*TFZB2001* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Yana dafe da kansa kwata kwata baisan motar ta kwacemai ba sai da yaji ta fara yawo a kan titi sannan ya dawo hayyacinsa yana kokarin kamo Sitiyarin motar ne Amina Data ke kuka cikin karan sautinta taga wata babbar mota tayi kansu gadan gadan sai gabanta ya fadi,Kukanta ya Dauke da batasan sanda tayi tsalle sai gata jikin Danmallan cikin rawan jiki Ta kwalla kara tana Fadin"Wayyo Allah babbar mota...! Wani bakinciki da takaici su kusa kasheshi,bai samu damar mata mgana ba sai da ya daidaita Motar sannan ya gangara gefen hanya yayi parking kafin ya juyo yana kallon Amina wacce ke rike dashi Saboda Tsoro ran sa bai kara baci ba sai da yaga gabadaya Hawayenta da majinanta ta gama gogemai saman kafada wani irin kallon kyama da Haushi yake binta dashi ita batama Lura ba saboda bata cikin natsuwarta ga Halin datake ciki ga Razanan da tayi na ganin babbar Mota ta nufesu gadan gadan. Ganin sai zare ido take yi taki sakinsa yasa ya saki wani siririn Tsaki kafin ya Daka mata tsawa yana fadin"Ke...! Sai alokacin ta dawo Tunaninta ta Dago tana kallonsa ganin irin yadda yake Hararanta ne yasa tayi saurin Sakin rigarsa data cukwikwiye da hannayenta ta koma kujerarta ta zauna da Duwawunta tana maida Nunfashi Lokaci daya da ruwan hawaye suna gudu Bisa kumatunta. Ransa ya kara baci da ya kunna Hasken motar yaga yadda Maikon hannunta ya sakamai Shatin Datti ajikin Rigansa baisan sadda ya kalleta cikin bacin rai yana fadin"Ke wata irin kazamar yarinya ce mara natsuwa..?Ko sau daya tak a rayuwarki bazaki yi wani abu da zai nuna ke mace bace..? Yafada yana kallonta cikin Idanuwansa da suka fara sauya Launi Saboda bacin rai. Bata dago ba kanta ta kara maidawa kasa tana sharan kwallah kalmar kazaman daya fadamata bata Dameta ba kamar yadda yace mata mara natsuwa duk sanda ya fadamata haka sai ya sakata kuka yanzu ma Kukan ta fara Tana neman kara baremai baki da Sauri yace"Kika kuskura naji ihim dinki Wlh sai kin raina kanki..kinsan Zafin hannuna kuwa..?Baki sani ba na su Jafar kika sani to kika bari kika kaini bango da wannan banzan kukan naki wlh in na mareki sai bakin ki ya juya Hagu..Uselesss kawai..! Yafada Cikin Kufuluwa acikin ransa yana Faman kokuwa da yanayinsa Gabadaya an kuntatama rayuwarsa yanzu banda a kashesa da ransa Lokacinsa bai ba..?yi ta ina zai iya zama da wannan yarinyar..?Kukanta kadai ya isa yasa Hawan jini ya kamashi..! Ko kara kallonta bai yi ba ya maida kansa wajen kokarin tada Motar ammh sai me sai yaji kukan na kwace mata da sauri ya juyo yana kallonta Cikin mamaki ganin haka yasa tayi Saurin saka Hijabinta ta Danne bakinta Hawaye kamar famfo suna zuba bai mata mgana ba ya tada Motar suka hau kwalta ya fara Tafiya kenan kawai yaji ta bare baki ta saki kuka Da waani karin mamaki ya kara Binta da kallo yama rasa me zai ce mata,Hannunsa Daya rike da Sitiyari Daya kuma Dafe da kansa yana Bin ta da kallo ji yake kamar ya Tsaya a hanyar nan yayi wurgi da ita kalli Daga gidan mallam zuwa gidansa yarinyar nan har ta fara chazamai kai. Saboda bacin rai baisan sadda yace"Au kukan kike yi ko .? To wai ma tsaya me akayi miki ko kuma uban me kike so..? Cikin kukan tace"Ni kamaidani gida..bazan iya kwana wajen da ba Hanne da Hamida ba..! Harara ya jefa mata kamar ya Daketa Haka yake ji Cikin Fusata yace"To anki a maidake din..Sai kiyi abunda zaki yi in kin isa..Haba..Wannan iskancin ya isheni wlh bazaki je kina Damuna da wannan kukan banza naki ba mganinki zanyi..! Amina sai ta kara wage baki tana Fadin"Wayyo ni..Hanne...Yiyiiyiiii..Hamida..Wajen su zan je na shiga uku..Yiyiiyiiii..! Reras fa hake ta kuka Danmallan yayi zaune kawai mganarsa ta kare Ya rasa ma abunda zai ce mata kawai ya Cigaba da Tukinsa bayan ya Dauke kansa,Tsabar bala"in yarinyar nan kansa har ya fara saramai ina Dalili ganin bata yi shuru ba yasa ya Daka mata tsawar da yasa ta kama bakinta Cikin Daga Sautinsa yace"To baza ki koma wajen su ba ko zaki yi kukan jini ne..Salon ki je chan ku cigaba da yima mutane iskanci da raini ko..? To anan ni zan gyara miki zama wlh in baki min shuru da bakin ki anan wajen ba..Daganan Gidan gyaran Hali zan kai ki inda ake ladabarta da kangararrun yara marasa jin mgana irin ki sai kinyi kwana arba"in cikin mari kinji ma na Rantse..! Amina ta kallesa tsab tasan zai aika sai hankalinta ya fara tashi maimakon tayi shurun daya ce sai kawai ta Duke kasan Mota hannunta Bisa kai ta rushe da wani kukan dayafi wadanda tayi sauti da kara Fadi take"Don Allah kayi hakuri..Don Darajan iyayenka kayi hakuri..! Wlh kadan ya rage bai Bugama wani mai adaidaita ba saboda yadda Ihun ya shiga kansa ransa yakai kololuwar baci in ya zauna acikin motan nan zai iya ma yarinyar nan Lahani yasa baisan sadda ya Gangara gefen kwalta ba ya faka Motar a fusace ya Bude bangaransa ya fita Amina kuwa ta zata ita ya tsaya ya Daka yasa ta koma ta Lafe jikin kofa tana Rufe bakinta Cikin kuka sai taga ya fita ya Rufe kofar da karfi kamar zai ballah. Bayan Motar ya koma ya Dafe kansa cikin wani yanayi yake maimaita Hasbunallahi wani'imal wakeel..! Bai saurara ba sai da yaji ya Dawo Cikin natsuwarsa ya zai yi da wannan Fitinanniyar yarinyar da ke neman chajamai kai..? Wlh bazai iya zama da yarinyar nan ba Tun aTarihin rayuwarsa bai taba Daga Sautinsa irin na yau ba bai taba Fada irin na yau ba ko Sakina ta batamai rai baya Biyemata yana da Hakuri da kawaici sai ta Dade tana abunta bai Dago ya kalleta ba shi in ya tashi nashi Lokaci Daya zai yi shikenan kuma ya huce ballatana Sarood da bata da Hayaniya banda ma dan matsalan da suka samu da zasu taho Bikin nan. Karamin Tsaki yaja kawai afili yana kokarin samo ma kansa mafita Visar sa zai yi kokari ta fito Cikin Satin nan ya kara gaba kafin yarinyar nan ta kai shi bango yayi mata Dukan mutuwa Tunda ya Lura Baba mallam ya gama batata sannan su jafar ba Hukunci suke mata ba wani Burauban nata Harda iskanci da rashin natsuwa. Ya lura ba yarinta bane Tsabar iskanci ne da samun wuri banda haka kamar ita tasan ta iya waya da Saurayi a boye har suna haduwa..?ai shi sanda Mallam ke fadamai yana ta fadin yarinta ke damunta jinsa kawai yake wannan abun ya wuce yaro yayi sa tana Sane da duk abunda ta aikata shine Hajiya ke son ya kwasheta ya kaita Madina wlh ya tabbata watarana sai ta jawo silar abunda zai sa a Dauresa in ma bata yi sanadiyar barowarsa kasar ba gabadaya bama. Yana cikin wannan Tunanin wayarsa Dake gaban aljihun rigarsa ta Dauki kara,Daukota yayi ganin mai kirasa yasa ya saki ajiyar rai da salama da sauri ya Daga kiran yana Fadin"Ka kira alokacin Dayace Aliyu..! Ko sallama bai tsaya yayimai ba Tsabar Tashin hankali Aliyu dake zaune afalon gidansa ya gyara zama yana fadin"Shehi ango..Angon Sixty.. Tsabar Rudewar ne yasa yau Shehi ya manta da sallama..? Ya fada cikin shakiyancinsa Umar ya Saki karamin Tsaki kafin yace"Salamu alaikum..Na sha"afa ne Aliyu kaina ya Fara ciwo wlh..! Aliyu yajisa cikin wani yanayi yasa yace"Meya faru ne..? Baka koma gidan bane ko baka je gidan Mallam din bane..? Daman sunyi mgana Kafin ya fita Daga gida Cikin Kar ya Sauti yace"Na je gidan mallam..Bakasan wani abu ba..yarinyar nan fa suka hado da ita Aliyu..! Aliyu yace"Wata yarinya..? Danmallam ya Dafe kansa kafin yace"Kazamar yarinyar nan mana..! Aliyu yace"Nifa ban gane wata yarinya ba Sakina wai kake mgana..? Yafada cikin Danne Dariyansa Umar ransa ya baci cikin Haushi yace"Sakinar ce kazama Aliyu..? Amina fa nake maka mgana da nace maka Hajiya ta matsa sai ta tare yau din nan abu kamar za"a gudu..Ko kuma ana jirana Aliyu..! Aliyu ya saki yar dariya kafin yace"Au to..Kaine ka fadi sunan yarinya kaki kana ta fadamin kazama ni to ya zan yi na ganeta..? Wai yanzu kana nufin kuna tare..?To tana ina..? Yafada daidai sanda Aliya matarsa ta shigo Falon ganin yadda yake zaune yana waya ne yasa jikinta ya bata da Umar yake mgana Hararansa take ta kasan ido domin itama tashin Datayi Da Sakina taje Daki sukayi mgana Wlh tafi sakina Jin kishi da wannan auran Rainin da Umar yayi haba in ba Raini ba wannan kazamar yarinyar ta ina zata iya hada miji da ita komawa baya ne wlh,Ta fadama Sakina kada ta Sake ta bari ta shigar mata Dakin miji sai ta zata sun zama Daya da ita kenan sai dai ta nemi Dakin kwana Tun da Sakinar ta fadamata Labarin Tarewar ranta yake bace Har Aliyun taji Shima Haushinsa take ji tunda ya shigo take fadin rai yana ganin haka shima ya shareta bai bi ta kanta ba. Ganin yadda ta zubamai ido ne Umar na fadin"Wlh Aliyu yau kadai dana Dauko yarinyar nan har na fara gajiya..Can u just imaging kuka take min amota har tana wayyo Allanta har barazanar kaita gidam mari nayi taki yin shuru kafadamin ya zanyi..Wlh kaina har ya fara ciwo na rasa ya zanyi..? Yafada lokaci Daya yana Dafe kansa dayake Saramai Tun dazu Aliyu, Aliya yaga tana kallonsa yasa ya mike yana Fadin"Shehi me yayi zafi..? Kai da zakayi lallashi sai ka Bige da zuwa gidan mari..! Yafada yana Dariya Lokaci Daya yana Ficewa daga Falon zuwa bedroom dinsa yana jinta tana raka sa da fadin"Girma dai ya fadi wlh..! Shi yasan kan mganar domin tun da yadawo take sakin tsaki Lokaci bayan Lokaci sai tace an dai ji kunyar Wlh mutum ya rasa wazai aura sai yar Cikinsa ko batayi mgana ba yasan da Umar take so take ya tankata shima yau gidan nasu ya koma yakin Biyafara banda mata ma mata ne ina Ruwanki da batun gidan wata kai abun na bashi mamaki..! Sai da ya shiga Dakinsa ya kulle sannan yace"Ina jinka..na baro Falo ne..kasan nima yau gidana irin gidanka ne..Aliya na taya Sakina kishin ka yo musu amarya da karamar yarinya wai kama raina su..! Ya karishe fada yana yar Dariya Umar ya saki hanci kafin yace"Bangane tana taya ta Kishi ba..!? Nan Aliyu ya labartamai abunda ya faru Danmallam ya shafa gemunsa yana Fadin"Meyasa mata suke da karamin Tunani ne..?,Ita Aliya Daman haka take..!To yau in kai in zaka kara aure ya kenan..? Inaga baka ba kara aure Aliyu..! Aliyu yace"Wane ita..?Har ta isa wlh tallahi sai dai in banga wacce nake so ba..Ina da sha"awar kara aure Shehi in kaga ban yi ba to hakan na cikin Abunda Allah ya Tsaramin ne..! Umar yace"Lalle akwai yaki..Aliya zata cin na ma gidanka wuta..! Yafada yana yar dariya Aliyu yace"In ta fasa..Ni fa ba irinka bane da zan zauna anamin iskanci ban ci ubam Mutum ba..Wlh ban kai ka Hakuri ba Umar..Ina da kawaici ammh ba kowani Lokaci ba yanzun ma Daka ga na kyaleta Lokaci na bata in ta bari na tankamata sai ta raina kanta ni ba Sakaran Namiji bane ka sani..! Umar na yar dariya yace"Allah dai ya kyauta..! Aliyu ya amsa da Ameen kafin yace"Wai ina ka barta ne..? Umar yace"Tana cikin mota..Kaina ya fara ciwo wlh kukanta zai sakamin Dagaaawar jini Aliyu..! Agogon Wayarsa Aliyu ya Duba kafin ya maida wayar kunnensa yana Fadin"Shehi Dare fa yayi..Pass 9 goma ta kusa..ka lallabata tayi hakuri kasan Rabuwa da gida..kuma kada ka manta aure yakin mata..Sannan ita ga yadda abubuwa suka zo shehi Dole tayi kuka..Gata yarinya ce karama Kasan kaima sai ka kara Hakurinka sannan Hajiya da Mallam sun zama gatanga gareta Dolene ko baka so kayi Hakuri da ita na dan Lokaci ne nan da wani Lokacin in ka fara cin amarci kana jin Dadinta zaka bani Labari mutumina..! Danmmalan ya saki Tsaki kafin yace"Ammh dai Aliyu kai mutumin banza ne.. ko..? Bai jira amsar sa ba ya katse kiran yana Fadin"Ko kunya Bai ji..Yana mganar wannan abun da wannan yarinyar..! Tsaki yayi kasa kasa kafin ya maida wayarsa aljihu sai da ya bata Lokaci kafin ya Dawo Motar budewa yayi ya lekata ganinta nan kasan kujeran ta Dunkule yasa ya shigo Motar karan Rufe motar ne ya Dawo da ita cikin Tunanin data Fada na gata chan agidan kangararru an sakamata mari. Tana ganinsa ta zabura tana Kokarin kara sakamai kuka wani banzan kallo yayi mata kafin yace"Ki bari naji ihim dinki ki gani..Wlh na rantse yau sai kin kwana gidan mari karyan iskanci kike da rashin kunya chan akwai Uban ninki a tacewa..! Bakinta ta kama tana Hawaye Tsawa ya Daka mata kafin yace"Tashi ki hau Kujera..! Da Sauri jikinta na Rawa ta koma ta zauna tana Danne Bakinta ko kara kallonta bai yi ba ya Tada Motar suka fara tafiya Amina ko Tsoron za"a kaita gidan mari ga kuma tsoron zata je wani gidan inda ba Hamida ba Hanne Ta tsorata dashi duk muguntar su ya Jafar tana ganin ya Darasu tunda su basu taba cewa zasu kaita gidan mari ba,Shiyasa duk son kukanta ta bame Bakinta gam sai da na zucci a haka suka iso gidan Danmallam Dake kofar arewa. Yana hon megadi yazo ya Budemai get din gidan ya sulala da Motarsa parking space sai da ya gama Daidaita motar kana ya kashe ta ya Fito har Lokacin Amina na zaune ta kasa Motsi sai da ya fita yana gaisawa da Buzun megadinsa yaga bata fito ba kai ya girgiza Booth ya Bude ya Fito da Kayanta ya ijiyesu nan Kofar Falon kafin ya isa wajen motar ya Bude mata Murfin yana fadin"Sai nace ki fito sannan zaki fito ko me kike nufi..? Dasauri ta fito tana faman sharan kwallah ko kallonta bai yi ba yayi gaba ya barta nan tsaye yana kallonta bai ce mata komai ba ita kuma Tsoro take ji kada tayi wani abu yace zai kaita gidan mari duk da bata taba zuwa ba,Ai Baba mallam na kai ziyara Lokaci bayan Lokaci yana zuwa tare da Aba ko su ya shamsu har jawad an sha zuwa dashi tana jin labarin yadda ake gana musu azaba abakinsu ina zata yi wani abu wannam mara Imanin ya mikata chan kafin Su Baba mallam su ji labari su je su karbota ta kusa mutuwa..! Shi kuma yana ganinta Tsaye yayi kamar bai ganta ba Yasan in ya bar mata kayan bazata iya Dauka ba yasa ya Fara Dauka yana shigar mata dasu Cikin Falon gidan Yazo Daukan na karshe ne ya Dago yana kallonta cikin Haushinta yace'"Shima sai nazo na kama hannunki na shigar dake gidan sannan zaki shiga..? Jin haka yasa tayi saurin wucewa gaba shi kuma yabi bayanta. Tana shigowa Falon suka hada ido da Sakina data fito daga Dakinta Cikin kwalliyarta Less ta saka riga da Sikat sun kamata ta shaba kwalliya kamar wacce zata je gasan kyau na Duniya bakinta Cingam ne tana Taunawa kas kas kafarta cikin wani takalmi mai Dubu kallon kallon suka tsaya yi da Amina cikin kyama da wani Tsana take kallonta ita kuma Amina sai ta kasa gaba ballatana baya saboda ganin Sakina shima daya shigo ya ganta sai yayi kamar bai ganta ba Tun bayan tafiyar Anty mgana bata Kara Hadasu ba Dakinta ta shige shima ya shiga nasa har ya je amsa kiran Mallam bai sata a ido ba jidalin Dake kansa sun ishesa inda zata gane da ta barsa ma yaji da abunda ke Damunsa..! Ta gefen Amina ya raba ya wuce ko barayin Sakina bai kallah ba Dakinsa ya Nufa zai Bude yaji a kulle Cikin mamaki ya juyo yana kallon Sakina kafin yayi mgana ta wucesa zuwa kan Daya daga cikin kujerun falon ta Zauna ta Dora kafa Daya kan Daya Tana cigaba da Taunan cingam tana kas kas..! Ransa ya baci ganin Amina Tsaye awajen yasa ya sausauta Cikin sanyinsa yace"Waya kulle Dakin nan Sakina..? Ina key din..? Sakina ta kallesa Cikin wani Bakinciki yau ita ce ke shakan Numfashi da wannan yarinya a matsayin Mijinsu Daya gaskiya Umar ya gama Cutar da ita. Kai ta kauda batayi mgana ba ya kara Sausauta Murya yana fadin"bada ke nake mgana ba Sakina..? Sakina ta wani kallesa a karkace kafin ta Hura bakinta ta saki kwan cingam din Dake Binta ta wani Rausayar Dakai Cikin Wani yanayi tace"Makullin na hannuna..Ni kuma na kulle Dakin..! Bai ji mamaki daman yasan ita zata kulle ba kowa ba cikin son kara nazarinta yace"Saboda me yasa kika Kulle Dakin bayan na Fadamiki Hajiya tace yarinyar nan ta zauna aciki..! Sakina ranta daman yana bace ne ga Kishi kawai sai ta mike tana fadin"Wlh Umar baka isa ka Tozartani ba..Ni zaka wulakanta bayan auran wannan yarinyar da kayi ban ce komai ba..Shine saboda a kara Kuntatamin sai ace Dakin mijina zata zauna..? To wlh bazata sabu ba...Ko Mijin bazan raba da wannan kuchakar yarinyar ba ballatana Dakin miji..Bazai taba yuyu ba..! Tafada tana bayyana bacin ranta Hannu kawai ya kama a kirji yana kallonta Amina ma ita take kallo ita aranta ma Dadi taji Allah yasa taki Bude Dakin ya maidata gida. Cikin Kaushinsa yace"To yanzu ya kike son ayi sakina..? Kai Tsaye tace"kai ka sani..! Daga haka ta koma ta zauna tana Jijjiga kafa Lokaci Daya tana Hararan Amina Dake ta sharan kwallah. Bai ce komai ba ya kalli Amina yana nuna mata hanyar Dakin Sakina Lokaci daya yace"Zo ki wuce..! Kamar tayi mgana sai kuma ta fasa ganin yana mata wani kallo Sakina da mamakinsa ya cikata na ganin Dakin daya nuna ma Amina Dakinta ne. Sai dai batayi mgana ba sai da taga Aminar ta nufi bedroom dinta sannan ta Mike kamar kububuwa sai gata gaban Amina ta tare gabanta Cikin Zare mata ido tace"Kan uba..Badai Dakina ba..Allah ya Tsareni wannan kazamar ta shigarmin Daki..! Sai Amina ta Tsaya ta kasa gaba ballatana baya Umar yana Tsaye inda yake yana kallon Sakina da Idanuwansa da suke kokarin bayyana yanayin dayake ciki. Kokarin Daidaita kansa yake yi yasa bai yi mgana ba Sai da yaga Sakina ta Hankada Amina sai da ta kusa kaiwa kasa tayi Saurin Dafa Kujeran Dinning Sakinar kuma ta jawo kofarta ta Rufe da makulli tana fadin"Yau ni Sakina naga Rainin hankali..Dakin nawa zaka saka Kishiyata..?Allah ya tsareni ma da ta zama kishiyata Har Abada..! Take fada tana jijjigan Jikinta Danmallan yayi tsai yana kallon wani waje bai yi mgana ba. Babu makullin daki ko daya a hannunsa na Gidan duka yana hannun sakina Sauran kuma suna gida wajen Hajiya,sannan akwai wajen Jafar,Shi bai taba Hausan makullayen gidan sa su zauna awajensa ba. Bayason su yi wani abu gaban wannan yarinyar girmansa ya Zube shiyasa ya dinga maimaita sunan Allah har ya samu ransa yadan sauka Cikin Sanyinsa ya juya yana kallon Sakina kafin ya mika mata hannu yana Fadin'"Naji bazata zauna adakina ba..da Dakin ki ba.Bani key din Dakin Sarood sai ta zauna aciki..! Shekeke take kallonsa sai dai taji shakkansa Lokacin daya kara sakarmata wani Kallo yana fadin"Ko shima bazaki bani ba..? Jin haka yasa ta nufi kofar Dakin ta saka makulli ta Bude kada ta basa ya Bude Dakinsa tunda duka suna Hade ne waje daya gwara Dakin Sarood din ita kam banda nata Dakin kuma shima ban da nashi. Tana gama Bude Dakin ta koma gefe tana kallonsa bai kara ko kallon inda take ba ya kalli Amina Dake dannen kukanta yace"Shiga..! Ba musu ta shige shi kuma ya Dauki ghana dinta guda Biyu yabi bayanta Tana Tsaye Tsakiyar Dakin ko zama ta kasa yi bai ko kalleta ba ya ijiyemata kayanta nan ya fice tana bin Dakin da kallo ya sake shigowa ya ijiye mata Dayan ghana din ya Sake fita wannan karon har yana bame mata Kofar ta bisa da kallon ganin ya Ficen ne yasa ta sulale nan kasan Cafet din Dake Dakin ta hada kanta da Bango ta fashe da kuka,kukan da ko Rasuwar yaya batayisa ba kukan kewa da rasa wani abu a Rayuwa ta yaya zata fara zama in da ba hanne ba Hamida ba mamanmu.! Tuna haka yasa ta kara sakin wani kukan ta dora kanta jikin gadon ta cigaba da Rera kukanta,Bata ma ji shigowarsa ba sai karan bude kofa taji tana Bude ido ta gansa ya shige wani kofa Dake Dakin ya kullo,sai tayi tsit tana ware idonta da sukayi zuru zuru da kuka duk ta wani yarkace ko motsi bata karayi ba ita azatonta uwar Daka ya shiga shiyasa ta kasa motsi sai chan taga ya fito Fuskarsa na Digan ruwa alamun alwala yayi ko barayinta bai kara kallah ba ya sake Ficewa ya bame mata kofar yana Fita ta Dora hannu akanta ta fashe da kuka tana fadin"Na shiga uku ni Amina..! Sai kuka harda Birgima a kasa kamar wata yar yarinya ita kadai bamai lallashinta. Tanayi tana rufe bakinta kada ya jiyota ya shigo,yadda take kukan sai ka Tsausayamata kuka ne Dake fitowa Daga kasan ranta. Sakina tana tsaye tana jijjiga jikinta ya fito nan saman cafet din falon ya Daidai gabas ya tada sallah Shafa"i da wuturi yayi sannan ya zauna yana Tasbihi da hannayensa ko barayin Sakina bai sake kalla ba har ya gama yayi addu"a ya shafa Rigarsa ya Cire ya rataye ta nan saman kujera daga shi sai dogon wando ya samu Filon filon kujerun ya jera saman kujera 3siter ya kwanta Kansa na kallon Rufin Falon hannayensa kuma ya Saka ya Dunkule su waje daya ya Dora su saman Filo kansa na kai. Wayarsa daya ciro cikin aljihun rigarsa ya ijiyeta nan saman center Table din Dake falon,Sakina sai Binsa take da kallo ta kasa mgana sai alokacin kuma jikinta yayi sanyi mganganun Anty suna dawo mata da tace kadatayi wani abun da ran Umar zai baci tabi komai a sannu ammh ita Kishi ya Rufe mata ido da kuma mgaganun Aliya dazu da sukayi mgana ita ta kara tunzurata. Takowa ta farayi cikin Falon Cikin Sanyin jiki a gabansa ta Tsaya tana kallonsa kafin ta sauke numfashi tace"Bari na bude maka Dakin ka..! Baice mata komai ba ta koma ta Bude Dakin sannan ta Dawo gabansa tana Fadin"tashi ka shiga ciki Habibi..! Mikewa yayi ta Dauka zai shiga Cikin ne sai taga ya isa ma kunni wutar Falon ya kashe duhu ya gauraye wajen gabadaya ido ta zaro tana Fadin"Habibi...! Ko kallonta bai yi ba ya koma ya kwanta Har da Juya mata baya Sakina taji ta Muzanta Sai ta Duka gaban inda yake kwance tana saka hannu ta riko hannunsa tana fadin"Habibi..Dom...! "In kika kara tabani Sakina wlh tallahi zan sharara miki mari..Zaki ga Oder side of me da baki taba gani ba..! Ya katseta Cikin Tsawa Daidai Lokacin daya juyo yana kallonta Cikin hasken Dake shigowa ta windows din Falon Baya Sakina taja tana zaro ido kafin tace"Ni zaka mara Habibi..? Ni kace zaka mara saboda ka kawo wannan kazamar yarinyar nace bazata shiga Dakin ka ba..? Wani matsiyacin kallo yake binta dashi bayaso yayi wani abu Saboda Amina na gidan yasa ya koma ya kwanta ai sai Sakina ta saka kuka ta Durkushe a wajen tana Fadin"Shikenan..Nagode yanzu har ka fara wulakantani saboda wannan yarinyar Habibi..? Saboda na hana ta shiga Dakin ka kakemin ihu haka..? Yar Cikin ka ce fa karamar yarinya da bata isheka komai ba..! "Karamar yarinyar da kike mgana akanta yanzu Daya kike da ita a wajena Sakina..Dani da mutanen da sukasan abunda suke yi..! Ya katseta a fusace,Sakina ta ji kukanta ya Tsaya Cikin mamaki tace"Daya fa take dani kace Umar..? Saboda ma ya tabbatar mata yasa ya Mike Zaune yana fadin"Eh..Kamar yadda kike matata haka take matata..Kamar yadda igiya uku ta hau kanki..Nawa itama suna kanta Sakina..Saboda haka dake da ita Daya kuke awajena..! Galala tayi tana Binsa da kallo Kafin tatashi Fuuu ta je ta kunna wuta Haske ya bayyana kafin ta Dawo gabansa tana kallonsa cikin karaji tace"Maimata abunda ka fada..Dazu baka kallon idona yanzu kuma idona na cikin naka nake so ka maimata Umar..! Karamin Tsaki yaja ya koma ya kwanta yana Fadin"Sai ki sani na maimaita din..! Sakina idonta ya rufe ta mike tana Fadin"Har gaban abada bazan zama Daya da wannan kazamar yarinyar ba..Wacece ita..?Yaushe take..? Wlh ita bata isa in yi zaman kishi da ita ba in nayi da Sarood ita bata kai wannan matsiyan ba..Amina ba Sa"an auranka bace Umar ba sa"an zaman kishina bace..! Kamar ya Rufe ta da Duka haka yake ji kai Tsaye ya mike zaune yana kallonta yace"Wacece ita kike tambaya Sakina..? Kinsan wacece ita ai..in ma kin manta bari na tuna miki..Ita diyar BABA SA"IDU ce kuma Diyar YAYA ce..Sannan Unarnin HAJIYA DA MALLAN NE..Ta riga ta Hada mutane masu Daraja atare dani..Ko ba aure Tsakanina da ita ni me rike Amina ne acikin gidan nan Sakina ballatana da aure Tsakanina da ita in kina Tunanin Zata bar gidan nan to kidaina kamar yadda zaki zauna itama haka zata zauna..Kuma da kike mganar Ita ba sa'an aurena bace..Daman sai sa"an auranka zaka aura..? Wlh in da ana bin chanchanta har Abada Dake sakina baki CHANCHANTA dani ba..! Yafada yana nuna ta da yatsa cikin fushi ido ta zaro mgana take son yi ya hanata Cikin Kaushinsa yace"Ba shawara nake nbaki ba..ba kuma Umarni ba.ki natsu ki zauna lafiya da yarinyar nan domin zamanta Daram acikin gidanan in kika ki natsuwa ke kika sani ni dai tafiya zan yi..in kin kama girmanki ta girmamaki in baki kama ba ta fiki iskanci sai ku goga wata dai bata isa ta kori wata ba..! Sakina taji jikinta yayi sanyi me kalaman Umar suke nufi..!? Gabanta ya fadi kada kishinta ya Bullo mata wani sabon aiki Dakyar ta Hadiye miyau tana Sharan kwallah tace"To don Allah in ka tashi tafiya ka tafi dani Habibi..wlh bazan iya zama da yarinyar nan anan gidan ba..! Umar ya kalleta daga sama har kasa kafin ya koma ya kwanta yana Fadin"Sakina na yi rantsuwan bazaki koma ba yanzu Ki tashi ki bani waje bana son yawan mgana kaina ya riga ya fara ciwo..Kada zamanki agabana yasa na rasa Control dina..! Batayi musu ba ta mike Cikin kaushinsa yace"Ki kashe min hasken da kika kunna min..! Ta juyo tana kallonsa kafin tace"Bazaka ko..! Kallon da ya bita dashi ne yasa tayi Saurin yin gaba Hasken ta kashemai ta Fada Dakinta gabanta na Fadi Gabadaya mganar Umar na ita ma bata Chachanta dashi ba ya Tsorata ta In ta Kira Anty ta Fadamata tasan sai taci Zagi Allah yasa ba abunda suka Binne bane yake son ya bayyana ba.. Da sun shiga uku kuwa..! Mafarin komai in ya lalace ai sun gama yawo..! *28 September 2022* *Janafty**TFZB2002* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Karfe hudu na asuba ya farka kamar yadda ya saba,Kwata kwata bai ji dadin barcin ba akan kujera sannan zuciyarsa tana cunkushe ne ya dade bai samu barci ba kuma kasala ya rufeshi ya kasa tashi yayi ko nafila ne. Sai da asuban ya shiga dakin nasa yayi wanka ya dauro alwala Jallabiya mai ruwan madara ya saka da Hula ya Dau cashabahansa ya fice zuwa masallaci ko ta kan Sakina bai bi ba ballatana wata Amina. Sai shidda saura ya shigo gidan,yana shigowa tsakiyar falon suka ci karo da Sakina ta fito daga dakinta yarkace yarkace da ita idanuwanta sun kumbura sannan kanta ba dankwali kanta ba kitso gashinta ya baje kansa tana sanye da rigar barci mai taushi iyakarta gwiwanta ayanayin yadda yaganta sai da ya kara kallonta ganin yanayinta. Kamar zai mata mgana sai kuma ya fasa ya dauke kansa zai shiga Dakinsa Da hanzari ta daga kafa zata bisa jin takunta yasa ya Dakata bai juyo ba taji muryansa yana fadin"Ina zaki..? Cak ta tsaya jikinta yayi sanyi kanta ta maida kasa kafin tace"Da..Dama zan gaisheka ne Habibi..! Shuru yayi mata bai yi mgana ba taga yana shirin shigewa ya barta yasa tayi saurin cewa"Ina kwana Habibi..! Kamar bazai tankata ba sai kuma ya amsata kamar baya so da Lafiya Lokaci daya ya shige dakin nasa ya banko mata kofa saman fuskarta baya taja Hannunta Dafe da kirji tana fadin "Na shiga uku ni Sakina..! Kasa tsayuwa tayi kamar mahaukaciya haka ta kwashi gudu zuwa Dakinta saman gadonta ta koma ta Zauna gabanta na fadi meta aikata kenan .?Jiya ko barci batayi ba in ta tuna Kalaman Umar zuwa gareta. Taso ta kira Anty tun jiyan sai ta kasa Tasab Halin Anty in taji abunda ta aikaata sai ta Zageta saboda haushi Saboda sai da ta tausheta akan kada tayi wani abu sai ta tambayeta yanzu in ta Kirata ta fadamata abunda ya faru ta tabbata sai Anty ta mata fada sosai. Sai dai bata da wata mafita Anty zata kira ta fadamata abunda ke faruwa ko zata samamata mafita. Wajen shidda da rabi ta dokama Anty Amarya kira tun da taga kiran tasan ba Lafiya cikin Tashin hankali ta Daga kiran tana fadin"Sakina kada ki fadamin kin kara aikata sakarcin naki ..? Sakina tafara Fiki Fiki da ido tana fadin"Anty...! "Don ubanki ki fadamin abunda ya faru..! Sakina cikin sanyi ta fara fadamata Duk abunda ya faru jiya har zuwa yau Anty Amarya ta mike Har hijabin jikinta datayi sallar asuba na neman Hardeta ta fadi ta Dafe jikin gadonta Cikin Firgici tace"Kikace Umar da kansa yace baki Chanchanta dashi ba..!? Sakina tace"Wlh haka yace Anty..! Anty Amarya bakinciki suka kusa kasheta alokacin cikin Tsawa tace"Sakina na rantse da wanda Raina ke hannunsa in kishin ki na banza yayi sanadiyar Tono Abunda muka Binne da Dadewa babu ruwana..zan zame kaina ne na barki ke kadai..Kin kuma Tabbatar ma kanki wannan kokawar tafi Karfinki..! Jin haka yasa Sakina ta kara Rudewa kawau sai ta saki kuka tana Fadin"Anty don Allah kiyi hakuri..Ba laifina bane..Kishi ne ya rufemin ido kinsan ina son Umar bazan juri ganinsa da wasu matan ba..Sannan Aliya tacemin kada na barta ta zauna Dakin Mijina..! Anty Amarya ta lailayo Ashar ta saki kafin tace"Aliya Burauban ki Sakina..Ina ruwanta da wannan mganar ban fada miki kada kiyi wani yunkuri sai nace ba..? Da kika kwantar da hankalinki Lokacin Sakaryan balarabiyar nan ba gashi yanzu muke da riba ba..Itama in kin kwantar da hankali kamar haka zata zama nayi alkawarin ko zan rasa komai Amina bazata yi zaman kishi Dake ba Sakina ammh shegen Taurin kan ki yana neman jawo mana matsala..! Sakina na sharan kwallah tana Fadin"Nidai Anty ki fadamin ya zan yi..?Wlh ko son ganina bai yi ina mgana Dakyar yake amsa mun..! Anty Amarya tace"sai kin bata komai kizo kina Damunna da kukan banza..Yanzu ina ita Aminar..? Sakina ta tabe baki kafin tace"Tana chan Dakin Sarood..Tun jiya bansan isalinta ba..! Anty Amarya tace"Shi kuma fa..? Sakina tace"Ya dawo daga masallaci ya shiga Dakinsa ya kulle..! Anty Amarya tace"To ki tashi ki shiga kitchen ki hada breakfast ki yi wanka da kwalliya kije ki tasosa ki basa Hakuri..Mganar Amina kuma kada ki shiga mganarta ki koma gefe ki zama yar kallo kawai a na nan ana aiki akanta kin ji ko..? Sakina ta gyada kai kafin tace"Anty Dakyar ya Saurareni fa..! Tsaki Anty Amarya taja kafin tace"To Tunda bazai Saurareki ba..ki Zauna..! Daga haka ta katse kiran tana Huci ita Kadai adaki Sakina fa Bata san ciwon kanta tasan kudin data kashe kafin Umar ya kalleta da sunan so..? Tasan wahalan data sha kafin Umar ya kalleta da kalmar aure..? Batasani ba shiyasa take son bata komai ba bazata yi wannan saken ba in abubuwa suka fara Lalace mata bata samu Cikar Burinta ba anyi ba ayi ba kenan ko zata rasa komai sai Sakina ta zama Tauraruwa awajen Umar da danginsa gabadaya Wata mace bata isa ba kuma tayi kadan. Ashe Sakina duk zaman data ke yi batayi sallah ba,Sai da suka gama waya da Anty tatshi ta Dauro alwala tayi sallah sama sama ta Daura Zani saman rigarta ta fita zuwa Kitchen,Sakina ta iya girke girke Anty Amarya bata barin ya"yanta haka tasan duk cikar ya mace in bata iya Girki ba Saura ce shiyasa ba wacce bata koyama girki ba hatta da Sa"adatu da Sabeeha..! Cikin Hanzari take aikinta Cikin Lokaci ta kamallah Doya ta Dafa sai tayi miyar kayan miya ta yayyanka mai kwai,Sai ta Dafa Ruwan tea ta soya Buredi da kwai saman Dinning ta jera komai kafin ta gyara Kitchen din sannan ta koma Daki ta shiga wanka. Bayan ta fito ta shirya Cikin Doguwar rigarta ta atamfa ta gyara gashinta tayi Daurinta na Maryam babangida..! Gabanta fadi yake bata san wani Tarba Umar zai sake mata ba ta zata Ya kulle kofar ne sai da ta Tura taganta a Bude Cikin Takunta na Takama ta shiga Dakin da sallama sanin Halinsa yanzu sai ya maidata waje. Yana zaune a kasa saman Darduma yana karatun Qur"ani a hankali cikin Sautinsa mai Dadin Sauraro Dakin tabi da kallo komai neat,Gado ne kawai sai wardrope sai ma"ajiyar takalma sai cafet babba da ya malale Dakin gefen gadon ta zauna tana Jiransa ya idar da karatun ammh wajen Minti Goma sha biyar bai rufe karatunba sai ta fahimci in tayi shuru to sai rana ta Dago zai tashi daga wajen nan. Gyaran Murya tayi kafin tace"Ina kwana..Wajen ka fa nazo Habibi..! Ta karishe Fada Cikin shagwaba. Yana jinta yayi kamar bai ji ba sai da ya kai inda yaga damar Tsayawa sannan ya rufe Qur"ani ya Daga hannu Sama yana addu"a tare suka shafa ya mike ya ijiye Qur"anin saman Side drower din gadon,Yana kokarin Ninke Darduman ne tayi saurin mikewa ta karba bai hanata ba ya sakarmata Ta ninketa ta maidata wajen zamanta tana gani ya hau saman gado ya kwanta harda juya mata baya. Bata damu ba ta Durkusa saman kafafunta tana fadin"Don Allah kayi hakuri Habibi..Da abunda ya faru sharrin Shedan ne da kuma Kishi.. Ammh nayi alkawarin bazan kara ba..! Kaji..! Kamar bazai tanka ba sai chan taji yace"Zaki kara Sakina..! Da sauri tace"Allah bazan kara ba..! Ajiyar rai ya sauke kafin ya juyo yana kallonta Lokaci daya yace"Ya wuce..! Mirmishi ta saki kafin tace"Nagode..Ga breakfast chan na gama Hada maka ka taso muje ka karya..! Lumshe ido yayi kafin yace"Am ok..Bana jin yunwa..! Marairaicewa tayi tana fadin"Haba Habibi..Ko baka hakura bane..? Da Sauri yace"Bani da riko kema kin sani..! Jin haka yasa tace"To in hakane ka taso muje..abunda kafi so na Dafa maka Doya..! Muskutawa yayi ya mike zaume yana Fadin"Naji..Zan yi wanka ne ganin nan fitowa..! Taji dadi sosai ta mike tana Fadin"Bari na taimaka maka Habibi..! Duk yadda yaso ya yakiceta bata yarda ba Tun yana kin sakin mata har ya sakarmata ita ta taimakaima ya Cire kayansa ta hadamai ruwan wanka ya shiga yayi wanka daya fito ta taimakamai ya shirya Cikin Riga da wando na pakistan sannan ta Tarosa Hannunta Cikin nasa zuwa Falon har saman Dinning jikinta na rawa ta yi Sarving dinsa kallonsa tayi tana zubamai Ruwan tea din dayaji Ganyen shayi masu kamshi tace"Kana so da yawa ne Habibi..? Kai ya girgizamata kafin yace"Rabin kofi..! Haka kuwa ta sakamai ta Turamai gabansa baya son madara siga ya kara kadan ya fara sha Bai san yana jin yunwa ba sai da ya gansa gaban abinci Rabonsa da abinci tun jiya da rana.. Ita Tea ta hada maa kanta tana Hadawa da Buredi da kwai shi kuma yana cin Doya daman mutuniyarsa ce. Ranta yayi mata Fes ganin ya sauko har suna dan mgana jefi jefi Shine ma yace mata"yana da kyau in ana cin abinci a Dakata da mgana har sai an kamallah..! Daman sai yayi mgana bai cika son tana mai mgana in suna cin abincin ba yasa tayi shuru tana kurban tea tana kallonsa shima kuma in ya Dago suka hada ido sai yayi mata Yake kawai. Sai da ya kusa gama cin abinsa sannan Amina ta fadomai arai kamar ya Tuna da wani abu ya Dakata da komai yana kallon Sakina Cikin wani yanayi yace"yarinyar nan ta fito kuwa..? Wani irin Kallo tayi mai kafin tace"Wata yarinya kenan..? Yadda ya kalleta ne yasa tayi Saurin gyara mganarta da cewa"Bansani ba..Nidai ban ganta ba..! Tsam yayi yana wani Tunani bata ci abinci ba,Ba domin yadda Hajiya da maallam suka saka shi a Tsakiya ba da sai yace ta Dauwama adakin ai yunwa ba"a mata iskanci sai dai in ya kyaleta Allah zai kamasa kuma Hakkin mallam da Hajiya na wuyasa..! Tuna haka yasa ya kalli Sakina kafin yace"je ki kiramin ita..! Ido ta Zaro kafin tace"Ni kuma..? Kai Tsaye yace"Eh ko bazaki ba..? Jin haka yasa tace"ban ce ba..! Tashi tayi tana Tura baki ta wuce ya Bita da kallo daman yasan lambo Tayi Sakina ai bazata Daina Halinta ba. Afusace ta Buga kofar ta shigo Tana bin Dakin da kallo lokaci daya tana wani yamutsa Fuska nan kasan Cafet ta Hango Amina ta Dunkule waje daya acikin Hijabinta,Ga ghanas dinta nan inda ya ijiyemata ko kauda su batayi ba Ranta ya kara baci Cikin kufuluwa tace"Kee...! Cikin Tsswa Amina bata jita ba Domin barci ne na wahala ya kwasheta bata sani ba Jiya yadda taga rana haka taga Dare bazata kwatanta kwana awajen da ba Hanne ba Hamida ba bata taba tsamanin wannan ranar ba ballatana ta Shiryama zuwanta Tunda ta shigo Dakin ta zube anan kasan Cafet ko motsi bata karayi ba tayi kukan har ta gaji ga Tsoro Daki ita kadai abunda bata saba ba,Bata iya barci ba Tsoro da Fargaba da kewa basu barta ba Dakyar ta Rarrafa da Asuba ta shiga Toilet din Dakin tayi alwala tazo ta Rama Sallar Isha"in da ake Binta jiya da kuma Sallar asuba shine fa tana nan zaune bata ma san barci ya kwasheta ba. Sakina jin tayi banza da ita kuma taki Motsi yasa ranta ya baci a Tunaninta da gangan tayi mata yasa ta isa kusa da ita ta saka kafa ta Shureta daya sa Firgigit Amina ta farka Daman a Tsorace take cikin muryanta da Bata Fita sosai saboda kuka tace"Wayyo..! Sakina ta saki Tsaki kafin tace"Baki ce wayyo ba sai nan gaba..Badai kin ce dani Zaki kishi ba yarinya..Ai wayyo Salamu Alaikum..! Amina ta bita da kallo da kumburarrun Idanuwanta Hancinta ya Toshe da majina sai ja take ga kuka ga sanyin Dakin Domin A.C a kunne kuma fanka ma haka ita kuma bata yi Hausan tashi ta kashe su ba. Sakina ta koma da baya tana mata wani kaskantattacen kallo kafin tace"Kazama kawai..Sai ki taso yana kiranki..! Amina ta kalleta da mamaki kafin tace"Shi wa..? Cikkn Shakewar murya Sakina ta ga tama raina mata wayau yasa ta juya tana fadin"Uban ki ba..! Amina ta bita da kallo har ta fita itafa bata gabanta ita yanzu kokuwa take da wannan Sabuwar rayuwar shiyasa Zagin Sakina bai ma Dameta ba kamar bazata je ba Domin jiri take gani in ta mike ammh Tuna Kalaman ya Danmallam yasa ta mike jiri na Dibanta ta fice Daga Dakin zuwa Falo Daidai sanda Sakina taja kujera ta Zauna Dammallam na zaune bai ce mata komai ba sai ga Amina ta fito tana Layi Cikin hijabinta kamar zata fadi Daga nesa ta Tsaya tana kallonsu kafin tace"Gani..! Daga sama har kasa yake kallonta alamu sun nuna ko mai yarinyar nan batayi ba tunda ga jiya kenan ganin yadda Fuskarta ta Kumbura ne ya bashi mamaki Sakina kuwa Kamar ta yi Tsaki haka taji da taga yana kare ma Amina kallo bata ma lura da kallon kyama yake binta dashi ba..! Saboda mugunta sai da tafi minti Goma a Tsaye tana neman faduwa sannan yace"kizo ki ga abun kari nan.! Amina da Tagaji da Tsayuwa tace"Ni na koshi..! Ko kallonta bai yi ba ya maida hankalinsa wajen cin Doyansa Sakina ta juya tana kallonta ta Harareta bata ma ganta ba ta juya tana Faman Kama Hijabinta ta koma inda ta Fito nan inda ta baro ta koma ta zauna ta Hada kai da gwiwa ta fara Rera sabon kuka Allah sarki sai yanzu ta kara Tabbatama da kanta da cewa tayi maraici tazo inda ba mamanmu ba Hamida ba Hanne,Wadanda sune ita in basu Rayuwar Amina bazata taba cika ba Aminu ne ya fado mata arai ko wani Hali yakeciki..? Tasan da shi ta aura ta tabbata zai lallasheta zai mata komai Saboda yana sonta ammh kalli inda Kaddara ta kawota inda ba"a san Darajanta ba Daga megidan har matan gidan basu da Imani Allah ya isanta wlh bazata taba yafe musu ba mugaye kawai..! Tun daga Lokacin Amina ko motsinsu bata sake ji ba tun tana Daurewa har ta kasa Cikinta ya kulle yunwa take ji ga jiri ga rashin barci sai mulmula take saman cafet dafe da Ciki tana faman kuka ita kadai Zata mutu acikin wannan gidan wayyo ita Amina..! Umar kuwa agida ya wuni bai Fita ba sai da yammah da ya kira Jafar yazo suka hadu shima iyakarsa haraban gidan bai shiga b,Mganar Visa dinsa sukayi so yake cikin satin nan ya koma Madina bazai iya sake wasu kuma kwanaki ba,gabda mangariba Jafar ya tafi shi kuma Daganan masallaci ya wuce sai da akayi sallar Isha"i ya dawo ya iske Sakina tayi sabon wanka bayan ta gama girki ta gyara gidan yana tashin kamshi Sai ransa yayi fari,Yana son Sakina saboda Tsabtarta,sannan uwa uba kuma kwalliya,yau din ma ta tsuke cikin Riga da wando,ko Dankwali bata saka ba gayu take ji yau din,Ko bai yi mgana ba tasan ya yaba tunda yana ta kallonta yana mirmishi. Abincin mara nauyi tayi musu Faten Dankwalin Turawa da hanta sai Coffea data hada musu tare suka zauna suka ci abincin su kafin su dawo Falo su zauna Sakina ta Dora kanta saman cinyar Umar shi kuma yana wasa da gashinta,Hankalinsa na wajen kallo a tashar Sunna Tv Qur"an,sakina kuma har ta fara barci bata damesa da mgana ba sanin Halinsa hira in ya sota suna yi bai so ba kuma baya son ana damunsa Duniya ta mata sabuwa yadda taga ya manta da Halittar Amina acikin gidan Kamar wasa wayarsa ta Dauki Sautin kidan Larabawa Sakina ta Bude ido tana fadin"Habibi kamar ana kiran wayarka fa..! Chan saman dinning ya barta da sukaci abinci,Yasa ya Daga kansa yana Fadin"itace..! Mikewa tayi tana fadin"Bari na Dauko maka..! Sanda ta karisa ta Dauko wayar sai da gabanta ya fadi ganin sunan mallam,sai da Annurinta ya Dauke tsayawa tayi har wayar ta katse jin ta Shuru yasa ya dago yana kallonta kafin yace"Waye ke kirana..? Sakina ta kariso ta mikamai tana Fadin"Mallam ne..! Gabansa sai da ya fadi ya karba da Sauri Lokaci daya yana fadin"Dauke min karar nan..! Ba musu ta Dauki Remot tayi kasa da Volume din shi kuma yabi bayan kiran Mallam Da sallama mallam ya daga Kiran Umar ya zamo daga kan kujera kamar yana gabansa yace"ina yini mallam..? Mallam na zaune afalonsa Gefensa Hajiya ce yaa amsa yana fadin"lafiya lau Umaru ya wajen iyalan naka..? Ya amsa da lafiya kalau kansa na kasa kamar yana gabansu Sakina na kallonsa ta gefen ido a duniyar nan Umar na bala"in ji da mutanen nan guda Biyu mallam da Hajiya na ukun su kuma wannan Mayen Baba Sa"idun inyana mgana dasu kamar ya kwanta musu saboda Biyayyah..! Mallam yace"Masha Allah..lafiya yau baka shigo anguwan namu ba..? Nace to bari na kiraka naji Allah yasa ba Rigiman me sunan mamana bane har yanzu bata bari ba..Domin yanzu nan yan"uwanta suka tashi daga nan tun jiya suke kuka ko makaranta ba su je ba suna ta koke koke sai da na kira su yanzu nayi musu nasiha na lallashesu da cewa su bari tayi ko sati Daya ne sai suje su mata yini..! Danmallam yayi shuru bai yi mgana ba Mallam ya gyara zama yana fadin"Ina ita maman tawa..?ina fatan ta Daina kukan ko..? Danmallam kansa na kasa yace"Eh ta bari Baba..! Runtse ido yayi yayi karya Domin bai san ko ta bari ba.. Mallam yace"Madallah Sai kayi hakuri Umaru kaji ko..?Mamana yarinya ce karama yanzu bata da kowa sai kai..Kai zaka zama mai mata Tarbiya Tunda ta bar karkashinmu..In tayi ba Daidai ba kamata nasiha cikin jan hankali,Duka ko Tsawa basa gyara Tarbiya jan mutum ajiki da nuna mai so shi ke sa ya rage wasu abubuwan..Don Allah Umaru ka kula da Mamana..itace karama acikin matan ka ba lalle ta kai su wasu abubuwan ba..ku rika mata uzuri in ta aikata wani abun Umaru..! Kansa na kasa ya gyada kai kamar Mallam na ganinsa kafin yace"Insha Allahu..! Mallam ya cigaba da fadin"Ina ita abokiyar zaman nata..?fata dai ba wata matsala..?? Cikin Ladabi yace"Babu mallam..! Mallam ya jinjina kai kafin yace"Dakyau itama Saratun nayi waya da Mahaifinta namai bayanin komai har ita nace abani nayi mata Nasiha sosai..ina rokin Allah ya hada kanku..Sannan kai kuma Allah ya baka ikon yin Adalci..! Umar ya amsa da Ameen Ameen daganan yayi shuru kafin yaji mallan yace"Ina ita maman tawa..! Ko tayi barci ne..? Umar ya runtse ido murya kasa kasa yace"Eh..! Mallam yace"To shikenan Allah ya zaunar daku lafiya..ga Hajiya nason mgana Dakai..! Bai gama zufan karyan daya yi ma maallam ba Hajiya ta karbi wayar suka gaisa kafin tace"In fatan Amina taci abinci kafin ta kwanta..? Dakyar yace"Eh Hajiya taci..! Kai ta kada kafin tace"Shikenan ka kula da ita kaga dai yarinya ce..Wlh ban yarda ka hada kai da matanka ku cutar da ita ba..Domim ba sa"ar su bace..! Yana jin Hajiya bai iya mgana ba ta cigaba da fadin"Ina mganar mu ta kwana..? Sannan yaushe zaka koma..? Kai Tsaye yace"Ina so cikin satin nan Hajiya Visa na nake jira..! Hajiya tace"Kake jira..?Ita Sakinar fa..? Kai Tsaye yace"Nan zan barta..Sai na Sake dawowa..! Hajiya ta bude baki tana kallon mallam shima yana kallonta kafin tace"to ka dai samar ma Amina wajen zama domin na fada maka da ita zaka tafi in har ka sake dawowa..! Insha Allahu yace mata,Sannan ta cigaba da fadin"Mganar karatunta da islamiya da Boko zata cigaba da zuwa..ammh nace ta huta na sati Daya..Idi Direba in ya Dauko su hanne Daganan zai biya ya Dauketa in suka Dawo ya sauketa agida sai sun dawo islamiya sai ya maidata gidanta..! Shi dai nashi dan bi ne yasa yace"Duk yadda kika ce haka za"ayi hajiya..! Hajiya tace"Shikenan..Allah yayi muku albarka gabadayanku..! Ya amsa da Ameen Ameen yana fadin Allah ya kara girma. Daganan sukayi sallama ta katse wayar,Sauke wayar yayi ya koma ya Jingina da kujera yana Neman yafiyar Allah yayi ma iyayensa karya karo na Farko arayuwarsa..! Sakina kuwa kallonsa take yi Ta gama Sarewa tunda taji yama Furtama Hajiya bada ita zai koma ba Tabdijam akwai Daru in dai ita da kazamar yarinyar nan zasu zauna awaje daya..! Mamaki ya kamata Da taga ya mike Tsam cikin Mamakinsa tace"Habibi badai barci ba ko..? Kai Tsaye yace mata"A"a..! Bata gama mamaki ba taga ya nufi Dakin da Amina ke ciki har Lekasa sai da tayi gabanta na faduwa ita dai bataji me mallam da Hajiya sukace mai ba ammh tabbas suna da alaqa da Shigarsa wajen Amina komawa tayi ta Zauna tana girgiza kafa tasan halinsa da sai tabisa Dakin taga abunda zai mata.. Shikuwa kai Tsaye ya Tura kofar Dakin ya shiga da sallama,Sai dai sallamansa ta makalene daya ci kusa cin karo da Amina Da azaban yunwa da ciwon ciki yasa ta gangaro har kofar Dakin,Baya yaja da Sauri yana kallonta Lokaci daya yana karema Dakin kallo hatta jakunkunarta yadda ya shigo dasu haka suke kofar Bayi a Bude ta barsa tana nan cikin Hijabin nan ko wanka yana da Tabbacin batayi ba ga ruwan hawaye nan da majina duk ya bushe mata abaki batama san ya shigo ba kwance take hannunta Dafe da Cikinta kamar mai barci Ransa ya baci da wannan kazantar,wlh ba domin mallam da Hajiya sannan kada Allah ya kamasa da Laifin Saba musu ba bazai leko Dakin nan ba kamar ma Zarnin Fitsari nan da nan yaji zuziyansa ta fara tashi toshe Hanci yayi da hannunsa kafin yace"Ke...! Kamar a mafarki taji muryansa da Sauri ta Bude ido suka hada ido harara ya sakarmata kafin yace"Miye haka..?Tashi zaune..! Da Sauri tatashi Ta koma ta Jingina da gado sai hawaye kamar an Bude Famfo. Cikin Bin Dakin da kallo yace"Fitsarin kwance kikayi..!? Bata kallesa ba ammh aranta sai da tace ita bata Fitsarin kwance ammh a sarari sai ta girgizamai kai Cikin Takaici yace"Baki da baki ne..? Muryanta a shake tace"A"a..! Kallonta yake yi yana kauda kai kafin yace"To zarnin nan da nake ji daga ina ne..? Kanta na kasa ta kasa mgana Tsawa ya Daka mata kafin yace"Ina mgan kina jina ke kurma ce..? Da Sauri tace"A bayi ai nake yin Fitsarin ..! Sai kuma ta sakamai kuka karamin Tsaki yaja kafin yace"Banda kina kazama a ina aka taba yin Fitsari ba"a kora ruwa ba..Sannan a kasan tiolet din kike tsuggunawa kina yi bakya hawa Sit din..? Kai ta gyada mai alaman hakane ransa ya kara baci kafin yace"Kin ma yi wanka..!.? Nan ma tace "A"a..! Ya kara kallonta kafin yace"Lalle kazantarki ta shahara..! Ya sake bin kayan ta da kallo kafin yace"Wadanan kayan fa..?waye zai kauda miki..?Ke banda kazanta baki iya komai bane..? Nan ma kai ta gyada mai cikin mamaki yace"Eh fa kikace..? Sai ta kara Saka kuka cikim kukan take fadin"Ni ban iya ba..agidama Hamida take min ko mamanmu..! Galala yayi yana kallonta aransa yana Auna yadda aka gurgurta rayuwarsa da aka auramaaa wannan yarinyar. Kofar Tiolet ya nuna mata yana fadin"Maza tashi ki shiga ki sa ruwa ki wanke zarnin fitsarinki..Sannan ki Tabbatar da kin yi wanka sannan kizoki Sauya kayanan dake jikinki..! Kasa tashi tayi sai da ya Daka mata Tsawa sannan ta mike jikinta na rawa cikin Haushi yace"Dilla cire wannan Hijabin sai wari yake..Tun jiya abu na Jikin ki baki cire ba saboda kazanta..! Bazata iyamai musu ba na farko tana Tsron Rashin Imaninsa na Biyu kuma mganar Aba Dayace in tayi mai gaddama bai yafe mata ba. Hijabin ta cire ta Tsaya Tsumi tsumi tana kallon kasa tiolet din ya nuna mata yana fadin"Oya shiga..! Tafiya ta farayi sai jiri ya kwasheta zata Fadi da hanzari ya saka hannu ya Rike hannunta kafin ya saketa ta Fada,kan gado Cikin mamaki yake kallonta tana kuka tana Dafe da Cikinta tana fadin"Wayyo Cikina..! Kai Tsaye yace"Yunwa ko.? Kamar tana jira ta dagamai kai yar Dariya yayi kafin yace"Ai ita yunwa ba"a mata iskanci..Duk Taurin kanki ai gashi nan ta koya miki hankali..! Tsaki yaja ya fice Daga Dakin ta bisa da kallo aranta tana addu"a da Fatan Allah yasa abinci zai kawo mata domin ta kusa rasuwa..! *Janafty**TFZB2003* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Sakina na zaune inda Umar ya barta taga ya sake fitowa cikin mamakinta sai taga ya nufi Dinning ya Dauki katon mug ya tsiyaya ruwan tea ya saka madara da Milo sai siga bata iya shuru ba sai da tace"Habiba yau kuma Tea zaka sha da madara..? Saninsa tun abaya madara bata wani Damesa ba,Bai mata mgana ba taga ya Dauki mug din ya nufi Dakin da Amina take wajen kallonsa kadan ya Rage bata fado daga kan kujera ba sai da taga shigansa sannan ta maida kallonta acikin ranta tana fadin kan uba..! Shi kuwa yana shiga ya iske Amina inda ya barta kwance tana numfashi Sama sama,Kai tsaye yace"Tashi zaune..! Ba musu ta mike tana wani karya wuya saboda yunwa mikamata Kofin yayi ta karba tana wani lankwashewa Cikin bada Umarni yace"Shanyesa yanzu..! Ba musu ta kafa kai ta fara sha Jikinta da Hannunta na rawa Lokaci Daya yana tsaye ya jingina da wardrope din Dakin yana Binta da kallo ganin yadda jikinta ke rawa yasan taci Ubanta da yunwa yaji dadin haka shifa Tana cin Darajan masu Daraja ne ammh ba domin haka ba ko zata mutu ne bata isheshi kallo ba wlh. Duk da kyamkyamin Dakin dayake yi bai fita ba yana Tsaye yana Nazarinta Abun dariya ya basa Daya ga karamar kafarta Dauke da Jan lalle tare da Hannayenta wai nan shi akayi mawa ko. ? Shi allah kada ya nuna mai sanda zai kula wannan yarinyar wacce bakomai acikinta sai iskanci da rashin kunya. Yana wannan Tunanin baisan tashinta ba sai kakarin amai da ya jiyo a Tiolet lekata yayi yana fadin"Ke miye haka..? Amina na Duke daga cikin Tiolet tana maida numfashin wahala tace"Cikina ne ke juyamin..! Tafada tana kara Dafe Cikinta Saboda yadda yake Hautsina mata Ta Dade bataci komai ba shiyasa Dan mallam karamin Tsaki yaja bai yi mgana ba Sai ga Amina ta fito tana layi ta sake fadawa saman gadon Cikin mamaki yake kallonta ganin harta gaban Riganta ya fara baci da amai haka gefen bakinta zuciyarsa yaji ta Fara tashi yayi saurin matsawa baya yana Fadin"Ke meyasa kin cika kazanta ne..? Aman da kikayi wa zai wanke miki..?Sannan ji bakin ki da gaban rigarki duk amai baki da Hankali ne..? Ya karishe fada yana kauda kansa Sabida bayason kallonta kyama take basa ita kuma ga ciwo ga fadansa kawai sai ta fashemai da kuka tana Fadin"Nifa banda lafiya in na mike jiri nake gani..! Daure Fuska yayi yana fadin"To ba anan ba maza mike ki wuce Tiolet ki Tabbatar da kin wanke kazantar ki sannan ki tube kayan jikin ki,kin yi wanka..Wlh kada ki bari na Dawo na iskeki a haka ranki zai baci..! Kukanta ta karama Volume tana fadin"Wlh bazan iya ba..! Tsawa ya Dakata mata Lokaci Daya yana Fadin"Zaki tashi ki wuce ko sai na saka miki hannu..?Tunda kika zo gidan nan kike sakani mgana ki yi abunda nace tun kafin na yarda da Shawaran zuciyata na kaiki inda ake gyaraama irin ku zama..! Ai bai gama mgana ba Amina ta mike tana Kuka ta shige Tiolet din Kamar ta Fadi Jikinta ba karfi Tsaki yaja ya Fice aransa yana Jinjina kazanta irin na Amina bai taba Zaton haka take ba. Sakina ta na nan inda ya barta Tana jiran fitowarsa,kusa da ita yaje ya zauna yana sauke numfashi sai yanzu yaji ya shaki iska ammh Dakin chan wlh ba yanayi mai Dadi ganin yadda ya Zauna yayi ne yasa ta gyara zama tana Fadin"Meya faru Habibi..!? Bai kalleta ba ya mike yana Fadin"Abinci ya yi saura..? Cikin mamaki tace"Menene..? Yana Tafiya wajen Dinning yace"Zuba ma yarinyar chan a filet ki shigar mata dashi..Sannan Daga yau ki rika Dafa abinci da ita kin ji ko..? Sakina kadan ya Rage bata Danna ma Umar ashar ba sai ta Tuna mijinta ne ammh sai da ta Hararesa kafin tace"Nine ma zan rika girka mata abinci ina aika mata Dashi Daki ko..? Kai Tsaye yace"Haka nace..! Sakina ta kallesa Daga sama har kasa kafin tace"Saboda wani Dalili..? Ka manta kai kace Matsayina da nata Daya ne..? Bai son doguwar mgana yasa yace"Saboda ita yarinya ce..Kuma Amana ce a wajenmu..! Sakina ta yi shewa kafin tace"yarinya kuma suka aura maka ita..? Amana kuma ai takace ni dai ba wanda ya bani wata amana..! Gani yayi zata raina masa wayau yasa yace"Su wa kike mganar sun auramin ita cikin Raini Sakina..? Yafada yanayinsa na sauyawa ganin haka yasa tayi saurin cewa"Ni fa ba su nace ba..kawai dai kai ma baka taki adalci ba..Zan Dafa abinci ammh wlh bazan Dafa mata na Bita dashi adaki ba in ta fito shikenan in bata fito ba ita ta sani..! Tana gama Fadin haka ta Mike Dauke da wayarta zata shige Dakinta ya Daga Muryansa yana fadin"bazaki zuba mata ba kenan..? Juyowa tayi kafin ta kallesa Duk da ta tsorata da yadda ya Hade ransa ammh wlh bazata zauna tana Boyin boyin Amina ba, yasa kai Tsaye tace"Eh..Kai ka zuba ka kai mata tunda ta zama Dolenka ammh bani Sakina ba..! Daga haka ta shige ta barsa ya bita da kallo bayason Fitina ne yasa bai bi ta kanta ba ya isa ga kular abinci ya Dauki Filet ya Bude ya zubama Amina Daidai ya rufe ya Daukar mata Ruwan gora guda Daya mganar Mallam kawai yake tunawa yasa zai taimaketa kada Cutar yunwa ta mata Lahani fatansa Visar  sa ta fito wannan Satin ya saka kafa ya tafi sai yaga karyan iskanci daga ita har Sakinan sai su kashe junansu shi ba ruwansa. Sanda ya koma Daki tayi wanka sai dai abun haushi kayan jikinta ta maida nan kasan Cafet ya ijiye kayan hannunsa yana hararanta  kafin yayi mgana ma ta mike jikinta na rawa tana fadin"Ban..baga kayan bane..! Ghanas dinta ya nuna mata yana Fadin"Ai kinsan kayanki ne acikin nan ko suma sai na ciro na saka miki..? Da Sauri ta girgiza kai ta wuce sumi sumi wajen jakunkuna ta Duka ta Bude Daya taga Littafan makarantar ne aciki sai da ta Bude Dayan ne taga kayan a goge sai da tayi hawaye tasan aikin Mamanmu ce ko Hamida aranta tace Allah sarki Hamida da hanne ina kewarku..! Wata Doguwar riga ta Dauko na Material sai bakin dankwali,zata maida ta rufe yace"Ciro wani Hijabin ki Cire na jikin ki malama..! Ba musu ta ciro aranta ta kudira ta gama mai gaddama gashi mara imani ga mganar Aba ayadda take din nan bata fatan ta kara yin wani abun da Aba zai yi Tir da ita,Tayi alkawarin har Abada an dai kaimasa kararta. Kayan ta Dunkule Cikin Hijabinta ta gabansa ta wuce zuwa Tiolet chan ta Sauya kayan ta Sake fitowa da na hannunta yana Dakin bai fita ba ganin zata maida masu Dattin Cikin jakar yasa yace"ke wai meke damun ki ne..? Masu dattin zaki maida Ciki kuma..?Common maida su Tiolet akwai kwando Dogo ki saka aciki nan zaki rika tara kayan Dattin da kika cire..! Sumi sumi ta koma ta saka a inda yace sannan ta kara fitowa abinci ya nuna mata yana fadin"Ki zauna kici..Wannan shine na karshe da zan kawo miki abinci ruwanki ne ki Fita ki nema ruwanki ne ki zauna da yunwa..Kin ga dai ishara ko..?,Ita yunwa ba"ayi mata Taurin kai..! Ba musu ta zauna Daman yunwar take ji dan Tea din Data sha ta Amayar dashi kama hanyar fita yayi kafin ya Juyo yana kallonta har taja Filet din gabanta Hararanta yayi ta kasan ido take kallonsa kanta na kasa cikin Sanyinsa yace"Ki tabbatar kuma kin sanya duka kayanan cikin wardrope bna so na kara ganinsu anan wajen kin ji ko baki ji ba..? Da kai ta gyada mai kafin tace"To..! Bai kara mgana ba ya fice ya ja mata Kofa kamar tana jira ta Fara cin faten Dankalin hannu baka hannun kwarya sai da ta da shi duka ta kora da ruwa sannan ta kara da sauran Tea din Dazu su Amina har ana lashe Filet,Sai Lokacin taji ta dawo daidai Ajiyar rai ta Sauke ta yaye Hijabin jikinta tana kara shan iska sai da ta huta sannan tatashi taje ta wanke hannu,ko ta kan Filet da kofin batayi ba ta fara Bude kayanta tana watse su a kasa domin bata son ya sake shigowa ya gansu Allah kadai yasan me zai mata in batayi abunda yace ba tana Tunanin su ya jafar ne mugaye sai yanzu take fahimtar akwai wanda ya Shafe su a mugunta ya Danmallam Tana da tabbacin daga shi har shegiyar gajerar matar nan tasa basu da Imani gwara ta bisu a sannu su wanye Lafiya. A wardrope din ta saka kayan kamar yadda yace,ba komai acikinsa sai Rigar barci Daya da Jallabiya guda Biyu Saman Madubi kuma sai Tararuka Amina ta matsar da su gefe ta saka kayanta aranta tana fadin ita yar Saudi bata ijiye kayanta anan ba kenan..? Har da littafan makarantar ta da takalmi da jakar Cikin wardrope ta Nausa su ta hada da ghanas din duka ta Tura kada dai yazo ya gani kafin ta gama bayanta ya kage ta koma ta zauna bakin gado tana Tuna Hamida afili ta Furta"Allah sarki Hamida kin sha Fadamin watarana baki tare dani zan tuna dake..Sai gashi Kaddaran data Rabani dake ko kwana Daya ban yi Cikinta ba na Tunaki hamida..! Sai hawaye ta tabbata da Hamida na nan tare da ita duka wannan aikin ita zatayi Kan gadon ta koma ta Dunkule tana kukanta na fama sai da taji sanyi ya isheta ne sannan ta tuna batayi sallar mangriba da isha"i ba..dole ta mike ta koma Tiolet din ta Dauro alwala tazo ta Daidai ci gabas tayi sallarta tana idarwa ta kwanta nan Saman Cafet din tana Tunanin rayuwarta a wannan gidan,Sai kuma ta fara kuka kewar yaya ta isheta Sai kuma ta ji mutuwarta ta dawo mata Sabuwa sai kuma ta tuna da mamanmu da su Hamida sai kuka wiwi har barci ya kwasheta tana kuka bata sani ba. Da safe tana tashi da filet da kofunan taci karo tana idar da sallar asuba ta makara sai da gari ya waye ta tashi ta Dauke duka harda goron ruwa ta fara Tunanin in da zata kai domin in wannan dan bala"in yazo ya gani kashinta ai bushe. Yanke shawaran fita tayi ta kai kitchen daman ya sa mata sabon suna wai kazama ai in yaga wannan sai ya kara kiranta da Hujja.. Koda ta fito shuru falon ba kowa sai da ta leka ta tabbatar da ba kowa sannan ta fara Tafiya Sadaf Sadaf zuwa Kitchen ai tasan hanyar tunda sun taba zuwa. Tana shiga kitchen din nan ma ba kowa sai dai tas kitchen din ba Datti kamar ba"a girki a wajen saman Cabinet din kitchen ta ijiye kayan hannunta ta juyo kenan zata fito suka kusa cin karo da Sakina data ganta sai da gabanta ya fadi ta ja baya tana Zare ido. Sakina Dake sanye da Riga da wando na plazo ta kalli Amina Daga sama har kasa cikin kaskasci kafin tace"Me ya kawo ki kitchen dina..? Amina ta kalleta taso tace ne bata sani ba ammh kuma bata da wannan karfin gwiwan yanzu ta kanta take yi yasa batace mata komai ba ta raba ta gefenta zata fita ran sakina ya baci ta Finciki hijabinta ta Dawo da ita baya ta Shake mata wuyan Hijabi tana Fadin"Ke don ubanki ni nake miki mgana kina sha min kamshi..? Tafada tana Zare mata ido Amina ta kalleta ammh ta kasa mgana aranta Tana Tunanin Sakina tazo Lokacin da Bazata iya maida mata martani ba..Ammh ta bari wanchan mara imanin ya tafi wlh bata zagi Aba a banza ba sai ta rama mai. Ido ta dago karaf suka hada ido da Danmallam dake tsaye daga falo yana kallonsu yana sanye da Jallabiya baka da Hula Cashaba ce a hannunsa kamar Dawowarsa kenan daga masallaci. Amina tana ganinsa sai da gabanta ya fadi da sauri tace"Kiyi hakuri abu na kawo..! Sakina zatayi mgana kenan taji Muryansa daga bayanta yana Fadin"Saketa Sakina..! Sai Lokacin ta juyo tana kallonsa sannan ta saketa ammh sai da ta Murje mata kafa da takalmin Dake kafarta Amina taji azaba ammh bata nuna ba Da sauri  ta fice Daga kitchen din kamar ta kifa ko barayinsa bata kallah ba ta koma Dakin datake tana shiga ta Dafe kirji tana Sauke Numfashi kamar wata mara galihu haka ta koma saman cafet ta zauna tayi Tagumi bata son hawa gadon ne bata saba da irin shi ba sannan ta saba kwana cikin mutane,akwai watarana ma da ita da Hamida suke kwana agado daya hamida tayi ta mitan ta matseta ammh Amina ta mata Burus wai ga inda Rayuwa ta kawota ita kadai kamar mara galihu. Tunda ta shigo Dakin bata kara jin motsin su ba sai chan rana Sakina ta shigo Lokacin har barci ya fara Fizganta koda ta Bude ido sai taga ta Dungurar mata da Filet din abinci tayi Tsaki ta fice Daman yunwar Amina take ji domin tayi alkawarin daina zama da yunwa in ta mutu Danmallam da matarsa basu da asara. Data gama da Filet din ta fita takai kitchen bata ga sakina ba yasa ta Tsaya ta Bude Fridge ta Dauki ruwa ta sha ta Koshi ta koma Daki da Daddare ma Sakinar ta kawomata Fuskar nan tata kamar Hadari saboda hadewa,Ta ballama Amina Harara Dake zaune taba kallonta sai da ta fita taji Dariya ya kamata aranta tace bani kadai yake ma Mugunta ba harda matar tasa tasan badomin shi ba Bata isa Sakina ma ta kalleta ba.. Kamar ta sani tun abunda tace mai jiya da Daddare ya dinga Daure mata shiyasa sai ta ganshi sai ta zuba abincin ta kaima Amina tana cika tana batsewa shi dai ko kara bi ta kan Sakina bai yi ballatana Amina,ita kuma Sakina Dadinta Daya ganin Aminar da ita da banza duk daya a wajen Umar sannan suna waya da Anty Amarya tana fadamata komai ita tace tarika bama Amina abinci ba komai suke da nasara.. Washegari tun safe Umar ya fita kan mganar Visa dinsa kano yaje tunda ta chan zasu tashi sai dare ya dawo an samu Visar nan da kwana Hudu zasu tashi,Farinciki ya ishesa sai kuma aranar yaje chan Gida bayan tafiyarsa da Amina sun hadu da Aba yayi ta mai fadan kada ya saurarama Amina in tayi mai wani abu yayi mganinta kada ya Ragamata shidai bai ce komai ba. Taya ya zai biyema Aba ya taba Amina hajiya ko mallam su ji labari ai sai su Tsine mai ya samu dai ya lallaba ya kara gaba ba"a gansa ba ballatana ace wani abu. Tare da mallam sukayi sallar isha"i Daganan ya shiga cikin gida ya gaida matan mahaifinsa,Shashen Hajiya ne na karshe,ya shiga tana zaune afalo tana gyaran farcenta ya zauna nesa da ita a kasa suka gaisa tana tambayansa Amina yace tana lafiya. Shuru na wani Lokaci kafin ya muskuta yana fadin"Hajiya na samu Visa ina ga nan da kwana hudu zan tafi..! Hajiya ta Dago tana kallonsa kafin tace"Allah ya kaimu..Allah kuma ya Tsare..! Kansa na kasa ya amsa da Ameen kafin Hajiya tace"Yanzu ba da ita Sakinar zaka koma ba kenan..? Kai Tsaye yace"Eh Hajiya..! Hajiya tace"Ai shikenan ma da nazata da ita zaka koma nayi ma mallam mganar Hamida da hanne su koma chan su taya Amina zama har ku dawo..! Yana jinta bai ce komai ba tacigaba da Fadib"Ammh tunda ta na nan shikenan..Sai dai kafin ka tafi zaka siya mata ko karamar waya ko Danmallam..? Kansa na kasa kafin ya Dago yana Fadin"To Hajiya sai a siya mata..! Hajiya tace"Ya kamata gaskiya tunda kaga itama Sakinar nada wayarta. sannan in ka tafi chan sai ku dinga mgana ta wayar da zaka siya mata hakan zai fi..! Danmallam dai nasa cewa to ne Domin Gata kan Amina ta fisa gata a wajen su Hajiya. Shuru ya kara giftawa na wani lokaci kafin tace"yaran nan ma yan"uwanta har yanzu basu saki da kewar Amina ba..Nace zasu je mata cikin Satinan tunda ma zaka tafi bari in ka tafi sai su tafi su mata ko kwana Biyu ne nasan zataji Dadi..! Dan mallan kansa na kasa aransa yace"Zataji dadi tunda abokan iskancin nata suna kusa da ita..! A fili kuma bai ce komai ba Hajiya ta shiga Fadamai zata je maidguri Cikin watanan yar yagana zatayi aure ya Dago yana fadin"Hajiya daman tana da wata ya agabanta ne..?Na dauka Suhailu ne kadai autanta..! Hajiya tace"A"a tana da karamar ta zaituna itace zatayi aure..! Bai wani damu ba yace"Allah ya kaimu hajiya..Allah ya bada zaman lafiya ke kuma Allah ya kaiki lafiya ya Dawo Dake..! Ta amsa mai da Ameen kafin tayi mgana Hanne da Hamida sun shigo Falon suna ganin ya Danmallam suka natssu suna gaishesa ya amsa yana kallonsu ganin yadda sukayi wani iri Hajiya ta kalle su tana fadin"Nasha chan zaki yi kwanciyar ki hanne..! Hanne batayi mgana ba kanta na kasa Hamida ce tace"ni ce zan kwana anan Hajiya..! Hajiya tace"Shikenan yau dai kun ma Balaraba Yaji..Ita kadai sai jawadu..! Basu ce komai ba kansu na kasa Hamida ke taba hanne ita kuma taki mgana Hajiya ce ta gansu Dariya tayi kafin tace"Ku sha kuruminku..Karshen sati zaku je kuga Amina..! Baki suka washe suka hada baki wajen Fadin"Da gaske hajiya..? Hajiya tace"Yanzu ma muka gama mgana da yayanku..! Suka wani daka Tsalle suka Rumgume juna wani kallo yayi musu dayasa suka natsu waje daya ganin haka yasa ya mike yayi ma Hajiya sallama ta amsamai tare da cewa"Kace ma Amina su hanne na nan zuwa zasu zo mata da sako tayi hakuri..! A kasan makoshi ya amsa ma Hajiya kafin ya fice Daga Shashen yana jin ihun yaran bayan ya fita kai ya girgiza kaawai. Falom Mallam ya koma sukayi sallama shi da Aba ne suna mgana Daganan ya shiga motarsa zuwa gida koda ya koma Sakina ta gama komai taci kwalliya tana jiransa ta tarbesa ta taimakamai yayi wanka ya sauya kaya suka fito saman Dining suna cin abincin sai alokacin ya kalli Sakina yana fadin"Kin kaimata abinci..? Sakina ta amsa mai da kai,Yaji dadin haka kai tsaye yace"Allah yayi miki albarka..! Tana Mirmishi mugunta ta amsa mai da Ameen Ameen domin ta gama wasa wukanta jira take ya saka kafa ya Tafi sai Amina tayi nadama wlh. ********* Washegari.. 9:30am. Adaidaita ta shiga yana ta Gudu da ita kamar zai bar garin gumel da ita sannan naga ya Tsaya bakin hanya inda ba yalwar giftawan abun hawa Fitowa tayi sanye da Hijabi Dogo har kasa ga Nikab a Fuskarta karamar Jakarta ta Dauko ta bashi kudinsa kafin ta fara tafiya ta mike wata Hanya tayi tafiya sosai kafin ta fara Hango ta tana zaune saman wani Dutse tana jiranta sai da ta tazo gabanta sannan tace" Aci balbal Fitilar sharri..Ko babu mai kina kai safe. Kwalba ko kin fashe da sauran sharri kibiyar ajali kike mai Ratsa rigar karfe..Madina ikon Allah gabanki Fari bayanki baki..!gaba salamun baya salamun damisa mai maida Fatar kura nama..! Wata irin Dariya Anty Amarya ta saki Lokaci Daya tana mikewa tsaye hannu ta bama ta Tsayen suka tafa ji kake tas..kafin tace"Ban kai ki sharri ba Dayyaba..Domin ni daman chan ban taba aron Fuskar salihai ba..ke kuma fa kin fini zama kwalbar sharri..An aminta Dake kin ci Amana sannan a yarje miki kin yi ha"inci..! Tare suka kara saka Dariya kafin ta yaye Nikab din data Rufe fuskarta sai ga Mamanmu ta bayyana..! Cikin wani yanayi tace"Babu abunda zan ce da ke madina..Sai Allah ya Cika miki naki Burin..! Saura kadan na gama mallakan Sa"iduna a hannuna madina kiris ya rage .! Anty Amarya dake sanye itama da Dogon Hijabi tace"Kwarai naga alama..Ammh meyasa kika batamin Lokaci kinsan tun yaushe nake tsuggune anan wajen ina faman jiranki..!? Mamanmu tace"sai da ya fita sannan na samu na fito daga gidam..Kinsan dai yanayin da ake ciki..Lokacin da yaya nan ne nake samun fita akai akai in nace zan shiga gidanku yanzu kuma gida ni kadai ce Hamida na makaranta ita da jawaad..Kuskure kadan zan yi sai kiga na bata komai..! Anty Amarya tace"kiyi hanzari ina kan hanya ne..! Ba musu ta Bude Jakarta ta Dauko Kudi masu yawa ta Damkama Anty Amarya tana fadin"Shashashan wai fa bani yayi nayi ma Amina siyayyan kayan amfani shine nayi sama dasu..! Anty Amarya tayi dariya kafin tace"Shegiya Balaraba...! Mamanmu tace"kul..Dayyaba nake in kika Kirani balaraba kamar kin Ragema Kwalba sharri ne..! Tare suka kasa Dariya kafin Anty Amarya tace"Mallam fa ya fara korafin kin Daina zuwa yanzu sai dai nazo ni kadai kada ya fara Tunanin ko dan kin Samu Biyan Bukata ne..! Mamanmu tace"ki kai masa wannan kudin na karin kudin aiki ne..Mganar zuwana kuma in zaki koma dani zamu koma nace miki nan da Sati Biyu zan je gusai bikin gidansu..Sai na Fake da Guzuma na Harbi karkasa..! Anty Amarya tayi dariya sosai kafin ta Fito da jakarta babba ta Tura kudin aciki kafin tace"Shikenan bari nayi hanzari..bana so nayi Dare..! Kallonta tayi kafin tace"Kwana zaki yi..? Kai Tsaye tace"Eh in nayi Dare sai gobe zan dawo..Zuwan daman na Sakina ne so nake Mallam yayi aiki kan Umar ya koma da ita madina..! Bana son zamanta da wannan shegiyar Yar taki..! Mamanmu ta bata rai kafin tace"A"a fa ki bari madina..Allah ya Tsareni ni Uwar Zulfa nake da Zahra kuma uwar Hamida...! Anty amarya tayi dariya kafin tace"Mamannu...Mamanmu ..! Tana kwaikwayon muryan Amina aatare suka fashe da Dariya suka tafa Kafin mamanmu tace"Uwarta na kabari..! Wani Tsari kika rakata ne ni ban kara ma bi ta kanta ba tun sanda ta bar min gidana..! Anty amarya tace"Tsarin auran ya zo a banza ya kare a banza..Domin Sakina ta tabbatarmin ita da banza Duk Daya suke awajensa..Kinga kenan haka zata gaji da zama har mallam da Hajiya da suka kulla abun su gaji su Rabashi..Sannan nace ma mallam ya kara mata rashin kunya da Tijara tayimai ya Sako shegiya..! Mamanmu tace"Ni kuma Daga Lokacin zan karata gaba..Bana son na kara bude ido na ganta agidan nan har Abada gidanan nawa ne ni da ya"yana..! Anty Amarya tace"Kadan zaki jira..Burinki zai gama cika..! Ni ce dai naga Tafiyata akwai Tsawo..Burina kawai sakina ta samu Ciki ta Haihu in hakan ta Faru kamar na gama cika duka Burina ne..! Mamanmu tace"Kema lokaci kadan ya Rage..Dukkanmu wahalar mu bazata tashi a banza ba..! Anty Amarya tace"Tabbas..Domin bazan gaza ba..Sai naga abunda ya Turema Buzu nadi..Zan tafi yadda ake ciki zan kiraki..! Mamanmu tace"Ki sanar da mallam Sa"idu ya fara zuwa hannu..Ammh ina so ya zama ni nake fadi yana amsani.. Anty amarya tace"Kamar yan amshin Shata kenan..! Gabadayansu dariya suka saka kafin su tako atare har bakin Titi kowacce Adaidaita Dabam Dabam suka hau Daya ta koma cikin gari Daya kuma ta Mika hanyar tashar garin na Gumel..! _SHIN KINA DA LABARI AKAN HAƊIN SABAYA KOKUMA IN ƘARA MIKI BAYANI AKANSA DOMIN WANNAN HADIN INGANTACCE NE BA IRIN WANDA KUKA SABA AMAFANI DASHI BANE_ Shi wannan din SABAYA COCONUT FLAKES ne, duk wani hadi da ake nema na gyaran jiki akwaishi aciki duka hajiyata, naturally zaki cicciko babu abubuwan illa aciki. *Ina ƴan mata da zawarawa kai harma da matan Aure? To ku matso kusa ga Sabaya wanda akayi hadinsa da coconut flakes kuma kun san kwakwa ba karamin taka rawa yake wajen gyaran jikin 'ya mace ba, SABAYA COCONUT FLAKES zai taimaka wajen ciko da duk wani lungu da saƙo na jikin mace, ta dawo mul-mul da ita tamkar jinin ƴan Chadii.* *yana sa ƙirjin mace ya ciko sosai, idan ma ƙirjinki a kwance yake sabaya na iya miƙar dashi ya koma kamar na buduwar ƴar shekaru sha 18. Duk wannam aikin na SABAYA COCONUT FLAKES ne shi kaɗai 💃💃💃, bayan haka yana ƙara ni'ima a jikin mace gamida ƙara mata ɗumin jiki. Ga matar Aure kuma yana ƙara mata juriya wajen gamsar da mai gidanta cikin sauƙi. Tareda ɗorewar nishaɗin su gabaɗaya.* *Hajiya maza ki nememu don ki mallaki SABAYANKI, don kema ki zama mace mai aji kuma ƙasaitacciya, karki yarda ki zauna yarkace-yarkace kamar kin fito gidan Yari😂, Gyara shine Mace Hajiya, idan bakya gyara jikinki sunanki mata maza, ko kuma in kiraki da suna wadda ta rako mata duniya Kawai🙅‍♀️* *_Domin niman ƙarin bayani ku tintiɓeni kai tsaye ta wannan lambar:_* +234 706 548 1260 *_Muna tura kayan mu ko wani gari da zarar kinyi order 💃. Kuma duk akan farashi mai Rahusa🥰 muna maraba da masu siyan daya ko sari..mungode sai kunzo🙏 07065481260 *Janafty**TFZB2004* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* BAYAN KWANA BIYU. Amina ta gaji da kuka ta daina domin ta tabbatar ma kanta ita inda kaddaranta ta kawota kenan bata da wani tsumi ballatana Dubara kukan tayi shi har ta gaji ta hakura cikin kwana Biyun nan duk ta rame tayi Firgai Firgai ba walwala bata da sakewa sai zama waje daya da zaman kunci tundaga ranar bata kara saka Ya danmallam a idonta ba itama taji dadin haka sannan In yana gidan ta lura Sakina zata kawo mata abinci sau uku arana in kuma ranar baya gida to sai dai ta sha yunwarta sai dare bamai lekota ita kuma bazata iya fitowa ba har alokacin akwai sauran tashin hankali da kuma kokuwa da abunda ya sameta sannan uwa uba kuma rashin Sabo da inda take zaunen. Amina bata wanka rabonta da wanka Tun ranar da Umar ya Tursasata tayi bata kara ganin ruwa ba sallah ce da ta zame mata dole take yinta sai abinci in Sakina taga dama ta bata wannan kam tana ci domin ta tabbatar ma kanta in ma bata ci ba sai dai ta Mutu daga sakinar har mijin nata ba wanda ya damu da ita acikin gidan sai filet din sun taru take fita dashi kitchen bata bari su hadu da Sakina domin har yanzu bata shiryama wannan rigimar datake janta dashi ba. Ruwa kuwa bata matsama kanta ba na Tiolet take tara ta sha abunta Daki ba Shara ba komai Amina ita dai ta Wuni aciki ta kwana aciki ne kadai aikinta in kewar su hanne ya isheta taji kamar ta gudu gida sannan tana kewar makaranta abaya ranta baci yake yi in Monday ta zagayo ko Asabar sai gashi yanzu ido rufe take kewar makaranta tana ji dama ace tana da wannan damar da kewa bata isheta ba taji tana son zuwa makarantar ba Dama baba mallam bata kara ganinsa ba ballatana Hajiya kai wani Daga chan gidan ba wanda tagani balle taji ita ya makomar karatunta tunda yazo nan ya sar da ita bai damu data rayu ko karta rayu ba Allah sarki rayuwa tasan su hanne suna cigaba da zuwa makarantarsu tasan kuma yan ajinsu suna ta tambayanta kila sun fada musu an mata aure har an kawota gidan wannan mara Imanin. Abunda bata sani ba shi Danmallan mantawa ma yake da ita agidan Shiryen Shiryen Tafiyarsa kadai yake yi Sakina sai da ta ga tafiyarsa tasa ta taso sannan Hankalin ta ya tashi Ana saura kwana Biyu Jirgin su ya tashi Ranar ya dawo da Daddare taji suna mgana da Aliyu ta waya yana Fadamai zai Dauki kimanin wata bakwai Cikin na takwas kafin ya Dawo. Hankalin Sakina ya tashi duk da sun yi mgana da Anty ta Fadamata ta kwantar da hankalinta mallam ya tabbatar mata da cewa ko Umar ya tafi Bazai iya sukuni ba sai ya Dawo ya Tafi da ita saboda in ya barta anan ai anyi ba"ayi ba kenan Ga zamanta da wannan kazamar yarinya ga kuma rshin miji a kusa ta ina zata samu Cikin in baya nan bayan duka kokarinsu kenan yau ta ganta ta samu juna ya Tsaya mata ba ya bare kamar yadda yayi mata har sau uku ba. Kafin ya gama waya ta Durkushe gabansa tana ruwan hawaye kallo Daya yayi mata yasa kwanan zencen sai ya shareta,Shifa gabadaya sha"anin mata ya fara fita kansa yau sai da ya yi ma Sarood fada soaai bisa yadda ta Kirasa tana kuka tana mai korafin ya tafi ya manta da ita tunda yana da mata har Biyu anan to ta gaji in bai dawo ba zata Biyosa bai hanata ba yace tazo ammh ta sani nan zata zauna itama bai kuma fadamata ga shi dawowa ba ya riga ya gama Shakan takaicin su gabadayansu ba Sakinar ba,Ba sarood din ba dukkansu ba kwanwar lasa bane,A baya sai yake ganin Sarood mai Hakuri ashe itama kyallece haka kawai ya fadamata ya Datse kiran yayi Rantsuwan in har tazo wlh sai dai ta Dauwama a Nageria ita da Madina sai da ziyara ai shima ba kasarsa bane cin arziki yake yi shi yanzu Damuwarsa daya yadda Hajiya ta Dage sai ya nema ma Amina muhallin Zama a Madina Tsakani ga Allah zai Takura baisan ta ina ma zai Fara ba kuma yadda Hajiya ta kafe din nan ko mallam bazai iya Tankwasata ba shima baya so ya fara Saba Umarninta tunda bata taba katsalanta kan sha"aninsa da matansa ba wannan ma Saboda yar gold ce. Sakina ganin yaki bi ta kanta yasa ta fara jan Hanci tana fadin"Yanzu Habibi haka zaka tafi ka barni sai bayan wata bakwai ka dawo..? Kana ganin ko ta bangaran addini kayi Daidai kenan..? Suna Cikin Bedroom dinsa ne yana zaune gefen gadonsa tana sanan Cafet yayi mata kallon sama da kasa kafin ya Dauke kai Sakina ta riga ta tabbatar ma kanta bazai taba Sauya Ra"ayinsa ba. Shiyasa ta mike tana fadin"Shikenan kasan dai ni macece kuma in da Hakki a kanka..In sha"awata tatashi Watarana har na cutu kai da Allah Umar..! Ta karishe fada tana jan majinan kuka,har ta fice yana kallonta kafin yaja karamin tsaki bata san shi bane sai yanzu zata san shi ko ajikinsa komawa yayi ya kwanta yana jinsa kamar akan kaya ya kosa ya Bude ido ya gansa a madina matsalan Sarood karamace tsakaninsu ne ya lura in bata ganin Sakina tafi Hankali da natsuwa da kuma Hakuri ammh in dai tana Ganin Sakina akusa da ita tafi korafi da kananun mganganu. Sakina na fita Dakinta ta koma tana Shesahekan kuka ta daga waya ta Kira Anty wacce ke shashen baba mallam alokacin sun gama cin abinci kenan dukkansu yaransun fita sai su dake falon gabadayansu har da Hajiya Babba suna hira kan yadda Zaman lafiya da rashin Tsaro ya yawaita hirar Tsakanin Mallam ne da Hajiya Babba sai Haj.Uwani Haj.Nasara na gefe tana saka baki jefi jefi,Anty Amarya ne keda Mallam aranar shiyasa tana gefe tana kallonsu bata saka baki daman tana da yawan ware kanta acikinsu Wayarta na Hannunta sanda kiran Sakina ya shigo sai taki Dauka sai da taga Kiran yaki ya kare ne sannan ta tashi ta fita ba wanda ma ya lura da ita sai Hj.uwani da take ta sakin munafukin Murmishi Domin duk wani Motsin Marliya ai a tafin Hannunta take duk ta gama kokarin nata sai ya tashi a banza.. Sai da ta isa shashenta sannan ta Daga kiran Sakina Dayaki karewa Cikin Fada tace"Miye haka sakina..? Kina kirana da wannan daran in Kika bada Kofa aka ganemu fa..? Kuma mijinki na gida in ya fara Zargina fa..? Ke meyasa baki da Hakuri ne..? Sakina cikin kuka tace"To Anty yau fa naji yana fada in ya saka kafa ya tafi sai bayan wata takwas fa zai dawo..! Anty Amarya tayi Tsaki kafin tace"To shi ne me..? Sakina tayi kasa da Murya kafin tace"Anty kin manta ne..?in yana chan a ina zai ganni har auratayyah ya shiga Tsakaninmu na samu Cikin da muke Fata..? Sai alokacin Anty Amarya ta Dawo Cikin Hayyacinta cikin Tashin Hankali ta Dafe kanta kafin tace"Kin gane duk nasan da wannan..Na fada miki mallam yace ko ya tafin zai dawo ya tafi dake Sakina ki daina Damuwa..! Sakina tace"Nidai Anty mu tafi Taren hankalina zai fi kwanciya..!.Anty tace"To sai dai in Tuntuba ta bangaran Mallam,Ammh ta bangaran Umar kina ganin abunda yace min bazai saurareni ba in na matsa ma sai ya fara Zarginmu..! Ki bari yau ni ke da Turakan mallan in wadanchan matan nasa sun watse zan mai mgana naji..! Sakina tace"Yauwa Anty nagode don Allah kimai mgana don Allah..! Anty Amarya tace"Naji zan mai mgana nace..Ki kuma ki daina Damuwa ki kuma rika hakuri kada wannan zalaman naki ya bata mana aiki..! Da toh sakina ta amsa daganan sukayi sallama Anty Amarya tayi Tsaki afili ta Furta"Sakina tana da matsala wlh..! Daganan Toilet ta fada domin ta sake Sabon wanka so take ta ruda mallam da nata salon yadda bazai mata gardama ba. Achan Falon mallam kuwa bayan Fitan Anty Amarya itama Hj.nasara tayi musu sallama ta koma Shashenta ya Rage daga hajiya sai mallam Sai Haj.uwani Dake zaune gefen Hajiya Bisa kujera mai zaman mutum biyu Cikin kissarta data shiga Jikinsu gabadaya domin Hajiya ta yarda da ita Dari Bisa dari hakama mallam. Sai da ta kalli Hajiya kafin tace"Oh Hajiya wai bawanda zai koma ya Dubomana Amina..?Tunda Suka tafi fa ba wanda yabi bayansu..! Hajiya batayi yunkurin mgana ba Mallanlm ne ya Murmusa kafin yace"Kamar wasu yara kanana Uwani..? In ita Amina yarinya ce ai Shi Umaru yana da Hankali na tabbata kuma zai kula da ita..Sannan ai ba ita kadai bace Sakina na tare da ita sannan ko Dazu nan mukayi sallar isha"i dashi kinga kuwa suna nan lafiya..! Kafin tace wani abu Hajiya ta amshe mganar da cewa"Daman ina da niyyar su hanne su je mata..Na bari ne tayi ko Sati ne ta saba da chan kada su je yanzu ta fara koke koken suma ba Tunani ne dasu ba haka zasu hadu su kara Tada mata hankali..! Haj.uwani tayi mirmishi kafin tace"Hakane kuma hajiya..ni daman nace ne ko zamu lekata Amina wlh da ita nake kwana araina Tsausayi ta bani Ranar da zasu tafi..! Mallam yace"Da haka kowa ya saba..kema ai haka kika yi ta kuka ranar da zan taho dake daga Tsafe .! Har Hajiya gatanan tayi wannan koke kokem ko ba haka ba Hajiya. ? Hararan wasa hajiya ta sakar mai batayi mgana sukayi Dariya Dukkansu mallam ya cigaba da fadin"Zai koma ma jibin nan..in ya tafi su je su ganta su wunin mata sai taji Dadi..! Hajiya tace"Eh har kwana ma sai suyi mata..Uwani ai mun girma da zuwa gidan yranmu yanzu sai dai in wani abu ya taso wanda ba"a Fata..! Haj.uwani ta rausayar dakai kafin tace"Ammh in ya koma nan zai barmana ita ko..? Hajiya tace"Eh nan zai barta ita da Sakina zasu zauna agidan su..! Haj.uwani tayi mirmishin jin Dadi kafin tace"to Allah ya zaunar dasu lafiya..! Gabadaya suka amsa da Ameen basu wani jima ba sukayi mai sallama suka fita,Hj.uwani bata koma Shashenta ba ,shashen Hajiya suka yada Zango suna hira sai hillatan Hajiya take yi tana jin wasu sirrikan saboda ko Mallam bai Fada maata abu ba zata jisa abakin Hajiya harta matakin da Hajiya ta Daukan kan tafiyar Amina madina sai da ta fada mata Hj.uwani tace"Wlh gwara haka hajiya..Yazo ya tafi da matarsa..Ni fa marliya ban yarda da ita ba..so suke su mallake Umar din shi kadai to ta Allah bata su ba..! Hajiya tace"Ameen da yardan Allah Amina da Danmallam mutu ka raba. ! Aran Haj.uwani sai da tace ba Ameen ba afili kuma ta amsa da Ameen kafin tayi ma Hajiya sallama ta koma Shashenta Cikin Farincikin da sai da ya Bayyana akan Fuskarta Umaima ta leka ta isketa tayi barci gyara mata Bargo tayi ta fice ta koma Dakinta,Tana shiga tayi wani Shewa lokaci Daya tana Fadin"Cikin ruwan sanyi..Burina zai cika..! Wayarta ta Dauka Dake saman Mirror ta Kira Batula kanwata tana Dauka ta Sakin mata Shewa tana fadin"Batula albishirinki..! Dagachan bangaran Batula tace"Goro Uwani Sikari baki farin banza..! Dariyar Nishadi ta saki kafin tace"Tsarin da muka dora yarinyar nan su Hajiya sun taimaka mana ya tafi Daidai batula..! Batula tace"kai don Allah..?,Bani na sha..! Nan uwani ta warware mata komai ta Karishe da fadin"Kinga jibi zai koma kuma sai ya Dau Lokaci kafin ya Dawo..Zuwa kafin ya dawon na riga na Dorata kan Tsarin koda ma zai kulatan watarana kamar Sakinar ce haka ko ta samu zai bi Rariya..! Batula tace"Dakyau..Hakan yayi kyau sai dai kada ki yi sakaci har adauki wani Lokaci bata hau Tsarin ba kinsan yadda zaki yi ko ta Halin kakane ...Cikin kwanakin nan Namiji fa baka shedarsa..! Haj.Uwani tace"Naso haka sai dai tunda suka tafi batazo ba..Sannan naso na sakama Hajiya Tunanin muje mu Dubata taki bada Dama..ammh nasan zata zo jibi fa zai tafi Batula wlh ina da Tabbacin Mai mata kamar Sakina da balarabiya bazai kula Amina ba kinganta ne..? Kwaila ce fa ga kazanta ga rashin Natsuwa ina da tabbacin bazai taba kulata ba..! Batula tace"Shikenan tunda kina da yakinin haka..Sai dai ina tsoron kada su shammacemu..! Haj.Uwani tace"Na yarda da aikin Mama..Ba wanda ya isa ya shammaceni Batula sai dai ni na shammacesu kamar yadda na saba..! Dariya suka saka gabadayanau kafin su cigaba da mganarsu sun manta cewa Allah ne ke zana kaddaran bawa ba Mutum ba,abunda basu sani ba shine Komai da zai faru nan gaba Allah ya riga ya Tsara faruwar hakan Lokacin kawai ake jira. Tabbas Uwani zata Tsammanci abunda batayi tsammani ba. Bama ita kadai ba iri irenta ma zasu tsammanci abunda basu taba Tsammani ba..! Anty Amarya sai da ta chanchara kwalliya,ta fesa turaruka sannan ta koma Shashen mallam cikin gayunta,Mallam bashi a falo yana cikin Bedroom dinsa chan ta Bisa ta iske ya fito wanka kenan ya sauya kaya zuwa saukakkiyar Jallabiya mai ruwan madara furfuran kansa duk yana Waje ne tana shigowa da sallama ya amsa mata yana Binta da kallo Lokaci daya da Mirmishi Gefen gado ta nemi waje ta zauna tana kallonsa kafin tace"Mallam kayi wanka baka jira ni nazo na tayaka ba..! Mirmishi yayi mata kafin yace"Na Hutassheki ne marliya..! Mikewa tayi ta isa garesa ta amshi Man dayake shafawa a Hannunsa ta Lakuto tana tayasa shafawa Lokaci Daya tana fadin"Aikina ne fa..Kada kamin Rowan lada mana mallan..! Yana kallonta yace"Mun girma marliya wannan aikin duk na Dauke muku yanzu..! Marairaice masa tayi tana fadin"A"a nidai ban yarda mungirma ba....! Yana yar dariya yace"Baki yarda mun girma ba..?,To in ke kina da yarintarki ai yunusa kan ya Tsufa..! Tura bakinta tayi kafin tace"Ni dai wlh Mijina bai Tsufa ba..Yaro ne Danye Sharaf..! Dukkansu yadda ta fadi mganar yasa sukayi Dariya atare ita ta karishe Shafa mai man suka koma saman gado suka zauna mallam ya mike kafarsa tana shafamai man zafi Saboda sun faramai Tauna kuma aki"da ne duk Dare sai ya shafa yake kwanciya Tana shafamai suna Hiransu samasama sai da ta gama hillatansa sannan ta kallesa kafin tace"Ni ko mallam yaushe Danmallam zai koma ne..? Kai tsaye yace mata"Jibi in Allah ya yarda yacemin jiya..! Kai ta Rausayar kafin tace"Ya sanar dakai nan zai bar Sakina..? Mallam yayi shuru kafin yace"A"a bai sanar dani ba..! Anty Amarya ta gyara zama tana fadin"To ni dai baisan me ya faru Tsakaninsu ba..kasan yaran nan su yi ta shirme basa neman shawara ashe sanda zasu taho Bikin su Abida yace ta Zauna achan ta matsa sai tazo Shine fa yace bazai koma da ita ba yanzu..! Mallam ya yi shuru yana kallonta kafin yace"Haka akayi .? Anty amarya tace"Eh mallam ita kuma Sakinar ta damu tana ta kirana tan kukan wai na rokesa ya koma da ita bazata iya zama ita kadai ba nidai Fada nayi mata nace Laifinta ne da nace bazan saka Baki bane tace nayi maka mgana don Allah ka Rokesa ya tafi da ita..! Har ta gama mgama yana Nazarinta Kafin ya sauke ajiyar rai yace"Naji batunki marliya kinsan Allah ni bansan ma duka anyi haka ba..Umaru da na ne ammh bana hirar iyalansa Dashi..Tsakani na dashi Hirar duniya sai kuma ta aiki in ta kama sai kuma ta Rayuwa haka ammh ni bana shiga Sha"anin ya"yana da matansu kinsani marliya..Umaru mijin Sakina ne sannan bansn meya faru Tsakaninsu ba domin ina Mahaifinsa ya gama tsara abunsa sai na kirasa nace masa ya Sauya..kina ganin hakan ba rashin girma bane..? sannan kuma shiga Hurumin da ba nawa bane tunda dai bai Tuntubeni da mganar ba..! Ya karishe fada yana kallonta itama shi take kallo jikinta yayi sanyi domin taga ba Nasara,girgiza kai tayi cikin sanyin jiki kafin mallam ya cigaba da fadin"To kin gani bai kamata nayi mai mgana ba..Sannan ai ba ita kadai zata Zauna ba ga mamana nan itama nan zai barta sai ya sake dawo wa ki bata Hakuri ta zauna inda mijinta ya ijiyeta..! Anty Amarya sai ta kasa mgana Shuru kawai tayi,Ganin kamar yanayinta ya Sauya ne yasa Mallam yace"Kiyi hakuri marliya..kema kada ki saka baki wannan ba Hurumin mu bane..! Da Toh ta amsa mai tana kokarin nuna komai ba komai bane kada mallam ya Fahimci yanayinta.. Washegari ta kira sakina ta lallasheta akan tayi Hakuri da mganar Binsa ta bari in ya koma mallam ya tabbatar mata zai dawo domin ya koma da ita Tunda Sarood bata da wani amfani kamar Hoto take. Sakina ta yarda ta Hakura ammh tace yana tafiya itama Dutse zata je tayi Sati Daya ta huce daga Bakincikin yadda zata fara zama da Amina agida Daya Matsayin Mijin su daya. ********** Ana gobe tafiyar Danmallam Da Daddare Sakina ta Fadamai Tana so gobe in ya tafi zata je Dutse ta gaishesu,bai ce mata komai ba alokacin sai da safe domin jirginsu 12pm zai tashi zuwa Jidda,lokacin yayi wanka ya shirya Cikin Shigar jallabiya Fara da bakin wando sai Hula yana Fesa jikinsa da Turaransa na Arab Sakina ta shigo Dakin Cikin Shigarta na kwalliya kamar ko yaushe sai da ta isa kusa dashi ta karbi Turaran Hannunsa ta karishe Fesamai bayan ta gama ta maida Turaran kan Madubun Dake Dakin ta Rumgumesa tana Fadin"Zan yi kewarka Habibi..! Shima riketa yayi na wani Lokaci kafin ya dago kanta ganin Hawaye ya Cika idanuwanta yasa ya Girgizamata kai yana fadin"Kada kiyi kuka..Ki batamin kwalliya..! Jin haka yasa ta kara Narkewa tana mai yar shagwaban zai tafi ya barta nan ya lalace wajen ya lallashinta sai da karar wayarsa ta katsesu sannan ya Saketa Wayarsa Dake kan gado ya Dauka ganin Aliyu ne yasa ya Daga yana Fadin"Badai har ka iso ba..? Dagachan bangaran Aliyu yace"To akace maka ni irinka ne..Gani Falon mallam muna jiranka..! Umar yace"Ina Jafar ya iso..? Aliyu yace"To mu da bamu da sabuwar Amarya Swt sixteen ai duk mun Hallara..!tsaki yaja kawai ya Katse kiran yana girgiza kai yana Tunanin Aliyu bai da girma sai na Jikinsa. Sakina ta kuramai ido tana kallonsa Hannunta ya rike yana fadin"Muje su Aliyu nachan gidan mallam suna jira na..! Marairaicewa tayi kafin tace"To haka zaka tafi baka karya ba..? Yana kokaron Daukan jakan kayansa yace"Kinsan bana iya sakama cikina wani abu in zan hau jirgi..Kada ki Damu zan ci wani abu ko achan ne..! Saman kafadansa ta Dora kanta tana fadin"Zaka tafi bakace min komai ba..! Kai Tsaye yace"Name fa..? Ta karkace kai tace"Na tafiyana Dutse mana..su Daada nake son naje na gaishesu tun fa Bikin Sadiya ban koma ba..! Kai Tsaye yace"Kije ammh ba yau zaki Tafi ba ki bari gobe..! Da sauri tace"Saboda mene Habibi..? Har na kirasu nace fa ina tafe yau..!. Hancinta yaja kafin yace"Saboda Haka nace..Kuma ba Sati zaki yi ba..kwana Uku na baki..! Baki ta Bude tana kallonsa sai ya Rufe mata bakin da nasa ya bata sumba mai tsawo kafin ya saketa Jakarsa ta amsa ya Riko hannunta suka fito Har Falon,har ga Allah ya manta da Amina sai da ya kalli Dakin sannan ya Tuna da ita Hannun Sakina ya saki kafin yace"Jirani ina zuwa..! Tana hararansa ya shige dakin Sarood wanda ya zama na Amina yanzu..! Barcinta take sha sosai domin barcin da batayi bane kwana Biyu take ramasu ga Filet da mug nan har da Sauran Buredi a kasa dataci ta Rage sannan Dakin duk ya Hargitse ga Hijabai nan da kaya saman gadon bata Kwashe ba,Amina sai jiya ta Sake wanka shima kayan jikinta ne suka isheta tayi wanka ta sauya tayi Daidai kan gado tana barci Daga ita sai Zani Tayi Daurin gaba ko Riga bata saka ba.! Kamar zai tasheta domin zarni da wari ya ishesa yasa kawai yayi Tsaki ya fice Daga Dakin yana Fitowa yaci karo da Sakina inda ya barta tana kallonsa shima ita yake kallo kafin yace"Sakina..! Ta amsa da Na"am cikin Kaushinsa yace"Zan tafi kada ki shiga shirgin yarinyar nan ki kama girmanki..in kin yi Girki ki bata..Sannan gobe in zaki Tafi ki Fadamata domin ta Rika fitowa tana sama ma kanta wani abu..Ban son Rigima Allah in naji wani abu ke zan bata ma rai saboda ke na bar ma Amanar gidana..! Sakina ta Tura baki kafin tace"Ni fa bazan dinga mata girki tana kwance ba..Itama ai matarkace sai ta fito ta girka nama na kaima kayi Adalci..! Kai tsaye yace"Wannan me ta iya banda kazanta..? Sakina ta Hura hanci kafin tace"Sai tayi kazantarta taci kayanta Daman bani zata mawa ba..! Kai ya kada kafin yace"Allah ya kyauta sannan Hajiya tace zata koma makaranta nan Idi zai rika zuwa Daukanta..! Aran sakina tace to ni ina Ruwana batayi mgana ba shima bai ce komai ba ganin zai tafin yasa ta rikesa ta sakamai kuka ganin haka yace ta sako mayafi su tafi gidan mallam tare jiki na rawa ta je ta Dauko hijabi suka Fice shi ya tuka Motar da kansa bayan ya sallami megadi itama Sakinar ya bata katin bankinsa guda daya suna Mota yace mata"Na amfanin yau da kullum in ya taso ke da yarinyar nan kuyi amfani dashi..kayan abinci kuma in ya yi kasa Jafar ko nasir zasu kawo..! Karba tayi kafin tace'Ni dai ka daina Hadani da kazamar matarka meyasa baka bata nata ba..? Kai Tsaye yace"Saboda kice babba sannan kuma kin Fita Hankali..kuma Amanar komai da komai a Hannunki na bari..! Bata kara mgana ba har suka iso ita Cikin gida ta shige shi kuma Falon mallam suka gaisa Aliyu nata kallonsa yana Dariya cikin gida ya shiga yayi ma Duka matan sallama Shashen Hajiya ne na karshe yana Duke gabanta tana fadin"Allah ya sauke ku lafiya..Allah ya Tsare..! Yana ta ansa mata da Ameen Yana shirin tashi tace"Ina wayar da nace ka siya ma Amina ka ko siya ne..? Sai alokacin ya tuna kansa na kasa yace"Na manta Hajiya..ammh yanzu zan barma Jafar kudin zai siya mata..tunda su zasu rakani Airport shi da Aliyu..! Hajiya tace"Ai ya shigo mun gaisa..Sannan ka shiga gidan Sa"idu kuyi sallama da shi da balaraba..! Da toh ya amsa mata ya tashi ya fice ta Bisa da Fatan nasara. Bai koma falom mallam ba sai ya wuce gidan Aba ya iskesa ma yana shirin Fitowa haka ya tarbesa ko zama bai yi ba sukayo sallama ya kira Mamanmu suka yi sallama Fadi take Allah ya Tsareka Umar..Allah ya bada sa"a ina Diyata Amina..? Ina fatan tana lafiya..! Kansa na kasa yace mata tana lafiya har Haraba ta rakosa tana ta addu"a sai da suka fice da Aba ta saki shewa kafin tace afili"Komai na tafiya daidai..yadda muka Tsara..! Wajen goma da wani abu suka mika Hanya Jafar da Aliyu zasu rakasa Filin Jirgi,Sakina kuma har suka tafi bai kara ganinta ba. Ita kuwa tana Shashen Anty Amarya sai da ta tabbatar da sun tafi sannan ta fito ta mata Anty Amarya sallama Domin ta fadamata ne ya barta tatafi Dutse,bata fada mata yace sai gobe zata tafi ba sanin bazata barta tatafi ba in ta fadamata gaskiya. Gida ta koma ko ta kan Amina bata bi ba,Ta hada kayanta akwati Cike da kaya ta kulle Ko"ina harda Kitchen sai da ta kulle ta saka key din a jaka Dakin da Amina ke ciki ne kadai ta bari sai falo tayi Ficewarta Ta sanar ma da megadi zatayi tafiya ammh akwai wata yarinyar agidan ya bita da Allah ya kiyaye Su Danmallam ko Kano basu kai ba Sakina ta kama Hanyar Dutse ko ajikinta. *Janafty**TFZB2005* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Sun isa Filin jirgin mallam Aminu dake kano shabiyu saura na rana sai dai sun iske jirgin su Danmallam da zai tashi zuwa Jidda da misalin 12pm na rana an fasa ya koma sai 3pm na rana sakamakon Weather babu kyau an dan samu Tsaiko kadan jin haka yasa Umar yace Aliyu da Jafar su koma kawai basai sun jira ba Tunda an sauya Lokaci. Basu wani jima ba suka mai sallama suka tafi daman da motar Aliyun suka zo kafin su tafi sai da Umar ya bama Jafar akan ya siyama Amina waya domin in ya sake yatafi bai siya ba Kashin shi ya bushe wajen Hajiya shi kanshi Jafar yayi mamakin jin yace har da layi zai siya mata ya mata Rigister. Sun koma gida da Labarin Tsaikon da aka samu su maallam suka bisa da Fatan Alheri Aliyu bai tsaya ba Daganan yayi sallama dasu mallam ya Dauki hanyar Dutse.. Amina bata san wainar da ake toyawa ba,sai da ta gaji da barci sannan ta tatashi shima kiran sallar azahar ya tasheta da ake ta kwalawa a wani masallaci dake kusa dasu sannan ta iya tashi gabbanta duk sun gaji Tsami ma kafafunta ke mata sosai,Dakyar ta iya mikewa taja jiki ta shiga Tiolet ta Sha ruwa a famfo sannan tayi alwala tazo tayi sallah sai dai kuma yunwa take ji,Ammh duk da haka bata fita ba ta koma ta kara nadewa a Tunaninta Sakina zata kawo mata kamar yadda ta saba sai har wajen uku saura na Rana bataji motsin kowa ba cikinta har ya fara Curewa waje daya yana mata Rugugi. Tunawa da tayi sakina ba Imani gareta ba Daga ita har megidan sai su barta ta mutu basu da asara shiyasa ta mike ta taimaki kanta kayan datayi amfani dasu da safe ta Dauka ta fita zuwa Falo tana leken sakina sai dai bata ganta ba ko motsi ma babu agidan. Bata gama mamaki ba sai da taga Kitchen a rufe sannan Hankalinta ya tashi,Sai alokacin ta Lura duka Dakunan suna kulle ne mamaki ya kara kamata to ina yan gidan suka shiga ne..? Tabe baki tayi daga baya aranta tace ina Ruwanta dasu sun dade basu tafi ba suma shekara waya damu..! Nan saman Dining ta watsar da kofin da Filet din,kamar zata koma daki sai wata zuciyar tace mata bafa kowa agidan ki sha iska tuna haka yasa ta koma falo ta samu kujera ta zauna tana kara bin Falon da kallo tana nazarinsa baki ta tabe ko ajikinta. Sauran buredin data rage da Safe ya Taimaketa shi ta Samuka ya cikamata Ciki,Har barci ya Dauketa nan saman kujera bata sani ba sai bayan La"sar ta tashi tayi mamakin irin barcin Datake yi kwana biyun nan,Tashi tayi ta koma Daki tayi sallah sannan ta kara fitowa Ciki dai ba abinci shiyasa duk ta kasa sukuni Allah ya taimaketa a saman Dinning Sakina ta manta da kayan Tea su Amina ta samu ta sha da Ruwan Sanyi tunda ba na zafi ta kuma Samu katon Buredi a wajen ta hada dashi taci ta koshi tayi Dam ta koma Daki aranta tana fadin kafin su dawo nayi barci Domin ni bana Tare da yunwa..! Sai dai kuma har akayi mangariba bata ji Duriyar kowa ba sai Hankalin Amina ya fara tashi Har sake fitowa tayi ta Duba ba wanda ya Dawo ta koma ta zauna tayi Tagumi sai kuka tana Tunanin yadda Sakina da Mijinta suka zama marasa imani suka tafi suka barta ita kadai agida wannan Rashin Imani ne Allah ya isanta Bata yafe ba in wani abu ya sameta su da Allah..! Bata kara Tsorata ba sai Dare yayi Amina tsoro ya cikata gashi nepa sun Dauke wuta Duhu ya cika gidan ita kuma batasan inda ake kunna Solar ba batama san da ita agidan ba,Ga shi Daga waje Hadari ya Hadu Farkon Damuna,sai ta kasa zama itace Dakin ta ko falo ta kasa zama sai ta zauna motsi kadan dataji sai ta mike tana waige waige ta fara Firgita sai kuka Amina Bilhakki da gaskiya take kuka saboda Tana tsoron saukan ruwa barin ma in ana iska ko tsawa,tana wannan kukan aka fara iska mai karfi winduna na kadawa da Labulai sai Amina taji kamar ta yi iska ta ganta agida Bayan mamanmu ko Hamida saboda tsoro Daki ta koma ta Dunkule kan gado tana Kuka Lokaci daya da makyarkyata Idanuwanta a kulle gam bata so ma ta bude ga ko"ina duk Duhu Hankalinta gabadaya ya tashi banda Salati da wayyo wayyo babu abunda take yi. Adaidai Lokacin aka tsuke da ruwa mai karfi kamar da bakin kwarya,Ga iska ga Rugugin Tsawa Amina ta rasa ina zata sa kanta taji dadi gabadaya ta Tsorace,ta kamkame jikinta waje daya,ta tusa kanta cikin Filo tana rufe kunnuwanta ga iska sai kada winduna yake yi da Labulai kamar zasu balle Fitsari kamar Amina zatayi a wando Saboda Tsoro hawaye kuwa ya wanke mata fuska da majina bata sanin ma sanda yake fitowa wani na Fitowa wani na Kara fitowa. Adaidai Lokacin Adaidaitan da Danmallam ya hau daga Tasha zuwa gidansa koda ya fito rike da Jakarsa sharkaf yake da ruwa,har diga yake yi sai rawan sanyi yake kudi ya bama mai adaidaitan baisan ko nawa bane Saboda yayi mai Hallaci tunda suka sauka atashar Gumel aka fara Ruwa shi yana da Allagis din Ruwa ya tabasa komai kankantarsa sai yayi mura da Zazzabi in ma bai kwantar dashi ba yayi ta taran masu adaidaita suna cewa baza su shigo Cikin gari ba Dakyar wannan ya Daukosa ganin yana rawan sanyi Ganin irin kudin Daya basa ne yasa ya Leko yana fadin"Nagode yallabai Allah ya kara Budi..! Da kai ya amsamai lokaci daya ya wuce zuwa Bakin get din gidansa ya kwankwansa har sau Biyu shuru Wayarsa ya ciro a aljihun wandonsa yaga ta Mutu daman ba chaji tun suna Filin jirgi Take buga Battery low,sannan kuma ga ruwa ma ya tabata domin sosai ta jike,Kara buga Get din yayi Allah yasa Buzun megadin yaji ya fito da sauri ya leko lokaci Daya yana haskasa da Fitilansa mai Haske ganin Danmallam da kansa yasa Cikin mamaki yake kallonsa bai Damu ba yace ya Budemai get da Sauri ya Budemai karamar kofa ya shiga gidan megadin ya bisa yana tambayansa bai samu tafiya bane..? Eh kawai yace mai lokaci Daya ya Nufi Kofar da zata sada sa da Falon gidansa so yake ya samu yayi wanka da Ruwan zafi ya kwanta,jikinsa kamar ba Nasa ba. Sai da yana shiga Duhu ba Haske abun ya bashi mamaki yana Tunanin ko Sakina ta kwanta ne kafin a Dauke Wuta ba"a kunna Solar ba,Isa Cikin Falon yayi ya isa inda makunnin Solar yake ya kunna Haske ya gauraye duka gidan falon yake bi da kallo ganin sa Tsab ba kuma Hayaniyar kowa Bai Damu ba ya kama Hanyar Dakinsa sai dai kuma me..?Sai yaji sa a rufe Mamaki ya kara kamasa sai ya Nufi Dakin Sakina yana kiran sunanta nan ma yaji kofa a Rufe bai kawo bata nan ba ya fara mata knooking yana Kiran sunanta ammh Shuru..! Amina na dunkule akan gado tana rawan jiki taga lokaci Daya Haske ya kawo leko da kanta tayi sai taji dan sanyi a zatonta nepa sun kawo wuta ne,Sai rabin hankalinta ya kwanta ganin haske sai dai kuma me sai taji kamar tana jin motsi saurarawa tayi sai kuma bata karaji ba sai da ruwan yadan Dauke sama sama taji ana kiran sunan Sakina sai ta kara Tsoracewa kara Dunkulewa tayi saman gado jikinta na rawa kamar a mafarki taji an shigo Dakin data ke sai Amina ta kara shigar da kanta Cikin Filon ba inda jikinta ba ya rawa addu"a kadai take yi duk abunda yazo Bakinta sai ta fada Hawaye kuwa kamar an Bude famfo. Kamar a mafarki taji muryansa yana Fadin"Ke...ina Sakina..? Haka ya fada yana Tsaye daga kofar Dakin yana binta da kallo Cak ta Tsaya da rawan jikin sai da ta Leko ta filon ta hangesa Tsaye sannan ta sauke Numfashi Cikin Dan salama ta Dauke Filon Fuskarta ta mike zaune tana kara Dunkule Hijabin jikinta. Kallonta yake yi ganin hawaye Chaba Chaba a fuskarta yasa yace"Me yasa same ki kike kuka..? Ina sakina taje ne..? Kanta na kasa tace"Ni bansani ba..Ni kadai ce agidan..kuma tsoro nake ji ina ta jin motsi..! Sai ta kara fashemai da kuka bai Damu da kukanta ba Fadi yake yi"Sakina bata nan..? Cikin alamun Tambaya Amina ta Dagamai kai kafin tace"tun dazu ba kowa agidan sai ni kadai agida..Tsoro nake ji don Allah ka maidani gida..! Bai ma Saurareta ba gabadaya ransa ne ya baci kenan Sakina bataji mganarsa ba sai da tatafin yau kyafci yayi kawai yana Sakin Hucin Zafin zuciya,Allah ya kaddara bazasu tashi ba Koda ukun tayi matsalan bata kau ba nan aka sanar dasu sai jibi zasu tashi da Daddare yaso ya kama Hotel anan kano har zuwa jibin sai kuma yaji ya kasa gwara ya dawo gida bayason ya Wahalar da su Jafar yasa bai kira kowa ba ya tafi tasha ya hau motar Gumel sun fara tafiya Motar ta samu matsala wajen awa biyu kafin agama gyaran koda suka shigo gumel an yi issha"i sannan sun zo ana ruwa kamar da bakin kwarya,Shi ba ya iya Fakewa ako"ina shiyasa ruwan ya Tabasa sallar kadai ya tsaya yayi a wani gidan mai,kamar zai wuce gidan Mallam sai kuma ya fasa saboda bayama son sun san Tafiyarsa bata Yuyuba. Sai gashi ya dawo ya iske wannan Rainin da Sakina tayimai gashi bai da key din kowani Daki acikin gidan Suna wajen Hajiya,Sannan akwai wani hannun Jafar yanzu kuma Dare yayi bazai yuyu ya kira yace a kawomai ba sai ya Tada musu hankali a yanayin Dayake ciki ko Ta kan Amina bai bi ba dake sharan hawaye Jakar hanmunsa ya Sabule nan saman Cafet ya taka ya nufi Cikin Tiolet din Dakin ya Rufe. Ransa sai da ya kara baci ganin yadda kazantar Amina ya maidashi ga kayanta nan data cire saman kwandon wanki bazata iya Budewa ta saka ba sannan ga pant din ta nan da ta wanke basu fita ba ta shanya ajikin Famfo ransa ya kara baci bayin Daga gani an Dade ba"a wankesa ba Bashi da wani Zabi sai nan Tiolet din Shiyasa bai fito ba sai da yayi wanka ammh kuma sai da ya wanke Bayin tas sannan ya iya yin wanka da ruwa mai Zafi ya gasa jikinsa yana jin yunwa ga Mura ta kamasa ga kuma Sanyi Dayake ji Towel ya Dauro a kugunsa ya fito kayansa kuma Cikin kwandon wankin ya Bude ya saka yana Fitowa suka hada ido da Amina yadda ta Zabura sai da ta bashi tsoro Ido ta Runtse ta sheka da gudu ta Fice Daga Dakin tana fadin ta shiga uku da Harara ya Bita kafin yaja Tsaki Afili ya Furta kazama kawai. Lotion din Sarood dake saman madubi ya shafa saboda komai nasa na Dakinsa,Jakarsa ya Bude ya sanya Jallabiya baka mai kauri kauri Saboda yana jin sanyi kan gadon yabi da kallo duk kaya ransa ya kara baci kamar zai Dauketa mata sai kuma ya fasa ya fita Falo ya ganta zaune saman cafet ta Dunkule waje daya asaman kanta taji mganarsa yana fadin"Wanene zai Dauke miki wadanchan kayan da kika zubema mutane akan gado..? Agidanku haka kika ga anayi..?Ina amfanin Wardrope din Dake Dakin..? Amina ta kasa Dagowa itafa tunda ta gansa ba riga jikinta ke rawa ashe haka yake da girma itafa saboda Tsoro ko kallonsa ma batayi ba azatonta bai da rigan ne Har lokacin. Shiyasa ta kasa Dagowa tsawa ya Daka mata yana fadin"Ina mgana kina banza dani ni sa"anki ne..?Zaki zo ki kwashe kazantarki ko sai nazo na Tattakaki..! Jin haka yasa ta mike jikinta na rawa tana fadin"Ka..yi hakuri..! Hanyar Dakin ya nuna mata cikin fushi ta wuce sumi sumi tana tsoron yakai mata hannu haka ya tasata gaba sai da ta kwashe kayan saman gado ta Tura cikin wardrope a yamutse ya Dakamata Tsawa yace ta kwaso ta Ninke su hakanan ta kwaso ta ninke ta saka aciki tana sharan kwallah bayan ta gama ya nuna mata kofar Tiolet yana fadin"Shiga ki Tararra kazantar da kika shanya ki Samu waje ki boyesu da safe ki fita dasu bola..! Amina ta kallesa kafin tayi mgana ya Rigata da fadin"zaki wuce ko kuwa..? Da gudu ta shiga ta Tatarra kayan har da Pants din ta Tusa cikin kwandon Tana kuka fadi take"Mamanmu..Hajiya..mallam..! Yana jinta har dasu Hamida ta Kira Dariya ma ta bashi ya tabbatar ma kansa yarinyar nan bata da kunya iskancinta kadan ne. Haka ta fito tana Labe labe tana sharan kwallah kallo Daya yayi mata ya fice daga falon yunwa yake ji sosai kuma ga shi ba wani abu zaune yake saman kujera yayi Tagumi ya rasa mafita har na tsawon wani Lokacin ganin ba mafita yasa ya gyara kwanciyarsa saman kujera mai zaman mutum uku sai dai ina Sanyi da Zazzabi suka Damesa ga shi har Lokacin ana yayyafa kamar ma ruwan zai Dawo Takurewa yayi waje Daya saboda bargon Dakin Amina ko Sanyi  zai kashesa bazai iya saka Jikinsa aciki ba ya tabbata ya fara Warin Datti. Har barci ya fara Dibansa yaji ruwa ya Dawo da iske tashi yayi ya Zuge Duka wimdunan falon sannan ya koma ya kwanta yana Faman kokuwa da yunwar Dake damunsa Ko achan Filin Jirgi Tea kadai yasan sha shima bada yawa ba tun kuma shine acikinsa. Yana bukatar yasha ruwan zafi ko zai gasamasa ya"yan Hanjinsa sannan kuma da Zafin da jikinsa ya Dauka kafin wani Lokacin Hancinsa ya toshe Saboda Mura. Yana kwancen yaji wata Tsawa da akayi shi kanshi sai da ya Bude ido Lokaci daya da walkiya mai Haske da Sauri yace"Bismillah...! Kamar ihunta yaji kafin ya mike yaji ta, ta fadomai ajikin jikinsa tana rawan jiki yana Daga kwancen yajita kan jikinsa yadda ta kamkamesa kamar zata balla sa yana ma yi mamakin karfin hannun yarinyar. Kokarin riketa yake ammh taki basa Dama kanta take tusawa saman kirjinsa da Karfi Tana kuka lokaci Daya tana fadin"Na shiga uku..Ka boyeni Tsawa..Tsawa...! Haka take fadi jikinta na rawa sai kuma ta fara wani abu irin na kakkafewa Saboda an karayin wata Tsawar ganin haka yasa shima sai ya Riketa ya fara Tofamata addu"a ganin yanayinta ya fara tunanin wani abu. Addu"an dayake tofamata yasa sai ta bar kafewan ta koma ta kamkamesa ta fashe da wani kuka mai cin rai har Muryanta na Shidewa fadi take"Wayyo mamanmu...! Haka take fada Cikin kuka duk yadda yaso ya cireta acikin jikinsa ya kasa kamkamesa tayi kamar zasu zama abu Daya tana kuka Danmallan yaji wani bakon al"amarin daya Faru dashi wanda bai taba Faruwa dashi ba ko da akan Sakina ne. Wani irin Dumi yaji jikinsa ya kara Dauka wani abu ne yake yawao ajikin jikinsa Tunda ga yatsun kafarsa har saman kansa nan da nan yaji sa cikin wani yanayin yanayin da bai Taba Riskan kansa ba. Hannuwansa yasa duka Biyu ya Dafe bayan Amina yana Lallashinta lokaci Daya yana Tofa mata addu"a sai aka samu tayi sanyi da kukan data ke yi,Neman yake yi ya rabata da jikinsa ko zai daina jin yanayin dayake ji,ammh ina ta rikesa gam taki Sakinsa ga sanyi ga Iskar ruwa tunda kamar ruwan ya Dawo ne da Bakin kwarya yasa ya mike rike da ita har Cikin Bedroom din da Amina ta baro,Saman gadon ya so ya kwantar da ita ammh Amina taki yarda yana so yaga Fuskarta taki bari sai boye kanta take yi a jikin jikinsa Danmallan ya kalleta sosai yana kara nazarinta meke damun yarinyar nan..?Addu"an ya cigaba da tofa mata sai jikinta yadan saki kadan ammh kuma taki sakinsa gam take rike dashi Cikin Sanyin murya yace"Sakeni mana..An daina Tswan baki ji bane..! Amina taki sakinsa fadi kawai take"Don Allah ka boyeni tsoro nake ji..! Dole ya koma ya zauna saman gadon yana Rike da ita addu"a bata bar bakinsa ba har sai da yaga ta Dawo Cikin natsuwarta sannan ya kyaleta bayan ya kalleta yace"To sakeni..! Da sauri ta sakesa ta koma gefe ta lafe jikin gadon tana raba ido Sauka yayi Daga kan gadon sai gata itama ta Dirko ta rirrikesa juyowa yayi yana kallonta kafin yayi mgama tayi saurin Fadin"Don Allah kada ka fita ina jin Tsoro..! Cikin idanuwanta yake kallo yaga gaskiyanta itakuma kanta ta maida kasa sai hawaye,Cikin Taushinsa yace" ba fita zan yi ba..Nan kasan Cafet zan koma na kwanta ke ki kwanta saman gadon..! Cikin Tsoro ta ce"To..to...to..Don Allah ka da ka fita..Wlh tsoro nake ji..! Ta karishe fada da kuka karo na Farko da ta bata bashi Tsausayi sai ya Tausasa Murya yana fadin"bazan fita ba..ki koma ki kwanta in kin ji tsoro sai kiyi addu"a..! Kai ta gyada mai cikin Sauri yana Tsaye rike da hannunta ya maidata kan gadon ta kwanta tana Raba ido sai Hawaye sharr ganin haka yasa yace"In baki bar kuka ba zan yi tafiyata..! Jin haka yasa da Sauri tace"Toto...To...Don Allah kada ka fita..! Kai ya gyada mata kafin ya Dauki Filo ya jefar a kasa zai kwanta tana binsa da kallo ganin zai kwanta a kasa yasa ta mikamai Bargon Dake kan gadon tana Fadin"ka shimfida bargo ya Danmallam..! Juyowa yayi yana kallonta kafin yace"Kefa..? Kai Tsaye tace"Bana lulluba dashi..! Kamar bazai karba ba sai kuma ya sa ka hannu ya karba Domin yana jin Sanyi,Kwanta wa yayi sannan ya Rufe kafarsa da Bargo sai da ya tabbatar da baya wari lafiya kalau yake shi. Dukkansu idonsu biyu sun kasa barci Yana jin motsinta sai ta tashi ta lekasa sai tagansa sai ta koma ta kwanta Shima bai iya barcin ba yana mamakin Lamarin Amina ne ya fara Zargin yarinyar nan na da wata matsalar da bakowa ya Santa ba. Har barci ya fara Daukansa Yaji ihunta Da Sauri ya bude ido ya mike Lokaci Daya sai gata ta Dirko Daga kan gado ta Fadomai,Tana wani rawan jiki Cikin tashin hankali ya riketa yana faman kiran sunanta bata ji ba Fadi take ye ya Boyeta Tsoro take ji Dakyar da addu"a ta Dawo Daidai sai kuka Rumgumesa tayi gam tana Fadin"Ya Danmallam kayi ma girman Allah ka hawo gadonan mu kwanta..Ko ka maidani gida wlh agida in na tsorata abayan mamanmu ko na Hamida nake iya barci..! Tsausayinta ya kamasa bai iya mata gaddama ba tana rike dashi suka karisa kan gadon sannan yace mata"To sakeni ki hau gadon..! Ba musu ta sake sa ta hau gadon shima ya Hayo yana hawa ta kara Rikesa baki ya saki kawai yana kallonta kafin yace"Kina addu"a kuwa in kikaji irin wannan tsoron..? Kai ta gyada sai hawaye kafin yace"To me kike karantawa..? Amina sai ta Rushemai da kuka baki ya Saki kawai yana kallonta Ya fara Zargin wani abu na Damun yarinyar nan,kansa ciwo yake yi yasa ya samu yalallasheta ta bar kukan yana dora kansa saman Filo tabisa ta Danne kamar zata maida shi Ciki Danmallan ya Dafe kansa kawai yana Salati ita bata san in tana tabasa yanayinsa na Sauyawa bane. Ta gefensa ya zura hannu ya kashe Hasken Solar Dakin ganin Duhu yasa Amina ta saka Ihu Saurin Daka mata Tsawa yayi yana fadin"In kika sake min Ihu zan tashi na yi tafiyata Wlh..! Jin haka yasa tayi Tsit ta koma kan kirjinsa tana Sauke Numfashi Wani al"amari ne da Allah kadai ya bar ma kansa sani yanayinsa yake ji yana Hauhawa Tare da tafiyar Numfashin Amina Dake kan kirjinsa abunda bai taba Tunanin zai Faru dashi ba in yayi Duba da wasu sabbin Abubuwan da suka faru dashi bayan auran Sarood. Lamarin ya faru ne batare daya shirya ba ko nace sun shiryama hakan ba Dukkansu,Umar bazai iya Dora komai akan lamarin dayake shirin Faruwa ba,Amina bata Farga ba Domin tana cikin Tsoro sosai,shiyasa sai da abun yayi nisa ta Farga tayi kokarin kwace kanta sai dai ina Bakin alkalami ya Riga ya bushe..! Acikin wannan Daran ana cikin Tsuga wannan ruwan na Farkon Damina Wani al"amari ya Faru Tsakanin Amina da Danmallam,Umar ya karanto addu'ar da Annabi ya koyar damu acikin Ransa yana kuka,kukan kokowa da yanayinsa ya Ratsa Amina Ratswar da zai zama silar abubuwa Dadama wanda bawa bai tsammani ba.. Wasu basu zata ba..Tsammanin Abunda basu yi Tsammani bane zai Farun.. Alkwarin Allah ya sake cika. Zanen kaddaransu ya hadu. Allah ya amintar da Ruhinsu ya Gauraye jininsu waje daya batare da masu kokarin hana Faruwar hakan sun Farga ba..! *Janafty**TFZB2006* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Shudewar tsawon mintina Talatin kafin Umar ya mirgina gefen Amina kansa ya nausa kan filon da suke kwance akai dashin yaji alamun hawaye ammh baisan Lokacin da hawaye suka fito daga cikin idanuwansa ba abu daya ke masa yawo a saman kansa na lamarin daya faru tsakaninsa da Amina abunda bai Taba zaton zai iya faruwa ba ko da zai Faru bai taba tunanin shi nan kusa ba.. Yana jin kukan Amina cikin sarkewar murya Tsausayinta ya kamasa sosai sai alokacin abubuwan da suka faru suka Dinga dawomai Daki ashe ashe komai da ya faru saboda wannan ranar ce..? Ashe auran gaggawan da Mallm yayi masa da Amina saboda wannan kaddaran ne..?Ashe Matsawan da Hajiya tayi kan tarewar Amina saboda wannan Kaddaran ne..?Ashe Fasa tafiyarsa duk yau duka Tsarin na Ubangiji ne da faruwar abunda ya faru Tsakaninsa da Amina Duka Tsarin na Ubangiji ne Lalle sarki ne Tare da Godiya ga Allah shugaban Hallitun Duka Duniya. Abunda ya faru bazai iya kwantanta ya akayi ya faru ba sai dai abu Daya ya sani komai daya faru kudurin Allah ne Kaddaransa ne wanda bawa bai isa ya gujemata ba. Bai taba Zaton agaban Amina zai iya Zama namiji ba tun la"akari da abunda ya faru dashi bayan auransa da Sarood in dai yana tare da ita shi ba Namiji bane har yau har gobe bai Taba kasancewa da ita ba bai taba Zargin kowa ba koda Sakina ce kuwa Tunda la"akari da ita a kanta Lafiyarsa kalau sai dai ya barma Allah lamarinsa yana ta addu"a daga baya Daya ga kamar yana cutar da Sarood din yayi mata mgana kan ko zai sauwake mata ne saboda kada ya cutar da ita sai dai taki yarda ta ce zata zauna dashi Har Allah ya basa lafiya,bata taba sanin a wajen sakina Lafiyarsa kalau ba sai da Sakina tayi barin nan suna madina ta fara Zargin wani abu na Faruwa wanda bata sani ba Da tayimai mgana sai ya fadaa mata gaskiyan cewa akanta ne bai iya Zama Namaji ammh a wajen Sakina Lafiyarsa kalau bata kara mai mganar ba tundaga ranar,sai dai ta Dauke mai ba kamar farko datake kokarin nunamai bata Damu ba. Ko tsirara zai ganta bazai taba jin Sha"awarta ba shifa in ba Sakina ba bayajin sha"awar kasancewata da wata mace ko Amina wlh bai ji haka ba Abun yazo ne lokaci daya ne jin Sha"awar da Faruwar abunda ya Faru Duka Lokaci kalilan ne jinsa yayi mai lafiya Fiye da yana Tare da Sakina ma. Amina ta sha wuya sosai sai dai yaga Dauriyanta matuka sosai domin yayi Tunanin zata yi mai ihu fiye da Tunaninsa sai kuma batayi ba kuka dai ta shashi har ta godema Allah Kiran sunan mamanmu da Hamida dasu Hanne kamar hadda har dasu mallam da Hajiya da su ya Jafar dukkansu sun sha kira Harda yaya Dake Kabarinta cikin salama sai da Amina ta kira sunanta. Acikin Duhun Dakin ya Dago kansa yana kallonta ta nade cikin  Hijabinta daya yaye mata cikin Fitan Hayyaci sai kuka take muryanta har ya Dishe Saboda tsoro ta koma chan gefe ta takurai kamar wacce za"a ce kyas ta gudu zazzabi ne ke neman kwantar dashi ammh hakanan ya mike ya Rarrafa ya sauka Daga kan gadon ya lalubi makunnin Wutar solar ya kunna sai yaga nepa sun maido wuta sannan Ruwan ya Dauke sai garin yayi wani sanyi lokaci Daya da wani yanayi mai Dadi. Jallabiyansa ya Laluba ya saka yana mai jin kunyar kansa na abunda ya aikata ma karamar yarinya har ya shige Tiolet bai iya kara kallon Amina ba itama kunya da wani yanayin datake fama dashi tun Faruwar lamarin ta kasa ma ta yi wani Tunani sai kuka. Tana jin karar saukan ruwa a bandaki ta kara dunkule jikinta waje daya sai kuka abunada ya faru ya shammaceta matuka Domim bata taba zatonsa nan kusa ba ayadda abubuwa suka faru da ita Daki Daki ashe ashe bata gama Karban nata kaddaran ba..?wani na tafe bata sani ba..? Bata gama Daukan abunda ya Sameta ba ga wani babban lamarin ya sake kanayayyeta,wai yau itace kwamce gado Daya da ya danmallam har..Har yayi yayi mata..! Sai ta kasa karisa lamarin acikin ranta sai ta saka kuka kawai tanasan abunda ya faru da ita an gayamusu a islamiya sannan kuma tasan irin wannan abun a karance karancen datakeyi ammu batataba auna shi akanta ba har Abada..! Ko da ta hasoshi akanta bata Daukesa nan kusa ba ta Daukesa wani Lokaci mai Tsawo kafin ta riski hakan sai dai ina Bakin Alkalami ya riga ya Bushe yayi Bushewar da ba wanda ya isa ya Hana Faruwar abunda Allah ya Zartar. Tana jin Fitowarsa tayi luf ta Daina kukan Fili sai dai na Boye shi kuma ita yake nazari yana Tunanin yadda zai taimaka mata Gabadaya jikinsa yayi sanyi sannan kuma kunyar Amina yake ji sosai yau ace shi ya Haikema wannan kazamar yarinyar me yafi wannan Abun kunya..? Karisawa yayi bakin gadon yana kokarin Daidaita kansa Jallabiyan jikinsa ya maida jikinsa na Digan ruwa baisan ko karfe nawa bane Saboda wayarsa tunda ta mutu tana Falo saman kujera bai sake bi ta kanta ba. Zama yayi gefen gadon yana kiran sunan Amina cikin sanyinsa. Kira biyu yayi mata bata amsa ba sai ya tashi ji tayi kamar zai hayo gadon yasa tayi Saurin Bude ido muryanta ta Dishe ta amsa da"Na"am...! Bata yarda ta iya Hada ido dashi ba sai ta maida kanta ta kwanta Hawaye na Bin gefen kunnenta. Shima bai kalleta ba saboda kunya kai ya kauda kafin a sanyaye yace"Ki yi hakuri ki bar kukan nan..ki taso na Taimaka miki ki gyara jikinki..! Amina taji wani abun banbarakwai wai ya Taimaka mata duk da Haka take gani a Littafan hausa,ammh ita kam bada ita ba daman ita da Aminunta ne ammh yaya Danmallam bazata iya mikewa ta Hada ido dashi ba sannan jikinta fa ba kaya haka zai ganta..!? Tana wannan Tunanin taji mganarsa yana Fadin"Ko bazaki iya tashi bane..? Amina taji kunya ya kara kamata Duk da Zafin dataji kasanta da jikinta ya Dauka gabadaya ta kasa yin wani motsi ganin haka yasa ya fara Tattare hannun Rigan Jallabiyansa ganin haka yasa tace"Ba..bani da kaya to..! Sai kuma Hawaye sharr ko Sauraranta bai yi ba ya hau kan gadon ya isa gareta Amina ta Fara kuka tana fadin"zan tashi da kaina..Don Allah ka bari..bani da kaya..! Bai Tsaya Sauraranta ba ya Dauketa Cak ita da Zanin gadon ya shiga Cikin Tiolet da ita Daman ya tara mata Ruwan Zafi Cikin jazucci ya toshe rariya ya sakata Ciki Lokaci Daya yana Zare mata Zanin gadon data nade jikinta dashi Amina ta yanka ihu ga na azaba ga na Bata da kaya gaban Mutumin data ke jin kunya fiye da kowa a rayuwarta Sannan bama Haka ba Amina bata da Dabi"ar bayyana Tsiraicinta ko da su Hamida ne bata da wannan Sakewar ballatana gata yau gaban Ya danmallan wanda bata taba kawo ma ranta aure dashi ba ballatana wannan Babbar al"amarin ya gifta a Tsakaninsu ba. Shi kuwa duk da yadda ihunta ya cikamai kunni kansa ya cigaba da Sarawa bai kyaleta ba Idanuwansa na Runtse yana fadin"kiyi hakuri..Kiyi hakuri..Kiyi Hakuri ana asif..Ba da gangan bane..! Sai larabci ya tashi Amina na jinsa ta kasa mgana sai kuka itama idanuwanta ta runtse bata son kallonsa hakanan yana jin kunya yana komai ya taimakamata ta gasa jikinta saboda yasan yanayin. Ita kuwa bata yarda ta Bude ido ba ballatana su hada ido wannan abun da kunya shi kanshi don ya zama Dole ne ga Kunya gashi bai da lafiya Har Lokacin Hancinsa a toshe yake ga Zazzabi ga mura. Sai da ya tabbatar data gasa kanta sannan ya juya mata baya yana fadin"Kin iya wankan Janaba..? Innalillahi Amina ta fada aranta ta rasa ina zata sa kanta taji Dadi wannan abun kunyar har ina jin tayi Shuru ya fara mata bayani Dallah Dallah yadda zata gane sosai Ita dai bata san ma ya juya baya ba domin bata Bude ido ba har ya gama mata Bayani ya fice Daga Tiolet yana Jadaddamata tayi yadda yace mata. Sai da taji karan Rufe Tiolet din ta Bude ido sai ta ga ya fita kirjinta ta fara bi da kallo ganin yan kananun nonuwanta atsaye ihu ta saki mai Hade da kuka Danmallam ya cuceta haka ya Tasata ya kare mata kallo ta Tabbata sai da yagama Zaginta ganin yan nonuwan nata kamar Lemon  tsami Saboda kankanta Tiolet din take bi da kallo ganin zanin gadon daya Daukota dashi ya Watsa sa cikin kwandon wanki tana Hango Jini ajikinsa Domin taga ya baci. Wankan Tsarkinta tayi tana yi tana kuka Sai da ta gama ta Dauko Zanin gadon nan ta kama inda ya baci ta wanke jinin haka kurum take jin bai kamata ta barsa ba. Sai da tagama kuma ta rasa tayaya zata fita bata da kaya ko zani babu acikin Tiolet din,Kasanta Zafi yake mata asannu ma take iya tafiya Cikin kwandon kayan wankin ta fara Kokarin Duba abunda zata saka kamar wasa taji shigowarsa Lokaci Daya da fadin"Kin ga...! Mganarsa ta makale ne sakamkon juyowa da tayi ta kallesa sai kuma ta kalli kanta kafin ta yanka ihu ta koma ta Duka tana kare jikinta cikin kuka take fadin"Don Allah ka fita..Ka fita nace..! Haka take fada tana wani irin kuka Daman Zani ya Dauko mata Cikin kayanta ya miko mata baya ya juya mata bayan ya ijiye mata Zanin nan saman fanfon tiolet din ya Juya ya Fita yana Dafe kansa sai da ta tabbatar da ya fita sannan ta iya tashi ta dauki Zanin ta saka tana cigaba da Sharan kwallarta. Lallabawa tayi ta Leko ta jikin kofa sai taga baya Dakin sannan ta iya fitowa  Tana tafiya sannu sannu ko Mai bata Tsaya shafawa ba jikinta na Haduwa waje Daya ta Rarrafa ta koma kan gadon ta kwanta ta Rufe jikinta da Bargo Tana jin gabobinta na ciwo sannan ga Zazzabi na neman Rufeta,Sanyi take ji gashi ta fara rawan sanyi Hakoranta na Haduwa waje Daya. Shi kuma ihun Datake yi ne baya so sannan ga Halin Dayake ciki yasa ya bara mata Daki ya koma Falo ya Dunkule saman kujera zazzabin bai Damesa bama yadda kansa ke wani Saramai shiyasa ya kasa tashi yaje ya Duba Amina Idanuwansa Biyu aka kira Sallar Farko na asuba yana kwance Cikin matsanancin ciwon kai sannan ga faman kokuwa da Numfashinsa yasa ya kasa tashi ballatana ya Duba Amina sai da yaji an Fara kiran salla na Biyu awasu masallatai ya iya Rarrafawa ya tashi, yana cikin wani Hali Sakina ta Cutar daahi yanzu da Dakinsa na Bude ko panadol sai ya sha sannan yana da mganin mura tunda baya rabo da yin mura Lokaci bayan Lokaci. Sai alokacin ya koma Dakin Daya baro Amina Halin daya isketa sai yaji nasa ma ba komai bane koda ya yaye bargon Jikinta ya jike da Zafin Zazzabi sannan ta kasa barci sai jan Numfashi take daya taba jikinta sai da hankalinsa ya tashi bai Tsaya ba ya Fada Tiolet ya Dauro alwala ya tafi yana kallon Amina Dake neman shidewa rasa ya zai yi da ita yayi ba Mota a hannunsa gidan Baba mallam ya barta sannan key din na wajen Jafar. Kuma yanzu ba lalle ya samu abun hawan da zai kai su asibiti ba,Shiyasa ya karisa gareta ya Ciccibota saman jikinsa yana fadin"Amina ki yi hakuri kin ji ko..! Ba mota a hannuna sannan yanzu asuba ne ba lalle mu samu abun hawa ba balle na kaiki asibiti..! Amina hannunsa ta kamkame sai kuka Hawaye na bin wasu shima Riketa yayi gam Hannu Daya kuma yana Faman share mata hawaye gabadaya ya shiga wani yanayi tsausayinta ya kamata ganin yadda Take neman shidewa sai ya Tsorata ammh bai bar natsuwarsa ba sai ya shiga Tofe ta da addu"a yana Shafa mata a goshi zuwa kirjinta cikin ikon Allah sai ta Fara Sakin numfashinta asake bai daina mata addu"an samun Sauki ba har barci ya fara Fizgarta aransa yasani ko yunwa sai ya mata Illah Shima yunwar har da ita ta sashi yake jin jiki Ganin ta samu barci yasa yana ji ana Sallar asuba ya kasa tashi Saboda Duka Amina tana kan jikinsa ne shiyasa bai yi kokarin tashi ba har aka idar da sallar asuba sai wajen karfe shida ta farka da kuka lokacin Har gari ya waye ga Haske nan ta Window din Bedroom din. Bai Tsaya ma wani Lallashinta ba yace"Amina ki bar kukan nan kaina na kara Daukan zafi wlh..Bari nayi sallah muje asibiti..! Haka ya koma ya kwantar da ita ya Isa gabas ya tada sallar ko kafin ya Idar Amina ta cika Dakin da kuka Dole yana idarwa ya mike yana neman mata wani Hijabin da kayan da Zata saka. Doguwar riga ya Daukomata Amina na kuka tana Faman rintse ido wai kar ya tabata ya Daka mata Tsawa yana Fadin"Dillah kima mutane shuru..Taimakom ki fa nake son nayi ko baki ga halin Da kike ciki bane..? Jin Muryansa cikin Fada yasa ta koma tayi Gum sai hawaye shi ya saka mata kaya har pant shi ya saka mata saboda ya gansu Cikin kayanta Bra ne bai gani ba kuma bai nema ba Tunda bai ga abunda zata sama bra ba. Ta daa ita yayi Tsaye ya Zura mata Hijabi yace tayi sallah bari yazo fita yayi zuwa Haraban gidan suka gaisa da Buzu megadi ya fita waje chan bakin Titi ya samu adaidaita suka Dawo Tare sannan ya shiga Cikin gida ya Taho da Amina Walet dinsa kadai ya Dauka wayarsa kuma yasata a chaji Tana kashe. Sai alokacin Megadi yatuna da Sakina ta fadamai akwai wata agidan sai sannu yake jeramata cikin Hausansa. Ganin yanayin ta yasa Umar ya Dauketa Cak sai cikin adaidaitan tana faman hawaye ba kukan Fili tunda yayi mata Tsawan nan. Wani Asibitin kudi ya kaita likitan Dake kula da asibitin abokinsa ne Tare sukayi primary babansa ne ya Budemai asibiti yana kula dashi sun ci sa'a kuwa sun same shi acikin asibitin Lokacin da Nurse ta shiga Office dinsa ta Sanar dashi Umar bazanga  ne yazo wajensa nan da nan ya bada izinin a shigo dasu. Halin da suka shigo da Amina yasa ko gaisawa ma basu yi da Umar ba yace ya Dorata saman gadon marasa Lafiya Dake office din ya fara Attending dinta shi kuma ya samu kujera ya zauna ya Dafe kansa..! Daga yanayinta da kukan datake yi ya Fahimci wani abu Nurse ya kira ya Fadamata abunda zata karbo masa a phamarcy cikin Lokaci sai gata ta Dawo. Amina tunda taga yana Hada allura ta Fara Ihu ganin da gaske ita za"ayi mawa ta fara zumduma musu ihu,Dr Ghali ya Dago yana kallon Danmallam Dake Dafe kansa yace"Bazanga ina ga fa muna bukatarka anan wajen..! Cikin wani yanayi ya taso kansa ma Saramai yake yi ganinsa a wajensa yasa Amina tayi tsit sai Zaran jajayen ido take cikin wani yanayi yace"Dr yi mata..Bana son hayaniya kainq kamar zai cire..,! Dr.Ghali Cikin nazarinsa yace"Ai tunda kuka shigo na Fahimci 2 patient ne..! Shi dai bai ce komai ba kansa ya kara Dafewa Nurse din dake Dakin ta Rike Amina da karfi aka mata allura Fadi take"Wayyo Mamanmu..Wayyo Allah na Aba..,. Nurse din tana ta lallashinta tana Fadin"Is ok..ai an gama Haba Sister na ki Daina kuka mana an gama baki gani bane..! Amina kukanta take yi bata Saurara ba Dr Ghali na Dariya yace"yanzu zamu ji shuru barci zata yi..! Ko minti goma bata kara ba Amina kaji Tsit sai barci Dr.ghali ya samu Damar Nenan jijiyanta ya saka mata Drip guda Daya. Sannan ya Sallami Nurse din Danmallan ganin hijabin Amina ya Yaye rigarta maa haka har ana ganin Cinyarta yasa ya saka hannu ya gyara mata yana kallonta cikin Lokaci daya ta Rame. Dr.Ghali ya kallesa yana fadin"Ta samu barci kar ka damu bazanga..! Juyowa yayi yazo ya zauna inda ya Tashi kafin yace"Bata fa ci abinci ba Tun jiya..! Dr yace"kada ka damu in tatashi zata ci..bari na Duba ka naga meke damunka dai kafin mu gaisa..! Umar ya Dafe kansa yana Fadin"Ciwom kai ne da mura ne sai Zazzabi..! Tasowa yayi da abun awon Bp yazo ya aunasa kafin ya kallesa yana Fadin"Bp dinka ya yi sama kadan Bazanga..! Sai Murar dakace shiya saka maka ciwon kai..! Aransa fadi yake ai ihun Amina kadai ya isa bp dinsa yayi sama. Mgani ya Rubuta a takarda ya saka Telephone ya Kira Nurse din Data fita da sake shigowa yace taje phamarcy ta karbo masa mganin ba Dadewa sai gata ta dawo da mganguna Da yawa a leda da Tambarin asibiti. Dr.ghali ya Fito dasu yana mai bayanin nasa da na Amina sai da ya gama sannan yace"In ruwan ya kare zata farka sai ku tafi gida..Sannan kai sai ka sha naka saboda kan ya Fadamaka..! Umar ya girgirza kai kafin yace'No sai na koma gida..,! Dr ghali ya jinjina kai kafin yace"Bazanga aure ka kara ba labari..? Aliyu dai mun hadu last yace min ka sake auran wata balarabiya ammh kuma sai naga wannan ba ita bace sannan kuma yarinyace wannan..! Umar ya rasa me zai ce gashi ya Tsare shi da ido daman tun abaya ghali Haruna akwai son ji kwakwaf bakinsa yaji kawai yace"Matatace..Mallam ya auramin ita..! Dr Ghali ya Bude ido yana yar Dariya kafin yace"i see..na zata zakamin wasa ne..Kasan na Fahimci komai fa..Gaskiya kai gentel ne Bazanga baka jimata rauni ba duk da tana karamar yarinya kayi abunda ya Dace..Sannan abu Daya ya wahalar da ita tana jin yunwa sanda abun ya Faru shiyasa ta jigata.. Ammh na mata alluran barci sannan ga Drip nan na saka mata zai taimaka wajen Dawo da Karfin jikinta ga mangunanta na pain reliver dana ciwon jiki in kun koma taci abinci mai kyau sai ka bata tasha ta kwanta ta huta..Kaima kana bukatar Hutu..Ango..Ango ya sha kamshi..! Dariya Umar yayi kawai bai yi mgana ba,shi ya kauda mganar Amina suka shiga hirar duniya yana tambayansa yana madinan har yanzu..? Sannan suka gangaro Hirar yan ajinsu da sukayi makaranta Tare wasu sun taka matsayin manya manya a gwannati sun Dade suna Hira har Umar yaji ya dan warware kadan awa Uku Amina ta kwashe tana barci sannan ta Farka Lokacin Drip ya kare Allah ya taimaka tatashi ba kuka ita kanta taji karfi ajikinta sai abunda ba"a rasa ba Nurse din nan ya Kira ta Cire mata Canulan ya Sallame su Danmallam ya rike hannun Amina bayan ya taimaka mata ta sanya Hijabinta ayadda ya rike ta Hannunsa Daya rike da ledan mganin sai da suka Burge Dr.ghali matuka yaga sun bala"in dacewa matukar sha"awar auran yarinya mai irin shekarun Amina ya kamasa. Godiya Umar yayi ma Dr.ghali sukayi Musabaha Dr ghali yace"Allah ya bada zaman lafiya bazanga .! Aciki ya amsa da Ameen,suna gabda Fita Daga offoce din yace"Kada ka manta ta dinga shiga ruwan zafi..! Kai ya jinjinamai kafin su fice Har wajen asibiti yana rike da hannunta Adaidaita ya samar musu suka shiga basu koma gida ba sai da ya biya dasu wani Reataurant ya siyan musu abinci Takeway biyu sannan ya siya kaza da Youghourt da Hollandian sannan suka koma gida. Yadda ya fita da ita haka ya maidota Allah ya taimaketa ta Daina kuka sai dai da gaske tasha yunwa Takeway din Jallop din shinkafa da nama yayi mata shi kuma yayi ma kansa na Tuwon shinkafa miyar agusi. Amina duka ta cinye shinkafa ko lallashinta bai yi taci ba saboda yunwa tana ci jikinta na rawa. Bayan ta gama ci ya bata kazan taci Rabi ta Dora da madaran youghourt bata Shanye duka ba sannan taji ta koshi shi ya zauna ya balla mata mganugunanta tasha duka ba gaddama ammh kanta na kasa bata iya Hada ido dashi. Sai da ya rakata Daki ta kwanta Bisa gado,ya lullba mata bargo sannan ya Dawo Falo yaci nasa abincin ya sha Holladian ya Sha mgani shima ya koma kan kujera ya kwanta ba"a Dauki Lokaci ba wani barci mai nauyi ya kwashesa..! *Janafty**TFZB2007* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Tunda ya kwanta bai tashi ba sai karfe biyu narana da wani abu Allah ya taimakesa daya tashin ciwon kan ya sauka harda muran ma ta fara sakinsa bai ji dadi ba tun jiya yake rasa salla cikin jam"i abunda baya faruwa dashi sai da wata lalura mai karfi. Dakin da Amina take ciki ya shiga har Lokacin tana ta barci sanin Halin Datake ciki yasa bai tasheta ba Tiolet ya shiga ya Dauro alwala ya fita Falo yayi sallah jin sa yake yi sakayau kamar ansauke mai wani kaya mai nauyi ajikinsa nan kan kujeran ya cigaba da zama yana Tunanin makomar abunda ya faru Tsakaninsa da karamar yarinya irin Amina inda Allah ya Rufamai asiri natsuwarsa acikin jininsa take bai ce baya rasa natsuwarsa wani Lokacin ba ammh bai cika rasa shi duka ba yanzu da ya zo ma Amina da karfi ya jimata ciwo har ta kai da wata matsalan da asirinsa ya Dade da Tonuwa in kuma Hakan ya faru akwai kunya da kuma zubewar kimarsa ko mallam da Hajiya baya fatan su ji labarin aika aikan daya aikata ita kanta yarinya yana ta mamakin Dauriyanta da jarumtar ta sosai ta bashi mamaki bai taba zaton zata iya Daukansa ba,Duk da abun ba wani Dadewa akayi ba sannan abu ne da yafaru dukkanasu basu da zato ko Tsammani. Gajiya yayi da zaman shuru yasa ya tashi ya kunna Tv tashar Sunna tv ya saka yana sauraran wa"azin Dr.Jabir mai hula har la"asar tayi ya tashi yayi sallah baya so ya fita ya bar Amina ita kadai ta farka ta fara kukanta na Fama har kuma Lokacin bata tashi ba ya Lura kamar akwai mganin Dake sakata barci aciki shiyasa ya barta ta Huta ba laifi ai taji jiki tana Bukatar Hutu. Sai wajen Biyar da Rabi na yammah Amina tatashi shima din ya shiga ya Dubata ne ya isketa zaune kan gado tana ganinsa ta dukar dakai bata son suna Hada ido shima dim kunyarta yake ji yasa ya kauda kansa yana fadin'"Ya jikin ki..? Kanta na kasa ta amsa da cewa da Sauki Tiolet ya shiga ya Hada mata ruwan zafi ya fito yana fadin"Tashi kiyi wanka..Kiyi sallar dake kanki..Azahar da la"asar..! Batayi gaddama ba ta Sauko daga kan gadon tana jin kuzarinta ya fara Dawowa sannan jikinta ya Daina mata Ciwo kamar dazu sai dai har Lokacin kasanta na mata Zafi Tafiya kadan kadan take yi kamar yar koyo zata wuce ta gabansa ba zato taji hannunsa saman kanta ya taba Lokaci Daya yana fadin"Zazzabin ya sauka..!? Cikin sigar Tambaya duk da sanda ya Tabatan dukkansu sai da tsigar Jikin su tatashi da sauri ta gyada mai har jikinta na rawa ta shige Tiolet din da Sauri ya Bita da kallo. Darduma ya shimfida mata ya ijiye mata Hijabi sannan ya koma Falo kada ya Takura mata sai bayan wani Lokaci ya Dawo ya isketa ta gama Sallah bai Tsaya ba ya fita ya Dauko mata Ragowan kazan dazu da youghourt,ya bata daman kamar ya sani Cikinta kamar an yi yasa sai dai bakinta ne ba Dadi ya tasata sai da ta Cinye ta Dora da mdaran sannan ya bata mgungunanta na Rana lum da ido ta dinga yi tana so ta kwanta nan kasa ya Hanata Cikin Sautinsa yace"ki zauna mganin yabi jikinki..Kika kwanta zaki iya yin amai..! Amina ta ji hawaye ya kawomata cikin Sanyin murya tace"Barci nake ji..! Mikewa yayi yana Fadin"Ba kyau barcin yammah dazu ma don naga baki tashi bane..! Ita dai batace komai ba ta maida kanta kasa Filo ta ga ya Dauka ya Fita tana ganin haka ta kwanta saman Cafet ba zato ta ga ya sake dawowa Saboda kada ya ganta yasa ta mike da Saurin da sai da kasanta ya amsa ta Cije baki tana fadin"Wash..! Kallonta yayi kafin yace"Sannu..Ki taso muje falo ki zauna..yammah tayi kwanciyar bata da amfani..! Bataisa tayimai gaddama ba ammh da zai gane da ya barta anan ta zauna din bata son hada ido dashi ko zama kusa dashi ammh bai kyaleta kafa kafa ya Satasa suka koma falo kan kujera mai zaman mutum daya ya zaunar da ita bayan ya kara mata Filo shi kuma ya koma mai zaman mutum biyu ya zauna Lokaci daya ya maida kansa wajen kallon abunda ake haskawa a Qur"an tv Saudi domin ya sauya tasha. Bai kara ma ko kallon barayin Amina ba sai chan ya duba barayinta sai yaga tana barci a zaune mirmishi kawai ya Saki yana da tabbacin mganin akwai mai sa wannan barcin bai tasheta ba sai da aka kira sallah bayan ya Dauro alwala yace taje daki tayi alwala tayi sallah zai tafi masallaci ya dawo Daganan ya fice. Kamar yadda yace haka tayi sai bayan data idar da sallar shuru shuru bai Dawo ba ta fara jin tsoro ita kadai agida Falo ta koma ta Rakube kan kujera tana Zaran ido abu kadan ke sakata kuka yanzu sai kuka Allah ya Taimaketa akwai wutar nepa. Shi kuma bai bar masallaci ba sai da ya Tsaya yayi sallar isha"i yaje Atm ya cire kudi saboda na hannunsa sun kare Allah ya taimakesa ba banki Daya garesa ba,Guda uku garesa anan gida sannan yana da Biyu achan Saudiya ba domin haka ba da Abunda Sakina ta aikatamai da kashinsa ya Bushi wato haka take so koda ya tafin yunwa ta kashe yarinyar Mutane tajamai bala'i wlh Nageria tayi kadan shi da Sakina sai ya nuna mata shi ke auranta ba ita ke auransa ba! Restaurant yaje ya siyo musu abinci da abun sha sannan ya Dawo koda ya Dawo tara ta kusa Amina ya samu nata kuka shi ya zata ma ko ciwon ne ya Dawo ya fara tambayanta ina ne ke mata ciwo..!? Cikin Hawaye tace"Tsoro nake ji..Ni kadai agida..! Bai yi mgana ba illah abinci da yace ta Sauko taci ferfesun ganda ya siyo ma kansa ita kuma na kayan ciki sai Fruit salat saboda a yanayin datake ciki yasan zata ji dadinsa sai ruwa da Maltina da yawa,kuma taci sosai saboda barinta yayi ya koma Daki yayi wanka ya Sauya kaya zuwa wata Jallabiya koda ya fito ta cinye duka harda shan romo tana ganinsa ta koma ta nade waje daya kanta na kasa bai nuna ya Fahimceta ba tambayanta yayi ko ya isheta ta Daga kai Fruit salat din ya Turamata gabanta yace ta sha,cikinta ya cika yasa bata sha da yawa ba mganinta ya bata ta sha bayan ta tabbatar mai da tayi sallah yace taje ta kwanta kamar ya sani barci take ji ammh sai ta kasa tafiya Tsoron kwanciya take yi ita kadai ganin haka yasa yace mata ta je in ya gama abunda yake yi zai shigo..! Dalilin dayasa tatafi taje ta kwanta kenan ba jimawa sai gashi ya shigo shima kadan yaci gandan ya sha mgani nan kasa ya shimfida bargo ya kwanta Alokacin har Amina tayi barci batama sani ba shi ya cire mata Hijabin Jikinta data kwanta dashi Saboda tasha iska ko motsi batayi ba bayan ma mgani ya Lura tana da nauyin barci. Shima yana kwanciya bai Dade ba sai barci saboda na muran yana saka barci karfe hudu na asuba ya tashi yayi wanka ya fice zuwa masallaci sai 6 ya dawo ganin Amina bata da Niyar tashi ya tasheta yace tayi sallar kamar mashayiya haka tatashi tana Idar da Sallar ta koma ta kwanta tana samun Hutu sosai. Shi kuma yana falo yana kallon labarai wayarsa tun jiya ta cika ammh Hakanan yaki kunnata baya so ma wani yasan yana nan Tafiyarsa shekaranjiya bata samu ba sai yau,Sai wajen 8am na safe ya leka Amina tana ta barci bai tasheta ba ya shiga Tiolet kayan data tara a Kwandon wanki ya kwashe harda zanin gado yaso ma ya Kira mai musu wanki ne sai kuma ya fasa,Gwara ya wanke su da kansa yasan in ya tafi bai wanke ba akwai matsala Amina bata san ciwon kanta ba Tukunnah ko kuma yace ba"a koyamata ba Daga yanayin yadda bata iya komai sai tace Mamanmu ko Hamida ke mata Daga gani su suka batata ammh ace kamar ta ace batasan gyara ba sai kazanta. Ta harabn gidan akwai wata Kofa inda suke da famfo da tankinsu na ruwa nan ne sukayi wanki ko shanya in wani abu ya faru na gaggawa,nan ya kwashe kayan ya fita dasu Allah yasa Megadi na Dakinsa bai gansa ba ba Omo kwata kwata agidan sai da ya Fita ya siyo ya Zage ya wanke zanin gadon nan tas da kayan Amina pants dinta kuma Data wanke basu fita ba ya Zubar a Bola domin bazai iya wanke mata ba, ba domin yana kyamarta ba yana da kyamkyami sosai ne sosai bazai iya wankewa ba,Ammah ai karshen kyamkyami kuma ai ya kare tsakaninsa da Amina tunda mai afkuwa ta riga ta afku Abun da ya kusa bashi Dariya Har da Vests cikin kayanta shi yaushe Rabon da ya ga ana sa Vest aransa yace shi ne madadin Bra dinta shi kadai yana wankin yana Dariya har alokacin in ya Tuna Haduwarsa da Amina sai yaji wani iri acikin Ransa yanayi ne da bazai iya Fasaara shi ba ammh yaji matukar mamakin yanayin daya shiga Lokacin kasancewa da ita ko shi yasa Aliyu ke son auran irin su masu kananun shekaru..? Yadan gano sirrin kadan duk da Abun bai wani Samesa Yadda yake so har yaji ya ishesa ba an Dai Taba kawai an bari shima Tabawan kamar kudirin Allah ne. Tas ya wanke su ya Daureye ya shanya su saman igiya sannan ya koma Cikin gida ya Zage ya gyara falon ya Share saboda duk yayi kura saboda isar da akayi shekaran jiya.. Dakin da Amina take ciki ya koma har Lokacin tana barci Zagewa yayi ya shiga Tiolet ya wanke shi Tas ya zo kuma ya gyara Dakin ya share duk ya Gaji bayansa har ciwo yake yi bai zauna ba wanka ya shiga yayi ya fito ya Saka Jallabiya baka ya Dauki walet dinsa ya fita yaje ya siyo musu abinci da katan din Faro sai na maltina Saboda Amina da kuma Tafiyarsa. Sanda ya dawo ta tashi Daga barcin Kuma tayi wanka batare da yace mata ba Sai dai kayan jiya ta maida sai yace ta Cire ta sauya wasu ita daman tayi wankan ne saboda ta Lura yadda yake son wanka kamar kwado koma batayi ba sai yace tayi shiyasa tayi ammh yaushe zata jure wannan aikin kamar wata yar ruwa..! Atamfa ta saka Riga da Sikat sai Alokacin yake ganin Rashin girman Jikinta tsawo dai gareta ba Kiba,Ammh a shekarunta in da tana da manyan gabbai da Tuni tayi Jiki Tunda Hamida da Hanne sun fita Girma yan kirjinta yake kallo kamar yayi Dariya abun chan manne Lalle kwaila ce Tabbas kwailace ya aura kuma kwailan nan ne ta Daukesa Tsab Allah mai iko domin ya yarda da akace abun ba daga shekaru ne ko Girma ba..! Chiips ne ya siyo mata shi kuma Ruwan zafi yace su bashi achan yazo dashi ya sha Tea da buredi ita kuma ta Dora da maltina tayi gatsa ta sha mgani da ruwa yace taje ta kwanta Haka ta mike tana Tafiya sannu sannu ya Bita da kallo Hankalinsa ya kwanta ganin har tafiyarta ta Fara Daidaita ya Fara Tunanin in ya tafi yau Amina bazata iya zama agidan nan ita kadai ba ita kuma wanchan baisan yaushe zata Dawo ba..! Shi kan shi akwai gajiya ajikinsa yasa ya kwanta saman kujera sai barci sai gabda azahar ya farka Sauri Sauri yayi alwala ya tafi msallaci bai Tsaya ba Illah abinci da siyo ma Amina da kayan su Fruit ayaba kankana lemo da Sauransu koda ya dawo ta tashi tayi sallah tana kwance ammh ba barci take yi ba. Inda yayi wanki ya koma ya kwashe kayan Tunda sun bushe ya kawo su Falo ya zauna ya ninke mata sannan ya Shigar mata dashi har Cikin Wardrope ya saka mata yana Fadin"Mai wanki duk bayan sati daya yake zuwa karba..Ki rika Hada kayanki wadanda suka kamata banda Undies nasan ba hankali kika cika ba sai ki Hadamai da Vest dinki..! Kunya ta kama Amina taji kamar ta Nitse shikenan ita kuma ya gama ganin komai nata Zanin gadon ya Ciro ya kalleta yana Fadin"Tashi na Shimfida..Kije falo na siyo miki abinci da Fruit..! Kamar zata fita sai kuma ta fasa ta kallesa yana kakkabe gadon zai shimfida Zanin gadon tace muryanta kasa kasa"Kawo na shimfida..! Ko kallanta bai yi yace"Ki wuce nace..!. Da sauri ta wuce har tana Hardewa sai da taji wani iri a kasanta duk da ya fara warkewa sosai ta ke tsarki da Ruwan zafi tana gani a littafan Hausa in haka tafaru kuma tana so ta warke shiyasa batayi wasa ba sannan kuma Ai da sukaje asibiti Dr haka ya fadarmuau hakan. Tana fita ta jawo ledojin priderice sai kayan Marmari  Ayaba kadai taci sai kankana cikinta ya cika sosai mganinta na Dakin ita kuma tana jin kunyar komawa ba Dadewa sai gashi ya fito da mganin ya zauna gabanta yana Fadin"Matso na nuna miki yadda zaki sha kowanne..! Ba musu ta matso ya nuna mata Duka kuma ya tabbatar da ta gane ya bata ganin bataci abinci ba ya Tambayeta tace sai an juma ta koshi. Da kanta ta maballi mganin tasha ta koma gefe ta Rakube kanta na kasa shima bai bi ta kanta ba ya sha Kankana kadai ya mike ya bar mata falon ta Bisa da kallo aranta tace ashe yana da Mutumci wani lokacin..! Wanka ya shiga Sauri Sauri yake yi Saboda yana so ya isa kano da wuri kuma Motar haya zai bi jirgin su karfe Takwas na Dare zai tashi zuwa jidda. Sannan kuma wa zai kira yanzu yace mai bai tafi ba..?Kowa na da uzurinsa sannan kuma basusan an samu wannan Tsaikon ba,Duk da yasan sun neme sa a layinsa na Saudiya zasu ji a kashe layinsa na nan kuma bai kunna wayar ba yasan zasu yi Tunanin gajiyar tafiyace yasa bai Dora Layin ba yana da Tabbacin harda mallam ya Kirasa yaji ya ya sauka bai samesa ba..har ya shirya cikin Pakistan riga da wando masu ruwan madara yana Tunanin mafitar yadda zai yi da Amina baza ta iya zama ita kadai ba sannan Hajiya bazata taba yarda ya maidata agida ba. Tunanin kiran Hajiya yayi yace ko su Hanne ta saka idi ya kawo su yasan Aminar zata ji dadi da wannan Tunanin ya fito Cikin Shirin Tafiya Rataye da Jakarsa Amina ya iske tana Barci a zaune ya Dade yana kallonta karamar Fuskarta har ta Fada sai yaji Tsausayinta gashi zai tafi ya barta ba wani babba kusa da ita Allah yasa ma taji Sauki sosai. Fuskar yaya yake gani a Fuskarta sai yau ya kara kare ma Amina kallo yaga ba inda ta bar yaya a kama,Baisan sadda ya Furta"Allah ya jikan ki yaya.! Afili yana kara kallon Amina lokaci Daya yana kara ganin yarinta muraratun a kanta ganin har Biyu ta gota yasa ya karisa gabanta ya Durkusa yana Buga jikin kujeran Data jingina tana barci lokaci Daya da Kiran sunanta. Firgigit ta mike tana Raba ido sai ta gansa a gabanta Tuni jikinta ya Fara rawa tana kokarin tashi ya Rike duka Hannuwanta yana fadin"Ki natsu mgana zamu yi..! Duk da ta natsun ammh ta kasa kallonsa Kanta na kasa tana kallon yadda ya rike da hannunta sosai. Cikin Taushinsa yace"Ya jikin ki..? Fata kin sami lafiya..? Kai ta gyadamai alaman eh Cikin bude murya kadan yace"Da baki zaki amsamin..! Sai da runtse ido kafin tace"Eh da sauki..! Kai ya kada kafin yace"Ba inda yake miki Ciwo..? Kai ta kara dagamai kafin kuma da Sauri tace"Ba ko"ina..! Shuru ya gifta na wani Lokaci kokarin Kwace hannunta take yi yaki Sakinta wani yanayi take ji Daya riketa shi kuma sai faman kai da kawon mganar yake yi kafin yayi shahada ya kira sunanta. Amina..! Amsawa tayi ammh bata Dago ba shima bai Damu ba cikin Taushin lazafi yace"Abunda ya faru Tsakaninmu Sirrinmu ne ko..? Yafada yana kallonta kanta na kasa bata yarda ta Dago ba ta gyadamai kai Cikin jin nauyi shima ya cigaba da Fadin"Yauwa to kuma kinsan duk wanda yake fadan sirrin aure Allah zai kona sa ko..? Ba kyau nasan an fada muku a islamiyanku ko..? Nan ma kai ta gyada mai kafin ya cigaba da Fadin"To ina so abunda ya Faru Tsakamin mu ya tsaya iya mu Biyu..Kada ki sake ki Fadama kowa kin jini ko..? Sai alokacin ta Dago ta kallesa suna Hada ido tayi saurin maida idonta kasa shima Fuskewa yayi kafin yace"Kin ji ko baki ji ba Amina..? Cikin sanyi tace"To Allah fa..? Ai ya sani ko..? Mamakinta ya kamata sai bai nuna mata Cikin yanayinsa yace"Eh Dagani sai ke sai Allah..Daman ai shi yana Sama kuma yana kallon Duk abunda muka aikata..! Bana so ki fadama kowa..Koda Hajiya ce ko mallam ko Aba ko Hannatu da Hamida. ! Kai tsaye tace"Harda Mamanmu..? Da Sauri yace"Har da ita kada ki Fadamata in kuma kina so Allah ya Konaki Ranar Lahira shikenan..! Yafada da sigan ya Tsoratarwa Amina mamakinsa ya kamata me ya maidata ne..?Sauma kiramana shashasha kenan..! Da bata san me take yi ba da zata bama wani wannan Labarin mai kunyar Fada ita ba Haka take ba ko da ya ganta yarinya tana da wayau..! Shi a dole zai mata wayau sai abunda ya bata Dariya har sai da ta Murmusa kafin tace"naji insha Allahu bazan Fadima kowa ba..! Jinjina kai yayi Cikin jin Dadi kafin yace"Good naji Dadi..Ki kula da kanki kinji ko..?Kirika wanka sau uku ko Biyu arana sannan ki rika shan mganinki kin ji ni..? Nan ma kai ta gyada mai ba Zato kawai taji ya saka mata kudi a Hannunta ganin yan Dubu Dubu yasa ya Zare ido kafin tayi mgana ya mike yana fadin"Ki rike su a hannunki..Ni yau zan koma..! Zaro ido Amina tayi kafin tace"Ina..?Madina..? Kai tsaye yace mata"Eh tafiyar ma bata yuyu bane da Tuni na tafi..Jafar zai kawo miki waya zamu rika mgana ..!ina dai gargadinki kada ki Fadama kowa..! Amina bata ma jinsa Tunaninta na kan yadda zata zauna ita kadai agidan nan gashi bata san ina gajeran matarsa taje ba tun ranar bai kara mganarta ba..kafin ya ankara Amina ta Fashe da kuka cikin mamaki yake kallonta kafin yace"Kukan me kike yi..?cikin kuka tace"Wlh bazan iya zama agidan nan ni kadai ba Tsoro nake ji ka maidani gida..! Kai Tsaye yace"Nima  naso hakan sai dai  Hajiya da maallam bazasu bari ki koma ba..! Amina na Jan majina tace"Gidammu zan koma bazasu sani ba..! Dariya mganarta ta basa da sai ya Dara kafin yace"In jiwa..? ai da gidanku da gidan mallam Duka Dayane Dole zasu sani..Ki daina kuka zan kira Hajiya ko Hannatu sai tazo ta Zauna Dake kafin Sakina ta Dawo..!. Jin sunan Hanne Daya ambata yasa ta bar kukan ta Dago tana kallonsa kafin tace"Da gaske..? Kai ya gyada mata wani mikewa tayi kafin tace"Yauwa harda Hamida don Allah ya Danmallan kaji..? Ashe tasan sunansa kallonta yayi kafin yace"Wato ku hadu ku fara rashin ji ko..? Kin san dai yanzu ba da bane ko..? Da Sauri Amina tace"eh wlh babu abunda zamu yi..! Kai ya jinjina mata kafin yace"Shikenan sai su zo..! Tsalle ta Daka tana Hawaye tana Dariya zafi taji a kasanta yasa ta Duke tana Wash wash Kallonta yayi kafin yace"Ki rika kula da kanki fa..Kina da Sauran Rauni..! Bata Dago ba ta mikamai kudinsa tana Fadin"Babu abunda zan yi da kudi..!. Shi kuma yace"Ki rike a hsnnunki. zaki koma makaranta Dis Coming monday ki rika yin kudin Break sannan in kina Bukaar wani abu in Sakina ta Dawo ita zaki rika tambaya kina jina ko..? Kai ta gyadamai ammah aranta tace Tab wannan matar muguwa din. Afili kuma cewa tayi"Allah ya kiyaye hanya..! Ya amsa da Amen yana kallonta kanta ya Dafa kafin yace'Allah yayi miki albarka..Na tafi sai in kuma na Dawo..! Sai kuma taji kamar kar ya tafi yana mata Kirki na kwana Biyu wayarsa ya Dauka anan wajen kayan kallo ya Fice ta rakasa da kallo sai da ya Dade da Fita sannan ta koma ta Zauna da kudi a Hannunta tayi Tagumi haka kurum taji kamar kar ya tafi sai dai kuma taji Dadin da su Hanne zasu zo Dadi ya isheta.! Shi kuma yana Fita Tasha ya wuce Direct Allah ya taimakesa ya samu Motar kano ta kusa cika ita ya shiga kuma Motar nada Lafiya sun yi gudu kuma koda biyar tayi yana Filin Jirgin Aminu kano,bayan yayi sallah ne ya kunna wayarsa ya Kira Hajiya.. ****** Hajiya na Cikin Bedroom dinta tana Duba littafin 40 Rabbana Hanne na Tsaye awajen Wardrope dinta tana gyara mata kayanta Jiya mai wanki da guga ya kawo wayar Hajiya Dake kan madubi ta fara kuka alamun kira Hanne tafi kusa da wayar yasa Hajiya tace ta miko mata. Tana Dauko wayar tace"La Hajiya ya Danmaallam ke kiranki..! Hajiya ta ijiye abunda ke hannunta kafin tace"To ya natsa kenan tunda ya kira..! Bata Tsaya Duba lambar ba ta Daga Kiran Lokaci Daya tana amsamai Sallamarsa cikin Sanyinsa ya gaisheta ta amsa tana Fadin"Kun sauka lafiya..?Mallam nata kiran ka bai samu ba Nima har da Safe na gwada layinka nachan ban samu ba..! Cikin Taushinsa yace"Hajiya ai ban tafi ba..Sai yau ne zamu tafi jirgimu zai tashi da karfe takwas na Dare. ! Hajiya ta Bude baki kafin ta Dago wayanta tana kallon Lamba sai Lokacin ta Lura lambarsa ta nan ne saboda ta chan Danmallam2 ta sakamai. Cikin mamaki tace"Ikon Allah to meya faru ba wanda yaji labari don ko da Safe Jafar ya shigo nan nake tambayansa yace shima bai samu wayarka ba..! Umar yace"Matsalan hazo ne Hajiya shiyasa tafiyar bata yuyuba aranar..! Hajiya tace"To Allah yasan hakan shi yafi Zama alheri..! Ya amsa mata da Ameen kafin yayi shuru itama jinsa shuru yasa bata yi mgana ba sai da taga bai da niyar mgana sannan tace"Danmallam lafiya kuwa..?ka kira kuma kayi shuru..? Ya sosa kansa kafin yace"Hajiya ina Filin jirgi kanon tun dazu..! Hajiya tace"Madallah Allah ya Tsare..ya wajen su Aminar ina Fatan Lafiya ko..? Cikin Kasa da Murya yace"Suna lafiya Hajiya..Daman zence ne in ba Damuwa Hannatu da Hamida su tafi yanzu su je su zauna da ita gidan ba kowa..! Hajiya tace"Bangane ba kowa ba Sakinar fa..? Kai Tsaye yace"Bata nan Hajiya..! Bata Damu da tace ina taje ba tace"Allah ya kyauta..To yammh tayi kuma mallam baya gida sannan Gobe jumma'a suna da makaranta Danmallam.. Kai Tsaye yace"Hajiya kiyi hakuri su bar makarantar ta gobe su je su kwanan mata Biyu..In sakina ta Dawo Shikenan sai su dawo gida..kinga tayi kankanta da Zama ita kadai.. sannan ita ma Ranar monday sai ta fara zuwa makarantar..! Hajiya tace"Shikenan bari na Tura su yanzu Daman na bari ne sai Asabar sai su hakura da Haddar su je mata tunda kuma ga wannan laluran bari na nemi ko Uzairu ne ya kai su sabod maallam da idi ya fita..! Danmmallam yace"Uzairu ya Dawo ne..? Hajiya tace"Eh jiya ya Dawo..! Kai Tsaye yace"Hajiya ki basu keys din gidanan su tafi dashi..!. Hajiya bata da bin Diddigi kai Tsaye tace shikenan daganan sukayi sallama ta bisa da Fatan isa Lafiya..tana gama wayar Hanne data kasa kunni taji ta cikin jin Dadi tace'Hajiya wajen Amina zamu..? Hajiya ta mike tana fadin"Eh da naso sai jibi ne ammh yace kuje yau sakinar bata nan..!. Hanne ta Daka Tsalle tana Murna Hajiyw tace"Daman na gama Hadamata komai jiya ma kinsan a kawo Dinkunanta da mallam yayi mata Sabbi yanzu shiga gidan Sa"idu kice ma Balaraba zaku wajen Amina in tana sako ta bada..! Ai da gudu Hanne ta fita Tana murna Hajiya kuma ta fara Hadaa Sabbin kayan da mallam ya Dinkama Amina kala goma da Hijabai sai ita kuma ta mata Turaran wuta da Humra sai Dambun nama dasu Samosa duk an yi package dinsu sai kamshin girki kala kala har da curry har da su Cake sannan ta Siya mata Sabbin panta da sikat da Vest. Ba jimawa sai ga Hamida da Hanne kamar bakinsu zai Tsage saboda murna Hamida ta Dauko kayanta kala Biyu Hanne ta bama Hajiya Turaran Tsinke guda Daya a ledansa wai inji mamanmu akai ma Amina.. Hajiya mamaki ya kamata ko jiyan nan Sa"idu ya sake fadaa mata ya bama Balaraba kudi ta yi ma Amina siyayyan abun Bukata shiyasa ta aika mata ammh sai taga wannan abu haka..? Abun ya bata mamaki ace wajen Amina fa za"aje koda Sa"idu bai ce ya bata kudi ba ta Dauka kayan da zata Hadama Amina sai yafi ma wanda ta Hadamata ammh sai bata saka kokonto aranta ba ta barshi a kila bata siyan mata bane tukunah sai Daga baya..! Hajiya batace komai ba ta Hada Cikin kayan sannan ta Dauko musu keys din gidan ta basu sannan tace Hanne ta Diban ma Amina sinasir din da sukayi da Miya su kai mata jiki na rawa suka Diban mata a coolers suka saka miya Dabam sai murna suke yi Hajiya ta Jaddada musu ranar  Lahadi idi zai Zo ya Daukesu sannan taja kunnensu da su natsu da sakon su gaida Amina..bata yi gaban kanta ba sai da ta kira mallam sukayi mgana da Farko cewa yayi"Hajiya yara nan su kadai agida kina ganin zai yuyu.? Kodai Aminar ta dawo gida kawai har Sakinar ta dawo..! Hajiya tace"Hakan ba mafita bace in mukace haka bazata saba da gidan auranta ba gwara ta zauna watan watarana zata saba..! Da haka mallam ya yarda da Hujjanta yace su Hamidan su tafi da kanta ta Kira uzairu yazo ya kaisu da Daya daga Cikin motocin gidan Daman tun jiya daya Dawo key din motar ke hannunsa. Har suka tafi Hajiya bata Daina mamakin Balaraba ita sai kawai taji abun yayi mata wani iri. Sai da ta koma shashen nata ta ga Sinasir din datace su hanne su dibar ma Amina saboda sauri sun manta dashi kawai ta girgiza tana mirmishi suna ta zumudi dole su manta. Ita kuwa mamanmu Rana Tsaka kawai hanne tazo tace Hajiya tace ta bada Sako zasu wajen Amina.. Ita har ga Allah mantawa ma take da wata Amina kudi kuma tabi ta kansu  Shiyasa ta Dauko wannan Turaran Tsinke wanda mamata ma ta bata shi ya Dade bata taba amfani dashi ba tamikama hanne domin bata taba Zaton Sa"idu yayi zencen ya bata kudi da Hajiya ba. ganin suna ta Murna yasa batace komai ba gwara Hamidan taje ta gano wani irin Halin da Amina ke Ciki don ta tabbata Sakina bazata mata wasa ba ita fa a gayyas gida yanzu ya Rage daga ita sai mijinta Jawaad yanzu in Aba ya Dawo yadaina zuwa saboda samunsa tayi tajamai kunni yaro kuma da Tsoro ko Aba ya Dawo ko ya kirasa daya zo sai yace yana da Homework sai ya tafi hakan yafi ma Mamammu Duniyarta take so taci ita kadai bata san Takura. *Janafty**TFZB2008* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Amina tana rakube a falo tsoro duk ya cikata tunda Danmallam ya fita take duban idon su hanne ammh har Dare ya fara shiga ana gabda kiran sallar mangariba bata gansu ba Tsoronta Allah kada Dare yayi basu zo ba bazata iya kwana ita kadai ba Tana jin tsoro. Tana zaune kan kujera a rakube saman kujera tana fiki fiki da ido,kamar mara gaskiya ko kwakwaran motsi bata yarda tayi ba, saboda tsoro,Saboda yanayin Datake ciki yasa ko karan Bude get bata ji ba sai ihun kiran sunanta da Hanne da Hamida suke mata kamar daga sama haka taji tana kyalla ido kawai taga Hanne da Hamida da kaya niki niki a Hannunsu,bata san sadda ta Diro daga kan kujera ba duk da yanayin Datake ciki bai sa ta tsaya ba Cikin Farin ciki da murnan da Rabonta da tayi har ta manta ta fada Jikin Hanne Tana Fadin"Oyoyo..oyoyo..! Haka take fada sai hawaye sharr kafin ta Saki hanne ta Rumgume Hamida tana Fadin"Nayi kewarku..Nayi kewarku ba adadi Hanne da Hamida..! Ta fada tana sharan kwallah suma sai da kwallar ta kawo musu suka kara Rumgumeta suna fadin muma mun yi matukar kewarki Amina. Hannunsu taja tana fadin su kariso mana Bakinta yaki Rufuwa Saboda Murna basu Tsaya a falo ba sai Dakin Data kan gadon suka yada Zango Hanne da Hamida suna ta bin Gidan da Dakin da kallo. Amina Murna yasa ta rasa me zata basu kallonsu tayi tana fadin"Kuna jin yunwa.? Ga Abincin chan da ya danmallan ya siyomin kafin ya tafi zaku ci na Dauko muku..? Binta kawai suke da kallo har ta Fice sai gata ta Dawo da shi a Hannunta Hade da maltina,tana shigowa Hamida tace"Mufa mun koshi Sai dai anjima..! Amina ta Dago tana fadin"Hanne kema bazaki ci ba..? Hanne tace"Mun ci abinci agida..Sannan ni ba abincin siya zan ci ba girkin Amarya Amina zan ci..! Hararanta Amina tayi kafin tace"ai sai ki ci abinci bayan matar gidan ta Kulle Kitchen dinta ta tafi bansan inda taje ba..! Hamida ta zaro ido kafin tace"Bangane ba..? Hanne ta karbe da cewa"Naji Hajiya na Fada ammh inaga ya Danmallam ya mata mgana ga keys din gidan gabadaya na wajen Hajiya tace nazo miki dashi..! Amina ta tabe baki batayi mgana ba, Hamida da Hanne sai binta suke da kallon kurillah Amina sai ta Tsargu ta balla musu harara kafin tace"Wai kallon fa na miye..? Hamida ta kalli Hanne suka Tsintsire da Dariya Amina sai ta sha kuni Tana Fadin"Bana son munafunci hanne da Hamida..! Hamida tace"Ba wani gulma munga kinga sauya ne Amina kin rame sannan kinyi wani sanyi kamar bake ba..Eye Amarya Amaryan Ya danmallam to ya amarcin ne da Dadi ko ba Dadi..? Amina sai Hararanta take yi kafin tace"Sai dai ango..Sannan ba Amarci ba amaro..! Gabadayansu suka saka Dariya Farimciki ya cika Amina bakinta yaki Rufuwa Hanne ce tabi Dakin da kallo kafin tace"Dakin waye wannan hala..? Amina tace"Na Sarood ne..! Hamida tace"To ba kayanta a Dakin ne..? Amina tace"Dillah kun isheni ko bari ma na Tambayi mutanen gida baku yi ba..Hamida shegen son jin kwakwaf to da kayanta zaki ganni aciki ne..? Hamida na Dariya tace"Allah ya baki Hakuri Daga tambaya..! Amina ta mata banza ta zauna kusa da Hanne tana Fadin"Hanne ya su Hajiya da Baba mallam..ke kuma Hamida yasu Mamanmu da Aba ina Jawaad su ya Zeenatu sun san an kawo ni nan..? Ta fada a marairaice kamar zatayi kuka Hanne ta tura mata Ledan Hannunta tana fadin"Kowa lafiya..Ga Sakon hajiya tace mu kawo miki Sannan tana gaisheki sosai..! Hamida ma tace"Mamanmu ma na gaisheki Aba da Jawaad duk suna lafiya sannan kowa yaji kina gidan ya Danmallam sunce duk a gaisheki..! Sai Amina ta jawo leda ta fara fito da kaya bakinta yaki Rufuwa Fadi take yi Duk ni kadai wannan..? Tana Daga kaya da Hijaban tana fadin"Wannan nasan aikin baba mallam ne..! Ta daga su yaji da kayan da Hajiya ta Hadamata tace"Wannan kuma na Hajiya ne..! Hanne tace"Kamar kin sani ta kasa sukuni komai sai tace na Amina ne..! Amina sai hawayen Farinciki Fadi take nagode nagode sosai Kafin ta kalli Hamida tana fadin"Hamida ina abun Dadin da mamanmu ta bada ki kawo min bana son wasa fitomin dashu kafin raina ya bci..! Tafada tana mikamata Hannu Har da shan kuni. Hamida sai taji wani iri ta kasa mgana Domin ita dai mamanmu bata bata komai ta kawoma Aminar ba Hanne ce ta ceceta ta Dauko mata Turaran  wutan da mamanmu ta bata ta Saka ma Amina a Hannu tana fadin"Ga shi in ji mamanmu..! Amina ta karba tana jin Dadi tace"Kai nagode sosai nayi kewarta sosai Allah Sarki mamanmu..! Haka take ta fada suna Binta da kallo Sai da tagama gani duka sannan zata kwashi kayan ta maida a ledan Hamida ta hanata ta karba tana fadin"Bari na jera miki Cikin Kwabarki..! Amima tace"Wayyo Anty Hamida i miss u..! Ta fada tana Rumgumeta Hamida ta kwace jikinta tana fadin"Ni sakeni..Dole kiyi missing dina anan bamai miki nasani..! Amina tace"Wlh kuwa kamar kinsani..Ya Danmallam ne in yayi mun masifarsa nake dan ninkewa shi baya son ganin Datti.. Hanne tace"Tab baki san kyamkyamin ya danmallam bane baya shiri da kazami sam Amina sai a Rage son jiki..! Amina ta Harari Hanne kafin tace"In an ki fa..!? Hanne ta mike tana Dariya tace"Sai a Daku..Don Wlh keda megidan ne ba ruwana.! Jin haka yasa Amina tayi shuru su kuma suna mata Dariya Hamida ta Bude Wardrope din taganshi Tsab Cikin mamaki ta juyo tana kallon Amina kafin tace"Amina kece yau da gyaran kayanki..Lalle aure dabam ne..! Amina ta tabe baki kafin tace"Bani na gyara ba shi ya gyara ni fa tunda nazo gidan nan ban saki jikina ba sai yau dana ganku..! Atare Hamida Da Hanne suka Hada baki wajen fadin"Shiwa..? Amina ta kallesu kafun ta ce"Bansani ba..! Lokaci Daya tana juya musu ido Dariya suka kwashemata da shi Hamida tace"Soyayya ruwan zuma ka sha ka bama masoyi..! Amina taki cewa komai ta kyalesu suna ta mata iskanci Hanne ta taya Hamida suka gyara ma Amina kayanta suka jera nasu suma da suka zo dashi suka tsinke da labarin makarantar su da Amina sai dai ta tambayi wance da wance sai jin Dadi take yi Amina ta Dauka Aminene ta tafi kenan sai ta gane cewa har yanzu Aminene na nan Rayuwa ce ta sakata tayi sanyi nan da nan kewar makaranta ya kamata Cikin Jin Dadi tace"Ai ranar monday nima zan koma in ji ya Danmallam..! Hanne tace"Naji yana fadama Hajiya.! Hamida tace'Yauwa gwara ki Dawo Wlh daga Unity har islamiya ba Dadi baki Amina..!. Amina tace"Nima bakusan yadda nake kuka in na tunaku bane kamar in yi Tsalle in gani agida..! Hamida tace"Wlh muma Hajiya take Lallabamu da mallam in sukaga muna kuka ko mun Damu Saboda baki nan..! Hira ce kawai ta Tsinke kamar bakin su bazai gaji ba Daga Dakin Amina Kitchen sukaje suka Bude Hanne ta Sassaka ma Amina su Samosa da danbun namanta a Fridge kar ya lalace suka kuma jera maltinan aciki Duk da akwai lemuka kala kala aciki Sannan suka Diba samosan Hamida ta soya musu. Sai alokacin sukaje sukayi sallar mangariba Amina kamar an bata Kujeran Hajji Saboda murna yau gata ga Hanne ga hamida Bayan sun idar da salla su ka koma Falo sukaci Takeway din nan suka hada da samosa suka kuma sha Tea suka Dora da maltina ransu Fes gashi akwai Wuta basu Dauke ba Amina bata manta da shan mganinta ba bayan sun yi sallar isha"i ta Dauko Zata sha su Hamida suka tambayeta tace tayi Zazzabi ne basu matsa mata ba Tunda daman sunga ta rame kadan sai suka yar da da mganarta.. Afalo suka baje suna Hira Hanne ta kuna kallo gabadaya Tasoshin na wa"azi ne dana addini Ta kashe ta Dawo ta zauna tana fadin"Na manta gidan ustazai ne nan ba"a kallo..! Hamida ta yi Dariya kafin tace"Ko agidanku ai ba kallon kike ba..! Amina tace"Gulma da iyayin Hanne mana..ku wai ina Sa"adatu ne..? Hanne tace"Tana nan mun manta da mun mata mgana mun zo da ita..! Amina ta Harari Hanne kafin tace"Wlh da kuwa daga ke har ita ba matsiyaciyar da zata shigomin gida..! Hanne ta Bude baki ita da Hamida kafin su kalli juna su hada baki suna Fadin"Uhm masu gida da miji..ammh nan ana kuka ana ba"a so..! Ashe dai ana son ya Danmallam din..!.Hanne ta karishe Fada tana Dariya Amina ta karkace baki tace"Allah ya isa Tsakanina daku..Kuma Wlh wuta..! Suka karisa mata da bal bal..! Suna Dariya ta tashi tana jefansu da filon Kujera tana fadin"Munafukai kawai..! Sai da suka gaji suka koma suka zauna Hamida tace"Wato Hanne Halin mutum zanen dutse Amina ko ta Sauya akwai wasu hallayanta da Har Abada bazata sauya su ba..! Hanne tace"Kamar Taurin kai da Tsiwa da Fada..! Amina ta kallesu ta harare su batayi mgana ita kanta ta zata ta koma Ruwan sanyi ammh Sanadin zuwansu yasa ta Fahimci Aminene bata Mutu ba Doguwar suma tayi ta Fara Farfadowa yanzu. Sai kusan goma na Dare suka je suka kwanta achan dim ma wata Hirar suka Dasa tuna irin abubuwan da sukayi suke yi suna Dariya Amina in ta Fara Dariyan mugunta har da Hawaye yau gata ga Hanne da Hamida suna kwance waje Daya Amina ce a Tsakiya Hamida tace"Wai har yanzu baki daina shegen tsoron nan ba..Ke in ba kin kwakwume mutum ba bakya iya barci..? Hanne tace"Ga ya danmallam sai ta Rika kwantamai abaya in suna barci..! Amima ta balla musu harara kafin ta juya ta yi Daidai hannunta kan Cikin Hanne kafanta kan kafafun Hamida suna Tureta tana kara Dorawa Dole suka gaji suka kyaleta Daga haka sukayi addu"an barci suka kwanta. Dayake sun riga sun saba da tashin asuba kiran sallar farko suka tashi suka yi alwala sukayi Raka"atul Fijir sukayi sallah sannan suka koma barci su Hanne an samu waje sai goma na Safe suka tashi suka shiga Kitchen sune har store sai da suka Bude babu abunda babu na kayan abinci kamar ma ba"a Dade da Zuba su. dankalin Turawa Amina tace su soya da kwai haka kuwa akayi Hamida ta Fere Dankalin ita da Amina Hanne ce mai soya kwai wajen Rabin Kires suka soya yazo yayi musu yawa ga Tea nan suka Ragesa cikin su ya cika Hanne tace"Ko zamu kaima megadi ne..? Hamida tace"Ke ina ruwanki ga matar gida batace ba..! Amina data gama shan mganinta ta koma ta kwanta saman Cafet Cikinta ya Cika tace"Uban matar gidan ce Ina ga da wannan gajerar matar yayan Hanne kike mgana itace mai gidan..! Dariya sukayi kafin Hanne tace"Kema me gidan ce wlh..Gashi Dalilin ki har mun Dankwali arziki ko ba Haka ba Hamida..! Ta Daga mata kai suna Dariya har da ta tafawa Amina tayi karamin Tsaki kafin tace"Yan iska kawai..! Sukace sun ji ba bakomai karshenta saman Dining suka maida suka rufe amjima zai musu amfani. Amina Daganan barci ya kwasheta su koma sai suka tashi Hamida ta gyara Dakin da suka kwana da Kitchen Hanne ta gyara Falo suka goge shi Tas sun nemi burner nasa Turaran wuta basu gani ba sai suka kunna na Tsinke Gidan ya Dau kamshi Sai da suka gama Amina tatashi ganin aikin da sukayi ne yasa tayi mika tana Fadin"Dadina da Kawayena akwai aiki kamar Dawakai..! Baki suka saki suna kallonta Hamida tce"Zaki ga Dawakai nan da jibi in muka tafi in kika fara yi da kanki..! Amina tamarairaice kafin tace"wai ku nan da gaske tafiyar zaku yi..? Hanne tace"Wlh Hajiya tace Ranar Lahadi idi zai zo ya Daukemu..! Amina tace"Tare dani kenan domin kafar ku kafata..! Suka Sheke da Dariya kafin Hanne tace"Wa ?ai kin zo kenan yarinya har Abada..! Hararansu tayi ta tashi ta shige Dakin nan ta gansa tas har da Tiolet Hamida ta wanke shi Tas kwanciya tayi kan gado tana kara jin Dadin ganin su Hanne Tare da ita. Su kuma basu kwanta ba Wanka sukayi Hanne ta farayi sannan Hamida da suka ma Amina mgana bayan sun Daketa tatashi Tana masifa Hanne tace"Ki tashi kiyi wanka malama sai ki kwanta..! Amina ta koma ta kwanta tana fadin"Jiya nayi wanka..Wlh ni yau bazan yi ba haba kamar wata kwado..! Basu yi mamaki ba Saboda susan Amina bata shiri da wanka Hamida tace"Amina da fa da yanzu ba Daya bane..Ke yanzu matar aure fa kazanta bana ki bane..! Ko kallonsu batayi ba Hanne tace"Ita ta sani..kishiyoyi dai har Biyu gareki kuma Duka yan gayu ne sannan ya Danmallam bai shiri da kazanta..! Hamida tace"Kuma bazamu ji Dadi ya raina mana ita ba ko kishiyoyinta su ran mata ba..! Amina ta Dago kanta kafin tace"Da ku da Kishiyoyin duk naci ubanku na Zauna Lafiya..! Hamida ta kalli Hanne suka Hada ido suna kunshe Dariyansu tana ganinsu tayi banza dasu daman Hanne da Hamida akwai gulma sun kware wajen munafunci. Haka Amina ta wuni batayi wanka ba sun gaji da mata mgana sun kyaleta da Rana basu yi girki ba sauran kwan daya rage suka ci suka kuma kara soya samosa suka ci suka hada da maltina da Daddare kuma suka Tarun ma Dambun mana suka ci suka kwanta Washegari Hamida da Hanne Dakyar suka ga Safe suka kwana Murdawan Ciki da Zawo Amina Daman akwai Lafiyan ciki bakomai ke bata mata Ciki ba. Haka ta Dinga musu Dariya Hamida tace"Hanne Amina wlh muguwace tasan cikinta ita lafiyansa kalau ba sai tace kada mu ci da yawa ba..! Hanne daman nada ulcer tana Mai da Numfashi tace"Ni sam na manta inda Ulcer ma..! Amina me zatayi ban Dariya Cikin Dariya tace"Hajiya ni tace ku kawo ma abu ammh Saboda maita ku sai an ci komai daku kadan kuka gani..ma..! Haka ta wuni yi musu Dariya Ranar ban da Tea basu iya cin komai ba sai da Daddare da suka ji sauki Zawon ya Tsaya da ciwon ciki sannan suka Dafa Doya sukayi miyar kwai suka ci suka kwanta. Washegari ma barcin su suka sha sai sha Biyu suka tashi suka karya da Sauran Doyan jiya suka gyara gidan Amina na zaune tana kallonsu An samu Amina tayi wanka jiya ammh yau kam tace bazatayi ba ta gaji sudai sukayi suka Sauya kaya Daganan aka Fara Tunanin me za"a Dafa. Amina tace Hamida tayi musu wainar Fulawar datake yi agida mai Dadi Tunda ga Yajin da Hajiya ta kawo mata . Nan da nan suka yarda da mganar Amina suka Dunguma zuwa kitchen suna neman Faluwa sun sha mamaki Fulawa buhu Guda ko kwata ba"a taba ba Nan suka Diba suka kwaba suka saka kwai ma"ishi suka yanka albasa Hanne tayi Gireting din kayan miya da suka gani Cikin Freezer harda nama wanda Amina tace soya shi za su yi Hanne tace sai dai Ferfesu basu da lafiyan ciki..Amina na Dariya tace"A soya yafi Dadi..! Hanne tace"Muguwa muguntarki ta kare miki Amina..! Sai Dariya Amina ke kyatatawa har tana Hawaye. ******** Mamanmu na kitchen tana soya kifin da Aba yaba Jafar ya kawo Dazu wayarta Dake tsakar gida kan Tabarma ta Dau kara alamun kira Gidan ba kowa sai ita kadai Hamida suna gidan Amima jawaad kuma sun tafi Hadda. Burin Mamanmu ya cika ita kadai ke juyi a gidan Sa"idu sai abunda tace akeyi sai kuma an nemi Shawaranta. Fitowa tayi da Sauri bayan ta juya kifin Dake kan gas kada kafin ta Dawo ya Kone. Tana Daukan wayanta taga Madina ke kiranta sai da gabanta ya fadi Bata rai tayi afili ta Furta"Har Abada madina baza ta barni na Huta ba Haba wannan kawwazzaba dame tayi kama mtswww..! Ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta Daidaita kanta ta Daga kiran tana Fadin"Buhun Sikari baki Farin banza ba..! Dagachan bangaran Anty Amarya ta Katseta da Fadin"Ba bu abunda zaki Fadamin Ya sanyayamin rai Dayyaba..Ki ma yimin shuru kawai..! Mamanmu ta marairaice kafin tace"Me kuma ya faru..? Allah yasa ba kwabarmu ce zatayi Ruwa ba..! Anty amarya tace"Kwabata dai Zatayi Ruwa Dayyaba...aike kin samu abunda kike so shiyasa kika maidani Wata Shashasha ko nema na baki yi Dayyaba Tunda na gama Taimaka miki kin samu Sa"idu a Hannunki ni kuma kin kasa taimakamin nawa Burin ya cika ko..? Ni ban raba Maallam da Sa'idu ba sannan ta bangaran Sakina har yau ba wani mgana mai Dadi..! Mamanmu ta Harari wayar kafin tace cikin karyewan murya"Haba Madina meyasa kin cika gaggwa ne..? Kin Tsaya na gayamiki irin kokarin da ni ke nan ina yi miki akan abubuwa su Daidaita kuma da kike Fadin na Samu Sa"idu ai ban ga samunsa ba Domin har yanzu akwai rina akaga Hajiya da mallam sun sha gabana..mganar Sakina kuma ai mun gama mgana kince zaki sa ka mallam yasa turama danmallam son ko ya tafi sai ya Dawo ya Dauketa sannan mu na Fatan Zata samu ciki kuma zai zauna Zata Haifesa da yardan Allah mganar Shegiyar yarinyar nan kuma Amina sai dai su mallam su gaji su Raba bazai Taba wani amfani ba..! Sai alokacin Anty Amarya taji ta dan Sauka Cikin Saukan Numfashi tace"Dayyaba ni Hankalina yaki kwanciya gani nake yi abubuwa duk suna ta lalacemin Tsarina duk ya lalace..Umar din ya tafi ni Kawai Burina ya Dawo ya Dauki Sakina su koma,in har ya tafi mallam yace ba lalle ya dawo nan kusa ba kinga mallam da Hajiya haka zasu gaji da ganinta ahaka su raba auren daman wanchan balarabiya Hoto ce itama in ta gaji zata kara gaba ne.. Mamanmu tace"Sosai ma ina amfani Zama da miji Hotiho ba wani amfani ina mai Tabbatar miki bazata zauna ba..Ki kwantar da Hankalinki Saura Kiris burinmu ya cika kada ki manta Sakina ba Juya bace tana samun cikin yana Barewa ne..! Anty amarya tace"Dayyaba shine abun Damuwata ko an samu cikin baya Zama na fara Tunanin akwai wani a kasa..! Mamanmu tace"Ko..? Kanar na menene..? Anty amarya tace"Ciki wajen sau Hudu da an sanu sai ya lalace anya Dayyaba..? Mamanmu tace"To kin sa malam ya Duba mana kuwa..? Tace"Eh ya Duba yace bai ga komai ba..Ammh ni haka kurum nake ji akwai wani wanda muke Tufka Daga Gefe yana mara warwara ko shakka bana yi.. kinsan daman ya taba Fadamin acikin matan mallam akwai wacce itama bata zauna ba..bai dai Fadamin sunan kowa ba. Mamanmu tace"to wa kike Zargi..? Anty Amarya tace"Cikin matan mallam ne dai..Ko Haj.Nasara ko Hj.Uwani..Akwai wacce acikin su bata so mu cimma namu burin..! Mamanmu ta zaro ido kafin tace"in ma sune to saboda mene..? Anty amarya tace"Saboda cikar Burinta itama..Kamar yadda muke son mu cimma namu Burin..! Mamanmu tace"Tabdijam akwai kura Tsugunno bata kare mana ba..! Ni fa basu nake zargi ba ina Tunanin ko dai Hajiya ce bata so Sakina ta Haihu..? Anty amarya tace"Ba Hajiya bace..Bata yar da za"ayi ta hana Sakina Haihu wa kada ki fa manta Umar D'anta ne..zata fi kowa son ganin kwansa a duniya..! Mamanmu ta jinjina kai kafin tace"Kuma fa hakane..! Ni ban ma taba kawo wannan Tunanin ba sai da kika Fada na gane zai iya Faruwa..! Anty amarya tace"Ai ki bar mugu..Bai da kama Dayyaba..Da mugu nada kama da Tuni Sa"idu da ya"yansa basu baki Dukkan yarda ba..Da mugu nada kama da Yaya bata taba Sakin miki Ragamar ya"yanta ba har Abada..! Mamanmu ta bata rai kafin tace"Bangane ba..? Ki sa min jaye mugaye zaki ce..! Anty amarya tayi wata Dariya kafin tace"Ban kai ki mugunta ba Dayyaba. ina mai kara gayamiki ban kai ki ba..Domin ko ni sanda kika zomin da Fuskarki ta Dayyaba domin mu Hada Hannu na Girgiza ballatana Sa"idu da ya"yanku..? Ina mai Tabbatar miki kiji Dadinki yanzu ammh in alalan geren mu ya tashi yin Ruwa da Tsami wlh naki sai yafi Nawa Tsamewa..! Mamanmu tace"Da izinin lahi bazan ga haka ba..Ni Dayyaba Nasara na sani ba Faduwa ba Madina..! Dariya tasake yi kafin tace"Muna fatan haka yanzu ba wannan ba yaushe zamu hadu..? Ya kamata mu sauya Tsarin mu sannan mu san ta yadda zamu gano wanda ke kokarin batamana aiki..! Mamanmu tace"Ina so mu hadu bana samun Lokaci ne gida ba kowa sai ni kadai..Hamida bata nan tana gidan Amina..! Anty Amarya ta Zaro ido kafin tace"Wata Aminar..? Mamanmu ta tabe baki tana fadin"Wacce kika sani mana..Bakisan suna gidan Amina ita da Hanne ba Tun Ranar alhamis da yammah Hajiya ta turasu..! Anty Amarya ta mike Daga Zaunen Datake gefen gadonta tana fadin"Kan burauba..Bansani ba..Naji dai jiya Sa"adatun na fadin bata ganinsu a Hadda ban maida mganar mai ma"ana ba shiyasa ban bincika ba..Na Shigesu Dayyaba Sakinarma tun aranar da Umar ya koma tana Dutse..! Mamanmu tayi shewa kafin tace"Au to..Aiko tayi wauta suna chan ta bar musu gidan suna Yadda suka ga Dama..! Anty Amarya bata jira cewar Mamanmu ba ta yanke kiran ta bar Mamanmu da Hararan waya Lokaci Daya ta Ijiyeta nan kan Tabarma ta koma Kitchen tana fadin"Kawai kin zo kin Tsaidani kan mganar banza..Badai nawa Burin ya cika ba..Ban Damu ba..In dai ni na samu abunda nake so Uban kowa kada ya samu..! Bana kaunar Amina ta Dawomin gidan nan zata lalatamin Tsarina Yadda tatafi tatafi kenan har Abada Shegiyar yarinya mai kama da Uwarta..! Haka tayi ta manganganu ita kadai.tana ciga da suyan kifinta Duniya tayi mata Dadi. Anty Amarya kuwa Lambar Sakina ta Kira sai da kusa katsewa ta Daga ko Sallamanta bata amsa ba ta fara Fadin"To shashassha..kina nan kwance ga Amina chan da su Hamida suna yadda suka ga dama da gidanki. ! Sakina na kwance ne sai da ta mike tana Fadin"Bangane ba.? Nan Anty ta shaida mata abunda mamanmu ta fadamata Sakina tace"Kuturun uba.... to ubansu zasu ci na kulle ko"ina har Kitchen fa..! Anty Amarya kamar ta Zageta haka taji cikin Tsawa tace"Dayake ke kadai ke da key din gidan ba..? Karki manta Uwarsa ma na dashi kuma na tabbata sun tafi dashi ki cigaba da zama agidan da nayi Burin ki Rayu ke kadai tun ba"a je ko"ina ba yana neman ya zama ba naki ba..! Daga haka ta Datse kiran tana Faman Huci Dagachan Dutse kuwa Sakina ta Diro Daga kan gado ta Fada wanka sai yanzu ta Dawo Cikin Hayyacinta. Allah ya taimaketa akwai wani yayanta zai taho kano shi ya Daukota har Gumel har kofar gidanta ya ijiyeta sannan ya wuce alokacin Shida na yammah har tayi san da ta abuga get din megadi yazo ya Bude mata bata Tsaya amsa sannu da zuwansa ba taja akwatinta ta nufi Cikin Falon. Amina da Hanne suna Zaune Saman Cafet hamida na Saman kujera suna Hira sannan ga filets nan da suka gama cin wainar Fulawarsu nan da Ferfesun naman rago da sukayi ga Kofuna ga abun maltinan da suka gama sha Falon dai kaf ba Kintsi  Saboda  tunda suka gama suka koma gefe suna Hira sun ma manta yau zasu koma gida Tsabar yadda Rayuwa tayi musu Dadi gaddamace ta Sarke Tsakanin Hanne da Amina kan lokacin Bikin su ya Abida Amina na Fadin yadda Hanne ta manne ma Sa"adatu saboda yar"uwatance ita kuma Hanne tana kokarin nuna ma Amina Daga su har Sa"adatu duk Dayane hamida kuwa bata sako bakinta ba sanin Halin gaddaman Amina ko bata da gaskiya bata saki. kwata kwata basu san Sakina ta Shigo ba ashe ta Dade Tsaye taba Bin Falon gidanta da kallo yadda ya zama. Ranta in yayi Dubu ya baci akwatin Hannunta ta saki ji kake garam lokaci Daya ta Rike kugu tana fadin"Kutumar Uban chan Falo na ne ya koma kamar gidan abinci? Lalle yau zaku gane baku da wayau duk sai naci Ubanku daga ku har kazamar data jawo ku..! Ta karishe fada tana Cire gyalenta ta Ci Darama dashi Tana jifan su Amina da wani matsiyancin kallo wadanda sai alokacin suka san da wanzuwarta afalon Hamida da Hanne ne suka Tsorata Amina kuwa ko ajikinta itama kallon rainin ta maida ma Sakina kafin ta tabe baki ta kauda kai. Hanne ce da Hamifa suka mike da Sauri Jikinsu na rawa Hanne na faman Fadin"Sannu da zuwa Anty Sakina..! Ita kuma Hamida ta fara Tattara filets din tana fadin"Kuyi hakuri yanzu zamu share mu gyara ko"ina..! Sakina ta kariso Falon tana Hararansu Lokaci Daya tana fadin"Dilla kumin shuru..uban wa ya baku izinin zuwarmin gida batare da sanina ba.? Hannu hamida tabi da kallo kafin tace"Kan uba har kitchen dina ma kuka Bude kuka shiga kuna min kazanta..? Yau zan ga wanda zai Rabamu daku acikin gidan nan..! Amina mamaki kamata yayi ganin yadda Hamida da Hanne suke bata Hakuri jikinsu na rawa sai Faman Zaginsu take yi ranta ya baci ta Dauka tayi sanyi ashe batayi ba batasan Sadda ta Mike ba sai jin muryanta sukayi tana fadin"Dillah ku daina bata Hakuri..Kun zo din ai ba gidan Uban kowa bane nan..Gidan mijina ne kamar yadda yake gidan mijinta sannan kada ta manta nan din gidan yayanku ne ko sama da kasa Zata Hade shi din jininku ne wata fa..?Yar karo ce..Saboda haka ku saki jikin ku ku Wala ba wacce ta isa ta Daga muku Hannu ina gidan nan wlh..! Ta karishe Fada itama tana Hararan Sakinar da manyan idanuwanta. Hamida da Hanne suna ta kyafta ma Amina ido bata bi ta kansu ba Sakina ta nuna kanta tana fadin"Wai dani kike..? Amina ta karkace baki tace"Ban kira suna ba..Ammh in kin Tsargu ba ruwana..! Sakina taji ranta ya kara baci Tayi kukan kura tayi kan Amina tana Fadin"Yau sai naci Ubanki acikin gidan nan.! Su Hamida suka shiga Tsakani suna bata Hakuri Hanne sai ta Fara kuka tana fadin"kiyi hakuri yanzu zamu gyara ko"ina Hanida ko ba"a zo Daukan mu ba yanzu zamu tafi..! Amina datayi ke Tsaye Cikin mamakin ko Sakina Dukanta zatayi tayi Shewa kafin tace"Wlh badai ubana ba..kin gama Zagin Ubana na kyaleki..! Sakina tace"Sai nawa Uban ko..? Amina ta Tura dankwali Gaban goshi kafin tace"To nidai ban ce ba..Ko banza nasan Darajan tsohon wasu..! Sakina ta Harzuka haka take Zagin Amina har tana fadin"Badai ke yar iska bace ko...? Bari  zan kira  habibin Wlh bazan iya Zama Da kazama irin ki acikin gidana ba. ! Amina tace"Gidanki ko gidanmu..? Malama ki kara Min jaye..! Mu uku keda wannan gidan Dake da ni Amina da yar balarabiya baki da kuma yadda zaki yi..! Ran sakina ya baci tana mamakin yadda yarinya karama ta zauna tana Fada mata mgana Hamida da Hanne na Faman bata Hakuri suna fadin zasu tafi. Amina ta kallesu tace"kudai wlh bazanye ne..To uwarki ce ita..kun zauna kuna ta wani bata Hakuri tana Kara Zagin ku..bazaku gyaran ba tayi abunda zatayi..! Hanne tace"A"a Amina mu muka bata bari mu gyara mu zo mu tafi..! Amina tace"In kun tafi Allah tsinan naga mai fita agidan nan..! Ta fada tana wani juya ido kafin taja Tsaki Sakina taji kamar tayi Bindiga ta koma ta Dauko akwatina Kamar Kububuwa ta wuce ta Bude Dakinta ta Shiga tana Tunanin yadda zata yi Biji Biji da Amina Umar ya ja mata raini wajen wannan yarinyar. Tana shigewa ta banko kofa Amina tayi Tsaki ta koma ta zauna hakanan taji Ranta na kuma kamar tayi Bindiga haka take kada kafa tana Girgiza jikinta Hamida da Hanne suka Bita da kallo basu tankata ba Azaton su Jidalin Amina ya ragu ashe karuwa yayi basu sani ba hamida ta tatattara komai Takai kitchen ta Hada wanke wanke Hanne kuma ta Fara gyaran Falon Amina na Zaune tana kada kafa Ranta na mata wani Zafi kamar ana Hura mata wuta ita kanta Hanne bata taba ganin Amina tayi irin wannan ba,Shiyasa bata tankata ba itama batace mata komai ba..! *Janafty**TFZB2009* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Hamida da Hanne cikin rawan jiki suka gyara komai Hanne ta share falo ta goge shi tas hamida kuma ta kintsa Kitchen din ta wanke kwanukan da suka bata ta goge kitchen lokacin har an fara sallar mangariba a masallatai yasa suka wuce dakin da Amina take suka isketa Ta fara salla,suma alwalan suka Dauro suka zo suka jera da Amina suka tada salla har suka idar Amina bata musu mgana ba suma ganinta cikin wannan yanayin yasa suka mata shuru. Tana ganinsu suna hada kaya sai ranta ya kara baci Haka kurum take jin wani zafin zuciya wanda ko a baya ba irinsa take ji ba tasan dai tana Saurin Hasala ammh Bata da Saurin Harzuka kamar na yanzu sai ta Danganta haka da Tafiyar su Hanne Abunda bata sani ba wannan zafin zuciyar da aka kara mata ne maimakon tayi shi ga wanda akayi Domin sa sai ya kuskuremai Bashi a kusa da ita sai abun zai tsaya ga wanda ke kusa da ita da kuma wanda ke bata mata rai a kusa. Sallar da tayi ne ma yasa taji dan Dama Dama ammh ranta yagama baci da abunda Sakina tayi mata yau ji take yi daman ta Tabata da sunan daambe da ta gane bata da wayau a yadda take jin kanta da karfi sai sun kwashi yan kallo domin karfin jikinta ya Dawo sannan ta warke kasanta ma batajin wani ciwo ruwan zafi da mgangunar nan sun tainaka mata wajen dawowa da ita Daidai shiyasa ko su Hanne basu Fahimci komai ba tota ina ma zasu gane..? Amina ta fi su Budewar ido kan irin abubuwan nan saboda ita tana karance karancen Littafan hausa su kuma fa dukum ne su basu riga sun san wasu abubuwan kamar yadda ta sani ba. Suna cikin Hada kayan ne suka ji knooking daga kofar falon Amina ta Dago tana kallonsu hanne ma ta kalleta kafin ta mike tana fadin"Ina ga Idi ne..! Ba jimawa sai ga shi ta dawo tana Fadin"Shine Hamida..Hajiya tace maza maza ya Daukomu gobe akwai makaranta..! Hamida batace komai ba ta Zura Hijabinta haka Hanne suka Dauki Ledan kayansu Hamida ta kalli Amina Dake Zaune tana kallonsu tace"Amina mu zamu tafi.. Amina tayi kamar bata ji su ba kuka taji yana neman tasomata Hanne ce Cikin karfin hali tace"Kiyi hakuri ai gobe zamu biyo mu Dauke ki..Ki shirya da wuri..! Hamida da Hanne suma karfin hali suke kada su yi kuka ganin yadda Amina Tayi ganin ta musu banza yasa Hanne taja Hannun Hamida suka Fice Daga Dakin Amina na ganin haka ta mike Zaraf ta biyosu falon tana Fadin"Yanzu wai tafiya zaku yi..? Ku bari gobe mana basai mu tafi makarantar tare ba..! Hanne tace"To ai uniform din mu na gida kuma kinga Hajiya ce ta aiko a Daukemu..! Amina bata kara mgana ba kawai ta Juya ta koma Dakinta ta Zauna gefen gado sai kuka wiwi kamar wacce aka Daketa Tana jin karan Bude get tasan su Hanne sun tafi kawai sai ta kwanta Saman Cafet ta cigaba da kukanta kuka mai Cin rai rabin kukan na kewa ne da Zaman kadaici rabin kukam kuma na kuncin zuciyar da ta rasa Dalilinsa wani Kululune ya Tsaya mata  arai yaki wucewa tana Tunanin in tayi kuka zata samu sauki. Sakina kuwa ko da ta shiga Dakinta ko gani batayi Ranta ya gama baci tana Tunanin karamar yarinya kazama kamar Amina ce zata tsaya tana Zaginta Lalle sai ta gane bata da wayau Zata Kira Habibi ta Fadamai Rashin kunyar Amina sai ya Dauki mataki akanta domin ita bazata iya Zama da ita haka ba Allah nagani. Wayarta ta Dauka ta kira Lambarsa ta Saudiya ta shiga sau biyu bai Dauka ba ta Duba Lokaci bakwai Saura na Dare su achan zai zama tara da wani abu kenan bai isa ya kwanta ba Duk da Tun da ya tafi sai jiya ta kirasa suka gaisa bai tsawaita mganar ba yace mata yana Aji ne in ya koma gida zai kirata kuma bai kara kiranta ba. Ganin bai Dauka ba Sarood ta kira ita kan ta Dauka suka gaisa take tambayanta Habibi ta sanar da ita baya nan ya tafi Cikin gari masallaci Har yanzu bai shigo ba. Sakina ta gyara zama tana cema Sarood  ta rokar mata Umar don Allah ya zo ya Dauketa yaki komawa da ita Madina Sarood tace mata kawai zata mai mgana da haka suka rabu Sakinar ta Lura kamar Sarood din bata son Wata Doguwar magana da ita tana sota kawomata Labarin Amina sai tayi Saurin Dakile mganar da cewa Tana girki ne kada ya kone.. Abunda bata sani ba ita kanta Sarood din tunda ya Dawo sama sama suke domin daman kafin su tafi sun yi Rigimar tahowa tun Tarkon da Sakina ta Hadama mata ita kuma ta Fada har sai da Mahaifinta ya shiga mganar To kishi da kuma takaicin abunda ke Faruwa Tsakaninamsu ya Rufemata ido gani take yi yana chan yana jin Dadinsa da Sakina da Amaryansa ita kuma ya barta anan ita bata ga Tsuntsun ba ga Tarko shiyasa taso ta Biyosa batare da sanin ko iyayanta nata ba Sai dai kalmar daya fadamata na sai tazo ne ya bata tsoro yasa ta fasa zuwa Tasan Halinsa kaifi Daya ne. To kwana Hudu Tsakani ya Dawo Tunda ya Dawo ta sakamai Rigimar ita bazata yarda ba, da gangan yake yi Ba wai bazai iya kadaicewa da ita bane meyasa shi da Sakina Lafiya kuma gashi har yayi amarya itama tasan ai lafiya kalau meyasa sai itane bazai iya Raba ba . Alokacin akwai gajiya tare da shi,Shiyasa bai biyemata ba sannan kuma ta wani Fannin tana da gaskiya ta wani Fanni kuma bata dashi Saboda ai ba Laifinsa bane sai da yace su sanar da manya mganar in da cutarwa tace taji ta gani sai kuma Daga baya ta Bullo da wata mgana Ba domin ma Su din ba su cika yarda da Sihiri ba, da haka yasan zatace Duk da shima lamarin ya bashi mamaki ammh bai Taba Zargin wani ba ga Allah kadai ya Dogara shiyasa yake Neman waraka daga garesa..! ****** Amina batayi wani barcin kirki ba Saboda kuncin zuciya sannan ta dinga Tsorata acikin barcinta da Daddare barcinta sai ya zama sama sama ne tasan a gida bata iya barci sai acikin mutane ammh Tsoronta bakai na yanzu ba ko ya ta kwanta ta fara barci sai taji kamar ana Tabata sai ta Tashi a Firgice daganan sai kuka in tayi addu"a ne ta koma sai barcin nata yadan yi Tsayi. Yau da wuri tatashi ga rashin barci sannan tasa ka Komawa makaranta aranta yau din tayi wankanta sannan tayi sallar asuba Saboda zumudi Amina ko Karyawa bata tsaya tayi ba ta Saka Uniform dinta dake goge Daman Hamida tun agida ta goge mata ta fito da Jakar makarantar data Islamiya ta tura ta islamiyar da Hijabin cikin jakarta saboda chan zata zauna sai sun dawo daga islamiyar yammah Ta saka Safa da Takalminta ko Falo bata fita ba kuma bata ji motsin Sakina ba. Tun bakwai na Safe ta gama shiryawa tana zaman jiran su Hanne cikin kudin da Danmallam ya bata ta Dauki Dubu Daya yau zasu ci su sha ita dasu Hanne su Sa"adatu kuma Sai dai suga anayi yan bakinciki. Har takwas saura sai ta fara Tunanin ko dai sun tafi ne sun barta ayadda tayi Shirin zuwa makaranta yau sai ta kama gabanta don bazata fasa ba Kamar daga sama taji Hon din mota dayake motar tasu akwai kara bata gama Tantancewa ba taji Muryan Hanne na Kiranta tayi Zaraf ta Fito Daga Dakinta bayan ta kulle kofar Hanne na ganinta ta washe baki Tana Fadin"Amina Aminene ikon Allah..! Amina tayi Fari da ido kafin tace"Kwarai ba dai ta mutum ba sai ta Allah wlh..kainuwa Dashen Allah .! Hanne tayi Dariya kafin ta kalli jakar Amina Datake neman rinjayanta tace"Meye kika sako ajakar ko Abun Dadi ne na amare..? Tafada sanda suka fice Daga Falon Amina tace"Uban na Amaren ne..Hijabin islamiya ne da Jakata..! Hanne tace"Kin ga kuwa Sai da Hajiya tace na Tuna miki kada ki manta..! Amina tace"Ina zan manta..yarda na kosa na ganni a makaranta..! Hanne na Dariya yace"Yau watarana Amina na murna zata makaranta..! Amina ta murguda mata baki kafin tace"Yau Litini to munafuka..! Hanne na Dariya suka fita Daga gidan Dayake Idin bai shigo get ba Tunda suka fito yan motar suka sako ido suna bin Amina da kallo musamman Sa"adatu. Amina na shiga motar Idi kawai ta gaisar banda su Akilu da suka wani kame agaba Zubairu ne yace"Amina ba gaisuwa..? Wani kallon Tara saura kwata tayi mai kafin ta Dauke kanta Akilu yace"Kaima da wata mgana..So kake ta raina ka. Ta karo iskanci mana tana ganin ta matar ya Danmallam..! Tana jinsu ta musu banza kusa da Hamida ta zauna tana fadin"Baki ganni bane ko kimin oyoyo..! Hamida tace"Tunda kika shigo nake washe miki baki kikayi kamar baki ganni ba..! Ta Rumgume Hamida tana fadin"Sorry ban lura ba..Wata ke min kallon banza na maida mata.. Ta fada tana Hararan Sa"adatu Dake kallonta Daga sama har kasa Sabeeha kanwarta ce tace"Ya Amina daman gidan Anty Sakina kika dawo..? Amina tace"Eh Sabeeha baki sani ba..? Yarinya ta girgiza kai kafin tace"Shiyasa bana ganinki..! Sa"adatu ne ta Harari kanwarta Shiyasa tayi shuru Hanne kusa da Sa"adatu ta zauna Amina ta kalleta Cikin mamaki kafin tayi ma Hamida rada tana fadin"Hanne fa munafuka ce..Dubeta ita adole mai yar"uwa..! Hamidai dai Dariya tayi batace komai ba. Har suka isa makaranta Amina bata kara ma Hanne mgana ba da aka Sauke su ma ana Assamble ne Hanne na ma Amina mgana tayi kamar bata jita ba ta Nufi Zainab isa Dake Faman Daga mata Hannu Amina bakinta yaki Rufuwa ganinta a makaranta ashe ma karatun wani Lokaci zuwansa Rahma ne sai da aka kaita wannan kurkukun gidan nan ta san da haka. Ba dadewa aka gama Assamble din suka Tafi aji yan ajin su Amina sai mata ya jiki suke saboda Rashin Lafiya su Hanne suka ce tayi Saboda Hajiya ta gargade su kada su sake suce aure tayi har Sa"adatu sai da ta kira ta ja mata kunne. Gabadaya Amina sai taji ta kamar a aljannah ta saki jikinta sosai ana tashi Break taje ajinsu Hanne ta ta jasu Shagon makaranta ta siya musu banza ta siya musu wofi Hamida ke Fadin"Amina ina kika samu kudi haka.? Amina ta Kalleta tana shan Nutrimilk din data siya tace"Mijina..!. Tafada Cikin gatse Hamida da Hanne suka kalli juna kafin su Tsintsire Da Dariya Hanne tace"masu miji..To tunda ya bar mana kudi zamu ci mu sha ko Hamida..!? Suka tafa atare suna Dariya Amina tace"Kuma kika bama sa"adatu abuna Alah ya isa Hanne..! Hanne tace"kai wannan kiyayyar Dake Tsakaninki da Sa"adatu bansan irinta ba..! Amina ta wuce fuu tana fadin"Kika dai bata in na yafe Allah tsinan kin ji ma na fada miki..! Daga haka ta koma ajinsu ta siya ma zainab maltina ta bata,Daman sun fi Shakuwa tun Jss1 tana juran Jidalin Amina Sa"adatu na shigowa Amina sai da ta kalleta sannan ta ga Nutri dinta tana sha aranta tace bakinciki kan sai dai ya kasheki Amina kam tafi karfinki haka kurum ita Amina bata kaunar sa"adatu kuma hakan ya samo asali ne da yadda ta Tsani Anty Amarya. Sai biyu da rabi Idi yaje ya Dauko su suka koma gida mota na Tsayawa Amina ta Dira sai gida Hamida da Hanne suka bita da kallo Akilu ya rike baki yana fadin"Ya dammallam dai an Hadasa da kwaila..! Shi da zubairu sai Dariya suke yi. Amina da gudu ta shiga gida tana Kiran sunan mamanmu da Karfi da Jawaad taci karo ya fito daga Kitchen yana shan ruwa yana ganinta ya jefar da Kofin hannunsa ya Nufeta yana Fadin"Yaya Amina oyoyo.! Amina ta jefar da Jaka ta Cafeshi Taso ta Dagasa sama ne taji yafi karfinta ta Sauke shi tana fadin"Jawaad din yaya ya kara girma..! Cike da Tsantsan murnan yaga yar"uwansa yace"Ya Amina ina ta kuka da baki nan ina ta cema Aba ya kaini wajenki yace ba yanzu ba..! Sai Amina taji kwalla ta taso mata ta Kama Jawaad ta Rumgume cikin wani yanayi take fadin"Watarana zaka zo inda nike kaji jawaaad..! Kai ya gyada mata ita kuma tace"Daga yau kullum zaka dinga ganina kaji ko..? Baki ya washe yana fadin"Da gaske..? Jakarta ta Dauko ta Zage ta fito da sweets din data siyamai ta bashi ya amsa yana ta Tsalle tana Dago kanta suka Hada ido da mamanmu da tunda ta shigo da Kwakwazo ta jita tana kuryan Daki tana Faman Lissafim kudin da Aba ya bata yau da Safe na siyan Turaranta Datace mai ya kare ba gaddama ya tambayeta kudin tace mai 10k ya ciro ya bata,ita kam yanzu bata cikin wani bakinciki Burinta ya cika in ma bai cika ba kadan ya Rage mata. Alokacin da Amina ke mgana da Jawaad hararansu take yi tana Tsine musu acikin ranta in ma tana da wata Damuwa sune su Jaleela suna gidan auransu sai su Dade basu zo ba Jawaad ne da Jafar  wanda har yanzu Ta kasa shan gabansa ta Lura shima a Tsaye yake ammh zai yi Laushi Tunda Sa"idu yayi Laushi Amina Datake murnan ta Rabu da ita kuma sai gata Koda yake daman Ai Jiya ta shiga wajen Hajiya gyara kanta Tunda Hamida ta Dawo ta bata Labarin sha tara na arzikin da mallam da Hajiya suka Hadama Amina sai taji ta muzanta kafin Hajiya ta fara Dora zargin akanta yasa ta shiga tana mata kame kamen bata san da zuwansu Hamida ba shiyasa bata siya mata komai ba ammh Zata  siya mata su humra ta kai mata da kanta kudi ne bashi a Hannunta shiyasa. Hajiya babba bata kawo komai aranta ba sai ta nuna ma Mamanmu bakomai kada ta Damu Amina bata bukatar komai yanzu to anan nema Hajiyar ke fadamata Tsarin Amina zata koma makaranta sannan nan zata Dinga wuni sai yammah in sun Taso islamiya sai idi ya maidata gida. Amina na hada ido da Mamanmu tayi Falati da Jakarta ta Nufeta cikin murna tana fadin"Oyoyo mamammu..! Itama ganin haka sai ta saki Ranta Bakinta har kunne ta Rike Amina ta rumgumeta tana fadin"Oyoyo yata Amina..Nayi kewarki..! Amina tace"Nima haka mamanmu..kullum sai nayi kuka in na Tuna daku ina Aba..! Ta fada tana Sakin mamanmu Daidai Lokacin da Hamida ta shigo. Mamanmu tace"Aba dinku yana Lafiya Amina ya bakon waje..? Hamida ta fadamin irin Dibar albarkar da Shegiyar Sakinar nan tayi muku..Nidai ki Daina kulata kada ta nakasamin ke baki kaita karfi ba..! Amina tayi Dariya kafin tace"Haba mamanmu ita din banza..?Wlj ba cika baki ba ni Amina Aminene nafi karfinta wlh ta taba nin watarana Tagani..Sai ta raina kanta..! Mamanmu ta saki baki tana kallon Amina kawai gabanta na Faduwa ashe bakinta bai mutu ba jiya da Hamida ke fada mata ta sha mamaki ta Kira Anty Amarya sukayi mgana tace kokarinta Daya Umar yazo ya tafi da Sakina sai Amina taci iskancinta ita kadai Mamanmu tace tabbas..! Hamida ita ta Dauke ma Amina Jaka takai Dakinsu Mamanmu kuma ta shiga kitchen ta Debo mata abiinci da ruwa,Ta sakata gaba kamar ta bata a baki sai Dukan ruwan cikinta take yi ko zata ji wani abu Hamida Dakin su ta shige Tayi sallah ta Debo abinci dama ta shigo Dakin da suke korarta Mamanmu tayi saboda tana so sai taji yanayin zaman Amina da Danmallam kafin ya koma Madina. Shiyasa Amina na cin abincinta Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Ni ko Amina Allah yasa Danmallam dai kafin ya koma bai miki komai ba ko..? Gaban Amina ya fadi ta Dakata da cin abinci ta Dago tana kallon mamanmu Cikin mamaki ita tunaninta ko ta Fahimci abunda ya shiga Tsakaninsu ne yasa cikin sauri tace"Name ne mamammu..? Ni babu abunda yayi min..! Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Yauwa Allah yasa ma baya shiga Harkanki..! Amina tace"To ina ruwana dasu..! Ni har ya tafi ma ban gansa ba..! Ya cika fada haka yayi tamin masifa ranar da muka tafi Daganan..! Mamanmu taji Dadin haka yasa tace"To ai kin gani irin wannan abun na Gudar miki yasa naso araba wannan auran kika ki bani Dama..! Amina tace"Bakomai Mamanmu hajiya da Mallam sun wuce komai a wajenmu..Sannan ni nayi alkwarin Aba bazai kara bacin rai saboda ni ba..! Mamanmu tayi shuru tana kallon Amina kafin tace"Hakane kuma ammh ki Daina tankama Sakina Da shi din ne dai da nace ki yi tamai Fitsara har ya gaji ya sako min ke na aura miki mai sonki Aminullah..! Amina tayi Tsai tana kallonta sai taji bata ji Dadi ba datace a asakota Saki fa ba Kyau ance sai al'arshin Allah ya girgiza sannan ita karan Hauka ya Cijeta  da zata ma ya Danmallam rashin kunya sai dai Sakinar itace Daidai da ita. Daganan bata kara mgana ba Mamanmu kuma sai janta take da Labari Amina ba domin Rokon Umar ta Boyema mamammu komai ba,,sai saboda Tana jin kunyarta da Tunanin in taji abunda ya faru zata yi mata Fada kila ma ranta ya baci shiyasa bata gayamata ba.. Ita kuma mamanmu adole Allah zatayi ma wayau batasan bakin Alkalami ya riga ya bushe ba,Haduwar jini ta Haifar da gudan jinin da zai yi Sanadiyar Fallasan duka sirrukansu. Amina sai da taci ta koshi tayi sallah kan gadonta ta fada tana Fadin"Nayi kewarka gado na..! Take fada tana Shafa gadon Hamida na kallonta kafin tace"Sai a Daukesa akai miki chan..! Amina tace"Da naji dadi kuwa..! Hamida ce tace"Hajiya sai da tambayeki fa Amina..! Amina ta mike Tana fadin"Bari na shiga..! Uniform dinta ta cire ta sauya dana gida akwai wasu cikin kwabarta na gida hamida ta rakata gidansu Hanne. A bakin shashen Hajiya suka ga Haj.Uwa tunda taji zuwan Amina ta kasa zama tana ganinsu ta washe baki Tana fadin"Ga Amina Amarya..! Sai kunya ya kama Amina ta Dukar dakai tana gaisheta Hannu taja tana Fadin"Au bazaki shiga Shashena mu gaisa ba..? Yar"uwarki ma Umaima bata da lafiya jiya ko barci bamu yi ba..! Amina tace"Allah sarki bansani ba..! Hamida tace"Mun manta ne bamu Fada miki ba..Jiya kwana tayi ihu mallam da su ya Akilu suka kwana suna mata karatu..! Amina taji Tsausayi ya kamata sosai Ta kalli Hamida tana fadin"muje na Dubata Hamida..! Da Sauri Hajiya Uwa tace"ai ita sun shigo sun dubata da Safe..Ke dai muje Diyata Amaryan Umaru Faruqu..! Tafada tana jan Amina Hamida sai bata bisu ba tunda taga kamar Haj.uwa ta fi son Amina ita kadai. Sai ta juya ita ta shige Shashen Hajiya babba. Kafa kafa Haj uwani ta dinga yi da Amina har shashenta kai tsaye kuma har Dakin da Umaima ke kwance tana barcin Wahala duk ta kara ramewa sai Dogon wuya Amina ta kalleta Cikin Tsausayinta tace"Allah ya bata lafiya..! Haj Uwani ta kalli Umaima sai ta fara Sharan kwallah kafin tace"Wlh ciwon nan na Umai ya fara damuna Sa"o'inta duk suna Dakunansu har da ku ma kannen bayanta ita ko kalli Halin Datake ciki..! Amina tace"sai hakuri Allah ya bata lafiya..bari na tafi..! Haj Uwa tace"Bazaki tafi ba sai kin sha wani abu muje..! Ta kaita har falo ta zaunar da ita kan kujera tana fadin"Umaru dai ana Madina ko..? Amina tace"Uhm..! Daganan bata kara mgana ba mamaki abun ke bata Duk da Tasan Hajiya uwa bata da matsala ammh bata janta ajiki kamar na yau sai kawai taji bata yarda da ita ba. Tana nan zaune sai gata ta fito da Jug da kofi ta kawo gaban Amina ta ja Center table ta dora lokaci Daya tana Fadin"Lemon kankana nayi tun Safe kinganshi nan yayi sanyi zaki ji Dadinsa Amina..! Amina ta yi kasake tana kallonta ganin haka yasa ta Zauna gefenta tana Fadin"Kada ki damu nan Umaru ke karyawa indai yana gari dagashi har matansa abinci shashena basu da Shamaki dashi..! Amina dai batace komwi ba ta Dauka ta Tsiyaya kadan Ta Daga kofin takai Bakinta Hj.uwa na kallonta zuciyarta Cike da Farinciki zata aiwatar da Tsarinta Cikin Sauki kamar yadda ta Saba.! Amina acikin ranta taji bazata sha wannan abun ba,ba domin tana Zarginta ba sai domin cikinta ya cika sannan in ta fada mata bazata yarda ba Sai dai kamar an kwato bakinta Ta Furta. Bismilallahi..! Sannan ta Kurba kadan Haj.Uwa taji kamar an sakata acikin Aljannah Ta Bude zatayi mgana kenan Kukan Umaima ya katseta tatashi da gudu tatafi Dakin tana cema Amina tana zuwa..! Tana shigewa Amina ta Dawo da na bakinta wanda bata gama Hadiye ba jin wani makaki a makogwaronta waige waige ta farayi ganin Haj.Uwa bata fito ba yasa tatashi Sadaf Sadaf ta shiga Kitchen dinta ta Juyesa a wajen wanke wanke taga yana wani yauki mamaki ya kamata da sauri ta Bisa da Ruwa ya wuce sannan ta samu ruwa ta Kuskure bakinta ta koma Falo da Sauri ta ijiye kofin ta zauna kenan sai gata fito Idonta kan kofin tana ganinsa ba komai ta wani Saki ajiyar rai kafin ma ta zauna Amina ta mike tana cemata zata tafi Cikin Murna da Cikar Burinta tace"To shikenan Aminatu Sai na shigo shashen Hajiyar..! Harda Dari biyar ta bama Amina tace bazata karba ba ta matsa mata ta karba Amina ta fice cikin mamaki sannan uwa uba kuma Makogwaronta bai yi mata Dadi ba Tunda tasha wannan lemon Tana Fita Haj.Uwa ta Daga Kofin kafin ta Sheke da wata Dariya a Fili ta Furta"Kema kin Hau keken beran kamar yadda na Dora na bayanki..! Sai ta wani Saki shewa Duniya Sabuwa..burinta ya kusa cika Nazeem Sauransa wattani kadan ya gama makaranta Uzairu kuma ya gama Degree dinsa na farko Services ma yake shirin tafiya ta fara Hango kanta a matakin datake Wahala Shekaru masu yawa. Abunda bata sani ba Kafin nata Tsarin Ta manta Allah ma da nashi..? To nashi ya riga nata sannan abunda Allah ya rubuta shi zai faru wannan gudan jinin sai ya fito Duniya wannan Cewarsa ne..! Amina haka taje Shashen Hajiya ba cikin natsuwarta ba cikinta nata Juya mata sai dai bata cema kowa komai ba suka gaisa da Hajiya tana ta Tambayanta ko ba matsala tace mata eh Dakin su hanne suka shige suna Hira Amina ta kasa natsuwa sai da ta shiga Tiolet ta dinga Tura Hannunta Cikin baki sai da ta samu Wannan dan Lemon daya shiga Cikinta ya fito harda Abincin data ci sai da ta Amayar dashi tayi sauri ta wanke wajen ta fito su hanne suna chan suna Hira basu ji karan Kakwazon aman nata ba. Sai alokacin ta samu salama. Allah yayi ikon sa Ko tasha wannan nganin bazai zauna acikinta ba sai ya fita saboda ba koda yaushe kake aikata abu kaci nasara ba daga Lokacin daka fara Hango nasara Daga lokacin kila Lokacin bayyanan wasu abubuwan ne. La"asar nayi suka shirya suka tafi islamiya irin su mariya sai kallon Amina  suke domin Sa"adatu ta Fesa musu Amina ta auri yayansu mijin Anty Sakina to sanin Halin Amina Shiyaasa ba wanda ya Tareta da mganar har aka tashi. Suna Dawowa gida Amina taso ta Tsaya wai taga Aba da Mallam Hajiya tace maza ta wuce idi ya maidata gida Mallam yana Hadeja sun je bude wani masallaci ba yanzu zai dawo ba shi da Aba Dole Amina taje tayima mamanmu sallama ko mangariba agidan ta tayi ta sai kunci take yi. Aranar dai bata Hadu da Sakina ba sai Washegari da Idi ya maidota da yammah ta ganta afilo suka kalli juna kasa kasa kowacce ta kauda kanta bata Damu da abinci ba, tana ciko Cikinta Kafin ta Dawo da Safe kuma Tea kadai tashe sha watarana ma haka take Tafiya. Asatin nan kaf haka Rayuwar Amina ta cigaba da gudana kudin hannunta sai da ta gama kashe ma su hanne gbadaya sannan Hankalinta ya kwanta Ranar jumma'a daga makaranta bata koma gida ba Ta jira sai da Mallam da Aba suka Dawo ta gaisheshesu Aba sai mamakin Amina yake a idonsa yaga kamar ta kara mishi girma sannan tayi hankali Kadan Mallam kuma kamar ya maidata Ciki saboda so Shiyasa bata koma gida ba sai Ranar Lahadi da yammah Mallam yace tayi kwana Biyu saboda Har da Hajiya bata so ba Ammh Tunda mallam ya saka baki shikenan. Jafar kuwa sam ya manta da Kudin wayar da Danmallam ya barmasa ya siya ma Amina sai da Umar din yaji Shuru ya kirasa sannan ya Tuna Hakuri ya basa aranar bayan ya Dawo Daga wajen aiki ya biya ya siyama Amina waya karama Nokia sai washegari ya siya mata layi yayi mata Rigister sannan yazo ya kawoma Hajiya wayar Tunda Aminar na makaranta Hajiya ita har ta ma manta da Batun wayar sanda ya kawo mata Cikin wardrope dinta ta saka wayar sai kuma Allah ya mantar da ita har Amina ta dawo ba ta bata ba. Wajen kwana Hudu da Jafar ya sanar ma da Danmallam ya siya waya ya kaima Hajiya ta bama Amina sannan ya Turama sa Layin Aminar sai dai tun Washegarin ranar yake ta faman kiran wayar a kashe sai ya fara Tunanin kodai Hajiya bata bama Amina wayar bane.? Shi kuma ya kasa Hakuri ya rasa meke Damunsa Daidai da rana Daya Tunda ya Dawo madina Zuciyarsa bata manta Amina ba. Wannan yarinyar daya ke kira kazama Kwaila itace ya kasa mantawa da ita ko Sakina da suka Dade tare baya jin nauyi da wani Damuwa da ita akan yadda yake ji kan Amina wani al"amari ne da Ubangiji ya barma kansa sani abu Daya ya sani yana matukar son yaji muryanta sannan yaji lafiyanta baya fatan ace yau yabar baya da kura. Sannnan yarinyar itace ya Hada Abu mai muhimmanci da ita abunda bai Taba Hasaahen zai iya Faruwa Tsakaninsa da ita ba.. Abunda bai sani ba Addu"an Hajiya da Mallam ne Allah ya amsa sannan Addu"ar yaya ce Allah ya amsa ya Amintar da Ruhin Amina da Umaru waje Daya..Aminci na har Abada..! *Janafty**TFZB2011* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Bayan Sati daya da dawowar su Hajiya Daga maiduguri Ranar wata lahadi da misalin karfe goma na Safe sai ga Aliyu a falonta Danmallam ya aikosa tun daga Dutse har gumel wajen Amina. Hajiya mamaki ya cikata Lokacin da Ta fito falo suka gaisa da Aliyu yake sanar da ita yazo neman Amina ne mamaki bai bar Fuskar Hajiya Babba ba ta kalli Aliyu Dake zube saman Cafet din falon nata kansa a kasa cikin ladadinsa kamar abokin nasa Sai da ta gyara zama kafin tace"Amina..? Cikin sigar mamaki kansa na kasa yace"Eh Hajiya..Yace nazo ne na kawo mata waya yana so zasu yi mgana.. Hajiya tayi wani kayattacen mirmishin su irin na manya kafin tace"To ban da abun Danmallan don wannan sai ya Tadoka tunda ga Dutse har Gumel..haka ake yi..? Ai da ya kirani sai na basa Aminar suyi mgana sannan ni nace zan kirasa nayi mai bayanin yadda mukayi da mallam kan wayar da jafar ya kawomin sai na manta zuwana Bikin nan sannan da na dawo ma ban zauna ba Sabga tayi yawa..! Aliyu kansa a kasa bai ce komai ba shima so yake ya gama da Hajiyar ya fita ya Tsitsiye Shehi yaji Dalilin sa na neman yarinyar daya gama Cema kwaila kazama. Hajiya tacigaba da Fadin"Tashi ka tafi abunka Aliyu Amina bata nan suna Hadda Yau ma inaga da wuri zasu dawo Saboda hutu zasu yi sun fara Jarabawar tun awanchan satin ne In ya kiraka ka Fadamai ya kirani muyi mgana..! Aliyu kansa na kasa ya mike yana Fadin"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma mungode..! Ta amsa da Ameen da Fatan ya gaida iyalansa daganan ya fice zuwa shashen maallam yamai sallama suka Hade da Anty Amarya ya gaisheta cikin Ladabi ta amsa tana kallonsa cikin mamakin ganinsa da Safe haka sai dai bata Tsawaita mamakinta ba Sanin Aliyun yana zuwa gaida Hajiya da mallam Lokaci bayan Lokaci koda Danmallam din baya kasar Shashen mallam ya koma yamai sallama zai koma domin nan ya fara shiga suka gaisa bai dai zauna bane ganinsa suna mgana da Aba yace bari ya shiga ciki ya gaida Hajiya Mallam bai kawo ma kansa shima wani abu ya kawo Aliyu ba sanin Yadda yake Darajasu Dalilin kawai suna iyayen Abokinsa Umar. Sallama sukayi yana ta sakamai albarka da Fatan Allah ya kaisa gida Lafiya kiran Danmallam bai shigomai ba sai da ya bar Gumel ya dau hanyar Dutse Gefen titi ya samu yayi fakin sannan ya Daga kiran nasa Daga chan bangaran Danmallan yayi mai sallama kamar yadda kowa yasan shi da zarar ya Dauki waya da sallama itace Farko a bakinsa Aliyu bai wani amsa sallamarsa ba yace"Shehi wai miye sirrin ne..? Umar yace"Sirrin na mene..? Aliyu yace"To gani nayi ka bi ka Rude kan karamar yarinya sa"ar yarka ta Fari kuma kwaila..kuma kazama ka tadani Tundaga Dutse zuwa gumel haka Hajiya ma ta Dinga mamakin wannan aikin naka..! Umar ya Dafe kansa dagachan bangaran kafin yace"meyasa ka bari kuka Hadu da Hajiya..? Aliyu yace"Dole kuwa mu hadu don Daga Falon mallam shashenta naje neman Amina ta tabbatar min da batanan suna makarantar Hadda..! Umar yace"Kash..Da tace haka sai kayi Tahowarka ba sai ka fadamata Dalilin zuwanka ba..! Aliyu yayi wata Dariya kafin yace"Ai aikin gama ya riga ya gamu Shehi tuni na Rattafamata komai tace in munyi mgana Dakai na sanar maka ka kirata zaku yi mgana .! Umar yayi shuru kafin yace"Kai dai baka da biyan Bukata duk ka bata komai ni fa kunyarta nake ji shiyasa ban kirata ba ita da mallam..! Aliyu yace"Oho zakace haka mana Tunda na gama Biya ma Bukata akwai ai watarana ba agama ba..! Umar yace"Naji bakomai dai nagode zan kirata yanzu..! Aliyu yace"Ni fa baka Fadamin sirrin ba..! Umar yace"Wani sirrin kenan..? Aliyu na Dariya yace"Sirrin abunda ya susuta ka kan Aminatu mana..! Umar ya saki karamin Tsaki kafin yace"bansani ba..! Aliyu ya saka Dariya kafin yace"To to..Nagano Sirrin ma..Shiyasa jiya daka kirani bakace min wannan kazamar yarinyar ba kai Tsaye ka kira sunanta Tabbas yanzu ta tashi Daga kazama kwaila ta koma Sweet Amina..Ko Honey ce..? Umar ya tsaki again kafin yace"Kai fa Dan iska ne..! Daga haka ya Datse kiran Aliyu yabi wayarsa da kallo yana Dariya sosai in ya Tuna sanda aka aurama Umar Amina yana ta fada yar cikinsa ne ina zai kaita sai gashi kaji sa shuru ya shiga komar yara ya kasa sukuni. Duk da yayi matukar mamakin yadda Komai ya faru Tsakanin Amina da Shehi sai dai bai Tsananta ba Sanin Tsakanin miji da mata sai Allah ammh Shehi ya bani a wajensa ya Dinga Tsokanarsa kenan. Yana Mirmishin ya Tada motarsa ya bi hanya yana kara Dariyan Abokin nasa yana kuma Fatan yasa Amina ta mai mugun kamun da sai ya raina kansa.! Bayan Tafiyar Aliyu Hajiya tayi ta Tunanin me yasa Danmallan ke son mgana da Amina haka da har ya kasa Hakuri..? Bata samu amsar ta ba sai tayi Tunanin kila yana so yaji Lafiyanta ne sannan ya tambayeta ko tana Bukatar wani abu daganan ta watsar da Tunanin ta koma Bedroom dinta tana gyarawa ba Dadewa ta samu kira Daga Danmallam bayan ta Dauka sumgaisa kamar yadda suka Saba sai kuma yayi Shuru yana jin kunyar yayi mata mgana ta san Halinsa Tunda ita ta Haifesa. Yasa ta gyara Zama tana fadin"Dazu Aliyu abokin ka yazo..akan kai ka aikosa ya kawo ma Amina waya zaku yi mgana ko.? Dakyar ya iya amsa ma Hajiya gani yake kamar zata Fahimci abunda ya Faru Tsakaninsa da Aminar. Cikin Dattakonta ta cigaba da fadin"To nace yayi tafiyarsa Sabgoginsa ka taso mutum Tunda ga nisan Duniya Danmallam..! Ai sai ka Kirani muyi mgana ko ba Haka ba.? Kai tsaye yace mata"Kiyi hakuri Hajiya.. Cikin Ladabinsa bata Damu ba tace"Ni ba laifi kamin ba..gani nayi ka basa wahala..Daman ina ta so na kira ka nayi maka bayanin Dalilin Dayasa ban bana Amina wayar nan ba duk da ni nace ka siya mata mgana mukayi da mallam ya nuna min Rike waya ga Amina yayi sauri sannan Duba da har yanzu akwai kuruciya a tare da ita..hakan zai Dauke Hankalinta har ya Taba karatunta da muke Fata ta Samu,ya nuna min na bari sai zuwa gaba in kazo ka tafi da itan sai ka siya mata wayar Lokacin tana gabanka zaka kula da Motsinta yanzu kuma ya nuna min gaskiya a"a shiyasa kaji Shuru ban bata wayar ba tana nan na ijiyeta..! Cikin gamsuwa da mganar ta yace"Hakane Hajiya..! Hajiya tace"To kaji yadda mukayi da mallam da Dalilin dayasa kaji shuru..Sannan yace in kana son jin Lafiyarta ne ka kirani ko mallam din sai in ta na nan sai abata ku gaisa..! Danmallam yace"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma..! Hajiya ta amsa da Ameen kafin tace"suna Hadda ammah ina ga bazasu Dade ba in sun Dawo zan kiraka sai na Hadaku..! Cikin Ladabinsa ya shiga Fadin"Allah yasa agama Lafiya Hajiya Allah ya kara Nisan kwana..! Ta amsa da Ameen suka rabu bayan ta Tambayi Iyalansa da ayyukansa. To sun ma gama wayar ba Dadewa wajen azahar sai ga su Aminan sun Dawo suna ta Murna an basu Hutun Sati ukun Dadinsu Daya gobe zasu fara Exam din second Semister a makarantar boko satin daya gabata Gabadaya Revision sukayi. Amina ke fadin Dama islamiya ma ta bata da Hutu ai da sun ji Dadi. Ba"a basu Sakamakon su ba sai Sun dawo Hutu sannan. Anan Shashen Hajiya sukayi sallah Sukaci abinci Hajiya na ciki bata san Amina da Hamida sun koma gida ba Tana zuci zucin ta Kirata sai ta Kira Danmallam din ta Hadasu ko da ta Fito sai Hanne kawai ta gani a Falo ita ke Fada mata Su Amina sun tafi gida kai Tsaye tace Hanne taje ta kira mata Aminar. Hanne ta mike ta saka Hijabi ta tafi tana zuwa ta iske su acikin Dakinsu har Amina ta kwanta bata ga mamanmu ba tana cikin Dakinta ta kwanta in ji Hamida jawaad ke ta wasa da Karamar kwallo a Tsakar gidan. Da Farko Amina Dataji Hanne na Tashinta kin tashi tayi sai da tace mata Hajiya ke kiranta sannan ta Mike tana fadin"Kice Wlh Hanne..! Hanne ta mike tana fadin"Au nace ma Wlh..!? To ki zauna kin ga tafiyata..! Amina ta mike tana fadin"Tsayani Hanne mu je..Fatana Allah yasa ba gida zata saka Idi ya kaini ba..! Hamida da Hanne suka kalli juna kafin Hanne tace"To in chan din ne fa..? Ai kince gidan mijinki ne..! Amina na saka Hijabi batayi mgana ba sai da ta gama sakawa sannan ta Dago Tana fadin"Ni yaushe na Fada..? Allah ya isa na, wuta bal bal in ban Fada ba..! Hamida na Dariya tace"Daman chan Allah ai ya ishi kowa Amina..! Harara ta balla musu kafin ta bangaje Hamida ta wuce fuu hamida da Hanne suka.bita da kallo Hanne tace"Kamar an kara mata bala"i wlh bayan auran nan..! Hamida tace"Kowa ma haka yake fadi..ya danmallam zai yi mganinta bari su koma Madina ki gani nan ta raina achan Ubanwa zata mawa .! Hanne na Dariya tace aifa Daganan ta bi bayan Amina zuwa gidansu. Koda Taje Amina da Hajiya na kuryan Daki Hanne na shiga Hajiya Data Kira Danmallam bai Dauka ba ta kalli Hanne ta nuna mata kofa Tana fadin"Jirata afalo..! Hanne ta Tura baki kafin ta fita Amina ta Fakaici idon Hajiya tayi ma Hanne gwalo ita azatonta wani abun Dadi Hajiya zata bata sai da wayar Hajiya ta shiga kidan larabawa taga Hajiyqn ta Dauka ta mika mata tana Fadin"Karbi Mijinki ke son mgana Dake..! Ta fada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Dakin Harda Rufo mata kofar Bedroom din Amina gabanta ya Fadi tabi wayar da kallo ga sunan Danmallan nan baro baro na kan Layi sai jikinta ya fara rawa aranta tace na shiga uku ni Amina Allah yasa ba wani Abu akace mai nayi ba.. Jikinta a sanyaye ta kara wayar kunne Daidai Lokacin da Sanyayyiyar Muryansa ta Doketa Cikin Sallama da Hausansa daya Cakude da Larabci. Sai da ya kara maimaita Sallamar sannan ta amsa Bakin da jikinta na rawa Tun kafin ya gama rufe baki Tace"Ina yi..yini..! Ajiyar zuciyar daya sauke har sai da ta jisa a kunnenta Dayaji muryanta sai yaji Salama da natsuwa Cikin Taushinsa yace"AMINA...! sai taji kamar yafi kowa iya Fadar sunan nata jin yadda ya kirata ita bazata iya tuna ko yama taba kiran sunanta ba Haka ba, jin tayi shuru yasa ya kara cewa"Amina kina lafiya..? Cikin Sanyin Jiki tace"Na"am..eh lafiya kalau..!" "Ya jikin ki..? Ina fatan kin warke babu kuma inda ke miki ciwo..? Ya fada kai Tsaye domin baya Fatan ace wani abu kuma ya tashi bayan Tafiyarsa kunya ta kama Amina ta Dukar da kanta kamar yana ganinta ta kasa mgana sai gabansa ya Fadi da Sauri yace"Ko da wata matsala ne..? Da Sauri tace"A"a na warke..! Afili ta Furta"Alhamdulillah..! Kafin yace"Naji Dadin haka ina Fata kamar yadda kikamin alkawarin baki gayama kowa ba ko..? Sai da ta gyadamai kai kafin tace"Eh ban fadama kowa ba..! Cikin jin Dadi yace"Dakyau naji Dadin Haka..Ya karatu fata kina maida Hankali wajen karatu..?. Da Sauri tace"Eh yau ma mun yi Hutun Hadda..Gobe ma zamu Fara Jarabawa a boko..! Kai ya gyada kafin yace"Allah ya bada sa"a..ki rika maida hankali kinji ko..? Ta gyada kai ya cigaba da Fadin"Sannan ban da wasa ban da Fada ban da gujeguje ke yanzu ba yarinya bace kin tashi Daga su Hamida ke matar aure ce ba Daya kike Dasu ba kina jina ko..? Nan ma kai ta gyada mai yace"Baki da baki ne..! Ba nace ki daina min mgana Da kai ba .! Da Sauri tace"Naji insha Allahu..! Ajiyar rai ya Sauke kafin yace"Kina Bukatar wani abu..? Tace bakomai kai Tsaye yace"Ki rika gaida Sakina in kun hadu tana gaba Dake kinji ko..? Amina ta Tura baki kafin tace"Ni fa in na ganta batamin mgana sai tayi ta Hararana har zagina ma tanayi..! Cikin mamaki yace"Ita Sakinar..? Amina tace"Eh shiyasa nafi son zaman nan fiye da chan sannan achan ina jin Tsoro da Daddare bana iya barci don Allah ka Fadama Hajiya ta rika barina ina kwana anan in ka Dawo sai na koma achan..! Kawai sai ta sakamai kuka sai yaji Hankalinsa ya tashi meke Damun yarinyar nan ne Cikin Tausasa Murya yace"Naji ki daina kuka zan mata mgana..Daman baki daina Firgita cikin barci ba..? Tace mai eh sai da yayi shuru kafin yace"Ki samu mallam yau da Daddare in ya natsu ki Fadamai abunda kike jin in zaki Firgita kin ji ko..? Tace"Na Fadamai..? Yace"Eh ki Fadamai sannan mganar Zagin ki da Sakina ke yi kada ki Fadama kowa har su Hajiya zan mata Fada insha Allahu zata Daina ke dai in kin koma gidan kun Hadu ki rika gaisheta saboda ko bakomai Tana gaba Dake kuma a islamiya an koya muku yin biyayya ga na gaba da ku ko ba Haka ba..? Tace eh ya cigaba da fadin"To ki rika bata girmanta kin ji ko..?. Ta amsa da toh bai Tsawaita mganar ba yace"Zan ce ma Jafar a Cefanan wannan watan ya siya miki Goldenmorn da Cornfkles Saboda Saukaka miki Wahala sai ki Rika sha in zaki tafi makaranta..! Tace "To nagode..! Ya amsa ta da Fadin"Kada ki damu komai kike Bukata kada ki tambayi Hajiya ko mallan ki yi ma Jafar mgana ko kuma ki Dauki wayar Hajiya ki kirani kinji ko..! Nan ma tace mai da toh tagode Dagnan yace ta maida Hankali a karatunta ta amsa mai Daganan ya mata sallama ya kashe wayar. Tabi Wayar da kallo Tana Tura baki wai ta rika gaida Sakina Tab wannan mara mutumcin ne zata gaisheta.. Shi kuwa sai da sukayi mgana yaji Hankalinsa ya kwanta har ya natsu ya Cigaba da Duba Takardun Dalibansa da sukayi gwaji. Da suka gama wayar kunya ta Hana Anina fitowa sai da Hajiya ta Shigo Daukan abu ta ganta zaune tayi shuru tace"A a Mamah tunda kun gama wayar ki fito falo hanne na jiranki mana sai ki zauna ke kadai..! Jin haka yasa ta mike ta mikama Hajiya wayar, ta karba ta Fice da Sauri Hajiya ta bita da kallo tana Mirmishi a Cikin aranta tana Fatan addu"an su Allah ne ya karba na amitar da Ruhin Amina da Danmallam waje daya. Amina na fita Hanne ta taso tana Tambayanta da wa tayi waya Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bansani ba..! Hanne na Dariya tace"Nasani Ya Danmallam ne..ko..? Amina ta mata wani kallo kafin tace"In ma shine sai na Fada miki..? Sirrin miji da mata..! Hanne ta saki Dariya kafin ta Ja Hijabinta tana fadin"Bari naje na gayama Hamida..Sabon Update..! Amina tayi Tsaki kafin tace"Ai ke Hanne mijinki ya shiga uku..duk wanda ya aureki ya auran ma kansa sai kin hada Fada a Family din mijinki Saboda munafuncinki..! Hanne bata bi ta kanta ba ta fice Amina tayi zamanta Falon Hajiya chan sai gasun dawo Tare Hamida sai kara maimaita abun da Hanne ta gayamata take yi Amina ta musu wani banzan kallo kafin tace"kusan dai ni yanzu ba Sa"arku bace ko..? Igiya uku ne akaina..Taimaka muku ma nake yi ina yawo da yara. ! Hanne da Hamida suka saki baki ganin haka yasa ta Musu gwalo tatashi da gudu ta Fada Dakin su Hanne Tana Dariya suka mara mata baya suna fadin yau sai ta gayamusu su waye yara..? Ranar dai anan suka wuni Shashen Hajiya suna abunda suka saba sai bayan sun dawo islamiya ne Hajiya ta saka aka maida Amina gida tana kunkuni Tana komai bata samu yima Baba mallam bayani ba sai washegari da suka dawo makaranta ta Fadamai ya Dade yana mamaki ya tambayeta yaushe ta fara tsorata tace tun tana karama ta dade mallam ya Dinga Fadin Sakacin mamanmu da Aba da Amina na Fama da wannan Laluran ammh bsu sani ba Hajiya ce ma ta Lallasheshi ya bar mganar da yace har Aba din sai ya kira da mamanmu ya musu Fada. Shi ya Rubuta mata addu"o'i ya bata yace ta Rika karantawa Duk Dare in zata kwanta Tare da Sauran addu"an barcin da Annabi ya koyar damu. Amina yadda Taga Mallam ya Dau abun ne yasa itama bata Dauka da wasa ba sannan Danmallam ma sun sake mgana da wayar Hajiya Data Fadamai yadda sukayi da mallam ya mata Fada kan ta Dage kada wasa ya Dauke mata Hankali ta rika kwanciya bata karanta su ba. Shiyasa ta Dake bata kwanciya sai ta karanta sai gashi kuma Cikin ikon Allah tunda ta Dage sai ta samu Saukin Firgita din sai abunda ba"a rasa ba Danmallam har da mallam sun yi mgana Mallam nata fada yana Fadin da Haka Umaima ta Fara gashi nan suna so su taba mata kwakwalwa Dannallam yana so ya Fadama Mallam bayan haka ma yana Zargin akwai wani abu Tattare da Amina sai dai kuma bai da Hujjan hakan ammh yana so sai in ya kara Dawowa ya Zauna ya Fahimci matsalanta Domin Ranar da abun nan ya Faru tsakaninsu da Washegarin nan da Safe yaga tana wasu abubuwan da Dole tana da wani abu a Tattare da ita. ******* Kwantashi ba wuya a wajen Allah su Amina har sun gama Jarabawarsu sun yi Hutu taso ta zauna anan tayi Hutunta Hajiya ta hanata sai ta Roki Baba mallan kan su Hanne su Bita ko Sati Daya su yi da Farko Hajiya ta Hana sai da Mallam ya saka baki Sannan ta amince suka Tattara suka koma chan da Niyar Sati Daya zasu yi Saboda islamiya basu yi Hutu ba. Mamanmu bata Damu ba da akace Hamida zata je gidan Amina Domin alokacin tana Tsakar Cin Duniyarta ne Domin komai tace Aba ya bata baya Gaddama Kudi yake sakar mata bana wasa ba ta zama Tauraruwa a wajen sa Mamanmu ta samu Cikar Burinta Fiye ma da yadda take fata shiyasa ta manta da kowa da komai ko Anty Amarya ta kirata bata ma kaunar Hakan gani take tana neman Takura mata Shiyasa Amina ma bata gabanta Ta barta da Anty Amarya chan itace Zatayi mganinta ita yanzu Sa"idu ne agabanta yanzu shawaran komai sai yayi da ita sai abunda tace koda yace Jafar yace kaza ya kamata ko Hajiya sai tasan yadda tayi ta Kushe mganarsu ta sauya da nata Shiga kawai take tana fita Daga kayan alfarma kamar wata Yarinya sannan Malaminsu tana sakarmai kudi sosai Domin ta yaba da aikinsa Anty Amarya kuma tana nan tana Jiran gawom Shanu domin ta yarda da aikin Malam ya sanar da ita Nasara tatace shiyasa bata Damu ba ta koma ta Zauna tana jiran tsammani kamar yadda ta basa duka yardanta Shiyasa ko Sakina ta kirata tana mata Korafi take mata Fadan bata da Hakuri aiki nawa suka basa kuma ya Biya musu Bukata..? To wannan ma ta Zauna ta Jira komai zai zama Daidai da yardan Allah abunda basu sani ba Daga wannan Lokacin aikin ya kuskure musu sannan zasu cigaba da jiran majirata ne Jiran da zai kai su ga Ranar Nadamar su da Tonon asirin su..! Ko Hutun da su hanne suka tafi Sakina kamar ta Haukace saboda Bala'i Amina Mahaukaciya take so ta maidata,gwara ma su Hanne suna dan jin mganarta banda Amina sai ta gama masifarta sun ba'ta mata Falo ko Kitchen Amina ta mata gwalo ko Ta mata Tsaki ta shige Daki abunta Sakina taci ji Yatsa kamar me..? Kamar yadda yace a Cefanan watan nan an kawo su Goldemorn su Amina an samu banza ana ta Wadaka madara kuma da kayan Tea kafin Sati sun kare saboda yadda suke barnan sa basa da aiki sai dan sululu ko Wainar Fulawa gashi Sakina bata son kazanta su kuma in suna aiki a Kitchen din sai sun yi kaca kaca dashi in tayi mgana Hanne da Hanida kadai ke Sauraranta banda Amina da take maidata ma mahaukaciya. Sakina abun ya isheta kullum sai ta Kira Danmallan ta kaimai karan Amina da kannensa shi har ma ya gaji Saboda bai isa ya kore su ba Amina Matarsa ce sannan su Hanne kannensa ne ko ba aure suna da Damar zama agidansa watarana da abun ya ishesa sai yace ta bama Amina wayar da an bata ya fara mata Fada sai ta saka kuka tace In ta gaishe da Sakina sai taki amsawa ta bita da Zagi sannan bata barin su suna shiga Kitchen sai tace suna mata kazanta Ayadda take mgana ne yasa Dole ma ayadda da ita sannan tace ga su hanne ma yaji ta bakinsu su hanne kuma basu taba kwaye ma Amina baya ba, sai su karantamai yadda Amina tace Daga karshe sai abun ya koma kan Sakina yayi mata Fadan itace babbar banza tana Biyema yara sun rainata sannan kada ta kara Hanasu shiga kitchen ta bar su dafa abunda suke so itama ta Dafa nata baya son Fitina. Tunda ga ranar ko Takai ma Korafin Amina ta mata kaza bai Sauraranta Anty ma Zaginta take yi tace ta Daina Danunta tunda ita Sakarya ce zata Zauna yara kanana su gagareta Alhalin basu san yadda yaran nan suka Sakata gaba bane barin ma Amina in ta fito falo ta gansu ta rika waka kenan tana cema mata agwagwa in ta yi mgana ta maidata mahaukaciya sannan ba Tsayawa ma take yi ba,ballatana ta Daketa ta huce. Su hanne wajen kwanansu goma Daga su Har Aminar basa zuwa makaranta da Hajiya tayi mgana ne Mallam yace ta rabu dasu Idi ya rika zuwa yana Daukosu yana kawo su makarantar Daganan,saboda dukkansu yara ne sannan nan gaba kadan In Aminar ta bar garin ina zasu ganta..? Sannan kuma suma watarana gidan auransu zasu watarana sai dai labari..da Haka ta kyalesu suka zauna achan sai dai Idi ke zuwa yana Daukosu da an tashi kuma ya maida su. Cin Duniyarsu da Tsinke suke yi ko ajikinsu Sakina ta koma zaman Daki bata Fitowa saboda su in tana son Tsira da Mutumcinta Ranar kwatsam sai ga Aliya matar Aliyu sun zo kawo Amarya wata Diyar kanwar mamanta ne shine tazo gidan ta iske Sakina cikin Daki Amina ta gagareta bata iya ma Fitowa sanda Sakina ke Fadamata tana kuka Sai taga Laifin Sakinar da ta Zauna yarinya karama ta gagareta. Taja Sakinar suka fito su Amina na Falo sunyi Daidai ga Filets nan da Kofuna da gorinan lemuka da suka gama dasu nan basu Dauke ba suna Hira Ita a Dole sai ta kwatan ma Sakina yancinta.. Haka ta Dinga surfama Amina Zagi tana kiranta kwaila kazama mara Tarbiya su hanne sukayi Tsuru Tsuru Amina ranta ya baci ta mike ta rama Zaginta da Aliya ke yi ita kuma tace Zata Daki Amina ai ko sun ga Hauka Amina ta Tsaya kikam idanuwanta sun juye ba baki sai Fari tace in Aliya ta isa ta tabata tagani Sakina ke jan Aliya tana ta bari kada ta tabata ta ja mata bala"in wajen su Hajiya. Ita kan Aliyan ta Tsorata bata Taba Aminar ba suka koma Daki tana Borin kunya Amina kuwa ba wani Abunda ya Sameta Zafin ranta ne ya taso mata Taso ta tabata ne Daga Sakinar har Aliyan sai sun raina kansu Wlh sai kuma Allah yaso su su Hanne na tabata Hakuri ta balla musu harara tace sun cika Tsoro ba wanda ya isa ya Takura musu acikin gidan nan. Aliya taso kwana ne ammh ganin yanayin Amina yasa taki kwana ta koma gidan Amarya ta kwana ko Washegari Datace zata dawo bata Dawo ba ko da Sakina ta Kirata tace mata gata a Hanya zata koma gida ammh Tana zuga Sakina kan Wlh in Amina ta kara mata rashin kunya ta kamata ta mata Dukan tsiya Sakina jinta kawai take ina ita ina taba wannan yar gold din ai sai Hajiya ta saka Umar ya Saketa. Allah ne ya taimaketa suka koma makaranta Hajiya tace su Dawo gida idi yazo ya Dauketa sai ta Samu Sauki Bata ma haduwa da Aminar sai ta bar gidan take Fitowa sannan Daga ranar jumma"a sai Lahadi take dawowa tana ganin Lokacin Dawowarta yayi zata shige Daki karfi da yaji Bala'in Amina da jindalinta ya Saka Sakina ta kasa Sakewa agidanta. Gashi Danmallam ya Daina Sauraranta indai kan Amina ne yace yana wata kasar ta daina tadamai da Hankali baya so in bazata kama girmanta ba bazai iya Hana Amina ta mata Rashin kunya ba abu goma da Ashirim ga rashin miji ga Fadan Anty Amarya Data Kirata sai tace laifinta ne sannan ga Amina ta Sakota gaba..! Ana cikin Haka Sadiya Diyar Anty Amarya ta Haihu bakwaini yarinyar tazo ba rai anan Dutse su Sakina ana ji sune gaba gaba ita da Hj.Nasara da Hajiya Babba suka tafi suka Duba Sadiya Dake asibiti domin ance ta Zubar da jini sosai achan suka Rabota Tunda Danmallan ya barta ita ta zauna da Sadiyan har aka sallamota Daga asibiti duk da ga yan"uwa ammh Anty Amarya tafi yarda Sakina ta Zauna da Sadiyan. Bayan sun Dawo gida ne Sakina ta Fara Zazzaabi har da su karin ruwa koda akaje asibiti akayi Test aka gano Tana da Shigar ciki kimanin wata Uku da kwanaki Ashe koda Danmallam ya Tafi ya jefa kwallinsa araga a maran Sakina basu sani ba. Murnan wajen Anty Amarya da Sakina ba"a mgana kamar an basu aljannah Hajiya da mallam ma Tare da shi kanshi gogan Danmallam Domin yana matukar son yaga kwansa a Duniya,Sannan da kansa ya Sanar da Sarood ta tayasa murna Har dai yanzu shuru ne ba wani cigaba ammh basu sare ba suna cigaba da shan mgani shi dai har yanzu ne bai yarda da Shawaran Aliyu na ya kira mallam ba yana tunanin al"amarin nasu ba Sihiri bane. Mamanmu dataji itama tayi murna sannan tasan yanzu tunda Cikin Sakina ya samu sai Madina ta barta taci Gumin Wahalarta ta Daina Damunta. Su ba Fatan cikin ya zauna suke yi ba kansu yayi girma suna ta Feleke Anty Amarya taso Sakina ta Dawo gabanta ta raini cikin mallam ya hana Saboda za"a bar Amina ita kadai Gidanta ta koma ammh sai Ta tafi da Sa"adatu tana kula da ita ana zuwa Daukansu Ita da Amina da ko mgana basa ma juna Amina taji zencen cikin Sakina ko ajikinta tunda ko"ina Zencen cikin ya Zaga. Haj uwani na gefe tana kallonsu aranta Dariya take musu domin tasan wannan karon ma ba zai zauna ba Haka kuwa akayi yana da wata Hudu watarana da Daddare Sakina ta tashi Cikin Jini Hankalin Sa"adatu ya tashi ta Kira Anty Amarya koda ta zo ita da Idi Direba suka tafi asibiti sai wankin Ciki akayi ma Sakina cikin jikinta ya Sake fita karo na Hudu. Abunda Haj.Uwani bata sani ba in na Sakina ya sake zubewa daman chan Allah bai yi Rayayye bane ammh wanda Allah zai rayasa yana nan har ya fara zama gudan jini batare da kowa ya Farga ba Hatta kuwa da wacce Cikin ke jikinta. *Janafty**TFZB2011* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Bayan Sati daya da dawowar su Hajiya Daga maiduguri Ranar wata lahadi da misalin karfe goma na Safe sai ga Aliyu a falonta Danmallam ya aikosa tun daga Dutse har gumel wajen Amina. Hajiya mamaki ya cikata Lokacin da Ta fito falo suka gaisa da Aliyu yake sanar da ita yazo neman Amina ne mamaki bai bar Fuskar Hajiya Babba ba ta kalli Aliyu Dake zube saman Cafet din falon nata kansa a kasa cikin ladadinsa kamar abokin nasa Sai da ta gyara zama kafin tace"Amina..? Cikin sigar mamaki kansa na kasa yace"Eh Hajiya..Yace nazo ne na kawo mata waya yana so zasu yi mgana.. Hajiya tayi wani kayattacen mirmishin su irin na manya kafin tace"To ban da abun Danmallan don wannan sai ya Tadoka tunda ga Dutse har Gumel..haka ake yi..? Ai da ya kirani sai na basa Aminar suyi mgana sannan ni nace zan kirasa nayi mai bayanin yadda mukayi da mallam kan wayar da jafar ya kawomin sai na manta zuwana Bikin nan sannan da na dawo ma ban zauna ba Sabga tayi yawa..! Aliyu kansa a kasa bai ce komai ba shima so yake ya gama da Hajiyar ya fita ya Tsitsiye Shehi yaji Dalilin sa na neman yarinyar daya gama Cema kwaila kazama. Hajiya tacigaba da Fadin"Tashi ka tafi abunka Aliyu Amina bata nan suna Hadda Yau ma inaga da wuri zasu dawo Saboda hutu zasu yi sun fara Jarabawar tun awanchan satin ne In ya kiraka ka Fadamai ya kirani muyi mgana..! Aliyu kansa na kasa ya mike yana Fadin"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma mungode..! Ta amsa da Ameen da Fatan ya gaida iyalansa daganan ya fice zuwa shashen maallam yamai sallama suka Hade da Anty Amarya ya gaisheta cikin Ladabi ta amsa tana kallonsa cikin mamakin ganinsa da Safe haka sai dai bata Tsawaita mamakinta ba Sanin Aliyun yana zuwa gaida Hajiya da mallam Lokaci bayan Lokaci koda Danmallam din baya kasar Shashen mallam ya koma yamai sallama zai koma domin nan ya fara shiga suka gaisa bai dai zauna bane ganinsa suna mgana da Aba yace bari ya shiga ciki ya gaida Hajiya Mallam bai kawo ma kansa shima wani abu ya kawo Aliyu ba sanin Yadda yake Darajasu Dalilin kawai suna iyayen Abokinsa Umar. Sallama sukayi yana ta sakamai albarka da Fatan Allah ya kaisa gida Lafiya kiran Danmallam bai shigomai ba sai da ya bar Gumel ya dau hanyar Dutse Gefen titi ya samu yayi fakin sannan ya Daga kiran nasa Daga chan bangaran Danmallan yayi mai sallama kamar yadda kowa yasan shi da zarar ya Dauki waya da sallama itace Farko a bakinsa Aliyu bai wani amsa sallamarsa ba yace"Shehi wai miye sirrin ne..? Umar yace"Sirrin na mene..? Aliyu yace"To gani nayi ka bi ka Rude kan karamar yarinya sa"ar yarka ta Fari kuma kwaila..kuma kazama ka tadani Tundaga Dutse zuwa gumel haka Hajiya ma ta Dinga mamakin wannan aikin naka..! Umar ya Dafe kansa dagachan bangaran kafin yace"meyasa ka bari kuka Hadu da Hajiya..? Aliyu yace"Dole kuwa mu hadu don Daga Falon mallam shashenta naje neman Amina ta tabbatar min da batanan suna makarantar Hadda..! Umar yace"Kash..Da tace haka sai kayi Tahowarka ba sai ka fadamata Dalilin zuwanka ba..! Aliyu yayi wata Dariya kafin yace"Ai aikin gama ya riga ya gamu Shehi tuni na Rattafamata komai tace in munyi mgana Dakai na sanar maka ka kirata zaku yi mgana .! Umar yayi shuru kafin yace"Kai dai baka da biyan Bukata duk ka bata komai ni fa kunyarta nake ji shiyasa ban kirata ba ita da mallam..! Aliyu yace"Oho zakace haka mana Tunda na gama Biya ma Bukata akwai ai watarana ba agama ba..! Umar yace"Naji bakomai dai nagode zan kirata yanzu..! Aliyu yace"Ni fa baka Fadamin sirrin ba..! Umar yace"Wani sirrin kenan..? Aliyu na Dariya yace"Sirrin abunda ya susuta ka kan Aminatu mana..! Umar ya saki karamin Tsaki kafin yace"bansani ba..! Aliyu ya saka Dariya kafin yace"To to..Nagano Sirrin ma..Shiyasa jiya daka kirani bakace min wannan kazamar yarinyar ba kai Tsaye ka kira sunanta Tabbas yanzu ta tashi Daga kazama kwaila ta koma Sweet Amina..Ko Honey ce..? Umar ya tsaki again kafin yace"Kai fa Dan iska ne..! Daga haka ya Datse kiran Aliyu yabi wayarsa da kallo yana Dariya sosai in ya Tuna sanda aka aurama Umar Amina yana ta fada yar cikinsa ne ina zai kaita sai gashi kaji sa shuru ya shiga komar yara ya kasa sukuni. Duk da yayi matukar mamakin yadda Komai ya faru Tsakanin Amina da Shehi sai dai bai Tsananta ba Sanin Tsakanin miji da mata sai Allah ammh Shehi ya bani a wajensa ya Dinga Tsokanarsa kenan. Yana Mirmishin ya Tada motarsa ya bi hanya yana kara Dariyan Abokin nasa yana kuma Fatan yasa Amina ta mai mugun kamun da sai ya raina kansa.! Bayan Tafiyar Aliyu Hajiya tayi ta Tunanin me yasa Danmallan ke son mgana da Amina haka da har ya kasa Hakuri..? Bata samu amsar ta ba sai tayi Tunanin kila yana so yaji Lafiyanta ne sannan ya tambayeta ko tana Bukatar wani abu daganan ta watsar da Tunanin ta koma Bedroom dinta tana gyarawa ba Dadewa ta samu kira Daga Danmallam bayan ta Dauka sumgaisa kamar yadda suka Saba sai kuma yayi Shuru yana jin kunyar yayi mata mgana ta san Halinsa Tunda ita ta Haifesa. Yasa ta gyara Zama tana fadin"Dazu Aliyu abokin ka yazo..akan kai ka aikosa ya kawo ma Amina waya zaku yi mgana ko.? Dakyar ya iya amsa ma Hajiya gani yake kamar zata Fahimci abunda ya Faru Tsakaninsa da Aminar. Cikin Dattakonta ta cigaba da fadin"To nace yayi tafiyarsa Sabgoginsa ka taso mutum Tunda ga nisan Duniya Danmallam..! Ai sai ka Kirani muyi mgana ko ba Haka ba.? Kai tsaye yace mata"Kiyi hakuri Hajiya.. Cikin Ladabinsa bata Damu ba tace"Ni ba laifi kamin ba..gani nayi ka basa wahala..Daman ina ta so na kira ka nayi maka bayanin Dalilin Dayasa ban bana Amina wayar nan ba duk da ni nace ka siya mata mgana mukayi da mallam ya nuna min Rike waya ga Amina yayi sauri sannan Duba da har yanzu akwai kuruciya a tare da ita..hakan zai Dauke Hankalinta har ya Taba karatunta da muke Fata ta Samu,ya nuna min na bari sai zuwa gaba in kazo ka tafi da itan sai ka siya mata wayar Lokacin tana gabanka zaka kula da Motsinta yanzu kuma ya nuna min gaskiya a"a shiyasa kaji Shuru ban bata wayar ba tana nan na ijiyeta..! Cikin gamsuwa da mganar ta yace"Hakane Hajiya..! Hajiya tace"To kaji yadda mukayi da mallam da Dalilin dayasa kaji shuru..Sannan yace in kana son jin Lafiyarta ne ka kirani ko mallam din sai in ta na nan sai abata ku gaisa..! Danmallam yace"Shikenan Hajiya Allah ya kara girma..! Hajiya ta amsa da Ameen kafin tace"suna Hadda ammah ina ga bazasu Dade ba in sun Dawo zan kiraka sai na Hadaku..! Cikin Ladabinsa ya shiga Fadin"Allah yasa agama Lafiya Hajiya Allah ya kara Nisan kwana..! Ta amsa da Ameen suka rabu bayan ta Tambayi Iyalansa da ayyukansa. To sun ma gama wayar ba Dadewa wajen azahar sai ga su Aminan sun Dawo suna ta Murna an basu Hutun Sati ukun Dadinsu Daya gobe zasu fara Exam din second Semister a makarantar boko satin daya gabata Gabadaya Revision sukayi. Amina ke fadin Dama islamiya ma ta bata da Hutu ai da sun ji Dadi. Ba"a basu Sakamakon su ba sai Sun dawo Hutu sannan. Anan Shashen Hajiya sukayi sallah Sukaci abinci Hajiya na ciki bata san Amina da Hamida sun koma gida ba Tana zuci zucin ta Kirata sai ta Kira Danmallam din ta Hadasu ko da ta Fito sai Hanne kawai ta gani a Falo ita ke Fada mata Su Amina sun tafi gida kai Tsaye tace Hanne taje ta kira mata Aminar. Hanne ta mike ta saka Hijabi ta tafi tana zuwa ta iske su acikin Dakinsu har Amina ta kwanta bata ga mamanmu ba tana cikin Dakinta ta kwanta in ji Hamida jawaad ke ta wasa da Karamar kwallo a Tsakar gidan. Da Farko Amina Dataji Hanne na Tashinta kin tashi tayi sai da tace mata Hajiya ke kiranta sannan ta Mike tana fadin"Kice Wlh Hanne..! Hanne ta mike tana fadin"Au nace ma Wlh..!? To ki zauna kin ga tafiyata..! Amina ta mike tana fadin"Tsayani Hanne mu je..Fatana Allah yasa ba gida zata saka Idi ya kaini ba..! Hamida da Hanne suka kalli juna kafin Hanne tace"To in chan din ne fa..? Ai kince gidan mijinki ne..! Amina na saka Hijabi batayi mgana ba sai da ta gama sakawa sannan ta Dago Tana fadin"Ni yaushe na Fada..? Allah ya isa na, wuta bal bal in ban Fada ba..! Hamida na Dariya tace"Daman chan Allah ai ya ishi kowa Amina..! Harara ta balla musu kafin ta bangaje Hamida ta wuce fuu hamida da Hanne suka.bita da kallo Hanne tace"Kamar an kara mata bala"i wlh bayan auran nan..! Hamida tace"Kowa ma haka yake fadi..ya danmallam zai yi mganinta bari su koma Madina ki gani nan ta raina achan Ubanwa zata mawa .! Hanne na Dariya tace aifa Daganan ta bi bayan Amina zuwa gidansu. Koda Taje Amina da Hajiya na kuryan Daki Hanne na shiga Hajiya Data Kira Danmallam bai Dauka ba ta kalli Hanne ta nuna mata kofa Tana fadin"Jirata afalo..! Hanne ta Tura baki kafin ta fita Amina ta Fakaici idon Hajiya tayi ma Hanne gwalo ita azatonta wani abun Dadi Hajiya zata bata sai da wayar Hajiya ta shiga kidan larabawa taga Hajiyqn ta Dauka ta mika mata tana Fadin"Karbi Mijinki ke son mgana Dake..! Ta fada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Dakin Harda Rufo mata kofar Bedroom din Amina gabanta ya Fadi tabi wayar da kallo ga sunan Danmallan nan baro baro na kan Layi sai jikinta ya fara rawa aranta tace na shiga uku ni Amina Allah yasa ba wani Abu akace mai nayi ba.. Jikinta a sanyaye ta kara wayar kunne Daidai Lokacin da Sanyayyiyar Muryansa ta Doketa Cikin Sallama da Hausansa daya Cakude da Larabci. Sai da ya kara maimaita Sallamar sannan ta amsa Bakin da jikinta na rawa Tun kafin ya gama rufe baki Tace"Ina yi..yini..! Ajiyar zuciyar daya sauke har sai da ta jisa a kunnenta Dayaji muryanta sai yaji Salama da natsuwa Cikin Taushinsa yace"AMINA...! sai taji kamar yafi kowa iya Fadar sunan nata jin yadda ya kirata ita bazata iya tuna ko yama taba kiran sunanta ba Haka ba, jin tayi shuru yasa ya kara cewa"Amina kina lafiya..? Cikin Sanyin Jiki tace"Na"am..eh lafiya kalau..!" "Ya jikin ki..? Ina fatan kin warke babu kuma inda ke miki ciwo..? Ya fada kai Tsaye domin baya Fatan ace wani abu kuma ya tashi bayan Tafiyarsa kunya ta kama Amina ta Dukar da kanta kamar yana ganinta ta kasa mgana sai gabansa ya Fadi da Sauri yace"Ko da wata matsala ne..? Da Sauri tace"A"a na warke..! Afili ta Furta"Alhamdulillah..! Kafin yace"Naji Dadin haka ina Fata kamar yadda kikamin alkawarin baki gayama kowa ba ko..? Sai da ta gyadamai kai kafin tace"Eh ban fadama kowa ba..! Cikin jin Dadi yace"Dakyau naji Dadin Haka..Ya karatu fata kina maida Hankali wajen karatu..?. Da Sauri tace"Eh yau ma mun yi Hutun Hadda..Gobe ma zamu Fara Jarabawa a boko..! Kai ya gyada kafin yace"Allah ya bada sa"a..ki rika maida hankali kinji ko..? Ta gyada kai ya cigaba da Fadin"Sannan ban da wasa ban da Fada ban da gujeguje ke yanzu ba yarinya bace kin tashi Daga su Hamida ke matar aure ce ba Daya kike Dasu ba kina jina ko..? Nan ma kai ta gyada mai yace"Baki da baki ne..! Ba nace ki daina min mgana Da kai ba .! Da Sauri tace"Naji insha Allahu..! Ajiyar rai ya Sauke kafin yace"Kina Bukatar wani abu..? Tace bakomai kai Tsaye yace"Ki rika gaida Sakina in kun hadu tana gaba Dake kinji ko..? Amina ta Tura baki kafin tace"Ni fa in na ganta batamin mgana sai tayi ta Hararana har zagina ma tanayi..! Cikin mamaki yace"Ita Sakinar..? Amina tace"Eh shiyasa nafi son zaman nan fiye da chan sannan achan ina jin Tsoro da Daddare bana iya barci don Allah ka Fadama Hajiya ta rika barina ina kwana anan in ka Dawo sai na koma achan..! Kawai sai ta sakamai kuka sai yaji Hankalinsa ya tashi meke Damun yarinyar nan ne Cikin Tausasa Murya yace"Naji ki daina kuka zan mata mgana..Daman baki daina Firgita cikin barci ba..? Tace mai eh sai da yayi shuru kafin yace"Ki samu mallam yau da Daddare in ya natsu ki Fadamai abunda kike jin in zaki Firgita kin ji ko..? Tace"Na Fadamai..? Yace"Eh ki Fadamai sannan mganar Zagin ki da Sakina ke yi kada ki Fadama kowa har su Hajiya zan mata Fada insha Allahu zata Daina ke dai in kin koma gidan kun Hadu ki rika gaisheta saboda ko bakomai Tana gaba Dake kuma a islamiya an koya muku yin biyayya ga na gaba da ku ko ba Haka ba..? Tace eh ya cigaba da fadin"To ki rika bata girmanta kin ji ko..?. Ta amsa da toh bai Tsawaita mganar ba yace"Zan ce ma Jafar a Cefanan wannan watan ya siya miki Goldenmorn da Cornfkles Saboda Saukaka miki Wahala sai ki Rika sha in zaki tafi makaranta..! Tace "To nagode..! Ya amsa ta da Fadin"Kada ki damu komai kike Bukata kada ki tambayi Hajiya ko mallan ki yi ma Jafar mgana ko kuma ki Dauki wayar Hajiya ki kirani kinji ko..! Nan ma tace mai da toh tagode Dagnan yace ta maida Hankali a karatunta ta amsa mai Daganan ya mata sallama ya kashe wayar. Tabi Wayar da kallo Tana Tura baki wai ta rika gaida Sakina Tab wannan mara mutumcin ne zata gaisheta.. Shi kuwa sai da sukayi mgana yaji Hankalinsa ya kwanta har ya natsu ya Cigaba da Duba Takardun Dalibansa da sukayi gwaji. Da suka gama wayar kunya ta Hana Anina fitowa sai da Hajiya ta Shigo Daukan abu ta ganta zaune tayi shuru tace"A a Mamah tunda kun gama wayar ki fito falo hanne na jiranki mana sai ki zauna ke kadai..! Jin haka yasa ta mike ta mikama Hajiya wayar, ta karba ta Fice da Sauri Hajiya ta bita da kallo tana Mirmishi a Cikin aranta tana Fatan addu"an su Allah ne ya karba na amitar da Ruhin Amina da Danmallam waje daya. Amina na fita Hanne ta taso tana Tambayanta da wa tayi waya Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bansani ba..! Hanne na Dariya tace"Nasani Ya Danmallam ne..ko..? Amina ta mata wani kallo kafin tace"In ma shine sai na Fada miki..? Sirrin miji da mata..! Hanne ta saki Dariya kafin ta Ja Hijabinta tana fadin"Bari naje na gayama Hamida..Sabon Update..! Amina tayi Tsaki kafin tace"Ai ke Hanne mijinki ya shiga uku..duk wanda ya aureki ya auran ma kansa sai kin hada Fada a Family din mijinki Saboda munafuncinki..! Hanne bata bi ta kanta ba ta fice Amina tayi zamanta Falon Hajiya chan sai gasun dawo Tare Hamida sai kara maimaita abun da Hanne ta gayamata take yi Amina ta musu wani banzan kallo kafin tace"kusan dai ni yanzu ba Sa"arku bace ko..? Igiya uku ne akaina..Taimaka muku ma nake yi ina yawo da yara. ! Hanne da Hamida suka saki baki ganin haka yasa ta Musu gwalo tatashi da gudu ta Fada Dakin su Hanne Tana Dariya suka mara mata baya suna fadin yau sai ta gayamusu su waye yara..? Ranar dai anan suka wuni Shashen Hajiya suna abunda suka saba sai bayan sun dawo islamiya ne Hajiya ta saka aka maida Amina gida tana kunkuni Tana komai bata samu yima Baba mallam bayani ba sai washegari da suka dawo makaranta ta Fadamai ya Dade yana mamaki ya tambayeta yaushe ta fara tsorata tace tun tana karama ta dade mallam ya Dinga Fadin Sakacin mamanmu da Aba da Amina na Fama da wannan Laluran ammh bsu sani ba Hajiya ce ma ta Lallasheshi ya bar mganar da yace har Aba din sai ya kira da mamanmu ya musu Fada. Shi ya Rubuta mata addu"o'i ya bata yace ta Rika karantawa Duk Dare in zata kwanta Tare da Sauran addu"an barcin da Annabi ya koyar damu. Amina yadda Taga Mallam ya Dau abun ne yasa itama bata Dauka da wasa ba sannan Danmallam ma sun sake mgana da wayar Hajiya Data Fadamai yadda sukayi da mallam ya mata Fada kan ta Dage kada wasa ya Dauke mata Hankali ta rika kwanciya bata karanta su ba. Shiyasa ta Dake bata kwanciya sai ta karanta sai gashi kuma Cikin ikon Allah tunda ta Dage sai ta samu Saukin Firgita din sai abunda ba"a rasa ba Danmallam har da mallam sun yi mgana Mallam nata fada yana Fadin da Haka Umaima ta Fara gashi nan suna so su taba mata kwakwalwa Dannallam yana so ya Fadama Mallam bayan haka ma yana Zargin akwai wani abu Tattare da Amina sai dai kuma bai da Hujjan hakan ammh yana so sai in ya kara Dawowa ya Zauna ya Fahimci matsalanta Domin Ranar da abun nan ya Faru tsakaninsu da Washegarin nan da Safe yaga tana wasu abubuwan da Dole tana da wani abu a Tattare da ita. ******* Kwantashi ba wuya a wajen Allah su Amina har sun gama Jarabawarsu sun yi Hutu taso ta zauna anan tayi Hutunta Hajiya ta hanata sai ta Roki Baba mallan kan su Hanne su Bita ko Sati Daya su yi da Farko Hajiya ta Hana sai da Mallam ya saka baki Sannan ta amince suka Tattara suka koma chan da Niyar Sati Daya zasu yi Saboda islamiya basu yi Hutu ba. Mamanmu bata Damu ba da akace Hamida zata je gidan Amina Domin alokacin tana Tsakar Cin Duniyarta ne Domin komai tace Aba ya bata baya Gaddama Kudi yake sakar mata bana wasa ba ta zama Tauraruwa a wajen sa Mamanmu ta samu Cikar Burinta Fiye ma da yadda take fata shiyasa ta manta da kowa da komai ko Anty Amarya ta kirata bata ma kaunar Hakan gani take tana neman Takura mata Shiyasa Amina ma bata gabanta Ta barta da Anty Amarya chan itace Zatayi mganinta ita yanzu Sa"idu ne agabanta yanzu shawaran komai sai yayi da ita sai abunda tace koda yace Jafar yace kaza ya kamata ko Hajiya sai tasan yadda tayi ta Kushe mganarsu ta sauya da nata Shiga kawai take tana fita Daga kayan alfarma kamar wata Yarinya sannan Malaminsu tana sakarmai kudi sosai Domin ta yaba da aikinsa Anty Amarya kuma tana nan tana Jiran gawom Shanu domin ta yarda da aikin Malam ya sanar da ita Nasara tatace shiyasa bata Damu ba ta koma ta Zauna tana jiran tsammani kamar yadda ta basa duka yardanta Shiyasa ko Sakina ta kirata tana mata Korafi take mata Fadan bata da Hakuri aiki nawa suka basa kuma ya Biya musu Bukata..? To wannan ma ta Zauna ta Jira komai zai zama Daidai da yardan Allah abunda basu sani ba Daga wannan Lokacin aikin ya kuskure musu sannan zasu cigaba da jiran majirata ne Jiran da zai kai su ga Ranar Nadamar su da Tonon asirin su..! Ko Hutun da su hanne suka tafi Sakina kamar ta Haukace saboda Bala'i Amina Mahaukaciya take so ta maidata,gwara ma su Hanne suna dan jin mganarta banda Amina sai ta gama masifarta sun ba'ta mata Falo ko Kitchen Amina ta mata gwalo ko Ta mata Tsaki ta shige Daki abunta Sakina taci ji Yatsa kamar me..? Kamar yadda yace a Cefanan watan nan an kawo su Goldemorn su Amina an samu banza ana ta Wadaka madara kuma da kayan Tea kafin Sati sun kare saboda yadda suke barnan sa basa da aiki sai dan sululu ko Wainar Fulawa gashi Sakina bata son kazanta su kuma in suna aiki a Kitchen din sai sun yi kaca kaca dashi in tayi mgana Hanne da Hanida kadai ke Sauraranta banda Amina da take maidata ma mahaukaciya. Sakina abun ya isheta kullum sai ta Kira Danmallan ta kaimai karan Amina da kannensa shi har ma ya gaji Saboda bai isa ya kore su ba Amina Matarsa ce sannan su Hanne kannensa ne ko ba aure suna da Damar zama agidansa watarana da abun ya ishesa sai yace ta bama Amina wayar da an bata ya fara mata Fada sai ta saka kuka tace In ta gaishe da Sakina sai taki amsawa ta bita da Zagi sannan bata barin su suna shiga Kitchen sai tace suna mata kazanta Ayadda take mgana ne yasa Dole ma ayadda da ita sannan tace ga su hanne ma yaji ta bakinsu su hanne kuma basu taba kwaye ma Amina baya ba, sai su karantamai yadda Amina tace Daga karshe sai abun ya koma kan Sakina yayi mata Fadan itace babbar banza tana Biyema yara sun rainata sannan kada ta kara Hanasu shiga kitchen ta bar su dafa abunda suke so itama ta Dafa nata baya son Fitina. Tunda ga ranar ko Takai ma Korafin Amina ta mata kaza bai Sauraranta Anty ma Zaginta take yi tace ta Daina Danunta tunda ita Sakarya ce zata Zauna yara kanana su gagareta Alhalin basu san yadda yaran nan suka Sakata gaba bane barin ma Amina in ta fito falo ta gansu ta rika waka kenan tana cema mata agwagwa in ta yi mgana ta maidata mahaukaciya sannan ba Tsayawa ma take yi ba,ballatana ta Daketa ta huce. Su hanne wajen kwanansu goma Daga su Har Aminar basa zuwa makaranta da Hajiya tayi mgana ne Mallam yace ta rabu dasu Idi ya rika zuwa yana Daukosu yana kawo su makarantar Daganan,saboda dukkansu yara ne sannan nan gaba kadan In Aminar ta bar garin ina zasu ganta..? Sannan kuma suma watarana gidan auransu zasu watarana sai dai labari..da Haka ta kyalesu suka zauna achan sai dai Idi ke zuwa yana Daukosu da an tashi kuma ya maida su. Cin Duniyarsu da Tsinke suke yi ko ajikinsu Sakina ta koma zaman Daki bata Fitowa saboda su in tana son Tsira da Mutumcinta Ranar kwatsam sai ga Aliya matar Aliyu sun zo kawo Amarya wata Diyar kanwar mamanta ne shine tazo gidan ta iske Sakina cikin Daki Amina ta gagareta bata iya ma Fitowa sanda Sakina ke Fadamata tana kuka Sai taga Laifin Sakinar da ta Zauna yarinya karama ta gagareta. Taja Sakinar suka fito su Amina na Falo sunyi Daidai ga Filets nan da Kofuna da gorinan lemuka da suka gama dasu nan basu Dauke ba suna Hira Ita a Dole sai ta kwatan ma Sakina yancinta.. Haka ta Dinga surfama Amina Zagi tana kiranta kwaila kazama mara Tarbiya su hanne sukayi Tsuru Tsuru Amina ranta ya baci ta mike ta rama Zaginta da Aliya ke yi ita kuma tace Zata Daki Amina ai ko sun ga Hauka Amina ta Tsaya kikam idanuwanta sun juye ba baki sai Fari tace in Aliya ta isa ta tabata tagani Sakina ke jan Aliya tana ta bari kada ta tabata ta ja mata bala"in wajen su Hajiya. Ita kan Aliyan ta Tsorata bata Taba Aminar ba suka koma Daki tana Borin kunya Amina kuwa ba wani Abunda ya Sameta Zafin ranta ne ya taso mata Taso ta tabata ne Daga Sakinar har Aliyan sai sun raina kansu Wlh sai kuma Allah yaso su su Hanne na tabata Hakuri ta balla musu harara tace sun cika Tsoro ba wanda ya isa ya Takura musu acikin gidan nan. Aliya taso kwana ne ammh ganin yanayin Amina yasa taki kwana ta koma gidan Amarya ta kwana ko Washegari Datace zata dawo bata Dawo ba ko da Sakina ta Kirata tace mata gata a Hanya zata koma gida ammh Tana zuga Sakina kan Wlh in Amina ta kara mata rashin kunya ta kamata ta mata Dukan tsiya Sakina jinta kawai take ina ita ina taba wannan yar gold din ai sai Hajiya ta saka Umar ya Saketa. Allah ne ya taimaketa suka koma makaranta Hajiya tace su Dawo gida idi yazo ya Dauketa sai ta Samu Sauki Bata ma haduwa da Aminar sai ta bar gidan take Fitowa sannan Daga ranar jumma"a sai Lahadi take dawowa tana ganin Lokacin Dawowarta yayi zata shige Daki karfi da yaji Bala'in Amina da jindalinta ya Saka Sakina ta kasa Sakewa agidanta. Gashi Danmallam ya Daina Sauraranta indai kan Amina ne yace yana wata kasar ta daina tadamai da Hankali baya so in bazata kama girmanta ba bazai iya Hana Amina ta mata Rashin kunya ba abu goma da Ashirim ga rashin miji ga Fadan Anty Amarya Data Kirata sai tace laifinta ne sannan ga Amina ta Sakota gaba..! Ana cikin Haka Sadiya Diyar Anty Amarya ta Haihu bakwaini yarinyar tazo ba rai anan Dutse su Sakina ana ji sune gaba gaba ita da Hj.Nasara da Hajiya Babba suka tafi suka Duba Sadiya Dake asibiti domin ance ta Zubar da jini sosai achan suka Rabota Tunda Danmallan ya barta ita ta zauna da Sadiyan har aka sallamota Daga asibiti duk da ga yan"uwa ammh Anty Amarya tafi yarda Sakina ta Zauna da Sadiyan. Bayan sun Dawo gida ne Sakina ta Fara Zazzaabi har da su karin ruwa koda akaje asibiti akayi Test aka gano Tana da Shigar ciki kimanin wata Uku da kwanaki Ashe koda Danmallam ya Tafi ya jefa kwallinsa araga a maran Sakina basu sani ba. Murnan wajen Anty Amarya da Sakina ba"a mgana kamar an basu aljannah Hajiya da mallam ma Tare da shi kanshi gogan Danmallam Domin yana matukar son yaga kwansa a Duniya,Sannan da kansa ya Sanar da Sarood ta tayasa murna Har dai yanzu shuru ne ba wani cigaba ammh basu sare ba suna cigaba da shan mgani shi dai har yanzu ne bai yarda da Shawaran Aliyu na ya kira mallam ba yana tunanin al"amarin nasu ba Sihiri bane. Mamanmu dataji itama tayi murna sannan tasan yanzu tunda Cikin Sakina ya samu sai Madina ta barta taci Gumin Wahalarta ta Daina Damunta. Su ba Fatan cikin ya zauna suke yi ba kansu yayi girma suna ta Feleke Anty Amarya taso Sakina ta Dawo gabanta ta raini cikin mallam ya hana Saboda za"a bar Amina ita kadai Gidanta ta koma ammh sai Ta tafi da Sa"adatu tana kula da ita ana zuwa Daukansu Ita da Amina da ko mgana basa ma juna Amina taji zencen cikin Sakina ko ajikinta tunda ko"ina Zencen cikin ya Zaga. Haj uwani na gefe tana kallonsu aranta Dariya take musu domin tasan wannan karon ma ba zai zauna ba Haka kuwa akayi yana da wata Hudu watarana da Daddare Sakina ta tashi Cikin Jini Hankalin Sa"adatu ya tashi ta Kira Anty Amarya koda ta zo ita da Idi Direba suka tafi asibiti sai wankin Ciki akayi ma Sakina cikin jikinta ya Sake fita karo na Hudu. Abunda Haj.Uwani bata sani ba in na Sakina ya sake zubewa daman chan Allah bai yi Rayayye bane ammh wanda Allah zai rayasa yana nan har ya fara zama gudan jini batare da kowa ya Farga ba Hatta kuwa da wacce Cikin ke jikinta. *Janafty**TFZB2012* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Wannan karon ba Anty Amarya kadai da Sakina suka shiga Tashin hankali ba harda mallam da Hajiya Tare da Uban gayyar Danmallam da kuma ilahirin Masoyansu sun tausaya musu bisa rasa wannan cikin ma a karo na hudu kamar sauran. Mallam shi ya saka ayi ma Sakina gwaje gwajen mahaifa domin a Fahimci inda matsalan take Dayake wani asibitin kudi dake cikin gari Anty Amarya ta kawo Sakina duk kudin da aka kashe mallam ya Dauki Nauyi sannan suna tsaye kan Sakina shi da Jafar da Nasir da ita kanta Hajiya da Aba din sakamakon Sakina ta Zubar da jini yasa sai da aka mata karin jini gabadaya yan"uwanta ne Anty Amarya ta kira tana kuka ta Fada musu wadanda ke kusa suka zo aka samu aka gwada jininsu sai Allah ya taimaka jinin kaninta wanda ke bimata yayi daidai shi aka diba aka sanya mata. Sakina sai da ta kwana ta wuni sannan ta farfado ko ba"a fada mata ba tasan ta rasa cikin ta ma a wannan karon domin haka take yin indai zata yi bari tayi ta zubar da jini sannan ta Fice Daga Hayyacinta na wani Lokaci. Sakina tayi kuka kamar ranta zai fita wannan karon Anty bata da bakin lallashinta domin ta Sare ta kuma kara yarda da Hasashenta na Tabbas akwai wanda ke lalata cikin Sakina akwai wanda ke neman shiga Tsakaninta da Cikar Burinta ko waye kuwa in ta ganosa sai ya gane bai da waye ita Madina bata fito ba sai da ta shirya. Anyi ma Sakina gwaje gwajen da Mallam yace an kuma tabbatar musu da komai lafiya harta mahaifanta Lafiyalau ita Hajiya har tana Fadin ko kila Sakinar tana da Raunin mahaifa ne ammh sai likita ya tabbatar musu da Komai lafiya Sanadin barin dai bai gano wani abu ba sai a bar shi da Allah ke ikonsa Domin shi ke kashewa ya kuma ya rayashi alokacin dayake so Sannan Haihuwa ta sa ce ga wanda yaga Dama yake bamawa Haka Mallam ya dinga fadama Sakina alokacin Dayake mata Nasiha a daran Data cika kwana Hudu asibitin Daya kara zuwa Dubata shi da Hajiya da Daddare. Hajiya ma ta kara da nata Nasihun Saboda duk mai imani in yaga yadda Sakina ta dawo sai ya Tsausayamata kuka kadai take yi,mganganunsu kwata kwata basu shiga kunnenta ba Hango kanta take a matsayin Bora duk Ranar da Haifarma Umar magaji ya kuskure kanta sannan ta Fara Sarewa da Tunanin Anty bazata iya ba Sannan wannan Burin nata bazai Taba cika ba Nasara kuma su daina Hasasota nan kusa tana da Nisa kafin su isketa bama domin haka ba itama Tana so ta Haihu sosai take son Taga ta Haihu sannan tafi so kowa Sanin yadda Umar ke son Haihuwa ya Fada mata ba Sau Daya ba sau Biyu ba,kawai yana da kawaici ne sannan addininsa yasa ya yarda da Allah ke yi alokacin da yaso shiyasa bai cika nuna Damuwarsa sosai ba.. Shiyasa har su mallam suka fita Sakina ma bata cikin Hayyacinta Anty ke kwana da ita tana kula da ita suna Fita Sakina ta Fashe da wani kuka mai karfi Daga karkashin ranta Anty Amarya ta taso zata riketa ta Daga mata Hannu tana fadin"Don Allah Anty kada ki hanani kuka ki bar ni nayi domin shine kadai zai sa naji Sanyin abunda ke damuna acikin Raina..! Tafada tana Dakatar da ita da Hannu Dole Anty ta koma baya ta Jinjina kai gabadaya bata cikin natsuwarta Saukinta Daya yadda mallam da Hajiya da yan"uwan Danmallam ke Tsaye kan sakina da shi kanshi Danmallam din,arana ya kira fiye da sau Biyar yana tambayan Lafiyan Sakina Sannan ya Turo abokinsa Aliyu dashi ake ta Zirga zirga in bai zo yau ba zai zo gobe har da matarsa Aliya yazo Abinci kuwa baya zuwa hannu Rabbana da kwalayen maltina da kayan maarmari saboda karin jini ga ita Sakinar Ta kira Dayyaba sun yi mgana gobe take so in kanwarta A"i tazo daga Dutse zata bar mata Sakina ta kula da ita zata koma wajen mallam tamai bayani so take ta gano wanda ke lalata mata aikin data wahala tayi shekaru tana Fata akansa in ko Zarginta ya Tabbata kan Uwani sai ta raina kanta sai ta Fahimci wacece madina ba marliya ba. Tana gani Sakina na gunjin kuka bata da karfin gwiwan hanata saboda ta gaza Duka alkawarin data mata ta kasa cikamata,maimakon ta Fahimci Talalar da Allah yayi musu ta kare ne suke ganin sabawa akan lamarinsu ammh ina idonsa ya rufe gani suke a koda yaushe nasara tasu ce. Suna Mota zasu koma gida Hajiya Dake gefen mallam ta kallesa tana Fadin"Mallam ka kira Danmallam ka yi mai Nasiha da Hakuri ko..? Domin jiya da mukayi mgana yace min yana gida kwance bayajin Dadi..kuma ko shakka babu abunda ya faru ne ya tabasa kamar yadda ya taba Sakina wannan karon..! Mallam ya muskuta kafin yace"Na kirasa da Safe munyi mgana..Sosai nayi masa nasihan na kuma tunasar dashi cikar imani shine yadda da kaddara mai kyau ko akasinta na horesa da yayi Hakuri ya jira kadan kila Tanadin da Allah yayi masa yana gaba ne Rashin hakurinsa sai ya bata komai..! Hajiya tace"Hakane kan mallam..Allah yasa mu dace Allah ya basa zuru"a Mai albarka..!. Mallam ya amsa mata cikin Damuwa a karkashin ransa yana jin Tsausayin Umaru ache kana neman rufe shekaru arba"in ko Haihuwan fari bakayi ba sa"o"insa ya tabbata Har da masu ya'ya goma wadanda sukayi aure da wuri ma kenan ga dai Amininsa Aliyu nan baya baya yayi aure ya"yansa Biyu tabbas yasan akwai Damuwa ammh bazai barsa ya nuna gazawarsa ba zai cigaba da Tunasar dashi Hakuri da Rayuwa a duk sanda tazo masa da kuma yanayin datazo maka sai ka saka Hannu Biyu ka karbeta. Kamar yadda Anty Amarya ta kwana da kuduri gari na waye saboda ma tana Sauri bata jira A"in tazo ba sun dai yi waya tana Hanya ta kusa shigowa ta bar Sakina tace mata zata je ta Dawo alokacin har Jafar da Nasir sun kawo breakfast Matan su suma suna kokari sunzo sun duba Sakina Daganan kowannen ya wuce wajen aikinsa. Batare da ko Sanin Mallam ba ta Dauki Hanyar Dutse tunda Gidan malamin nasu chan wani kauye ne kafin a shiga garin Dutse ne da wuri ta isa akwai layi ta jira kadan sannan aka bata izinin shiga tana shiga ko kafin tayi mgana ya Zayyana mata Duk abunda ya faru yace Garzali ya sanar dashi komai saboda haka ta Bada kudin da aljanu zasu sha jini kawai tayi tafiyarta nan da Sati Daya zai kirata abunda ke nan zai sanar da ita komai nan ta Bude bakin jaka ta Zazzage mai kudi da batasan ko nawa bane Kudi ne dai masu yawa har da wadanda Sakina ke samu a asibiti in anzo gaisheta sannan shekaranjiya Jafar ya kawo mata 30k yace in ji Danmallam yace ta rike a Hannunta koda wani abu zai taso ta saka a jaka Saboda komai na kudi mallam ke gudanarwa ko sisinsu basu kashe ba Har da su ta zubema Malamin nasu sannan ta kamo Hanyar Gumel Ranta na kuna ta kosa agano wacce ke neman shiga Tsakaninta da Burinta yadda zuciyarta ke azalzalanta Har taje ta Dawo ba wanda ya Sani daga ita sai Dayyaba sai Allah kawai yasan inda taje ko da tadawo Sakina ta samu barci kanwarta kuma ta zata Gida ta koma tayi wanka ta Huta Shiyasa bata Damu da Tambayarta ba. Sai da Sakina ta kwana goma asibiti sannan aka sallameta ta koma gida Saboda yanayinta yasa sai mallan ya yarda da Rokon Anty Amarya kan Dawo da Sakina gabanta har sai ta Warware,Daman Amina tunda akayi haka tana nan gidan Mallam bata koma chan ba mallan yace Tunda hakane dukkansu su zauna anan in Sakina ta kara jin Sauki sai su koma Tare abun yayi ma Amina Dadi daman ta Tsani zama agida chan sannan ta Tsani zama inda ba Hamida ba Hanne ita dai murnanta da Farincikinta ta gansu tare tana musu Jidalinta suna Dauka. Har ta da Amina duk kinta da Sakina sai da ta Tausayamata ganin ta yadda ta Rame sai katon kai,Dayake ranar da aka sallamo su suna makarata sannan bayan sun dawo islamiya suka tafi sai da suka Dawo ita da Hamida da Hanne Hajiya tace su shiga su gaisheta suka iske ta cikin Dakin sus Sa"adatu zaune ana bata abaya abaki sai ido zuru zuru kamar na mayu in ji Amina da suka fito. Hamida tace"Gaskiya ta bani Tausayi ji beta kamar ba ita ba duk ta rame..! Amina tace"Sai yanzu na kara ganin Gajartan ta ga Katom kai ashe ma dan jikinta na Rufa mata asiri..! Hamida tace"Amina ciwo dai na kan kowa..! Amina ta Harareta kafin tace"Ai ban ce bai kan kowa ba..In kin ji mgana na Tsausaya mata ne..! Hanne dai batace komai ba sai alokacin tace"Tasha Wahala inji Hajiya tace sosai.Sannan ta tada Hankalinta barinta na Hudu fa kenan har ya Danmallam naji hajiya namai Fada har ciwo sai da ya kwanta fa..! chan madina..! Hamida tace"Wayyo da Tsausayi kam..Allah ya basu rayayye..! Hanne ta amsa da Ameen banda Amina da Haka kurum taji ranta bai yi Dadi ba, wai har ciwo yayi saboda barin Cikin wanchan gajerar matar basu Fahimci yanayinta ba ta wuce Shashen Hajiya ta bar su nan Daman a Bakin Shashen Haj.Nasara suka Tsaya suna maida Zencen. Tun daga lokacin sai Kulawar Sakina ta koma karkashin Anty Amarya tunda ashashenta take sannan Hajiya ma har nan take zuwa tana Dubata ta saka su Ladidi su yi ma Sakina Fatan wake da ferfesun kayan ciki Saboda jininta ya Dawo sosai har Hajiya nasara ba barta a baya ba ita da Haj.Uwani Wacce Anty Amarya ke jin takaicin inda ta ganta ta rako Hajiya tana wani iyayi ita hakanan aranta taji bata yarda da ita ba.. Sannan Har mallam ma ya kan shigo ya Dubata Lokaci bayan Lokaci uwa uba kuma duka kannen Danmallam wadanda ke gidan auransu sun ji Labari sun kuma kira sun ma Sakina Sannu harta da Nazir da matarsa matan su Jafar kuma sun je asibiti sannan da suka Dawo ma sun zo sun Kara Dubata Ikram dake kusa tazo ita da Sadiya da Zulaihat sun zo sun kwana Daya sun Dubata sun koma Tunda Mamanmu ta Kirasu ta Fada musu har da goggo Husai Dake Jordan taji Labari ta kira tayi ma Sakina Ya jiki da jajen Abunda ya Faru haka su ya Jawahir suma sun kira harta Aba da basa wani Shiri da Anty Amarya Yaje assbiti bai san iyaka ba da suka Dawo gida ma sau biyu yana shiga Dubata ba saboda alherin kowa ba sai Saboda Danmallam In sakina ta fara kokenta Anty Amarya ta Dinga ce mata kenan"Ai kuka bai kamaceki ba Sakina..Godema Allah zaki yi..Ki kalli abunda ya faru Dake mijinki bai juya miki baya ba yana Tsaye kanki da lafiyarsa da Aljihunsa shi da Danginsa da yan"uwansa hajiya da mallam Sakina kullum suna tafe Shashen nan wajen Duba Lafiyarki wannan kadai ba matakin nasararmu bace.? Tabbas mun samu nasara domin ko bakomai Danmallam da Danginsa suna kimanta ki Sakina suna Darajaki Daraja mai yawa ban gane haka ba sai da wannan abun ya sake Faruwa..! Sakina cikin kuka take fadin"Na rasa Cikina a karo na hudu Anty..Na kara rasashi yaushe zan samu wani Cikin har ya zauna na Haihu..? Anty Amarya tace"Kada ki damu zaki Samu wani cikin..kuma da yardan Allah sai kin Haifar ma Umar Magaji in baki Haihu ba to sai dai ya Dauwama shima bai Haihu ba..Na Rantse da wanda Raina ke hannunsa in Zargina ya Tabbata sai na yi Fito na Fito da duk wanda ke Rusamin aikina ko waye shi kuwa..!. Tafada cikin kaushinta akoda yaushe kalamanta yanzu tuni sun Daina ma Sakina aiki a kanta ta fara Sarewa da al"amarin kwata kwata. Amina suna cigaba da zuwa makarantar su,Sannan tafi zama bangaren Hajiya har Hamida ma tare suke sai suyi sati basu kwana agidan Aba ba suna Shashen Hajiya saboda Hanne sannan ita kanta Mamanmu bata wani Damu ba Amina ba yanzu Duniya ta samu,Daga ita sai Aba ko Jawaad wani Lokacin Wajen su Amina yake kwana ashashen Hajiya Duniya ta samu yanzu Aba bai mata gaddama ko Hajiya da mallam tasha gabansu sai su gama mgana dasu yazo mamanmu na tambayansa zai kwashe ya Fadamata shawara kuma akomai da ita yake sai abunda tace shi yake yi ta kankane komai tana baza buraubanta yadda ta gama Dama shiyasa har Hamidan ba Damuwa da take yi da ita ba yanzu tasan dai lokacin auran su nayi za"a aurar dasu Amina kuma Daman sunan auranta gantali Ita kanta Aminar tasan Mamanmu ta Rage kula da ita kamar baya sai ta Danganta hakan da yanzu ba Yaya ba su ya Zeenatu Hidima tayi ma mamammu yawa tayi mata uzuri sosai,Su Hajiya kuma basu wani Lura ba saboda basu fiya saka ido ba ko da yaya nada rai Amina da Hamida yan Shashenta ne kowa ya sani shiyasa ko yanzu da suka Tare anan bama wanda ya Damu. Sannan in Allah zai ikonsa kan wani abu da karesa da kansa sai ya kaudar da Tunanin mutane akan hassashen wani abu to kamar hakane ya Faru da Amina cikin Lokaci kadan gabobinta suka fara girma kirjinta ya fara Cika har yazo ma yafi na Hanne yana neman fin na Hamida sannan Daga kasanta Hips dinta ya Bude ta fara Fashewa kibanta Daga sama ya Fara sai kuma ta Bude ta kasa sannan Fuskarta ta Ciko sosai yawancin kayanta ma sun mata kadan riguna sai da Hajiya ta saka aka kai aka Buda mata itama taga kiban da Amina tayi sai bata kawo komai ba azaton Cin abincin da Amina ke yi saboda cin abincinta ya ninka na baya har Cikin Dare ci take sannan ga shan Tea madara bata sati take karewa Amina hakanan take hambalamta har sata take yi tatafi da ita makaranta. Har su Hamida sai da suka ce Amina tayi kiba yanzu ko Hamida albarka. Ita kanta Aminar tana jin Canji Ajikinta ammh bata Damu ba Sai itama take Tunanin cin abincin datake yi shiyasa da kuma kila girman da batayi bane abaya sai yanzu take yi. Ranar ma suna shiri zasu makaranta da Safe Dakyar Amina ta iya saka Rigarta ta matseta duk da an kara Budeta. Ta saka tana Nishi kafin tace"ni dai girman nawa bai zo min da Dadi ba..Ku kalle har Tumbi fa na fara..! Suka bi Cikin nata da kallo kafin su saka Dariya Hamida tace"Kirjinki wlh sun fi nawa..Tumbi kuma wlh gashi nan Hanne..! Tafada tana Taba cikin Amina Daya Fara tasawaa taji Tauri ta cire Hannunta Tanacfadin"Sai Taurin bala"i..! Hanne tace"Ke kuwa wannan Abincin Datake narka ai ba Lafiya bane..Dole ta Ijiye Timbi taurinsa kuma Uban Madaran Dake sha ne wlh in baki Daina ba kikayi Kiba Ya Danmallam bazai je dake madina ba domin in kika Hau seleken awon Nauyi aka ga kin yi kiba bamai zuwa Dake..! Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Dama wake son zuwa..? Dariya suke mata ita kuma tana masifan ita ba inda zata je Daganan suka shashantar da mganar. Aranar da sukaje gaida mallam kan su tafi makaranta da suka fita yana Tare da Hajiya ne sai da yayi mata mganar Kibar da Amina tayi hajiya tace kila gabobin girman nata basu bayyana ba sai yanzu Shima sai ya yarda da Haka. Duk wanda ya ganta bai kawo ma kansa wani Tunani sai Tunanin gobobin girma ne suka bayyanan mata Mamanmu kuma bata bi ta kan Amina ballatana ta iya ankarewa da wani abu na Faruwa Anty Amarya kuma sai tayi sati ma bata ga Amina ba in ma ba ta ganta ba, bata ma Tsayawa kare mata kallo balle ta zargi wani abi zai faru. Ana cikin haka aka fara Biyan kudin jarabawar fita ta su Akilu Hajiya tace a biyama Amina sai maallam yace da Aminar da sa"adatu da Hannatu da Hamida duk a Biya musu su zana a SS2 dinsu da hajiya ta nemi jin Dalili sai ya sanar da ita cewa in Umaru yazo ya tafi da Amina madina su hanne kewa zai musu yawa sannan sun ma isa auran suma da su zauna suna Damuwa da rashin Amina suma zai aurar dasu nan da wattani kadan zasu cigaba da zuwa hadda da islamiya kafin Mazajen nasu su bayyana Hajiya bata yi gaddama ba Tunda daman Jafar da Nasir sun fadamata cewa Karatun SS3 din duk maimaici ne da Reviosion shiyasa sai tayi na"am da mganarsa acikin Satin akaje aka biya musu su shida har da Akilu da Zubairu. Amina da taji murna kamar me baza"a rabata dasu hanne ba Sa"adatu ne bata so ba,tayi ta kuka Anty Amarya ko ta kanta bata bi ba, abunda ke gabanta yafi karfi wannan iskancin na Sa"adatu. Allah shi ke batar da Tunaninmu wani Lokaci ga abu a kusa damu sai mu Dade bamu Fahimcesa ba..! ******** Danmaallam achan madina Ko Sarood sai da ta Tausayamai yadda ya kwallafa rai akan cikin Sakina sannan yazo kuma ya tafi Ranar da Mallam ya kirasa ya fadamai da Zazzabi ya kwana,kwanansa biyu agida baya Fita Tana kula dashi,Ita kanta ta Damu sosai sai ta sakamai kuka ganin ya Daina Cin abinci sosai ballatana yawan mgana,da taimakon Mallam da Hajiya da Aliyu ya Dawo daidai da kuma Sarood itama tayi kokarin matuka wajen kula da shi Sosai take basa Tausayi tana da sanyin Hali kamarsa da kuma Hakuri shi kanshi yanzu ya Fara Tunanin mafitan da Aliyu yaso ya Nema tun farko yaki yarda da mganarsa ammh a yanzu yafi Sarood Damuwa Tsausayi take basa ita macece mai Rauni sannan kuma yaji yana Fatan in bai samu Haihuwa ta bangaran Sakina ba,me zai hana ya roki Allah ya basa ta bangaron Sarood Amina dai bai ma saka ta a Lissafinsa ba bai Taba kawo mata Daukan cikinsa nan kusa ba..!..abunda bai sani ba Daman Sau tari Allah yafi bamu abun da muke nema a inda bamu taba Zato ko Tsammani ba..! Washegari yana cikin makaranta ya kira Aliyu da niyar ya Tuntubesa da mganar sai gashi shima ya fara mai mganar bayan sun gaisa Aliyu ke tambayansa matsalansa da Sarood ya ake ciki..? Yace mai har yanzu ba Sauki domin ko ya jaraba jiya iyau ne. Aliyu ya kada baki yace"Shehi ni dai kaki jin Shawarata ne..Naso ka kira mallam ka sanar dashi matsalanka kila ya samo maka waraka Tunda yafimu sanin abubuwan da suka Shafi addini da irin wannan banace ka yarda wani yayi maka ba kasa aranka bamai yi sai Allah kuma wajensa kake neman waraka..! Umar yayi shuru kamar bazai yi mgana ba Jin haka yasa Aliyu yace"Tunda Sakina ga matsalan da ake Samu Shehi me zai hana ka Jaraba Sarood din itama mu gani..! Nasan fa kana son ya"ya bama kai da abun nan yake Faruwa Dakai ba ni kaina abokinka i feel ur pain Umar ina Fatan kai ma ka ka ijiye masu yi maka addu"a watarana..! Danmallam ya gyada,kai kamar Aliyu na ganinsa kafin yace"Shikenan Aliyu zan jaraba shawarka..bari na Kira mallam muyi mgana..! Aliyu yaji Dadi suka rabu bayan ya Bisa da addu"an Allah yasa adace a samu waraka kamar yadda suke fata.. Nan take ya kira mallam sai dai baya gida yace mai yana Jigawa sun zo Taro ne nasu na Da"awa ammh bazai Dade ba zai koma gida in ya koma zai kirasa. Dayake abun na ransa kuma ya Kudiri niyar fadama mallam komai yasa bayan awanni kadan ya Sake kiran mallam din Lokacin har ya koma gida Misalin goma na Dare anan madina Nageria kuma suna fitowa sallar mangariba. Mallam Shashensa ya koma abunda ba Dabi"arsa ba sai sun gama Sallar Isha"a yake shiga gida ammh ganinsa da waya yasa aka san uziri ne ya taso ma mallam din.Tabbas Uzuri ne domin yadda yaga Umaru ya Damu yasa yasan ba lafiya ba wani abu na Faruwa. Bayan ya Dauka sun gaisa da Tambayan gida da iyalai kamar kullum mallam yace"Umaru meke Faruwa ne.? Wannan kiran naka bana Lafiya bane ko..? Danmallam ya kaskastan da kansa Waje ma ya fito saboda ba ya so Sarood taji mganarsu cikin Ladabi yace"Eh ba Lafiyan ba mallam matsala ne dani tuntuni nayi iya bakin kokarina ta bangarena ammh abu ya ci Tura shiyasa na yanke Shawaran kiran ka na Sanar Dakai..! Mallam ya koma ya zauna gefen gadonsa domin kurya ya shige kada ma wani abu ya katsesa a yadda yaji Umarun yasan da wani abu. Cikin Dattakonsa yace"Ina jinka..Allah yasa Zan iya maka mganin matsalan ka Umaru..! Cikin Kunya kamar yana ganinsa ya farama mallam bayanin Tundaga Farkon matsalan har karshe da Mganin Shafan Aljanun da siya mata Tayi amfani dashi ammh matsalan kuma bata kare ba har alokacin..! Mallam yayi shuru yana jinsa har ya gama kansa ya Daure na wani Lokaci,daya sa ya kasa mgana Har sai da Umar ya Kira sunansa sannan ya amsa Cikin Alhininsa yace"Ta bangaranka da ita Sakinar lafiya kalau ko..? Duk da yasanni ammh so yake ya Tabbatar in da lafiya ai in ba lafiya ba ta Dinga samun ciki hartana barinsa ba. Danmallam ya amsa da Eh cikin kunya aransa yana addu"an Allah yasa kada mallan ya sako Amina Har ga Allah bai shirya fadamai ya haikema wannan yarinyar ba duk da ba Haramci yayi ba matarsace ta sunna. Sai Addu"arsa ta karbu mallam bai Tsawaita tambayarsa ba illah kai da ya Jinjina kafin yace"Umaru kana jina ko..? Ka bani nan da zuwa gobe zan yi Bincike na acikin littafan malaman musulunci sosai sunyi bayanai game da ira iran wadanan matsalolin naka..Insha Allahu zuwa gobe zan kiraka da kaina nayi maka bayanin komai..! Danmallam yace"Shikenan mallam..Allah ya kara girma Allah ya kara nisan kwana..! Mallam ya amsa da Ameen Ameen ya Cike da fadin"Kada ka damu da Yardan Allah zamu samu mafita..Domin Qur"ani waraka ne gamu bayin sa kaji ko..? Ya amsa cikin yakinin kamar ma ya Samu mafitan daganan sukayi sallama Mallam ya koma yayi jugum yana nazarin matsalan Umar.. Tabbas yana da zurfin ciki sannan yaga Hakurin ita Saratun,bazai ce ga matsalan ba kai Tsaye tunda Basir ko Sanyi na Haifar da haka ammh nasu sai dai Raunin gaban namiji ba ta ki yin amfani ba gabadaya sannan shi da Sakina lafiya lau ita Saratun ne matsalan. Lalle akwai wata mgana a kasa shi ba Malamin Duba bane ko na Shirka shi malamin sunna ne da Qur"ani in an kawo matsala ba kansa Tsaye yake yi ba yana Duba Littafan addini na malamai da kuma Qur"ani Domin neman mafita sannan akwai Irin irin matsalolin nan na Sihiri da malamai Dabam dabam sukayi littafai da Dadama Domin warware ma Mutane kai dasamun Mafita shima haka zai yi bazai yi zargin wani abu kai Tsaye ba sai ya bincika. Ana Idar da sallar isha"i ya Sake dawowa cikin gida yau ko Aba basu Tsawaita Hira ba sukayi sallama ya wuce Shashensa Ranar hajiya ke da Turaka ko da tazo ta iske malama nata Nazarin wasu littafai sama sama ma suka gaisa abinci ma sai da ta matsamai yaci kadan Abun bai bata mamaki ba taga ko barci bai kwanta ba tasan sa da son nazari wani Lokacin ammh bai hanasa kwanciya ammh sai gashi ya kasa barci data tambayasa yace yana wani Nazari mai muhimmaci ne,tayi kwanciyarta in ya gama zai zo ya sameta Dole ta shiga ta kwanta ta kyalesa. Shi kuma sai wajen biyu na Dare ya gama Bincikensa sannan bai kwanta ba ya Dauro alwala yayi nafilfilu da addu"o'i sannan ya kwanta wajen uku da Rabi Biyar na cika ya Farka ya Tada Hajiya ya fice zuwa masallaci. Sai Chan Safe ya Dawo Shashensa ya Tsaya masallaci sun yi meeting da Dattajan anguwannin kusa dasu. Wanka kawai yayi ya karya Lokacin Hajiya ta koma bangaranta ya Kira Umar bai Dauka ba sai da ta katse sannan ya Kirasa yana aji ne yana karatu yana ganin kiran maallam ya nemi lamini ya fita waje ya kirasa. Bayan gaisa kamar yadda suka saba Mallam ya fara mgana cikin Dattakonsa kamar haka. "Umaru ka yarda da Allah shine mai yi kuma mai hanawa..Sannan ka yarda da duk abunda ya samu bawa Daga garesa ne sannan kowata Lalura daga garesa ne sannan Waraka ma yana wajensa ko..? Danmallam ya amsa da eh Mallam ya Cigaba da nuna mai Duk abunda zai Faru da bawa koma ya faru kada ya Zargin kowa ya Dauka Daga Allah ne kuma garesa zai nemi waraka bai Fito ya mai bayanin Sihiri bane ammh Cikin Dattakonsa yace"Ka san Acikin Qur"ani akwai ayoyin da Allah ya Fadamana suna karya sihiri ko asiri ko .? Ai kasan su..? Cikin Sanyinsa yace"Eh mallam..! Maalllam yace"karantomin su naji..! Umar ya gyara Tsayuwa ya fara fadin"SURORIN AL'QUR'ANI GUDA SHIDA DAKE KARYA SIHIR KO ASIRI. 1. SURATUL TAUBA: AYATA 14. 2.SURATUL YUNUS :AYATA 57. 3.SURATUL NAHIL: AYATA 69. 4.SURATUL ISRA"I :AYATA 82. 5.SURATUL SHU'ARA :AYATA 78_82 6.SURATUL FUSILAT: AYATA 44. mallam ya jinjina kai kafin yace"Dakyau..To kamar yadda ka lissafasu ka samu ruwan zamzam ka karantasu duka ka tofe aciki ka rika Shafe al"auranka duk dare in zaka kwanta da jikinka gabadaya sannan ka rike addu"a da azkar domin koma menene Yana jikin ka ne ba jikin ita Saratun ba..! Danmallam ya jinjina kai yana Fadin"zanyi haka insha Allahu nagode mallam Allah ya kara girma..! Mallam ya amsa da Ameen yana fadin"Allah ya warware mana..Allah yasa adace Allah yasa asamu waraka..! Daga haka sukayi sallama Danmallam Ya Dade tsaye kafin ya koma cikin ajin sa ya cigaba da koyarwa karkashin Ransa kuma yana gasgasta mganar Aliyu koda mallam bai fito yace sihiri bane ammh Yanayin addu"o"in da ya basa na karya duk wani Sihiri ne ko asiri. Yana fitowa da ga ajin ya koma Office ya Kira Aliyu ya fadamai yadda sukayi da maallam Aliyu ya rike baki kafin yace"Kaji mganata ko..? To ka gaggauta fara abunda yace maka Fatan nasara Allah y bamu waraka..! Daga haka suka rabu Daga cikin makaranta gida ya wuce daman yanaa da Ruwan zamzam din Sarood bata nan tana makaranta sannan in ta Dawo Zata biya gida Mami Sara na Fama da Zazzabi. Alokacin ya samu Lokaci yayi Duk abunda mallam ya Umarcesa ya Tofesu acikin Ruwan zamzam din a kuma wannan Daran ya Fara amfani Dashi da yakinin Ciwonsa Daga Allah ne kuma waraka na wajensa..! Sannu sannu dai..Bata hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba..! Daga yanzu aikin nasu ya fara Lalacewa Alalan geronsu ya riga yayi Ruwan da bazasu taba iya Dauresa ba koda kuwa sun mai Cikon Gari acikinsa..! ***** Sati dayan da Malam ya Dibar ma Anty Amarya na cika ya Kirata a waya Daman kiransa take jira tana Lissafe da Ranakun. Sai dai yana fara bayanin Idanuwanta suka Rufe Daga sanda yace Wace ke Lalata Cikin Sakina tana cikin matan mallam sannan tafi kusa da Hajiya da kowa acikinsu sannan bama Take lalalata Cikin ba ko yau sakina ta kara Samun ciki bazai taba zama a mahaifanta ba akwai abunda aka bata Tacin ma cikinta wanda yake hana Cikin zama acikin maranta. ! Anty Amarya na Tsaye ne acikin Dakin su Sa"adatu in da su Sakina suke bata gama Sauraran mganar mallam ba ta yi wurigi da wayar sakina ta Tsorata tabi ta kallo ganin yadda ta fita a fusace. Haj.Uwani na gaban madubin bedromm dinta tana Saka dan kunne a kunnenta Kamar Daga sama taji an bango kofar lokaci Daya da shigowa Cikin mamaki ta juyo tana kallon ikon Allah.. Idonta fes a na Anty Amarya wacce ke kallonta Cikin Jajayen idanuwanta da suka rine da bacin rai da wani Bakinciki. Haj.Uwani Cikin mamaki tace"A"a Amarya Lafiya kika shigomin har Cikin kuryan Daki ba sallama..? Kawai sai Anty Amarya ta Nufeta ta Shako wuyanta idanuwanta sun firfoto waje cikin Karaji take fadin"Ke baki chanchanci sallaama ba..Baka mai bakar aniya muguwa azzaluma mai fuska Biyu da izinin Lahi Uwani sai kin ga sakamokon ki Tun aduniya muguwa macuciya azzaluma kaawai..! Haj.Uwani ta Fincike Wuyanta Cikin Wata irin kallo take bin Anty Amarya da shi kafin ta kece da wata irin Dariya tace"Azzalumai bakake masu bakar Aniya zaki ce Marliya sannan ki rika saka min jaye..Bazamu gama da Duniya Lafiya ba DA NI DA KE..tunda duk jirgi Daya ya kwasomu..! Tafada tana dariya lokaci Daya tana mata kallon Nasan ki, ni tuntuni ke kuma sai yanzu kika sanni..? *Janafty**TFZB2013* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Anty Amarya ta dago tana kallonta cikin rawar baki dana jiki tace"Ban..ga ne ba..? Me kike nufi Uwani..? Haj.Uwani ta saki wani kayattacen Mirmishi mai hade da cin nasara tana kallon cikin Idanuwan Anty Amarya wacce ta fara tsorata da Lamarin Uwanin tace"Kina sane da abunda nake nufi marliya ko na kira ki da Madina ne..? Tafada cikin tsaida kallonta kan Anty Amarya wacce ta zaro ido jin Sunan da Uwani ta Kirata dashi Sunan da mutanen da suka santa dashi ba su da yawa suna ne da ta saka ma kanta Tun tuni domin cikar wani Buri nata. Haj.Uwani ta fara taku acikin Dakinta tana Zagaye Anty Amarya tana Sakin Dariya kasa kasa kafin ta nufi kofar Bedroom dinta ta kulle ta harda Murza key ta juyo tana Fadin"Komai na Bukatar sirri madina duk da bansan da wacce kike zo ba..? Anty Amarya da tagama Tsorata da mganganun Dake bakin Hj.Uwani baisa ta yi saurin karaya ba yasa cikin Gyara Tsayuwarta tace"Kina sane da duk abunda nazo dashi Uwani..Tunda ke kike aikata shi..Kashe rai fa kike yi fa Uwani..? Kina lalata duk cikin da Sakina take samu yanzu in wannan mganar ta fita kina Zaton zaki kara Minti Daya acikin gidan nan ne..? Tafada tana kallon Haj Uwani wacce ba karaya ko nadama ko kaadan a Tare da ita sai ma Zama da tayi gefen gadonta ta Dora kafa Daya kan Daya tabi Anty Amarya da kallo kafin tace"Ranar Biyan Bukata rai ba abakin komai yake ba Marliya a wajen ki na koyi wannan Tsarin sannan Da kike mganar in Labarin nan ya fita bazan kara ko minti Daya agidan nan ba..? To wayace miki zai fita yanzu..?. Ai ko zai fita sai na gama cika Burina Likacin na zama giwar mata ko mallam babu yadda ya iya dani marliya ballatana Hajiya da ban Dauketa wata Tsiya ba..Atafin Hannuna take kinsani..! Bama ita ba gabadayanku a nan dina kuke ba wacce bansan duka motsinta ba..! Ta karishe Fada tana Nunatafin hannunta cikin gadara Anty Amarya tayi wani mirmishin takaici kafin tace"Aiko kunyi kuskure Uwani..Wlh yadda kika yi sanadiyar Salwartar da Cikin Sakina sai nayi Sanadiyar da asirunki ya Tonu yau a idon Duniya..Yanzu ba sai anjuma ba, zan je na Sanar ma Hajiya komai domin ta gano Muguwar bakar Fusarki..! Tafada a fusace kafin ta juya zata fita ta tsinkayi muryan Haj.Uwani Cikin Gadara. "Bani kadai zaki tona ma asiri ba marliya Har da ke karan kanki..da wacce ta hada hannu Dake kuka KASHE YAYA..sannan kuma baya zatayi Zani marliya harta Danmallan zai gano cewa ba da Ra"ayinsa ya auri Sakina ba ke kika shiga kika fita hakan ta kasance..! Da wani irin mamaki da al"ajabi da Faduwar gaba Anty Amarya taci Burki ta kasa juyowa ta Fuskanci Hj.Uwani Domin tana faman kokuwa da Faduwar gabanta na yadda Uwani ta san wannan Boyayiyun sirrukan da ga ita sai balaraba sai Malaminsu suka san anyi haka sai gashi a bakin Uwani to garin ya akayi ta san duka sirrukan su haka su basu taba sani ba..? Tana wannan Tunanin taji Muryan Uwani a saitin kunnenta tana fadin"Kin yi mamakin ya akayi nasan Duka wadanan sirrukan naki ko nace naki keda Balaraba ko..? Anty Amarya ta kasa gaba ballatana baya ba inda jikinta baya rawa Haj.Uwani ta saki Dariyan nasara kafin ta fara Tafiya zuwa gaban madubin Dake Dakinta tana Fadin"Nayi mamakin da sai a yanzu malaminki ya gano miki ni marliya ai na Dade ina shirina kusan ma nace na Rigaki shirya komai..Ni tuni Mama ta Bincikomin komai naki da ke da wacce ke tayaki dukkan ku wani motsinku ko sirrinku yana Cikin Tafin Hanuna Marliya abunda baku sani ba Kuna aikin ne ni ina warware muku..Kamar yadda Sakina ke barin Cikinta haka in wannan balarabiyar ta samu ciki ita ma haka zatayi ta barinsa hakama Amina ita kanta ban kyaleta ba na shigo da ita cikin Tsarina..Tsarin da zai kai ni nan da Lokaci kadan na cika Burina..! Sai alokacin Anty Amarya ta Juyo tana kallon bayan Haj.Uwani Cikin Rawan baki tace"Wani irin Buri ne wannan da kika Zabi ni ki hanani Cikar nawa burin. A bar batun Rufa Rufa Uwani Tunda kinsan komai ba amfani na cigaba da Boye miki manufata ni in kinyi Hakuri ba mallam nake so na mallaka ba..Kawai Sakina nake so ta Zama Mowar mata wajen umar da Danginsa..Sannan ita kadai ce nayi ma alkawarin zata haifa ma Umar magaji ta kuma Haifa ma Hajiya da mallam jika mafi soyuwa bayan ita ban yarda wata tazo Daga baya ta fita ba..Sannan in hakan ta faru nasan nima zam zama Shalele a wajen mallam da Umaru tunda nice silar duk abubuwan da suka faru..! Ki fadamin meye naki burin da yasa ni kika ki bari nawa burin ya cika..? Ina so naji irin naki Burin akan mallam da zur"arsa..? Haj. Uwani ta juyo tana kallon Anty Amarya ido na cikin Ido kafin tace"Ko baki tambayeni ba zan fada miki..Boye boye ai ya kare. tunda malamin ki ya gano miki ni Marliya..Karkade kunnuwanki Ki sha Labari yanzu zan sanar Dake yadda naki Cikar Burin ke neman yayi min Cikas kan nawa Burin da nayi shekaru ina Wahala akansa..! Komawa tayi ta zauna ta kara Dora kafa Daya kan daya kafin ta fara Fadama Anty Amarya duka shirinta da nata tsarin da Burin datake dashi akan mallam da ahalinsa ta karishe da Fadin"In har na bar Sakina ta Haihu Da Umar kin batamin Tsarina marliya..shiyasa na hana faruwar haka sannan bama ita ba indai ina Raye Umar bazai ga kwansa a Duniya ba..Tunda na gano Mallam yana matukar son yaga jikokinsa ta bangaran sa na mike tsaye na shiga na Fita na hana faruwar hakan..Ya"yana kadai ne zasu haifama mallam jikoki kuma ya sosu ni kadai ce zan zama Tauraruwa ba Hajiya ba..In ta samu mallam a baya awannan gabar Lokacinta ya kusa karewa..! Nasan zaki ce ina Nazir da Nasir da na bari suka haihu.? Ai suma din ba gazawata bane Marliya Tsarin aikina ne..Daga ya"yan Nazir din har Nasir din wa kika gani mallam ya Damu dasu? Ai nasa mama ta Dakushe wannan Tasirin har Abada kuma bazasu yi shi a idanuwansa ba Nazeem ne kadai da Uzairu zasu haifa masa jikoki su zama Sanyin Idanuwan mallam bayan su kuma nayi alkawarin har Abada ba wanda zai haihafama mallam Jika Tun balle ma Danmallam da mallam ya fi so cikin ya'yansa shiyasa kika ga inayin Duk abunda nake so..! Niso nake nan gaba ya"yana su zama sune Hop din mallam gabadaya Sune komai nasa bashi da yarda zai yi sannan kuma alokacin ni zama giwar a cikin matansa ko yana so ko baya so..Ya'ya ne kan gaba a dukiyarsa sannan wajen haifa masa jikoki ma sune kan gaba Dole kauna da soyayya ta koma kaina da Ahalina gabadaya..Mganar Sa"idu bai gabana domin ke da Balaraba kun Rage min wannan aikin..Lokaci kadan nake jira na Aiwatar da Tsarina akansa kamar yadda na Tsara..! Ta karishe Fada tana kallon Anty Amarya wacce tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi da jin wannan labarin lalle Haj.Uwani ta fi su zama Shedaniya,Su ashe bakomai ma sukeyi ba,Shekaruna nawa ta kwashe tana Wahala ammh Lokaci kadan Uwani tana neman Tsawartata to bazata bari ba,Bazata yi Saurin karaya ba,sai ta nuna mata in ita a Tsaye take ita a tafe ta kwana..! Ta kalli Uwani cikin Bakinciki kafin tace"meyasa Burinki ya yi kamanceceniya da nawa .? Meyasa sai dole kin Tsawartsani Uwani meyasa haka..? Haj.Uwani tayi kasa da Murya kafin tace"Ki yi kasa da muryanki mana marliya..Ai na riga na Fada miki Dalilina..Bake kadai na taba ba..Na Fada miki yadda na Raba Hajiya da ya"yanta a kusa da ita,Na maida Nasir mara amfani a wajen maallam na hanata ganin jikanta ta Tsatson babbar Danta ita meyasa batace ina so na Tsawartata ba sai ke da Duka Dagani har ke muna kan Turba Daya ne marliya..? Anty Amarya na Huci tace"To baki isa ba..wlh uwani karyan ki ta sha karya..! Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Nama isa ai marliya..Kaawai ki yi Hakuri ki mara min baya Burina ya Cika in hakan ta faru nayi miki alkwarin Raba komai gida uku na Dauki Biyu na baki kashi Daya. ! Anty Amarya ta harareta kamar Idanuwanta zasu fado tace"Me kike nufi..? Haj.Uwani tayi Dariya kafin tace"Ki hakura da Sai Sakina ta Haihu marliya..! Anty Amarya ta Zumduma ashar kafin tace"Ina..Baki isa ba Uwani..Bazaki Hada baki dani ba..Kowa ya Tsaya da kafafunsa..Sannan kuma sai dai ki kare a muguntarki kina ji kina gani Sakina zata haifarma mallam da Hajiya jika sai dai bakin ciki ya kasheki. ! Tafada tana kumfar Baki Haj.Uwani ta tabe baki kafin ta Daga kaafadanta tace"Shikenan marliya..Kije ki cigaba da Wahala..Ammh ina mai kara gayamiki..in sau Dubu sakina zata samu Ciki sai ya Zube haka Sarood hakama Amina ke ko aure ya kara itana irin Tsarin dana Dora su itama akan shi Zan dora ta Marliya na Fada miki kan Cikar Burina zan iya aikata komai..! Anty Amarya taji wani abu ya Tsaya mata a wuya kawai sai tayi kukan kura ta kara shako Haj.Uwani cikin Hargagi take fadin"Me kika baa sakina tasha..? Ki Fadamin abunda kika Binne da kudin da kika kashe akan hana Sakina Haihuwa Uwani..? Kwace wuyanta tayi tana Hararan Anty Amarya Lokaci daya tana Fadin"Wlh in kika kara saka hannunki kika rikeni sai na Sharara miki mari marliya..! Ki kama kanki kafin Zuciya tajaki ki aikata abunda zaki zo kina Nadama..! Anty Amarya na Haki ta nuna Haj.Uwanu tana fadin"Wlh kin yi kadan..Nayi alkawarin sai nayi sillar Tona miki asiri..! Haj Uwani tace"To ai ban Hanaki ba..tunda baki min godiyar Taimakon ki da nayi ba akan Amina da Sarood ba, wato sakina kadai kike so ta Haihu ban da su ko..? To tunda baki ga Hallacin da nayi miki ba Shikenan jeki fadama wanda zaki Fadamawa ammh ki sani in asirin ya tashi Tonuwa naki sai yafi muni Marliya ni iya ka dai mallam ya Sakeni ko..? To in ya sakeni ai bai kare ba ina da Zaratan maza har uku ko da sun ji abunda ya faru basu isa su sauya ni a matsayin uwa ba marliya,Sannan kuma dole zasu neme ni kefa wa kike dashi..? Duka ya"yan ki mata ne baki da wani gata anan duniya iyayanki zasu yi Tir Dake ya"yan ki mata zaki bar musu abun kunya in ma bai taba auransu ba,Sannan Uwa uba kuma agaban idon ki Umar zai Saki Sakina kinga Daganan kin kare a Tutar babu..Wahalar ki tatashi a banza kenan kuma ke ahakan ma naki Tonuwar asirin mai kyau ne,akan na Balaraba ita wlh ko kaffara bazan yi ba kare sai ya fita Daraja in sirrin Boye ya fito Fili sai ta wulakanta ta Tozarta a wajen Sa"idu da Danginsa da kuma ya"yan Yaya da kukayi Sanadiyar barinta Duniya Saboda cikar naku burin..! In kin yarda da duka Faruwar wannan shikenan u can go..Ki je ki Fadama Hajiya sai mu shirya bankadewar siirikan namu dani da ke da balaraba alokaci Daya ko banza na San Dagani har ke bamu samu cikar Burukan namu ba..! Tafada tana wata yar Dariya Anty Amarya duk yadda taso kada ta nuna Rauninta sai da ta nuna Hawaye ya wanke mata Fuska ta nuna Haj.Uwani da yatsanta Cikin Kaushim murya mai Cike da karkawa tace"Ki Rubuta ki ijiye Uwani Indai ban samu abunda nake so ba..Na rantse ko Zan yi yawo Tsirara sai naga kema baki samu abunda kike so ba..In juran ki sammako ni madina a tafe na kwana mu Zuba mu gani..! haj.Uwani ta bata amsa da cewa"Shege ka fasa marliya..! Daga haka Anty Amarya ta murza key din ta Bude kofar ta Fice tana kuka Duk yadda taso ta shanye kukanta ta kasa bakinciki da Takaicin sun taimaka wajen Fitar Da ita daga natsuwarta uwa uba kuma da yadda Gabadaya sirrukansu yake tafin Hannun Haj.Uwani Hajiya ta fito kenan Daga Shashenta zata shashen Haj.Uwani suyi mganar wani Turaran wuta da suka je Bikin nan maiduguri tace tana so yagana ta kirata kan mganar ne yasa tace bari ta shiga ta fadamata.. Ta sawo kanta Falon kenan Anty Amarya na fita da gudu tana kuka Hajiya sai ta Rude hankalinta ya tashi ta rika fadin"Subhanallah Amarya Lafiyanki kuwa..? Ina ko jinta batayi ba batama ganta ba Domin kuncin datake ciki ya Rufe mata jinta da ganinta har ta fice Hajiya na Kallonta sai jikinta ya kama rawa tana Fatan Allah yasa ba wani abun ne ya Faru da Sakina ba kamar ta bi bayanta sai kuma ta fasa ta karisa Cikin Falon Haj.Uwani tana Fatan taji abunda ya faru Daga bakinta. Ita kuma Haj.Uwani Anty Amarya na fita ta yi shewa ta kara Sakin shewa kafin tace"Mu zuba mu gani marliya..Karki fara ja da Uwani Domin ni walkiya ce ban Fito ba sai da na shirya..! Haka take ta fada tana Dariya tasan Daman zatayi mamakin yadda tasan komai nasu Mama hatsabibiyar Bokanyance Dake Niger ita take Sanar da ita duka aikin marliya ita da Balaraba ita kanta da Farko ta Razana da jin sunan mamanmu domin bata taba Zaton matar mugun halinta yakai haka ba, sai dai batayi mamaki ba Sanin yadda Idon kowa yake Rufewa kan neman Duniya..sannan Ta kara jinjina ma wannan kalmar na rai ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata Tunda Balaraba ta saka aka kashe yaya Matar data Zauna da ita Tsakani ga Allah ta bar mata gidanta da ya"yanta kawai saboda Cikar Burinta na mallakan sa"idu..! Tana wannan Tunanin kamar Daga Sama taji muryan Hajiya tana Sallama sai ta Rude ta mike da Sauri ta fito Tana kokarin Daidaita yanayinta Hajiya dake tsaye Tsakiyar Falon Uwani ko Zama ta kasa ta kalli Uwanin Yadda ta fito tana abu kamar wani abu dai ya faru yasa da Sauri tace"Wai ni Uwani me ya faru ne acikin gidan nan bansani ba..? Naga Amarya ta fita Daga shashen ki da Gudu tana kuka ina ta mgana bata jini ba kema mayi sallama kin Fito kamar kina ma a firgice ne Hankalina ya tashi muke Faruwa..? Haj Uwani na jin haka kawai sai ta Zube saman Cafet din Falonta ta Fashe da kuka yi take yi ba Saurarawa ta kara Tadama Hajiya da Hankali Cikin Rudewa tace"Ko Cikin yaran mu ne wata ta rasu kuke Boyemin..? Hajiya Uwani na jan majina da Hanci tace"Ai gwara ma Mutuwa da wannan Zargin da Amarya ke jifana dashi Hajiya..! Hajiya tace"Wani Zargi kuma Uwani..? Haj.Uwani na kara saka kuka tace"Hajiya wai ni Amarya tazo ta sama tamin zagin kare Dangi da Zargina wai ni nake asiri ina Zubar ma Sakina da cikinta..Fitar nan da kika ga tayi ni tazo ta kare ma Tanadi Hajiya..! Hajiya ta Zaro ido kafin ta saka Salati ganin haka yasa Haj.Uwani ta karkace baki ta Cigaba da fadin"wai malaminta ya mata Duba yace ci kin matan mallam ne..kawai hajiya sai tace ni ce..Nan tazo ina ta mata Rantsuwa taki yarda dani ina Fadamata kada tayi saurin yarda da irin mallaman nan na karya masu Hada Fada bata Saurareni ba Hajiya haka ta fita tana kukan da Ikirarin sai ta ga Baya na..! Hajiya nan da kika gani daman wajenki Zani Na fada miki abunda ke Faruwa naji Ciwon wannan abun sannan na Fadamiki bazan kyale Amarya ba sai ta san tayi min kazafi..! Ta karishe Fada tana kuka Wurjajan..hajiya kuwa sai Faman Salati take yi kafin tace"Kinga Uwani bar kuka..wannan mganar ba tawa bace..Bari naje na kira mallam na Sanar dashi abunda ke faruwa wannan mganar tayi muni da yawa Uwani..! Haj.Uwani na jan majina tace"Ko kin gayamai Hajiya ni bazan yafe ba..Sai an Bimin Hakkina akan kazafin da Amarya tamin..! Hajiya bata Saurareta ba ta Fice tana Jimamin wannnan abun aranta tana Jin Haushin Anty Amarya bata taba Zarginta da shiga malamai ba ammh jin abunda ta aikata sai taji duk ta Zube mata ina amfanin wannan aikin..?ta Biyema mallaman karya suna neman hada fada acikin gida. Hajiya na fita Haj Uwani ta mike ta Share Hawayenta ta yi Dariya kafin tace"Marliya tun a yau zaki san kin Hada Hanya da Uwani Diyar Hamza Tsafe..! Ta fada tana Dariya har ta Hango yadda Marliya zata gane bata da wayau a falon mallam Dakin da Umaima take ta leka barci take yi Domin yanzu ko Makarantar Haddar ta Daina zuwa saboda Ciwon nata ya tashi gadangadan ana ta dai fama da mgunguna ne. Hajiya ko na fita Bedroom dinta ta shige nan ta bar Hanne da Hamida afalo suna rike da Littafansu bata ma Bi ta kansu ba ta Shige Daki wayarta ta Dauko ta Kira mallam bai yi nisa ba yana gidan mai anguwa ya Kirasa kan Cases din Filin wasu marayu da aka kawo mai mganar to daman mai anguwa in wani abu irin haka ya Faru na bangaran addini yana kiran mallam Domin su Tattauna. Yana jin Hajiya tace yazo gida ba Lafiya yace mata suna ma kan Hanya. Lokacin ana gabda kiran Sallar La"asar ne yasa suna Dawowa yace bari ya Tsaya yayi sallah kafin ya shiga Cikin gidan Hajiya ta fito ranta a jagule sai yanzu ma ta lura bata ga Amina ba Tunda dazu da suka Dawo daga makaranta,yasa ta kalli Hanne da Hamida dake ta yin aikin da malamin Lissafinsu ya basu a makaranta tace"Ina Mamah yau. ? Hanne tace"Tana gidan baba Sa"idu dazu da muka shiga gaida mamanmu ta kwanta sai ta fara barci mu kuma da Zamu tahilo bamu tashe ta ba..! Hajiya bata ce komai ba ta kada kai kafin tace"ku tashi kuyi sallah Lokaci yayi..! Daga haka ta koma Cikin Bedroom dinta Ammh aranta sai da tayi Tunanin barcin Amina yayi yawa kamar kasa yanzu ko da asuba fa Dakyar ake tashinta wani Lokacin da Daddare kafin takwas Amina ta kwanta sannan in suka Dawo makaranta sai tayi barci ammh sai bata kawo wani Tunani ba tafi Barinsa a Saboda Basa Zama a zirga Zirgan makaranta da Sauransu. Hajiya ta idar da Sallah kenan Kiran mallam ya shigo mata yace gashi ya shigo Gidan Hajiya batayi kasa agwiwa ba ta saka lullubinta ta Biya Shashem Hajiya Uwani Dake zaman jiran Kiran mallam suka tafi Falon mallam suna zuwa Hajiya tace ta fara gayama Mallam yadda taga Anty Amarya sannan tace Uwani ta maimata abunda ta Fadaamata Haj.Uwani ta gyara Zama ta Fara Rattafama mallam yadda ta Fadama Hajiya ta karishe cikin kuka tana Fadin"Mallam abu dayane in na Tuna yake min ciwo..Da Amarya ta Zargeni da laifin kisa Mallam..? Ashe haka ta Tsaneni bansani ba..Ta rasa kazafin da Zatamin sai kazafin kashe gudun jini Tun kafin ya Fito Duniya..? Wannan in gaban yan Sanda za"a kai ai babban cases ne mallam..! Mallam da ransa ya gama baci ko mgana bai yi ba ya Daga wayarsa ya kira Anty Amarya wacce ke cikin Bedroom dinta tunda ta Dawo Daga Shashen Uwani ta shige ta rufe kanta tana kuka kukan rashin mafita da madafa kukan takaici da gazawa a karo na farko ko sallah bata tashi tayi ba sai ga Kiran Mallam sai da gabanta ya Fadi balle Dayace tazo ta same sa afalonsa a kausashe. Ai bata gama Sarewa ba sai da Sawo Hijabinta Fuskarta duk ta kode ta iso Falon mallam ganin Hajiya da Haj Uwani sai da yasa gabanta ya Fadi Jikinta ya fara rawa ta Tsaya Cak ta kasa gaba ballatana baya. Mallam cikin kaushinsa yace ta kariso ita ake jira,Jiki a sanyaye ta kariso ta Zauna gefen kafar Hajiya a kasa tana kallon Uwani dake mata Dariya a kasa kasa Daganan tasan wani makircin ta kulla mata.. Kanta ya Daure sanda Mallam yake karanta mata abunda Uwani tace ya Kalletaa Cikin bacin rai yana Fadin"Marliya ashe ban Dade ina muku nasihan yarda da malaman tsubbu ba..? Shine kika kai kanki bayan kin yarda dashi shine ya karanto miki karya kika zo kika Hadamin Fada acikin Ahalina alhalin na Dade ina gargadinku..? Anty Amarya ta Tsure hankalinta ya tashi ta kalli Haj.Uwani dake matsan kwallar karya ta maida kallonta kan mallam taga yana mata wani kallo Sai kuka ya taso mata ta Fashe da kuka Tana fadin"Wlh ma..! "Karki ce tak a nan wajen marliya..Baki da abunda zaki fadamin bana Kiraki Domin kimin karin bayani bane..na kiraki ne naja miki kunne Wlh Tallahi in na karajin mgana makammancin wannan sai na Saba miki in ma ban yanke Igiyan auran dake tsakanina Dake ba. domin ina kyamatar Zama Dake Marliya tunda kin zama Mushuruka mai bin malamai da yan Tsubbu makiya Allah..! Anty Amarya ta tsorata ta Duka gaban Hajiya ganin yadda mallam yake mgana tasan ransa ya baci Uwani tayi nasara akanta tace"Hajiya don Allah ki bama mallam Hakuri ba Laifina bane kuskure ne..da sharrin Shedan..! Sai kuma ta rike kafan Hajiya tana gunjun kuka Hajiya taji Tsausayinta ta Duka ta riketa tana fadin"Tashi ki Zauna marliya..! Komawa tayi ta zauna tana kallon Haj.uwani Dake matsar kwallah tana mata Dariya ba wanda ya Lura Hajiya ta kalli mallam kafin tace"Mallan kayi hakuri don Allah..Tace Sharrin shedan ne ayi mata uzuri..! Kema Amarya ki gyara wlh bazan Boye miki ba kimarki ta Zube awajena tunda naji kina daga Cikin masu Bin malaman karyan nan ammh Tunda kin bata Hakuri ya wuce..Mallam kai ma kamata Hakuri..!mallan cikin bacin rai yace"Bani zata bama Hakuri ba Uwani gatanan baiwar Allah da ta zargeta tana zaman zamanta zata bama Hakuri in kuma wlh bata yafe mata ba sai Allah ya kamata ! Yafada cikin nuna bacin ransa lokaci Daya yana Kauda kai baya son kallon Anty Amarya Hajiya ta juya tana kallon Anty Amarya tun kafin ma tayi mgana ta Zube gaban Uwani tana Fadin"Kiyi..hakuri sharrin shedan ne ki yafemin..! Haj.Uwani ta share Hawayenta kafin tace"Shikensn tunda Hajiya da mallam sun saka baki..Ammh wlh da naso ne sai na kai mganar nan gaba..Ammh Tunda kin bada Hakuri ya wuce sai ki kiyaye ki daina yarda da mganar makaryatan malama nan makiya Allah da addininsa..! Hajiya tace"Tabbas Allah ya Karemu gabadaya..! Haj.Uwani ta amsa da Ameen da karfi mallam ya mike yana Fadin"Sannan mgana ta karshe bayan mu Hudun nan kada naji wannan mganar abakin wani..Na kasheta Daga yau..! Daga haka ko mgana bai kara ba ya shige ciki bakincikinsa Daya yana tafe wa"azi akan mata masu Bin malamai ammh yau agidansa ma ake yi wannan aikin..? Tayaya ransa bazai baci ba..? Hajiya kuwa sai da ta kara yima Anty Amarya Nasiha sosai da nuna mata illah rashin yarda da Allah da kaddaran da Illah barin Shedan ya saka mutum wasi wasi da kuma illar Bin malaman karya na Tsubbu. Sannan ta sallame su Anty Amarya ta Mike kamar tana kan kaya ta Fice Haj.Uwani sai daga baya ta fito Hajiya kuma ta bi mallam ciki ta Rarrasosa..! Haj Uwani har takai shashenta tana Dariya Allah Allah take yi ta Kira Batula ta labatar mata abunda ya faru yau sai ta Kira ta bata Dauka ba Shiyasa ta bari sai an juma ta Sake nemanta kan kujera ta kame a falonta ta Dora kafa Daya kan Daya tana Mirmishin jin Dadi da Nishadi ko banza yau ta bama Marliya Daya daga Cikin Tsoronta..! Anty Amarya kuwa haka ta shiga Shashenta bata gani tana jin Sakina da Sa"adatu na kiran sunanta da suke Falo bata bi ta kansu ba ta shiga Daki ta Bame kofa da key jikinta na Rawa da Hannunta ta Dauki wayarta Dake kan madubi ta Dokama Balaraba kira. Mamanmu na cikin bedroom dinta bata Dade da tashi daga barci ba tayi sallah tana Zaune tana Tunanin irin girkin da zata Tsarama Aba da Daddaran nan Tunaninta ba kowa agidan Jawaad na Haraban gida yana Kwallo Su Hamida basa nan suna gidan mallam Domin bata Dauka Amina bata bisu ba dataji Fitansu ta Dauka gabadaya suka fita..shiyasa bata Damu data leka Dakin su Aminar ba da ba kowa acikinsa yanzu sannan Dazu da ta fita alwala taga kofar Dakin a Sakaye abunda bata sani ba Iska ne ta Dan Tura kofar Dakin Amina na ciki tana barci. Wayarta Dake gefenta ne ya katse mata tunani ita azaton ta Aba ne Domin yanzu ko yana wajen aiki haka suke cikin waya yana tambayanta ko ba wata matsala sai taga Madina ne ke kiran Wani katon Tsaki ta saki kafin tace"Kai madina bazata barni na Huta ba..ya kamata ta Hakura tunda ita dai kamar bata da sa"a ne..matsaww...! Sai da ta Daidaita kanta sannan ta Daga Kiran tana fadin lafiya"Madina Allah yasa lafiya kira da bayan la"asar haka..? Anty Amarya cikin kuka tace"Dayyaba mun kade mun gama yawo..Ashe duk abunda muke ciki siirinmu yana Bankadane bamu sani ba..Tabbas muna Shuka a idon makwarwa Dayyaba. ! Mamanmu ta ce cikin mamaki"Bangane ba madina..? Waye yasan sirrinmu..? Anty Amarya tace"Hajiya UWANI 'ce Dayyaba..A tsirara take kallonmu Duka Sirrukanmu dani Dake yana Tafin Hannunta ne. ! Mamanmu ta mike Dafe da Kirji Tana Fadin"Mun shiga uku Madina wani irin labari kike son ki Fadamin..? Anty Amarya ta share hawayenta tana Fadin"Ai bama uku muka shiga ba goma ne Dayyaba..! Nan ta fara gayamata komai da komai Tunda daga farko da zuwar da tayi ta Samu Haj Uwami da yadda suka kare da Sharrin data kulla mata ta karishe da Fadin" Kinga yadda take kuka afalon mallam kyce ta Allah ce Dayyaba..Wlh Uwani ta shirya yin Fito na fito damu kuma in muka yi wasa..Tana gabda Kware mana Zani a Tsakiyar kasuwa..! Mamanmu ta Mike Cikin wata irin Murya tace"Karya take yi madina..Uwani bata isa ba..In juranta Sammako mu mun Dade atafe..Bata isa ta zo ta lalatamana Aikin da mukayi wahala mukayi shekaru muna Wahala ba Haba Madina Hajiya Uwani muguwar matace bata da mutunci kuma bata da imani Tsakani ga Allah yadda Hajiya ta yarda da ita sai da ta Cutar da ita..? Sannan ina laifin in ta Hana Amina Haihuwa ko zama da Umar daman haka muke so auran yadda yake gantale ya kare a gantale itama wannan Balarabiyar ai in ta Hanata Haihuwa mu taimakon mu tayi ammh Sai ta Hado da Sakina..? Tasan shekara nawa kika kwashe kina Wahala kan Sakina ta Samu Ciki ta Haihuwa ta zama Mowar mata agidan Umar..? Ko kuwa tasan Shekara nawa ni na bata ina Zaune da Fuskar balaraba Domun cikar Burina..? Shekaru fin Talatin ina Kun san bakin Cikin Sa"idu da Matarsa YAYA shekaru talatin na kwaahe ina Bautama ya"yanta shekaru masu yawa na kwashe ina nuna ina son yarinyar nan Amina har saki sai da Tsinnanniyar tajamin sai acikin wannan shekarar ne na samu yadda nake so shima bayan kasa ta Shafe idon yaya..To bata isa ba ki Fadamata bata isa ba..Bazamu bari ta Rusa mana Shekarun da muka kwaashe muna Wahala na Samu Sa"idu Dakyar Madina saboda haka fa na Hada kai Dake domin cikar Burina ke kina komai Saboda Sakina ni kuma inayin komai saboda Sa"idu ne ko JAFAR daya so ya nuna taurin kansa nayi mganinsa yanzu..Duk da abaya ba AMINA NASO ta kangare ba..Ba ita naso ta zama mara kunya ba..Ba ita naso ta koma haka ba Jafar naso ya koma haka ammh duk da Haka ban Sare ba Madina lamarina ba ja da baya kuma ba Faduwa ballatana Na karaya kema bai kamata ki karaya ba Madina..! Ta karishe Cikin Hargagin ta na Daukan ita kadai ce agidan idonta ya Rufe bataji bata gani. Amina dake Tsaye Tsakiyar Falon Mamanmu sai da ta rike bango Sakamakon wani wawan jiri Daya kwasheta jin kalaman dake fitowa daga bakin mamammu wanda suke mata amsa kuwa acikin kunnuwanta tana Fatan yasa abunda taji ba gaskiya bane ba Mamanmu bace ke wannan mganar ba. Tasowarta Daga barci kenan ta fito tayi alwala ta Duba Bayinsu na Daki ba Ruwa sai taji kanar mgana Daga Dakin mamamu sama sama yasa ta fasa yin wajen famfo ta shigo Dakin da niyar kiran sunan mamanmu sai dai mganar data ji ne yasa ta tsaya sanda Taji kalaman mamanmu da suka kusa saka Zuciyarta ta Buga. Bata gama Dawowa daidai ba ta Sake jin muryan mamamu Cikin Fusata tana Fadin. "Ita din banza Madina da zata Tsorataki. me akayi akayi HAJIYA UWA..? Muka kauda YAYA har Lahira ballatana ita..? Karki manta Saboda Cikar Burina kika taimakamin muka saka Malam ya Kara mata gudu zuwa Lahira.kamar yadda nake kokarin taimaka miki auran AMINA DA UMAR ya kare ahakan sannan bazata taba Zama wata mai Daraja awajensa ba Sakina ce kadai zata haifasama D'a jikan mallam da Hajiya..Saboda haka ki kwantar da Hankalinki Rai fa ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata AMARYA..! kai Amina ta Dafe saboda ya Fara juyamata Hannunta Duka Biyu ta saka ta Toshe kunnuuwanta Lokaci Daya tana girgiza kanta Hawayen da suka fito mata suka fara ambaliya saman Fuskarta kamar an Bude famfo..! *Janafty**TFZB2014* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* To mu kawar da ita nace madina tunda zata kawo mana matsala mana..Nafa fada miki tun abaya wajen biyan bukata rai ba abakin komai yake ba ke kika kara tunatar dani hakan madina Lokacin da kikace mu Kawar da YAYA naki baki Dama ina ganin kamar a lokacin bai kamata ta mutu ba naso ne sai na kunsa mata kwatan kwacin bakincikin da ta kunsamin amamh da kika nuna min mutuwarta itace masalaha bagashi tatafi ta barmin Sa"idun ba kuma sai da ta kauce na samu abunda nake so to kamar hakane in dai Hajiya uwani zata zame miki matsala wajen cikar naki Burin Madina mu kawar da ita kawai..! Amina Tsabar Rudin data ke ciki yasa kafafunta suka kasa Daukanta bata san sanda ta sulale ta zube saman Cafet din dakin mamanmu Lokaci daya tana Saka Hannuwanta duka biyu ta toshe Bakinta saboda kuka ne ke son kwace mata ba taredata sani ba. Mamammu fa..?mamanmu Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un ita ke fadi da bakinta ta kashe Yaya ta kashe yaya wannan mganar amsa kuwwa take mata sannan mganganun sun Haifar mata da juyawar kan data kasa gane wani yanayi take ciki abu daya ta sani Taji abunda Tunda take bata taba jin makancin sa ba taji abunda Hasashe ko zato ko Tsammani bata ba Zato zata jisa Daga Bakin data aminta dashi ba. Rarrafawa tayi kamar mai koyon Zama saboda ta kasa tashi ta Dage labulen Dakin mamammu na ciki ta gefe kadan so take ta Tabbatar da abunda taji domin gani take yi kamar ba Mamanmu din bace mai irin Muryanta ne sai gashi taga Fuskar mamanmu cikin yanayin da bata taba ganinta ba Tana Tsaye tana waya ta cigaba da mgana cikin Zaro ido tana Fadin"to maza ki kira mallam..Ayi mana mganinta mu koma gefe muna Cin Duniyarmu da tsinke a Matsayin Dayyaba da Madina chan gefe kuma muna Cigaba da yaudaran mutane da Salihan Fuskokin mu na Balaraba da Marliya..! Bata tsaya ma ta gama ji ba ta juya Cikin Rarrafen har ta fice Daga Falon batare da tayi wani motsi ba Hawaye kuwa kamar an bude Famfo haka wasu ke fita wasu na kara Bulbulowa Idanuwan mamanmu ya rufe shiyasa kwata kwata bata ji wata alaman akwai wani acikin gidan ba. Amina na fitowa Tsakar gida tayi tayi tatashi sai ta kasa Domin gabadaya jikinta ya Saki Lokaci Daya ta kasa gasgasta abunda taji kuma ta gani Mamanmu kadai kanta ke iya fadi da sunan yaya Anty Amarya bata wani bata mamaki ba jin sunanta Daman ita Tuni Tasan Halinta ammh acikin wannan yanayin ace Mamanmu ce ke da Alhakin Duka abubuwan da suke Faruwa ta yaya zuciya zata iya Daukan wannan Gaskiyan..? Dakyar ta iya mikewa sai da ta rike Karfen barandan su sannan gabadaya kanta juyamata yake Bata gani Dakyau wani irin Biji Biji take gani Allah ya taimaketa taga Hijabin Haddar Hamida kan igiya data wanke ta Taka Sannu sannu tana Nunfashi Sama sama ta Daukosa ta sakasa ko Takalmi babu a kafarta haka ta Fice Daga gidan Cikin wani yanayi duk Takun da Zatayi sai kalaman mamanmu sun mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta Daki Daki Dayasa Cikinta ya Cure waje Daya Dakyar take iya taka kafarta a Haraban gidan taga Jawaad yana kwallo yana ganinta ya nufeta yana Kiran sunanta sai kawai Amina ta kallesa ta kara kallonsa Tabbas sai Allah ya Tsine ma balaraba ko da Hakkin Jawaad aka barta sai Rayuwarta ta D'aida'ice Rumgumesa kawai tana so ta Fashe da kuka ammh ta kasa acikin Kirjinta take jin wani zafi kamar zata mutu batare da tamai mgana ba taja Hannunsa suka fice domin gabadaya gidan ne yayi mata wani zafin Datake jinsa har acikin jikinta suna tafe yana Fadin"Ya Amina ina Takalmin ki. ? A islamiya an ce mana ba kyau tafiya ba Takalmi..! Bata ma Sauraransa ita dai kawai Jefa kafa take yi Allah ne ya kaita Falon Hajiya ba Domin tana ganin Hanya Dakyau ba suna shigowa Hamida da Hanne suka Dago suna kallonta gabansu ya fadi ganin Hawaye Kaca kaca a Fuskarta Hannun Jawaad ta Saki ko barayin bata kallah ba Ta nufi Dakin su Hanne tana jin ita da Hamida na Faman kiran sunanta suna tambayanta me ya faru take kuka ko Waigowa batayi ba a yanayin Datake Ciki ba kowa zai iya Fahintarta ta ba Tunda bata da Uwa a raye a Duniya to ta samu kadaicin da zata Zauna Tayi Tunanin makomar ta a wannan Duniyan da Rayuwar data ke cike da Tarin azzalumai maciya amana..! Tana shiga Dakin ta Ture kofar bata ma iya karisawa Kan gadon ba ta Sulale nan saman Cafet a kofar Dakin Tana Dafe Saitin zuciyarta Daya Dunkule waje daya ga cikinta Daya Cure waje Daya yana murdamata Sosai da sosai Hawaye da majina Har da Miyau haka suke kara kaina akan Fuskar Amina batare data Damu Data Share su ba. Achan Falo kuwa Hamida ta kalli Jawaad tana fadin"Wai me ya faru ne Amina ta shigo tana kuka..? Shima ya girgizamata kai kafin yace"Bansani ba nima ina kwallo na ne tazo tana kuka taja Hannuna muka zo nan..!. Hanne ta mike tana Fadin"Hamida muje mu gani..; Tare suka Dumguma suka Nufi Dakin suna Tura kofa suka kusa cin karo da Amina atare suka saki Salati Hanne ta Duka gaban Amina tana Fadin"Amina meke Faruwa ne..? Amina ta runtse ido sai wasu Hawayen ta Dafe saitin zuciyarta Dake mata Zafi bakinta yayi Nauyin da bazata iya mgana ba. Hamida ta kalli Hanne Cikin wani yanayi kafin tace"Ko zaki je ki kira Hajiya a shashen Baba mallam ne..? Hanne ta mike tana mai yarda da mganar Hamida da Sauri Amina ta Rike kasan Sikat dinta bata so ta Kira Hajiya domin in tazo bata san me Zata Fada mata ba, ta tabbata ita kanta ba Domin taji ta gani ba ko Duniya Zasu Taru su fadamata Bakaken Halayyar mamanmu bazata taba yarda ba shiyasa ta Dago Jajayen idanuwanta Dakyar tace"Kada ki kirata..! Hanne tace"To kuma kina ta kuka..! Amina ta Runtse ido kafin tace"Ba..bani da lafiya ne..! Hamida tace"Kan ki ke ciwo..? Daman tasan Amina da Raki ciwo kadan sai ta Fara kuka da Sauri Ta gyada kanta Hanne tace"To ki tashi kici abinci ki sha mgani sai ki kwanta..!. Saboda su kyaleta yasa tace musu tasha mgani agida Muryanta a Dakushe Hamida ne tace Hanne ta Taya ta su taimaka ma Amina ta koma kan gado tunda bata da Lafiya haka suka taimaka mata ta hau kan gado ta Dunkule ta Runte ido kamar mai barci har Hamida ta Lallube kafarta da Bargo suka fice bayan sun turo mata Kofar sai da suka fita ta Bude idanuwanta Allah Sarki Hamida mai kyakyawan zuciya tunda Take da Hamida bata taba ganin wani sharrinta ba sai Alheri ya zata ji in ta ji Halin Mahaifiyarta..? Kai Innalillahi Yaya ashe ashe kasheta sukayi Shiyasa ta kwanta Lafiya lau sai gawanta aka gani shin me yaya ta Tsare ma Mamanmu..? Ta bar mata ragamar gidanta ta bar mata Ragamar duka ya"yan data Haifa ace ko don haka mamanmu bazata Raga mata ba..? Tunda take bata taba ganin Aba yayi bambamci tsakanin Mamanmu da Yaya ba har tana Kwatantashi Cikin masu adalci Tsakanin matansa. Ashe ashe alheri yana komawa Sharri ashe ashe haka Duniya ta gada..! Sai yanzu ta Fahimci Bakin Zaren Ta Dade tana Tunanin da wa Anty Amarya take waya kwanaki tana ambaton sunanta da kokarin Hanata Tarewa a gidan ya Danmalam sai yau Sirrin Boye ya fito Filo ashe mamanmu da Anty Amarya Bakin su Daya..? Ita tanayin komai Saboda Aba ne ita kuma Anty Amarya saboda Sakina ne..? Ita fa Haj.uwa dataji suna ambatkn sunanta ita me ta ke aikatawa..?! Sannan domin wa take yin abunda take yi har suke Tunanin in zata basu matsala su kawar da ita..? Lalle Duniya ba abun yarda bace abunda ko a mafarki ko Finfinan India dana Hausa bata jiba ai ko a karance karancen datake yi bata taba Haduwa da makirci da mugunta irin wannan ba Shekaru Goma sha Shidda Mamanmu ta kwashe tana kassara Rayuwarta ko da da rana Daya bata taba bari ta rabu da Yaya tasan Dadi da Martaban uwa ba shekaru sha Shidda ta kwashe tana Gurgunta Rayuwarta sai alokacin abubuwa suka Dawo mata Daki Daki Tun Farko kovsau Daya mamanmu bata taba Zaunar da ita tayi mata Fada kan wani abu ba sai dai ta rika Fadin yarintace in ta girma Zata Daina Ammh ai Hamida bata mata Haka bama ita ba kaf ya"yanta tana Dorasu kan Hanyar mai kyau tun daga bangaran Tarbiya har bangaran Ayyukan gida da Sauraran abubuwa ashe da gangan ta Sangartata ta Shagwabata Duk cikin Lalata Rayuwarta ne bata sani ba Kaiconta ashe ashe duk wasu abubuwan datake yi ba yin kanta bane tasan wasu abubuwan na tadda Hali ammh wannan Rashin Tsoron da Zafin Zuciyar duk ba nata bane Mamanmu ne taso ta kassara Rayuwar ya Jafar sai abun ya Tsaya akanta ta Godema Allah da abun ya Tsaya kanta Domin daman karamin alhakin daka raina Watarana shi zai tsole maka ido. Tafara Tunanin yadda ta rika turata sai taje ta ce ma Hajiya ko mallam bazata tare ba batasan Dannallam sai yanzu ta Fahimci komai wato tana Taya Anty Amarya ne kamar yadda ta Taimaka mata ta kashe musu uwa anya Balaraba zata ga Annabi kuwa..? Idan ta Mutu kila kasa bazata taba karbanta ba ashe ashe bata son tarewarta da ya Danmallan ta Tabbata Auran ma Allah ne yaso da bazasu taba bari ba ta Tuna sanda take tusa mata ra"ayin tace ya saketa Tsoho ne bai dace da ita ba ta tuna yadda take Zaunar da ita tana Dukan ruwan cikinta in taje gidan Danmallan tayi Weekend ta Dawo tasha Turketa ta Tambayeta ko suna waya sai tace mata A"a data ga kuma kamar abun yayi musu yadda suke so ne ta fita Sabgarta ashe Duniyar ce ta Fara Samuwa ba shakka Taga Aba ya Rage damuwa da wasu al"muran sannan ko Jawad sai ya kwana wajen su a ashashen Hajiya Aba bai Damu ba abaya kuwa yana Dawowa sai ya nemi Jawaad inda ya Saka kafa nan yake sakawa shima sai da Mamanmu ta rabasu taji Dadi ashe ashe Sihiri ne ajikinta shiyasa take Fama da Zafin zuciya bata sani ba..! Sai ta Tuna Aminu sanda yake Fadamata watarana ga Mamanmu din ammh har Abada bazata Shafe mata matsayin UWA BA..ta yarda kuma ta amince a wannan Ranar kewar Uwa ne ya Taso mata da tana Raye da a kan kafadarta zata kwanta tayi wannan kukan ammh ina Duk da Lokacinta ne yayi domin mamanmu bata isa ta yi Ajalin yaya ba tunda ita ba Allah bace ta sani Daman chan kwanakin da suka Rage mata a Duniya kenan Mamanmu da izinin Lahi sai tayi mutuwar wulakanci sai tayi mutuwar kaskanci wannan Duniyar datake Fatan ta samu bazata taba cinta ba Har Abada tunda har tayi sakacin Datasan sirrinsu tayi alkawarin sai ta Daidaita Rayuwarsu daga ita har Anty Amarya kuma da yardan Allah zama da ya Danmallan yanzu ta fara Zama Daram Kuma Haihuwa da izinin Lahi indai Allah ke badawa sai ta Rokesa ya bata Ta Haifar masa dozin yan Bakinciki da mahasada sai dai su Fadi su mutu Allah Sarki bawan Allah yana chan yana aikinsa a nan an saka sa agaba Allah Sarki Hajiya da mallam kuna Zagaye da makirai da mugaye baku sani ba. Ita ne nan zata zama sillar Tonuwar asirinsu. An riga anyi walkiya ta gansu. Sannan an Dade ana ruwa kasa tana Shanyewa.. Ita nan Amina Aminene ikon Allah badai ta mutum ba sai ta Allah kainuwan Dashen Allah indan Rana ta fito Tafin Hannu bai isa ya kareta ba..Daya bayan Daya sai sun tsinci abunda suka shuka wannan alkwarinta ne..! Kukan da Amina bata samu tayi ba sai yanzu ya kwace mata sai da Filon Datake kwance akai ya jike da Hawaye kanta ciwo yake yi Idanuwanta sun mata nauyi ga Cikinta na murdamata Har da yunwa tana jin Hajiya ta shigo Dakin bayan ta Dawo daga Falon mallam sukace bata jin Dadi ta shigo ta Dubata ita kuma ta Tusa kanta cikin Hijabi tayi Luf kamar mai barci har ta fita tana fadin Ta samu barci. Duk tana kwance taji Su Hamida sun shigo sun yi sallar mangariba sai alokacin Hajiya ta leko tana Fadin"Hamida ku tada Mamah mangariba tayi..! Hamida ta mike ta isa wajen Amina tana tashinta kafarta tataba Taji Jikinta kamar wuta ta Dago tana Fadin"Zazzabi ya kamata jikinta Zafi..! Hajiya ta kariso Dakin tana Fadin"Asshsha..Mamah Daure ki tashi kiyi sallah sai kici wani abu ki sha mgani..! Dole Amina ta mike Hajiya sai da ta Tsorata da ta ga yadda idanuwanta suka koma Cikin wani yanayi tace"Amina meya faru kike kuka kinga idanuwanki yadda suka kumbura kuwa..? Amina ta mike Zaune tana fadin"Hajiya Yaya na tuna..Sai na fara kuka sai kirjina ya fara ciwo da kaina sai Zazzabi ya kamani..! Daganan kawai ta saki kuka Hajiya ta Dafa kanta Cikin Tsausaya tace"Addu"a zaki mata in kin Tuna ta kin ji ko mamah ba kuka ba..? Kai ta gyada tana kara sharan Hawayen wasu na ambaliya ita ta mike ta kama Aminar da Jikinta ke Rawa ta kaita Tiolet ta barota ta Fito tana kallon su Hanne da Jikinsu yayi sanyi tace"Zo ki kar ban mata magani ke kuma Hamida shiga kitchen ki zubo mata abinci ga Jawaad ma chan afalo ki zubamai yaci kafin yayi barci.! Da toh suka amsa mata ta fice suka bi bayanta Hamida tayi yarda Hajiya tace ta Zubama Jawad Jallop din Taliya da Miyar kifi ne ta Zubama Aminata kaimata ta iske tana Sallah a Zaune Hanne ma ta kawo mata mganin da Ruwa suka koma Falo suka barta kada su Dameta. Tana Idar da sallah ta zauna sai kuka take yi ta rasa addu"an ma da zatayi kawai sai ta Daga Hannu tana rokar ma Mamanmu tabewa da bala"in Duniya kala kala tanayi tana kuka Kafin ta kife kanta ta cigaba Tana wajen aka kira isha"i daga Zaunen ta yi sallar ko abincin bata kallah ba sai da taji kamar Hajiya zata shigo sannan ta Jawo Filet din ta fara ci Turawa kawai take yi ko Rabi bata ci ba Cikinta ya Cuse zuciyarta ta fara tashi ta Nufi Bayi a guje sai amai sai da ta Amayar dashi Duka sannan ta koma gefe tana maida numfashi koiya Fitowa batayi ba sai da Hamida tazo ta fito da ita ta iske Hajiya da Hanne afalon abincin tace a Dauke a Hado mata Tea mai kauri to shi ta dan samu ta sha ya Zauna ta hada da panadol Hajiya ta fice zuwa shashen mallam ta Sanar dashi cikin wani yanayi yace Allah ya Sauwake in ba sauki gobe sai Hajiya ta kaita asibiti tun abunda ya Faru ne Dazu Mallan bai Saki ba har yanzu..! Awannan Daran yadda Amina taga Rana haka taga Dare domin barci ko barawo bai Saceta ba ga kuncin zuciya ga Zazzabi Cikin Dare kaf Abunda ke Cikinta sai da ta amayar dashi kafin Safe Jikinta yayi zafi sai rawan sanyi take da Haduwar Hakora sallar asuba ma Dakyar ta iya yi tana neman Faduwa Hanne ta jira sai da Hajiya ta Dawo daga Shashen mallam ta Fada mata cewa tayi su sauya ma Amina Hijabi bari ta Fadama mallam ya ma Idi mgana yakai su asibiti. Mallam na jin jikin Amina yayi zafi Hankalinsa ya tashi ya Kira Idi a waya yace yazo ya kai Hajiya asibiti ba Dadewa sai gashi Lokacin Hajiya har ta Shirya Amina ko Tafiya bata iya yi Saboda yadda Jikinta yayi zafi Hanne da Hamida suka riketa har Bakin mota ta shiga Suka Bita da fatan samun Sauki Cike da Tsausayi mallam ma Sai da ya Tsausayamata ganin yadda ta koma Cikin kwana Daya yace su Hajiya su yi gaba komai kenan ta Kirasa. Kafin su tafi sai da Hajiya tace su Hanne su shirya su tafi makaranta Harda da Jawaad suka amsa mata da Toh suna masu Tsausayin Amina. Suka koma Shashen Hajiya suka yi wanka suka karya suka yi shirin tafiya makaranta Harda Jawaad sai da suka fito ne suka ga Aba suka gaisa sai Lokacin ya rike Jaawad yana Fadin ya yi musu yaji shi da balaraba ko Mallam na wajen yace to yaga su Hamida sun dawo ina zai zauna in da ba kowa abunda mallam bai sani ba in Aba baya ga Jawaad bane yanzu mancewa ma yake yi dashi. Hamida ta shiga gidansu ta gaida mamanmu ta sameta cikin kwalliya kamar wata yarinya ita abun ma sai ya bata mamaki sama sama suka gaisa ta shiga Dakinsu ta Dauki littafinta na Biology data manta Dashi bata ma samu Fadama Mamanmu Amina bata da lafiya ba Shidai Mallam ya sanar ma da Aba sai dai ba gida ya koma ba gidan gona ya wuce Shiyasa Mamanmu bata ji ba Sannan a matan mallam ba wacce ta Bude shashenta ma ballatana tasan abunda ke faruwa..! General Hospital tace Idi ya kai su suna zuwa ta Kira Nasir a waya ta Fadamai yace bai riga ya shigo asibitin ba ammh gashi nan kan Hanya ba Dadewa sai gashi ya iso ya Iske har Hajiya ta yanki kati suna bin layi Tunda gidan mallam bai Dauki wani Family Doctor ba ba ruwansa da wannan,Duk da ba bangaran yara bane A sanshi a asibitin shi ya karbi katin su Hajiya ya shiga wajen Likita yamai bayani ganin Dr.Isa ne abokinsa ne yamai bayanin Hajiyarsu ne ta kawo kanwarsu ba Lafiya jin haka yace su shigo kawai. Dole sai Nasir ne ya rike Amina Saboda tana mikewa jiri ya kwasheta ta kusa fadi Allah yasa yana kusa ya Tareta Hajiya bazata iya ba ita kadai Ganin yadda suka shigo da ita a rirrike yasa Dr Isa yace su shimfidar da ita kan gadon dayake ganin marasa Lafiya nan Nasir ya Dorata shi kanshi ya ji Tsausayin Amina jikinta kamar wuta Saboda Zafin Zazzabi. Likitan yazo ya Duba bayan ya cire mata Hijabin jikinta ya taba Temprature din jikinta ya gwale mata ido ya kuma Duba Tafin hannunta bayan ya kalleta na tsawon mintina goma kai ya girgiza kafin ya Dawo ya Zauna ya kalli hajiya da Nasir yana Fadin"Zamu dibi jininta za ayi Test..sannan akwai yunwa tare da ita zan kara mata drip da allurai wanda zasu taimaka mata ta Dawo Cikin hayyacinta..! Ba musu Hajiya tace"Ayi abunda ya kamata likita in ma gado zaka bamu ba Damuwa..! Yana Rubutu saman wata Takarda yace"A"a mama Ba gado bane zamu dai mu riketa na awa daya ko biyu zuwa uku mu saka mata Drip muyi mata allurai kafin Lokacin Sakamakon gwajin mu ya fito..! Wata Nurse ya kira tazo yace ta Dibi Jinin Amina aka kai lap yana son abun da Sauri ne Amina duk Tsoron Alluranta bataji ba yau ko Ihun batayi ba tana gama Diba ta fice  shikuma Nasir Likita ya bashi Takardan Daya Rubuta allurai da Driip yaje phamarcy cikin asibiti ya siyo ya kawo mai nan da nan ya saka Handgold ya Hada allura biyu ya yi mata ta Jijiya Biyun kuma tana Cikin Drip din Amina ahalin Datake ciki kuka ma Har ta gaji da yi ashe sai kana da ma natsuwa kake jin zafin wani abu ita ko Zafin Alluran ma yau bata ji ba.. Kamar almara ba Dadewa Amina sai barci ganin haka yasa Nasir ya tafi bangaransa inda yake aiki yace in da wani abu Hajiya ta Kirasa waje ta fita Tana jira domin Dr.Isa ya cigaba da ganin mara sa Lafiya kamar yadda aka saba..! Hajiya na babban Falo zaune tana jira sai ga Kiran mallam ta Dauka sukayi mgana tace mai Amina na ciki ta samu barci yace su dan jira na wani Lokaci Da haka sukayi sallama Idi bai koma ba yana nan yana jiransu. Awa Biyu da wani abu Hajiya ta kwashe Tana jira sannan wata Nurse tazo ta Kirata zuwa Office din Likita koda ta shiga har lokacin Amina barci take ammh Ruwan ya kare har an cire mata. Kujera yanuna ma Hajiya yace ta zauna, ta Zauna tana Sauraransa wata Farar Takarda Doguwa ya mika mata Hajiya ta karba Tana Fadin"Likita wannan Takardan fa..? Fadamin abunda ke faruwa kune yaran zamani yan Boko..! Mirmishi yayi kafin yace"Amina Sa"idu yarki ce Hajiya ko..? Hajiya ta Dagamai kai da Sauri kafin ya Cigaba da Fadin"Tana da aure ne..? Hajiya taji gabanta ya fadi sai ta basar kafim tace"Eh likita..! Ina fatan ba wata matsala ko..? Da Sauri yace"Babu Mama..Takardan Dake hannunki Sakaamakon gwajin da muka ma Amina ne..Sakamako ya nuna mana tana Dauke da Ciki kimanin Wata Hudu da kwana goma..! Hajiya sai taji kamar bata ji da kyau ba ta Zari ido kafin tace"bangane ba..Likita wani irin ciki..,? Dr Isa yace"Ciki dai na Haihuwa mama .! Hajiya taji jikinta ya Saki Cikin mamaki ta juya ta kalli Amina Dake Sharan barci kafin ta kalli Likitan tana Fadin"yanzu nan Likita Amina ciki gareta har na Tsawon wata Hudu da wani abu bamu taba ganin alamu ba..? Dariya Dr.Isa yayi kafin yace"hakan yana Faruwa sosai Mama...naga shekarar ta 17 ajikin katinta ko..? Hajiya ta gyada kai tana mamakin ikon Allah acikin ranta. Likita ya Cigaba da fadin"ba abun mamaki bane in baku gane ba..Tana da karancin shekaru sannan Cikin nata irinsa ne Hausawaa ke cema Kurman ciki bai cika bayyana kansa yana karami ba sai ya kusa fitowa Duniya..Sannan in kun lura Cikin yabi Jikinta ne ya kuma yazo Lokacin ta na age din kuruciyarta ne sannan tana da Tsawo sai ya shanye shi ajikinta inbamu masana abun ba, ba lalle ku iya gane tana da ciki ba..! Hajiya ta jinjina kai kafin tace"Ko fa Laulayi batayi ba Likita sai dai ta rika cin abinci sosai..da yawan barci..! Dr ya gyada kai kafin yace"Ba lalle sai tayi ba ai kowani Ciki da nasa Salon mama..Ita nata nacin abinci ne da yawan barci kila ko zatayi Laulayin sai nan gaba kadan..! Hajiya ta sake jinjina kai kafin tace"Sai jiya tayi ma amai sau Daya..! Dariya wannan karon yayi kafin yace"Normal ne..Mama kila ma Daga yanzu Lokaci bayan Lokaci in taci abund bai karbi Cikin ba Zata iya yin amansa.! Hajiya ta Damke Takardan Hannunta tana Fadin"Nagode likita yaushe Zamu tafi gida..? Yace"Yanzu da zarar ta farka..alluran barci nayi mata yanzu zata saketa..! Suna ma cikin mganar Amina ta Farka tana Kokarin tashi Hajiya ta karisa gabanta ta mata sannu Dr Isa ya taso ya kara Dubata ya tambayeta me take ji tace ba komai jikinta ya rage Zafi Zazzabin ya Sauka mganganuna ya Rubuta mata ya Sallamesu sai ga Amina na takawa da Kafarta har wajen mota sai alokacin hajya ta kare mata kallo Taga Cikin da Likita yace yabi Jikin Amina Allah mai iko Annabi mai Dumbin Daraja. Basu tafi ba sai da ta Kira Nasir yazo haraban asibitin ya same su koda ya Tambayi Hajiya me likita yace sai taki Fadamai ta dai basa Takardan mganin daya bata shi kuma yace ta Jira yaje ya siyo ba Dadewa sai gashi ya Dawo da Ledan mai Tambarin General Hospital Gumel. Shi Nasir bai wani tsaya duba takardan mganin ba shiyasa bai Fahimci ko na menene ba. Daganan sukayi sallama bayan ya leka Motar yayi ma Amina Sannu ta amsa tana Dagamai kai. Har suka kai gida Hajiya ta kasa gasgasta abunda taji Aranta kawai sai ta shiga wani Tunani Tsakanin miji da mata sai Allah bata Zargin Amina har ga Allah sai dai kuma likita yace Cikin Jikinta wata Hudu da kwana goma sannan in ta Lissafa dai dai Danmallan shima nada wajen wata hudu da sati Biyu in bai fi ba da komawa Madina,kenan kafin ya tafi ne in ma wani abun ne ya shiga Tsakaninsa da Amina Allah mai iko sai abun ya bata mamaki matuka. Sanda suka Dawo Mallam bai fita ba ammh yana Sauri zai je Fadar Sarki ana nemansa shiyasa bai Tsaya ma sun yi mgana da Hajiya ba ganin Amina Taji Sauki har gata ma tana Tafiya da kanta kuma cikin ikon Allah har suka kai Shashen Hajiya basu hadu da kowa ba. Suna shiga Hajiya bata Zauna ba ta Hado ma Amina tea mai kauri ta matsa mata tasha ta bata mgungunanta duk yawancin na karin Jini ne sai na Vitamin C da polic acid na masu Ciki sai kuma panadol sai da ta sha ta natsu Fatan ta kada tayi Amai sai kuma Allah yasa batayin ba. Hajiya ta rakata Dakin su Hanne ta kwantar da ita kan gado sannan ta Zauna gefenta tana kiran sunanta Aminaa na kokarim mikewa Zaune Hajiya tace ta koma ta kwanta. Hajiya ta kalleta Cikin ido kafin tace"Mama kinsan me Likita yace yana Damunki..? Amina ta girgixa kai kanta a kasa Hajiya ta gyara Zama kafin tace"Yace Kina CIKI har na Tsawon wata Hudu da kwana goma..! Dam!!! Gaban Amina ya fadi ta kalli Hajiya da Kumburarrun Idanuwanta ta maimaita Cikin mamaki "Ciki ...? Hajiya ta gyada mata ai sai acikin Ran Amina tayi wata Hamdala ta yi kabbara ta sake yin wata kabbara domin mganar mamanmu take Tunawa da tace bazata Haihu da Ya Danmallam ba sai Sakina sannan kuma auran haka zai kare ba Fa'ida Ashe ashe basu sani ba Allah ya Riga yayi ikonsa..! Ganin kamar bata wani Razana Sosai bane yasa Hajiya tace"ko kin san da shi ne Amina baki Fadamin ba..? Amina na sharan Hawayen data rasa ko na Dadi ne ko na Murnan Karshen mamanmu da Anty Amarya yazo ne. Bata sani ba cikin kukan tace"Wlh bansani ba Hajiya bansani ba..! Hajiya ta Dafa hannun Amina Kafin tace"Basai kin Rantse ba nima da naga Jiya naga yau ban gane ba sai ke yarinya karama Mamah..? Yi shurunki..! Hajiya ta fada tana Faman share ma Amina Hawaye Tsausayinta na kamata. Hajiya ta Dakata tana Fadin"Tambayarki zan yi Tsakaninki ga Allah Mamah..kada kiji nauyi na ina so na gasgata wani abu ne.. Shin Kafin tafiyar Danmallam wani abu ya shiga Tsakaninku ne..? Ai sai Amina taji kamar kasa ta Bude ta Shige sai ta juya baya ta Dunkule kanta tana mai jin kunyar Hajiya abunda ya faru Tskaninta da Danmallam yana Dawo mata kamar a jikin magiji. Hajiya ta Daga hannu tayi kabbara Tare da Hamdala ta mike tsaye ta Fice Tana Mai Farinciki wanda ya kasa Boyuwa a saman Fuskarta. Tana fita Direct Dakinta ta shiga waya ta Dauka ta Kira Danmallam bakinta kamar Gonar auduga saboda Murna Yana gida bai fita ba yaga Kiran Hajiya sai da gabansa ya fadi suna Falo Tare da Sarood ne ya barta ya shiga Cikin Bedroom dinsu,kafin ya Katse kiran yabi bayan kiran Hajiya Tana Dauka ko amsa sallamarsa batayi ba tace"Danmallam kana jina..? Cikin Wani yanayi yace"Ina jin ki Hajiya..! Ta cigaba da Fadin"Tambayarka zan yi kuma ina so ka fadamin gaskiya..! Zama yayi gefen gado yana fadin ina jinki Hajiya..! Hajiya tace"Wani abu na auratayya ya Shiga Tsakaninka da Amina ne kafin tafiyarka.? Ina kasa ta Tsage Danmallan ya shige ya kasa mgana gabadaya sai jikinsa ya Fara rawa kamar yana gaban Hajiya,Ya kasa mgana ma kamar ya kashe wayar haka yake ji meya kawo wannan mganar..? Badai wani abu ne kuma ya faru ba..? Jin yayi shuru yasa Hajiya tace"Amsar ka tana da muhimmanci Danmallam..! Muryansa a shake yace"Ehhh..! Hajiya tace"Allahu akbar Sarkin gagara Misali..UMAR  ka godema Allah..Amina nada ciki har na Tsawon wata Hudu da kwana goma cikin ka Umaru..! Haka yaji Hajiya tace kafin ta katse kiran sai ya fara Tunanin kodai bai ji Daidai bane..? Wata Aminar ke da Ciki..? Kwakwalwarsa ta Fara Hasko masa Amina ita ce ke Dauke da Cikinsa kuma ya Tabbata Hajiya bazata Kirasa tamai wasa ba..! Allahu akbar ya furta sau uku ashe Ashe Daman wannan kwan Hallitar yasa tafiyarsa bata yuyu ba aranar  Allah ya Kaddara mahaifan Amina Zata Dauki wannan hallitar shiyasa tafiyarsa bata samu ba sai da ya Dawo gida sannan cikin abunda bai Tsammani ba ya tara da Amina ashe ashe ya saka mata kwan haihuwa ashe ashe ya zama Daya da ita baisani ba..! Wannan shine ake kira Zanen kaddaran..? zakaran da Allah ya Nufa da Cara ki ana muzuru ana shaho sai yayi. Yau Cikin Farinciki suka tashi shi da Sarood na warkensa gabadaya jiya ya tabbata namiji ga Sarood ya maida ita mace shiyasa bai fita ba ya Zauna yana kula da ita Allah yayi gaskiya Qur"ani waraka ne bai san Sadda ya Durkushe a saman cafet din Dake Bedroom din ba ya Daidai ci gabas yayi Sujudul shukur Muryansa cikin Zaki da gardi yake fadin. "Alhamdulillah..Alhamdulillah..Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban Halittun duniya Annabi muhammadu Sallalahu alaihi wasallam.." *Janafty**TFZB2015* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Hajiya na fita Daga Dakin Amina ta Dago kanta sai da ta tabbatar da Hajya ta shige Dakinta sannan ta Mike Zaune kan gadon ta yaye rigar kikinta Cikinta Daya fara tasowa kadan take kallo sai da ta kuramai ido sannan ta Fahimci ba"a sama yake ba yana kasan maranta ne dan tasawar da yayi ashe ashe ba Timbi bane kamar yadda suke Tunani ita dasu Hanne Ciki ne na Haihuwa..? Ita yau Amina ke da Ciki zata Haihu..? Yau ina yaya take..? Bata raye saboda haka bazata ga wannan ranar ba..? Mamanmu ta rabata da yaya Har gaban Abada mamanmu bazata ga Daidai a Rayuwarta ba Tana hawaye tana shafa Cikinta Daga jiya zuwa yau wanu Tsanar mamanmu ne ke yawo acikin ranta Tsanar da ko Anty Amarya bata yi ma irnsa ba Domin ta Cutar da Rayuwarta tundaga matakin Haihuwa har zuwa jiya da asirinta ya Tonu Shafan Cikinta take yi ta ke taji wani kaunarsa na mamaye aranta Dariya tayi acikin Ranta tana Hango Amina da y'a tab lalle za"a ga uwa anan wajen Sun so su hana ta Tarewa auran ma ba da son ransu bane sai dai In dan Rana ta fito tafin Hannu bai isa ya kareta ba Allah yace kuma ya isar da Cewarsa Hawayenta ta share wani kunci na Shiga aranta Tana Dafe da Cikinta tace"Allah ya kare min duk abunda ke Cikina..Allah ba ikona bane ko Dubarata ba ne da ka bani wannan kyautar ajikina kuma ka karesa batare da kowa yasan dashi ba Ya Allah ina Rokinka da kariyarka ka cigaba karesa har ya fito Duniya domin Fitowarsa Duniya ko bayyansa Shine Zai Taimakamin wajen Tona ma mugaye azzalumai asiri mara sa Tsoron Allah Kamar yadda suka ce na Ratso aikin su batare da sun sani ba nayi alkwarin Dawowa Amina Sa"idu gusai dina mai Biyayya da ladabi Mai Tsayawa ga Kafafunta nayi alkwarim Daga yau bazan kara kuka Domin na gaza ba sai domin imanin ka ya Allah ka Tsareni da Tsarewarka kabani Kwarin gwiwan da zan bankada Azzalumai dani suke zencen mu zuba mu gani shege kafasa Aminene nike kirarina badai ta mutum ba sai ta Allah..! Ta karishe fada Lokaci Daya wani karfin gwiwa na shiganta Tsoro yana barin ranta son Cikinta da son ta Rainesa ya fito Duniya ya Zauna aranta Abu Daya take son gani Tozartan Mamanmu da Sauran masu mugayen zuciya irin su Anty Amarya da Haj.Uwani yau gata da ciki in sun isa su hana Allah ya ikonsa ashe karyan Boka da mallam suke tunda suka kasa bankado musu wannan sirin Shashashan banza azzalumai Da Yardan Allah karshen ku yazo ku Fara Kirga Lokacin da zaku wulakanta. Hajiya ta rasa ina zata saka kanta Saboda Farinciki,Ta kasa zama ta kasa Tsayuwa waje daya ta Daga Hannunwanta duka biyu sama tanayima Allah kirari domin wannan shi ake kira tsammanin Abunda baka yi Tsammani ba. Hajiya ta rasa da wa zata ra ba wannan Farinciki na ganin Amina Dauke da cikin Danmallam ta Dade batayi farimciki irin na yau ba gashi mallam baya nan balle ta ruga ta Fadamai suyi wannan murnan tare yaya kuma bata Raye balle ta Ruga ta Fadamata Amina zata zama uwa nan bada Dadewa ba Amina zata koma yadda take so sai Bata a duniya lokacin da hakan ta faru sai dai tana Fatan Ta cikin samu salama acikin kabarinta har Abada. Haj.Uwani ta Fado mata arai itace tafi Kusa da ita in wani abu ya sameta bayan mallam da Sa"idu itace ta ukun Datake sani yasa ta kwashi Sauri zuwa Shashen nata bakinta kamar zai tsage Saboda murna. Koda ta shiga Falon ba kowa tsit tana Tunanin kila tana ciki ne yasa ta yi sallama sai dai ba"a amsa mata ba ta Bude baki zata sake wata sallama ne Taji Muryan Haj Uwani cikin shewa da Dariya tana Fadin"Batula naso kina wajen nan kiga idanuwan marliya gaban mallam da Hajiya..? Kinga yadda ta muzanta ba halin ta Fadi wata mgana na riga na gama Daureta da Jijuyoyin jikinta..sai uban kuka take yi mallam kuwa yayi mata Fata Fata Hajiya har da yar Nasihan kan Marliya ta Daina bin malamai wlh Batula naso kiga yadda marliya ta koma abun Tsausayi..! Shuru na wani Lokaci ya biyo baya Hajiya bata Fahimci kan zencen ba ganin kamar tana waya da Yar"uwanta Batula yasa Ta juya da niyyar Barin Falon AllaH barshi ta Dawo an juma ko in ita Uwanin ta shigo sai ta Sanar da ita sai dai tana Daga kafarta da niyar Fita taji Uwani na Fadin"Haba ni ce fa Batula kar kin manta ni..Ai marliya bazata kara kiran mai alewa bata da kudi ba..Alokacin da nake fadama Marliya Irin Tuggu na sai ta ga nata ai bakomai bane Batula na Fadamata zan yi shekaru aruru ina bin bayan Hajiya ne kamar wata Sakarya..? Na Fada mata na riga fara aiki akan biyan Bukata saboda haka sai da ta hakura da nata Cikar Burin ta barni na cika nawa in burina ya gama cika zan sallameta sai ta nuna Taurin kai cewa ita bazata yarda ba sai na Fadamata me nayi ma Sakina da yasa ta ke Barin duk cikin data samu. ? Nace mata ta kwantar da Hankalinta ba Sakina kadai ba, har ita Balarabiyat da ita kanta Aminar ko sau D'ari zasu samu Ciki sai yabi Rariya alkawari ne na Daukan ma kaina Nazir ya fara Haihuwan ma mallam Jikiko guda Biyu hakan ya Zama kuskure ammh yanzu bazan kara maimata kuskure na ba..Duk da Haka sai da nasa aka maida su mara sa amfani a wajen mallam kamar yadda aka maida Nasir yanzu abubuwa nawa akeyi agidan nan kafin kiji mallam ya kama sunansa an Dade..? Kamar yadda na saka Mama ta sa Nazir yayi nisa da Gumel din da har Abada bazai iya zama na Sati Daya acikinta ba na saka ta Lula kurciyar Danmallan madina yadda bazasu zauna ma agarin bama ballatana Mallam ya gansu ya ce zai Dorasu kan dukiyarsa Batula kin san yadda na sha Wahala shekaru aru aru kan ganin ya"yana akan gaba akomai agidan nan to Wahalata ta kusa zuwa karshe Nazeem sauran kadan ya karisa ya Dawo uzairu kuma yana Bautar kasa kafin ya gama Nazeem ya Dawo daganan zan Dora harshashen Burina ya fara cika ga Shamsu shima ya fara nasa karatun kina ganin zan bari marliya tazo ta rusamin Shirina na ne..? Shine na Tauna Tsakuwa domin aya taji Tsoro Batula na tabbata na Saka tsorona azuciyar Madina,bama ta da wayau ne ni da ya kamata ta godemin Batula..? Nan ta maida balarabiyar nan kamar Hoto wajen Umar kan Tariyan Amina kuwa babu abunda basu yi ba ita da mai tayata din saboda kar ta tare ammh sai da ta taren sai ni kuma na karisa musu aikin na Dorata kan Tsarin dana Dora Sauran..Domin na Riga na fadamata indai ina Numfashi Cikin matan Umar ba wacce ta isa ta Haihu ya"yana basu fara Haifama mallanm jikoki ba Domin Tunda Mama ta Fadamim mallam ya son ganin Ya"yan Umar tunda yafi soyuwa wajen ya'yansa ni kuma na mike Tsaye na hana Faruwar hakan sai dai ya Mutu bai taba Haihuwa ba batula. ! Hajiya tsabar mamaki da Rudewa sai da ta Bude baki kamar sau goma tana Rufewa Jikinta yayi wani irin sanyin mamaki da al"ajabin jin kalaman Dake Fitowa Daga Bakin Uwani Duniya Haka ta lalace bata sani ba..? Kana Zaune da Mutum Tsakani ga Allah shi kuma yana nan yana Cutarka ta karkashin kasa duk da bata Fahimci wasu mganganun ba ammh ta Fahimci Daga marliyan har Uwanin basu da zuciya mai kyau sannan Duk Jirgi Daya ya kwasosu sannan abunda ya Faru jiya wannan Tsakaninsu ne sannan Daga baya Uwani ta maida abun kan Marliya..? Ashe Uwani ke zubar da Cikin Sakina..? Ita tayi ma su Nazir kurciya kin zama a kusa da mallam..? Gabadaya sai taji kanta ya kulle ta kasa wani Tunani har zata tafi ta koma Shashenta sai ta fasa so take taga Idanuwan uwani taga ko zata iya Hada ido da ita Hajiya mace ce mai Juriya da Takwalli shiyasa koda taji haka Razanan Dake zuciyarta bai nuna a saman Fuskarta ba Murya ta Bude kadan ta kara yin wata sallaman tana Fadin"Uwani ko bakya Ciki ne..? Haj.Uwani Dake waya taji kamar mganar Hajiya afalo gabanta ya fadi ko sallama bata yima Batula ba ta Datse kiran ta fito falo da Sauri har Zaninta na neman Faduwa har ga Allah sai da gabanta ya fadi data ga Hajiya Cikin Daburcewa da kinganta kinsan bata da gaskiya ta washe baki Tana fadin"Hajiya ke ce daman..? Yaushe kika shigo. ? Hajiya ta kalleta na wani Lokaci ganin yadda take zufa yasa tayi wani Mirmishi aranta tace ruwa ai ya kare ma Dan kada kuma Uwani a Fili kuma cewa tayi"Eh shigowata kenan ina ta Sallama shuru..! Ajiyar zuciyar data saki sai da Hajiya ta jita ta sauke Numfashi tana Fadin"Eh wlh ina cikin Tiolet ne Fitowa ta kenan naji sallamanki..Sannu da zuwa hajiya.. Ki zauna mana kina Tsaye..? Hajiya ta kada kai kafin tace"A"a ba zama nazo yi ba..Naga duk yau baki Fito bane shine na leko naga ko lafiya.? Haj.uwani na sosa kanta tace"Lafiya lau barci ne a idona Hajiya jiya ban samu barci ba Umaima tatashi tana ta Kuka cikin Dare..! Hajiya ta kada kai kafin tace"Allah ya Sauwake ya bata lafiya..!. Uwani ta amsa da ameen Cikin Fuskar Tsausayi taso taja hajiyar da Hira sai hajiyar tace mata tana wani abun ne bari ta koma Shashenta sai ta shigo Suka Rabu da Uwanin akan zata shigo har da raka Hajiya tana fita ta kulle kofar Shashenta lokaci Daya tana Sauke Nunfashi Fatanta Daya Hajiya bataji wayar ta da batula ba ai da aikinta na Shekaru ya rushe alokaci Daya bata ma san meyasa ta bar Falon nata abude ba..! Hajiya har ta kai Shashenta mamakin Abunda taji Uwani na Fadi bai bar ranta ba ko iya karisawa Dakinta batayi ba ta samu saman kujera afalonta ta Zauna tayi Tagumi tunani take ko Tun Zamanta da uwani tun suna Gusai tataba Cutar da ita ne..? Balle itama ta rama ta Hanyar abunda take Fadin ta aikata..? Sai taga bata samu komai ba sai Mutuntawa da girmama juna da Tarin Alherinta ga Uwani ashe daman alheri na komawa sharri..? Allah Sarki Danmallam Uwani ta Curar dashi wajen salwantar mai da Cikinsa bama ita kadai ba tace har Amina in ta samu Ciki sai yabi Rariya..To ita Allah ne..? Ta isa da taja da abunda yace ne..? Sai jikinta ya fara rawa kada Uwani ta Farga da Cikin Amina shima ta ga bayansa Domin bata da Imani Allah Sarki Nasir bawan Allah har da shima bata barsa ba..? Ba ruwansa mai Sanyi da Hakuri Duniya ma bata Damesa ba duk Cikin ya"yanta shi kadai ne tabbas maallam bai wani Damu da lamuransa ba ashe da Dalili .? Ga Nazir da ya"yansa suma din badai kaji mallam na mganarsu ba duk da yake son ganin jikikinsa a gabansa shima ashe da Dalili..? Sai dai Uwani tayi kuskure tana Takama da Boka da mallam ne su kuma Allah suka Rike ko Daya abunda tama ya"yanta bai Dameta ba don sun yi nesa da ita bashi ke nuna sun manta da iyayensu ba Bata bakinciki da Haka Tunda suna chan suna neman na kansu ne kuma tana da yakinin addu"arta garesu shi ke Tsare dasu Duk kwanan duniya sai sun kirata sun gaisheta sannan haka mallam sannan Duk wata Daga Nazir har Danmallam suna aiko ma ta da kudi hakama mallam koda basu Cikin wahala ammh Basu manta cewa iyayensu dana Hakki akansu ba ko Nasir sai dai tace Allah ya biyasa da gidan Aljannah Shi da Jafaru ga Sa"idu wh Tallahi yau ko mutuwa Umaru da Naziru sukayi bazata ce tayi kukan maraici ba Domin sa"idu da ne kamar da goma sannan ga Nasir da Jafaru da bai Taba sakawa ta Ji zafin Rashin Zaman ya"yanta Biyu kusa da ita ba ga matansu Tsakaninsu sai mutumtawa da Martabawa har ta Matar Nazir Hidiya in bata kirata yau ba zata kirata gobe ta gaisheta kuma in suka zo garin bata Sauka a ko"ina sai shashenta sai in itace tace taje shashen Uwani ko Nasara tafi ma Darajata Fiye da Sakina domin kaf Cikin Surukanta bama wacce ta raina ta irin Sakina to me zai Dameta..? Ita Allah ta rike kuma dashi ta Dogara boka ko mallam basu isa su ja da Ikonsa ba..! Zata numa Uwani da dukkan mugaye irinta su Marliya da ma wasu Boyayyin wadanda Allah bai bayyanasu ba Domin ta tsorata Ta kasa ma yarda da kowa gani take Tunda Uwani ta Cutar da ita to wanda batayi Tunani ba shima zai iya Cutar da ita kafin Su farga da Cikin Amina ya kamata tayi wani abu a matsayinta na Uwa yau dai ta cire kawaici da kunya da nuna ikonta in takamar su boka da mallan ita ta rike Allah sannan bawa bai isa yayi ma Mutum abunda Allah bai masa ba. Zata kare Amina da abunda ke Cikinta Har sai ya bayyana Lokacin da Danzaki ya girma basu isa su ga karshensa ba Umaru zai haihu Tabbas zai ga kwansa Daga Tsatso mai Daraja Tsatson Sa"idu da Hadiza ta sani addu"arta ne Allah ya amsa ta Dade tana Fatan Ganin Zuru"a mai yawa ta bangaran Umar da Amina tun kafin mallam ya Hada wannan auran Burin haka ke ranta. Zata nuna musu ba su isa ba..Allah ya Fisu sannan suna Raye za"ayi komai Da yardan Allah sun fara ganin Rashin Nasara har abada acikin Rayuwarsu sannan burikansu bazasu taba Cika ba..! Tsam ta mike Amina ta leka taga ta Samu barci kafin ta kada kai ta Shiga Dakinta wayarta ta Sake Dauka ta Kira Dannallam har alokacin yana Cikin Daki bai fito farimcikin abunda Hajiya ta Fadamai ya kasa sakinsa Tsammamin abunda baka Taba Tsammani ba wajen wanda bakayi Tsammani ba..! Sarood na falo tana ta samu barci ya lekata ya gani shiyasa ya Dawo Daki ya Zauna kawai yana ta Tasbihi da yima Allah kirari Lokaci Daya soyayyar abunda ke Cikin Amina ya shiga ransa shiga ran da ko Sakina in ta Samu Ciki bai taba jiba Fata yake da Addu"am Allah ya bar masa wannan Ciki shi kadai yake tunanin Haihuwar Amina Zai faranta ran mallam da Hajiya da Baba Sa"idu fiye da Tunaninsa alokacin Kirjinsa ke Budewa Da sunan Amina da dukkan abunda ya Faru Tsakaninsu sai ga wani Kira Daga Hajiya gabansa ya fadi ya rika Allah Allah yasa ba cewa Zatayi wasa take mai sai da ta gama Ringing sannan yabi bayan kiran. Sai a wannan karon ne Hajiya ta bari suka gaisa Cikin Yanayinta na rashin Dadi tace"Ina fatan mganar da na Fadamaka baka Fadama kowa ba ko..? Kai tsaye ya amsa mata da Eh Hajiya ta gyara Zama tana fadin"To ka min alfarman bazaka fadama kowa ba Ciki kuwa har da matanka da Sa'idu da abokinka Aliyu ko yan"uwanka ban amince ka Sanar da kowa Amina dana Ciki ba .! Cikin mamaki yace"Hajiya har da mallam..? Hajiya tace"Ni zan sanar dashi Dakaina wannan..Ta bangaranka ka bar mganar nan asirri Umar..Ban yarda da kowa ba za"a iya Cutar da Abunda ke Cikin Amina nayi alkawarin da sunan Allah zan bata kariya saboda haka kayi shuru da bakinka ..! Cikin gamsuwa yace"Na Fahimta Hajiya..Allah ya saka da alheri..! Hajiya ta amsa da Ameen ta Cigaba da Fadin"Sannan zan Dauke Amina Daga idon mutane..Saboda wasu Dalilaina bana son bayan ni dakai da mallam wani yasan da mganar Cikinta da kuma inda zan kaita ajiya har zuwa Lokacin da Cikinta zai isa Haihuwa..! Cikin mamaki yace"Hajiya ina kenan..? Kai Tsaye tace"Abuja zan kaita Wajen Aisha..Chan zata Zauna na wani Lokaci kafin abubuwa su Daidaita..! Danmallam mamaki ya cikasa sai dai baya yima iyayensa gaddama yace"Shikenan Hajiya kiyi duk abunda ya kamata..! Ta jinjina kai kafin tace"Kada ka Damu zuwa Lokacin duk zaku san Dalilina na hakan sannan zan bata Wayar nan a hannunta in ta koma chan ku cigaba da mgana ta waya..! Cikin girmamawa ya amsa mata kafin Cikin wani yanayi yace"Tana Lafiya ko..? Hajiya tayi Mirmishi kafin tace"Lafiya kalau..jiya ne ta kwana da Zazzabi shine yau mukaje asibiti likita ya auna jininta sai ga Ciki kaji abun Allah ko..?ko ni Da nike Tare da ita Allah bai bani ikon gano hakan ba..Shiyasa na yarda akwai abunda Allah ya Boye kan cikin nan na Amina..Umaru ka Dage da addu"a don Allah azkar safe da yammah da Karatun Qur"ani na yarda Bawa bai isa yayima Mutum abunda Allah bai mai ba addau"armu gareku bazata taba Faduwa kasa banza ba duk Salolinka kada ka manta da Rokar ma Amina Tsarewar Allah da ita da Abunda ke Cikinta kaji ko..? Sai duk jikinsa yayi sanyi da kalaman Hajiya duk da tana yawan fada musu su dage da Addu"a ammh na yau na Dabam ne Cikin Sanyinsa ya amsa mata ta Dinga sakamai albarka kafin suyi sallama tace Zata kirasa in sun yi mgana da mallam zuwa gobe take son ta kai Amina Abujar bazata ba ta Lokaci ba. Bayan ta gama mgana da Danmallam Nazir ta kira suka gaisa shima abunda tace ma Danmallam tacemai shima sai yaji wani iri Hajiya kamar tana barin Wasiya suna gama waya ya Kira Danmmallam a chan madina yana Tambayansa ko sun yi waya da Hajiya yace eh sai yake tambayansa ko ta yimai nasiha da rokom ya Dage da addu"a yace eh sai nazir ya fara Tambayansa ko Hajiya bata da lafiya ne ya Tabbatar mai da lafiyanta kalau sun Dade suna tattaunawa kafin su rabu kan Shi Nazir din ranar Lahadi zai zo yaga Hajiya ya koma saboda Hajiya is d Best mother in d word. Bashi ba ko Hidiya na Fadin bata ga Uwa kamar Hajiya ba mai kirki mai kawaici sai ta kirata sau goma su gaisa bata kira dan data Haifa ba Tunda suke da Hajiya sai dai ta Bisu da addu"a bata taba Saka ido kan samun su ba bata taba tambayansu wani abu ba sai dai su Dauka su bata ta amsa tana godiya tana saka albarka ita da Mallam samun a iyaye is a Bleesing basu taba Dogara ga abun hannun ya"yansu ba sai dai su bisu da saka albarka da addu"an nasara. Hajiya kuma suna gama mgana da Nazir ta shiga wanka Saboda tana sauri suka Fita asibiti bata Tsaya yi ba tana fitowa taga wayarta na Haske tana Dubawa taga Mallan ke kiranta ta Dauka sukayi mgana yace mata ya Dawo tace mai gatanan zuwa Daman shi take jira,Mai ta shafa ta shirya Cikin wani sabon less din da Mijin Aisha ya Dinkamata suka aiko mata dashi har da mallam ma sun dinkamai shadda ganin Dattakon Mijin Aisha da kuma sanyin Aishan yasa ta Zabi ta kai mata Amina ta Zauna awajenta tasan zata kula da ita sannan kuma ba wanda zai san tana wajenta indai ba ita Hajiyan ta Fadama wani abu ita kuma tayi alkwarin bama Amina da abunda ke Cikin kariya da ikon Allah..! Kitchen din Shashenta ta shiga ta Dora ma Maallam Ruwwn Tea dinsa Datake dafamai na Sassaken mganungun Musulunci mganin sanyi ne sai da ya tafasa ta Juyemai a Fulas Ta Dauka da kofi saman wani katon Faranti ta fita zuwa Kitchen din Tsakar gida suka gaisa da su Lami taga Doya suka soya sai Miyar albasa da sukayi ta Diban ma mallam din ta Nufi Shashenta ahanya ta Hadu da Anty Amarya ta Dawo daga wajen mallam din Fuska kozai kozai kamar wacce tatashi Daga jinya sama sama Hajiyar ta Tsaya suka gaisa ta wuce Anty Amarya ita kanta sai da ta Bita da kallon mamaki ganin yanayin Hajiya na yau din da bata taba gani ba ,ko Sakina bata tambaya ba akwanakin nan kuwa ko bata shiga ba in suka Hadu sai ta tambayi Jikin Sakinar sai ta Danganta hakan da abunda ya Faru Jiya Uwani ai tatashi Wasa da ita yanzu ma mallam taje kara bama Hakuri har ya Sallameta bata samu wani kyakyawan kallo Daga garesa ba. Ta bi shawaran Dayyaba ta kira mallaminsu ta gayamai yayi mata mganin Uwa sannan ta sanar dashi ya Dakatar da Barin Cikin da Sakina take yi yace zai kirata nan da kwana uku ta Saurareshi,so take kafin Lokacin ta Samu mallam ya kalleta da kallon yafiya da kauna sai abun da yazo mata da Sauki ammh kalli fa mallam ko son ganinta bayayi ai Uwani ta gama Cutar da ita..! Hajiya koda ta shiga Falon mallam yana zaune yana nazarin Wani Littafin labarci ya amsa mata sallamanta ta shigo ta ijiye farantim Hannunta ta Zauna gefensa suka gaisa Ya tambayeta jikinn Amina tace da Sauki ya karya Tukunnah sai suyi mgana Littafin hannunsa ya ijinye ya Sauka kasa ya Tankwashe kafa ta Zubamai ya fara ci Hajiya na gefe tana kara Nazarin shawaran data yanke tana fatan Allah yasa mallam ya yarda da Tsarinta kada ya matsa sai yaji Dalili duk da awajensa ya"yansa suka Dauko Rashin son jim abunda ba"a so su ji ba Suma haka suke basu da yawan Tafiya ballatana Bin kwakkwafi. Sai da ya gama sannan ta tattara komai ta matsar gefe ita ko yunwar bata ji Cikinta ya Cushe da yanayin Data ke Ciki shima mallam din kallonta yake yi Cikin wani yanayi yace"Zainabu Fuskarki ta bayyana Damuwa..? Me yake Faruwa ne..? Hajiya ta Sauke Numfashi kafin ta mike tana fadin"Mganace dani mallam mu shiga ciki..! Yayi mamakin jin tace su shiga Ciki bai mata musu ba ya tashi yabi bayanta zuwa Cikin kuryan Dakinsa abunda ya basa mamaki suna shiga ta Sakayo kofa shidai yana binta da kallo ta Dawo ta Zauna agabansa asaman Katuwar Dardumar Dake Dakin. Cikin ajiyar rai tace"Mallam Munje asibiti likita ya Dibi Jinin Amina an aunata kuma yaga Ciki wanda yakai kimamin Wata Hudu da kwana goma ajikinta..! Mallam sai yayi mata kyar yana kallonta na tsawon Lokaci kafin kawai ya saki kabbara..! "Allahu akbar..! "Allahu akbar..! "Allahu akbar..! Sai da ya maimaita sau uku sannan Cikin Tsantsan Farinciki yace"Kin gani ko Hajiya..? Allah shi kadai yasan Lamarin Daya Boye kam Mamana da Umaru ...Kai wannan labarin Farinciki ne Hajiya Masha Allah ina mamar tawa fata Dai Likitan yace ba wata matsala ko..? Hajiya tace"Ba wata matsala..! Mallam na jinjina kai Cikin Farinciki yace"madallah..Allah ya inganta Allah ya Bata lafiya ya zaunar dashi Allah yasa ta Sauke lafiya..! Hajiya ta amsa da Ameen Mallam yaga yanayin ta wani a sanyaye yasa yace"Hajiya naga bakya murna ne..? Ko da wata matsala ne..? Sannan ya kamata a Fadama mijinta..! Hajiya tace"Na fadamai..! Cikin mamaki yace"kin fadamai fa kikace..!? Ta gyada kanta kafin tace"Eh mallam..Kuma na rokesa bayan ni da kai da shi ko Sa"idu bazai ji labarin Cikin nan na Amina ba mallam..! Mallam ya kalleta yana fadin"Bangane ba.? Hajiya ta gyara Zama tana fadin"Ina da Dalilina mallam..Bana son cikin nan na Amina ya fallasa..Daga ni sai kai sai Danmallam shima don yakamata ya sani ne tunda shine Uban cikin..Mallam kamin wannan alfarman cikin matanka ba wacce Zata sani ko Sa"idu kada yasani mallam Don Allah..! Mallam yayi shuru kafin yace"Duk naji Toh ammh meyasa kika ce haka..? Miye Dalilinki..? Hajiya tace"Zaka ji Dalilina ammh ba yanzu ba sai nan gaba Dalilin nawa zai bayyana kansa.. Mallam yayi shuru kafin yace"To sai yaushe Sa"idu zai sani..? Balaraba fa..?bai kamata ta sani ba makafin uwa take ga mamana fa..? Hajiya taji har Balaraban yanzu bata da yarda da ita ba yasa ta girgiza kai kafin tace"ya kamata ta sani..ammh a wannan gabar itama bai kamata ba mallam..Nidai kayi hakuri akwai Lokacin da zan fada maka Dalilaina nayin haka sannan zasu sani in lokacin su sani yayi..! Mallan ya tari numfashinta da Fadin"Yaushe kenan..? Hajiya ta kallesa Cikin ido kafin tace"Kafin abunda ke Cikinta ya Fito Duniya..! Ya kalleta yana mamakinta meyasa Hajiya tace haka sai kuma yaga bazai iya Ture alfarmanta ba. Yasa ya jinjinamata kai kafin yace"Shikenan..! Hajiya tace"Ba shikenan ba..Alkawarin zakamim ba wanda zai ji sannan kuma ina so na Fada maka zan Dauke Amina Daga gidan nan zan kaita inda zata yi Renon Cikinta har Zuwa Lokacin da zai bayyana kansa shima bayan ni da kai da Danmallam ba wanda zai san inda Amina take..! Mallam ya fara Tunanin da wani abu Cikin mamaki yace"Ina zaki kaita..!? Kai Tsaye tace"Gidan Aisha Abuja..! Mallam yace"Aishan ce zata iya kula da mai Ciki..? Nawa take ko itama ta Haihun ne bansani ba..? Hajiya tace"Ko Daya bansani ba ko tana da Ciki ammh ina da Dalilina na kaita Chan din ni na Haifi Aishan nasan Halinta Zata kula da Amina Sosai kuma ba ita kadai bace agidan yanzu akwai kakar megidanta da tadawo gidan da zama kaga kenan zata Tayata kula da Amina da abunda ke Cikinta..! Mallam ya kalli Hajiya ya kara kallonta kafin yace"Duk me ya kawo wannan..!? Sannan in tatafi karatunta fa kin san fa sun kusa fara jarabawar da kika matsa na Biya mata ita da yan"uwanta sannan mijinta ya kusa zuwa ya Dauketa kamar yadda kika basa Umarni..! Hajiya tace"yanzu ba lokacin karatu bane..Ta Haifi abunda ke Cikinta Lafiya sai komai ya Biyo baya mallam..! Zai yi mgana ta Riko hannayensa tana Fadin"Don Allah mallam.! Idonta sai ya ciko da kwallah gani take in tayi wani Sakaci Amina Zata Shiga wani Hali..ganin haka yasa ya Jinjina ma Hajiya kai kafin yace"Naji na amince mijinta fa..? Kinsan bazaki Dauke matarsa bai sani ba ko..? Sannan ita Aishar ai ba ita keda kanta ba An nemi izinin mijin nata..? Hajiya tace"Danmallam bai da matsala na Fadamai ya amince Megidan Aisha kuma Usman kai ne zaka kirasa kai mai mgana nasan ma bazai ce konai ba ni kuma zan kira Aishar na Fadamata komai zuwa gobe nake so mu tafi..Kada ka manta mallam iya ni dakai da Danmallam ko Sa"idu kar ya sani ballatana Sauran yaran don Allah..! Mallam bai da tacewa illah gyada kai kafin yace"Shikenan nayi alkawari..Zan kira Usman din muyi mgana..Allah yasa hakan shi yafi Zama alheri bazan ja da mganarki ba Domin baki taba aikata wani abu Sabanin Tarbiyan gidana ba na baki Dama ki kula da Mamana da abunda ke Cikinta Allah ya raba su lafiya..! Cikin jin Dadi Hajiya ta amsa da Ameen Ameen sannan ta mike tana Fadin"Nagode mallam..Ka taya mamarka da addu'ar Allah ya Tsareta ita da abunda ke Cikinta ya rabata da Sharrin mugum mutum da aljan..! Wannan karon bai boye mamakinsa ba sai da yace"Hajiya kodai wani abu ya Faru ne..? Da Sauri ta girgizamai kai kafin tace"Ko Daya..Kasan duniyar ne ta lalace..Ba kowa ke zaune dakai don Allah ba..Sannan ba kowa ke son ganin cigabanka ba. ! Daga haka ta Bude Dakin ta fice ya Bita da kalli yana kara nazarinta aransa yana Tunanin me ya faru..!? Hajiya bata Cika irin wannan mganar ba.? Tabbas wani abu ya faru sai dai bazai matsa mata sai yaji ba yasan ta bata aikata wani abu bata da Dalili mai karfi shiyaasa zai bata goyon baya insha Allahi zai kuma taya Amina da addu"a kamar yadda tace Duk da bai taba gazawa da mata addu"an shirya da Daidaituwa Tsakaninta da Umaru ba..! *Bakina yayi kadan wajen nuna godiyata ga masoyana..Nagode kwarai da gaske ina ganin Addu"o'in ku gareni Yadda kukemin Fatan Alheri nima ina bin ku dashi Godiya ta musamman ga Masoyan da suka siya wannan Littafin Allah ya rubanya muku da Alheri Allahu ya bar zumunci Ameen..* *Janafty**TFZB2016* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* Hajiya Shashenta ta koma cikin wani yanayi,yanayin da take ciki tun Lokacin dataji wayar uwani da kanwarta,wani irin dakiya da kwarin gwiwa tare da yakinin babu wani mai yi sai Allah ne suka shigeta. Ta samu sukuni da sukayi mgana ta Fahimta da mallam yanzu zata jira har ya Kira shi Usman din mijin Aishar duk da tasan ba matsala Aisha kuma sai sun isa goben zata mata bayani haka kurum taji Hankalinta ya kwanta da Aishar saboda tana da bambamcin Hallayar da sauran sannan Halinta kamar Halin Danmallam ne, bata da Hayaniya ballatana yawan surutu. Ta yi ta leka Amina tagani ko tatashi bata tashi ba sai wajen sha biyun rana Data Sake lekata ta ga ta tashi Hajiya da kanta ta shiga Tiolet ta Hada mata Ruwan wanka ta taimaka mata ta shiga tayi wanka bayan ta fito ita ta Dauko mata wata Doguwar riga ta saka Duk ta rame ta wuya idanuwanta sun kumbura kadan Saboda kuka. Tea Hajiya ta sake hado mata da sauran Doyar da suka karya dashi da Safe,Kadan Amina taci Doyar Tea din ta Shanye duka domin cikin jikinta na son shan Tea musamman ma Dayake akwai madara aciki. Sai da Hajiya ta barta ta natsu sannan ta Dawo domin tayi mgana da ita Amina na Zaune Saman Cafet ta jingina da gadon Hanne tana maida numfashi Lokacin da Hajiya ta Sake shigowa Amina kuka take yi domin bata Zaman mintina goma bata tuna da Yaya ba da irin yadda mamanmu ta Dai'dai'ta Rayuwarsu. Tana ganin Hajiya sai tayi Dubara ta share Hawayenta,Bata sani ba Hajiyar ta gani ammh sai tayi Tunanin Sabida yanayin datake Ciki Domin abubuwa sun faru ne duka Tsammanin abunda basu yi Tsammani ba dukkansu. Gabanta Hajiya ta Zauna ta Tankwashe kafa Amina tana kokarin gyara Zamanta Hajiya ta Dakatar da ita da fadin"A"a mamah yi zamanki..! Kanta ta maida kasa domin kunyar Hajiya take ji. Hajiya ta kalli Amina Lokaci Daya ta Kira sunanta ta amsa jin muryan Hajiya Daga gani mganace a bakinta. Hajiya ta cigaba da fadin"Amina ina so kiyi hakuri ki kuma Dauki Rayuwa yadda tazo miki. domin bawa bai isa ya Zabama kansa wata Rayuwa ba illah wacce Allah ya Zaba masa..! Amina dai batace komai ba Hajiya ta kara Gyara Zamanta tacigaba da Fadin"Ina so na fada miki..Gobe zamu Tafi Abuja gidan Aisha chan zaki Zauna kiyi Renon Cikin ki Zuwa wani Lokacin..! Amina ta Dago da mamaki tana kallon Hajiya kafin tace"Hajiya gidan yaya Aisha..? Hajiya ta gyada kai kafin tace"Nan Amina nasan zaki yi ta mamakin meyasa haka..? Ina da Dalilina Amina akan hakan Dayasa bazaki zauna anan ba..Sannan bana so kowa yasan da mganar Cikin ki Mamah ko Hanne da Hamida ne kada ki Fadama kowa sannan shima Batun Tafiyarki ban ce ki sanar dasu ba..In na Dawo goben Daga kai ki Zan musu bayani bana son koken koken nan naku..! Kiyi hakuri Jarabawarki bazaki yi ta yanzu ba sai in kin haihu nayi miki alkawarin karatu zaki yi shi har sai kin gaji..Danmallam ma bazai taba Tauye miki Hakki ba..! Amina sai ta fara Tunanin ko Hajiya tasan wani abu ne kan mamanmu da Anty Amarya..? Sai dai bata ga wani alama ba,Ita yanzu zata iya yin komai Saboda Cikin jikinta sannan Zatayi komai Saboda Tonama mamanmu asiri da Anty Amarya kuma Cikin jikinta ne makami shiyasa bayanin Hajiya bai Dameta ba Hawaye suka kawo Idanuwanta in ta tuna Shekarun data kwashe bata san Dadi da muhimmancin Uwa ba,Gashi yanzu tana Cikin wani Siradi,Siradin da uwa ce kadai Zata tallafamata sai dai ina Mamanmu ta yanke wannan abun Saboda son zuciyrta da kuma Mugunta da zalunci. Ganin Tana Hawaye Yasa Hajiya tayi Tunanin Rabuwa da su hanne da karatunta yasa ta saka Hannu ta Rumgumo Amina kan kafadarta Tana Lallashinta Lokaci Daya tana Fadin"Kiyi hakuri Amina..ki daina kuka na dan Lokaci ne watarana sai Labari..! Amina na Shesshekan kuka tace"Hajiya ba ina kukan hukuncin ki bane.. Ina kukan rashin yaya ne..ayau bata a Duniya ina jin matukar kewarta..! Hajiya Tsausayinta ya kamata ta Dagota tana share mata Hawaye lokci Daya Tana fadin"In kin Tunata ki mata addu"a kin ji ko..?.Sannan in kin ji kewarta ki tuna Dani Domin tamkar Uwa nake gareki ina nan Saboda ke Amina ni ba Uwar Umar nake ba Har Abada ni ina matsayin mahaifiya gareki ne nayi kuma alkawarin Kareki da yardan Allah ke da abunda ke Cikin ki..! Tana Fada tana share mata Hawaye wasu na Bulbulowa Hajiya fadi take"ki daina kuka nasan zaki ji Dadin Zama da Aisha na dan Lokaci ne Zaki Dawo in Lokacin hakan yayi.! Amina ta gyada kai tana Fadin"Hajiya ke da mallam nasan har Abada bazaku kai ni inda Zan cutu ba..Sannan duk abunda kuka Zartan kan Rayuwata ina maraba dashi..Na yarda da Hukunci ku kuma Insha Allahu Zaki Sameni mai Bin Umarninki..! Hajiya taji Dadin haka ta Dinga shafa kan Amina ta saka mata albarka kafin ta mike tana fadin"Kayan ki duk suna gida ko..? Amina tace"Eh akwai wasu anan hajiya..! Hajiya tace"To ai ba kaya da yawa Zaki Diba ba nan gaba ma kadan zasu yi miki. Sai ta Dinka miki wasu achan kawai..! Har Hajiya ta Fice Daga Dakin Amina bata kara mgana ba,wani irin Dakiya ne da Taurin zuciya ke shiganta da kwarin gwiwan da bata san tana Dashi ba Duk da tasan zatayi kewar su hanne da makaranta ammh Gaskiyan Hajiya ne datace na dan Lokaci ne watarana sai labari. Daya da wani abu na rana su Hanne suka Dawo sun ji dadin ganin Amina taji Sauki basu damu da yanayinta ba sun Dauka saboda bata da Lafiya ne ita kuwa kallon su kawai take yi Tana Tunanin sai dai suga Hajiya ta Dawo ita kadai zasu yi kewarta kamar yadda itama Zatayi kewarsu Hamida kuma Tsausayinta take ji domin in ta kalletasa sai taji kuka ya taso mata ya Zataji in taji Abunda mahaifiyarta take aikatawa..? Bazasu iya Daukan wannan abun ba su take Tsausayi domin ba d'an da zai so uwarsa ta kasance bata gari ba abun akwai taba Zuciya ammh Dolen wata watarana Allah ya Tona musu asiri kamar yadda ya Fara Tona musu awajenta. Kamar sun san Amina zata koma wani wajen Ranar wuni sukayi tare ko Hamida bata ko leka gida ba suna Tare har Dare,Da mallam ya shigo har Shashen Hajiya ya Dubata ya Dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka..Allah ya Saukeki lafiya ya kareki mamana..! Ta amsa kanta na kasa kafin ya Sake fadin"Kina tsorata Cikin barcin ki har yanzu ko kin bari..? Amina tace"Yayi sauki baba..! Malam ya jin jina kai yana Fadin"Zai bari gabadaya ki Dage sosai ki Daina kwanciya ba alwala sannan ki Rike addu"o"in nan da yawaita karatun Qur"ani..! Amina ta amsa da toh ya Dade yana mata Nasiha kafin ya fita,Dakin Hajiya ya shiga sukayi mgana ya Fadamata ya Kira Usman mijin Aisha yace ba wata matsala sannan bayama gida yana Lagos,Daganan sukayi mgana sama sama kafin ya fice Daman shi da Aba suka shigo shima ya shiga ya gaida Amina bai Dade ba shima ya fita Amina bata Damu ba Sai ma wani Tsausayinsa Daya kamata Mace tatasa shi gaba da makircinta. Mallam nan ya bar Aba Hajiya tamai mganar Zata kai Amina gidan D'aya Daga Cikin yaran nan tadan koyi wasu abubuwa tunda ga yanayin yarintarta bata koyi wasu abubuwa ba sannan nan da Lokaci kadan Danmallan zai zo ya tafi da ita madina.. Aba bai Tambayi ina Za"a kai Amina ba Sai kawai yabi Hajiya da godiya yana komawa gida ya Fadama mamanmu yadda sukayi da Hajiya anan nema take jin Amina bata da lafiya Mamanmu dataji haka shewa ta Saki aranta tace auran da Zai kare a gantali ne za"a je koyon zama da Miji..!? Shiyasa kwata kwata bata Damu ba,ita Atunaninta Wahalar da kai kawai Hajiya take yi ammh Amina da Umar ai sai hange Daga nesa ammh a fili sai ta nuna Tasauyawanta da cewa da Safe zata shiga ta gaida Ameenan kafin su tafi ko aranta bata Damu da Sanin ina Hajiya zata kai Aminar ba wannan baya gabanta yanzu. Adaran Hajiya Ta kira Aisha tace gobe tana nan tafe Aisha taji mganar kamar Daga sama murna ta Cikata Dayake Usman din bai riga ya Kirata ya Fadamata ba Hajiya ta rigasa sai taga kamar ta zama mai sa"a domin Hajiya basa zuwa gidan mutum hakanan sai da babban Dalili ammh ita yau gata Hajiya Zata zo gidanta Murnan ta ya kasa Boyuwa suna gama mgana da Hajiya ta tafi Dakin kakar mijinta Dake zaune tare Dasu da suke Kira Yakaka ta sanar da ita Hajiyarsu na tafe gobe. Har gari ya waye su hanne basu san komai ba da Safen dai Hajiya tace ma Hanne zasu fita da Amina su shirya su tafi hadda sukace to basu yi wani tunani ba, sai sukayi Zaton Ko asibiti zasu koma basu damu ba. Ammh Sanda suke shirin tafiya Amina na kwance na kallon Hamida na shiryawa ta fito wanka aran Amina tana tunanin Hajiya zata zame ma Hamida uwa kamar yadda ta Zame mata uwa,Idonta ya kawo ruwa in ta Tuna zatayi nesa dasu saurin share Hawayenta tayi ta kira sunan Hamida bata Damu data waigo ba ta amsa mata. Amina tace"Hamida don Allah ki kula da Jawaad..! Hamida sai da ta saka Rigar wata atamfar dake jikinta sannan ta Juyo jin abunda Aminar tace da yanayinta yasa Cikin mamaki tace"Wasiya kika fara bari ne Aminene .!? Amina tayi Mirmishi tace"Eh mana kinsan Rayuwa haka ta gada..muna tafe ne bamu san muna tafiya da mutuwarmu ba .! Hamida ta fara Dariya tana Fadin"Lalle Amina ta fara Tunanin mutuwa..Hanne tazo kiji..Hanne. ! Ta shiga kwalama Hanne kira sai gata ta Dawo da Faratin kayan karinsu tana Fadin"Kiran me kike min hamida kamar kin bani ajiya..? Hamida na Dariya tace"Amina ce ta fara barin wasiyya..! Hanne ta ijiye abun hannunta saman Cafet tana kallon Amina Lokaci Daya tace"Topa ta fara Tunanin mutuwa ne..? Ko azara"ilu ta gani..? Ta fada tana yar Dariya Amina ta balla musu harara tana fadin"Bansani ba. kufa yan iska ne baku san abun arziki ba.! Hamida tace"Mu ko ke ne bamu san abun arziki ba..? Ke Amina uban wa ya kaiki maida abun arziki na fada ma. ! Hanne ta Zauna tana Fadin"Ki zauna mu karya hamida kada mu makara..Amina inaga asibiti zasu koma da Hajiya. ! Hamida tace"Shiyasa ta fara barin wasiyya kenan. ! Duk tana jinsu batace musu komai ba illah tasowa da tayi tace su karya Tare harda Jawaad daya shigo yanzu gabadayansu suka karya suna yi suna Hira Amina tana tunanin shine na karshe Zaman su tare Indomie ne sai soyayyan kwai da Tea Amina kwan taci ya taso mata da zuciya sai da tayi Amai ta koma ta kwanta tana maida Numfashi su Hanne na mata sannu da Zasu tafi haka taji kamar ta Bisu har suka fice tana musu bye bye suka fita Suna Dariyanta wai Amina ciwo yasa ta fara Tunanin mutuwa Basu san cewa Amina Zatayi nisa da su na wani dan Lokaci ba..suna fita ta Fashe da kuka sai da tagaji tatashi ta rarrafa tayi wanka sai a yanzu da aka Tabbatar tana da Ciki take jin wani Sauye Sauye ajikinta na masu juna Biyu. Ta shirya Cikin Riga da zani na kayan da Hajiya ta Dinka musu ita da Hanne da Hamida abunda yasa ma rigar tayi mata daman tun farko dinki yayi mata yawa saboda Sizes din Hamida aka mata kuma tun Lokacin ba"a rage kayan ba Ta yi shirinta da wuri ne Sabida Hajiya tace da wuri zasu tafi Tunda ita ayau din zata Dawo. Yan kayanta Dake nan kawai ta Hada kala uku sai Azakar da addu"o"in da mallam ya Rubuta mata' sai mangunanta,wasu kayan nata suna gidan Aba wasu kuma suna gidan ya Danmallam bata kwaso duka ba,Zama ta yi kawai tayi Tagumi tana Tunanin yadda Sabuwar rayuwa zata Bude mata ita da abunda ke Cikinta tana tunani tana Hawaye sai ga Hajiya ta shigo tayi saurin goge hawayenta saboda kada ta gani ashe ta gani sai bata nuna mata ba Kallonta tayi tana Fadin"Mamah kin gama shiryawan .? Amina kanta na kasa tace"Eh Hajiya ina kwana..? Hajiya ta amsa tana fadin"To kin kar ya kuwa..? Ta gyada mata kai tana Fadin"Eh hajiya..Tare da su hanne muka karya. ! Juyawa tayi ta Fice tana Fadin"To bari Idi ya dawo kai su makaranta sai mu wuce..! Fitan ta ba Dadewa ta Leko tace ma Amina ta fito Dogon Hijabinta ta Saka Jakar data Hada kayan nata Hajiya ta karba ta farayin gaba itama ta shirya Tsab da ita,Hajiya na gaba tana Binta abaya har falon Mallam suka gaisa ya kara mata Nasiha sai ga Idi ya Dawo Hajiya ta mike tace zasu tafi mallam yace"Ko in kira Sa"idu ne su yi sallama..? Hajiya tayi shuru kafin tace"kyalesa kawai ai na Fadamai jiya.. Mallam bai kara mgana ba shi ya rakosu har bakin mota sai ga Hajiya Nasara ta fito domin ita ke da Turakan mallam jiya ganin Hajiya da Amina yasa tace ko anguwa zasu je Hajiya tace eh ba Dadewa zasu yi ba mallam dai na gefe bai ce komai ba domin yayi alkwarin bazai ma Hajiya kaladan kan abunda ta Tsara ba ya yarda da ita fiye da duka matansa bazata taba aikata ba Daidai ba. Agaban idon Hajiya Nasara da Mallam Suka fita Daga gidan idi ke jan su a Motar mallam din prado baka suka Dauki Hanyar Abuja Amina na ta sharan kwallah Hajiya na kallonta batace komai ba Domin bazata hanata ta koka ba. Su hajiya basu yi nisa ba,Aba ya fito zai Tafi gidan gona mallam ke Fadamai su hajiya sun tafi yayi mata Fatan Dawowa lafiya bai Dade ba gaiswawa kawai sukayi da Mallam ya shiga Motarsa ya tafi bayan tafiyarsa sai ga mamanmu ta shigo gaida Amina da Haj.Nasara ta fara Cin karo ita ke shaida mata Hajiya sun fita da Amina mamanmu bata Damu ba aranta tace agayas ayasha ta gaida ayyah..! Shashen Anty Amarya ta shiga ta Duba Sakina sannan suka kule Daki suna Kulle kullensu da suka saba mamanmu ke fadama Anty Amarya Abunda Aba ya fadamata Hajiya ta Sanar dashi kan Amina da Tafiyar tasu yau. Anty Amarya ta tabe baki Tana Fadin"Ko shiyasa Daga jiya zuwa yau take wani Shan kamshi..ko Sakina ta Daina lekota su gaisa. ! Mamanmu tace"Yau she kuwa..? Tana chan tana shirin kaita inda Zata kwace miji..!. Anty Amarya tace"Aikin banza ne wannan..Ai Danmallan din yana Tafe nan da wata Biyu in ya Dauki Sakina suka koma ai sai naga karyan koyon kula da miji..! Wai ina ma Zata kaita..? Mamanmu tace"Oho ni dai yace min Gidan Da'ya Daga Cikin yaran mu..! Anty Amarya tace"Ni ba ma wannan ne agabana ba Dayyaba..Mallam nake jira ya Kirani so nake ayi ma Sakina mganin abunda uwani tayi mata Datake bari in aka gama da wannan bangaran mganinta bamai matsala bane..! Mamanmu tace"Ai Allah dai ya Tsine ma Uwani..! Anty Amarya tace"Amin matsiyaci ce..Ta gaban anuna ma jarida. ! Nan suka Cigaba da Tattauna yadda zasu Taru suyi mganin Uwani hankali kwance in sun gama da matsalan Sakina suna ganin Amina bata gabansu.Suna ganin ita karamar alhaki ce bata isa ba yanzu. Abunda basu sani ba wanda bai isan ba Allah yafi nuna isarsa akansa sannan alokacin da Uwani ta Dauke musu hankali Dan Zaki zai girma sannan Tsammanin abunda basu tsammani ba zai faru..!. ***** Abuja..! Misalin karfe Shadaya na rana suka isa gidan Aisha Dake maitama Abuja Kwatsam sai dai ta ga Hajiya abun Farincikin ma harda da Amina Aisha ta kasa Boye Murnanta ta Daka Tsalle ta Rumgume Hajiya sannan ta rumgume Amina Hajiya ta kalleta tana Fadin"Ki mata a hankali bata jin Dadi..! Sai alokacin Aisha ta Lura da yadda Amina tayi kiba Sannan Fuskarta ta Kumbura,haka ta jasu falonta Cikin murna tana da yar aiki wata yar matashiya ita ta cika gabansu da Kayan Taba ka Lashe,Amina sai Bin Gidan ya Aisha take da kallo mai kyau dashi. Aisha ta rasa ina Zata saka su Hajiya Saboda Murna Hajiya ta kalleta tana Fadin"Aisha to ki Zauna mana..!. Ta Zauna gefen Amina tana Fadin"Hajiya murna ce..Ga ki ga Amina. Hajiya ta yi mirmishi kafin tace"Yanzu dai ba wannan ba. ki sama ma Idi waje yaci abinci ya Huta kafin mu tafi..! Da azama ta mike tana amsa ma Hajiya yar aikinta mai suna Saude ta ma mgana taa shiga da Idi Dakin Baki na waje tazo takaimai ruwa da abinci. Tana Dawowa tace ma Hajiya"Hajiya Zaku gaisa da yakaka kakar Usman. ! Hajiya tace"Zan shiga mu gaisa Aisha kada ki damu..! Aisha ta koma ta Zauna kusa da Amina tana Fadin"Aminene ikon Allah Amaryan ya Danmallam ya naga kin yi Shuru ne bakya mgana..! Nice fa ya Aisha..? Ko bakin ya mutu ne basu Hamida..? Amina tayi Mirmishi ta gaisheta ta amsa tana Fadin"Amina kinyi Kiba Lokacin Bikin su Abida kina lange Langenki fa..! Hajiya tace"Na sanar Dake bata da Lafiya ne Dalilin zuwana ma kenan..! Aisha tace"Eh usman ya Fadamin sunyi mgana da mallam..Dama Amina ce Zata Zauna damu Hajiya..? Hajiya sai da ta gama shan ruwa sannan Ta gyada mata kai Aisha ta Zaro ido kafin tace"Hajiya ba ta tare gidan ya Danmallam ba..? Ko ansamu wata matsala ne .? Hajiya ta mike tana Fadin"Mu je Ciki mu yi mgana..Amina kici wani abu kafin mu gama. ! Ta daga ma Hajiya kai Aisha na gaba Hajiya na bayanta har bedroom dinta Gefen gado suka Zauna Aisha Duk ta Tsorata fatanta kada ace auran ne ya Lalace. Hajiya ta kalleta tana Fadin"Kada ki damu ba wata matsala bane..Auran su na nan sannan da sanin shi Danmallam din da Mallam kanshi na kawota wajenki. ! Sai alokacin Aisha ta ji sanyi Tace"Hajiya har gabana ya fadi na Zata ko wani abu ne ya samu auran nasu..! Hajiya tace"Ko Daya..Sai dai matakin dana Dauka duk saboda Kara Karfafa auran su ne Aisha..Ina mai Sanar Dake Amina na Dauke da Cikin yayanku har tsawon wata Hudu da kwanaki. ! Aisha ta zaro ido kafin tace"Ciki Hajiya..Aminar..? Kai ta gyada mata tana fadin"Kwarai kuwa baki ga alama ba ko..? Aisha ta washe baki tana Fadin"Bangani ba Hajiya sai kibar Data kara..Alhamdulillah na taya ya Danmallam Murna daman ga Sakina na ta samun bari Allah yasa na Amina ya Zauna ta sauka lafiya..! Hajiya ta amsa da Ameen kafin ta Kira Sunan Aisha ta amsa mata Cikin bada Hankalinta ganin yanayin Hajiyar. Hajiya tace"Aisha na yarda Dake kaf Cikin ya"yana shiyasa na Zabi Amina ta Zauna agidanki ki kula da ita ta Reni Cikinta na wani Lokaci Sannan na zabe ki saboda baki da Surutu achan gida dagani sa mallam sai Danmallam muka san da Amina nada Ciki sai ke yanzu sabida haka ina so ya Zama sirri Tsakanina Dake..Ban so wani yaji labarin Cikin jikinta ballatana labarin tana wajenki Shima ba wanda ya sani Harta ko da Sa"idu da su hanne basu san komai ba.ki kama Bakin ki koda tambayarki akayi kice baki sani ba Dani kadai zamu Dinga mgana in wani abu ya taso kina jina..? Aisha ta gyada kai Cikin mamaki Hajiya ta Cigaba da Fadin"Nasan Zaki yi mamakin meyasa nayi hakan..!? To ina da Dalilina ammh ba yanzu zaku sani ba sai nan gaba..Fatana ki kula da ita don Allah da abunda ke Cikinta sannan ki koyamata Girke girke da Sauran Kissa na mata Amina haka tataso Sakaka ba wani abunda ta iya Kinsan Tana da abokan zama dole sai ta kara wayewa kan wasu abubuwan..! Aisha tace"Insha Allahu Hajiya Zan yi Duk yadda kikace Sannan zan rike Amina kamar yadda Zan rike Hanne .! Hajiya taji Dadi ta Dinga saka mata albarka sannan tace tatashi ta Rakata Dakin kakar mijin nata su gaisa. Tare da Amina Hajiya tace suka shiga Dakin da Yakaka take Zaune Yar Dattijuwa kamar zata girme ma hajiya hutu ne da jin dadi suka boye girmanta ta amshe su da Fara"a tana Fadin bata son zuwansu ba,da ta fita sun gaisa Tana nan tunda ta idar da sallar walha bata matsa ba..Hajiya tace bakomai suka gaisa sai kallon Amina take yi Hajiya ta mata Bayanin kanwa take wajen Aisha tana da Ciki zata dan Zauna na wani Lokaci Tare dasu ta karishe da Fadin"Hajiya don Allah a kula..Daga Aishar har Aminan yara ne suna karkashin kulawarki Hajiya ga Amana nan..! Yakaka na kallon Amina tace"Insha Allahu Hajiya..Na karba zan kuma kula da ita..Allah Sarki gata yarinya karama Allah ya bata..To Allah ya Rabasu lafiya..! Su Hajiya suka amsa da Ameen Amina ta gaisheta ta amsa Cikin Sakewa tana da Sakin Fuska ga Fara"a nan da nan Hira ta barke tsakaninsu da Hajiya Har Aisha taja Amina suka fita ta nuna mata Dakin dake kusa da na yakaka nan takai mata kayanta Tace nan zata Zauna Daki ne babba mai katifa a kasa sai Cafet da Tiolet aciki Dakin ya Hadu sosai. Nan Aisha ta bar Amina ta shiga wanka ta fito Cikin Farinciki zata Zauna da Amina sannan gefe Daya tana Tunanin yadda zata inganta Rayuwar Aminene jidali ZUWA Aminene mai aji da Haiba. Taya Saude tayi suka yima su Hajiya girki ta Dibarma Idi da megadi ta Dibar ma Amina ta mika mata na Hajiya kuma da yakaka Saude ta mika musu Dakinsu. Aisha tare da Amina sukaci abinci tana yi tana janta da Hira Farar shinkafa ce da wake mai miya Amina kadan taci sai Amai Aisha ta Tsausayama Amina ganin yadda ta wahala wajen amai sannan gata da karancin Shekaru Allah ya bata wannan kyautar ita da tana son Cikin ammh har yau ko bari bata taba yi ba Allah bai kawo ba. ! Ita ta Wanke inda tayi aman a Cikin Tiolet ta kamo Aminar suka tafi tana Tambayanta me zataci tace Tea shi ta Hado mata ta samu ta sha ya Tsaya Daganan Aisha ta barta ta koma Dakin Yakaka ta iske su Hajiya sai Hirar garinsu Bama suke da yakaka nan Hajiya ke fadamata ai su ma sun a zauna a bama su yakaka asalinsu yan Maiduguri ne a bama da labari ya yi Labari Hajiya ta san har gidan su yakaka anan bama kafin yan Boko Haram su Tarwatsa su kowa yayi ta kansa.. Daman ai Yakaka ba ruwanta akwai Hira tare suka ci abinci da Hajiya tayi Sallarta anan wajen Uku saura tayi Shirin Tafiya suka rabu da Yakaka Cikin Aminci kafin su tafi Hajiya ta Damka ma Amima wayar nan da Jafar ya taba kawo mata. Ta bata ta Sanar da ita Tuntuni mijinta ya aiko da ita sai dai a wanchan Lokacin bata bata ita bane Saboda wasu Dalilai ammh yanzu gata nan zata Fadama Danmallam Saboda ya rika kira yana jin Lafiyarta Sannan tama Aisha bayanin Da Amina Zata Zana jarabawa ammh Dalilin haka yasa zata fasa sai wani Lokacin in ta Haihu. Amina sai da taga Hajiya Zata tafin da gaske sannan ta riketa tana ta kuka Hajiya tana llashinta tace zasu yi mgana ta waya tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta sai kuka Aisha ce ta Zauna ta na bata baki Saukinta Daya ma akwai ya Aishar duk da ba kamar su hanne ba ammh da Sauki akwai wanda ka sani a kusa Dakai.... Sai da tayi sallar La"sar barci ya Dauketa Yakaka kuma na jin ance Amina ta kwanta tace maza Aisha ta Tasheta ba kyau barcin yammah Sannan gata da Ciki Dole ta tasheta ita yakakan tazo Dakin Aminan ta Zauna da ita tana janta da Hira ai Tun Amina bata Saki ba har ta Saki jikinta Saboda Yakaka akwai ban Dariya da barkwanci haka ta Dage tana bama Amina labarin Lokacin suna bama farkon hareharen yan Boko haram yadda suka ringa Gudun ceton ransu sai ga Amina na Dariya harda kyatatawa Aisha taji Dadi sosai domin yakaka uwace kamar Hajiya yadda take Daukanta kamar yarta Shiyasa ta matsa sai da Usman ya Daukota daga kaduna wajen kaninsa ya dawo da ita wajensu tasan Amina Zataji Dadin ZaMa da ita sannan zata Dauki darasin wasu abubuwan..! Hajiya sai Dare ta Kira tace sun isa lafiya har sukayi mgana da Amina ta bata Labarin yadda su hanne suka Dinga kuka ta Fada musu Ta kaita wani waje bazata Dawo ba yanzu Amina itama taji kamar tayi kuka Hajiya ta kara Lallashinta da Fadin kada ta saka Damuwa har ya shafi abunda ke Cikinta To in batayi hakuri ba ya Zatayi..? Ai hakuri ya Zama Dole tunda haka Allah yayi da ita daga wannan sai wannan..! *Janafty**TFZB2017* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488* _A WEEK LATER._ Bayan Sati Daya da Tafiyar Amina Abuja acikin Satin Dayan data yi a garin Abuja karo na farko tun da take ta fita garin gumel taje wani waje da sunan Zama na wani dan lokaci. Alokacin da Hajiya ta mata mganar zuwanta Abuja ta shiga Damuwa,Da kuma Tunanin zatayi zaman kadaici ba hanne ba Hamida sannan inda bata Saba ba sai gashi kuma Cikin kwanaki da zuwanta Abuja ta Saki jikinta sosai da garin Musamman ma da Yakaka data kasance mai kirki da Dattako Sannan Aisha ma na iya Bakin kokarinta sosai akan Amina abaya Amina tasan ya Aisha bata da Hayaniya sosai da yawan mgana ammh yanzu haka zata zauna tayi ta jan ta da hira suna tuna irin Rashin ji da su kayi ita dasu hanne Tana bama Yakaka Labari itama Dayake sunan Amina gareta ake ce mata Yakaka tace ai masu suna Amina haka suke yarintarsu an sha kwallo sannan haka suke basu Daukan raini su taru da Amina su yita yabon masu sunansu Nan da nan Amina ta Saki jikinta Dakin Yakaka ma take kwana yanzu Saboda bata son kwana ita kadai yakaka tace ta dawo Dakinta su Zauna tare itama ta samu abokin zama. Haka kuwa akayi sai da ya Aisha taga Amina ta kwashe kayanta takai Dakin Yakaka suna Zamansu lafiya batayi mgana ba saboda ko bakomai yakaka Zata kula da ita sannan ga Ciki ajikinta tana Bukatar wani a kusa da ita. Usman mijinta ya Dawo ya ga Amina har sun gaisa saboda yasanta abakin ya Aisha lokacin tana amarya in kewar gida ya isheta sai ta Zauna ta rika basa labarin kannenta Amina da Hamida da Hanne sannan yasan mganar auranta da ya Danmallam din Tunda sukan yi mgana da shi Lokaci bayan Lokaci haka Itama Aminar tasan Usman sun taba ganinsa Sanda yazo wajen ya Aisha kafin auran sannan sun gansa ranar Daurin auran shiyasa dukkansu basu Tarbi juna abaki ba.. Achan gumel kuwa Hanne da Hamida sun gaji da tambayar Hajiya ina takai Amina..! Sun kyaleta saboda bata gayamusu sai dai tace Amina na nan Dawowa insha Allahu sun Damu Matuka,Ammh kuma Dole suka hakura sai dai kana ganinsu kasan sun rage walwala Sannan a makaranta ko an tambayi Amina cewa suke yi tayi tafiya,Hamida har mamanmu tama mgana ko tasan inda Hajiya takai Amina..? Mamanmu tace bata sani ba tadai san Hajiya tace ma Aba bata wuce Tsakanin gidajen yaran gidan nan ko na gidan mallam ba,ita duk a Tsammaninta bata wuce Tsakanin gidan Jawahir ko Jalela ba tafi ma Tunanin Jalela saboda tayi mgana da yan Gusai kuma bataji Labarin Zuwan Amina ko Hajiya abakinsu ba ita bama wannan ne agabanta ba shiyasa bata Damu da tasan Inda take ba,Saboda kada azargeta da rashin kula da Jawad yasa ta jawosa ajiki ganin yana neman yaki Zama wajenta ya koma wajen Hajiya Hamida kuma ganin ba Amina sai ta Dawo kwana agidansu tana kula da kanta da jawaad tunda Daman Amina ta bar mata Amanarsa to shima ganinta yasa bai Damu ba Duk da shima ya gaji da tambayar ina ya Amina..? Sai dai Hamida tace mai tayi tafiya ammh ta kusa Dawowa.. Sun kusa fara jarabawar Fita nan da Sati uku hanne da Hamida suna Zaton Amina Zata dawo kafin su fara jarabawa Tunda Hajiya bata sanar dasu komai ba. Sakina ta koma gidanta mallam yace Tunda taji Sauki ta koma Gidanta ta Jira Mijinta Dole ta tattara tatafi ammh Sai da ta roki mallam ya bata Sa"adatu tatafi da ita sai yace sai dai Tatafi da Sabeeha tunda ta gama primary zata shiga Jss1 kafin a sakata to da Sabeehan ta koma bayan mallaminsu ya Kira Anty Amarya ta koma wajensa ta Zubaimai kudi ya bata wani kullin mgani yace Sakina ta sha da Ruwan Zafi duk abunda Uwani ta bata taci ko ta sha Zatayi amansa ko Tayi kashinsa Domin ya tabbatar ma da Anty Amarya wani abu ne Aka bama Sakina taci acikinta.. Haka kuwa akayi ranar data sha mganin kwana tayi tana Zagayawa har safe ta Kira Anty ta Sanar da ita Tana jin haka Cikin farimciki tace in Sha Allahu nasara tasu ce. Tsakaninta da Haj Uwa kuma ko mgana basa yi sai agaban idon da bai san tsakaninsu ba kamar mallam da Hajiya da Suke Dauka bata san boyayyin Fuskokinsu ba..Ammh in suka hadu su Biyu su harari juna sannan kuma kowacce ta wuce tana ikirarin sai taga bayan yar"uwanta. ***** Achan Madina kuwa Danmallam dai da Sarood balarabiya suna ta gwangwajen amarcin su sosai fa ya Saki jiki yana Morewa Saboda ai ya Dade Rabonsa da mace tun Kan Amina wannan kuma ai ya Daukesa a matsayin Rabo ne shiyasa daya samu wannan Damar yake ta amfana da ita Domin Daman Daurewa kawai yake yi Yana fama da azumin Litini da alhamis saboda kariya da Tsare kansan. Ita kanta Sarood din sai alokacin tasan ta yi aure sai kuma ayanzu tasan tana kishin Mijinta ada kamar bata Damu da kishin Sakina ba ammh yanzu da tasan waye Umar sai taji har Sakina ma tana matsanancin kishi da ita ballatana Amina datafi Tsayamata arai ganin itace yarinya sannan kuma Amarya. Sosai take ta shagwabanta shi kuma yana lallabata Dalilin haka ne ma yasa har yau bai kira Amina ba Saboda ai sun yi mgana da Hajiya washegarin Ranar data koma Gumel a wayar Nazir Saboda ya cika alkwari yaje ya kwana Daya Ranar Litini da Safe ya hau Jirgi ya koma hankalinsa ya kwanta daya ga Hajiya lafiyanta kalau Cikin koshin Lafiya. Da farko kafin Bullowan Cikin jikin Amina har ya fara Cuku cukun nema mata Takardan Zama madina sannan har sun yi shawara da Aliyu kan zai shigar da Takardan kan zai karbi Gidan malamai na makaranta Saboda gidansa yayi musu kadan sai ya saka Amina ana Cikin makaranta,Sai kuma ga wannan al"amarin da hajiya tace ya Dakatar da komai Shiyasa ya dan Samu Sauki ya fara shirin Tahowa saboda Sakina sannan uwa uba Amina yana son yazo ya ganta Tunda ya tafi bai fi sau hudu sukayi mgana ta waya ba sannan Sakina duk sanda sukayi mgana ta Dinga mai kuka keman tana fadin yazo ya tafi da ita Tsausayinta yake ji ganin halin Datake Ciki yasa yayi mata alkawarin zai zo nan da wata Biyu zai zo sai su koma Tare Umra yake so yayi shiyasa ya Dakata da Tafiyar Sannan Sarood ma tayi Damara sai taje kuma in yace bazai je da ita yayi rashin adalci ko Iyayanta sai sun ga rashin adalcinsa...! Tunda suka yi mgana da Hajiya tace kada ya sanar ma kowa ko Aliyu bai Fadama komai ba yadai Fadamai laluran nan tasa Allah ya basa waraka da Taimakon shawarwarin mallam Daganan kuma sun ma Dade basu yi mgana ba daya kirasa sai ya Fara mai Tsiyan ya barsa ne yaci amarcinsa da yar Balarabiyarsa Danmallam Tsaki kawai yake yi da Dariya domin ba karya yana fa shan amarci. Sai da Amina tayi kwana Goma A Abuja sannan ya nemi wayarta da lambar da Jafar ya Dade da Turomai sai kuma ya kara jin wayar a kashe bai ji Dadi ba in yace Amina bata aransa yayi karya abubuwa ne suka sha mai kai sannan da Tazaran Dake Tsakaninsa da ita da rashin shakuwa da kuma Basu wani saba da juna ba. Aisha ya kira kawai saboda ko ya Kira Hajiya bata kusa da Amina. Daman duka kannensa suna kiransa awaya suna gaisheshi lokaci bayan Lokaci Haka suke basu yar da tarbiyan gidan mallam ba ko da yayyinsu basa kusa dashi suna Kiransu a waya suna Zumunci dasu Lokacin Ba'rin Sakina sun ta Kiransa suna mai Jaje. Lokacin da yake tambayan Aisha mganar yaji wayar Amina akashe ya Aisha tace bata sani ba ammh Zata tambayi Aminar taji tunda ita tama manta da mganar wayar sannan batama Taba ganin Aminar da wayar ba. Yace to ta fadama Amina yana son mgana da ita ta kuna wayarta Ya Aisha ta amsa da insha Allahu zata Fada mata ya tambayeta ya jikin Aminar..? Ta sanar dashi lafiyanta kalau sai godiya Zazzabin Dare dai take fama dashi sai amai sannan bata iya cin kowani abinci sai Tea sai Kuma wainar Fulawa,Komai Taci baya Zama sai ta Amayar dashi sai yaji Tausayinta gata yarinya ga shi ya Dora mata nauyi sun yi mgana da ya Aisha sosai ya sanar da ita suje asibiti tace eh Usman ne yace ta bari ya Dawo yaje Kaduna wani aiki Da haka suka rabu.. Suna gama wayar Aisha ta nufi Dakin Yakaka tana shiga ta iske Amina Zaune saman Cafet tayi Daidai tana cin wainar Fulamai mai manja da Saude mai aikinta tayi mata Tun Safe bata ci komai ba Tea din ma yau taki sha ita sai Wainar Fulawa Shine Yakaka tace Saude tayi mata Wainar Fulawan har Sauden tana Dakin ne suna ta Hira Yakaka na basu labarin Cikin kakan su Usman har ta Haihu kanwa ne abincinta sai da bakinta ya Lashe saboda Cin kanwa tana Fadama Amina ta godema Allah tayi ma Ciki mai kyau tunda batayi mugun laulayi ba sannan ta iya shan Tea da Cin wainar Fulawar tayi kyan ma Laulayi. Amina sai cin abunta take yi tana Dangwala yaji tana Sanye Cikin Bakar Doguwar riga cikin kayan ya Aisha ne da ta bata take sakawa tunda kayanta sun Daina Shigarta Cikin fa Kiba kawai da Budewa yake saka Amina ta bari ne Usman ya dawo su je asibiti da kasuwa ta siyo ma Aminar Dogayen Riguna tunda duk ta bata na wajen nata sannan sun ma Aminar karanci. Shiga Dakin tayi da Sallama Suka amsa mata,Saude tama mgana tace taje Kitchen ta Dora Girkin Rana Ta amsa da Toh ta fice sai da ta fita sannan ya Aisha ta kalli yakaka tana Fadin"Yakaka sannu da Hira..! Tana Dariya tace"Yauwa Sannu Aisha..Hala har kin kwanta Hirarmu ta, tada ke..? Aisha tace"A"a Wlh ina ta gyare gyare ne ma Yakaka ban ji ma Hirarku ba..! Yakaka tace"Au ho..Ai ina nan ina ma Takwarata Tsiya ina fadin ta godema Allah tayi Ciki mai kyau ba laulayi sannan ta na cin abincin Zamaninmu ni lokacin da nayi Cikin Gaddafi har na Haihu kanwa ce abincina..! Ya Aisha ta jinjina kai tana fadin"Kanwa..? Taba..Yakaka kin sha wahala..! Ta yi Dariya kafin tace"Ai Darajan Uwa ta Daban ce Aisha..Allah dai ya bama kowa nashi kema ina miki addu"an Allah ya baki naki Aisha ita Aminatu ai tana mai kyau ma Kinga banda aman da take yi to sai Zazzabin Daren dana ce miki tana Faama dashi..! Ya Aisha tace"Eh zamu je asibiti taga Likita ma yakaka in Usman ya Dawo..! Ta jinjina kai kafin tace"Hakan yana Dakyau..Allah ya Dawo dashi lafiya..! Suka amsa da Ameen harda Amina Data gama ci ta Kora da ruwa ta koma Tana Sauke Numfashi. Ya Aisha ta kalleta tana Fadin"Amina ina wayar da Hajiya ta baki da Zata tafi..? Amina ta Dafe Cikinta daya Fara Fitowa ta yamutsa Fuska kafin tace"To ina na sani..? Tunda ta bani chan Dakin na wurgar da ita..! Ya Aisha ta hararrta tana Fadin"To daman don ki ijiye Aka baki wayar..? Kefa kina da sarkaci bayan ma jidalinki wani Lokaci..! Amina ta kalleta kafin ta Tura baki ya Aisha tace"Tashi muje ki Daukomin ita na saka miki chaji tunda Daman Hajiya tace Sabuwa ce..Mijin ki ya Kirani yace yana son mgana Dake in fada miki ki kunna wayar hannunki..! Amina ta kalleta Shekeke kafin tace"Mijina kuma..? Ya Aisha tace"Eh ko ba mijin naki bane..? Amina ta Hura Hanci kafin tace"Ina Laifin kice yaya danmallan..? Ya Aisha tace"Ni yayana ne ke kuma Mijin ki ne..karyan iskanci kike yi bakin ki ya Bude yanzu ko..? Amina ta Yi fari da ido kafin ta bata rai Lokaci Daya tana Fadin"To ni yaushe rabon daya nemeni? Ko tawayar Hajiya yaushe da Rabon Daya Kira yace abani..! Tafada tana bata rai saboda Tsakani ga Allah tana jin takaicin hakan wato bai Damu da ita ba..? Ya Aisha ta rike baki Tana Fadin"Au Daman kina jiran sai ya nemeki ne..? tab kina da aiki kada ki manta wata matar garesa achan sannan anan ma yana da Sakina mu masu mu kadai muna Kula da Mazajenmu ballatana ke mai Kishiyoyi har biyu.? To ki rage wannan Sakarcin naki ko ba Haka ba Yakaka..? Yakaka ta gyara Zama Tana Fadin"Au to gayamata dai ai ni nan Tunda naji yarinyar nan da Zama da kishiyoyi har Biyu nace Zama bai ganni ba..Tana Haihuwa Gyaran yan maiduguri zan Mata wanda ba su biyu ko su Uku ne itace ta Hudu sai ta fita Zakka..Ai mu masu sunan mu ba Borori bane..Muna da Tasiri sannan wlh badai mutum ba Sai ta Allah.. Amina na Dariya Ita da ya Aisha wacce tace"To ai Kirarin ta kenan Yakaka Aminene badai ta Mutum ba sai ta Allah..! Yakaka tace"Ai Gaskiya ne..Ke kwantar da Hankalin ki yar nan har nan Zai zo yana mana yar murna sai mun Wahalar dashi ammh dai kafin nan tashi maza ki Dauko wayar ajonata in ta Cika sai ki kirasa ai mune akasansa ba komai in min nemesa muma watarana Zai nememu ko don Darajan wannan abun da ke Tare Dake in ya manta Dake don Kaniyarsa ai bazai manta da wannan aikin Daya kunsamiki ba..! Amina sai ta kasa mgana kunya ya kamata ya Aisha kuma ta Fice sum sum tana Dariya Dole Amina ta mike tabi bayanta suka shiga Dakin atare ta Dauko wayar nan Gefen katifa inda ta Watsar da ita Aisha ta karba ta Bude ta a kwali ta jona mata achaji Tana ta mata Fada fadi take"Wlh ijiye wannan Jidalin naki Zaki yi agefe wajen bautar aure ba wannan ake Bukata ba..ki iya Kissa da Kisisinan rike miji..Ni ban ma jin balarabiyar nan Sakinar ce mai ido a Tsakar ka..Kema ki Samu ki Zama mace awajensa..! Amina dai batace komai ba aranta Tace ai so ma suke ya Sakeni baki sani ba. Afili kuma batayi mgana ba Saboda abun ya fado mata arai duk da Tana kokarin Cire abun aranta ammh kuma har Abada bazai taba Fita ba.. Har ya Aisha ta gama fadanta ta fita batace komai gefen katifa ta koma ta Zauna tayi tagumi in ta Tuna kalaman mamanmu na kashe mata uwa sai taji ta tsaneta kamar tayi tsuntsuwa ta ganta agabanta ta Chaka mata wuka har sai  ta Daina Numfashi. Sannan ga kewar yaya aranta ga kuma Rashin samun wanda Zata Fadamawa baalle ta samu sauki ta kwanta akan jikinsa tayi kukan abunda ke ranta. Haka ta Dinga kuka ita kadai ta Share Hawayenta ta sulale nan saman katifar ta kwanta ta na maida Numfashi har barci ya kwasheta bata Sani ba sai Wajen Biyu na rana ta Farka shima Ya Aisha ce ta tada ita tayi sallah Sai da tayi wanka tayi salla Ta maida Doguwar rigar jikinta ta koma Dakin yakaka ta Haye gadon ta kwanta tana jin yakaka Dake zaune a saman Cafet tana goga goranta tana Korafin ta rage yawan barci mai Ciki da zirga Zirga aka santa tana jinta ta kara Dunkule kanta Cikin Filo aranta tana fadin Yakaka ba kisan irin barcin dana ke ji bane ita dai sama sama ta dinga jin yakaka dagachan kuma barci ya sake Daukanta la"sar nayi yakaka tatasheta tace ta tashi tayi salla ta Daina kuma barcin la"asar. Fadi take"Ke bake kadai ba..Ki rika barci har yamma tayi in kina son Lafiyanki da abunda ke Cikin ki sai kin kiyaye wasu abubuwan ku yaran yanzu komai Cikin gata kuke yi mu alokacin da in kina da Ciki ko barcin sai kin Ragesa har na Dare bama na yammah ba..! Amina dai batace komai ba ta Fada Tiolet ta Dauro alwala tazo tayi sallar tayi addu"a domin ta daina Sakaci da addu",an kamar baya da kuruciya yake Dauke mata hankali. Tana Idarwa ta Dauko Sauran wainar Fulawanta ta Sake ci tana ci tana jan yaji Yakaka na kallinta tana Girgiza kai fadi take"Ki Sautata ma kanki Cin yaji nan wajen haihuwa nake jiyemiki basir ya taso miki..! Amina tace"Au daman yana Tasowa ne..!? Yakaka tace"Zaki sani ne in kika shiga Dakim Haihuwa..! Amina Dariya kawai tayi sai ga Ya Aisha ta shigo tana Fadin"Amina wayar ta Cika na kunna miki..Rike ta Hannunki na Fadama ya Danmallam Zai kiraki yace..! Ta Fada tana mika mata wayar ta karba tana Tura baki ya Aisha ta Dunguremata kai Tana Fadin"Kinsan Allah ki fita Daga idonaa Amina na Rufe..! Zamu zo mu Tsara abubuwan da Zaki rika koya fanni girki da gayu dasauran abubuwa sannan har karatu Zamu rika yi,ga yakaka nan na san ban da matsala zata koya miki Dubarun Zaman duniya..! Yakaka tace"Ai ita Duniya basai an koya maka Dubarunta ba..Ita ke koya maka yin Hankali da ita..barni da ita ai muna Tare har Madina in tayi ba Daidai ba tasha rankwashi..! Amina tace"Tab wazai bisa madinan..? Ya Aisha tace"Yakaka kina jinta ko..!? Tace"Yi tafiyarki barni da yar nema..! Bata lambar mijin nata ta Kirasa da kanta..! Ya Aisha tace"Munyi mgana yanzu yace zai kirata..! Yakaka ta amsa da Toh fita Aisha tayi ta barta da yakaka sai Fada take mata ta shiga bata labarin irin yadda tayi gwagwamarya agidan kakan su Usman Cikin mata Biyu har sai mijinsu ya rasu ana ta Kishi da ita Amina dai tayi bakam tana jinta kafin tace"Yakaka in ka hadu da masu asiri fa suna zuwa gidan Boka..? Yakaka tace"To Sai me..,? Ai akwai su duniya ta lalace sai ka koma gefe ka rike Allah ka sa aranka Bawa bai isa yayi maka abunda Allah bai maka ba..yar nan rike gaskiya ki rike Allah ko min Dadewa gaskiyanki Zata bayyana sannan Allah baya barin Azzalumi da sannnu hakki zai bayyana .! Kai ta jinjina domin ta gamsu da mganar Yakaka suna Cikin hirar ne Taji karar wayar dake gefenta da Farko ta Firgita sai da Yakaka tace mata wayar tace sannan hankalinta ya kwanta Mikewa yakaka tayi da Go ranta ta fice tana Fadin"Mgana mai Dadi kuma ban da Tura masa wannan bakin..Ki ce sabuwar amaryansa tana gaishesa .! Ta fice ta bar Amina da waya a Hannunta sai da ta Katse sai kuma ya Sake kira tabi jerin lambobin da kallo bata Nigeria bane,Daukan wayar tayi Domin sak irin ta yaya ce tasan yanayinta tana Daga Kiran taji Sanyayyar Muryansa yana mata sallama sai taji kamar an kwara mata Ruwan sanyi ko"ina na jikinta yayi Sanyi har Bakinta ma yayi nauyi ta kasa amsa mai sai da ya maimaita sannan ta iya amsa murya shake Cikin Haibansa yace"Amina ya jikin ki..? Tura baki tayi kamar yana ganinta kafin tace"Ni ai lafiyata kalau..! Gemunsa ya sosa kujeran Office dinsa tana Dan juyawa dashi,yace"To ko ya nauyin jiki zan ce..? Amina sai taji kunya ta kasa mgana cikin wani yanayi yace"Nayi ta Kiranki ban samu ba tunda Hajiya tace min ta baki wayar..! Uhm kawai tace ya Cigaba da Fadin"Amina kinga lamarin Ubangiji ko..? Wannan rabon Dake Tsakanin mu shine silar Faruwar duk abunda ya Faru..! Amina tayi shuru batayi mgana ba shims shurun yayi kafin yace"Ba inda ke miki ciwo ko..? Amima sai taji wani Rauni ya shigeta kafin tace"Eh..! Cikin Rudewa yace"Eh kuma..? To ina ke miki ciwo..? Amina kai Tsaye tace"Menene mgani in an yi ma mutun sihiri sannan ta wata hanya Zai gane an yi masa..? Umar yaji mamakin mganarta Cikin mamakin yace"Amina waye akayi ma Sihiri..? Cikin wani yanayi Amina tace"Ni ce..! Baki ya Bude kamar tana ganinsa Cikin mamaki yace"Ke kuma..? Ta ce"Eh..! Sai kuma kawai ta Fashemai da kuka Har da Sheshsheka Saboda Dacin abun na taso mata lokaci Daya Rauninta na bayanna. Danmallan jikinsa yayi sanyi Cikin wani yanayi yake fadin"Kinga Amina..bar kuka nan yimin bayani yadda zan gane..! Ina ko jinsa batayi sai faman kuka take yi Dagacin kukan datake yi Daga karkashin Zuciyarta ne kansa ya Dafe Cikin wani yanayi duk da yasan yarinyar akwai kukan banza har da na siyarwa sai dai jin kalamanta da wannan kukan datake yi tabbatar wani ya faru wanda kedamunta acikinta kuma ta kasa fadamawa kowa..! Cikin sigar lallashi yake fadin"kiyi hakuri ki daina kuka sanar dani abunda ke faruwa..! Sai taji muryansa kamar wani waraka ne ga matsalanta yasa tace mai cikin kuka"ban taba Fada ma kowa ba sai kai..Wlh duk abunda Zan fada maka ba karya bane ya Dannallam..! Da Sauri yace"Eh naji bazan Fada ma kowa ba taimakeni kibar wannan kukan saboda yanayin Dakike Ciki..! Amina ta share Hawaye tana jan majina tace"Yaya..Yaya. ! Ta fada sai kuma ta kara sakamai kuka Umar ya shiga wani yanayin Tashin hankali da jin kukanta Cikin mamaki yace"Yaya. ? Amina tace"Eh yaya ba mutuwa tayi ba Kasheta MAMANMU tayi..! Ta fada tana matse bakinta kada kukanta ya kara fitowa yana Zaune ne sai da ya mike Cikin wani yanayi a Muryansa yace"Yaya ba mutuwa tayi ba kuma..? Mamanmu ta kasheta..? Amina ta amsa mai da Eh Cikin kuka Umar ya katseta Cikin Muryansa da kaifi yace"Ki bar wannan kukan yimin bayani sosai yadda Zan gane..! Amina sai kawai taji ta yarda Data Fadama Danmallam abunda taji ko zai Daina Damunta aranta ko Zata Samu Saukin abunda take ji.. Cikin kuka ta fara Fadamai komai Tun farkon wayar da taji Anty Amarya nayi a ranar da Hajiya tace zata tare da kuma Ranar da Ta kama mamanmu tana mgana da duka mganganunta,Sai dai ta Boye sunan Hajiya Uwa tunda bata san meye Tsakaninsu ba.. Amina ta sharbe hawaye tana Fadin"Da kunbina naji suna waya ya Danmallan..Da kunnina naji mamanmu na Fadin malaminta ta saka ya kashe mana uwa Saboda ta Samu Aba yadda take so Sannan da kunnena naji tana Fadamin Ba ni taso na ZAMA haka ba ya Jafar taso ya lalace da kunnina naji Tana Fadin Bazan haihu Dakai ba Sai Sakina sannan sukace har Abada sai dai aurena Dakai ya kare a gantali..Zuciyata tana min Zafi tun Ranar da naji haka..nayi kukan rashin Uwa Ya Danmallam bansan Dadinta ba Duka Mamanmu ta nesanta dashi ya Zanyi..? Abun na Damuna Zuciyata zafi take min kamar Zan mutu. ! Ta karishe fada Cikin kuka Danmallam Zufa kawai yake yi kansa na juyawa Mamaki da Dimuwa da al"ajabi sun kamasa ya kame awaje daya salati kawai yake maimaitawa acikin Ransa kafin ya samu yar natsuwa Cikin Wani irin Sauti yace"AMINA..!Kin tabbatar da mganar da kika Fadamin..? Amina ta kara fashewa da kuka Tana Fadin"Wlh in nayi maka karya Allah ya..! Da Sauri ya Katseta da Fadin"Amina ba kyau irin wannan rantsuwan ba kyau..! Sai yaji yama kasa mgana Saboda mamakin abunda yaji,Amina kuka ta Cigaba da yi kamar ranta zai Fita yana jinta ya kasa mgana sai chan yace"Kin Sanar da Hajiya ne..? Saboda yana tunanin kodai Hajiya ta sani ne Data Dauki wannan matakin sai Amina tace bata Fadama kowa ba...kansa ya Daure Tunaninsa ba Lokaci Daya bane yana Bukatar natsuwa Cikin lallashi yace"Ki daina kuka..Sannan ki cire damuwa aranki..Zan yi Bincike a barayina in dai mganar ki gaskiya ne akwai yuyuwar kowa yaji labarin nan,Alkawari Zaki min zaki Daina Tunani da Damuwa bakin gayamin ba .? Da yardan Allah komai zai zama Daidai kada ki damu..! Amina ta koma sheshshekan kuka tana Fadin"Haka mamanmu ZAta kashe mana uwa a banza kenan ya Danmallam..? Kai ya girgiza kafin yace"Ai hakkin Rai ma bazai barta ba Amina..In ma da Gaske ne Allah bazai barta ba sai ya Wulakantata aduniya..Sannan ai Allah ya nuna musu basu isa ba..Suna nasu ne Allah shi kuma yayi nashi..Amina Kina da juna Biyu wannan kadai ya isa kisan Allah ne Kadai mai yi alokacin da yaso a kuma Sanda yaso..! Amina taji jikinta yayi sanyi ammh bata bar kuka ba shi kuma ya tattaro Jarumtarsa yana ta bata baki da lallashinta Shima kenan datake da shekaru ya shiga wannan Halin balle ita mai karancin shekaru kamar Amina..? Dakyar ya samu Amina ta bar kuka shi Tunaninsa ma kada Damuwar ta Haifar da Matsala ga abunda ke Cikinta sai da ya tabbatar da ya lallasheta tare da alkawarin komai zai zama Daidai ya karishe da Fadin"Zan zo Gida watan gobe..In nazo sai mu Sake zama muyi mganar musan yadda zamu bullo ma lamarin ni dai ki daina Damuwa Sannan kada ki Fadamawa kowa..! Amina ta gyada kai kafin tace"Zaka zo nan ne..? Wajena..? Yace"Eh zan zo na ganki naga yadda Kika koma in kuma ga yadda Cikina ya zauna ajikinki ! Sai kunya ta kama Amina ta kasa mgana shi ma bai wani Damu ba,baya Cikin natsuwarsa Daganan ya mata sallama ya katse kiran. Zagayen office dinsa ya farayi kansa ya Dafe ya shiga Tunanin mganganun Amina bai san mamanmu a boye ba sai dan Zahirinta Daya sani kadan ana Fadin Kirkinta,ko abakin yaya yasha jin haka Sannan shi bai da wani Sakewa da ita iyakarsa su gaisa sannan ita kanta Anty Amarya gaisuwa ce Tsakaninsu har gwara itama sukan yi Doguwar mgana Sanadin Sakina Sai dai kuma ya fara jiyo kamshin gaskiya kan mganar Amina Duba da Yaya ance Lafiyalau ta kwanta sai gawa duk da ita Mutuwa ko da Ciwo ko ba Ciwo sai an tafi..! Ammh Amina yarinya ce ba yadda Zata Zauna ta Tsara mgana haka in ba ji tayi ba Sannan ya tuna yadda Sakina tada hankalinta kan Auran sa da Amina da kuma Matsalan data Faru tsakaninsa da Sarood Aliyu ya fara Hangomai Lamarin a matsayin Shihiri ammh bai yarda ba sai da Mallam ya sanar dashi Cikin Hikima har ga Allah bai zargi Sakina ba ammh kuma yanzu Dayaji wannan mganar sai ya shiga kokonta ya tuna Bakin kishi Sakina da Burinta ita ta Samu Ciki ta Haihu har wani Lokacin ya Dinga mata Fadan ta roki mafi alheri.. Bawai ya yarda da mganar Amina Duka bane sai dai kuma ya shiga Rudi da kokwanto agidansu ake wannan Tsantsan jahilcin da mugunta har da kashe rai..! Indai ko gaskiya ne Anty Amarya da mamanmu Allah bazai barsu ba sannan sai ya nuna musu basu isa su raba auran da Allah ya kulla da kansa ba. Cikin tashin Hankali ya kira jafar a waya yana Tambayansa Amina na karya?.. tunda sun fisa sanin yarintar ta shi ba mazauni banw baisan komai kan Rayuwarsu ba. Ya jafar ya fara fada yana Fadin"Hala iskancinta ta maka..? Ai Amina sai Allah..Wlh ya Danmallan ka daina Sake mata ne. ! Cikin haushinsa yace"Tambayata zaka bani amsa ko zaka Tsaya kana gayamin abunda zan yi da matata ne..? Saj jafar ya rike baki yana yar Dariya kafin yace"Amina bata da Halin karya..Bata da kumbiya kumbiya ita Free take abunta bata da Tsoro sannan tana da kafiya da Taurin kai yadda kasan zuciyan kafuran farko bantaba ganin wanda duka baya Sata tayi Laushi ba sai Amina..Ko zaka kasheta sai tayi mgana sannan abunda yake gaskiya take fada Bansanta da karya ba gaskiya..Sai dai Rashin kunya da tsiwa da Tonen fada da Yawon tsiya..! Danmallam ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya Datse kiransa ya jafar afili yace"Ko son Amina ya Danmallam ya fara ne..? Dariya yayi kafin yace"Tab..bai Fada hannu na gari ba..Amina ai jidali ce..! Danmallam kuwa suna gama mgana ya saki Huci Amina tana da gaskiya wani abu na Faruwa sannan ya Fara ZArgin Hajiya tasan wani abu shiyasa ta hana Amina ta zauna a gumel sannan kuma ta hana kowa yasan da Cikin jikinta tabbas ya hasaso wani abu.. Sai dai koma menene ya kamata yaje Negaria yaga Amina su yi mgana sosai sannan yaga ta ina zai Bullo ma al"amarin da ke faruwa agidansu karkashin Tarbiyan mallam..? Lalle ana Zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka..Zuciyarsa ne taji ta Bude da duka mganar Amina da Tsausayinta da bai taba jiba ba..Dole ya tafi gida cikin watanan mai Shiga abubuwa Dadama suna Bukatar yaje ya gabatar dasu tukunnah..! *Janafty**TFZB2018* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Tun daga ranar Danmallam bai taba kwana batare daya Kira Amina ya lallasheta ba ganin da gaske fa abun na cinta aranta Fatansa Allah yasa kada Damuwar ta haifarma da abunda ke cikin wata matsala sannan bayaso ta fadama kowa abunda ta Fadamai mganar tana Bukatar Bincike da Lura sannan ba kowa bane zai iya Daukan mgar har ya Fahimceta sannan yayi tunanin mafita Shiyasa yake kokarin kiran Aminar yana amfani da Hikimarsa wajen kara Lallashinta da bata Baki. Wani Lokacin yafi Kiranta in yaje Wajen aiki ko in ya bar gida Zashi masallacin Madina ammh in yana Gida baya Kiranta Daga ita har Sakinar saboda Gudun matsala Ga Sarood kamar ta goyasa haka take ji Dashi bazai so yayi abunda zai ci mata Fuska ba shiyasa yake kiyaye wasu abubuwan sannan nauyi ne akansa ya kwatanta adalci Tsakanin mtansa. Abunda Amina ta Fadamai na nan aransa kamar ya Tuntubi Hajiya da mganar sai kuma ya fasa yana Tunanin ta ina Zai fara duk da fa yana da Zargin Hajiya tasan wani abu Shiyasa ta Boye Amina da Cikin Dake jikinta,Mallam ma kamar Zai mai mgana sai kuma yaga ai bai da wata Sheda itama Aminar ji tayi bata Nadi murya ba Tunkarar wani da wannan mganar ma a yanzu bai taso ba,Sannan abu ne na Kashe rai duk da daman kowa yasan Mutuwa ta Allah ce sai dai mutum ya Zama Sanadinta. Bangaran Sakina kuma ai ya Dade da Fahimtar mganar Amina Hakane kodaga yadda bata taba mai mganar Amina ba Ranar Dayake so  ji ta  Bakinta suna waya sai Rigima take mai kan yaushe zai zo ya Dauketa..? Ita ta gaji da Zama agarin nan baya nan sannan ta yi bari tana son maida Cikinta,Mirmishi kawai yayi kenan mganar Amina ta fito su Burinsu kawai Sakina ta Samu Ciki ta Haihu..? Saboda ya jarabata yasa yace mata Bata taba Tambaynsa ina Amina ba..? Sai Sakina tayi Tsaki kafin tace"To ni ina Ruwana..Tunda ta bar min gidan mijina ban damu ba..Ba"an ce hajiya takai ta wani waje ba..? Yana jinta ammh Daganan bai kara mata mganar Amina ba Itama Sakinan bata Damu ba,ita kamar ma Dadi Take ji tunda ta bar mata gidanta ai taje koma ina ne bata Damu ba Allah ya raka taki gona..! Allah duk ya shafe musu Tunanin Mezai sa rana Tsaka a Dauke Amina Daga Gumel..? Duk basu yi wannan Tunanin ba Idonsu ya Rufe da nasu Cikar Burin dukkansu. ****** Usman mijin Aisha ya Dawo washegari suka kai Amina asibiti shi da Aisha speacialist  Hop suka kaita Inda Aisha ke zuwa in Bukatar Hakan tataso,anyi mata Scan cikin Amina Har ya shiga wata na Biyar sannan jininta yana sama kadan Saboda Tana saka Damuwa sannan kuma Sugar masu Ciki na son kamata ammh ita da Abunda ke Cikinta suna Cikin koshin Lafiyan an bata mganin karin jini su Vitamin c da sauransu sai kuma  na cin abinci tunda Aisha Tayi Korafin batacin abinci Likitan yace Normal ne indai tana cin abunda Cikin yake so ba wata Damuwa...! Ya sanar dasu zata fara zuwa awo Duk bayan Sati Hudu sannan in yayi  shiga wata shidda za"a sake mata wani Scan din Basu Dade a asibitin ba suka Dawo Gida suka ijiye Amina suka kara Fita kasuwa suka shiga Aisha ta Zabo ma Amina Dogayen Riguna guda Biyar da Wanduna plazo sai ruguna masu yalwar wadanda zasu mata Saboda ta kara kiba kaya wanda tazo dasu sun mata kadan sannan nata bazasu wadaceta ba. Data kawo ma Amina taji Dadi sosai kamar ta goya ya Aisha tana Daga rigunan adakin Yakaka take fadin"Yakaka kalli Rigar nan bata miki kyau ba .? Tana zaune saman Cafet tana Gogan goranta tace"Sosai ma ai sai ma kin sakata Ajikin ki takwarata ai mu duk kayan da muka saka sai ya karbemu..! Ya Aisha na Dariya ta Fice tana Fadin"Ki fito kiyi ma Darling godiya yana Falo..! Amina in Aisha ta Kira mijinta Da Darling mamaki take bata,agida shuru shuru kamar bazata aikata ba kamar ma batasan komai ba. Kwashe kayan tayi ta maida a leda ta Saka Hijabinta ta fita falo ta Durkusa tama Usman godiya ya amsa mata yana Fadin"Bakomai Matar yayanmu..Kin dai ji abunda Likita yace ko..? Ta gyada mai kai kanta na kasa tana jin kunya ya cigaba da Fadin"To sai ki yaye in kina Bukatar wani abu ga Sweety nan ga kuma Yakaka Dukkansu They are Their for u..! Kanta na kasa ta amsamai Lokaci Daya damai godiya kafin tatashi ta koma Dakin yakaka tana Santin kayanta ta gwada wannan ta gwada wannan tana nuna ma yakaka ita kuma tana yabonta Amina ta gwada wata Riga Mai yalwa ta juya ta Sake juyawa kafin tace"Sai yanzu najini Daidai...Ammh wacce ya Aisha ta bani jan nan tamin kadan fa yakaka..! Yakaka tace"To Daman ai irin wannan ne Daidai dake..Daga gani ba wani Girman Ciki Zaki yi duk a kiba Zai tsaya .! Amina ta bata rai kafin tace"Wai sai nama kara Kiba yanxu..? Yakaka na cin soyayyan gyadan da su Aisha suka siyomata a kasuwa tace"Af ai sai kin ninka kibanki na yanzu.. Ai sai Amina ta Zauna akasa ta Fashe da kuka Yakaka ta saki baki tana kallonta Kafin ta tabe baki tana Fadin"Yarinyar nan kin samu waje..Ki bari Balaraban Madina yazo sai ki mai wannan shagwabar..! Amina Ta tura baki Batayi mgana ba Yakaka tayi Dariya kafin tace"Tsoro kike ji kada su kwace shi..? Amina tace"Tab..Allah ya Tsareni ni bana tsoron su har ita gajeran ma..! Yakaka tayi Dariya kafin tace"yauwa haka nake son naji Tsoro ai ba namu bane..kada ki Damu kina Haihuwa Zaki Dawo silandiyan dinki..! Amina ta washe baki Tana Fadin"Da Gaske kike yakaka..? Yakaka tace"sosai ma ai mu ko da kiban mu muka je mune agaba bazamu taba komawa baya ba. ! Amina ta amsa da wlh kuwa Daganan ta warware suka Cigaba hirarsu Daman kukan Aminar na Tabara ne da jidalinta. Hajiya suna waya da Amina ta wayar Amina Tunda Aisha ta Tura mata lambar Aminar koda yaushe sukayi mgana sai Amina tace ina su hanne abasu su gaisa sai Hajiya tace ba yanzu ba ko Aba bata yarda ta Kira ba sai Mallam kawai ta Turo mata Lambarsa ta Kirasa suka gaaisa ya Dinga mata nasiha da Saka albarka yaji Dadin jin tana Lafiya kalau.. Amina tana jin kewar su Hanne sosai Kamar yadda suma suke kewarta Tunda suka ga sun fara Jarabawar Fita Amina bata Dawo ba suka Sare Hanne tace da sun san ba tare da Amina zasu zana Jarabawar Fita da Mallam ya bar su sun gama SS3 Kamar kowa sai dai ina bakin alkalami ai ya Riga ya bushe. Duk damuwarsu basu kai Sa"adatu ba wanda hakan da mallam yayi yanuna cewa bazasu Dade agida ba suma zai aurar dasu Shine tashin hankalinta su kuma su Hanne Amina ce Damuwarsu Saboda rayuwar ba Dadi ba ta abaya ashe ba Rashi sukayi ba Tunda Amina na kusa dasu yanzu kuma da basu da tabbas din ina take sai Damuwar tafi ta baya,Sun gaji da Tambayar Hajiya sun kare har Mallam sun tambaya yace su tambayi Hajiya Hamida data tambayi Aba shima yace Hajiya bata Fadamai ba. Ganin Hamida ta Damu ne yasa Mamanmu ta Kikkira su Jaleela ta tambayesu ko wajen su Hajiya ta kawo Amina ammh har Jordan ta Kira amsar Daya ne A"a sai ta fara Dawowa Hankalinta ta fara Tunanin ina Hajiya takai Amina..? Har su Zulaihat ta Kira suma suka ce mata bata wajensu kuma kowacce ta Kira sai ta nemi karin bayanin ina Aminar ba"a ganta bane..? Sai Mamanmu tace wayasani Hajiya dai tace Zata kaita Gidanjenku gashi Wajen Wata Daya da wani abu ba Labari sannan Hajiyar taki Fadan inda take in sukaji basa Damuwa cewa suke ai Hajiya bazata kai Amina inda Za"a Cutar da ita kada ma mamanmu ta Damu Hajiya Zata Dawo da Amina kamar yadda ta tafi da ita. Mamanmu ta fara Tunanin kodai da wani abu ne..? Sai kuma ta Tuna ance Dubaran Zaman aure za"a koyamata tuna haka yasa ta watsar da mganar Amina aranta tana ma Hajiya Dariya Tana Wahalar da kanta ne saboda auran Amina da Danmallan ai haka zai kare agantale. Da sukayi waya da Anty Amarya ma sai da ta mata batun Anty Amarya ta Saki Tsaki Tana Fadin"Nace miki ki daina mana wannan mganar mun gama da wannan shafin..Ba inda Zata kaita Daya wuce maiduguri garinsu tana da inda yafi chan ne..? Mamanmu tayi Dariya kafin tace"Ai Tunanina bai kawo nan ba..To Allah ya raka Taki gona ya mganar Sakinan..? Madina ina son kema naga Burinki ya Cika kamar yadda nawa Burin ya Cika .! Anty Amarya tace"kada ki Damu Saura kadan..Cikin watan nan Danmallan zai zo ya tafi da Sakina kinga in ya tafi da ita shikenan sai naji da Hajiya uwani kuma..! Mamanmu tace"Ai Hajiya Uwani matsiyaciyace..! Anty Amarya tace"Babba ma kuwa sai kin ga yadda take shigema Hajiya..Kamar ta Allah..! Abunda basu sani ba ai Daman in Dubunka Zata cika rasa Dubara kake yi Hajiya gefe ta koma tayi bakam tana karban kowa yadda yazo mata Sannan tana Daina yarda da kowa ta gama Sarewa da lamarin duniya sannan Haj.uwani bata san wani abu ba ita adole tana shigema hajiya tasan wasu sirrukan ai ta Dade da Cin Taliyar karshe tunda Hajiya ta ganota ta DAina bata labarin abunda ya Shafeta da ya"yanta.. Har Falonta tazo tana bin bakin jin ina Amina take taki Fadamata Saboda Sai Daga baya tasan ma Aminar bata bata nan shima abakin Haj Nasara taji Data Tambayi mallam yace hakane ita mamakinta Daya meyasa Hajiya ta Kauda Amina Daga gabanta..? Ko madinar Aka Turata sai dai tana Tunanin ba Haka bane Tunda taji ana mganar Dawowar Danmallan din Cikin wannan watan.. Sai Hajiya ta bangarar da Tunanin Haj.Uwani da cewa Amina ba Nisa tayi ba Jarabawa take yi a inda take in ta gama Zata Dawo to ganin suma su Hanne sun fara sai ta yarda da mganar Hajiya aranta tace ita wannan auran ai su Amarya da Balaraba sun gama gantallar dashi. Dayake itama ba Aminar ne agabanta ba Sai ta Watsar da mganar ta Ita yanzu babu abunda ke gabanta sai Shirye shiryen dawowar Nazeem gabadaya Cikin Sati mai Shiga yace mata Zai dawo gabadaya in ya Dawo kuma aikin da zata karisa ai kadan ne har ta Fara hango kanta ta Cika Burinta mganar Anty Amarya kuma bata gabanta tasan ko giyan wake tasha bazata fasa mganar nan har wani yaji ba..Kuma tasan Mama ta sha gaban Bokansu har Mganin Data Karbo ma Sakina sai da mama ta labartamata Dariya kawai tayi in su suna zaune ita ai ta Dade da kwana atsaye kan Cikar Burinta ko kofa bata taba badawa ba ballatana a samu matsala..! Ashe ashe bata sani ba shi Allah ba"a masa Dubara sannan a lokacin Daka ke Tunanin ka Rufe kofar gefenka ta kofar da bakayi Tunani ba sai Allah ya Wangale taa asirinka ya gama Tonuwa a idon Jama"a. ******* Kamar yadda Aisha tayi ma Hajiya alkwarin ta kuma ta gayama Amina bata  sauya Shawara ba Haka take tasa keyar Amina Kitchen in suna Girki da Saude ta rika gani tana koya mata Saukakkun girke girke,Tun Amina na Tura baki tana kunkunin tana barcinta ya Aisha na takura mata har tazo ta saki ta Fara maida hankali To Saboda ko ta koma Daki Yakaka ke Fatattako ta dole ta Dage tana maida Hankali ballema ya Aisha data koyi Fada tunda tayi aure. Haka Zata Zaunar da Amina tana koyamata yar shagwaban nan da yadda zata rika ma ya Danmallam mgana da karaiyaya Amina sai ta Dinga Dariya aranta tana Fadin a ina ya Aisha ta san wasu abubuwan agidan kamar in ka samata Hannu abaki bazata Cija ba Kamar ya Aishan tasan abunda take Tunani ta Dunkure mata kai tana fadin"Ban son iskanci ana koya miki yadda zaki zama Tauraruwa wajen ya Danmallan kina Iskanci ko..? Nasan kina mamakin ina duk nasan wadanan abubuwan ko..? To ai gidan aure makaranta ne Amina sannan tunda ya siyamin babbar waya nake dan shige shige ina koyan wasu abubuwa sannan Addini ma ai ya koyamana yadda zamu yi mu"amala da kowa har da gidan auranmu..! Amina ta jinjina kai Domin tana ganin  yadda ya Aisha ke yi in ya Usman yana gari kwalliya da salon mgana da kwarkwasa duk tana gani kuma tana Dauka Domin a Zahirin gaskiya itama tana so ta zama mace sannan tunda ga inda kaddara ta kaita ai sai ta Dage Uwa uba kuma taci Uban Sakina ta nuna mata nasu ba irin nata bane Sannan bazatace ta fara son ya Danmallam ba ammh sun fara Shakuwa da juna tunda koyaushe suna Tare a waya kullum Cikin Tambayar baki da wani Damuwa ko.? Yau da gobe bata bar komai ba sannan ita ai Zuciya tana son mai kyautata mata Amina tana da Budaddiyar zuciya ne shiyasa nan da nan mutum ke Shiga ranta abunda bata sani ba shi ya Danmallam ai jinin jikinta ne shi da take Dauke da Kwansa acikin jikinta,Sannan kuma ba kamar Soyayyarsu da Aminu bane,da ba Sakewa Cikin Tsoro da Fargaba tayi ta wannan kuwa a sake take sannan in suna waya sai tarika jin wannan fa ai mijinta ne wani abu ke shiga ranta batare data sani ba. Sannan abunda ya Faru Tsakaninsu ya Haifar da wani bond mai karfi wanda Bawa bai isa ya hasaso farkonsa ba ballatana karshensa ba abu Daya ta saani tana jinsa aranta sannan tana Kishi da Sakina daman chan tana jin haushinta balle yanzu da suka Hada miji ko sunanta taji sai ranta ya baci bata ma Damu da balarabiyar nan yadda ta Damu da Sakina ba. Ko kwana Daya yayi bai kirata ba ta Dinga fushi kenan tana Tura baki in ya Kira taki Dauka Sai Yakaka ta mata Fada da cewa"Tsiya na Dake Sarkaci Takwara..Haka ake karban miji a Hannun kishiya..? Amina na hura Hanci tace"To bashi bane Jiya fa bai kirani ba..! Yakaka ta aika mata da Dakuwa tana Fadin"Kin ga naki nan..? Don bai Kiraki ba sai me..? Ai kinsan yana da uzuri ko..? Kada ki Dauka sai ki barma ita balarabiyar ki koma baya ke ko yan Dubaran nan na yaran Zamani da suka iya su Tadama Mazajensu hankalinsu in suna nesa saboda su zo wajensu da wuri baki iya ba,Sai Sakarci da Kunkuni kadai kika iya..! In yakaka ta fara fadanta bar mata Dakin Amina ke yi abunta ranar kuwa sai taja mai aji Zata Daga kiransa in kuma ta Dauka yana mgana ta basar dashi yasan Laifinsa sai yayi mirmishi yace"Amina kiyi hakuri..! Sai ya fara fadamata Uzirinsa sannan Zata Hakuri koda yaushe Cikin Tambayanta lafiyanta yake yi tana Bashi amsa ba wata matsala bawani Hira suke ba na ma"aurata ba sai dai suna Hirar abunda ya shafi mganar da Amina ta Fadamai koda yaushe sai tace mai yaushe zai taho Ranar dai yace mata"Cikin karshen watanan..Sannan yana so yazo da Sarood su yi Sati Biyu sai su koma Tare da Sakina..! Ai Har suka gama wayar Amina bata kara Dariya ba wani Tukikin Takaici take ji wato zai zo da wannan balarabiyar sannan ya koma da Sakina ita ko Oho..? Sai kuka da Ya Aisha tazo ta ganta Tana kuka Har Hankalinta ya tashi ta Zata ko jikin ta ne take jin wani abu..? Sai Amina na kukan ba Hawaye tsabar Takaici tace"ba ba..ya Danmallan bane yace wai zai zo da balarabiyar matarsa ba..Sannan in sun tashi tafiya su koma da wannan gajerar matar tasa..! Galala Aisha ta Saki baki tana kallon mgana kafin ta Tsintsire da Dariya Amina ganin haka yasa ta kara bare Baki ya Aisha ta buge bakin tana Fadin"Kefa ko ya'ya Dubu Zaki haifa na tabbata wannan iskancin naki bazai barki ba..Miye na bare min baki kmar na yankaki Salon yakaka Dake Daki Taji tace nayi miki wani abu..! Amina ta hura Hanci kafin tace"To bake bace ina gayamiki mgana kina min Dariya ba .! Ya Aisha ta matso ta kama Hannunta tana Fadin"to na bari kanwata gayamin yaki keso ayi..? Amina tace"To ni kada ya tafi da Sakinar nan gaskiya..ni fa kadai zai bari anan kuma sai ya Dade kafin ya Dawo. ! Ya Aisha tace"Yanzu waya isa ya hansa tafiya da matarsa Amina..? Ai bamu isa ba matarsace kuma kinga Daman achan take sannan duk keki keda matsala ina nan ina Koya miki irin  kissar da zai saka Miji yazo gareka bai sani ba kin ki Dauka nace miki watarana ki sakamai kuka kice cikin ana Miki motsi ke zaki mutu ki Tadamai hankali yayi lallashi ki kinyi Shuru Da gudu zai taho ma Lokacin Tafiyarsa bai yi ba ammh sai ki kalleni kina Dariya..,! Amina tace"To ai kunya nake ji..Kuma kuma..! Ya Aisha tace"Kuma me..? Amina tace"to ai naga shi babba ne. ! Dariya ya Aisha tayi kafin tace"to ai ke kin ji Dadi ma baki san sirrin auran irin su ya Danmallan ba..? Gaki da kuruciyarki Amina da Shagwaba da Yarintarki zaki sacemai Zuciya shi kuma ya lalace akanki Wlh irin ku an fi sonku kiyi ta Jidalinki yana lallabaki shiyasa na Fada miki shima wannan Jidalin naki aikwai Inda ZAI miki amfani balle nasan shima ya Danmallam din ai yana son soyayya..! Amina tayi Dariya "To kuwa matarsa bata iya ba..bandai sani ba ko wannan Sarood din..! Ya Aisha tace"Ke ya akayi kikasan bata iya ba..? Amina tace'Tab ai na Zauna da su..! Aisha tace"ai bata iya komai ba sai Fadin rai ita kuma wannan Sarood din naga kamar ta Biye mata sun maida ta wata wawiya ma..! Amina tace"ai kamar ma wawiyar ce..! Dunkure mata kai ya Aisha tayi tana Dariya tana Fadin"Tunda ke kin iya sai ki Dage ki rikitamana yayanmu.! Amina taji kunya ta kasa mgana. Tundaga ranar ta Bude kunne tana kwasan Abubuwa awajen ya Aisha Da gaske take yi duk sai ta nuna ma su Sakina basu iya komai ba Aminene ai Ta musu Zarra. Bangaran karatu kam sai da ya Aisha tasha mamakin Amina ba inda baza"a bude mata a Qur"ani ta karanta ba Hadisi kuwa tunda ga na farko har na bakwai suna kanta sannan ta haddace Arba"una Hadith sira ma haka Tajwid wasu Littafan Ya Aisha mamakin Amina ya isheta sai da ta Furta mata tace"Yanzu daman Amina kin iya wannan duk abubuwan kike iskanci a makarantar islamiya da Haddda..? Amina Dariya kawai tayi tana Fadin"ai ya Aisha ba kowani Hali muke sani na mutanen da muke Tare dasu ba..Muna sanin wanda suka bayyana mana ne..! Ya Aisha ta jinjina kai tace ba Shakka ko bangaran Boko sai da ta Kusa raina kanta sun yi kunsan mintinaa Talatin suna hira da Usman Cikin Harshen Turanci Amina bata kage ba sannan ba Turancin yan koyo ba Turancin ya Zauna abakinta sosai har Usman sai da yayi mamaki yace mata"Amina fa tana da kwakwalwa..In ta samu cigaba da makaranta sosai zata Zama wani abu watarana. ! Ya Aisha ta jinjina kai tana Fadin"Agida ko sai kace bata gane komai..Bama Damuwa tayi da karatun bafa..! Dariya yayi yace"ai irin su sun fi raina ma mutane hankali da basa ganewa nan kuwa sun fi kowa Dauke komai Lokaci Daya..Muma lokacin muna Secodary sch muna da wani Dan ajin mu haka mai suna yahaya kamar wawa fa ana karatu yana wasa wlh a Exam shine Overoll..! Ya Aisha tace"irin Aminace..A aji Dakikiya a Result sai kaga ta Doke kowa ko su hanne Dake maida hankali Tana gabansu..! Usman yace"Da yawam irin masu baiwar nan basa samun masu Courage dinsu ne in ana kushe su ana cewa basa yi sai su boye baiwarsu sun fi bayyanasa wajen wanda ya yarda suna da ita kanta baiwar..! Ya Aisha ta jinjina kai domin tagamsu da hakan yanzu sannan baba mallam koda yaushe Cikin Fada yake Uwata yar baiwace nan gaba sai mun baku mamaki aiko gashi ta bata yau wlh Bata Taba jin Amina tayi Turanci ba Duk azatonta batajin komai sai Tsinta tsinta. Daman haka Lamarin Allah yake Tsammanin Abunda baka Tsammani ba..! ******* Bayan kwana Shida..! Nazeem ya Diro gumel Ranar wata Laraba da yammah tun Safe Haj.Uwani ta kasa zama ayi chan ayi nan tasa su Baba lami sun shiryamai kayattacen abincin daya fi so Priderice da soyayyan kaza an yi pepe dinta da kunin aya,Tasa su Akilu sun Share masa Dakinsa an gyara an goge an Baza Turaran wuta Duk ta kasa Zaune sai da ya Shigo gidan Abunda yafara bata mata rai duk yadda Taci Burin Dawowarsa sai da ya Fara Shiga Shashen Hajiya suka gaisa ya Dade ma suna Hira sannan ya kariso wajenta ammh Dayake yar Duniya ce sai bata nuna mai ba ta karbesa Cikin maraba da lalenta kamar ko yaushe. Ya Duka yana gaisheta ta amsa Cikin Sakewa tana Fadin"An gama karatu gabadaya Nazeem an dawo gida..? Daman ance kowa ya bar gida..Gida ya barsa..! Yana Dariya kansa a kasa yace"Hakane Mommy..Mun dawo sai Fatan mu samu aiki atayamu da addu"a..! Tana Dariya cin nasara tace"ai kama samu aiki ka gama Nazeem..kai fai tashi ka karisa Dakinka kayi wanka ga abincinka nan tafe. ! Ya mike yana mata godiya har ya fara Tafiya tana Binsa da kallon alfahari ganin ya kara girma sam bai yi kama da ita ba yafi kama da Mallam ne kuma suna bala"in kama da Danmallan. Juyowa yayi yana Fadin"Mommy ina Umai..? Ya jikinta..?haj.uwani tace"Taji Sauki har ta koma ma islamiya da Hadda. Kai ya jinjina ya fice yana fadin Allah ya bata lafiya.. Yana fita itama ta fita Kitchen din Tsakar gida tace su kaimai abincinsa da komai da komai tana Tsaye sai da Taga an Dauka an kai ta koma Shashenta ta Kira Batula ta Fadamata Dawowar Nazeem. Batula tace"Dakyau..To gobe zan yi Sammakon zuwa Minna in samu mama na mata bayani yadda ake Ciki Zaki ji..! Haj Uwani tace"Nagode batula..Kada kiyi sanya..Kinsan wani Lokacin jinkiri ma yana batamana aiki. ! Da sauri Batula tace"Haba a baya ma ban yi sanya ba..Ballatana da yanzu da muke gabda Cikar Burinmu..? Kedai sai kin jini.. Daga haka suka sauke wayar Haj.Uwani Bakinta har kunne sauran matan ma su Anty Amarya sai Da Daddare suka san Nazeem ya Dawo da suka gansa Falon Mallan har suka gaisa Mallam yaji Dadin Dawowarsa Saboda Nazeem akwai natsuwa ga Hnkali yana ta mai fatan alheri da fatan samun aiki mai kyau. Ranar Hajiya Uwani bata Samu kebewa da Danta ba washegari ma Tare da yan"uwansa Nasir da Jafar suka shigo mata ranta ya sosu sai bata nuna ba ta barsa sai da ya kwana Biyu da ya shigo gaisheta da Safe tana Dakinta taji suna gaisawa da Umaima da Jikin nata yayi sauki yanzu har tana Fitowa falo ta Zauna. Daman jiransa take yi yana shigowa bayan sun gaisa ta sako mai mganar Dake ranta Cikin Dakiyarta tace"Tunda ka Dawo gida..sai ka fara bin Baban ku sa"idu gidan gona kana Duba wasu abubuwan tunda kaima Harkan kasuwancin nan ka karanta..Wani abun gwara ku masu Dukiyar kuna kusa zaku fi ku kula dasahi Dakyau akan bare..! Ya Dade yana mamakin kalamanta kafin yace"Mommy ai baba Sa"idu kuwa ba bare bane kema kinsani..Kada ma ki Fada baba yajiki bazaki ji Dadi ba sannan shekaru aruru yana kula da kasuwancin Baba ko Da rana Daya bamu taba jin kansu ba..Sannan infact ma ni bana Sha"awar aiki a karkashin Mahaifina gwara na samu aiki na tara gumina..Na ma yi interview da wani kamfanin Sarrafa fata dake Lagos sun ce xasu neme ni Albashi 100k sukace zasu rika Biyana Duk wata..! Kafin ya gama mgana ya sha Harara nan ta Rufesa da Fada tana Fadin"Inda Uzairu ya fika kenan shi Burinsa ya gama karatu yazo ya taimaka ma mahaifinku kai kuma Shashaha kana wani mganar kamfani Dubu Darin banza..? Kasan iya adadin Dukiyar mallam ne..? To ahir dinka..ba inda zaka yi aiki sai karkashin mallam kuna chan sake da Baki wasu dagachan nesa suna amfana da abunda yake watarana mallakin ku ne. Gargadi na shine in mallam yamaka mgana ka amsa mai wlh ka kunyatani sai na sabamaka..! Har ya fice yana mamakin me yasamu mommy ne take irin wannan mganganu ? Washegari Batula ta kirata tace Mama tace yau da Daddare ta tunkari mallam da mganar bazai mata gaddama ba. Cikin jin Dadi da Nasarar ta Ta tunkari mallam adaran Daman ita keda Turaka yana cin abinci ta lamkwashe kafa agabansa tana Fadin"Mallan nace tunda Nazeem ya gama karatun nan ya Dawo gida kafin aiki ya samu kasan kasar tamu yadda takkoma sai Kana da wani asama..Sai naga Tunda shima bangaran Kasuwanci ya karanta mai zai hana ya fara Bin Sa"idu gidan gona yana ganin waau abubuwan yana taimakai ko wajen Rubuce rubuce ne tunda naga Jafar ke taimakamai shima kuma kaga ga aikinsa..! Har ta Sare da ba nasara taji mallam yace"Hakane..Zan m Sa"aidun mgana sai ya fara Binsa yana da kyau hakan Zai taimakamai..! Haj.Uwani taji kamar ta goya Mallam Dole ta karama Mama kudi haka ta shiga yi ma mallam godiya sai da ya ji mamakinta. Abunda bata sani ba wani abun yana Tarda Sa"a ne mallam yayi la"akari da nazeem ya Dawo gida Zaman banza zai yi kafin ya samu aiki daman kuma yana da wannan Tunanin shiyasa bai mata gaddama ba. Da Safe da Aba yazo su gaisa ya Sanar dashi yaji Dadi Sosai,suna ma Cikin Tattaunar ne sai ga Nazeem ya shigo gaida mallam nan ya sanar dashi bai iya cewa komai bs tunda Haj.Uwani tace in yayi gaddama sai ta sabamai. Shi dai zai bi umarninta dana mallam ne ammh yana samun aiki bazai Zauna ba. Aranar suka fara tafiya gidan gona shi kanshi a wuni Daya kawai da yayi aikin Lissafi kadai ya yi sai da ya Jinjina Dukiyar baba mallam Aba na Fadamai a duk sati ana Fita da kwai Fin na miliyan Daya sai da ya Rike baki ya dai san gidan gonar babbane ammuh bai Taba maidakai akai ba. Da Daddare suka Dawo Haj.Uwani daya Shigo Falonta Tana jansa da Hira anan nema ya gayamata tana jin Uban kudi ta zare ido tana Fadin"kaji ko..? To ban da na gonakinsa kila in kaji abunda yake samu a shekara sai kanka ya Kasa Dauka..! Sai jin Dadi take yi tana Mirmishi shi dai wannan baya gabansa dukiyar Mallam bazata Burgesa ba Tunda ba nasa bace. Kwana Hudu da Fara zuwan Nazeem gidan gona da Sakar masa ragamar Wasu abubuwan da Aba yayi Mamammu taji labari shima suna Tare ne taji yana waya da Nazeem da ya gama ta tambayeshi yake fadamata Tare suke kasuwancim mallam yanzu yana taimakamai sosai da Umarnin mallam din. Mamanmu jiki na rawa ta koma Daki ta kwalama Anty Amarya Kira ta Sanar da ita abunda Aba ya Fadamata. Anty Amarya ta lailayo ashar ta maka kafin tace"Ammh Uwani dai an yi bakar Tsinanniya..Allah dai ya Tsine mata albarka.. Mamanmu ta amsa da Ameen madina da gaske take yi fa..! Anty Amarya tace"Ai na rigata..Nasha gabanta wlh..! *Janafty**TFZB2019* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Mamanmu tace"To yanzu menene mafita..? So nake ki nuna ma Hajiya Uwani ita din banza da wofi..bata isa ba kuma bata kai ba wlh.. Anty Amarya tayi kwafa kafin tace"Ki kyaleni da ita Dayyaba..Ni yanzu abu Daya ke gabana Umar yazo ya tafi da Sakina Madina,kuma Hakan na gabda Faruwa saboda Cikin sati nan mai shiga yana tafe sakinar ma ke fadamin jirgin yawo zai fara yo gaba da kayansu..Kinga suna komawa shikenan hankalina ya kwanta Sai na Fuskanceta na nuna mata bata isa ba Daga ita har Sa"idun sai sun Dawo karkashin cewata ai Fara Bin sa gidan gona ba shi ne Mallam ya sakar mai komai ba Tukunnah dai Dayyaba akwai sauran rina akaba..! Mamanmu gabadaya yanayinta ya Sauya jin kalaman madina har suka gama wayar sama sama take amsata tana faman mata gatsine,Har dai ita mamanmu tagaji ta katse kiran lokaci daya tana bin wayar da Harara tana fadin"Haka kurum na kiraki da kudina da wayata ki Zauna kina neman gayamin mgana ina Dalili..! Dukiyar ai bataki bace Ko shi mallam din Daya tara bai Damu da ita ba sai ku kuna ta neman halaka kanku Saboda ita har kina Fadin har sa"idun sai ya Dawo karkashin cewarki..? Haka kurum ba kara sai ki maidamin Miji kamar kwallo ki dinga garasa yadda kika ga Dama to wlh madina Baki isa ba kan Sa"idu zan iya yin komai Ciki har da Raba Hanya Dake sai kowa yayi ta kansa kan mene ina Dalili wannan Bakinciki ina jin Dadi na Samu yadda nake so aikuwa Allah ne ya Hada mallam da Sa"idu ban ga mai rabasu ba haka kurum Madina ke wata mganar banza..! Surutun ma tana yi ne bata san tanayi ba Aba ne ya fito zai shiga bayi yaji tashin mganarta har ya shiga ya fita tana mganganunta shiyasa ya Leka Dakin nata yana Fadin"Balaraba ke da waye kike ta fada haka..? Tun dazu nake jin tashin mganarki nama Zata ko da hamida kike ne sai na Leka Dakinsu naga sun kwanta ita da Jawaad. Sai alokacin mamanmu ta Dawo Cikin Hayyacinta ta fara inda inda tana Fadin"Ni da masu yarenan ne yan iskan sai su kira ka suna maka gwaranci ko kai basa kiranka..?. Ya saki labulen yana Fadin"To da kin ji sune ai sai ki kashe wayar ki ni ai bani da Lokacin Sauraran irin su. ! Da haka ya koma Dakinsa Mamanmu ta Sauke ajiyar zuciya ta biyosa tana Fadin"Shikenan kuwa haka zan dinga yi musu sai mu rabu lafiya. ! Aranta sai taji salama da Aba bai Tsinkayi wasu daga cikin magnganunta ba. Ai data shiga goma ba uku ba. Acikin Satin kamar yadda Danmallam ya Tsara jirgi ya fara yo gaba da kayansu saboda yayi ma iyayansa da matansa siyayya musamman ma Amina Komai ya gani sai yace zai ma masu Ciki kyau harda kayan jarirai masu kyau duk ya siya ammh bai bari Sarood ta gani ba sannan yazo da Ruwan Zam zam mai yawa saboda mallam yamai mgana yana so da Dabinio sai sauran abunda ba"a rasa ba kuma bai sanar da kowa shi da Sarood zai taho ba sai dai agansu kawai. Kwana Biyu Tsakani kayan suka iso Jafar da Nasir suka je Filin jirgin Kano suka karbo kayan Direct Gidan mallan akayo da kayan Dakin Hajiya Daman kowa yasan in irin wannan ya faru kayan da komai Shashen Hajiya ake ijiyesu kafin ya Danmallam din ya sauka. Sakina ana chan ana shiri miji zai Dawo tayi gyaran kai tayi kunshi Sannan tayi gyaran jiki da na chan Shawaran Aliya ne ita ta Hadata da mai kayan matan ta siya awajenta. Miji kawai take jira ta riga ta gama Shiryawanta. Ko Amina in sukayi mgana in ta tambayeshi yaushe zai dawo sai yace ya kusa bai saka mata rana ba,yaki gayamata ranar da zai dawo so yake ya bata mamaki sai dai ta ga ya Kirata da Layinsa na Nageria. Haka kuwa akayi Ranar laraba suka sauka da karfe sha biyun Dare,kwana Biyar da sau kan kayansu suka iso a kano jirgi ya saukesu saboda Dare ne yasa bai kira kowa ba suka samu Tashar Mota shi da Sarood sai jakar kayansu suka nufo gumel sai wajen Biyu da wani abu na Dare suka iso gidansa ya wuce kai Tsaye sai dai Sakina taga Bakin Dare sai murnanta ta koma Ciki ganin Sarood sai da ta nuna afuskantar duk yadda taso ta boye hakan Sarood ko Cikin Murna taje ta Rumgume Sakina Tana Murnan ganinta.... Sakina tayi yake kawai tana Tunanin yadda Umar ya maidata banza ai bai gayamata kafarsa kafar matarsa ba Tana jin dadi ta gagari Amina Zama agumel shine zai jajibomata wannan Sakaryan. Dakin da aka bama Amina ta Zauna Sarood ta shiga sai dai yanayin Dakin da sauran kayan Amina Data gani yasa tasan an zauna adakin Saboda Gajiyan Hanya da kuma Dare yasa sai da Safe ta ma Sakina Zencen tunda suna Dawowa Umar Dakinsa ya nufa yayi wanka ya kwanta Sai barci sai da Safen suna kari Sarood ke tambayan sakina kayan waye tagani adakin ta..? Sakina Cikin kissa ta ke sanar da ita kayan Amaryan sa ne Amina nan ta Zauna Sarood ta kallesa sai dai batace komai ba ammh ranta ya baci meyasa Sai Dakinta baga Dakinsa ba..? Sannan wato ita aka raina meyasa bai ce ta Zauna Dakin Sakina ba..? Kwafa tayi har suka gama karyawa batace komai ba Sakina sai jin Dadi take yi ranta Fes domin da asuba sai da ta ribaci Umar yayi wani abu da ita kuma taga Chanji Sosai yadda ya rikice mata sannan karin jin Dadinta yadda ta zuga Sarood Cikin Ruwan Sanyi batare data gane ba Tunda ita Sakaryace shi kuma Danmallan kunu yasha baisan wata mgana yasan Nufin Sakina tunda ba yau ta saba raina ma Sarood din hankali ba. Ganin yadda ya Hade rai ne yasa Sarood din bata yi mganar ba Sai dai Daga yanayin ta sha ka matuka da Kishi Sosai. Suna gama karyawan suka shirya suka suka nufo Gidan Mallam Jafar ya Kira yazo da mota ya Daukesu daman Tun shekaranjiya an san sun iso Gida ya Rude da Murnan dawowarsa Gabadayansu har da Matan nasa duka Shashen Hajiya suka fara Sauka Har Sakinar domin ba hanyar da zata fara wucewa Shashen Anty Amarya ganin yadda ya Tsare gida.. Gabadaya matan mallam har da Anty Amarya nan shashen Hajiyar sukazo musu maraba su Hajiya Uwani kada aji labari sai barin jiki take yi Danmallan kallon Anty Amarya kawai yake yi yana Tuna labarin da Amina ta sanar dashi bai san Dalili ba sai yaji bai yarda da ita ba Tun balle ma ganin yadda take ta Kiftama Sakina Ido tana so su kebe suyi mgana ganin wannan balarabiyar da bata san da Zencen zuwa da ita ba, yana ganin su yayi kamar bai gani ba. Nan ya barsu ya tafi falon mallam shi da Nazeem suka hadu da Aba suka gaisa basu Dade ba suka tafi gidan gona ya Dade shashen mallam suna kara Tataunawa . Fitarsa ne ya bama Sakina Daman sulalewa ta koma Shashen Anty Amarya suka kebe Anty Amarya Cikin Bacin rai tace"Sai naga kuma wannan Sakaryan. ? Sakina ta tabe baki kafin tace"Nima yadda kika ganta haka na ganta..Ashe da ita zai taho..! Anty Amarya tace"To me kika fahimta da Zamansu tana nan a Hotonka ko kin Fahimci sauyi. !? Sakina tace"Anya..?nidai ban Fahimci komai ba..! Anty Amarya tace"To ki saka musu ido duk nasan aikin mallam na Dadewa yana Tasiri..! Da toh sakina ta amsa mata suka Ciga da Kulle kullen su tana bata Labarin Tambayar da Sarood tayi na wacce ta Zauna Adakinta da abunda Sakinar tace mata Anty Amarya na Dariya tace"Gwara da kika fadamata haka..Sakaryan sai ta bisa da tsiya..Ai Amina ba zaman gidanki ba ma Mijin da garin gumel gabadaya ne ya gagareta. waya gayamata Barno gabas take..! Sakina Tayi dariya kafin tace"Wlh kamar fa anyi ruwa an Dauke ko mganar fa bayayi..!. Anty Amarya tace"Ai bazai yi ba..Wayama sani ko auran ya Dade da Mutuwa fasawa ne ba"ayi ba kada aji kunya su Hajiya an yi Zani an yi Riga. ! Sakina tace"Zai iya yuyu wlh Anty..! Allah ma yasa hakan ne..!. Ta amsa mata da Ameen suna Dariya Ranar dai suna gidan har Dare wannan karon Sarood Shashen Hajiya ta Zauna tare da su Hanne tunda suna gida basu da Jarabawa wannan karon Sakina taji Haushin zuwa da ita da akayi yasa bata jata ajiki kamar baya ba Sai Dare suka koma gida,Washegari shi kadai yazo su suna gida Shashen Hajiya ya yada Zango aka Bude kaya ya bama Hajiya Tsarabanta na Turaren da Hijabin larabawa na mata sai Dogayen riguna guda Biyu masu kyau da Tsada da takalmi haka ma Anty Amarya da Haj.Nasara da Haj.Uwa dogayen riguna da Turare,Wannan karon har Hanne da Hamida yama Tsaraba domin bazai manta da kaunar da Amina ke musu ba, waya goma sai ta ambace su shiyasa daya siyo mata suma ya siyo musu Ya kuma nuna mata tsaraban Amina da Siyayyan kayan Jariran Da yayi,Hajiya Taji dadi sosai ta dinga yabawa sai dai Bata ga Tsaraban Mamanmu ba Tunda Har Aba ya yoma Tsaraba Sai alokacin ya tuna ma da ita Har ga Allah bai yi niyyar bata bane kawai Saboda tundaga Labarin da Amina ta basa yaji matar bata kwanta masa ba sai bai nuna ma Hajiya ba yace ya manta ne sai Hajiya tace bari ta bata Cikin nata. Sai ta hada mata da Ruwan Zam zam da Dabino. Hajiya ta aika ma su Haj.Nasara da Tsaraban Danmallan suna ta godiya haka su Hanne suka yi ta Tsallen murna,Ganin har dasu a Tsaraban Hamida da Hannen ma suka kai ma Mamanmu nata ta karba tana ta godiya da Santi tana auna kanta in tayi ma Aba kwaliya da ita.. Mallam dai Turarensa ne na Arab sai Zam zam da Dabino. Tsaraban sakina gida yakai mata nata Sai jin Dadi take yi ganin har da takalma ga kayan masu kyau da Tsada Na Amina kuma wajen Hajiya ya barsu su hanne kuwa tunda suka ga basu ga Amina ba kwana uku da Dawowar ya Danmallam ba labarin Dawowar Amina sai suka cire rai da Mganar Hajiya da kullum take sanar dasu Amina zata dawo nan kusa sai suka Sare.. Gashi har sun yi nisa a jarabarwarsu suna gabda gamawa gabadaya sai basa jin Dadin zama,ba Amina suma sun yi ahuru kamar basu agidan da ko da Amina ke nan wlh sai su shiga gidan mallam sau goma gidan Aba ma haka Rashin jinsu kawai yasa Dole ma asan dasu ammh yanzu sai a kwana awuni ba ba"aji ko motsinsu ba. Islamiya da Boko ma an gaji da Cigiyar Amina Daga baya ma su Hanne cewa kawai sukayi an cireta Daga mkaranta bata agarin harta mariya abokiyar fadanta da malaman makarantarsu Mallam Datti da kansa ya Kira mallam ya tambayesa Amina Mallam yace mai Amina bata gari ne shiyasa..! Kwana hudu da dawowarsa Ranar yazo Gidan da Safe Ya shiga shashen Hajiya suka gaisa da sauran matan Sannan ya koma wajen mallam to basu Dade da Mallam ba aka kirasa agidan mai anguwa Idi ya tafi kaisa Aba kuma baya nan sai ya tafi Dakin Nazeem ya dan kwanta ya Huta Sarood Tun abunda Sakina ta Fadamata take shamai kamshi sai bai Biye mata ba Sakina kuma kamar rana Daya zai mata Ciki takuranta ne ya Ishesa,yake barin mata gidan ita da Sarood din su ci kansu. Amina kuma tun washegarin ranar daya sauka daya Kirata bayan ya saka Layinsa na nan ya fadamata ya Dawo suka gaisa har take fadamai sun je asibiti ta fara awo sannan an mata Scan,basu wani jima suna mgana ba yace zai sake kiranta,kuma bai Samu Lokaci ba,Basu zauna sun yi mgana da Hajiya bane yana so yaje ya ganta kafin ya koma tunda ba wani Dadewa zai yi ba Sati Biyu ne zasu yi,zasu koma. Yana kwance har ya fara barci yaji sallama kamar daga sama yana Bude idanuwansa ya ci karo da Hanne da Hamida suna rabe raben shigowa Hanne na Tura hamida itama tana Turata mikewa Zaune yayi Daga kan gadon yana fadin"Ku shigo mana..! Jin haka yasa suka shigo Dakin kansu na kasa kamar wasu marayu duk suna Sanye da manya Hijabi har kasa mamakin ganinsu yayi gabansa suka Duka kamar masu neman gafara gaishesa sukayi ya amsa yana Dan Nazarinsa dazu a falon Hajiya yaga Hanne sun gaisa hamidan ne dai bai gani ba. ! Hamida kuma hanne ce taje ta jawota kan suzo su tambayi Ya Danmallam Tunda Hajiya taki fadamusu inda Amina take kila shi zai fadamusu shine suka zo a bakin Hajiya sukaji yana Dakin ya Nazeem Shine suka zo sun kuma kasa mgana saboda ba Sakewa Tsakaninsu sannan yana musu kwarjini. Shine yaga suna Sunkuye sunkuye kai da taba juna yayi mirmishi kafin yace"Lafiya..? Baku je makaranta bane yau..? Hanne tace"ai jarabawa muke yi yau bamu dashi sai monday..! Ya gyada kai sai yanzu ya tuna da Tsarin Tun farko,tunda Hajiya ta sanar dashi yadai manta ne,Cikin Sanyinsa yace"Kuyi mgana ina Fatan dai lafiya ko..? Hamida ta sanda kanta kasa tana Fadin"Dama..Dama..Muna so mu tambayeka ne ya Danmaallan..! Zama ya gyara yana Fadin"Allah yasa na sani..! Hanne ta zungura ita kuma sai ta kara kasa da Murya tana Fadin"Dama kan mganar Amina ne yaya.. Kai Tsaye yace"Amina..? Me ya faru da Aminar.? Hanne tace"Bakomai tunda Hajiya ta tafi da ita har yanzu bata Dawo ba..Muna ta tambayanta ina take taki gayamana gashi har mun fara jarabawa ba Amina muna kewarta ne Hajiya sai tayi ta ce mana zata Dawo Zata Dawo ammh shuru..Shine mukace bari muzo mu tambayeka muji ko kasan inda take..? Wlh kuma bamajin Dadin Zama ba Amina..! Hanne ta karbe da cewa"Kawayen mu sai tambayan mu ita suke yi..Kowa sai yace ina Amina.? Mu kan mu muna son sanin inda take..! Sai da suka gama Mgana yana kallonsu kafin ya saki Mirmishi ya tuna sanda ya kira Amina yace ya Dawo abunda ta fara tambayansa yaga Hamida da Hanne..? Don Allah ya gaishesu yace tana missing dinsu.ai shi shaida ne Saboda Rabin wayarsu mganar Hanne da Hamida ne ya Dade yana jinjina wannan kaunar Dake Tsakaninsu Amina tana matukar ji da Hanne da Hamida in tana Hiransu haka Zakaji Farinciki da Murna acikin muryanta Shi bai wani zauna dasu ba ammh yasan dai tare suke su uku ammh baisan Rayuwarsu ba gaskiya. Gyaran Murya yayi kafin yace"Kada ku Damu Amina na Cikin koshin Lafiya..Itama tace na gaisheku sosai tana kewarku..! Suka kallesa kafin su koma su kalli juna sai Hawaye duk ya Cicciko Idanuwansu Hanne tace"Muma muna kewarta don Allah tana ina..? Kuma yaushe zata Dawo..? Kai Tsaye yace"kuyi hakuri bazan iya Fada muku inda take ba..Ammh tana Cikin Koshin lafiya..Sannan zata Dawi kowani Lokaci itama bata manta daku ba koda yaushe Cikin Zencen ku take yi..! Kawai sai suka fara mai sharan kwallah ya kallesu baki bude bai yi mamaki ba in ya Tuna yadda suka rika uban kuka Ranar da zai tafi da Amina gidansa. Gyara zama yayi kallesu yana Fadin"ku share hawayenku..Ku Zauna Dakyau yau labarin Amina zaku bani Tundaga Farko har karshe..! Yau ina so naji nima..! Hama kurum yake son jin Labarin Amina,batare da yasan Dalili ba. Jin haka yasa suka gyara zama suka Fara bashi Labarin Amina da yarintarsu Hanne tayi in ta gaji Hamida ta karbe in suka fadamai wani abu baya sanin ma yana Dariya jin jina Jidalin Amina kawai yake yi aransa ashe haka tayi nisa bai sani ba ? Kirarinta ke basa Dariya in ya Tuna wai Aminene ikon Allah badai ta Mutum ba sai ta Allah lalle yarinyar nan sai Allah taci kuma kirarinta.. Hanne ta Karbe da Fadin"Wlh ya Danmallam Amina tana da kirki sai wanda ya Zauna da ita ya sani...Tana da son yan"uwanta sai dai akwai abu Daya Amina tana da riko in ta Tsaneka sai Alllah sannan tana da Fada da Tsiwa kuma bata Laushi ko bata da gaskiya sannan ga son jin gulma,Amina fada ko ba nata bane siyanta take yi a makarantar boko da Islamiya ba malami ko Dalibin da baisan Jidalin Amina ba,ba wanda ta Kyale tana da Fara"a sai dai bata Daukan Reni bata kuma son arainata kan Hamida da hanne Amina Zata iya yin komai tasha Fada saboda mu kuma duk wani abu da ake yi Amina ce gand leader din mu. Ya Danmallam ga ni Amina wata Hudu ta bani Hamida kuma wata uku ta bata ammh nuna wa take kamar ta Girmemu Amina bata san Faduwa ba bata nuna gazawarta Wlh ko su ya Abida ban shaku dasu yadda na shaku da Amina ba tunda muka taso bamu taba Rabuwa ko na kwana Daya ba,Shiyasa Rashinta ya ke sakamu cikin Wani hali komai baya mana Dadi..! Hamida ta karbe da Mirmishi tace"kuma ba"a zaman minti goma da ita ba"ayi fada da ita ba..tafi Fada dani Fiye da Hanne saboda ni bana gani na kyale Hanne kuma bata da yawan mgana,Mu yi fada mu Shirya hakanan muke zaune duk duniya ba wanda yakaimu sanin Amina sannan mun san Halinta sai muka ci Mganin zama da ita, jidalin Amina ni da Hanne kadai muke iya Daukan ta, ko Ciwo tayi kowa sai yaji wani iri saboda Amina mai Fara"a ce sannan tana da Dadin zama ga wanda ya santa sai dai kawai Fada da Zafin rai sannan bata Daukan Reni Haka Aminene take bata da tsoro bata Shakka Kirarinta badai ta mutum ba sai Allah..! Ko abunda ya faru na Aminu Tsausayi ne wlh ba Halin Amina bane nan ta shiga bashi labarin soyayyar ta da Aminu tundaga farko Har karshe da abun da ya Faru Hamida ta kareshe da Rantsuwan wlh tallahi ya Danmallam Tsautsayi ne ammh wannan ba Halin Amina bane barta da Jidalanta ammh Namiji baya gabanta soyayyarta da Aminu kaddara ne ta Ubangiji..! Da Dukkan Hankalinsa yake sauraranasu duka labaransu suna shiga kansa wasu labaran na Amina abun Dariya ne wasu kuma ya Dauki wasu abubuwa da mganar Data Fadamai akwai kamshin gaskiya ko wani yaro akawai irin yarintarsa ammh na Amina yayi yawa wannan Rashin Tsoro da rashin jinta yayi yawa ba nata bane ita kadai da gaske an kara mata ne duk da abun ya Tarda Halinta ne ya gasgasta mganar ta Dalilai da dama sannan ga abunda ya Lura dashi a wajenta lokacin da ya kusanceta din nan ya Fahimci akwai matsala sannan ga mgangan su Hamida sosai yaji tsausayin Amina da wani Kaunarta na shiga ransa bai sani ba.. Mganar Aminu kuma mallam yadan Fadamai kadan Daga Cikin abun da ya faru Lokacin bai wani mai da kai ba kan mganar tunda alokacin yana ganin Aaminar kamar ta riga ta gagarane aransa kuma sai yaji ya baci da jin Labarin yadda su Jafar suka Dinga Dukan mai mata gaskiya ransa ya baci da Yana Kasar sai ya hanasu ai wannan abun yayi yawa kamar sun sanu jaka su bazasu Fahimci wani abu kan Amina ba..? Yayi mamakin da ko mallam bai Taba kaawo wani abu acikin Ransa ba sai dai kila wani abu Allah bai Cika bayyanasa da wuri ba sai Tafiya tayi tafiya mganar Aminu kuma bai Damu ba yasan ba son shi Amima ke yi ba yarinta ne da kuma kaddaran auransa da Amina shi kamar ma taimakonsa yayi sannan da kuma karfin rabon dake Tsakaninsa da ita Mirmishi yayi har Hakoransa suka bayyana kafin yace"Wato Aminene dai ikon Allah ce badai ta mutum ba sai ta Allah..! Hamida da Hanne sukayi Dariya suka Dukar dakai shima Dariya yayi yana tuna wai tace ma malamar corper dinsu tana warin maza kawai sai yaji wani abu mai gardi da Zumudi kan Amina na kara mamaye ransa To ai a jidalin nata zata zama uwa..! Lalle akwai kallo sannan Jidalin akwaishi kam Nan ya samu ya lallaba su hanne yace zai hadasu suyi mgana da Amina ammh bai sanar dasu inda take ba sun ji Dadi da sanyi tunda Amina dai tana Lafiya sannan tunda yace zai hadasu susan bazai musu karya ba sannan yace kada su fadama ko Hajiya mganar da sukayi. Adaran yayi ma Hajiya mganar zuwa Abuja Hajiya tace ko da yaushe ya shirya yaje mana ya ganta.. Kansa na kasa yace zai sanar da Mallam jibi sai ya tafi gobe zai je Dutse shi da su Sarood su gaida Aliya matar Aliyu tana asibiti Ciki na bata Wahala... Hajiya ta jajanta kai Tsaye tace ma Danmallam ya Dauki Aliyu ya rakasa Abujan mana. Cikin mamaki yace"Hajiya kin manta kin ce ko shi kada yasan komai..? Hajiya tace"Ka sanar dashi nasan shima bazai sanar da kowa ba..Bai kyautu kaje kai kadai bane..! Ko Jiya sai da nayi ma Sa"idu Tsiya kawaicinsa yayi yawa bai Taba Tambayana ina Amina ba ko ina na kaita ba.? Anya akwai Uba irin Sa'idu kuwa..? Cemin yake yarda da nayi Dake Hajiya yarda kika rikeni Tsakani ga Allah na Tabbata duk inda Zaki kai Amina Za"a kula da ita kuma bazaki kaita inda Za"a Cutar da ita ba .! Danmallam mirmishi kawai yayi bai ce komai ba Tsakanin Baba Sa"idu da Hajiya ko mallam baisan Tsakaninsu ba ballatana shi da ba mazauni ba sun Dade suna Hira da Hajiya kafin ya mata sallama Shashen falon ya koma sukayi mganar Tafiyarsu Dutse gobe da zuwansu Abuja shi da Aliyu mallam yace yana da kyau hakan Aliyu ai Aminini sosai sannan ya bada Sakon gaisuwarsa ga Mamarsa Amina. Daya fito daga wajen Mallam shi da Nazeem suka yi hira sai after 10 ya koma gida Sarood ta kwanta Sakina dai na Zaman jiransa ya riga yaci abinci shashen mallam shiyasa bai ci wanda suka shiryamai ba yasan Daman abunda take mawa shi har mamaki take basa zafin nema na kawo samu ne..! Tunda ya Dawo bata barsa ya Huta ba koda yaushe abu Daya ce mata akayi haka ake samun Ciki..? Koda yake duba da Cikar Burinsu ai yasa tama Fita daga hankalinta Kada ya Danne mata Hakkinta yasa ya Biye mata kuma duk Shawaran Anty Amarya ne Ta Dake ta maida Cikinta Datayi barinsa. Washegari karfe tara na Safe suka Dauki Hanyar Dutse shi ke Driving din Sakina na gidan gaba Sarood na baya sun isa da wuri Ajiyan aka Sallami Aliyan tana gidan chan suka wuce Direct bayan sun ci abinci sun huta sai mazan suka shiga Cikin gari suka bar matan agida Sakina da Aliya suna mgana da Hausa suna Yamutsan fuska suna zunden Sarood, ita kuma tana kallon su tana washe baki batajin me suke Fadi Daga baya ma tashi sukayi suka shige Ciki suka barta ita kadai afalo kamar mayya su kuma sai bayan La"asar suka Dawo abokansu suka ziyarta da sukayi makaranta tare da aiki ya kawosu Dutse da zasu dawo suna Hanya Danmallan yace gobe da Safe ya zo zai rakasa Abuja Aliyu bai kawo komai ba Tunaninsa wani abun zai kai Umar din Abuja. Yasa bai matsamai da Tambaya ba ya amsa masa da toh Allah ya kaimu. Bayan La"asar suka Dauki Hanya bayan su Aliyu sun rakosu da Fatan isa Lafiya da suka Dawo gidan mallam suka Sauka sai aranar suka shiga gidan Baba Sa"idu suka gaisa da mamanmu shima adaran ya shiga shida Aba suka gaisa da ita sai kallonta yake yi yana Nazarinta haka kurum daman shi tun Farko kirkirta bai mai ba sai kuma ta kara Dora kanta azargi da Aba ya shiga Shashensa ta fara tambayansa Amina harda sharan kwallarta na karya wai Hajiya taki sanar ma kowa inda takai Amina.. Mirmishin yayi kafin yace mata shima bata Fadamai ba sai ta fara sallallanmi tana Fadin Allah yasa to dai lafiya. Har ya mata sallama ya fita yana Auna mganganunta Biri dai yaso yayi kama da mutum a kaunar datake ma Amina in har na gaskiya ne Amina Bazata kai wannan wattanin bata nan ba bata wani damu ba gaskiya bai yarda da ita ba daman mutum ya cika Kirki wani Lokacin mugu ne. Sai dare ya kwashi matansa suka koma gida adaran ya Fada musu gobe zai je Abuja wani aiki zai kaisa ba su Damu ba ita kanta Sakina bata kawo komai aranta ba ta Dauka dai aikin zai kaisa kamar yadda yace. Washegari kuwa agidan mallam suka Hadu da Aliyu bayan ya gaida su Hajiya suka Dauki Hanya,Hajiya ta bata Goriba da su Rama da zogale da kulu su gauta da yalo da Daffafiyar gurjiya akaima Amina sun yi mgana da Aisha ta fada mata abincin zamani Amina bataci sai na gargajiya. Danmallan ya taho da Tsaraban Amina tare da Ruwan zam zam din daya riga ya karanta mata duka ayoyin dake karya sihiri aciki sannan da Sauran addu"o"in Tsari Domin ya yardan ma kansa Amina ba ita kadai bace. A motar Aliyu sukayi tafiyar dayake sun tafi da wuri sha Biyu suka shigo Abuja Usman mijin Aisha Danmallam ya Kira yayi musu kwatance cikin Lokaci sai gasu a anguwan maitama Dayake gidajen akawai lamba sai gasu agidan Usman ya Fito ya tarbesu daman yana gida ya samu dan break yana Hutawa kuma shima sai da Safen nan Ya Dannallam ya kirasa ya fadamai suna tafe kuma yace kada ya Fada su Aisha..! Sai da suka iso gidan ne Aliyu yaga Usman sanna ya kalli Umar yana Fadin"Daman gidan Aisha zamu zo..? Ko wannan ba mijinta bane..? Lokacin Usman din yayi gaba suna Binsa abaya zuwa Cikin gidan. Danmallam yace"Eh ammh ba wajenta nazo ba..! Aliyu Cikin mamaki yace"To wajen wa kazo..? Ai naga har sako Hajiya ta baka ka kawo mata. ! Kamar bazai yi mgana ba sai kuma yace"Zaka ganta ita wacce nazo Dominta..! daidai suna shiga kayattacen Falon na gidan Aisha. *Janafty**TFZB2020* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Har cikin babban falon gidan Usman ya kawosu yana musu maraba suka samu Daya daga cikin kujerun falon mai zaman mutum biyu suka zauna suna kallon falon ko'ina tsab sai tashin kamshi yake yi sai talabijin dayake ta babatunsa shi kadai cikin Tashar Arewa24. Usman kitchen ya wuce Direct saboda gida ba wanda ya tashi sai Saude mai aiki shima kiran Danmallam ne ya tashesa bayan ta gaisheshi yace ta kawo Ruwa da lemo akwai baki a falo ta amsamai da toh Cikin girmamawa. Yana fitowa ya zauna saman kujera mai zamam mutum daya suka kara gaisawa da Danmallam da Aliyu. Sannan Usman ya mike yana fadin"Bari na mata mgana..Gidan ba wanda ya tashi..! Da haka ya nufi Bedroom dinsu shi kanshi ai kayan barci ne masu taushi ajikinsa Aliyu ya bisa da kallo har ya bace ma ganinsa Umar ya kallah yana kara nazari da Tunanin me suka zo yi gidan Aisha..? Shi dai yasan ko gidajen su Jafar a kirga zuwan Umar ko Nazir kila sau Daya ya taba Taka Lagos in bai manta ba bama shi kadai ba ko su isu isu matan Mallam bai yarda su rika Bin gidajen juna ba sai da kwakkwaran Dalili ballatana shi namiji kuma in bata ma da Lafiya ne ya tabbata sai dai Cikin su Hajiya za su zo bashi ba Gabadaya mamaki ya kamasa daya kasa mgana shi kuma Umar kansa ya Jinginar jikin kujera Idanuwansa a Lumshe fatansa da Burinsa yaga Amina yaga cikisa Dake Jikinta Da yanzu yakai wata shida. Usman Cikin blanket ya Samu Aisha ta nade tana barci yaye blanket din yayi yana kiranta. Sweety..! Dakyar ta Bude ido cikin Barci Tana Fadin'"Darling ka barni nayi barci don Allah..! Kafarta ya matsa yana Fadin"Baki fa mukayi..! Bude ido tayi da Sauri tana Fadin"Baki kuma..? Da sassafan nan..? Mikewa yayi yana Fadin"masu muhimmaci ne kuma ba Safe bane wajen 12pm fa yanzu rana tayi! Mikewa tayi tana mamakin wasu irin baki ne haka sai ta saka aranta yan"uwan Darling ne ammh Daga barayinta bata tsammani haka ba. Dogon Hijabinta ta Zurma na sallarta ne kan kayan barcinta Doguwar riga ta Sako Silafas dinta na yawo Cikin Gida ta fito shi kuma yana Biye da ita a baya har Cikin Falon. Wadanda ta gani ne yasa ta Tsaya Cak tana kallon Usman baki Bude Dariya yayi mata ya koma ya zauna yana Fadin"Suprise..! Saboda murna sai ta kasa zama Cikin wani yanayi a muryanta tace"Ya Danmallam .! Ya Aliyu..! Tafada Cikin farimciki suka kalleta gabadayansu suna mata Mirmishi ai da gudu ta nufi Danmallan ta Rumgumesa daga Zaune saurin Kwacewa yayi yana Fadin"Miye haka kanar wata yarinya..? Tana yar Dariya tace"Allah ya Danmallam nayi murnan ganinku ne ko Jiya mun yi mgana da Hajiya bata fadamin zaka zo ba..! Kai Tsaye Danmallam yace"Ban tabbatar da tafiyar ba nima..! Kasa ta koma ta zauna tana gaishe da Aliyu ya amsa cikin Fara"a sannan ta gaida Danmallan ya amsa mata ta Tambayi sakina da Sarood yace"Duk suna Lafiya sarood da ita muka zo Tana gumel..! Aisha tace"Allah Sarki..Sannun ku da zuwa gaskiya ammin zuwan bazata kuma Harda Darling aka hada baki ko..? Tafada tana Hararansa da Sauri Aliyu yace"Kada ki ga Laifinsa ba ruwansa ko ni da ya Daukoni Tundaga Dutse bai Fadamin gidan nan zamu zo ba..Ga mai Laifi nan yayanki..! Yafada yana Hararansa da bai masan yanayi ba,Aisha zatayi mgana kenan sai ga Saude da Faranti Cike da kayan ruwa da Lemo Aisha ta karba tana Fadin"Bari nazo Kitchen din Saude yayyina ne suka zo..! Ta amsa cikin Fara"a tana gaishesu suka amsa mata sannan ta fice Daga Falon taja Center Table din Dake Falon ta Dora musu akai tana Fadin"Ku fara da wannan yaya..bari a sama muku abun karyawa..! Aliyu na Dauka goran ruwa yace"Tab ai mu nan sai da na Rana..ni kinsan ban cika irin wannan abun na bature ba..Sai dai shehi kila shima bai karya ba ya fito..! Sai yanzu ya Hararesa Yana dan kallon Usman da hankalinsa baya kansu yana kaa wayar hannunsa ya karkata daidai saitin kunnensa yace"Kaima kenan Dake da mata Daya kayi karin ka agida ballatana ni Dake da Daya biyu uku..! Ya Fada yana Kirgasu da Hannu Aliyu na Dariya yace"Ba shakka..! Usman ya mike yana isa kusa da Aisha a hankali yace"Kefa ba waJen ki suka zo ba.Wajem Amina nefa ammh kin Tsaya kina ta kallonsu..! Kanta ta Dafe ta juya tana Fadin"Murna ce ta sa na Rude Darling..! Mirmushi yayi mata sai bai bita ba yace ma su Aliyu bari yazo ya tafi ya basu wuri kada ya Takura musu. Amina na Dakin yakaka kwance akan gado tana barci yakaka kuma na Saman Darduma ta daidaici gabas tana Ta lazimi tun bayan data gama Sallar walha ko Hijabin jikinta bata Cire ba ammh sai faman gyangyadi take yi. Aisha ta shigo Dakin da Sallama yakaka ta amsa cikin Fara"a tana Fadin"Aisha kin tashi..? Gaban yakaka ta Durkusa tana amsa mata Lokaci Daya da gaisuwa Ta amsa tana Tambayan Tashin Usman tace mata Lafiya Amina ta kalla data yi kwanciyar gefe saboda Cikin jikinta tace"Yakaka ita wannan bata tashi bane..? Yakaka tace"Tun dai da ta koma bayan Sallar asuba bata tashi ba..Kinsan ta da barci kuma kila Cikin mganin da likitan ya bata akwai na barci ne inaga..duk da dama tun jiya naganta tana tura baki tana kunkuni bansan me aka mata ba. Aisha tace"To ina ga...,Yakaka ai Takwaranki jidalinta tashi yake yi ko ba"a mata komai ba.. Yakaka tace"A"a yafi dai tashi in an Tabamu..! Ya Aisha tayi Yar dariya kafin tace"To ai tashi zatayi yanzu yakaka mijinta ne yazo..! Yakaka ta zaro ido Lokaci Daya tana Fadin"Wani mijin nata..,? Ya Aisha ta mike tana Fadin"Ya Danmallam mana yakaka..! Yakaka sai ta mike tana Fadin"Allahu akbar kice bakin Madina garin manzon Allah Sallahu alaihi waasallam..Zuwa haka ba sanarwa..? Ko daman kin san da zuwansa..? Aisha tace"Bai fadamin ba yakaka..! Yakaka na gyara Hijabin tace"Ahto bari na fita mu gaisa ki tasheta in ta Tsaya wannan kunkunin nata kice na tafi kwace mijin sai ya cike ta Hudu dani ya Rufe kofa..! Ya Aisha na Dariya tace"To yakaka .! Ta fice tana Fadin"Tadata ta taso ai barcin ya isa haka..! Ta fice abunta ita kuma ya Aisha ta dan Daki gefen katifa tana kiran sunan Amina sai chan ta jita ta dan Dago kai Cikin barci ta Bude idonta ya Aisha tace"Dilla ki tashi barcin ya isa haka..! Amina zata sake juyawa Aisha ta Make mata hannu tana Fadin"Ya Danmallam ne fa yazo Amina..! Da sauri ta dan mike zaune tana Fadin"Da gaske..? Ya Aisha ta mike tana fadin"Ko nace ya shigo ne..? Amina ta Tura baki batayi mgana ba Ya Aisha tace"Suna falo suna gaisawa da yakaka ki Sauya kaya ki sako Hijabinki ki fito ku gaisa..! Daganan ta fice Daga Dakin Amina ta Bita da Harara tana kunkuni tace"Ba"aza afiton ba sai yau ne ma zai zo wajena tunda ya dawo ya manta dani ya samu guzumayen matansa ko kirana bayayi..! Ashe Fushinta datake yi kenan tun jiya Saboda sau daya suka yi mgana Daya Dawo. Aisha na fita falo ta iske yakaka sai Hira suke sha da Aliyu Har da ya Danmallam da bai mgana Dariya kawai tayi yakakace fa balle ai yasanta Saboda in suna waya da Amima yana jin mganarta sannan sun taba gaisawa sau biyu da ita kuma ai Hajiya ta Fadamai akwai kakar Usman agidan tun kafin ta kawo Aminar. Tana ganin Aisha tace"To ina takwaran tawa.? Na ganki ke kadai..? Aisha tace"To nidai na tasheta na Fadamata ban sanin mata ba..!. Yakaka tace"Kajimin shegentaka ace maka ga mijinki ya taso daga wata uwa Duniya domin ka sai ka Tsaya Sakarci..? Ahtto ni dai dan madina tunda Takwaran tawa tana ja maka aji gani sai ka Rufe kofa dani mu Daga garin manzo sai dai taji asalansa..! Dariya Aliyu yayi tsohuwar farat Daya ta shiga ransa sai da yana ta mamakin waye wannan da Aliyu yazo gani..?. Saboda shi bai taba sanin Amina bata nan ba.. Danmallam ne yace ma yakaka"Shikenan baaba..Sai mu tafi Dake ai ni naga Amaryata. Ta washe baki tana Fadin"ah to in ita bata so..Ai ni ina son abuna..Daman ita naso na raka garin na manzo Tunda na mata fashin Mijin ai shikenan kowa yayi ta kansa..! Har Aisha sai da ta Dara yakaka ta mike tana kallon Aisha kafin tayi mgana sai ga Amina ta shigo Falon da Karamar sallamanta tana Tura baki Sanye take da Dogon wando plazo Sai Dogom Hijabin Dake jikinta duk hannun Data sanya mbai iya kare Cikinta Daya bayyana ba sannan tayi Kiba har ta Fuskarta ta Cicciko Idanuwanta duk girmansu sun shige Ciki. Yakaka na ganinta ta koma ta zauna tana Fadin"ki zauna kina wani Tafiyar wahainiya ni dai na riga na yi fashin Dan Madina abuna..! Amina ko kanta bata Dago ba har ta kariso falon Aliyu Sai kallonta yake yi ya Bude baki yafi a kirga yana Rufewa saboda mamaki Danmallam kuma Hannayensa Sarke saman kirjinsa yana kare ma Amina kallon Tundaga sama har kasa yana mamakin girmanta yarinyar daya barta marabanta da kwaila kadan ne itace ta koma wata Big mama..? Ko"ina ya cika haka? Cikinta kawai yake kallo duk nacinsa taki yarda su hada ido shi ko Aliyu ba mamakin ganin Amina bane ya Razana shi ba illah Cikin Dake jikinta ne ya fi bashi mamaki ya kalli Umar yafi sau goma ya kasa mgana shi kuma sai ya basar dashi bai shirya mgana dashi ba yanzu. Amina kuwa kanta na kasa ta nemi kasan Cafet ta zauna Dakyar yakaka na fadin"kada ki takura kanki kowa yasan Lalurace hau kujera ki zauna mana..! Ko kallon yakaka batayi ba tayi zamanta Saman cafet kanta na kasa Ya Aisha sai kallon Amina take yi tana Hararanta ganin yadda ta hade rai Yakaka ta saki baki tana kallonta kafin tace"Yau naga Tsiya Indo..? Amina fa sai Addu"a jira take su gaisheta kenan..? Amina sai alokacin ta Dago kanta karaf suka Hada ido da ya Danmallam Daya gama kafeta da ido tun shigowarta ya kasa dauke ganinsa akanta yana ta mamakin girmanta sannan yana Tunanin yadda yaganta da Cikin nan bai taba Hasaso hakan nan kusa ba akanta ba sai gashi Allah ya nuna nashi Ikon. Saurin Dauke kanta tayi Saboda wani Dum dataji da yanayin kallon nasa sai da taji dan Cikinta ya koma gefe daya Ta Cikin Hijabin ta dora hannunta kan cikinta tana jin wani kaunar abunda ke Cikinta na kara shiganta Tun ranar da sukaje Scan aka hasko mata abunda ke Cikinta wani soyayyarsa ta ratsa kirjinta taji duk duniya bata da wanda take so kamarsa abun ya bata sha"awa dan mutum acikinta yana Rayuwa.. Bata kara kallonsu ba cikin shakewar murya tace"sannun ku da zuwa..! Aliyu ne ya amsa yana kallonta Cikin Shanye mamakin sa yace"Yauwa Amina ko..? Amina ta dago ta kallesa kafin ta maida kanta kasa ta gyada mai kai Cikin mirmishi yace"Allah Sarki ashe kina nan..? Ya nauyin jiki kuma..? Sai ta kasa mgana Yakakace ke fadin"Ai ta Dade anan watan ta biyu ko Aisha..? Ya Aisha tace"Eh ta dan jima..! Aliyu ya jinjina kai yana kallon Amina yace"Allah ya rabasu lafiya..! Yakaka da Aisha suka amsa mai da Ameen ya Danmallan dai bai ce komai ba,Sai kallon Amina yake yi kasa kasa. Aisha tana Lura dashi sai ta isa wajen Amina tana fadin"Amina taso na ganki mana..! Tafada tana taimaka mata ta mike Tsaye yakaka ta kalleta tana Fadin"Ahto gwara ki jata ki Fadamata gaskiya ko zataji..Koda yake ta makara na riga na kwace mijin Dani zai koma garin Manzo..! Aliyu na Dariya yace"Kwarai baba. ! Hararanta Amina tayi tana Tura baki Yakaka tace"Ni miye nawa..? Ga wanda zaki tura ma bakin nan..!. Tafada tana nuna Danmallam da suka Hada ido da Amina ta Tura mai bakin sannan tabi bayan Aisha Mirmishi ya subucemai tuna Kirarinta Aminene ce fa..badai ta mutum ba sai ta Allah .! Yakaka ta bita da kallo tana rike baki tace"Mun shige su ta ko turamai bakin Ali kana dai gani ko..? Dariya yayi yana Fadin"Kyalesu yakaka chan tsakaninsu ne mu ba ruwanmu..!. Yafada yana kallon Umar Dayaki yarda su hada ido. Inda su Amina suka shiga ya kurama Ido Yakaka da Aliyu suka cigaba da Hirarsu tana ta mai Hirar zuwanta Saudiya ne na farko yana shan Dariya shiko Danmallam gabadaya hankalinsa na kan Amina shi yasan Laifinsa tun kafin ta fada. Suna shiga Dakin ya Aisha ta ja ta tsaya tana Hararan Amina.. Amina ta nemi gefen gado ta Zauna tana Fadin."To wai ni me nayi ne..? Ya Aisha tace"Bansani ba..Kada kiban Haushi na make ki wlh..! Amina ta tura baki batace komai ba ya Aisha ta zauna gefenta tana Fadin"Haka ake gaida mutane .? Shi fa ya Dannallam ko gaishesa baki yi ba ballatana ya Aliyu..! Amina tace"To ba nace musu sannu da zuwa ba.! Ta fada tana Hura Hanci Aisha tace"Ai sannu da zuwa ba gaisuwa bace malama. ! Amina ta tura baki tana fadin"Ni ba ruwana dashi sai fa yau yazo alhalin yafi kwana hudu da zuwa kuma kuma ma sau daya ya kirani tunda yazo wato yana chan wajen guzumayen matansa ni kuma yamin ciki ya barni da Wahala..! Sai hawaye Ya Aisha ta saki baki tana kallon Amina Dariya na cinta tana auna Dimarar da za"ayi in zama waje Daya ya tabbata Tsakanin Amina da su Sakina akwai kallo. Ya Aisha data Fahimci kishi Amina ke yi bata sani ba yasa Cikin sigar lallashi tace"To ai gashi yazo yanzu ko..? In ma zaki nuna bacin ranki bata haka Zaki nuna ba kamata yayi yanzu ki tashi kiyi wanka ki sauya kaya ki gyara Jikin ki kina tashin kamshi,Sai in dan ya shigo kuka gaisa sai ya ce ya kike..? Ko ya bby na..? Sai kice ai baka so kasan ya nake ba Tunda kazo su Anty na sun sa ka manta dani..! Irin haka dai cikin shagwaba..! Amina ta kalleta Sheke sheke kafin tace"Tab uban wa zai ce musu Anty..? Allah ya Tsareni ni ko abaya ban ce mata Anty ba ballatana yanzu da muka Hada miji kowa yayi ta kansa .! Ya Aisha na danne Dariyanta tace"To naji Kiyi hakuri ki tashi kiyi wanka ni yanzu Kitchen zani na sama musu abunda zasu ci ni da Saude kin karya ko..? Tana kunkuni tace"nasha kunin da Saude ta Damama yakaka..! Ya Aisha ta mike tana Fadin"To yi wanka in mun gama sai Saude tayi miki wainar Fulawanki..! Da haka ta fice bayan ta kara Lallaba Aminar ganin kishin Ya Danmallam take yi bata sani ba.. Falon ta koma yakaka dai da Aliyu sai hira suke sha,Danmallam kuma na Zaune yayi shuru,Tace bari ta shiga Kitchen suka amsa mata sai da ta leka Usman ta iskesa yana waya sai ta fice ta shiga Kitchen domin taya Saude wasu ayyuka,sun saba tun agida basu taso da son jiki ba. Amina tana Fushi tana kunkuni tatashi tayi wanka tazo ta Shafa Lotion din da Ya Aisha ta siya mata ta Dauko Cikin Dogayen rigunan da Aisha ta siya mata mai kalan baki da Zanen ja ajiki. Ta saka Rigar kenan ta juya saman gado ta Dauko bakin Dankwalin Rigar sai ta dan taka Rigar ta kasa ta dan Zame tayi baya zata fadi har ta Sadakar ta sha kasa taji ta ta Fada Hannun mutum tana Bude ido suka Hada ido da ya Danmallam har Gemunsa na taba Fuskarta. Kallon kallon sukama juna kowa da abunda yake sakawa gajiya yayi da Zaman falo yakaka da Aliyu na Hiransu ya tashi ya shigo Dakin da Amina ta shiga tun dazu Aliyu ya Bisa da kallon mamaki Yakaka dai batama Lura dashi ba Ta tsinke da Hira abunta. Amina ta lumshe ido jin kallon nasa har Cikin kanta Saurin tashi tayi ya taimaka mata ta tsaya sosai yana Fadin"Ki kula fa Aminene..! Da mugun mamaki ta kallesa tana Tunanin ina yasan ana ce mata Aminene..? Gira ya Daga mata yana Sakin mata Mirmishinsa na koda yaushe Daga sama har kasa yake kallonta yana kara more kallonta Har da jingina jikin Madubin Dakin yana dunkule hannayensa saman kirjinsa yana binta da kallo da dukkan zuciyarsa. Ita kuma ganin yadda yake kallonta yasa ta Tura mai Baki ta juyamai baya tana kokarin Daukan Dankwalinta ta Rufe Kitson kalaban da ya Aisha ta mata. Kawai sai jinsa tayi a bayanta gemunsa na taba wuyanta saboda ya fita Tsawo ita tana iya kirjinsa ne Dankwalin ya karba ya rankwafa yana mata rada"Ya kika juya..? Kada kimin rowan ganin Yadda Cikina ya sa kika tashi daga kwaila kika koma Big mama .! Batasan Sadda ta sakarmai Dankwalin ba ga kunya sannan ga fushi sai ta ki juyowa tana Tura baki hannunsa duka Biyu ya sa ya juyo da ita yana kallonta Runtse ido tayi taki Budewa. Dariya ta basa sai ya ja karan Hancinta yana fadin"Duk fushin ne yasa ko kallona ma an kasa yi..? Kara Turo bakin tayi sai ji tayi ya Sakar mata Kiss a saman bakin da Sauri ta Bude manyan idanuwanta ta ware akansa cikin mamaki gira ya Daga mata yana kallonta itama shi take kallo ya kara fari sannan yayi kiba Yana sanye da Shadda fara dinkin Tazarce da hula sai tashin Sayayyan kamshin Turaransa yake yi mai Dadin Shaka wanda Amina taji yana mata Dadi har Hancinta take Budewa tana kara shaka.. Gemunsa take kallo ganin ya kara Tsawo sai dai yana sheki yaji gyara sosai ya shagala da kallonta yaji ta jamai gemu da Sauri ya kalleta yana Waro ido tura baki tayi lokaci Daya ta kara Juya baya.,Mirmishi yayi kafin ya taka zuwa Gabanta yana kaallonta kokarin kara juyawa take yi ya rikota Cikin mararaicewar da baisan ya iya ba yace"Haba MEENA..a daure a fadamin Laifina mana..? Meenar da yace ne yasa ta Kallesa Cikin wani yayi a baya Aminu kadai ke kiranta da wannan sunan a kuma Lokacin sai taji yafi kowa iya Kiranta da haka sai dai yau sai taji Duk Duniya sunan a bakin mai Daraja wato Danmallam yafi dadi Lumshe ido tayi sannan ta Bude tana kallonsa hannunta Daya ya rike Dayan kuma ya Dafa Cikinta yana Fadin"Ko saboda Abunda ke Cikin ki Amina .! Baki ta kara Turawa kafin tace"Ba kai bane..Sai yau kazo ganina..! Sai ido ya kawo ruwa da Sauri yace"Am sory kiyi hakuri kinsan gajiyan hanya..Sannan kinsan Dole sai na natsa na samu natsuwa ko .? Amina ta Hura hanci tana Fadin"kuma ai baka kara kirana ba Tun ranar da kace zaka kirani. ! Sai hawaye sharr suka zubo baisan Lokacin Daya jawota jikinsa ba ya Rungumeta har Cikinta na Dukansa bai Damu ba kam ya rumgumeta yana jin wata natsuwa da salama abun mamaki itama hannayenta tasa ta Zagayo bayansa ta rikesa kanta ta baje saman kirjinsa domin sai taji kamar ta samu kafadan data Dade tana nema domin tayi kuka ta kauda kuncin zuciyarta yau ba yaya aduniya ita kadai ce zata kwanta ajikinta tayi kuka son ranta to sai Mijinta Datake ganin bata da kamarsa sannan yasan abunda ke faruwa yasa ta barke mai da kukan da yayi wata Biyu yana cinta acikin ranta,Lallashinta yake yi da sigar Shafa bayanta zuwa kanta yana dan jijjigata,ammh kamar ana bude mata famfo haka ta saki kukan nata riri riri sai ya rude hankalinsa ya tashi daman tun Fil"azal shi bamai son kuka bane ballatana Hayaniya,Sannan kukan ma irin na Amina duk sai yaji ya Durbuce haka ya sake kamkameta yana fadin"Shikenan is ok..Daina kukan na amsa Laifina..! Ina bata ma jisa ba kuka take har da Shessheka sai ya fara tunanin kukanta ba na iya fushinsa bane akwai wani abu cikin wata irin murya yace"Uhm fadamin me ya faru..? Cikin kukan Amina tace"Ka da ka hanani kuka ka barni nayi..Nayi watanni ina fama da nauyi acikin kirjina bansan kafadan da zai tallafamin in yi kukana sai yau..Don Allah yaya Danmallam kar ka hanani kukana.. abu mafi ciwo da Mamanmu tamin arayuwata na iya Tsawon rayuwata bata barni nasan Dadin Uwa ba..Yaya..YAYA bata taba sanin jin dadina ba sai akasin haka har ta koma ga Allah ya kake so nayi..? Taya zan manta wannan zaluncin Datamin.?anan zuciyata ke min zafi kamar zan mutu..! Tafada tana gunjin kuka Lokaci Daya tana Dora Hannunsa saman kirjinta Wani Tsausayinta da sonta da baisan ma akwai aransa ba ya taso ya fara share mata hawaye da Hannayensa yana Fadin"Ki yi kuka ammh kadan bamai yawa ba kin ga dai bake kadai bane ko..? Bazan yafe ma kaina ba in wani abu ya Sameki keda abunda ke Cikin ki ba Amina .! Amina ta kamkame Hannayensa tana Cigaba da kuka kamata yayi rumgumeta yana fadin"Ki yi kukan dai kadan na Samun saukin zuciya Kafadata da kirjina da Hannayensa zasu miki garkuwa har Abada..Kiyi hakuri ki ma yaya addu"an Allah ya jikanta kuma ni nasan har ta koma ga Allah addu"a take miki bazata taba aibataki ba. ! Jin haka yasa ta kara barkemai da kuka Tana fadin"Shikenan sai a barta ta kashemana uwa kuma tana zaune lafiya..? Hannunsa a bayanta yana shafawa yake fadin"A"a ai Allah ne zai fara mata hukunci da ita da duk wanda suka hada hannu wajen kashe rai Amina..Duk da munsan Allah ne mai kashewa kuma ya raya ammh su sun zama Sanadi in har sun aikata wannan girman laifin Allah bazai bar su cigaba da zalunci ba sai ya Tona musu asiri kowa ya gansu sannan zasu yi rayuwar kaskaci domin hakkin Rai bazai barsu ba..! Amina tace cikin kuka"Insha Allahu sai sun Dai'daita aduniya sai sun wulakanta.. Ganin tana neman fita Hayyacinta yasa ya Dago kanta sai ji kawai tayi ya Toshe bakinta da nashi Lokaci daya ya fara sumbatarta kamar Allah ya aikosa cak ta nemi kukanta ta rasa Ta waro ido tana kallonsa shima ita yake kallo yana jin yadda zuciyarta ke faman Bugawa tare da nashi Amina bazata iya ture wannan lamarin ba,Bata san sadda ta lunshe ido ba ta tallafi Hannayensa domin taimakamai shi kanshi yayi hakan da niyar ta natsu sai gashi ya Zarce bai sani ba Daga baki ya koma ya rikice yana Taba duk inda Hannunsa yakai mamakin jin yadda hannunsa ya Cika da kirjinta yake yi Cikin Fitan hayyaci yace"Amina sun kara girma k'wai na mai kyau ne..Aminana ta tashi daga mai Nonon lemon tsami ta koma na kankana .! Yana fada yana damukansu Amina ma jinsa ai ba baka sai kunne Tana karban wannan sakon sosai fiye da Tunaninta duk da na farkon haduwarsu bata fahimci komai ba saboda farko ne alokacin Sannan abun da ya faru ya faru ne dukkansu batare da sun tsammanci Faruwarsa ba. Shiyasa wannan karon bata san ta Saki jikinta ba,Kuka kuwa Tsab ya tsaya ta nemesa ta rasa tana jinsa yana mgana sama sama bata ma fahimcesa ba sai kara shigewa jikinsa take yi kamar wata mage neman rasa natsuwarsa yake yi domin wata irin bukatuwan kasancewa da Amina ne ya taso mai kamar an mai Tuni ya Tuna da gidan Aisha fa kuma kanwa take garesa yana kokarin Daidaita kansa yaji ana knooking da Sauri ya Raba Amina da jikinsa kasa Tsayuwa tayi sai ta koma ta zauna bisa gado ta juya baya shi ya yafa mata gyalen rigarta sannan ya bada izinin shigowa Ya Aisha ce ta shigo da Faranti shake da kayan kari Dan mallam ya tarbeta ya amsa yana mata sannu ta amsa Amina ta kallah wacce ko juyowa batayi ba sai yanzu kunya ya kamata na aikin data aikata. Dariya kawai tayi Danmallam yace"Ina Aliyu..? Aisha tace"Yana falo shi da Yakaka yana cin abinci naka ne wannan..! Danmallam ya kalli Amina kafin ya kalleta yana fadin"ita fa..? Ya Aisha tace "Ai bata cin abinci iri iren wannan ga wainar fulawanta chan Saude na soya mata. ! Sai alokacin ya tuna da Sakon Hajiya kai Tsaye yace"Kice ma Aliyu ya Dauko Sakon Hajiya da wata leda a Mota. ! Aisha ta amsa mai da toh ta fita tana Fita ya Zauna akasa ya tankwashe kafa yana kallon Amina kasa kasa Dariya ta basa ganin yadda ta kara juya baya baki ya rike kafin yace"bayan kin gama Damuka ni kuma miye na juya baya .!? Ai tana jin haka sai ta kara juya baya kunya kamar ta nitse dariya yayi da sai da taji Sautinta aransa kuma fadi yake yaro man kaza. Farantin yaja gabansa tea ya hada ya sha sai Dankali da kwai da yaci duk Amina na zaune ta juya baya Lokaci bayan Lokaci tana satan kallonsa sai zai juyo sai ta kauda kai shi kuma yana Lura da ita Dariya da sha"awa take basa. haka kamar bazata aikata irin abubuwan data aikata ba. Sai da ya natsa sannan yayi Hamdala ya Ture farantin gabansa wayarsa ce tayi kara kidan Larabawa a gaban aljihunsa ya Dauko yaga Sakina ke kiransa satan kallon Amina yayi kafin ya Daga kira suka gaisa da Tambayan Hanya sai ta bama Sarood suka sauya Yare zuwa Labarci Amina tunda ya fara mgana ranta kawai sai ya baci yana Sauya yare ta mike fit zata fita Daga Dakin tana kunkuni tace"In dai akayi gulma ta dai ban yafe ba..! Yajita sarai yasa ya rike hannunta tazo zata gifta ta gabansa tana Dagowa yana mikewa sai ji tayi ya kara rike hannunta gam yana kuma cigaba da wayarsa. Sai ga ya Aisha ta shigo ta kawo leda babba Daya sai karama guda Daya ganin yanayinsu yasa ta fice da Sauri tana ma Amina sigina duka yana ganinsu. Har ya gama wayar bai saketa ba sai da ya maida wayar aljihu yana kallonta bata san sanda ta ballamai harara ba Dariya yayi yana Fadin"kikace in anyi gulmarki baki yafe ba. ? Ido ta Zaro Cikin mamaki tana Fadin"Ni..? Kanta ya shafa yana fadin"Eh ai na jiki..Bama su san wajen ki zan zo ba..! Amina ta tabe baki batayi mgana ba Cikinta ya shafa sannan ya Duka agabanta yana kallonta ita da Cikin kunya ya bata ta yi saurin kauda kanta Kansa ya kara jikin cikin yana Fadin"Assalamu Alaikum...Ana Abbuka! Ya fada yana manna ma Cikin Kiss Sai ya bata Shawa"awa tana chan ta shagala da kallonsa sai da taji itama ya mata peak a kumatunta sannan ta farga ta Hura hanci ta tura baki Bai biye mata ba domin kada tasa ya aikata abun kunya. Ledojin da Aisha ta shigo dasu ya Dauko ya kawo gabanta ya bata na Hajiya bayan ya fadamata daga Hajiya sai nashi yace Tsaraban madina da kayan bbys daya siyo suka Zauna akasa suna ganin kayan sun mata kyau matuka Amina sai Daga wani Overrol na Jarirai take yi tana Fadin"Ya Danmallam yanzu jaririn da zan haifa wannan zai shigesa..? Yana Dariya yace"Sosai yara suna jariri basu da girma ba kina ganin su ba..? Ta gyada kai tana Daga kayan nata ya Nuna mata yana fadin"Basu miki kyau bane .? Ta amsa tana fadin"Wlh sun hadu nagode sosai kamar kasan bana sa atamfa yanzu sai dogayen riguna tun ina gida suka min kadan. ! Kallonta yayi kafin yace"Nagani kin tashi Daga kwaila kin koma Big mama. ! Kunya taji ta sunkuyar dakai suna Dariya. Shi ya kwashe kayan ya maida mata aledan sannan ta bude na Hajiya ai bakinta sai yaki Rufuwa ta fara Cin ramar tana fadin"Wlh Daman ina ta neman abu mai tsami tsami Allah Sarki Hajiya..kwalkwal tayi zatayi kuka yayi saurin cewa"To miye abun kuka kuma.? Keda kike da jidalin kuka..! Sai tayi Shuru itsace cin rama cin Zogale gutsiran yalo gatsan goriba sai murna take yana ta kallonta Cikin sha"awa. Kai tsaye yace mata"Kawayenki kawayen jidalin ki Hanne da Hamida na gaisheki..! Amina ai sai ta Dagata da Ciye ciyenta tana fadin"Da gaske..? Kai ya gyada mata yana fadin"Sosai ma..Har hira ma mukayi suka bani labarin Aminene ikon Allah..Har da Labarin Anty Sara mai Warin maza.! Amina ta zaro ido tana Dariya shima Dariya yake yi yana fadin"Kinganki wlh bakya jin mgana Allah ya shiryamin ke ! Dariya take yi tana bashi labarin yadda Anty Sara ta Dinga kuka Data ji labarin an ce tana warin maza har fa irin nganar ta saida Amina ta kwatanmai kallonta kawai yake yi yana jin Dadin ganinta Cikin Farinciki. Bai san Lokaci ya tafi ba sai da yaga biyu na rana yayi ya mike yace mata su yi sallah shi ya taimakamata ta mike suka shiga tiolet tare ta fara kama Ruwa kuma yaki fita tana tajin kunya ya kalleta yace"Ji min yarinya ke da na sanki Ciki da baya kina kwailarki ma..! Ai bata kara mgana ba tayi Fitsari tayi Tsarki tayi alwala ya taimaka mata ta fito Shi kuma ya koma yayi alwala bayan ya kama ruwa shima,Tare sukayi sallah ya jasu jam"i suna Idarwa ya jawo Amina jikinsa ya fara Tabata haka kurum yaji yana Bukatar jinta akusa dashi ita kuma batamai gaddama ba ga karatun Ya Aisha ga mganar Aba data Zauna aranta tun ranar da zasu tafi yace in tamai gardama bai yafe mata ba. Itama ta lula Cikn wata Duniyar sai karar wayarsa suka ji kamar Daga sama shi ya katse ma Umar hanzari bai saki Amina ba ya Daga kiran ganin Aliyu yana Dauka yace mai"Lafiya..? Aliyu yace"Kai shehi kaji tsoron Allah..Gidan fa kanwarka kake..? Ka shige kurya da yar mutane kana Lalubeta. ! Tsaki yaaja ya kashe wayar yana kallon Amina data boye kanta cikin kirjinsa Dagota yayi yana fadin"zaki bini Amina..? Cikin wani yanayi tace"Ina..? Bai mata mgana ba ya taimaka mata ta mike ya Dauko mata hijabinta Dake kan gado ya saka mata yasaka mata takalmi Daya gani bakin gado yaja Hannunta suka fita Daga Dakin. Falo ba kowa Aisha na Dakinta ita da Usman Yakaka ta shiga Dakin Amina tayi sallah bayan Aliyu ya tafi Sallah Dakin Dake yammah acikin falon na Saukan baki. Awaya Umar ya Kirasa yana Dauka yace"Fitomin da key din motarka..waje..! Daga haka ya ja hannun Amina suka fita Daga falon bayan ya katse wayar. Aliyu cikin mamaki ya fito haraban dan madaidaicin gidan yana kallon Umar Dake jiransa yana zuwa a bakin motar yaga Umar da Amina har kuma Lokacin yana rike da Hannunta. Aliyu ya rike haba zai yi mgana Danmallan ya warce key din a Hannunsa Amina kunya ya kamata ta kasa Motsi hannunta yaja sannu har inda zata shiga mota bangaran mai zaman banza ya Danna wani abu jikin key din motar ta Bude ya bude mata ta shiga ya taimaka mata ya zagayo bangaren Direba zai shiga yana cema Aliyu"To na bar gidan kanwata sai ka hanani shakatawa da Matata..! Daga haka ya shiga ya kunna Motar yayi hon megadi ya Bude masa get ya sulala waje ya bar Aliyu da baki sake yana yar Dariya afili ya furta"Shege Shehi..Ya dirkama yarinya ciki ya Lallabo zai kwashe romon..! *Janafty**TFZB2021* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Batayi mgana ba sai da taga sun fita Daga anguwan sun dauki Wani shararren Titin garin na Abuja sannan ta kallesa hankalinsa na wajen tuki tace"Ina zamu..? Bai kalleta ba yace"In bazaki je ba kada na Takuraki sai mu koma..! Kallonsa tayi sai taji bazata iya mai gaddama ba yasa kanta na kasa tace"A"a zan bika.. Mirmishi yayi kafin yace"Kinsan dai bazan cutar dake ba ko..? Ta gyadamai Alamar hakane kai ya jinjina kafin yace"Good. ! Da haka basu kara mgana ba suna dai tafe kawai kowa da abunda yake sakawa aransa ba wani sanin garin Abuja yayi ba saboda shi bai yi Cikakken rayuwarsa anan ba gwarama Gumel da Dutse da Jigawa su zai ce yadan waye acikinta ammh banda nan sauran sai dai Ilimi da karatu su fitar dashi. Cikin ikon Allah suna cikin tafiya yana Dube dubensa suka samu wani Hotel saman Hanya kai Tsaye nan yayi kwana ya shiga Cikin motar ya barta ya shiga bayan wasu mintina sai gashi ya Dawo ya bude mata kofar mota ta fito ya taimaka mata suka shiga ciki. Daki mai lamba 206 ya kama musu Amina sai mamakin take yi tana faman kalle kalle tasan ai nan din Hotel ne domin ta karanta ajikin Sambol din kafin su shigo ita sai dai taji hotel a Littafi bata taba zuwa ba sai yau shi ya Bude Dakin yajata suka shiga sannan kuma ya sake rufe kofar ya jata har saman gadon Dake Dakin ya Zaunar da ita Lokaci Daya ya jawota ya Rumgumeta yana Sauke Numfashi. Ai basai yayi mgana ba yanayin yadda ya fara aika mata sakonsa cikin gaggawa yasa ta Fahimci yana matse da ita ne tun suna zaune har ya jata kan gado bayan ya cire mata Hijabin jikinta Amina kan tayi lamo tana karban sabon karatun ya Danmallam gareta. Bata dawo hayyacinta ba sai da tafiya da mika sannan ta fahimci karatun sai ta tuna wahalar data sha ranar farko sai ta fara kuka tana kokarin kwatan kanta ammh ina is too late a wajenta Domin alokacin kome zatayi bazai iya kyaleta ba sai dai yana ta binta a Hankali bai bari ya rasa natsuwarsa ba Duka ganin yanayin datake ciki. Jin yadda jikinta ke rawa yasa ya kamkameta cikin kunnenta ya rada mata"Ki saki jikin ki Amina..Bazan miki da zafi ba.. Amina na Hawaye tace"Don Allah kayi hakuri wlh da zafi..Wayyo.! Bakinta ya hade da nashi kawai ya saka kai sai dai ya sha mamaki yadda wajen ya koma ya Hade kansa sai da ya sha wahala kamar na farko sannan ya iya shiga Amina taji azaba na Ratsata awanchan ranar komai ya faru kamar a mafarki ne bazata iya tuna yanayin azaban ba ammh sai taji kamar wannan ya fisa zafi Dakewa tayi ta kwace bakinta anasa ta sakarmai kuka fadi take"Wayyo..Wayyo..Ya Danmallam kayi ma girma ka bari da zafi..! Yana fizgar mganar sama sama yace"Shii..A hankali zan yi..baki ji ba .! Yake fada cikin fitan Hayyaci da Sauti daganan ya kara toshe mata baki da nata ya cigaba da kokarinsa. Tun Amina na hawaye har ta bari ta koma tana sauke nunfashin azaba ba kadan ba tajiki Saboda Sau daya tasan harkan bayan nan kuma an Dade ba"a Hadu ba.. Danmallam wannan karon sai da ya More sosai ba kamar na farko ba,Sannan ya koma lallashi Amina na sharan kwallah ta juyamai baya tana Tura baki rumgumeta yayi yana bata Hakuri Amina tace cikin shakewar murya"Ina ta cewa wayyo da Zafi..ko ka jini sai ma awani Toshe ma mutum baki ake yi a hanasa kuka.!. Sai tasamai kuka kara riketa yayi yana Fadin"To yi hakuri ban ji bane..Kuma ai nayi miki a Hankali ko..? Wani Harara ta juyo ta makamai da yasa yayi Dariya har sai da taji Sautinta ya cusa kansa a wuyanta yana Shafa Cikinta Lokaci Daya yana Fadin"Allah yayi miki albarka Aminene..Nagode sosai Shukran. ! Haka yake ta sakamata albarka wanda albarkar dayake saka mata yasa ta yi Dauriya bata kara nuna Rakinta ba tare sukayi wanka duk kunyar Amina Danmallan bai biye mata ba shi ya taimakamata Tana sunne kai yana Dariya yace"Kina bani mamaki yarinya da tun kina Kwailarki nagama ganin komai..! In yace haka kunya kamar tayi yaya shi kumyar nata ke basa shawa"a domin Sakina bata san kunya ba to har gwarama Sarood basu san kunya tana kara miki Daraja da soyayya wajen mijinki ba. Alwala suka Dauro sukayi sallar La"asar atare suka koma saman gado suka kwanta suna Hira duk yawanci Labarin gida suke yi sai jin Dadi take yi yana mata Hiransu hanne ta Saki jikinta suna ta Labari suna Dariya ahaka ya kara shammanta ya kara sai da tafiya tatafi taso ta turje bai bata Dama ba da tana kuka ce mata yayi wai saboda wajen ya saba ne saboda Sakacinsa wajen bai goge ba sosai mamaki take yi haka ya Danmallan Daman yake bata sani ba..? Zuwa Dare ta galabaita sai da yaga zata Faramai Ihu sannan ya kyaleta suka je sukayi wanka sai da ta shiga ruwan Zafi ta gasa kanta Tausayi ta bashi ganin yadda take tafiya ammh kuma albarka ta shashi har sai da ya fara bata Tsausayi sai ta Daina Raki Saboda bata so yaga kamar da gangan take mai kuka shi kanshi yasan ta gaji kuma tayi kokari dashi shiyasa ya kyaleta ko waje basu kara fita ba nan sukayi sallar Mangarba da isha"i suka yi Jam"i tare. Oder din abinci yayi musu Amina dai Tea kawai tace zatasha yana kallonta yace"kina da shan zaki ko..? Batayi mgana ba sai chan tace"Bazamu koma gida bane ya Danmallan..? Yana gefenta yace"Kina so ki barni ki koma ne..!? Kallonsa tayi batayi mgana kawai sai ya ji ta ja gemunsa Waigowa yayi yana kallonta cikin wani yanayi yace"Da zafi fa Amina. ! Tana dariya tace"Sha"awa yake bani..! Kallonta yayi kafin yace"Da gaske .? Ta dagamai kai Goga mata gemun yayi a wajen hancinta zuwa Kumatunta yana fadin"ai naki ne kiyi yadda kika ga dama dashi..! Kallonsa tayi kafin ta batarai tace"Ba nawa bane ni kadai..! Cikin mamaki ya Dago yana kallonta kafin yace"To keda waye..!? Gani tayi ma ya raina mata wayau kawai sai ta yi mai Fuska ta juya mai baya kallonta yake yi yana auna Shekarun Amina tasan kishi..? Bai samu zarafin mgana ba aka yi knnoking an kawo abunda yayi Oder Tea ne sai fatan dankali mai ruwa ruwa Tea din kadai Amina tasha yayi yayi taci Faten Dankali taki tace Amai Zatayi sai ta kyaleta. Misalin Tara na Dare Aliyu ya kirasa a waya lokacin suna kwance da Amina tana kan kirjinsa kamar ma har ta fara barci a hankali ya Dauki Wayar Dake gefensa ganin Aliyu ne yasa ya Daga Aliyu Daga bangaran Gidan Aisha acikin Dakin da aka Saukesa Tunda dai Umar ya tafi da matarsa. Yana Daga Kiran Aliyu bai jira cewarsa ba yace"ai ka kyauta..Ka daukoni Daga gida kazo nan ka barni a gantale kai kuma ka Dauki matarka kun tafi chan kana jin Dadin ka ni kuma ko Oho ko ka kira kace min ba yau zamu koma ba .! Umar yace"to sai na Fadamaka damam ba yau zamu koma ba..? Hankalinka bai baka Haka ba..? Aliyu na yar Dariya yace"Kuma fa hakane..An dade ba"a hadu ba wajen akwai Danko ko shehi..? Tsaki Umar yaja ya kashe kiran yasan Halin Iskancin Aliyu in fara bai san ya bari ba. Suna gama waya da Aliyu Kiran sakina ya shigomai sai ya duba yaga kamar barcin Amina yayi nisa sannan ya Daga wayarta sukayi mgana suna ta mai koken wai suna ta jiransa sun ji shuru sun kira wayarsa bata shiga sai da suka kira Aliyu yace musu sai gobe zasu dawo. Yace musu eh sun yi dare sai gobe zasu dawo Duk Amina na jinsu har aka bama Sarood ya sauya yare sukayi mgana Daganan sukayi sallama ko kafin ya gama wayar Amina ta mike ta shiga bayi ya bita da kallo sai da ya gama wayar ta fito ko kallonsa batayi ba ta Hade rai sai yasha Jinin jikinsa sai kuma yaji bai kyauta ba meyasa bai fita waje ba..? Yadda ta Hade rai yasa ko mgana ya kasa mata bata kwanta kusa dashi ba sai tayi mai kwanciyaer kai da kafa yana ganin haka yayi mirmishi aransa yace za"a buga da Amina kenan.. Bai yi fushi shi ya bita ya kamkameta yana mata rada a kunne ta yi kamar bata jisa ba tana Turamai Baki aranta tana fadin yama rainata yana kwance da ita yana waya da Guzumayen matansa. Bakin Datake turamai ya kama tsotsa daganan sai wasan ya sauya,bai dai mata komai ba ammh dai ta sha Jagwalgwala,sai da ta faramai kuka sannan ya kyaleta suka kwanta sukayi barci da asuba bayan sun idar da salla ya lallabata ya koma ya kara kwasan Danko ta bakin Aliyu sannan sukayi wanka suka koma barci sai goma na Safe suka tashi yayi musu Oder din abun kari Aminaa dai taki cin komai tace sai sun koma gida taci ramarta da Zogalenta Umar kuma wayarsa ya kashe saboda bayaso Aliyu ya Damesa.. Amina taso su koma gida tun Safe bai barta ba sai wajen uku na rana shima ganin bata ci komai bane sannan shima haka ya rabeta ya lallaba ya kara kadan sannan suka sake yin wanka sukayi shirin tafiya. Kamar jiya shi ya rufe Dakin ya riko hannunta suka fito sai da yakai mota sannan ya koma ya sallamesu ya Dawo suka Dauki hanya. Basu isa gida ba sai da ya Tsaya wani kanti ya siyan mata kayan Zaki Chaculate kala kala sai wanda ya manta,da sauran kayan kwalama Sai Hudu Saura suka shigo gidan. Aliyu ya cika fam saura Kiris ya Fashe Usman baya nan sun fita da Aisha zuwa Gidan wani abokinsa Aliyu ne kawai da yakaka agidan suna Falo sai mai Hira suke tana ganin Amina ta fara musu maraba tana Fadin"Megida tafiya kuma jiya ba Sallama..? Kai ya sosai bai yi mgana ba ya Duka yana gaisheta ta amsa Cikin Fara"a Amina Daki ta nufa bata ko gani Saboda yunwa bata ga sakon Hajiya ba ta fito tana Tambayan yakaka Aliyu da Danmallam basu afalon sun fita waje. Yakaka tace"To ki tambayi Saude kila Aisha ta kwashe miki..! Kitchen ta shiga suka gaisa da Saude ta Tambayeta sai tace suna cikin Fridge,tana budewa ta gansu tasan aikin ya Aisha ne a kitchen din ta samu Roba ta Hada rama da Zogalen ta saka yaji da kuli da magi taci ta koshi ta kora da ruwa ta koma Daki ta iske Yakaka na sallah itama alwalan ta Dauro tazo tayi sallah. Tana Idarwa Yakaka sai kallonta take yi Amina ta tura baki tana Fadin"Wai na Chanza miki ne da kike ta Kallona haka..? Yakaka ta tabe baki tana jan Carbinta tace"Kya ji da gulmarki. Amina tatashi ta Hau gado ta kwanta Domin ta gaji matuka badadewa sai ga su Dannallam sun shigo har Dakin yima yakaka sallama zasu tafi ta rike baki Tana fadin"Da yamman nan..? Na zata fa sai gobe ga su Usmanu basu nan ai kwa jira su kuyi Sallama ko..? Aliyu yace"zamu yi musu a waya Baaba..Saboda wajen aikin mune akwai matsala..! Jin haka yasa tace"In hakane kuna da gaskiya ai ma mungode Allah ya bar zumunci Allah kuma ya kaiku lafiya..! Suka amsa mata da Ameen Ameen Aliyu 5k ya bama yakaka Umar ma haka ta ki amsa suka matsa sai data amsa tana ta musu godiya,Da kuma godiyar Ruwan zamzam da Dabinon da suka kawo musu jiya taji Dadinsa matuka. Danmallam ya mike yana kallon Amina data juya baya tana barci yace"Baaba barci take yi ne..? Yakaka ta kalli Amina kafin tace"Waya sanin mata ko duk tana jin mu..? Ko da fa kuka shigo sai wani Ture turen baki take yi kalli ledan chan data shigo da ita inda ta watsar..! Mirmishi yayi kafin yace"Shikenan tunda ta kwanta a kyaleta zamu yi waya..! Yakaka taso a tada Amina Danmallan yace ta kyaleta har Waje ta rakasu tana musu godiya sai da taga motarsu ta fita daga gidan sannan ta koma cikin Gida Daki ta koma ta leka Amina taga barcinta take sha sosai Yakaka na yar Dariya tace"Yar nema waya gayamiki Borno gabas take..! Ledan data shigo dashi ta Duba duk kayan Zaki ne ta tabe baki tana Fadin"Shi mai ya kaisa biye mata..? Ai munan hanata shan zakin nan muke wajen haihuwa nake jiye mata zaki yayi mata yawa ajiki mu shiga uku..! Guda Daya ta Dauka ta Bude ta faraci tana Tabe baki sai gashi ta Cinye har da kari tana Fadin"Abun kuma Dadi ne dashi..! Su Aisha sai dai suka Dawo sukaji Tafiyar su Danmallam ya Aisha bataji Dadi ba sai da ta Kirasa a waya sukayi sallama Amina kuma har Lokacin bata tashi ba tana ta barcin gajiya yau din Daga yakaka har Aishan ba wanda ya Takuramata ko miye Dalilinsu..? Sai da suka Dauki Hanya Sosai Sannan Aliyu ya juya yana kallon Danmllam Daya kwanta jikin kujeran mota yayi shuru kamar wani mara Lafiya. Aliyu yayi dariya kafin yace"Ko zan zauke ka ne ka koma..? Umar ko kallonsa bai yi ba ballatana yasan yana mgana sai da ya kara saka Dariya sannan ya gintse fuska yace"Shehi How comes abubuwa suka faru haka banda Labari..Amina nada Ciki dawowarta Abuja da sauransu..? Bamu taba mganar dakai ba..! Yafada yana maida Hankalinsa wajen Tukin Dayake yi. Sai alokacin ya Dago jin Aliyu yayi Serious mgana Cikin sanyinsa yace"Nima haka abubuwan suka zomin a bazata Aliyu..!. Nan ya shiga bashi Labarin abunda ya faru,tunda ga farko har karshe ya karishe da Fadin"Hajiya ce ta kawo Aminan nan sannan ta hana Fallasa Cikin a wajen kowa Dagani sai ita sai mallan sai kai yanzu dana Fadamawa ko Baba Sa"idu mahaifinta bai san Amina dana ciki ba kuma baisan tana Abuja ba..bansa Dalilinta ba Domin Dagani Har mallam batace mana komai ba.! Aliyu yace"Alamarin Allah ya wuce wasa Shehi..Ba wanda ya taba Zaton haka..! Danmallam yace"Whl kuwa..! Aliyu yace'"To Allah ya raba Lafiya..Hajiya kuma tana da Dalilinta na sani sannan ni kaina sai naga hakan is Better fa..! Umar ya kallesa kafin yace"Meyasa kace haka..? Aliyu yayi mirmishi idonsa na kan Tuti yace"Araina naji hakan da tayi shine Daidai sannan hauwasa na Fadin abunda babba ya hango yaro ko yahau Rimi bazai gani ba..! Ko mgana Danmallam bai karamai ba sai suka bar ma wannan mganar suka shiga wata Hirar har suka iso gumel bayan Isha"i,Agidansa Aliyu ya ijiyesa ko shiga bai yi ba adaran ya juya Dutse. Sakina tayi ta rawan jiki dashi yayi wanka yayi Sallolin Dake kansa yaci abinci yace zai kwanta Dole ta kyalesa Sarood daman tana Falo bata cusa kanta ba ganin Sakinar ta tare komai sai ta mata uzurin ai ita suna Tare wattani achan ita kuma na dan Lokaci ne. Sai Washegari yaje gidan mallam su Hajiya suka gansa yace sai jiya suka Dawo ya tabbatar musu da Amina tana lafiya tace agaishesu da Aisha mallam yaji Dadin haka shi da Hajiya Duk da Hajiya tasan daman Amina Zata samu kulawa sosai a inda ta kaita Hanne da Hamida ma ya basu Sakon Amina na gaisuwa,ammh ya gargardesu kada su fadama kowa yaje wajen Amina sukace bazasu fada ba Hankalinsu ya kwanta Tunda Amina na Cikin koshin lafiya. Aranar Amina ta kirasa suka yi mgana ta Tambayesa ya suka sauka yace Lafiya lau basu yi wani mgana ba suka yi sallama Har alokacin Amina Haushinsa take ji baisan me yayi mata ba ita ko Tunda yace zai tafi bakin ciki ya isheta in ta tuna inda zai koma shiyasa tayi kwanciyarta kamar tana barci da zai tafi Ahalin idonta Biyu bata son tatashi din ne. Shima ganin yanayinta sai bai matsa mata ba,shirin tafiya ma suka fara domin yana ta Cukun cukun nema musu Visa, cikin ikon Allah kuma an samu Visar da wuri zasu tashi nan da kwana Hudu tunda ya fadama Amina zai koma da Sakina da Sarood Amina ta Daina walwala a kaduna Ya Aisha duk tasan Dalili itama abun na Amina ma Dariya yake bata wani Lokaci kishi sosai take yi in kuma an ce tana son ya Danmallan tace atafau ita bata son shi. Ana saura kwana Biyu su koma ta Tadamai hankali awaya tana kuka Dole washegari ya taho Abuja da kansa ya Tuko kansa sai dai suka kara ganinsa kwatsan jidalin Amina yayi kira,Ranar bai kwana ba ko Awa Hudu bai yi ba ya Samu ya lallashi Amina ta Daina kuka bai dai yi shagalinsa chan ciki ba sai dai ya sha Shagalimsa Daga sama kuma bata Hanasa ba sai ma ta taimakamasa,Da wuri ya tafi bayan ya bata kudade a hannunta saboda Tasowar wani abu Amina kuka riris take yi kamar karamar yarinya mamakinta kawai yake ya rumgumeta yana lallashinta yana Fadin"Da Hajiya zata bari da na tafi dake Amina ni kaina ina Bukatarki kusa dani..! Baki Ta tura tana Hawaye tace"In ka tafi yaushe zaka Dawo..? Yana rike da Hannayenta yace"Wlh bazan Dade ba ai nasan Halin da na barki ga kuma waya ZAMU dinga mgana da juna kin ji ko..? Kai ta gyadamai tana share kwallah ya taimaka ya share mata Cikin salonsa Sannan ya kalleta Cikin ido yace"Zan yi kewar ki Aminata..! Baki ta Turamai kafin tace kasa kasa"Uhm in guzumayen matanka sun barka kayi kewata ba. ! Yajita sai da ya Bude baki yana kallonta da Sauri ta juyamai baya yafa riga ya sani Amina kishinsa take yi dashi da matansa ba nawa wasa ba Na Sakina kadan ne. Juyo da ita yayi ya kama bakinta ya tsotsa sosai sannan ya saketa yana Fadin"Ba ruwanki da matana..Ai nasan dasu nazo wajenki Tundaga Gumel Amina..? In kikace haka sai naga kamar ban yi miki adalci bane .? Ganin ya Damu yasa ta fada jikinsa ta Rumgumesa sai Hawaye tace"Kayi hakuri..! Yana shafa bayanta yana fadin"Baki tabamin komai ba..Sai kuka ne kadai Tsiya na Dake kuma shima na yanke shawaran ki gayamin kudinsa na siyesa na Huta.!. Tana Dariya tana Dukan kirjinsa yana Tayata ganin zai bata Lokaci yasa ya saketa yana fadin"MEENA zan tafi..! Kanta na kasa tace"Allah ya kiyaye hanya..Allah ya tsareka. ! Ya amsa da Ameen cikin sanyinsa har ya juya ta rike mai riga ya waigo yana kallonta kafin ya sami bakin mgana ta Zo gabansa ta yi Dage ta kama Bakinsa da Hannayenta ta yi mai Dogowar sumba sannan ta a sakesa tana sharan hawaye ta shigo Tiolet ta kulle sai da ya tafi ta fito duk ta sha kuka ya Aisha da yakaka na mata tsiyan bata som miji tana kuka zai tafi sai ta kara fashe musu da kuka ji take yi kamar zata mutu shikenan sai tayi wattani zata sake ganinsa..? In da ma shi kadai ne achan da sauki ammh har da matansa fa shine karin Haushinta.. Shi kanshi Danmalllan in za"a bashi Zabi Tsab zai ijiye sakina ya tafi da Amina sai da bamai zai fara ba Hajiya bazata taba yarda ba,Wlh har acikin Ransa yake jin mgana washegari jirgin yammah suka bi zuwa Jidda kamar an zare mai lakka haka yake ji bai da karsasashi kan tafiyar har su Sakina sun fahimta. Anty Amarya dai sai hamdala domin Hankalinta bai kwanta ba sai da Sakina ta kirata tace sun sauka a madina sannan taji Ta Sauke numfashi ta gama da wannan bangaran yanzu Haj.Uwani zata nuna ma bata isa ba zasu goga shege ka fasa..! Domin Taga alamar zata iya nasara akanta Tunda har yanzu Tare da Nazeem Aba ke komai abunda bata sani ba,Haj.Uwani ta fita sanin komai kan Dukiyar mallam,Domin zama take da Nazeem tana dukan ruwan cikinsa tana jin komai balle ma da Aba ya sakarmai bangaran Lissafi da Shigar kudi da Fitarsu Hajiya uwa ta gama Tsara taci nasara ma ta gama Domin ta fara hango kamshi hakan. Amina bata warware ba saibayan kwana Biyu da suka yi mgana Danmallan yace mata sun sauka Lafiya ya kuma bata Lokaci wajen bata baki adaran ranar ya kirata yamata bayanin yadda zata sha ruwan Zam zam din Dake ledan kayan Tsaraban Daya kawo mata yace duk Dare ta rika shafe jikinta ko"ina dashi ta yi addu"a in zata kwanta Tunda tace ta Daina Tsorata in tana barci. Sannan yace mata ta dinga shan ruwan Cokali uku Kullum arana sau uku ta sha da Bismillah da Fatan waraka a wajen Allah. Bata ko yi kasa a gwiwa ba ta fara yin sa kamar yadda yace mata sannan wani Lokacin in zata kwanta shi ke kiranta ya tuna mata watarana ma baya kashe wayarsa sai tayi sunyi addu"an tare ta kwanta sannan yake a kyaleta kuma Sakina ko Sarood ba wacce ya bari ta Fahimci wani abu yana Kafa kafa domin shima yanzu ya gane Dan adam ba abun yarda bane. Barin ma wanda kake tare dashi yafi Cutar Dakai. Bangaran Mamanmu kuwa babu abunda ya Shafeta harkan gabanta kawai take yi ta samu Duniya yadda take fata Hamida ne kawai agabanta Sai Jawaad data jasa ajiki saboda kada ta bada Fuskar da za"a zargeta itama Shawearan Madiina ce ta Dauka Aba kuma yanzu ba kowa agabansa sai Balaraba,Da shawarta yake komai ko Jafar ya fara ganin Sauyi domin sai sun gama mgana da Aba sai kuma ya sauya mgana in yace meyasa sai yace Balaraba ce tace in akayi kaza yayi..? Tun baya mamaki har ya fara ko yaya Lokacin tana da rai Aba bai taba cewa tace kaza ba ballatana mamanmu akan harkan da bai shafeta ba sai dai bai Taba mgana ba sannan Tsakaninta yaran Lafiyau suna waya ko da yaushe sun rike matsayin uwa harta da Jafar din kuwa Amina kuwa in ba hirarta akayi ba mancewa take yi da ita ke ma fada ma yan gusai Hajiya takai Amina maiduguri kowa yaji sai yace saboda mene .? Mamanmu tace ita bata sani ba to ba wanda ke Mgana sanin Hajiya ai bazata Cutar da Amina ba. Su Hamida sun gama WEAC suna Shirin Fara Neco har sun fara Sabawa da rashin Amina.. Ranar suna zaune afalon mallam Gabadayansu matan yaran ne kawai basa nan suna ta kallon tashar Labarai suna Hira sama sama. Anty Amarya ta kalli Haj.Uwa suka ma juna wani irin kallo kafin taa kalli Baba maalllam tana fadin"Mallan nace Hala dai Nazeem shi zai gaji Sa"idu awajenka kenan..? Kowa ya tsaya yana kallonta ita kuma da Biyu tayi saboda Uwani tasan matsayinta. Baba Mallam ya kalleta kafin yace"Bangane tambayar ba marliiya..!? Hajiya kuwa sarai ta gane Sai dai batace komai ba Huruminta bane. Anty Amarya tace"To ai gani nayi yanzu tare suke komai..kamar Sa"idun ya fara sakarmai komai..! Baba Mallam ya kalleta na wani Lokaci kafin yace"Cikin ku wake da Tunanin cewa watarana zan sauke Sa"idu daga kan dukiyata na Dora wani Cikin ya"yanku .? Dukkansu suka kasa mgana Haj.Uwani banda Hararan Anty Amarya bata komai ita kuma sai mirmishin nasara take yi.. Mallam ya kallesu Daya bayan Daya Cikin kaushinsa yace"To in ma wata Cikin ku na wannan Tunanin ta Ciresa daga zuciyarta..Dukiyar da Sa"idu ya sha wahalan tarata ba tare da Taimakon ko Daya daga Cikin ku ko na ya"yanku ba rana Tsaka kawai sai na Dauketa daga hannunsa saboda na Zama Butulu..? To ba haka nake ba..Nazeem yana samun aiki zai kara gaba daman saboda ya taimaka ma Sa"idu ne ba wani abu ba ko Mutuwa nayi yau RABIN Dukiyata ba tawa bace kuma sani Daga yau din nan..! Gabadaya suka kallesa da mamaki banda Hajiya da riga tasan Mallam ya Bama Aba Rabin duk abunda ya mallaka saboda mallam yace shi yayi walahanta tun yana matashinsa har Tsufansa.. Haj.Uwani Cikin wani yanayi tace"Na waye ..? Mallanm ya mike yana Fadin"Ta SA"IDU ce..Da iyalansa..! Komai yana nan a Rubuce yadda ya Bauta ma samuna ko Duka na basa ban biya sa ba..In ma zaku bama ya"yanku shawaran neman na kansu ku basu Dukiya dai tawace ba ta Daya Daga Cikin ya"yanku ba..! Daga haka ya tashi ya shige Hajiya tayi wani mirmishi ta mike ta fita Haj.Nasara ke da Turaka tabi maalllan Ciki akabar Haj.Uwani da Anty Amarya na kallon kallo. Haj.Uwani na kallon Anty Amarya kamar ta Tashi ta mata Duka itama ta mata Dariyan mugunta. Mikewa tayi ta isa gaban Haj.Uwani Tana fadin"Kin dai da kunnen ki ko..? Ko kina bukatar na kara sanar dake. ! Haj.Uwani ta mike ta bangaje Anty Amarya sai da ta kusa Fadi Cikin kaushinta tace"Wlh Tallahi ki sa aranki bani kadai zan rushe ba Marliya..Dukkamu sai dai mu rushe uban kowa ya rasa..! Daga haka ta fita Daga Falon kamar Zata tashi sama,Anty Amarya ta Bita da Dariya itama tabi bayanta ammh ko Ita Dariyan karfin Hali take Sa"idu dai shi gaba ta kaisa sannan Dayyaba ta samu Duniya Har takai shashenta Bakinciki ne ya Cika ka ita ta ma Dayyaba Hanya ta samu abunda take so ammh ita duk wannan Wahalan tana neman tatashi a Tutar babu..Tabdijam..Daman ai balaraba ta Rage neman ta ko wajen mallam sai dai ta Zagaya tatafi ita Kadai wato ta gama samun komai tana neman ta watsa mata kasa ido to bata isa ba kamar yadda Uwani tace ba Zata taba yarda ta rushe ita kadai ba sai dai kowa ya rushe.. Daga ita har Balaraba har Uwani indai ita bata samu Cikar nata Burin ba to sai ta tsawarwatsa nasu Cikar burin uban kowa ya rasa. *Janafty**TFZB2022* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Yau da gobe bata bar komai ba Daga yini mun shiga kwana Daga kwana sai a fara kirga kwanaki Daga kwanaki sai a fara kirga satittika Daga Satittika sai a fara kirga wattani to kamar haka ne tunda gashi har su Hanne sun kamallah duka jarabawarsu ta kamallah babban Sakandiri suna gida sai jiran sakamako sai dai basu Daina zuwa islamiya da Hadda ba Daga Umarnin Baba mallam. Har zuwa wannan Lokacin Daga ban garan Hajiya ba"a wani bayanin inda takai Amina ba,Sai dai irin Anty Amarya da mamanmu da sauran masu Tunani irin su suna Daukan Amina tana maiduguri sannan ganin Dadewa da akayi ba labarin takamammen inda Aminar take sai suke Tunanin auranta da Danmallan ne ya Lalace Hajiya ke son gyarashi. Ita dai ta koma gefe tayi bakam bata taba nuna tasan wani abu ba, yanzu in an isheta da Tambaya sai tace bata sani ba,Har Abida data isheta haka ta Fadamata har kuma ya Aisha ta kira sun yi mgana ammh bata taba ce mata Amina na wajenta ba ta riga ta rike alkawarin Hajiya da gargadin datake mata akoda yaushe kan Boye Cikin Amina da zamanta a wajenta. Anty Amarya ita da Uwani ake takun saka yayinda mamanmu ta koma gefe ta Zama yar kallo domin bata da wata matsala,In Anty Amarya ta Kirata sai ta mata Dadin baki da mganganun nasara ta rufe bakinta sai sun gama mgna ta rika mata Dariya Haj.uwani kuwa Amarya bata gabanta domin tana kallonta karamar alhaki ne badai Nazeem din na tare da Sa"idun ba har an sakarmai komai ba..? Maji mgani an tura uwar Amarya Biko ita har ta hango kanta a matsayin data Dade tana Hango kanta Tunda Dadewa. ***** Achan Abuja kuwa a bangaran Amina cikinta na cikin na wata Takwas kenan ta kara kiba sannan komai na Jikinta ya fashe hancinta bakinta komai ya kara girma sannan sai da cikin yakusa wattanin Haihuwansa sannan yayi wani irin girma Allah yasa tana da Tsaho ai da ya shanyeta,Tana cigaba da zuwa awo da ganin Likita In usman baya nan ita da ya Aisha take zuwa ko Zuwansu na karshen nan an tabbatar musu da Abunda ke Cikin Amina yana cikin koshin Lafiya. Amina in ta kalli kanta a madubi sai ta fashe da kuka wai duk ta sauya kamar ba ita ba watarana Yakaka tayi ta mata Nasiha ranar da yan Fada ke kusata ta mata fada ko kuma tayi mata bakam kamar bata jita ba. Kishin Amina akan mijinta ba irin na Sauran mata bane nata na Dabam ne akwai Tsabar jidali da neman rigima atare da ita koda yaushe suna waya da Danmallam domin yaji lafiyanta inda ta gane koma wani abu ne mamanmu ta mata ya fara rabuwa da ita ko tace ya rabu da ita gabadaya saboda ta gama amfani da duka mganin da ya Danmallan ya kawo mata Ta daina jin zafin zuciya da kunci sannan ta rage Taurin kai da Kafiya ammh fa bata rage rashin Tsoronta ba Sannan bakinta bai mutu ba Jidali kuma ta gama Fahimtar Halintarta ne sannan kuma Hali ai zanenn Dutse ne.. Ita yanzu ban da su Hanne da Haamida da Hajiya da mallam to sai Aba duk ba mgana take yi dashi ba yana ranta tana kuma bada sakon gaisuwa duk sanda sukayi mgana da Hajiya tace tana gayamai,Mamammu kuma ko Sau daya bata taba cema Hajiya a gaiisheta ba abun na bama Hajiya mamaki sai dai bata ma Aminar mgana ba Sauran yan"uwanta kuma duk da bata waya da kowa acikinsu suna ranta tana tunawa dasu Lokaci bayan Lokaci watarana in bakincikin ya isheta sai ta Zauna ta rika Tunano Rayuwarta Tun daga farko har zuwa yadda yau ta kasance da ita sai ta hau kuka sai tayi ya isheta take yin shuru ta koma tana Sauke Numfashi Watarana in ta tuna da Aminu sai tace ko yana ina yanzu..? Bata da masaniya sai dai tana mai Fatan Duk inda yake yana cikin koshin Lafiya duk yanzu bata san Dalili ba,bata jinsa aranta ko Domin tayi aure har da ciki ne..? Ammh ai da Farko ai tana jinsa aranta ammh yanzu sam sai da ta tuna dashi tausayinsa ya kamata. Danmallam kuma yana madina ne ammh Babu abuda Bai gani na Jidalin Amina bata barinsa yayi sukuni baya Kiranta in yana gida sai dai in ya fita Wajen aiki ita kuma Amina sai ta Fahimci hakan sai ta hada mai Tsiyarta bata kiransa sai ta Daidaici goman Dare a nan Nageria ko sha Daya sai ta kirasa shi kuma baya iya Share Kiran Amina data zama wata bangaransa a yanzu ammh baya yarda ya dauki waya gaban Sakina ko Sarood saboda komai na Bukatar sirri sannan akwai Tambayan da Sarood tatabamai bayan sun dawo wai ina Amina..? Ko sun Rabu ne..? Ya dade yana mamakin tambayarta Daya turketa sai ta fadamai wanda ya Fadamata saboda ba Tunaninta bane yadda yaga tayi ne yasa yasan Tsara mata akayi kuma ba kowa bace face Sakina abakinta ne Sarood zata ji wannan mganar bai ce ma Sarood komai ba ya bar mganar shiyasa yake kafa kafa bai taba bada Kofar da zasu Fahimci wani abu ba. Ko a wayarsa Da NOOR yayi mata Saving din Lambarta hankalinsu kuma bai taba kaiwa wajen ba Saboda ma Tsaro yasa duk inda Zashi wayarsa na Hannunsa ko tana Jikinsa Daya ga Kiranta yake kashewa sai ya ce bari yazo ko ya shiga Dakinsa ko ya fita waje in kuma yana Ciikin gari ya tafi masallaci sai ya sallami Amina da Rigimarta wanda shi da kukan nan nata in da zata mai kudi tsab sai ya siyesu da ya huta basu taba waya sun gama Amina bata tadamai hankali ba haka kurum sai ta kirasa ta sakamai kuka shi kuma Hankalinsa ya tshi bayason yaga Mace na kuka macen ma Amina fa duk yadda baisan Hayaniya yanzu sun kulla abota da ita Saboda Amina.. Ko dan wuni yayi bai kirata ba Daya Kira zata sakamai kuka tace ya manta da ita tana cikin wani Hali shi yana chan yana jin Dadinsa haka zai zauna yayi ta lallashinta har sai ta Sauko watarana ma in ta ji iskancinta bata Daga kiransa sai dai in ya gaji ya Kira Wayar Aisha suyi mgana sai an Lallabeta sannan take Daukan wayansa ta bakin yakaka tace duk ta rikita bawan Allah ita ya Aisha har mamaki take yadda Amina take juyaa Danmallam kamar waina a Tanda da Iskancinta iri iri. Wani Lokacin fa sai da tashi cikin Dare ta Dokamai kira bata Tunanin wani Hali yake ciki yana tare da matansa ne ko basa tare..? Ita kawai in ta kasa barci sai itama tace bazai yi ba,ai D'ansa ne ya hanata barcin shiyasa yawancin yanzu a Falo yake karihe barcinsa saboda da Zarar yaga Kiranta sai ya lallaba ya fita Falo in ya gama Lallashin nata bai komawa ciki sai yayi kwanciyarsa anan wani Lokacin ma barci ke Daukansa bai sani ba Tun Sakina bata saka Ido ba har ta Fara Tuhumansa ammh bata taba kamasa yana waya da Amina ba. Ai shi ya kara ma saka mata suna Aminene jidali Aminene rigima duka taci sunanta domin ba wanda baya gani. In ta fara kuka tana Fadin wai Cikinta ya Dunkule waje Daya ta kasa barci sai mamaki ya kamasa daman ai Dole Zata Fuskanci haka tunda Wani Hallita ne ke Rayuwa acikinta wani Lokacin sai ta faramai kukan duk tayi muni ta xama katuwa kamar ba ita ba Shi dai ai nashi ban Hakuri ne da lallashi Ranar datake jin yan arziki kuma ayi ta mai Shagwaban an yi kewarsa to sai ayi soyayya ranar kuma da yan tsiyan suke kusa sai a wuni ana Rigima ko kuma ta rika mai kananun kuka ya tafi chan ya manta da ita saboda yana da matansa achan shidai baki yake bata yana kawo mata Uzurinsa sannan take hakura kadan shidai fa yaga Jidalin Amina ganin idonsa ba Labari baa. Dayake bata da matsalan kudi a waya Ya Usman na saka mata haka ma ya Aisha sannan ko kudin da ya Danmallam ya barta mata bata taba komai aciki ba sannan su ya Aisha bata karbi kudin ba tace Aminar ta ijiye a Hannunta tunda bata Bukatar Komai na Bukatar Rayuwa babu abunda ya Aisha da ya usman suka Rageta dashi. Mganar siyayyan Kayan Haihuwan kuwa Hajiya ya kira sa suka Tattauna yace zai turo mata kudi cikin satin da sukayi mgana Jafar ya kawo mata kudi 100k daga ya Danmallam,ita kuma bata taba komai ba sai ta nuna ma mallam shi kuma sai yace ta bari ya kara wani abu akai sannan yayi mganar Hada lefen da Umar bai samu hada mata ba mai zai hana a Hada ayi mata gabadaya..? Sai Hajiya taga haka ya chachanta sai tace mallan din ya Kira Umar din suyi mgana haka akayi shi ya kirashi yamai tuni kuma ba domin ya Tunaamai ba sam ya manta yace zai Turo wasu kudin a kara dasu ammh zai siyan mata wasu kayan anan,Duk da bai da wani kudi a Hannunsa sosai bai Fadama mallam ba ammh shi mallam din ya Fahimci haka saboda Biyayyah Umaru garesa yasa kawai yayi ma Aba mgana aka fitar da kudi Dubu Dari hudu ya damkama hajiya yace a Hadama Amina lefe gangariya da kayan Haihuwa Bakin Hajiya yaki Rufuwa Amina ta fita Tsara Sai dai Danmallam yaji mganar kudin da mallam ya bada abakin Hajiya mamaki yasa ya kasa mgana Daya Kira mallam zai yi mgana sai ya hanasa albarka kawai ya sakamai tare da Fatan Cigaba da aminci a Rayuwarsa.. Danmallan kamar yayi kukan karamcin mallam agaresa wani kaunar mahaifinsa yana kara shiga ransa mallam kuma yasan tun bayan da Umaru ya tsaya da Kafafunsa bai Taba karban wani abu Daga garesu ba Sai ma shine da alherinsa baya yankewa koda dayake wani kasar Sannan yanzu Iyalai sun mai yawa ga Zama inda kasarsa ba akwai kashe kudi Sosai shiyasa yayi mai wannan karamcin domin ya nuna mai jin Dadin yadda ya amshi Umarninsa da Mutumci na auran Amina kuma ya riketa Bisa gaskiya da Amana. Hajiya ita kanta taji Dadin hakan Sannan ai Dannallam ya chachanci komai a wajensu saboda Biyayyarsa,batare da Sanin kowa ba ta Kira Aisha sukayi mgana ta kuma Tura mata kudin duka 500k din tace a siya duka abunda ya kamata Hade da kayan Haihuwa ita kanta Aishar tayi mamakin uban kudin sai dai Tasan Amina ta Chanchanci dukkan gata yadda Hajiya da mallam ke sonta. Duk ta Online tayi duka Siyayyan Tundaga kan akwatina da Sauran kayan Size din Amina kadai ta karba Duka har na bbys din ta Online ta siya so take sai ta gama Hada komai a kawo mata tunda anan Abujan matan mai saida kayan take Direba kadai zata bama Sako ya karbo mata. Ko Amina bata san da kayan ba sai da aka kawo kuma na Jarirai kadai ta nuna mata ita da Yakaka Lefen kuma Damam Hajiya tace kada ta nuna ma kowa,Amina ita bata ma wani Damu ba Damuwarta ta Haihu Lafiya saboda ta fara Tsoron yadda ake fadin Haihuwa take Yakaka tayi ta saka albarka tana fadin basu da Tsara ita da takwaranta. Acikin satin da Aisha ta gama Hada kayan Hajiya tazo ta Duba Amina ta kuma ga kayan wannan karon ma banda Mallam ba wanda yasan da zuwanta Amina taji dadin ganinta ta makaleta har da Hawayenta Hajiya mamaki ganin yadda Amina ta koma sai ya kamata ta fara Tunanin anya Mutum Daya ne acikin Amina ganin yadda girman cikinta ya wuce misali Har Aisha sai da ta ma mgana batace komai Sai Dariya datayi Hajiya bata kwana ba kamar wanchan zuwa Idi ya koma da ita bayan tayi ta ma Yakaka Godiyar irin kulawar datake bama Amina ta kawo mata kyautan Turaman Zani guda Biyu da Turaruka Yakaka nata godiya Hajiya ta tafi bayan ta sanar da Aisha ta bar duka kayan a Hannunta In Lokacin isan su gumel yayi zata mata mgana..! Batare da kowa ya sani ba Danmallam ya yi ma Aliyu mgana ya neman masa gida anan gumel,yana so zai siya wannan karon bai nemi Jafar ba ballatana Nasir ko Aba ko Hajiya da mallam basu sani ba Aliyu kuma bai Fadamawa kowa ba an samu gida flat mai kyau da Tsari an gama ginasa kenan wanda aka bama kyautar kuma yace zai saida ne,An yi Ciniki Miliyan shida Tunda gidan bai da wani girma Bedroom biyu sai falo sai kitchen sai Haraban gidan karami shigar mota Biyu,To bayan ya fadama Danmallam kudin sai da akayi kwana uku ya Turomai kudin Saboda sai da ya Saida wani Share dinsa na harkan Saida gold da suke yi da wani Abokinsa Balarabe ne Riyad yake zaune Tare sukayi karatu shi sai ya koma kasuwanci,to shi yayi ta ma Danmallam Sha"awar fara kasuwanci har dai ya yarda ya saka Hannun Jarinsa suna dan yi tare to Kuma ba Laifi yana samun Alheri saboda Tasowar Hidimar Dake gabansa ya sa ya Karbi duka share dinsa Daga Hannun Abokinsa nasa. Ya turo ma Aliyu kudin gidan sauran kuma ya rike a Hannunsa,Daman yana Tunanin siya ma Amina gida Saboda wanchan bazai Dauke su ba gata Zata Haihu tana Bukatar wajen da Zata zauna ita da abunda ta Haifa daman yana Tunanin yadda zai yi abubuwa sun mai yawa sai ga Tallafin mallam Daya Dauke mai hidimar Hala ma Amina lefe sai shi kuma yace bara ya wanke masu Hajiya zuciya da wannan gidan duk da daman akwai Sharadin siyan ma Amina Gida Tsakaninsa da su Hajiyan. Gidan yana nan a anguwan Babura ne Dake garin Gumel makullan gida da Duka Takardun suna Hannun Aliyu ne tunda Shi yayi komai Yaso Umar ya Fadama mallam sai yace zai Sanar dasu sai Lokaci yayi yasan Tabbas Hajiya bazata bar Amina ta Haihu a Abuja ba gida zata Dawo da ita to yana so in ta haihu bazata zauna gidan Baba Sa"idu ko gidan mallam ba Insha Allahu sai dai ta Zauna agidanta. Ana cikin hakane Mallam ya tara Su Hajiya duka matansa ya sanar dasu Cikin watan nan manema auran su Hanne da Hamida da Sa"adatu zasu zo su gana dasu basu yi wani mamaki ba Daman ai su san tunda sukayi jarabawa a SS2 susan mallam bazai zuba musu ido ba aurar dasu zai yi Anty Amarya ce kadai ta nuna Damuwarta ta kalli Mallan tana Fadin"Mallam nawa duka duka yaran nan suke..? Shiyasa naso da ka bari sai wannan shekarar su zana jarabawar tasu kamar yadda duka yaran gidan nan suke yi..! Mallam yace"To ai nasu tsarin ne yazo ahaka sun gama zaman me zasu yi..? Kuma daman tun kafin haka suna da mgana akansu ai bazan zuba musu ido suna zaune haka ba sannan da kike mganar yara su hannatun ne yara..? Ko basu kai sha takwas ba nasan sun kusa ko Hajiya..? Hajiya na gefensa tace"Ai sun ma Shiga a watan musulunci mallam..Su kansu sauran yan"uwan nasu suna Sha takwas wasu sha tara ake aurar dasu nake ga..! Mallam yace"Ahto .Nidai na fada muku ku sanar da yaran ku su fara Shiri Insha Allahu bikin kuma zai kai karshen watan gobe ne bazan Dauki Lokaci ba..Su kuma su Akilu na yi ma Wani abokina Dake Jami"ar ABU mgana zai tuntubamin in sun samu gurbin karatu chan zan tura su tare. ! Hajiya ta amsa da Allah ya bada Sa"a ya kuma yi albarka Hajiya ita da Hajiya Nasara Hajiya uwa dai duk yadda takai ga Boye Damuwarta Sai ta bayyana Mallam nata aurar da duka ya"yansa ya manta da Umaima ne .? Bai taba mganarta ba ya Jingineta gefe ba boko ba islamiya sannan ba mganar aure Tunda ta ke ganin ta kusa Cika Burinta sai kuma Umaiman yanzu ne damuwarta. Ita ke da mallam yau yasa su Hajiya suka fice suka barta sai da suka shiga Ciki bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya ta kallesa tana Fadin"Mallam naji kayi mganar auran su Hanne ne..? Ban ji ka saka Umaima aciki ba..? Na zata wannam karon zaka Hada da ita ne..? Sai da ya Zauna gefen gado ya dora kafafunsa saman gadon sannan ya Fuskaceta yana fadin"Umaima da bata da Lafiya Uwani..?. Kuma ma ba wanda ya kaawo min mganarta ne har yau shiyasa kikajini shuru da ita..Sannan ni fata na ta samu Lafiya sai komai ya Biyo baya. ! Sai hajiya Uwani ta saka kuka tana Fadin"Haba mallam domin Allah ya Daura mata wannan Laluran sai kace bazatayi aure ba .! Ai sai ita ma ka hadata da mijin daya Dace da ita kamar yadda kake ma Sauran ya"yanka har da ma wanda ba Naka ba. ! Ta karishe Fada tana kuka kallonta kawai yake yi yana Nazarin mganarta Mimirshi yayi kafin yace"Uwani..Kinsan Kalmar wlh Rantsuwa ce..? Ta daga kanta ya Cigaba da Fadin"To wlh tallahi ban taba Tallata ya"yana ba ko ya"yan Sa"idu ba Duk Cikin yaran da na aurar dasu zuwa akayi aka sameni mganar ana son aure Cikin iyalaina abu Daya nake yi shine ni nake Zaban wacce ta Dace sai nace na bama wane na bama wane kaza..Sau Daya tak na taba Aikata haka kuma shine na karshe da yardan Allah mganar Umaima kuma ni bazan zama mara adalci ba kamar Zalunci ne na aurar da ita da wannan laluran batare da sanin wanda zai aureta ba Saboda haka in Bukatar hakan ya taso Lalle to sai an Bude komai a Fili in wanda yazo neman auran yaji ya gani Shikenan Uwani nima zan so ganin na gama Sauke Nauyin aurar da duka ya"yan Matan da Allah ya bani..! Daga haka bai kara mgana ba sai ma mganinsa na Ciwon kafa Daya Dauka yana Shafa ma kafarsa tasa. haj.Uwani tayi jagale tana kallonsa kafin ta Cigaba da matsan kwallarta Hujjan mallam ai ba Hujja bace in ya bata da ita yadda ake ganin girmansa ai bazata wulakanta ba ammh Saboda An ga gazawarta ne kowace mata za"a gama kwashe ya"yanta ita kuma ko Oho. Ranar haka suka kwana kowa da Abunda yake sakawa aranta,Da Safe data koma Shashenta ta Kira Batula ta Sanar da ita komai tana Fadin"Batula Hankalina ya fara tashi..kannen bayan Umaima mallam aurar dasu zai yi tana Zaune. ! Batula tace"Mafita kawai ki shiryo kizo Tsafe mu tafi Niger wajen mama..Bazamu bari aga gazawarmu b...! Da wannan shawarar Haj.Uwani ta Zauna adaran ta tambayi mallam zuwa Tsafe bai hanata ba yace Allah ya tsare ya bata kudi 20k da zata tafi da harda kayan abinci yace ta tafi dashi gidansu tana ta godiya idi ya kaita washegari bai kwana ba Aranar ya Dawo. Cikin Satin da mallam yayi ma su Hajiya mganar auransu hanne Tuni Labari yakai ko'ina tunda su hannen har masu auran dake wani garin iyayansu sun fada musu hanne da Hamida Hajiya ta kirasu ta Fada musu duk da daman ai susan haka zata Faru ammh sai da jikinsu yayi sanyi aure fa?tunda sukaji mganar basu da wani Walwala daman Amina na nan ne itace Cikin kowani yanayi bazata taba bari su damu ba Jidalinta kadai ai ya Ishesu Allah sarki Amina suna kewarta sun gaji da jiranta da saka ran Dawowarta har sun cire rai ma. Bangaran Sa"adatu kuma kuka ta Dinga ma Anty Amarya wai bata son aure yanzu sai da Anty Amarya ta kusa Dukanta sannan ta kyaleta Domin ko ta kai wacece ita bata isa taja da Umarnin mallam ba Sadiya yayarta Anty Amarya ta Fadamawa ita kuma ta Kira waya aka bama Sa"adatun ta mata fada shiyasa Sa"adatun tadan Saki ita kanta Anty Amarya bata so ba ammh to ya ta iya..? Mallam in ya Fadi mgana ai bamai Tada ita kuma sai Allah... Mamanmu da Aba ya Fada mata Murna ma ta Farayi zata yi Biki na kece raini wajen aurar da autarta hamida Saboda Tasan mallam gangariyan mazaje masu Nagarta yake aurar da ya"yansa da nasu garesu Shiyasa bata da wata Damuwa in akwai abunda Hajiya da mallam ke yi suna Burgeta wannan Sadaukarwan nasu ne, basa numfasawa sai sun ga duka ya"yan agidan auransu mai Cike da Nagarta ne Shiyasa da Anty Amarya ta Kirata tana Korafin auran yayi kusa sai da Mamanmu taji Haushinta da Tunanin tana Bakinciki to in ba Haka ba menene. ? Yara sun gama karatu to me zasu jira ai sai aure ammh tana neman ta nuna Bakinciki akan hakan,Sai dai bata Damu ba sanin ko me Anty Amarya zatayi Mallam dai bazai sauya mgana ba Sannan ai ita kakarta ce ta yanke saka Tunda tana ta amsan kudade wajen Aba da sunn siyama Hamida yan kayan kitchen tunda kayan gado da Sauransu mallam ke musu kowa ya sani ai ita fa Duniya sabuwa aranta tasha Fadin ko yanzu kasuwa ta Watse mata ai dan koli yaji Riba... Har Abuja sun ji Labarim auran su Hamida da hanne watan Gobe Aisha da kanta ta fadama Amina aranar Amina wuni tayi bakinta har kunne Domin ta Jiyo kamshin zuwanta Gumel sai dai takaicinta Daya bata nan ai da mutane sun ga Hura Hanci a Bikin Hamida da hanne ko su ya Abida sai ta rama suma wulakancin datake musu in ana Biki ita ko Cikin jikinta bata Duba ba hango kanta kawai take suna Kara"i ita dasu Hanne Tun kuma Daga ranar bata da wani Hira sai wannan Bikin yakaka har ta gaji da Haddace Labarin Bikim nan a bakin Amina shi kanshi Danmallam Topic din kenan kullum sukayi waya sai tace ranar Bikin su Hanne Hmm kaza kaza yana so yace da Cikin zaki yi kaza..? Yana tsoron ya ballo ma kansa Ruwa sai dai yana Tausayinta in Hajiya tace bazata zo ba ya zatayi..? Ai ya tabbata wannan Jidalin na Amina in ta fara shi ko mallam to sai kila sai dai shin zai iya lallashinta yadda taci burin Bikin nan ya tabbata bata ci burin haihuwarta haka ba. Shima ai yasan da labarin bai Fada mata ba Tunda Mallam ya fadamai haka Hajiya ma duk sun yi mganar su sakina ma bashi ya fada musu abakinsu ma yake jin suna kara zencen yace musu Hakane Sakina sai Murna take yi Nageria tayi kira abu nasu to Har Sarood ta Shirya wannan karon sai tazo itama shi dai ko ci kansu bai taba Ce musu ba kan Bikin ya zuba musu ido ne kawai yana kallon ikon Allah. Haj.Uwani kusan sai da shafe wajen kwana goma sannan ta Dawo ta saki Ranta ana ta sha"ani da ita Domin mama tace mata ta kwantar da Hankalinta ana gama wannan Bikin Itama Umaima za"ayi nata to shi yadan Sanyayamata rai sannan tana chan Tsafe Uzairu yazo gida Ya kwana Biyu bata nan daga Chan Delta in da yake Bautar kasarsa har ya tafi bata Dawo ba sai da sukayi mgana ta waya. Haka take shigema Hajiya ana komai da ita Hajiya bata taba nuna mata tasan Wacece ita ba ta barta ne sai Ranar kin Dillaci domin ta nan zuwa Ranar da Allah zai tona musu asiri a bainar nasi. Mazajen su Hanne sun zo kuma sun gana dasu,Manemin Sa"adatu ya fara zuwa Dan gombe ne ma"aikacin Costume mahaifinsa ne sukayi karatu da mallam a kano,Sai kuma na Hamida Dake lecutring anan Kango Abu Zaria shima yazo Cikin Daliban mallam ne da ya koyar da Mahifinsa tun zamansa a zaria yana Dalibi ma alokacin. Sai na Hanne da Shine Karshen zuwa Haifaffan garin Adamawa kuma mazaunin yola ne. Dukkansu ba wacce bata yaba da Zabin Maalllam ba,sai hanne da tun taga ta ganshi take kuka cikin Damuwa kuma taki Fadan Daliinta Hamida ne kadai ta sani kuma ita din ma batayi Zencen da kowa ba. Shiryen Shiryen Biki fa ya kamkama ta kowani bangare mamanmu ta fi kowa Shiri domin tayi alkawarin kece Raimin da bata taba yi ba sai a bikin Hamida Autarta duk tana Barikin cewa Jawaad ne Autanta wanda yanzu suka fara JSS1 Shi da Sabeeha a kasan ranta ko nan bata ma kaunarsa bataki shima ya mutu ta koma Daga ita sai Sa"idu ko ba ko Hajiya ta Daukesa ta daina ganinsa kamar yadda ta Dauke Amina daga gabansu. Danmallam da kansa ya Kira Mallam ya fadamai zencen gidan daya siya ma Amina mallam yaji dadi ya dinga sakamai albarka shi ya Kira Hajiya ya Fadamata addu"an da Danmallam ya sha kamar Hajiya zata goyasa albarka kuwa ya shata har sai da ya kusa kwallah yana Tunanin wanda bai Sakama iyayensa ba Allah kuwa zai barsa. ? Aliyu yama mgana ya kawo ma Mallam Takardun gidan sannan ya Dauke shi da Hajiya kai suka ga wuri Hajiya kamar tayi kuka fadi take"Allah ya tsareka Danmallam..ya yalwata arzikinka..Allah ya Jibanci lamuranka Allah ya kara budi na Alheri yadda ka faranta mana ka rike Amina da Amana Allah kai ma Allah ya rike Hannayenka cikin Aminci..! Mallam ma haka ya dinga sakama Danmallam albarka sai Tsausayinsu ya kama Aliyu da sukayi waya da Umar ya fadamai irin albarkar da ya sha Wajensu Hajiya Danmallam ya murmusa yana Fadin"Aminene ta mallam da Hajiya ce..Suna shiga farinciki matukar aka kyautatamata kuma kaunar Baba Sa"idu ce ta Shafeta. ! Aliyu yace"Ai kacigaba da kyautatama Amina..ka riketa Amana har ya'yanka sai albarkar Hajiya da mallan ya bisu..! Umar ya saki kayattacen mirmishi kafin yace"Insha Allahu..! Hajiya ta kasa auna farincikinta Daga ita sai mallam suka kara tsara kayan Gidan Amina kamar yadda mallam yayi alkwarin yima Amina kayan Daki kamar sauran yan"uwanta haka kuma akayi tare da nasu hanne aka bada Oder din kayan gidan sannan Hajiya ta Tsara in kayan sun iso ya"yan yagana yayarta zata kira ta bata aron su su biyu bayan sun tambayi izinin mazajensu su zasu taimaka mata cikin Sirri su gyarama Amina gidanta Sabida tana so duk ranar data dira agarin ta iske komai ya kamallah. Hajiya ta kudiri niyyar sai da wannan Bikin Amina zata bayyana sirin Boye zai bayyana a kuma Lokacin take Fatan Allah ya bayyana mugayen Fuskokin Dake tare dasu domin ba Shakka bayyana Amina da Ciki Sai ya Razana su kuma ita ta sani shiyasa bata yarda da kowa ba yanzu Daga ita sai mallam suke sirrinsu ko matan sun Lura da hakan sai dai daman ba wanda yasan Tsakanin Hajiya da mallam tare aka gansu irin su Hajiya Uwani da Anty Amarya sai Bakinciki Daga nesa..! Hajiya ta zama kadagaren bakin Tulu basu da yadda suka iya da ita. ! *Janafty**TFZB2023* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* *Gumel..* Yau ta kama laraba ne da wuri suka dawo daga islamiya saboda anyi rasuwa ne Baban wata yar ajinsu Samira yahaya ne ya rasu sai aka zabesu su goma sha biyar maza biyar mata goma sukaje gidansu samira gaisuwa,bayan sun dawo mallam Ahmad yace kowa ya wuce gida sai Ranar asabar. Dayake sun cigaba da zuwa islamiya da Haddarsu kamar yadda suka saba suna dawowa ba su wuce gidan Baba mallam ba sai suka yada Zangonsu gidansu Baba Sa"idu Sa"adatu daman bata je islamiyar ba wai batajin Dadin haka sukaji Sabeeha na fadama kawarta mariyan ajinsu. Mamanmu na cikin Daki ta baje a Tsakar falonta ta baje wasu Sabbin kaya sababbin Dinkunanta ne da tayi Domin da gaske take yi sai ta shiga ta Fita ta kece raini a wannan Bikin. Tana cikin Duba Dinkunan taji Sallamarasu kafin ta kauda kayan sun Daga Labule sun shigo Da fara"arta ta Tabersu tana fadin"A"a Amare ne da kansu Ashe daga ina haka..? hanne gefen Mamanmu ta Zauna yayinda da Hamida ta zauna kan hannun Kujera tana Fadin"Daga makaranta .! Mamanmu tace"To naga kun tashi da wuri Lafiya..? Hanne tace"Rasuwa akayi mukaje gaisuwa daganan mallam Ahmad yace kowa ya tafi gida sau ranar asabar..! Mamanmu tace"Oh..Allah ya jikan musulmi..! Suka amsa da Ameen kayan take Dagawa Bakinta Har kunne tana Fadin"Kayan da zan ci fitar Bikin ku ne fa..Kun gansu nan ba"a Dade da aikomin dasu daga wajen Dinkin ba.. Less din take Dagawa har Hanne ta amsa tana fadin yayi kyau Hamida kuma kayan take kallo da mamaki ita dai bata saba gani ba ko ana Biki mallam ke ma kowa kaya daga manya har su yara sannan kwananan mamanmu Facaka kawai take da kudi yawancin Suturunta duk ta sauya su Taoffinta kuma ta aika dashi Gusai Tana ta sota mata mgana kuma ta kasa bata san ta ina zata fara ba Sannan ko Jiya taje kasuwa ta nuna mata Dinbin kayan data siya mata na Kitchen da sunan ita ta siya mata alhalin Hajiya ke siyan komai bama haka ina Mamanmu ta samu uban kudi haka datake ta kashewa..? Abunda bata sani ba Aba yake bata ko Da bai yi niyya ba da tace ya bata bazai iya mata gaddama ba ko nawa tace ya bata haka zai dauka ya bata. Hanne ce kadai ta Daga kayan ta gani ta yaba Hamida kuma daga inda take tace sun yi kyau basu wani jima ba suka tashi suka koma Dakin su Hamidar Hanne kan gadon Amina ta kwanta daman ko gidan ta kwana nan take kwanciyarta Hamida kuma tana Tsaye tana ninke Hijabin jikinta Data Cire ta ga Hanne tayi tagumi tana Tunani. Sai da ta maida Hijabinta Cikin Dirowarta sannan ta isa kusa da Hanne ta Dafata da Sauri Hanne ta Dago tana kallonta cikin wani yanayi Hamida ta sauke Nunfashi kafin tace"Haba hanne wai wannan mganar har yanzu bata daina damunki ba .!? Hanne sai kwalkwal kamar zatayi kuka Cikin wani yanayi tace"Hamida ya Zanyi..? Da wani ido zan kalli Amina in ta Dawo taji yadda abubuwa suka koma..! Hamida tace"Na fada miki ki daina Sako mganar Amina a wannan mganar..Amina fa yanzu ba kamar da bane..Matar aure ce kinga kuwa Igiyar aure ai ya kore komai Hanne..Ayadda nasan Amina Zata fi son kwanciyar hankalinki fiye da nata Hanne ni shaida ce irin kaunar dake Tsakaninmu..! Hanne ta Saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta na wani Lokaci Hamida ta rike hannayen nata tana fadin"Dom Allah ki daina damuwa..Matar mutun fa kabarinsa Wani ai baya auran matar wani..haka ita ma matar wani bata auran mijin wata..Ga misali da Amina waya taba Zaton zata auri ya Danmaallam..? Ammah dayake matar sa ce tun daga Launil Mahafuz ba gashi ya faru ba..Ki kwantar da Hankalin ki hanne Hajiya da mallam bazasu taba Zaba mana Abunda zai cutu garemu ba..! Hanne ta cire hannayenta a kan Fuskarta lokaci Daya tana kakalo Mirmishi Hamida ta saka hannu ta Share mata hawayen tana Fadin"Bana son na ganki cikin Damuwa duk nima sai naji na shiga damuwa..! Hanne tayi yar dariya kafin tace"Nagode Hamida..Na rasa Amina ammh baki barni nayi kewarta sosai ba..! Hamida tace"dukanmu muka rasata Hanne..Kuma junanmu ne bamu bari kewarta ta mana illah ba..Sai dai Amina wata aba ce awajen mu da mantawa da ita abu ne mai Wahala..! Hanne tace"Ni damuwata har da yarda za"ayi auran mu hamida ba Amina..! Hamida tayi shuru kafin tace"Nima abun na raina..ko xamu je mu roki Hajiya ne don Allah Amina tazo mana Walima ko bayan Bikin namu ai sai ta koma inda basu san mu sani din..! Hanne tace"Kin kawo shawara mu yi sallar mangariba sai mu shiga. ! Haka kuwa akayi suna Idar da Sallah suka ma mamanmu sallama wacce ta idar da sallah ta amsa musu da sai da Safe saboda tasan har Hamida ba lalle ta Dawo ba Jawad ma ya shigo ya Cire Kayan makaranta ya saka na gida ya fitaa masallaci domin wannan tarbiyan ta salla Cikin jam"i ko yaro karami ne yasan da ita agidan mallam yunusa Bazanga. Sanda suka shiga shashen Hajiya sun sameta tana addu"a ne bayan ta idar da sallah sai da suka jira ta shafa Daman tun da ta ga shigowarsu sun wani uban buga Layi agabanta aranta ya bata mganar Amina ne domin shi kadai ke sakasu kaga sun zama kalar Tsausayi.. Tana rike da Cashabanta ta kallesu tana Fadin"Lafiya na ganku haka..? Ko duk Tunanin barin gidan ne ya"yan Hajiya..! Kansu na kasa suka gaisheta ta amasa Cikin Fara'arta tana fadin"Amaran namu duk sun rame sai dan wuya..! Mirmishi kadai sukayi kansu na kasa kafin tace"Nasan da mgana a bakin ku ko..? Hanne ta Dago tana fadin"Hajiya mganar Amina ce..haka za"ayi Bikin mu Amina bata zo ba Hajiya..! Hajiya sai da tayi dariya Har Hakoranta suka bayyana Cikin Girgirza kai tace"Daman ai nasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Daman ai labarin kenan Amina..Amina ita ma tana chan duk mganarta da Zencenta Hanne da Hamida..Wannan kaunar junan naku Allah ya barta har ya"yan ku da jikokin ku su hadu a aljannah Firdausi..! Suna Mirmishi suka amsa mata da Ameen kai ta gyada tana Fadin"Amina ce dai damuwar ko..? Atare suka Daga mata kai Tana jan Casbahanta tace"To ku sha kuriminka..Amina na nan tafe da yardan Allah da ita za"ayi sha"anin auran ku..! Ido suka zaro a tare suka ce"Da gaske kike yi hajiya..! Cikin Yar dariya tace"Insha Allahu..Itama tana chan tana shiri..Bikin Hanne da Hamida bazai wuceta ba insha Allahu..! Saboda murna sai da Hamida da Hanne suka rumgume juna kafin su saki juna suna ma Hajiya godiya ta amsa musu cikin sakin fuskar tana ce musu sai su sudaina ramewa Amina Zata Dawo haka suka fice suna Murna ammh bayan Hajiya ta gargade su kada su fadama kowa sukace ba wanda zasu fadamawa. Ita kanta Hajiya bata isa ta hana Amina zuwa Gumel ba wannan karon Duk taso sai Amina ta Haihu ta Dawo da ita ammh Mallam ya nuna mata kada su kwari Amina da yawa bata da Zence sai na Hanne da Hamida in har sukayi aure bata zo ba abun zai mata Ciwo suma haka sannan Mijinta ma yabada goyon bayan su taho tare da Aisha shiyasa ta amince bayan tayi wani Tunani sai taga haka din shine Daidai. Hanne da Hamida jin Labarin zuwan Amina wajen Hajiya Bakin da bazai musu karya ba yasa suka saki jikinsu Damuwasu ta ragu,Shiryen shiryen Biki kuma babu abunda aka fasa su dai basa wani shiru tunda basu da kawaye daman Amina ta fisu gayyar kawaye sai Sa"adatu su bama su fadin zasu yi aure da Bakinsu koma tambayansu akayi shuru suke yi abunsu.saboda lamarin yazo musu ne alokacin da basu taba zato ba ballatana Tsammani ba.. Daman ai haka rayuwa ta gada..Sau Tari abubuwa da dama suna Faruwa damu ne bamu tsammaci Faruwarsu ba..Haka lamarin Ubangiji yake. ****** *ABUJA..* Ya Aisha na cikin bedroom dinta tana gyara kayanta da aka karbo wajen mai wanki da guga nata dana Amina sai na yakaka tun jiya aka kawo bata samu Zama ta saka nata cikin Wardrope ba tana ta shirin tafiyarsu Gumel ita da Amina gashi Hajiya tace tare da kayan Lefen Amina da kuma kayan Haihuwarta zasu taho sannan itama Daga barayinta akwai abubuwan data siya mata sannan Darling ma ya bata kudi yace ta siya ma Aminar wani abu tunda in ta tafi ba Lalle bane ta Sake dawowa ba..jiya ma kasuwa taje bata samun zama Sosai shiyasa. Tana Tsaye ne tana Shirya kayan nata acikin Wadrope din Amina tayi sallama ta shigo Dakin ta juyowa tana kallonta Lokaci Daya tana amsa mata sallamarta. Kallon Amina take yi tana dan Mirmishi tana kara jinjina ma Ubangiji Amina da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe domin cikinta ya shiga watan Haihuwansa ko scan dinta na Biya ya nuna EDD Dinta karshen watab nan ne sannan ai Tsarinsa befare ne ko after. Ta kara Kumbura kafafunta da fuskarta sun kumbura sai da tana da Tsawo shi ya taimaketa ammh Cikin yayi girma sosai sannan sai yayi kasa soaai alamun ya kusa fitowa duniya. Har ta kariso Aisha na kallonta ta samu gefen gado ta zauna Dakyar Aisha ma mata sannu Sanye take da doguwar riga baka cikin Tsaraban ya Danmallam ne ta madina Daya aikomata daahi Amina na son Rigar bata san Dalili ba. Sai da ta zauna ta gama hakinta ya Aisha na mata sannu sannan tace"Ya Aisha yaushe zamu je gyaran kai ne..? Ya Aisha ta na yar dariya tace"Oh yau watarana Aminene na tambayan yaushe za"a je gyaran kai..? An girma an zama manyan mata an Daina kazanta raahin wanka da yin wata uku da kitso ba gyara kenan..! Amina tayi dariya da Idanuwanta da suka Shige Ciki tace"Ko abaya ma ba Laifina bane har da Sakaci da kuma rashin kula ya Aisha..! Cikin dan mamaki tace"Bangane ha..? Amina tayi wani mirmishi takaici kafin tace"Bazaki gane ba..Ammh ki yarda da mganata ai hamida da Hanne tare muka taso ai ba haka suke ba ko..!? Ko haka suke..? Ya Aisha ta girgiza kai tana Fadin"Sukan tun abaya suna da kokarin gyara kam..! Amina tace"ki barsa a yadda na Fadamiki..! Ita dai ya Aisha bata damu da mganar Amina ba yasa tace"Kada ki damu ki bari sai gobe in muka dawo daga asibiti sai mu biya mu yi gyaran kan ko..? Ni kitso zan yi kefa..?.ko kuma ki bari in kin yin Haihu Lafiya sai kiyi na suna..! Amina ta kauda kai tana Fadin"Sai na tambayi ya Danmallam in yace yana son Kitso sai nayi..! Ya Aisha ta rike Baki tana Dariya kafin tace"Ina yakaka tazo taji..Eyye masu miji manya..! Amina tayi mirmishi batace komai ba ya Aisha tace"To har yanzu bai tashi Daga ya Danmallam din bane..? Amina ta hura hancinta Daya kara Girma kafin tace"To ai nima bai sauyamin suna ba da Aminata yake kirana..! Ya Aisha tace"To ai ke zaki sashi ya Sauya miki ina ruwanki da sai kin jirasa..Shi da yake da mata Biyu kowacce da sunan data ke kiransa kema sai ki samu naki tunda dai shi balarabe ne ki rika cemai HAbibi..! Amina ta kalleta a karkace kafin tace"Allah ya tsareni..Habibi fa..Sunan da wannan gajerar matar tasa fa take kiran sa dashi kenan..! Sai nima na Dauka..!.? Ai na tasani kwaikwayo sai ta Rainani ma ya Aisha in taji ina kiransa da haka..! Ya Aisha na Dariya tace"Oh ai bansani bane da gaskiyanki tobari mu sami wani suna ki rika kiransa da Norul kalbi mana..! Amina ta yamutsa fuska kafin tace"Bai yi ba chanza wani..! Ya Aisha tace"To Hubby..! Amina tayi shuru kafin tace"Hubby..? To har gwara ma wanman..! Ya Aisha tayi dariya kafin tace"Yayanmu ya shiga uku..ya fada komar Aminenen hajiya da mallam..! Amina na Dariya tace"Ko zaku Cirosa ne..? Ya Aisha tace"Ina fa ai muna jin Dadi..Acigaba da kula mana dashi Allah ya kara kauna da soyayyah..! Amina tace"Shi yace miki yana sona..? Ya Aisha tace"Basai ya fada..Kowa ya ganki ai yasan kun fadama juna..! Amina ta Hura hanci kafin tace"Ku ke gani ba..Ammh ai matansa yafi so akaina..! Ya Aisha Dariya kadai take ma Amina Cikin zolayarta take kara gayamata Wasu sirrukan zama da miji,Amina ta Bude kunne tana Saurara bata da kalmar da zata gode ma Ya Aisha da yakaka zaman ta dasu alheri ga Rayuwarta har Abada bazata manta da gudumuwarsu ba. Ta Dade a Dakin ya Aisha Sai azahar ta fito ta koma Dakinsu ita da Yakaka tana Shigowa yakaka na goge goranta ta kalleta tana Fadin"Ki rika dan yawatawa Takwarata sai kafafuwan naki su saki sannan ita mai juna Biyu ba"a son ta rika kumewa waje Daya .! Amina tace"To yakaka ai baki rakani ba yau..! Yakaka ta mike tana fadin"To Dauko mayafinki mu taka zuwa Haraban gidan..Ai bana ki takama Takwarata ba..! Duk da dai kishiyatace ke domin kinsan dani komawa madina ba tashi..! Amina na Dariya tace"Sai kun dawo..Ai ina nan zaki dawo ki sameni in wadanan guzumayen matan nasa suka koroki..! Yakaka tace"Su har sun isa..? Ai mu in muka shiga mun shiga kenan Asiri ko tsafi bai isa ya Girgizamu ba..Allah muka rike shiyasa gamu nan a Tsaye ga Kafafunmu..Kainuwa dashen Allah..! Amina sai dariya take yi ta saka mayafinta tana fadin"Kwarai yakaka mu ikon Allah ne da na mutum ne da Tuni sun Shafe babinmu..! Yakaka tace"Af keda kika san komai..! Da haka suka fito daga Dakin Yakaka ce ta leka ta fadama Aisha sun fita takawa ita da Amina ta musu fatan Dawowa lafiya haka suke yi tunda Cikin Aminar ya tsufa. Yakaka kitchen ta shiga suka gaisa da Saude ta Daukan musu ruwa suka fice Tunda in Amina najin tafiyar har karshen Layi Yakaka take janta iyaka in sun gaji su zauna Amina ta sha ruwa ta huta. Sai da suka kai karshen Layin Maitama sannan suka juyo suka Dawo suna tafe a hankali suna Hira sama sama har suka dawo kuma Amina hakan ba karamin taimaka mata yake yi ba sai da suka dawo sukayi sallah Sannan suka zauna suka ci abinci Amina tuwo taci miyar kuka wacce Tun jiya Saude ta mata shi.bayan tashi ta koshi sai kuma ta kwanta ta Huta Daganan sai barci karar wayarta me ya Tada ita Daga barcin daman bata wani barci mai Nisa Tunda Cikinta ya tsufa..yakaka Dake Dakin ta miko mata wayar tana Daga kwancen tace"Gashi nan tun dazu ake ta kira..Ina jin mijinki ne to ban da ma shi ba wazai kira..? Amina ta amshi wayar yakaka sai ta fita kamar yadda ta Saba ta bata wuri. Sai da ya kara kira ta Dauka Cikin Shakewar murya suka gaisa jin yanayininta yasa yace"Meke faruwa ne..? Kai Tsaye tace"Me ka gani..? Dagachan bangaran yace"nayi ta kira baki Dauka ba..Sannan yanzu kuma kin Dauka naji muryanki ta Chuse fata dai ba jikin bane..? Amina ta muskuta ta mike Zaune tana Fadin"Lafiya lau na dan kwanta ne shiyasa ban ji kiran wayar ba..! Kai ya gyada kafin yace wani abu kawai yaji tace"HUBBY..! Tsayawa yayi yana Tunanin ko dai bada shi take ba sai da yaji ta kara maimaitawa"Hubby..nayi kewarka sosai yaushe zaka taho..? Danmallan Dake Cikin Office dinsa bai san sanda yayi baya da kansa kan kujeran Dayake zaune har da sabule Hula yana Shafa gashin kansa.. Cikin wani yanayin Farincikin Dayake Ciki yace"Yau nine Hubby Amina..? Yaushe na tashi Daga ya danmallam din..? Bakinta ta Tura kafin tace"To ko baka son sunan ne..? Da sauri yace"Wa ne ni..? Sosai sunan yayimin dadi..Sannan nima ai ina kewarki sosai..Zan dawo Cikin Satin Bikin insha Allahu kada ki Damu nima ina son nazo na ganki ke da Abunda ke Cikinki..! Amina ta murmusa kafin tace"Ammh ai nima baka sauyamin suna ba..! Dariya ta basa yasa ya Murmusa yana Fadin"Waya fada miki..? Amina tace"Ai ban taba ji bane..Da fa Amina kake kirana..! Kai Tsaye yace"Uhm kece dai baki Taba jiba..Ni nasan sunan da na saka miki Acikin raina sannan dashi nayi Saving din lambarki a wayata. ! Amina tace"Don allah ka fadamin..! Make kafada yayi kamar tana gabansa yace"Naki bazan fada ba. ! Amina ta fara Shagwaba tana Fadin"Don allah fa nace..! Kuma ai ni na fadamaka sunan da na saka maka..! Jin zata faramai kukanta na Fama yasa ya Dakatar da ita yana Fadin"Tsaya Tsaya.kafin ki faramin wannan kukan naki da bayajin Lallashi..Ai ke NOOR ce..Haske ce ke Amina acikin Rayuwata Tun da kika shigo Rayuwata nake ganin haske kan komai nawa sannan nake ganin Daraja kima da martabawa wajen Iyayena sannan suke kara sakamin albarka da godiya gareni..Daga nan na Fahimci ke haske ne ga Rayuwata..! Amina sai ta fara Hura Hanci tana jin Dadi sai wani Blushing take yi Cikin Fara"a tace"Da gaske ni Haske ne awajenka..? Yana shafa kirjinsa yace"Ki bari nazo ,zan kara tabbatar miki Noor..! Amina ta washe baki ta kasa mgana Dadi take ji akan ranta Cikin wani yanayi yace"Ya Bby na..? Yau yayi motsi kuwa..? Amina tace"Dazu muna dan takawa ni da yakaka sai naushi na ake yi aciki..! Tafada Cikin yar shagwaba har da Jan hanci Danmallam yayi dariya Amina na jinsa sai ta sakamai kuka tana Fadin"Dole kamin Dariya tunda kamin Ciki ka tafi ka barni da wahala kana chan kai da matanka kana jin Dadin ka shine har kana min Dariya..! Ya rude Hankalinsa ya tashi ya fara Lallashinta yana fadin"Wani jin Dadi baki kusa dani..?kinsan Allah ni fa kina Haihuwa zan taho Dake nan bazan jura zama baki kusa dani ke da abunda zaki haifa ba. na riga na samar Miki Shaidar zama a kusa dani..! Amina jin haka yasa tace"Da gaake..? Yace"Sosai ni dai kimin alfarman ko Hajiya tace bata yarda ba kice ke Zaki bi mijinki abunki..! Amina ta fara Dariya tana Fadin"Wlh ba ruwana..!. Wai shi zai mata wayau yana Fadin"Au baki son ki koma garin da Monzon Allah sallahu alaihi wasallam ya Zauna..? Baki son zuwa makka ne kiyi Hajji..! Amina tace"Ina so naje..In na ganni a gaban ka"aba Hubby kasan me zan fara roka..? Yace"A"a Noor..! Amina tacigaba da Fadin"Zan duka in Dafa ka"aba in rokar ma yaya Afuwa da salama sannan na roki Allah ya Hadamu a darussalam..! Kai Tsaye yace"Allah ya Amsa ina jinki sai me zaki roka..? Amina tace"Zan rokar ma Hajiya da maallam gamawa da duniya lafiya..Sai kuma Aba shima zan rikor masa kwanciyar hankali da Zama lafiya da wadata..! Danmallan yayi Tagumi kafin yace"Sai kuma me zaki Roka..? Amina tace"Sai kuma na roki Allah ya bama mijina Wadata na alheri Allah ya Zaunar damu lafiya Allah ya karamana kaunar juna ya shiryamana abunda Zamu haifa ya bamu ikom Musu Tarbiya bisa Amana da koyarwan addinin islama..! Ayadda take mgana sai da yaji ajikinsa Cikin mamakinta yace"Wani mijin naki..? Kai Tsaye Amina tace"Kai mana Hubby..dole zan gode maka..Domin kaima ka bani Taimako wajen dawowa da Rayuwata daidai sannan ka aureni Cikin wani yanayin da bakowani Namiji zai iya ba..Nagode kwarai Allah ya baka ikon yimana aldaci..! Danmallam sai yaji kamar yayi kwallah ashe haka Amina ke da Hankali..? Kai tsaye yace mata"Ameen Ameen Noor..Allah yayi miki albarka Allah ya Saukeki Lafiya insha Allahu Buriinki Zai Cika kin ji ko..? Ta amsa mai Cikin jin Dadi,Shuru na wani Lokaci kafin taji yace"ANA BEHABBIK YA NOOR.....! Amina ta ji mganar kamar Daga sama yasa tace"Me kace..? Shi a tunaninsa bata ji me yace ba Sabida Labarci ne ya fada sai yayi saurin cewa"Bakomai..! Kawai sai ta murmusa batace komai idonta ya kawo kwallah haka suka gama Hirarsu sukayi sallama Suna gama wayar ta rumgume wayar akan Cikinta tana Fadin"Ina son babanku..Wlh nima Ana Behabbak Hubby Umar..' Hawaye ya kawo mata tayi saurin sharewa tasani tana son mijinta so mai tsanani data bata san yaushe ya fara ba Sannan yadda take kishin sa ko matansa basu kaita ba shiyasa ta Tsani ko jin sunansu kamar ma ya sani in suna Hira baya mata mganarsu shine zaman lafiya. Washegari suka tafi asibitin tunda yanzu duk sati suke zuwa saboda Cikinta ya tsufa.da suka Dawo ne suka Tsaya Shagon salloon aka musu gyaran kai da Gyaran kafa Daman Amina ta Fadama Ya Danmallan yace kada tayi kitso ta bar mai gashin nan yafi son ya gansa haka ya fi bashi sha"awa ita kuma Amina duk abunda Zata Burgesa shi take yi bata Damu da kowa da komai ba sai shi sai Cikinta ke gabanta. ******* Ana saura Kwana goma Bikin su Hanne Oder din kayan Dakin su ya iso har da Na Amina,Kowacee kuma Dakinta inda zata zauna aka wuce mata dashi Hamida dai yayarta Zulfa taje ta taimakama ma"aikatan aka Gyaran kayan aka saka komai a muhallimsa anan zaria zata zauna Gaskiya Layout. Ita kuma Sa"adatu Gombe Kanwar Anty Amarya A"i sai Haj Nasara da Hajiya Babba suka je aka gyara Inda Sa"adatun zata zauna Sai washegari suka Dawo na Hannatu kuwa Haj.Uwani ce taje da Anty Amarya har Yola suka yi Jerin su,Tunda sun tafi da Kayan Kitchen din da Hajiya ta siyama Hanne da Hamida duka da Sauran na Hamidan da Mamanmu ta siya a mota ta saka ta aika ma Zulfa bata bari ko su Hajiya sun sani ba kada ta bar wata kafar da Za"a Zargeta. Har Zulfa sai da tayi mata mganan ina ta samu kudin siyan wannan kayan saj tace ai kiwo tayi a gusai da Bikin Hamidan yazo sai ta saida tayi wannan Hidimar da ita Zulfa sai ta yarda bata kawo Tunanin komai ba na wajen Hajiyan wajen mamanmu aka barsu da niyar sai ranar Daurin airan in za"a wuce da Amarya sai a wuce dasu. Bangaran gidan Amina kuwa batare da kowa ya sani ba Daga Hajiya sai Aliyu sai Mallam suka san an kawo kayan Dakin,Hajiya da bata samu kiran yar"uwanta yagana ba saboda Nisa Mallam ma yace ta kyalesu Fadila matar Nasir ta nema tare suka gyara gidan Amina ya fito Tsab komai an saka mata Labule ne kadai ba"a saka ba Aisha zata zo dasu Tunda tace ta siya ma Amima masu kyau oder dinsu tayi daga Dubai. Har kuma aka gama gyaran gidan Fadila bata san ko gidan waye ba,Tunda dai Hajiyan ta nemeta da Nasir bai sani ba,sai bata ma Fadamai ba Tunda bata da Hayaniya,ta kama Bakinta tayi shuru ammh bata taba kawo Tunanin gidan nan da komai na Cikinsa na Amina bane Aliyum ma Data gani Tafi Tunanin ko nashi ne ko na wani nashi kila. Shirye shirye ta ko"ina ya kamkama ana cikin kwanakin Bikin ne Sakina achan Madina tayi Zazzabi har da su Amaye amaye ana zuwa asibiti aka gwadata sai Ciki dan kimanin wata Biyu da kwanaki Labarin da ya yadu a Nageria abun mamaki shi Danmallan Da mallam kadai sukayi mgana ya fadamai hajiya ma mallam ya manta bai Fadamata a bakin Haj.Nasara take ji. Anty Amarya haka take yada mganar Cikin tana Hura Hanci Hangowa kawai take komai ya kare ana gama auran Sa"adatu zata fara kokarin ganin bayan Haj.Uwa Ita kuwa daman Dariya take mata domin ta tabbatar da cewa kamar sauran shima haka zai bi Rariya Hajiya dataji labari Fatan Allah ya Tsayar tayi mata har aranta bata Fatan wannan karon Sakina ta rasa Cikinta ai mugunta Fitsarin Fako ne mai shi yake ci. Amina ma taji labari abakin ya Aisha itama tace Sadiya ta kirata ta fadamata Amina sai taji Abu acikin Ranta ammh bata yarda ta Furtamai abunda taji ba shima kuma bai taba mata mganar ba sai mganar tafiyarsu Dayace Ranar Litini Jirginsu zai taso Daga jidda da Daddare zuwa Nageria shi da Sakina da Sarood. Da farko yaso Sarood ta zauna Hajiya Dataji mganar tace bai yi adalci ba Sai dai Sakina ta Zauna shi kuma baya son Rigima yadda Sakina ta ke Hura Hanci da Cikin jikinta da kuma wannan sha"anin in yace ta zauna ai sai ta nemi mai hayaniya sannan yana da kudi a Hannunsa yasa kawai yaga gwara su taho gabadaya sannan yana su dan jima tunda hutun karshen shekara ne. Su kuma su Amina suna ta shiri Ya Aisha bata siya ma Amina komai da kudin da Usman ya bata ba Daman kuma ta Bude Banki zuwanta Abuja sai da sukayi mgana da Hajiya tace ta barmata kudinta tunda kusan komai ta siya ma Aminar itama Aishan ta siya mata Zannuwan gado da sauran kayan Kitchen su blander Toster da Sauran su sai kayan Kamshin girki su kayan gyara kuma sai dai inda ta Haihu sannan har da Yakaka zata tafi gumel Usman baya nan yana Lagos za"a Yi Bikin Direba ne zai kawo su da kayan su. Amina ta rasa Bakin godiya Data ga Uban kayan lefenta da kayan da ya Aisha ta siya mata sai da tayi kwallah Tace Gudummuwar malam da Hajiya ne suka Dauke ma Danmallam lefe tasani ba"a taba kawo lefen kowa ba sai dai in kaje gidanka ka gani ammh Sai gashi ita da nata Lefen zata koma Allah Sarki Rayuwa daman ai abunda ya baka Tsoro watarana shi zai sakaka kuka. Ranar Talata da yammah Jirgin su Damallam ya sauka Filin saukan Jirage na kano Aliyu yazo ya Dauke su shi da Jafar suka kawo su Gumel gidansu suka sauka. *Janafty**TFZB2024* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Saboda Gajiyan tafiya yasa ko washegari basu fita ko"ina ba Har shi Dannallam din bai iya fita ba sai Ranar Laraba suka zo gidan mallam Lokacin baki daga nesa duk sun fara Hallata irin su ya Fatima da su ya Nazifa,Mutanen Jordan kuma Suma Jiya suka iso Goggo Husai da Jadwa Sannan aranar Hidaya matar Nazir da Jaleela suka sauka suma da yammah kuma sai ga Mutanen Parthercourt su yaya zahra,Gida fa masha Allah ya fara shiga da Dangi na nesa dana kusa Sakina saiwani Hura hanci take yi tana iyayi ita a dole mai ciki sai Tsirfa take yi kala kala Saboda Sarood wanda ita batama nuna ta damu ba,Bangaran Anty Amarya kuwa itama Sai harkokinta take yi Cikin jin Dadi Saboda ai tana ganin ita yanzu bata da wata matsala ga Sakina na da Ciki gashi Zata aurar da Sa"adatu duk da abaya bata so hakan ba ammh zuwa yanzu ta hango hakan a matakin Nasararta. Aranar bata koma gidan Danmallam ba nan ta kwana wai bata son kamshin Gidansu Danmallam ko ta kanta bai bi ba ya Dauki Sarood suka koma sai da Safe bayan sun Karya sun yi wanka ya Dawo da ita. Aranar da Safe yan gusai suka iso da su ya Abida,ya zulaihat su ya Zeenatu da ya zulfa da su ya Ikram dukkansu duk sun iso domin in ba irin wannan Sha"anin ba baka samun damar zuwa gida har ka dan yi kwanaki mallam baya barin su suzo sai da wani Dalili mai karfi. Hidaya wannan karon data zo Shashen Hajiya uwa ta sake sauka kamar yadda ta saba Hajiya bata nuna komai ba ko a Fuskarta,Shiyasa Hajiya uwa ta saki jiki anata kai da kawo da ita sai dai ta ciki na ciki in sun Hadu da Anty Amarya su rika ma juna kallon baki isa ba ita Hajiya Uwa Dariya Anty Amarya ke bata in taga tana wani iyayi saboda dai tasan Cikin Sakina ma wannan karon sai yabi Rariya kamar sauran ita kuma Anty Amarya tana takama da mallam yace Wannan matsalan ta kau har Abada. Hajiya babba kuwa bata bi ta kansu ba harkan gabanta kawai take yi,Shashenta itama ba Matsaka tsinke Danginta yan maiduguri sun iso suma kwansu da kwarkwatansu Tunda ai Auta Hajiya zata aurar wannan karon Ita in kaga tana mgana ko Shawara da mallam ne ban dashi ta daina yarda da kowa Tunda ta lura yanzu Rayuwar ga yadda ta zama sai addu"a kawai wanda bakayi Tsammani ba sai ya Cutar dakai ko Hajiya Nasara da bata taba kamata da wani abu bata Saki Jiki da ita ba an ce Sau Daya ruwa yake dukam mutum yayi hankali ita kanta ya Daketa kuma tayi Hankalin Sosai. Achan gidan Aba kuwa shima yana cike da Baki na nesa dana kusa yan Gusai Dangin Aba da Dangin mamanmilu Wannan karon yadda taci Burin Bikin nan yasa gayyata ba kama hannun yaro har da wadanda basu zo nasu Zeenatu ba sun zo wannan karon Mamanmu sai shiga take tana Fita Domin tun jiya ta fara sawa tana Cirewa Da Sabbin kaya Bakinta kamar zai Tsage saboda Fara"a kanta na Fashewa duk inda ta shiga ana Balaraba sannu da kokari Allah ya Biyaki da Aljannah. Tana amsawa da Ameen tana kara jin Dadi ita ta samu Duniya,Domin yadda ta amshi kudade hannun Aba Allah kadai yasan yawansu data Mika hannu bai gaddama yake bata sannan Duk abunda tace ko bai kwantamai ba ta ZAuna Hajiyar banza ai yanzu ta sha gabanta ballatana wani chan Tsoho mallam da kansa A tunanin ta ayadda ta ci wannan Burin bata taba Hasaahen ko kawo kanta da wani abu zai iya faruwa da ita da zai Tsawarwata wannan Burin nata ba ita kawai har kan gabanta take yi Ranta Fes da Tunanin Burinta ya Cika sannan tana kan cin Duniyarta ne kamar yadda ta Tsara. Abunda bata sani ba suna nasu ne Allah ya riga ya gama nasu..Basu sani ba Ranar tonon asirinsu ya kusa zuwa..Dama dama ace suna da sani da Allah wlh kafin Ranar hakan duk zasu gudu kafin bayyanan boyayyun Fuskokinsu. Bangaran Amare kuma suna gidan su ya jafar Kamar yadda aka saba Su da sauran yan"uwansu su ya Zeenatu ya Abida ya zulaihat da su ya Ikram da su ya Sadiya har sa"adatu bata ware kanta ba wannan karom duk suna Tare ya Aisha Kadai ce bata iso ba,Abida tayi ta Kiranta sai tace mata tana tafe yau komai Dare insha Allahu. Hanne da Hamida kam sai a hankali duk sun yi wani irin sanyi su Ya Abida nata musu tsiyan Amare,gwarama Sa"adatu ta saki jikinta ana ta harkokin yin Meatpie din walima da ita tunda su ya Abida ke yinsa anan gidan shi da Donut,su damuwar su Daya ayadda  biki ya zo ammh ba Amina sannan ai Hajiya ta musu alkwarin Amina zata zo ammh basu ganta ba ko da Safen nan da suka je gidan sun mata mgana ta musu Dariya tace kada su damu Amina Zata zo insha Allahu. Ya Danmallan kuma tunda suka Dawo basu hadu dashi ba Sunga dai Sakina,shima a shashen Anty Amarya,Sai sarood dake shashen Hajiya tuni Sakina ta Daina janta kusa da ita da sun iso garin zata janye mata sai dai ka ganta zaune bangaran Hajiya tana Bin kowa da kallo in taga mutum kuma ta fara mai Mirmishin ta din nan tunda ba jin abunda mutane ke cewa take yi ba. Misalin karfe Daya na Rana Hajiya ta kira Wayar Danmaallam yana gida alokacin domin tun bayan da ya kawo Sarrod ya koma ya kwanta Gidan mallam ya cika da Hayaniya damam sun gama mgana da Aliyu kenan shima suna tafe shi da matarsa da ya"yansa sai Jibi asabar zasu koma sai ga Kiran Hajiya daman tunda ya Dawo ban da gaisuwan da sukayi Jiya basu yi wata mgana ba gwara ma mallam sun samu zama shi da Aba sun yi Hira sosai saboda gidan ya cika da Jama"a banda ma shashen Hajiya bai shiga ko"ina ba. Da Hanzari ya sake yin wanka ya sauya kaya Cikin shigar Wani Farin yadi Dinkin riga da wando na Zamani da Hula,Allah ya taimakesa ko da ya iso ana salla nan masallacin mallam Duk da bai samu duka ba ya samu Raka"a Biyu mallam ma baya nan ya Shiga Cikin Collage din Gumel ta Fce suna da taron da aka gayyaceshi. Ya Shiga gidan cike da Mutane Kansa na kasa yana gaisawa da duk wanda ya Hadu dashi har Falon Hajiya inda ya Duka yana gaisheta da goggon ninsu na maiduguri,sauran yara yaran matan kuma suna gaisheshi yagana ne tace mai Hajiya na Ciki yasa ya tashi ya shiga sarood na Dakin su Hanne ta shiga Sallah shiyasa bai ganta ba. Koda ya shiga Dakin Hajiya suna waya da ya Aisha Shi dai baisan me tace ba yadai ji Hajiya na Fadin"Shikenan Allah ya kawo ku Lafiya zaku iya tasowa yanzu..Munyi mgana da mallam kafin ya fita..! Daganan sukayi sallama shi dai yana Duke agabanta kansa a kasa Hajiya ta gama wayanta ta juyo tana Fadin"Mutanen madina..!. Kansa ya shafa yana fadin"Hajiya mun same ku lafiya..! Hajiya ta amsa da Lafiya lai daganan suka gaisa da Tambayan Hidima shuru yadan Biyo baya kafin Hajiya ta gyara Zama tana fadin"Kun yi mgana da Amina tunda ka dawo..? Kansa na kasa yace"Eh Sau daya mukayi mgana da ita Hajiya..! Hajiya ta jinjina kai tana Fadin"Daman kan mganar tahowar su ne ita da Amina..Sun gama shirin su  ni na Tsaidasu saboda Wani Dalilina..Naso Da sun sauka Amina ta wuce gidanta sai mallam yace bai kamata ba nan zata sauka tukunnah Shiyasa sai na sauya Shawara yanzu dai nace su taho ita da Aishar ne da Aminar sai yakaka da zasu zo tare da Direba..! Danmallan kansa na kasa yace"Allah ya kawosu lafiya..! Hajiya ta amsa da Ameen tana Fadin"Yau dai abunda muke Boyewa zai bayyana..Amina Zata dawo ammh ba ita kadai ba da abunda kowa zai yi mamaki..! Shidai bai ce komai ba kansa na kasa Hajiya tace"Shikenan tashi kaje kiran da nayi maka kenan daman..! Ba musu ya mike yayi mata sallama ya Fice yana tunanin murnan da Amina ke Ciki jiya da sukayi mgana sai shagwaba take mai kan sun gama shirinsu Hajiya tace su Dakata shi ya Lallasheta da fadin kada ta damu da ita za"ayi wannan sha"anin. Yau kuma bai samu ya Kirata ba,Zumudin tafiyar ne yasa ko kiransa ma batayi ba sun dai yi mgana da Aisha da Safe kan asibitin da Amina ke zuwa awo sun je sun amso Takardun duka report dinta sannan ya basu shaidar ko a ina Amina zata Haihu in suka nuna wadanan takardun Babu matsala. Yaji Dadin Hikimar Aminar da Mijinta Saboda shima yana Tunanin ba lalle Amina ta koma ba,Duk da Hajiya bata fadamai ba ammh ai tace gidanta zata Zauna ta Haihu tayi jegonta. Yana fitowa daga shashen Hajiya suka ci karo da Anty Amarya ta fito Daga kitchen nan suka gaisa har tana cemai bazai shiga ya duba Sakina bane..? Sakina na ciki kwance Zazzabi ya rufeta bai damu ba yace zai mata waya mata sun yi yawa ya samu ya fice aransa kuma bai yi niyyar kiranta ba ai tasan dashi tun shekaran jiya bata nemesa ba Shima ya shareta ai ba ita kadai garesa ba balle ya Damu sannan Ciki kuma ai ba kanta Farau ba shi Allah ya tuba ma ko ZUMUDI bai yi ba wannan karln to me za"a a nuna mai shi da ke da mai Ciki haihuwa ko yau ko gobe..? Ai karyar barazana kuma ta kare yadda ta ke wani tsirfa ma mamaki take basa shiyasa tunda suka zo tace wajen Anty Amarya zata zauna bai damu ba Ko a kwalar rigarsa. Dakin su Uzairu ya shiga suna taba Hiran inda yake sarvice daya ke shima ya Dawo shima da Safen har shamsu ya iso Dazu shima wannan Bikin fa na musamman ne kowa da kowa yana nan Saboda bikin mata ne kuma Sune na layim karshe daga su sai maza su Nazeem in sun tashin yin kenan nan kusa Har Mutanen bazanga mata da basu Cika zuwa ba sun zo wannan karon Bikin su Hamida kan kowa yasan yayi goshi. Sun Dade suna hira dashi tare sukaci Abincin Rana da Hajiya ta aiko musu dashi Tunda tasan suna cikin Gidan sai La"asar suka fita Danmallam ya bada salla bayan sun idar ne sai ga Aliyu sun iso ya fita ya tarbesa Suka gaisa da Aliyu ya Dauki karamin yaronsu Hammad ita kuma Aliya da yar macen da Cikin jikinta Daya fara fitowa suka nufi Cikin gida. Sai da ta fara zuwa shashen Hajjya suka gaisa har taga Sarood tana ganinta ta fara bashe mata baki taga wanda ta sani ammh Aliya ko kallonta batayi ba Ko Dadewa batayi ba ta baro Shashen Hajiya zuwa na Anty Amarya wajen sakina daman sun yi waya tun kafin ma su fito Daga gida. Anty Amarya sai ina ka saka da Aliya take yi ita kuma Sakinar na kwance Dakin su Sa"adatu wai bata jin dadi Zazzabi ne ya rufeta Ammh ganin Aliyan sai ta mike tana wani yamutsa Fuska. Aliya na kallonta tana Dariya tace"Masu Ciki..Yan Laulayi..! Sakina tayi far da ido kafin tace"Kedai bari tunda muka iso ban jin Dadi..komai ma baya min Dadi..Chan gidan fa warinsa tadamin Hankali yake yi na baro sa na dawo nan..! Aliya tace"Sannu sai Hakuri..Zuwa gaba zaki ji Dama dama in Laulayin ya ragu..! Sakina tace"Allah yasa ya hanya..! Ina Aliyun da hammad..? Aliya tace"Suna wajen tare da Umar..! Sakina tace"Yazo kenan..? Aliya tace"To nadai gansa a waje fa..! Sakina tace"Rabona da ganinsa tun shekaranjiya da muka zo nan..! Bai sake nema na ba. ! Ta fada cikin wani yanayi Aliya tace"To kinsan kila saboda mutane..! Sakina tace"Waya fa..! Ai sai ya Kirani yaji ya nake duk wannan wahalan da nake sha duk shine Sila fa..! Aliya tace"Kuma fa hakane..kimai Uzuri dai ammh ai naga kishiyarki dana shiga Shashen Hajiya sai wani washe min Baki take yi nayi kamar ban ganta ba. ! Sakina tayi tsaki tana fadin"Bar munafuka ita wai ta ganki ta ganeki mana..! Aliya tace"Ta gane Ubanta..!!? Aiko taga wulakanci domin ko kallo bata isheni ba..! Sakina tace"ai tunda muka zo bata kara ganina ba..Na yakiceta ajikina..! Aliya tace"Ai hakan ya kamata ina Wani Cigaba ka hada kai da kishiya..Duk fa Kirkinta sunanta Kishiya..! Sakina tace"Ai saboda na sami abunda nake so ne..kuma na samu shiyasa na yakiceta Daga jikina..! Aliya tace"Wlh hakan ma yafi..! Daganan suka cigaba da Hirarsu suna ta zagin Sarood Aliya ce ta kalli Sakina tana fadin"Wai ina ita Labarin Kazamar yarinyar nan .? Sakina tace"Wace wai..? Aliya tace"Amaryanki mana..Waa ma take da suna..? Amina take ko wa..? Sakina ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta mike tana Fadin"Ina na sani..! Nifa na manta ma da ita kwatakwata sai da kikayi mganarta..! Aliya tace"Wato ma kin manta da ita..! Ni fa ina mamakin ina Hajiya ta kaita..?har Aliyu na Tuntuba yacemim bai sani ba bama suyi mganar da Umar ba. !. Sakina tace"Ai hashashemu ya tabbata. inaga ba auran nan..! Aliya ta zaro ido tana fadin"Ta ya akayi kika sani..? Sakina ta Bude kofar Tiolet tana Fadin"To in da auran da baki ganta ba. ?ai ba haka ake aure ba Aliya. Bari nayi alwala ban yi sallah ba .! Aliya ta bita da kallo tana fadin"Nima ki fito nayi muna hanya ta same mu..! Ammh a kasan ranta tana Tunanin Ta yaya Umar zai saki Amina..? Hajiya da mallam kuma sun sani basu ce komai ba..? Gaskiya tunanin hakan bai zauna mata ba sai dai in wani abun ne Dabam ammh banda mganar Rabuwa. Sakina na fitowa itama ta shiga tayi alwala sukayi sallah bayan sun idar Aliya taci abinci suka kimtsa Sakina tace su leka wajen Walima ana ta Tafiya,Koda suka fito duk an watse har Anty Amarya ta tafi da wasu yan"uwansu Daga Dutse Hajiya ce kadai ya rage bata tafi ba sai wasu yan maiduguri,Sakina gaba sukayi ita da Aliya sai a hanya ne suka hadu da su Zulfa da Yara sun dauko musu waina da za"a raba awajen Walimar suka Dumguma zuwa haraban makarantan koda sukaje har an fara Amaren ma sun iso sun yi shigar bakaken jallabiya da Farin Hijabi Sa"adatu ne dai Fuskarta acike ammh Hanne da Hamida sai kwarmin ido,sun yi wani Zuru zuru dasu su ya Aisha ne kan gaba ke ta Hidiman Baki. Aan basu kyauttuka Hamida an bata na Tajweed da Kira"a am bama Hanne na Larabci da sanin Nahahu sai Sa"adatu ita kuma na zuwa makaranta ba Fashi Hanne sai da tayi kuka sun farota da Amina ammh yau ba ta awajen da zasu yi bankwana da makarantar su haka ma Hamida sai da sukayi kuka,su ya Abida duk sum san kukan da suke yi na rashin Amina ne suma ai sun damu sai dai ba wanda yama Hajiya mgana, ba Tarbiyansu bane yin katsaladan a Hukuncin babba sai dai su hanne sun Fada musu Hajiya tace zata zo insha Allahu. Su ya Zeenatu aka bari da lallashin su Sai da suka saki ransu,Sannan suka koma Bangaran sallaman Baki su da sauran yan ajinsu na Hadda sannan kawar Hajiya tazo tayi ma Amare nasiha sosai sai shidda na yammah aka tashi Sakina anan suka Hadu da Sarood tana ganinta ta manne mata sai Hararanta suke ita da Aliya ita ko Allah Sarki bata sani ba tana tare dasu da zuciya daya ne,Har Hajiya tazo wajen Walimar chan gabda za"a tashi mamanmu kuma ai suna gaba gaba ita da Anty Amarya sun saka kayan alfarma Anty Amarya Shadda ta saka itama mamanmu shadda ce taji aiki ammh kalan kowa Dabam kafafunsu sun ji Lalle kamar wasu yara har yan gusai nama mamanmu Tsiya ta koma yarinya tace a wajen Sa"idu ai ita yarinya ce Danya sharaf Sai Dariya take yi cikin Nishadi suma suna tayata da tsiyan da suka saba mata musamman ma abokan wasan Aba Na gusai. Ana tashi daga wajen walimar aka Dumgumo zuwa gida Amaran dai Gidan su ya jafar suka koma su da ya Zeenatu da Abida sauran kuma sun koma gidan baba mallam wasu kuma gidan Aba Dayake ana ta kiran sallar mangariba suna komawa sai kowa ya fara shirin salla a waje kuma su ya Danmallan sunyi alwala suka Shiga masallaci duk da mallam ya Dawo shi ya bada salla da mangariba suna da Karatu yasa duk suna cikim masallacin suna Sauraran karatun Baba Mallam Har Nazir da shima Gabda mangariba ya sauka Daga Lagos. Adaidai Lokacin misalin karfe bakwai da yan mintina na Dare Motar Usman Mijin Aisha prado mai lambar Abuja ajikinta ta yi Diran cin Taya a kofar gidan Baba mallam Dake Dauke da Haske Tar domin an kunna Gen da wuri saboda Sha"anin da ake ciki ko"ina Haske ya bayyana sai dai kofar Gidam ba kowa duk suma masallaci Tsit mata kuma duk suna Cikin gida. Ya Aisha ta fara fitowa bayan Direba ya Bude mta kofar Mota ita agidan gaba ta Zauna yayinda Amina da Yakaka ke gidan baya. Tana fitowa tace"Salihu bude booth ka Fito da kayan Dake Ciki Duka..! Ba musu ya amsa mata ya nufi Booth din ya Bude ya fara Fiddo da akwatunan Amina Sabbi yana jerawa a kasa ita kuma Aisha ta Bude bangaran da Yakaka take tana Fadin"Yakaka Bismillah mun iso..! Yakaka ta Fara fitowa tana Salati Lokaci Daya tana Fadin"Mun isa barka..Tafiya ai yankin azaba ce..! Lokaci Daya tana kare ma gidan mallan kallo da yanayin anguwam ta Furta"Masha Allah..yau gani agidan mallam..! Take fada daidai Lokacin da Amina ta Fito Daga Motar kofofin Hancinta na Budewa da Shakkar Iskar gumel din Data Dade bata shaka ba,Gabadaya Sai taji ta kamar ba ita ba,Sai taji kamar bakuwa ce ita tana kallon kofar gidan Mallam da nasu gidan wasu abubuwan da suka shude a baya suna Dawowa mata Daki Daki kamar yanzu komai ke faruwa Sai da taji Hawaye sun kawo mata. Tana Sanye da Doguwar riga Baka na Saudiya cikin Tsaraban Danmallan ne sai jan hijabin Dake jikinta Tunda adon Rigar ja ne,hijabin gwiwarta kadai ya Rufe Cikinta gashi nan ya bayyana Kafarta sanye Cikin Takalmi mai Saukakken Tudu kafafun sun kara kumbura saboda Zaman mota Fuskarta ta kara Cika tayi kwaba kwaba kamar Danyen Nama. Duk wanda yasan Amina abaya in ya ganta yanzu da wahala ya ganeta komai nata ya sauya. Tsaye kawai tayi tana bin gidajen nan guda Biyu data yi Rayuwarta aciki da kallo acikin Ranta tana jin wani Farimcikin da bata taba ji ba Dazu suna Hanya sun yi mgana da Danmallam yace mata dukkansu matan suna wajen Walima har suka iso Bata kara mgana ba taso ta samu Walimar su Hanne ammh Allah bai yi ba. Tana jin ya Aisha na cema Yakaka bari ta kira waya a daukan musu kaya tunda ba yara a wajen kawai sai ga Ya Shamsu ya fito Daga gida zai shiga masallaci yaga ya Aisha ya tsaya suna gaisawa tana Fadin"Shamsu yaushe ka zo..? Yace"Dazu da yammh ya Aisha sannun ku da zuwa..! Ta amsa shi kuma ya juya yana gaida Yakaka ta amsa Cikin Fara"a. Ya Aisha ke Fadamai kaya ne daman za"a dauka don Allah ko zai taimaka ya kira mata su Akilu su Daukan mata,Yace to bari yayi musu mgana suna Cikin masallaci da Hanzari ya tafi ya kirasu sai alokacin ya Aisha ta Daga kai tana kallon Amina Data jingina jikin mota batace komai ba.. Cikin kulawa tace"Amina kari so mana..Ko jikin ya rike ne zaman mota ko..? Amina sai alokacin ta tako zuwa wajensu kafin tayi mgana Yakaka ta chabe da Fadin"Dafa gajiya..Ko mu da bamu da komai mun gaji ballatana ita mai Lalura..Jiki fa ya rike sai dai mun shiga ta samu ta watsa ruwa a shafe Jikin da man zafi taji Dama Dama..! Amina ta tura Baki tana Fadin"Man zafi kuma yakaka..? Yakaka ta Harareta Tana fadin"Shine zai sakar miki jiki har kiji Dadi wannan kumburin da kikayi duk ya Saki..! Amina bata samu bakin mgana ba Sai ga Shamsu ya fito bayansa Akilu ne da Zubairu har suka kariso suka gaisa da Ya Aisha da Yakaka basu lura da Amina ba sai da Ya Aisha ta nuna musu Kayan da zasu shigar musu dashi Ciki,Saitin akwatina guda Bakwai sai kuma wani saitin mai Hudu suma Dabam sai kayan su da kuma wasu kaya a kwalaye acikin wani babban Buhu. Ya Shamsu ne ya fara ganin Amina sai ya Tsaya kawai yana kallonta kamar Amina kamar ba ita ba ita kuma ganin Haka yasa tayi mirmishi tana Fadin"Ina yini ya shamsu..! Da Sauri ya kara ware ido yana kallonta har su Akilu suma sai alokacin suka ganta da sukaji muryanta ganin ya kasa mgana ne yana kallonta Daga sama har kasa ga Muryan Amina sannan wannan kuma gata babbace ga kuma ciki ajikinta Sai da ya Aisha taga haka sannan tace"Shamsu Amina ce fa ke gaisheka..! Dukkansu kusan Hada Baki sukayi wajen Fadin"Amina..? Cikin Sigan Tambaya Yakaka tayi Dariya tana Fadin"Sun ga ta zama uwar mata ga Ciki ga shi ta yi kiba..! Amina Mirmishi kawai tayi kanta na kasa kunya taji da Yakaka ta ambaci Ciki su kuma kawai ita suke bi da kallo mamaki ya kashesu. Shamsu har yana cin Tuntube Daya Dauki kaya zai shiga gida yana waige su Akilu ma mamaki duk ya kamasu wai Amina ce ta koma haka..? Kuma har da Ciki ikon Allah..! Harda Salisu Direba a masu Daukan kaya da wasu matasa da suka gani zasu shiga masallaci Ya Aisha ta rokesu suka Daukan musu ita sai ta Dauki karamar akwatinta da na Amina yakaka kuma ta Dauki wata babbar Leda Amina bata Dauki komai ba Saboda yanayinta suka bi bayan su Shamsu zuwa Cikin gida har megadi yana masallaci wajen karatun mallam. Su ya Nazifa da su ya Fatima duk suna Tsakar gida wajem kitchen ana ta Hidima hada Miyan gobe sannan wasu kuma suna ta gyaran kajin da aka kawo daga wajen Gyarasu,Hajiya na Shashenta Hajiya Nasara ne ke Madafin tana nuna ma su lami yadda komai zai tafidaidai sauran matan kuma duk suna Dakunansu kana dai jin Tashin Muryoyinsu suna ta Hira da Shewa. Sai ga su shamsu na Shigowa da kaya ya Fatima ce ke fadin"Shamsu wannan sabbin akwatin fa Daga ina..? Ya Shamsu yace"Ya Aisha ce da Amina suka iso yanzu..! Kusan dukkansu sai da suka maimata sunan Amina cikin mamaki karaf sai a kunnen ya Sadiya tayi Zaraf ta fito Daidai Lokacin da itama Hajiya Uwa ta Fito Daga Shashenta ya Aisha ta Rafka sallama ta shigo bayanta Yakaka sai Amina Dake bayansu tana Tafiya sannu sannu kamar wata bakuwa. Tana baya ba wanda ya Lura da ita su ya Aisha ake ma maraba Jidda ke ta Fadin"Maraba da mutanen Abuja..Ai muna ta jajenki mukace Aisha shuru kowa ya iso ban da ke..! Ya Aisha ke amsa musu cikin Fara"a Tana Fadin"Wlh kuwa muna hanya Tsaiko muka dan samu..! Salihu Direba ke tambayanta ina za"a kai kayan da sauran matasa ta nuna musu bangaran Hajiya. Aisha ke nuna musu yakaka a matsayin Kakar Mijinta suna gaisawa Sai Ya Aisha ta juya ta ga Amina abaya tana tsaye kamar bakuwa Cikin Fara"a tace"Miye haka Amina kina ta Nokewa kamar wata bakuwa..! Sai kallo ya koma inda aka ji an kira sunan Amina Lokaci Daya da Anty Aisha ta jawo Hannun Amina gaban mutanen Dake zaune awajen Gabadaya ido suka saki da Hanci suna kallon Amina ita kuma kunya cikin jikinta yasa ta Sadda kanta kasa tana wasa da Gefen Hijabinta. Hajiya Nasara ta Daga Baki Cikin mamaki tana fadin"Amina ce haka..? Allah mai iko..! Karaf a kunnen mutane Dadama har da Hajiya Dake shirin fitowa Tunda taga su shamsu sun shigo da kayan tasan Aisha da Amina sun iso. Anty Amarya kuma kamar a mafarki taji Hajiya Nasara na ambaton Amina shi ya fito da ita waje.. Dukkansu kusan atare suka ga Amina Ganin daya razanasu ranazar da basu Taba Zato ko Tsammani ba Hajiya uwa wayar hannunta sai da ta Subuce ta fadi saboda razana Anty Amarya kuma gani tayi kamar ba Daidai take gani ba sai da ta kara Murza idonta sannan ta kalli Amina ta kara kallon Sadiya Dake gefenta Cikin Rudi tace"Sadiya...wai..wai wa nake gani achan kamar Amina..? Sadiya Cikin mamaki tace"Amina ce Anty..Wlh Amina ce da Tsoho ciki! Sai anty Amarya taji kafafunta sun kasa Daukanta tana neman faduwa ba Domin Sadiya ba da wani Labarin ake yi ba wannan ba. Hajiya kuwa Mirmishi a saman Fuskarta ta kariso tana musu maraba da zuwa Fadi take"Yau ga Yakaka ta Rako Takwaranta..! Yakaka Cikin Fara"a tace"Wlh Hajiya ai nina nan sai takwara ta haihu mun yi wankan jegon mu na yan maiduguri daganan ai har chan garin ma'aiki Hajiya..! Tafada Cikin Fara"a Hajiya tace"Kafarki kafar Amina Yakaka da yardan Allah har garin madina..! YaKaka tace"Insha Allahu..! Hajiya ta kalli Aisha tana fadin"Ku shiga Ciki Aisha..MAMAH..barka Dawowa..! Tafada tana riko Amina wacce ta Fada Jikin Hajiya sai kuka Hajiya na Dariyan Farimciki tace"Miye na kuka mamah..! Baga kin Dawo ba Ai Daga yau Zaman Abuja ya kare miki Daganan Sai Gidan Mijinki da yardan Allah achan zaki haihu.! Tafada cikin Fara"a tana kallon Hajiya uwani Data ke Tsaye bata ko motsi da Anty Amarya da Sadiya ke tallafe da ita Hajiya nasara ce ta kariso tana Fadin"Hajiya Wai kina nufin Cikin jikin Amina na Danmallan ne..? Hajiya tace"Kwarai ma da gaske..Ai Cikin Amina Allah ya Killacesa..Dalilinsa Daya sa na kaita wajen Aisha ta zauna kinsan kana Zaune ne da mutane bakasam magautanka ba sai anemi a salwartar da Cikin..Kinga wadanchan akwatunan kayan Lefen Amina ne da kayan Haihuwarta sannam Da dankareren gidanta da Danmallam ya siya mata Chan zata tare ta Haihu achan kafin ta gama wanka ya Dauki matarsa su wuce Madina..! Yakaka tace"Da yardan Allah kuwa..takwarata sai madina tayi kira..! Hajiya Nasara ta rangada guda tayi juyi kafin tace"Allahu akbar..Lalle Allah ne mai Hikima ashe Rabo ne tsakaninsa da Amina auran nan yazo kowa bai Zata ba..? Amina..Amina ta zama uwar mata Allah ya raba Lafiya..! Su ya Fatima ma sai Guda suke suna Shewa wanda ya fito da su Sakina Dake daki dasu Aliya dasu Jidda Daidai Lokacin da Hajiya ta riko Amina tana tafiya da kyar Saboda Cikinta. Karaf kuma suka Hada ido Hudu da Sakina kallo kallon sukama juna da Amina Sakina da sai da Cikinta ya juya mata Jikinta na rawa ta kalli Anty Amarya dake Cikin wani yanayi da ganin Amina da kuma kalaman Hajiya,bata iya ma kallonta ba Tana Faman kokuwa da yanayinta Sakina ta kara Bin Amina da kallo har suka shige shashen Hajiya Sakina ta Kalli Su Sadiya tana fadin"Wa nake gani kamar Amima..Amina da ciki..? Kafin su bata amsa Hajiya Nasara ta sake rangada guda tana Fadin"Kai wannan abun yamim Dadi..Amina Zata Haifa ma mallam jika..Amina ai Yar gaban goshim mallam ce kamar yadda Danmallam yake dan gaban goshinsa wannan jika zai zama Dan gata gaba da baya..! Ta tafada tana Dariya kafin ta kalli su ya Fatima tana fadin" ku kuma zaman me kuke yi..?. Ku tashi muje mu ga kayan arziki in ji Hajiya..!. su ya Fatima na jin haka suka mike suka bayan Haj.Nasara zuwa Shashen Hajiya babba Hajiya Nasara kamar da gayyar take yi duk da bata san komai ba tasan Anty Amarya da Sakina bazasu so haka ba. Hajiya Uwani Data kame a tsaye ga wayarta Data fashe a kasa suka Hada ido da Anty Amarya suna kallon juna. Kowannensu yana Fama da Faduwar gaba suna faman kokuwa da abunda yake shirin faruwa dasu. Awannan Lokacin kowa ta kansa kawai yake yi,Kamar Daga Sama sai ga Hajiya ta leko tana Fadin"Uwani..Amarya ku shigo kuga kaya mana kuna Tsaye jidda Sadiya ku shigo mana..! Hajiya ta Fada tana Mirmishi sum sum kamar marasa kuzari haka sukabi bayan Hajiya Sakina sai da Aliya ta rike mata hannu tana Faman girgizamata kai. Suna shigowa tsakiyar Falon Hajiya an baje kayan gasu nan Amina na Zaune a kasan acafet kusa da yakaka kanta na kasa da Dangin Hajiya sai hira suke yi taga yan gida Hajiya tace"A kiramin Balaraba baza"a bude kayan nan ba sai uwar Amina na kusa da kuma goggonta Husai da Sauran yan"uwanta mata...Ke kuma Aisha kira Abida kice su yi maza su iso ga Amina ta dawo..! Ya Aisha ta amsa ma Hajiya da toh Cikin Yan Biki kuwa har wata ta Zari Hijabi ta bazama gidan Aba kiran mamanmu da goggo Husai da Sauran yan uwan Ami a mata ita kuma Ya Aisha ta dokama Abida kira tana Fada mata sakon Hajiya ta cikin wayar tana jin Sanda tace ga Amina tazo su Hamida suka Buga ihun Murna tayi Dariya ta kashe wayarta.! _Wani abu ya bani Dariya wai yan bati association sune ke korafin wai bai kamata yaya ta mutu bata ga Tonuwar asirin mamammu ba..? da sauran mganganun da ya zama wannan Ra"ayin su ne abu daya nake so ku sani Koda wannan labarin yake kirkirarre ne,kada ku dauke sa ba gaskiya bane..Gaskiya ne wannan Labarin gaskiya ne akwai sihiri gaskiya ne akwai mutuwa a zahiri sannan gaskiya ne acikin mutane akwai mugaye mara imani Sannan gaskiya ne akwai masu shirka sannan gaskiya ne kishi ya rufe maa mata ido suna aikata komai saboda kishi Sannan gaskiya ne kan Dukiya ba abunda ba"a aikatawa a cikin wannan Rayuwar da muke ciki..Sannan mu musulmai ne mun zo Duniya domin bautar Ubangiji ne Tsarin Rayuwarmu Daga Farko har karshensa Tsararre ne sannan Rubutattace ne Daga littafanmu dake wajen Ubangiji ina so ku sani mutuwa ta Allah ce shi ke kashewa shi kuma ke rayawa..Sannan in Lokacin ka yayi baka isa ka kara ko minti Daya ba zaka bar Duniya Abunda nake so na Fada shi ne meyasa yan"uwanmu da kawayenmu ko abokan arzikim mu suke mutuwa suna cikin gabar jin Dadin Rayuwarsu..? Meyasa su bamu ce bai kamata su mutu ba..? Sannan meyasa matasa ke mutuwa suna kam cim kuruciyarsu..? Meyasa su bamu ce bai kamata su mutu ba..? Mutane nawa suka gama wahalan karatu su mutu basu ci moriyarsa ba..? Meyasa su bamu ce bai kamata su mutu ba..? Mataa nawa suka rasa rayuwansu wajen Haihuwa suka mutu suka bar Abunda suka Haifa meyasa bamu ce bai kamata su mutu ba..? To ku Sani Mutuwa gaskiya ne..Duk wanda kuka ga ya mutu iya Lokacin sa ne..Sannan bakomai bawa yake samu yadda yake so ba..Yana Tafiya ne kan Tsarin da Ubangiji ya Tsara masa..! Labarin TA FITA ZAKKA reality ne ba Kamar sauran Labaran da kuke Tunani bane.._ *Janafty**TFZB2025* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Su Mamanmu na tsakar gida suna ta Hidima akazo da labarin Hajiya tace suzo ga Amina ta dawo Mamanmu sai taji kamar bataji da kyau ba badai Amina ba,in ma Aminar ne bata taba Tunanin ganin abunda zataje ta gani ba Saboda mai Fadar bata Fadi cewa Amina da tsohon ciki ta dawo ba. Ana fadin ga Amina ta dawo kowa da kowa ya zura Hijabi har da goggo Husai da su ya Jawahir domin sun yi kewar yar kanwar tasu tarr da mutanen Gusai,har da matan su ya jafar dake gidan tunda chan gidan su Abida suka bar ma gidan su suna nan ana ta aiki dasu. Mamanmu ko Hijabi bata tsaya sawa ba,Zanin goyon Zulfa ne Dake kan igiya ta Rataya sai gidan Baba mallam itace kan gaba so take taga da gasken Aminar ne..? Domin har alokacin gabanta bai Fadi ba bata sare ba ballatana ranta ya kawo mata yau ranar Tonon asiri ce. Sai dai me suna shiga falon sai kallo ya koma kansu Mamanmu bata lura da ko su Anty Amarya ba ballatana Uban kayan lefem Dake zube a falon Hajiya Burinta kawai taga Amina domin ta gasgasta abunda aka Fadamata yasa tana shigowa ta Daga Murya tana Fadin"Ina Aminar da akace ta Dawo..? Amina..! Ta fada da dan karfi domin ita a zatonta karye ne ba wata Amina,Sai dai ga mamakinta wata ta gani kamar Amina ta mike tsaye Dakyar har Yakaka na Taimakamata ta mike Sai ga Cikinta ya bayyana Cikin Ido tana kallon Mamanmu cikin wani yanayin Da ta kasa Fassarashi tace"Ga ni nan Mamanmu..! Tafada da wani Sauti na Rauni Sai taji bata ji kunyar cikin dake jikinta ba Ko Hannunta bata saka ta kare kamar yadda ta saba ba so take taga yadda Mamanmu zatayi in ta ganta da Ciki. Aikuwa Mamanmu ido ta Zaro Jikinta ba inda baya rawa ido ta murza ta kara Murza,kamar yadda su Ya Jalela suka saki Baki suna kallon Amina sun ma kasa mgana. Goggo Husai ce Cikin mamaki tace"Amina..! Tafada tana takawa gabanta Amina sai taji kunya kanta na kasa tace"Ina yini goggo..! Sai goggo Husai ta rike baki ta kara Leka Fuskar Amina kafin ta kalli Cikin jikinta ta rike Haba tace"Ikon Allah Zainabu duk yaushe haka ta faru ba Labari ina tunanin ko Sa'idu bai Tabamin zencen Amina ba Domin da Jadwa ta fadamin bata a gida dana masa mgana yace min kinsan inda take bai taba Fadamin Halin da yarinyar nan take ciki ba..! Hajiya na Tsaye ta murmusa Kafin tace"Ai ko shi Sa"idun bai sani ba..Dagani sai mallan Sai mijinta kadai muka san da wannan cikin Husai..! Gogggo Husai ta kara jinjina kai kafin tace"To ina tayi renon Cikin..? Hajiya tace"Abuja..wajen Aisha na kaita..! Goggo Husai sai ta samu waje ta Zauna tana Fadin"Ikon Allah..! Saboda abun ya bata mamaki ne dayasa kalamanta suka kare,Mamanmu kuma kamar suman Tsaye tayi daga inda take ko motsi ta kasa kamar yadda Anty Amarya da Haj.Uwani suke Dansare a tsaye sun rasa ma wani Tunani zasu yi duk yaushe hakan ta faru..!? Su ya Jawahir kuwa karisawa gaban Amina sukayi suna kiran sunanta sai ta amsa tana gaishesu har da su ya Zulfa ya Zahra suna ta kallon Amina mamaki yasa sun ma kasa mgana ya Zulaihat ne sai da ta Rumgume Amina tana fadin"Allah Sarki Aminene..Aminene ta kusa zama uwa. ! Amina batace komai ba kanta na kasa,nan da nan falon ya kwace me da Hayaniyar mata yan gusai suma suna ta Tofa albarkacin Bakinsu,yan"uwan Amina kallonta kawai suke yi kamar wata Hallita ya Jadwa Mirmishi take yi a kasan ranta Lokaci Daya Hawaye suka kawo idonta afili ta Furta"Yau ina Yaya take..? naso tana raye taga yadda Amina ta koma..Yau Amina ce da Cikin Haihuwa Sannan uwa uba Amina tayi hankali ba mgana ba fada ba tsiwa ba kunkuni madallah da uwa irin Hajiya madallah da Uba irin Baba mallam..Sannan madallah da Gwarzom Miji irin Yaya Danmallan..! Ya Jaleela ta share kwallah ta rike Amina tana fadin"Amina naji Dadin ganinki haka naji Dadi..! Kawai sai ta Fashe da kuka itama Aminar daman kiris take jira sai kuka Yakaka ta riketa ta koma ta zauna tana Fadin"ku daina sakata kuka tana da Lalura sannan kusanta akwai Daman arhan kuka..! Kamar an ce ta kara ne haka Amina ke kuka su Jaleela ma suna Tayata su suna kukan yadda Allah ya inganta Rayuwar Amina ne da kuma kukan Rashin Uwa garesu ita kuma Amina Wani Daci ne acikin ranta in ta Dago tana ganin Mamanmu a gabanta. Mamanmu kwata kwata kamar kunnuwanta sun Dode haka taji Hajiya na lura da ita tayi Mirmishi acikin Ranta kafin ta karisa gabanta ta Dafa Kafadarta kamar wacce Shooking ya taba haka ta Zabura sai kuma taga Hajiya Daga ganin yadda tayi Firgai Firgai sai ta baka mamaki Hajiya tace"Balaraba ki karisa mana ki gaisa da yar naki..Sannan ga kayan Lefenta nan nace baza"a bude ba sai kin zo ke da sauran yan"uwanta..! Mamanmu sai taji kamar Bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana Hajiya taja Hannunta har gaban Amina sannan ta Saketa Mamanmu kafafunta ne suka kasa Daukanta ganin wani irin kallo da Amina ke Binta dashi da shigargun Idanuwanta kawai sai ta Zube agaban Amina ta saka kuka sai kallo ya koma kanta Kuka take yi sosai tana rike da Hannun Amina Fadi take yi"Amina yanzu Ciki kike dashi bansani ba..? Nice fa Mamanki Amina duk duniya ko kowa baisan Halin da kike Ciki ba Ni bai kamata na Sani ba..? Tafada Cikin Karaji da nuna yadda abun ya Dameta Goggo Husai ce tayi mgana tana Fadin"Ke Balaraba to wa ya sani..!? Kina ji ai ko Sa"idu bai sani ba..! Mamanmu sai ta rumgume Amina ta na kuka Fadi take"Amina waya yi miki Ciki..? Cikin waye ajikin ki..? Mganar ta fito ne kamar ma bata san Sadda ta fito ba sai kallo ya koma kanta Cikin mamakin kalamanta Haj.Nasara ce ta kalleta tana Fadin"Ke kam Balaraba da wata mgana kike yi Amina ai kinsan tana da miji..Cikin jikinta kuma ai Jikan mallam da Hajiya ne..! Mamanmu sai ta Dago gabadaya ta Rude idanuwanta ta fara wurgawa Cikin Falon karaf suka hada ido da Anty Amarya Dake tsaye gefenta Sakina ce da Sadiya sai Aliya sai wasu Dangin su Daga Dutse. Kallon kallon sukayi ma juna,kallon da basu taba yima juna ba Mamanmu ta kara tsurewa cikin wani yanayi ta kauda kanta kafin ta kalli Haj Nasara tana Fadin"Ba...Ba sun rabu ba. ? Sai kowa ya Zaro ido yana kallonta Mamanmu sai ta rude ta fara inda inda Tana fadin"A"a na dauka da Hajiya ta Dauketa anan ne..Auren ne ya lalace..! Sai kuma ta kara saka kuka tana Fadin"Amina kece kika koma Haka..? Allah Sarkin kyauta da kari..! Sai kuma ta kara rike Amina wacce in ta riketa kamar wani abun kyama ya Tabata yadda ta Tsani mutuwarta haka ta Tsani ganin Mamanmu shiyasa sai binta da kallon mamaki take yi kamar yadda Hajiya ke gefe tana yi Lokaci Daya tana Sakin mirmishi. Kafin wani yayi mgana su Hanne sun shigo da Ihu suna fadin ina Aminar take..? Amina na jin muryan su Hanne ta Bangaje mamanmu ta mike Cikin Fara"a da Tsantsan murna bakinta kamar zai Tsage tace"Gani nan Hanne..Hamida..! Sai kuma Hawaye Hanne ne kan gaba sai Hamida sai su ya Abida dasu Sa"adatu idon su ya rufe ko Mutanen Falon basu tsaya kallo ba ballatana Cikin jikin Amina suna ganinta Hanne ce ta fara Buga Tsalle ta fada mata Sai Hamida da Zafira wacce dazu tazo Suna murnan ganinta. Kadan ya rage su kadata Yakaka da Hajiya har suna Hada Baki wajen fadin"Ku kula fa..Tana da Lalura..! Sai Sannan sukaji wani abu mai Tauri ya Tokaresu suka Dagota suna Binta Da kallo Daga sama har kasa,cikin mamaki da Budewar Baki Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka kalli Amina Dake sharan kwallah tana kallonsu cikin Annuri fadi take"Nayi kewarku..Nayi kuka nayi kukan kewarku kamar ba gobe..! Tafada tana dora kanta saman kafadan Hanne Lokaci Daya tana rike hannuwan Hamida Zafira dake gefe Ta leka Amina tana fadin"Amina..? Amina ta kalleta tana yar Dariya tace"Na"am zafira..Zafira..!. Tafada Cikin dariya da Hawaye zafira ta jingina da kafadan Amina tana Fadin"Itace.Wlh Amina ce..! Tafada tana Dariya,Amina ta rikesu kamar ta samu salama bakinta yaki Rufuwa Hanne ta Taba Cikin Amina tana kallon Hamida kafin tace"Hamida Wlh Ciki ne ajikin Amina..! Taba kiji..! Hamida itama ta taba Cikin kafin ta kalli Hanne tana fadin"Ciki ne..Amina Zaki Haihu ne..? Sai Amina ta kasa mgana ta Buge hannunsu tana fadin"Bansani ba..! Tana hararansu Lokaci Daya kawai sai suka Bushe da Dariya ga hawaye na Binsu suka hada Baki wajen fadin"Wlh Aminene ce..! Suka koma suka rumgume juna gabadayansu suna Hawaye suna Dariya kowa afalon sai da yaji kamar yayi musu kuka ya Abida ce da ya Zeenatu suka matso kusa ya Abida ta Dafa su Hanne tana Fadin"Dillah ku matsa ai Aminar bataku ce ku kadai ba..Har damu..! Suka saki Amina suna Dariya Amina ta Daga baki Cikin Murna tace"Ya Abida..! Tafada Cikin murna kawai sai tace"Na"am Aminene..! Sai suka rumgume juna suna mai Farinciki haka ma da ya Zeenatu ta Shafa kumatun Amina tana fadin"Allah mai iko Amina ba Fada ba tsiwa..Agaida ya Danmallam..! Amina ta sunne kai tana Dariya Goggo Husai tace"Ai rabon dake tsakanin su ne yasa auran yazo Cikin gaggawa..Allah ya Rubuta wannan Rabon ajikin Amina yake..! Mamata mahaifiyar Zafira tace"Kwarai Rabo ai bai bar komai ba..! Yakaka ta amsa da cewa"Ai yana ma kisa..In aka hanasa bayyana sai ya kashe rai..! Hajiya na gefe tana ankare da motsin kowa tana dan Mirmishi sai alokacin tayi gyaran murya tana fadin"Ku Dakata da wannan murnan ga lefen Amina nan da kayan Haihuwarta..Sannan akwai gidanta da Mijinta ya siyamata an zuba komai aciki Yana Babura Road zuwa gobe in an watse taron Amare sun mika za"a raka Amina Gidanta nan zata Haihu tayi Jegonta kafin tayi Arba"in Mijinta ya Dauketa su koma inda yake aiki..! Hajiya Nasara ta zabga Kabbara ita dasu ya Abida,Ya Aisha na Dariya jin Yakaka na fadin"Kwarai Hajiya. kafata kafar Takwarata sai garin ma"aiki..! Hajiya nasara ce ta fara Bude kayan su ya Jalela na Tayata su hanne na kamkame da Amina suna zaune suma suna kallon abunda ke faruwa Lokaci Bayan Lokaci suma bin Amina da kallon mamaki ita kuma sai ta Hararesu tace"magulmatan Amare kawai..! In tace haka dadi suke ji Aminar su bata tafi ba ta dawo wannan ranar ta Farinciki ne. Akwatuna Bakwai na lefe Biyu na kayam Haihuwa gabadayansu aka Bude su a Tsakar Falon Hajiya su Anty Amarya na inda suke sun kasa motsi ballatana Mamanmu da tunda ta Jabe ta kasa tashi Haj.Uwani na daga Bakin kofa rike da Fashasshiyar wayarta ta kasa gaba ballatana baya. Hajiya ta kallesu tana Fadin"Amarya..Uwani ku kariso mana..Sakina ku kariso mana..! Tafada tana kallonsu Daya bayan Daya Har Sa"adatu data koma barayin Uwarta tana kallon ikon Allah kamar kazar da bata da maiko haka suka tako Har wajen kayan suna Tsaye ana ta Daga kayan arziki su Mamata ne gaba gaba da wata abokiyar wasan Aba ana Dagawa su ya Abida na kirga kayan. Sai da aka Kirga manya atamfofi Talatin da Biyar lesuna Takwas Materil Biyar,Shadda Hudu,Abaya shida,Ya Abida ta Daddage ta Rankwada guda ya Zeenatu na Tayata aka fara Daukan sauran Innes da kayan kwalliiya kayan arziki sai wanda ya gani aka gama aka zo na kayan Haihuwa akwati guda na Amina ne Tsalalan Atamfofi da lesuna kala goma duk an Dinka sai dayan na Kayan yara ne masu kyau da Tsada sai wanda ya gani. Mamata ta kalli kayan kafin tace"Wadan ga duk kayan na Fitar suna ne Hajiya..? Ya Aisha ce tace"Duk na sunana Mamata..Na Amina Daya..sauran kuma na Bbys dinta..! Mamata ta jinjina kai kafin tace"Allahu akbar Diyar Balaraba tayi goshi..! Goggo Husai ta gyada kai kafin tace"Kaya sun yi kyau masha Allah..Naji Dadi Allah ya sauketa Lafiya..! Ya Abida ta kara sakin guda Hanne ta mike tana Tayata ita da zafira hamida ce ke Dariya Cikin Daga murya ya Abida ta kara sakin guda Hajiya ta Harareta tana Fadin"Nan gidan bai dace da gud'a ba..kabbara ya kamata kiyi..! Ya Abida ta kara karkacewa ta saki gu'da ya Aisha ta d'aka mata duka abaya tana Fadin"Mara kunya Hajiya na mgana..! Ya Jawahir itama ta Daga hanci ta saki nata gudan Ita da ya Zulfa sai Ya Zeenatu itama tayi nata ya Abida ta kara Dorawa suka ruda Falon Hajiya Mamata ma ta Dauka goggo Husai sai Dariya take ita da yakaka Hajiya sai Faman Hararansu take yi ba"a kara Saka Dariya ba sai da Hamida ta karkace tayi nata aka kwashe mata da Dariya Har Amina sai da ta Dara Hanne na Dariya tace"Gaskiya ne Amina TA FITA ZAKKA..wannan zakkan gaskiya ne gashi mun gani..ako"ina itace Zakka komai nata na mussaman ne..! Ya Abida ta amshe da Fadin"Kwarai Wlh..Aminene badai ta mutum ba sai ta Allah..! Suka kara karkacewa wannan karon har da su ya Zulaihat suna Sakin guda Hajiya kai kawai ta kada tana Mirmishi,Amina na zaune ita da Hamida suna kallonsu suna Dariya. Da gayya Hanne da ya Abida suke wannan gudar saboda Sakina domin har Bikin nan da suka hadu bata musu mgana ba tun Lokacin auran Amina da Danmallam bata kara musu mgana ba ko sun hadu sai ta kauda kai..shiyasa suke kallonta suna kara Ruda Falon da gud'a Sakina Gabadaya ta Jike da Zufa,Jikinta ba inda baya rawa kanta ya gama Daukan abubuwan datake ji har wani Dum..Dum yake yi kamar ba nata ba Hakama Anty Amarya gadai tanan ne kawai abubuwan sun tsaya mata Cak ta kasa wani Tunani kamar yadda Mamanmu ke jabe suna jin Abun Al"ajabi tare da Tsamanin Abunda basu yi Tsammani ba..! Duk wannan Budurin da akeyi Sarood na Falon nan sai kallon kowa take yi tana Bin Baki ita ba wani sanin Amina tayi ba shiyasa bata gane komai ba ammh kuma Kayan data gani ta Zata na su Hanne ne da za"ayi ma aure gobe Ita ba Hausa take ji ba,Shiyasa sai bin Bakin Mutane kawai take achan gefe kamar ma bata afalon. Haj.Uwani ce ta juya kawai ta Fice Daga Falom Idanuwanta sun kad'a sun yi Jajir Dishi Dishi ma take gani Saboda tashin Hankali. Tana fita saboda yadda ta Rude yasa bata ko nemi Kebewa ba tana fitowa ta Laluba wayarta Allah yasa gefenta Da saura ana gani haka ta saka lambar Batula saboda yanayin Datake Ciki bama zata tsaya neman Lamba ba. Batula ta kira gabda zata katse ta Dauka Cikin karaji da wani yanayi Haj.Uwa tace"Mun shiga uku mun Lalace Batula..Hajiya ta gama lalatamin Duka shirina..Hajiya ta Ruguzamin Burina da na Dade ina Tanadinsa..! Dagachan bangaran Cikin Tashin Hankali tace"Innalillahi Uwani me ya faru..? Haj Uwani tana Sharan gumin Goshinta tace"Komai ma ya faru Batula..Komai ya Lalace..Amina ce ta Dawo da Cikin Umaru ajikinta Batula..Sannan da kayan lefe dana Haihuwa kamar za'a Bude shago sannan ga Makullin gidan daya Siya mata Batula ni fa bama shi ya Dameni ba Batula Amina Tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe..! Batula Cikin tashin Hankali tace"Ciki kuma Uwani..?. Wai Wata Amina..? Haj.Uwani na faman kokuwa da yanayinta tace"Batula Amina dai da aka Aurama Umar ita ke da Ciki fa..! Batula tace"garin yaya..! Ta yaya hakan zai faru alhalin kince kin tabbata ta sha mganin Mama..? Haj.Uwani ta Runtse ido sai Hawaye Cikin Rawan murya tace"Bansani ba Batula bansani ba..Hajiya ta shammaceni..Shammatan datamin illah har Abada..! Batula tace"To yanzu menene mafita..!? Haj.Uwa ta Share Hawayenta Tana Fadin"Bazan karaya ba..Karaya ba na wa bane Batula..Dole ne nayi Nasara Batula ko ta halin kaka ne..Saboda haka ki Tashi sammako gobe ki koma wajen Mama ki fadamata Halin da ake Ciki..Ina so kada Cikin nan ya fito Duniya..Ina so a kashe koma menene acikinta ta haifesa ba rai kada yazo Duniya da ransa..Naji Samun Cikin kuskure ne sannan Hajiya in tasan wata ai bata san wata ba..Zan nuna mata Ni Uwani Kwalbar Sharri ce ko na Fashe ina da Sauran mamora..! Batula tace"Gobe goben nan zan yi sammako..Wannan Labarin ya Firgitani ammh Hajiyar nar Allah ya Tsine mata albarka..! Haj.Uwani Cikin Huci tace"Nayi alkwarin sai na Tarwatsa Farincikin su..Sai na Lalata musu wannan jin Dadin na su..! Daga haka ta Datse kiran tana Sakin Huci kamar zakayan,Ta juyo a Fusace Kawai sai taci karo da Hajiya Tsaye da waya a Hannunta tana kallon Hajiya uwani Cikin wani yanayi. Haj Uwani gabanta ya fadi ta Zaro Ido Jiki na rawa tana kallon Hajiya wacce ta Daga mata wayar hannunta ta nuna mata Sai ga sunan MALLAM baro baro alaman kira yana tafiya minti Goma sha Biyar alamun tun fara mganarta da Batula.. Jikinta na rawa Gabanta na Faduwa Zufa na keto mata ta ko"ina kawai sai ta Duka kan gwiwoyinta Domin tagama sanin Hajiya tasan wannan Boyayiyar Fuskar nata. Cikin Rawan murya ta hada Hannayenta tana Fadin"Dom Allah Hajiya ki Rufamin asiri sharrin Shedan ne..! Hajiya tayi mirmishin Takaici kafin ta kada kai tace"Ni ban isa na rufa miki  asiri ba Uwani..Asirinki Daman chan a bankade yake..Duk wanda yace Tukuyar wani bazata tafasa ba to nashi ko Dumi bazatayi ba..Ki Fito ki Fallasa kanki Uwani Domin asirinki ya gama Tonuwa kinga wannan wayar..!.To mallam ne akan layi tun Fara mganarki da kanwarki yaji komai ki jira sakamakon ki Uwani..! Daga haka ta katse wayarta agaban Haj.Uwani Dake zufa ko"ina na jikinta na rawa ta juya ta koma Shashenta Haj.Uwani na Rarrafe tabi bayanta tana kiran sunanta Hajiya Cikin wani yanayi ko waige bata karayi ba. Tana shigowa Falon nata ta iske su Abida nata shewa sun tasa Amina gaba da  shakiyanci sannan sauran matan kuma suna ta kara Daga kaya. Anty Amarya ta kallah Dake Tsaye ta kasa gaba ballatana baya Mamammu kawai take kallo Tana auna yadda Balaraba ta raina mata wayau Saboda rashin ta ido ta gagije ta koma Cikin su Mamata ana ta Daga kaya da ita babu Abunda ya shafeta ko Kaffara bazatayi ba Karya ne balaraba tace batasan Amina nada Ciki ba..? Ita Zata rufe abai bai..? Daman ai Tun tuni ta daina Hada hanya da ita saboda taga ta riga ta gama Taimaka mata ta samu Duniya shine zataci Amanarta ta juya mata baya..? Wlh yadda tayi alkwarin indai nata Burin bai cika ba to gayyar sai ta watse. Tana cikin wannan Tunanin ne kawai Taji Ihun Sakina da Sauri ta juya sai taga Sakina a kasa tana gunjin kuka su Aliya na riketa da Sauri  Anty Amarya ta kariso da Sauri tana rike Sakina bata so tayi wani abun da Hankalin Mutane zai dawo kansu yasa Cikin Tsawa tace"Miye haka Sakina.? Aliya da Sadiya ku kama min ita muje Bangarena .! Tafada tana kokarin wucewa Sakina tayi kukan kura ta Fincike daga rikon su Sadiya ta dira gaban Anty Amarya Duk da yadda Cikinta ke murda mata Ammh ina idonta ne ya Rufe bata ganin kowa sai Hango Amina da Ciki da kuma Uban Dukiyan da Umar ya Laftama Amina. Anty Amarya ta kauce ma Sakina tana Fadin"Miye haka..?muje bangarena Sakina..! Tafada tana kama Hannunta ganin yadda Hankalin kowa ya koma kansu Sakina ta Fizge hannunta Tana kallon Anty Amarya da Jajayen idanuwanta Cikin karaji tace"Ba inda zamu. Anan zamu yita ta kare..! Tafada Sai hawaye Anty Amarya tasan bata Cikin Hayyacinta yasa ta Fizge ta zasu bar Falon ammh sai Sakina ta Kwace hannunta ta Turke Anty Amarya tana Fadin"Kunya kike ji kada mutane su ji yadda kika Dade kina Rainamin wayau Anty..? Tafada tana sakar mata manyan Idanuwanta, Anty Amarya ta Zaro Ido Tana Fadin"Sakina kina cikin Hayyacinki kuwa..? Sakina ta Kwashe da wata Dariya kafin tace"Eh tabbas bana cikin Hayyacina..Daman ai na Haukace..kalli kazamar yarinyar nan da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe..Ni kuma kalleni shekara ta nawa ina Wahala ban samu ba..! Koda yaushe mganar ki kenan na kwantar da Hankali na ni kadai zan zana Mowa a wajen Umar da Danginsa..Hakan ne Mowa..? Ki kalli abunda ke faruwa a Falon nan kowa ni yake ma kallon kaskasci wannan ne Mowar..? Ko dai Bora na zama mara amfani..? Ina alkawarin naki..? Ashe duk karyace bazaki iya komai ba Daga ke har malaminki makaryata ne Babu abunda zaku iya tunda har Amina ta Samu Ciki da Umar baku sani ba..! Ta karishe Fada Cikin gunjin kuka Lokaci Daya tana jijjiga kafadun Anty Amarya tana Cigaba da Fadin"Kin manta kin Fadamin auran Amina haka zai kare a banza..? Kin manta kin Fadamin yadda aka Daurasa haka za"a kwance sa..? Ashe duk karya ce..? Ashe ni kika raina ma wayau Marliya..? Ta karishe Fada Cikin Tsawa da Budewar Murya da ya Sandarar da kowa acikin Falon har da su Sadiya da Jidda da suka zaro ido sun kasa Fahimtar me ya faru Hajiya na gefe tana kallonsu tayi mirmishi takaici ta Harde Hannayenta saman kirji Tana kallon abunda ke faruwa. sakina ta sulale kasa tana kuka Tana Fadin"kin cuceni kin sa na yarda da kowa sama Dake...Ashe karya kike Fadamin..Ashe bazaki iya ba..Bazaki iya ba..! Tafada tana Saka fuskarta Cikin Tafukan Hannayenta tana wani irin kukan Bakinciki da kishi. Anty Amarya tana kokarin Daidaita kanta kada su tona ma kansu asiri ta Duka Zata riko Sakina tana Fadin"Sakina Saurare n..! "Kada ki kara Tabani malama..! Sakina ta Katseta Cikin karaji da sai da Anty Amarya ta fadi kasa jidda da Sadiya suka karisa suka riketa Jidda Ta kalli Sakina Cikin bacin rai Tana Fadin"Sakina Lafiyan ki kuwa..? Kada Zafin kishi ya saka ki rasa natsuwarki mana..! Sakina ta Dago Jajayen idanuwanta Ta balla mata Harara kafin tayi mgana Anty Amarya tayi saurin kwace jikinta cikin nasu Jidda tana Fadin"Yau za"ayi walkiya kowa zai bayyana..Na rantse da Allah ni MADINA bazan karbi Faduwa ni kadai ba..Sai dai mu yi Faduwar Guzuma..! Tafada Lokaci Daya tana neman Balaraba Dake falon sai kawai ta Tsince ta Sum sum zata fice tun da taga Abunda ke faruwa tsakanin Madina da Sakina ta fara kokarin Barin Falon Cikin Rawan jiki Anty Amarya na Hangenta ta Daka Tsalle ta Rikota tana Fadin"Ina zaki kuma..? Munafuka..Ai sai ki Tsaya kiga yadda wasan zai kare ko DAYYABA..? Tafada Cikin tsaananin Tashin Hankali Datake Ciki da Jajayen Idanuwanta. Mamanmu ta fara kokarin kwace kanta Cikin Borin kunya tana Fadin"wata dayyaban kuma..? Marliya kada Zafin kishin ganin Amina da Ciki yasa ki fara Hauka mana.. Ko kafin ta rufe Baki Anty Amarya ta Tsinketa da mari mai Lafiya sai da kowa afalon ya Zaro ido Cikin mamaki Mamanmu sai da ta Duke Anty Amarya ta Bita ta Chakumo Wuyan riganta cikin karaji take fadin"Zaki ga Hauka yanzu nan Don Kutumar Ubanki Dayyaba..! Lokaci Daya ta Jawo ta Tsakiyar Falon kamar kayan wanki ya Zulfa ta tare Anty Amarya tana fadin"Meyasa kika mareta kuma kike janta haka..? Anty Amarya ta balla mata Harara da Jajayen Idanuwanta tana Fadin"Matsa ki bani wuri..Ai ke Mamanmu kika sani Balaraba baki san Wacece DAYYABA..ba yau zaku san aihinin wacece Fuskar wannan azzaluman matar..! Sai kowa ya saki Baki Amina na Zaune tayi Dariya jin Dadi sai Hawaye afili ta Furta"Komai yazo karshe..! Hamida ta kalleta Cikin wani yanayi tana Fadin"Me..ya ke faruwa..? Sai Amina ta kasa ce mata komai Tsausayi suke bata yau zasu yi kwanan bakinciki in suka gano wacece ainihin mamansu. Anty Amarya ta yarfar da Mamanmu nan Tsakiyar Falon Hajiya Goggo Husai ta mike tana Fadin"Ke marliya meye haka kuke yi kamar wasu yara..? Anty Amarya ta Cire Dankwalinta Taci Damara tana Zaran ido ta nuna mamanmu Dake kifta ido ta rasa mafita Tace"Wannan zaku tambaya Abunda ya faru..Domin tasan komai..Nima shi nake tambayanta yanzu..Dayyaba ni zaki munafunta..? Ni zaki yaudara ki Ha"inceni..? Wlh na yi Rantsuwan ko kaffara bazan yi ba kinsan inda Amina take da Halin Datake Ciki gani kikayi Burinki ya Cika Kin KASHE YAYA..sannan kin Samu Sa"idu yadda kike Fata shine yasa kika juyamin baya..? To wlh kin yi Kuskure Ni Madina Fitilar Sharri ce ko ba kalanzir sai na kai Safe yadda ta bare dani da Uban kowa sai ta bare yau..! Tafada Cikin karaji da Ihu kamar wata Mahaukaciya Daidai Lokacin da su Mallam sukayi sallama suka shigo Falon bayan sa kaf Zaratan ya"yansa ne kama Daga ya Danmallam Nazir ,Nasir,Nazeem,Jafar Uzairu,Shamsu Akilu da zubairu, Da Aba Aliyu abokin ya danmallam atare suka bayyana acikin Falon sai kuma waje ya Dau shuru kallo ya koma wajensu mallam. Hajiya na ganinsu ta murmusa kafin tace"Yauwa ku kariso..Yau abun dake Boye ne zai fito Fili..anyi walkiya za"a ga kowa sannan an Dade ana ruwa kasa na Shanyewa...! Kai Tsaye ta maida kallonta kan Anty Amarya da ko ganin su mallam bata Damu ba Burinta kawai gayyar ta watse Cikin wata murya tace"Marliya naj kin Fadi wata mgana da sunan HADIZA..? me kike so ki fada ne..? Anty Amarya ta kalli Mamanmu wacce ta ke kallonta Cikin Zaro Ido Jikinta na rawa ta tuma gaban Madina ta rike kafarta tana fadin"Madina don girma Allah ki rufamin asiri..Wlh na Rantse da wanda raina ke hannunsa bansan komai kan cikin Amina ba..! Anty Amarya ta saka kafa ta Ture Mamanmu ta fadi Gefe Cikin Taruwan Hawaye tace"Wlh baki isa ba Balaraba..Ai ke kwalba ce uwar Sharri..Qur"ani kadai zaki Fadamin na yarda Dake..! Yadda Kasuwar ta bare dani ban ci Riba ba kema yau sai ta bare dake Dayyaba..! Tafada Lokaci Daya ta maida kallonta kan su Hajiya tana fadin"Hajiya..Mallam Sa"idu ina ya"yan Yaya su Jadwa..? Tafada tana Binsu da kallo Cikin son suji me take son Fada suka tsura mata ido Ta juya tana kallon Mamanmu dake kuka tana rokonta kada ta Fada ta juya mata baya ta kalli Idon Aba tace"Kunga wannan matar ba Matar kwarai bace..Shekarun data kwashe tana Zaune daku duk na Cutarwarce..Muguwa ce Azzaluma ni Duk Mugunta na ban taba Kisa ba..Ammh Kunga wannan..? To Tayi kisan kai ta kashe rai Har Lahira..! Aba Cikin rawan baki dana murya yace"Wa...ta Kashe..? Kafin ta samu bakin mgana Daga bayansu sukaji wata murya Cikin Kuna tace "YAYA TA KASHE ABA..! Sai kallo ya koma inda akaji mganar sai ga Amina ta bayyana a Tsakiyar Falin gaban Anty Amarya da Mamanmu da ke tsuggune cikin Fitar hawaye Duka Biyu. Gabadaya sai kowa yaji wani sanyin jiki Aba sai da ya Dafa ya Danmallam Dake gefensa saboda jirin Daya kwashesa Anty Amarya kuma Amina take kallo da Mamakin a ina tasan wannan mganar..? Mamanmu kuma kasa kawai tayi Dakai yauma Tubular sara"i babu Tsima babu Dubara. Ya jalela da su ya Jadwa suman Tsaye sukayi ya jafar ne ya iya takowa ya iso gaban Amina ganinta da Ciki ba shi ne agabansa ba mganar data Fada ne abun Damuwa.. Cikin Fitan Hayyaci ya kama jijjiga Kafadun Amina yana Fadin"Wata Yayar ne ta kashe..? UMMANMU..? Ya fada Cikin Tsawa Idanuwansa Jajir kawai sai Amina ta Fashe da kuka ta Fada Jikin ya jafar tana nuna Mamanmu Cikin wata murya tana Fadin"Itace ta kashe mana Uwa ya Jafar..Itace ta rabamu da Aba..Itace ta rabani da Uwata Shekaru goma da wani abu bansan Dadinta ba.. Itace ta maka asiri domin ka lalace sai abun ya Dawo kaina. Itace ta hada kai da Anty Amarya ana Zaluntar ya Danmallam itace kuma suka ka Hada kai domin su ga bayan aurena da ya danmallan da alwashin har Abada bazan taba Haihuwa ba.. Ya jafar wlh wannan matar muguwace kuma azzaluma ce ta Dade tana Zaluntarmu bamu sani ba..itace ta kashe mana YaYA DA kunnena naji ta tana Fada..! Ta karishe fada Numfashinta na Sarkewa,Ya Jafar ya riketa Cikin wani yanayi yanayin da baya fatan ya Bude ido yaga abunda ke faruwa da gaske ne. Durkushewa Amina tayi kasa Jafar ya Bita ya Tallafeta,ya Danmallam ya kariso ya riketa yana Cire mata Hijabi Saboda ta samu iska tana ganinsa ta Damke hannunta Cikin rawan murya tana Fadin"itace..Ita ta kashe mana YAYA..! Malam dake tsaye yace"innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..! Sai kowa afalon ya Dauka Saboda kowa ya rasa abun Fadi. Mamanmu na wani irin gunjin kuka tace"Kaico na..Bansan akwai wannan ranar ba..Da ban aikata abunda na aikata ba..Don Allah ku yafemin..! Gabadaya kallonta kawai ake yi Cikin Wani yanayi Aba kuma zaman dirshan yayi a kasan Cafet ya kasa mgana su ya Jadwa kuma suna dai Tsaye da karfin Imani. Hajiya ce ta kalli mamanmu tana Fadin"Balaraba me Hadiza ta miki kika Kasheta kika raba ta da wannan Duniyar..? Tafada cikin wani yanayin muryanta kamar zatayi kuka Ranar da Danmallan yazo mata da wannan mganar bata gasgasta ba har yau tana cikin Tantaman balaraba zata iya Kasje Yaya sai yanzu da komai yake neman bayyana. Mamanmu tana kuka kanta na kasa ta kasa Dago kanta saboda kunya balle ta kalli Ya"yanta da yayan yaya ga Aba ga kunya mutanen Dake falon Anty Amarya kuma na Tsaye ta shirya komai ayau Sakina ma duk suna gefe banda kuka babu abunda take yi. Amina kuma Danmallam jikinsa ya Tarairayota ya azata yana ta faman mata fifita da Hijabinta Sakina na kallonsu tana jin kamar ta mutu saboda bakinciki. Kan Mamanmu na kasa ta fara mgana. "SOYAYYAR SA"IDU CE SILA..." *Janafty**TFZB2025* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Su Mamanmu na tsakar gida suna ta Hidima akazo da labarin Hajiya tace suzo ga Amina ta dawo Mamanmu sai taji kamar bataji da kyau ba badai Amina ba,in ma Aminar ne bata taba Tunanin ganin abunda zataje ta gani ba Saboda mai Fadar bata Fadi cewa Amina da tsohon ciki ta dawo ba. Ana fadin ga Amina ta dawo kowa da kowa ya zura Hijabi har da goggo Husai da su ya Jawahir domin sun yi kewar yar kanwar tasu tarr da mutanen Gusai,har da matan su ya jafar dake gidan tunda chan gidan su Abida suka bar ma gidan su suna nan ana ta aiki dasu. Mamanmu ko Hijabi bata tsaya sawa ba,Zanin goyon Zulfa ne Dake kan igiya ta Rataya sai gidan Baba mallam itace kan gaba so take taga da gasken Aminar ne..? Domin har alokacin gabanta bai Fadi ba bata sare ba ballatana ranta ya kawo mata yau ranar Tonon asiri ce. Sai dai me suna shiga falon sai kallo ya koma kansu Mamanmu bata lura da ko su Anty Amarya ba ballatana Uban kayan lefem Dake zube a falon Hajiya Burinta kawai taga Amina domin ta gasgasta abunda aka Fadamata yasa tana shigowa ta Daga Murya tana Fadin"Ina Aminar da akace ta Dawo..? Amina..! Ta fada da dan karfi domin ita a zatonta karye ne ba wata Amina,Sai dai ga mamakinta wata ta gani kamar Amina ta mike tsaye Dakyar har Yakaka na Taimakamata ta mike Sai ga Cikinta ya bayyana Cikin Ido tana kallon Mamanmu cikin wani yanayin Da ta kasa Fassarashi tace"Ga ni nan Mamanmu..! Tafada da wani Sauti na Rauni Sai taji bata ji kunyar cikin dake jikinta ba Ko Hannunta bata saka ta kare kamar yadda ta saba ba so take taga yadda Mamanmu zatayi in ta ganta da Ciki. Aikuwa Mamanmu ido ta Zaro Jikinta ba inda baya rawa ido ta murza ta kara Murza,kamar yadda su Ya Jalela suka saki Baki suna kallon Amina sun ma kasa mgana. Goggo Husai ce Cikin mamaki tace"Amina..! Tafada tana takawa gabanta Amina sai taji kunya kanta na kasa tace"Ina yini goggo..! Sai goggo Husai ta rike baki ta kara Leka Fuskar Amina kafin ta kalli Cikin jikinta ta rike Haba tace"Ikon Allah Zainabu duk yaushe haka ta faru ba Labari ina tunanin ko Sa'idu bai Tabamin zencen Amina ba Domin da Jadwa ta fadamin bata a gida dana masa mgana yace min kinsan inda take bai taba Fadamin Halin da yarinyar nan take ciki ba..! Hajiya na Tsaye ta murmusa Kafin tace"Ai ko shi Sa"idun bai sani ba..Dagani sai mallan Sai mijinta kadai muka san da wannan cikin Husai..! Gogggo Husai ta kara jinjina kai kafin tace"To ina tayi renon Cikin..? Hajiya tace"Abuja..wajen Aisha na kaita..! Goggo Husai sai ta samu waje ta Zauna tana Fadin"Ikon Allah..! Saboda abun ya bata mamaki ne dayasa kalamanta suka kare,Mamanmu kuma kamar suman Tsaye tayi daga inda take ko motsi ta kasa kamar yadda Anty Amarya da Haj.Uwani suke Dansare a tsaye sun rasa ma wani Tunani zasu yi duk yaushe hakan ta faru..!? Su ya Jawahir kuwa karisawa gaban Amina sukayi suna kiran sunanta sai ta amsa tana gaishesu har da su ya Zulfa ya Zahra suna ta kallon Amina mamaki yasa sun ma kasa mgana ya Zulaihat ne sai da ta Rumgume Amina tana fadin"Allah Sarki Aminene..Aminene ta kusa zama uwa. ! Amina batace komai ba kanta na kasa,nan da nan falon ya kwace me da Hayaniyar mata yan gusai suma suna ta Tofa albarkacin Bakinsu,yan"uwan Amina kallonta kawai suke yi kamar wata Hallita ya Jadwa Mirmishi take yi a kasan ranta Lokaci Daya Hawaye suka kawo idonta afili ta Furta"Yau ina Yaya take..? naso tana raye taga yadda Amina ta koma..Yau Amina ce da Cikin Haihuwa Sannan uwa uba Amina tayi hankali ba mgana ba fada ba tsiwa ba kunkuni madallah da uwa irin Hajiya madallah da Uba irin Baba mallam..Sannan madallah da Gwarzom Miji irin Yaya Danmallan..! Ya Jaleela ta share kwallah ta rike Amina tana fadin"Amina naji Dadin ganinki haka naji Dadi..! Kawai sai ta Fashe da kuka itama Aminar daman kiris take jira sai kuka Yakaka ta riketa ta koma ta zauna tana Fadin"ku daina sakata kuka tana da Lalura sannan kusanta akwai Daman arhan kuka..! Kamar an ce ta kara ne haka Amina ke kuka su Jaleela ma suna Tayata su suna kukan yadda Allah ya inganta Rayuwar Amina ne da kuma kukan Rashin Uwa garesu ita kuma Amina Wani Daci ne acikin ranta in ta Dago tana ganin Mamanmu a gabanta. Mamanmu kwata kwata kamar kunnuwanta sun Dode haka taji Hajiya na lura da ita tayi Mirmishi acikin Ranta kafin ta karisa gabanta ta Dafa Kafadarta kamar wacce Shooking ya taba haka ta Zabura sai kuma taga Hajiya Daga ganin yadda tayi Firgai Firgai sai ta baka mamaki Hajiya tace"Balaraba ki karisa mana ki gaisa da yar naki..Sannan ga kayan Lefenta nan nace baza"a bude ba sai kin zo ke da sauran yan"uwanta..! Mamanmu sai taji kamar Bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana Hajiya taja Hannunta har gaban Amina sannan ta Saketa Mamanmu kafafunta ne suka kasa Daukanta ganin wani irin kallo da Amina ke Binta dashi da shigargun Idanuwanta kawai sai ta Zube agaban Amina ta saka kuka sai kallo ya koma kanta Kuka take yi sosai tana rike da Hannun Amina Fadi take yi"Amina yanzu Ciki kike dashi bansani ba..? Nice fa Mamanki Amina duk duniya ko kowa baisan Halin da kike Ciki ba Ni bai kamata na Sani ba..? Tafada Cikin Karaji da nuna yadda abun ya Dameta Goggo Husai ce tayi mgana tana Fadin"Ke Balaraba to wa ya sani..!? Kina ji ai ko Sa"idu bai sani ba..! Mamanmu sai ta rumgume Amina ta na kuka Fadi take"Amina waya yi miki Ciki..? Cikin waye ajikin ki..? Mganar ta fito ne kamar ma bata san Sadda ta fito ba sai kallo ya koma kanta Cikin mamakin kalamanta Haj.Nasara ce ta kalleta tana Fadin"Ke kam Balaraba da wata mgana kike yi Amina ai kinsan tana da miji..Cikin jikinta kuma ai Jikan mallam da Hajiya ne..! Mamanmu sai ta Dago gabadaya ta Rude idanuwanta ta fara wurgawa Cikin Falon karaf suka hada ido da Anty Amarya Dake tsaye gefenta Sakina ce da Sadiya sai Aliya sai wasu Dangin su Daga Dutse. Kallon kallon sukayi ma juna,kallon da basu taba yima juna ba Mamanmu ta kara tsurewa cikin wani yanayi ta kauda kanta kafin ta kalli Haj Nasara tana Fadin"Ba...Ba sun rabu ba. ? Sai kowa ya Zaro ido yana kallonta Mamanmu sai ta rude ta fara inda inda Tana fadin"A"a na dauka da Hajiya ta Dauketa anan ne..Auren ne ya lalace..! Sai kuma ta kara saka kuka tana Fadin"Amina kece kika koma Haka..? Allah Sarkin kyauta da kari..! Sai kuma ta kara rike Amina wacce in ta riketa kamar wani abun kyama ya Tabata yadda ta Tsani mutuwarta haka ta Tsani ganin Mamanmu shiyasa sai binta da kallon mamaki take yi kamar yadda Hajiya ke gefe tana yi Lokaci Daya tana Sakin mirmishi. Kafin wani yayi mgana su Hanne sun shigo da Ihu suna fadin ina Aminar take..? Amina na jin muryan su Hanne ta Bangaje mamanmu ta mike Cikin Fara"a da Tsantsan murna bakinta kamar zai Tsage tace"Gani nan Hanne..Hamida..! Sai kuma Hawaye Hanne ne kan gaba sai Hamida sai su ya Abida dasu Sa"adatu idon su ya rufe ko Mutanen Falon basu tsaya kallo ba ballatana Cikin jikin Amina suna ganinta Hanne ce ta fara Buga Tsalle ta fada mata Sai Hamida da Zafira wacce dazu tazo Suna murnan ganinta. Kadan ya rage su kadata Yakaka da Hajiya har suna Hada Baki wajen fadin"Ku kula fa..Tana da Lalura..! Sai Sannan sukaji wani abu mai Tauri ya Tokaresu suka Dagota suna Binta Da kallo Daga sama har kasa,cikin mamaki da Budewar Baki Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka kalli Amina Dake sharan kwallah tana kallonsu cikin Annuri fadi take"Nayi kewarku..Nayi kuka nayi kukan kewarku kamar ba gobe..! Tafada tana dora kanta saman kafadan Hanne Lokaci Daya tana rike hannuwan Hamida Zafira dake gefe Ta leka Amina tana fadin"Amina..? Amina ta kalleta tana yar Dariya tace"Na"am zafira..Zafira..!. Tafada Cikin dariya da Hawaye zafira ta jingina da kafadan Amina tana Fadin"Itace.Wlh Amina ce..! Tafada tana Dariya,Amina ta rikesu kamar ta samu salama bakinta yaki Rufuwa Hanne ta Taba Cikin Amina tana kallon Hamida kafin tace"Hamida Wlh Ciki ne ajikin Amina..! Taba kiji..! Hamida itama ta taba Cikin kafin ta kalli Hanne tana fadin"Ciki ne..Amina Zaki Haihu ne..? Sai Amina ta kasa mgana ta Buge hannunsu tana fadin"Bansani ba..! Tana hararansu Lokaci Daya kawai sai suka Bushe da Dariya ga hawaye na Binsu suka hada Baki wajen fadin"Wlh Aminene ce..! Suka koma suka rumgume juna gabadayansu suna Hawaye suna Dariya kowa afalon sai da yaji kamar yayi musu kuka ya Abida ce da ya Zeenatu suka matso kusa ya Abida ta Dafa su Hanne tana Fadin"Dillah ku matsa ai Aminar bataku ce ku kadai ba..Har damu..! Suka saki Amina suna Dariya Amina ta Daga baki Cikin Murna tace"Ya Abida..! Tafada Cikin murna kawai sai tace"Na"am Aminene..! Sai suka rumgume juna suna mai Farinciki haka ma da ya Zeenatu ta Shafa kumatun Amina tana fadin"Allah mai iko Amina ba Fada ba tsiwa..Agaida ya Danmallam..! Amina ta sunne kai tana Dariya Goggo Husai tace"Ai rabon dake tsakanin su ne yasa auran yazo Cikin gaggawa..Allah ya Rubuta wannan Rabon ajikin Amina yake..! Mamata mahaifiyar Zafira tace"Kwarai Rabo ai bai bar komai ba..! Yakaka ta amsa da cewa"Ai yana ma kisa..In aka hanasa bayyana sai ya kashe rai..! Hajiya na gefe tana ankare da motsin kowa tana dan Mirmishi sai alokacin tayi gyaran murya tana fadin"Ku Dakata da wannan murnan ga lefen Amina nan da kayan Haihuwarta..Sannan akwai gidanta da Mijinta ya siyamata an zuba komai aciki Yana Babura Road zuwa gobe in an watse taron Amare sun mika za"a raka Amina Gidanta nan zata Haihu tayi Jegonta kafin tayi Arba"in Mijinta ya Dauketa su koma inda yake aiki..! Hajiya Nasara ta zabga Kabbara ita dasu ya Abida,Ya Aisha na Dariya jin Yakaka na fadin"Kwarai Hajiya. kafata kafar Takwarata sai garin ma"aiki..! Hajiya nasara ce ta fara Bude kayan su ya Jalela na Tayata su hanne na kamkame da Amina suna zaune suma suna kallon abunda ke faruwa Lokaci Bayan Lokaci suma bin Amina da kallon mamaki ita kuma sai ta Hararesu tace"magulmatan Amare kawai..! In tace haka dadi suke ji Aminar su bata tafi ba ta dawo wannan ranar ta Farinciki ne. Akwatuna Bakwai na lefe Biyu na kayam Haihuwa gabadayansu aka Bude su a Tsakar Falon Hajiya su Anty Amarya na inda suke sun kasa motsi ballatana Mamanmu da tunda ta Jabe ta kasa tashi Haj.Uwani na daga Bakin kofa rike da Fashasshiyar wayarta ta kasa gaba ballatana baya. Hajiya ta kallesu tana Fadin"Amarya..Uwani ku kariso mana..Sakina ku kariso mana..! Tafada tana kallonsu Daya bayan Daya Har Sa"adatu data koma barayin Uwarta tana kallon ikon Allah kamar kazar da bata da maiko haka suka tako Har wajen kayan suna Tsaye ana ta Daga kayan arziki su Mamata ne gaba gaba da wata abokiyar wasan Aba ana Dagawa su ya Abida na kirga kayan. Sai da aka Kirga manya atamfofi Talatin da Biyar lesuna Takwas Materil Biyar,Shadda Hudu,Abaya shida,Ya Abida ta Daddage ta Rankwada guda ya Zeenatu na Tayata aka fara Daukan sauran Innes da kayan kwalliiya kayan arziki sai wanda ya gani aka gama aka zo na kayan Haihuwa akwati guda na Amina ne Tsalalan Atamfofi da lesuna kala goma duk an Dinka sai dayan na Kayan yara ne masu kyau da Tsada sai wanda ya gani. Mamata ta kalli kayan kafin tace"Wadan ga duk kayan na Fitar suna ne Hajiya..? Ya Aisha ce tace"Duk na sunana Mamata..Na Amina Daya..sauran kuma na Bbys dinta..! Mamata ta jinjina kai kafin tace"Allahu akbar Diyar Balaraba tayi goshi..! Goggo Husai ta gyada kai kafin tace"Kaya sun yi kyau masha Allah..Naji Dadi Allah ya sauketa Lafiya..! Ya Abida ta kara sakin guda Hanne ta mike tana Tayata ita da zafira hamida ce ke Dariya Cikin Daga murya ya Abida ta kara sakin guda Hajiya ta Harareta tana Fadin"Nan gidan bai dace da gud'a ba..kabbara ya kamata kiyi..! Ya Abida ta kara karkacewa ta saki gu'da ya Aisha ta d'aka mata duka abaya tana Fadin"Mara kunya Hajiya na mgana..! Ya Jawahir itama ta Daga hanci ta saki nata gudan Ita da ya Zulfa sai Ya Zeenatu itama tayi nata ya Abida ta kara Dorawa suka ruda Falon Hajiya Mamata ma ta Dauka goggo Husai sai Dariya take ita da yakaka Hajiya sai Faman Hararansu take yi ba"a kara Saka Dariya ba sai da Hamida ta karkace tayi nata aka kwashe mata da Dariya Har Amina sai da ta Dara Hanne na Dariya tace"Gaskiya ne Amina TA FITA ZAKKA..wannan zakkan gaskiya ne gashi mun gani..ako"ina itace Zakka komai nata na mussaman ne..! Ya Abida ta amshe da Fadin"Kwarai Wlh..Aminene badai ta mutum ba sai ta Allah..! Suka kara karkacewa wannan karon har da su ya Zulaihat suna Sakin guda Hajiya kai kawai ta kada tana Mirmishi,Amina na zaune ita da Hamida suna kallonsu suna Dariya. Da gayya Hanne da ya Abida suke wannan gudar saboda Sakina domin har Bikin nan da suka hadu bata musu mgana ba tun Lokacin auran Amina da Danmallam bata kara musu mgana ba ko sun hadu sai ta kauda kai..shiyasa suke kallonta suna kara Ruda Falon da gud'a Sakina Gabadaya ta Jike da Zufa,Jikinta ba inda baya rawa kanta ya gama Daukan abubuwan datake ji har wani Dum..Dum yake yi kamar ba nata ba Hakama Anty Amarya gadai tanan ne kawai abubuwan sun tsaya mata Cak ta kasa wani Tunani kamar yadda Mamanmu ke jabe suna jin Abun Al"ajabi tare da Tsamanin Abunda basu yi Tsammani ba..! Duk wannan Budurin da akeyi Sarood na Falon nan sai kallon kowa take yi tana Bin Baki ita ba wani sanin Amina tayi ba shiyasa bata gane komai ba ammh kuma Kayan data gani ta Zata na su Hanne ne da za"ayi ma aure gobe Ita ba Hausa take ji ba,Shiyasa sai bin Bakin Mutane kawai take achan gefe kamar ma bata afalon. Haj.Uwani ce ta juya kawai ta Fice Daga Falom Idanuwanta sun kad'a sun yi Jajir Dishi Dishi ma take gani Saboda tashin Hankali. Tana fita saboda yadda ta Rude yasa bata ko nemi Kebewa ba tana fitowa ta Laluba wayarta Allah yasa gefenta Da saura ana gani haka ta saka lambar Batula saboda yanayin Datake Ciki bama zata tsaya neman Lamba ba. Batula ta kira gabda zata katse ta Dauka Cikin karaji da wani yanayi Haj.Uwa tace"Mun shiga uku mun Lalace Batula..Hajiya ta gama lalatamin Duka shirina..Hajiya ta Ruguzamin Burina da na Dade ina Tanadinsa..! Dagachan bangaran Cikin Tashin Hankali tace"Innalillahi Uwani me ya faru..? Haj Uwani tana Sharan gumin Goshinta tace"Komai ma ya faru Batula..Komai ya Lalace..Amina ce ta Dawo da Cikin Umaru ajikinta Batula..Sannan da kayan lefe dana Haihuwa kamar za'a Bude shago sannan ga Makullin gidan daya Siya mata Batula ni fa bama shi ya Dameni ba Batula Amina Tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe..! Batula Cikin tashin Hankali tace"Ciki kuma Uwani..?. Wai Wata Amina..? Haj.Uwani na faman kokuwa da yanayinta tace"Batula Amina dai da aka Aurama Umar ita ke da Ciki fa..! Batula tace"garin yaya..! Ta yaya hakan zai faru alhalin kince kin tabbata ta sha mganin Mama..? Haj.Uwani ta Runtse ido sai Hawaye Cikin Rawan murya tace"Bansani ba Batula bansani ba..Hajiya ta shammaceni..Shammatan datamin illah har Abada..! Batula tace"To yanzu menene mafita..!? Haj.Uwa ta Share Hawayenta Tana Fadin"Bazan karaya ba..Karaya ba na wa bane Batula..Dole ne nayi Nasara Batula ko ta halin kaka ne..Saboda haka ki Tashi sammako gobe ki koma wajen Mama ki fadamata Halin da ake Ciki..Ina so kada Cikin nan ya fito Duniya..Ina so a kashe koma menene acikinta ta haifesa ba rai kada yazo Duniya da ransa..Naji Samun Cikin kuskure ne sannan Hajiya in tasan wata ai bata san wata ba..Zan nuna mata Ni Uwani Kwalbar Sharri ce ko na Fashe ina da Sauran mamora..! Batula tace"Gobe goben nan zan yi sammako..Wannan Labarin ya Firgitani ammh Hajiyar nar Allah ya Tsine mata albarka..! Haj.Uwani Cikin Huci tace"Nayi alkwarin sai na Tarwatsa Farincikin su..Sai na Lalata musu wannan jin Dadin na su..! Daga haka ta Datse kiran tana Sakin Huci kamar zakayan,Ta juyo a Fusace Kawai sai taci karo da Hajiya Tsaye da waya a Hannunta tana kallon Hajiya uwani Cikin wani yanayi. Haj Uwani gabanta ya fadi ta Zaro Ido Jiki na rawa tana kallon Hajiya wacce ta Daga mata wayar hannunta ta nuna mata Sai ga sunan MALLAM baro baro alaman kira yana tafiya minti Goma sha Biyar alamun tun fara mganarta da Batula.. Jikinta na rawa Gabanta na Faduwa Zufa na keto mata ta ko"ina kawai sai ta Duka kan gwiwoyinta Domin tagama sanin Hajiya tasan wannan Boyayiyar Fuskar nata. Cikin Rawan murya ta hada Hannayenta tana Fadin"Dom Allah Hajiya ki Rufamin asiri sharrin Shedan ne..! Hajiya tayi mirmishin Takaici kafin ta kada kai tace"Ni ban isa na rufa miki  asiri ba Uwani..Asirinki Daman chan a bankade yake..Duk wanda yace Tukuyar wani bazata tafasa ba to nashi ko Dumi bazatayi ba..Ki Fito ki Fallasa kanki Uwani Domin asirinki ya gama Tonuwa kinga wannan wayar..!.To mallam ne akan layi tun Fara mganarki da kanwarki yaji komai ki jira sakamakon ki Uwani..! Daga haka ta katse wayarta agaban Haj.Uwani Dake zufa ko"ina na jikinta na rawa ta juya ta koma Shashenta Haj.Uwani na Rarrafe tabi bayanta tana kiran sunanta Hajiya Cikin wani yanayi ko waige bata karayi ba. Tana shigowa Falon nata ta iske su Abida nata shewa sun tasa Amina gaba da  shakiyanci sannan sauran matan kuma suna ta kara Daga kaya. Anty Amarya ta kallah Dake Tsaye ta kasa gaba ballatana baya Mamammu kawai take kallo Tana auna yadda Balaraba ta raina mata wayau Saboda rashin ta ido ta gagije ta koma Cikin su Mamata ana ta Daga kaya da ita babu Abunda ya shafeta ko Kaffara bazatayi ba Karya ne balaraba tace batasan Amina nada Ciki ba..? Ita Zata rufe abai bai..? Daman ai Tun tuni ta daina Hada hanya da ita saboda taga ta riga ta gama Taimaka mata ta samu Duniya shine zataci Amanarta ta juya mata baya..? Wlh yadda tayi alkwarin indai nata Burin bai cika ba to gayyar sai ta watse. Tana cikin wannan Tunanin ne kawai Taji Ihun Sakina da Sauri ta juya sai taga Sakina a kasa tana gunjin kuka su Aliya na riketa da Sauri  Anty Amarya ta kariso da Sauri tana rike Sakina bata so tayi wani abun da Hankalin Mutane zai dawo kansu yasa Cikin Tsawa tace"Miye haka Sakina.? Aliya da Sadiya ku kama min ita muje Bangarena .! Tafada tana kokarin wucewa Sakina tayi kukan kura ta Fincike daga rikon su Sadiya ta dira gaban Anty Amarya Duk da yadda Cikinta ke murda mata Ammh ina idonta ne ya Rufe bata ganin kowa sai Hango Amina da Ciki da kuma Uban Dukiyan da Umar ya Laftama Amina. Anty Amarya ta kauce ma Sakina tana Fadin"Miye haka..?muje bangarena Sakina..! Tafada tana kama Hannunta ganin yadda Hankalin kowa ya koma kansu Sakina ta Fizge hannunta Tana kallon Anty Amarya da Jajayen idanuwanta Cikin karaji tace"Ba inda zamu. Anan zamu yita ta kare..! Tafada Sai hawaye Anty Amarya tasan bata Cikin Hayyacinta yasa ta Fizge ta zasu bar Falon ammh sai Sakina ta Kwace hannunta ta Turke Anty Amarya tana Fadin"Kunya kike ji kada mutane su ji yadda kika Dade kina Rainamin wayau Anty..? Tafada tana sakar mata manyan Idanuwanta, Anty Amarya ta Zaro Ido Tana Fadin"Sakina kina cikin Hayyacinki kuwa..? Sakina ta Kwashe da wata Dariya kafin tace"Eh tabbas bana cikin Hayyacina..Daman ai na Haukace..kalli kazamar yarinyar nan da Ciki Haihuwa ko yau ko gobe..Ni kuma kalleni shekara ta nawa ina Wahala ban samu ba..! Koda yaushe mganar ki kenan na kwantar da Hankali na ni kadai zan zana Mowa a wajen Umar da Danginsa..Hakan ne Mowa..? Ki kalli abunda ke faruwa a Falon nan kowa ni yake ma kallon kaskasci wannan ne Mowar..? Ko dai Bora na zama mara amfani..? Ina alkawarin naki..? Ashe duk karyace bazaki iya komai ba Daga ke har malaminki makaryata ne Babu abunda zaku iya tunda har Amina ta Samu Ciki da Umar baku sani ba..! Ta karishe Fada Cikin gunjin kuka Lokaci Daya tana jijjiga kafadun Anty Amarya tana Cigaba da Fadin"Kin manta kin Fadamin auran Amina haka zai kare a banza..? Kin manta kin Fadamin yadda aka Daurasa haka za"a kwance sa..? Ashe duk karya ce..? Ashe ni kika raina ma wayau Marliya..? Ta karishe Fada Cikin Tsawa da Budewar Murya da ya Sandarar da kowa acikin Falon har da su Sadiya da Jidda da suka zaro ido sun kasa Fahimtar me ya faru Hajiya na gefe tana kallonsu tayi mirmishi takaici ta Harde Hannayenta saman kirji Tana kallon abunda ke faruwa. sakina ta sulale kasa tana kuka Tana Fadin"kin cuceni kin sa na yarda da kowa sama Dake...Ashe karya kike Fadamin..Ashe bazaki iya ba..Bazaki iya ba..! Tafada tana Saka fuskarta Cikin Tafukan Hannayenta tana wani irin kukan Bakinciki da kishi. Anty Amarya tana kokarin Daidaita kanta kada su tona ma kansu asiri ta Duka Zata riko Sakina tana Fadin"Sakina Saurare n..! "Kada ki kara Tabani malama..! Sakina ta Katseta Cikin karaji da sai da Anty Amarya ta fadi kasa jidda da Sadiya suka karisa suka riketa Jidda Ta kalli Sakina Cikin bacin rai Tana Fadin"Sakina Lafiyan ki kuwa..? Kada Zafin kishi ya saka ki rasa natsuwarki mana..! Sakina ta Dago Jajayen idanuwanta Ta balla mata Harara kafin tayi mgana Anty Amarya tayi saurin kwace jikinta cikin nasu Jidda tana Fadin"Yau za"ayi walkiya kowa zai bayyana..Na rantse da Allah ni MADINA bazan karbi Faduwa ni kadai ba..Sai dai mu yi Faduwar Guzuma..! Tafada Lokaci Daya tana neman Balaraba Dake falon sai kawai ta Tsince ta Sum sum zata fice tun da taga Abunda ke faruwa tsakanin Madina da Sakina ta fara kokarin Barin Falon Cikin Rawan jiki Anty Amarya na Hangenta ta Daka Tsalle ta Rikota tana Fadin"Ina zaki kuma..? Munafuka..Ai sai ki Tsaya kiga yadda wasan zai kare ko DAYYABA..? Tafada Cikin tsaananin Tashin Hankali Datake Ciki da Jajayen Idanuwanta. Mamanmu ta fara kokarin kwace kanta Cikin Borin kunya tana Fadin"wata dayyaban kuma..? Marliya kada Zafin kishin ganin Amina da Ciki yasa ki fara Hauka mana.. Ko kafin ta rufe Baki Anty Amarya ta Tsinketa da mari mai Lafiya sai da kowa afalon ya Zaro ido Cikin mamaki Mamanmu sai da ta Duke Anty Amarya ta Bita ta Chakumo Wuyan riganta cikin karaji take fadin"Zaki ga Hauka yanzu nan Don Kutumar Ubanki Dayyaba..! Lokaci Daya ta Jawo ta Tsakiyar Falon kamar kayan wanki ya Zulfa ta tare Anty Amarya tana fadin"Meyasa kika mareta kuma kike janta haka..? Anty Amarya ta balla mata Harara da Jajayen Idanuwanta tana Fadin"Matsa ki bani wuri..Ai ke Mamanmu kika sani Balaraba baki san Wacece DAYYABA..ba yau zaku san aihinin wacece Fuskar wannan azzaluman matar..! Sai kowa ya saki Baki Amina na Zaune tayi Dariya jin Dadi sai Hawaye afili ta Furta"Komai yazo karshe..! Hamida ta kalleta Cikin wani yanayi tana Fadin"Me..ya ke faruwa..? Sai Amina ta kasa ce mata komai Tsausayi suke bata yau zasu yi kwanan bakinciki in suka gano wacece ainihin mamansu. Anty Amarya ta yarfar da Mamanmu nan Tsakiyar Falon Hajiya Goggo Husai ta mike tana Fadin"Ke marliya meye haka kuke yi kamar wasu yara..? Anty Amarya ta Cire Dankwalinta Taci Damara tana Zaran ido ta nuna mamanmu Dake kifta ido ta rasa mafita Tace"Wannan zaku tambaya Abunda ya faru..Domin tasan komai..Nima shi nake tambayanta yanzu..Dayyaba ni zaki munafunta..? Ni zaki yaudara ki Ha"inceni..? Wlh na yi Rantsuwan ko kaffara bazan yi ba kinsan inda Amina take da Halin Datake Ciki gani kikayi Burinki ya Cika Kin KASHE YAYA..sannan kin Samu Sa"idu yadda kike Fata shine yasa kika juyamin baya..? To wlh kin yi Kuskure Ni Madina Fitilar Sharri ce ko ba kalanzir sai na kai Safe yadda ta bare dani da Uban kowa sai ta bare yau..! Tafada Cikin karaji da Ihu kamar wata Mahaukaciya Daidai Lokacin da su Mallam sukayi sallama suka shigo Falon bayan sa kaf Zaratan ya"yansa ne kama Daga ya Danmallam Nazir ,Nasir,Nazeem,Jafar Uzairu,Shamsu Akilu da zubairu, Da Aba Aliyu abokin ya danmallam atare suka bayyana acikin Falon sai kuma waje ya Dau shuru kallo ya koma wajensu mallam. Hajiya na ganinsu ta murmusa kafin tace"Yauwa ku kariso..Yau abun dake Boye ne zai fito Fili..anyi walkiya za"a ga kowa sannan an Dade ana ruwa kasa na Shanyewa...! Kai Tsaye ta maida kallonta kan Anty Amarya da ko ganin su mallam bata Damu ba Burinta kawai gayyar ta watse Cikin wata murya tace"Marliya naj kin Fadi wata mgana da sunan HADIZA..? me kike so ki fada ne..? Anty Amarya ta kalli Mamanmu wacce ta ke kallonta Cikin Zaro Ido Jikinta na rawa ta tuma gaban Madina ta rike kafarta tana fadin"Madina don girma Allah ki rufamin asiri..Wlh na Rantse da wanda raina ke hannunsa bansan komai kan cikin Amina ba..! Anty Amarya ta saka kafa ta Ture Mamanmu ta fadi Gefe Cikin Taruwan Hawaye tace"Wlh baki isa ba Balaraba..Ai ke kwalba ce uwar Sharri..Qur"ani kadai zaki Fadamin na yarda Dake..! Yadda Kasuwar ta bare dani ban ci Riba ba kema yau sai ta bare dake Dayyaba..! Tafada Lokaci Daya ta maida kallonta kan su Hajiya tana fadin"Hajiya..Mallam Sa"idu ina ya"yan Yaya su Jadwa..? Tafada tana Binsu da kallo Cikin son suji me take son Fada suka tsura mata ido Ta juya tana kallon Mamanmu dake kuka tana rokonta kada ta Fada ta juya mata baya ta kalli Idon Aba tace"Kunga wannan matar ba Matar kwarai bace..Shekarun data kwashe tana Zaune daku duk na Cutarwarce..Muguwa ce Azzaluma ni Duk Mugunta na ban taba Kisa ba..Ammh Kunga wannan..? To Tayi kisan kai ta kashe rai Har Lahira..! Aba Cikin rawan baki dana murya yace"Wa...ta Kashe..? Kafin ta samu bakin mgana Daga bayansu sukaji wata murya Cikin Kuna tace "YAYA TA KASHE ABA..! Sai kallo ya koma inda akaji mganar sai ga Amina ta bayyana a Tsakiyar Falin gaban Anty Amarya da Mamanmu da ke tsuggune cikin Fitar hawaye Duka Biyu. Gabadaya sai kowa yaji wani sanyin jiki Aba sai da ya Dafa ya Danmallam Dake gefensa saboda jirin Daya kwashesa Anty Amarya kuma Amina take kallo da Mamakin a ina tasan wannan mganar..? Mamanmu kuma kasa kawai tayi Dakai yauma Tubular sara"i babu Tsima babu Dubara. Ya jalela da su ya Jadwa suman Tsaye sukayi ya jafar ne ya iya takowa ya iso gaban Amina ganinta da Ciki ba shi ne agabansa ba mganar data Fada ne abun Damuwa.. Cikin Fitan Hayyaci ya kama jijjiga Kafadun Amina yana Fadin"Wata Yayar ne ta kashe..? UMMANMU..? Ya fada Cikin Tsawa Idanuwansa Jajir kawai sai Amina ta Fashe da kuka ta Fada Jikin ya jafar tana nuna Mamanmu Cikin wata murya tana Fadin"Itace ta kashe mana Uwa ya Jafar..Itace ta rabamu da Aba..Itace ta rabani da Uwata Shekaru goma da wani abu bansan Dadinta ba.. Itace ta maka asiri domin ka lalace sai abun ya Dawo kaina. Itace ta hada kai da Anty Amarya ana Zaluntar ya Danmallam itace kuma suka ka Hada kai domin su ga bayan aurena da ya danmallan da alwashin har Abada bazan taba Haihuwa ba.. Ya jafar wlh wannan matar muguwace kuma azzaluma ce ta Dade tana Zaluntarmu bamu sani ba..itace ta kashe mana YaYA DA kunnena naji ta tana Fada..! Ta karishe fada Numfashinta na Sarkewa,Ya Jafar ya riketa Cikin wani yanayi yanayin da baya fatan ya Bude ido yaga abunda ke faruwa da gaske ne. Durkushewa Amina tayi kasa Jafar ya Bita ya Tallafeta,ya Danmallam ya kariso ya riketa yana Cire mata Hijabi Saboda ta samu iska tana ganinsa ta Damke hannunta Cikin rawan murya tana Fadin"itace..Ita ta kashe mana YAYA..! Malam dake tsaye yace"innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..! Sai kowa afalon ya Dauka Saboda kowa ya rasa abun Fadi. Mamanmu na wani irin gunjin kuka tace"Kaico na..Bansan akwai wannan ranar ba..Da ban aikata abunda na aikata ba..Don Allah ku yafemin..! Gabadaya kallonta kawai ake yi Cikin Wani yanayi Aba kuma zaman dirshan yayi a kasan Cafet ya kasa mgana su ya Jadwa kuma suna dai Tsaye da karfin Imani. Hajiya ce ta kalli mamanmu tana Fadin"Balaraba me Hadiza ta miki kika Kasheta kika raba ta da wannan Duniyar..? Tafada cikin wani yanayin muryanta kamar zatayi kuka Ranar da Danmallan yazo mata da wannan mganar bata gasgasta ba har yau tana cikin Tantaman balaraba zata iya Kasje Yaya sai yanzu da komai yake neman bayyana. Mamanmu tana kuka kanta na kasa ta kasa Dago kanta saboda kunya balle ta kalli Ya"yanta da yayan yaya ga Aba ga kunya mutanen Dake falon Anty Amarya kuma na Tsaye ta shirya komai ayau Sakina ma duk suna gefe banda kuka babu abunda take yi. Amina kuma Danmallam jikinsa ya Tarairayota ya azata yana ta faman mata fifita da Hijabinta Sakina na kallonsu tana jin kamar ta mutu saboda bakinciki. Kan Mamanmu na kasa ta fara mgana. "SOYAYYAR SA"IDU CE SILA..." *Janafty**TFZB2026* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Gabadaya Ilahirin Falon sai da kallo ya koma kan mamanmu cikin mamakin kalamanta,ita kuma kanta ta kara saddawa kasa hawayenta na diga saman cafet din Daya malale falon Hajiya ta cigaba da fadin'"Tabbas kamar yadda na fada da farko Hakane soyayyar Sa"idu ce ta kaini ga komar Nadama dana ke ciki..! Na taso tun ina karamata ban taba ganin wani Namiji daya taba Burgeni kamar Shi ba,Tun tasowata shi kadai ne Namiji kwara Daya daya ke Burgeni Sannan na kamu da sonsa da kananun shekaruna batare dana sani ba,Sa"idu ya shiga raina yayi kane kanen da bazan iya rayuwa ba sai da shi Tun Lokacin suna Gusai kafin barowarsu chan su dawo nan Gumel da Zama saboda Sa"idu yasa ban taba Daga kai na kalli Samarin Dake kara kaina akaina ba ina ganin kamar zai so ni watarana sannan kuma Hankalina da duka Tunani ya karkata akansa shi kadai. Sai dai me..?sai da girma ya fara kamani Sa"annina suna aure sannan na Fahimci bana gaban Sa"idu bai taba min wani duba ba sai na yan"uwanta duk da kaunar da nike ta Nuna mai a Fakaici in yazo garin yazo Gidanmu Tunda ni ina matsayin Diyar abokin wasan Marigayi Baba Aminu ne,yazo kaida Babani Lokacin Tana Raye bana iya sukuni na Dinga Bare baren jiki kenan a kansa bani da wani Sauran sukuni ammh bai Taba Daga ido ya kalleni ba ballatana yasan Halin da na Dade aciki alokacin har Babani sai da ta Fahimci ina son Sa"idu so kuma bana wasa ba. Hankalina bai tashi ba sai da naji Zencen auransa ranar sai da nayi karamin Hauka Babani Allah ya jikanta ta Dinga Tausata ta bani Hakuri akan nayi hakuri na Cire Sa"idu a raina na bama wani Cikin Manema na Dama tunda dai Sa"idu bai Juyo gareni ba na Hakura dashi alokacin kamar in make Babani haka naji Sai dai ban nuna mata ba ammh a wannan gabar gaba nake kullawa ga Duk wanda yace na Rabu da Sa'idu ko waye shi kuwa..! Auran Sa"idu da Hadiza kadan ne ya Rage bai kaini kushe wata ba Saboda Bakinciki da Zafin kishi har sai da na Fara Tunanin na kamu da ciwon zuciya ammh duk da haka ban makara ba sannan ban cire rai ba. Ana cikin wannan Halin Babani ta amsa kiran Allah ta rasu dani a bakinta da Fatan na yi aurre kada na jirasa ammh ban jita ba Tunda ni kadai ce tare da ita bayan bakwai dinta sai kawu Salisu ya maidani babban gidanmu ina zaune a wajensa..! Saboda Sa"idu da Soyayyarsa sai da Kaf sa"o"i na suka tafi gidan mazajensu har kannen baya na ma an fara aurar dasu a wanchan Lokacin ana auran wuri ammh ni nafi Shekara ashirin ko Tsayayyen mgana bata akaina Saboda bayan Sa"idu har Abada bana jin zan iya bama wani Namiji Dama. Kwatsam Naji Labarin Haihuwar yaya da yadda Sa"idu ya dinga rawan jiki akanta da abunda ta Haifa sai Gyambo na ya Dawo sabo naji bazan iya Hakura ba,Da taimakon wata kawata Samira da mukayi Primary tare na Zayyane mata Damuwata tace ta kwana gidan Sauki ita ta Daukeni ta Fara kaini gidan wani malami ko Boka zan ce wanda ke mata aiki akan mijinta acikin garin Tsafe na ZAyyanemai Halin da nike Ciki ya Tambayeni me nake so nace Sa"idu nake so..Ya aureni ko ta Halin kaka ne yana so ko baya so ni ban Damu ba kawai Burina na ganni agidansa a matsayin matarsa..! Yace an gama ammh zan zube kudi masu yawa na karin aiki ban Damu ba Daman ta Fadamin na Tanadi kudi alokacin wajen Biyan Bukatata komai zan iyayi Zoben Zinaren da na gada wajen Babani na Saida na yi amfani da kudin wajen jawo cikar Burina. Kamar wasa sai ga karamar mgana ta Zama babba kawu Salisu ya Kira Sa'idu akan yazo yayi auran zumunci Dani alokacin ko gaddama bai yi ba ya Karbi mganar Daganan na Fahimci zama ba nawa bane samira ta Budemin ido da shiga malamai Domin Cimma Burina ban shiga Gidan Sa"idu ba sai da na saka aka kafani sannan aka Saka soyayyata da kaunata a zuciyar kowa banda ta Sa"idu domin bai kaunace ni Fiye da yadda nayi nazo ba,yafi kaunar yaya da Jafar d'anta data Haifa. Wannan shine Bakinciki na Biyu dana taba Fuskata agidan Sa"idu bayan aurena dashi,Da Farko ina ganin Komai ya kare tunda na auresa ammh Daga baya sai na Fahimci zama bai ganni ba Duk da kuwa Daga Su mallan har ya"yansu suna so na da Girmamani Uwa uba kuma Yaya itama ta Sakarmin komai kamar yadda na nuna Dayan fuskata ta Salihai. Na Dade ina Fama da kuncin zuciya da Bakimciki kauna da wannan Tsausayin da bana ganinsa akan kowa sai akan yaya ni kuma sai dai Zaman Tsausayi da yan"uwanta ka ban taba ganin wannan kaunar da nake son gani atare dashi ba Sannan sai na Fahimci Duk wani Buri na Sa"idu yana kan Jafar ne bashi da sukuni in yana gida yana Tare dashi ko da Ranar ni ke da girki sannan duk kokarinsa na yaboye wannan kaunar bata Boyu awajena ba Dalilin Dayasa Idona ya Rufe da Kishi kenan da Bakincikin yaya da ya shiga raina na har Abada. Hankalina ya kwanta dana Samu Cikina na Farko ina Tunanin Namiji zan Haifa nima Sa"idu yayi rawan jiki akaina da abunda na Haifa sai dai kuma ina hakan bata Faru ba haihuwar ZULFA sai ya koremin wannan Burin nawa sannan kuma sai na Fahimci kamar Sa"idu bai yi murna da wannan Haihuwar ba Duk da yadda ya dinga min Hidima yaya da Hajiya na Tsaye kaina ban taba Gani ba Saboda gani nake yi Itace ta Hanani Samun abunda nake so tun Farko Sannan tasha gabana a zuciyar Sa"idu. Na yi ta neman Samira domim mu koma wajen mallan sai na samu Labarin mijinta ya tafi da ita Lagos inda yake Neman kudinsa sai hakan ya katsemin hanzarina ban koma wajen maallam da wuri ba har Tafiya ta Cigaba da tafiya alokacin Yaya ta Haifi Jadwa da Jaleela ni kuma ina Goyon zahra kaf alokacin ni nake rainan duka ya"yan da yaya ta Haifa Saboda na kara jawo Hankalin kowa da Tunanin kirkina akansu kuma naci Nasara na zama ban damu da komai ba a Bayanne a boye kuma ba wanda ya kaini Bakinciki. Hankalina bai kara tashi ba sai da naga na kara Haihuwar Zulaihat ban samu Namiji ba sannan ga Jafar ya girma sai nake ganin yaya ita ke da gida ni kuma ta barni bani da Tsuntsu ballatana ta tarko sai nayi Shirin komawa wajen mallam sai dai nayi Rashin Sa"a an ce ya tashi Daga nan kuma ba wanda yasan inda ya koma Hankalina ya tashi Saboda alokacin na kasa Hakuri so nake ko ta Halin yaya ne na sami mafita na gaji da Kunsan Bakim cikin Sa"idu da yaya. Hakanan na Dawo gida tunda bansan wani Malamim ba sai dai kafin na Samu mafita zuciyata ta riga ta gama kekyashewa Tsanar yaya da ya"yanta ya gama Cikamin zuciya wannan Bakincikin Tun aurena da Sa"idu yake Cikin Raina bai Taba gushewa ba Sai Ranar da YAYA ta bar gidan Duniya..! Mamannu ta karishe Fada tana gunjin kuka Mallam ya girgiza kai Cikin Wani yanayi yana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un..! Kafin ya karisa ya samu Daya Daga Cikin kujerun falon Hajiya ya Zauna Rawaninsa duk ya jike da zufa Aba kuma yana Durkushe inda ya Sulale kansa na kasa ba wanda yasan Halin Dayake ciki su Nasir da su Nazir kuma duk kasa suka sulale suka zauna jin wannan labarin mai kama da al"amara. Su ya Jadwa da su Jaleela suma kafafunsu ne ya kasa Daukansu suka zube nan saman cafet suna Faman kuka kada su Zulfa su ji Labari gabadaya kowa da abunda yake sakawa acikin ransa Amina kuma na Rumgume jikin Danmallam Tana kuka yana faman share mata Hawaye yana Shafa bayanta Jafar kuma kansa ya Dukar kasa Hannunsa Daya Dafe da kan nasa ya kasa yarda da abunda yake ji kuma yake gani Gabadaya kowa acikin Falon ka kallah sai ka Hango tashin Hankali da al"ajabin wannan abunda dake Faruwa. Mamanmu ta Dago Jajayen idanuwanta ta Sauke kan Anty Amarya da jikinta ya fara rawa sai alokacin ta Fahimci Komai fa ya kare sai dai babu wani tsumi ballatana Dubara. Cikin Muryan kuka da Nadama Mamanmu ta Cigaba da Fadin"Ban taba Sanin bayan ni agidan Baba mallam akwai mai irin Halina ba Sai daga baya..Har ga Allah da Farko bansan Haka marliya take ba sai da watarana na jita tana waya da malamin Dake mana aiki kan Hajiya da mallam alokacin nasan itama irina ce..muna neman abu Daya agida Daya sannan alokaci Daya..! Ban nuna mata na jita ba Sai daga baya,Na koma na nuna mata fuskata na bayyana mata Duka Burina da Fatan zata bani Hadin kai mu cure waje Daya wajen Cikan nmu burin..! Tafada tana kallon Anty Amarya da kallo ya koma kanta komawa tayi ta Zauna Dabas saman Cafet sai kuka Cikin wani yanayi ta cigaba da fadin"Alokacin da Balaraba ta zo min da wannan bayanin na tsorata Saboda ko ni ban taba Tunanin haka take ba..Ammh data zauna ta warwaremin komai sai na Fahimci Rauninta nima ina Cikin irin haka..Sannan in muka Hada Hannu zamu cika namu Burin atare..! Mallam Dake zaune yana jin abun al"ajabi ya Bude Bakinsa Cikin wani yanayi yace"Ke menene naki Burin..? Burin daya sa kika fifita Duniyarki Fiye da Lahirarki marliya. ? Anty Amarya bata iya kallon mallam ba Saboda yadda taji muryansa ba wannan amon ballatana karkashi Abunda ke Faruwa ya Dakushe komai Tana sharan Hawaye ta Cigaba da Fadin"Ni burina shine na Zama Tauraruwa a wajenka..Na zama ni ce agabanka kafin kowa..Sannan Burina na zama na Dara duka matanka a wajenka..Sai dai ina burina bazai taba Cika ba indai Hajiya na Duniyarka na yi barnar kudi akan ka mallam da Hajiya Saboda kawai na Zama Tauraruwa a wajenka sai dai hakan bai Samu ba kowani aiki baya Tasiri akan ku saboda kun rike Allah sannan ko acikin Wani Hali baku daina ambatonsa ba. ! Sannan tun zuwana gidan nan na Fahimci Hajiya ta yi mana Fintikau,Komai naka itace,Daga ita Sai SA"IDU sune kadai suke gabanka da su kake shawara sannan uwa uba Sa"idu ne ke jan Ragamar Duka Dukiyarka nayi iya Bakin kokarina na Raba hakan sai dai ban cimma gashi ba..Sai na Sauya shawara da taku..Na Fahimci in ni bazan zama Tauraruwa ba ta Sanadin Sakina zan iya Cika Burina Har fiye da yadda nake Tunani..! Tunda ta ambaci Sakina Danmallam ya zura mata ido yana kallonta sakina kuma jin an zo wannan gabar kawai sai ta kara Volume din kukanta ta soka kanta Tsakanin Cinyoyinta tana gunjin kuka ko Aliya Dake gefenta bata da karfim gwiwan lallashinta. Anty Amarya na jan Hanci da majina ta Cigaba da Fadin"Har ga Allah Lokacin da na Dauko Sakina ta zauna awajena da zuciya Daya ne sai daga baya..Data fara girma na Fahimci Tana matukar Kaunar Umar in ta gansa ta Dinga mai rawan jiki kenan shi kuma alokacin bata gabansa ita da su Jidda da su Nazifa duk Daya ya Daukesu..Ban tabbatar ba sai da na Samu Sakina mukayi mgana ta Nuna min in ba Umar ba bazata iya auran kowa ba Daga Lokacin na hango Cin ma nasarata ta bangaran Sakina..! Ni na shiga na fita na Karkato da Hankalin Danmallan akan sakina..Duk da alokacin akwai ya"yan malamai manya wadanda suka fita komai da suka so su hada zuru"a da Maallam kwatsam yace Sakina yake so..Nasam ko Hajiya alokacin tayi mamaki Sanin ba wata alamar Soyayya a Tsakaninsu sai dai sanin ita bamai yawan maida kai kan sha"anin Umar bane yasa bata nuna komai ba ko a Fuskarta ba..! Hajiya ta jinjina kai tabbas ai Biri yaso yayi kama da mutum Rana Tsaka Danmallam yace Sakina yake so ashe Ba yin kansa bane lalle Allah shine Sarki. Anty Amarya tacigaba da Fadin"Mallam kuma bai nuna komai ba sai ma farinciki zai yi tuwona maina..Tunda yarcda ya rikeni Sakina Tsakani ga Allah haka yake rike da ya"yansa Daya Haifa,ammh duk ban gani ba Zuciyata ta kekashe da cikar Burina..! Ban yi salama ba sai da aure ya Kullu Tsakanin Umar da Sakina sannan naji Hankalina ya kwanta sannan na sanya aka doramai shakkar Sakina da Duk abunda zatamai bazai taba gani ba ballatana ya Dauki mataki akanta Shiyasa sai tayi ta yin abubuwa bai Taba Daga ,kai ya Dubeta ba Sannan wannan aikin mai girma ne Tunda shima yana da Tsari ajikinsa Dakyar aka samu nasara akansa..! A wannan gabar ne muka Hada hannu da Balaraba wacce ainihin sunanta ne Dayyaba..Ni kuma marliya nake ammh ana Kirana da Madina sai muka juya sunayemmu Domin kada Bacin rana a fahimci in da muka Dosa..! Ni na kai Balaraba wajen malamin Dake min aiki anan Dutse Bukatarta ta Farko shine ayima Jafar mugun asirin da zai Fandare ya zama gagararree ya bi Duniya ya lalace kada yaji mganar yaya ballatana ta Sa"idu ya Zama YA FITA ZAKKA Acikin Dangi wanda Daga karshe Sa"idu zai gaji ya tsine mai kada dai ya amfana da Haihuwarsa har Abada..! Sai akaji goggo Husai ta saka Salati Tana kuka tana Fadin"Innalillahi..Ammh wlh Balaraba kin cika bakar muguwa azzaluma..! Sai kawai ta koma ta zauna tana Fadin"Allah yayi gaskiya..Zai Tsare bawansa a duk inda yake..! Jafar kuwa ko Dagowa bai yi ta kasan Inda yake zaune Hawaye ne ke Digar masa Danmallan kuma Hannayensa Jimke Cikin na Amina tun labarin Anty Amarya na Sanadin Auransu da Sakina yake ta Hailala acikin ransa..! Mamanmu kuka take yi kamar ranta zai fita ita da Anty Amarya da suka san yau komai yazo karshe..! Ba wanda yace musu kala su kansu ya"yansu zuwa Lokacin sun Fahimci komai ban da tashin kukan au bakajin komai afalon..! Mamanmu na Toshe kukanta ta Cigaba da fadin"Sai dai an samu matsala..Aikin sai ya kuskure maimakon Jafar sai ya Sauka kan AMINA tun Yaya nada Tsohon Cikinta alokacin..!. Sai kallo ya koma kan Amina wacce ta kifa fuskarta kan hannun ya Danmaallan tana ta kuka,mamanmu na kallon Amina ta gyada kai tana fadin"Tabbas abun bai sauka kan kowa ba sai kan Amina..Mallam din da kansa ya fadamana haka ni da Madina da muka koma da Korafin aiki bai ci ba..Ya sanar damu aiki yaci Sai dai ba akan Jafar ba,akan Abunda ke Cikin Yaya..! Alokacin gani muke kamar wasa sai da Yaya ta Haifi Amina sannan muka gasgasta kowa yasan tun Haihuwan Amina ta fita zakka cikin ya"yan gidan da kowa ma,sai kuma nayi amfani da kissa na,na rika jan Amina ajiki ina nuna nafi kowa sonta tunda kowa baya kaunarta Saboda Rashin kunyarta da Kuma Yadda ta addabi kowa ban so Amina ta tsaya haka ba naso ne ta Lalace tabi Duniya ta Zama Karuwa sai dai ina burina bai Cika ba Allah ya Tsare Amina duk Rashin kunyarta bata mu"amala da maza ba Sannan Tarbiyan gidan su data gidam Baba Mallam ta Zauna mata Daram Sannan Allah ya Tsareta da Fadawa wannan Halakar..! Duk soyayyar da nike nuna ma Amina na karya ne bayan Sihirin Dake tare da ita nima na bada tawa gudummuwar wajen kara Lalata Rayuwarta,Ban taba mata Fadan tayi ba Daidai ba,Duk da alokacin in na Fadamata zataji Domin na Fahimci Duk Duniywa bayan ni da su Hajiya Amina bata yarda da kowa ba sannan tana kaunata Fiye da yaya data kawota Duniya da hakan nayi amfani na Gurbata rayuwar Amina ban taba bari ta ma kanta wani abu ba bana so watarana hakam ya amfaneta sai na Zabi na Sangartata kada ta iya komai ta tashi ahaka ta kuma rayu ahakan na Tabbata watan watarana sai haksn ya Zama illah agareta. Saboda irin Kaunar da nike nuna mata ba wanda ya taba Fahimta ta Komai sai dai in saka Hamida Amina kuma na Dauketa wata Shashasha ce da bazata iya moran rayuwarta ba Sannan na kara nesantata da Mahaifiyarta yar da har Yaya ta koma ga Allah Amina ko da na Minti Daya bata taba rabarta ba. ! Amina ta Dago jajayen idanuwanta tana kallon Mamanmu kallon Tsana da wani Bakimciki haka Hamida itama da su Zulfa suke kallonta Cikin kyama da wani Takaici Aba dai bai Dago kansa ba har alokacin..! Mamanmu bata Damu da kallon da suke Binta dashi ba ta cigaba da Fadin"Duk abunda kuka ga Amina nayi ba yin kanta bane..Tana da Sihiri ajikinta sannan da Shafar aljanu su suke sakata ya wan tsorata da kuma Mugayen mafarkai sannan duk abunda ya Faru da Amina kan Aminu na sani ammh ban taba Hanata ba..Ban kuma nuna mata na sani ba da Gangan nake ijiye wayata in da Zata gani saboda ta Dauka alokacin Naso ne Aminu ya lalata Amina Ya yi mata Cikin da zai yi Sanadiyar tsarwata zuciyar Sa"idu da yaya Tunda na Fahimci har ahakan Kaunar da suke ma Amina na Dabam ce ta fita zakka ko acikin ya"yansu ita din mafi soyuwarsu ce..! Wannan Karon har Hajiya sai da ta Saki Salati Amina taji kamar dan Ciikinta ya juya ta fara Kokarin tashi Daga jikin Dannallam kawai sai ya kamata ya Rumgumetw zuciyarsa na Bugawa Fat Fat ammh bai Daina kiran sunan Allah ba kada ya rasa natsuwarsa Amina ta nitse Cikin kirjinsa ta wani Fashe da wani marayan kuka Mamammu ta Cutar da ita Cutarwa da bazata taba iya yafe mata ba..! Mamanmu kanta na kasa tacigaba da Fadin"Sai dai Burina bai cika ba..Allah ya tsare Amina Daga tarkona..Acikin wannan tsukin mallam ya Shammacemu ya Daura mata aure da Danmallam auran daya sa na Harzuka Madina ta harzuka itama,Auran da shine Silar Sanadin mutuwar YaYA..! "KARYA KIKE YI..Hadiza bata mutu ba..Ke kika KASHETA Balarabaa..! kawai sai jin kakkusan muryan Aba sukaji ta karade Falom Cikin wani amo mai karfi da ba"a taba jinsa yayi irinsa ba..! Sai kallo ya koma kansa ayadda Idanuwansa suka kada suka yi Jajir kamar gauta sai ya baka Tsoro ya mike jikinsa na karkarwa yana nuna Mamanmu da yatsa yana Fadin"ke kika kasheta..Kika rabata da Duniya Batare da ta miki komai ba. ? Meyasa kikayi haka..? Meyasa kika kashe ran da bata taba Sauya matsayin ki aranta ba .? Balaraba Bazaki taba gamawa da duniya Lafiya ba..! Kawai sai kuka jikinsa ya fara rawa yana neman Faduwa Jafar ya mike da gudu shi da Nasir suka taroshi ya Fada Jikinsu yana kuka jikinsa na rawa yana karkarwa yake fadin"Ita ta rabani da Hadiza..Ya Allah ka wulakantata..!. Sai kuka gabadaya sai kowa yaji ya kara Raunana. Jadwa da Jaleela suka ruga wajen Abba suka rikesa suna kuka sai ga Jamila itama da Jawahir,har da Jawaad na wurin yana kuka duk da ba Duka yake Fahimta ba ya Fahimci kan Rasuwar Yaya ce. Ganin haka yasa Amina ta kalli ya Dannallan cikin rauninta tace"Ina so naje wajen Aba!. Bai musa ba ya Saketa Lokaci Daya ya mike ya taimaka mata ta mike ya karisa da ita gaban yan"uwanta dukkansu suka Dago suna kallonta Aba yana Kuka Kukansa na Fitowa yace"Ki yafemin Amina..ki yafemin..! Kawai sai Amina ta zube kan kafafun Aba ta wani saki kuka,kukan da kowa yaji sai da jikinsa ya kara yin sanyi Su Jamila suka Fada kan Aba suma suna kuka mai tsuma zuciya Danmallam na gefe yana jin kukan Amina har Cikin Ransa da Ruhinsa ammh ba yarda ya iya Bai isa ya hanata kuka ba..! Su Zulfa suna ganin su ya Jawaheer wajen Aba ammh kunya da Bakimciki sun saka sun kasa karisawa garesa suna Zaune sai sharban kuka suke kada Hamida ma taji Labari.. Anty Amarya ta runtse ido sai ga Hawaye lokaci Daya Tana Fadin"Tun Lokacin da naji labarin wannan auran Hankalina ya tashi..Saboda bai kamata wata tazo ta sha gaban Sakina ba..Duk da duk kokarina Burina bai Cika ba,Sakina ta samu Ciki sau hudu tana barinsa..Auran Amina ya razanani ni da Sakina razanan da bamu yi shi Lokacin auransa da Sarood ba Saboda ita na saka mallam ya maidata Hoto..An yi ma Umar Sihirin da bazai iya Zama namiji awajenta ba..Awajen Sakina ne kadai zai amsa sunansa Namiji..! Danmallam ya kalleta Tsam kafin ya juya ya kalli Mallam shima shi yake kallo. Danmallam kansa ya maida kasa bayan sun Hada ido da Aliyu da mamakin abunda ke faruwa yasa ko motsi ya kasa Anty Amarya ta Cigaba da Fadin"Yadda Mallam ya shammacemu ne yafi batamin rai..Sannan ina Tunanin da Sanin Sa"idu komai ya faru..shiyasa na yi alkawarin shima sai ya Kurbi kwatancin bakimcikin daya kunsamin na Kira Dayyaba muka yi mgana..Nace mata ya kamata Yaya TA,MUTU..ita kuma tace Tabbas ya Dace ta Mutum..Ko domin ta Rama Bakin cikin da Sa"idu ya Dade yana kunsamata aranar na Kira mallam na Fadamai komai,Adaran kuma ya Turo ma yaya Hayakin Daya Turketa ya Sarke mata Numfashi...Numfashin Da yayi Sanadiyar mutuwarta..! Anty Amarya ta karishe Fada Cikin gunjin kuka ita da Mamanmu gabadaya Falon aka Dauki Salati sai kuka Mamata na Sharan hawaye tana Fadin"Wannan wani irin mugunta ne..? Gaskiya Balaraaba bazaki gama da Duniya Lafiya ba sai kin lalace..! Hajiya kanta sai da ta Durkusa kan gwiwiyonta cikin rauni tace"Wani irin Rudin Duniya yake diban ku da har kukayi Tunanin Kashe ran da bata muku komai ba..? Kai Haabunallahi wa"inamal wakeel..! Hajiya take fada sai ga Hawaye ganin yadda Hajiya ke kuka ga Aba nayi da su Amina sai kusan kowa ma ya fashe da kukan banda Mallam da Mazan dake da sauran kwarin zuciya. Ammh yau kam Jafar shima kukan yake rerawa Hawaye wani na korar wani. Anty Amarya bata yi shuru ba ta cigaba da fadin"Mun so auran Amina da Umar ya kare a lalace ne Ganin An Dibi Lokaci basu tare ba sai muka Saki jiki..Sai kuma kwatsam Hajiya ta taso da mganar tarewar Amina Data rugazamin Shirina ni da Dayyaba ba yadda bamu yi ba kada hakan ta Faru ammh ina Bakin Alkalami ya riga ya Bushe Allah ya Rubuta kaddara zama Tsakanin Amina da Umar..Bayan ta tare na saka mallam ya kara mata rashin kunya da Fitsara saboda Umar ya gaji ya sakota sai kuma yazo ya bar garin ta kare abunta kan Sakina..Alokacin hankalina ya karkata kan yadda Umar zai zo ya tafi da ita Madina har kiranye na saka an yi mai ammh ba Nasara hankalina ya kara tashi Lokacin da Sakina ta samu Ciki ta karayin barinsa alokacin ne na gane bayan ni acikin matan mallam ma akwai wata mai Buri irin nawa..Saboda mallaminmu ya tabbatar min da ita ke lalata duk cikin da Sakina take samu..!. Anty Amarya kawai ake kallo wacce ta Runtse ido ta cigaba da Fadin"Dana Fahimci ko wacece naso nayi fito na fito da ita Sai dai ina sai ta nuna min In an shirye nake ita atafe ta kwana..Daga karshe sai ta nemi ta lalatamin Duka Shirina ta lankwasa komai ya koma kaina..awannan gabar na rasa madafa.sai da naga Umar ya Danu sannan su Hajiya ma haka sai Hankalina ya kwanta..Ban taba kawo ma kaina wani abu zai ya faruwa ba nan gaba ko da Hajiya ta Dauke Amina nayi Tunanin maiduguri ta kaita sannan Daga baya sai mukayi Tunanin ba auran ne sannan Balaraba kuma hankalinta ya karkata kan Sa"idu da ya koma sai abunda tace mai ni kuma ma samu Natsuwa tunda Umar yazo ya tafi da Sakina sannan Sarood bamu da damuwa akanta Sakina tajata ajiki da farko da sai da ta riga ta mata illah taja baya da ita..Sannan Mallam ya tabbatarmin dacewa sai dai ta gaji da zama dashi araba auran sannan ita kanta Aminar banmu taba Zaton wani abu zai shiga Tsakaninta da Umar har ta samu Ciki ba Shiyasa muka bar wannan Gibin bamu Cike ba..Na rantse har ga Allah Sakina bata da Laifi nice idona ya rufe da Cikar burina ammh ita bata san komai ba,sai soyayyar Mijinta da kaunarsa komai ta aikata ni ce Sila..Ni ce silar duk abunda ya faru..Don Allah ku yafemim..! Sai kuka har da Shasaheka Falon yayi shuru sai tashin koke koke Mallam kansa na kasa yana ta Salati kansa ya Daure acikin gidansa acikin zuru"arsa Shirka ya samu wajen zama bai taba Sani ba..? Bai sani ba sai da Hajiya da Danmallan suka zo suka same shi da mganganu wadanda ya kasa gasgasta su ya rude ya shiga Dimuwa Sannan alokacin ya kasa gasgasta mganarsu ammh yaji Daga Bakin da bazai mai karya ba Hajiya da Umaru...sannan Amina bazata taba fadin Wani abu kan Balaraba ba indai ba Gaskiya bane..ita kanta Hajiya ta shiga Rudani sanda Danmallan yake sanar da ita abunda Amina ta Fadamai sai dai bata ji ita kadai ba,ta tarasa suka isa gaban mallam ya sanar dasu abunda Amina ta Fadamai alokacin zuciyar Mallam ta raunana matuka tundaga wannan Lokacin baya barci Damuwa da bakincikin irin wannan abunda yake faruwa acikin iyalansa bai kara barinsa ya runtsa Dakyau sannan tun alokacin jikinsa yayi sanyi da bai Taba yi ba. Danmallam ma ya girgiza da jin wannan al"amarin ballatana mallam..? Hajiya kuwa duk ta san wani abu sai da labarin Balaraba ya girgizata. Dukkansu shuru sukayi da mganar Suna jiran wannan ranar da dukkan sirrin Boye zai fito Fili.! Baba Mallam ya Dago kansa Rawaninsa ya jike da Zufa duk da Sanyin A.C dake cikin Falon Cikin son ya kara Tattabarwa yace"Wacece ita wacce take Lalata Cikin da Sakina ta samu..? Muna so mu santa sannan mu ganta..Allah ne ya nufemu da Sanin Ainihin Fuskokin wadanda muke Zaune dasu..! Yafada cikin raunin murya raunin da ko Hajiya bata sam mallam dashi ba. Anty Amarya zatayi mgana kenan sukaji muryan Hajiya Uwani Daga Bakin kofar Falon na Fadin. "Gani nan..! Sai kowa ya juya yana kallonta Baki Sake Nazeem da Uzairu suka kalli juna suna mai Nuna Tsanatsanin mamaki. Baba mallan yana kallom Haj.Uwani har ta kariso Falon Idanuwanta sum kode saboda kuka ta Zube gaban mallam Tafashe da kuka Lokaci Daya tana Fadin"Nasan ko ban fallasa kaina ba kasan Abunda nake boyewa..! Don Girman Allah Mallam ka yafemin..Ni ce nayi ma Umar kuruciya shi da Nazir suka kasa zama kusa dakai sannan ni na mai da Nasir mara amfani a wajenka..Ni nake Hana Cikin Sakina Zama mallam duka nice na aikata hakan..! Ta karishe fada Cikin kuka Baba mallam yayi wani mirmishi Takaici kafin yace"Kema saboda ki same ni dani da Dukiyata ko..? Haj.Uwani kanta na kasa tace"Mallam kayi hakuri..Idona ya rufe..Burina naga ya"yana ne gaba akomai..Hajiya tasha gabana a wajenka..Sai nayi Tunanin in ya"yanta suka sha gaban ya"yana na gama yawo..Shiyasa na nemi Cikar Burina ido rufe..Ina da wata Bokanya Da muke cema Mama a Niger take ita take min aiki..Sannan ita ta bankadomin sirrukan Marliya da Balaraba,ita ta bani mgani na saka ma Sakina a tea tasha ita da Sarood har da Amina ma na bata..Ammh sai gashi na ganta da Ciki wanda Mama ta tabbatar min da cewa ko sun samu Ciki sai ya zube..! Ta karishe fada tana gunjin kuka ai Kowa a Falon sai ya kasa motsi ashe abun bai kare ba..? Hajiya Cikin Zubar Hawaye ta kalli Uwani Tana fadim"Saboda mene..? Meyasa kika zabi ki kashe rai Uwani..?.kinsan girman Laifinki kuwa a wajen Allah..? Haj.Uwani na kuka wurjajan tace"Saboda Mama ta fadamin maallam na Matukar son Umar Sannan ya"yansa da zai haifa sune masu soyuwa a wajensa shiyasa na hana matansa su Haihu shi Nazir bai da wani Tasiri ne shiyasa ban Damu dashi ba..Dalilina kenan na daya sa na Tura Nazeem ya rabu da Sa'idu a kan Harkokin dukiyar mallam Burina shine Nazeem da uzairu su zama kan gaba aduka Dukyarka ni kuma na zama nice gaba da Hajiya tunda ya"yana ne akan komai..Wlh sharrin shedan ne ku yafemin don girman Allah sai yau nayi nadama na Fahimci Zakaran da Allah ya nufa da Cara ko ana muzuri ko ana Shaho sai yayi..! Kuka take kamar ranta zai fita Mallam ya Datse Hakoransa waje Daya Cikin Bakiimciki,Sai ga Hawaye sharr na zubar ma mallam hawayen Tsausayin kansa da Bakincikin yadda iyalansa suka Gurbace suka gurbatamai zuru"a. Hajiya ce ta share Hawayenta tana Fadin"Allah ki kayi ma Laifi shi zaki roka uwani..Allah ya gani ban Taba Zama Daya daga Cikin ku da wata manufa ba Shiyasa Allah ya nuna muku iyakarku..Kun ga dai ku baku isa kuyi abunda Allah bai yi ba ko..? Amina tsohon Ciki gareta Haihuwa ko yau ko gobe ina Mganin da kikace kin bata..? Sannan ita kanta Saratun Ciki gareta yakai Wata Hudu ni nace kada a fallasa mganar Cikin ina mganin da kikace kin bata itama..? Sannan ke marliya ina Sihirin da kikayi ma Danmaallam..? Kin Fahimci in Allah yace kun yafakun bawa bai isa ba. ! Sai kallo ya koma kan Sarood da mamaki Sakina kuma cikin ta taji yana Juya mata saboda Tsabar Tashin Hankali. Hajiya ta cigaba da Fadin"Daga karshe nagodema Allah da komai naku ya kare a kanku..sannan ina kara Fada muku ni ban Dogara da boka ko mallam ba..Ni Allah na rike shiyasa na Gagarara har yau har gobe..Kuje Allah zai muku sakamakon abunda kuka aikata Hakkin Rayukan da kuka kashe kuka gurbata bazai taba barin ku ba..!. Hajiya ta fada tana juya baya Lokaci Daya tana sharan Hawaye.. Nazeem na kuka uzairu da shamsu nayi ganin yadda iyayen nasu ke kuka suna neman gafara. Nazifa har muryanta na Dishewa. Hajiya Nasara sai kuka take yi tana Fadin"Wlh ban taba sakama kaina Bakinciki ba..Da zuciya Daya har ga Allah nake zaune da kowa..! Kawai sai ta saka kuka Mamanmu da Anty Amarya da Haj.Uwani Duke suna kuka neman gafaran ya"yansu da Su mallam ammh ba wanda ya kallesu yan gusai kuwa haka suke aibata Mamanmu suna kirarin bazata gama da Duniya Lafiya ba. Tashi tayi tana kuka tana Rangaji ta isa gaban su Amina ta Duka tana kuka tana Fadin"Don Allah Sa"idu kai da ya"yan Yaya ku yafemin..Sharrin Shedan ne nasan na cutar daku..ammh ku yafemin ku yafemin ko domin Darajan su Hamida..! Tafada tana kokarin rike Kafafun Aba yayi Saurin janye kafarsa ya juya baya yana Fadin"Bazan taba yafe miki ba Balaraba..Insha Allahu sai kin girbi Abunda kika shuka..! Sai Hawaye Mamanmu ta Dukar da kanta tana Kuka tana kokarin rike Amina fadi take"Amina nafi cutar dake don Allah ki yafemin..! Amina bata yi sanya ba ta mike da katon Cikinta ta saka Hannu ta Dago mamanmu Tsaye kowa mamaki ya kamasa Ammh basu gama mamakin ba Amina ta Cire Hannunta ta Zabga ma Mamanmu mari kafin ta taso ta kara mata a Hannun hagu kafin ta kara tasowa ta kara mata Sai da ta Durkushe kasa,su Hamida sai kuka ba bakin mgana ba kuma wanda ya Hana Amina. Cikin hucin kuka da Hawaye ta nuna mamanmu tana Fadin"Marin farko na kashe mana uwa da kika yi ne..! Mari kuma na Biyu na yadda kika Lalata rayuwata ce..! Mari na uku kuma na Aba ne..Na yadda kika Raunana masa zuciya..Tsakaninmu Dake BALARABA allah ya isa..Bazamu taba yafe miki ba..! Amina tana Fada tana kuka sai kuma ta fara kokarin Sulalewa Numfashinta na Sarkewa kafin su ya jafar su farga Ya Danmallam yayi saurin isa gareta ta Fada Jikinsa jijjigata ya fara yi lokaci Daya yana Kiran sunanta. Noor..! Nooor...! Sama sama ta jisa kafin ta Bude ido ta fara ganin fuskarsa Cikin Fitan Hayyaci tace"Hubby...! Da Sauri yace"Na"am Noor..ki tashi kada ki tafi ki barni na shiga uku..Ina zaki tafi baki tsaya kin taramin zuru"a Daga Tsatsonki ba..? Tana kuka ta wani kamkamesa Ta fashe da kuka yau Dannallam ba kunya Hajiya bana Mallam da sauran mutanen Dake Falon ya kamkame Amina kamar zai maidata Ciki yana jinsa kamar yana yawo a gajimare kukanta na Dafa mai rai kamar ya Dawo da abunda take ji akansa bayanta yake shafawa a Hankali alamun Lallashi. Kallo sai ya koma kansu Hajiiya ta saki Mirmishi haka ma Mallam da su Ya Aisha Goggo Husai tace"Ajiyan Allah..Gaskiya ne Amina ta FITA ZAKKA acikin gidansu sannan ko azuciyan Mijinta ta fita zakka..! Tafada tana sharan kwallah Aba ma kallonsu yake yi yana jin bakincikinsa na dan raguwa,lokaci Daya yana kallon Mamanmu da wani kallo kallon kin gani..? Baki da yarda zaki yi Alkwarin Allah ne ya cika..! Sakina kuma sai taji kamar wani abu na Bin katafunta tana shafa kasanta tadago da hannunta taga Jini..Sai ta Zaro ido..tana kokarin mikewa jiri ya kwasheta ta zube kasa sumammiya..! Allah ya riga ya Rubuta har ta koma gq Allah bazata taba haihuwa ba.. Shi bawa bai isa ya kankare wannan kaddaran ba..! Cikin ya sake zubewa kamar yadda Sauran ma aka rasasu..! *Janafty**TFZB2027* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Su sadiya suka ruga da gudu wajen Sakina data fadi sumammiya jini na malala ajikinta,A"i kanwar Anty Amarya ta riketa lokacin Da ta ga jinin dake malala ta kasan Sikat din Dake jikin Sakina sai ta fashe da kuka. Ita kuka Sadiya kuka Jidda kuka Sa"adatu kuka,Anty Amarya ta taso hankalinta a tashe tana kuka zata rike Sakina,Anty A"i ta Daga mata Hannu Cikin kuka take fadin"Marliya kada ki kuskura ki taba Sakina..Kije Abunda kika aikata kawai ya isheki ko Alhakin Sakina ya isheki..! Daga haka tace ma Sadiya ta kamata Sakina suje asibiti da ita da yan"uwansu dake Dutse duk suna falon komai ya Faru Anty Amarya tana ji tana gani suka fice da Sakina Daga falon haka ma su Jidda suka Fice suka barta ko gizau Sa"adatu ne kamar zata tsaya sai kuma ta juya tabi bayansu tana kuka Anty Amarya nan ta Sulale tana gunjin kuka. Ganin yadda gabadaya Falon ba wanda yabi ta kan abunda ya faru,Har ta dashi Danmallan din kuwa yana rike da Amina bai Saketa ba ballatana Hajiya da mallam da wannan yanayin bai gama Sakin su ba.. Bakajin komai ba sai tashin koken koken su ya Zulahait kamar ransu zai fita,da kukan Mamanmu da na Hajiya Uwa,haka suke kuka kamar ransu zai fita. Nazeem ne ya fara mikewa Idanuwansa sun kala sun yi jajir Saboda yanayin dayake ciki Cikin wani yanayi ya kalli Uzairu da ya kasa tashi Har da kwallah shi sai da ya Zubar jin abunda Mahaifiyarsu ta aikata. Cikin Kaushi yace"Uzairu tashi mu tafi..Zaman mu bai da amfani a nan wajen...in muka ci gaba da zama anan wurin zuciyata zata iya bugawa..! Uzairu na jin haka ya mike yana Bin Hajiya Uwa da wani kallo kallon Tsana da Bakinciki kafin ya juya zai bi bayan Nazeem daya fara tafiya zai bar Falon da Sauri Hajiya uwa ta kira sunayensu suka tsaya batare da sun juyo ba. Haj.Uwa ta rarrafa zuwa inda suke Tsaye Cikin kuka take fadin"Meyasa zaku juyamin baya. ? Kada ku manta duk abunda na aikata Saboda ku ne..Wlh duk abunda na aikata Saboda ku ne..! Kuyi hakuri ku yafemin Don Allah..! Sai kuka har tana Dukewa saboda kuka,Nazeem ne ya juyo a fusace yana Fadin"kada ki kara jingina Zunuban ki da sunanmu..Tunda nake dake ban taba Fada miki ina son zama a Karkashin Baba mallam ba..Ko Uzairu ma nasan ba Ra"ayinsa bane Meyasa kafin ki fada wannan Halin baki zauna Damu kin tambayi Ra"ayin mu ba..? Me kika nema kika rasa..? Me Hajiya ta rage ki dashi ita da ya"yanta..? Me Baba mallam ya rage ki dashi..? Wlh Tallahi ban taba jin kunyar Hajiya da mallam ba sai yau mugin Halinki yasa na kasa Hada ido da yan"uwana..! Ya karishe fada yana Sharan hawaye Uzairu ma haka cikin Hawaye yace"Mommy meyasa kika Zabi wannan Rayuwar..? Baki taba Tunanin Sharri dan aike bane..?.inda ka aikasa nan ko min Daren Dadewa zai dawo maka..? Wlh ko Kaffara bazan yi ba Shiyasa kanwar mu Umaima take cikin wannan Jarabawar saboda irin abubuwan da kika aikata ne ta ke Fuskata..!mommy kun Cutar damu Kin sakamu jin kunyar Mallam da Sauran yan"uwanmu..Nasan Ya Nazeem bai Fada miki ya samu aiki da wani kamfani a Lagos ba,Sannan ni kuma ,masters dina zan koma bamu da burin komai sai muyi karatu mu nemi na kanmu Muma watarana mu taimakama iyayanmu da abunda muka Tara na Halaliyarmu..! Ya karishe fada Kamar zai Saki gunjin kuka kawai sai ya juya ya fice Nazeem ya mara mai baya Haj.Uwa ta bisu da Kuran sunanyensu ko waiwayo ba wanda yayi..nan ta durkushe tana wani irin kuka mai sosa rai Shamsu na Zaune ya mike shima cikin wani yanayi yazo gabanta ya tsaya sai ji kawai tayi ya Kira sunanta da Sauri ta Dago sai dai ganin kallonta Dayake Binta dashi yasa jikinta yayi sanyi. Kallon tsana da Bakikciki yake Binta dashi da tir da ita bisa yadda ta Aikata wannan abun kunya. Juyawa yayi kamar sauran zai fita Ta saka Hannu ta rike kafarsa ya juyo ya Fizge Kafarsa ya fice da Sauri yana Sharan kwallah Haj.Uwa ta Dora hannu akanta tana Fadin"Na shiga uku na Lalace..! Kaico na..Kai co na..! Wajen Nazifa ta nufa itama kawai sai ta kauda kanta tana kuka Haj.Uwani ta riko hannunta tana fadin"kema gujemin zaki yi nazifa..! Kada ku manta ni mahaifiyarku ce..! Duk abunda nayi yau saboda ku ..! Bata gama mgana ba Nazifa ta kwace Hannunta tana kuka Cikin kukan take Fadin"Ki daina kokarin dora mana Girman zunuban ki..Kin sakamu jin kunya Mommy..Nayi nadamar kasancewarki mahaifiyarmu ayau..Kin cucemu kin bar mana Tabon da har abada bazamu taba mantawa ba..! Tana gama fadin haka ta mike da gudu itama tabi bayan yan"uwanta tana gunjin kuka suka bar Hajiya tana wani irin kuka,kukan nadama da nasani mara amfani. Ita da Anty Amarya da Mamammu wanda ko Tsausayi basu bama kowa afalon ba. Baba mallam sai da ya Dauke kwallah a kwarmin idanuwansa kafin yayi gyaran murya yana fadin"Duk Sboda Dukiya ce yasa kuka kai kan ku ga Halaka..? Shirka acikin gidana da zuru"ata..! Allah ya tsaremana imaninmu..! Bayaso ya cigaba da mgana Rauninsa ya bayyana yasa ya Dakata,irin su Goggo Husai ne da su yakaka suka iya amsa da Ameen ko Hajiya kanta na kasa tana sharan hawaye. Mallam ya cigaba da fadin"Kun Saka ido kan Dukiyar da baku san Wahalar da Sa"idu ya sha wajen tarata ba..Rana iska damina yana Tsaye da Amana kan Dukiyata..Dai dai da Rana Daya bai taba gazawa ba..Sai yau rana Daya komai Dayake faruwa saboda ita ce..? Daman an ce Dukiya da mata sune abun shagala anan duniya..to bari in sanar daku abunda baku sani ba ko nace wasu basu sani ba..Gabadaya Dukiyata Rabinta mallakin Sa"idu ne..Rabi ne nawa shekaru kusan uku da suka gabata ribar da muke samu da nashi aciki..Na saka Lauyoyi sun yi Rubutu ko yau na Fadi na mutu Rabin Dukiyata na Sa'idu ne ya Chanchanta ya kuma Dace domin yafi wahala da ita Fiye dani dana mallaketa..! Ya karishe mganar cikin wani yanayi,Sai kallo ya koma wajen Baba mallam,Kar Baba Sa"idu da Ya"yansa su ji labari cikin mamakin jin kalaman Baba mallam.. Baba Sa"idu dake jikin Jafar ya Dago Cikin Rauni yana Fadin"Baba mallam ammh...! Hannu kawai ya Daga masa yana Fadin"Basai kace komai ba..Wannan ba mgana bace..Tuni an tabbatar dashi Tuntuni takardun komai yana nan a Rubuce..Sa"idu kai D'a na ne..Har yau gobe kana nan a matsayin Babba yaro na..Kafin na same su kai na Fara samu har gaban Abada bazan manta da karamcin Mahaifinka gareni ba..Kafin na Fara sanin kowa Ku na fara sani kai da Hajiya..Dole ku zama wani jigo nawa abunda baku sani bane ba boka ko mallam ba..nan Duniya ba wacce zata kai matsayim Hajiya a wajena..Hajiya ta zauna dani Tun ina amsa sunana Yunusa ban tara komai ba kuma ban da komai ban isa komai ba,ban kai ko'ina ba sannan ba wanda ya sanni..Itace ta wahala dani ta Zauna dani tun ina malamin zaure ta jure yawon gari gari da nake yi domin Da"awa sannan ta jure abubuwa da yawa akaina,Itace ta Fahimceni Fiye da kowa acikin ku..Sannan duk abunda na kawo mata Zata karbesa hannun Biyu bazata taba korafi ba,dukkan ku da na aure ku Hajiya bata taba Daga Bakinta akan hakan ba..Ban taba kawo mgana ta tsallaketa ba yadda ta Daukeni Allah ne kadai ya sani..Bayan ita sai Sa"idu Shima yazo ya wahala dani, wahalan da ko ya"yana basu yi dani ba..Har gaban Abada Hajiya da Sa"idu matsayin su bazai sauya a wajena ba..! Duk Kokarin mai kokari bai isa ya Ture abunda Allah ya kafa ba..Shiyasa duk kan sharrin ku ya koma kanku..Allah ya gani ban taba cutar daku ba..Ammh tunda kuka Zabi ku cutar damu bazamu ce komai ba..Sai dai zamu bar ku da Allah mai Fitowar rana da Faduwar ta,Kamar yadda ya Fallasaku yau..Sannu sannu zaku amshi Sakamakon a Hannunku..! Ya karishe Fada yana kauda kai Daga kallon Anty Amarya da mamammu Dake kuka kamar ransu zai fita. Gogggo Husai tace"Hakkin rai bazai barsu ba mallam..! Mallam yace"Tsakanin su da Allah ne wannan Husai..Basu isa su kashe rai ba..Saboda basu ke Kashewa su raya ba..Duka na Allah ne..Allah daman ya Rubuta Lokacin Hadiza yayi..Ko ba Sanadi zata rasu a wannan ranar..Allah ya rubuta Hakan Wa"adinta ya kare..Ammh sune Sanadin hakan Cutar da sukayi ma Sa"idu da ya"yansa kadai aka bar Balaraba da Marliya sai ya hanasu zaman Lafiya a Duniya..! Goggo Husai tace"Allah ya isarmu..Allah ya sakama Sa"idu..! Take fada tana kuka Yakaka na gefe tana jinjina kai mamaki duk ya cikata wannan aikin duk agidan malami kamar Mallam yunus..! Tsoron Allah ya kara kamata da tsoron rayuwa. ! Amina ko na jikin Danmallam tana Shesshekan kuka shi kuma yana ta lallashinta su ya jadwa na gaban Aba suna ta gunjin kuka. Mamannu ganin Aba ya juya baya su Jadwa ma sun juya mata baya suna kuka sai ta rarrafa wajen Zulfa kafin ta kariso ta mike ta isa gaban Aba ta Zauna tana kuka Daya bayan Daya suka koma wajen Aba da yan"uwansu suka zauna suna kuka suna Binta da kallon kyama..hamida ce ta mike tana wani irin kuka kallon Mamanmu take Idanuwanta sun juye. Mamammu ta rarrafa gabanta ta rike Kafafunta tana fadin"Hamida kema kada ki gujeni..Wlh sharrin shedan ne da Sharrin so..! Hamida ta yi wani mirmishi kafin ta Saki Dariya kamar mahaukaciya. Cikin Dariyan take kallon mamammu cikin wata murya tace"Tunda kike aikata wannan Muguntar naki baki Tunawa damu ya"yan ki ba..? Baki Taba Tunanin watarana abunda kika aikata zai taba mu ba..? BALARABA KO NACE DAYYABA..ki sani Duk abunda kika aikata kanki zai Dawo..Ba yaya kika kashe ba kanki kika kashe ba Amina kika lalata ma Rayuwa ba ya"yanki kika lalata ma Rayuwa Kika gurbatamu kika Wulakantamu..Duk abunda kika aikata tare damu ya"yanki zamu girbeshi..! Ta karishe fada cikin Kuka lokaci Daya da dariya kamar wata Mahaukaciya kowa sai ya koma kallonta cikin mamaki da Tunanin me ya Sameta .!? Mamanmu ta fara kokarin mikewa ta Rumgume Hamida cikin Fitan Hayyaci ta tureta Sai ta fadi kasa cikin muryan kuka tace"Kada ki kara tabani..baki sanni ba..Ban sanki ba..Tsakaninmu Dake sai Allah ya isa..Bazamu taba yafe miki ba kin cutar damu kin Cutar da kanki.Da izinin Lahi sai kin lalace sai Allah ya wulakantaki..Sai Allah ya Dai'daita Rayuwarki sai Allah ya tsarwatsaki BALARABA..! ta karishe fada cikin wani yanayin da sai da ta bama kowa Tsausayi Amina ta Baro Jikin Danmallan Tsausayin Hamida ya kamata kafin ta karisa wajenta Hanne ta isa ta rumgumeta tana kuka tana fadin"Hamida ki daina Fadin haka don Allah ki daina. ! Hamida na gunjin kuka take fadin"Ya zan yi Hanne..? Ina jin zuciyata kamar zata fashe..Kamar zan yi hauka.! Muryan Amina taji a bayanta tana Fadin"Ki rika maimaita innalillahi wa"inna ilaihirraju"un acikin ranki zaki samu Sauki..! Hamida ta saki Hanne ta karisa gaban Amina tana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un Amina da wane ido zan kalle ki ina jin kunyarki..? Take Fada tana kama kanta sai tayi suu kamar zata fadi Amina da Hanne sukayi saurin tarota ta fada jikinsu haka suka kankame juna su uku suna ta kuka kamar ransu zai fita. Kowa afalon sai da ya Tsausayamusu suna yi su ya zulaihat nayi bamai lallashin wani. Mallam ne ya mike yana kallon Hajiya yace"ki Rarrashi yaran nan Hajiya..kukan ya isa haka..Allah ya Tsaremu..! Ta amsa da Ameen Idanuwanta sun kada kafin tace"Cikin wannan halin da suke ciki za"ayi Daurin auran..? Mallam ya gyada kai yana Fadin"Insha Allahu ba fashi..! Ba wanda ya kara mgana Baba mallam yana gyara Rawaninsa yace"Sa"idu tashi muje shashena..Tashi ga Kafafunka da izinin Lahi bazasu taba ganin gazawarka ba..Allah ya Dauke Hadiza ni kuma nayi alkawarin Zan aura maka wacce ta fi Hadiza komai da komai kamar yadda na aura maka ita da farko..! Aba ya mike da taimakon Jafar yana kokarin Daidaita yanayin sa yace"Nagode mallam..Allah ya kara Nisan kwana..! Kawai sai yaji kamar yasaka kuka Baba mallam ya kariso ya rumgumesa yana Buga bayansa Kafin ya Dagosa yana faman share masa hawaye yakuma ja Hannunsa suka fice Daga Falom aka Bisu da kallon Tsausayi da kauna. Su ya jafar ma suka mimmike da su Aliyu jiki duk a sanyaye Ya Danmallan ne ya isa wajen su Hanne yana Fadin"Noor ki bar wannan kukan kinga fa bake kadai bane..Sake su..Ku saki juna hakanan..! Jin muryansa yasa suka saki juna suna kuka Sai suka basa Tsausayi sai ya fara rike hannun Amina sannan ya rike na Hanne da Hamida ya jasu har gaban Hajiya yana fadin"Hajiya ki yi abunda kika saba..! Don Allah kice subar kuka in suka bari Noor zata bari itama..! Hajiya tayi mirmishi ta Karbi Hannun Amina kafin ta karbi nasu hanne Hajiya Nasara tataso ta karbesu tana Fadin"kada ka damu Danmallam bazasu kara kuka ba Insha Allahu..! Ya kalleta kansa na kasa kafin ya juya yabi bayan su Nasir da suka fice tun dazu. Aka bisa da kallo sha"awa irin su Anty Amarya kuma sai kunci da Nadama mara amfani. Hajiya ta tasa su Amina Cikin Dakinta ta Kira Yakaka dasu Aisha tace su lallashe ita kuma ta koma Falo tace a kwashe kayan Amina akai Dakinsu Hanne.. Yan gusai kuma suka koma gidan Aba suma da su ya zulahait domin Hamida ce kadai tare da su Amina Su ya jadwa ma suna Shashen Hajiya suna faman kuka su kuma sai suka koma gida suka Hada kai suna ta kuka ya Zulfa da ya Zeenatu da ya Zulaihat sai yaya Zahra bamai lallashinsu su kansu yan gusai sai Tofin Allah tsine suke yi ma Mamanmu. Kamar wasu marasa galisu haka akayi banza dasu Haj.Uwani ta fara rarrafawa ta Fice cikin kunya da kuka sai Anty Amarya da ta fita tana kuka sai Mamanmu kallo arziki ba wanda ya kara yi musu har suka shige shashensu Daga Anty Amarya har Haj.Uwani Datse shashensu sukayi suna ta kuka ita Anty Amarya ba yan"uwanta duk suna asibiti wajen Sakina da tayi bari ita kuma Hajiya uwani Daga ita sai Umaima dake kwance batasan meke faruwa ba su Nazifa bata san ina sukayi ba,Bata Tunanin ma zasu nemeta nan kusa. Mamanmu kuma fakaitan idon mutane tayi ta shige Dakinta chan kurya tana kuka saboda yawanci bakin suna Dakin yaya ne yaran kuma suna Dakin su Amina kowacce tana Ciki tana Dirzan kukan nadama da nasani da kuma rashin madafa Daga mallam har Aba basu ce musu komai ba ballatana su san ina matsayinsu.! Su Amina kuwa Dakyar suka Daina kuka suka koma ajiyar zuciya.Yakaka tayi ta kokarin Lallashinsu. Sannan su kansu ya Jadwa sai da Hajiya tayi ta musu nasiha suka Saurara sannan Hidiya matar Nazir da Aliya matar Aliyu na tare dasu ita duk ta tsorata tasan tana da Zafin kishi ammh bata san Bin malamai ba..su matan su ya Jafar ma suna nan tare dasu Sarood Hajiya Nasara ta kaita Shashenta Hayaniya ya saka mata Ciwon kai,su fatima na Tare da ita suma duk jikinsu yayi sanyi sun kara Godema Allah Daya tsare imanin Mahaifiyarsu domin ba wayau bane kuma ba Dubaransu bane. Su ya Danmallam kuma suna Shashen mallam,shi da Jafar da Nasir sai Nazir,Aliya su shamsu dai suna Dakim su Nazeem sun kulle kansu Nazifa dai Ta koma Shashen Hajiya Nasara bayan sun gama kukan nasu. Su kansu zaman jugun jugum duk Dauriyan mallam Lamarin ya tabasa shi da Aba sai dai yayi kokarin nuna komai ba komai ba sabida Aba da su ya Danmallam. Mganar Daurin auran gobe suka Tattauna Daganan ya Sallamesu dukkansu ba wanda yayi kokarin komawa gidansa duka nan suka kwana Har Aba da su ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir a falon mallam kamar kwanan zaune ma sukayi su ya Nasir ne da Jafar suka kwana Dakin samarin gidan su Akilu da suma Jikinsu duk yayi sanyi har garin Allah ya waye ba wanda ya saka wani abu acikinsa ko su kansu matan sai da Hajuya tayi ta Fada ne suka sha Tea har su Amina. Mazan kuma da Safe kowanne ya koma gidansa Ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir gidansa suka tafi suka natsa kafin Lokacin Daurin aure kowa kagani ba walwala. Ammh Danmalam bai tafi ba sai da ya leka Amina ya tabbatar da ta daina kuka sannan tana Lafiya. Chan gidan Aba ma haka aka tashi Goggo Husai ne tazo ta zauna dasu Zeenatu tana nuna musu suyi hakuri Laifin Balaraba bazai shafesu ba su yi Hakuri Bikin kanwarsu ake yi to da hakane suka samu suka karya da Safe har suka Dan saki jiki Mamanmu kuma bana wanda ya san tana gidan ballatana abi ta kanta ta kwana kuka ta kasa fitowa ta zama mujiya yau gashi Bikin data cima burina ne ake yinsa ta zama kamar mujiya Cikin mutane. Haka ma bangaran Anty Amarya ita Kadai kamar mayya ta gaji da kiran wayoyin su Jidda sun ki Daga kiranta Har ta A"i taki Daukan wayanta ballatana taji wani Hali sakina ke ciki ta rasa ina zata saka kanta taji Dadi har Sabeeha bata nan sun tafi da ita. Hajiya Uwani kuma kafin Safe har ta Rame saboda tashin Hankali sannan tayi ta kiran Batula bata samu ba tana so ta Sanar da ita komai fa ya Tsaya. Alokacin Datake kiranta ita ta kama Hanyar Minna domin taje ta aiwatar da gudurin Uwani bata sani ba,Ajalinta ne yake kiranta. Domin sun fita Tsafe ba Dadewa suka samu Mummunan Hatsari da yayi Sanadiyar rasa rayuwakan mutum Hudu Dake motar har da Batula aciki..! Sai da Hajiya ta saka baki sannan su Ya Aisha suka Tafi da su Amina gidan su ya Jafar saboda su Shirya Sa"adatu kuma Mallan ya kira Jidda yace Sa"adatu ta Dawo gida ko batasan yau za"a Daura mata aure bane..? Ba Dadewa suka Dawo ita da Sadiya fuska duk ta Kode saboda kuka gidan su ya Jafar suka wuce tunda chan zasu shirya kafin Daurin auran. Anan ne su ya Aisha ke jin Labarin Sakina cikinta ya zube sannan tana chan ana mata karin jini bata san inda kanta yake ba. Sadiya ke maida musu zencen tana kuka su ya Abida na Faman bata baki Amina kuma na tare da su Hanne ita yanzu tama Daina kukan Hamida ce sai Ahankali ita da Hanne suna ta faman bata Baki ammh Taki sakin jikinta gashi ana Daura aure za'a tafi Dasu mallam yace bamai Daga wannan auran. Baba Mallam da Aba tun safe suka fita ba wanda yasan inda suka je sun dai yi mgana da Hajiya kafin su fita Sannan har yan bazanga da bakin gusai suka iso maza basu dawo ba sai wajen 12,da rabi na rana suka Dawo Shima Baki akayi daga maiduguri wani kawun su Hajiya sai D'ansa guda Daya wanda ko Hajiya bata san da zuwansu ba. Ashe Labarin abunda mamanmu ta aika yaje kunnen su kawu Salisu matan sun kirasu sun Fada musu komai,Kawu Salisu sai Fada yake yi yanaCema Aba ya saki Balaraba taje duniyace Mallam ne ma ke basa bakin kan mganar Aba dai bai ce koma ba ai ko bai ce balaraba ta bar mai gida ba in Tana da kunya basai ma ta jira yace ba zata san inda Dare yayi mata. Zuwa Lokacin Yan Daurin aure sun fara Zuwa Mutanen Yola ne suka fara zuwa da Mata guda biyu suka zo aka kai su Shashen Hajiya sai yan Zaria suma sun Iso da mace Daya. Na gombe ne karshen isowa su kan maza ne kadai suka iso banda mace ko Daya. Amaran nachan gidan ya Jafar an samu sun yi wanka sun saka wani Less din da Mallam ya Dinka musu mai Fari da Golden sai Hijabansu mai ruwan kasa Itama Amina ta shirya Cikin leshinta mai Tsada da ya Aisha ta Dinka mata iri daya da ita har da Yakaka sai dai ita Bubu tayi saboda Cikin jikinta kowa ka gani ba walwala ido Duk ya kumbura. Su ya Zulaihat sun zo da Safe suka Hade dasu Hamida da Amina suna ta kuka dasu ya Jadwa suna ta basu Hakuri su kuma suna cema musu ba Laifinsu bane sai da ya Aisha tace zata Kira Hajiya sannan suka sarara. Misalin karfe Daya da wani abu na Rana Kofar gidan mallam ya Cika ba matsaka Tsinke su ya Danmallam sai Lokacin suka iso Cikin shigarsu ta alfarma haka ma su Ya Jafar mallam ma da Sabuwar shadda da rawani haka ma Aba kowa dai yayi kokarin Boye abunda ke ransa har da su Nazeem kuwa. Alokacin kuma Hajiya Uwani ta san da abunda ya faru da yar"uwarta Batula sai ta rude kuka kamar zata Haukace bata tsaya neman kowa ba ta Hada kayanta Ko Umaima bata Tsaya bi ta kanta ba,ta ma bar Shashen nata tana Shashen Hajiya ta shiga Cikin yan Biki ita kadai ce batasan me ya faru ba mutane sun yi yawa yasa har ta fito ta tari abun hawa ta hau zuwa Tasha ba wanda ya lura da ita ammh Nazeem ya ganta sai dai bai nuna ya ganta ba yana Tunanin abunda ya Dace da ita kenan ya Dauka ta neman ma kanta mafita ne kafin mallam ya koreta. Anty Amarya kuma tana Shashenta ko kare bata kara gani ba,kaf Danginta suna asibiti wajen sakina su jidda kuma suna Tare da Sa"adatu domin cire mata Damuwar dake damunta duk da suma karfin Hali ne Mamanmu kuwa Sai da ta raina kanta Har Daki yan Gusai suka Bita suka mata tsofin Allah Tsine shiyasa ta kasa Fitowa Tayi kuka har ta bama uku Lada yan"uwanta sun Tsine mata kamar me sun ce ana Gama Biki yau gobe zasu koma sannan sun ga karfin Halinta Data iya Takowa gidan Sa"idu.. Ita kuma tana Tunanin ina Zata..? Bata da inda zataje a karbeta Ta riga tayi ma rayuwarta mummunan Tabon da har Abada bazai goge ba. Karfe Biyu aka Dauran auran su Hanne,Na Aba aka fara Daurawa da Hadiza Babbar Diyar kanwar Hajiya Yagana Datayi aure mijinta ya rasu bata kuma taba Haihuwa ba..! Hadizan ma da ita aka zo Biki Suma kansu basu sani ba sai da aka Daura shi ya kawo kawun Hajiya Tun Daran Jiya mallam ya kirasa yamai bayani Tun Safe kuma suka Biyo Jirgi Daman a Bauchi yake da zama shi da iyalansa. ! Daurin auran daya bama kowa mamaki Hajiya kam Bakinta yaki rufuwa Mallam a koda yaushe Tunaninsa mai kyau ne Daga nasa sai na Hamida sai na Sa"adatu na hanne ne na karshe Bayan an Daura auran aka shiga taya juna Murna ya jafar yayi mamaki Lokacin Daya ga wanda Hanne ta aura har ya bashi Hannu sukayi musabaha bai daina mamaki ba. Har sai da shi yace mai""Ya jafar Allah ya Rubuta Amina ba matata bace..Hannatu ce matata..,! Ya jafar ya jinjina kai aransa yana kara yima Allah kirari. Su Danmallam suna cikin jama"a suna ta Faman gaisawa da mutane Bakinsa har Kunne shi da Aliyu,da Nazir nan kasan ransa Halin da Amina take Ciki yake so ya sani Sakina kuma bata gabansa bai san Halin Datake Ciki ba Sannan basu kirasa ba shima bai nemi kowa ba. Suna cikin gaisawa da Mutanan ne ya Hango Amina suna tafe ita da Zafira Amina ta saka Hijabi mai Ruwan Sararin Samaniya kalan leshinta da Takalminta mai Saukakan Tudu tana Tafiya cikinta yana gaba da ita Saboda Girmansa har suka shige gidan mallam Ayadda Danmallam yaga Fuskarta ta Kumbura ne yasa Hankalinsa ya tashi yaja Hannun Aliyu suka bi bayansu Baya son yaga Amina na cikin Damuwa,suna shiga kuma haraban gidan yan bazanga suka taresa ana ta gaisawa yasa basu samu karisa cikin gidan da wuri ba. Amina kuma daman Ya Aisha ne tace Hajiya na kiranta, taso ta jira su taho dasu Hanne suna Sauya kaya yasa tace Zafira ta rakota su suna chan ko Mganar auran Aba din ma basu sani ba sai bayan tahowarta sannan Anty Fadila take fadamusu itama Mijinta ne ya kirata ya Fadamata. Amina har ta shiga Shashen Hajiya ta zama abar kallo da Sha"awa suna shiga Falon cike da jama"a. Da Hajiya suka ci karo da ta fito Daga Dakinta Taci gayunta itama bakinta Har kunne Amina suna gaisawa da yan Falon yawancin yan"uwan Hajiya ne taga dai ana nuna tw ita bata san me ya faru ba. Yakaka ce Amina ta Hango zaune itama ta sha gayunta ta karisa suka gaisa Yakaka na fadin"wasu baki ne suka zo suna son ganinki..Hajiya ta saka aka kiraki..! Hajiya ta kariso wajensu zatayi mgana kenan sai ga wata Farar mata gajera ta fito Daga Dakin Hajiya bayan ta wata mata ce itama suna yanayi sai da tana dan tsawo ita. Hajiya na ganinsu ta juya tana Fadin"Yauwa Nenne ga ma Aminar nan ta kariso..! Ta fada tana riko Hannun Amina har gaban matar da Amina ta kasa Dauke Ido a kanta. Wacce aka kira da Nenne ta Rike Hannun Amina cikin Fara"arta take Fadin"Allahu akbar Rahina..Kinga Aminar Aminullahi..Allah ya rubuta Ba matar sa bace..Rabo ne rabo ne ya Haddasa abubuwan da sukayi ta Faruwa..! Wacce aka kira da Rahina tabi Amina da kallo Kafin tace"Ba Shakka yau naga Amina..Aminar da kaf Danginmu ba wanda bai santa ba..Sannu Amina Allah ya raba Lafiya..! Tafada tana kallonta sai Amina ta kasa mgana ta koma tana Binsu da kallo Hajiya tace"Bafa ta gane ku ba inaga sai kun mata bayani..! Tafada tana Dariya. Nenne ta kara rike Hannun Amina Tana Fadin"Amina baki gane ni ba ko..? Ai nasan baki sanni a Fuska ba sai Muryata..Nice fa NENNE..Nennen Aminu fa..! Sai alokacin Amina ta Gane ina ta san muryan Ido ta waro kafin tace"Nenne..! Nenne na Dariya tace"Alkwarin Allah ya Cika Amina..Aminu da bai Sameki ba..Sai Allah ya kaddara yar"uwarki Hannatu ce RABONSA..! sai amina ta kara zaro ido Cikin mamaki bata samun Damar mgana ba Ya Danmallam da ya Aliyu suka shigo Falon bayan su kuma ya Nazir ne yana Cema yan Falon Tawagan Angon Hannatu zasu shigo su gaida su. Sai Amina ta juya suka Hada ido da ya Danmallam ya sakar mata ido ita bashi ma take kallo ba Wanda ya shigo ne cikin Farar shadda da babbar Riga shi da wasu maza su uku. Su ya Danmallam suka basu waje su ka kariso tsakiyar Falon suka Duka suna gaida wadanda ke falon. Kan Aminu na kasa ne Yaji Nenne na Fadin"Aminu yau dai naga AMINA..yau naga Amina..! Take fada Hakoranta duka suna Waje..Atare Aminu da Danmallam suka Dago kansu. Shi Danmallam Wanda aka kira da Aminu yake kallo shi kuma Aminu Nenne ya kallo sai kuma karaf suka Hada ido Hudu da Amina.. Mennarsa da rashinta yasa kadan ya Rage bai Haukaace ba itace agabansa ta Sauya har da Tsohon Ciki ma ajikinta..! *Janafty**TFZB2028* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Aminu kallon Amina yake yi da wani mamaki a saman fuskarsa yana mamakin ganin sauyawarta da komai ma acikin shekaru biyu da wani abu daya shafe bai ganta ba abunda yasa ya kasa daina kallonta Katon Cikin Dake jikinta wannan ya kara tabbatar mai da gaske ya rasa Amina rashi na har Abada..! Shi kuma Danmallan kallon Aminu yake da wani abu acikin ransa kamar almara sai yaji ransa na kuna da wani kishin Aminu acikin ransa in ya tuna abubuwan da suka faru sannan Abaya Amina taso Aminu shiyasa yaji wani Duhu ya mamayesa na ganin Aminu da irin kallon dayake bin Amina Dashi ko shi mallam bai tattauna dashi kan wanda Hannatu zata aura ba abunda a bazata yajisa. Aliyu dake gefensa shima Aminun yake kallo saboda ai shima yasan Labarinsa sai da Dariya ta kusa kamashi yadda yaga Shehi yake kallon Aminu kamar zai shakeshi yana Faman sakin Huci Sama sama. Aliyu ya raba ta gefen kunnensa yana Fadin"Cool Down mana Shehi..! Hararansa yayi kafin yace"Ta ina naga Wani Cool down baka ga yarda yake ta kallemin mata bane..?. Ko ba auran Hannatu a kansa bai san Noor ta Haramta garesa bane yake binta da kallon Daya wuce ka'ida..? Aliya na Danne dariyan sa Lokaci Daya yana Fadin"Yi hakuri zai bari..Kallo Daya ne fa na Musulunci..! Wani Kallo da yayi ma Aliyu sai da ya matsa yana Dariya lokaci Daya yana Fadin"Ana Asif..Shehin Amina..! Kwafa Umar yayi bai kara mgana ba Amina yake satan kallo ransa yayi fari Daya ga bata kallon barayin Aminu yanzu sai ya karkata yana kallon Aminu sai yaga kansa na kasa suna mgana da wanda ke gefensa ajiyar rai yayi har yana Hararan Aminu ta gefen ido Aliyu na ankare dashi yana Dariya aransa yana Ayyana wani irin so Shehi ke yi ma Amina..? Bai taba ganinsa ya nuna kishi kan abu ba sai ayau din nan. Nenne kuma na rike da Hannuwan Amina Fara"arta taki gushewa sai Faman washe baki take yi har gaban su Aminu dake Durkushe shi da Nura da Abokin aikinsa Oscar duk da yanzu ya Daina waka ammh ana tare ba"a rabu ba. Har gabansu takai Amina tana Fadin"Aminu kaga abunda nake fada maka ko..? Na sha Fada maka Allah ya Boye wani abu Tsakaninka da Amina saboda irin son da kayi mata..Rabo ne..Wannan Rabon ne ya raba Tsakaninku sannan da kuma Kaddaran auran yar"uwanta Hannatu Allah mai iko Amina..Rahinatu kin ga Ikon Allah ko..? Rahina ta jinjina kai kafin tace"Nagani Allah ya rabasu lafiya. ! Ta amsa da Ameen Aminu dai kansa na kasa ko Dagowa bai yi ba Amina na haka ta kasa sakewa sannan mamakin yadda al"amura suka juye basu barta ba. Nenne tace"Ina mijin naki Amina..? Ance Babban yaron Hajiya kike aure wanda ke zaune a madina ko..? Kai kawai Amina ta iya Daga mata Cikin Fara"a Nenne tace"Yana ina..? Ina so na gansa ne mu gaisa..? Amina ta Dago kanta tana kallon Dannallam da yayi saurin Dauke kansa Dukkansu suka bi wajen da kallo har shi kanshi Amunun Daidai da karisowar Hajiya wajen Dazu ta bar Falon ne sai yanzu ta shigo Nenne na ganinta tace"Hajiya wancan ne Mijin Amina..? Ta fada tana nuna barayin da su Danmallam suke Hajiya ta murmusa kafin Tace"Eh Shine..Danmallan ka kariso ku gaisa da Mahaifiyar Aminu wanda ya nemi Amina da farko Allah bai yi ba..! Tafada tana kallon Danmallan din Daya Hade ransa kanar bai taba Dariya ba,Aminu kallo daya yayi mai ya Maida kansa kasa azuciyarsa yana jin wani Nauyi Har yau har gobe bai Daina son Amina ba ya sota da dukkan Zuciyarsa ne sai dai ganin Danmallam a matsayin wanda ta aura sai ya Sare domin ai ta samu babban Goro ne. Sannan duk da bai taba ganinsa ba yasha jin Labarinsa wajen Amina ashe shine mallan ya aura mata..? Hakane mganar Nanne Rabo ne..Sannan bawa bai isa ya kankare abunda Allah ya Tsara ba,Sannan matar Mutum ya tabbatar mishi da itace Kabarinsa. Har su Danmallan suka kariso gaban Nenne bai iya Dago kansa ba yana jin Nura na mai mganar ga Mijin Amina wanda ya kasa sa nan bai ko Kara marmarin kallonsa ba. Ita kuwa kallon Danmallam take Cikin Fara"arta kafin tace"Masha Allah..Sannun kaji Allah yayi albarka..Ashe Amina kuma rabonka ce..? Aminu ya so Amina son da bai taba yima wata Diya mace ba..kaganshi nan Saboda rashin Amina Dakyar muka samo Aminu da Addu"o"i da Nasihu yakusa shekara yana jinyar Zuciyarsa Dakyar da sidin goshi muka samu ya Farfardo nasha Fadamai yayi Hakuri yayi takwalli Akwai tanadin da Allah yayi masa agaba haka kuwa akayi kwatsam sai ga Mallam ya Dira a yola wajen Alhaji Babba da mganar Ya bama Aminu auran Hannatu yarsa..Shima bai yi gaddama ba, ya amsa domin na Fadamai daman itace maatarsa Amina kawai Sanadi zata zame sa..Gashi kuma komai ya Faru yadda Allah ya Tsara..muna namu ne Allah na nashi..Allah ya baku zaman Lafiya dukkan ku..Ita kuma Amina Allah ya sauketa Lafiya yasa abokiyar arzikinkace..! Gabadaya suka amsa mata da Ameen har da Aminu da su Nura sai ya Danmallan yaji Nenne ta Burgesa kansa na kasa ya amsa mata lokaci Daya yana fadin"Mungode Mama...Allah ya kara girma..! Ta amsa da Ameen ita da Rahina Amina dai kanta na kasa tana Satar kallon Aminu sai taji ya bata Tsausayi Ashe har jinya yayi tayi bayan rabuwarsu..? Ai ita kanta Shaida ne Aminu ya sota sai dai bata Taba Zaton abun har yakai haka ba nan da nan sai Idanuwanta suka kawo kwallah. Jin yadda Nenne ke Fadama Hajiya wuyar da suka sha kafin Aminu ya manta da komai anan ne taji har ya bar Kano da waka gabadaya ya koma Yola yana cigaba da kasuwancinsa shekara daya da wani abu kenan an samu ya Dawo Cikin Hayyacinsa..! Hajiya ta jinjina kai ita kanta Lamarin ya Dauremata kai da Farko da Mallam ya Sameta da mganar zai nemi iyayen Aminu kan mganar Hannatu shi fa har yanzu sai yake ganin kamar bai kyauta ma yaron nan ba sannan da gaske yake yi tun a wanchan Lokacin da yace zai bashi Hanne. Hajiya bata iya yin gaddama da Shawaran mallam ba Sai dai tayi Fatan Inda Alheri Allah ya Tabbatar in babu kuma Allah ya watsar da al"amarin sannan Tunda taga mallam ya Dage sai ta bishi da Fatan Alheri tasan yana da Dalili Tunda bai taba Tallata ya"yansa ba wannan din ma Domin da Dalili ne. Daman yana da Lambar Alhaji Babba tun wanchan zuwan da sukayi ya karbi Lambarsa basu taba mgana ba sai da Mallam din ya yanke shawaran zuwa chan yola suyi mgana sannan ya Kirasa suka Tattauna a kuma Satin Mallam yaje Yola shi da idi suka gana da Alhaji Babba ya kuma karbi mganar hannun bibbiyu sannan ya labartamai yadda suka sha Fama da Aminu mallam yaji Tsausayinsa sosai alokacin aka kira Aminu yazo jin Bukatar yasa bai yi gaddama ba. Ya Dauki hakan a matsayin nasa kaddaran kenan Mallam ya ga karamcin rikesa sukayi sai washegari suka juyo shi da Idi.. Sannan sun biyosa Daga baya akayi neman aure aka biya Sadaki da Lokaci bayan nan ne Aminu yazo suka gana da Hannatu kowannensu yayi mamakin ganin Dan"uwansa barin ma Hanne da tayi ta kuka tana tunanin me zata ce Amina..? Shi kuma Aminu Kwatan kwacin Soyayyar da Amina keyi ma su Hannatu da wanda ke tsakaninsu yasa ya amince da auran Hanne Dari Bisa Dari. Nenne bakinta har kunne take ta Godiya tana Fadin"Munga karamci Munga Kauna da kara..Allah yayi ma wannan zuru"ar albarka..! Hajiya na amsa da Ameen aranta taji Dadi tasan Hanne bata fada hannun banza ba Nenne da zuru"arta masu karamci ne Amina na chan tayi nisa cikin Tunani ashe har su ya Danmallam da su Aminun sun yi ma su Hajiya sallama sun Fice Daga Falon tana chan cikin Tunani bata ma sani ba sai da suka Fice ta waiga taga basu afalon sannan ta iya Sauke Nunfashi mai karfi Sulalewa tayi daga wajen Nenne ta koma kusa da Yakaka ta zauna suna Hira sama sama rabin Hankalinta na kan Dangin Hajiya yan maiduguri Dake ta shiga suna fita sannan suna kuma Rangada guda sai da Hajiya ta Tsawar tar musu sannan suka Daina ita Amina bata kawo komai aranta ba ta Dauka dai suna yi ne saboda Bikin su Hannatu. Su Hanne take jira taji Dalilinsu na Boye mata Aminu ta aura Shuru Shuru basu kariso ba wayarta ta Dauka ta Dokama ya Aisha kira ta Dauka kafin Amina ta fara Mita tace mata suna kofar gida gasu nan shigowa.. Minti Biyar Tsakani sai gasu sun shigo Duka da Amaran har Sa"adatu da zugan su ya Jadwa Allah Sarki su ya Zulaihat suna baya baya duk sun yi wani zuru har su ya Jidda ma sun dan fi su Sakin jiki sai suka bama Amina Tsausayi sai da ta Share kwallah Bedroom din Hajiya aka shiga Dasu Amina bata bisu ba,ganin mutane nata shiga sannan su Nenne ma sun Shiga suga Amaryansu sannan taji Dadin zamanta bata so kuma tatashi. Sai da ya Abida tazo ta mata mgana Sannan ta iya jijjibiwa ta mike tana mata Dariyan Amina ta zama uwar mata Baki ta tura batayi mgana ba.. Daga Dakin Hajiya Dakin su Hanne aka Maido su daganan sai Falon mallam Abun ya Sauya wannan karon Duba da abunda ya faru jiya. Amina na shiga ta iske Hanne da Hamida sun hada kai suna kuka Sa"adatu kuma na gefe ita da ya Sadiya suma duk sunyi Laushi.. Cogewa tayi kofar Dakin da katon Cikinta tana Fadin"Meye kuma haka..! Kun wani Hade kai kuna kukan munafunci..? Sai alokacin suka Dago Hanne na kuka ta mike ta rumgume Amina,Amina sai ta riketa bata so tayi kuka tana Fadin"Ni sake ni ai fushi nake dake..! Hanne ta Dago Cikin kuka tana Fadin"Me nayi..? Amina tace"Yanzu Ashe Aminu ne kika aura shine jiya cikin ke da Hamida ba wanda ya Fadamin..? Ai kun kyauta..! Tafada tana kara shan kunu Hanne ta kara sakin kuka kafin ta juyama Amina Baya tana Fadin"Na kasa Fada miki ne Saboda bansan da wani ido zan kalle ki ba Amina..! Amina ta juyo da ita tana Fadin"Ki jimin gulma irin na Hanne Hamida..Da wani ido kika Saba kallona don kaniyarki..? Ta fada tana Maida abun wasa Hamida na sharan kwallah Tataso tana Fadin"Tunda yazo ta ganshi Hanne ke Cikin Damuwa..! Amina ta kallesu shekeke kafin tace"To Saboda mene..? Hamida ta kalli Hanne kafin tace"Saboda Tana jin kunyarki..Zata auri Saurayinki..! Amina tayi wata Dariya kafin tace"Ammah wlh Hanne kin bani mamaki yau ko ban yi aure ba ni mai bar miki abunda nake so ne..? Ai kin wuce haka a wurina na Daukeki kamar uwa Daya uba Daya ko Mijina ne ya nuna yana sonki ni mai basa goyon bayan ya aureki ne ballatana Wani Saurayi chan da muka yi soyayyah ina cikin yarinta..Wlh Hanne ki saki jikin ki ki daina Damuwa Dani Dubeni ni ban nemi komai na rasa ba ya Danmallan ne Duniyata yanzu komai baya gabana .! Suka Saki baki suna kallonta Amina ta Shafa Cikinta tana Fadin"Baku ga alama ba ma..! Ta karishe fada tana kashe musu ido Sai gashi sun kwashe da Dariya har da Tafawa ya Sadiya da Sa"adatu sai suka Tsargu tunda basa jin me suke fadi sai suka ga kamar sunayi dasu ne. Hanne tace"Amina dai bazaki taba Sauyawa ba. ! Amina tace"Dillah nayi hankali fa..Nan da wani Lokaci ni Uwa ce..Kun ga kuwa Dole na rage wasu abubuwan..! Suka Hada Baki wajen fadin"Ba shakka Mami Amina..! Dariya suka saka gabadayansu Kafin Amina ta rumgomsu dukkansu tana Fadin"ku daina kuka..Insha Allahu Alheri zaku tarar a gidajenku..Hanne ina miki albishir da kin Dace Aminu mai Kirki ne zai kula Dake..Sannan kin samu Suruka mai kirki irin Nenne..Kema Hamida duk da bansani ba..Nasan kema kin Dace saboda Baba mallam bai taba ma ya"yansa Zabin da bai kamata ba..! Gabadaya sun yarda da mganarta sai gashi Amina ita ke faman lallashinsu Sa"adatu da ya Sadiya basu mata mgana ba itama tayi kamar bata gansu ba Gabadaya Haushi suke bata sannan Daman basa wani shiru da Sa"adatun sai kallonta suke yi ita ko har da gayya take turo Cikinta Tana Tafiya irin ma masu Ciki aranta tace Dan Bakinciki sai dai ya mutu.. Su ya Abida ne duk suka shigo Dakin da su ya Jadwa da sauransu Su ya Zulfa sai da ya Aisha ta jawo su suka shigo nan suka hada kai da Hamida suna ta kuka an basu hakuru sun ki Dainawa Amina na gefe ita bata ma kuka ganitake yi a kyalesu su koka Domin Abun kukan ne yazo. Suna cikin Hakane ya Aisha ta Fallasa Labarin Auran Aba da Hadiza Amina mamaki ya kamata baki Bude wato shiyasa Dazu ake ta nuna ta tasan Anty Hadiza kuwa Diyar Goggo Yagana ne lokacin auran su ya Aisha ita tayi musu ma gyaran jiki sannan Da ita akazo wannan Bikin Dazu ta ganta tana Sanye da Hijabi sai Faman Dukar dakai take yi Ashe shine Dalili Kawai sai taji Hawaye ya kawo mata Alherin Mallam bazai fadu ba sai dai sumai Fatan ya gama da Duniya Lafiya. Nan fa su Ya Jadwa suka Rangada guda ya Jawahir cikin Hawaye tace"Yaya tatafi..Ga Wata YAYAr ta dawo..! Kai Allah ya saka ma Baba Mallam da Alheri gwara Balaraba ta san ba mai yi sai Allah sannan da ranta zata ga Aba da wata mace sai dai Bakinciki ya kasheta muguwar mata..!. Sai kuka ya Jamila ne ma ke nuna mata su ya Zulfa da sukayi wiki wiki ga bakinciki ga kunya ammh bakinta ita da ya Jadwa bai yi shuru ba sai Dakin ya koma na koke koke Su Hamida nayi su ya Jadwa nayi sai da Hajiya Nasara ta shigo ta tsawa tar sannan kowa yayi Shuru. Daganan Shashen mallam aka kai su Hanne yayi musu nasiha shi da Aba da Sauran yayyi irin su Ya Danmallam Amina dai ta gaji da Zirga Zirga tana Bangaran Hajiya sai alokacin Taga Sarood duk yadda taso ta karbi Fara"an Datake mata kasawa tayi Domin wani Kishi ne ya taso mata afakaice Hararanta tayi ta Dauke kanta ita kuwa Sarood daman Yar Fara,"a ce koda yaushe Fuskarta a Sake ne. Ita abunda ma ya bata mamaki yadda Aliya matar Aliyu ke ta faman mata Sannu in ta ganta alhalin a baya ko mganar arziki bata taba Hadasu ba Amina bata amsa mata ita bata son munafunci wato taga ta bare ma Kawarta Sakina shine zata zo ta mata Bariki aiko gidan ta taras itama sai ta basar da ita kamar ma bata ganta ba. Bayan an fito dasu Daga shashen mallan har yan gusai maza da basu koma ba sun yi nasu nasihan yan bazanga dai sun koma har ta da kawun Hajiya sun Dauki Hanyar Bauchi tunda sun yi mai wahalar an Daura auran Sa"idu da Hadiza kamar yadda mallam ya nema..! An riga an gama saka kayan gara da Sauran kayan da baza"a rasa ba a motcin da za"a tafi da Amaren su kawai ake jira Hajiya ta ga Hamida da Sa"adatu bai kamata su tafi basu yi sallama da iyayensu mata ba Yasa ta Damka Sa"adatun Hannun Sadiya tace ta kaita wajen marliya suyi sallama itama Hamida ta Damkata Hannun Zulfa tace suyi Sauri kada Mallam ya sani. Kowa mamakin Kirkin Hajiya da zuciyarta ake yi ganin ko a Fuskata bata nuna Wata alama ba. Haka kuwa akayi Sadiya takai Sa"adatu shashen Anty Amarya da ko kaunar barayin yanzu basa yi tana Ciki kwance daga kuka sai kuka cikin kwana Daya ta fara sauya kamanni Tana ganinsu ta mike jikinta na rawa Zata rumgume su suka matsa baya. Ya Sadiya ta kalleta Cikin wani yanayi kafin tace'Ba wata mgana ya kawomu ba. sa"adatu zata tafi gidan mijinta..gatan nan in kinga dama ki bata Shawaran daya dace in kuma kin ga Dama ki Dorata kan hanyar da kike kai ayau..! Da haka ta Saki Hannun Sa"adatu ta Juya tana Sharan kwallah ta Fice Daga Shashen gabadaya Anty Amarya taji gwiwanta yayi sanyi ta Duke gaban Sa"adatu tana Fadin"Sa"adatu don Allah kada ki gujemin kamar yadda Sauran yan"uwanki suka gujeni..! Sa"adatu ta girgiza kai sai Hawaye Cikin kuka tace"Abunda kika aikata abun kunya ne da abun Tir..Ina Fatan kada Rayuwarki ta Shafi namu Rayuwar..Ko Sau daya baki Tuna kina Damu ba..? Sai yanzu ne da Kika Fara Girban abunda kika Shuka zaki ce kada na gujeki..? Nagodema Allah da zan yi nisa da Rayuwarki gabadaya sannan kuma Insha Allahu zan zauna da mijina da Danginsa Lafiya zan masa Biyayya har karshen Nunfashina..! Daga haka ta juya tana kuka Anty Amarya ta Tashi Tana kiran sunanta bata juyo ba tana shirin Barin Falon tace"Wani Hali Sakina take ciki..? Cikin Dakushewar Murya Sa"adatu ta Tsaya Cak kamar bazatayi mgana ba Sannan tace"Saboda abunda kika aikata ta kara rasa Cikin jikinta..Sannan su Anty A"i sun Dauketa ita da sauran yayinta sun maidata asibitin Dutse Dazu da Safe..! Da haka ta fice ta bar Anty Amarya da Gunjin kuka Duniya ta juya mata baya alokacin da batayi zato ba ballatana Tsammani ba..! Abangaran mamanmu kuwa Ita take ganin Abunda ta aikata Domin ko yan"uwanta sun ce badai zuru"arsu ba Ta nemi wani Ahalin sukan sun yafe ta,Tayi kuka kamar ranta zai fita Tana gani suna Hada kaya sun ce ana wucewa da Amare zasu kama Hanya Tazama kamar wata mujiya acikin mutane ya"yanta kaf sun juya mata baya bama ta su Jafar wadanan tasan Da wuya su iya yafe mata. Ita kadai agidan dukkansu suna gidan Hajiya tana cikin Dakinta tana gunjin kuka,Sai ga su Hamida har aranta taji Dadi ta mike da Sauri zata rumgumesu Hamida ta tureta sai da ta Fadi Cikin Bakinciki ta nuna ta da yatsa tana Fadin"kul kar ma ki fara..Na Fada miki ban sanki ba baki sanni ba..! Zulfa ta kasa mgana sai kuka Daga karshe ma sai ta fice Daga Dakin Mamanmu na kwance in da ta Fadi tana wani irin kuka take fadin"Hamida ni fa mahaifiyarku ce..? Ko Duniya zasu juyamin baya na Dauka kuna tare dani..? Hamida tayi wani Dariya kafin tace"Wlh nayi Nadaman dana fito Daga Cikin ki..Nayi nadamar kiran ki da sunan uwata da nayi..Yadda kika Cutar damu kika bar mana Bakin Fenti kema Bazaki taba Gamawa da Duniya Lafiya ba..! Sannan ga wani karin albishir Aba Yayu din nan tare da auran mu mallam ya Kara Daura masa aure..Da Diyar kanwar Hajiya kin ga kenan tundaga nan kin fara ganin karshenki..! Mamanmu ta Zaro Ido gabanta ya Fadi cikin rawar baki tace"Au...Reee..? Hamida ta gyada mata kai Ta cigaba da Fadin"Kuma na tabbatar da cewa ke ba matar Aba bace yanzu..Gwara tun wuri ki neni inda zaki..Ni dai zan tafi gidan mijina ina Fatan kada Laifin ki ya Shafi rayuwarmu kije Duniya ce..Da Sannu zaki girbi abunda kika Shuka..! Ta juya tana sharan kwallah zata Fice Mamanmu ta riko kafafunta tana Kuka tana Fadin"Hamida kada ki tafi ki barni ina zan je..? Kuma ai Sa"idu bai ce ya sakeni ba ko..? Hamida na kuka da kuma Dariyan Bakinciki tace"lalle Balaraba kin raina ma kanki wayau ba kuma ki da kunya. ! Duk abunda kika aikata kina Tunanin kina da wani Sauran kima ne..? Kima kara gaba tun kafin kifara wulakanta..! Daganan ta Fizge kafarta ta fice tana kuka,a haraban gidan ta hadu da Zulfa suka rumgume suna kuka jin su shuru yasa Ya zulaihat ta Biyo bayansu ganin suna kuka itama sai ta Fara kai mamanmu ta lalata rayuwar ya"yanta. Hakanan suka fito suna kuka Daman duk an fito ana kofar gidan baba mallan ganin Tafiyar Amaran duk yadda Amina taso kada ta fito sai da ya Abida taje ta Taho da ita domin Hanne da Hamida sun ki shiga mota sai kuka suke yi Ganin Amina yasa suka kara rudewa Amina taso ta Daure ammh ta kasa itama sai kuka Aminu kansa kawai ya kauda har da su Nenne a yan Lallashi, Hajiya bata wajen tana cikin gidan su goggo Yagana da su Hajiya Nasara sai yan gusai dake wurin ya Danmallam ma na falon mallam ya Shamsu yaje ya Kirasa yazo ganin yadda suke kuka shima sai da ya tabasa ba kunya ya Riko Amina ajikinsa ya Rumgumeta yana lallashinta ita kuma jinsa ajikinta yasa ta kamkamesa tana kuka Da haka aka samu suka shiga Mota Sa"adatu tuni har sun mika Hajiya da kanta ta sakata a Mota Allah Sarki Hajiya mai rama Sharri da Alheri Su ya Abida suna ta gulmar ya Danmallan ganin ya nufi Cikin gida rumgume da Amina suna Fadin abaya ya Dammallan ko mgana da matarsa bai iya yi gaban mutane sai gashi yau har da su rumgumewa gaban mutane..! Dakin su Nazeem ya shiga da ita yana ta lallashinta Sai da ya dan mata jan ido ne ta Daina kuka ta koma ta Lafe a Kirjinsa tana kuka sai da ya tabbatar da ta daina kuka sannan ya fito da ita da kansa ya rakata har kofar shashen Hajiya sannan ya Dawo..sallama sukayi da Aliyu zasu wuce shida Aliya,Hajiya ta rkota har haraban gidan ta mata godiya bayan ta bata kayan Biki haka su Aliyu suka Dauki Hanya ba tare da sun kara tada mganar abunda ya Faru Jiya ba Sun dai yi mganar Amina yau za"a rakata Sabon gidanta Aliyu na mai Tsiyar yau ango yake shi kuma yana jin Dadi ita kuwa Aliya duk jikinta yayi sanyi ta kara tsorata da Duniya. Ana tafiya da amare yan gusai sukayi Harama Zafira dai tun kafin tafiyar su Hanne ita da mamata sukabi yan Daurin aure suka koma. Ba yadda Hajiya batayi su bari su raka Amina Gidanta ba sukace bakomai in ta Haihu zasu dawo suna gabadaya ransu babu Dadi kaf dinsu suka juya aranar gidan Aba bako Tsinke sai Mamanmu ita kadai da Halinta kaf su ya Jadwa sun koma Shashen Hajiya Babba. Hajiya uwani kuwa abakin Umaima sukaji bata agidan itama taje shashen taga ba kowa Ya Nazifa ke ta kula da kanwar nata ya uzairu ya koma inda yake Service ana gama Daurin aure Ko Tsayawa bai yi ba,Nazeem kuma nan da Sati Daya zai tafi Lagos ya Fara aiki sun yi mgana da Nazifa zata roki Mallan ya bata Umaima tatafi da ita Domin suna da Tabbacin zamam Mahaifiyarsu agidan mallam yazo karshe Duk da sai Dare ne mallam yazo da Labarin rasuwar Batula shima wani Cikin yayyin su Batula ya kirasa yake fadamai sai Lokacin ma kowa yasan bata agidan. Ba wanda ma ya Damu ana ta Hada Hadar raka Amina Sabon gidanta Hajiya ta kasa zama su ya Abida sun tafi tun Mangariba suna gyara gidan suna Share kura da saka labulanya sannan Hajiya tasa Hadiza Amarya Aba ta dan ma Amina gyaran jiki Dayake Sana"arta ce sannan tazo da kayayyanki Tunda tayi ma su Hanne yan"uwanta sai tsiya suke mata suna cewa zata gyara yarta ita kuma tana jin kunya ba Zato ba Tsammani taji auran nan Daga sama har ta fara kuka Hajiya tace kul dinta ta Godema Allah Sa"idu mutun ne har da Rabi,Tun bayan Rasuwar mijinta bata kara marmarin aure ba, ta koma makaranta Tayi NCE sannan ta ke kuma Hadawa da Sana"ar gyaran jiki. Sannan ita bazata ce ga Aba ba, Saboda ganinsa da tayi ba wani mai yawa bane ammh ai suna nan jiya abubuwan nan suka Faru marasa Dadi Hajiya ta mata fada tare da Rokonta ta rike auranta Hannu Bibbiyu. To me zatace..? Sai Fatan Allah ya Zaunar dasu Lafiya sannan bata da matsala macece mai wayewa da sanin Duniya.,Yanzu kawun su Hajiya yace bazata koma ba nan da Sati daya zata Tare wajen Hajiya zata zauna abunda kuma ba"a rasa ba Hajiya da Mallam sun Dauke komai akan abunda ya shafi Sa"idu jikinsu har rawa yake yi Tabbacin kaunace daga Allah. Shiyasa ko kafin ta gama yima Amina Dilkar da tayi mata sun Fara Sabawa Daman ita tana da Sakewa a manganunta Amina ta Fahimci Aba yayi Dacen mata suma kuma sun yi Dacen wata uwar Har su ya jadwa sun shaida haka yadda ta gyare Amina ta sakata tayi wankan Turare Kora su ya Abida tayi waje suna ta mata Shakiyanci Hajiya tace ta korasu waje tayi aikinta Tana yi tana hada ma Amina da yan Shawarwarin rike miji ta bata wata Zuma ta sha saboda cikin jikinta tace bazata sha wani mgani ba sai ta Haihu Tun Amina najin kunya har ta fahimci ita Anty Hadiza ba ruwanta sai itama ta saki jiki tana Sauraranta. Koda karfe takwas na Dare tayi Amina ta shirya Cikin Wata atamfa riga da Zani an Nadeta cikin Lafayan da Ya Aisha ta siya mata har kwalliya sai da Anty Hadiza mata aka fesheta da Turaren Humra masu kamshi Domin Hajiya tace da wuri za"a tafi kai Amina bata son Dare yayi. Sai alokacin Sarood tasan Amina ce Amaryan Umar ya Aisha ta gayamata Cikin Larabci sai kallon Amina take yi da mamaki sannan ga Ciki ajikinta Ahalin Umar bai taba mata Zencen ba sannan ta Fahimci Sakina wani abu ya faru da ita duk da batajin Hausa ammh koken koken da akayi tayi jiya bana Lafiya bane.. Kamar wanchan karon an kai Amina Falon mallam ya saka mata albarka Daganan Idi ya Dauki Hajiya da Amina sai Yakaka da Haj Nasara..Sauran su ya Aisha kuma suka Bi sauran motocin su ya Nasir har da ya Nazeem ya Kai mutane a Motar makarantar su Amina. Su ya zulahait suna baya baya Hajiya tace bai kamata ba su wuce su raka kanwarsu dole suka shige suma anayi dasu. Sune har Babura inda gidan Amina yake Kowa yaje yaga gida sai santi da son barka su ya Abida sun gyare ko"ina sai tashin kamshi Sannan ga wutar nepa haske ya gauraye gidan akwatinta Daya Ya Aisha ta Daukomata Sauran kayan sai gobe Hajiya tace zata za"a kawo mata.. Hajiya da kanta ta shiga da Amina gidanta bayan tace tayi addu"a har kan gadon auranta sannan ta Dafa kanta ta Saka mata albarka Matan kuma suna ta Zagayen gidan suna Santi Su jidda har da Sadiya duk sun zo ganin gida harta Sarood tazo aranta kawai ta Sadakar Umar na son Amaryan nan tasa tundaga abubuwan ma da suka Faru. Su ya Zulaihat suna sharan kwallah suna saka albarka Da wuri Hajiya tace suyi Haraman tafiya haka Amina ta rumgume yan"uwanta tana kuka bata bambamce su ba Har ta su ya Zulaihat Saboda su Daya suka Dauki juna aka suka Taru suna faman lallashinta sai da tayi shuru sannan suka fara Shirin Tafiya Tun dazu su hanne suka kira amare dukkansu sun isa gidajensu Lafiya sai fatan Allah ya bada Zaman Lafiya. Kafin karfe Tara na Dare duk sun watse an maida su gida sai Amina kadai aka bari tsoro ta fara ji gashi ba megadi bai riga ya Daukesa ba Sai misalin karfe goma na Saura na Dare Taji shigowar mota Daman ta kasa Zaman ciki tana Falon ta kasa Zama waje Daya duk Haduwar gidan tsoro bai barta ta wani Dubasa Dakyau ba Danmallam na shigowa falon da Amina ya fara cin karo Daman yasan Za"a rina Amina ce fa sarkin Tsoro rike da ledan kaza da madara ta fadamai ta rumgumesa tana mai kukan shagwaba ya barta ita kadai tana jij tsoro. Yana shafa bayanta da Hannu Daya Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta yace"Shii..Ba shikenan ba gani na shigo ba..Ni dai yau ataimaka kada kukan nan naki ya hanani Shagali..! Tana jinsa sai ta kara kamkamesa Shima yana rike da ita har suka zauna Saman Kujera ya Dora ta ita da Cikin Saman jikinsa bayan ya Sauke Lodojin Kasan Cafet harshensa ya sa yana Lashe mata hawayenta Lokaci Daya yana Fadin"Noor nidai kimin kudin wannan kukan naki na siyesa na kwana Biyar..Lokacin na gama Shagalina sai ki dawo da kukanki..! Yafada cikin Shagwaba yana kwaikwayon muryanta Dariya ta saka ta Fara Dukansa da Hannunta a kirji Tana fadin"Hubby..La..la..! Dariya shima yake ya rumgumeta yana Shafa Cikin jikinta Lokaci Daya yana Fadin"Eh Noor..Kinsan ai nayi kokari ko..? Kiyi hakuri yau kam bazan iya Hakuri ba..! Yana fada yana Shafa wuyanta Lokaci Daya yana shakan kamshin Turarenta dake jikinta Sama sama taji yana Fadin"Noor..! Chan kasan makoshi tace"Uhmm! Cikin wata kasalalliyar murya yace"Ya sunan wannan Turaran..? Itama cikin wani yanayi yace"Bansani ba..Anyy Hadiza ta sakamin..! Kai Tsaye yace"Wacece haka..? Kanta na nutsewa saman kirjinsa tace"Amaryan Aba..! Yar dariya yayi ya kamkameta yana Fadin"Ina yinta sosai..kamar tasan ina bala"in son kamshi..Barin ma irin wannan..! Daganan bai Tsaya ba ya shiga wata Duniya Har Lafayan shi ya warware yana Shagalinta itama saita Dafe shi Tana taimaka mai domin bata juya ma wannan al"amarin baya ba. Ganin zai shiga wani duniyar yasa ya Sarara mata duk tayi laushi yasa bai Takura mata ba,ya je kitchen da kansa ya Samo Filet da kofi yazo ya juye Zabbin Daya Siyo yana Fadin"Na Biya bashi kazan amarci..! Tana daga kwance tace"Biyan bashi kazan amarci Amarya da Tsohon Ciki..! Dariya ya Fashe da Shi yana Fadin"Ke bana son jidali..Kinsan dai Cikin maza sai an tona za"a samu mai kokarina ko..? Tana Dariya tace"Sosai ma Hubby..! Mirmishi yake mata yana jinsa cikin wani yanayi. Shi ya taimaka mata ta tashi zaune haka ya tasata yana bata abaki itama tana bashi Sun kusa cinyewa ta kalli Kazan tana Fadin"Kazan amarci ai kanka ka siyo mawa ko..? Yana Dariya yace"Naki ne..Na zata kin sam min ne fa..! Cinya ta Dauko ta Turamai abaki Tana Fadin"Ai tunda kaci kazar amarcin Amarya sai ka famshe mata..! Cikin Farinciki yace"Da gaske Noor..!? Yafada yana rike hannunta kunya ya kamata ta Dukar da kanta kawai sai ya Saketa ya Cika mata Kofi da madara ya bata tasha shima ya Cika ya sha bai Tsaya ma wasa ba ya Dauketa ita da Cikin sai Bedroom din su acikin Tiolet ya Sauketa yace su yi alwala shi ya taimaka mata tayi alwalan sannan shima yayi nashi suka Fito shi ya jasu Sallah raka"a Hudu sannan sukayi ma auransu da Zuru"arsu Addu"a. Jikin ya Danmallam har rawa yake yi shi ya Raba Amina da kayan jikinta duka bayan shima ya raba nasa da Jikinsa ya kamkameta suna Sharing din Body Cantact sannan suna jin Bugun zuciyar juna Cikin hankali ya fara Sarrafata Amina bata bari kunya ya Cutar da ita ba ta tallafesa tana taimakamai sai da Tafiya ta mika ne ta fara mai kukan shagwaba shi kuma ya mika bazai iya komawa baya ba sai kawai ya Tallafeta Sosai yadda Cikin jikinta bazai basa matsala ba Cikin karyewan Sauti yace"Noor..Ahankali fa zan yi..Kadan kadan..! Yake fada mata yana tusa kansa a wuyanta Amina tace"Hubby..Shi..Da Zafiiii...! Fadi kawai yake"Noor a hankali zan yi na rantse miki da Allah..! Daga gani baya cikin Hayyacinsa ba wani Zafi Amina take ji ba,kawai Kukan Shagwaba take jin Dadin mai Duk sai ya karamai karfin gwiwa. Ya Dauki Lokaci mai Tsawo tare da Amina lokacin da bai taba Samu ba Shudewar Mintina Talatin da biyar sannan dukkansu suka samu natsuwa da juna haka ya kamkameta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Noor..! Yadda kika farantamin Allah ya farantamiki..! Tana kwance saman kirjinsa yace"Ameen Ameem Hubby..Ana Behabbak.. Yana kamkame da ita yace"Ana bihabbeki Khatheran..! Haka suka kwana cikin Farinciki da Asuba bayan sunyi sallah suka koma Amina tayi Dauriya sosai wajen mijinta shima yasani yana ta saka mata albarka. Sai wajen goma sukayi wanka suka Sauya kaya Hajiya ta aiko Idi Direba da abinci da akwatun Amina Duka suka kwasa zuwa Cikin gida. Wuni sukayi suna cin amarcinsu Amina tabara kala kala take masa yana Biye mata Da rana ma Daga gidan mallam aka aiko musu da abinci da Daddare ma haka. Har sai da akayi kwana Biyu sannan ya Fita ya yi musu Cafane shi ke taya Amina Girki abunda bai taba yima Sakina ko Sarood ba..Bai taba Zaton Amina ta iya abubuwa haka ba bangaran Girki da bangaran kwanciya da miji ta kwancemai kai har mamaki ma take bashi wlh ga Ciki ammh bata taba nuna mai Raki ba. Saka albarka kuwa ta shashi har ta gode Allah Shiyasa take nuna juriyanta akan komai ganin yadda yake Lalacewa akanta. Su Hanne sun kirata da wayoyinsu da Hamida suka fara waya sai daga Baya Aminun ya siya ma Hanne waya tana Yola ita da Nenne suna zamansu Lafiya sai Hankalin Amina ya kwanta. Bangaran gidan mallam kuwa Baki na nesa da na kusa sun koma gidajensu Dakin Hajiya Daga Anty Hadiza sai Yakaka da tace sai Amina ta Haihu zata koma. Bangaran Aba kuwa baya kwana agidansa gidan gona yake kwana Jawaad kuma yana wajen Hajiya Mamanmu kuma ita kadai agida kamar mayya tayi kukan har ta gaji Ta rame ta lalace sannan ga Fama da Mutuwar jiki da kasala tunda akace Aba yayi aure zuciyarta ke zafi. Anty Amarya ma kamar mujiya bata ko Fitowa,Chan duste labari duk ya bazasu kowa yasan abunda ta aikata shi dai mallam ya zura mata ido bai ce mata komai ba ballatana tasan mafitanta Sannan duka ya"yanta ba wanda ya kara bi ta kanta har Sabeeha na wajen Hajiya sai jefi jefi take ganinta Turakan mallam kuma Daga Hajiya sai Haj.Nasara Bangaran Hajiya uwa tana chan gidansu Cikin wani irin Hali Duk da ba wanda yasan abunda ya faru sun fara Zargin akwai wani abu saboda mallam bai zo ba ballatana ya"yanta ko Hajiya ma batazo ba ahalin in Lafiya lau Tare da Hajiya zata zo haka aka watse bakwai din Batula da tata ta kare Aka bar Uwani ita kadai Tana Faman da Bugun zuciya mutuwar Batula ya kara Raunanata Gata nan kawai ammh ita kadai Tasan Halin Data ke Ciki kuka tayi shi kamar Idonta zai Tsiyaye Kiran wayan su Nazeem kam har tagaji basa Dauka Shamsu ne ma ya taba Dauka yace kada ta kara kiransa Nazifa kuma Blooking dinta ma tayi,bata da karfin gwiwan komawa Gumel domin tasan zamanta achan ya Kare. Rayuwa ta juya musu baya alokacin da basu zata ba,. Sati Daya na Cika Anty Hadiza ta tare adakin Yaya,sai abunda ba"a rasa ba Hajiya ta kara mata sannan Aba yayi mata akwati Biyu na lefe su Yakaka ne gaba gaba yan raka Amarya ita da Haj.Nasara. Aranar da Daddare Danmallan suka zo shi da Amina data matsa sai ya kawota taga Hajiya da Aba da Mallam,sai da suka zo sannan Hankalinta ya kwanta Shashen Hajiya ya barta yaje shashen Hajiya nasara ya ga Sarood Tunda tana wajenta yace ta koma gidansu na kofar arewa tace ya barta anan tasan ba wani Damuwa da ita zai yi ba yana da amarya Shi ko ba haka bane gani yayi ba yanzu zasu koma ba Sai nan da wata Biyu gwara ta koma gidanta zai fi in ya gama kwanakin sa wajen Amina sai ya koma mata ammh sai ta nuna bata so..! Sai kawai ya kyleta ganin kishi take shi ko aransa ma tunani yake sarood bata iya kishi ba ai kishi na wajen Aminaa Jidali. Shi tunda abun nan ya faru bai kara neman sakina ba,shi abakin ma Hajiya yaji Yan"uwanta sun maida ta Dutse daganan bai kara bi ta kan mganarta ba sai da komai ya bayyana sannan ya Fahimci bai taba Son Sakina ba komai ya kare acikin Ransa kwata kwata shi dai bai ma tsaya ya yanke wani hukunci akanta ba sai dai bata acikin Ransa kwata kwata. Basu koma ba sai Sha Dayan Dare Har gidan Aba suka je,Mamammu ta window take lekonsu tana Kuka kukan Nadama da Bakinciki. Amina Bakinta yaki rufuwa ganin Anty Hadiza Dakin Aba ta rumgumeta tana murna sosai itama ta riketa cikin Farimciki jawaad tana murna ya samu mama. Haka kowa ke shigowa yana fita bawanda ya Damu da wata mamanmu mamakin karfin Halinta ma Aba ke gani data ke cikin gidan bata kara gaba ba. Agaban idonta ya shigo gidan da Ledoji a hannunsa ga shi yaci Farar Shadda yayi kyau rabonta data gansa tun Ranar da komai ya bayyana..! Agaban idonta Sa"idu ya Shige Dakin Yaya da wata mace suka Sakayo kofa sai taji jiri na Dibanta ta Daga kafa kenan Jirin ya yarfar da ita faduwar da zai yi Sanadiyar shanyewar  barin jikinta Guda Daya..! *Janafty**TFZB2029* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Wajen kwana Biyar Aba yana cin Amarcinsa hankalinsa kwance ya samu natsuwa da Anty Hadiza fiye da yadda ya Tsammanin samunta. Bai taba zaton balaraba tana cikin gidan nan ba, bata kara gaba ba,saboda Dakinta yana rufe ne sannan bata fitowa yayi zaton tayi ma kanta Hisabi ne ta kara gaba Acikin ransa kuma wannan kuncin da bakinciki da Tsanar Balaraba baya jin zasu sake shi nan kusa yana jin har duniya ta Nade bazai iya Yafe mata ba. To shi kanshi baisan tana cikin gidan ba,ballatana Anty Hadiza da bata Dade agidan ba,Sai ranar kwana na shida ne Wari ya rika fitowa Daga Dakin da Kakarin mutum kamar zai yi Amai Lokacin Aba ya fita gidan Gona Anty Hadiza ke tsakar gida tana Shara taji wannan abun sai hankalinta ya tashi ta tsorata sai dai bata bar kiran sunan Allah ba Mayafinta ta Dauka ta je gidan mallam Shashen Hajiya ta gayamata abunda ke faruwa ita kuma Hajiya ta Sako Hijabi ta Biyo bayanta. Koda suka zo Dakin yana rufe ne ta Ciki ba yadda zasu yi su shiga sai an balle kofar sannan Hajiya tana da Tabbacin Balaraba na ciki Saboda ai ita tayi waya da yan gusai a manganganunsu bai nuna balaraba ta koma chan ba sannan tana da yakinin kunya da Nadama ne suka sakata ta kasa fitowa kamar yadda ya Kanannaye Marliya itama ko Kamshinta bamai ji itace ma Sarkin Tsausayi take umartan su Lami da in sun gama girki su shigar mata dashi Cikin Shashenta kada yunwa ta mata Illah. Hajiya mallam ta kira awaya bai yi nisa ba yana makarantar Haddar su Amina suna taro yace ga shi nan zuwa Daganan sai ta kira Aba tace ya Dawo gida shi har ya rude ya zata ko wani abu ne ya faru da Hadizar shiyasa yazo Hankalinsa tashe ko kafin ya kariso Mallam har ya dawo sannan ga Jafar ga Nasir su suka kira mai Balla kofa kafinta yazo ya Balle kofar Gabadayansu sai da suka toshe Hanci suka samu shiga Dakin Halin da suka Iske Mamanmu aciki Dole bawa ya kara Tsoron duniya.. Tana kwance a kasa inda ta Fadi Jiki ya jirkice Baki ya karkace Anan tayi kashi da Fitsari bazata iya tsshi ba Idanuwanta sun kafe saboda kuka sannan ta galabaita da yunwa da kishi Tana ganin Hasken rana ya shigo ta Fara laluban inda zata Hango mutane sai idonta ya koma yana ganin Duru Duru bakinta ya bushe ba"a kajin me take fada sai mgana take yi ba wanda ya Fahimta ashe ruwa take fadin a bata Anty Hadiza ce ta karkata kunnenta har taji abunda take fadi ta Ruga Kitchen ta Dauko ruwa Tsausayinta har ya kamata Idanuwanta ya ciko da Hawaye ta kasa ma Daga kanta ita kadai kuma ba wanda ya taimaka mata hakanan ta Zuba mata ruwan wani ya shiga Bakinta wani kuma ya Zube a kasa. Hajiya ta kalli mamanmu ta kara kallanta kawai sai ta gyada kai ta Girgiza kafin tace"In bawa bai ji Tsoron wannan rayuwar ba yayi asara..Allah ka Tsare mana Imaninmu..! Aba ko na tsaye yana kallonta aransa yana jin Dadi samnan yana mata Fatan abunda zata gani sai ya fi haka Ya Jafar ko nadaga bakin kofa bai ma kariso ba domin in akwai Hallitar Daya Tsana to ya ga mamanmu ne yanzu nan komai zai Dawo mai acikin kansa Nasir ne ke gefen Aba Mallam kuma Duke yake gaban Mamanmu ya kasa mgana Acikin ransa kuma Kabbara da Kirari yake ma Allah yana Tunanin yaushe bawa zai gane cewa Duniya ba matattaba ne. ? Yaushe zamu san cewa rayuwar nan tana cike da tashin Hankali ne..? Kai ya girgiza kafin yace"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un..! Haka kawai yake fada Aba kuma kawai sai ya juya baya zai fice Daga Dakin Mallam ya Daga kai ya kallesa kafin ya kira sunansa shiyasa ya Tsaya kafin ya Juyo yana kallon Mallam din. Mallam ya mike yana Fadin"Ina zakaje..? Baka ga Matarka cikin wani mawuyacin Hali bane..? Kallon Baba mallam yake yi Cikin mamaki kafin ya cije baki yace"Balaraba ba matatace bace..Tun Ranar da nagnee ita wacece na Tsinke saura igiya biyun Dake Tsakanina da ita..! Mallam ya jinjina kai Daman so yake ya tabbatar da hakan duba da yadda Sa"idun bai kara Tadamai da mganar ba,Hajiya tace"To yanzu ya za"ayi da ita..? Aba zai yi mgana kenan Mamanmu ta fara zakuda jikinta tana kuka tana mgana bamai gane me take fadi Sai da Hajiya ta Duka da warin Dake fitowa Daga Jikin Balaraba haka ta Daure tana Fadin"Me kike son kice Balaraba..? Cikin Daba daban mgana tace"Kuu u....yaaaa...fee ee..min..! Sai Hawaye Daga gani ta gama galabaita Hajiya ta Dago tana kallon su Aba kafin tace"Yafi yar ku take nema Sa"idu ni dai na yafe miki balaraba haka ma mallam..Sai dai Sa"idu da yaran nan..! Aba ya juya kawai yana Fadin"Har Abada bazan iya yafe ma wacce ta Cutar da rayuwata ba..Da yardan Allah kin fara gani kenan kafin ki Mutu sai Allah ya Dandana miki azaba mafi muni akan abunda kika aikata muguwa kawai..! Daga haka ya fice Daga Dakin a Fusace Jafar ya mara mai baya domin shima bazai iya yafe mata ba Anty Hadiza na gefe tsausayi duk ya Cikata sannan ta kara jin tsoron rayuwa da Duniya gabadaya. Ba wanda ya iya taimaka mata cikin wannan Halin suka barta Hajiya da mallam a falonsa suka shiga suka Zauna mallam yayi jigum Domin har yanzu abunda ya faru bai sakesa ba,Hajiya ma Tagumi kawai tayi tana kara Jinjina al"amarin kafin ta Daga kanta tana kallon Mallam cikin wani yanayi Tace"Mallan yanzu ya zamu yi da ita..? Ayadda Sa"idu ya fice bazai taba Sauraran kowa ba..! Mallam ya Sauke Numfashi kafin yace"Nima abunda nake Tunani kenan..Bazan taba takura ma Sa"idu akan wannan al"amarin ba kamar yadda ban takura ma kaina ba..Zan Kira chan gusai na Fada musu Halin da ake ciki yan"uwanta da suke Dolenta su zo su tafi da ita..! Hajiya ta jinjina kai alamun gamsuwa nan take ya kira Kawu salisu bayan sun gaisa ya Fadamai abunda ke faruwa shima Dagachan barayin yace kadan ta gani sun yi mgana kan zai Fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita Domin ta fara girban abunda ta Shuka ne da wuri. Bayan sun gama wayar Hajiya tace"Ya kuka yi dashi..? Mallam yace"Yace zai fadama yan"uwanta gobe zasu zo su tafi da ita.! Hajiya ta Sauke Tagumi kafin tace"AllAh ya kyauta..! Mallam ya amsa da Ameen Cikin wani yanayi Hajiya ta gyara zama tana Fadin"Mallam ya batun yaran nan..?. Kasan dai uwa ba abun wasa bane sannan duk abunda iyayansu suka aikata basu isa su sauyawa Tuwa suna ba..Na lura daga ya"yan Balaraban har na Uwani da Marliya tun da abun nan ya Fallasa suka gujema iyayan nasu kana gani Harta Umaima ina jin yan"uwan sun fadamata tana shashena ko Damuwa da uwar ma batayi ba..! Mallam na jinta kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Me kike so ayi..? Hajiya tace"so nake ka kira su kayi musu nasiha kan Muhimmancin Uwa awajensu sannan su yi hakuri su yafe musu su tallafesu domin su kadai ne yanzu suka Rage musu..! Mallam yace"Zan yi musu mgana Insha Allahu. ! Hajiya tace"Ya kamata gaskiya..! Gani tayi mallam na nemsn shigewa Ciki yasa ta kallesa tana Fadin"Mallam ya batun Uwani da marliya..,? Gwara Uwani tana gidansu Marliya kuma ta nan ko Fitowa batayi nine ma nake saka su Lami suna shigar mata da abinci..! Mallam ya Dakata yana kallon Hajiya kafin ya koma ya zauna yana Fadin"Duk da Sakin aure ba Dabi"ata bace..Ammh kuma ya zama Dole ne Bazan iya Cigaba da zama da Uwani da marliya a matsayin matana ba..Dukkansu zan tsinke igiyan aure koda Dayan Dake Tsakanina dasu ne Su je na yafe musu ni ban taba Cutar dasu ba..Allah suka ma Laifi sunemi gafara a wajensa..Zan samu Lokaci naje chan Tsafe gaisuwa zan sanar ma ita Uwani marliya ma zan sanar da ita abunda na yanke..! Hajiya sai taji wani iri sai dai tasan mallam ya tsorata da wannan al"amarin yasa kawai tace"Allah yasa hakan shi yafi zama alheri su kuma Allah yasa hakan ya Zame musu izna..! Ya amsa mata da Ameen kafin yace"Me Saratu take yi agidan nan ne..? Bata koma gidan mijinta ba..? Hajiya tace"Na tambayi Danmallam din yace min yamata mgana ta koma taki tace ya barta anan..! Mallam yace"Wannan mganar banzace..Bazai yuyu ba Dole yayi adalci Tsakanin matansa Raba musu kwana zai yi Saboda yayi adalci a Tsakaninsu ki Fadamata ta shirya ta koma Gidan auranta zan kira Umarun zan mai mgana..,! Hajiya tace"Shima yaso ta koma itace taki..Kasan ita kadai ce yanzu ko Rashin Sakina agidan yasa taji wani iri..! Mallam yace"Ita Sakinar tana chan Dutsen kenan wajen Danginta..? Hajiya tace"Eh sadiya ta fadamin tun washegari suka Dauketa Daga asibiti suka tafi da ita..Ta kara barin cikin nata ne.. Mallam ya jinjina kai kafin yace"Allah ya kyauta na gaba..Shi ya matsayin auran nasu da Sakinar..? Ko baku yi wannan mganar dashi ba..? Hajiya tace"Bai taba min wannan mganar ba..! Mallam ya koma ya jinginar da kansa Jikin kujera yana Fadin"bari zan Tuntubesa naji..Bazan mai Dole ba Sai dai zan bashi Shawara a matsayina na Uba a wajensa..Ina Fatan abubuwan da suka Faru su zama izna garemu da yan baya..Sannan ina Rokon Allah ya Tsaremu da zuru"armu gabadaya Daga Fadawa Halaka..! Hajiya ta amsa da Ameen Ameen basu wani Dade suna mgana ba ta koma Shashenta ta bar mallam zai kwanta Saboda tun faruwar abun nan bai wani Cikin natsuwarsa abun ya tabasa sosai,Ita kanta sai a Hankali ta gama tsorata da Duniya da mutanen Cikinta Har ita kanta Nasara sai ahankali gidan gabadaya sai yayi kamar ba kowa,shuru kowa kumazaka gansa baya cikin Walwalarsa. Hajiya bata yima Sarood mgana ba Illah ce mata tayi taje mallam na nemanta Sai da taje ne Mallam yayi mata Nasiha Daga karshe yace tayi Hakuri ta koma Gidan mijinta ta zauna kafin su tafi ta tabbarar mai da Insha Allahu zata koma sannan ya Sallameta Kai Tsaye kuma ya Kira Danmallam yace yazo yana nemansa Tun da yammah bai samu zuwa ba Sai Dare saboda Rigimar Amina wai sai yazo da ita bazata iya zama ita kadai ba yasan in yazo da ita sai ya shafada wajen Hajiya kamar yadda akayi Ranar shiyasa ya zauna ya lallabata Dakyar da Sharadin bazai Dade ba Sannan ta barsa ya fito. Sai da suka Idar da Sallar Isha"i sannan Suka gana da mallam a Falonsa mallam bai nuna mai ya san wani abu ya tambayesa zaman me Saratu take bata koma gidansa ba..? Sai ya karantamai yadda sukayi da ita Mallam yace"Wannan ba Hujja bane Umaru..ita macece kai kuma Namiji ne Shugaba..Kada ka manta adalci ne aikinka Tsakanin matanka..Kada ka bari Daya ta Rinjaye ka domin Ranar Lahira zaka tashi da Barayinka daya ne yana Rinjayan Daya. kada ka Duba wai Tare kuke achan duk wannan ba Hujja bace..Zaka raba musu kwana ne har Lokacin da zaka koma shine adalci..! Danmallan kansa na kasa yana gyada kai bai ce komai ba Mallam ya Cigaba da fadin"Na kira ta na mata mgana saboda haka yanzu ka Dauki matarka ku tafi gidanku..Allah ya zaunar daku lafiya..! Danmallam sai Lokacin ya Dago kansa yana Fadin"Naji Duka mganar ka mallam..Sai dai ina so kamin afuwa Zuwa gobe da zan cika Sati Daya awajen Amina sai na koma wajen Sarood din..!. Mallam ya kallesa kafin yace"Shikenan daman na Tunasar Dakai ne..Itama akwai Hakkinta akanka Umaru kuma ina yi maka kwadayin Zama mutum adali Allah yayu muku albarka ya wajen ita mamar tawa..? Fata dai ba wata Damuwa ko..? Danmallam yace"Lafiya lau mallam..! Daga haka shuru ya Biyo baya sai Danmallam din ne ya gyara zama yana Fadin"Mallam daman ina so nayi ma Hajiya mgana..Yakaka kakar mijin Aisha da bata koma ba tunda sun shaku da Aminar me zai hana ta koma chan Gidan Aminar su zauna tare..Ga Halin Datake ciki sannan in ina gidan Sarood bazan dinga Fargaba ba..! Mallam acikin Ransa Hamdala yake yi Saboda yaga kaunar Mamar tasa a cikin Idanuwan Umar. Kai Tsaye yace"Kayi Tunani mai kyau..Kada ka Damu zan yima Hajiyar mgana gobe sai ta saka Idi yakaita Yakaka akwai kirki da karamci Sosai shekaran jiya ta na nan har Dare muna ta hira da ita..! Danmallam yayi godiyar har ya mike zai tafi Mallam ya saka Baki ya ka kirasa ya Dawo ya Durkusa a gabansa Mallam ya kallesa Kafin yace"Ya mganar Ka Da Sakina..? Naji har yanzu baka ce komai ba..Sannan kana jin labarin Halin Datake ciki domin an ce ta kara rasa wannan cikin shima..Allah ya kyauta na gaba..! Danmallam kansa na kasa yace"Mallam ni bansan komai ba tadai Kirani Sau biyu shekaran jiya ban Dauki kiranta ba..! Mallam ya gyada kai kafin yace"Kaje kayi Tunani Umaru..Duk abunda ka yanke sai ka sanar dani..Ammh ina so ka Sani ka Bude zuciyarka Dakyau ka gani ko zaka bama Sakina Dama har ga Allah ina Tsausayinta domin Sharrin Marliya ne ya koma kanta Barin Ciki ga mace abun jin Zafi ne..Sannan abubuwa Dadama ba Laifinta bane..Kayi tunani kagani ko zaka iya yafe mata..Ban takura maka ba..Shawara ce Tsakanina Dakai..! Danmallam kansa na kasa yace"Nagode Mallam Insha Allahu zan karbi mganarka..! Daganan ya sakamai albarka sukayi sallama ya fito,Shashen Hajiya ya Shiga suka gaisa da yakaka da Hajiya nan yaga ma ya"yan Goggo Yagana sun zo wato yan"uwan Anty Hadiza sun kawo mata kayanta dake chsn da wasu Dake Dake daga mahaifiyarta Dazu da rana suka iso shiyasa bai Dade ba suna gaisawa yayi musu sallama ya fito a haraban gidan suka Hadu da Aba suka gaisa sun dan Taba Hira sama sama kafin ya shige motarsa ya bar gidan shi kuma Aba Falon mallam ya shiga. Koda ya koma Amina ta cika kiris take jira tayi kuka,Allah ya tsaresa da Jidalinta shiyasa ya kasa gayamata Zai koma wajen Sarood har washegari Suka je asibiti da Duka Fayel dinta na Aaibitin datayi awo a Abuja wajen Dr.Ghali suka je inda ya Taba kaita Farko al"amarin. Dr.Ghali nata mamakin wannan al"amarin Sha"awa suka basa har ya kasa Dauke ido Daga kansu ganin yadda Amina ke shagwaba Umar na Biye mata ya Dubata yace ba matsala Sai dai Jininta yayi Low sosai taci kayan ganye,Daga asibitin Da suka Dawo suka sake fita da kafa suka Zagayen anguwan saboda kafaduwan Amina su Saki suna Dawowa ba Dadewa sai ga Idi ya kawo Yakaka Murnan sai ya Dauke Hankalin Amina har ya sake wanka ya fita bata Damu ba. Koda yaje abakin Hajiya Yaji abunda ya Faru da Maamanmu da Labarin yan"uwanta yau sun zo sun Dauketa tana Fadamai irin yadda Duniya ta juyama Mamanmu abaya har ga Allah bai wani Tsausaya mata ba,Aransa ma yasan Kadan ta fara gani Da yammah ya Dauki Sarood suka koma gidansu batare daya Fadama Amina ba saboda bai son me zai ce mata Amina yadda take da kishi ya Tabbata in ya Biye mata sai ya shiga Wuta. Ganin yanayin Sarood din itama tana Fama da Laulayin jiki yasa ya Zage ya taimaka mata suka gyara Gidan suka share ko"ina Girki kuma yace kada tayi ta kwanta ta Huta zai taho mata Dashi Daganan Gidan mallam ya koma sukayi sallar Isha"i sannan yayi musu sallama ya nufi gidan Amina ya Iskesu afalo ta baje suna ta Faman Hira da yakaka Sai Hankalinsa ya kwanta.. Yana shiga Daki ta Biyosa Lokacin yana ta Tunanin abunda zai ce mata tana shigowa tace mai bari tayi Fitsari ya Bita da kallo Tana tafiya Dakyar ta Shige Tiolet sai ya fita Falo ya samu Yakaka ya roketa tayi ma Amina bayani ya kasa Yakaka tace kada ya Damu yayi tafiyarsa zata fadamata Tsorin Jidalin Amina yake yi shiyasa Daganan bai koma Falon ba ya Fice Tana Fitowa taji karan Rufe get dinsa ta kalli Yakaka tana Fadin"Hubby ya Fita ne..? Yakaka tace"Ya koma gidan Yar"uwanki chan zai kwana..! Tafada tana Hade rai tasan Halin Amina gwara a mata Zafi Zafi Amina taji dan Cikinta ya motsa da Sauri tace"bangane ba..? Ina kenan..? Yakaka tace"Mallam yace ya Dauki matarsa su koma gidansu wannan balarabiyar kinga ai tunda suka zo tana gidan mallam ke kuna ba kuma Tare da shi anan ba..? Sai Amina ta koma ta Zauna akasan Cafet ta Rushe da kuka tana Fadin"Shine ko yagayamin..Ya kama Hanya ya tafi wajen wannan banzar matar tasa..? Yakaka ta saki Baki kafin tace"Yau naga Tsiya..ke da zaki godema Allah miji na sonki Yan"uwansa kowa naji Dake..Ita wacce kike kishi akanta uban wa ma ya Damu da ita Labarci nan dai kinsan ba kowa ke jinsa ba..Bata da wani Sakewa kamar mujiya ki godema Allah bawan Allah nan na tafe rawan jiki akan ki ke bakya gani kina wani shanshanci ke kika sani..! Yakaka ta karishe da juya mata baya tana cire naman Daya makale mata a Hakori da tsinke domin Amina ta bata na zamani tace ta rabata tayi da wanda ta sani Amina mganar Yakaka bai sa ta Daina kuka ba Domin wani Kishi ne ya Rufe mata ido har wani Duhu Duhu take gani sai da ta gaji da kanta ta Daina gani kuma Yakakar tayi mata banza ta cigaba da Harkokinta yasa ta tashi da Turtsetesn Cikinta ta koma Dakinta ta kwanta tana Sauke Numfashi Yakaka ta Bita da kallo kamar tayi Dariya Har Washegari a kumbure tatashi Yakaka kala batace mata ba bayan gaisuwa Tana da garin kuni da Hajiya ta saka aka Dakata mata Yakaka ta Dama shi Sannan tayi musu Fanke bata jira Amina ba Data gama ta Dibar mata tana Tura Baki tace ta koshi Yakaka ta Kalleta kafin tatabe baki Tana Fadin"Ke kika sani..! Daga haka ta koma Falo ta sha kununta ta ci fankenta ta koma ta kwanta chan wajen sha daya na Safe Danmallam ya shigo gidan anan Falo yaga Yakaka ya Durkusa ya gaisheta ta amsa Cikin Fara"a. Kansa na kasa yace"Yakaka ina Mutuniyar taki na ganki ke kadai..? Yakaka ta tabe baki tana Fadin"Waya sanin mata..?tun jiya da ka tafi na Fada mata ka tafi wajen balarabiyar nan take kuka sai da taga na mata banza ta Rarrafa ta koma Daki yau fa Da Fushin tatashi ko abun karin da nayi bata ci ba..Dakyar fa ta iya gaisheni Danmallam..! Umar yayi mirmishi Daman yasan za"a rina Kansa ya sosa kafin yace"Bari na lallasota zamu zo Biko Yakaka..! Yafada yana mikewa Yakaka ta mele Baki kafin tace"ai kada kuzo kana tashi Tafiya kafata kafarka sai ta Zauna ita kadai.! Shidai yana yar Dariya ya shiga Bedroom din Amina ya isketa zaune da waya a kunnenta suna mgana da Hanne sai da ya zauna kusa da ita ya Fahimci da Hanne take mgana Saboda ganinsa yasa taja Hiran taki karewa har tana cewa ta bata Aminu in yana kusa su gaisa yana kusa kuwa Hanne ta basa karo na Farko suka gaisa da Amina Danmallan yaji bazai iya ba suna cikin gaisawar ya karbe wayar ya Kasheta ta Kuramai ido Cikin Kishi kafin tace"Miye kuma na kashe min waya..? Hararanta yayi kafin yace"Bansani ba..Baki ganni na shigo bane kike waya da wani kato..? Amina zan saba miki fa..! Shima ya mata jan ido daman jira take kawai sai ta saka kuka ta mike ta Fara jijjiga Jikinta tana Fadin"Dama kamin Fada mana..Kaje ka kwana da ita kazo kana min ihu akai..Tunda kamin Ciki ban da wani amfani awajenka..! Kuka har da majina Baki ya Saki yana kallonta Jidalin Amina yanzu shi kawai ke Diban fire akansa ganin abun nata nayi gaba gaba yasa ya Mike ya rumgumota yana Fadin"Wayace miki baki da amfani a wajena..? Amina har da wage baki wajen kuka ta kasa mgana kawai sai yayi mganinta ya Hade bakinsu waje Daya Dole ta natsu acikin kirjinsa Sai da ya Dauki Lokaci duk ya gama Shanye Hawayenta da majina sannan ya Dago Fuskarta yana Fadin"Ke ce abu mafi Daraja da kima awajena..Ina sonki AMINA..INA SONKI AMINENE..! Ido ta Bude tana kallonsa ranta yayi Fari,Idonta ta ware mai kafin tace"La.Har da Aminene..? Hancinta Yaja yana fadin"Sosai ma..Duk da Jidalin Datake min hakanan nake son kayana..! Rumgumesa tayi Da Sauri tana Dariya tace"Ni ba ruwana..! Yana jinta bai ce komai ba ya shiga wata Jahar kuma Duk da Nauyin Cikinta batamai gaddama ba Har sai da suka samu natsuwa sannan ta fara mai kukan bayanta ya kage shi kuma yana lallashinta haka ta kwanta yana ta Faman Matsa mata baayan da Kafafun nata bawan Allah. Ita dai Yakaka tunda taji su shuru ta Shige Dakin Data sauka ta kwanta afili Ta Furta"Gulmammiya.. ! Ranar ma gidan Sarood ya kwana ko Sallama bai yi ma Amina ba Daga bari yazo taji shuru,Da Safe sai chan rana ya Dawo gidanta Harara kam da Turen Turen baki yashashi yana shiga da ita Daki kaji shuru shiyasa in tana ma Yakaka Jidalinta sai ta kalleta tace"Nama Lura ni kika raina..Meyasa shi baki mai..? Yana zuwa kuka shige Daki sai naji shuru..! Amina sai taji kumya ta rufe ido tana Fadin"Ai ina mai acikin Dakin..! Yakaka ta mata Dakuwa tana Fadin"Raina min wayau..! Amina ta fara Dariya Yakaka na Hararanta kafin tace"Allah ya shiryaki Amina..! Ta amsa mata da Ameen haka suka cigaba da zamansu Lafiya Ranar dayake gidan Sarood ba sa sallaman arziki da Amina in kuma ya Dawo ya Dinga Fama da lallashi kenan ga Sarood din Cikim na bata wahala sai da ya kaita aaibiti komai taci sai amai Ga Jidalin Amina wlh baya kaunar ma ya Bata mata rai Tsoron kukanta yake ji. Amina na cikin Farinciki da kwanciyar Hankali ta kara Kiba ta zama katuwa Danmallam ya siya mata Sabuwar waya samsumg Tana waya da duka yan"uwanta har su ya Zulfa bata yada su ba Tana kiransu susha Hira tun basa Sakin jiki har suka zo suka saki Tunda duka ya"yan yaya basu nuna musu kyama kan abunda Uwarsu ta aikata ba Jadwa ne ta Dauki Zafi itama Daga baya ta Saki arana kuwa ita dasu Hanne sa yi waya fin sau hudu Har sai da Danmallam ya musu Fada yace basu da Hankali ne nan fa ba gida bane..? Su matan aure ne yanzu wani Shirmen dole sai sun barshi Baji sukayi ba aboye suna wayarsu barin ma in baya gidanta sai gashi yau Amina ke bama su Hanne wasu Shawarwarin sannan Fanin girki abunda ta iya ma basu iya ba Shiyasa har yau har gobe bazata manta da Hajiya da ya Aisha ba Duk tayi salla sai ta rokar musu Fatan gamawa da Duniya Lafiya. Haihuwa dai shuru har EDD dinta ya wuce sai dai bata Damu ba Tunda Daman Before ne ko after har asibitin sun koma Dr.Ghali ya tabbatar musu da komai lafiya sai hankalinsu ya kwanta. Bangaran Aba kuma komai Lafiya lau Anty Hadiza na kula dashi ta karbo Jawaad wajen Hajiya ya Dawo wajenta Abun yayi ma Aba Dadi tazo Ranar ta yinin ma Amina da Daddare Aba yazo ya Dauketa Dakyar ya shiga Gidan Amina yasa albarka Amina baki har Kunne saboda Murna Aba yazo Ruwa kadai ya sha ya saka albarka suka tafi Yakaka itama ta Bisu da saka albarka. Bangaran mallam kuwa acikin Satin nan ya samu Lokaci Yaje Tsafe Idi ya Tukasa yayi ma yan"uwan Uwani Gaisuwan rasuwar Batula,Akwai mahaifiyarsu agidan da abokan zamanta Biyu bayan yayi musu gaisuwa nan ake fadamai Uwani na kwance ba Lafiya an je asibiti an yi Duk Gwaje gwaje an kasa gano abunda ke Damunta sai tace kirjinta da zuciyarta ke ciwo an ta neman Lambarsa afadamai ba'a samu ba..! Sanda ya shiga inda Uwani take sai da ya kusa mata kuka tana kwance ta Zabge ta rame ta lalace Ba wannan kibar yau gata kwance ba kwalliya ba kayan kawa tana ganinsa ta fara kuka tana Fadin ya yafe mata. Mallam ya jinjina kai yana kallonta kafin yace"Na yafe miki uwani..Saura ke da wanda ya Hallicceki..Sannan zan yi mgana da su Nazeem zasu zo su Dubaki..! Daganan ya mike bayan ya ijiye mata Takardan daya rubuta mata Sakinta ya Fice ko bai Fadaa mata ba tasan ko na menene yasa ta Dinga kuka Tari ya Sarketa iyayanta yayi ma sallama da kudi 50k ya basu domin suna cikin yanayi don ma yaran maza na taimakawa. Sai bayan fitarsa mahaifiyar uwani ta shiga Dakin ita ta karanta Sakin da mallam yayi ma Uwani Sai ta saka kuka tana fadin daman tasan za"a rina Domin zaman uwani bana Lafiya bane ba ya"yanta ba Dangin mijinta tasan wani abu ta aikata aranar Duka yan"uwan Uwani suka taru tana kuka tana Nadama ta basu labarin duk abunda ta aikata,Sun ji tsoron Duniya sannan sun yi Tir da ita har ta mahaifiyarta sai da tayi tir da ita tana kuka tana Fadin Batula ta rasu a Hanyar Shirka wannan wani irin tabewa ne sun fito daga babban gida ammh sun watsar da Tarbiyansu Tundaga ranar harta mahaifiyarta ta Daina bi ta kanta tana yashe Cikin Daki sai wanda yaga Allah yaga Annabi ne ma yake lekota yau ina ya"yan nata Datake yin komai Saboda su..? Sun gujeta saboda mugun Halinta sannan ba mallam din ya Saketa ballatana ta hango cikar Burinta gata kwance ba Lafiya tana girban abunda ta Shuka kaiconta tayi kuka kamar ranta zai fita bamai lallashinta Aranar da mallam ya Dawo Daga Tsafe ya Kira Anty Amarya Har Shashensa ya bata takardan Sakinta Ko da bata karanta tasan Dalili ta Fadi gabansa tana kukan ya yafe mata ya kalleta yace"Na yafe miki marliya..Yanzu Tsakaninki da Ubangijij ne..! Daga haka ya shige ya barta nan tana kuka kukan nadama da rashin Madafa. Bata zauna ba Kayanta ta Hada ta Rufe Shashen ta bama su Lami key din tace su kaima Hajiya ta Fice Daga Gidan tana kuka yau ina Burin nata..? Ta biye ma rudin zuciya ta karre a Tutar babu Tana kuka ta isa tasha ta samu Motar Dutse lokacin data isa Gidansu sai da tayi nadama. Yan"uwanta basu karbeta ba haka suka gana mata tir da kaico har da uwar data Haifeta sai da ta juya mata baya ba yadda zasu yi su koreta ne ammh Kashi ya fita Daraja abinci sai dai yan aiki su bata tayi kuka tayi nadama Lokacin da bai da amfani ta Kira wayoyin su Sadiya ba wacce take Sauraranta. Sakina kuma tana Gidan A"i ita ta Dauketa tana kula da ita bayan an sallamosu Daga asibiti Dayake nan kusa take aure Ranar da Anty Amarya Taje sai da ta raina kanta Har Marin ta sai da kanwarta A"i tayi abaya yadda suke jin mganarta Saboda auran Babban mutum kamar mallam..agaban idonta Sakina tana kuka tace itace ta cuceta ta rabata da auranta da kuma Halin Datake Ciki gashi sanadiyar barin cikin data dinga yi mahaifarta ta samu rauni Har ta fara Dagargajewa yanzu haka an cire mata mahaifa ita da Haihuwa har Abada ta Tsaneta bata son ganinta Anty Amarya na kuka tana rokonsu gafara suka Tarkatota waje bayan A"i ta saka megadi ya sakar mata karnuka su suka kadata har waje nan bakin get din gidan ta durkushe tana wani irin kuka mai Cin rai kukan Nadama da nasani. ******* EDD din Amina har ya tsallake da wajen Sati uku Bata haihu ba Sannan Cikinta ya fita wata na Tara har ya shiga goma sai kuma hankula suka fara tashi ita kanta Aminar ta kosa ta Haihu Cikin ya mata girma ya koma yana Rinjayanta. Danmallam duk ya Damu ya koma yana matukar jin Tsausayinta Hajiya ta bada Shawaran su koma asibiti haka kuwa akayi da ita suka koma wajen Dr.ghali da Amina shi kanshi yanayin Daya ganta yasa yace zai sanya mata ruwan naguda ya gani. Allah Sarki Duk mai imani sai ya Tsausayama Amina an saka mata Ruwan Naguda ta fara asa asa kamar abun zai yuyu sai kuma shiru sau Biyu ana saka mata sai nagudan ta Fara ta Tsaya anan asibitin ta kwana Tare da Hajiya da Yakaka Danmallam kuma duk hankalinsa a tashe yake washegari asibitin ta cika da su Anty Hadiza da su Aba har da ya Jafar da matansu.. Mallam ma yazo ganin yadda Amina ke kukan azaba tana fadin acire mata Ckkin jikinta zata mutu yasa yace bari ya koma gida ya yi mata addu"a a ruwan Zamzam ya kawo mata tasha tagani shi ya hana asake mata alluran nagudan ganin yadda take wahala kamar zata mutu kuka reras haka Danmallam ke yi saboda ganin Halin da Amina ke ciki hatta Sarood da tazo asibitin sai da ta tsausayama Amina da kuma kanta Tunda itama ai cikin gareta Tafiyar mallam ba Dadewa sai gashi ya aiko Hajiya Nasara da ruwan zam zam din da yayi ma Amina addu"a shi kuma yana gida yana cigaba da taya Amina addu"an Allah ya sauketa Lafiya Hankula duk sun tashi. Kamar an kara ma Amina azaba tana sha ruwan zam zam din nan abubuwa suka taso mata haikan tana kamkame jikin Hajiya hannayenta cikin na Danmallam tana kuka tana Fadin su yafe mata mutuwa zatayi Aba duk Dauriyansa bayan rasuwar yaya da abunda Balaraba tayi mishi wannan ne karo na uku Daya ji ya raunana Waje ya fita chan haraban asibitin yana kuka tare da Fatan Allah ya Sauke Amina lafiya.. Anty Hadiza ma har da kwallarta Kowa fa jiki yayi sanyi ganin Haka yasa Danmallam yace ma Dr.Ghali a yi ma Amina aiki a ciro mata abunda ke Cikinta. Nan da nan kuwa aka fara shirin yima Amina C.S,Bayan Danmallam ya saka Hannu kudin aikin ma su jafar sukayi ta Zirgan Zirgan Biya Hajiya ta amince da hakan saboda Amina ta Wahala har mallam data kirasa ta Fadamai ya amince yace indai za"a samu mafita ayi din yafi Alheri. Koda aka shiga da ita Dakin Tiyata Amina ta fita Daga Hayyacinta Danmallan ko addu"a ya kasa yi ya Fara Hango kansa Rayuwarsa ta lalace in ya rasa Amina sai da Yakaka ta yi bashi baki sannan ya iya fita hataban asibitin ko Sallar da yaso yayi ya kasa Cikin Mota ya koma ya Dafe kansa kawai yana kiran sunan Allah hatta Hajiya ta kasa mgana Saboda itama ta Shiga Dimuwa..! Allah mai hikima ana shiga da Amina Dakin Tiyata Nagudan gaske tataso mata Sai dai su Hajiya suka ga Nurses suna kai da kawo da gudu suka zo suka karbi akwatin kayan Haihuwa suka shiga dashi Dr.ghali yayi matukar mamakin Lokacin Daya Duba Cm din Amina yaga Saura 2cm sannan kan yaro na kokarin fitowa Kananun shekarunta yake kallo yana Tunanin Haihuwa da kanta zai ja mata Tsinkau  Tsinkau ko yoyon Fitsari sai gashi Cikin Hikimarsa Amina ta fara kokarin Haihuwa da kanta Nishi kawai take yi da kakari da Taimakon Dr Ghali da Nurses dinsa Amina ta Sintalo manyan ya"yanta guda Biyu abun mamaki Kusan atare Jariran guda biyu suka Sulmiyo Daya na Fitowa Dayan ya Biyosa sai kuma Amina ta koma ta yi yaraf kamar bata da rai Dr.Ghali ya taimaka mata Uwar ta fito Nurses suka fara aikin gyara wajen Wasu kuma suna faman goge yaran bayan sun yanke musu Cibi Amina kuma Dr.Ghali ya samu natsuwa ganin tana Da rai allurai ya Hada yayi mata sannan ya fara kokarin gyara mata jikinta bai cika Tsayawa Irin haka ba da zarar mace ta Haihu ya gama mata abunda ya dace yake barin ma Nurse sauran ammh Amina ta Dabamce Matar Bazanga ce..! Yaran duka maza ne sannan sun fito a wahale yasa basu yi kuka ba sai da Nurses din suka Daga su sama suka Daki bayansu sannan atare suka Callara kuka Gabadayansu sai suka washe Baki Dr.ghali na mirmishin jin Dadi yace"Alhamdulillah..! Su Hajiya kuwa kamar amafarki sukaji kukan jarirai daga Dakin Tiyata sai suka fara Tunanin aikin ko yayi Sauri yanzu fa aka shiga da ita Hajiya tayi Hamdala acikin ranta suna nan dai Zaune suna jiran tssmmani. Rabin Sa"a kafin Nurses guda Biyo su fito da Jarirai guda Biyu Cikin kayan Sanyi Farare masu kyau Hajiya ta kasa gasgaata abunda ta gani Amina ta Haifi yara Biyu duka maza..? Allah mai iko Annabi mai Dubun Daraja. Hajiya Nasara ta karbi ya"yan tana Hamdala daga ita sai su Nasir da Aba da Anty Hadiza da matan su ya Nasir Baki yaki Rufuwa Hajiya kuma Hannu ta Daga sama tace"Alhamdulilah..Godiyata tabbata ga Allah Shugaban Duniya..! Sai hawaye tana sharewa sai ga Dr Ghali ya Fito Hajiya na ganinsa ta karisa tana Fadin"Sannu likita mungode fa..Ina Aminar ina fata Lafiya take..? Dr Ghali yace"Lafiyanta kalau mama..Na mata alluran hutu ne sannan ga karin albishir ma Amina da kanta ta Haihu bamu riga ma mun yi aikin ba..! Hajiya bakinta Har kunne take fadin"Alhamdulillah..Allah mun gode maka..Ashe yan Biyu ne acikin Amina bamu taba sani ba..? Nidai nace cikin nan yayima Yarinyar nan girma ashe ashe..! Dr Ghali yace"Hakan na faruwa Mama..ammh ni sanda suka zo na mata Scan na gani.Sai dai ban Fada musu bane ina Tunanin sun sani..! Hajiya tace"To mudai bamu sani ba.kila dai Aishan ta sani Dayake chan wajenta ta zauna har cikin girma...! Mungode Likita..! Ya amsa mata kafin ya karisa su gaisa da Aba da ya Jafar sai.Nasir sannan ya koma Office dinsa ba Dadewa aka Gunguro Amina kamar gawa sai numfashi zuwa Dakin da zata Huta. Hajiya Bakinta har kunne ta kira mallam tace mai tayi mazaje Shima Hamdalan yake yi Danmallam kusam shine na karshen sani Sai da Jafar ya Kirasa a waya ya Dawo Cikin asibitin. Ya kasa yarda Amina ta Haifamai yan Biyu Duka maza bai karbi Yaran ba sai da ya yi sudujul shukur Yayi ma Allah Godiya sannan ya Dago ya karbesu hannun Aba yaran kamar yayi kaki Sai dai sun Dauko Fuskar Amina kadan da idanuwanta sannan Kuma Indentical ne bamai iya bambamcesu Kadan ya gansu ya mikama Sarood su da Bakinta yaki Rufuwa Ya shiga Dakin da aka kai Amina ya ganta Hankalinsa ya kwanta ganin tana Numfashi haka ya Rumgumeta yana kwarara mata addu"a tasha albarka kamar me ya Tsausaya mata domin Hajiya ta fadamai da kanta ta Haihu bai Taba zaton Amina zata iya Haifan Daya da kanta bama biyu ba.sai gashi Allah yayi ikonsa..! Danmallam Aliyu ne mutum na Farko Daya fara Kira ya fadamai karuwar Daya samu Aliyu ya tayasa murna Bakinsa har kunne yana Fara"Barkallahu Fika Ya shehi..Amina kwaila yanzu ta zama giwar mata..! Umar yace"Kai fa banza ne meye kuma na Tuna baya..? Aliyu nayi ta mai Dariya shima bakinsa har kunne yace"Hakane fa..To Allah ya raya Allah yayi musu albarka Sai mun zo barka..! Da haka suka yanke kiran Kowa cikin Farinciki Aliya shi ya koma gida ya Fadama Aliya sai ta kara jin Imani ya Shigeta ta kuma kara yarda Duk abunda yaso Faruwarsa sai ya Faru..! Sakina take tsausayi domin suna waya tasan Halin Data ke ciki har Cire mata Mahaifan da akayi yau wagari ya waya..? Duk wanda ya bari Duniya ta Rudesa ya gama yawo haka zai zo ya kare a Duniyan ba riba Lahiran ma haka. Kafin yammah Labarin Haihuwan Amina ta Zagaye Dangi kaf yan"uwanta ba wanda bai ji wannan Haihuwar ba ya Aisha ce duk ta Kira ta Fada musu Hanne da Hamida sai Tsallen murna suna Tunanin Waya ga Amina da ya'ya har Biyu..? Ya Aisha har ya Sadiya ta kira ta Shaida mawa ita kuma ta kira Sa"adatu Fatan Allah ya raya sukayi Saboda Duniya ta koya musu hankali Sannan dukkansu sukace bazasu gayama Sakina ba kada Hankalinta ya tashi susan Halin Datake ciki..! Har Jordan Labarin Haihuwan Amina yakai da Gusai suna ji da gayyar aka Dinga Fada a tsakar gida har Mamanmu daje wani karamim Daki tana jinya taji,Domin tana jin mgana sai dai bata iya mayarwa ne sannan kuma bata gani yanzu idon ya koma sai Lalube. Taji Haihuwan Amina sai kukan zucci Lalle ta yarda Zakaran da Allah ya Nufa da chara..! Sakina ma ta ji Domin Aliya ta kirata ta Fada mata Kuka take yi reras dataji Labari shikenan Burinta bazai taba Cika ba har Abada bazata ga k'wanta aduniya ba..Tayi kuka ranar kamar ranta zai fita ita kanta Anty A"i ta kasa lallashinta Domin tana tausayama Sakina  gashi har yanzu basu kara ji Daga Bakin Danmallam ba ballatana makomar auran nasu sannan Sakina tace bazata kirasa ba Domin bata san da wani ido xata kallesa ba Anty A"in ne ma ta kirashi da wayar sakinar bai Dauka ba..! Haka Allah ke tsara lamarinsa Sau Tari wasu Burukan namu mattatu ne har mu koma ga Allah bazasu taba Cika ba..! Amina haka ta farka ta ga Kyautar da Allah yayi mata tayi kuka ta share Hawayenta ta Rumgume ya"yanta wani son su na kara kamata Ya Danmallam Yahadasu duka ya Rumgume lokaci Daya yana Fadin"Allah ya albarki Rayuwarki Noor Dake da zuru"arki gabadaya..! Amina na sharan Hawaye a kafadan Mijinta Uban ya"yanta UMAR YUNUS ABDULRAHAMAN BAZANGA murya shake ta Furta"Ameen Ameen Hubby..! *Janafty**TFZB2030* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Sai da Amina ta kwana Hudu a asibiti sannan aka sallameta ta dawo gida,saboda tasha wahala sosai har ka ruwa sai da tayi akayi mata Dinki Yakaka ke kwana da ita a asibitin Hajiya sai tayi mata kara Sai dai tazo da Safe ita da Anty Hadiza Da rana kuma Hajiya nasara ke zuwa sai yamma suke tafiya tare da yan Dubiya matan su ya Jafaru har Dangin Yaya sun zo barka goggo Jumai ta koma Hadeja sai ya"yanta ne suka zo sukayi ma Amina barka da sauka. Suna komawa gida aranar Yakaka ta saka aka nemo mata Murhun karfe da Itace domin tace jego mai kyau zatayi ma Amina bata son gantali wai wanka jego a gas ko a Kittle Hajiya kuma ta bata goyon baya aka hado mata da Tukunya gwarwa babba ta saka ruwan zafi ta saka aka nemo mata ganyayyakin wanka dasu ta Dafa ma Amina ta gasheta tas Amina ta zata zata yi kuka sai kuma batayi ba sai ma Dadin Ruwan dataji saboda jikinta sai Tauna suke kasusuwanta duk sun Sage Lalle ta kara jinjina ma uwa ba abun wasa bane Ta kara ganin Daraja da kimar yaya koda bata araye,Sannan tayi kuka,kukan yadda Rayuwarta tazo a wani yanayin da mahaifiyarta bata taba jin dadinta ba har ta koma ga Allah. Hajiya ita ta wanke yaran nan tas Hajiya Nasara ta shiryasu Yakaka na ta musu tsiyan sun ga Sabbin mazaje sun Rude ana ta Dariya ita kuma Anty Hadiza tayi girki Sarood da su Anty Fadila nata Faman gyara gyaran gida kowa ka gani Bakinsa har kunne Sarood har Cikinta ya fara fitowa Amina duk yadda taso ta share Sarood da jin haushinta ta sakar mata ganin Tunda ta Haihu a asibiti take wuni yau ma suka dawo gida da ita sai kama ayyuka take tana da Saukin kai da Dadin mu"amala ba ruwanta. Aliyu da matarsa sun zo duba Amina tun tana asibiti Amina ta ki sakar ma Aliya fuska duk ko yadda take ta wani Shige mata aran Amina tace ai kuma kin makara gwara ki koma inda kikafi auki ta dai karbeta sama sama ammh bata yarda ta saki jikinta da ita ba. Yan"uwanta kaf ba wanda bai kirata a waya ya gaisheta ba tare da barka da arziki Har Ya Jadwa dake Jordan ita da Goggo Husai sun kirata sannan Hotunan yaran tuni duk yakai ko"ina ya Nasir da ya Jafar suka Dauka a wayoyinsu suna turama mutane mamaki dai ya kare tunda ga Amina da ya"ya har Biyu a lokaci Daya. Su Hanne kuwa kullum sai sunyi mgana da Amina ji suke kamar su yi tsuntsuwa su gansu suna ta fatan Allah yasa mallam ya barsu su zo suna. Tunda akayi Haihuwa Danmallam gidansa yake kwana shi da Sarood duk da nan take yini sai dare suke komawa chan gidan tayi ta mai Hiran yaran tana santinsu aransa yana Fatan itama Allah ya Sauketa Lafiya. Washegarin ranar da suka Dawo Daga asibiti Dadaddare sai ga Mallam yazo shi da Danmallam da Aba aka kawo musu yaran suka kara ganinsu Mallan ya kalli Danmallam yana Fadin"Ka musu Huduba ne..? Kai ya girgiza kafin yace"A"a mallam..Daman kai nake jira..kayi musu Huduba da sunan YUNUS DA SA"IDU..! Mallam da Aba bakinsu yaki rufuwa saboda murna Hajiya na wajen Mallam ya kalleta yana Fadin"Hajiya kina ji dai Mazajen naku ma sunan mu sukace..To basu dai fimu ba. ! Dariya aka sanya cike da Farinciki nan take mallam yayi musu huduba da sunan da Babansu yace aka samusu sannan ya diga musu ruwan zamzam da Dabino abaki kafin ya Hadasu duka ya Dafa kawunansu yana musu addu"an kariya.. Hajiya tace"Ina Rokon Allah yasa ku biyo masu sunanyenku..Domin kun Dace da Nagartattun sunaye..! Aka amsa mata da Ameen basu wani jima ba suka tafi Amina ita kanta Bakinta yaki Rufuwa da wannan karan da Danmallam yayi mata eh mana ai ita yayi ma kara A duk duniya mallam da Aba sune ita Daman abun na ranta sai gashi ya Rigata wani kaunar mijinta da Soyayyarsa na kara shiganta Tunda ta auresa alheransa ke Lullube rayuwarta Allah ya barsu tare. Su ya Aisha suna so suzo suna suka kira mallan suka mai mgana yace ai ya Danmallam baya taron suna Hajiya ta saka Baki tace na Dangi ne sannan kuma ai na Farko ne, gaba ba lalle su zo ba To sai ya amince kuma Daman yana son ganin yaran saboda akwai Tunasarwa Dayake Bukatar yi musu kan wani abu da suka manta. Jin Dadi da sukaji Labarin mallam ya bada Izinin su taho ana Gobe suna ya Zulaihat da ya Ikram suka Diro sai Hamida da ya Zulfa Suka kamkame Amina suna Murna sai da Yakaka ta mata mgana akwai Dinki ajikinta Don na ta samu Jego mai kyau k'ashinta ya fara karfi shiyasa ta sami kwarin jiki Sannan Yakaka Jego take mata na Mutanen da sannan suna kauri abinci da Namoni da kifaye kawai takeci kafin me wannan Kibar na Amina kadan Tatafi ta riga tabi jikinta sai tafi kyau ma ahaka yar Duma Duma da ita..hamida ta Dauki yaran sai hawaye tana Tuna irin rayuwarsu ta baya Allah mai kyauta da kari Amina ce ta zama uwa haka..? Kaunar yaran ya mamayeta ta kamkamesu sai da ya Zulaihat ta mata Tsiyan ba ita kadai bace uwarsu sannan ta amince suka Dauka da yammah sai ga ya Aisha ta Diro ita da ya Abida duk sai sukayi ma gidan mallam Tawaye gidan Amina suke yada Zango. Sai Hira kawai ke tashi Cikin Farinciki Girkin suna agidan Baba mallam za"ayi su Anty Fadila da su Shamsiya sai matar ya Nazir itama tazo ita da Ya Jalela tare suka zo sune yan gayu zasu yi girki ya Zahra ma ita da Ya Abida sukazo Tunda garinsu Daya,Har ya Nazifa tazo ita da ya Fatima ya Akila ce bata samu zuwa ba sai ya Jadwa. Hanne kuma sunyi waya sai da Safe zata zo. Gida ya cika da Dangi an manta komai ana ta Hira da annushuwa Anty Hadiza tayi ma Amina kitso da kunshi Yan gusai da sukazo sai tsiya suke mata suna Fadin da wayau tana gyara yarta Harda Zafira akazo wacce za"ayi Bikinta nan da wata Uku. Adaran Sai ga Akilu da zubairu sun zo ma Amina barka aranar suka dawo Daga Zaria sun je Rigistration sun samu Admmision,Sai da suka Dauki yaran suka kallesu suka juya suna kallon Amina Dake zaune tana shan Tea Akilu ya kara kallonta kafin yace"Tab..Su Aminene an zama uwa..Sai arage Rashin kunya.. Sai kunga hararan da Amina ta Sakar musu sai kun Dara su kansu sai da sukayi Dariya Fari tayi musu kafin ta Hura Hanci tana fadin"Banson Wulakanci..Kun dai san yanzu ni ba Sa"arku bace ko..? Ya"yana Biyu..! Dariya suka saka mata itama sai da ta Dara su kallonta suke yi suna mamakinta wai Amina ce ta Haihuwa lalle Haihuwa ta Allah ce. Sun Dade kafin su tafi harda kudi suka bama yaran nasu Amina ta karba Tana fadin"Eyye..Kawu Akilu da Kawu Zubairu..! Yanayin yadda tayi mganar ne yasa sukayi Dariya har Hamida Dake wajen tace"Mai hali dai baya fasawa. ! Akilu yace"Wlh kuwa hamida..! Daganan suka musu sallama da Fatan Allah ya raya suka fita Daga Dakin sun dan bata Lokaci afalo tare da su ya Aisha kafin su tafi su suka zo da Umaima Hajiya tace su kawota ta zauna cikin Yan"uwanta zatafi sakewa..! Kusan kwana sukayi basu barci ba sai da Yakaka ta kora Amina taje ta kwanta yaran kuma sun fara kuka iyayansu suka Daukesu duk da Amina ruwan nononta ya kawo Dr Ghali ya Rubuta madaran da aka siya ana kara musu dashi suna da tsotson tsiya in ji Amina don ma Yakaka na mata jan Ido da sai ta horar dasu da yunwa Amina ce fa ai sai Allah kadai ne zai iya mata..! Washegari da Hidimar suna aka tashi su Mamata gidan Aba suka koma suka kwana da Safe suka shiga gidan mallam suna taimakawa da aiki,an yanka Raguna Hudu kowannen Biyu sannan an yanka kaji da Zabbin na Gidan gonar Baba mallan chan gidan su ya Zulaihat suke ta gyaransu da kuma aikin abinci duk ba su yi Taro ba isu isu ne kawai sai mutanen Gusai. Da Safen sai ga Aliya matar Aliyu tazo ita da yaranta zuwa karfe goma sai Mutanen yola Hanne da mijinta Aminu har cikin gida ya shigo ya zauna afalo suka gaisa da su ya Abida bayanan Amina ta sakayo Lullubi ta fito suka gaisa Hanne ta Dauko mai yaran ya Dauke su yayi musu addu"an aransa yana ganin mganar Nenne wato Aurensa da Hanne ne Sanadiyar Haduwarsa da Amina ita kuma auranta da Danmallam shine silar Haduwarsu da Amina Allah kenan ya Musu addu"a ya ijiye musu kudi yayi musu sallama kano zai wuce sai in zai koma zai Biyo ya Dauki Hanne su koma gida. Hanne ta rumgume Amina tana murnan ganinta ta Rumgume yaran ta kalli Amina kafin tace"Amina wai da gaske yaran nan naki ne..?. Amina ta Harareta kafin tace"Ba nawa bane..na mami Hanne ne da Mami Hamida..! Tafada tana Dariya ita Hanne gani take kamar wasa ta Yafito Hamida tana Fadin"Hamida kinga ikon Allah ko..? Amina an shiga kwaryan manya..! An zama uwa..! Amina na dariya batace musu komai ba Hamida tace"Sai a rage jidali Tunda an zama uwa ko Aminene..? Amina tace"To Allah yasa ya ragun kunsan ba yin kaina bane..! Suka Hada Baki wajen fadin"To yin waye..? Sai da tayi Fari sannan tace"Na Allah ne..! Dariya Hanne tayi ta Daka mata Duka abaya Amina ta sosa wajen tana Fadin"Lala sai na fadama Hubby na..! Dariya suka kwashe mata suna Fadin su Hubby an jiki..! Tun Safe Amina tayi wanka ita da yaran suka fara shiga suna fita suna fita gadonta kuma cike da kayan suna yan"uwanta sun mata kara ba wacce tazo Hannun Rabbana Aba ma da Turamansa da kayan yara Mallam ma kaya sai wanda ya gani Amina ba abunda zatace ma yan"uwanta da iyayanta sai godiya domin sun mata komai aduniya wajen ganin sun ingata rayuwarta. Ya Danmallam bai zo gidan ba Ranar suna Saboda mutane sun dai yi waya da Safe da wayar Sarood daman ai nan ta kwana tare dasu ya Abida,wajen azahar sai ga su ya Aisha da kololin abinci kala kala lemuka daman da ruwa tun jiya aka Sauke su nan da nan aka fara Cin abinci Daman tuni kowa yayi wanka ya Shirya kansa Yakaka da Safe gidan Baba mallam ta koma tace bazata iya ba ta bar ma su Abida gidan su shakata.. Abun da ya bama Amina mamaki Sai ga Sa"adatu da ya Sadiya har da ya Jidda sun zo mata suna abun Sai da ya bata mamaki ammh bata nuna ba ta Saki Fuska suma sauran yan"uwa suka karbesu hannu Biyu da suna Dari Dari Daga baya suka shige Cikin yan"uwana ana ta Hiran masu Ciki su ya Abida da su ya Zeenatu har ya Zulaihat duk ciki garesu su ya Ikram kam yama tsufa tana ta fama dashi Chan da yammah sai ga su mariya da Samira yan makarantar Haddarsu Amina baki ta rike tana kallonsu tace"Su Mariya ne da su Samira. ! Suna dariya Mariya tace"Wlh mune su Amina..! Sai dukkansu sukayi Dariya Hamida ta Fadama mariya Dayake suna Chart ai sukace sai sunzo sun ga Amina da abunda ta haifa aiko sun sha kallo Amina ta zama zara aciikin wata Duk inda tabi ita ake kallo ta zama abun Sha"awa kuma duka taron Saboda itane nan suka Hade dasu Hamida suna ta Hiran baya da irin abubuwan da suka faru Lokacin suna makaranta Har Sa"adatu ta shige Cikinsu Dayake abun na malamai ne ba Kida ba wani Hayaniya ko Hotuna ta wayoyinsu suka taru yan"uwa suna ta Daukan kansu ya Danmallam kuma yayi walima achan masallacin Baba mallan anyi wa"azi sannan an ci an sha an raka yara da addu"a da Fatan Allah ya rayasu. Aliyu na Tare dashi a matsayinsa na Amini sai su ya jafar da suka Dawo Daga wajen aiki da yammancin ranar tunda matan suna chan gidan Amina sai suka Sauke gajiyarsu Shashen Mallam nan sukaci abinci suka cigaba da Hira. Aliya kuwa sai haba haba take da Amina abu kadan tace Amina kaza amina na yankwanata sai da Hanne ta mata mgana Amina ta mata wani kallo kafin tace"Ke ni fa na tsani Cusa kai..Ni ba kawartace ta kama kanta..! Hanne tace"Kodai yaya ne ki mata uzuru ai don ke tazo.! Amina ta bangaje Hanne tana Fadin"Naji..! Hanne ta Bita da kallo Baki Bude akwai Hallayan Amina da Har Abada bazata iya sauyasu ba ance Hali ai Zanen Dutse ne. Su mamaki ma ta basu da suka ga suna mgana da Sarood Cikin Harshen Labarci wayar Sarood din DanMallam ya Kira yace ta kaima Amina saboda ya yi ta Kiran wayanta bata Dauka ba Shiyasa ta kawo ma Amina ta karba sukayi mganar yace ina ta Jefar da wayarta tace bata sani ba suna cikin kaya mganar komawarsu asibiti yayi bayan yace mata sun yi mgana da Hajiya in sukaje kawai za"ayi ma yaran kaciya ne su Huta Amina tace ba Matsala Duk yadda suka yanke har ya bata Aliyu ya kara mata barka Sannan sukayi sallama ta fita Falo ta Nemo Sarood ta bata wayarta.. Hamida ce sai da tayi mgana ta kalli Amina sanda ta shigo Tana Fadin"Lalle Matar ya Danmallan kece kika kware da Labarci haka sai yarata kuke ke da yar Balarabiyar kishiyarki..! Amina ta harareta Saboda su Sa"adatu na wajen yasa batayi mgana ba ammh ina ita ina wani Sakin jiki da Sarood ai kishiya sunanta Kishiya duk da tana da Kirki ammh dai kowa yayi ta kansa abunda ya faru agidansu ai Ishara ne ga masu sakarma Kishiya Ragamar gidansa da ya"yansu duk da ba Duka aka taru aka zama Daya ba akwai nagari acikin na banzan ammh Dai na banzan su sukafi yawa. Sai dare ya Danmallam suka zo da Aliyu da su ya Jafar suka Dauki yaran su ya Aisha na fadin ayi ma yaran alkunya Danmallam yace kul..Da Mallam da Aba za"a dinga kiran su sune alkunyansu Daganan sai suka ja bakinsu sukayi Shuru ranar dai gidan Amina ya Cika da Baki duk nan suka kwana Ya Danmallan kuma da Abokinsa Dakin su Nazeem suka kwana.. Washegari wasu har sun yi shirin komawa irin su ya Zulaihat Sai ga Sakon mallam zai yi mgana dasu Dukkansu anjuma sai tafiya ta fasu kowacce ta Share waje ta zauna aka cigaba Da Hira Saboda an Haadu ba"a son Rabuwa da juna...gidan Amina aka kawo kan ragunan da aka gyara suka Dafa suka ci sannan Naman kuma achan su Mamata suka soya sai da aka musu nasu tunda dagachan aka Rabasa yadda kowa zai shaida harta Aba da Baba mallam an yi musu kullin su na Nama Anty Hadiza kuma ita tayi Yajin jego,zuwa yammah duk sun gama gyara ma Amina gidanta Yakaka ta Dawo ita tayi ma ma Amina wankan yammah ko kafin mangariba duk sun watse sun koma gidan Baba Mallam har su Hanne Amina da Farko Har da sa Rigiman ita ma sai taje Yakaka tace da Danyen Jegon ne zata fara yawo Dole ta Hakura ta koma tana ta Faman gunguni. Achan gidan ya Danmallam kuwa Ana Idar da Sallar Isha"i mallam ya Hada Taron daya ce za"ayi Sannan har da su ya Nazeem da Uzairu sun iso aranar dukkansu mallam ya kira su yace yana som ganinsu gabadayansu suna Falon mallam illah banda Amina da ya Akila da bata samu zuwa ba sai ya Jadwa. Ammh harda su ya Danmallan suna wajen,Aliyu dai sun tafi dazu da yammh shi da Aliya,Sai su ya Jafar da ya Nasir ya Nazir shima bashi wajen Tunda bai samu zuwa ba sai Aba sai Jawaad har Anty Hadiza da su mamata mallam yace su shigo Tunda Tunatarwa ne ya kamata suna wajen.. Nasir ne ya Bude taron da addu"an sannan Mallam ya fara jawabinsa da Farko Yayi musu wa"azin riko da Zumuncu da yadda zasu Hada kansu waje Daya su zama Dangi Daya kamar yadda yake fata sannan ya gangaro kan wa"azi kan shirka da azaban da Allah yayi tanadinsa domin masu Hadashi da wasu,Tunda ya fara mgana suka Fahimci inda ya Dosa sai jikin kowa yayi sanyi bai fito ya Fada musu Sakin daya shiga Tsakaninsa da Uwani da Marliya ba ballatana ta Bangaran Aba yadai gyara Zama ne ya Fara karanta musu muhimmancin Uwa ga ya"yanta sannan da irin yadda Annabi ya Fadi Darajan uwa. Mallam ya kallesu Daya bayan Daya kafin ya Cigaba da Fadin"Ita uwa tana Daraja da kima..Annabi ya ambaci abi uwa sau uku kafin yace abi uba kunga ko ta haka kadai ya isa kusan Tasirin uwa..Sannan duk lalacewar Uwa uwace..Domin ta Dauki Ciki na Tsawon Wata Tara ta sha wahala kafin ta Haifi abunda ke Cikinta ga azaban Radadin Naguda wanda aka Fadama cewa acikin Azaban mutuwa ne aka Dibosa kadan..Kuma dukkanku kusan mutuwa tana zafi da azaba Saboda Alokacin da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam zai bar Duniya Sai da ya ce Lalle mutuwa tana da zafi tana azaba da magagi Annabi ma kenan wanda ya kasance Shugaba ne na Hallitun Duniya ya Dandana azaban mutuwa ballata mu bayi da kowa kowan ba..? To acikin wannan azabar ne aka Dandana ma uwa wajen Haihuwa bayan ta haihu kuma ta fara Wahalan shayarwa da Reno walwalun duniya akanta suka kare taki ci taki sha Duk domin ta inganta rayuwarka Sannan ta Jajirce wajen tarbiya bata barci Saboda ganin ta inganta Rayuwarka komai lalace uwa komai nata kan ya"yanta ne,kuma komai zata aikata mai kyau ko mara kyau ne to bazata Fara Duba kanta ba sai ta Duba ya"yanta ku Saki ranku ku Bude zuciyarku..Ku sani Cewa Uwa ta wuce wasa komai ta Zama awannan Duniyan bai kamata ta Fuskanci Tsagwamma da Kyama awajen ya"yan data Haifa bq ..Ko kuwa kowa zai gujesu bai kamata ku ya"yansu ku juya musu baya. ! Mallam ya Karishe Fada yana nazarinsu ganin yadda Gabadaya Jikinsu yayi sanyi ne yasa ya Cigaba da Fadin"Komai kuka samu anan Duniya baku isa ku biya kwayan Zarra na wahalan da iyayanku sukayi akan ku ba..Sannan kada ku manta Kisaar da wani cikin Sahabai yace ya Dauki mahaifiyarsa a saman kafadansa yayi dawafi da ita shin ko ya Biyata wahalansa da tayi akansa..?. Annabi ya shaida masa cewa ko Kwayan Zarra bai biyata ba kun ga kenan Allah ne kadai yasan Alherin Uwa ga abunta ta Haifa..Da wannan Tunasar da nayi muku nake Fatan zaku Hankalrta..Uwani da Marliya da Balaraba sun aikata Laifi mai muni ammh kuma ga wajen Ubangiji abu ne mai Sauki in suka Rokesa zai iya yafe musu sannan muma mu sani afuwa da yafiya abu ne mai kyau tunda muma muna kuskure sannan Allah Gafurin Rahimun ne yana yi mana Gafara a duk sanda muka aikata Laifi yana mana afuwa koda Laifin mu yakai Cikin Duniyar nan ne to meyasa mu bazamu yi musu afuwa ba .? Sai mu barsu su ji da Laifinsu Tsakaninsu da Ubangijinsu,Sannan ku sani aibata su ko gayamusu mummunar kalma bai Dace ba..Ku Sausauuta kalamanku kan iyayanku Domin Fadin mummuna mgana akansu Tamkar ja da hukuncin Allah ne Tunda shi ya Kaddari komai Daya Faru..Daga karshe ina Umartanku Gobe kuje ku Duba iyayanku mata sannan ku Musu kalamai mai Dadi Daga karshe ku yi afuwa ga laifikansu ko Wani Nauyin Zai ragu daga garesu..! Gabadaya Falon baka jin komai sai Shesshekan kukan su ya Zulaihat Hamida ma sai kuka take jikinta Duk yayi sanyi,Saboda tasan ta aikata kuskure ta yi ta yabama mamanmu manganganu Allah ta Tuba dukkansu haka Suke fada aransu sannan Jikinsu Duk yayi sanyi da Nasihan mallam bayan nan ma Hajiya ta Dora da nata kafin su tashi sai da suka Tabbatar ma da mallan cewa komai ya wuce sannan zasu bi Umarninsa.. Haka taron nan ya tashi kowa jiki ba Dadi alamu nasihan mallam ta Shigi Kowa sannan Hatta Aba yaji Nauyin Zuciyarsa ta Ragu yana Tunanin zai iya yafe ma Mamammu har ya Jafar ma yaji aransa ya yafe mata shi da su ya Jawahir aransu sukaji sun yafe ma Mamanmu tun balle ma da su mamata ke Labarin Halin da mamanmu ke Ciki nan da suka ji Tsausayinta bayan sun Furta sun yafe mata. Washegari Mota guda sukayi su ya Zulaihat zuwa Gusai har da Ya Jawahir da ya Jalela sukace zasu ce sai ya Sadiya da Jidda da Sa"adatu suka Dauki Hanyar Dutse sai Ya Nazeem da Nazifa da ya Uzairu sai Umaima suka Dauki Hanyar Tsafe sun yi waya da Shamsu zai samesu achan..! Dukkansu Halin da suka iske iyayan nasu ya Raunana ta su sun kara Tsorata da Duniya Mamanmu nata yafi muni Tana kwance Cikin kashi da Ftsari bata iya mgana abinci ma ko ambata rabi ke shiga Cikinta ba baki ba Ido haka su ya Zeenatu ke kuka kamar ransu zai fita har ta su ya Jawahir sun koka Mamanmu sai dai taji muryansu bata gani sai kuka tana Faman mika hannunta mai Lafiya. Allah Sarki ya Zeenatu da ya Zulfa da ya Jawahir suka Zage suka gyara mamanmu suka Sauya mata kaya ya Jaleela ta bada shawaran su kaita asibitin Basu ji Haushin kowa ba Ganin yadda aka banzarta da mamanmu ka shuka alheri ma ya ka kare ballatana ka shuka Sharrin General Hospital Gusai suka kaita Liktoci nata Fadan an bari Jikinta ya Saki agida Dayake akwai kudi nan da nan aka karbeta aka shiga da ita aka Fara bata Taimakon gaggawa su kuma suna gefe suna ta Faman sharan kwallah Zuwa yammah ta Dan fara Dawowa Hayyacinta sai dai anan asibitin zasu riketa zasu rika yi mata gashin kashi sannan sun saka mata abun Fitsari ta kasanta sannan da Drip wanda zai taimaka ya Dawo mata da Ruwan jikinta Daya zaganye a kwance aranar dai basu samu daman Dawowa ba Sai washegari da Mamammu ta dan Fara mgana kadan kadan tana kuka tana Rokonsu gafara suka Rumgumeta suna kuka suna Fadin sun yafe mata Jaleela ce da Jawahir suka Dawo Gumel aranar saboda washegari zasu tafi  zulfa da Zahra suna chan sai Hamida sai washegari zata koma Zulaihat ma Dagachan ta koma Jigawa sun bar ya Zahra data tambayi Mijinta zatayi sati wajen mamanmu Alla barshi ya Zulaihat zata Dawo ta karbeta sai ita ta koma gida. Achan Tsafe ma abun ba Dadi Haj.Uwani ciwo ya kusa cinyeta ta rame ta lalace kamar ba ita ba su ya Nazeem suma sunyi kuka Halin da suka iske mahaifiyarsu aciki suma basu ji Hauahin kowa ba domin Gaskiyan mallam ne a wannan gabar sai su ya"yanta suma sun yi kokarin kaita asibiti aka Fada musu ko sun je baza"a ga komai ba Yayanta ne yayi musu kwantance wani mai mganin gargajiya anan kauyen Tsafe nan suka kaita ya Dubata yace babu abunda zai mata Ciwonta kaikayi ne ya koma kanta Sai dai Kawai ya bata wani mganin da Zata rika sha kirjinta ya kwanta mata da Tarin dake Sarketa haka suka Dawo da ita gida suka tasata suna faman kuka tana Hawaye tana Nishi wajen rokonsu gafara suka riketa suna Fadin sun yafe mata Nazeem shi yaje yazo da Likita ya Dubata yayi mata alluran barci Saboda ta samu barci sai abakin kakarsu suka san Mallam ya Saketa to damam ai sun san haka zai faru sai dai sun jinjina ma mallam ba Tozarci Cikin Lamarinsa Mutum ne mai Dattako..! Ganin yaranta sun Sauko sun nemeta yasa suma yan"uwanta suka Sauko Daman Hannunka bazai taba Rubewa ka yanke ka yarba Dole itace Dolensu,Nazeem da Uzairu kwana Biyu sukayi suka koma bayan sun bar ma Nazifi kudi sosai Dayake Nazeem ya Fara aiki Shamsu kuma Sai ranar da zasu tafi ya iso nan suka barsa,Umaima dai gata nan ne dai sai ahankali Ita kanta aljanun su taba kwakwalwarta yau lafiya gobe Hauka ne Nazifa ce aka bari tana kula da Hajiyan Uwanin wanda har taji Sauki Data ga ya"yanta sannan Danginta sun mata afuwa..! Chan Dutse ma abun yayi muni Domin sun je sun iske Anty Amarya ta Fita Daga cikin Hayyacinta Domin Tsorata take yi acikin barcinta sai ta rika ganin Yaya tana fito mata Tun abun na karami har ya Girmama bata iya barci Sai abun ya taba kanta gabadaya ta Birkice yan"uwanta sun taimaka mata sun kaita asibiti Shashen mahaukata ana Dubata To Cikin wannan Halin suka isketa ta Rame ta lalace duk ta Firgice kamar ba Marliya yar kwalisa ba alokacin Duka yan"uwanta sun koma Tsausayinta harta Sakina da Anty A"i sun koma suna Tsausaya mata ganin Halin data koma ko da Rana ne ana Zaune sai ta mike tana Firgita da Ihu su ya Jidda suma sun koka matuka haka suka Rumgumeta suna kuka Tsausayin Mahaifiyarsu ya kamasu Nadama suka kamasu na yarda suka ki nemanta na tsawon Lokaci. Sukaji aransu sun yafe mata har Abada anan suka Hadu da Sakina da ta Dawo nan da zama sai sabon kuka Tana Faman fada musu ta gaji da kiran Danmallam bai Dauka ba ta turamai sako ba adadi bai mata Reply ba in ya Saketa ne ya Fadamata sakina duk ta Rame gwanin ban Tsausayi.. Nan Sa"adatu ke fadamata daga wajen sunan Amina suke yara sun ci sunan Aba da Mallam sannan Sarood ma Cikinta har ya fito Sakina sai kuka Nadama da tsoron Rayuwa na kara shiganta har hotunan yaran ta gani Aliya ta Turo mata ita yanzu ta gama ganin rayuwa wani kishi baya gabanta ta sanu ta san makomarta kawai irin yadda Anty Amarya ta koma ya isa mai Hankali ishara..! Sa"adatu ce ta fara komawa gombe Daga baya kuma ya Jidda,Ya Sadiya na nan Dutse ita tunda sunzo ne ita da Mijinta Tana Cigaba da kula da Anty Amarya..! Mallam yaji Dadi da yaran suka kirasa sukace sun je sun Duba iyayan nasu ya Dinga saka musu albarka sanna yaji ba Dadi da labarin halin da suka samu su Marliya abun dai sai Addu"an da Fatan gamawa da Duniya Lafiya..! Hajiya ma dataji Hankalinta sai ya tashi ta tambayi Izini Mallam bai hanata ba ya barta ita da Hajiya Nasara da Anty Hadiza suka tafi Gusai suka Duba Mamanmu a asibiti haka ta rike Hajiya tana kuka,Hajiya na Faman share mata hawaye tana Fadin ta Yafe mata har ta Hajiya Nasara Sai da Jikinta yayi sanyi,Sun iske Zulaihat na asibitin ita ke kula da ita,Basu jima ba suka gaisheta da kayan Dubiyansu Daganan suka Dawo Washegari kuma Tsafe sukaje suka Duba Hajiya Uwani..Hajiya Babba sai da tayi mata kuka tana kuka tana rokonta gafara ta yafe mata da ita da ya"yanta Hajiya tace bakomai Nazifa ta nan bata tafi ba,Sannan Umaima na nan jiki Sai ahankali kawai.. Basu jima ba sallah kawai sukayi suka juya Dagan suka je Dutse suka Duba Amarya Halin da suka ganta sai Allah Amarya hauka Tuburan sun isketa sai da aka Rirriketa,Sadiya ke nan tare da ita da Sakina Hajiya sai da ta Tausaya ma Sakina duk ta Bushe ta gaida Hajiya sai Sharan kwallah take Sai ta bama Hajiya Tsausayi har tayi alkawarin yima Danmallan mgana in suka koma..! Koda suka koma Jikinta Duk a Sanyaye bata samu yima Danmallam mganar ba sun dai yi da Mallan shima ya jinjina ya kada kai yayi musu Fatan Dacewa mganar Sakina kuma yace tana Hannun mijinta abunda ya yanke shine Daidai. Amina kuma ana chan ana ta Jego Yakaka sai da Allah ya sakamata ita ke kula da Amina da yaranta sun koma asibiti an yi ma yaran Shayi na pampers har sun warke,Yaran sun yi Kiba sun yi Bulbul Saboda Amina Nononta mai kyau ne sannan Danmallan kullum sai yazo ya Dubasu Safe da yammah kwana ne yake yi Wajen Sarood Amina bata dai nuna Damuwarta ne ammh fa abun na cin Ranta,Don ma Yakaka na mata Fada sannan ta Dage da kokarin gyara Amina kamar yadda tayi alkawari hakama Anty Hadiza ba"a barta abaya ba Tana kokarin gyara Diyar tata. Hajiya na Shirin samun Danmallam da mganar Sakina sai gashi yazo yana mata mganar Sarood zata koma Madina sun koma makaranta shi zai jira in Amina ta gama wankan jego su tafi Tare Hajiya batace komai ba tace Allah ya Tsare daganan ne tamai mganar Sakina sai ya nuna mata Sakon Datake Turamai na ban hakuri Harda mganar cire mata mahaifa da akayi Hajiya jikinta ya karayin sanyi da Rayuwar nan ta kalli Danmallam cikin wani yanayi tace"Kayi hakuri Danmallam in har baka saketa ba kaje ka Daukota ka maidata gida..Na tabbata ta ga Ishara ga abubuwan da suka faru. ! Danmallam yace"Ban saketa ba Hajiya..Sai dai ina tsoron na Sake Dawo da ita ta batamin zama na..Ta Rikitamin gidana Hajiya. ! Hajiya tace"Bazatayi haka ba..Insha Allahu..! Kai ya kada kafin yace"Shikenan insha Allahu in na gama chukun Chukun Tafiyar Sarood zan je na Taho da ita .! Hajiya tace"Allah ya bada iko..Sannan ina so in kun sun samu Lokaci kai da su Nasir da Jafaru kuje ku Duba su Uwani da Marliya suna cikin wani Hali. Bai yi gaddama ba ya amsa mata Domin sunyi mganar dasu Jafar zasu je su Dubasu ciwo ya kore komai ko don Darajan zaman tare da kuma ya"yan da suka Haifa. Danmallam ba yi gigin Fadama Amina zai Dawo da Sakina ba asatin aka sama ma Sarood Visa ya kawota sukayi sallama da Amina yana zaune yana kallon Amina da mamakin yadda yaji labarci na Fita abakinta Kanar wacce ta zauna a madina bai Taba Sanin ta iya ba ballatana yayi Zaton tana ji.. Ta bama Sarood Atamfa da Su Turare da Sabulai Saboda ta mata kokari Sannan ta Dauki su Aba da suka yi Wayau ta Rumgumesu har Yakaka sai Yabon Sarood take yi,Haka ta Rumgume Amina suka rabu kan sai sun zo tunda Danmallan yace tare zasu Taho da Amina ita Aminar bata ma san mganar ba. Daganan gidan mallan ya kaita tayi musu sallama Hajiya ta bata Turaren Wuta tace ta kaima Mami Sara. Washegari ya kaita kano Jirgin yammah Tabi zuwa Jidda dare yayi mai ya kwana a Hotel da Safe ya Dawo. Lokacin Amina saura kwana Uku tagama wanka Danmallan nata musu Shirin komawa Madina Hajiya tayi mai bakam sai da Amina tayi arba"in yayi mganar Tafiya Hajiya tace sai ta Zaga yan"uwanta ransa ya baci sai dai bai nuna ba gashi yana son kebewa da matarsa an hanasa da gangan Yakaka ke Tsare waje in ya shigo bata so basu gama gyara ba ya bata musu saboda ta Lura ita kanta Aminar Ja'ira ce..! Kwana Biyu da arba"in dinta suka fara yawo ta fara zuwa Hadeja wajen goggo Jumai ta kai musu Yaran ta gani ta saka albarka suka kwana Daya ita da Yakaka Idi yakai su bayan sun Dawo Washegari suka tafi gusau wajen kwanansu Hudu,Har asibiti taje ta Duba Mamanmu Halin Data ganta sai da taji ta manta da komai ta yafe mata Ya Jamela ta rakata Mamanmu na Hawaye Amina ta Dora mata su Aba Ajikinta haka take son tayi mgana ba hali Hannunta mai Lafiya ta saka ta Dafa kansu tana hawaye ya Zeenatu suka samu a wajenta tana kula da ita raba raba suke da junansu. Amina ta yawata Dangin Aba kusfa kusfa Har kwana sai da tayi agidansu Zafira,suka sha Hira Yakaka kuma ta Shige Cikin Dangi kamar yar gida Ta zama yar gidan baba mallam yanzu. Ranar da suka Dawo gidan mallam suka kwana washegari suka tafi Dutse Gabadayansu har ya Danmallam da Su Ya jafar da Hajiya ta koma suka Duba Anty Amarya data koma bata mgana sai kuka duk ta Firgice wani Lokacin in abun ya tashi sai an Daureta Amina da su ya Jafar sun kara jin Tsoron Duniya Sadiya ta nan tare da ita Sannan sunga Sakina Amina tayi mamaki Sakina har da karban su Aba duk ta rame sai Amina taji ta bata Tsausayi basu Dade ba Daga Dutse Tsafe suka wuce chan din ma sai ahankali Hajiya uwani dai ba wani Cigaba tayi ta rokonsu Danmallan da Amina Gafara Allah yasa ita da Bakinma sai dai Ciwo duk yaci Jikinta Nazifa ta koma sai Yan"uwan Hajiya uwani ke kula da ita itama har Su Aba aka Doramata kan jikinta tana kallonsu tana Kuka. Da zasu Dawo suka Dauko Umaima suka Dawo da ita,Umarnin mallam ne Washegari kuma su ya Danmallam suka je gusai suka Duba mamanmu Suma kansu jikinsu yayi sanyi Tana kuka ba baki tana mika musu Hannu Tana neman gafara sukace sun yafe mata Duniya da Lahira sun bama Zeenatu kudade kafin su kamo Hanyar gida suna Hirar yadda Allah ke nuna ishara da izina tun a Duniya. Amina taso taje gidajen yan"uwanta Mata Mallam ya hana yace ta shirya tabi mijinta alokacin Sai Hajiya ta hana tace sai dai yaje ya Dawo ,sai ya tafi da ita Lokacinn yaran sun kara wayau bazai Daukesu tana Danyen Jego ya Hau jirgi da ita. Sannan kuma zatayi Jarabawaarta ta Fita alkawari tayi kuma sai ta cika. Mallam sai yama kasa mgana Daga baya yaso ya nuna ma Hajiya bata isa ba sai dai data mai bayani sai ya gane gwara Amina tatafi da Tarkadunta sannan yaran su kara Wayau shi ya Lallashi Danmallam da bai da tacewa Hajiya ai tagama dashi. Ya samu Amina yana mata magiyan taje tace ma Hajiya ita zata Bisa su tafi Amina tace bazata iya ba sai yayi Fushi batare da sanin kowa ba ya Nema ma kansa Visa shi da Sakina Sai ana Saura kwana Biyu Tafiyarsu yaje ya Daukota Sakina sai da tayi kuka har ta cire rai da auranta da Umar ganin san da suka zo ko fuska bai Sakin mata baHakama yan"uwanta nata jin Dadi,Gidan mallam ya fara kaita Hajiya da mallam suka Taru suka mata Nasiha mallam kanshi yaji Dadi yadda Umar ya zama mai Afuwa Sai alokacin yake shaida musu jibi zasu koma Madina shi da ita Hajiya tasan don Turama Amina Haushi yayi sai bata nuna mai ba kuma bai Fadama Amina zai koma ba Dauke mata kafa yayi ana gobe Tafiyar yazo yaga yaransa ita tana barci sai da Safe Yakaka ke Fadamata,Bata san ya tafi ba Sai da sukayi waya da ya Aisha take Fadamata Ya Danmallam ya tafi da Sakina itama Hajiya ke Fadamata Ranar Amina wuni tayi kuka Yakaka na lallashinra abun fa da Ciwo aiko bai Fadamata komai ba ya Fadamata Zai Dawo da Sakina ammh Duk Sai dai Taji Daga sama itama sai ta Zuciya ta Cigaba da kula da kanta da ya"yanta. An biya mata Jarabawar ta a Unity dinsu da an fara zata fara zuwa sannan Huce Takaicin abunda Danmallam yayi musu Hajiya ta saka Baki mallam ya barta sukaje Abuja suka kwana Biyu ita da Yakaka dagachan har da ya Aisha suka Dumguma sai Zaria wajen Hamida suka kwana Daya gidanta suka kwana Gidan ya Zulfa suna ta murna da ina suka saka da yan"uwansu sun je har kaduna gidan Abida sun je kano gidan ya Jidda Lagos ne da parthercourt yayi nisa basu je ba Amina ta taka yola Wajen Hanne sai gata agidan Aminu Taga Nenne Dangi kuwa sai zuwa ganin Aminan Aminu ake yi yara kam sun sha Dauka shi kanshi Aminun ya kasa sukunu ya siyo wannan ya siyo wanchan,Amina sai yi ma Hanne Tsiya take ganin ta da Ciki. Kwanansu Biyu suka Dawo Gida suka Sauke Gajiya.. Danmallam bai nemeta ba itama kishi da Haushin Abunda yayi mata ta yi biris dashi,Shi ma Yayi zuciya ransa ya baci da abunda tayi mai sannan kuma bayan ya tafi bata nemesa ba abakin Mallam yaji Tafiye Tafiyen da Amina tayi ko izininsa ba"a nema bai Taba Jin Haushi in Hajiya ta yanke Hukunci kan matansa ba sai kan Amina ya Lura tafi son Ma Amina da kowa komai take so shi take yi.. Amina Taurin kanta bai barta ba,Tana nan dashi shiyasa ta nuna ma Danmallam kalanta Har Yakaka taji Haushinsa Sai dai tayi ta lallashin Amima kada ta Damu sai ya Nemesu. Ana cikin haka suka fara WAEC ta Dinka sabbin kayan makaranta ta fara zuwa Ranar datake da paper yakaka take barin ma yaran Agidan mallam in ta Dawo sai ta biyo sai yammah su koma gida Domin yakaka bazata iya Ronon yaran ita kadai ba gasu sun fara girma da kiba suna samun kulawa sosai.. Tana kokarin ya kice Takaicin Danmallan aranta taurin kanta yasa bata ko nemesa ba shima yaki nementa Amina tasan yaushe zai nemeta yanan chan wajen Guzumanyen matansa ita kuma tana nan tana mai renon ya"ya..! Zai gane shayi ruwa ne da Aminene yake zencen..! *Godiyata ta musamman ga iyayena guda biyu da sune silar tsayuwa kan kafafuna da nayi ayau din nan Alhaji Umar Muhammad mailoki da Malama Hadiza Muhammad Ba"are,Baba, mama ina matukar godiya da jajircewan ku akaina Ina godiya da Goyon bayanku ina godiya ga Allah da kuka kasance iyaye nagari a wajenmu Allah ya saka muku da Alheri ya muku Tukwaici da gidan Aljannah Firdausi Ameen Ina matukar son ku Babanmu da Hajiya mama tamu Allah ya kara muku nisan kwana da kwanciyar Hankali Ababen Alhafarinmu..* *Janafty**TFZB2031* *Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488* Shifa Namiji duk inda yake sai ya nuna kansa barin ma in yana da mace fiye da Daya,Sannan su fa abunda muke kallonsa abun kunya a wajensu Daidai ne kuma mai kyau ne sannan in zaki shekara kina kyautatamusu Rana Daya in kika karkace sai ya manta baya ya Dora miki laifin duk Duniya akanki sannan ba kasafai suke Fahintarmu yadda Ubangiji Ya bamu ikon mu fahimcesu ba. To kamar haka ya faru Tsakanin Danmallan da Amina ko yaya ne so yake ya nuna mata ba ita kadai garesa ba in bata bishi ba ai ya tafi da Sakina Sannan yayi hakane domin ya kure Hakurinta yana ganin kamar in ya tafin zata nemesa ta basaa hakuri sai kuma yaga akasin haka ya fahimci Tana da Taurin kai da kafiya domin shima Daurayewa yake da bai nemeta ba shi adole sai ta nemesa ta basa Hakuri sannan su sai su daidaita ammh Ina Sai ya Fahimci Amina tayi nisan da batajin kira. Wajen watansa Biyu da Tafiya ko Flashing bai taba mata ba, itama haka Sai dai ya Kira Hajiya ko mallam yaji Lafiyansu wani Lokacin ma suna gidan in Amina ta tafi Jarabawarta koda wasa bai bari kowa ya Fahimci akwai baraka Tsakaninsa da Amina ba ballatana ita data share batunsa Sai dai Yakaka Datake zaune da ita ta Fahimci Tsakanin ma"aurata basa mgana Dole wani abu na faruwa. Amina sun gama WEAC dinsu Cikin Nasara suna jiran Ta gaba lokaci Daya tana kula da ya"yanta sai kuma alokacin Danmallam ya gaji da Jiran Amina ta Kirasa su sansanta shi ya Sauke Girman ya Kirata taki Dauka Har sai da ya jera mata wajen sati yana Kiranta Tana gani bata taba Dauka ba sai abun ya kara bashi mamaki gashi dai anan hankalinsa yana kwance ne saboda Sakina tayi Laushi Sosai kamar ba ita ba,ga Sarood Daman bata da Hayaniya Cikinta ya shiga watansa na bakwai kusan duka ayyukan Sakina ta Dauketa mata ita ke yi tace Sarood din ta Huta duk yadda yake jin Haushin Sakina Sai da ya Tsausayamata da aka cire mata Mahaifa,duk son ta Haihu Allah ya nuna mata nasa ikon Da Farko bai Sakar mata ba sai daga bayaa shima din ba Sosai ba kadahan kadahan dai kada ya shiga Hakkinta sannan ya Duba Nasihan mallam da Hajiya ammh Daidai da rana Daya bai taba mantawa da Amina ba yana Madina ne ammh gabadaya ransa da Tunaninsa na Nageria wajen Amina da ya"yansa yaso ya jure sai ya kasa ammh Sai gashi yana kiranta bata Daga wayarsa. Daya Dameta sai ta Fara Dagawa ammh yayi sallaman Duniyan nan tayi mai bakan sai da yayi ta jin kananun kukan su Aba na yara tun yana ganin Lamarin nata wasa har ya Fahimci abun nata yayi nisa,Ita kuwa yadda Danmallan ya kunsa mata Bakinciki ya raina mata wayau ne ta Dauki alkwarin sai ya gane bai da wayau sai yasan ya wulakantata Shiyasa ko da yazo yana kiranta Daga baya bata Taba bashi Dama ba Tayi alkwarin sai ta rama Fiye da yadda yayi mata sannan ta koyamai Darasin da har Abada bazai kara gigin mai da ita mara amfani a wajensa ba ! Yakaka Tasan basa mgana da Mijinta ammh bata taba mata mgana ba Sai Ranar Aba na wajenta mallan ne ke wajen Amina tana basa Nono,ta kawo mata shi kenan ta iske waya gefen Amina ta saka ta speaker Muryan Danmallan Tar yana mgana sai magiyan kiran sunan Amina yake yi tayi kamar bata ji ba, Hankalinta ma na kan bama Mallam Nono kamar yana Kiran Dutse..! Fadi yake yi "Noor don Allah ba don Halina ba kiyi mgana..! Amina haba Amina..Haba Amina da Allah fa nake hadaki..Nasan kina jina..! Kiyi mgana saiki fadamin Laifina i Promise you zan baki Hakuri..! Kinji Amaryata..! Amina tayi wani Dariyan rainin Hankali har sai da yaji aranta tace su Amarya an ji jiki ai baka san ni Amarya bace sau na nuna maka matsayina..! Yakaka na bakin kofa baki ta saki Tana Bin Amina da kallo Har Danmallam ya gaji da magiya ya Datse kiran Sannan ta kariso Dakin koda Amina ta ganta bata Damu da taji ko bata ji ba yadda ta yi nisan nan Mallam ko Hajiya ne kadai zasu saukar da ita Su kuma tana da Tabbacin ya Danmallam bazai bari su sani ba..! Mallam ta karba ta miko mata Aba Amina ta karbeshi tana bata rai tace"Ni wlh na fara gajiya yaran nan duk sun gama tsotseni na fara yamushewa..!. Tafada tana wani Tura mai Nonon a baki ruwan nonon ya kawo yaran ya Shake ya fara Tari Yakaka tayi Saurin Ijiye mallam Kan gadon Amina ta karbesa ta Daga sa sama tana shafa Bayansa Cikin Lallashi Lokaci Daya Tana Hararan Amina data kauda kanta Gefe kamar bata ganta ba..! Cikin Ikon Allah aka samu yayi barci ta Lallaba ta kwantar dashi gefen Dan"uwansa sannan ta Dawo kan Amina tana Fadin"Ashe zama na Dake bamai amfani bane Amina..?. Ina ga gwara nayi tafiyata sai ki zauna ki yi yadda kika ga Dama..! Yakaka ta fada Cikin bacin rai ta Juya da Niyyar Tafiya Amina ta mike ta Riko Hannunta tana Fadin"Haba yakaka me kuma ya faru..? Yakaka ta juyo tana Hararanta tace"tambaya ta ma kike me ya faru ko..? Ai kina Sane Mijinki ya kiraki kin Dauka kina ji yana mgana kin yi banza Dashi Sannan kina bama yaro nan Nono kina mai mugunta kina so ki kashe ya"yanki ne..? Kada ma kiyi Tunanin domin kun samu matsala da Babansu kike jin Haushin su yaro ina ruwansa..? Sannan ki Sani yaki dan zamba ne Amina kuma abunda Hakuri bai baka ba Wlh Tsiya bazai taba baka shi ba. ! Kawai sai Amina ta saka kuka ta sanya Tafukan Hannayenta ta rufe Fuskarta dashi tana wani irin kuka mai cin rai Kukan Daya Dade yana Damunta aranta sannan Hade yake da Kishi da Takaicin D'a Namiji. Yakaka sai Tsausayinta ya kamata ta Jawota jikinta ta rumgumeta tana Buga bayanta alamun Lallashi. Amina sai ta Bude muryanta tana kuka sosai har da Shessheka. Yakaka na Dafa bayanta Lokaci Daya Tana Fadin"Kidaina kuka Amina. bari kada yaranki su tashi su ga kina kuka. ! Gefen gado ta zaunar da ita tana Share mata Hawaye Amina ta Dago Tana kallon yakaka Lokaci Daya tace"Yakaka meye laifina da ya Danmallam zai min wannan wulakancin..? Yakaka tace"Me ya faru ne..? Amina tace"Kan mganar komawarmu Madina tare ne Lokacin da zai koma ai kinsan dani zai tafi Daga baya sai Hajiya ta hana tace sai nayi jarabawa Sannan yara sun yi kwari ko..? Yakaka tace"Eh anyi hakan..! Amina na sharan kwallah ta Cigaba da Fadin"To shine fa yazo ya sameni wai sai naje na samu Hajiya nace ni zan Bisa..Ina aka taba yin hakan yakaka..? Tsakanina ga Allah fa Hajiya matsayin uwa take gareni tana da kimar da zata yanke Hukunci kan abunda ya Shafeni nayi shuru da Bakina Saboda bazata taba aikata abunda zai zama Cuta gareni ba..! Yakaka tace"Kwarai Amina..Daga ke har Danmallam din Hajiya ta isa ta Zartar da komai akan abunda ya Shafe ku batare da kun Daga ido kun kalleta ba..! Amina na kuka tace"To shine fa Dalili Saboda nace mai ni bazan iya zuwa nayi ma Hajiya musu ba..Hajiya tamkar uwa take gareni tamin abunda ko Uwata Data Haifeni sai haka Tayaya zata ce ga abunda ya kamata kuma na bata kunya..? Na fadamai bazan iya ba shima yayi hakuri nan da wata Biyar komai ya Daidaita sai in na koma chan ba Jeka ka Dawo shine yayi fushi Yakaka ya tafi ya Dauko Sakina fa ya tafi da ita yakaka Wlh kin ji rantsuwan musulmai bansan ya tafi ba ko sallama bai mim ba ballata nasan da Sakina zai koma in ya gayamin zan Hanasa ne ai matarsa ce Tare na gansu..Ammh sai yaki Darajani ya saka Kafa ya tafi ya manta Dani Ko waya bai tabamin ba sai acikin kwanakin nan duk wani abun na yaran nan ko kayan abinci sai dai su ya Jafar su kawo ni bai taba mgana Dani ba..Sai yanzu ya san Dani..?. Yakaka ina Laifina domin naki Sauraransa don Allah..! Amina ta karishe Fada Cikin kuka Yakaka ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya Umaru bai kyauta ba..Nima da Hajiya ta Fadamin da Sakina ya tafi sai da naji ba Dadi to ganin baki min mganar ba yasa nima ban miki ba..! Amina na jan majina tace"Yakaka ki Duba mganar nan ina Laifina aciki..? Yakaka tace"Baki da Laifi Amina ai Hajiya tana gaba da Umar bama ke ba..Sannan abunda babba ya Hango ai yaro ko Rimi ya hau bai isa ya Hango ba.Sannan ta yaro kyau take bata Karko..kiyi hakuri Ki kara Hakuri ke Macece sannan shi Mijinki ne kuma Shugabaanki ne kina kasan shine biyayya ya zama Dole gareki Ki yi Hakuri ki Sauraresa kiji ko dame yazo..! Amina ta mike cikin Wata murya tace"Yakaka kiyi hakuri bawai bazan Saurari mganarki bane..A"a naji mganarki sai dai nayi Rantsuwan bazan Taba sauraransa ta waya ba..In ya matsu ya tako yazo ya Sameni in yana so na Sauraresa ammh matukar yana Chan wajen wadanan matan nasa bazan taba Sauraransa ba..Ya zauna dasu Tunda su ya Zaba..Zai gane muna mata ya tara..ga inda suke nan suke bata mawa su nuna an musu ba Daidai na rantse ga Allah Sai na nuna mai ni ba abanza nake ba Sannan nafi karfin yamin wannan wulakanci yaci banza. ! Ta karishe Fada tana Huci Yakaka tayi Dariya kafin tace"Na tabbatar miki da zai zo..mu ai ba"a isa a wulakantamu ba..Na goyi bayan ki nuna mai kema kina da Muhimmanci..! Yakaka ta bama Amina goyon baya Sai dai ta mata Fada tabi komai a Sannu sannan ta Sasaauta. Ana cikin wannan Tsukin Ya Ikram ta Haihu Amina sai taji Dadi tunda basu Fara Neco ba Da ita akayi suna ya Zulahait ne kadai tazo sai ya Fatima Sauran duk basu samu zuwa ba,Kuma har alokacin Danmallam bai Daina Kiran Amina tana banza Dashi ba Shi kuna yaki Hakura ita kuma Taurin kanta bazai barta ta Saurareshi ba.. Suna waya dasu Hanne har Hamida yanzu tana da ciki sannan bata Taba Fada musu ga abunda ke faruwa ba tadai Samar dasu sai ta gama Jarabawa zata bi ya Danmallan madina sai Tsiya suke mata wai wa ya ga Amina a madina ita kuma tace sai ma sun ga ta Saje da Larabawa..! Sun Fara Neco dinsu cikin Nasara wani Lokacin da Yakaka suke zuwa makarantar in suna kuka takan fito ta basu Nono malaman makaranta su kansu mamaki suke Amina ce ta zama uwa ta kuma natsu kamar ba ita ba Tsakaninta da kowa sai gaisuwan mutuntawa Kamar ba itace a ka sha Gwagwamarya da ita ba Daman Haka Rayuwa ta gada Danmallam kuma Amina na Neman ta Hauka tashi ko barci ba yayi yasa ya nemi Tahowa sai dai bai sami Dama ba Sai karshen wata Yasa sai ya bari karshen wata in yazo sai su yi ta kare shi da Amina yarinya karama zata chazamai kai da Rigimanta Shi yana ganin Rigiman mata ammh na Amina na musamman ne ita kadai take Fushi Dashi yaji ya Damu yanzu hakama Duk ya kasa sukuni har su Sakina sun Fahimci wani abu na Damunsa ya Dade da Samin Amina nada Jidali Sai dai baisan haka take da Taurinkai ba sai yanzu da ta nuna mai Sai yaji yana raina ta ashe ta wuce nan sannan kuma yana raina matsayinta aransa sai yanzu yasan Amina ta fita zakka ko acikin zuciyarsa komai in da tayi Birgesa take yi. Bai yi shawara da kowa ba ya nemi Visa suma su Sakinan sai ana gobe zai Tashi ya Sanar dasu zai je Nageria Duk da bai Fada musu ba susan wajen Amina zai je basu ji Haushi ba Matarsa ce sannam kuma uwar ya"yansa.! Washegari yabi Mota zuwa Jidda Sannan Daganan jirgin Dare yabi zuwa Abuja,washegari suka sauka Filin Jirgin Nnamadi azikiwe Dake Abuja da yammah sallah kadai ya Tsaya yayi ya hau Motar Haya zuwa Gumel batare da ya kira kowa ba. !motar bata gudu sosai basu isa Gumel ba sai Dare misalin Karfe Tara a masallacin Anguwan ya Tsaya yayi Mangariba da Isha"i sannan ya nufi Gidan Amina get din na Rufe Daman bai Dauki megadi ba ta cikin gida ake Rufewa..wayar Amina ya Kira Duk da yasan bazata Dauka ba Haka ya Dinga jera mata Kira bata Dauka ba. Sai ya Hakura ya koma yana Faman Buga get din Amina na Dakinta kwance ita da ya"yanta har sun gama Hira da yakaka ta nufi Dakinta ita kuma tazo tayi wanka yaran daman yakaka ta musu na yammah ta Gaji yau English sukayi tun Safe sai yammah suka Dawo Har yaran sun gaji suna shan Nono sukaji Ruwan zafi suka fara Barci itama barcin Take ji Tana Fitowa wanka tayi salla ta Saka Rigar Barci masu Taushi Riga da wando ta saka Hula ta kwanta wayar ma na chan gefen gadon kuma tana Silent ne shiyasa ma bata ji ba Sannan har buga gidan bata jiba sai Yakaka ce Data fito Daukan ruwa a Kitchen taji kamar ana Buga gida. Sai ta Tsaya ta kara Saurarawa taji Dai da Gaske ne har zata leka Amina sai kuma ta fasa jikinta ya fara rawa tana Tunanin waye ne da Daddaran nan..? Sai tayi tunanin ko su Jafaru ne..? Yasa ta Dauki Tocila ta fita har Haraban gidan dayake an Dauke wuta tana fitowa taji buga get din anan ne yasa ta karisa jikin kofar tana Fadin waye..? Danmallan Dayaji muryan yakaka sai Hankalinsa ya kwanta Cikin Muryansa mai Sanyi yace"Ni ne Yakaka..!itama ta gane Muryansa Cikin mamaki tace"Danmallan..? Yana mirmishi yace"Nine yakaka..! Da Hanzari ta Cire sakatan kofar get din sai gashi ya bayyana a gabanta Har ya shigo tana cikin mamaki ita ta koma ta kara kulle kofar get din ta Juyi Tana Fadin"Danmallam zuwa ba Sanarwa haka.? Danmallam ya shafa kanshi bai ce komai ba yana Sanye da yadi mai Santsi riga da wando kansa ba Hula sai Sumar kansa data Fara Tahowa yana gaba tana Binsa a baya har Cikin Falon gidan sannan suka gaisa yaga gidan da Duhu Lokaci Daya yace"Yakaka Sun Dauke wuta ne..? Yakaka tace"Da yammah nan suka Dauke ammh nasan zasu dawo dashu..!. Danmallam yace"Yakamata aa Hada muku Solar Duhu ai ba Dadi..! Yakaka tace"Dayake ma suna barin wutar..Sannu da zuwa kasha Hanya...bari na kawo maka ko ruwa na yau bamu yi girki ba Takwara makaranta ta wuni sai da zamu Dawo ne muka biya gidan mallam muka Dauko waina gatanan in zaka ci na Zubi maka... Danmallam yace"Bakomai yakaka wanka ma nake so na farayi..! Yakaka tace"Eh to ya kamata shiga Ciki Aminar na ciki ina ga sun kwanta daga ita har yaran sun gaji..ya amsa mata da Toh ya juya kenan Tace"ahf kaga na manta ya wajen su Sakinar ne da mai juna Biyu..? Fatan dai suna Lafiya..! Danmallam ya juyo yana amsa ma yakaka da Lafiyarsu kalau sannan ya shige Dakin Amina a gaban gadon ya Tsaya kawai yana kallon Amina tana Barcinta Cikin kwanciyar Hankali ta saka Hannunta ta rumgume ya"yanta su Aba yake mamakin girmansu da kibansu wani Annuri na shiga cikin Ransa yana kallon Amina aransa yana auna yarda yar yarinyar nan ta Hanashi Sukuni Zama yayi gefen gadon bayan ya Sauke karamar Jakar Hannunsa yana kokarin Dauke hannun Amina kan yara saboda ya Samu ya Daukesu Caraf ta Rike Hannunsa da Karfi Lokaci Daya tana Bude idonta sai ya Fada kansa suka kura ma juna Ido na wani Lokaci shi na murnan ganinta ne da wani sonta da sha"awarta ita kuma na Bakin ciki da Takaici ne Daya Taimaka wajen Dakushe Zumudinta. Kauda hannunsa tayi ta mike Zaune Fuskarta ba Fara"a tace"Mallam Lafiya..? Girman Idonsa ya kara yana kallinta Cikin mamaki kafin yace"Mallam kuma..? Kawai sai taga ma zai raina mata wayau ya sake kai hannu zai Taba yaran da Sauri ta make hannun nasa ya Dago Cikin mamaki yana kallonta kafin yace"Amina ni kike bige ma Hannu don zan Dauki ya"yana..? Amina tamai wani kallon Tara saura kwata kafin ta sauko Daga kan gadon batayi wata wata ba ta Dauki Aba ta goya ta saka showel din Dake gefe ta Daureshi dashi sannan ta Dauki Mallam a Hannunta ta juya zata bar Dakin da Sauri ya mike yana kiranta, "Amina..! Da farko taso tayi Ficewarta ne sai kuma ta ja ta tsaya bata juyowa ba Da Hanzari ya taka har gabanta ya ja ya Tsaya yana Binta da kallo ita kuma ta Kara Hade rai cikin mamaki yace"Me kika yi haka? Amina tace"Dani da ya"yana bamu da Muhalli a wajenka..saboda banga amfani Daukan su da zakayi ba..! Baki ya saki yana kallonta Duk da yasan za"a rina Daman rigima sai wacce ya gani sai dai bai nuna ya karaya ba ya mika mata hannu yana Fadin"Bani su..Sai muyi mganar Daga baya..! Amina ta kallesa Daga Sama har kasa kafin tace"Wadanan ya"yan Amina ne sai ka bari in Sakina ko Sarood dake da Mutumci a idonka sun haifan maka sai ka Dauka..Bani waje na fice kafin Raina ya kara baci kaga abunda baka Taba gani ba wlh..! Sai mamakinta ya kamasa yadda take kallon Tsabar idonsa tana mai rashin kunya sai ya tsawarta mata yana Fadin"Ban sauke kaina kasa don ki raina ni ba Amina ki shiga Hankalinki..!. Wata Dariyan Rainin Hankali ta sakamar kafin ta raba ta gefensa ta Fice Daga dakin ransa ya baci yabi bayanta yana Fadin"Amina ki dawo nace..Nace ki dawo ko..? Amina ko Sauraransa batayi ba ta Fada Dakin Yakaka shi bai yi zaton Yakaka na Dakin ba ya bi bayanta kawai sai suka Hada ido da yakaka Amina na Tsaye ta Cika kamar ta Fashe Daman Yakaka tasan yadda Amina ta Zuciya Danmallan bazai ji Da Dadi ba. A matsayinta na Babba yasa ta mike Daga zaunen Datake ta mikama Amina Hannu tana Fadin"Bani yaran..Ki koma ku cigaba da Rigimarki kada ku saka yaran da basu san me Duniya ke ciki aciki ba. ! Sanda ta Fadi haka sai Danmallam yaji kunya ya koma da Baya ya fice Daga Dakin Amina sai ta sakama Yakaka kuka ita kuma ta karbi Aba ta kwanto Mallam Dake baya tana Fadin"Ban son Sakarci kin gama kuma Nuna mai Matsayinki ya tako ya Biyo ki sai ki Bata wayonki..? Maza Share hawayenki kada ki sake mai kuka kije ki karbi Lallashin shi ko Banza yasan Darajan ki yanzu..! Amina ta Share Hawayenta sannan ta juya ta Fice Yakaka ta bita da kallo aranta tana Fatan Allah ya Daidaita Tsakanin Ma"auratan..! Amina na komawa Dakin ta iske shi Zaune gefen gado yayi Tagumi yana ganinta ya taso zai riketa ta kauce ta sakamar Jajayen idanuwanta tana Fadin"Bana so..Kada ka tabani..! Sai ya Janye mata Kan gadon ta koma ta kwanta ta Juyamai baya sai kawai ya koma ya zauna ya kara yin Tagumi. Yana mamakin Amina zata Haukatasa ganin kamar ma batasan yana Dakin ba yasa ya Sauko Ya Duka a Gaban gadon inda yake kwance yana Kiran sunanta..! Amina..! Noor..! Kamar yana kiran Dutse haka tayi mai yasan Laifinsa yasa ya fara mgana"Amina kiyi hakuri Ana Asif..Nasan ban kyauta ba da na tafi ban Fada miki ba..Ammh kema ai kinsan kin batamin ko..? Kamar tana jiransa ta juyo Lokaci Daya ta Mike zaune tana Fadin"Au nama bata maka ko..!? Saboda ban je nayi ma Hajiya Rashin kunya nace zan bika ba ko..? To ai da nayi hakan da nagane bani da wayau domin ka nuna min Tabbas ku maza baku da Tabbas haka zan bika kuje ku Hadu da matanka kuna wulakantani Tunda ka nuna musu ban da Daraja..duk lalacewar naka ai naka ne. watarana Hajiyar dai itace Uwata kuma wajenta zan koma bari kaji na Fada maka har yau ban yi Nadaman Kin binka ba..Indai kan Umarnin Hajiya ne da kai ma ta isa Dakai bama niba..! Ta fada tana bayyana bacin ranta Danmallam sai ya kasa mgana yana kallonta Amina taji hawaye sun kawo mata sai tama kasa Cigaba da mganr Danmallam ya Bude baki yana Fadin"Amina n...! Dakata..! Tafada tana Dagamai Hannu kafin ta kallesa Tana fadin"Ba sai kace min komai ba..Ka nuna min matsayina amfanina ya kare Tunda kamin ciki na Haihu ni Aikina kenan shiyasa Domin ka nuna min ni din ba wata bace yasa ka Dauki matarka kuka koma Tare bansani ba.? Saboda ka nuna min in ban bika ba kana da Biyu irina ko..? To ai bakomai yanzu ma sai ka koma wajensu ni ban kira ka ba sannan ban aika maka da katin gayyata ba..! Daga haka ta juya zata kwanta ya riketa da karfi tana so ta kwace jikinta yaki barinta sai ma gadon da ya hau ya Rumgumeta sosai Duk yadda taso ta kwace kanta yaki barinta sai kawai tayi Lamo sai kuka Danmallam ya kamkameta yana Fadin"kiyi Hakuri Amina na Tuba nabi Allah..Na biki..Nasan ban kyauta miki ba ni Haushina da na shirya tafiya Dake kika bi na..Wlh Amina na kasa zama in baki kusa dani ina Bukatarki kusa dani Amina..Noor ina sonki..Wlh ina kaunarki ki yafemin..! Amina ta kara sakarmai kuka Tana Fadin"Baka sona ka nuna ka fi son matanka akaina..! Yana kara riketa cikin jikinsa yace"A"a kada kice haka.. Kema kinsan ina sonki..Tunda na koma bana cikin natsuwata na gama Fushin na Sauko na nemeki baki bani Daman kare kaina ba..Sannan ki duba na kasa zama a madina saboda ke..Hankalina ya tashi ko Barci bana iyawa..! Wannan duk ba so bane. ? Wannan duk bai sa kisan kina da Daraja ba..? Amina na jinsa ta masa banza sai Faman mata rantsuwa yake yi yana Lallashinta Amina na karamai Bore Gajiya yayi ya Hade Bakinta da nashi Duk yadda taso ta hanasa ta kasa Domin itama ai ta gyaru tana Bukatar Mijinta a kusa da ita tun ana Lallashi har aka Sauya salo Danmallan yadda ya Samu Amina yasa sai da ya raina kansa kuka reras ya Dinga rairamata Albarka kuwa tashashi har sai da tagaji Sai da suka samu natsuwa sannan sukayi wanka tare bayan sun fito taje ta Hada masa Tea ta kawo mass Yakaka da yaran Tuni har sun yi barci. Sai janta da Hira yake yi taki Sakarmai Fuska sai dai eh ko A"a shima yasan ai yaga karshensa ina shi ina kara ma Amina Laifi..? Irin wannan Hukunci haka..? Duk Fushinta kafin wayewar gari ta Sauka sannan ya Lallabeta suka koma Ruwa wajen Danko yake mai Amina tasha gyaran da yasa Danmallam ya kara raina kansa da duk abunda yake Takama dashi. Amina sai yanga take mai sai da Safe ne ya Dauki su Aba bayan Yakaka ta musu wanka Allah yasa bata da Paper ranar ammh taso tana dashi tayi Tafiyarta ya karata shi kadai Tunda ya Dawo bai fita ba ko Sallah acikin gida yake yi wayarsa ma kasheta yayi saboda yasan Halin Amina da zafin kishi yanzu ya samu ta Dan Sauko ai sai su Sakina su Ballomai ruwa ya shiga uku..! Yakaka sai ta koma zaman Daki Ta bar ma"auratan su ci Lokacin su Taji Dadi Data ga sun sasanta kansu. Allah ya taimaki Danmallam kwana Hudun da yayi Amina bata da Jarabawa da su yayi amfani ya Gurji Amarcin sa sannan ya samu ya Nuna ma Amina matsayinta duk da ta gamsu bata wani Sakin mai sosai shifa Jidalin Amina shi zai bada Labari Domin shi yaga komai ganin Idonsa..! Ranar kwana Biyar tana da Jarabawan Safe sai da taje tayi ta Dawo bai Fita ba har tace mai ko gidan mallam bazai leka ba saboda ya wanke maata zuciya yasa yace Zuwan nata ne baki ta tabe bata nuna mai tawani ji Dadi ba aranta kuma ai tasan ko yanzu kasuwa tatashi Dan koli yaci Riba..! Sati Dayan da Danmallam yayi komai ya Daidaita Tsakaninsa da Amina Saboda kada ya kara ballo ma kansa ruwa yasa yace in ta gama jarabawar ta shirya tafiyan ta gaya masa sai yasa Jafar ya nema mata Visa sannan ya Sanar da ita ya Sama mata Takardan zama achan na Dindin bata wani Nuna murnanta ba sukayi sallama Ta Abuja ma wannan karon ya kara tashi Sai washegari ya isa jidda Daganan mota ta kaisa garin Madina Ya kirata ya samu ta Daga wayan Daman kafin ya Tafi sai da ya roketa alfarma shi yanzu Lallaba Amina yake tasha shi ya warke..! Yar ya tafi su mallam basu san yazo ba bai gayamusu ba sannan kuma itama Aminar bata gayamusu ba tayi gum da Bakinta itama Yakaka bata Fadama kowa ba..! Danmallam Daya koma sai ya Fara Cukun Cukun sama ma Amina gida sun yi shawara da Aliyu akwai kudi a Hannunsa zai siya mata gidanta ne ya Fasa,karban na cikin makaranta Yasan ko giwan wake yasha bazai Hada Amina zama dasu Sakina ba..! Tafi su kishi da Jidali zaman ma bazai yi Dadi ba,Sannan Aliyu ya bashi goyon bayan ya samata gidanta ita kadai Saboda tana da yara sannan kuma hakan ne ma ya Dace zai fi Samin kwanciyar Hankali da hakan suka Tsaida mgana da Taimakon Abu Kattab ya samu karamin gida nan cikin gari kusa da Masallacin madina..! Bedroom biyu sai Falo sai Kitchen da karamin haraba kafin dai abubuwa su Daidaita,sannan yasa aka gyara gidan ya Zuba abubuwan amfani na Daidai misali Duk da ya Takura bai da kudi sai da Aliyu ya turomai wasu suna waya da Amina ta fadamai sun kusa gama Jarabawa. Ya kira jafar suka yi mgana kan zai nema ma Amina Visa ammh sai ta amince sannan Jafar mamaki ya kamasa su ya Danmallan an shiga Hannun Amina sai Allah..! Ko su Hajiya bai Fadama Amina yake jira ba sun zata fushin da yayi bai Sauko bane suka zubamai do suga iya gudun ruwansu..! Amina sun gama jarabawarsu Cikin Sa"a sai Fatan Nasara asatim Matar Aliyu ta haihu Aliya jin haka yasa Danmallam yace ta shirya taje suna ta kwana Daya batamai musu ba ana Gobe suna Idi yakai su ita da Yakaka da yaran Aliya nata ina ta saka dasu sai Faman nuna ta take yi a matsayin Amarya abokin mijinta Amina dai Sama Sama domin ita bata da yarda ne kan wasu abubuwan sannan bazaka nuna mata ki da Farko ba Sannan ka Dawo ka nuna mata so ba, Daga baya baya ba..! Kuma Aliya sukan yi mgana da Sakina ammh ba kamar baya ba Sai dai Sama sama kawai kowacce tasan matsayin yar"uwanta sakina kuma sai dai a gaisa da Labarin Duniya Tariga ta gama Shiga Taitayinta..! Kwana Daya sukayi suka Dawo Gumel ammh sai da Amina taje ta kara Duba Anty Amarya abun sai addu"a Yanzu takai sai ana kulleta adaki Itama Daga Bakin window ta Lekata Sai da ta mata kwallah Mamanmu ma suna waya da su ya Zeenatu an sallameta tana gida sun ce dai da Sauki ammh ba Baki har yanzu ganin ma dai sai ahankali ita kanta Hajiyar uwar ma Duk ba wani Cigaba sauki sai na Allah itama har yau an kasa gane Cutar Dake Damunta..! Amina batayi gaban kanta ba sai da ta Samu Hajiya ta Fada mata yadda sukayi da danmallam da yazo sai dai Ta Boye Rigimansu Hajiya tayi ta Dariya aranta Ta kuma godema Amina sannan ta godema Allah ko banza yarta nada Daraja Hajiya tace zasu Tattauna da mallam tana mai mganar yace ta shirya tabi mijinta Hajiya tace to..Anty Hadiza tama mgana aka Hada mata kayan gyaran jiki Sannan da Dake Dakem kayan kamshi da sauransu na Tafiya. Sannan Hajiya ta kira Danmallam taji Tsarin Tafiyar na Amina da inda Zata zauna ya fadamata ya siya mata gida Hajiya taji Dadi tana ta sakamai albarka..Sannan ta mai mganar Yakaka yace sai in Amina ta Fara Tahowa sai yaga yarda za'ayi shima yasan zaman Yakaka da Amina taimako ne sosai Danmallam bai saka a fara neman mata Visa ba sai da Amina ta Kirasa da kanta tace ta amince zata taho sannan ya yarda Jafar yazo ya amshi pasport dinta sannan yace ta Hada kayanta saboda jirgin yawo zai yi gaba Dashi..! Jin haka yasa Hajiya ta siya mata Kamshin Girki kala kala da su garin kuni aka shanya mata wake surfaffen da Danyen shinkafa kaya da marasa Nauyi da su fulawa da Sauransu,Sai kayan sawanta dana yara duk da ba Duka ta Diba ba..! Ansamar mata Visa zata su tashi nan da kwana goma ta Abuja,sai Amina ta Cigaba da shirinta ta kira duka yan"uwa awaya tayi musu sallama su Hanne suna ta Fadin zasuyi kewa da kuma Fatan in suka Haihu Allah yasa tazo tace tasan da wuya. ! Ana jibi zasu tashi Suka kulle gidan suka je gidan Baba mallam tayi sallama da Aba da Anty Hadiza anan ma gidan ta kwama itama Yakaka ta musu sallama Domin abuja gidan Ya Aisha zata koma kayan su Tuni suna Madina har Danmallan ya karba. ! Washegari Idi yakaisu Abuja gidan ya Aisha suka kwana washegari karfe Uku na Rana su ya Aisha da mijinta da Yakaka suka Raka Amina Filin jirgi tana Sabe da ya"yanta daya a gabanta ta Sakashi Cikin Abun goyo Daya kuma yana Kafadanta suma yaran sun yi Bul Bul Dasu suna Daga mata Hannu Amina sai da tayi kuka Lokacin da Jirginsu ya Daga Tana Salati Allah yasa akwai wata Farar mata agefenta ita taimaka mata ta saka mata Belt sannan ta rike mata Aba Dake hannunta.. Amina jikinta sai rawa take yi yau gata ajirgi duk bata cikin natsuwarta addu"a kan har ta shiga bayi sai da tayi matar dake gefenta nata mata Dariya saboda ganin yadda take yi sai da Tambayeta ammh bata taba shiga Jirgi ba tace eh tayi Dariya tace kodaga gani to maatar ne ma yasa ta Saki jikinta ba kamar Farko ba suna ta Fira nan tasan sunan matar Surayyah a Nageria take itama aiki yakai mijinta madina suka koma yanzu ma tazo ganin gida ne su yan Abuja ne suna ta Hira da Amina duk da ta Girmeta itama ta Fadamata wajen Mijinta zataje sai santin su Aba take tana jin Dadin ta samu yar"uwa a Nageria..! Sai Dare suka sauka a jidda Danmallam Daman tun tasowarta ya Sani yana Jidda shi da Sarood da Sakina suna jiran Saukan Amina Saboda ya gayamusu sai ko ga Amina ita da Surayyah wacce ke rike da Aba ita kuma mallam na Hannunta .! Sakina baki ta saki tana kallon yadda Amina ta koma Cikin Abaya baka tayi Rolling jan gyale Takalmin kafarta ja ne da Jakarta ga yaranta sai dai kace Masha Allah Danmallam ya nufeta Ya karbi Jakarta lokaci da mallam yana mata maraba har da Rumgomta sannan suka gaisa da Surayyah Amina ta Fadamai irin taimakonta da tayi a jirgi ya mata godiya itama Mijinta yazo Daukanta har suka gaisa da Ya Danmallam sai ma suka ga sun san juna suna Haduwa wajen karatu a masallacin cikin madina suka gaisa cikin girmamawa basu rabu ba sai da Surayya ta karbi Lambar wayar Amina da alkwarin zata zo har gida sannan ta shiga mota suka wuce ita mijinta, Amima kuma ta saki Fuska suka gaisa da su Sarood har da rumguma Sakina kuwa Amina sama sama ta amsa mata ko Hannun Datake bata,ta kauda kanta bata karbi Musabahanta ba,Motar Haya suka shiga zuwa Madina Danmallam na rike da Aba Sarood ta kankame Mallam itama cikinta har yayi girma Sakina na gefe kamar maraniya mamaki ya kamata jin yadda Amina da Sarood ke Hira Cikin Larbaci..! Gidan su Sakina suka fara zuwa Sai da Amina tayi sallah taci abinci sannan suka Dumguma zuwa gidanta ta iske komai an gyara har kayanta da suka Rigata isowa Data tambayi Danmallam yace mata Sakina ce Sarood suka zo suka gyara bata kara mgana ba nan suka barsu ya rakasu suka Hau mota suka koma gidansu Yau dai ga Amina amadina Duk Gajiyan da ta kwaso na Tafiya Sai Da Danmallan ya Famshe sai washegari ya barta ta Fara barcin gajiya sannan shi ya Kira chan Nageria ya Fada musu saukanta .! Saboda ita bai riga ya siya mata Layin nan ba,Amina kamar bugagiya wajen Sati tana Hutawa sannan ta Fara Fita ita da Danmallam gidansu Abu Kattab suka fara zuwa ta wuni mami Sara nada Kirki sannan Amina taga inda Sarood ta Dauko rashin Hayaniya har suka bar gidan Su Aba na hannunta tana wahala dasu Daga Ranar Amina bata zauna ba suna Fita Cikin gari yana nuna mata wurare Amina tayi kuka data ganta a msallacin ma"aiki Bata taba Zaton haka ba,Sannan sun raba kwana yana kwana Biyu gidansu Sakina ita yana mata kwana Daya Sai dai tana Wahalan Renk ita kadai ta Saba yakaka ta Saba mata duk sai ta Sangarce. Ammh yanzu Reno kadai ya isheta sai in yana nan yake tayata Reno Sai Daga baya ne ya siya mata layin chan ta saka suna mgana da yan'uwanta Amina daman kusanta da son yawo ballatana an samu garin Madina tuni tasan ko"ina Ballatana ma da Surraya ta Kirata tazo gidanta ta wuni itama Ranar Danmallam ya kaita ta wuni Amina ta sami Sake tunda Danmallam bai mata shamaki da Fita ba Saboda wani Lokacin baya kusa ko yana cikin makaranta waya kawai Amina take mai tace zataje masallaci Kusan koda yaushe nan take sallar mangariba da Isha"i kafin kace me Fatar ta Goge ta zama kamar bakar Balarabiya atamfa sai tana Gida in zata fita kuma Jallabiya ce Ita da kyawawan yaranta gwanin ban sha"aawa..! Watan Amina Daya da zuwa Madina Sarood ta Haifi Yar mace kyakyawa a gida ta Haihu sai daga baya sukaje asibiti aka Dubata Yarinya kamar tace sak kamar yar larabawa,Amina tana zuwa kullum saboda suna dan dasawa da Sarood Tsakaninta da Sakina kuma sama sama ne ko" ya"yanta sai a bayan idonta take Dauka In Amina na wajen bata bari Har Danmallam yaso yayi mgana Sanin Jidalin Amina yasa bai mata mgana ba..! Ba suna akayi ba an dai yi taro na Murna Har Surayya sai da tazo wacce suka kulle da Amina suka zama kawaye Ballatana da Surayyah ke kaunar Amina Saboda Allah sannan tana son Haihuwa shekara tara da auransu bata taba ko batan wata ba..! Agida Nageria an ta kira ana ma ya Danmallam barka da arziki sannan yarinya taci sunan Hajiya wato Zainab suna kiranta Banu princesss..! Sai da aka tura musu Vidoes da Hotunan Bby kamar yar Labarawa to ai uwarta balarabiya ce..! *********** *BAYAN SHEKARU BIYU..* Bayan shekaru biyu da komawar Amina Madina da zama abubuwan alheri sun faru sosai ciki har da karin Haihuwan da Amina da tayi ta Haifi mai sunan Yaya Hadiza suna kiranta Iman,Sannan Amina ta koma jami"ar Madina tana karatun a bangaran Islamis studies,Sannan Yakaka tana wajen Amina Danmallam ya cika alkawari yayi ma yakaka takardan zama agarin na har abada tazo tana zaune a gidan Amina suna tare. Sannan Sarood ta kara Haihuwan Namiji yaci sunan Kattab suna kiransa da Kattab dinsa..! Sannan Danmallam ya cikama Amina Burinta taje Saudiya ta Sauke Farali Taga ka"aba tayi addu"a sosai addu"o"in da tayi Fatan ta roka ma kanta da iyayenta da mijinta sannan bangaran su Hamida duk sun haihu ita da Hanne wacce ke da wani Cikin ya Aisha ma ta Haihu su ya Zulaihat ma Duk sun Tara zura"a..! Sannan an samu rashi Mamanmu ta amsa kiran Allah Rasuwarta ya girgirza Amina sai da tayi kuka basu je ba ammh ta Kira yan"uwanta ta Musu gaisuwa Hajiya uwa na nan kwance Jinya taki karewa sannan Anty Amarya kam ta Haukace abun dai ba Dadin ji sai ka tsausaya ma ya"yansu saboda Halin da iyayensu ke Ciki bayan tahowarta sun je gida Sau Daya dukkansu shima rasuwar Umaima ce ta kai su Umaima Allah yayi mata rasuwa wahala ta kare ance Mutuwarta ce ta kara girgiza Hajiya uwani Jikinta sai ya rikice..! Sannan bayan Dawowarsu Hajiya da Mallam da Aba da Anty Hadiza da ya Jafar da ya Nasir da Aliyu suka zo Madina Aikin Hajji basu sauka agidan Danmallam ba suka kama Hotel kar su kara musu nauyi sai dai sun je sun ga inda suke Dukkansu har gidan su Sakinar sannan suna Haduwa a masallaci gabadayansu sannan a wannan shekaran ma suma sun isa makka sun kara Sauke Farali. Basu Dawo ta Madina ba Daga makka jidda suka koma suka hau Jirgi suka koma Nageria cikin jin Dadin yadda suka ga Danmallam shi da iyalansa cikin Shiga mai kyau da muhalli. Su Aba kuma suna Tafiya ba inda basa zuwa sun yi wayau suna da Shekara Biyu Cikin na uku ga Imam har tana Rarrafawa..,! ******** *MURFI..* Yau tun safe Amina ta kasa sukuni ita ke da Miji yau,Sai shiga take tana fita,Tana Sanye da riga da wando na pakistan, Amina da ta zama babbar mace yanzu yar kimanin shekaru Ashirin da Daya a duniya. Iman tana rarrafe nan tsakar Falon Yakaka na zaune gefenta Mallam ke hawa bayanta yana Sauka Aba kuma na rike wuyanta Yakaka na fadin"Sai kun karisa ni kenan..! Take fada tana Dariya Iman ta Rarrafo Tana turesu Yakaka tace"Yauwa uwar Hakuri Korar min su..! Amina na jinsu hankalinta baya kansu Alkubus take yi ma Danmallan yau da Miyar agusu saboda da sukaje Gida tazo dashi,kuma ya Kirata yace yana so tayi mai shi haduwarta da Surayyah yasa ta kara kwarancewa wajen girke girke da Sannin siirukan Zama da miji Har gobe tana godema Allah tana godema Hajiya domin sune Sillar Inganta rayuwarta ita da mallam.! Hankalinta bai kwanta ba sai da gama komai ta gyara gidan yana tashin kamshin Turarukan wuta masu kamshi Sannan yakaka tama yaran wanka suka Fito Tsab suna tashin kamshi suma Sannan banda Yakaka bamai ma yaran Hausa Babansu Larabci yake musu ita kuma Amina Tana musu labarci da Turanci Kuma yaran sun iya domin sun fi iya yaran fiye da Hausa sannan suna zuwa wata Tahfiz su Aba tun Safe sai yammah shiyasa harshensu ya tashi da Labarcin sosai. Yakaka ce ma ke fadan meyasa basa musu hausa suna Hausawa suna wani iyayi ita dai Amina sai dai tayi Dariya bata mgana. Iman ce suke bala"in kama da Banu din Sarood itama kamar Sarood din ta Haifeta ga gashi gata kamar yar larabawan wasu ma Dauka suke Sarood din ta Haifesu Amina ta yarda da komai banda Sakin Ragamar mijinta da ya"yanta wajen kishiya abunda ya Faru agidansu ya zame mata izinina..! Bata dai mufin kowa da Sharri..Ammh Sama sama ne gwarama Sarood har lambar wayar juna suna da ita banda Sakina da Amina bata ma son tana Daukan mata yara Ita kuma ga son yara wlh kamar kayi mata kuka akwai ranar dasu Amina sukaje chan gidan Iman ta rarrafa wajenta ta Dauketa Amina ta karbe yarta abun yayi ma Sakina zafi tayi ta kuka har sai da yakaka ta mata Fada Sannan ta Sanar ma da Danmallam ya mata Fada ai Amina data Fara Fushinta sai da Danmallan ya raina kansa ya koma yana Lallashinta abunda ya Faru ya sa ma Amina rashin yarda kuma shi bazai iya Cire mata wannan abun acikin ranta ba sai dai ya tayata da addu"a..! Yau bata shiga mkaranta ba sai gobe take da karatu kuma tasan sai bayan Isha"i zai shigo gidan shiyasa kafin Lokaci ta shirya Cikin Riga da wandonta,Masu roba sun kama jikinta Sosai ta taje gashinta ta Daureshi Tana gayu dashi yaran sunci abinci da yakaka Iman kuma ta bata Nono har tayi barci tana Dakin yakaka su Aba nata Damunta da Hayaniyarsu sai ga ya Danmallam ya Shigo Gidan Amina taje ta Tarosa kamar yadda ta Saba ya rumgumeta yana Kiran sunanta. Noor nayi kewarki..! Itama tace nayi kewarka Hubby..! Danmallam daya kara zama babban mutum kimanin shekarunsa na Haihuwa Arba"in da biyar kenan ya kara haske sannan Hutu da jin Dadi da yanayin zaman garin madina yasa ya koma kamar balarabe sannan uwa uba kulawar matansa garesa musamman Amina sun taimaka wajen bayyanar da kwanciyar hankali ajikinsa da zuciyarsa. Jansa Amina tayi zuwa Ciki bayan ta taimakamai yayi wanka suka fito Falo sannan yaran sukaji muryansa suka Fito suma na mai oyoyo. Ya rumgume su yana Murnan ganinsu Yakaka ta fito suka gaisa sannan ta Janye yaran suka koma ciki Sai Amina ta Fara Cinyar da Mijinta kamar yadda ta Saba yana ci yana kallonta aransa yana saka mata albarka. Suna gamawa ta kwashe komai takai Kitchen sannan suka Tallafi juna zuwa Cikin Bedroom dinsu Suka Zube kan gado Amina ta Haye saman ruwan Cikin ya Danmallam tana sukuwa Dayake ya Cire Jallabiyan jikinsa Dagashi sai karamin wando..! Danmallam na nishi yace"Noor kefa ba yarinya bace yanzu..shekarunki ashirin fa..! Amina tace"Kama ragemin na shiga da Daya..! Dariya ya sakamata yana Shafa Cikinta yace"Ammh har yau kina nan kamar yar sha shidda awajena Menene siirin..? Amina tamai Fari kafin tace"Kai ne Sirrina Hubby..! Kansa ya shafa yana Fadin"A hakan..? Na fa fara Furfusa Noor Shekarata arba"in da biyar fa..? Amina ta kwanta akan jikinsa tana Fadin"ahakan kafi min dan shekara Ashirin da bakwai kai ai Jarumi ne Hubby..! Yana Dariya yana kara shafa Cikinta yana Fadin"Ko nayi ajiya ne..? Da sauri tace"Ba ruwana ni karatu nake yi.! Danmallam ya marairaice yana Fadin"Karatu yafi ki haifamin yara ne Noor..? Kinsan yadda nake jin ki a zuciyata kuwa..? Wlh ina miki son da bansan kwatankwancinsa ba..Abu daya na sani kin FITA ZAKKA Amina..A ko"ina ke Zakka ce..! Amina ta runtse ido Dadi na Ratsata kafin tace"Na sani Hubby..Nima zolayarka nake yi..Bani da wani Buri sai na yi ta Haifa maka ya"ya ina saka ka cikin Farinciki da Annushuwa..! Danmallam ya rumgumota sosai kafin ya Hade Bakinsu waje Daya Amina ta Tallabesa na wani Lokaci kafin su Dago su kalli juna Danmallam yace"Ana Behabbeki Noor..! Itama tana kwanciya saman kirjinsa tace"Ana Behabbika ya Hubby..Behabbeka Kathiran..! Daga haka ya sakata Cikin jikinsa sosai suka lula wata Duniyar da ya Danmallam kadai yasan inda take...! *Tammat Bihammdulillah..Alhamdulillah Alhamdulillah Allah ne abun godiya Salati tare da Tsira su tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wasallam Tsira da gafara da salama su tabbata kan iyalansa gabadaya Nagode ma Allah da yau Laraba 26 ga watan October na sauke Nauyin hakkin ku dake kaina Masha Allahu naji salama da sukuni Ina godiya gareku Dimbin masoyan Labarin Aminene bakina yayi kadan wajen nuna muku godiyata naga soyayya da kauna har ba iyaka ni ban isa nasan Karshenta ba sai Ubangiji ne ya sani Sannan jinjina da godiya ga Masoyana masu son cigaba na da suka iya cire wani abu daga cikin kudinsu suka siya karishen wannan Labarin ina matukar godiya yan group din TFZB2BANDGROUP,Allah ya bar Zumunci Nagode sosai sannan ina Fatan zaku min afuwa Saboda duk Dan Adam Tara yake bai gama cika goma ba Ubangiji Shi kadai ne ya cika Cif dari bisa Dari ni yar Adam ce kuma mai Kuskure ce kila acikin Rubutun nawa akwai inda nayi muku Daidai kila kuma akwai inda na Saba muku to ina mai baku hakuri ku yafemin Ajanci ne na Dan adam sannan ban isa na Rubuta Daidai Dari Bisa Dari ba kila ba haka kuka so Labarin ya tsaya ba sai kuma ya tsaya a hakan to ku sani kuskure irin ne da ajanzi na dan adam,Ina Fatan zaku yi amfani da abunda kuka karanta mai amfani zaku zubar da na banza,Sannan ku tayani rokon Allah ya Hadamu cikin abunda na Rubuta na Lada acikin wannan Tafiya kuskurena da zunuban da na Rubuta kuma Allah ya yafemin su domin bada gangan nayi su ba acikin Rashin Sani ne Daga karshe zan mika sakon godiyata ga yan"uwana Janaf gabadayansu tare da Daukacin BA"ARE'S Family Allah ya bar zumunci Sannan ina mika sakon jinjinta ga Masoyiyata Aisha muhammad Alto da uwata Ummi Khadija Salisu yusuf ina gaisuwar ban girma gareki Besty na Halima yusuf gwarzo dake da Tawaganki gabadaya irin su Suwaiba,Mrbb,Saratu,Da Duka wadanda ban ambata ba ina godiya da karamcinku da kaunar ku gareni ku sani Janafty mai karban masoyanta ne Hannun biyu da kuma Godiya garesu Bissalam nan zan Dakata sai kuma in Allah ya kara Hadamu a Wata Tafiyar in muna Raye da yardan Allah..Nagode..Nagode Nagode Allah ya bar zumunci Ameen..Sannan ku sani duk wacce ta cire kudi ta siya Littafina na adana Lambarta acikin wayata domin ku din masoyan gaskiya ne.* _Kamar yadda na Fada TA FITA ZAKKA zai zama Softy Copy and Hardcopy to Softy copy ya kamallah saura Hardcopy ga masu Bukatarsa Bugaggensa zasu iya min mgana ta wannan Lambar domin jin yadda Tsarin yake 09069067488_ *Janafty*