga mutane ma sai ki fara baccin karya ko?" Baki ta dan turo ta juya tace "To ni yaushe na ganka tinda kuka zo ma ko nema na bakai ba sai ta yaron ka kake." Tai magana hawaye na taruwa a idon ta ya zagayo gaban ta yana kallon yadda hawayen ya taru a idon ta, hannun ta ya kama suka karasa wani waje da yake da dakali suka zauna yace "Yanzu ni dake waye me laifi?" Da hannu ta nuna sa, yace "To ni menene laifin nawa?" "Gashi nan baka nemana ko son ganina bakayi ina ta murna zaku zo amman shine kai baka neman na." Tai maganar tana sunkuyar da kanta dan bata san yadda akai ta fada masa ba kawai abin na ranta ne bata ji dadi ba ace wai yazo kwana biyu amman basu hadu ba bai kuma damu da neman ta ba, sai Haidar tare suke yini gaba daya fa sai jiyan nan ta ganshi ai dai ko kiranta yayi ashe saboda Haidar yake kiranta. "To shikenan am sorry nayi laifi amman ke meyasa bazaki neman ba." Ido ta dan zaro tace "Mata ita ke zuwa wajen namiji?" "Menene a ciki, naga yanzu kin zama matata." Kai tayi kasa dashi yace "Ko dan ni ba a so na, ai da Muhammad ne da zaki nemesa ko a waya ne, amman ni fada min tin da kuka zo Kano kin neman in bani na neme ki ba." Baki ta dan turo tace "Uhmm kai ma ai Haidar kake nema." "Ohk naji na nemi Haidar amman ai ta wajen ki ko? Kuma sai mun gaisa in naso zan kira Aunty Nusy ta kira min shi ko Alkasim." "Uhmm uhmm to kayi hakuri ni bansan me zan kira nace ba." "Oh har gaisawa." "Uhm uhmm to naji kayi hakuri." Kamo hannun ta yayi ya juyo da ita yace "To na hakura, yanzu gani kalle ni shikenan gani." Ta dago ta dan kalle sa sai ta dauke kan ta, yace "Oh har kin gama kallon nawa." Mikewa tayi tace "Uhmm ni wajen Sitti zani sai da safe." Ta juya zata tafi ya kamo hannun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kamshin turaren su na tashi, dagowa yai yana kallon ta, itama shi take kalla, Yaa Farouk ne ya shigo kamar ance ya juyo ya gansu baki ya saki yana kallon love wayar sa ya zaro ya fara snapping nasu picture hasken flash din shi yasa suka juyo a tare da sauri Aliyu ya sake ta yana hade rai ya kalli Farouk yace "Menene haka?" "Alhaji Yaa Hamma tuba nake soyayya na gani kuma abun yai kyau shiyasa na tsaya koya." Ya fada yana murmushi Haidar ya karasa yana kama kunnen sa yace "Gidan ku." Da sauri Maryam ta bar wajen, Farouk ya hau ihu yana fadin "Tuba nake Yaya, Dr Hamma." Ya rankwashe shi ya amshi wayar yana kallon screem din picture din yayi kyau sosai, sun shagala kallon junan su ba karamin kyau sukai da dacewa da juna ba. Ya mika masa wayar yace "Tafi ka ban waje." "Allah kara girma da lafiya Yaya na." Farouk ya fada yana dariya dan murmushi Haidar yai ya juyo wajen Maryam sai dai me? Ba kowa a wajen dube dube ya fara sai ya saki murmushi kenan ta gudu, fita yayi ya tafi kawai. Tana shiga ta zauna a gefen Sitti tana fadin "Bakuyi bacci ba?" "Bamuyi ba daga ina kke?" Yaa Farouk da ya shigo yace "Daga soyayya take Sitti." Maryam ta dago tana marairacewa tace "Kai Yaa Farouk soyayya kuma dawa?" "Da mijin ki Dr Hamma na." Ido ta zaro tace "A ina ka gamu tare." Wayar sa ya nunowa Sitti Maryam ta mike da sauri ta warce wayar tana fadin "Sharri zai mana Sitti." Sitti na murmushi tace "Ai Faruku bashi da dama." "Sitti menene kuma Faruku ko dadi babu Farouk ake cewa fa." "Dan nace Faruku da bance Umaru ba." Daman ke da Inna haka kuke kuyi ta batawa mutane suna." Inna dake gyangyadi ta bude ido tace "Me nayi ake kira na." Juyawa yayi yace "Ni sai da safe." Maryam ta mike tace 'Nima bari na tafi Yaya Faruku tsayani." Juyowa yayi ya harare ta ta sunne kai tana fadin "Sorry Yaya na." Tare suka fita ta shiga sashen su shi kuma ya shiga bangaren Yaa Abdullah dan tare suke. Kwanan su uku suka wuce Adamawa, Shigar yamma sukai nan aka hau tarbar su dan sun san da zuwan nasu Malam kuwa da yaga Maryam bakin sa yaki rufuwa, haka da yaga Haidar ya kamashi yana fadin "Masha Allah, kamar su daya kuwa da mahaifin nasa, Allah masa rahma." Masauki aka basu, dan kowa yaje ya huta aka cika su da kayan ci da sha kala kala, Maryam kuwa daman sakin shan fura ai ita tai ta dirka Haidar ma ita ya sha sai gashin nama da suka ci amman sunki cin abinci shi da Maryam sam. * Washe gari da safe, Malam ya kira meeting, domin kowa yana gidan Abbi da Yaa Usman ne kadai ba a garin ba to shima bayan su Abbi sunzo ya iso da iyalan sa. Bayan kowa ya hallara ne, Malam yayi godiya da Allah da ya dawo da Maryam lafiya tare da godiya ga su Ummi akan rikon da sukai wa Maryam. A take ya umarci Maryam da ta basu labarin abunda ya faru da ita, da asalin cikin waye, Malam ya kalli Maryam dan ta fara, tai kasa da kai murya a sanyaye ta fadi komai da ta sani bayan ta gama ta mika masa wata jakar ta inda a ciki ne sadakin ta yake na sarkar gold din da Aliyu ya bayar da marriage certificate tare da wayar da akai vedion komai. Malam ya dauka ya bawa Yaa Alkasim ya duba komai ya kunna wayar tare da nuna musu vedion wanda Malam yasa akai connecting nasa da TV dake dakin, wanda kowa yaga abinda akai kamar a lokacin a kai, wanda duk jikin mutanen dakin yai sanyi, Mami da Maryam kuwa kuka suke dan ganin Aliyu a vedion sai ya dawo musu da rasuwar sa sabuwa ganin sa yana motsi da murmushi da magana. Bayan an gama Malam ya dago ya kalli yan dakin yace "Alhamdulillah duk da Muhammad yai min bayanin komai akan auren sirrin dasu Maryam sukai nasa ta bayyana komai saboda ku sani kuma ku tabbatar Maryam ba zina tayi ba da aure ta haifi yaron ta wanda ga shaida nan, Ahmad abokin Haidar ya kai Muhammad har wajen malamin kan Maryam tazo da wadan nan shaidu, dan haka ba abinda zamuce sai godiya ga Allah da ya tsare mana zuria daga aikata zina, sai dai akwai jan hankalin da zanyi ga kowa na nan wajen, wannan kaddara ce ga Maryam ya tashi jarabtar ta duk da tayi aure da Aliyu amman kasancewar bata bawa iyayen nata damar aurar da ita ba shiyasa bata samu abinda take so ba, kuma Allah ya nuna isharar sa, dan da Aliyu bai son ta bayan ya same ta zai iya watsi da ita amman da yake ba abin Allah wadai sukai ba sai soyayya ce ta dadu, to kunga yadda karshen su ya kasance duk da ba su sa'bawa Allah ba amman sa'bawa iyaye da rashin sanin su shine silar barin ta gida da shiga wata rayuwa wanda 'kaddarar auren Aliyu ita ce zan ce ta sa ta bar gida, jan hankalin da zanyi shine mu kasance masu bawa iyayen mu mahimmanci a komai, yau da Maryam da Aliyu sun sanar da iyaye akai musu aure da kan rasuwar Aliyu sun jima da zama a inuwa daya wacce ba zasu na jin shakar komai ba, haka nan da Muhammad ba zai fushi ya kori Maryam ba, amman da yake Allah ya k'addarta haka sai mu gode masa, amman ku sani ba kowa ne karshen sa zai zo irin nata ba naka zai iya fin nata in har kace zakai koyi da nata, kamar lokacin da ta bar gida zata iya cin karo da mutanen banza ko a 'ki taimaka mata shaidan yasa ta fada mummunar hanya amman Allah sai ya takaita wanda kila dan basu bi son zuciya wajen sa'ba masa ba ya hada ta da wadan nan bayin Allah to mu kiyaye shi Aliyu Allah masa rahma yasa ya huta. To kunga barin ta gida ta samu kalubale da yawa wanda har auren ta aka fasa wanda ba abinda yafi wannan tashin hankali amman sai gashi wadan nan bayin Allah suka hada auren 'dansu da ita ba abinda zamuce sai godiya, Allah ya saka muku da gidan Allah, Maryam ke kuma Allah ya miki Albarka ya kiyaye gaba rayuwar Maryam ta zama izina garemu, Haidar ya rasu wani ya dawo ya maye gurbin sa a matsayin mijin ta Allah ya basu zaman lafiya ya raya Haidar karami yai muku albarka." Duk dakin jikin su yai sanyi dan haka gaba daya suka hada baki wajen fadin "Amin!" Haka Malam ya kara musu nasiha mai ratsa jiki akan tsoron Allah da illar sa'bawa iyaye wanda su Maryam rashin sanar da iyaye ne kawai sukayi amman Allah ya nuna musu wanna isharar to wannan izna ce ga yan baya in tata tai kyau to ta wani ba dole ne tai kyan da tata tayi ba. Bayan komai ya lafa ne aka yi liyafa anan babban falon Malam inda akaci aka sha anyi yanka raguna kaji da abubuwa sosai, suna tsaka da liyafa, Ahmad ya shigo tare da jagorancin d'aya daga cikin almajiran Malam, Yaa Alkasim ne ya mike suka karaso ya zauna, bayan an gama yace "Ina Maryam din ne?" Ciki Yaa Alkasim ya shiga bai jima ba sai gashi ya dawo dauke da Haidar, Ahmad na ganin Haidar sai da gaban sa ya fadi ya amshi yaron ya rumgume hawaye na zubowa a idon sa yace "Masha Allah, burin Aliyu ya cika ya sunan ka boy?" "Haidar!" Haidar ya bashi amsa ya kara rumgume shi yace "Masha Allah." Hijab ne sanye a jikin ta, ta fito daidai lokacin da Ahmad ya d'ago kansa. Suna hada ido, idonta ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai. Ya kura mata ido yana kallonta Maryam ta dad'a kyau ta zama cikakkiyar mace ba kamar shekarun baya ba. Ta karaso yace "Maryam kece haka?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. Ya dada zama cikakken mutum, a gefen Yaa Alkasim ta tsaya ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye, bayan sun gaisa tace "Yaa Ahmad ai bazan ganeka ba" Ya dan saki murmushi dan wani dadi yake ji, ji yake kamar ya rumgume ta dan farin ciki da dadi yau Maryam ta dawo gida cikin iyalan ta ga yaron su burin sa kenan ya kusa ya cika. Haidar dake hannun sa ya hango Aliyu yace "Adda kinga Abbi na." Gaba daya suka waiga suka ga Aliyu tsaye yana kallon su, suna hada ido da Maryam ya hade rai ya juya ya bar wajen, Haidar ya hau kwada masa kira yana fadin "Abbi Abbi." Juyowa yayi Ahmad ya sauke shi ya tafi a guje yaje yace "Abbi ina zaka?" "Yanzu zan dawo jeka maza." Ya juya ya koma wajen su Maryam yace "Abbi unguwa zai je Adda?" Ahmad yace "Boy kasanni?" Kai ya girgiza ya rumgume yaron ya kara yana jin wani son sa da kaunar sa na dada shigar sa burin sa kawai ya auri Maryam su kula da dansu. Ahmad yace "Nima Abbin ka ne." Dagowa Haidar yayi ya kalli Maryam yace "Adda ni Abbi na uku ne?" Ahmad yace "Kana da Abbi da yawa." Ya zaro wayar sa yace "Kasan wannan?" Ya nuna masa picture din Aliyu, amsa yayi yana murmushi yace "Adda ta nuna min tace shine Abbi na na farko, kuma Abbi muna kama ko?" Ya jefa tambayar ga Ahmad. Ahmad ya gyada kai yace "Sosai ma to kaga Abbin naka da yawa ga Uncle Alkasim ga Uncle Muhammad da yawa fa." Yai dariya yace "Yeee ina son ku dukka Abbi." Ahmad ya rumgume shi yace "Muma muna son ka Haidar. Allah maka albarka." Ya amsa da amin. A haka suka rabu Haidar na wajen sa daga ya kalle sa sai ya rumgume sa. Kwanan sa daya ya tafi gida sanar da labarin ganin Maryam, wanda Maryam tin lokacin ko sun hadu da Aliyu sai dai hade fuska ko gashe shi tayi sai ya gadama yake amsawa duk ta damu. Aliyu kuwa sosai ya saba da su Inna da Hajja kakkanin Maryam dan zasu zauna su sha hira wani lokacin har dan tsokanar su yake bama in su Sitti na nan yai ta fama wannan yasa suke son sa sosai. * Kwance take a kan gadon Inna mahaifiyar Abbin ta wato takwarar ta, sallamar sa ta jiyo ido ta lumshe dan tayi kewar sa na kwana biyun nan ba magana ba dan sakin fuska sam. "Mai gidan." Innar Abbi ta fada ya zauna yana fadin "Yauwah Uwar gida na furar nan nazo na sha kan mu fita zaga gari." Inna ta mike tana fadin "Ai gata cikin daki bari na kawo maka." Ta shiga ta dauko ta kalli Maryam da tai saurin rufe ido, ajiye masa tayi ya fara sha yana santi hadi da mata hira, zaune Maryam ta tashi tana mamakin anya kuwa Yaa Haidar ne a falon Inna, tabbas muryar sa ce amman kuma har yaushe ya saba da Innar da suke hira haka, mutumin da magana wahala take masa, mikewa tayi ta nufi kofa ta tsaya a gefen labule tana leken sa, dago kan da zai ya hango ta kai ya dauke dan har yanzu bai huce ba ganin tan da yayi da Ahmad tana tai masa murmushi. Haka ya gama sha ya mike yace "Gaskiya za aje dake Uwar gida zan zo na sha ta yamma godiya nake." Sukai sallama, yana fita ta fito ta zo ta zauna a gefen Inna tace "Oh daman ba baccin kike ba takwara" Ido ta mutsaka tace "Hirar kuce ta tashen." "Oh mai gidan naki ne ai, yaron yana da hankali da ladabi ya dauke mu tamkar nasa kakanin ke dai kina dace Maryam dan Allah kiyiwa yaron nan biyayya ko dan yadda yake son yaran ki kinji." Kai kawai ta gyada tana mamakin Aliyu. *Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe Amin.* *Antty* [12/5, 13:30] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 76 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ana gobe zasu tafi Malam ya kirata a parlorn sa, ta shiga kan ta a kasa zama tayi daga gefen, dagowar da zatai taga Aliyu zaune a kusa da ita, kai ya dauke ta gaishe da Malam ya amsa sannan ta gaishe da Aliyu ya amsa ba yabo ba fallasa, ita ta rasa saboda me yake mata haka kwanan nan ko dan yaga ta damu da shariyar da yake mata ne, kai ta dauke kawai. Malam ne ya fara magana wanda duk nasiha ce yake musu mai shiga jiki, daga nan kuma ya fara jan su da hira ita dai shiru tayi amman tana jin yadda suke ta hira da Aliyu sai kace wanda suka jima da sanin juna. Suna zaune taji sallamar Haidar karami ta dago tana kallon kofa shima yana shigowa ita ya fara arba da ita dan yau kwata kwata bai ganta ba dan daga wannan ya dire wannan zai dauke shi kuma akwai sa da son mutane ganin sa cikin yan uwa yasa ya sake. A guje ya fada jikin ta yana murnar ganin ta, ta rungume shi tana mai jin wani iri, dan Yaa Haidar ne kadai ya fado mata da ace yana raye da komai bai faru ba da ta ina Yaa Aliyu zai na bata mata rai ta ina ma zata san shi bare har ya share ta taji haushi. Yana lura da yanayin ta duk sai yaji ba dadi, kai tayi kasa dashi tace "Malam bari naje na kwana sai da safe." "Allah tashe mu lafiya, Allah muku albarka." Ta mike ta fita dauke da Haidar da ya rumgume ta, da kallo ya bisu yana mai jin kamar yabisu ya lallashe ta sai dai kuma wata zuciyar tace ya barta. Tana shiga ta samu kakanin nata gaba daya dasu Inna da Sitti zama sukai Haidar ya lafe a jikin ta dan ya gaji bacci yake ji. Hankalin su suka dawo dashi kansu, ganin yanayin ta duk yasa sukaji ba dadi, nan su Inna suka hau lallashin ta da mata nasiha da jan kunne, kafin daga bisni suka 'buge da hira, wajen tara da rabi suka shige daki ita da Haidar suka kwanta. * Washe gari wajen karfe 10am suka kammala shirinsu gaba dayansu, Malam dasu Inna har bakin mota suka rako su Abbi, Maryam har da hawayen ta dan sati dayan da sukai taji dadin garin taga gata da kulawa Haidar karami ma da Abbin sa sunji dadin garin sosai ba wanda yaso ya bar garin a lokacin, haka Malam ya loda kayan abinci da amfanin gona dasu nono, kaji, zabi, kwai akan a bisu Ummi dashi wanda daga nan kayan aka sa su tafi can Abuja su Ummi saje su tadda shi dan sai sunje Kano kafin su wuce Abujan. Ranar da suka iso a ranar Yaa Ahmad ya sauka a garin Kano shima, da dare suna zaune a falo ita da Ammi ya aika cewa ace Ahmad ne yazo. Ammi tace "Allah Sarki Ahmad gaskiya ya rike alkawari kinsan baya wata bai zo ba duk da kina ganin ba a garin nan yake ba kullum yana cigiyar ki yau kun dawo ma ya kasa zaune bare tsaye, shi ya fara warware mana komai akan alamari nan. Allah ya saka masa da alheri dai." Maryam ta amsa da amin tana daukar hijab din ta, ta saka, sallamar Ahmad suka jiyo suka amsa ya shigo cike da ladabi ya gaishe da Ammi ta amsa fuska a sake. Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma daki, Maryam ta durkusa ta gaishe shi ya amsa yai mata ya hakurin Aliyu, wanda har hawaye ya kawo a cikin idon ta, cikin lallashi yace "Kiyi hakuri haka rayuwa tayi damu ban tashi sanin rasuwar Aliyu ba sai bayan wata kusan uku, a lokacin naji mutuwar na shiga damuwa da tashin hankali wanda na rasa yaya zanyi dana zo shine Alkasim yake fada min bakya ma gida ga abinda ya faru, ni na fara sanar dasu cewa da aure tsakanin ki da Aliyu na wata uku, ni na dauki Abbi na kai shi wajen malamin da ya daura auren anan aka kara bazama neman ki sai dai Allah bai nufa za a same ki ba sai yanzu, naji dadi da farin ciki da aka ce an ganki." Kanta a kasa tana wasa da yatsun ta, ta dago tace "Nagode Yaa Ahmad Allah saka da alheri." "Ba komai ai an zama daya." Shiru sukai can yace, "Kinsan ni da Aliyu abokai ne, wanda dagani har shi bama boyewa juna sirri dan ni na karfafa masa gwiwar yin auren ku, to Maryam bayan rasuwar Aliyu sai na yanke shawarar akan ko yaushe kika dawo ina son ki zan aure ki dan mu rike amanar yaron da kika haifa ni nai alkawarin zan rike shi tamkar d'an ciki na." A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya "Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Aliyu bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki." Mikewa tayi tana girgiza kai, dai dai shigowar Yaa Aliyu, wanda bata san dashi ba, daki kawai ta shige ta bar Ahmad wanda ya bita da kallo, yasan haka zata faru dan yasan kan Maryam taso wani abune mai wuya dan soyayyar su tsakanin ta da aliyu ta wuce tunanin mai tunani. Mikewa yayi ya zura hannu a aljihu ya bi hanyar da tayi da kallo ya girgiza kai kawai ya juya zai fita yaga Aliyu tsaye fuska ba yabo ba fallasa hannu ya mika masa sukai musabaha ya fice. Ran Aliyu in yayi dubu ya baci, hanyar da ta shiga yabi duk da bai san dakin waye ba amman tabbas sai yaje. Akan gado ya same ta kwance tana kuka ya shigo ya karasa ya dago ta a fuskace ta kusan yin baya zata fadi ta dafe bango ido ta zaro tana kallon sa fuskar nan a hade ransa a bace yace "Kina kuka akan aure na ko? Saboda an aura miki wanda bakya so ga wani yazo da zaki iya soyayya da shi ko? To ki sani da aure akan ki, kome zaki ki bari na fara sauwake miki, na fada miki in har bakya so na, bakya son zama dani zan miki abinda kike so amman a yanzu ba zan iya ba sai dai ke ki fadawa iyayen mu cewa bakya so na ni kuma nai miki alkawarin zan tsaya miki har sai kin auri wanda kike so, amman ba haka ne zai sa kina kula wasu da aure na akan ki ba. Ina da kishi akan abun da yake nawa dan haka kada ki kara, kwanaki kinyi dan banyi magana ba shiyasa kika karayi ko to bana so bana so na fada miki. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai a kanki." Kai ta dafe dan wani irin sara mata yake, ta dago da niyyar magana ya juya a fusace ya bar dakin. Kan gado ta fad'a tana sakin wani irin kuka. Tun bayan rasuwar Aliyu ta cire rai da sake samun soyayyar wani d'a namiji sai dai kaddarar ta na farko da ya mantar da ita komai wanda ta so Muhammad a yanzu kuma zuciyar ta ta fara rinjayar ta ga Yaa Haidar amman kuma meyasa yake haka? Ta sani ko giyar wake ta sha ba zata ta'ba tinkarar iyayen su da cewar bata son sa ba ko da bata son sa zata zauna dashi a haka balle zuciyar ta, taje ta fada tarkon sonsa, wanda da tana da iko da ta hane ta. Meyasa yaki ya tsaya yaji me yake faruwa zai zo ya fara fad'a. "Kishin ki yake." Zuciyar ta, ta fada mata, kai ta hau girgizawa fana fadin "Ana kishin abinda ake so ne." "Kika sani ko son ki yake." Wata zuciyar ta bata amsa. Kai ta hau girgizawa tace "Never i know matar sa kawai yake so nice Allah ya dauran son sa wanda nasan wahala kawai zan sha wanda nasan wannan wata sabuwar jarabawar ce rayuwa da wanda baya son ka." Da wadan nan tunanin bacci barawo ya dauke ta bayan ta sha kukan ta ta gama. Aliyu ma daki ya koma ya fada saman gadon sa yana dafe kan sa da yaji yana masa ciwo saboda fadan da yaje yayi, ya rasa meyasa yake jin kishin ta meyasa bai son kowa ya tunkare ta. "Saboda igiyar dake kan ta." Kai ya girgiza yana fadin "A da da ba igiyar tawa fa?" Ido ya lumshe take fuskar ta ta bayyana a cikin idon sa, wanda yana kallon fuskar ta wacce yanzu ya baro ta take cike da rudani, tsaki ya saki yana fadin "Allah kai ka dauran son wannan yarinyar Allah ka dauran dangana da hakuri akan lamuran ta, Allah kada kasa ta wahal dani, Allah kada kasa ta amshi shawara ta wajen zuwa ga iyayen mu tace bata so na da yaya zanyi da alkawarin da nai mata." Haka ya dinga juyi da tunanin mafita da kyar bacci ya dauke shi cike da tunanin Matar sa. * Kwana ta biyu rabon da ta ganshi shi wanda har komawa sashen su Inna tayi amman ina ba Aliyu ta shiga damuwa gashi in ta tafi kamar ta kira sa sai ta fasa, ganin bata da mafita yasa ta hana Haidar fita kwana d'aya tal ba inda yaje wanda abun ya damu Aliyu dan daman tare suke yini da Haidar shine dauke shi su fita yau da bai zo ba kadai duk ya damu haka ya shigo gidan da rabon sa dashi tinda ya shiga ya mata fada sai yau, bangaren su Inna yaje babu shi ba alamar sa ya jima har ya tambaya suka ce bai shigo ba haka yaje bangaren Ammi ita kadai a falo suka zauna suna dan ta'ba hira a siyasance yake tambayar Ammi Haidar danya fara tunanin ko bai da lafiya amman batace komai ba dan ita bata san yau bai fitan ba. Maryam kuwa ta rike shi a daki ta cika masa gaba da kayan wasa dana ciye-ciye. Har dare ba Haidar hankalin Aliyu ya tashi, yana son ya kira Maryam kuma baya so duk da ya damu da rashin ganin ta koyaya ne. Fara neman layin ta yayi tana shiga ba a jima ba aka dauka yanajin tana sallama yai shiru kawai, ganin ko baya jin tane, ta kashe, kara kira yayi ya kara shiru bayan ta kashe yai murmushi ya fara rubuta mata sako. Gaban ta ne ya fadi lokacin da taga sakon _Idan Haidar baiyi bacci ba ki hadani da shi, ba muryar ki na kira na ji ba ai kin sani amman kin tsaya sai Hello kike._ Wani dan murmushi ne ya subuce mata, sai ta dan saki tsaki tana cije lebe, baya minti uku sai ga kiran nasa nan, Haidar ta bawa tace "Ga Abbi nan." Ta shiga bandaki tai wanka har ta fito waya suke, shirin kwanciyya tayi ta zo ta amshi wayar duk da basu gama ba ta saka a kunnen ta dan murya sa kawai take so taji ko ta samu nutsuwa. "Hello, Hello, Haidar." Ya fada cikin sanyin muryar sa mai dadin sauraro, ido a lumshe tana sauke wata ajiyar zuciya da tasa ya gane wayar na wajen ko wanene, ido ya lumshe ya bude a hankali. murmushi yayi kamar tana kallonsa kawai ya kashe wayar. Shi kadai yace "Me hakan yake nufi?" Zuciyar sa tace "Itama tana son ka." Kai ya girgiza yace "Anya kuwa kar na yaudari kai na. Amman zan gwada na gani." Shi kadai yake maganar murmushi dauke akan fuskar sa. * Ahmad zata yayi Maryam ta'ki tsayawa ne dan ya kawo mata maganar soyayya wanda shi shaidane in aka ce Maryam zata amshi wani bayan Aliyu zai ce karya ne amman ba komai zai cigaba shi ko bata so shi ba ta yadda suyi aure wanda a sannu zai koya mata sonsa. Ya sani Maryam zata iya cewa ba zata kara aure ba wanda shi aure wani babban jigo ne a rayuwa, auren shine mutuncin ta shi ba cewa yayi ta daina son Aliyu ko ta cire shi a rai ba in yai mata haka ma bai mata adalci ba sam, ya sani a yanzu ba zata gane me yake nufi ba amman zai bata lokaci tai tunani zai je ya samu iyayen sa da suke so yai aure cewar su fara shiri domin matar sa ta dawo. Da wannan ya tafi yana mai kara son Maryam na riko da alkawari da har bayan ran Aliyu ta kasa bawa wani soyayyar ta. * Kwance take a daki Haidar kwance akan ta sai damun ta yake dan bata cikin mood din ta, ganin taki ta kula sa yasa ya mike ya farai mata kuka ta mike tace "Wai menene Habiby?" "Adda ki taso mu fita." "Dan Allah ka kyale ni tashi ni kaje ai duk ni na janyo da na hanaka fita." Kuka ya fara yana dira kafa shi lallai sai tare zasu fita, ganin yana kuka yasa ta mike dan su fito ko wajen Ammi ne daga nan ta samu ya tafi wajen su Sitti, ta mike ya sauka yace "Adda ki goyani." Kallon sa tayi tace "Ai ka wuce goyo Habibty sai dai kai ka goyani." "Yes Adda zo in goya ki." Ya juya mata baya, daukar sa tayi tana fadin "Tayaya zaka goyanin." Yana dariya yace "Adda zan iya fa." Suka shiga falon tana murmushi tace "Iyye yarona jarumi zai goya Addar sa." Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan sa. Shadda ce ruwan madara a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a lokacin ba, Haidar ya dire a jikin ta ya karasa wajen Yaa Aliyu yana fadin "Oyoyo Abbi." Ya rumgume shi yace "My son ya kake?" Ammi dake zaune sai murmushi take, Maryam ta zauna a gefen Ammi kan ta a kasa tana satar kallon sa tace "Ina yini?" "Lafiya lou ya kuke?" "Alhamdulillah." Ta daura kan ta a kafadar Ammi, Ammi ta mike ta bar wajen ya rage daga Aliyu sai ita da Haidar. Gaba daya Aliyu ya bawa Haidar hankalin sa sai hira suke tana zaune tana kallon su, can sai ga Aisha nan tai sallama mikewa tayi tana murmushi hadi da fadin "Maman biyu." Ta karaso sai ga Rukayya a bayan ta, a guje suka karasa suka rumgume juna, wanda Aliyu da Yaa Alkasim suka tsaya kallon su, daga murna kuma sai kuka aka rasa mai lallashin kowa dan har Aishan ma kuka take. Yaa Aliyu ne yai karfin halin fadin "To menene abun kuka, komai da ya faru ga bawa kaddarar sa ce ku godewa Allah ku bar kukan nan." Yai maganar cikin sanyin murya wanda gaba dayan su sukai dif, sai hawaye zubowa yace "Kukan ba abinda zai kara muku bashi da amfani kunji." Kai duk suka gyada, Yaa Alkasim ya shigo yana fadin "Ai basu da aiki sai kuka." Ya zauna suna dada gaisawa da Yaa Aliyu. Rukayya ta gaishe da Yaa Aliyu, Aisha ma haka sannan suka mike suka shige dakin Maryam. Acan aka bude babin hira wani ai kuka wani jimami wani kuma ai dariya har akai magariba sai kiran sallah sukaji duk suka mike sukai sallah. Washe gari Da dare suna daki suna hira Yaa Ahmad ya kira wayar ta bayan ta dauka yace "Ina waje kizo muyi wata magana." "Yaa......" "Ki fito kawai." Ya fada yana katse ta ba yadda zatai ta mike fuska cike da damuwa kamar zatai kuka. Rukky tace "Ya dai?" "Yaa Ahmad ne." "Abokin Yaa Haidar ko? Daman yana nan?" "Taso muje." "Ku barni ni kadai nima bari naje wajen su Ummi." Aisha ta mike da katon cikin ta, Maryam tace "Sannu maman biyu." Sukai dariya, Aisha tace "Zan rama ne." Suka fice Aisha ta gaisa da Yaa Ahmad, Maryam da Rukky suka fito, kanta a kasa ta karaso Rukky ta gaishe dashi ya amsa yana fadin "Rukky kwana yawa ko a bikin Aisha bamu hadu ba duk kun girma wallahi." Tana murmushi tace "Kaji ka Yaa Ahmad kai ma ai ka girman." Ido ya zaro yana kallom Maryam yace "Kina jin ta ko? Wai na girma da yaya nake?" Duk sukai dariya, a dai dai wannan lokacin Yaa Aliyu ya shigo gidan da motar Yaa Alkasim, Haidar na gefen sa, yana shigowa ya hango Maryam da Yaa Ahmad suna dariya ransa in yai dubu ya baci, tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa. Maryam ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai, meyasa ba zata gujewa bacin ransa ba, dan me bayan a yanzu bata da wandan zata farantawa bayan shi, dama bata fito ba abinda take ta tunani kenan. Amman kuma dole ta fito ko dan ta sanar da Yaa Ahmad tana da aure ko ya hakura ya kyale ta. Daga Rukky har Ahmad sun kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Maryam haka ma Rukky dan taga gaba daya hankalin Maryam na wajen. ****** *Allah mana rahma ya jikan mu. Amin* *Antty* [12/6, 13:31] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 77 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ido ya lumshe zuciyar sa kamar zata fito dan bacin rai, baya so ya fito yayi abinda ba dai dai ba shiyasa ya fara ambaton Allah a cikin zuciyar sa, a hankali yaji bacin ran ya ragu sannan ya bude kofar ya sanyo kafar sa, farar kafar sa dake cikin brown kalar takalmin ce ta fara bayyana sannan ya fito gaba dayan sa, sanye yake da milk din shadda tai masa kyau kan sa sanye da hula brown kala yai kyau sai tashin kamshi yake yi, zagayawa yai inda Haidar yake ya bude masa ya fito ya dauke shi tare da daukar ledar da yayo masa siyayya. Tin da ta daura ido akan sa taji bugun zuciyarta ya tsananta, a haka ya fara tinkaro su, yana tunkaro su kamshin turaren sa na kara musu sallama wanda ya kashewa Maryam jiki, so yai ya wuce amman kuma sai ya fasa ya karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Ahmad hannu yayi masa sallama. Ahmad ya karbi hannun shima cikin fara'a suka gaisa sai kuma suka kalli Maryam. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya. Da kyar ta saita kanta tace "Yaa Ahmad wannan shine Yaa Aliyu, wanda yake a matsayin miji na a yanzu." Dif haka gaban Yaa Ahmad ya buga, bata lura ba ta nuna Yaa Ahmad da yatsa tace "Wannan shine Yaa Ahmad abokin Yaa Aliyu ne sosai." Duk halin da Ahmad ya shiga bai hana sa kara mikawa Yaa Aliyu hannun ba yana murmushi, tace "Ummin sa ita ta tsince ni a wajen su nai rayuwa na tsawon shakara bakwai ban san kowa ba sai su, sun rike ni tamkar 'yar cikin su basu taba kyama ta ba wanda suka fifitani a fiye da ya'yan su a karshe suka aura min shi a matsayin miji na, Haidar bai taba sanin wani a matsayin Abbin sa ba sai shi, saboda yadda ya kula dashi sosai fiye da yadda na bashi kulawa Yaa Haidar ya bashi." Ji yai abinda ke ransa ya fara yayewa haka ma Yaa Aliyu, dan haka Ahmad ya kara rike hannun Aliyu yana fadin "Masha Allah, muna godiya Allah ya saka da alkhairi ya bada lada. Gaskiya kunyi abinda ba kowa zai ba kun cancani komai a rayuwar Maryam Allah ya saka da mafificin alheri ya biya ku da gidan aljanna." Murmushi Yaa Aliyu yayi kawai ya saki hannun sa, yace "Bari na shigar da Haidar yayi bacci." Yai ciki Maryam tabi bayan sa dan ta amshe shi, amman yana shiga sai ya nufi dakin ta kamar ta juya sai tabi bayan su, tana shiga yana ajiye Aliyu akan gado. "Sannu." Ta fada dan tasan zai iya barin ta ba tare da yace mata komai ba, dagowa yai ya wulla mata wani kallo yace "Maryam wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki da wani namiji tsaye da ba muharamin ki ba. Na fada miki in bakya son auren mu kije ki sanar da iyayen mu ni na miki alkawari zan fahimtar da su." Kai ta sunkuyar tana jin furucinsa kamar yana caka mata wuka a cikin zuciyar ta wai ta fada bata son sa zai shige mata gaba. Jin yayi tana sheshekar kuka abinda yafi tsana kenan kuma ace matar da yake so ita ke kuka shi ya bata mata rai ko har ya juya mata baya sai ya juyo ya karaso hannun sa ya saka ya dago habar ta, ido suka hada da sauri ya saki habar ta ya janyo ta jikin sa ya rumgume yana shafa bayan ta a hankali wanda jin ta a jikin sa yasa ya fara jin wani yanayi, abinda ya gani a cikin idon ta yake so ya gaskata, shin da gaske ne son sa yake gani a cikin idanun Maryam ko kuwa gizo abin yake masa, a hankali ya matsar da bakin sa saitin kunnen ta yana fadin "To ya isa menene na kuka?" "Ni ka daina cewa bana son ka Yaya." "To kina son nawa ne?" Shiru tayi yace "Uhmm gashi nan, na sani bakya so na auren dole akai miki, duk da haka kina da chance na sanar da iyayen mu i will do you what u want and i will support you kinji." Jikin ta ta janye dan da gaske maganar sa bata mata rai take cikin murya kuka take fadin "Ko da bana son ka ba zan taba fadawa iyaye na ba, ko da bana son ka nayi alkawarin zama dakai na har abada, ko da ba zaka na kallo na a matsayin mata ba zan kasance a matsayin kanwar ka, amman ka daina cewa bana son ka, kun min abinda ba zan ta'ba kin ku ba, kun dauken a lokacin da baku san ko ni wacece ba, baku kyamacen ba har kuka fifitani a cikin yan uwan ku, a karshe aka aure min kai Yaya meyasa zan 'ki ka, wane aibu ne da kai da zan ki ka, bayan ni tin baku san wacece niba kuka soni kuka kaunacen Yaya in nace bana son ka nayi karya a duniya daga iyaye na a yanzu sai Ummi da kai nafi so da kauna." A hankali ya tako gaban ta yace "Wannan kaunar ta hallacin da mukai miki ce Maryam ba 'kauna ta auratayya kike min ba." "Menene bambamcin ta, tinda duk 'kauna ce Yaya?" Matsowa yayi dab da ita ya dago kanta yace " 'Kauna da soyayya da sha'awa kuma wacce ita zata bamu damar sanin sirrin juna." Ido tai saurin runtsewa jin yadda yake yawo dan idonsa a cikin nata, hannun sa dake rike da kanta ya saka yana shafa gefen fuskar ta wanda hakan ya fara haifar mata da wani iri a jikin ta so take ta kwace amman ta kasa, ta janye jiki ta juya zata bar dakin cikin zafin nama ya kamo hannun ta ya janyo ta da karfi ta fado jikin sa, hannun sa ya sa ya zagaye ta dan yasan yanzu zata ce zata gudu, ganin ba zata iya kwacewa ba yasa tayi kasa da kanta yace "Kunyar kuma fa?" Kai ta girgiza ya dago kanta wanda hakan yasa tai saurin runtsa idon ta ya saki murmushi yana fadin "Ni dai dan Allah ki daina tsayawa da ko wanne namiji wallai baki ji yadda nake ji ba." Kai ta gyada yace "Ki min magana ba gyada kai ba." "To Yaya ba zan kara ba." "Allah miki albarka." "Amin." Ya sake ta ya juya zai fita har ya kai kofa tace "Yaya!" Juyowa yayi tace "Please ka ban dama nai masa bayani a baya bai san ina da aure bane shiyasa." Kallon ta ya tsaya yi ta langwabar da kai tace "Nasan me nake Yaya nasan ba kyau tsayawa da wanda ba muharami na ba ka yadda dani Yaya ba zan wani abu ba dai dai ba." "Ba komai." Ya fada ya juya ta kara fadin "Yaya!" Juyowa yayi sai tayi kasa da kanta dan ji tayi bata so ya tafi, ganin ta kasa magana yasa ya karaso ya zo daf da ita ya janyo ta jikin sa tare da dago kanta yace "Fada min menene?" Kai tayi kasa dashi yace "Shikenan tinda na zama sirikin ni bari naje na kwanta." Ya juya ta kamo hannun sa ya juyo sai ta fada jikin sa tana fashewa da kuka. Yace "Menene kuma?" "Yaya please ka yafe min, tinda na san ina da aure na cire kowa a raina, sai kokarin ganin na saka soyayyar ka nake." Hannu ya saka yana shafa bayan ta yace "To na shiga zuciyar taki?" Shiru tayi ya dago kanta da hawaye ke kwance a fuskar ta yace "Uhmm." Ido ta lumshe ya saki murmushi yace "To ni sakeni tinda ba zaki fada min ba." "Uhmm ba dan kaga na fara ba shine kake hukuntani." Da sauri ya dago kanta yana kallon ta ji yake kamar ba ita tai magana ba yace "What?" Kanta ta tusa a cikin kirjin sa tana girgiza kai, kara matse ta yayi a jikin sa yana mai godiya da Allah da ya fara karkato masa da hankalin Maryam kansa, Kansa ya shafa yana kallonta ya dago ta yana kallon ta sam baya gajiya da kallon Maryam ko kadan. "Maryam kina sona?" Jikin sa ta fada tana boye fuskar sa yai murmushi yace "Any way, fada da fatar baki bata lokaci ne, later in kika shigo gida na baki san lokacin da zaki fadan ba, wanda before then ur reaction will say everything." Sakin sa tayi da sauri ta juya masa baya, ya karasa yana fadin "Oh kunya ko? Naga ke dai kika hanani tafiya ko? Na tafi to." Ya fada yana juyawa yana tafiya yana juyowa, yana karasawa bakin kofa yace " *Matar Haidar* " Cak komai ya tsaya mata, abubuwa da yawa suka hau dawo mata, da gaske dai ta tabbata *Matar Haidar,* da gaskiyar Yaa Haidar da yace ko ya tafi zata kasance *Matar Haidar,* kasa juyowa tayi idon ta na kawo hawaye bana komai bane sai na godiya ga Allah, Yaa Aliyu da yake kallon ta shima wai abun ne ke masa yawo da gaske dai Maryam ce zata kasance matar sa, ya rasa Maryam wata Maryam din mai irin halin ta ta kara shigowa rayuwar sa, har ta kara zama matar sa ya kara zama Mijin Maryam kenan. Ya juya ya fita ta fada saman gado tana mai lumshe idon ta, a falo suka hadu da Ammi zaune ita da Aisha wata kunya yaji ya rasa yaya zaiyi da kyar ya karasa ya gaishe da Ammi sannan ya fice yana sunne kai. Ahmad ya gani da Rukky suna ta hira ya wuce bangaren su Ummi yai musu sai da safe ya fito ya kara ganin su suka sallama ya fita. Aisha na ganin fitar sa ta shiga dakin ganin Maryam a kwance ta daka mata duka tace "Kin gama soyayya shine kika kwanta kina wani lumlumshe ido ki tashi ki bishi in bukatar sa kike mana." Ido ta zaro tana fadin "Ni ba zaki lalatani ba wallahi." Ta mike tai bandaki bata jima ba ta fito daure da towel, Aisha tace "Uhmm har wanka ya sakaki." Kamar zatai kuka ta juyo tace "Dan Allah ki bari ni wallahi ba ruwa na kunya nake ji." "Zama ki ji kunya ne ke da idon ki yake fes tin ba yanzu ba." "Allah ya sakan wancan lokacin duk yarinta ce ban san komai ba." "Yanzu fa?" Banza tai mata, Aisha tace " 'Kya yi shiru ma kun gama tsots...." "Wallahi ba abinda mukai magana fa mukai akan Yaa Ahmad." 'Me ya faru dashi?" "Kinsan yazo ne wai yana so na." "Ina? *Matar Haidar* ai sai Yaa Haidar din." Baki Maryam ta tabe, Aisha tace "Ni sai naga kamar bakya son sa." "In ni ina son sa shi yana so na?" "Ke macece tinda bai nuna rashin 'kin ki ba yana so kenan, ke zaki kara karkato da hankalin sa." Rigar bacci ta saka tazo ta zauna tace "Aisha nima fa ina son sa, ban kara sanin haka ba sai kwanan nan." Nan ta bata labarin dukka rayuwar su, sai da ta gama Aisha ta saki buda tana fadin "Malama shi fa yana son ki kema kawai ki bada kai bori ya hau, kin yi dace kin rasa Yaa Haidar kin samu wani Yaa Haidar din in their structure they look alike behavoiur din ne dai, but shima wannan naga da ya shigo hannu zaki saisaita shi dan shi naga yana da dan tsare gida ne ba kamar Yaa Haidar ba, amman ni dadin da naji shima yana son ki ga yadda yake son Haidar kinga kuwa ai ki godewa Allah." "Amman kuma fa yana da yan mata." "Son su yake?" Kai ta girgiza Aisha tace "Ke zaki kara hanashi son nasu tinda yana son ki." "Ki bar cewa yana sona Yaa Aliyun?" "Yes." "Uhmm." Rukky ce ta shigo ta fada saman gadon tana fadin "Shine kika gudu kika barni ko? Kin taho soyayya." "Kada tayi?" Aisha ta fada. "Ah ni na isa na ce, Allah taimaka ni da so nake da kin sauke da wata shida itama ta sauke." Filo Maryam ta jefa mata tace "Sai dai mu sauke tare." "Kamar ya?" "Zan jira har ki aure sai mu samu tare mu haife tare." "Kaji muguwar mata ko hutawa da cin amarci ban ba, a'ah na dai barki miki, ranar sunan ki na fara laulayin dai." "Ah da wa zamu sha ne?" "Tukkuna ni mazan ne tsoro suke bani ku dai kun dace Allah ya samu a danshin ku." "Amin, Allah zai baki miji na gari insha Allah." "Allah ya yadda." Daga haka suka cigaba da hirar su har wajen sha biyu, wayar Maryam ita ta katse musu hirar ta janyo yana fadin "Waye da wannan daren?" Ta dauka sai taga number Yaa Haidar, dauka tayi ta kai kunnen ta tana yin sallama. Ya amsa cikin muryar sa mai dadin sauraro ido ta lumshe yace "Baki bacci ba?" Ido ta bude tace "Eh muna hirar yaushe gamo." "Jiyama haka kuka kwana kenan." "Uhmm." "Kina son ki ciwon kai?" "A'ah to maza yanzu aje a kwanta gobe a karasa kinji?" "To yaya sai da safe." "Yauwah kije kiyi alwala ki kwanta tare da addu'a." "Insha Allah gud nyt." "Have a nice dream." Ta kashe wayar. * Washe gari da yamma tana daki, sai ga kiran Yaa Ahmad nan dauka tayi cikin sanyin jiki, yace "Nazo ne Matar Haidar, kizo muyi magana akan kawar ki." " 'Kawata wacce?" "Wacce kuwa banda Rukayya." "Me ya faru?" "Tin da ban samu matar Haidar ba ai sai na koma ga 'kawar Matar Haidar ko? kila wasu daga cikin halaiyar tasu ya zama iri daya." "Kai amman naji dadi sosai. Ina zuwa gani nan." Ta kashe wayar har ta mike kuma ta koma ta zauna, wayar ta ta dauka ta fara kiran layin Yaa Haidar, har ta katse ba a dauka ba zata kara kira sai ga kiran shi nan, dauka tayi ta kai kunne tare da sallama. Muryar sa mai sanyi ta daki kunnen ta, ido ta lumshe yace "Ya kike?" "Ina yini Yaya?" "Lafiya lou." "Uhmm Yaya daman.. Daman Yaa Ahmad ne yazo yace yana son ya ganni, shine nace bari na fada maka naje?" "Me zai miki?" "Akan maganar wai 'kawata ce." "Maryam ki sa hijab kuma ban yadda da murmushi ba, minti biyar na baku yanzu zan fito." "Nagode Yaya." *Please Read* _Dan Allah mai son abu a waje na, ko mai son min magana, da yayi sallama ya rubuta abinda yake so wanda ina gani in da hali na bashi amsa ba sai kayi sallama na baka amsa ba sannan a kara gaisuwa, sannan ace kuma za a fadi abinda ake so, please da kayi sallama da gaisuwa fadi abinda kake so kai tsaye, abubuwa da yawa in nace haka za ana tafiya abun da yawa ba za akai inda ake so ba daga haka kuma sai ace anyi wulakanci, bama yan facebook please ku gyara 😀 nagode_ Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono). Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji. Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 *Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Allah ya yafe mana. Amin.* *Antty*💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 78 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Dis page is ur Amina Yar'adua i really appreciate with all ur comment keep it up. I heart you Mamanah* Ya kashe wayar tabi wayar da kallo sai ta mike, hijab ta saka har kasa sannan ta fice daga dakin, a compound ta same shi ta karasa tana fadin "Ina yini Yaa Ahmad?" "Lafiya lou, ya gida ina My son?" "Yana can wajen su Ummi ina jin." Sukai shiru sai kuma ya dago ya dan kalle ta yace "A baya naso na maye gurbin aboki na amman Allah bai nufa ba, Allah ya karasa kin tabbata a matar Haidar din ba abinda zance sai fatan alheri." Kan ta a kasa tace "Nagode Yaa Ahmad." Yayi mata murmushi "Babu wata godiya mata zaki bani kawai." Itama tayi murmushin tace "Wacece nai alkawarin ni kuma Insha Allahu." Yai murmushi yace "Shi nazo na fada miki amman ina neman wata afarma." Kai ta gyada yace "Ina so ki dauken tamkar Alkasim wanda in kina bukatar taimako ko wani abu direct zaki fada min ni kuma zan ji dadi fiye da yadda zaki zato, kuma ina son ana bani Haidar yana zuwa gidana hutu." "Insha Allahu Yaa Ahmad, Haidar kuma d'an ka ne." "Haka ne sai batu na biyu." Kai ta gyada yace " 'Kawar ki nake so Maryam, a jiya na fara jin wani abu game da ita, ta kwanta min itama tana da sanyin hali kamar naki, ina fatan zaki tayani mika kokon barata, a gida an damen da batun aure ina ta dojewa dan ina sa ran dawowar ki to yanzu kin dawo a matsayin Matar aure kin ga dole nima na nemi mata ko?" "Haka ne Yaya duk da mun jima ba tare ba amman har yanzu Rukkaya na nan a yadda na san ta, tana da sanyin hali da hakuri, tabbas kun dace da juna ba tin yau ba nake maka sha'awar ta, ashe dai da rabon, Allah nagode maka, Yaa Alkasim ya auri Aisha kai kuma Rukayya, nice dai na rasa Yaa Haidar, ko da yake nima ban rasa shi ba tinda ga wani Yaa Haidar din." Tai magana hawaye na taruwa a idon ta sai yaji tausayin ta kai ya dauke yace "Zan tafi yaushe zaku koma?" "Jibi!" "Ok zan zo muyi sallama gobe, ki turon number Rukuyyan." Kai ta gyada ta juya kenan Yaa Haidar ya karaso kusan cin karo sukai ta dago da sauri, idon ta dake cike da hawaye ta dago suna kallon juna, gefen sa tabi tayi cikin gida ya karasa wajen Yaa Ahmad suka gaisa yace "Ai ban san da aure a tsakanin ku ba sai jiya, ina maka fatan alheri da fatan Allah ya kawo zuria ta gari, muna godiya da dawainiyya Allah saka da gidan aljanna." "Amin Amin Ahmad." Ya saki hannun sa yabi bayan Maryam dan duk hankalin sa na kan ta, yana shiga falo ba kowa dakin ta ya nufa direct, yana shiga ya same ta kwance akan gado ko hijab din ta bata cire ba, karasawa yayi ya zauna a gefen gadon yana dago ta gaba daya, a zabure ta dago ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya, a jikin sa ya matse ta yana fadin "Menene?" Kai ta hau girgizawa yace "Fada min sirrin zuciyar ki." Kin magana tayi, yasa hannun sa ya dago kanta, ta runtsa idon ta yace "Ni dai na gaji wallahi dan Allah fada min abinda na jima ina gani a cikin idon ki." Da sauri ta bude idon ta tana son taji me ya jima da gani a cikin su, ganin Maryam na son raina masa hankali yasa ya sake ta tare da fuskantar ta, hannun ta dukka biyun ya kamo ya rike ya dago fuskar ta ya saita da tashi yace "Ki tsaya a haka." Kallon sa take, ya kalle ta shima yace "Akwai shekarun baya da zan tafi na fada miki komai akan ina karantar mutum, to saboda me ba zan karanci ma wacce nake so ba, a lokacin na so ki sanar dani sirrin zuciyar ki, amman kika ki, har kika yaudari yaron mutane, dan nasan ba son sa kike ba kin amshi shi ne kawai a rashi na, wanda naso nai wauta da na kasa fada miki sirrin zuciyata har wani yaso ya dauken ke, ni dake mun so muyi zurfin ciki, amman Allah ya kaddara cewa ke din Matar Haidar ce, in tambaye ki da kin aure shi yaya zakiyi da soyayya ta?" Idon ta lumshe yace "Fada min." "Yadda zakaji haka zanji koma naji fiye da nakan." "Kinsan da cewa ina sonki?" Kai ta sunkuyar ya saka hannun sa ya dago kan nata yace "Kin sani?" Kai ta girgiza yace "Karya kike Maryam, yadda nake mu'amalantar ki kadai zaki kawo akwai wani abu a kasa, kawai dai ke sai kin wahalar dani ko?" Fuska ta kawar tace "Aah." "Gashi nan, kinsa sai wahala nake, shakara fiye da bakwai ina dawainiyya da son ki, na sha wahala akan sonki." "Meyasa kaki ka fada min?" Ido ya lumshe yana fadin "Ban gama yadda da so bane a baya na zata tausayi ne dan tin da na fara ganin ki wani abu ya darsu a zuciya ta, ba wata soyayya mukai da matata kan ta rasu ba kafin aure sai da mukai aure nake matukar son ta bansan haka son yake ba, kin bani wahala Maryam a ko da yaushe da sonki nake kwana dashi nake tashi." "Kai Yaa Haidar amman kake guje min in nazo waje ka bar wajen ko makamantansu." "Hmmm so kike kisan sirrin komai dai ko, to zan fada miki amman kema sai kin fada min naki sirrin zuciyar. Na fara gujewa haduwa dake bayan kin haifi Haidar dan a lokacin ko ganin ki nayi kasa bacci nake, nai ta mafarkanki da wasu sigogi kike zuwar min na rasa kwanciyyar hankali, ki tadan bukata ki tadan hankali, sai nai kwana biyu bana cikin nutsuwa ta ba abinda nake so sai kasancewa dake, duk lokacin da muka samu body content ko na taba hannun ki ni kadai nasan halin da nake ciki wannan yasa nake gudarwa ganin ki, amman daga baya ba wanda yafi ni son ganin ki, har ta window nake labewa na hango ki daga bangaren Inna ko na biki can, ke shaidace akan zuwan da kikai gidan Sitti kasa jurewa nake ina miki wani irin so da bansan yawan sa ba, ban taba jin son abu kamar yadda nake son ki ba. Kece buri na kuma Alhamdulillah sai gashi na same ki." "Ka kusa kai asara." "Ko muyi dai gaba dayan mu, nayi shiru na mi'ka komai ga Allah ne nasan shi zai iya min kuma gashi yayi min." Ido ta lumshe hawaye na zubo mata ya janyo ta ya rumgume wanda sukaji wani sanyi gaba dayan su, yace "Ki bar kukan nan." Ajiyar zuciya ta sauke yace "Tin yaushe kika fara so na?" Kai ta girgiza tana fadin "Na zata ba son ka nake ba, na zata kawai dan kana kyautata min da Haidar ne, tabbas nayi soyayya da Yaa Muhammad amman gaba d'aya hankali na da tunani na suna wajen ka, sai dai kai na kasa gane inda ka dosa...." Tai shiru, kanta ya dago tai saurin runtse idon ta, kallon kyakyawar fuskar ta ya tsaya yi, wacce take dauke da dogon siririn hancin ta, sai mayan idanu da madaidaicin bakin ta wanda yake pink kala, daura idon sa akan lips din ta yasa yaji wani iri a jikin sa ba abinda yake sha'awa sai yin kiss bai san lokacin da ya matsar da fuskar sa zuwa fuskar ta ba, batai aune ba sai jin numfashin sa mai kamshi tayi na dukan fuskar ta da sauri ta bude ido dai dai lokacin da ya bawa bakin ta wani kiss wanda Maryam ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da wacce ta manta da ita a rayuwar ta, abubuwa da yawa ke yawo a kwanyarta, zuciya da jikinta, Yaa Aliyu a wannan lokacin wanda shi kansa ya kasa sanin a ina yake, ya kasa daina sumbatar ta kuma ya kasa rabata da jikinsa. Gaba daya sun manta a inda suke in banda kissing nata ba abinda yake, a hankali ta bude idon ta wanda ta hango Aisha na fita a dakin, wannan yasa ta tina a inda suke ta fara kokarin janye jikin ta amman sam Aliyu bai san ma tana yi ba, hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma kokarin janye jikinta, amman ya hanata kan ta ya fara kokarin dagowa, yana dagowa takai tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Murmushi ya saki ya kai bakin sa yana mata rada a kunne, da sauri ta fara jujjuya kai tana rufe kunnen ta da hannayen ta, mikewa yayi yana kallon ta, ita kuwa fadawa tayi saman gadon tana rufe fuskar ta da filo, dan bata taba yadda Yaa Aliyu ne yai kissing nata ba, Yayan ta, wannan abun ya bata kunya. "In dawo ne?" Ya fada yana rakwafowa, da sauri ta girgiza kai, yana murmushi ya fita a dakin, ita kuwa kunya ta hanata ta fita a dakin tasan yanzu Aisha zata sata a gaba, Allah yaso da ya fita ba kowa a falo, dan Aisha kitchen ta shiga tana ganin fitar sa tai murmushi tana mai jin dadi ko ba komai tasan Yaa Aliyu zai maye gurbin Yaa Haidar a wajen Maryam dan shima ta ga yana son ta gashi yana da qaulities din da duk za a so mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin "Bacci kike ne?" Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace 'Menene kike kallo nane?" Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace "Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV." "Amarya Matar yaa Haidar." Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala. * Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba. "Bacci kike?" Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi. A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace "Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?" Da kyar ta iya cewa "Eh" "Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm." Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace "Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi." “Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?" Wani murmushi ya saki mai sauti yace "Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam." Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce, "Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci." Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace “Maryam haka zamu yi da ke ko?” Shirun ta karayi ya mike zaune yace “Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba." Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace “Zo mu yi hirar!” Jikinta na makyarkyata ta ce, “Ni bacci nake ji” “Tunda na kasa kema ba za ki yi ba” “Yaya don Allah ka zo ka tafi, kada Ammi ta fito, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka. Cewa zatai ni nake kai kaina wajen maza.” Dan murmushi yayi yace "Ai da aure in ma kinbi." Kafada ta make abin sai ya bashi dariya ma, Maryam kuwa gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto. A tausashe ya ce, “Zan tafi, but on one condition....” Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata. “I only want to kiss you again! matata don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!” Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono) Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 *Allah yai mana rahna, Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* . *Antty* [12/8, 12:31] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 79 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ba ta motsa daga inda take ba, sai shi din ne ya taso ya tako a hankali ya tadda ita har inda take. Ya dauke ta suka koma kan gado, jikin sa ya jata yai mata wani irin rikon tare da cafkar bakin, yadda ya rike ta da irin yadda ya fara kissing nata ya tabbatar mata he will go far beyond abinda ya roka din, za ta gayawa aya zakinta idan ta sake ta bashi dama. Bata taba sanin haka romancing yake ba sai yau, domin kuwa taji jiki, basuyi aune ba sai ji sukai an fara kiran sallah, bai nemi ya tara da ita ba amman fa bakin ta da kirjin ta sun sha matsa har zugi suke mata. Jin ana kiran sallah ne yasa ya barta ba dan yaso ba sai dan lokacin sallah yayi, wannan yasa ya tafi ya bar ta cikin bargo. Jikinta babu sauran kuzari ko kadan ya gama gigitata na fitar hankali, da kyar bayan taji Abbi ya tada sallah ta sauko daga kan gadon da kyar take tafiya ta shiga bandaki, bakin ta ta hau dubawa dan ji take kamar ya cinye mata bakin, ba abinda yayi sai dai gaba daya yayi ja haka fuskar ta ma, rigar ta ta cire inda dukiyar fulanin ta ta bayyana, kan niples din nan yayi jajir, bakin yana tsatsaye saboda azabar da ya sha, ruwan dumi ta hada ta gasa jikin ta sannan tai wanka ta dauro alwala ta ta fito ta tada sallah, bayan ta idar ta mike ta fada saman gado dan rama baccin da bata samu ba. Sai karfe goma ta farka, tayi mika tana runtsa ido ta mike ta shiga bandaki, wanka ta kara ta fito ta shafa mai ta shirya cikin wata doguwar rigar material maroon kala ta zura hijab ta nufi kitchen dan yunwa take ji, tana shiga ta hada tea kan ta nemi komai sai da ta fara sha sannan ta bude flask ta zuba dankali, da plantain da kwai, sai da ta ci ta koshi sannan ta mike ta shiga dakin Ammi, a zaune ta same ta ta karasa ta zauna a kusa da ita tace "Ina kwana Ammi?" "Lafiya lou yau baccin me kike tayi Ummi?" "Wallahi Ammi, kinsan kwana biyu bama bacci da su Rukky sai yau na samu na dan rama." "Yanzu Fadima ta kira ai, tace yanzu zata karaso." "Yaya Zainab fa?" "Itama nasan zata zo, Ummulkairi dai tace in zaki tafi zatai rakiya har Abujan." "Ammi ke bazaki zo ba?" "Me zanzo nayi Ummi?" "Au ba zaki kaini dakin ba." "Daman Uwa ce ke kai 'ya dakin miji." "Ammi dan Allah kizo kema kinji?" "Zan zo Ummi amman sai daga baya kinji?" "Shikenan nasan Mami na tare zamu tafi." "Oh Ummi, ga Ummin ki nan ai ke fa baki da matsala kina da uwa tana son ki tana kula dake, ki godewa Allah, yana hada ki da sirikan kwarai." Kwanciyya tayi a jikin Ammi, a haka Yaya Fadima da Yaa Abdullah suka shigo Yaa Abdullah yace "Me nake gani haka?" Tai murmushi tace "Ammi na ce ai ba taka ba." "Yarinya ke da zaki tafi." Baki ta turo, tace "Ammi ni nama fasa anan zamuyi zaman mu." Yaya Fadima tace "Kinga ni tashi muje." "Ina?" "Daki." Ta kalli Ammi, ta gyada mata kai mikewa tayi ta fita Yaya Fadima tabi bayan ta. Daki suka shiga Yaya Fadima na nuna mata wasu abubuwa bayan nan ta dinga bata sirrikan kula da miji da na rayuwa, wanda Aisha ma ta shiga suka cigaba da wayar mata sa kai, ita dai jin su kawai take, suna zaunen nan taga kiran sa yafi sau biyar amman bata dauka ba har sai sa Yaya Fadima ta lura tace "Ba kiranki ake ba?" "Kyale shi damuna zai." Ido ta zaro tace "Oh damunki zaiyi ko kin dauka ko sai na batar miki." Dauka tayi ta kai kunne yace "Matar Haidar." "Uhmm ina kwana?" "Alhamdulillah ya na baro ki?" "Uhmm..." "Fada min, in dawo?" Kamar zatai kuka tace "A'ah kai zaman ka" "Uhmm uhmm ni wallahi i need my wife." Ya fada cike da shagwaba baki ta saki kawai jin wai wannan Yaa Haidar ne anya kuwa. "Kinji." Ya fada kamar zai kuka." "Yayahh." Ta kira sunan sa cikin wani irin salo. "Matar Yaya." Ya fada, tace "Kayi hakuri." Kafada ya make yace "Naki." "Uhmm ni yaya kake so nayi to?" Ta fada kamar zatai kuka. "No nifa bance ki min kuka ba, amman kinsan me inzo mu dan fita?" "Uhmm a'ah ni kunya nake ji." "Kunyar wa?" "Uhmm Ammi, Ummi." "Matatace fa." "Dan Allah Yaya kai hakuri." "Na hakura matar Haidar amman say u love me." "I love u." Tana fada ta kashe wayar * Da dare ta fito daga bangaren su Ummi, bacci takeji tana shiga barander bangaren su taji an janyo hannun ta, a tsorace ta juyo sai dai ganin Yaa Haidar yasa ta hau sauke ajiyar zuciya, sanye yake da blue black boyel yai masa kyau ya fito da hasken fatar sa sai hula dake kan nasa wacce ta kara masa kyau sai tashin kamshin turare yake bata san lokacin da ta lumshe idon ta ba, yace "Me yasa ake gudu nane?" Shiru tayi ya sa dayan hannun ya dago fuskar ta da sauri ta lumshe idon ta ya saki murmushi yace "Wai kunyata kike ko? Ko da yake kina so na kara abin jiya ko?" Da sauri ta bude idon ta tana girgiza kai yace "Ki min magana in ba haka ba...." Yai kwafa, baki ta turo yace "Inyi kenan?" Dagowa tayi ta dan harare shi da gefen ido, yace "Uhmm ni kike harara ko?" Kai ta girgiza ya kalle ta kasa kasa yace "I want to hug you" Ta bata fuska a shagwabe, tace "Wai Yaya kai baka jin kunya." "Kunyar wa zanji ni da matata." Agogo ya kalla yace "Goma ta wuce me ya fito dake ko ni kike fito nema?" Ya fada yana kanne mata ido daya tare da kokarin danne dariyar sa, dan yaga yadda ta saki baki tana kallon sa, "Ko baki taba fito neman nawa bane?" Hijab din jikin ta taja ta rufe fuskar ta, tana murmushi kasa kasa ashe yasan ta fito neman sa ranan. Kunya yake bata ji take kamar kasa ta bude ta shige, fargaba kada wani ya fito ya gansu. Dan matsawa tayi ya matso yana magana a hankali "Gobe zaki tare ne?" Juya masa baya tayi tana girgiza kai, tace "Yaya ni dai sai da safe, kada Abbi ya fito ya ganmu fa." "Matsoraciya Matata, kada kisa na dauke ki yanzu mu tafi can wani waje mu kwana." Yai maganar yana zuro kansa ta wuyan ta, hannun sa ya sa ya zagaye kugun ta, sai kuma ya sake ta ya juyo da ita suna fuskantar junan su, kanta ya dago yana kallon lips din ta, ido ta lumshe wanda tana rufewa taji ya hada bakinsa da nata. Ido ta zaro tana dukan sa da hannun sa, amman sai da ya dauki minti biyu yana kissing bakin ta sannan ya dago kansa yana karewa fuskarta kallo, ji yake kamar ya dauke ta suje su kwana abinsu, kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rumgumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna, sakin ta yayi, yai kissing goshinta sannan yace "In ban tafi ba zanyi iya wani abun, sai da safe." Ya juya yana daga mata hannu, tana jin rufe kofar sa jiki a mace ta ja kafa ta shiga dakin, Ammi ta gani, da sauri tai kasa da kanta dan gani take tamkar Ammi zata ga abinda tai, dan haka taki yadda ta dago, Ammi dai da ido ta bita har ta shige daki, girgiza kai kawai tayi ta fita ta rufe kofar ta nufi sashen Abbi. Tana shiga daki bandaki ta fada, wanka tayi ta dauro alwala ta fito. Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta, juyi ta dingayi akan gadon har kusan daya saura, ba alamar bacci a idon ta sam, tana tsaka da tunanin mijin nata, wayarsa ta shigo. Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani kawai, tana dauka yace "Me ya hanaki bacci?" Muryar nan tasa taji ta har cikin jikin ta, rufe ido tayi taki magana "Ni ne ko? Am sorry daga gobe zaki ta baccin ki mai dadi a kirjin mijin ki." Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa, shiru tayi yace "Ko bakya so?" Kai ta gyada tace "Eh!" Yai murmushi yace "Kar na fara karyata matata amman dai wannan ta fada ba dai dai ba." Shiru tayi, yace "Kinsan me?" "Aah." Ta bashi amsa. Yace "Ina so na zama komai naki, Miji, Yaya, Aboki, da, jigo, yadda komai kika debo ni, dan haka ki saki ranki kina fadan komai zanyi kokarin fahimta ba zan taba jin haushi ko makamancin wani abu ba kinji. Ina so ni da matata mu zama abokai ko fada mukai ba mai jin mu, mu zamu shirya kanmu, mu kasance kullum cikin farin ciki da fahimtar juna, mu samu ya'ya masu albarka kyawawa kamar Haidar ko?" Tayi dan murmushi tace "Allah ya tabbatar da alheri" Ta fada tana gyara kwanciyya tare da yin hamma dan ta fara jin bacci har biyu tayi, yace "Bacci ko?" Tana ji amman bata so ta daina jin wannan muryar tasa dan haka sai ta girgiza kai. Yace "Gobe muna da tafiya ki samu ki kwanta ki huta kinji. Sai da safe take care." "Allah tashe mu lafiya." "Amin." Ta kashe wayar tana rufe ido wani bacci mai dadi ya dauke ta, wanda sai da ta kusan makara da asuba. * Washe gari da safe suka tafi Abuja, da Yaya Fadima, Yaya Zainab, Yaya Ummulkhairi da wasu daga cikin kannen Abbi, sai Rukayya da Aisha, sai kuma su Ummi, da su Yaa Abubakar da Mami. Maryam ta sha kuka kamar kar ta tafi Abbi da Ammi sukai mata nasiha sosai. Tana jikin Ummi a kwance ta rufe fuskar ta da hijab din jikin ta, Yaa Aliyu na gidan gaba gefen driver sai Yaa Farouk dake driving inda, Aisha ke gefen Maryam. Bayan ta gama kukan nata ta mike ta jingina da kujera, Yaa Haidar ya karkato da mudubin motar yana kallon ta kamar ance ta dago suka hada ido, ido daya ya kanne mata da sauri ta lumshe idon ta, wayar ta ce tai kara alamar shigowar sako, dauka tayi ta duba sai tai sauri ta rufe wayar ta ajiye kawai tana ji wani text din ya kara shigowa amman taki ta duba daga haka ma sai bacci karya da ta hau yi dan ya kyale ta. A haka suka karasa wanda Mami tai musu tarba mai kyau, a sashen Mami suka sauka gaba daya, suna falo bayan an gama cin abinci Mama ta shigo gidan, da kallo ta bisu sai ta karaso suka gaisa cikin mutunci, sosai Ummi tai mamaki, bama da taga yadda Maman tai la'asar dan har ita ta gaisar tana tambayar ya hanya. Mami ta kalla Mami tai murmushi kawai. Sai yamma duk sukai daki, Kannen Abbi biyu da Mami suka wuce sashen Ummi, wanda Yaya Ummulkhairi da Zainab da Yaya Fadima suna sashen Mami, Maryam da Rukayya kuwa wajen Inna suka gudu. Aisha tayi tayi su taho sunce zasuje daga baya. Da yamma Maryam na dakin Inna, Jawahir ta shigo suka tashi suka rumgume juna, Jawahir ta zauna tana fadin "Dan kin samu su Aisha shine kika yadani ko?" "Kina raina wallahi abubuwa ne sukai min yawa kawai." Ta zauna tana mikawa Rukky hannu suka gaisa, tace "Kun dawo lafiya?" "Alhamdulillah ya gida yasu Momy?" "Suna lafiya ai munzo bakwa nan." "Ayyah." "Yaa Khalifa ya shiga damuwa sosai, baki ga yadda ya koma ba Sister ya rame yayi baki tinda aka daura auren sa bai kara lafiya ba kullum yana asibiti, daga farko jinin sa ne ya hau, sai ulcer, wanda a haka kullum yake damuwa da rashin bacci ya hana jinin sa ya sauka." Idon Maryam ne ya ciko da hawaye, a ranta take fadin daman haka yake son ta, Allah yayi ita ba matar sa bace sai dai zatai masa addu'a basa lafiya kuma yayi hakuri ya amshi zabin iyayen sa kila ya zamo masa alheri. "Kira min shi a wayar ki nai masa sannu." Nan da nan ta kira mata shi yana kwance yaji kiran ya dauka tace "Yaya nazo gidan su Maryam ne tace na baka kuyi magana." Ta mikawa Maryam, amsa tayi tace "Yaa Muhammad ina yini?" "Lafiya lou Maryam ya gida yasu Haidar?" "Suna lafiya ya jikin?" 'Alhamdulillah." "Allah kara sauki, kayi hakuri Yaya ka amshi kaddarar ka, Allah yayi ni ba matar ka bace, dan haka ka amshi zabin iyayen ka kila ya zamo alheri a rayuwar ka bana jin dadi da akace ka saka damu baka ci baka sha baka bacci in har kana so na to Yaya ina so daga yanzu ka cire ko wacce irin damuwa dan Allah ka cigaba da rayuwar ka dan Allah." Hawaye ya biyo fuskar sa yace "Nagode Maryam Allah miki albarka, naji ance kin hadu da iyayen ki insha Allahu, in komai ya warware har Kanon zani na gaishe su, nagode sosai ina miki fatan alheri." "Nagode Yaya. Sai anjima." Ta kashe wayar hawaye na zubo mata ko ba komai yana son ta kuma ya damu da ita ya nuna mata kulawa da tsantsar soyayya ta san ba zata taba mantawa da Yaa Muhammad ba. Shiru kuma sukai, sai bayan magariba Jawahir ta tafi, tana fadin "Yaushe zaki dawo makaranta an koma wannan satin fa." Baki ta dan tabe tace "Next week." "Ke da zaki tare ai nasan kyayi hutun a kalla two week." Murmushi kawai tayi sukai sallama. Da dare Inna na daki tana gyara durowar ta, Maryam na falon tana kallo, Rukayya taje wajen su Yaya Fadima, idon ta na kan TV taji an bude kofa dagowa tayi sai taga Yaa Aliyu da sauri ta mike tana gyara zaman ta daga kashingiden da take hijab take nema ta saka, ya karaso ya dauke hijab din yana binta da wani kallo wanda yasa tsigar jikin ta ta tashi zama yayi a kusa da ita yace "Me kike nufi ne? Kada ki manta fa ni mijin ki ne ba saurayn ki ba" Fuska ta shagwabe kawai tana mammatse jikin ta, dan jin ta take a takure bata saba ba ko da yaushe da hijab suke ganin ta ko mayafi, sharewa yayi yace "Me kike anan?" "Anan zamu kwana." "Ke dawa?" "Rukayya." Kai ya hau girgizawa yace "No Matata a dakin mijin ta zata kwana" *** Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono) Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 *** *Allah ya yafe mana yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/8, 12:31] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 78 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Dis page is ur Amina Yar'adua i really appreciate with all ur comment keep it up. I heart you Mamanah* Ya kashe wayar tabi wayar da kallo sai ta mike, hijab ta saka har kasa sannan ta fice daga dakin, a compound ta same shi ta karasa tana fadin "Ina yini Yaa Ahmad?" "Lafiya lou, ya gida ina My son?" "Yana can wajen su Ummi ina jin." Sukai shiru sai kuma ya dago ya dan kalle ta yace "A baya naso na maye gurbin aboki na amman Allah bai nufa ba, Allah ya karasa kin tabbata a matar Haidar din ba abinda zance sai fatan alheri." Kan ta a kasa tace "Nagode Yaa Ahmad." Yayi mata murmushi "Babu wata godiya mata zaki bani kawai." Itama tayi murmushin tace "Wacece nai alkawarin ni kuma Insha Allahu." Yai murmushi yace "Shi nazo na fada miki amman ina neman wata afarma." Kai ta gyada yace "Ina so ki dauken tamkar Alkasim wanda in kina bukatar taimako ko wani abu direct zaki fada min ni kuma zan ji dadi fiye da yadda zaki zato, kuma ina son ana bani Haidar yana zuwa gidana hutu." "Insha Allahu Yaa Ahmad, Haidar kuma d'an ka ne." "Haka ne sai batu na biyu." Kai ta gyada yace " 'Kawar ki nake so Maryam, a jiya na fara jin wani abu game da ita, ta kwanta min itama tana da sanyin hali kamar naki, ina fatan zaki tayani mika kokon barata, a gida an damen da batun aure ina ta dojewa dan ina sa ran dawowar ki to yanzu kin dawo a matsayin Matar aure kin ga dole nima na nemi mata ko?" "Haka ne Yaya duk da mun jima ba tare ba amman har yanzu Rukkaya na nan a yadda na san ta, tana da sanyin hali da hakuri, tabbas kun dace da juna ba tin yau ba nake maka sha'awar ta, ashe dai da rabon, Allah nagode maka, Yaa Alkasim ya auri Aisha kai kuma Rukayya, nice dai na rasa Yaa Haidar, ko da yake nima ban rasa shi ba tinda ga wani Yaa Haidar din." Tai magana hawaye na taruwa a idon ta sai yaji tausayin ta kai ya dauke yace "Zan tafi yaushe zaku koma?" "Jibi!" "Ok zan zo muyi sallama gobe, ki turon number Rukuyyan." Kai ta gyada ta juya kenan Yaa Haidar ya karaso kusan cin karo sukai ta dago da sauri, idon ta dake cike da hawaye ta dago suna kallon juna, gefen sa tabi tayi cikin gida ya karasa wajen Yaa Ahmad suka gaisa yace "Ai ban san da aure a tsakanin ku ba sai jiya, ina maka fatan alheri da fatan Allah ya kawo zuria ta gari, muna godiya da dawainiyya Allah saka da gidan aljanna." "Amin Amin Ahmad." Ya saki hannun sa yabi bayan Maryam dan duk hankalin sa na kan ta, yana shiga falo ba kowa dakin ta ya nufa direct, yana shiga ya same ta kwance akan gado ko hijab din ta bata cire ba, karasawa yayi ya zauna a gefen gadon yana dago ta gaba daya, a zabure ta dago ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya, a jikin sa ya matse ta yana fadin "Menene?" Kai ta hau girgizawa yace "Fada min sirrin zuciyar ki." Kin magana tayi, yasa hannun sa ya dago kanta, ta runtsa idon ta yace "Ni dai na gaji wallahi dan Allah fada min abinda na jima ina gani a cikin idon ki." Da sauri ta bude idon ta tana son taji me ya jima da gani a cikin su, ganin Maryam na son raina masa hankali yasa ya sake ta tare da fuskantar ta, hannun ta dukka biyun ya kamo ya rike ya dago fuskar ta ya saita da tashi yace "Ki tsaya a haka." Kallon sa take, ya kalle ta shima yace "Akwai shekarun baya da zan tafi na fada miki komai akan ina karantar mutum, to saboda me ba zan karanci ma wacce nake so ba, a lokacin na so ki sanar dani sirrin zuciyar ki, amman kika ki, har kika yaudari yaron mutane, dan nasan ba son sa kike ba kin amshi shi ne kawai a rashi na, wanda naso nai wauta da na kasa fada miki sirrin zuciyata har wani yaso ya dauken ke, ni dake mun so muyi zurfin ciki, amman Allah ya kaddara cewa ke din Matar Haidar ce, in tambaye ki da kin aure shi yaya zakiyi da soyayya ta?" Idon ta lumshe yace "Fada min." "Yadda zakaji haka zanji koma naji fiye da nakan." "Kinsan da cewa ina sonki?" Kai ta sunkuyar ya saka hannun sa ya dago kan nata yace "Kin sani?" Kai ta girgiza yace "Karya kike Maryam, yadda nake mu'amalantar ki kadai zaki kawo akwai wani abu a kasa, kawai dai ke sai kin wahalar dani ko?" Fuska ta kawar tace "Aah." "Gashi nan, kinsa sai wahala nake, shakara fiye da bakwai ina dawainiyya da son ki, na sha wahala akan sonki." "Meyasa kaki ka fada min?" Ido ya lumshe yana fadin "Ban gama yadda da so bane a baya na zata tausayi ne dan tin da na fara ganin ki wani abu ya darsu a zuciya ta, ba wata soyayya mukai da matata kan ta rasu ba kafin aure sai da mukai aure nake matukar son ta bansan haka son yake ba, kin bani wahala Maryam a ko da yaushe da sonki nake kwana dashi nake tashi." "Kai Yaa Haidar amman kake guje min in nazo waje ka bar wajen ko makamantansu." "Hmmm so kike kisan sirrin komai dai ko, to zan fada miki amman kema sai kin fada min naki sirrin zuciyar. Na fara gujewa haduwa dake bayan kin haifi Haidar dan a lokacin ko ganin ki nayi kasa bacci nake, nai ta mafarkanki da wasu sigogi kike zuwar min na rasa kwanciyyar hankali, ki tadan bukata ki tadan hankali, sai nai kwana biyu bana cikin nutsuwa ta ba abinda nake so sai kasancewa dake, duk lokacin da muka samu body content ko na taba hannun ki ni kadai nasan halin da nake ciki wannan yasa nake gudarwa ganin ki, amman daga baya ba wanda yafi ni son ganin ki, har ta window nake labewa na hango ki daga bangaren Inna ko na biki can, ke shaidace akan zuwan da kikai gidan Sitti kasa jurewa nake ina miki wani irin so da bansan yawan sa ba, ban taba jin son abu kamar yadda nake son ki ba. Kece buri na kuma Alhamdulillah sai gashi na same ki." "Ka kusa kai asara." "Ko muyi dai gaba dayan mu, nayi shiru na mi'ka komai ga Allah ne nasan shi zai iya min kuma gashi yayi min." Ido ta lumshe hawaye na zubo mata ya janyo ta ya rumgume wanda sukaji wani sanyi gaba dayan su, yace "Ki bar kukan nan." Ajiyar zuciya ta sauke yace "Tin yaushe kika fara so na?" Kai ta girgiza tana fadin "Na zata ba son ka nake ba, na zata kawai dan kana kyautata min da Haidar ne, tabbas nayi soyayya da Yaa Muhammad amman gaba d'aya hankali na da tunani na suna wajen ka, sai dai kai na kasa gane inda ka dosa...." Tai shiru, kanta ya dago tai saurin runtse idon ta, kallon kyakyawar fuskar ta ya tsaya yi, wacce take dauke da dogon siririn hancin ta, sai mayan idanu da madaidaicin bakin ta wanda yake pink kala, daura idon sa akan lips din ta yasa yaji wani iri a jikin sa ba abinda yake sha'awa sai yin kiss bai san lokacin da ya matsar da fuskar sa zuwa fuskar ta ba, batai aune ba sai jin numfashin sa mai kamshi tayi na dukan fuskar ta da sauri ta bude ido dai dai lokacin da ya bawa bakin ta wani kiss wanda Maryam ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da wacce ta manta da ita a rayuwar ta, abubuwa da yawa ke yawo a kwanyarta, zuciya da jikinta, Yaa Aliyu a wannan lokacin wanda shi kansa ya kasa sanin a ina yake, ya kasa daina sumbatar ta kuma ya kasa rabata da jikinsa. Gaba daya sun manta a inda suke in banda kissing nata ba abinda yake, a hankali ta bude idon ta wanda ta hango Aisha na fita a dakin, wannan yasa ta tina a inda suke ta fara kokarin janye jikin ta amman sam Aliyu bai san ma tana yi ba, hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma kokarin janye jikinta, amman ya hanata kan ta ya fara kokarin dagowa, yana dagowa takai tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Murmushi ya saki ya kai bakin sa yana mata rada a kunne, da sauri ta fara jujjuya kai tana rufe kunnen ta da hannayen ta, mikewa yayi yana kallon ta, ita kuwa fadawa tayi saman gadon tana rufe fuskar ta da filo, dan bata taba yadda Yaa Aliyu ne yai kissing nata ba, Yayan ta, wannan abun ya bata kunya. "In dawo ne?" Ya fada yana rakwafowa, da sauri ta girgiza kai, yana murmushi ya fita a dakin, ita kuwa kunya ta hanata ta fita a dakin tasan yanzu Aisha zata sata a gaba, Allah yaso da ya fita ba kowa a falo, dan Aisha kitchen ta shiga tana ganin fitar sa tai murmushi tana mai jin dadi ko ba komai tasan Yaa Aliyu zai maye gurbin Yaa Haidar a wajen Maryam dan shima ta ga yana son ta gashi yana da qaulities din da duk za a so mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin "Bacci kike ne?" Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace 'Menene kike kallo nane?" Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace "Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV." "Amarya Matar yaa Haidar." Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala. * Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba. "Bacci kike?" Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi. A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace "Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?" Da kyar ta iya cewa "Eh" "Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm." Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace "Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi." “Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?" Wani murmushi ya saki mai sauti yace "Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam." Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce, "Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci." Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace “Maryam haka zamu yi da ke ko?” Shirun ta karayi ya mike zaune yace “Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba." Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace “Zo mu yi hirar!” Jikinta na makyarkyata ta ce, “Ni bacci nake ji” “Tunda na kasa kema ba za ki yi ba” “Yaya don Allah ka zo ka tafi, kada Ammi ta fito, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka. Cewa zatai ni nake kai kaina wajen maza.” Dan murmushi yayi yace "Ai da aure in ma kinbi." Kafada ta make abin sai ya bashi dariya ma, Maryam kuwa gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto. A tausashe ya ce, “Zan tafi, but on one condition....” Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata. “I only want to kiss you again! matata don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!” Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono) Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 *Allah yai mana rahna, Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* . *Antty* [12/9, 18:20] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 80 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Ido ta zaro tana mai girgiza kai kamar zatai kuka tace "Ni dai dan Allah Yaya kayi hakuri Allah ba zan iya ba." Mikewa yayi batai aune ba sai jin tayi ya dauke ta gaba dayan ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa yasa ta hakura sai hannun ta da ta zuro ta wuyan sa, tana fadin "Dan Allah Yaya kayi hakuri ni wallahi kunya nake ji dan Allah ka sauke ni." "In baki min shiru ba har dakin Ummi zamu a haka." Take tai dif kamar ruwa ya cinye ta a haka suka shiga falon, Allah yaso ba kowa har wata ajiyar zuciya ta sauke zasu shiga dakin kenan Ummi ta fito daga kitchen basu ganta ba dan sun juya mata baya, ita ce ta gansu kai kawai ta girgiza tana mai addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa yasa Aliyu yaso ta su zauna lafiya ya basu zuri'a ta gari. Har bedroom ya shiga da ita ya ajiye ta, akan gado matsawa tayi karshen gado tana takurewa ya karasa wajen kofa ya saka key sannan ya shige bandaki, sai da ya dauki wajen minti ashirin sannan ya fito sanye da armless riga da three quarter sai zuba kamshi yake, kayan sun masa kyau, wajen ta ya karaso ya zauna a gefen ta ya dagata ya daura akan kafar sa, motsu motsu ta fara dan duk ta kasa sakewa, kanta ya dago yana kallonta, ido ta lumshe sai ga hawaye na zuba a idon ta, harshen sa yasa yana share mata su yanayi wasu na zubowa, a hankali yace "Menene?" "Dan Allah Yaya ka bari kar Inna taje taga bana nan tazo kuma taga bana nan." "Naga matata ce." "Dan Allah ka bari Yaya ai ban tare ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kin fiso na kwana ina fushi dake." Jikin sa ta shige tana girgiza kai, yace "To ki shiru ni ba abinda zan miki kawai ina son na kwana a jikin matata ok?" Ido kawai ta lumshe ya kwantar da ita ya tashi ya kashe fitila tana ji ya hawo gadon ya jata jikin sa, rumgume ta kawai yayi yana cusa kan sa a wuyan ta a haka sukai baccin dan ya ga duk ta takura taki sakewa, sai asuba suka tashi, ya shiga bandaki, kan ya fito ta fice ta bar masa dakin, sama ta wuce da sauri ta shiga dakin Haidar karami acan tai wanka tai alwala tai sallah. Sai karfe bakwai ta fita ta gaishe da su Ummi sannan ta koma dakin Inna. Rukayya ta sama tana ta baccin ta, Inna kuwa na kitchen tana ta hada kayan karyawa a falo ta zauna tana sauraron azkar din da ake yi a TV, idon ta a lumshe bataji shigowar sa ba sai kamshin turaren sa da taji tana bude idon ta ta ganshi durkushe a gaban ta, zama ta gyara tace "Ina kwana Yaya?" Ido ya lumshe ya bude a hankali yace "Matar Haidar ta gudu ta bar mijin ta ko?" Kai ta girgiza ya dan saki murmushi dai dai fitowar Inna da tray ta ajiye, tace 'Menene haka nake gani?" Fuska Aliyu ya hade ya koma ya zauna, baki Inna ta tabe tace "Kazo zaka takurawa yar mutane me ya kawo ka sashe na da sassafen nan?" "Wajen Matata nazo." "To ba a sashe na ba tashi ka fitar min tinda ka zama marar kunya." "Sai na ciyar da ita tukkuna Inna kawo na bata taci ta koshi sai kici sauran ta." "Tinda Aisha ce ta girkan ba, Ja'iri." Ta shiga ta fito da kayan ta shiga daki dan taso Rukayya tea ya hada mata mai kauri dan sosai yaiwa Inna ta'adin madara ya debi dankalin da ta suya da pepper soup ya zuba a bowl ya kalli Maryam yace "Sauko kici." "Dan Allah Yaya ka tafi ni zanci da kaina." "Da yawa?" Yai mata tambayar yana binta da wani kallo wanda yasa duk jikin ta yai sanyi. Kai ta gyada yace "To shikenan." Ya mike har ya kai kofa tace "Yaya kai fa?" "Ni me?" "Abincin?" Ta fada tana sunkuyar da kanta, yai murmushi yace "To an damu in ci ne?" Kai ta gyada, ya doshi kofar yana fadin "In an damu naci azo a bani." Murmushi kawai tayi Inna da Rukky suka fito, tare suka karya bayan sun gama suka shiga kitchen suka wanke kwanukan, suna kitchen suka jiyo sallamar Najwa tana fadin "Amaryar Yaya." Inna tace "Wacce irin Amaryar Yaya, Antyn ki." Maryam ta fito tana fadin "Ai kuwa dai." Suka zauna, tace "Mutanen Kano, kinga yadda kikai kara kyau." Rukky ce ta fito Najwa tace "Wannan ce Rukky ko?" Kai ta gyada suka gaisa tace "Kinga tashi zaki muje a dan gyara ki ai amarya ba ta tafi ba dan lalle bare gyaran kai ba ko?" Inna tace "Yauwah yar gari, ga mijin nata naga ya zama bita zai zai." Sukai murmushi, Maryam ta sunkuyar da kai, Najwa tace 'Bari naje wajen su Yaya Fadima ki shirya dan naji Ummi na fadin yau zaki tare gwara muje mu shirya da wuri ko?" Ta mike ta fita, Maryam ta nufi sashen Ummi, wanka ta sake sannan ta saka doguwar riga tai rolling din mayafi ta fito falo, zasu fita kenan Yaa Aliyu ya shigo gidan da kallo ya bita zata shiga mota wani horn ya danna da yasa duk suka tsaya da abinda suke, bai fito ba ya kure ta da ido, Najwa tace "Alhaji Yaya mulki, to kije kiji." "Ai Yaya wallahi ya fiya rigima." "Je ki dai jiran ki yake." Kofa ta saki ta juya ta nufi wajen sa ta inda yake ta tsaya da yake tint ne yana ganin ta amman ita bata ganin sa, baki ta dan turo dan yaki sauke glass din, kofar dayan side din ya bude zagayawa tai ta shiga, zaune ta ganshi cikin shiga ta wandon jeans da riga orange kala tai masa kyau sai tashin kamshi yake, kallo ya kafe ta dashi, ta dago tace "Yaya." Zama ya gyara, baki ta dan kara turowa tace "Yaya fita fa zamuyi na barsu suna jira na." "Da izinin wa?" Ya fada yana duba agogon azurfan dake hannun sa. "Haba Yaya yau kadai fa." "Me din?" Kai tayi kasa dashi yace "Kalli a yadda kika fito sai kace ba matar aure ba salon ki fita maza suna tsayar dake ko?" "Haba dai Yaya ko a da bana tsayawa bare yanzu." "Abinda bana so din kenan ai wani ya kallen min ke." "To kayi hakuri." "Ina ma zaku?" "Uhmm Najwa ce ta matsa wai sai munje lalle." "Kace ni za ai wa gyara." Kai ta gyada yace "Ok yanzu kije ki sako hijab da nikaf kinji?" Kai ta gyada ta fita, ciki ta koma bata jima ba ta fito sanye da hijab da nikaf ta karaso tace "Nayi?" "Sosai ma kuwa." Ya dauki wayar sa ya danyi dane dane yace "To sai kun dawo ko nazo na kaiki?" "A'ah zamu tafi kawai." Taji karar shigowar sako dubawa tayi sai taga kudi yai mata transfer, dagowa tai yace "Aje ai lallen dasu sai anjima in mun hadu a gdan mu." Ya fada yana kanne mata ido da sauri ta bar wajen ta nufi wajen su Najwa suka bar gidan. Tin da sukaje ake gyara ta, aka gyara mata fata, kafar ta da hannu sannan aka gyara kanta akai mata lalle, sosai tai kyau fuskar ta ta kara wani kyau tai fresh. Sai biyar da wani abu suka dawo, suna shigowa abinci sukaci Ummi tace ta shiga tai wanka, da kanta ta hada mata wani ruwan turare ta shiga tayi, tana fitowa ta bata wani turaren ta shafe jikin ta sannan ta turare jikin ta take wani kamshi mai dadi ya hau tashi a jikin ta. * Sai da tayi sallah sannan Ummi ta shigo ta kamata suka fita, mayafi ne rufe a kanta inda take sanye da wata farar atamfa da akai ado da ja da blue atamfar tai kyau ta yafa farin mayafi ta saka flat white shoe, duk inda ta gifta kamshi ne ke tashi, a haka suka karasa bangaren Inna, wacce tai mata bankwana da karai mata nasiha da saka mata albarka, wajen Mami aka kai ta itama tai mata nasiha sannan Mama ma tace "Allah bada zaman lafiya." Wanda daga Maryam har Ummi mamakin canjawar Maman suke, daga nan suka fito suka shiga wata hadadiyar mota wacce Yaa Farouk ke driving, gida ne babba mai kyau tun daga waje ga filawoyi sun fito ta saman katanga. Gidan sai kamshi yake tin daga compound zaka san gidan amarya ne dan yadda kamshi yake tashi, wanda tin safe su Yaya Ummulkairi ke aikin kintsa gidan dan sai da suka gyara jeren da akai dan an kwaso kayan duk kayan da aka kai gidan Muhammad, bangaren Maryam kawai aka zubawa kayan dan bangaren Aliyu akwai kayan sa dan dawowar sa a canja su, sai da suka wuce falo har biyu sannan aka dangana da ita ga dakin ta, wanda ba karamin kokari Ummi da Abba sukai ba, ba karamin kudi suka kashe mata ba yan uwan ta duk sunji dadin wannan soyayyar da su Ummi kewa yar tasu wannan yasa suka kara basu wani matsayi. Daga nan aka wuce da ita dakint baccin, wanda sima ya hadu sosai, kanta a rufe yake tana hawaye har aka zaunar da ita a bakin gado. Yan uwan ta suka karai mata nasiha sannan sukai mata ban kwana suka tafi. Bayan tafiyarsu daga ita sai su Rukky, Najwa, da Aisha wanda daga baya falo suka sauko dawo, wajen karfe takwas sukaji an bude gate, wanda sai gaban Maryam ya fadi, tsoro fargaba ya kamata yau gata a gidan auren ta a karo na biyu, waccan karan da ango bai shigo gidan nasa ba, wannan karon ma sai tsoro ya kamata kada abinda ya faru waccan karan ya sake faruwa, ido ta runtse tana jiran taji me zai faru. Sallamar sa taji cikin muryar sa mai dadi da sanyi, Yaa Farouk biye dashi da Yaa Abubakar wanda yake aboki ga Yaa Aliyu, sai Yaa Alkasim amsawa sukai suka shiga, Yaa Farouk ya ajiye ledojin hannun sa, tana ji Yaa Haidar ya zauna a gefen ta, bayan sun gaisa Yaa Abubakar yai nasiha sosai sannan ya rufe da musu addua. Tin sallamar Yaa Haidar bata karajin bakin sa ba, har sai da suka gama suka mike zasu tafi ya kalli Najwa yace "Ina Abdul din?" "Yaya a gida zan kwana ne." "Ok sai Farouk ya ajiye ki ke da Rukayya, Alkasim kuma ya dauki Aisha, Abubakar kuma sai ka tafi gida kai tsaye dan ban rike ka ba kada Aunty tace ni na rike mata miji." Duk sukai murnushi ya mike ya tafi rakasu, tana ji suka fita aka rufe gate sannan ya shigo ya rufe kofar falon, kanta a kasa taji tafiyar sa, tana ji ya karaso inda take wanda kamshin sa ya cika mata hanci, ba tai aune ba taji ya bude mayafinta ya shigo da kansa ciki. Hannu yasa ya tallabo ta ta fado jikin sa, idonta rufe cike da kunya. A hankali yake mata magana "Kinyi kyau Matar Haidar." Sake runtse ido tayi tana jin wata irin kunyarsa tana karuwa a zuciyarta. Ya dago kanta tare da matso da bakinsa kusa da nata ga hancinsu yana gugar juna "Ko na daukeki ne?" A hankali ta bude ido suka sauka cikin nasa. Murmushi tayi masa wanda yaji gaba daya ta hargitsa masa lissafi. Hannun ta ya kamo ya dago ta, hannun ya kama suka fara tafiya har suka karasa dakin ta sannan ya sake ta yace "Kiyi alwala kafin na dawo" Da sauri tayi cikin bandakin ta dauro alwala, ya bita da kallo yana murmushi, bai jima ba ya dawo dakin, sanye da kayan bacci sky blue, riga da wando, sallaya ya dauka ya shimfida masu sannan ya nuna mata kan sallayar mikewa tayi ta tsaya a bayan sa ya tayar da sallah, lokacin da ta fara jin kira'ar sa ido kawai ta lumshe dan har tsigar jikin ta taji tana tashi, yadda yake karatun cikin tajwid yana bawa ko wacce harafi hakkin sa. Raka'a biyu suka yi sai shafai da wutri sannan ya shiga jero addu'a da larabci kamar bazai dena ba. Bayan ya kai karshe suka shafa ya dawo gabanta ya dafa kanta ya sake wata sannan ya tashi tare da kamo hannun ta, falo suka fita, ya dauko ledar da suka shigo da su, kitchen ya shiga ya dauko cup da plate bayan ya wanke ya fito. "Yau komai yiwa amarya ake ko?" Shiru tayi tai kasa da kan ta. Ya bude leda ya dauko wani park wanda snacks ne a ciki, meat pie, spring roll, samosa, cake ko wannen an masa column dinsa, sai wata leda da kaza ne a ciki ya dauko ya juye a plate, sai wani pack wanda kayan ciki ne aka musu wani gashi mai ruwa ruwa yaji kayan kamshi dai kamshi yake, sai kalolin lemo da madara da youghurt. "Bismillah.' Kai ta girgiza dan ji tayi duk a takure take, murmushi yayi, dago ta yayi daga inda take ya daura ta akan cinyar sa, ya dago kanta yana kallon ta yace "Yanzu fa na zama mijin ki, sirrin ki majibancin alamuran ki, wanda zan kasance komai naki, bana son wannan kunyar ki ajiye ta gefe ki kula dani kawai, ina son kula ina son soyayya dan haka dole ki ajiye wannan kunyar kinji?" Ta rausayar da kai gefe guda tana kokarin zillewa. "Idan bazaki ci ba nima haka nake so kinga sai mu shige daki abun mu akwai abubuwa da yawa a gaban mu." Baki ta turo tace "Uhmm zanci mana yunwa nake ji." "Good girl." Ya janyo abubuwan tana kan cinyar sa ya dinga bata, sai da taci sosai dan bata wani ci abincin kirki ba tin safe da suka dawo ma lemo kadai ta sha ita ta shiga wanka da shirya. Bayan sun gama ta mike dan kwashe abubuwan ya mike yace "Yau ni zan komai." "A'ah Yaya gani wane aiki zakai kuma." Ta amsa ta nufi kitchen din wanda yake biye da ita a baya sauran abinda basuci ba ta saka a firij, juyowar da zatai sukai karo ya taro ta a haka suka fito tana jikin sa. "Sai soyayya ko?" Ya fada yana kallon idon ta, kanta ta kawar tace "Nifa bacci nake ji Yaya bari na tafi daki na na kwanta." "Menene kuma dakin ki, dakin mu dai, ki sani ban yadda da wai dakin ki ko dakina ba komai nawa yanzu ya zama naki kamar yadda komai naki ya zama nawa dan haka daga wancan part din har wannan dukka dakin mune kin gane?" Kai kawai ta gyada yace "To yau a wanne zamu kwana?" Inda aka fara kai ta ta nuna yace "No zo muje can ki gani. *** Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga mama guyn sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono). Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji. Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata. Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 *** *Allah mana rahma ya yafe mna, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin* *Antty* [12/10, 13:41] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 81 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Hannunta ya kama suka tafi. Ni'imtaccen kamshi da sanyi ne suka doki hancinta. Ba karamin burge ta dakin yayi ba, suna shiga ya saki hannun ta ya shiga bandaki, gefen gado ta zauna yana fitowa ya nufi wardrobe din sa wasu kayan bacci ya fito dasu masu shege kyau akan gado ya ajiye. Dagata yayi yace "Bari na shirya matata." Kafada ta make, ganin ta kasa sakewa ya mika mata rigar yace "Shikenan ki shirya bari na baki waje minti biyu." Ya fada ya juya ya bar dakin. Rigar ta d'aga ta juya ta kara juyawa, da kyar dai ta saka, ta dauki mayafin ta ta rufe jikin ta. Yana shigowa yai arba da ita, takure waje daya, dan murmushi ya saki tare da lumshe ido ya karasa ya rumgume ta, hawaye ne suka soma fita daga idon ta saboda tina irin wannan makamanciyyar ranar da ya shude wanda a lokacin baya ta kasance cikin zumudin tarbar Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, ranar farin cikin su, a ranar ya koma ga mahallacin sa, hakika duk abinda ya faru da ita jarabawa ce kuma ta sani sau'ki ne a rayuwar ta, da hakan bai faru ba da bata san yadda zatai rayuwa ba Yaa Haidar ba, amman da ta bar gida taje wani waje tai rayuwa ta samu sassauci daga abinda take ji na rashin Yaa Haidar tin da gashi a yau har zuciyar ta ta aminta da wani ta bashi gurbin soyayyar ta, sai dai ta sani ba zata taba mantawa da Yaa Haidar ba kuma ba zata taba daina masa addua ba, take taji zuciyar ta na kara rauni na tuna abubuwa masu yawa, sosai Yaa Haidar ya rude da ganin halin da take ciki, tambayar ta ya hau yi amman sam ta kasa magana sai hawaye dake zuba a idon ta, wata irin rumgume yai mata wacce take nuna tsananin so da kulawa ga abinda ake so, kansa dake wuyanta yana shakar wani kamshi da ya rasa wane iri ne ya gama cika masa ciki, sai furzar sa yake, ya dago yana kai bakin sa dai dai kunnen ta ido ya bude a hankali numfashin na sauka a cikin kunnen nata wanda ya fara haifar mata da wani irin yanayi, ido ta lumshe, kan ya fara magana cikin kunnen nata a hankali yana fadin "Kin tuna Aliyu ne? Addu'a ya kamata kiyi masa ba kuka ba. Kinji?" Wani abu taji yana wayo a jikin ta, ido ta runtse hawaye na cigaba da zubowa, tabbas ta tuna Yaa Haidar amman kuma bai kamata a wannan lokacin ba a wannan yanayin da suke ciki, so take tai masa bayani amman ta kasa ta gaza motsa bakin ta ma bare ta fada masa wani abun, ganin yadda take kukan yasa ya kwantar da ita a saman gadon yace "Am sorry i don't means to hurt you Baby, in barki ki ta begen Yaa Aliyun ko?" Mikewa tayi ta fada jikin sa tana wani kuka mai tsuma zuciya da tada hankalin mai saurare. Dole tayi kuka a wannan rana ko taji sauki a ranta, a wacan karon taso taga wannan tsayin daren tare da Yaa Haidar sai dai Allah bai ba, duk burin Yaa Haidar na irin wannan daren Allah bai nufa zai gani ba, dagota yayi yana kallon fuskar ta, kirjin sa ta kwantar da kansa ta zagaye shi da hannayen ta, "Bansan me yake damun ki ba da kike kukan nan haka ko duk akan Haidar din ne?" Saukar hawaye mai dumi yaji a kirjinsa tace "Yaa Haidar don Allah da gaske kana sona?" "Ashe duk yadda nake fada miki na ina sonki baki taba yarda ba tunda har kike kokonto Maryam ban taba jin son wata mace bayan Mami da Ummi na ba sai a kanki, ban ta'ba soyayya mai zafi ba sai akan ki, ke kadai nake so Maryam ki yadda dani kece kadai buri na da farin ciki na. Yes naso Maryam amman ita sai bayan auren mu, sai da naga yadda take da hankali da kyautata min, amman ke fa? Ranar da na fara daura ido na akan ki Allah ya d'auran son ki da kaunar ki, ina son ki, ina kaunar ki, ina bukatar matata, ina bukatar soyayyar ta, baki ba zai iya furta miki adadin irin son da nake miki ba. But my reaction in this nyt can tell u how much i love you." Ya d'ago kanta yana fuskantar ta kunya sosai a tare da ita, "A irin wannan ranar na rasa farin ciki na a baya wanda ban kara sanin zan samu wani farin cikin ba sai a yanzu Allah ya kara bani, ban ta'ba zaton zan kara son wani namiji ba sai gashi yau ni nake jin son ka har cikin rai na, ina tsoro kar na kara rasa ka Yaa Haidar." Allah Sarki, tausayinta yaji ya kama shi sosai har tasa zuciyar sa raunana ya hanata karasa maganar ta hanyar da yasan dole tayi shiru, shine ya hade bakin su waje daya, sai da ya gama kissing dinta ya sanya yatsansa a saman bakinta. Tana kallonsa da fuskarta mai hawaye "Ko wannen bawa da irin tasa kalar kaddarar insha Allahu sai munga ya'yan mu da jikokin mu, sannan zamu mutu, kuma insha Allahu tare zamu tafi ki bar kukan nan ba zan tafi na barki ba kinji?" Wata rumguma tayi masa, a kunnen ta yace "You are the only *Matar Haidar* anan duniya da gidan aljanna insha Allah!" Ya fada yana kwantar da ita akan pillow yana kallon fuskarta "Ina son na samar miki abinda kika rasa, Ina so na zama farin cikin ki. Ina son wannan burin naki ya cika a yau da gobe da har abada, a yau nake so ki kara sanin yawan son da nake miki, a yau zan tabbatar miki da cewa ke dai ce wacce nake so, ki yadda dani." Maganganunsa sun sanyaya mata zuciya. Har ta tsaya kallon sa tana mamakin wai wannan shine Yaa Haidar din ta miskili, mai tsare gida, anya kuwa. Rakwafowa yayi kan ta tare da riko fuskata a tafin hannuwansa ya matso da ita daidai da tasa yana mata wani irin kallo, wanda yake aika mata da wani salon sa take jikin ta yai sanyi, tsigar jikin ta ta hau tashi, ido ta runtse dan abinda take gani ya girmama a cikin zuciyar ta. * 5:30am Ido ta bude a hankali wanda tana gama budewa taga Aliyu zaune a gaban ta ya zuba mata ido, da sauri taja bargon kan gadon ta shige tana mai jin kunyar sa, in akace mata Yaa Haidar zai mata abinda yai mata ba zata ta'ba yadda ba, hakika ta yadda ta aminci da son da Yaa Haidar yake mata, domin ya nuna mata, ya bata zallar soyayyar sa, ya bata kansa da duk komai nasa, murmushi yayi ya hau ya janye bargon yana fadin "Morning sweet heart, kin tashi lafiya, na kasa tashi na barki Baby, a gaskiya naso nai asara da Muhammad ya same ki da nayi asarar da ban ta'ba yin irin ta ba a rayuwa, shin me ya hana tin da kika haifi Haidar bance a daura mana aure ba, gaskiya na bar dadi a baya amman ba komai zan fanshe abu na." Ido ta runtse dan wata irin kunyar sa take ji wanda shi taga babu wannan a wajen sa sam. "Mun makara fa Baby." Kai ta hau girgizawa tana fadin "Yaya lokacin sallar yayi ne?" "Oh duk wannan lokacin da muka debe muna shan soyayya kika rudani da salon ki kike cewa lokacin sallah yayi, to shida saura." Kukan shagwaba ta fara tana jujjuyawa yace "Wannan kin cika son kuka duk kukan da kika sha jiya bai ishe ki ba ko? Ko kina son dadi ne?" Da sauri ta rufe masa baki, tana mikewa ta shige bandaki, kan ta rufe ya shiga ciki. A can ma soyayyar su suka sha kafin ya dauko ta nade cikin towel ya fito ya ajiye ta akan gado sai kakkare jikinta take, fita yayi bai jima ba ya dawo dauke da doguwar rigar ta, shi ya saka mata yana fadin "Nifa kunyar nan a rage ta, haba haka ake, tin yaushe nace ki rage ta amman ke sai dadowa kike ko?" Kafada ta make, ya kama hannun ta shi ya jasu sallah bayan sun idar sukai addu'a sosai sannan ya juyo yana fadin "Allah Yayi miki albarka *Matar Haidar,* Yadda kike faranta min nima Allahu Ya bani ikon yi miki haka." "Amin, Allah bani ikon sauke hakkin ka da yi maka biyayya." "Amin *Matar Haidar,* Ummu Haidar da Maryam." Kai tayi kasa dashi ya mike ya dauke ta yace "Zo mu rama baccin mu ko?" Suka kwanta wanda gaba dayan ta a cikin jikin sa take, tana jin sa ya sanya hannayen sa yana massaging, kowace gab'a ta jikin ta a hankali Maryam jin yadda yake mata tausar a nutse cikin wani irin salo ya saka ta lumshe idanunta gabaki d'aya kasala ta saukar mata sai ajiyar zuciya take saukewa. Hannayensa taji daya saman kirjinta ya fara shafarsu a hankali yana lailaya kan cikin kwarewa, dayan saman cikinta yana mata tafiyar tsutsa yana shafowa daga cikinta zuwa marata had'i da tafiyar tsotsa. Daga jiya zuwa yau kawai ta gane Yaa Haidar yana son kirjin ta, jin hannayen sa na a saman marar ta yasa tai wata zabura tare da kamkame shi. Face d'insu ya had'e yana mai hade bakin su tare da bata wani lafiyayyen kiss, a hankali ya kamo harshen ta ya fara tsotsa kamar wanda ya samu alawa, still hannayenshi na jikin ta suna kara ruruta mata yanayin da take ciki. Bakinsa ya madai k'irjinta, wanda Maryam bata san lokacin da tai wani zullo ba tana kara turo masa kirjin ta, wanda hakan da tai ya kara susuta Aliyu ya shiga romancing nata da zafi zafi.... Sai da suka samu nutsuwa sannan ya kara janyo ta jikin sa yana kamkame ta kamar zai maida cikin sa, idon sa a lumshe bakin sa akan kunnen ta yace "Wallahi Maryam baki da maraba da budurwa a jiya na sha mamaki a yadda na sameki da ba dan a gaba na kika sauke cikin Haidar ba da nace ke din budurwa ce, abinda ya kara ban mamaki yadda na ji ki jiya haka ma yau, sai dai dadin har yafi na jiya, dan Allah Maryam da gaske kun tara da Haidar kafin ya rasu?" Hawaye ne suka hau zubo mata na jin dadin wannan yabo daga mijin ta hakika ko ba haka bane ya faranta mata balle itama tana jin da yadda ya shige ta, wanda itama ta ji jikin sosai, kuma yadda ya dinga mata kuka da sunbatu bata taba zata ba, harshen sa ya saka yana share mata hawayen tare da lallashin, ta wanda ya kara rumgume ta yana fada mata kalamai masu dadi da sanyaya zuciya, take bacci ya dauke ta shima take baccin ya dauke shi dan daga ita har shi a matukar gajiye suke. *Matar Haidar Fans group i really appreciate with ur love and support, i heart you all* *In naji ruwan comment anjima zan kara yi muku posting din second page.* 😂😂😂 *Kusa Yayan mu a addu'a Allah yai masa rasuwa jiya Allah ya jikan sa ya masa rahma ya haskaka kabarin sa ya raya abinda ya bari yasa can tafi nan amin* *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani amin.* *Antty* [12/10, 19:09] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 82 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Karfe sha biyu da rabi ya bude narkakun idon sa wanda suke cike da shauki da soyayyar matar sa, a hankali ya lumshe idanun nasa yana tuna halin da suka kasance a jiya da dazu, wata nutsuwa yaji wacce bai bata jin irin ta ba, a hankali ya fara bud'e idanunsa, ya sauke akan fuskar Maryam wacce take kwance a saman k'irjinshi. Murmushi ya saki tare da tura hannun sa cikin rigar ta, wanda a take ta bude idon ta akan fuskar sa, wani tsadaddan murmushi ya sakar mata wanda ya kashe mata gaban jiki, ya kama hannunta ya manna mata kiss, ido ta lumshe tana mai sakar masa nata murmushi. Idon ta a rufe taji ya janye jikin sa ya sauka, baya ta juya masa tana sakin murmushi ita kadai, ji tayi ya ciccibo ta gaba dayan ta yai sama da ita da sauri ta kamkame shi, dariya yayi yace "Ni fa ba yar dake zan ba Baby." Kanta ta daura akan kirjin sa tana me zagaya hannayen ta, ta bayan sa, a haka suka shiga bandakin ruwan d'umi ya had'a musu suka shige ciki luf abinsu ruwan na ratsasu, take ta fara jin gajiyar da ya saukar mata na sauka, jin hannun sa taji yana kara lallubar ta yana shashshafa ta, kukan shagwaba ta saki dan wata yunwa take ji, nan ya rikice yana tambayar ta menene tare da lallashin ta, kamar zatai kuka tace "Yaya yunwa nake ji." Bakin sa ya tura mata cikin bakin ta, ai kuwa ta kama tana tsotsa, sai da ta sha sosai sannan ya zare bakin, wanka sukai suka fito. Lokacin har sha biyu tayi, dakin da aka kai mata kaya yaje ya d'auko mata wata atamfa dinkin riga da siket ne, tana gaban mirrow tana shafa mai ya shigo ya ajiye kayan akan gado yana fadin "A'ah wannan aiki nane." Tai murnushi ya amsa ya shafa mata da kansa ya saka mata kayan, dinkin riga da siket ne yai mata kyau sosai sun zauna a jikin ta das, shima ya shirya cikin brown kalar shadda ya dauki turaren sa mai dadi ya musu barin sa, wayar sa ya dauko ya kunna tare da daukar Maryam suka fita a dakin, falon suka nufa ya ajiye ta akan kujera yana fadin "Bari na samar miki abinda zaki fara ci ko Baby?" Mikewa tayi tana fadin "A'ah Yaya bari na shiga na girka mana." Kamo ta yayi ya zaunar yace "Ina kika taba ganin amarya da girki?" "Yaya yan mata ne wadan nan ai." Durkusawa yayi a gaban ta yace "Nima matata budurwa ce." Tai murmushi, ya sakar mata kiss a kumatu sannan ya mike yai hanyar kitchen, knocking yaji ana yi ya dawo yace "Bari naga waye." Ya nufi can main falo inda kofar take, budewa yayi yaga Baba Mai gadi ne, tsaye hannun sa rike da katon basket, rissinawa yai ya gaishe shi, ya amsa ya mika masa basket din yace "Tin dazu Farouk ya kawo yazo yana ta knocking kila baku tashi ba." Hannu Yaa Haidar ya sa ya amsa yana fadin "Mungode Baba, bari na kawo maka naka." Ya juya yai ciki, a tsakiyar falo ya ajiye kayan abincin yana fadin "Kinga Ummi ma da kan ta ta aiko da abinci saboda kada wahala tai wa 'yar ta yawa ga ta d'an ta ga ta girki." Fuska ta boye a jikin kujera tana jujjuya kai, ya zauna kusa da ita ya jata jikin sa ya dago kan yana kallon kyakyawar fuskar ta, ido ta lumshe dan ba zata iya kallon wannan abun na idon sa ba, bakin sa taji cikin nata yana kissing dinta, itama biye masa tai dan yadda yake shan bakin nata kowa akaiwa irin haka sai ya bada kai, sun dauki sama da minti goma suna kissing junan su. Rumgume take a jikin sa, kamar zai maida ta cikin sa, dauko ta yayi ya ajiye kan center carpet din dake kasa, ya shiga ya kwaso cups da plate, basket din ya janyo ya dauki flask din tea ya ajiye ya bude dayan wormer soyayyen dankali ne da plantain da kwai, sai dayan da aka zuba farfesun kayan ciki, dayan kuma wainar shimkafa ce a ciki, dayar kuma miyar wainar ce wacce taji naman kaza da na kasuwa sai kamshi abincin yake. Baba Mai gadi ya zubawa yaje ya kai masa sannan ya dawo ya zuba musu a plate daya, ya fara bata ruwan tea tana sha shima yana sha a haka suka karya sosai Maryam taci abincin dan wata yunwa take ji, Yaa Haidar ma ba laifi yaci amman ba da wani yawa ba, bayan sun gama ta mike dan kwashe kayan hannun ta ya kamo yace "Amarya bata aiki." Fuska ta shagwabe tace "Shikenen ni zan samu ladan ba." Ido ya lumshe tare da sauke su akan ta yace "Lada zaki samu zo nai kissing naki shima ladan zaki samu." Ya janyo ya jikin sa, zamewa tayi tace "Uhm uhmm mukai kayan sai na taya ka ko?" Ta debe plates din da cups shi kuma ya dauki basket din suka shiga tare suka wanke abubuwan tana wankewa yana dauraye wa, bayan sun gama ta goge su ta jera a ma'ajiyar su. Daukar ta yayi suka koma falo, tana murmushi tace "Yaya wai bani da nauyi ne?" "Kamar Haidar nake dauka haka nake ji." Tai murmushi tana fadin "Tab Allah ban yadda ba." Ta fada tutturo baki da bubbuga kafa, kallon yadda take shagwabar yai abun yana burge shi ya sunkuyo wajen kan ta yana fadin "You see, Haidar ma ba zai haka ba, amman ace Ammin sa ce take haka." Jikin shi ta shige tana fadin "Ni da ni dai ku daina cewa Haidar yafini abu d'an yaron nan." Ya rumgume ta yana fadin "I love you My Hayyatie" "I love you more Hubby nah." Tana jikin sa yana dan massagiing nata suka jiyo kiran sallah, har sai da aka idar da kiran sannan sukai addu'a ya dauke ta sukai alwala, hijab ta dauko ya karaso ya tsaya ta bayan ta tare da rumgumo ta yace "My Noor zan tafi massalaci, daga can zanje gida bazan jima ba zan dawo.” Fuska ta shagwab'e ta juyo ta rumgume shi tana dan bubbuga kafa tare da fadin "Please Yaya ka tafi dani tsoro nakeji karka barni please kaji.” Ta k'arshe maganar tare da daura hannayen ta a saman kafadar sa, tana guntun hawaye, rikicewa yayi ganin hawaye a idon ta wannan yasa ya kamo lips din ta yana bata wani irin kiss mai sanyayya zuciya da duk gabban jiki, a jiki sa ta narke sai da yasan ya gama narkar mata da jiki ya zare bakin sa yana fadin "Baby ta karya mana alwala." Kanta ta kife a kirjin sa tana mai sakin murnushi, hannun ta ya kamo suka shiga bandaki wata alwalar suka dauro sannan suka fito, ya sanya mata hijab yace "Bari naje nai sallah sai na dawo mu tafi yayi?" Kai ta gyada tana mai sakin murmushi, ya mata kiss a kumatu ya juya ya fita ta mike tare da saka hijab din ta ta tayar da sallah, bayan ta idar ta jima tana addu'o'inta, sannan ta mike ta koma gaban wardrobe din ta wani less ta dauko wanda yake peach kala ne an masa sa'ka da maroon kalar zare yai kyau sosai duk jikin sa stone, dinkin riga da siket ne ta saka kayan sun zauna a jikin ta cif, turaren ta ta shafa ta murza hoda kadan ta saka man lebe ta dauki mayafin ta da takalmi ta fita zuwa falo tana mai jira Yaa Haidar. Tana zaune tin daya har biyu da rabi, wayar ta ta dauka ta fara neman layin sa, yana dauka taji muryar Inna na fadin "Ina ka baro Maryam din ita kadai?" "Inna yawo zan nayi da ita dan ai ta kallen mata?" Ya kai wayar kunnen sa yana fadin "Uhmm Baby na ya gidan?" Kukan shagwaba ta saka nasa tace "Shine ka gudu ko?" "No Baby ba haka bane, ki hakuri kinji yanzun nan zan dawo i promise you sannan in na dawo ba inda zan kara fita sai masallaci uhmm!" "Shikenan Allah ya tsare hanya amman ba ruwan da kai." Murmushi ya saki mai sanyi yace "In aka ganni za ai ruwan dani, bye i love you." Ya kashe wayar, Farouk da ya shigo ya saki baki yana kallon Yayan nasa da mamaki in akace masa Aliyu zai haka zai ce karya ne, ko da yake irin su Yaya daman in aka samu waje ai sai Allah. Ya shigo yana fadin "Yaya ango." Yana sakin dariya kasa kasa, hannun sa Yaa Haidar ya kamo yana zuwa gaban sa ya kama kunnen sa ya murde, "Tuba nake Hamma Dr, ya Antyn nawa?" "Dariyar me kake?" "Ba komai fa." Ya saki kunnen yana kallon Inna yace "Me zan kaiwa Maryam din Hajiya Inna?" "Ai ko na bayar ni ba kai zan bawa ba ita kadai zata ci." Ta shiga ta fito da leda ta mika masa ya amsa yace "To mungode Inna kinsan yanzu ai da ni da ita mun zama daya kinga kuwa komai nata nawa ne ko?" "Iyye Aliyu ni nake fadawa kun zama daya kana so kace min ka danne yar mutane ko?" Murmushi Aliyu ya saki yace "Nifa ba haka nace ba Hajiya Inna bari naje wajen Ummi." Ya juya zai fita, Farouk yace "Dazu fa Yaya nazo kawo muku abinci in ta bugu ba ku buden ba ko baku tashi ba?" Bai kula shi ba ya fice, dariya Farouk ya hau yi har da rike ciki yana fadin "Allah Inna nima auren nan zanyi kinga Yaya daga jiya zuwa yau ya canje, Hhhh kai Alhamdulillah." "Ai haka nake so in akace ba zai canja ba ina amfanin auren to, ni daman na dade da gane yana son yarinyar nan." "Kai Inna Yayan?" "Ban sani ba, me ka mai dani, muma fa a zamanin mu munyi soyayyar nan, Allah sarki Alhaji Allah maka rahma yasa kana Aljanna Allah ya hada mu a Aljanna gaba daya." Ta fada da dan guntun hawayen ta. "Amin Inna." * Suna gama waya da Yaa Haidar ta fara neman number Ummi ta kira bugu d'aya ta d'aga da sallama. Maryam ta amsa tana d'orawa da fadin "Ummi ina yini? Ina ta kewarki.” Ummi dake murnushi tace "Lafiya lou daughter nima haka, da fatan dai kuna lafiya, ina Yayan naki? Ina fatan ba wata matsala ko?" Sallamar Aliyu ta jiyo, Ummi ta amsa tana fadin "Kinga dan halak ana maganar sa sai gashi, shine ka baro min daughter ita ka dai a gida ko?" Ya zauna a gefen ta yace "Eh mana ai yanzu fada ta da ta kwace zan amshe abata tinda bata nan." Kukan shagwaba Maryam ta saka tace "Ummi ki kore sa kinji." "Yanzu kuwa daughter. Kinci abinci dai ko?" "Naci Ummi." "Yanzu za a kawo na rana kinji, kada ki wahalar da kanki." "To Ummi mungode Allah kara lafya da nisan kwana." "Amin. Me kike so yanzu fada min daughter." "Uhmm ba komai Ummi na." "Kin tabbata?" Kai ta gyada tace "Eh." "To masha Allah, ayi ta hakuri kinji daughter." "Insha Allahu Ummi nagode sosai." Sukai sallama. * Su Najwa ne suka shigo dakin suna fadin "Ummi gidan Aisha zamu mun fasa na Maryam." "Ah saboda me?" Yaa Aliyu suka kalla sukace "Kawai." "To ita daugther fa?" "Ma je wata rana." "Shikenan sai kun dawo amman da in kuka je zataji dadi, ina abincin nata to?" "Yaya ya amsa." Aliyu ta kalla, ya dauke kai yana danne danne har suka gama suka fice, Ummi ta kalle shi tace "Aliyu ba dai kai ka hana su zuwa ba ko?" "Ummi me zasu je suyi mata yanzu fa zan koma." "Kada ka kara Aliyu kada ka hanata zumunci da yan uwanta kaji ko?" "Naji Ummi bamu gaisa ba, ina yini?" "Lafiya lou ya Daughter ta? Da fatan kana kular min da ita?" "Sosai ma Ummi, masha Allah." "Ina Haidar?" "Yana sama wajen su Fadima." "Ok." Ya mike yace "Bari mu gaisa sai na tafi." Yai sama acan ma suka gaisa suna fadin ya Maryam ko da yake yanzu ta kira su muka gaisa, Haidar ya dane Yaa Haidar yana fadin "Abbi yanzu Adda ta kira na gaishe ta, Abbi yaushe zaka kaini wajen Adda, Ummi tace, wai sai dai akai ni wajen ta." Ya dauke shi suka fita, Ummi ya sama a kasa yace "Ummi a bamu kayan Haidar sai mu tafi." Hannu ta mikawa Haidar ya tafi da sauri tace "Yanzu ba zaku bar min Haidar ba daga kai har Maman shi kun tafi shima dauken shi zakuyi?" "A'ah Ummi kiyi hakuri." "Ba komai in kuna son d'an ku zan baku amman kunga yanzu yaushe kuka tare kuma kaga kai aiki ita makaranta abun zai mata yawa ka bari tinda sun kusa gamawa sai ku dauke shi, in kuma lokacin an samarwa Haidar kani ko kanwa ne shikenan." Murmushi yayi ya mike yace "Bari na shiga wajen su Mami." Ya kalli Haidar yace "Maza jeka wajen Uncle yana dakin Inna ya kai ka ya siyo maka chocolate." Tare suka fita shi ya nufi wajen Inna shi kuma wajen su Mami. * Maryam bayan sun gama waya, Najwa ta kira, Najwa dake driving ta saka wayar a handfree tace "Amarsu ta ango." "Ina kuke ne ina ta zuba ido shiru haka ake dan Allah ai kwazo kunsan zan bukace ku ko?" "Waye zai zo gidan ki Maryam?" "Kamar ya?" "Yanzu fa mun shirya zamu zo Yaya ya ganmu wai ina zamu, muka ce gidan ki wai a'ah mu bari sai wani lokacin yanzu shima zai koma. To kinga me zamu zo muyi shiyasa muka canja akala mukai gidan Aisha." "Ai shikenan kun kyauta." Ta kashe wayar, tana mai mikewa dan ta gyara gidan tin da ya tafi ya barta dakin sa ta shiga ta fara gyarawa ta canja zanin gado ta saka turaren wuta haka ta gyara dakin ta, da dayan dakin, dukka falon ma haka ta gyara ta saka turaren wuta, bayan ta gama ta kunna kayan kallo ko sa debe mata kewa. * Karfe uku da rabi da minti bakwai ya shigo unguwar wanda yai dai dai da kiran sallah da ake a massalacin dake kusa da gidan shi, parking motar sa yayi anan bakin gate ya fito ya nufi massalacin ya zauna yana tasbihi har aka tada sallah suka hada sahu sukai sallah, sai da ya idar da sallah ya fito motar sa ya shiga mai gadi da lokacin shima ya dawo daga massalaci ya bude masa gate take ya cinna hancin motar ta shiga cikin katon farfajiyar gudan nashi wanda zata dauki a kalla motoci sama da guda shida gashi an kawata farfajiyar da shuke shuke masu kyau wanda suka karawa wajen kyau da sanyi. Maryam ma dake kallo kiran sallah yasa tai dakin ta bayan ta idar ta kara gyara fuskar ta wannan karan har da jan baki ta kara shafa turarukan ta masu dadin kamshi ta dawo falo ta kwanta akan kujera, bata jima da kwanciyya ba ya shigo bakin sa dauke da sallama, amsawa tai tana kallon sa, kayan hannun sa ya ajiye ya buda mata hannu, a hankali ta tashi, tana tafiyar ta mai daukar hankali ta karasa wajen sa ya rumgume ta yana daga ta sama sukayo cikin dakin, akan kujera ya ajiye ta yace "Sannu da zuwa Yaya." "Yauwah My Noor ya gida?" Kukan shagwaba ta fara tace "Shine ka gudu ka barni....." Bai batar ta ta gama maganar ba ya hade bakin su yana aika mata da wani zafaffan kiss, wanda tini tai lukum da ita sai da ya mantar da ita batun sannan ya dago ta ya matse ta a faffadan kirjin sa, wanda kamshin junan su ke ratsa jikin su da ruhin su, "Kina jin yunwa ko?" Ya rada mata cikin kunnen ta, kamkameshi tayi jin yana sauke mata numfashi a cikin kunnen ta, kansa ya janye ya kwantar da ita ya dauko musu kayan da ya shigo dasu, abincin da Ummi ta bawa su Najwa su kawo mata ne sai fruits din da ya siyo musu a hanya bayan ya ajiye ta ya dauki ledar yai kitchen tare suka gyara friut din sannan suka dauko plate, a jikin sa ya zaunar da ita yana bata abincin shima yana ci har suka koshi suka fara shan fruit din da ta hada musu. Bayan sun gama ta kwashe kwanunkan ta wanke su ta dawo falon zata zauna a gefen sa ya miko mata hannun sa ya saka ta a cikin jikin sa yana fadin "Indai daga ni sai ke ne, nan ne wajen zaman ki kinji?" Ya fada yana tura kan sa 'kansa wuyanta yana shakar kamshin turaren ta mai dadi wanda yake kara fuzgar shi yana kara masa wutar sha'awar kasancewa da ita. "Baby wanne turare ne wannan?" Gaban ta ne ya fadi, dan Yaya Fadima ce ta bata shi, murya a sanyaye tace "Me turaren yayi?" "Ya min dadi." "Humra ce." "Uhmm so sweet i like it." Ya sakar mata kiss a wuyanta wanda take tsigar jikin ta ta tashi. Haka suka wuni manne da juna yana bata wata irin kulawa tamkar zai maidata cikin cikinsa, Maryam kuwa sai kara shishige masa take tana sakar masa shagwab'a, wacce take kara masa shiga wani yanayi yana nan nan da ita, suna a wannan halin akai kiran sallah magariba, tare suka shiga daki yai alwala ya tafi massalaci ita kuma ta tada sallar ta a daki, bayan ta idar ta zauna tana azkhar da lazumi ta dan ya fada mata sai yayi isha'i sai shigo gidan. Bayan ta idar da sallah isha'i ta mike ta shiga tai wanka ta fito daure da towel, bangaren da aka ajiye mata yan kananun kayan ta ta nufa dan dauko wanda zata saka, dan duk da an mayar wa da Muhammad lefe sunce ta rike amman Abbi yace sam ba zasu amsa ba, to wannan yasa Ummi ta shiga kasuwa da kanta ta siyo mata kananun kaya masu kyau da tsada haka, daman lokacin bikin sun mata dinkuna masu yawa. Rasa wanda zata dauka tayi, sam bataji sallamar sa ba sai ji tayi an rumgume ta ta baya, firgita tayi, ya saka kansa a tsakanin wuyan ta yace "Ya dai My Noor." "Ka ban tsoro Yaya." "Tsoro kuma? Duk sallamar da nayi tunanin me kika tafiyi?" "Na rasa kayan da zan dan saka ne." Tai maganar cikin shagwaba, Kamo hannun ta yayi ya ajiye ta akan gado ya juya ya nufi gaban wardrobe din kayan ya dinga dauka yana kallon sitikan kayan dake jere a haka idon sa ya sauka akan wasu wanda ya kasance mini siket ne da yar karamar riga red colour ne, su ya dauko ya karaso ya ajiye ya dauko mata pant da bra duk ya kawo yace "To na zabo miki." Ta dago tana kallon kayan wata kunya taji ta kamata tace "Nifa basu zan sa ba Yaya." "To ni su nake so ki sa min." Ya dauko pant din nata yace "Tashi ki saka." "Uhmm Uhmm Yaya ni bani zan saka da kai na." Kai ya girgiza yace "Ni zan shirya matata." Dan dole ta hakura ya saka mata, haka a wajen saka bra ma, tana ganin yadda yake kallon kirjin ta har sai da ya tsotsa ya samu yar nutsuwa ya saka mata kayan wanda ba karamin kyau sukai mata ba, gashin kan ta ya zare wa ribom din ya sake shi ya sauko har bayan ta, yana fadin "My Baby u look so take away, wallahi da zan iya hadiye ki da na hadiye ki." Jikin sa ta fada tana rufe fuskar ta, dan wata kunyar sa taji gani take kamar ba Yaa Haudar din nan bane mai tsare gida wai shi ke mata wadan nan abubuwan, dago ta yayi yace "Dago na kara kallon ki My property!" Ya dago ta yana kallon ta tin daga sama wacce rigar iyakar ta cibiya ta sai siket din da kungun ta ya bayyana sosai iyakar sa cinyar ta dogayen fararen cinyoin ta duk a waje, gaban mirrow yayi yana fadin "Ina turaren nan yake?" Kwalbar da yake ta nuna masa kwalbar ma kanta abar kalla ce ya dauko ya zuba a hannun sa ya fara shafa mata a wuyan ta zuwa cikin ta da cinyoyin ta, daga baya ya dauke ta suka fita falo, TV ya kunna mata ya juya yace "Five minute." Ya shiga daki wanka yayi shima ya shirya cikin three quartern wando da riga armless yayi barin turare, yana fitowa ana knocking karasawa yayi wajen ta yai kissing nata a kumatu sannan ya nufi babban falo, yana budewa yaga Farouk ne, "Ranka ya dade Yaya Angon Anty Maryam." "Farouk wai yaushe na fara wasa da kai ne?" "A'ah Yaya nifa auren nan nake so, dan dana san da kai za ayi da tini nima zance ayi." "Tinda ga sa'an ka ko?" "Ah haba ni na isa Yaya, ina Auntyn tawa?" "Bacci take." "Shikenan agaishe min da ita kan nazo cin abincin amarya." Juyawa Aliyu yayi yace "Sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." Ya juya yana dariya kasa kasa. Yana shiga ya ajiye kayan abincin ya nufi wajen Maryam ya dago ta ya rumgume yana bata wani kiss sai da suka dade a haka sannan ya zuba musu gashin kazar da Ummi tai musu da kayan ta wanda taji kayan hadi sai kamshi take, ita kadai suka ci, sannan suka shiga suka wanke kwanukan, falo suka koma suka kara makalewa juna Yaa Haidar na kara rikirkita Maryan da salon sa. *Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe Amin.* *Antty* [12/11, 09:46] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 83 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Kwanan su Yaya Fadima biyar suka zo gidan Maryam, ranar Aliyu yini yayi a takure sai ta kai masa abinci ko wani abu yake samu ya dan rike ta ya dan tsotsotse ta sannan ya bar ta da kyar, sai yamma suka tafi wanda washe gari suka daga Kano ta dabo ko da mai kazo an fika. A haka suka kwashe sati biyu suna shan amarcin su, a cikin sati biyun nan ba karamin kulawa da tarairaya Maryam ta samu a wajen Yaa Haidar ba, dole ta sake take biyewa Yaa Haidar suke shan soyayyar su, soyayya suke mai tsafta da fahintar juna kowa na son kowa kowa na son faranta ran junan su, yadda suke soyewa sam baki bazai fad'i irinta ba, dan wata irin soyayya sukewa junansu, kamar zasu cinye junansu soyayyace mai cike da kulawa da tattalin juna. A haka suka cinye sati biyun hutun sa, ranar Monday tin asuba bata koma ba dan tasan ranar zai fara zuwa aiki itama kuma zataje makaranta, tsaye take a kitchen sanye da wani wando iyakar sa cinya sai yar vest wacce bata da hannu, kanta sanye da hula fara tas, tana ta hada-hadar musu breakfast, wanda shi kuma Yaa Haidar shigowar sa kenan daga massalaci sanye da jallabiya milk kala ya ji ta a kitchen, kitchen din ya karasa ya shiga da sallama, ta amsa tana fadin "Welcome Honey." Ya karasa ya rumgumo ta ta baya yace "Morning Noor ya aiki? Yau na barki da aiki ko?" "To ya za'ai tinda fita zamuyi." Suyar ya amsa yace "Kawo na karasa aiki na." Ta sakar masa tana komawa bayan sa ta saka hannunta ta zagaye kugun sa, ta saka kanta a bayansa, "My Noor ni dai ji nake kamar na bar aikin na mu cigaba da zaman mu a gida." Sakin sa tayi tana dariya tace "Kai Yaya kaga daga nan nima sai kace na ajiye karatun ko?" "Allah Baby da ace karatun ki yafi shakara daya da hakura zaki dashi." Ido ta zaro tace "Kai Honey." "Allah da gaske nake." "To yanzu dai a barni na karasa ko dan na cika burin Yaya da ni kaina ko?" Ya juyo yana binta da wani kallo, da sauri tai kofa tana dariya hadi da fadin "Karasa bari na gyaro daku nan kada ka makara." Sam Maryam bata da nawa kuma daman dakin ba wani datti yayi ba tana shiga ta gyara ta turare shi ta fito tana gyara falon da shima ba dattin da yayi, tana cikin mopping taji ya daga cak yayi hanyar bedroom din su da ita, "Yaya ban gama aikin ba fa." "Muje kiyi wanda yafi shi samun lada, Allah yau ni kadai nasan irin missing din ki da zanyi." "Haba Yaya awa nawa ne?" "Ke kike ganin haka." Ya fada yana dire ta akan gadon tare da hayewa kanta. 8:30am Tsaye take yana saka mata kaya sai turo baki take ya dago ya kamo bakin yana kissing nasa, wanda ya dauki minti wajen uku yana kissing bakin nata kafin ya saki, tace "Uhmm ina fushi ka makarar damu shine kake son kara wani laifin ko?" "Allah My Noor bana gajiya dake, kiyi hakuri danasa kika makara kinji?" "Kai Honey nifa da wasa nake in kana son ka dada mu koma mana." Riko hannun sa tayi zata jasa, ya janyo ta yana murmushi yace "A'ah zo muje mu karya sai mu tafi." Suka fita falo a cinyar sa ya daura ta suka karya ta kwashe kayan ta wanke sannan ta fito ta dauko mayafin ta kato mai dubu ta fito, Aliyu dake zaune ya dinga bin ta da kallon har ta karaso tace "Yaya ya dai?" "Ina zaki a haka?" Kallon kanta tayi, cikin kamilar shigar ta doguwar riga ce ta atamfa sai babban mayafin ta da jakar ta, kansa ta fada tace "Me shigar tayi?" "Hijab zaki saka." Ya janye ta a jikin sa yai cikin daki bai jima ba ya fito rike da brown kalar hijab din ta kalar atamfar ta, ya mikar da ita ya zare mayafin ta ya ninke ya saka mata hijab, wani kyau yaga ta kara, mayafin ya dauka ya shigar dashi daki sai gashi rike da ba'kin abu, kallon sa take har ya karaso ya daura mata nikaf din tace "Oh Honey har da nikaf?" "Kinga yadda kike ne? Haka kurum ana kallon kaya na." Tai murmushi tace "Ba mai kallar maka fa ba Honey." "Yanzu ba da nai maganin abun." Ya kamo hannun ta ya dauki jakar ta da tashi suka fita shi ya bude mata sashen ta ta shiga tana sakin murmushi tare da fadin "Ina godiya Jarumi na." Murmushi ya sakar mata sannan ya rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fita a gidan, suna hanya ta kira Jawahir amman da yake suna lecture bata dauka ba sai text tai mata, a haka suka karasa makarantar yai parking ya kamo hannun ta tare da dage nikaf din fuskar ta, murmushi ya sakar mata yace "Give me bye bye kiss." Kan cinyar sa ta haye ta hade kansu ta kama lips din sa tana tsotsa, sam sun manta a inda suke karar da wayar Maryam tayi ita ta dawo dashi hayacin su, ya saki lips din nata ta lafe a jikin sa yana shafa bayan ta, wayar tata ce ta kara kara ta dauko shi kuma ya hau zuge mata zip din rigar ta tare da gyara mata zaman hijab din ta, wayar ta kai kunne, cikin kasallaliyar murya tace "Gamu a mota ki karaso." Ta kashe wayar tana kallon Yaa Aliyu da shima ke kallon ta cike da so da kauna, light kiss ta sakar masa a kan lips din sa tare da sauka a cinyar shi tana fadin "Ya dai Honey." "Kema kin sani." Tai murnushi dai dai zuwan Jawahir yadda su suka ganta tinda tint glass ne, ya sauke glass din, Jawahir ta gaishe dashi ya amsa yana fadin "Ga amanar Matata nan." Tana murmushi tace "Baka da matsala." Ya dauko jakar ta tare da zuba mata kudi a ciki yace "Baby sai munyi waya ko?" "Eh Yaya Allah ya tsare ya bada sa'a Allah ya kiyaye min kai, ka kula da kan ka." Hannun ta ya kamo yai kissing sannan ya saki ta kamo nasa itama tai kissing sannan ta bude kofar ta fita tana daga masa hannu, har sai da ya daina gano su sannan ya bar wajen, lecture goma suka shiga, goma da rabi taji karar shigowar sakon sa, ta duba tana murmushi ta mai da masa reply, basu fito ba sai da suka dauki awa uku sannan suka fito lokacin daya saura, material din karatu Jawahir ta bata ta fara koya mata abubuwan da akai na sati uku bata nan wanda karfe daya da rabi sukaje sukai sallah, bayan sun idar ta fito ta fara neman layin sa "Honeyyy!" Ta fada kamar zatai kuka. "Matar Haidar menene fadawa Haidar din ki uhmm" "Honey na gaji." "Sannu kinji dear sannu, ko nazo nai miki tausa?" "Uhmmm!" "Da gaske?" "A'ah Yaya muna da lecture biyu yanzu mukai sallah, sai hudu zamu fito." "Shikenan zan san yadda za ai na karaso kan hudu." "Yaya ba sai biyar kake dawowa ba." "Da da yanzu ai ba daya bane." Tai murmushi tace "To ya aikin?" "Ba dadi babu Baby na a jiki na i so much miss you." "I miss you more Honey." "Take care ki samu kici wani abun kinji?" Kai ta gyada ya kashe wayar, Jawahir tace "Wai yaushe kuka zama masoya haka ne?" "Idon matambayi." Tai dariya tace "Muje muci abinci." "Ke ni lemo kawai zan sha." "An dawo za a cigaba da rashin cin abinci ko? To wallahi Yaya Haidar zan fadawa." Tai dariya tace "Ina Yaa Muhammad kuwa?" Yana nan jiya yake tambayar ki nace baki dawo school ba." "Ina matar tasa?" "Suna na lafiya." Ta fada tana tabe baki. A haka suka gama suka shiga lecture sai karfe hudu da rabi suka fito, wanda yai dai dai da zuwan Yaa Haidar, waya yai mata ta fito, tare da Jawahir, mota ta shiga ta zauna yace "Jawahir kizo mu ajiye ki man." "Yaa Haidar hanyar ai ta baude nasan yanzu za a zo dauka ta." "Zo mu tafi ma hadu a hanya." Ta shiga motar suka dauki hanya sai da suka kusa gida sannan suka hadu da drivern nata ya taho dan ya zata sai biyar zasu taso haka suka rabu suna dagawa juna hannu. Hannun Maryam ya kamo ta juyo tace "Yaya ka kaini wajen Ummi dan Allah." "Yaushe?" "Yanzu." "Yanzu kuma Baby?" Kai ta gyada ya sa hannu yana shafa fuskar ta yace "Kiyi hakuri this weekend acan zaki yini amman yanzu mijin ki ke bukatar ki, kinga yadda kika gaji ma kuwa salon Ummi tace 'yar ta ta rame." "Wayo dai kawai Yaya." "Muje gida na nuna miki." A hanya yaga masu gashin kaji ya tsaya ya siya musu suka nufi gida. Shida saura kwata suka shiga gida, tin daga compound ya dauke ta sukai cikin gida, akan gado ya ajiye ta ya fara cire mata kaya shima ya cire suka shiga sukai wanka tare da dauro alwala kananun kaya ya saka masu kyau da tsada ya fesa turare sannan ya sumbaci matar sa ya tafi masallaci. Itama shiryawa tayi ta tada sallah tana idarwa ta shige kitchen. Abu mai sauki ta fara daura musu kan ai isha'i ta gama fried supergette wacce ta hada musu lemon kwakwa ta jere a dining, dakin ta ta shiga ta kara wanka ta shirya cikin wasu riga da wando wanda wandon iyakar sa gwiwa sai rigar da ta dan sakko ta baya ta rufe, gaban kuma bata rufe ba gata shara shara ana ganin abun da ke ciki ta feshe turare ta zubo da gashin ta gadon baya, gaban mudubi ta karasa tana kallon kan ta ita kanta tasan tayi kyau juyi tayi tana sakin murmushi tare da nufar falon nasu, tana fitowa yana shigowa bakin sa dauke da sallama, yana daura ido akan sa yai mutuwar tsaye, a haka Maryam ta karasa inda yake cike da tafiyar ta mai daukar hankali tana karasawa wajen sa ta rumgume shi, shima rumgume ta yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya dan yau kadai da ya yini a wajen aiki ba Maryam yaji wata kewar ta ji yayi kamar ba shi ba, "I miss you so much My Noor!" Ya fada yana hade bakin su, ido ta lumshe ya dauke ta ya dire ta akan kujera, a jikin sa ta lafe tace "Honey yunwa." "Muje muci abinci." "A'ah uhm uhmm!" "To me kike so?" "Ni Honey nake so." "Ni zaki ci?" Kai ta gyada yace "Taso na fara ciyar dake daga baya zaki cini har ki gaji" Hannu ta sa ta rufe fuskar ta tace "Ni fa ba haka nake nufi ba Honey yau na gaji sosai na jima ban shiga school ba sai naji abun daban." Ya kamo hannun ta yana fadin "Zo muci abinci sai nai massaging din ki." Haka ya sauko da ita yana binta da wani sihirtattacen kallo a haka sukaci suka koshi, yana jikin ta ta gama wanke wanke suka fito sukai daki, kwanciyya tayi yana mata tausa tare da mata hira mai dadi a haka ya fara sauya salon hirar tashi wanda Maryam ta bashi hadin kai har suka faranta ran junan su. Bayan wata hudu A ciki wata hudun nan abubuwa da yawa ya faru, wanda a lokacin Aisha ta haihu an samu namiji Yaa Alkasin ya saka masa suna Haidar, wanda bikin Rukayya da Yaa Ahmad ya rage wata biyu, sai Najwa dake turawa da kyar da tsohon cikin ta yau ko gobe. Rayuwar Maryam da Yaa Haidar rayuwa ce da suke yin ta cikin fahimtar juna da kaunar juna, Maryam akwai sanyin hali da hakuri, wanda Yaa Haidar ma akwai kawar da kai, a cikin wata hudun nan ba wani abu na bacin rai da ya taba gilma musu dan da daya yace daya yai masa abu a take zasu bawa junan su hakuri, basa taba kaura daga junan su basa taba raba wajen baccin su, su Mami, Ummi da kowa mamakin Aliyu suke domin Aliyu ya canja sosai a gaban kowa kula yake da matar sa, tare da tarairayar ta har mamakin Aliyu suke dan ko lokacin marigaiya matar sa bai mata haka ba wani so yakewa Maryam kamar ya maida ta cikin sa, soyayya suke zubawa wacce samun irin masoyan yake da wahalar samu, gaba daya sun gama macewa akan son junan su, sun yadda sun aminta soyayyar su daga Allah ce dan yadda suke son junan su sukan su har mamaki suke, Aliyu har mamaki yake bama a bangaren nuna kulawa soyayya ko rayuwar aure a baya sai ya kwashe sati biyu bai nemi matar sa ba amman a yanzu dakyar yake iya kyale Maryam ta yini ba tare da yaji sa a jikin ta yana shan ni'imar ta, wanda Ummi da kanta ta gane yadda Yaa Haidar ke matsa mata dan ko gida suka zo yini sai yasan yadda yayi ya lallatse ta ko ya tsotse a barsa, wannan yasa kullun take kara wayar da kan Maryam, ga kuma yan uwanta da kullum nasiha da bata hanyoyin kula da kanta da mai gidan ta yake, ta zama yar gata kowa ta tatta yake. A lokacin har sunyi semester daya sauran daya su gama karatun su, kuma auren sam bai bata matsala ba dan lokaci guda suka ware Yaa Haidar na koya mata karatu sam bata da matsala ga practical da wani lokacin in yana da aikin weekend take bin sa asibiti, kowa yaga Maryam da Aliyu sai sun burge ka tare da baka sha'awa. Likitocin asibiti masu harin Aliyu kuwa suna ganin Maryam cllasic lady suke raina kan su, dan bata da makusa ko kadan ga kyau ilimi da tarbiyya da nutsuwa kowa yaga Maryam da Aliyu sai sun burge shi sosai suka dace da junan. Maryam takara kyau tai haske ga jikin ta ba rama tai kubulbul da ita duk da ba kiba tai ba amman jikin ta ya murje kowa ya ganta sai ya so kara ganin ta haka Yaa Haidar ya kara kyau da cika kamar ba shi ba jin dadi da kula sun zauna masa arziki ya dada gaba rayuwar farin ciki mai cike da sha'awa suke gudanarwa. Duk wannan tsawon lokacin kullum shike kai ta makaranta ya dauko ta ko da bai gama aikin ba wata rana asibiti suke komawa ta zauna a office shi kuma yana aiki duk dagowa daya da zai sai ya sumbace ta ko ya rumgume a bar sa. * Zaune take a dakin Haidar karami dan yau gidan Ummi suka zo suka yinar mata, Haidar ne kwance akan cinyar ta, sumar kansa take shafawa tana mai jin soyayyar yaron a cikin zuciyar ta, kamar an tsikare shi ya mike ya nufi wardrobe da kallp ta bishi, har ya dauko abu ya dawo ya zauna a gefen ta yana fadin "Adda kinga." Dagowa tayi tana kallon abinda yake nuna mata, picture din Yaa Haidar ne wanda ba zata manta ba tin a gida da sukaje ya dauka, wanda har yanzu yake kallon picture din, kusan kullum sai ya dauko ya kalli Abbin nasa, bai san sa ba amman yanajin son sa sosai da sosai duk da karancin shekarun sa, baya fasa yiwa mahaifin nasa addu'a, bama da Maryam ta kasance na sashi yana yiwa mamata addu'a. "Adda kullum na duba mudubi sai naga muna kama da Abbi na, Adda har wannan abun fa." Ya fada yana nuna kumatun sa alamar dimple. "Adda." Ya katse mata tunani, kallon sa tayi yace "Adda da wannan Abbin nawa da Abbi na suna kama suma yan uwa ne?" Murmushi ta saki tana shafa kansa, yace "Adda ina son Abbi na dukka, Adda yaushe zani wajen Abbi na wannan?" Picturen ta karba ta kalla sannan ta mika masa tace "Haidar kana cigaba da yiwa Abbin ka addu'a a ko da yaushe, Abbin ka yana son ka, yana son ka tin bai san da kai ba, yana son ka tin baka zo duniya ba dan haka kaima ka so shi, soyayyar da zaka nuna masa kenan yi masa addu'a, ko da Abbin ka ba uba ne gareka ba, to Yayan mu ne, kuma yana son mu, bai son kukan mu. Kasan me?" Kai ya girgiza, rumgume shi tayi tace "Abbin ka ya kula dani tin ban kai ka ba." Dagowa yai yana kallon ta, kai ta gyada masa tace "A lokacin shi ke kaini makaranta da siya min kayan dadi kamar yadda Abbin ka ke maka." Murmushi ya saki yace "Adda ashe shima yana da kirki, shiyasa nake son sa Adda." Rumgume shi tayi tace "Yauwah my boy ka cigaba da son Abbin ka kaji, kana masa addu'a kaji kada ka taba mantawa da shi, kasan menene sakon sa a kullum gareka?" Kai ya girgiza yana kara lafewa a jikin ta, "Cewa yake kullum ki fadawa Ya'yan mu, ina son su, ki fada musu Abbin su na son su da kaunar su, mutumin da ke son ka tin kan kazo duniya shi kuma baya nan me za kai masa?" "Addu'a Adda, Allah masa rahma yasa yana aljanna, Allah ya hadamu a aljanna gaba daya." "Amin Amin Haidar." "Adda kika ce tin kina karama yake siya miki kayan dadi da kai ki school?" "Yes Haidar." "Lallai shima he is kind like my Abbi ko?" "That is why i love him Adda, i love you and My Abbi's." "We love you too Habiby." "Adda ki cigaba da bani labarin Abbi na kinji." "To Haidar." Ta fada tana jin wani abu a kasan zuciyar ta, hakika sai yanzu ta kara sanin mutuwa yankan kauna gareta, in ba da ba haka ba da tini ita da yaron ta da mijin ta suna tare, dan hawayen da ya zubo mata ta goge ta cigaba da bashi labari tana bashi yana mata tambaya shi kadai sai murmushi yake kamar yana gane komai da take fada masa. A haka Yaa Haidar ya shigo ya same su, ya tsaya yana kallon su, cike da so da kauna, jin son su yake har cikin zuciyar sa, bama Haidar jin sa yake tamkar d'an sa yana son yaron yana tausayin sa shiyasa yai alkawarin kula dashi har karshen rayuwar sa kuma yai alkawarin ba zai taba nuna bambamcin ba ko da Allah zai bashi ya'ya. Karasowa yayi ya zauna a gefen Maryam tare da rumgume su gaba daya sai a sannan suka san da shigowar sa, ta dago tana kallon su, ya sakar masa kiss a idanun ta yace "Mu tafi ko?" Kai ta gyada tana kara rumgume Haidar, dan wani iri taji a kasan zuciyar ta, ya amshi Haidar yace "Mu tafi tare?" Kai ya gyada ya dauke shi ya sauka a gadon, ya kalli Maryam dake zaune cike da damuwa yace "Taso mana." Ya fada yana mika mata hannu, kamowa tayi ta mike, Ummi suka sama a falo, ta kalle su tace "Daman ai nasan yau sai kun dauke d'anku." Kai Maryam tai kasa dashi tana murmushin yake, ta zauna tana fadin "Ummi ni ba ruwa na Yaya ne fa yace mu tafi dashi." "Sai kuje ai, Haidar tafiya zakai ka barni ko?" Kai ya girgiza yace "Ummi kwana biyu zanyi." Ya fada yana nuna mata da yatsun sa guda biyu, tai murmushi tace "To amana a kular min da yaro na." "Insha Allah." Suka fada sannan sukai mata sallama suka tafi, dan da kayan sa a can gidan. *Ehemm ehemm, kamar yadda jiya ma na fada yau ma zan kara fada dan jiya naga comment sosai shiyasa nayi shafi na biyun, to yau ma zan gani in har yanzu ana son *Matar Haidar* in kuma ba a so ma zan gani. Bye see u later amman fa in naga comment, in kuma ban gani ba sai gobe in Allah ya kaimu.* *Samira Malami, Amina Yar'addua, Aina'un Mardiyya, Zuwaira Zuzu, Ubaidah da sauransu i really appreciate, much love* *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe Amin* *Antty* [12/11, 18:21] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 84 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Kan su shiga gida har Haidar yai bacci suna zuwa ta kai shi d'aki ta canja masa kaya tare da masa addu'a, bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci, tana shirin kwanciyya ya shigo yana fadin "Me nake gani haka?" Ya iso ya dauke ta yana fadin "Wai me yake damun ki ne?" Ya fada yana ajiye ta akan gado, idon ta ne ya kawo ruwa, yace "Ba zan taba kishi da Yaa Haidar ba Maryam, amman wallahi in na ganki a damuwar ni kadai nasan me nake ji dan Allah ki fada min da me kike tina shi ni kuma in maye gurbin hakan." Murmushi ta saki tace "Yaya na i love u the way u re, a kullum in zan tuna da Yaa Haidar sai na tina da kai dan sanadin ka na ke raye cikin jin dadi, in Yaa Haidar ya kula dani a baya yanzu kai ke kulawa dani, in Yaa Haidar ya soni a baya yanzu kai ke so na, in na kasance da Yaa Haidar a da yanzu da kai nake tare, ka mayewa Haidar gurbin sa, dan haka ka sani kai kadai ke zuciya ta da tunani na dole na tina Yaa Haidar Yaya amman ba haka zai sa nace bana son ka ba, ina son ka, kuma in na tuna shin addu'a nake masa, please Yaya kada kai fushi ko kaji haushin sa akan haka, yau Haidar karami ya tina min da Abbin sa, kuma na kara sauke mata wani nauyi dake kaina, kai min alfarmar ko ya'ya muka haifa zamu sa musu soyayyar Yaa Haidar, dan suna masa addu'a saboda abinda yake so kenan." "Ya'yan mu na Yaa Haidar ne Maryam, kamar yadda Haidar yake nima 'dan na, dan haka na miki wannan alfarmar kuma nima zan kasance cikin masa addu'a Allah masa rahma ya kyautata namu zuwan." "Amin My honey." Ta fada tana shigewa jikin sa. Rumgume ta yayi tsam a jikin sa kamar zai mai data cikin sa yace "In nace nafi Yaa Haidar son ki zaki yadda?" Kai ta dago tana kallon cikin idon sa, wanda ba abinda take gani sai tsantsar son ta, ido ta lumshe tace "Ba Yaa Haidar Yaya dole kai ne me sona a yanzu fiye da kowa, ni na isa na karyata Yaya na bayan baka taba batan rai ba kullum kula kake bani kamar 'yar sa, abinda Innan Abbi na ta fada kenan nake ganin ta fada ne kawai cewar ina dacen masoya a lokacin ban san da gaske take ba sai a yanzu nake gaskatawa, hakika nagode Allah da ya jarrabcen ya kuma bani ikon cinye jarabawar har yai min canji da mafi alheri, Allah ya jikan Yaa Haidar, ya barni da kai har a aljanna Yaa Haidar, ina son ka ina kaunar ka kuma na yadda da duk soyayyar ka." Idon ta cikin nasa take maganar nan wanda yaji son ta da kaunar ta na kara ninkuwa a cikin zuciyar sa, goshin sa ya hade da nata inda hancin su ke gugar juna, ya kara yin kasa da fuskar sa bakin su ya hade da na juna, wani irin kiss yake bata mai ma'anoni da manufa da yawa, a haka ya cigaba da romancing nata tare da faranta ran juna su kamar ba ita ba ta zage suna shan soyayyar su. * Washe gari da safe, sam sun manta da Haidar baccin su suka hau yi, wanda Haidar ya farka wajen takwas, da kan sa yai brush ya fito falo, ya kunna kayan kallo ya kai mbc 3 ya zauna yana kallon cartoon, da yaji yunwa ya shiga kitchen ya nufi store ya dauko fresh yoo da biskit ya dawo ya zauna yaci ya koshi daga haka ya cigaba da kallon sa, wanda bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba, sai karfe goma suka farka, wanka sukai suka shirya sai da ta zata bude kofa ta tuno da Haidar karami da sauri ta fita ana fadin "Honey mun manta da Haidar." Ya fito da sauri yana fadin "Kuma ya tashi?" Suka fita a falo suka same shi yana bacci gefen sa robar fresh yoo da ledar biskit din da yaci, karasawa Yaa Haidar yayi ya dago Haidar yana rumgumewa Maryam ta nufi kitchen dan hada musu breakfast. Sai da ta gama suka zo ta je ta karai masa brush suka karya, a jikin su ya yini daga ya fada jikin wannan sai na wannan, da yamma Yaa Haidar ya dauke su suka je park, wanda daga can suka shige wani reaturant acan sukai dinner daga nan store sukaje sukai shopping sannan suka koma gida, haka the next day ma da yamma suka fita zaga gari sai dare suka dawo. Washe gari Monday suka shirya suka tafi aiki, bayan sun ajiye Haidar a makaranta, sai yamma Yaa haidar ya dauko Haidar sannan suka wuce suka dauki Maryam daga school, satin sa daya yace wajen Ummi zai koma wannan yasa suka mai dashi. * Yau sai shida zasu fito daga lecture wannan yasa tin kafin su shiga karfe hudu ta kira shi, lokacin fitowar sa kenan daga treater ya ji kiran nata dauka yayi yana fadin "My Baby." "Uhmm i miss you Honey." Wani sihirtacen murmushi ya saki yace "I miss you more ko nazo na dauke ki muje gida mu rage gajiyar dake tare da mu." "Da kuwa naji dadi." "Karatun fa." "Uhmmm Allah yaya na fara gajiya da ba dan burin ka bane da tini na ajiye shi na zauna na rumgume miji na ina samun lada, amman Honey kalla fa kaga yau tin safe har shida ban kara saka ka a ido na ba ban jini a jikin ka a uhmm uhmm ni wallahi i miss you Honey." Ta karashe maganar da sakin kukan shagwaba, da kyar ya iya bude office din sa ya shiga ya fada samman kujerar dake office din tare da sakin wata irin ajiyar zuciya ido ya lumshe hannunsa d'aya cikin sumar kansa, yana jin yadda tsigar jikin sa ke tashi na kukan da Maryam take masa wanda ba hawaye sai tsabar tsokana da son tada masa da hankali, A hankali cikin laushin murya ya kirata "My Noor!" "Uhmm Honey!" Tai maganar cikin zallar shagwaba, kina so nazo makarantar yanzu ko? Kin tadan hankali na ba abinda nake so sai kasancewa dake gashi na bada appointment da wani Babban mutum zai zo karfe biyar kina so na taho ne?" Ashagwabe tace "No honey amman ka sani i miss you so much." "Na sani Baby nima haka baki ji jiki na ba duk ba dadi na rashin ki, gaskiya in ba a canja muku wannan lecture ba zan na zuwa ina dauke matata sai na dawo da ita four din." "Uhmm" Ta sauke masa wani nunfashi duk da ba sa tare sai da ya sagar masa da jiki yace "Baby am sorry kinji sauran watanni mu huta ko?" A shagabe tace "Eh Honey i love you i miss you." "Miss you more me kika ci?" "Bana jin yunwa." "Hmmm ban yadda ba kije kici abinci yanzun nan kan ku fito zan zo daukar ki kan six kinji?" "Yes honey bye." "Bye." * Karfe biyar da rabi ya gama da asibiti, gida ya nufa cikin hanzari so yake kan six din ya karasa wajen Maryam. Karfe biyar da arba'in ya iso k'ofar gidansu ya fito a gaggauce ya shiga gidan yai bangaren Mami a tattsaye suka gaisa sannan ya fito yai bangaren Ummi. Lokacin daya shiga falon ba kowa, yana sallama kai tsaye ya nufi stair amman motsin Ummi da ya jiyo a kitchen yasa ya juya ya nufi kitchen din, a gaban sink ya gano ta tana wanke wanke kitchen din ya dumame da kamshi. "Ummi nah." Ya fada yana karasawa tare da amsa abin da take dauraye wa ya karasa wanke wa, tace "Dr ya kake ya gida? Ina daughter?" Murmushi ya saki yace “Lafiya lou Ummi, Baby fa Ummi tin safe dana fita daga gida ban k'ara komawa ba yanzu nan ne ma zanje na dauko ta yau six zasu fito, Ummi nasan ta gaji ba abinda zata iya in mun koma shiyasa nazo na amsar mana abincin Ummi." “Allah sarki My Daugther, Allah muku albarka, ai kune kunki mai aiki da kan ku koma ta rage mata wani aikin, yanzu ace kan ta fita sai tayi aiki, sannan ta dawo ace sai tayi aiki? Gaskiya dai Aliyu dole a samar mata mai aiki." Ta fada tana nufar wajen kwanukan ta dauko flask ta fara zuba masa abincin da tayi, vegetables rice tayi sai miyar da taji kaji sai hadin salad da zobo da ya sha kankana ta zuba a basket tana fadin "Gashi nan maza kaje dan shida saura kada tai ta jiran ka." Amsa yayi yace "Thank you so much Ummi, we really love you." "Maza jeka Allah muku albarka." Ya juya har ya kai kofa ya juyo yace "Ummi My Son fa?" "Nasan suna hanya shima." "Agaishe shi zamu zo mu dauke shi yai mana weekend." "Ba inda zashi kuna barin sa da yunwa bakwa tashi da wuri in kaga yazo to sai na samar muku mai aiki ita ta kular min dashi." Kai yai kasa dashi kawai ya fice yana murmushi, dakin Inna ya karasa ya same ta zaune daga bakin kofa ya tsaya tace "Au bazaka shigo ba." "Ina sauri nake zan dauko Matata daga makaranta." "Aliyu ai bance ba matar ka ace da kake kara jadadda min wai zaka dauko Matar ka." "Nifa gaishe ki nazo dan sauri nake Hajiya Inna." Ya juya tace "To tsaya ka kai mata abu mana tin shakaran jiya nayi jiya na manta ban baka ba yau ma kada na manta Umaru yazo ya cinye mata " Ta shiga kitchen bata jina ba ta fito da bowl ta mika masa tace "Ka gaishe da ita kwana biyu ma bata leko ba, gobe Najwa ma zata dawo gida haihuwa ita tana da cikin ko tukkuna dai?" "Zan kawo ta sai ki auna mana ita." Ya fita yana fadin "Mungode Inna." Ya fita karfe shida da minti goma ya shiga cikin makarnatar a can gefe ya hango ta tsaye ita da Jawahir a jikin motar su, har inda suke ya karasa ta kalli Jawahir tace "To sai gobe." "Allah kaimu." Ta daga mata hannu ta shige cikin mota, Maryam ma ta fara tafiya wajen Yaa Haidar da ya zuba mata ido, tafiyar tata ma kadai abar sha'awa ce, a haka ta karaso tana shiga ta zame nikaf din fuskar ta tana fadin "Sannu Honey." Ta fada tana fadawa jikin sa tare sa makalkaleshi tana kissing d'in goshinsa kumatunsa, tana zuwa kan labb'ansa ta kamesu baki d'aya ta sak'alo hannayenta wuyanshi, idanunsu cikin na juna ta fara tsotar labb'an nasa tana lumshe idanunta, ta tura hannunta cikin yalwatacciyar sumar kansa tana shafawa, ta fara wasa da harshensa cikin irin salonsa da ya koya mata, take kamo harshen nashi tana tsotsa tana had'awa da labb'ansa tana lalubar bakin nasa lungu dan sak'o cikin wani irin salo mai jeda mutum cikin wani hali, kissing nasa take tana shafa sumar kansa ta maida hannunta d'aya saman fuskarshi tana shashafawa. Idanunsa kawai ya zuba mata cike da tsantsar k'aunarta wacce ta gama gauraye jini da b'argonsa. Ya sanya hannayenshi dukka biyu ya rungumeta tsam yana shafa bayanta, a hankali yana kara taimaka mata, ba abinda kake ji sai sautin tsotsar bakin su da fitar da numfashin su. Tinda yaji wayar su ta dazu yadda take masa shagwaba da cewa yazo a time din shi kan sa yasan Maryam really need him. Maryam jin yadda yake romancing nasa yasa tai luf a jikin sa tana jin dad'in yadda yake tsotsar bakin nata, ta sanya hannunta cikin rigarsa tana shafa kwantaccan gashin k'irjinsa. Tuna a inda suke yasa ta manna masa cizo a harshe yadda bazaiji zafi ba. Ya saki bakin nata da gangan yana, yana shagwabe fuska kamar yadda take masa tare sa yarfe hannu yace “Aushhhhh harshe na” Kyalkyalewa tayi da dariya tana ruk'unk'umeshi tace "A titi dai muke Yaya." Har ya sha'afa a inda suke dan da ta barshi zai iya zarce inda yake, murmushin ya sakar mata yace "Ai kam sai kim ban yar nutsuwa zan iya kai mu gida." Ya janyo ta ya cafki bakin ta tare da fara romancing nata da zadi da zafi, sai da ya samu ya dan nutsu sannan ya rumgume ta a haka ya tada motar suka tafi. Yana parking ya kalle ta yadda jikin ta duk ya mutu, fita yayi yana murmushi ya bude side din da take ya dauko kamar Baby har bedroom ya kaita sannan ya fito ya dauko saura kayan dake cikin mota ya kai ciki, yana shiga ya jiyo ta tana wanka shima wankan ya shiga yayi ya fito ya nufi masallaci wanda yana zuwa sauran raka'a daya yabi su sai da aka idar har yayi isha'i sannan ya fito ya nufi gidan, akan sallaya ya samu Maryam ta daga hannu yana addu'a hawaye na bin fuskar ta, karasawa yayi ya zauna yana kallon fuskar ta yace "Lafiya Baby?" Ya fada yana janta jikin sa, rumgume ta yayi yace "Baby i love u!" "I love u more Honey." Kan ta ya dago yace "Fada min me yake damun ki?" "Yaya ina son ka bana son na rasa ka." "Waye yace zaki rasani?" "Ina tsoro ne Yaya yadda na rasa Yaa Haidar kar na rasa ka, ji yadda kake so na fa." Hannu ya daura akan bakin sa yace "Wayace miki dan ana son mutum sai ka rasa shi, shima Haidar din lokacin sa ne yayi, kuma kowa lokacin sa yayi dole ya tafi, fatan mu dai Allah yasa mu cika da kyau da rahma." "Amin." Suka amsa. Ya hau share mata hawaye yana fadin "To ki bar kuka da damuwa, *Matar Haidar* " Murnushi ta sakar masa yai kissing lips din ta ya dauke ta suka fito yace "Me kika ci a school?" "Snacks." "Shiyasa naji baki dan yi nauyin kin ci abinci ba." Dariya ta saki tace "Kai Yaya?" "Allah yanzu in kika ci abinci na dauke ki zanji kin dan dada nauyi." Tai murmushi, tare suka ci abinci, sai da suka gama sannan suka fita zagaya gidan dan abincin ya sauka. Bayan gidan sukaje da zasu taho ta tsaya tare da kin tafiya juyowa yai ya kalle ta yace "Ya dai?" Kafa ta hau bubbugawa tace "Ni na gaji." Juyowa yai yana murmushi yace "Shine kuma sai kinyi kuka?" Baki ta turo, ya durkusa yace "Hau to." Da sauri ta hau ya dauke ta, tana dariya a haka suka karasa cikin gidan akan gado ya ajiye ta ya fara massaging jikin ta. A hankali ya birkitota ta dawo k'asa yana samanta ya tallafo fuskarta bakin su ya hade daga haka suka shiga bajaulin soyayyar su. * Kwance suke rumgume da juna Maryam da idon ta ke a lumshe tana jin yadda Yaa Haidar ke massaging jikin ta da hannun sa, tace “Uhmmm I love u Honey i can't live without u, taya zan iya rayuwa babu kai a haka? Wallahi bazan iya ba." Ta fada tana sakin wani kukan, "Baby wai menene yau kike ta kuka ne?" Shiru tayi ya shiga share mata hawaye yace "In dai nine Haidar insha Allahu i will always be with you, bani da kowa bani da komai sai sonki da kaunar ki su na saka a gaba kawai, a baya in ance zan so wata mace ba zan taba yadda ba, so please Baby ki bar kuka da sawa a ranki zan rabu dake, insha Allahu i will always be with u for ever uhmmm?" Wata irin rumguma ta bashi tare da kissing bakin sa tana kara rikita shi da salon ta duk abinda tasan yana so shi take yi ai kuwa ta ruda shi. * Washe gari da rana tana school Najwa ta kira ta ta sauka lafiya tana asibiti murna wajen Maryam kamar me haka ta kira Yaa Haidar yana ganin kiran ta ya dauka yace "Baby na!" "Uhmm Yaya dan Allah kazo ka dauken naje na gano Baby." "Ba lectures zaki shiga ba? Kiyi hakuri zan zo biyu dai dai kinji?" "To shikenan pkease Yaya kaje ka daukon picturen ta." "An gama ranki ya dade." "Thank you My love." Ta kashe wayar, shima tana kashewa ya karasa dakin da Najwa take, Babyn na hannun Ummi ya karasa yace "Baby ce take ta rigima naje na dauko ta, tazo taga Baby." "Aliyu ya kamata ka bata mota tana driving itama." "A'ah Ummi ni bana son ta wahala wallahi." Sai da yai maganar ya tuna da wa yace sai ya share kawai yace "Baby tace nazo na daukar mata kan ta karaso." Ya dauke shi yana fadin "Bari naje Ummi." Ya juya ya fita. Tana aji amman ta kunna data, yana turowa ta bude wani murmushi ta saki tana fadin "Allah sarki Sis Allah ya raya mana." Ta kashe datar. Har Allah Allah take malamin ya fita dan sai taga lokacin ma baya gudu a haka har biyu tayi sallah kawai tayi sai ga Yaa Haidar, sallama suka da Jawahir suka tafi asibitin. Lokacin da sukaje ta dauki Babyn kuwa ta hana kowa sai sannu takewa Najwa, har yamma suna nan sai da aka sallame su gaba daya sukai gida. Da dare ya shigo dakin Ummi inda Najwa da Maryam suke, bayan ya zauna ya mike yace "Tafiya fa zamuyi." "Yaya please na kwana?" Wani kallo ya aika mata yace "Kada ma ki soma ki sauko mu tafi." Ummi da ta shigo tace "Ah Dr kaci abinci ne?" Kai ya girgiza yace "Wa zai bani?" Ummi tai murmushi tace "To tashi ki zuba masa." "Ai tafiya zamuyi ma." Yaa Aliyu ya fada. "Ummi please ya barni na kwana." Kofa ya nufa da sauri yana fadin "Ina kasa ina jiran ki." Ummi ta kalla ta tabr baki tace "Ummi please." "Maryam kwanan me zakiyi?" Ummi ta fada tana zama kusa da Najwa. Mikewa tayi tana turo baki tace "To sai da safe." "Allah bamu alheri ki dibar masa abincin fa." Fita kawai tayi, Ummi tace "Kuje ku karata, ni nasan ba barin ta zai ba." Najwa tai dariya tace "Itama Maryam rigima dai kawai Ummi." Sukai dariya Ummi ta mike tana fadin "Taje can tai masa." Ta fita, a kitchen ta samu Maryam tana dibar masa abinci, sai da ta gama suka nufi kofa tace "To sai da safe?" Kai ta gyada, ta fita tana daga mata hannu kamar zatai kuka wai duk dan Ummi taji tausayin ta. *Allah mana rahma kasa muyi kyakyawan karshe Amin.* *Antty* [12/12, 09:51] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 85 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* A mota ta same shi ta shiga ta zauna ta dauke kai tana kallon waje, murmushi kawai yayi ya tada mota suka fita a gidan, hannun ta ya kamo yana murzawa a hankali yace "Wai yau dani ake fushi." Bata juyo ba a haka ya dinga murza hannun ta har suka karasa gida yana bude kofa ta bude ta fita tare da dauka flask din da ta shigo dashi, a falo ya same ta zata shiga daki ya karasa ya rumgume ta yace "Tab Allah baki isa ba ki ma daina tin wuri kuma abu daya zan fada miki kada ki soma sawa a ranki zan iya barin ki zuwa wani waje kwana dan ba zan taba iya kwana ba a jikin ki ba ki tausayawa dan Babyn ki mana, kema kinsan komai dai." Dariya da tausayi ya bata dan tabbas tasan ba zai iya ba, yini daya in bai yi da ita ba ma ya ba lafiya bare ace kwana. Haka ya dinga lallashin ta da kalamai masu dadi da nuna mata illar barin sa shi kadai din da haka ta hakura ta taya shi sukai wanka ta bashi abinci da kanta sannan suka zauna suna shan soyayyar su. Tin ranar da Najwa ta haihu kullum daga makaranta can yake kai ta sai dare suke dawowa, ana ya gobe sunane da kyar ya yadda zata kwana. Duk abinda take bukata ta saka a cikin akwati, tana cikin hada kaya ya shigo ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda take ta zuba kaya a cikin akwati, dagowa tayi ta saki murmushi tace "Yaya in ta so mu tafi?" "Ba zaki lecture ba?" Baki ta turo tace "Yaya ba dole ne yayi ba ni kawai ka kaini gidan Ummi." Ya karaso ya amshi akwatin yana rufewa yace "Wannan uban kayan fa?" "Kala uku ne fa Yaya." "Gobe dai zamu dawo." "Naji." Ya dauke akwatin ya ajiye, a kasa yace "Dauko mayafin naki." Ya fita da akwatin. Har gida ya shiga ya dauki kayan ya shiga dasu sama ta wuce dakin Najwa acan ta samu Aisha tana shiga Baby ta dauka suka gaisa sannan ta tafi wajen Ummi da Babyn A can ta samu Yaa Haidar, gaisawa sukai da Ummi sannan ta koma dakin Maryam, da kallo Haidar ya bita, har Ummi ta gane, yana dagowa suka hada ido da sauri ya mike yana sussunne kai yace "Ummi bari naje sai na dawo." "Allah kiyaye hanya Allah bada sa'a." Yana fita ya fara neman layin Maryam, tana zaune cikin su Aisha kiran ya shigo, dauka tayi tace "Yaya." "Matar Haidar zan tafi." "To Yaya Allah kiyaye hanya." "A'ah a'ah ban yadda ba." "To me zan maka Yaya?" "Maza ki zo ki wa mijin ki bye bye common my dear.' Babyn ta mikawa Aisha tace "Honey ba dai rigima ba bari naje." Dariya sukai ta mike ta fita, a kasa ta same shi zaune, ta karasa tana fadin "Honey gani." Hannun ta ya janyo ta fada saman sa ya rumgume ta kallon dakin ta fara tace "Yaya a gidan Ummi fa muke." "Bake kika zaba ba." Baki ta turo ya matso da face din sa ya fara kissing lips din ta, kofa sukaji an bude da sauri ta zare bakin ta tana barin jikin sa, Mami da ta gansu ta dauke kai kamar bata san da mutane a falon ba, Maryam ce tace "Ina yini Mami?" Mami ta juyo tana fadin "Ah yaushe kuka shigo?" "Dazu." Aliyu ya mike ya sauka kasa yana gashe da Mami ta amsa tana yin sama, mikewa tayi ta nufi stairs tana fadin "Ni dai Yaya sai ka dawo." Hannun ta ya kamo, ta juyo kamar zatai kuka tace "Yaya ni dai ni dai." "Allah in baki zo kin ban goodbye kiss ba, ba kwanan da zakiyi." Kafa ta hau bubbugawa, ya juya ya nufi kofa da sauri ta bishi da gudu tana fadin "To ba gani ba." A bakin kofa ta cimmasa ta rumgume shi ta baya, ta daura kan ta a bayan sa, ya juyo da ita, ta tsaya a gaban sa wanda ya fita tsayi, dage tayi ta kamo baki sa ya saka hannu ya zagaye kugun ta, kissing juna su suke cikin kwanciyyar hankali, sai da suka jiyo motsi ana tahowa sannan ta janye bakin ta, rumgume ta yayi sannan ya sake ta yana fadin "Sai na dawo." "A dawo lafiya Honey." "Take care." Ya juya ya fita ta leka tana kallon sa har ya fice, sannan ta koma sama. Tare da mai jego akai musu lalle da kitso. * Karfe shida ya dawo alwala kawai yayi ya nufi massalaci sai da akai isha'i ya shigo gidan a dakin sa ya shiga yai wanka yana fitowa ya kira Maryam lokacin ta fito daga wanka tana shafa mai ta dauka yace "Shine ko ki nemen ko?" "Ba haka bane Honey lalle ne a hannun fa, ka dawo?" "Eh yunwa nake ji." "To ya za ayi?" "Ki kawon abinci." "To ina zuwa." Ta nufi akwatin ta kayan bacci ta saka doguwar riga ta saka hijab, kitchen ta shiga ta dauki abincin sa, dakin sa ta nufa ta shiga da sallama baya falo, dan haka ta nufi bedroom din sa yana zaune a gefen gado, yana ganin ta, ya mike ya karaso ya amshi tray din ya ajiye, sannan ya jayata jikin sa yana kissing, da kyar tace "Yaya baka ci abinci bafa, kuma kace yunwa kake ji." "In na same ki ai zaki gusar min da ko wacce irin yunwa." "Naji amman ka fara cin abinci." Ta sauka tana zuba masa, ita ta dinga bashi yana ci sai da ya gama ta dauki kwanon zata fita dashi ya kamo hannun ta yace "Zo tukkuna." Ya janyo ta jikin sa yana mai aika mata da sakon da dole ta biye masa. 10:00pm Ummi ce ta shiga dakin da Najwa take, ita kadai ta sama kwance akan gado, ta karasa tana fadin "Ina Maryam din?" "Ummi kema kinsan Yaya ai ba barin ta zai anan ba." Shiru kawai Ummi tayi tana girgiza kai can tace "Shikenan sai da safe." "Allah bamu alheri." 5:15am Ta bude idon ta, ta sauke akan Aliyu dake zaune akan sallaya, yana ganin ta tashi ya mike ya karaso yana shafa fuskar ta yace "Morning Baby Love." Baki ta dan turo tace "Shine ka hanani tafiya ko Yaya ni wallahi kunyar Ummi nake ji." Murnushi yayi yace 'Bazaki makarar dani da rigimar ki ba Baby." Yai kissing goshin ta ya mike ya fita dan har an tada sallah, bayan sa tabi da kallo sannan ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta tada sallah bayan ta idar tai azkar sannan ta muke ta gyara masa dakin ta saka turare ta fice ta koma dakin Najwa. Tana kwance tana bacci ta shiga kaya ta canja ta sauko ta nufi kitchen dan tasan Ummi na can, a can kuwa ta same ta har kasa ta durkusa ta gaishe da Ummi tana dan jin kunya, Ummi amsa tana fadin "Har kin tashi." "Eh Ummi kawai nai aiki." "A'ah barshi kije ki huta." "Ummi please ni da na tashi yanzu." Ta karasa tana taya ta aikin. Suna kitchen Haidar karami ya shigo yana ganin Maryam ya karasa ya rumgume ta yace "Adda anan kika kwana?" Ta daga sa da kyar tana fadin "Yaro nan ya kara nauyi ai ban kara daukar ka." Ummi tace "Daman ai tin bai kai haka ba kike cewa yana da nauyi." "Allah Ummi na zata da wasa Yaa Haidar yake, yace Haidar ya fini nauyi." "Inji shi Aliyun?" Sai da Ummi tai tambayar sannan ta tina abinda ta fada da sauri ta dauke Haidar suka fice tana fadin "Bari muje wajen Inna." A compound suka hadu da Yaa Haidar, Haidar ya sauka a hannun Maryam dake tafiya tana nishi ya rumgume Yaa Aliyu yace "Morning Abbi." "Morning my son ka tashi lafiya." Kai ya gyada, ya juya yana kallon Maryam ta karasa tace "Ina kwana." Ba tare da jin kunyar Haidar ko tsoron wani ya gansu a haka ba ya janyo ta jikin sa yana kissing wuya ta yace "Haka kika saba gaishe ni?" Janye jikin ta tayi tace "Haidar dai na nan." Ya kara janyo ta yace "Ba ruwan yaro na." Ya kalli Haidar yace "Maza muje wajen Inna." Haidar yai gaba, Aliyu kuma ya dan rakwafo ya kama bakin Maryam yana kissing nata, sannan ya saketa ya kama hannun nata sukai bangaren Inna. A kitchen suka jiyo ta ita da Haidar suna ta magana Maryam ta sa murmushi ta nufi kitchen din tana fadin "Me Hajiya Inna take girka mana?" "Ai jiya ina ta zuba ido na zata anan zaki kwana?" "Bacci ne ya dauke ni da wuri." "Kaji Inna ga mijin ta sai ta taho wajen ki." "Ni dai ban maka magana ba ah toh." "Haba Hajiya Inna uwar gida na nifa da wasa nake miki." Baki ta tabe ya karasa ya kama hannun ta yana fadin "Ni dai mu shirya mu daina fadan nan." Taja kunnen sa da karfi ya rike hannun yana fadin "Baby zata ciren kunne na." Maryam da Haidar karami na dariya sukace "Inna kiyi hakuri." Ta saki kunnen tana fadin "Ai dan na huce abinda yai min ne kan na hakura." Suka fito daga kitchen din gaba daya da kayan da ta hada anan suka zauna, Yaa Haidar ya zuba uwar madara a cup ya hadawa Maryam ya dauka zai hada ta dauke madarar tace "Wacce ka kawon ta kare ba ita bace wannan." "Haba Hajiya Inna, ai sai ki magana a dado amman ni yanzu ba za a barni na sha ba ai da yake yar lallen ki ce Maryam kin bari na zuba mata." "Cokali daya zaka zuba." "Gaskiya tai min kadan." Ta zuba masa biyu, ta dauke madarar tana gani Maryam ta mika mata nasa amman sai yaki amsa dauka tayi ta hade musu ta raba sannan suka karya gaba dagan su suna hira da wasa da dariya, Inna na lura da Aliyu abu kadai ya kalle ta ya aika mata da wani kallo, Maryam dai sai basarwa take. Daga baya ta tafi ta barsu a wajen inna. Babyn Najwa taci suna Mami suke kiran ta da Zuhrah, ansha suna sosai akai taron suna inda gidan da yamma ya cika dan anyi walima, ranar ma gaba daya bata ga Yaa Haidar ba tin safe sai karfe biyar da rabi ya dawo lokacin suna conpound ya shigo yai parking, ba inda idon sa ya fara sauka sai akan matar sa, ya lumshe ido dan wani kyau yaga tai masa sanye take cikin wani amry green less wanda akaiwa ado da dark pink yai mata kyau tasa dan kunne da sarka da abin hannu ba tai make up ba amman tai kyau sosai kana ganin ta kaga wacce hutu da jin dadi ya zauna mata ta murje tai kyau fatar ta tai fresh. A hankali ya bude murfin motar ya fito yana kara kallon inda suke ita dasu Yaya Asiya da Hanna da Bilkisu ne sai hira suke abin sha'awa basu san da dawowar su ba sai ganin sa kawai sukai ya karaso wajen ya nufi wajen da Naryam take, dagowar da za tai suka hada ido kai ta girgiza masa, dan tasan yanzu zai ce zai kamata ai kuwa bata sauke idon ta ba taji ya kamo hannun ta ya dago ta tare da hada ta da jikin sa yana mata magana kasa kasa. Fuska ta shagwabe kamar zatai kuka tace "Yaya da fa mutane." "Ina ruwa na ni dai matata kawai nake bukata, ke haka ake? Ace dan kin samu yan uwa sai ki manta da mijin ki Allah in haka ne zan na hanaki zuwa taro." "Haba Yaya kayi hakuri kaji." "Muje ki tayani yin wanka naci abinci ko?" Fuska ta marairaice ya fara janta, Anty Asiya tace "Yaya ai ma gaisa ko?" Anty Hanna dake rike da waya tana daukar Maryam da Yaa Haidar tace "Masha Allah! Perfect Match Yaya." Ya kalli Maryam yana sakin murnushi wanda hakan ya kara sawa su daukar shi a hoton, sannan suka gaishe shi yaja Maryam sukai bangaren Ummi ta baya saboda yadda mutane ke cikin compound din gidan. Suna barin wajen Ummi tazo tace "Ina daughter?" "Yanzu Yaya ya dawo ya dauke ta." "Oh Dr yanzu ana taron ma ba zai barta cikin yan uwan ta ba." Ta girgiza kai ta bar wajen. Anty Hanna tace "Kinga yadda karamar yarinya ta dauke hankalin Babban mutum kamar Yaya." Anty Asiya tace "Ni wannan miskilancin da daure fuskar kai duk babu shi." "Ke kuwa ina zai yi su ya samu yar yarinya yana kwasar dadin sa." Anty Bilkisu ta fada. "Ai naji dadi wallahi Allah ya kara basu zaman lafiya ya basu zuri'a mai albarka amman sun dace da juna sosai." "Kinga fa picturen nan dan Allah kalle su, kamar wanda akayi su dan juna." Hanna ta fada tana nuna pictures da tai snapping nasu, amsa sukai suna gani kan kace me duk sun tura suna yaba yadda suka dace da juna. Maryam kuwa sanin Yaa Haidar bai cin abincin taro yasa tin rana ta hada masa nasa ta kai dakin sa, ita ta taimaka masa yai wanka sannan ta fito gabatar masa da abinci sai da ya ci ya sha sannan ya lallalube ta da kyar ya barta ta tafi cikin yan uwan nata. 2 month later Bikin Rukky wanda ya rage kwanaki biyar, zaune take a jikin sa sai shagwaba take masa akan tafiyar tata dan Aisha tini suna Kano, dago ta yayi yace "Menene kuma Baby?" "Honey dan Allah ka bari gobe mu tafi da Najwa." "In kinje kuma ki kwana nawa?" "Sati biyu, kaga fa Yaya tinda muka tare banje gida ba wajen wata shida." Ta fada tana shigewa jikin sa tare da bashi wani irin kiss, ido ya lumshe yana amsar abinda take masa. Sai da ta saki bakin nasa ya saki wani numfashi tare da fadin "Yanzu a haka kike so na barki ki tafi Baby wa zai na kula dani." "Yaya please please!" Rumgume ta yayi yana fadin "Baby zan duba." Jikin sa ta kara shigewa tana kara rikitashi da salon ta, sai da ta gama rikirkita shi sannan ta kara maimaita bukatar ta, bai san lokacin da ya amince mata ba. Sai daga baya bayan ya dawo hayyacin sa da dare ya ganta tana hada babban akwati da karami, zama yayi yana kallon ta yace "Duk kayan nan fa?" Kamar zatai kuka tace 'Na tafiya man." Yai murmushi yace 'Menene na kukan to?" "To ai nasan halin ka, Yaya har da Jawahir fa kuma duk danni zamu tafi amman kai kana son ka hanani zuwa haba Yaya na." "So nayi ana gobe daurin aure sai mu tafi." "Amman Yaya ai an gama event kuma na fada maka dalili na wata shida banga Ammi na ba." Sai ga hawaye na bin kuncin ta da sauri ya karaso yace "Nifa bance a'ah ba." Rumgume ta yayi yana lallashin ta. * Bayan ya tafi masallaci ya nufi gidan Ummi, a dakin ta ya same ta akan sallaya ya karasa ya zauna ta shafa addu'a tana fadin "Ina ka baro daughter ka fito da daren nan?" "Tana gida sai rigima take." "Rigima kuma?" "Eh wai sai ta tafi Kano Ummi." "Haba Aliyu saboda me to ba zatan ba? Bikin kawar tane fa bama wannan ba wata wajen bakwai da tarewar ku fa amman bataje gida ba haba Aliyu ka barta taje kwana nawa take so?" "Sati biyu fa Ummi ai yayi yawa." "Aliyu kana dagawa yarinyar nan kafa fa, kullum kuna tare dan taje taga iyayen ta na sati biyu shine zakace a'ah kuma naga kaima nan da kwana hudu zakabi ta uhm." "To Ummi shikenan goben sai suje." "Yauwah Allah maka albarka, sai su tafi tare da Haidar zan hada masa kayan sa shima yaga yan uwan sa." "To Ummi bari naje naji ana kiran sallah, da daga can zan tafi gida." "Allah bamu alheri agaishe min da ita." "Zata ji." Ya fada yana mikewa ya fita. * Washe gari kamar ba zasu rabu da juna ba makale da juna suka yini har lokacin da ya fito dan kawosu gida daga nan su tafi airport bayan sun shiga taje taiwa Mami da Inna sallama, bangaren Ummi ta shiga sukai sallama sannan suka tafi tare da Haidar dake ta dagawa Ummi hannu. A airport suka hadu da Jawahir da Najwa bayan Haidar ya fita ya jata jikin sa yana kissing nata sannan ya sake ta yace "Zanyi kewar ki." "Nima yaya i love." "Love u more." Sannan suka fito hannun ta rike da nashi haka da suka karasa da kyar suka rabu, sai da yaga tashin su sannan ya koma asibiti. Suna sauka ta kira ta fada masa, wanda Yaa Abdullah yazo daukar ta, har suka karasa gida waya suke da Yaa Aliyu sai da suka shiga falo sannan sukai sallama ta rumgume Ammi tana fadin "Ammi nah i miss you." "Dan Allah jibe ki kin fa girma kalli Haidar" Yaa Abdullah ya fada "Ina ruwa na ni." Ammi tai murmushi tanawa su Najwa da Jawahir sannu da zuwa tare da amsar Zuhrah, nan aka kawo musu kayan abinci sai da sukaci sukai nak sannan Aisha ta shigo da Babyn ta wanda shima yayi wayoo. Ranar sunga gata a gidan wajen matan yayen Maryam, komai suka kwaso su Maryam, haka komai in za ai sai an tambaye su me za ai musu ma suke so. Yaa haidar kuwa baya minti goma bai kira Maryam ba haka suka kusan kwana ido biyu suna hira a waya, haka washe gari ma suna zaune gaba daya zai kira dole sai ta bar wajen dan sai su dauki wajen awa suna abu daya. Sunje gidan su Rukayya wanda ake ta shirye shirye Yaa Ahmad ma har gida yazo yaga Haidar suka gaisa dasu Maryam. Aisha ce ta dauko musu mai kunshi akai musu lalle da gyaran kai. Haka akai kamu da dinner wanda Yaa Haidar ya iso ranar juma'a dan asabar za a daura aure, Ammi da kan ta ta shirya masa abinci dan ranar da ya iso su Maryam suna can gidan su Jawahir ana arabi'an night, sai wajen karfe tara da wani abu suka karaso gidan wanda tana fitowa wayar ta na daukar kara, dauka tayi tana ganin mai kiran, kunnen ta takai tana fadin "Yaya na ka iso ne?" "Na iso yaushe zaku dawo?" Dai dai shigar ta bangaren su tace "Gamu mun dawo yanzu. Kaci abinci?" "Ammi ta kula da d'anta sosai." Murnushi tayi tace "Masha Allah yanzu sai ka kwanta ka huta ko?" "Wane irin na kwanta na huta ina jiran matata yanzun nan." "Yaya....." "Shittt bana son jin komai kizo kinji kema kinsan nayi kewar ki." "To ina zuwa." Ta shiga falon inda suka samu Ammi zaune ta kalle su tace "Yan biki kun dawo?" "Wallahi Ammi, ai wai sai mun kwana acan to ita Marham mai gida zai zo ina taga ta kwana." "Kai Najwa Yayan ya zo ne?" "Kaji mata yanzu fa kuka gama waya." Mikewa tai ta fira tana fadin "Wallahi zan rama ne." Ta nufi sashen Yaa Abdullah da nan ta gyara masa tin jiya dan yafi sakewa tin da shi yaki yai aure. *Allah ya jikan mu yai mana rahma Amin.* *Antty* [12/12, 19:36] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 86 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Yana zaune a falo sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu wacce akai layi-layin fari, ja da ba'ki, sai kamshi yake kamar ka dauke shi ka gudu kwana biyu da tayi bata ganshi ba kawai sai taga ya kara kyau, itama gani yai ta kara kyau da haske sanye take cikin doguwar riga pink kala wacce duk jikin ta stone ne tai kyau sai walwali take, hannu ya bude mata ta karasa ta fada jikin sa tana sakin murmushi tare da kissing nasa a kumatu, ya dago kan ta ya hade bakin su yana bata wata irin sumbata wacce ta nuna mata yayi kewar ta sosai da sosai. Daga nan wasan ya canja salo, sai da suka samu nutsuwa sannan ya fara fadin yadda yai missing nata, tana jikin sa har wajen sha daya ta mke tace zata tafi, yadda ya marairaice mata yasa ta zauna lallashin sa, wanda Aliyu ya kara cika ta da salon sa tafiyar da batai ba kenan sai kwanan sashen. Ai kuwa asubar fari yana tafiya masallaci itama ta koma bangaren su, sallah tayi sannan ta shiga kitchen dan haka musu breakfast. Bayan ta gama tai wanka ta debi nashi ta nufi bangaren sa, yana zaune akan kujera hannun sa rike da waya ta shiga ya amsa sallamar yana kallon ta har ta karaso sanye take da doguwar rigar atamfa tai mata kyau ta ajiye tray din aka stool din dake dakin ta karasa ta zauna akan cinyar sa tare da tallafo kansa tace "Morning Honey." Tare da kissing lips din sa, lips din nata ya kama ya dan tsotsa sannan yace "Morning too My Noor." Ya bi ta da wani kallo yace "Ina Haidar?" "Yana can bangaren Yaa Muhammad." "Uhmm yaga yan uwa." Ta saki murmushi ta mike tare da nufar kayan da ta shigo dashi, kunun gyadan da tai masa ya sha madara ta mika masa ya amsa tare da janyo ta jikinsa yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye ya fara bata dankalin da ta soya masa sai da suka gama sannan tace "Yaya yanzu fa zamu tafi?" "Karfe nawa ne daurin auren da zaku tafi yanzu?" "Sauran awa daya fa Yaya gwara muje da wuri so tayi mu kwana fa." "Amara kenan." Tai murmush tace "Bari muje mu shirya." Ta masa kiss ta fice, kaya ta canja ta saka wata Sky blue din shadda wacce ta sha aiki da stone ja sosai tai kyau ta dauki half covern takalmin ta, da jan mayafi ta saka dan kunne da sarka na mai red stone sosai tayi kyau kamar ka dauke ka gudu da ita ta fito tare dasu Najwa da Jawahir, Yaa Alkasim ne zai kaisu, Yaa Abdullah ya bawa Aliyu mukullin dayar motar gidan nasu, wanda ya dauki Maryam da Jawahir, Aisha da Najwa kuna suna motar Yaa Alkasim sai da suka ajiye su sannan suka tafi wajen durin auren. Bayan an daura aure da yamma akai yini inda dukkan su suka saka ankon atamfar da akayi sunyi kyau abinsu, karfe biyar aka kai amarya gidan ta inda aka bar su Maryam a wajen ta, sai da ango yazo sannan su Yaa Alkasim da suka rako su sukai tafi da matan su. Yau ma dauke matar sa yayi sukai bangaren Yaa Abdullah acan suka kwana sai washe gari ta koma wajen su suka shirya wajen sha biyu suka tafi gidan Rukayya. Kwanan su Najwa bakwai suka tafi suka bar Maryam dan sai ta kara yin sati daya wanda shi kuma Yaa Aliyu kwana biyu yayi ya tafi ya barta. Bayan tafiyar su kuma sai ta fara zazzabi, da wani irin ciwon kai, da yamma bayan sun dawo daga gidan Mami ita da Haidar kaami suna zaune a falo, yace "Adda Ummi ita ce maman Abbi, ita kuma Mami maman Abbi na da ya mutu ko?" Hannu ta saka tana shafa sumar kansa tace "Eh Habiby." "Adda da Ummi da Ammi wacece Ammin ki?" Murmushi tayi tace "Duk Ammi nane, amman Ammi ita ta haife ni." Kai ya gyada, yace "Adda, su Momy fa?" Yana nufin su Yaya Fadima, tace "Yayye nane." "To Adda su Momyn Abuja fa?" Tai murmushi tace "Suma Yayye nane." Dagowa yayi yace "Adda su Abbi na na nan gidan fa?" Dariya tayi tace "Suma dukka haka." "Adda kina da yan uwa da yawa." "Kai ma haka my son." Murmushi yayi ta rumgume shi a haka, Ammi ta shigo ta same su, ita kan ta da ta gansu sai da ta tina da Yaa Haidar da yana raye da kila suna da ya'ya wajen nawa, da yana raye da suna tare dashi, ba abinda zasuyi masa sai addu'a Allah jikan sa ya kyautata namu zuwan, Amin. Gidan yan uwan ta ta fara ziyarta tare da Haidar, taje gidan Yaya Ummulkairi, da Yaya Rukayya, a gida Yaya Fadima da taje yiwa kwana daya ciwon nata ya fara zafi, wani dare suna zaune suna hira, Maryam take fadawa Yaya Fadima yadda Yaa Aliyu baya son ta matsa ko nan da can. Yaya Fadima cikin jin dadi tace "Ni daman na sani a sannu zaku so junan ku, wallahi kun dace da Aliyu kuma nasan ba wanda zai samu 'kanwata yaki ta." "Ah ah fa Yaya Fadima banda cika baki." "Ai nasan wacece 'kanwata shiyasa, kada ki damu tsananin son kine yasa haka ke dai ki kula da mijin da fatan kina abinda nace kina yi?" "Eh Yaya Fadima ina yi kuma ina jin dadin sa, Yaya Fadima Humran nan ta kare kuma naga Honey yana son ta." "Ai na fada miki Humra na da kyau kada ki damu kan ki tafi za kawo miki, dan Allah Maryam na san ki da tsafta da gayu da son turare ki daure ki cigaba kinji." "Insha Allahu Yaya Fadima ina godiya sosai dan in kika sani abu nayi ni kadai nasan albarkar da nake sha a ranar." Tai murmushi tace "Ki rike mijin ki da yan uwan sa, kinga yadda suma suke son ki kada ki soma kin nasa, ki na sashi yana taimaka masu ba wai yan uwan ki kadai ba dan Abbi yace duk wata sai yayo masa aike." Ido Maryam ta zaro tace "Ikon Allah wallahi Yaya fadima ban sani ba sai dai Abbi yace nai masa godiya ko naji suna waya yana fadin ai shima mahaifin sa ne ya daina godiya da makamantan su, in na tambaye shi ma sai yace ina ruwa na shima Abbin sa ne." Sukai murmushi, Yaya Fadima tace "Bawan Allah kenan, Allah ya barku tare ya baku zuri'a ta gari." "Amin Yaya Fadima." "In kina da matsala kar kiji nauyin na ki sanar min kinji Autah." Tai dariya tace "Wallahi har nayi missing diin ku Yaya Fadima, sai kika tino min da Yaa Haidar." "Allah masa rahma." "Amin." Haka ta cigaba da zama da yayar tata wanda zazzabin kamar wasa sai ga Maryam har da kwanciyya a asibiti dan yadda ciwon kan ya matsa mata bayan sun mata aune aune ne suka gano cikin dake jikin ta wanda bai kai watanni biyu bama, zo kuga murna wajen yan uwan ta, abinda aka kasayi a cikin Haidar kenan, Yaa Aliyu dake can Abuja hankalin sa ba karamin tashi yayi ba da ya kira wayar tata akace masa tana bacci saboda jikin nata, dan tin da ta fara zazzabin shi ya rubutowa Yaa Alkasim Maganin ya siyo mata amman sai abun ya kara yin gaba, wanda yau tin safe yake kiran ta Yaya Fadima tace suna asibiti bacci take yi. Gida ya koma ya fadawa Ummi abinda ke faruwa, Ummi ta kalle shi yadda duk ya damu tace "To menene na damuwar Dr?" "Ummi yau ban san a halin da take ba sam ban ji murtar ta ba. Please ki kira Ammi nasan zata fada miki komai." "Shikenan bari na kira tan." Ta dauki waya ta kira Ammi bayan sun gaisa ne Ummi tace "Ashe daughter ce ba lafiya." "Uhmm ai ciwon na karuwa ne Ummin Maryam, da akai mata test dai sai ya nuna tana dauke da ciki." "Ah Masha Allah! Alhandulillah Allah raba lafiya." "Amin Yaa Allah, ai mata sannu in tashi zan kira sai na duba jikin nata." "To Ummi mungode." Sukai sallana, Yaa Haidar da ya zuba mata ido yana son tai masa bayani ta kalla tace "Ka zuban ido." Zama yayi yace "Me ya faru Ummi naji kina Allah raba lafiya, ba dai ciki ne da Baby ba?" Hararar sa tayi tace "Ni kake cewa Baby a gaba na ko?" Baki ya danne da hannu ya dariya dan ba yau ya fara ba yau ne dai ta magantu, yana dariya yace "Ni dai Ummi please ki fada min." "To mun samu karuwa, jika na yana wahalamin da Babyn ka." Ido ya zaro yana fadin "Please Ummi da gaske?" Dariya tayi tace "Sure." Ummi ya rumgume yana fadin "Alhamdulillah!" Sai hawaye, Ummi ta kama hannun sa tace "To menene na kukan?" "Ummi ki tayani addu'a Allah ya bata lafiya ya sauke ta lafiya, ina son nima naga jini na Ummi ina son naga jini nan Ummi." "Insha Allahu zakaga jinin ka har ma tattaba kunne Aliyu." "Allah yasa Ummi." "Amin." "Gobe zani Kanon Ummi." "Ai tare zamu na dubo ta." "Yauwah Ummi na sai muga jikin in da hali sai mu taho gaba d'aya ko?" "A'ah fa Aliyu kada ka matsa mata dan Allah ka barta kawai in tawarware sai ta dawo, ni dai yaro na kawai zan dauko saboda makaranta." "To Ummi ita kuma nata karatun fa, kina gani sauran wata daya su fara exam fa." "Insha Allahu zata ji sauki kan lokacin." "Ina tsoro kada ta sha wahala kamar yadda ta sha a cikin Haidar." "Insha Allahu wannan zai zo mata da sauki." "Allah ya yadda." "Amin." * Washe gari da yamma suka sauka a Kano, a gidan su Ammi suka sauka sai da sukaci abinci Yaa Alkasim ya kai su asibitin, Maryam tana bacci suka shiga bayan sun gaisa da su Ammi da Yaya Fadima suka dan fita suka basu waje, suna fita Yaa Haidar ya matsa wajen gadon yana kallon yadda ta dan fada, hannu yasa ya shafi wuyan ta, a hankali ta bude idon ta, tana ganin Yaa Haidar ta saki murmushi tana fadin "Yaya." Zama yayi yana kama hannun ta yace "Ya jikin Baby?" Baki ta tabe kamar zatai kuka tace "Yaya kai na shi yake damuna." Hannu ya daura akan nata yana fadin "Sannu kinji Allah sauwake." Kai ta tace "Ya hanya ina Ummin?" "Suna waje ita da Ammi? Me kike so?" Kai ta girgiza tace "Ba komai Yaya baki na duk ba dadi." "Sannu kinji?" Kai ta gyada ya zura hannun sa cikin rigar ta ya daura a kasan marar ta yana shafa wajen a hankali a hankali, ido ta lumshe tana jin kewar mijin nata, daya hannun ya daura akan ta yana shafa kan nata, a haka Ummi da Ammi suka shigo har da Mami da zuwan ta kenan wannan yasa Aliyu ya tashi da sauri ya gaishe da Mami tare da fita ya barsu a wajen ta, jikin Ummi ta lafe tana zuba mata shagwaba, Ummi na ta biye mata, sosai Mami da Ammi abun ya burge su suka kara yabawa Ummi na yadda take son Maryam. A haka sukai kwana biyu wanda Ummi ce ke kwana a wajen Maryam sam ta hana Ammi da Yaya Fadima sai dai su zo, Yaa Aliyu ma sai kula yake da matar sa, dan dakin aka bar musu in ba wani ne yazo dubata ba suna makale da juna, ranar da sukai kwana biyu aka sallamo su suka kom gida, washe gari suka daga da Haidar Karami saboda makaranta, haka ta cigaba da jinya wanda sai da tai sati hudu a Kano sannan ta koma gida wanda shima ba gama warwarewa tayi ba, anan gidan Ummi suka cigaba da rainon cikin ta wanda a haka da kyar take zuwa makaranta, wani abun ma sai ta dawo Yaa Haidar yake kowa mata, satin ta uku da dawowa suka fara jarabawa wanda a lokacin aka kai kudin auren Yaa Farouk da Jawahir. Da kyar a haka yau lafiya gobe babu suka gama jatabawa wanda a lokacin bikin Jawahir saura sati uku, wanda yai dai dai da cikar cikin Maryam wata uku, ba laulayin nan sam sai kwadayi kuma, ganin ta murmure yasa Yaa Haidar ya dauke matar sa suka koma gidan su da mai aikin Ummi dan Yaa Haidar yace sai ita in ba ita ba baya son wata mai aiki. Satin su biyu da komawa gida aka fara bikin Jawahir inda suka sha shagali har Rukkayya sai da tazo itama da cikin ta wata biyu, Maryam na mata tsiya tace "Daman nace tare zamu sauke." A lokacin bikin su Momy da Basma suka zo har da su Tasleem, wacce itama an sa mata ranar auren ta amman son Aliyu na nan cikin zuciyar ta, a dinner suka hadu lokacin zuwan su kenan dan da kamar ba zasu zo ba sai da Yaa Haidar ya gama sha'anin sa sukai wanka ta saka wani blue less sai zare silver da stone dinkin doguwar riga ne sosai yai mata kyau, ta saka silver takalmi mai tsini da jaka da farin mayafi sosai tayi kyau duk da ba make up ba amman tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu. Tana gaban mirrow tana gyara daurin ta Yaa Haidar ya karaso sanye da sky blue din shadda sai zuba kamshi yake ya saka yar ciki da babbar riga, hannu ya mika mata ta saka masa agogon azurfa da ya mika mata, ta dago ta mudubi taga yana kallon ta, dan jin gina tayi dashi tana fadin "Honey kallon fa?" "Ta yadda zan fita dake da wannan kwalliyar bayan maza zasuje su ta kallan min matata." "Oh oh oh! Wai Yaya kai ka dai ne mai mata da za ai ta kallo na." "Kyan naki ne yafi na kowa." Ido ta zaro tace "Tab ai kuwa Yaya akwai wadan da suka fini kyau." "A idon na ba wacce ta kai ki kyau, ba wacce ta kamo kafar ki ko tsarar ki, ke mata ma duk maza nage ganin su, ke kadai nake gani a matsayin mace, so ki bar zancen wasu, wallahi ke me kyau ce, nagodewa Allah da ya bani ke Alhamdulillah, yanzu ya za ayi?" "Na me fa?" "A fasa zuwa dinner nan." Jikin sa ta fada tana kukan shagwaba tace "Abinda kai min a bikin Najwa zaka mai maita min ko Yaya?" Rumgume ta yayi yana murmushi kasa kasa dan sai yanzu ya tino da lokacin da ya hanata sakat, kafa ta hau bubbugawa da sauri ya rike ta yana fadin "Haba Baby, our baby fa, kila yana bacci zaki tashe shi kina bubbuga kafa ni fa da wasa nake." "Da gaske?" Kai ya gyada ya janyo ta ya rumgume ta, jin irin rumgunar da yai mata yasa tasan yana son ya cika ta da salon sa ne dan kawai zuwa dinner ta shiririce da sauri ta janye jikin ta ta nufi kofa tana fadin "Ni dai wallahi dare yanayi Honey." Bayan ta yabi yana fadin "Zan kamaki ne." Suka fita shi ya bude mata mota ta shiga sannan ya rufe ya zagaya. Suna karasawa inda ake dinner yaki bude kofar motar ta juyo tace "Honey menene kuma?" "Allah kamar mu juya." Idon ta ne ya fara kawo ruwa, da sauribya fara lallashin ta yana fadin "Ki rufan asiri kar Ummi taga hawaya tace na saka mata 'ya kuka." Tai murmushi ta rumgume shi, tace "Kuma kai din ne ba." Zai magana yaji ana knocking, ta gefen Maryam ne ya dago yaga Tasleem ce, da yake tint ce wannan yasa bata ganin su, zooming glass din yai kasa yadda iya kan sa take gani kawai dan Maryam na kwance a jikin sa. "My love!" Ta fada, wani dum Maryam taji a kirjin ta ga wani abu ya tsaya mata a kirjin ta, kallon Tasleem yake yace "Yaushe kuka zo?" "Jiya." Ta fara kokarin bude mota taji a rufe, murya ta shagwabe tace "Oh My love ka bude min mana." Da sauri Maryam ta dago, ta dannan tare da tura kofa, turus Tasleem tayi tana kallon Maryam dan sam bata gane ta ga, taji ance yayi aure amman hakan bai sa ta cire damarar ta ba duk da Abban ta ya bada ita ga dan abokin sa, amman ganin Maryam ba karamin girgiza ta yayi ba, yarinyar kyakyawa ga iya kwalliya duk da batai wani heavy makeup ba amman tayi kyau, ba kamar ita da tai heavy makeup ba. Kan ta farga taji an rufe kofa da sauri ya fita yana kiran ta, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya, ya karasa inda take ya sha gaban ta ya mika mata handbag din ta yana fadin "Menene to?" Wani kallo ta watsa masa tace "Sai ka koma wajen ur love." Dan murmushi ya saki yana fadin "Kishi ya motsa." A cikin ransa. A fili kuwa cewa "Ah ah fa Baby kar na koma kuma kizo kina jin haushi." Dagowa tai ta sakar masa wani kallo, na kenan sai ka koma din?" Hannun ta ya kama yace " *Matar Haidar* ita kadai." Duk da taji dadin kalmar amman tana tsoro kar fa ace ya auri wannan fitsararriyar yarinyar ai kuwa da ta kade, dan kalmar da Tasleem ta fada kawai ta tsaya mata a wuya sam taji ta ji ta wuce mata. Idon ta ne ya kawo kwalla da sauri ya janye ta suka koma gefen motar sa inda Tasleem ta kame tana kallon su, ita kanta tasan sun dace da juna, gani ya rumgume ta yana lallashin ta da wasu tsadaddun kalamai wanda bata san me yake fada mata ba yasa taji zuciyar ta ta baci da sauri ta bar wajen ranta a bace amman tai alkawarin sai ta batawa Maryam rai kafin su rabu. *To fah Tsaleem ya da haka?* *To wa ya sani ko Tasleem ta shiga gidan Haidar a ta biyu, tinda ta nace, kuma naga takwara akwai kishi kamar My Sis Nusy* 😝 *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya." *Antty*[12/12, 19:36] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 86 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Yana zaune a falo sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu wacce akai layi-layin fari, ja da ba'ki, sai kamshi yake kamar ka dauke shi ka gudu kwana biyu da tayi bata ganshi ba kawai sai taga ya kara kyau, itama gani yai ta kara kyau da haske sanye take cikin doguwar riga pink kala wacce duk jikin ta stone ne tai kyau sai walwali take, hannu ya bude mata ta karasa ta fada jikin sa tana sakin murmushi tare da kissing nasa a kumatu, ya dago kan ta ya hade bakin su yana bata wata irin sumbata wacce ta nuna mata yayi kewar ta sosai da sosai. Daga nan wasan ya canja salo, sai da suka samu nutsuwa sannan ya fara fadin yadda yai missing nata, tana jikin sa har wajen sha daya ta mke tace zata tafi, yadda ya marairaice mata yasa ta zauna lallashin sa, wanda Aliyu ya kara cika ta da salon sa tafiyar da batai ba kenan sai kwanan sashen. Ai kuwa asubar fari yana tafiya masallaci itama ta koma bangaren su, sallah tayi sannan ta shiga kitchen dan haka musu breakfast. Bayan ta gama tai wanka ta debi nashi ta nufi bangaren sa, yana zaune akan kujera hannun sa rike da waya ta shiga ya amsa sallamar yana kallon ta har ta karaso sanye take da doguwar rigar atamfa tai mata kyau ta ajiye tray din aka stool din dake dakin ta karasa ta zauna akan cinyar sa tare da tallafo kansa tace "Morning Honey." Tare da kissing lips din sa, lips din nata ya kama ya dan tsotsa sannan yace "Morning too My Noor." Ya bi ta da wani kallo yace "Ina Haidar?" "Yana can bangaren Yaa Muhammad." "Uhmm yaga yan uwa." Ta saki murmushi ta mike tare da nufar kayan da ta shigo dashi, kunun gyadan da tai masa ya sha madara ta mika masa ya amsa tare da janyo ta jikinsa yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye ya fara bata dankalin da ta soya masa sai da suka gama sannan tace "Yaya yanzu fa zamu tafi?" "Karfe nawa ne daurin auren da zaku tafi yanzu?" "Sauran awa daya fa Yaya gwara muje da wuri so tayi mu kwana fa." "Amara kenan." Tai murmush tace "Bari muje mu shirya." Ta masa kiss ta fice, kaya ta canja ta saka wata Sky blue din shadda wacce ta sha aiki da stone ja sosai tai kyau ta dauki half covern takalmin ta, da jan mayafi ta saka dan kunne da sarka na mai red stone sosai tayi kyau kamar ka dauke ka gudu da ita ta fito tare dasu Najwa da Jawahir, Yaa Alkasim ne zai kaisu, Yaa Abdullah ya bawa Aliyu mukullin dayar motar gidan nasu, wanda ya dauki Maryam da Jawahir, Aisha da Najwa kuna suna motar Yaa Alkasim sai da suka ajiye su sannan suka tafi wajen durin auren. Bayan an daura aure da yamma akai yini inda dukkan su suka saka ankon atamfar da akayi sunyi kyau abinsu, karfe biyar aka kai amarya gidan ta inda aka bar su Maryam a wajen ta, sai da ango yazo sannan su Yaa Alkasim da suka rako su sukai tafi da matan su. Yau ma dauke matar sa yayi sukai bangaren Yaa Abdullah acan suka kwana sai washe gari ta koma wajen su suka shirya wajen sha biyu suka tafi gidan Rukayya. Kwanan su Najwa bakwai suka tafi suka bar Maryam dan sai ta kara yin sati daya wanda shi kuma Yaa Aliyu kwana biyu yayi ya tafi ya barta. Bayan tafiyar su kuma sai ta fara zazzabi, da wani irin ciwon kai, da yamma bayan sun dawo daga gidan Mami ita da Haidar kaami suna zaune a falo, yace "Adda Ummi ita ce maman Abbi, ita kuma Mami maman Abbi na da ya mutu ko?" Hannu ta saka tana shafa sumar kansa tace "Eh Habiby." "Adda da Ummi da Ammi wacece Ammin ki?" Murmushi tayi tace "Duk Ammi nane, amman Ammi ita ta haife ni." Kai ya gyada, yace "Adda, su Momy fa?" Yana nufin su Yaya Fadima, tace "Yayye nane." "To Adda su Momyn Abuja fa?" Tai murmushi tace "Suma Yayye nane." Dagowa yayi yace "Adda su Abbi na na nan gidan fa?" Dariya tayi tace "Suma dukka haka." "Adda kina da yan uwa da yawa." "Kai ma haka my son." Murmushi yayi ta rumgume shi a haka, Ammi ta shigo ta same su, ita kan ta da ta gansu sai da ta tina da Yaa Haidar da yana raye da kila suna da ya'ya wajen nawa, da yana raye da suna tare dashi, ba abinda zasuyi masa sai addu'a Allah jikan sa ya kyautata namu zuwan, Amin. Gidan yan uwan ta ta fara ziyarta tare da Haidar, taje gidan Yaya Ummulkairi, da Yaya Rukayya, a gida Yaya Fadima da taje yiwa kwana daya ciwon nata ya fara zafi, wani dare suna zaune suna hira, Maryam take fadawa Yaya Fadima yadda Yaa Aliyu baya son ta matsa ko nan da can. Yaya Fadima cikin jin dadi tace "Ni daman na sani a sannu zaku so junan ku, wallahi kun dace da Aliyu kuma nasan ba wanda zai samu 'kanwata yaki ta." "Ah ah fa Yaya Fadima banda cika baki." "Ai nasan wacece 'kanwata shiyasa, kada ki damu tsananin son kine yasa haka ke dai ki kula da mijin da fatan kina abinda nace kina yi?" "Eh Yaya Fadima ina yi kuma ina jin dadin sa, Yaya Fadima Humran nan ta kare kuma naga Honey yana son ta." "Ai na fada miki Humra na da kyau kada ki damu kan ki tafi za kawo miki, dan Allah Maryam na san ki da tsafta da gayu da son turare ki daure ki cigaba kinji." "Insha Allahu Yaya Fadima ina godiya sosai dan in kika sani abu nayi ni kadai nasan albarkar da nake sha a ranar." Tai murmushi tace "Ki rike mijin ki da yan uwan sa, kinga yadda suma suke son ki kada ki soma kin nasa, ki na sashi yana taimaka masu ba wai yan uwan ki kadai ba dan Abbi yace duk wata sai yayo masa aike." Ido Maryam ta zaro tace "Ikon Allah wallahi Yaya fadima ban sani ba sai dai Abbi yace nai masa godiya ko naji suna waya yana fadin ai shima mahaifin sa ne ya daina godiya da makamantan su, in na tambaye shi ma sai yace ina ruwa na shima Abbin sa ne." Sukai murmushi, Yaya Fadima tace "Bawan Allah kenan, Allah ya barku tare ya baku zuri'a ta gari." "Amin Yaya Fadima." "In kina da matsala kar kiji nauyin na ki sanar min kinji Autah." Tai dariya tace "Wallahi har nayi missing diin ku Yaya Fadima, sai kika tino min da Yaa Haidar." "Allah masa rahma." "Amin." Haka ta cigaba da zama da yayar tata wanda zazzabin kamar wasa sai ga Maryam har da kwanciyya a asibiti dan yadda ciwon kan ya matsa mata bayan sun mata aune aune ne suka gano cikin dake jikin ta wanda bai kai watanni biyu bama, zo kuga murna wajen yan uwan ta, abinda aka kasayi a cikin Haidar kenan, Yaa Aliyu dake can Abuja hankalin sa ba karamin tashi yayi ba da ya kira wayar tata akace masa tana bacci saboda jikin nata, dan tin da ta fara zazzabin shi ya rubutowa Yaa Alkasim Maganin ya siyo mata amman sai abun ya kara yin gaba, wanda yau tin safe yake kiran ta Yaya Fadima tace suna asibiti bacci take yi. Gida ya koma ya fadawa Ummi abinda ke faruwa, Ummi ta kalle shi yadda duk ya damu tace "To menene na damuwar Dr?" "Ummi yau ban san a halin da take ba sam ban ji murtar ta ba. Please ki kira Ammi nasan zata fada miki komai." "Shikenan bari na kira tan." Ta dauki waya ta kira Ammi bayan sun gaisa ne Ummi tace "Ashe daughter ce ba lafiya." "Uhmm ai ciwon na karuwa ne Ummin Maryam, da akai mata test dai sai ya nuna tana dauke da ciki." "Ah Masha Allah! Alhandulillah Allah raba lafiya." "Amin Yaa Allah, ai mata sannu in tashi zan kira sai na duba jikin nata." "To Ummi mungode." Sukai sallana, Yaa Haidar da ya zuba mata ido yana son tai masa bayani ta kalla tace "Ka zuban ido." Zama yayi yace "Me ya faru Ummi naji kina Allah raba lafiya, ba dai ciki ne da Baby ba?" Hararar sa tayi tace "Ni kake cewa Baby a gaba na ko?" Baki ya danne da hannu ya dariya dan ba yau ya fara ba yau ne dai ta magantu, yana dariya yace "Ni dai Ummi please ki fada min." "To mun samu karuwa, jika na yana wahalamin da Babyn ka." Ido ya zaro yana fadin "Please Ummi da gaske?" Dariya tayi tace "Sure." Ummi ya rumgume yana fadin "Alhamdulillah!" Sai hawaye, Ummi ta kama hannun sa tace "To menene na kukan?" "Ummi ki tayani addu'a Allah ya bata lafiya ya sauke ta lafiya, ina son nima naga jini na Ummi ina son naga jini nan Ummi." "Insha Allahu zakaga jinin ka har ma tattaba kunne Aliyu." "Allah yasa Ummi." "Amin." "Gobe zani Kanon Ummi." "Ai tare zamu na dubo ta." "Yauwah Ummi na sai muga jikin in da hali sai mu taho gaba d'aya ko?" "A'ah fa Aliyu kada ka matsa mata dan Allah ka barta kawai in tawarware sai ta dawo, ni dai yaro na kawai zan dauko saboda makaranta." "To Ummi ita kuma nata karatun fa, kina gani sauran wata daya su fara exam fa." "Insha Allahu zata ji sauki kan lokacin." "Ina tsoro kada ta sha wahala kamar yadda ta sha a cikin Haidar." "Insha Allahu wannan zai zo mata da sauki." "Allah ya yadda." "Amin." * Washe gari da yamma suka sauka a Kano, a gidan su Ammi suka sauka sai da sukaci abinci Yaa Alkasim ya kai su asibitin, Maryam tana bacci suka shiga bayan sun gaisa da su Ammi da Yaya Fadima suka dan fita suka basu waje, suna fita Yaa Haidar ya matsa wajen gadon yana kallon yadda ta dan fada, hannu yasa ya shafi wuyan ta, a hankali ta bude idon ta, tana ganin Yaa Haidar ta saki murmushi tana fadin "Yaya." Zama yayi yana kama hannun ta yace "Ya jikin Baby?" Baki ta tabe kamar zatai kuka tace "Yaya kai na shi yake damuna." Hannu ya daura akan nata yana fadin "Sannu kinji Allah sauwake." Kai ta tace "Ya hanya ina Ummin?" "Suna waje ita da Ammi? Me kike so?" Kai ta girgiza tace "Ba komai Yaya baki na duk ba dadi." "Sannu kinji?" Kai ta gyada ya zura hannun sa cikin rigar ta ya daura a kasan marar ta yana shafa wajen a hankali a hankali, ido ta lumshe tana jin kewar mijin nata, daya hannun ya daura akan ta yana shafa kan nata, a haka Ummi da Ammi suka shigo har da Mami da zuwan ta kenan wannan yasa Aliyu ya tashi da sauri ya gaishe da Mami tare da fita ya barsu a wajen ta, jikin Ummi ta lafe tana zuba mata shagwaba, Ummi na ta biye mata, sosai Mami da Ammi abun ya burge su suka kara yabawa Ummi na yadda take son Maryam. A haka sukai kwana biyu wanda Ummi ce ke kwana a wajen Maryam sam ta hana Ammi da Yaya Fadima sai dai su zo, Yaa Aliyu ma sai kula yake da matar sa, dan dakin aka bar musu in ba wani ne yazo dubata ba suna makale da juna, ranar da sukai kwana biyu aka sallamo su suka kom gida, washe gari suka daga da Haidar Karami saboda makaranta, haka ta cigaba da jinya wanda sai da tai sati hudu a Kano sannan ta koma gida wanda shima ba gama warwarewa tayi ba, anan gidan Ummi suka cigaba da rainon cikin ta wanda a haka da kyar take zuwa makaranta, wani abun ma sai ta dawo Yaa Haidar yake kowa mata, satin ta uku da dawowa suka fara jarabawa wanda a lokacin aka kai kudin auren Yaa Farouk da Jawahir. Da kyar a haka yau lafiya gobe babu suka gama jatabawa wanda a lokacin bikin Jawahir saura sati uku, wanda yai dai dai da cikar cikin Maryam wata uku, ba laulayin nan sam sai kwadayi kuma, ganin ta murmure yasa Yaa Haidar ya dauke matar sa suka koma gidan su da mai aikin Ummi dan Yaa Haidar yace sai ita in ba ita ba baya son wata mai aiki. Satin su biyu da komawa gida aka fara bikin Jawahir inda suka sha shagali har Rukkayya sai da tazo itama da cikin ta wata biyu, Maryam na mata tsiya tace "Daman nace tare zamu sauke." A lokacin bikin su Momy da Basma suka zo har da su Tasleem, wacce itama an sa mata ranar auren ta amman son Aliyu na nan cikin zuciyar ta, a dinner suka hadu lokacin zuwan su kenan dan da kamar ba zasu zo ba sai da Yaa Haidar ya gama sha'anin sa sukai wanka ta saka wani blue less sai zare silver da stone dinkin doguwar riga ne sosai yai mata kyau, ta saka silver takalmi mai tsini da jaka da farin mayafi sosai tayi kyau duk da ba make up ba amman tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu. Tana gaban mirrow tana gyara daurin ta Yaa Haidar ya karaso sanye da sky blue din shadda sai zuba kamshi yake ya saka yar ciki da babbar riga, hannu ya mika mata ta saka masa agogon azurfa da ya mika mata, ta dago ta mudubi taga yana kallon ta, dan jin gina tayi dashi tana fadin "Honey kallon fa?" "Ta yadda zan fita dake da wannan kwalliyar bayan maza zasuje su ta kallan min matata." "Oh oh oh! Wai Yaya kai ka dai ne mai mata da za ai ta kallo na." "Kyan naki ne yafi na kowa." Ido ta zaro tace "Tab ai kuwa Yaya akwai wadan da suka fini kyau." "A idon na ba wacce ta kai ki kyau, ba wacce ta kamo kafar ki ko tsarar ki, ke mata ma duk maza nage ganin su, ke kadai nake gani a matsayin mace, so ki bar zancen wasu, wallahi ke me kyau ce, nagodewa Allah da ya bani ke Alhamdulillah, yanzu ya za ayi?" "Na me fa?" "A fasa zuwa dinner nan." Jikin sa ta fada tana kukan shagwaba tace "Abinda kai min a bikin Najwa zaka mai maita min ko Yaya?" Rumgume ta yayi yana murmushi kasa kasa dan sai yanzu ya tino da lokacin da ya hanata sakat, kafa ta hau bubbugawa da sauri ya rike ta yana fadin "Haba Baby, our baby fa, kila yana bacci zaki tashe shi kina bubbuga kafa ni fa da wasa nake." "Da gaske?" Kai ya gyada ya janyo ta ya rumgume ta, jin irin rumgunar da yai mata yasa tasan yana son ya cika ta da salon sa ne dan kawai zuwa dinner ta shiririce da sauri ta janye jikin ta ta nufi kofa tana fadin "Ni dai wallahi dare yanayi Honey." Bayan ta yabi yana fadin "Zan kamaki ne." Suka fita shi ya bude mata mota ta shiga sannan ya rufe ya zagaya. Suna karasawa inda ake dinner yaki bude kofar motar ta juyo tace "Honey menene kuma?" "Allah kamar mu juya." Idon ta ne ya fara kawo ruwa, da sauribya fara lallashin ta yana fadin "Ki rufan asiri kar Ummi taga hawaya tace na saka mata 'ya kuka." Tai murmushi ta rumgume shi, tace "Kuma kai din ne ba." Zai magana yaji ana knocking, ta gefen Maryam ne ya dago yaga Tasleem ce, da yake tint ce wannan yasa bata ganin su, zooming glass din yai kasa yadda iya kan sa take gani kawai dan Maryam na kwance a jikin sa. "My love!" Ta fada, wani dum Maryam taji a kirjin ta ga wani abu ya tsaya mata a kirjin ta, kallon Tasleem yake yace "Yaushe kuka zo?" "Jiya." Ta fara kokarin bude mota taji a rufe, murya ta shagwabe tace "Oh My love ka bude min mana." Da sauri Maryam ta dago, ta dannan tare da tura kofa, turus Tasleem tayi tana kallon Maryam dan sam bata gane ta ga, taji ance yayi aure amman hakan bai sa ta cire damarar ta ba duk da Abban ta ya bada ita ga dan abokin sa, amman ganin Maryam ba karamin girgiza ta yayi ba, yarinyar kyakyawa ga iya kwalliya duk da batai wani heavy makeup ba amman tayi kyau, ba kamar ita da tai heavy makeup ba. Kan ta farga taji an rufe kofa da sauri ya fita yana kiran ta, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya, ya karasa inda take ya sha gaban ta ya mika mata handbag din ta yana fadin "Menene to?" Wani kallo ta watsa masa tace "Sai ka koma wajen ur love." Dan murmushi ya saki yana fadin "Kishi ya motsa." A cikin ransa. A fili kuwa cewa "Ah ah fa Baby kar na koma kuma kizo kina jin haushi." Dagowa tai ta sakar masa wani kallo, na kenan sai ka koma din?" Hannun ta ya kama yace " *Matar Haidar* ita kadai." Duk da taji dadin kalmar amman tana tsoro kar fa ace ya auri wannan fitsararriyar yarinyar ai kuwa da ta kade, dan kalmar da Tasleem ta fada kawai ta tsaya mata a wuya sam taji ta ji ta wuce mata. Idon ta ne ya kawo kwalla da sauri ya janye ta suka koma gefen motar sa inda Tasleem ta kame tana kallon su, ita kanta tasan sun dace da juna, gani ya rumgume ta yana lallashin ta da wasu tsadaddun kalamai wanda bata san me yake fada mata ba yasa taji zuciyar ta ta baci da sauri ta bar wajen ranta a bace amman tai alkawarin sai ta batawa Maryam rai kafin su rabu. *To fah Tsaleem ya da haka?* *To wa ya sani ko Tasleem ta shiga gidan Haidar a ta biyu, tinda ta nace, kuma naga takwara akwai kishi kamar My Sis Nusy* 😝 *Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya." *Antty* [12/13, 12:33] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 87 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Daga baya mota suka koma sai da ya gama shanye jan baki ta sannan ya kyale ta, ta dago tana masa hararar wasa mai cike da so da kauna, daurin ta ta fara gyarawa ta kalli kan ta a mirrow, duka ta kai masa a kirji tana fadin "Shine ka shanyen jan baki ko?" "To ya za ayi Ranki ya dade?" "Kaje ka siyo min yanzu." An gama ya fara kokarin tada motar da sauri ta zare mukullin tace "Yadda zakaji dadin mai dani gida ko?" Yai dariya yace "Sai na kawo karshen rigimar ko?" "Yaya." Ta kira sunan sa, ya kalle ta dan yadda ta kira sa kadai zaka san abun da zata fada mai mahimmanci ne, "Matar Yaya." Ta saki murmushi tace "Ni dai in mun shiga kada kayi dariya kaji." Dariya yayi yace "To saboda me?" Baki ta turo tace "Ni bana so." "To toh an gama ranki ya dade uwar gida kuma amarya a gidan Aliyu Haidar." Ta bude jaka ta dauki mudubi ta shafa man lebe, kallon ta yake har ta gama ta gyara daurin ta sannan tace "Ya nayi?" Tai maganar tana dage masa gira, murmushi ya saki yace "Yes kamar mu koma gida." Hannu ta sa zata bude kofa yai saurin saka lock yace "Ranki ya dade ki tsaya ki daina abu da sauri fa yanzu kin san akwai little a cikin ki." Ya fada yana shafa cikin nata cikin wani salo, hannun sa ta buge tana mai shagwabe fuska kamar zatai kuka tace "Allah Honey ka bari." "Na bari." Ya fita yana dariya ya zagayo ya bude mata kofa ya mika mata hannun sa ta kamo ta fito ya rufe a haka suka karasa hall din da yake cike da mutane hannun ta cikin nasa, kowa ya sha kwalliya ya kece raini bama da yake sun hada biki da masu siyasa. Suna shiga Yaa Muhammad ya hango su sai da gaban sa ya fadi dan tin ranar dinner su bai kara ganin Maryam ba sai yau, sai yaga ta kara kyau tai haske da sauri ya dauke ido yana istigifari dan yadda shaidan yasa zai fara yabon matar wani, hannun Maryam cikin na Yaa Haudar suka fara shiga nan su Yaa Hannah, Yaa Asiya da Yaa Bilkisu da Najwa da Basma wanda suka sha kwalliya cikin hadadden less suka karaso suka rufe su suna liki tin kan su karasa tsakiyar hall din nan aka hau musu kirari, Tasleem bakin ciki kamar ta hadiyi zuciya. A haka sukaje suka gaishe da su Ummi da Mami, da Momy, da Mama sannan suka karasa wajen da aka ware musu ita dashi wanda an anjiye musu lemo da ruwa, tana zama ya kalle ta yana sakar mata murnushi, ta dan harare shi tace "Murmushin me kake?" "Shikenan ni kuma ba zan wa matata murmushi taji dadi ba." "Hmm Yaya wannan daban kayi shi." Wani murmushin ya kara ta mike tace "Kaga ni bari naje wajen amarya da ango." "Yanzu fa kin zama Anty ki zauna zasu zo su kwashi gaisuwa." Ya fada yana dawo da ita ta zauna, ai kuwa ana kiran amarya da ango su fito wajen su Yaa Haidar suka fara zuwa mai vedio da camera suka hau biyo su har suka karaso aka hau musu picture nan su Najwa suka karaso duk akai dasu daga nan suka shiga fili suna musu liki sosai sukai musu liki, su Najwa, m Yaya Hannah ana ta rawa, Yaa Haidar ya janyo hannun Maryam dan yaga yadda Najwa ke jijjiga ta wai sai tai rawa shi kuwa bai son ana jijjiga ta dan baya son a wahalar masa da Babyn sa. Suna zama ta bude ruwa ta tsiyaya a cup ta mika masa amman yai bai sha ba ya kai mata baki dan kurba tayi, sannan ya sha sauran ta, akan idon Tasleem da ta kasa dauke ido akan su, su kuwa basu san da ita bama. Maryam dake kallon wajen da su Najwa suke rawa sai murnushi take, kamar an ce ta dago ta hango Yaa Muhammad na tinkaro su, da sauri ta dauke kai tana danna wayar dake hannun ta, tana jin kamshin sa ya farai musu sallama amman bata dago ba har ya karaso bakin sa dauke da sallama cikin muryar nan tashi mai sanyi, Yaa Haidar ya amsa yana dagowa dan yaso ya gane muryar, ganin Muhammad yasa ya saki murmushi yana fadin "Bismillah!" Ya bashi waje ya zauna, zama yayi yana mika masa hannu sukai musabaha yana tambayar ya iyali, sosai suka gaisa Yaa Haidar ya zura kafa ya dan taka kafar ta dagowa tayi cike da shagwaba tana aika masa da wani kallo, murmushi ya saki ya kamo hannun ta yana murzawa yace "Sorry sorry, kinga Muhammad fa." Dagowa tayi suna hada ido ta dauke kanta tana fadin "Ina yini Yaa Muhammad?" "Lafiya Ahamdulillah ya taro?" "Alhamdulillah." "Allah sanya alheri ina Haidar?" Dube dube ta fara tace "Yana nan cikin hall din nan." "Ya kara girma ko?" Yaa Haidar ya amshi da fadin "Gaskiya kam ba laifi kusan shakara daya fa." "Haka ne, Allah yayi masa albarka " Amin suka fara hira abinsu, sun jima suna hira sannan ya mike yace daman gaisawa yazo suyi, ya tafi. Abinci aka kawo musu Maryam ta sa hannu zata dauki spoon Yaa Haidar yace "Abincin zaki ci?" "Wallahi Yaya ina gani yawu na ya tsinke." Yasan babu ta yadda zai hanata ci dan haka sai ya saki hannun ta ta dauki spoon din ta fara yagar naman kazar tana ci tana lumshe ido tace "Yaya Allah da dadi kaci kaji." Kai ya girgiza yace 'Wannan sai ke Baby." Haka ta cinye tata half kazar da aka kawo ta koma kan tasa itama ta fara ci, shi lemo kadai yasha bayan ta gama Najwa tazo ta janye ta, idon sa na kan Maryam suna can ana musu picture kala kala da kawayen nasu da su Najwa da su Yaya Hannah, Aisha da Rukky, kamar daga sama yaji tana fadin "Sweet bro." Dagowa yayi yace "Tasleem amarya." Zama tayi tana yamutsa fuska tace 'Yaya amman dai kasan ina son ka ko? Ni wallahi kai nake so ba shi ba." Dan murmushi ya saki yace "Ki hakura da zabin iyayen ki, kila ya zamo alheri a gareki kamar yadda Maryam ta zama alheri a rayuwa ta, ni dai kinsan ba iya rike mata biyu zan ba, bana son hayaniya ku kuma mata daga an hada ku ba abinda kuka iya sai hayaniya." Kamar zatai kuka tace "Yaya ni dai in har ka yadda ba zanyi ba." "Ita kuma matata fa?" "Sai ka sake ta in zatai." Wani kallo ya bita sashi, tace "Allah yaya ina son ka nasan nafita son ka." Kallon ta yake cike da mamakin kalaman ta na ya saki Maryam, to shi yanzu wa zai saka shi ya saki Maryam babu, shi da Maryam mutu ka raba amman dan ya samu su rubu ta sanyi yasa yace "Kinsan me? Yanzu ina abinda nace ki fara." "Me?" "Canja shigar ki da daukar halin yar uwar ki." Fuska ta shagwabe tace "Wallahi Yaya sam bana iya saka Hijab damu na yake yi." Dai dai lokacin da Maryam ta hango su kenan, take hakalin ta ya tashi zamewa tayi tayo wajen da suke fuska ba walwala ta karaso ta kamo hannun sa da sauri ya mike yana tambayar ta menene? Duk ya damu ganin fuskar ta ba walwala, rakwafawa yayi yana mai tambayar ta, a hankali tace "Mu tafi gida." "Tin yanzu kuma?" Kai ta daga tana kallon sa, idon ta cike da kwalla wanda da sauri ya kamo hannun ta suka fice da daga hall din wajen motar sa suka karasa suka shiga gidan baya ya rumgume ta yana fadin "Menene to?" "Kake cewa tin yanzu saboda kana hira da budurwar ka ko?" "Nifa ba hira muke ba magana muke kinsan Tasleem kanwata ce ai." "Ni bana so to, kana ganin abinda take maka ai kasan son ka take ni mu tafi gida kawai." Ta fada hawaye na zubo mata, jikin sa ya jata yana lallashin ta yace "To naji ki bar kukan uhmm!" Kai ta gyada ya goge mata hawayen ya fita ya kamo hannun ta suka koma gidan gaba sannan ya tada motar suka bar wajen dinner, a gida ma rigima ta dingai masa ya rasa gane kan ta, har da su kuka yayi tambayar duniya menene amman taki tai magana, da kyar da lallashi ya samu tai bacci yana rumgume da ita, idon sa a lumshe yake tunanin me yasa meta amman ya rasa ganewa sai yake ganin ko cikin nata shi ya fara sata wannan abun, kara rumgume ta yayi yana ji har tana dan kara ya kissing goshin ta tare da mata addu'a ya shafe su sukai baccin su. Tasleem kuwa bakin ciki kamar ya kashe ta ganin yadda Yaa Haidar duk ya shiga damuwa daga gani sauyi akan fuskar Maryam, da suka bar wajen kuwa kan ta ta kife akan table din tana sakin kuka mai taba zuciya. * Washe gari yini, tin safe taso ta tafi gidan Ummi amman Yaa Haidar sam ya hana ta sakat sai lugwigwita ta yake, sai yamma bayan ya dawo daga massalaci suka hau shiryawa cikin ankon atamfar da sukai ta dasu Anty Hanna, Anty Asiya, Anty Bilksu da Najwa wanda dinkin riga da siket din cikin jikin ta da yasa ta dan kara jiki siket din ya zauna cif a jikin ta, rigar ma ta kamata daga kirji tai kyau sosai tana cikin parking gashin ta, wayar ta ta hau kara, Yaa Haidar dake zaune yana kallon yadda take shiryawa ya dauki wayar yana fadin "Najwa ce." Ya danna received ya saka mata a kunnen ta, tace "Yar uwa ya akai." "Kina ina ne?" "Yanzu nake shiryawa." "Tin dazu ake miki waya kina gaki nan, gaskiya kya same mu acan dan har amare fa sun shirya." "Kai Sis." "Ba wani kai Sis kin makale a wajen Yaya ma hadu acan." "Shikenan sai mun karaso." Ta zare wayar ta juyo kamar zatai kuka tace "Ai ka kyauta gashi nan sun tafi sun barni." "Shine me? Sai na kai matata." Baki ta turo ta dauki dan kwalli ta daura, ta shafa soft perfurm ta dauki mayafin ta ta yafa ta dauki takalmi zata saka ya amsa ya saka mata ta dago tana shafa sajen sa tace "Thank you." Yai kissing lips din ta, yana rumgumota, "Ni dai mu tafi." Ta kamo hannun sa, jakar ta ta dauka suka fita, a mota ma sai da ya gama jan aji sannan suka tafi. Su Najwa basu dade da zuwa ba suka karasa, wanda sukai sallama da Yaa Haidar ta fito suka rumgume juna ita da Najwa, Aisha da Rukky suka karaso ta amshi Baby tace "Mai gida na." Sukai cikin wajen, basu jima da zuwa ba amarya da ango suka shigo su suka shigo da ita aka cigaba da gudanar da yini ranar tana cikin yan uwan ta suna ta hira abinsu. Karfe shida aka tashi wanda Yaa Haidar yana unguwar anan yai sallah, yana karasowa Tasleem ta ganshi da sauri ta karasa ta bude mota ta shige, suna waya da Maryam yana cewa ya karaso ta shiga dagowa yai ya kalle ta yace "Menene haka?" "Dan na shigo motar ka Yaya." Kai ya dauke tace "Ina yini?" "Lafiya lou." "Yaya a gidan ka zan kwana fa." Dagowa yai zai magana ya hango Maryam ta karaso kan yai magana ta kama kofar ta bude turus tayi ganin Tasleem ta hade fuska kicin kicin tana jiran ta sauko amman sai taga ta kara juyawa tana fadin "Yaya mu tafi tinda ta fito." Kallon su ta tsaya yi, Aliyu zai magana Tasleem tace "Ki shiga mu tafi mana." Ta fada tana mata fari da ido, kofar motar ta rufe ta juya Aisha ta gani zata shiga mota da sauri ta bude baya ta shiga, Yaa Alkasim ya juyo yace "Ke lafiya?" "Ku ajiye ni a gidan Ummi." "Ina Yaa Haidar din?" "Bai zo ba." Aisha ta shigo ya tada motar ya bar wajen, Yaa Haidar da ya cika da mamaki ganin ta rufe kofa ya bude side din sa da sauri ya fito amman ina bai ga Maryam ba, ciki ya koma yana duba ta amman sam ba ita ba alamar ta, dawowa yayi ya shiga mota ya dauki wayar sa yana kiran layin ta amman tana ganin kiran taki ta dauka, Tasleem ya kalla ya aika mata da wani kallo yace "Sauka." "Yaya nace a gidan ka fa zan kwana." "Nace ki sauka ko?" Da yadda yai maganar sai da ya bata tsro bata san lokacin da ta sauka a motar ba, ya tada motar ya bar wajen, gidan Ummi ya nufa ransa a matukar bace dan me zata tafi kuma yana kiran ta taki dauka, Yaa Alkasim na sauke ta ta nufi sashen Inna dan tasan Inna ce kadai taza goya mata baya, tana shiga ta shige bedroom din ta tai kwanciyyar ta, Inna da ta fito daga toilet tace "Ah anan zaki kwana ne!" Kai ta gyada tace "Eh Inna ki ara min zani ma na cire kayan nan." "Tashi ki dauka." Ta nufi kofa, "Inna." Maryam ta kira ta. Juyowa tayi tace "Menene?" "Inna yunwa nke ji." "To bari na samo miki wani abu " Ta juya ta fita. Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan Inna ta tada sallah tana kan sallaya Inna ta shigo da kwano ta ajiye mata har da ruwa da lemo. Maryam na murmushin yake tace "Amman nagode hajiya ta." Ta juya zata fita tace "Inna dan Allah ko da yaya zai zo kice ya barni na kwana ni kwanciyya ma zanyi." "Shikenan kici ki kwanciyyar ki sai da safe." Ta fice. Yana shigowa yai parking mota sashen Ummi ya nufa kai tsaye ya tafi sama tana dakin ta dan shigowar ta kenan ya shigo ta kalle shi tace "Ah baku tafi ba." Ki ya gyada yaxe "Ina take." "Wa?" "Maryam mana Ummi wai kawai ta taho ta barni acan" "Maryam din je ka duba dakin a su Nawa suke kila su ta biyo." Ya juya ya shiga, ba ta nan amman duk da haka sai da ya tambaya ko tare suka taho duk suka ce a'ah fita yayi kawai ya tafi yin alwala yai sallah dan yasan bangaren Inna ta tafi kenan tinda ya tambayi masu gadi sunce ta shigo. Sai da ya idar sannan ya nufi sashen Inna inda Maryam har taci abinci tai sallah ta kwanta. Inna ya sama a falo tana gyangyandi, a hankali ya tsallake ta ya nufi bedroom din ta, Maryam na kwance tana juye juye dan duk ta kasa baccin ya shigo dakin, kamshin turaren sa ta fara juyo wa da sauri ta juyo sukai ido hudu dashi yana tsaye a jikin kofa ya harde hannu a kirjin sa, juya masa baya kawai tayi tana kara lullu'ba. Karasawa yayi kan gadon ya ciccibo ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa ta kasa dan haka kuka kawai ta saka masa, kofa ya nufa da ita, ya bude suka fita falon Inna sai baccin ta take, tace "Ni anan zan kwana ka ajiye ni." Ko kula ta bai ba zatai magana ya hade bakin su wanda sai da suka fita daga falon ya saki bakin nata, har cikin mota ya saka ta wacce yai parking a kofar part din Inna ya zagaya ya tada motar suka fice a gidan tin da suka fita take kuka, yana jin ta zuciyar sa kamar ta tarwatse haka yake ji dan bakin ciki ga kukan da take masa yana taba zuciyar sa, ganin ta raba masa hankali gida biyu yasa yai parking a gefen titi batai aune ba taji yai kasa da kujerar ta ya kwantar tare da rufa mata baya ya hade bakin su yana bata wani hot and romantic kiss wanda yasa kukan nata ya tsaya cak sai da ya dauki kusan minti goma yana kashe mata jiki da salon sa sannan ya sake ta. Lakwas tayi akan kujerar idon ta a lumshe, ya dago yana kallon ta yana sakin wani murmushi da shi kadai yasan manufar sa. Motar ya tayar suka karasa gida, yana zuwa yai parking har ya fito idon ta a rufe, ya zagayo ya bude barin da take ya ciccibe ta tana jin sa amman tai masa shiru, kofa ya bude suka shiga ciki direct bedroom ya ajiye ta akan gado, bai wata wata ba ya fara cire mata rigar jikin ta, sai da ya cire ya kunce zanin jikin ta ya zare ya rage daga ita sai underwear da vest, juya masa baya tayi hawaye na zubowa a idon ta, kayan jikin sa ya cire ya hau gadon ya janyo ta jikin sa, danshin hawayen ta yaji da sauri ya juyo da ita yana fadin "Wai me yake faruwa ne?" Ture shi ta farayi tace "Bama kasan me yake faruwa ba." Ta dire kafar ta a kasa da sauri ya janyo ta ta dawo saman gadon, wata rumguma yai mata wacce ta dole ta hakuri da son tashin da take, "To ki fada min menene?" Banza tai masa yace "Rashin fada min shi zai kawo rashin fahimta a tsakanin mu, yadda muka faro da sanin sirrin juna da fahimtar juna bai kamata ki canja haka ba." Kuka ta fashe dashi ya hau lallashin ta yana fadin "Naji kiyi hakuri to, akan Tasleem ne?" Kai ta gyada yace "To ke menene na damun kanki, uhmm." "Me ya kawo ta motar ka? Har take cewa na shiga mu tafi." Rumgume ta ya karayi yace "Ina zuwa ne fa ta shiga, ke kuma kika zo kuma kika tafi kika barni dan wa nazo wajen?" "Amman dan me ka barta ta zauna a motar bayan kasan zan fito, ni ka fada min in kana son ta ne." Kai ya hau girgizawa yana fadin "Lala lalah ni mijin Maryam ne kadai, kuma Maryam ce kadai *Matar Haidar* dan haka ba wata mace da nake so in ba Maryam ba." Kanta ta kwantar a kirjin sa tace "Ni in haka ne ba ruwan ka da ita." "An gama ranki ya dade." Ya fada yana kissing bakin ta, ido ta lumshe ta dago yace "Amman ke sai kiji haushi ki taho, ke da mijin ki, kin bata dama kenan fa." "Bana son nayi abinda ba zai mana dadi bane." "Da kika tafi dakin Inna me kike nufi?" "In yi kwana na man, ai nasan da ka shigo idon ta biyu ko bakin kofar dakin ba zata barka ka karaso ba." "Lallai ma 'yar nan kina son kina hukuntani da yin nesa dani bayan kinsan abinda yafi komai wahal dani kenan." "To ya zanyi ai ba kai ka dai kake wahalar ba." Ta fada tana dan lasar wuyan sa, ido ya lumshe ya zura hannun sa cikin vest din ta yana shafa saman cikin ta zuwa marar ta wanda take jin abun, take ya yafara hautsina mata tunanin ta nan da nan ta birkice masa suka hau sarrafa junan su son ransu. *Wallahi da farkon fara rubuta MATAR HAIDAR ban taba zaton zai samu masoya masu karanta shi ba, ashe dai haka ake karanta MATAR HAIDAR, hakika a ko wanne littafi ina haduwa da masoya wanda ko bayan littafin zumuncin mu ke kara daurewa, akwai da yawa daga cikin makaranta littafi na da suka zamar min tamkar yan uwa, mun yadda da juna, hakika ina godiya ga masoya makaranta MATAR HAIDAR, wanda na sani da wanda ban sani ba dukkan ku ina godiya Allahu ya bar kauna. Amin* *Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.* *Antty* [12/14, 19:48] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 88 By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Washe gari daurin aure tare suka tafi ya ajiye ta a gida ya nufi wajen daurin auren, a gida ta samu su Najwa da Yaa Hanna dan duk kwana sukai, bata dade da zuwa ba Aisha da Rukayya suka karaso, Basma da taga Maryam ta rumgume ta, Maryam ta ture ta tace "Ni ba ruwa na dake daki 'kaki zuwa ki kwanan mana" "Kai Anty ance gidan ku ai bai zama." Basma ta fada, Najwa, Maryam ta kalla ta harara tace "Nagode shiyasa ai Rukayya ma taki tazo Allah ya saka min tinda abinda kuke min kenan." "Ba wani nan Rukayya ai ke shaida ce da muka ce zamuje ba hana mu yayi ba." Najwa ta fada tana mai da tambayar ga Rukkaya "Abu kusan shekara dan iskanci." Maryam ta fada, Aisha ta dafa ta tace "Ke rabu dasu kada su zo din." Kamar zatai kuka tace "Amman ai ba dadi ko?" Dariya Aisha tayi, dan Maryam in abun yazo akwai shagwaba ji akan dan wannan abun zatai kuka, Anty Hanna da ke jin su tace "To ba sai suyi tayi ba, ai ni abinda nake so kenan, Yaya yana kular min dake." Kallon Anty Hannah suke ta dan harare su tace "Taso kinji kanwata in baki wani sirrin da zaki kara rikita Yaya." Ta kamo hannunta suka mike, Najwa da Aisha suka ce "Haba Anty muma muna so." "Ba wanda zan fadawa tinda tsiya kuke mata." Sukai sama abinsu acan ma lallashin ta tayi, tare da nuna mata yadda zata cigaba da kula da mijin ta, haka Yaa Asiya da Bilkisu suka shigo suka same ta suka zauna suna tattaunawa da hirar su. Can sai gasu Najwa nan da Aisha gaba dayan su. Sai yamma da za ai Walima Tasleem ta zo gidan cikin wani material wanda akai masa wani banzan dinki, a kasa ta zauna wajen da aka saka kujeru tana kallon kowa d'ai d'ai, Maryam kuwa na sama Najwa ta tsare ta wai dole ai mata kwalliya inda ake mata amman duk ta gaji, sai da aka gama gaba dayan su sunyi anko cikin wata atamfa da sukai anko sosai sukai kyau kamar a debe su gudu, Najwa, Anty Hanna, Asiya, Bilkisu, Aisha, Rukky, da ita, kasa suka sauko suka bar Maryam wajen Haidar dake mata rigima ta dauko masa lemo, suka nufi store ta dauko masa ta bashi ya amsa yana fadin "Thank you Adda nah." Yai mata kiss a kumatu yai sama wajen Ummi. Ta mike tana murmushi tare da fara neman layin Aliyu dan basuyi waya ba tin dazu, yana cikin mutane yaga kiran dan sunje reception ya fito yace "Ya dai Baby?" "Ina ka shiga ina ta missing naka." "In zo mu tafi gida?" "Kai Yaya sai dare." "Yanzu zamu karaso gidan ai." "Ohk sai kunzo." "Bye muahh." Ta kashe wayar ta fita, tana fita ta karasa wajen su Najwa da suke zazzaune, Tasleem na gefen Najwa Maryam ta zauna a gefe Aisha, Aisha tace "Uhmm an gama soyayyar?" "Ina ai bazamu taba daina soyayya ba ni da Honey." Hannu Najwa ta tafa tace "Rashin kunya su Anty Hanna suka koya miki kenan ko?" Baki ta murguda tace "A gun mijin nawa ne ya zama rashin kunya." Sukai dariya suna hira abinsu. Jawahir ce ta kira ta bayan ta dauka tace "Uhmm ni daman nasan yau ba zan ganki ba please dear kinsan bani da wata 'kawa bayan ke dan Allah kizo kinji." "To yanzu ya zanyi Yaya bai dawo ba." "Zan kira Baby sai ya fada masa please Dear." "Ok kira shi nima zan kira shi yanzu sai mu taho dasu Najwa." "Yauwah dear." Ta kashe wayar, ta fara neman Yaa Aliyu, yana dauka ta sakar masa shagwaba yace "Ya dai Baby." "Yaya gidan su Jawahir zamu tafi." "Me zakuyi acan?" Cikin kissa da iya magana tana yi tana shagwabe murya tace "Kasan fa yadda muke sam bata da wata 'kawa bayan ni." Duk da basa tare amman sai da yaji tsigar jikin sa ta tashi da yadda tai maganar dan haka yace "To ya za ayi?" "Najwa zata kaimu." Ido ya lumshe yace "Baby ki kula da kanki." "Insha Allahu, thank you my love, bye." Ta kashe wayar tana fadin "Ku tashi muje gidan su Jawahir." Aisha, Najwa, Rukky, Bamsa da Maryam suka tafi, acan ma yinin ake sosai suna tare da amarya har akai magariba ta shirya motocin daukar amarya suka zo aka tafi da amare. Maryam ce zaune a kusa da Jawahir da ta rike hannun ta abokan ango na addu'a Yaa Farouk sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa. A haka suka gama ya mike zai rakasu su Aisha ma suka mike dan duk mazajen su sunzo, Yaa Haidar ne bai karaso ba bayan sun fita Jawahir tace "Wallahi tsoro nake ji Sis." Dariya Maryam ta saki tace "Haba Jarumar mata, menene na tsoro uhmm." Ta fada tana kanne mata ido, hararar ta tayi tace "Abar wasa na zamar miki ko?" "No sorry nasan Yaya he is gentle dear." "Uhmm!" Ta fada tana kamo hannun ta ta saka a kan kirjin ta, yadda zuciyar take bugawa, wannan yasa Maryam ta fara lallashin ta, suna cikin haka Yaa Haidar ya kira cewa yana kofar gida. Da dabara da wayo ta tafi ta bar Jawahir inda suka hadu da Yaa Farouk a waje, sukai sallama suka tafi. * Washe gari da safe a makare suka tashi, saboda gajiyar biki, wajen karfe sha daya, ta fito falon sanye da wani wando wanda iya kar sa cinya da riga karama gashin ta ya baje a gadon bayan ta, ji tayi ya rumgumo ta yana fadin "Ki tsaya ni man." Juyowa tayi ta rumgume shi tace "Honey yunwa nake ji." Ta fada tana diddire kafar ta daukar ta yayi yace "Muje na samar miki abinci ni da na kwakwule ki." Ya ajiye ta akan kujera, ta dago tana sakin murmushi, kamar ance ta kalli bakin kofa, ta kalla, ido ta dan zaro ganin ta tsaye a bakin kofar. Wani murmushi ta saki, tana kara shigewa jikin Yaa Haidar idon ta akan kofa tana kallon Tasleem dake tsaye ta zuba musu ido, Yaa Haidar da bai gajiya da kasancewa da ita ya kara rumgume ta yace "Ke da kika ce yunwa kike ji." "Uhmm amman ba abinci zan ci ba." Hannu ya zura cikin rigar ta yana shafa cikin ta da ya d'an taso yace "To me zaki ci." Hannu ta saka tana zagaye bakin sa dashi tace "In na sha wannan ma ai zan koshi." Tana fada tare da fara kissing bakin nasa, Yaa Haidar da abinda yake so kenan ya biye mata suna kissing junan su, kamar wanda basu taba ba haka suke jin wani dadi da basu taba jin irin sa ba, gaba daya ta manta da wata Tsaleem Yaa Haidar da bai san da zuwan ta ba kuwa yana ta bidirin sa, Tasleem kuwa ganin abu yana son yafi karfin ta yasa ta fice a gidan da sauri hawaye na zubo wa a idon ta, bata taba zaton Yaa Haidar haka yake son Maryam da kula da ita ba dan tana ganin shi bai da lokacin mace amman sai gashi akan idon ta yadda yake kula da ita, tabbas akwai wani abu a kasa da ta kasa sani. Ko da yake jiya tana jin hirar su Anty Hannah da suke fadin canjawar Yaya da yadda suke shan soyayyar su basa kunyar kowa, hawaye taji ya fara zubo mata na karaya tabbas tana son Yaya amman taga alama dole ta hakura dashi tinda a baya da bai da kowa ma bai kula ta ba ina yanzu da yake da wacce matar mai kama da aljannu yar iska wacce take ta'ba miji a gaban ta. Ita kadai ta dinga zagin Maryam har ta koma gidan Sitti ranta a matukar bace, danasanin zuwa Nigeria take gaba daya. Sai da suka kara samun nutsuwa sukai wanka sannan ya shiga kitchen cornflask ya hada mata ya kawo mata ta fara sha sannan ya shiga yai worming farfesun kayan cikin da tayi jiya ya debo kayan tea, anan jikin sa ya hada mata tea bayan ta sha taci kayan cikin yana kallon ta yana jin son ta na dada shigar sa, sai kuma mamakin cin da take yanzu wanda a da karamin cup take sha na tea amman yau Maryam ce ta sha cornflask tasha tea taci kayan ciki, murmushi yake ta dago tace "Ya dai Yaya?" Dariya yayi yace "Baby na yanzu abinci kike ci" Baki ta dan turo tace "Ai Babyn ka ne." Hannu ya daura akan cikin ta yace "Allah maka albarka." Ta saki murmushi tace "To kaci mana." "Kin koshi?" Kai ta gyada sannan ya fara ci. Bayan sun gama tare suka gyara gidan duka kara wanka sukaci kwaliyya abinsu suna zauna suna kallo tana jikin sa sai da zai tafi massalaci sallah ta tuna da wata Tasleem ita kadai a daki ta dinga dariya tana fadin "Ko ina ta tafi." Bayan ya dawo daga masallaci yace "Baby zani gida gobe su Momy zasu tafi zanje muyi sallama." Bai rufe baki ba ta dauki mayafi tana fadin "Zan rakaka Honey." Kallon ta ya tsaya yi, yasan yana cewa a'ah to daru zata hau yi masa dan haka ya kamo hannun ta kawai suka fita, gidan Ummi suka fara zuwa, suka gaisa suka tafi bangaren Inna dake zaune tana ganin su ta washe baki tace "Ah Maryam kune bakya gajiya duk zaryar nan da aka sha kika kara biyo sa kuka fito ai kya zauna a gida ko dan ki huta ko?" "To ai ita tace sai ta fito ni ba ruwa na." Yaa Haidar ya fada, Maryam ta kalla, Maryam ta girgiza mata kai, Inna tace "Ba wani nan, kai kuwa da baka son tai nesa dakai, wai ya akai shekaran jiya na neme ki na rasa." Baki Maryam ta turo tace "Ba zuwa yai ya dauke ni ba, har da rufen baki dan kada na tashe ki ki taimakan." "Yanzu Aliyu haka ka koma da jaraba ace yarinya ba zakana daga mata kafa ba." Mikewa yayi ya nufi kofa yana fadin "Amman Inna ai dai naga matata ce ko?" Salati Inna ta fara tana tafa hannu tace "Yau ni kake cewa Maryam matar kace ko? Ai na sani ba sai ka kara fada min ba tinda gashi nan har ciki nagani a tare da ita...." Da sauri Maryam ta mike ta nufi kofa tana fadin "Mun tafi Inna." "To ku gaida gidan." Ta karasa wajen Yaa Haidar suka shiga mota, kallon ta yayi yace "Inna tafiya neman magana." "Kai Yaya ai gaskiya ta fada." Hararar ta yayi ya tada mota, gidan Sitti suka nufa suna zuwa Basma ta rumgume Maryam tana fadin "Oyoyo Anty Maryam." Falo suka shiga suka gaishe da Sitti, da Momy. Tasleem dake zaune rike da waya ko kallon su batayi ba, Yaa Haidar ya dan kalle ta ya dauke kai yace "Ke baki iya gaisuwa bane." Baki ta turo, Sitti tace "Gata nan tin safe da ta fita ta dawo take cicin magani ko magana ta kasa." Maryam ta dan saki murmushi, Sitti tace "Ya gajiyar biki?" Maryam tace "Tabi jiki Sitti." Ta mike sukai ciki ita da Basma, tana daki Jawahir ta kira ta tana fadin "Wai ba zaki zo bane." Ido ta zaro tace "Wa A'ah aci amarci lafiya ya gajiya." "Ban sani ba." Ta kashe wayar, dariya Maryam tayi sukai waya dasu Aisha da Rukayya da su zasu d'aga yanzu. Sai yamma suka tafi gida. Tasleem kuwa ko marmarin kallon Maryam da Yaa Haidar bata son tayi dan in ta kalle su a yanayin da ta gansu da safe take kara ganin su, haushin su take ji gaba dayan su. Bayan an gama biki kowa ya koma ya cigaba da rayuwar sa, wanda Maryam lokacin ba inda take zuwa kullum tana gida duk lokacin da Yaa Haidar yaji kewar ta ko yana waje aiki gida zai karaso yazo yaga matar sa tai masa abin dadi ya koma dan har abinci take aika masa bama in ta san zai kai yamma a asibiti. A haka suka cigaba da rainon cikinta sosai take samun kulawa daga gare shi da Ummi, watan cikin ta biyar Yaya Fadima da matar Yaa Muhammad suka zo duba ta, taji dadin zuwan su sosai, kwanan su biyu suka juya tayi kewar su. Kullum cikin yiwa Ammi magiya tazo amman tace me zatazo tai mata ga Ummin ta nan, haka Mami suna waya sosai, haka da Haidar karami ma suke waya ya saba dasu gaba dayan su. A haka suka cigaba da rainon cikin su har ya shiga wata tara wanda a lokaci kuma cikin sai ya safa rigima abu kad'an kuka da shagwaba, sam bata iya ko bacci in bata tare da Yaa Haidar haka duk inda yake zata nemo shi ta kwanta a jikin sa yana massaging jikin ta da mata kalamai masu dadi har bacci ya dauke ta. Tin da satin haihuwar yazo suka koma wajen Ummi ta cigaba da kula da ita wanda kwana su biyu da safe bayan ya tafi aiki nakuda ta fara da sukaje aka duba ta akace da sauran, Aliyu na tare da ita daga baya hannun ta ya kama tana tattakawa in abun yazo zata duke a wajen sannan su tashi su cigaba a haka har haihuwar tazo gadan gadan aka shige da ita aka fara taimaka mata bata jima ba ta haifi babyn ta katuwa da ita kyakyawa mai kama da Abban ta sak. Lokacin da Yaa Haidar ya dauki Babyn kuka ya saka yana mai godiya da Allah da ya nuna masa jinin sa kan ya koma ga Allah, Haidar karami ma sai murna yake Momyn sa ta samo masa kanwa. Tana kwance Yaa Haidar ya karasa gadon da take rike da Baby, zama yayi a gefen ta yana nuno mata fuskar Babyn ido ta lumshe ya shafa kanta yana sakar mata kiss a goshin ta yace "Sannu *Matar Haidar* Allah miki albarka ya baki lafiya, ina son ki *Ummu Haidar* " Ido ta lumshe tana mai karajin son mijin ta, Najwa da ta shigo tace "Yaya a gadon asibitin ma sai kunyi soyayya." Ummi ya kalla dake waya ya dan harari Najwan yace "Bar nan marar kunya." Baki ta turo tace "Bani 'yar tawa to." Ta amsa ta basu waje, Yaa Haidar kuwa sai addu'a yake wa Maryam da kalamai masu dadi wanda yasa take jin wani sanyi da dadi a cikin zuciyar ta. A ranar aka sallame su suka koma gida, d'akin ta aka gyara suka zauna ita da Babyn ta, da dare wajen goma ya shigo dakin nasu, tana zaune rike da Babyn da ta gama shan mama ta mika masa ya amsa ya saka a kafada yana shafa bayan ta sannan ya sauke ta ya ajiye ta akan gadon, Maryam ya janyo jikin sa yana shinshinar wuyan ta dake tashin kamshi, yace "Kamar ba mai jego ba." "Kai Yaya." "Uhmm ni bama wannan ma yau a ina zan kwana?" Dariya ta dan saki tace "Ka tafi d'akin ka nima baka ga a inda nake ba." "Anya zan iya kuwa?" Kofar d'akin aka budo Ummi ta shigo da sallama, turus tayi, Maryam ta janye daga jikin sa da sauri, Ummi tace "Ka tashi ka tafi ka barta tai bacci ta huta." Kai ya hau shafawa yana fadin "Ummi korata zaki." "Ai dare yayi Dr." "To bari naiwa Baby bye bye." Ya dauki babyn yai masa addu'a ya ajiye, Ummi ta fita, Maryam da ta juya musu baya ya janyo yana daura ta akan cinyar sa, sauka tayi tace "Yaya kada Ummi ta dawo fa." "Amman ai mayi sallama ko?" Bakin sa ta kama ta dan tsotsa sannan ta sake shi tana fadin "Sai da safe." Kamo ta yayi ya hade bakin su sai da ya jima yana kissing nata sannan ya sake ta, ya gyara mata kwanciyya yai musu addu'a sannan ya sauka ya tafi dakin sa. * Ana ya gobe suna yan Kano suka sauka, zo kuga murna sun tahowa da Baby da maman Baby kayan barka masu yawa da kyau da tsada, ranar suna Babyn taci sunan Ummi Aisha suke kiran ta da Humairah haka akai taron suna lafiya, Maryam ta samu kayan barka daga yan uwan ta, dan jin ta take tafi kowa gata yan uwa ne da ita ga na Kano gasu Yaya Hannah da suka zame mata suma yan uwa masu son ta da kaunar ta, haka nan Yaa Abubakar ya dauke ta tamkar kanwar sa ta ciki d'aya duk wata sai ya turo mata kudi tare dayiwa Haidar siyayya haka zai kira su gaisa yaji me take so, akai akai kuma yake sa Anty zuwa ta dubo ta, dan haka itama ta dauki shi tamkar su Yaa Alkasim, tana kara girmama shi tare da son sa da dan uwan sa da d'an dake tsakanin su, haka Mami ma da tazo barka ta kawo musu kaya masu yawa da tsada, ita kuwa me zatace ga yan uwan Yaa Haidar, ai ba abinda zatai musu sai addu'a shima Allah ya jikan sa ya kyautata makwanci. Ta yadda ita da Haidar ba wanda ya kai su gata da yan uwa masu son su. Bayan suna da kwana biyu su Yaya Fadima suka koma. * Sosai Maryam take jin dadin jegon ta dan Ummi ba karamin kula da gyara ta take ba, cikin satin su na biyu suka kara kyau ita da Babyn sukai jajir abin sha'awa dasu. Zaune take a dakin ta tana bawa Humairah mama, taci kwalliya sai kace mai shirin zuwa wajen biki, sai kamshi take yi, Yaa Haidar ne ya shigo bakin sa dauke da sallama, amsawa tai tana mai sakar mata murmushi shima ya sakar mata ya karaso ciki ya zauna a gefen su yana rumgume ta a jikin sa, ido ta lumshe tace "Sannu da zuwa Yaya." Babyn ya cire daga shan Maman ya ajiye a gefe ya daga Maryam ya daura a cinyar sa yana shafa kirjin ta, ido ta lumshe ta kwantar da kanta a kirjin sa. "Wai wannan wankan dole ne?" Ido ta bude a hankali tace "Haba Honey, kwana nawa ya rage." "Wallahi na gaji Baby kuma naji Ummi na fadin zakije Kano?" Kai ta gyada tace "Zanje Ammi da Abbi suga Humairah." "Dan Allah ki bari in mun koma gida sai muje muyi kwana biyu mu dawo." "Duk yada kace Yaya." "Yauwah yar aljanna shiyasa nake son ki." Ya kama lips din ta yana tsotsa. A haka suka dan ragewa junan su zafi. * Ana gobe arba'in ya samu Ummi zaune a daki, ta kalle shi tace "Jibi fa tafiyar su Maryam banji kana shiri ba." "Ummi ai nace a bari in mun koma da sati sai muje tare ko?" "Aliyu ba dole nake so nai maka ba amman kana gani tinda Maryam taga yan uwan ta bata taba zuwa tai kwanaki cikin yan uwan ta ba, ni da ta tawa ce ka barta ta tafi jibin, daga can taje Adamawa ta nunawa su Malam Babyn kaga suma zasuji dadi itama haka amman ace bata da damar da zata gida ta dade taga yan uwan ta." "Shikenan Ummi." "Yauwah Dr Allah maka albarka." Ranar da sukai arba'in washe gari suka daga Kano har da Haidar karami da suka samu hutu, kwanan ta biyu a gida duk suka tafi Adamawa, satin su daya acan wanda taga gata sosai da soyayyar yan uwan ta sannan suka dawo gida Kano taje gidan duk yan uwan ta yini suma sun zo gida sun sha hira sosai suka kara gyara yar uwar tasu, wanda satin ta biyu Yaa Haidar ya sauka, kwana sa biyu suka juya gaba dayan su, gidan Ummi suka sauka sai dare sannan suka wuce gidan su. Tin a mota yake rawar kafa, Maryam dai sai dariya take masa, yan d'an harare ta yace "Allah ban kara yadda da wannan tafiyar mai tsayi in har ta zama dole to sai dai ayi dani." Tana dariya tace "Nima zanso na kasance a tare da miji na." "Ba wani nan kina can kinawa Ammi shagwaba naga dai ke ba auta bace." Ido ta zaro tace "Wa yace maka. Ai i will always be Ammi's Autah." "Kin girma fa ya'ya biyu." "Allah yaya ko goma ne am Ammi's Autah, and i will always do what u ever i want to both you and them." "Allah ya kawo goman." "Yaya da yawa fa." "Ni ina so ai." "Allah ya kawo mana masu albarka." Ya fada yana shafa kan Humairah dake bacci. Bayan sun shiga gida. Ta kwantar da Baby, tare suka shiga wanka tin acan suka fara shan soyayyar su wankan da ba ai bama suka fito. A ranar soyayyar da aka jima ba ayi ba ita aka sha aka yi nanuwa juna yadda sukai missing junan su, sai da suka gamsu da junan su, suka nutsu, suka kara yadda da soyayyar juna su, sun yadda in ba daya daya yana cikin garari wanda suke addu'a Allah ya barsu tare. _Muna ta bankwana fa, *Matar Haidar* yana ta hade kayan sa._ *Baki na ya kasa rufuwa ido na ya ciko da kwalla saboda soyayya, hakika zanyi miss naku, more especially Amina Yar'adua, Shaheedah, Jamila. Amina Yar'adua your comment makes me laugh even if am not in the mood, i so much love you Mamanah, i will miss your comment i hope u will be with me in my coming books, i really appreciate with your love, ban taba jin kewar irin wannan ba, ina fatan ta alheri ce, to ban sani ba ko shine last book dina, kila ba zan kara wani rubutun ba zan mutu, in haka ta faru please wanda na bata wa wanda na sani da wanda ban sani ba ya yafe min, ni na yafewa kowa dan wannan soyayyar taku tana sani naji zuciya ta ta karye har hawaye ya zubo min. Ina son ku da kaunar ku. Allah ya sada mu da alheri Amin. Please in na mutu kuyi min addu'a Allah ya yafe min ya jikan mu baki d'aya.* *I will miss you readers* 😢 😢 😢 *Allah jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe.* *Antty* [12/15, 18:56] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗 Page 89-90 *Epilogue* By *MARYAM S INDABAWA* *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* HAJOW ✍🏻✍🏻✍🏻 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐 (United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.) Facebook @Maryam Sulaiman Instagram @Maryam S Indabawa Wattpad @MSindabawa *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *JAN HANKALI* *BAN YADDA WANI KO WATA YA COPY KO YA JUYA MIN LABARI, KO YA KARANTA MIN A KO WANNE CHANNEL BA TARE DA IZINI NA BA. NAGODE* 6 years later Masha Allah rayuwace mai dad'i da zaman lafiya suke ciki gaba daya familyn kowa sai sam barka duk da wani lokacin akwai wasu kalubale da Allah kan jarabci bawa amman Alhamdulillah komai yana zuwan musu da sauki baya fin karfin su saboda sun rike Allah da bauta masa ba dare ba rana haka nan sun kyautatawa iyayen su da yan uwan su, a tsakanin su baka taba jin wani fada ko sabani kowa yana son dan uwan sa duk inda suka hadu zaka kamar su cinye junan su ya'yan na da zumunci da son junan su. Cikin wannan shekarun Aliyu ya kara zama babban mutum dan har asibitin sa ya bude wanda yake aiki tare da matar sa duk da ita bata fiya fita aiki ba bama da ta cigaba da karatu har ta zama babbar likitan mata wanda ake ji da ita ba a iya Abuja ba har a Nigeria baki daya dan ma ba aiki take sosai ba in kaga ta shiga asibiti to an samu masu bukatar taimakon ta sosai wanda dole sai ita sannan take shiga asibiti ta. Sosai suka samu cigaba daga asibitin nasu dan yadda suke da kwararun likitoci. A cikin wadan nan shekarun Maryam ta sake haihuwar Baby girl sau biyu, ta farko aka saka mata suna Maryam din suke kiran ta da Islam sai ta biyun ta aka saka mata sunan Mami suke kiran ta da Sajida, Najwa ma ya'yan ta uku maza biyu mace daya sai Aisha ma ya'yan ta uku mata biyu namiji daya, Rukayya ya'yan ta biyu mace da namiji inda namijin yaci suna Yaa Haidar, Anty Nusaiba matar Yaya Abubakar ma ta sake haihuwar ya'ya biyu duk maza, Yaa Farouk da Jawahir ma ya'yan su biyu mace da namiji daya sunan Mama ya saka mata sai namijin yasa suna Abba Usman. * Zaune take a falon Ummi sanye cikin wata atamfa fara ce wacce akai mata ado da blue and orange kala dinkin doguwar riga ne wanda yaji stone tai kyau ta sha dauri ga sakar gold wuya da hannun ta, Maryam ta kara kyau ta ciko ba rama a jikin ta ta kara haske kana ganin ta kasan kwanciyyar hankali ta zauna mata, Ummi ce ke zaune a gefen ta tana kallon tana murmushi, yadda take magana kamar zatai kuka, tana fadin "Dan Allah Ummi ki sa baki yaki ya barni naje sam kuma Ummi kusan shekara fa rabo na da Kano, in ba irin hakan ce ta faru fa bai fiya bari na naje ba." Tai maganar cike da shagwaba wacce har yanzu taki ta barta. Haidar, da kannen sa Humaira, Islam, da Sajida, suka shigo a tare cikin shiga iri daya, dogayen riguna ne a jikin su, red and white kala wanda kansu an musu kitso jelar ta fito ta kasan hular dake kan su iri daya hatta takalmin su iri daya ne, in kaga Humaira da Islam sai ka zata yan biyu ne dan basu da nesa sosai, Sajida ce yar shekara uku, Haidar ma wando ne jeans da har riga a jikin sa, sai takamlmi baki yaran kyawawa dasu abin sha'awa dukkan su leda ce a hannun su. Sajida ce ta nufi wajen Maryam ta hau an cinyar ta tana fadi "Momy kinga abinda Dady ya siyo mana." Janye ta tayi dan ita so take taji abinda Ummi zata fada dan tana son taje Kano ta hadu da yan uwan ta, wanda Matar Yaa Abdullah ce ta haihu take son zuwa sunan. "Daughter ki bar damuwa zan masa magana shikenan?" Kai ta gyada tana sakin murmushi, Sajida ta makale mata daukar ta tayi tana fadin "Menene Sajida?" Ta rumgume yarinyar da take kama da ita sak, dan Haidar kama yake da Abbin sa haka Humaira da Islam kamar su daya da Abbin su, Sajidar ce tayo ta gaba daya kamar ita haka su Ammi ke fadi. Yaa Haidar ne ya shigo dakin da sallama cikin shiga ta alfarma sai tashin kamshi yake, amsawa suka ya zauna akan kujera yana fadin "Ku fito mu tafi gida." Sajida, Maryam ta ajiye tai sama dan hado kayan su, da kallo ya bita sannan ya kalli Ummi yace "Ummi yar taki sai rigima take ji fa." "Ai Aliyu in ma tayi ba matsala tinda kai ka jawo." "Ni kuma Ummi?" "Dole fa kana barin ta tana shiga yan uwan ta, dan ma ka same ta mai hakuri ne, in wata ce ba zatana wata biyu bataje gida ba amman ita daga nan zuwa Kano ace kai ta hana ta zuwa sai ta shekara bataje ba, gaskiya Aliyu kana barin ta tana zuwa sai kace wata uwa duniya." "Ummi saboda makarantar yara ne fa." "Yanzu ai hutu suke, ka barta taje ta shiga cikin yan uwan ta." "Shkenan Ummi, amman in ta tafi ni kuma fa. "Kai meyasa baka da hakuri in dai akan Maryam ne, duk tsiya fa in taje ba zatai sati uku ba." "Ummi ba zaki gane bane, wallahi kwana daya in nayi babu ita ni kadai nasan me nake ji, shiyasa sam bana son tai nesa dani amman tinda kinsa baki shikenan amman sati daya Ummi." "Sati daya yai kadan Aliyu ka barta tai sati biyu kaga hutun su Haidar da yawa." "Ummi...." "Dan Allah Aliyu." "Ummi an gama Allah ya kaimu shikenan." "Allah maka albarka." "Amin." Saukowa tayi da jakar ta da jakar kayan su Haidar ta ajiye tace "Bari naiwa su Inna sallama." Ta fita ta nufi sashen Inna acan sukai sallama ta shiga taiwa Mama da Mami sallama ta fito a compound ta same shi da yaran Ummi na tsaye, ta karasa ta rumgume Ummi tace "Ummi mungode sai da safe." "Allah bamu alheri amman in kun dawo su Islam zasu zo suyi mana kwana biyu?" "Abinda nace kenan sai su karasa hutun su." Yaa Aliyu ya fada "Shikenan ku gaida gidan." Suka shiga mota suna dagawa Ummi hannu, sai da suka fita a gida ya kamo hannun ta yace "To kiyi murmushi mana *Matar Haidar.* " Juyowa tayi ta saki murnushi, ya kai hannun ta bakin sa yai kissing yace "I love you." Murmushi kawai ta sakar masa, har suka karasa gida. wanda yaran duk sunyi bacci, Sajida ta dauka ta shiga da ita ta canja mata kaya, Ya Haidar ya shigo Humaira da Islam itama ta canja masu kaya, addu'a tai musu sannan ta nufi dakin Haidar da shima Yaa Haidar ya kwantar dashi, addu'a tai masa sannan ta fita, bayan ta kashe masa fitila. Fita tayi nufi bangaren masu aikin su, Baba Ramma ta sama tana gyangyadi ta zauna tana fadin "Baba kije ki kwanta mana, ina Salamatun?" Baba da ta farka tace "Tana ciki, banji duriyar ku ba shiyasa ban kwanta ba, kun dawo lafiya yasu Ummin?" "Suna lafiya suna gaishe ku." "Muna amsawa." Ta mike tace "Bari naje na kwanta sai da safe." "Allah tashe mu lafiya." "Amin." Ta mike ta fita. Bangaren su ta shiga ta nufi dakin ta ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wata pink kalar rigar bacci tai mata kyau sosai ta shafa turare mai dadin kamshi, kofa ta nufa inda tana daura hannu taji an bude ta ja baya ya shigo yana binta da kallon so da tsantsar sha'awa, jikin sa ta shige tana sauke ajiyar zuciya tace "Yaya nah!" Ya kara rumgumo ta yana fadin "Noor ina son ki bana son ki nesa dani." "Nima haka Yaya." Ta fada tana daura bakin ta akan wuyan sa, tana bashi wani kiss, dan janyewa yayi yace "Ba wani nan gashi nan har da fadawa Ummi dan kinsan in tace dole ayi, ni nasan me zanyi tinda wahala nake in zaki gida aure zan kara yadda in kin tafi zan samu mai kula dani da kin dawo kuma shikenan." Jikin shi ta shige tana sakin kukan shagwaba tace "Ni dai ban yadda ba Allah in haka ne na fasa zuwa shikenan." Ya daga ta ya ajiye akan katon gadon da ya sha sabon zanin gado sai kamshi ke tashi a kai, kissing nata ya fara a haka suka cigaba da faranta ran junan su, washe gari ma da yai maganar tafiya cewa tayi ta fasa amman yace ta shirya tinda yaiwa Ummi alkawari the next day suka daga Kano cike da kewar mijin nata, kwanan su daya akai suna gaba daya yan uwan ta sun zo yaran su suka hadu gaba dayan su, familyn Abbi ya hadu aka sada zumunci, tin bayan sunan ta fara jin sauyi a tare da ita da kanta tai wa kanta test ta gane shigar cikin dake jikin ta. Murna tayi sosai tana fadin "In Yaya ya gane ko yaya zai?" Dan Aliyu yana son yara duk lokacin da ta samu cikin in kaga yadda yake murna kamar bata taba haihuwa ba, haka in ta haihu yadda yake mata kyauta da nuna musu kulawa kamar ya mai dasu cikin sa. Kullun kuwa suna makale da waya da dare kusan kwana suke soyayya a waya a haka suka cinye sati biyun su suka tashi tafiya, shi ya dauko su, tin a hanya yake binta da kallon mai cike da so da kauna, ganin sun kar kata hanyar gidan Ummi tace "Ina kuma zaka kaimu?" "Su Haidar zan ajiye dan gaskiya ina son nima na huta da matata bana son kowa ya damen." "Kai Honey waye zai dame kan?" "Ga Sajida nan da bata son barin jikin ki kullum kuna makale da juna." Dan hararar sa tayi ta shafa kan Sajida da zuro da kan ta ta baya tana wasa. A haka suka karasa gidan suna shiga suka bude kofa suka fita a guje, da kallo ta bisu tana mai fadin "A tafi a hankali dai." Ai ina sun fice har Sajida, hannu ta sa zata bude kofar taji ya saka lock juyowa tai ta kalle shi tace "Ka bude min mana." "Gida zamu tafi." "Haba Yaya ai ma gaisa da Ummi ko?" "Wallahi Baby a matse nake kawai muje." Ya fada yana kunna motar, tare da ficewa a gidan. Tin daga compound ya dauke ta kamar Baby suka shige ciki, a kan gado ya ajiye ta wanda yai dai dai da fara ringing din wayar ta dauka tayi tana ganin Ummi tace "Kaga ko ni ban san me zan ce mata ba." Wayar ce ta katse wani kiran ya kara shigowa amsar wayar yayi ya kai kune yace "Ummi kinga su Haidar ko? Mun shige gida ne sai gobe zamu shigo." "To a gaishe min da daugther." "Zataji." Ya kashe wayar yana fadin "Ummi na ai wayayyiya ce ba ruwan ta." Hararar sa tayi tace "Bari na watsa ruwa." Ta mike tana zuge zip, tana zare rigar taji ya rumgume ta ta baya ya fara kissing dukkan jikin ta, daga haka ya dauke ta suka haye gado suna shan soyayyar su. Kwance yake akan gadon Maryam kwance a jikin sa idon ta a lumshe hannun sa na bayan ta yana massaging nata, saukar hannun sa akan hips din ta yasa ya dan bude ido yana fadin "Noor let me check you." "Me zaka duba?" "You know what?" Kai ta girgiza ya kai bakin sa kunnen ta yana mata rada, hannu ta daura akan bakin sa tana fadin "To wa ya sani?" "Please am i right?" Fuska ta rufe da hannayen ta tace "Na yadda kai Dr ne." Ta fada tana murmushi, yai murmushi yace "Da gaske dai Sajida zata samu 'kani ko 'kanwa?" Kai ta gyada tana rufe kan ta a jikn sa, murmushi ya saki yana kara rumgume ta tare fadin "Alhamdulillah, Allah nagode maka a baya nayi zaton ba zan kara aure ba bare har na ga jini na sai gashi yau ni ne da ya'ya har hudu ina shirin samun na biyar, Alhamdulillh, Allah nagode maka, Allah ya kara min ni'ima Allah ya yasa ki haifa min yan uku." Ido ta zaro tana fadin "Dan ba kai kake haihuwar ba ko?" "Zan amshi wannan baki ga wannan cikin ba ruwan sa ba." Bakin sa ta kama tana kissing, sannan ta saka ta dago tana kashe shi da wani kallon so da kauna, hannun ta yana wayo a jikin sa, idon sa a lumshe tace "Wannan naga bukata ya dada min ni kadai nasan yadda naji a Kano lokacin da bama tare." "Ai naga alama, tinda tin da kika zo kike tsotse ne." "Kai Honey har da sharri kai ban ce ka tsotse ni ba sai kai." Bakin ta yai kissing yana fadin "Zo na kara tsotse kin." Ya hade bakin su yana romancing nata daga nan suka cigaba da soyayyar su. A haka suka cigaba da rainon cikin wanda bata da matsalar komai kulawa take samu daga Aliyu har yan uwan ta. Cikin watan ta tara ta haifi dan ta kyakyawa namiji mai kama sak da Abbin sa, sosai Yaa Aliyu yayi farin ciki inda ranar sunan yaron yaci sunan Abbin Maryam Muhammad. Two years later Zaune suke a cikin jirgi Maryam sai Aliyu dake gefe ta, kan ta ta daura akan kafadar sa tana mai lumshe ido, kan sa ya sunkuyo ya dan yi kissing bakin ta, " 'Dan ka dai yana kallon ka." Ta fada tana nuno masa Haidar dake zaune a kujerar dake opposite din su kunnen sa makale da earpease yana sauraron karatn Alkur'ani, yaron shekara goma sha shida wanda yana shekara sha biyar ya haddace Alkur'ani ya gama secondary school din sa har ya zana jamb addmission kawai yake jira. Ya Haidar ya rumgumo ta yana fadin "Ina ruwa na da shi, dan shi sai naki kula da matata?" Murmushi ta saki ta rumgume shi tana fadin "Miji na sirri na, Mijina abin alfahari na." "Matata farin ciki na, matata abar alfahari na." "Ina son ka mijin Maryam." "Nima ina son ki *Matar Haidar,* Ummu Haidar, Humaira, Islam, Sajida, Aslam, and Sabir." Dan dagowa tayi tace "A ina Sabir din?" "Coming soon." Dariya tayi tace "Gaskiya yanzu sai na huta Yaya." "Haba Noor wane hutu kuma kin yaye Aslam uhmm." "In dan sha soyayya wai da." "Wannen cikin ne ya taba hanaki soyayya? Ai ke dai ki ta haifa min ya'yan so nake nan da shekara uku nagan mu da ya'ya bakwai ko takwas." Ido ta zaro tana fadin "Amman ba dani kadai ba ko?" "Da wa kenan?" "A'ah ban sani ba ko dai a gano wata yar baby." "Lalalalah, Haidar mijin Maryam ne kawai, Maryam ce kadai *Matar Haidar* insha Allahu." "Allah ya yadda Mijin Maryam i so much love you." "Am eager to be with u at home Baby." Narkewa ta karayi a jikin sa, tace "Kano zan tafi muna sauka." "Da izinin wa?" "Izinin My." "Ban yadda ba ki bari muje next week muyi two days ko?" "An gama Ranka ya dade." "I love you Honey." "I love you more." Ya rumgume matar sa suna 'kara keta hazo dan dawowa gida Nigeria daga 'kasa mai tsarki da sukeje sukai aikin hajj. *Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!* Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon da kuma karshen littafin *MATAR HAIDAR,* Allah ya yafe min kuraren da nai darasin dake ciki Allah ya ba mu ikon amfana da shi. *Afwan ina neman yafiyarku mace ko namiji babba ko yaro wanda na sani da wanda ban sani ba wanda na tab'a magana dashi ko ita da wanda ban tab'a magana ba ni na yafewa kowa. Fatan alheri.* *JAN HANKALI* *BAN YADDA WANI KO WATA YA COPY KO YA JUYA MIN LABARI, KO YA KARANTA MIN A KO WANNE CHANNEL BA TARE DA IZINI NA BA. NAGODE* _Na sadaukar da littafin nan ga My first and last love Ummi nah, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana Allah ya biya miki bukatun ki na alheri, Allah ya kara budi ya faranta miki duniya da lahira, Allah yai miki tukwici da gidan Aljanna madaukaki Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum. I so much love you My Mommy._ *Our Momy Hajiya Nafisa ina godiya da yadda kika kara min kwarin gwiwa tare da addu'a Allahu ya saka miki da gidan Aljanna, Allah ya biya miki bukatun ki na alheri Allah ya raya zuri'a Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.* _Mariya Kabir Bako (Bintu Sheihk), Fatima Muhammad Sani (Habibty), Sadiya Mohd (Barrister Sady) nagode da kauna da yadda kuke kara min kwarin gwiwa Allahu ya bar kauna Allah ya saka muku da gdn Aljanna. I so much love you Sisters._ *Ba zan manta daku ba makaranta *MATAR HAIDAR* ina godiya da yadda kuka bibiyi labarin nan tin daga farko har karshe nagode sosai da sosai.* Godiya ga dukkan member na wandan nan groups din *Indabawa Hausa Novels* *Matar Haidar Fans Group* *Hakuri da Juriyya Online writers* *Maryan Salisu Maidala* *Special Room Ummu Farisa* *Marahmad Chatting forum* *Sona Hausa Novel/ Qalbina comment group* *Masarautar Zeedan* *Romantic Hausa Novels* *Khaleesat Haydar Novels* *Kasaitattun Mata Group* *Na'ikke Hausa Novels* *RAZ Novella* *Bakuwar Fuska Fans* *Sirrin Zamantakewa* *Bintu Sheihk Hausa Novel group* *Hausa Novels* Da sauran da ban lissafo ba dukka ina godiya. I will not forget with my Facebook fans, the groups are many, but dukkan ku kuna raina na ina godiya da yadda kuke min comment da addu'a Allahu ya bar zumunci u all are the best thank you. *My Wattpad Fans, you too i really appreciate with all your, vote, comment, i heart u all, especially Aishaummulkairi and BarakaJoda, MamanAlmeen da sauran gaba saya* _Ba zan taba mantawa daku ba My whatsapp fans Amina Yar'adu'a, Samira Malami, Caramella Queen (Shaheedah), Nabila, Jamila, Zuwaira Zuzu, Ubaidah, Ummi Glomor, Kaltoom, Maryam Danlitti Sheshe, da sauran kuna da yawa sosai, nagode da yadda kuka kasance dani tin daga farko har karshen labari na nagode da yadda kuka dinga bani nishadi da addu'a tare da ban kwarin gwiwa i so much love you._ *Am so glad, i never know that MATAR HAIDAR will have such followers, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!* Sai kuma idan mun sake tarayya da ku a littafi na gaba, idan mai komai mai kowa ya yarje mana. AM SAYING A GOOD BYE TO *MATAR HAIDAR FANS* I GONNA MISS YOU ALL THANK, YOU, THANK YOU, THANK YOU. ```Dan Allah duk wanda ya karanta wannan littafin nawa yanzu ko nan gaba yai min addu'ar gamawa lafiya in kuma na mutu yai min addu'a Allah min rahma ya jikai na. Amin nagode``` ```Yaa Allah ka kawo mana dauki a cikan wannan rashin tsaron da muke fama dashi, Allah ka kare mu da duk al'ummar musulmai Allah ya daukaka musulunci da musulmai Allah ka karya karfici da kafirai Allah ka dadawa Annabi Muhammad SAW daraja Amin.``` _Allah ya jikan mu ya gafarta mana Allah ya mana rahma ya kyauta namu zuwan Allah yasa muyi kyakyawan karshe, Allah jikan dukkan musulmai ya kyautata namu zuwan Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum._ Fatan alheri daga taku har kullum *Maryam Suleiman Indabawa* *Subhanakallahumma wabi hamdika, ashahadu an la'ilaha illa anta, astagfiruka wa'atubu ilaika*